***Baccin shi ya takarkare ya shaka kamar babu gobe sosai kwakwalwarshi da gangar jikinsa suka huta daidai yanda ake bukata shiyasa ras yatashi da asubah yayi salla sannan yasake dan komawa ya kwanta hankalinsa kwance wani lafiyayyen baccin yasake kwasheshi bashi yasamu farkawa ba sai misalin karfe 8 nasafe lokacin tuni andade da kai Aryan makaranta shi kansa yayi mamakin dalilin da yasa Aryan yau bai shigo dakinsa ba to kodai yazo yana bacci kuma bai samu nasarar tashinsa ba?
Wanka yayi yashirya cikin dark blue din shadda sabuwa fil sannan yafita,kamar koda yaushe table ashirye yake tsaf da kayan karyawa kala kala,
Shi arayuwarsa yana mutukar kaunar Irish amma yanayi yasa baya zama yaci yau dai ya zauna akan table domin karyawa saboda jiya Dr Al'amin yayi masa maganar rashin cin abinci kuma hakan na iya haifar masa da wata matsalar duk da dama matsala kam sai dai ayi fatan sauki amma yana tattare da ita,
Soyayyen dankali da kwai ya dan zuba sannan yahada coffee kamar yadda yasaba,dan ci yayi ba wani mai yawa ba sannan yasha coffee yana shirin tashi umma barira tashigo ganinshi saman table yasata dan murmusawa tana cewa,
"Mu'azzam yau ansamu damar cin abinci?,ai gara ka rinka dan ci ko kayi kumari..."
Murmushin shima yayi yasauka kasa ya gaidata sannan yamike yana fadin,
"Wallahi kuwa umma, yau banga mutumin ba ko laifi nayi shiyasa ba ako lekani ba?"
Dariya umma tayi taja kujera ta zauna,
"Ai Aryan yau akwai abinda ya dauke masa hankali amma yashiga wajen naka bai dai tasheka bane...."
"Nima nayi wannan tunanin nace duk yanda akayi yashiga bedroom din nawa tashina ne dai baiyi ba,umma ni bari inwuce wallahi mutane na can suna jirana a office tun 7"
"To shikenan adawo lafiya, Allah ya tsare yabada sa'a, Allah yadawo dakai lafiya"
"Amin umma nagode,sai nadawo"
Juyawa yayi yabi ta kofar babban falo yafita,duk da bai son maganar Hanan tazama issue acikin al'amuransa dan baida lokacinta amma sai da ta zama,abun ya tsaye masa arai bai san dalili ba,wai shi ta kira da mai budurwar zuciya,kasa yakice maganar yayi acikin ransa haka ya wuni da ita.
***
Amarya Hanan kuwa kowa yaganta yasan acikin bacin rai take domin fuskarta babu walwala sam, ga haushin rashin baccin da bata samu jiyaba saboda bakin cikin abinda minister yayi mata, dama su masu kudin nan wulakanci garesu basa ganin kowa da gashi sai junansu,
Tana ta faman babbata fuska ta shirya ta tafi gidan anty salaha can ta iske mujahid yana jiranta cikin motarshi a kofar gidan. Bude side din mai zaman banza tayi tashiga ta zauna take tafara hawayen da tajima tana dakonsu acikin zuciyarta,
Tagumi mujahid ya rafka yana kallonta shima nasa idanuwan jajur kamar ya hadiyi kunama,shi kansa badan dauriya da juriya irin na maza ba da tuni yajima da fashewa da kukan amma dai yadaure,sunfi mintuna goma zaune shiru babu wanda yayi ko tari acikinsu sai sautin kukanta da yake fita kadan kadan,
"Hanan.... Ki daina kukan nan da kikeyi domin ahalin yanzu shi yafi komai tayar min da hankali... Kiyi shiru kinji,kiyi shiru kiji abinda zan fada miki"
Ahankali take rage sautin kukanta har tasamu nasarar tsayar dashi gaba daya sai ajiyar zuciya da takeyi kadan kadan,
"Kiyi shiru kinji...., Kin dai san ina sonki kuma najima ina son mallakarki a matsayin matata amma yau gashi k'addara na neman rabamu..... Kiyi shiru kar ki sake yimin asarar hawayenki"
Ajiyar zuciya ta ja mai karfi sannan ta kalleshi da idanuwanta wadanda suka yi ja,
"Mujahid ni wallahi idan bada kai ba bazan iya rayuwa ba, wallahi kai nake so...."
"Hanan nima ke nake so amma babu yanda zamuyi,kiyi hakuri ki yiwa iyayenki biyayya idan har na zugaki ko na goya miki baya kan ki bujirewa umarnin iyayenki to ban yimiki adalci ba sannan son da nake yimiki na karya ne,wallahi dagaske nake sonki kuma tsakani da Allah,tunda har k'addara ta raba to ni ina ganin kawai muyi hakuri kuma muyi wa juna addu'a da fatan alkhairi....."
Wani kallo tayi masa mai cike da ma'anoni daban daban kafin daga bisani ta daure fuska cikin fushi da bacin rai tasoma magana,
"Dama ashe son da kake ikirarin kana yimin duk na karya ne kuma na yaudara,idan dagaske kana sona meye naka na fadin haka? Maimakon ka nemo mana mafita shine zaka ce wai inyi hakuri indauki k'addara, mujahid ni zaka yaudara? Ni zaka rainawa hankali? Wannan shine irin soyayyar da kake ikirarin kana yimin? Yayi kyau kuma nagode"
Bata saurari bayaninsa ba ta balle murfin motar tafita ta nufi cikin gidan anty salaha tana sake rushewa da wani sabon kukan mai cin rai.
Ganin shigowar ta tana kuka yasa anty salaha dake wanke wurin da tagama wanke wanke dakatawa da abinda takeyi ta nufi wurinta hankalinta atashe saboda duk zatonta ba kalau ba,
"Hanan.....meya faru kuma? Wanine ya mutu ko hatsari akayi? Ki fada ni abinda yafaru kin barni atsaye cikin zulumi..."
"Anty wai dama haka k'addara take? Idan ta afko maka kowa sai yajuya maka baya? Gaba daya sai ka kasa gane kan kowa? Wai haka k'addara take?"
Ajiyar zuciya anty salaha ta sauke sannan ta nemi wuri ta zauna nan cikin falonta tana kallon Hanan wacce har lokacin bata bar kuka ba,
"Hanan dan Allah ki dauki wannan auren amatsayin hanyar samun aljannar ki,ki dauka cewa wani nauyine iyayenki suka dora miki suke son ki sauke shi,kiyi hakuri dama shi aure mukaddari ne daga Allah,aduk inda mijinka yake sai yazo ya sameka anyi,kuma ke ki godewa Allah ma domin yayi miki gatan da ba kowa yayiwa ba,duk cikin danginmu da kawayenki babu wacce ta taba aurar babban mutum sai ke, minister fa Hanan,kin kuwa san suwa ake kira da minister? Wallahi ba kananan mutane bane....."
"Anty ni babu ruwana da wani arzikinsa ni wallahi mujahid nake so,mujahid shine sa'an aurena shine yaro shine muka jima tare mun san halin juna mun san sirrin juna babu abinda bamu saniba na junanmu....."
Sakar baki anty salaha tayi tana kallonta sannan cikin faduwar gaba tace,
"Hanan kar dai ko wani abu ya taba shiga tsakaninku da yaron nan..?"
Cigaba tayi da kukanta tana jin wayarta ana kiranta taki dagawa tasan bazai wuce mujahid ba,
"Tambayarki nakeyi,wani abu ya taba shiga tsakaninku?"
Girgiza kai tayi alamar a'a sannan taci gaba da kukanta,anty salaha zama tayi taci gaba yimata nasiha tana kwantar mata da hankali.
Dakyar ta daina wannan kukan ta share hawayen ta,wuni guda tayi agidan anty salaha har lokacin mujahid bai bar kiranta ba amma taki dauka yakirata yafi sau 20,sai magriba takoma gida,
Tunda ta koma kuma taci gaba da kuncinta har lokacin bacci yayi nan ta shirya ta kwanta bakin ciki kuma yace muje zuwa,saida taci kukanta ta share sannan ta dauki wayarta,
_Akwai Allah._ shine kadai abinda ta turawa Khalil ta ajiye wayar.
***
Yana kwance saman Rug da laptop agabanshi Aryan na gefenshi yana bacci yaji shigowar text,bai duba ba har saida yagama abinda yake yi sannan yadauki wayar yaduba ganin abinda tace yasashi girgiza kai sannan yasoma tura mata da reply,
_Nifa bawai yimin kikayi ba, kawai zan aureki ne saboda ki rike min yarona amma ni bakida wani abu da zai burgeni ko yaja hankali na atare dake infact ma ni banko san kamanninki ba bare insan ya kike,soo kisan inda yake yimiki ciwo._
Tunda Hanan taga wannan sakon nasa bacin ranta yasake nunkuwa zuciyarta har tafarfasa take yi dan bacin rai,wai ita zai cewa saboda ta rike masa yaro zai aureta,mai neman kuka ne aka jefeshi da kashin awaki nan tasoma kokarin mayar masa da reply dama haushinsa takeji saboda girman kansa da wulakancinsa dan ko sako ne sakonshi baya wuce layi biyu,
_Nima ai ba sonka nakeba kuma da kake maganar zaka aureni saboda in rike maka yaro to ni ba yar aiki bace kuma ba baiwa bace tun wuri ka nemi mai rike maka yaronka._
Wannan karon sakon nata ya bata masa rai fiye da wancan,wai wannan yarinyar dame take tak'ama da har take fada masa maganganu kanta tsaye ko tsoro bata ji kamar wata sa'arshi,dan kawai yace zai aureta sai aka fada mata sonta yake? Shi yanzu aduniya ai babu yarinyar da zata ja hankalinsa har ya sota,tsaki yayi ya ajiye wayar agefe yatashi ya shiga bathroom.................鉁?
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:07 AM - Ummi Tandama: 漏锔? *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of expert & perfect writers)_
*D'AND'ANO....*
*MIJIN MATACCIYA.....*馃挒馃挒
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
*Wattpad-ummishatu*
*10*
***Kamar ya rabu da ita dan har ya shimfida Rug din salla yaji bazai iya kyaleta ba duk da yasan ko tantama baya yi a haihuwar kaji ya haifeta amma gara dai ya nuna mata ita ba kowan kowa bace agareshi. Sai bayan da yagama da ita sannan yaje ya tada kabbarar sallar da yayi haramar yi,
Har lokacin ita kam bata jin ta huce wani irin zafinsa take ji kamar taje har inda yake ta shakeshi saboda yashiga hakkinta da yawa,tana tsaka da sharar hawaye taji shigowar wani sakon wanda ko tantama batayi daga gareshi ne,yanzu kuma Allah ne kadai yasan irin bakar maganar da yaturo mata tunda ta lura shima dan zafin kaine bai da hakuri kamar ba babban mutum ba,
K'wafa tayi sannan cikin bacin rai tace "Ai wallahi idan tsoho baiji kunyar hawa jakiba to kuwa jaki bazai ji kunyar yin totso dashi har ya damfara shi da kasa ba,duk abinda zaka fada am too much ready in baka amsa daidai da maganar ka..."
Text massage din nashi ta bude nan ta soma karantawa afili,
_Ki dauki kanki bakida maraba da mai rainon yarona, sannan ina son infada miki akwai dokoki da sharruda masu yawa wadanda zan kafa miki akan yarona mutukar kika bisu zamu zauna lafiya amma karya doka daya daidai take da rugujewar dukkan dokokin da kika bi,idan har kina son aji kanmu dake to ki gwada saka kafa ki shure daya daga cikin dokokin._
Ranta idan yayi dubu to ya baci saboda wannan sakon da yaturo mata,ai kuwa wallahi sai dai ayi wacce za ayi amma ita ba yar raino bace,
Kiris dama take jira shiyasa ganin wannan sakon nasa yabata damar amayar da abinda ke nukurkusar zuciyarta,
Ko bayan da ta tura masa sakon ji take bata huce ba daga cin mutuncin da yayi mata gashi yana yin komai nasa isa isa iko iko,tasan dan girma kam ya girme mata nesa ba kusa ba to amma Menene zai rinka nuna mata gadara harda wani cewa a yar aiki ya dauketa kamar wata baiwar da yasaka kudi yasiyo a kasuwa zai tsaya yana fadin wai zai kafa mata dokoki da sharruda,
Sakon mujahid ne yashigo mata cikin wayarta adaidai wannan lokaci,ji tayi tausayinsu shida ita duk ya mamaye ilahirin zuciyarta baki daya saboda tasan yanda batayi bacci ba shi dinma gashi can kwance bai samu baccin ba duk kawai dan mutum daya,gaskiya saima Allah ya saka musu ita da mujahid,duk tsawon shekarun da suka dauka suna shirya yanda rayuwarsu zata kasance idan sunyi aure yau kwatsam rana daya wani tsohon banza can mai budurwar zuciya yazo ya rusa musu mafarkin su da suka dade suna yi,
Bude sakon tayi tana kuka kamar wata mai arahar hawaye,
_Dan Allah wify karki cigaba da wannan fushin dani,ki tsaya ki saurare ni,sanin kankine ina mutukar sonki kuma wallahi har na mutu da sonki dankare cikin zuciya ta zan koma ga mahaliccina,dan Allah ki daina fushi dani kijira kiga irin matakin da zan dauka._
Sai lokacin taji ta dan samu nutsuwa jin mujahid yace akwai abinda yake shiryawa, sauke ajiyar zuciya mai nauyin gaske tayi sannan tasoma kiran wayar mujahid din,ada kam ji take bata wani damu dashi ba amma ahalin yanzu tana jin soyayyar sa kamar idan babushi aduniya bazata iya rayuwa ba,ita kanta bata san yaushe wannan soyayyar ta shigeta ba sai yanzu, bata san yaushe tafara son mujahid har haka ba a iya saninta dai sai da aka fara turka turkar auren nan sannan wannan matsananciyar soyayyar tasoma tasiri agareta.
Bugu uku taji ya katse kiran sannan ya kirata,dauka tayi tai kasa da dasasshiyar muryarta wacce ke fita dakyar kamar wacce mura taci karfinta,
"Wify meyasa baki tsaya kinji uzuri na ba,meyasa kika dauki fushi dani har haka? Kema kin san ai ina sonki,u know how much you mean to me and i soo much loves you...."
"To ai dafarko dinne sai naga kamar baka damu da rabamun da za ayi ba shiyasa,naga kamar ni daya keta haukana you didn't make any effort..."
"No wify,ba haka bane,gashi kina gani nakasa bacci...,akwai abinda nake shiryawa, kawai all what i want from you is ki kwantar da hankalinki ki daina damuwa kima daina nuna kwata kwata cewa kina cikin damuwa,nikuma ina can bayan fage ina shirya abinda nake shiryawa..."
Dan murmushi tayi mai dauke da jin dadi sannan cikin sanyin murya tace,
"Ok har naji relief wallahi,gobe insha Allah zan koma Abuja saboda ban dauki excuse ba nataho dama kawai nataho weekend ne fa"
"Babu matsala zamu hadu before kitafi,yanzu ki kwanta kiyi bacci kinga 2 ta kusa"
Sallama sukayi ta katse wayar tana jin farin ciki yana ziyartar birnin zuciyarta,haba har taji sanyi aranta.
***
Kamar kada ya bude sakon nata amma sai ya dake yabude aransa yana fadin "wannan yarinyar bata da kunya sam"
Yana budewa yaga tace,
_Girma dai ya fadi kasa wanwas masu budurwar zuciya._
Tsaki kawai yaja ya kashe wayarsa yayi kwanciyar sa bisa luntsumemen gadonshi mai azabar laushi,shi idan ta barshi da abinda ya dameshi ma ya isheshi bawai sai ta kara masa da tata matsalar ba domin shekara da shekaru acikin matsala da damuwa yake kawai yana daurewa ne amma acan kasan ransa babu kwanciyar hankali ko jin dadi atare dashi,
Bai kara bi ta kanta ba domin aganinsa ai ita ba sa'ar kace nace dinsa bace,nawa take da har zai zauna yana haka da ita? Ai ubanta shi shine abokin yinsa bawai itaba kuma duk ranar da ta kara yunkurin yimasa rashin kunya zai fada mata ubanta shine daidai shi bawai ita ba. Washe gari kamar yadda yasaba 9 yabar gida ya nufi kaduna saboda yana da wani muhimmin taro da zai halarta sannan kuma aranar yana son zuwa gombe zaije ya duba jikin hajiya haka kuma zai ga kayan aurenshi da aka gama hadawa cikin kwanaki kadan,
Wurin lokacin sallar la'asar yabar kaduna suka tasamma gombe wanda basu suka isa garin ba sai bayan magriba,
Saida suka fara yin salla a masallaci sannan yashiga cikin gidan,akwatuna ne gasu nan set biyu a falon hajiya Zaitun hadaddu dasu masu tsada kowanne damfare da kaya dan ko rufuwa ma basayi saboda tsabar cika,
Wuri yasamu ya zauna kansa babu hula suna gaisawa da hajiya wacce ke kishingide saman kujera.
"Mu'azzam dama kayanne nake son kazo ka gani kafin aje akai musu kasan abubuwan nakune duk cikin gaggawa kuka yisu kun debi lokacin auren kadan amma hakanma yayi daidai gara ayi ayi kawai..."
"Hajiya ai Abba ne ya bukaci hakan amma nidai bani nace asa rana kadan hakaba"
"To ai babu aibu hakanma,ni dama kullum fatana inga kayi auren nan zaman ka kai daya babu aure baya min dadi yana damuna wallahi.....ga kayan nan bari yaran nan suzo su bude maka kagani"
"Toh hajiya..."
Tashi tayi tafita zuwa kitchen da kanta ta harhado masa abinci ta kawo masa,tuwon accha miyar busasshiyar kubewa sai dafaffen zogale wanda aka kwadantashi da kuli kuli,dafaffen kwai,tumatur, cucumber da sauran kayan lambu,sai bottle water da kunun aya da zobo,
"Hajiya duk wannan abincin ni daya.."
"Ehh ai gara kaci dan yanzu Allah kadai yasan rabonka da abinci Khalil,shiyasa nake murna da zakayi auren nan domin nasan idan kasamu mai nutsuwa zata kula da abincin ka"
Filet din zogalen da ta kwadanta masa yaja gabansa yafara ci,mazauna gidan sai shigowa akeyi ana gaisheshi kamar yadda aka saba duk ranar da yazo,
Sosai yaci zogalen da yawa ya sha zobo kadan domin shi yana son irin wadannan kayan marmarin kamar kwadon yakuwa,kwadon rama, kwadon zogale da sauransu,
Su mufida ne suka zo suka bubbude masa kayan wanda shi bama wani gani yayi sosai ba kawai dai dan kar hajiya tace bai gani bane,yana jin ankira salla yatashi yafita masallaci dama neman hanyar tashi yake domin yagaji da kallon kayan gashi sunki karewa,
Yana fitowa suka hadu da Zaid wanda shima shigowar shi gidan kenan,musabaha sukayi Zaid ya gaisheshi sannan suka shiga masallaci tare,
Lokacin da yakoma ciki bayan yafito daga salla sallama yayiwa hajiya akan zaije asibiti yaduba sirikin Abban London wanda ke can kwance a asibitin kudi baida lafiya kuma ta can zai wuce Abuja, kudi ya ajiye mata mai yawan gaske saboda hidindimun da ba arasa ba musamman ma yanzu da biki yake dososu.
Jama'a cankam a kofar gida yagani lokacin da yafito dama duk ranar da yazo hakace take faruwa shiyasa saida yayi rabon kudi sannan yawuce suka nufi asibitin standard dake nan cikin garin gombe,acan dinma duk da asibitin kudine sai masu hali ke zuwa saida yabi yayi rabon kudi sannan yabar asibitin,shi haka rayuwarsa take Allah bani inbayar ne da yasamu zai rabar,matasa kuwa suna morewa duk ranar da suka samu ganinsa shiyasa a gombe da mai matasa ake kiransa.
K'arfe 1 na dare yashiga gidansa acikin Abuja,gidan shiru kamar koda yaushe,ji yayi cikinsa yana yimasa wani irin ciwo amma haka ya lallaba yayi wanka yasanya farar jallabiya yafita zuwa dakin Aryan,yana kwance ga tulin tady nan akan gadon kamar hauka Kuma manya manya,kwashe tady din yayi ya matsar masa dashi gefe sannan yayi masa addu'a yafita,
Acikin daren yakira Dr Al'amin saboda dagaske cikinsa ciwo yake yi bada wasa ba kuma yakasa gane musabbabin faruwar hakan..........鉁嶏笍
_Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din._
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:07 AM - Ummi Tandama: 漏锔? *HASKE WRITERS ASSOCIATION.*
_(Home of expert & perfect writers)_
*D'AND'ANO.....*
*MIJIN MATACCIYA.....*馃挒馃挒
*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_
*Wattpad-ummishatu*
*11*
***Zuwan Dr Al'amin yasashi fitowa daga cikin bedroom dinshi zuwa falo inda yake zaune yana jiransa,
Fitowarsa ta sa Dr Al'amin mikewa tsaye dan girmamawa,kan daya daga kujerun dake kawace afalon yasamu guda daya ya zauna,
"Dr ciwon ciki ke damuna tun bayan dawowata gida..."
"Ayya Allah yabada lafiya yallabai amma yau me da me kaci?"
"Da safe tea kadai nasha sai dazu da naje gombe shine naci zogale da tuwo dan kadan...."
"To ai ranka yadade ga inda matsalar take nan,dan abubuwan da kaci dinne suka dan ruda maka cikin naka gashi dama bai saba ba"
"Wallahi duk ya takura min gashi bacci nake son inyi"
"Babu damuwa Allah yakara lafiya bari yanzu inbaka magungunan da zaka sha insha Allah zaka samu bacci..."
Lumshe idanuwanshi yayi ya dan kishingida jikin kujerar yana sauraren Dr Al'amin, sai da yagama hada mishi magungunan sannan yatafi,
Cikin bedroom yakoma bayan tafiyar Dr yayi shirin bacci ta hanyar saka gajeren wando na bacci sannan ya dauko robar ruwa guda daya daga cikin bedside fridge dinshi,zama yayi yasha maganin da Dr yabashisannan ya kwanta yana lumshe idanuwanshi cike da bege da kuma tunanin Ramlat, Allah sarki Ramlat Allah dai yasa tana gidan aljannah,shi kam yasan shima har yakoma ga mahaliccinsa bazai iya mantawa da Ramlat ba kullum da tunanin ta yake kwana yake tashi.
***
Duk da tana cikin damuwa sai dai yau bacin ranta ya ragu da damuwar ta amma fa duk da haka dai sai ahankali yanayin nata,
Karfe 8 nasafe ta kammala shirinta tsaf na komawa Abuja sai kuma satin biki sannan zata dawo,
Dakin Abba taje tayi masa sallama nan yasake dan yimata nasiha sannan yasaka mata albarka ta taso tafito, sallama tayi dasu mamaye yaya shamsu ya rakata tashiga napep zuwa tasha inda zata shiga mota,
Tun tana cikin napep din sukayi waya da mujahid kan cewa zasu hadu a tasha inda zata shiga mota,tana zuwa shima babu jimawa sai gashi ya karaso cikin motarshi,
Karasawa tayi wurinshi ta bude gaban motar ta shiga tana dan harararshi,take away din dake ajiye seat din baya ya dauko ya mika mata saboda dama yasan bata ci abinci ba,
"Good morning my love,gashi kici...."
Dan makale kafada tayi sannan ta kawar da kanta saida ya dan yimata magiya sannan ta yarda ta karba koda ta buda dankali da kwai tagani nan tafara ci mujahid na sake kwantar mata da hankali yana cemata insha Allah akwai matakin da zai dauka yana nan yana shirinsa a boye ita kanta zata sha mamaki, wadannan kalaman nasa ne suka sake sakawa zuciyarta nutsuwa har taci abincin da yakawo mata da yawa dan kadan ta rage yabata ruwa tasha,5k yabata wai tayi kudin mota amma dakyar ta karba daga nan ya rakata mota sukayi sallama dan tuni motarsu ta cika.
Agajiye lis ta isa dan karamin d'akinta dake quarters din malamai,salla kawai tayi ta dafa noodles ta kwanta domin ta huta wanda ba ita ta tashi ba sai la'asar lis wannan dinma wayarsu hajara ce ta tada ita bayan ta dauka suke cemata wai zaman wuri dayane ya ishesu yau suna son su kawo mata ziyara,
Tashi tayi tai wanka ta shirya tsaf cikin doguwar riga ta atamfa sannan ta dora musu abinci kafin su karaso,
Tana shirin sauke sphagettee jalop din da ta dafa mai dauke da kifin gwangwani su hajara suka karaso,sunyi murnar ganin juna sosai saboda rabonsu da haduwa tun ranar clearance na wancan watan dan wannan watanma basu haduba saboda ba rana daya sukayi ba,
Har magriba suna tare amma sam bata sanar dasu cewa za ayi mata aureba. Sha'anin gabanta kawai takeyi dan koda anty salaha ma ta kirata akan maganar gyaran da sauran abubuwan gyara da ake yiwa amarya cewa tayi bata so,anty salaha kuwa tace to ko bata so ita zata yimata inyaso ta zubar,
"Ai kuwa wallahi zan zubar,inma anyi auren kenan" tafada cikin kunkuni,anty salaha na jinta amma dai bata yi magana ba kawai sai ta kashe wayarta,
Agefe guda kuma mujahid naci gaba da bata tabbaccin sai maganar aurenta da minister ta rushe,sai yahana wannan auren indai yana raye to baza ayishi ba sai dai afasa da minister shi ayi dashi wadannan kalaman nasa ne ke sakawa zuciyarta cikakkiyar nutsuwa da farin ciki shiyasa take abinta gaba gadi,kallon kowa take yanda gida suka dauki abin da muhimmanci gashi komai akayi sai yaya shamsu ko anty sun kira sun fada mata dan ko dazu saida anty ta kirata wai za akawo lefenta gobe gasu agida sai aikin nama suke yi amma snacks sun bada kwangila sun biya ayi musu,
Baki ta tabe aranta tace sayi sa gama aure dai ba yinsa za ayiba kamar yadda mujahid ya saba sanar da ita kuma wani sharri na Shaidan ayanzu kusan kullum sai sunyi waya da mujahid fiye da sau biyar sabanin da wanda ada idan ya kirata ma ganin nacinsa take yi amma yanzu ko bai kirata ba ita tana kiransa saboda wani sonshi ne kullum ke kara shigarta.
Kamar yadda anty salaha ke sanar da ita ankawo kaya kuma anyi bajinta anyi rawar gani kowa yaga wannan kayan yasan babu karya ankashe masu gidan rana dan har da kudin dinki dubu dari, kuma gashi biki ya matso dan haka yakamata ta dawo gida tazo ayi abinda yadace,
Kuka ta fara yi ta kira mujahid tana fada masa abinda ke faruwa nan yace mata babu komai tayi yanda suka ce din hakan bazai basu matsala ba, hutu taje ta rubuta har na tsawon sati uku domin bikin saura sati daya da kwanaki biyu,
Kamar wacce idan ta tafi ta tafi kenan haka ta harhada kan kayanta tsaf washe gari ta nufi kano.
Bayan ta koma gida aboye suke haduwa da mujahid suna yin hira yana sake kwantar mata da hankali,tun ranar da ta koma kuma anty salaha tafara kawo mata kayan gyara irin na amare amma bata sha sai dai ta faki ido ta zubar,gaba daya gidan shirin biki akeyi ganga ganga bugu da kari ansake gyare gidansu tsaf yasha fenti yasha gyara na musamman.
***
Duk shirye shiryen da can gida gombe ke faman yi shi kuwa mai gayya mai aiki wato ango yana nan Abuja yana harkokinsa domin ayyuka sun sakoshi gaba bashi can bashi nan kullum cikin yawon ayyuka yake bashi da kwakkwaran lokacin kansa kullum da garin da zaije banda yawon taruka da bude ayyuka da yake halarta,
A gaggauce yake fitowa daga tamfatsetsen dakinshi hannunshi rike da agogon azurfa na Rolex yasha skye blue din shadda mai tsada da kyau,
Yana tafe yana kokarin daura agogon sukayi kicibus da Aryan wanda ke sanye cikin kayan shan iska kasancewar weekend ne babu school,
Rungumeshi ya ida yi sannan ya daga kai yana kallonshi,
"Papa...... Zan bika wurin mommy"
Murmushi yayi ya daga shi sama ya rikeshi yana kissing din face dinshi,
"Good morning my lovely son...., Waye yace maka wurin mommy zanje? Zanje lokoja ne fa,ba gombe zanje ba"
Makale kafada Aryan yayi ya sake rikeshi kamar zaiyi kuka,
"Zan bika Daddy,ni ka kaini wurin mommy,hajiya tace ankusa kawota nan"
Kan dining ya nufa dasu yana murmushi wallahi shi har mantawa yakeyi da wani batun auren nan saboda sam bashine agabansa ba shi sabgogin gabansa ma sun isheshi domin yawa garesu wanda idan har ba mai cikakkiyar lafiya kamarsa ba to mutum bazai iyaba shi dinma da yake da lafiyar ya aka kare stress da zama babu cin abinci kusan koda yaushe cikin kara masa drip ake shiyasa amafi yawan lokuta yafi danganta wannan mukamin nasa da wahala,
Zama yayi saman kujera ya dora Aryan akan glass table din yana kallon shi,
"Aryan kabari inje lokoja indawo zanzo indaukeka muje gombe din but yanzu ka zauna gida kaga anjima kadan lesson teacher dinka zaizo..."
Bata fuska Aryan yayi yasoma murtsuka ido,
Dakyar yasamu ya lallasheshi yakaishi wurin umma barira sannan yafita ta kofar baya.
A lissafinsa ma shi baza ayi bikin nan yana k'asar ba domin zai tafi kasar Spain shida yan wasan kwallon kwando inda za aje akara wasan kuma yana son ya halarta domin yana da muhimmin abinda zai gabatar acan,sai dai yana shakkar sanar da hajiya duk da harka ce ta aiki watakila tayi fada tace dan me zai tafi bayan gashi bikinsa za ayi, addu'ar sa dai Allah yasa kar tayi fadan.
Aranar saida yaje gombe kuma basu tafi da wuriba dan ko lokojan da yaje bai dawo ba sai karfe biyar na yamma,suna zuwa Abuja suka dauki Aryan suka wuce,
Koda sukaje gombe tuni yaga shirye shirye sunyi nisa domin ita hajiya da gaske ta dauki lamarin bada wasa ba shiyasa yayi ta fargabar sanar da ita tafiyar da zaiyi daga karshe dai yaja bakinsa yayi shiru ya zabi yasanar da ita daga baya ta waya,
Sai bayan karfe tara sannan suka baro gombe lokacin tuni Aryan yajima da yin bacci ajikinsa, PA dake gaban mota yayiwa magana,
"Gobe in Allah yakaimu zan aikeka kano,hajiya tace aje akaiwa yarinyar nan kudin menene wai ita da friends dinta...."
"To yallabai Allah yakaimu"
Shiru yayi bai kara cewa komai ba sai tunani fal da yasoma zagaye ilahirin kwanyarsa.
***
Amarya Hanan kam tana cike da damuwa duk da mujahid kullum na sake bata kwarin gwiwar cewa aurenta ba tabbatacce bane dan haka ta kwantar da hankalinta tajira taga abinda zai faru,
Duk da idan taji yafadi haka takan ji ranta yayi sanyi amma hakan baya hanata shiga damuwa da jin faduwar gaba mai tsanani akoda yaushe,
Yau tunda sassafe taji abba na barwa mamaye sallahun wai ta fada mata zatayi bako,ranta bakikkkirin ta wuni tana jiran taga wannan bakon da zaizo tunda tasan dai bai wuce tsohon banzan nan wato angon.
Wurin misalin karfe 2 na rana nura PA yazo,ranta ahade kamar kullum taje bayan sun gaisa yazaro envelope yabata yana cewa,
"Ranki yadade gashi inji yallabai saboda yan hidindimun da zakuyi keda kawayenki, sannan yace idan kuna bukatar wani abu sai ki sanar dashi"
Karba tayi fuska ahade tace,
"Bama bukatar komai kawai dai kafada masa inada bukatar yaje asibiti yayi gwajin cutar HIV,sai yabada result din akawo min...."
Jin abinda tace yabawa nura PA mamaki amma baice komai ba kuma gaskiya bazai iya fadin wannan sakon nata ba dan yayi masa mutukar nauyi,tayaya zaije yafadawa uban gidansa haka? Dan russunawa yayi sannan yace,
"Ai ina ganin ranki yadade gara dai kawai ki fada masa da kanki ko ta waya ne saboda ni din ba lallai nasamu ganinsa ba"
"Ok to ni zan fada masa"
Daga haka tajuya takoma cikin gida tana kunkuni,kudi ne cikin envelope din da yabata har kimanin dubu dari yan dubu dubu sabbi fil ita tama yi mamakin ta yadda akayi kudin yashiga cikin envelope din,
Aranar anty salaha tasa aka fara yimata gyaran jiki wanda Hanan bawai ason ranta bane amma ko ba komai dai za agyara mata fatarta duk da auren bamai yuyuwa bane. Mujahid ke kaita gidan gyaran jikin sannan ya daukota yadawo da ita gida,tayi tayi dashi akan ya sanar da ita plan dinshi amma yaki kullum sai dai yace mata kawai ta zuba ido zata sha kallo,
K'unshi da saloon ma da kin yi tayi sai da mujahid ya lallabata shine ma yakaita kuma yajira ta har ta gama sannan yadawo da ita gida lokacin bikin yarage saura kwana biyu.
Kamar yadda nura PA yace mata ta fada da kanta da kan nata kuwa ta fada dan sako ta turawa gogan tana rubutawa tana tsaki aranta tana cewa,
"Ance shekararsa wurin 9 babu mace wai tunda matarsa ta mutu,to waye yasan abinda yake aikatawa tunda da kudinsa gashi a Abuja yake zaune babu dangin iya bare na baba, watakila ma a hotel yake yin gaba daya weekend dinshi,kai may be ma bazai rasa karuwar da ya ajiye ba za ma ta iya yuyuwa baturiya ce"
Ita kadai taketa wadannan maganganun har ta tura masa text din sannan ta ajiye wayar ta tashi tafita tsakar gida inda take jiyo hayaniyar su anty salaha wadanda keta aiki.
***
Kamar yadda ya shirya sai ana igobe zai tafi k'asar Spain sannan ya sanarwa da hajiya ai kuwa tafara fada tana cewa to kuma auren nasa fa? Taya zasu yarda su bashi aure adaura babu ango?
"Hajiya "yar abokina ce fa yarinyar,kuma wallahi wannan tafiyar dole sai dani za ayita shiyasa"
Jin abinda yace yasa hajiya sakin ajiyar zuciya sannan cikin mamaki ta furta,
"Yarku mu'azzam? 'yarku fa? To ai shikenan"
"Yawwa hajjaju adai yimin addu'a da fatan alkhairin da aka saba"
Addu'a tai tayi masa sannan sukayi sallama,katse wayar yayi yana murmushi acikin ransa kuma yana cewa,
"Ga inda nasarata take, addu'ar hajiya itace take zame min jagora adukkan nasarorin da nake samu cikin rayuwata"
Yana kokarin tashi daga office kuma sakon marar kunyar nan yashigo kamar yadda yake kiranta domin tuni ya rada mata wannan sunan acewarsa bata da kunya ko kadan,dubawa yayi aransa yana cewa yau kuma dame tazo?
_Ina bukatar HIV test result dinka before adaura aure._
Tsaki yaja yamike daga kan kujerarshi yana danna kararrawar dake kan teburinshi alamar yana kiran masinjanshi sannan cikin sanyin murya yana fadin,
"Wannan yarinyar baki da hankali,you are very stupid"
Saida yabar office sannan yatura mata da reply _'Ok'_ shine kadai abinda yatura mata saboda baida lokacinta shi idanma bata saniba to da asuba zai bar k'asar baida lokacin zuwa yayi wani HIV test sai dai kar subashi auren,
Toma wai yarinyar nan me take nufine da sai yayi HIV test? Ko suna tsammanin shi mazinaci ne? Mtswwww tsaki yaja daga nan bai kara bi ta kanta ba har yabar kasar.
Ayau itace ranar da za adaura auren Ibrahim Sulaiman Ibrahim da Sa'adatu mustapha mai jama'a daurin auren da yatara manya manyan yan siyasa da masu rikeda manya manyan mukamai na k'asar Nigeria,
Amarya acike take famm sakamakon wayar mujahid da taketa kira bata samuba duk da kusan kwana sukayi suna waya daren jiya tana ta bashi labarin wulakancin da minister yayi mata wai tace yayi HIV test yaki yayi yace mata kawai ok,ita wallahi bata sonshi ita mujahid take so kuma kowa haushinta yakeji ana cewa ga arziki Allah yakawo mata har gida amma ta runtse ido,arziki na binta tana gudu.
K'arfe 11 na rana ake son adaura auren da tuni ma andaura ana jiran waliyyin ango yakaraso ne wato Alhaji Idris kanwa tsohon gwamnan jihar gombe,dama Abban London tuni yajima da karasowa shida tawagarsa,
Zuwan waliyyin ango yayi daidai da isowar mujahid wanda yacaba ado tamkar shine angon tare da zugar abokansa dake take masa baya..........鉁嶏笍
_Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din._
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:07 AM - Ummi Tandama: 漏锔? *HASKE WRITERS ASSOCIATION.*
_(Home of expert & perfect writers)_
*MIJIN MATACCIYA.....*馃挒馃挒
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
*WATTPAD-UMMISHATU*
_Alhamdulillah wannan shine karshen Dandanon da zan baku (free pages) duk mai bukatar karanta cigaban labarin sai yaturo da 200 ta account din 3112877210 Aisha Ibrahim first bank,sai atura shaidar biya ta wannan number 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta wannan number din,dan neman karin bayani sai a tuntubi marubuciyar kai tsaye ta wannan number din 07044644433._
*13*
***Kwana tayi tana kuka sam bacci baiga idonta ba, abubuwa biyu ke sakata kuka abinda mujahid yayi mata da kuma abinda minister yafada mata dagaske dai raino zataje tayi masa na yaro,kaico,kaiconta inama iyayenta sun san manufar wannan auren nata,inama sun san abinda ke lullube da wallahi tasan ko za ayi kuli kulin kubra dasu bazasu yarda ayi wannan aurenba amma da yake wasu mutanen Allah yahore musu baiwar iya tsara mugunta da cuta shine aka rufi kura da fatar akuya aka yiwa iyayenta ungulu da kan zabo su sunata murna yarsu ta auri babban mutum basu san nan kuwa a matsayin yar raino ta fito ba,ai kuwa minister zaisha mamaki domin zata saka kafafunta duka biyu tayi kolin kolin fatali da wadannan sharrud'an nasa inyaso idan yaji haushi ya korata gida.
Da bacin rai da bakin ciki ta wayi gari wanda ko diss bata samu bacci ba,wanka tayi bayan tayi salla wanda su anty salaha ne suka tilastata bayan sun shigo cikin dakin,humrah masu sanyin kamshi da jan hankali suka shasshafa mata sannan tasaka kaya wadanda suma suka sha turare na daukar hankali,
Doguwar riga zuwa gwiwa tasaka da zaninta duka na atamfa orange and blue colour bayan sun gama shiryata tasaka su sarka da dan kunne akayi knocking a kofa aka shigo yanmata ne guda uku wato mufida da Sarah da Zarah kowaccensu dauke da madaidaitan warmers masu kyau iri daya,kasa kasa take kallon yanmatan wadanda daga gani kasan jin dadi da hutu sun jima da samun muhallin zama a jukkunansu,
Kayan breakfast ne suka kawo musu sannan suka gaggaishesu sai kallonta suke suna dan magana kasa kasa shiyasa taji duk sun isheta domin ta tsani kallo,kamar sun san abinda ke cikin ranta suka tashi suka fita.
Abincin karyawa ne na gani a na fada domin farfesun koda ne da soyayyar agada sai wainar kwai fal sannan ga wainar shinkafa itama da zuma ga kuma kayan tea da ruwan zafi agefe abinci dai kaca kaca gashi nan sai wanda ka zaba ita kam ruwan tea din kadai ta iya sha sai da anty salaha suka bude mata wuta sannan tasamu ta danci farfesun kuma suka tilasta mata saida tasha romon tass,sake gyara mata jikinta sukayi suka nada mata lafaya suka fita zuwa dakin hajiya Zaitun,
Ita ma taci ado Sosai cikin wani leshi, kama Hanan tayi ta rungume tana dan shafa bayanta ahankali take yimata magana,
"Barka da zuwa cikinmu Sa'adatu,lale marhabun dake,kinyi dace da miji mai biyayya ga iyayensa bawai dan nina haifeshi ba a'a sai dan kawai halinsa ne,ko kai ka haifi mutum halinsa shi zaka fada,ki zauna lafiya da mijinki kiyi masa biyayya duk abinda yayi miki wanda ba daidai ba ki sanar dani,tsawon shekaru kusan bakwai kenan rabonshi da mace tunda matarsa ta mutu wurin haihuwar yaronsa shikenan bai kara aure ba nayi nayi amma baiyi ba sai yanzu bagatatan yazo min da maganar ki kuma gashi da yake Allah ya kulla anyi, Allah yayi miki albarka, Allah yayi miki albarka....." Wadannan sune kalaman mahaifiyar sa wanda harda kwalla take yi lokacin da take fada mata domin duk da fuskarta arufe take amma tana fuskantar komai kuma tana jin lokacin da matar Yakumbo ke cewa,
"Haba hajiya kema kukan zakiyi Khalil din da ba shine auta ba......."
Sun dan jima awurin hajiya sannan akace sufita domin tafiya Abuja,kamar jiya yauma zaid ke jan motar da take ciki tun daga garin gombe har Abuja wanda tafiyar awanni kadance ta kaisu,tana jin anyi parking gabanta ya tsinke ya fadi,
Da addu'a abakinta ta taka tashiga da k'afar dama wadda iyaye keta nanata mata wadanda ke tare da ita, Masha Allah, Masha Allah,shine abinda kunnuwanta keta jiye mata lokacin da suka shiga gidan gashi babu laifi tafiya taki karewa abisa dukkan alamu gidan da zurfi dan harda su hawa bene taji anyi daga bisani aka danyi yar tafiya taji anbude wani daki sun shiga wanda sanyi da kamshi ya cikashi kai gaba daya cikin gidanma sanyi da kamshi ne acikinsa dan tunda suka shigo taji yana shigarta,abakin wani luntsumemen gado taji an zaunar da ita kan wata hadaddiyar katifa mai sifrin tamkar kahau irin gadon nan na da irin na karfen nan wanda zakaji yana tsalle dakai,
Har lokacin bata bude fuskarta ba tana jin lokacin da su anty badi'a suka shigo anty badi'a tazo kusa da ita ta zauna cikin rada take cemata,
"Wallahi yarinya kin more da gida, aljannar duniya,kinga gidanki kuwa Hanan? Wallahi girman wajen nan ya isa mata hudu su zauna basu takura ba, Allah yasa rabonki ne yasa gidan zamanki ne har abada, Allah yasa mutuwa ce kadai zata raba..... Ai tun dazu muna kasa muna ta santin wannan aljannar duniyar, Masha Allah wallahi gidanki ko a London iyakaci kenan sannan gaki ga Villa...."
Ai Hanan ji tayi kamar ta dora hannu aka saboda takaicin wadannan addu'o'in na anty badi'a danme zata rinka yimata addu'ar kare rayuwarta a wannan gidan da yafi kurkuku tsanani agareta babu kunya bare tsoron Allah aranta ta rinka cewa, "Ba amin ba"
Tana tukunkune atakure har saida dakin yarage daga ita sai su anty salaha sannan ta bude fuskarta,tamkar amafarki tajita lokacin da tayi ido hudu da dakin da ake kira da mallakinta bata san lokacin da ta furta,
"Masha Allah"
Ba kadan ba taga dakin yayi bala'in haduwa gashi tangamemen gaske duk kayan ciki dark purple ne masu dan sirki sirkin haske ko ina sai sheki yake magana ta gaskiya bata taba cin karo da furnitures makamantan wadannan ba wurin kyau da haduwa, sunkuyar da kanta tayi saboda bata son su gane dakin take kallo tabari har sai sun tafi sai ta bude idonta ta kashe kwarkwatar idonta dakyau gida kamar akasar turai?.
Saida suka ci abinci sukayi sallar azahar sannan yan kawo amarya aka fara haramar tafiya nanfa Hanan tace bata san zance ba domin zama tayi ta rinka rusar kuka ahaka suka tafi suka barta, kwanciya tayi saman gadonta tana cigaba da kukanta cike da kunar rai har tayi tagaji tunda babu mai rarrashinta dan abisa dukkan alamu ma ita kadai ce agidan sai ko ma'aikata domin bata ji motsin ko kare ba duk da cewa ma gidan yana da girma da fadi ko da ace akwai wani ciki ba lallai kasani ba indai bawai yashigo side din da kake bane,ita kam ko tantama batayi tasan ita kadaice cikin wannan katon gidan domin dazu lokacin da suna kan hanya tana ji zaid yana waya da wani wanda bata san ko wanene ba yana cewa wai su umma barira da Aryan na tsohon gida ita amarya yanzu sabon gida za akaita amma suma su umma barira din nanda anjima ko gobe za akawo su sabon gida basu karasa parking din kayan su bane. Saida tayi kukanta ta gaji dan kanta sannan ta tashi da niyyar yin alwala domin la'asar ta kusa zaman dirshan tayi tana bin d'akinta da kallo wanda ya amsa sunan aljannar duniya, mai karatu Hanan bata san ta inda yadace tafara kwatanta muku haduwar da d'akin baccinta yayi ba domin komai yajine ba karya komai yadace da muhallin da aka ajiyeshi tun daga kan labulayenta gadonta wardrobe dinta,da komai dake cikin dakin sannan daga can dan gaba kadan da gadonta wasu hadaddun kujeru ne guda uku suma dark purple an dan yi circle dasu an ajiye glass table a center sai wurin yabada ma'ana tamkar dai aturai sannan ga wurin sallarta nan an tanada ga katuwar tv ta bango da dan karamin fridge kawai dai komai yaji ne fa,sauka tayi ahankali da niyyar zuwa toilet nan ta tsaya yin wani kallon domin shi kansa bathroom din nata da glasses aka zagaye shi marassa duhu sai dai ba lallai ne ka iya hango mutum ba idan yana ciki amma ta yuyu zaka iya ganoshi tsaff,kamar mai shirin daukar kwai haka takama kofar bathroom din ta tura ahankali tashiga,bandaki kamar wani filin shakatawa? Ta fadi hakan aranta domin shima an kawatashi an shiryashi sannan anzuba daula acikinsa kamar ba wurin wanka da fitsari ba,irin haduwar da bathroom dinnan yayi fadarshi bata bakine yahadu fiye da duk yanda zaka kissimashi cikin ranka,ita dai gidansu ba hamshakan masu kudi bane shiyasa sai da tabi komai asannu gudun kada tayi barna domin wasu abubuwan ma yaune tafara ganinsu haka dai ta lallaba tayi alwalar tafito tazo ta bude wardrobe ta ciro hijabi daga cikin jakunkunanta wanda su anty salaha suka saka mata cikin wardrobe dinta dazu.
Rasa wacce irin addu'ar da zatayi tayi saboda ita dai bata son zaman gidan nan ko kadan bare tayi addu'ar Allah ya tabbatar da ita agidan,daga karshe dai sai kawai ta roki Allah da ya zaba mata abinda yafi alkhairi a rayuwarta,
Saman gado taje ta hau ta kwanta domin bata san abinda zatayi ba ayanzu juyi kawai tashiga yi tana ta tunanin rayuwa wai yau itace acikin wannan gidan wanda ko acikin mafarkin ta bata taba mafarko gida makamancinsa ba a tarihin rayuwarta,duk da gidan ya cancanci akirashi da aljannar duniya ita kam bata yiwa kanta fatan tabbata acikinsa, nasihar Abban ta ce ta fado mata inda yake cewa,
"Hanan ki yiwa mijinki biyayya kibishi sau da k'afa ban yadda kiyi ko musu dashi ba sannan ban amince miki kiyi koda yaji ba bare ki nemi saki a hannunshi,kada naji kuma kada nagani,duk ranar da kika zo gidan nan da sunan yaji to ba zamu kwashe dakyau ba,mijinki shine aljannarki domin tana karkashin kafarsa ne dan haka kiyi masa biyayya iya iyawarki daidai gwargwadon yanda zaki iya..... Allah yayi miki albarka"
Wasu tagwayen hawaye ne suka zubo mata sakamakon tuno wannan nasihar ta abbanta da tayi,to wai ita yanzu ta ina yadace tafara ne? Wanne irin zama zatayi a wannan gida? Wanne irin zama zatayi da abokin mahaifinta? Wacce irin rayuwa zatayi da dansa da sauran jama'ar da ke rayuwa cikin wannan gida? Menene makomar rayuwarta? Wadanne irin kalubale ke jiran rayuwarta saboda auren babban mutum da tayi shin zai dauke mata dukkanin bukatunta ko kuwa zai yi watsi da lammuranta? Wadannan tambayoyin sune keta circulating acikin kwakwalwarta wanda ta gagara bawa kanta amsa.....................鉁嶏笍
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:07 AM - Ummi Tandama: 漏锔? *HASKE WRITERS ASSOCIATION.*
_(Home of expert & perfect writers)_
*D'AND'ANO......*
*MIJIN MATACCIYA.....*馃挒馃挒
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
*WATTPAD-UMMISHATU*
*12*
***Wata zazzakar guda ta jiyo babu k'akk'autawa wata mata wacce Allah yabaiwa baiwar hanci ta dage sai rangada ta take yi kamar anyi mata bishara da kujerar hajji ko ta umarah kafin daga bisani tafara jiyo maroka suna faman yin kirari,tsam ta dakata daga kokarin saka sarkar da take yi awuyanta,
"Ayyiriyiriyiriiiiiiiiiiiii....... Aure ya kullu,amarya Sa'adatu rai yakaiki..... Allah yasa gidan zamanki ne..... Ayyiririiiiiiiii" Matar da keta faman rangada guda agufi agufi tafada tana sake bude makogaro wurin rero wata gudar, sake saurarawa tayi dakyau har tana mika kunne domin jiyo abinda marokan nan ke fadi,
" _Sa'adatu sa'ar mata, Sa'adatu mai sa'a babu shakka kin tako sa'a da auren baya goya marayu dan mulki kuma jinin sarauta, yagaji arziki da sarauta dan na gada ba dan na koya ba, wato Alhaji Ibrahim Khalil ga kudi ga mulki... Ina amarya Sa'adatu,kifito kibani kyautar mota da kujerar hajji amarya bakya laifi ko kin kashe dan masu gida...._"
Ai bata iya karasa jin karshen kirarin da marokan nan ke zuba mata ba jikinta yahau rawa wanda har kyakkyawar sarkar hannunta na neman sulmiyewa,anty badi'a yar gidan yayar mamaye itace tayi gaggawar riketa sannan ta rike sarkar tasoma kokarin saka mata,
Ita anty badi'a duk azatonta rudewar Hanan akan an daura auren ne bata san ita jin sunan wanda aka daura auren dashine ya rudata ba saboda taji ana ambaton wani daban sabanin mujahid. Hawaye ne suka shiga wanke mata fuska babu k'akk'autawa kamar anballe bakin fanfo,
Jin shigowar anty salaha yasata juyawa tana tambayar ta domin zuciyarta na fada mata kamar fa kunnenta karya yayi mata bai jiyo mata daidai ba,
"Anty dawa aka daura auren? Da mujahid?"
Wani kallo anty salaha ta watsa mata sannan ta fusge hannunta tana harararta,
"Waye wani mujahid? Dama ya kawo miki kayan aure ne? Mtswww" Daga haka anty salaha ta dauki abinda zata dauka tayi waje tabarsu ita da anty badi'a wacce ke faman rarrashinta amma ina hawayen dake kwaranya daga idanuwanta sun kasa tsayawa, tambayar kanta take faman yi to ina plan din da mujahid keta ikirarin ya hada? To kodai plan din baiyi aiki ba? Inama zata farka taga acikin mafarki take,inama inama....!!! Wani kukan ta sake fashewa dashi ta fada saman gado ahaka aka aiko kiranta,tashi tayi tafita tana sanye da wani dandatsetsen leshi baki mai adon pink ajiki yasha manyan stones wadanda suka kara haskashi kuma suka fito da tsadarsa fili,pink din takalmi ne akafarta wacce tasha lallen amare ja da baki,kai gaskiya ba dan wannan yanayin da take ciki ba da ita kanta sai ta yabawa kanta da kanta saboda tsabar haduwar da tayi. Su Abba tasamu zaune da kaninsa baba mahe nan suka zaunarta suka yimata nasiha akan tayiwa mijinta biyayya sannan kuma ga sadakinta nan har naira dubu dari,da wani kukan ta sake fita ai kuwa cincirindon matan dake tsakar gidan suka hau guda suna fadin,
"Ke kikace kina so da bakice kina so ba da ba abaki shi ba...."
Ko takansu bata bi ba tawuce daki tana matsar kwalla ita yanzu gaba daya tarasa me zata kira wannan abun,wai mujahid meya faru ne da har plan dinsa yarushe? Tasan inbanda mujahid din babu wanda zai iya bata amsar wannan tambayar tata gashi ita yanzu ma kwata kwata bata san inda wayarta take ba,
Zama tayi gefen gado taci gaba da kukanta,kowa yazaci kukan rabuwa da gida take yi amma ita kadai tasan dalilin kukanta,dakyar anty badi'a takawo mata maltina da madara tasata agaba tasha saboda yau bata ci abinci ba. Bayan misalin karfe 3 aka gama shirya amarya tsaff inda za atafi garin gombe da ita ta can kuma za awuce da ita gidan mijinta dake garin Abuja,
Zaid ne ke jan tsadaddiyar motar da amaryar ke ciki ita da iyaye wadanda zasu rakata sai faman sharbar kuka take ta cikin mayafin dake lullube da ita,
Daf da magriba suka shiga garin gombe ita dai bata iya gane komai amma tana jiyo hayaniyar jama'a wacce daga ji tasan suna da yawa sannan tana ta jiyo kade kade da raye raye gamida bushe bushe, fuskarta a rufe aka shiga da ita sashen uwar ango wato hajiya Zaitun wacce ke hakimce afalo ita da wasu hamshakan mata wadanda akalla zasu kai su biyar zuwa shida,biyu daga ciki matan Abban London ne daya kuma matar Alhaji Idris kanwa ce sai yakumbo da anty saudat banda wasu matan da yanmata dake biye dasu sai faman daukarsu ake yi awaya,
Gaban hajiya Zaitun aka kaita ta zauna nan hajiya Zaitun din ta kama hannayenta wadanda suka kawatu da lalle ta rike tana saka mata albarka tare da addu'ar samun zaman lafiya mai dorewa agidan aurenta, daga bisani kuma aka gudanar da addu'o'i bayan anshafa hajiya Zaitun tace akai amarya ta huta taci abinci tayi wanka bayan tayi salla domin ta sha hanya ta gaji tana bukatar hutu inyaso gobe sai atafi da ita dakinta. Hakan akayi yakumbo ta kamata zuwa wani daki marar tarukuce ciki domin iya wani kantamemen gado ne kadai aciki sai mirrior da bedside drawers shikenan sai carpet dake shimfide gaban gadon amma fa ba karya dakin ya hadu yayi kyau fiye da hasashen mai hasashe,
Sai bayan da yakumbo tafita sannan anty salaha da anty badi'a suka shigo dauke da dan madaidaicin akwatin kayanta,
Salla ta farayi sannan suka zuba mata abinci shinkafa da chicken pepe soup,ita dai dakyar ta daure ta dan ci abincin wannan dinma saboda tana gudun fadan anty salaha ne domin tasan matsawar bata ci ba to sai anyi fadan da aka saba,
Tana jinsu ita da anty badi'a sai faman yaba karamci da dattako irin na surukan nata suke yi suna cewa tayi dace tayi sa'a Allah ya zabeta yabata abinda ba kowacce mace ce zata samuba wato miji na kwarai da danginsa na arziki masu sonta da mutuntata,ita dai jinsu kawai take yi bata cewa komai amma can kasan ranta wani irin tafarfasa zuciyarta keyi alla alla take taji daga mujahid tana son jin abinda yafaru har hakan ta kasance. Sai bayan da tayi wanka ta shirya cikin jar night gown mai santsi tasha humra da turare kai kace angon yana nan wannan kuma duk aikin anty badi'a ne wai ko ango baya nan ai gara ta kasance cikin kamshi,
Saman gado ta haye zata kwanta anty badi'a ta kalleta,
"Ke Hanan bafa kwanciya zakiyi ba kinaji, lecture zamu yimiki yanzun nan dan gobe iyanzu kina dakin miji..."
"Kibarta badi'a,saura kije ki samu wuri ki yita kwasar bacci babu kula da miji,mijinki dai kinga ba yaro bane da hankalinsa kuma saboda tsabar son da yake yiwa matarsa ance tunda ta rasu baiyi aure ba anbishi anyi anyi dashi akan yayi aure amma yaki dan haka idan har kikaje kika tsaya kallon ruwa wallahi kwado ne zaiyi miki kafa tunda shikam already da kudinsa kara aure ba wuya zaiyi masa ba..."
"Kwarai kuwa maganar salaha na kan hanya,ki zauna ki nutsu ki koyi dabaru da salo na rikon miji yarinya wallahi aure babu abinda yafishi dadi mutukar akayi dace da abokin zama na gari,maza na son macen da ta iya kula dasu wacce zata rungumesu ta rarrashesu kamar baby,suna son mai kunya mai girmama su da mutuntasu amma fa bance kije kiyi masa dinkim a master bedroom ba,acan zagewa zakiyi kifito a yar bariki sak kima fishi rashin ta ido kin gane? Yanzu dama nasan baza ki iya hakanba saboda rashin sabo da kuma kunya amma ahankali ahankali kina sakin jiki dashi kina sake samun wayewa aharkar dan wasu abubuwan ma shi zai koya miki to daga nan fa kema sai kifara naki salon tunda anriga da anzama daya babu kuma sauran kunya..... Inbaki wasu sirrika akan maza? To bude kunnenki dakyau kiji yarinya"
Nanfa anty badi'a tafara farfada mata abubuwan da yadace ta rinka yimasa wadanda maza keso ita wallahi duk sunsa kunya ta kamata gashi ma ita hankalinta ba awurinsu yakeba kadan kadan dai take jinsu amma gaba daya tunaninta yatafi ga mujahid su kam babu maganar kunya bare boye boye sai fada mata abubuwan da yadace tasani suke yi musamman ma anty badi'a wacce ta takarkare tana yimata dalla dalla yadda yadace ta kula da shinfidar mijinta da yadda yadace ta sarrafashi a wannan lokacin daga karshe ta rufe da yimata bayanin irin kulawar da zata bashi a lokacin da take yin period domin mata da yawa na daukar last position a wannan yanayin,lumshe idanuwanta ita dai tayi wani bayanin tana jinsa yayinda wani kuma bata ji,
"Yar kare kike wani sissinne kai kina rufe idanuwa nan da yan wasu kwanaki zamuji ki difff da zarar kin shige gidan miji...." Inji anty badi'a wacce ta dan daki kafadarta kadan,
"Ke kyale asara,kuma irinsu sunfi zakalkalewa ba" Anty salaha tafada tana sake kishingida,ita dai bakam tayi tana jinsu sunata sake karawa maganganun nasu haske ta yadda zata fahimta sosai ahaka akayi knocking anty saudat tashigo,duk kallonsu yakoma kanta,baka ce siririya doguwa sosai tana sanye cikin material pink colour,
"Manyan yayu ataimaka abar mana amaryar mu ta huta haka tasamu dan bacci inji hajiya,ga dakinku can inda zaku kwanta"
Ai wani sanyi Hanan taji jin zasu fita su barta ita kadai,
"To ba matsala muje,amarya ga wayarki may be zaku dan taba hirar dare da ango kar mu tauye muku hakki...." Anty badi'a ce tayi wannan maganar sannan ta fito mata da wayarta ta mika mata,sake tukunkune fuska tayi saboda bata son anty saudat dake tsaye bakin kofa taganta.
Tattarawa sukayi gaba daya suka fita suka barta nan ta duba wayarta jikinta har wani tsuma yake saboda yanda take hanzarin taba wayar,miss called sama da guda 15 tagani sai massages guda biyar bata bi ta kan massages din da miss called din ba tafara kiran layin mujahid amma duka akashe,ji tayi kamar ta fashe da kuka amma babu hali sakamakon wani dunkulen abu mai kamada curin karago da yazo ya tsaya mata a kirji ya tokare mata makoshi,
Miss calls din tabi ta duba kusan fin rabi kiransa ne sai na sauran abokan arziki wanda bata tsaya bi ta kansu ba, massages takoma dubawa nan taga sakon bank guda daya anturo mata alawee sai sakon minister shima guda daya sauran kuwa duk sakon mujahid ne,
Na mujahid din tabi tafara karantawa daya bayan daya gaba daya jikinta sai yayi mata sanyi tamkar bata da sauran laka ajikinta wai ashe duk abubuwan da mujahid yajima yana fada mata gaba daya zirata yayi akwali yarufe wai dama wallahi baida niyyar yin wani abu dan yahana aurenta da minister kawai yayi hakane dan ya kwantar mata da hankali amma kamar yadda yafada mata abaya shi mai taimaka mata ne dari bisa dari tayiwa iyayenta biyayya bazai taba goyon bayanta wurin bujirewa umarnin iyayenta ba saboda soyayyar gaskiya yake yimata kuma har gobe yana sonta,ayau dashi aka daura auren ta domin ya halarta kuma yayi musu addu'a ita da mijinta Allah yabasu zaman lafiya dan Allah tayiwa mijinta biyayya fiyeda yadda taso yiwa shi mujahid din sannan ta sani ko gobe aurenta ya mutu wanda baya yimata fatan haka ashirye yake da ya aureta yakaita gidansa domin yana sonta har gaban abada,
Wadannan kalaman nasa sune suka kashe mata duk wata kafar laka dake jikinta sannan kuma suka tsayar da tunaninta cak na dan wani lokaci tabbas abunda mujahid yayi abune da yadace ta yaba masa kuma taji dadi amma kasancewar akwai Shaidan sai taji samm hakan bai burgeta ba ita wani haushi ne ma ya turnuketa dan me mujahid zai yaudare ta yamayar da ita karamar yarinya wacce bata san ciwon kanta ba? Wallahi da tun farko tasan wannan tuggun yake hada mata da tuni ta samarwa kanta mafita amma dan mugunta bai sanar da itaba sai a kurarren lokaci, lokacin da bata da matakin dauka,
Sakon minister ta bude tana jin kwalla na ciko mata ido wanda sai lokacin hawayen suka samu zarafin fitowa,
_Kamar yadda na fada miki zan kafa miki dokoki akan yarona,nafarko ba a dukan min yaro,ba a zaginsa,ba a yimasa tsawa sannan duk abinda yake so abashi,kuma ki sani ko harararshi kikayi zai sanar dani._
Ganin abinda yaturo mata yasata wurgi da wayar can karshen gado amma dai Allah yaso bata kai ga faduwa kasa ba,fashewa tayi da kuka aranta tana cewa wannan shine inuwa zafi rana kuma k'una........鉁嶏笍
_Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din._
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:07 AM - Ummi Tandama: *Littafin mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*
*14*
***Tun bayan tafiyarshi k'asar Spain ya tsinci kanshi cikin yanayi na rashin lokaci duk da a bangare daya yayi tafiyar ne dan ya kebance kanshi wuri daya kwakwalwarshi da gangar jikinsa su samu hutu koda babu yawa amma baiyi katari da samun hakanba har sai bayan yan wasu kwanaki da zuwanshi k'asar.
Ranar da aka daura aurensu da Hanan Khalid ne yafara yimasa albishir ta hanyar turo masa da sakon karta kwana ta wayarshi,
Lokacin yana kwance adaki mai lamba 9 cikin babban hotel din da ya sauka wato luxury 5 Stars hotel wanda ke cikin tsakiyar birnin na spain wato birnin Madrid,yana ganin sakon sai yaji hankalinsa ya dugunzuma mutuwar Ramlat ta dawo masa sabuwa kamar yanzu ne akayi ta,
Samun kansa yayi da zubar da hawaye kamar wani karamin yaro kankani,mutuwa mai yankan kauna,mutuwa yanke buri,bai taba kawowa Ramlat mutuwa ba a lokacin da ta mutu amma wai sai mutuwar kawai yaji,a wannan lokacin saida rayuwar da suka gabatar tare ta dawo masa tun daga ranar da yafara ganinta har izuwa ranar da aka daura musu aure da irin tsaftacacciyar rayuwar da sukayi tare har izuwa samun juna biyunta da kuma mutuwarta duk saida suka dawo cikin kwakwalwarshi a wannan lokacin,wai yau gashi shine aka sake daura masa aure da wata saboda rashin Ramlat da ace Allah yabarshi da Ramlat dinsa ai shida kara aure har abada saboda ita kadai ta isheshi rayuwar duniya dai wadda ba matabbaciya ba. A zamansu da Ramlat yasha fada mata cewa bazaiyi mata kishiya ba ita kadai ta isheshi a lokacin sai tayi murmushi tace wannan fa tatsoniya ce kawai yake yimata ba komai ba,idan kuma Khalid na nan sai yarinka tsokanarta yana cewa ai karya Khalil din yake yi bayan shi yake ma rakashi zance ta shirya kwana kwanannan zasu kawo mata amarya,
A takaice dai ranar wuni yayi acikin daki wani lokacin yayi kuka wani lokacin kuma yayi murmushi tamkar wanda ya zauce ko yasamu tabi,amma ta wani bangaren yana jin sanyi acikin ransa idan yatuna da ya cikawa Aryan burinsa dan irin farin cikin da zaiyi sai Allah. Bai samu fita ba sai bayan da yayi sallar magriba bayan yayi wanka, kananan kaya yasaka jeans da t shirt dukkansu bakake sannan ya dora jar jacket asama bayan yasa bakin takalmi sau ciki,amafi yawan lokuta irin wannan shigar yake yi aduk lokacin da yabar gida Nigeria, kananan kaya yake sakawa sai yakoma Nigeria ne yake saka manyan kaya kuma shima bai fiya amfani da babbar riga ba a'a sai dai doguwar riga da wando da hula su yafi ta'ammali dasu,
Wayarshi ya dauka yafita bayan yasaka hular dake jikin jacket dinshi yarufe kansa,saida yabar harabar hotel din domin dan mike kafarsa sannan yakira Aryan yasan dai lokacin ba afi la'asar ba a Nigeria tunda akwai dan banbancin lokaci,
Zama yayi kan wani bridge sannan ya kalli screen din wayar domin video call yakira,ganin Aryan yayi da hijabin umma barira ajikinsa yana kan cinyarta dare dare,
"Papa Uncle...... Daddy"
"Aryan,shine ka haye min kan cinyar gyatuma saika karasa mata kafafun ko? Oya tashi maza dagata"
Kafada ya makale yana dariya,
"No Papa.....uhm uhm"
"Bar ja'iri dai ai sai na kaishi an aske masa wannan sumar tashi dake kansa" umma barira ta fada cikin tsokanar Aryan ai kuwa sai yafara kuka yana cewa baza ayi masa aski ba dan tunda aka haifeshi ba ataba yimasa aski ba tun bayan na suna har yau dinnan sai dai ataje sumar wani lokacin kuma akaishi saloon a dan gyara masa ita shikenan saboda shi kansa baban shima ba askin yake yiba sai dai gyaran fuska amma shima kansa haka yake,
"To ya isa kyale umma babu mai yiwa abbana aski..... Daina kuka"
"Papa momy tazo ko? Zamuje wurinta nida umma balila"
Dariya umma barira tayi ta d'aukeshi cancak ta dora saman kujera tawuce gaban gado ta zauna tana cewa,
"Daina bata min suna dan nema.."
"Momy tazo tana sabon gida,are you happy?"
"Yes Daddy,ka siyo mata kaya mai kyau"
Kamar yadda ya tsammata sai da yagaji da surutun Aryan dan har saida yaji yamanta damuwar da ya wuni acikinta, Aryan na debe masa kewa Sosai aduk ranar da yasamu kansa cikin damuwa da zarar ya kasance da yaron sai yaji hankalinsa ya kwanta ko dan irin son da yake yiwa yaronne oho.
***
Zaman kadaici,shiru da rashin sanin abinyi takamaimai shine ya taru ya dabaibaye Hanan wacce ke kwance cikin daki lamo ita kadai batare da abokin hira ba har magriba tayi tana kwance saman gado bata ma san magribar tayi ba saida ta kunna wayarta wacce ke kashe da niyyar kiran yaya shamsu taji ko Allah yasa sun isa gida sai lokacin taga ashe har lokacin salla yayi,yaya shamsu takira bugu uku ya dauka,
"Yaya shamsu kun karasa gida ne?"
"Ehh"
Shine kadai abinda yafada yakashe wayarshi saboda baya son tayi masa kuka yasan yanzun nan zata fara koke koken nata,
Itama tasan dalilin da yasa yakatse wayar kenan duk da haka saida taji hawaye sun zubo mata tamkar ruwan zafi saboda duminsu,kiran mujahid tayi amma har lokacin wayarshi akashe take,lallabawa tayi ta tashi tashiga bathroom tayi alwala tafito tayi salla nan ta zauna awurin bata tashiba har lokacin sallar ishah yayi,mikewa tayi ta gabatar da sallarta sannan ta tashi takoma saman gado,gaba daya tagaji da kwanciyar ma amma kuma babu yanda zatayi babu yanda ta iya,sake tashi tayi ta canja kayan jikinta izuwa na bacci riga da wando lainon c green rigar mai botira ce da gajeren hannu shi kuma wandon dogo ne, kwanciya tayi duk ranta tsoro fall amma tasan insha Allah babu abinda zai sameta saboda katon gida irin wannan akwai security duk da dai Allah ne mai karewa ita abinma mamaki yake bata wai itace daren farkonta ya kasance ahaka,lallai Allah shine mai tsara rayuwa amma ko amafarki bata taba tunanin wai daren farkonta zaizo ta wannan sigar ba. Tajima tana juye juye amma kasancewar akwai ramukon bacci da yawa akanta bata san lokacin da bacci ya dauketa ba wato shiyasa bacci yakeda dadi domin akwai wani sirri acikinsa duk damuwarka ko ciwo ko bacin rai kana mantasu a lokacin da kayi bacci baka tuna komai har sai ka farka,
Hakance tafaru gareta itama domin tunda tayi bacci tasamu nutsuwa tayi baccinta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali wanda ba ita ta tashi ba sai bayan asuba wannan dinma tasowar hadirine yatasheta saboda iska,salati tayi tai maza tashiga bandaki tayi alwala tafito lokacin tuni anfara ruwa misalin karfe 6 da kwata na safe,
Sai bayan da tayi salla sannan tashiga wanka tafito,make up kit dinta ta bude ta dan shafa lotion tasaka powder sai kwalli shikenan ta saka kayanta shadda brown colour da sarka da dan kunne ta dan fesa turare sama sama sannan ta bude kofa tafita domin wata lafiyayyar yunwa take ji duk hanjin cikinta sun sarke da juna,tamkar sakaliya yau haka ta zama sakamakon ganin haduwar da falonta yayi yasha purple colour din furnitures hatta wallpaper din dake bangon falon purple colour ne amma mai dan haske sannan ga wata tangamemiyar plasma ajiye wacce ke barazanar cinye bangon da take,agaskiya gidan yayi kyau ya hadu kuma ya tsaru sannan ankashe miliyoyin kudi wurin shiryashi, ita kanta cikin falon nata wurin bedrooms hudu ne aciki banda kitchen da store da dining area haka dayan part dinma dake opposite da nata,daga tsakiya kuma akwai wani dan corridor mai dauke da wasu hadaddun kujeru kai daga ganin wurin kasan anyi ne domin shakatawa dan ga flowers nan masu kamshi shuke agefe cikin tukwanen kasa wacce aka yiwa fenti da golden gashi yadda aka you roofing din wurin dabanbanci da sauran domin wannan anyishi ne da wani style mai ban sha'awa sosai ya burgeta dan daga nan inda kake ma kana iya hango cikin unguwar ta glasses din dake zagaye da wurin kana iya hango kyau da tsari irin na unguwar wacce ke dauke da manya manyan gidaje kerarru ga korayen ciyayi da shuke shuke da suka yiwa unguwar kawanya, gaba kadan kuma wata kyakkyawar kofa ce katuwa mai dauke da security code ajiki amma ita arufe take balle taga abinda ke ciki dan haka tajuya ta nufo kasa, babban falon dake kasa shima yana dauke da kitchen da store da dining room sannan ga guest room, atakaice dai gidan yakai part 4 waje waje ko ina kuma a tsare wani wurinma bata san dashi ba. Babu kowa cikin falon sai sanyi da kamshi dake ta faman tashi ta ko ina, kan dining ta duba abinci ne reras cikin warmers mai kyau kala kala wanda ita abinma har yaso bata tsoro to ina za akai wannan abincin sai kace wanda mutane goma zasu ci bayan bata ji motsin kowa ba? Lallai masu kudi suna shagalinsu a duniyar nan ta Allah,
Zama tayi ta debi dankali da kwai sai farfesun kayan cikin saniya dan su kadai zata iya ci,tana ci tana sake karewa falon kallo wanda yake kamar baza amutu ba dan tsabar haduwa tab irin wannan gidan idan mutum ba mai cikakken imani bane ai sai yamanta da mutuwa domin zai shagaltar dashi shi kansa dining area din abun kallo ne kujerunshi na karfe ne milk colour sai wani show glass mai fadi da girma glass da glass anzuba kwanukan cin abinci duk na tangaran plates, spoons, cups da sauran kayan amfani irinsu dinner set. Bayan tagama ci ta mike ta dauraye hannunta da bakinta awurin wanke hannu wanda aka tanada a dining area din dan hadda sabulun wanke hannu ajiye awurin nan ta matsa ruwa yafito ta wanke hannunta sannan ta leka cikin kitchen din wanda ke tafare da kayan amfani na wuta dan gaba daya electric ne kayan ciki gashi kuma babba dashi ba karami ba kayan ciki kuwa yaci ayiwa yanmata biyar aure dashi cikin wadata kuma,mayar da kofar tayi ta rufe takoma sama tana mai sake jinjina wannan gida acikin ranta,da ace wanda ta aura take so ko yaro ba tsoho ba ai zata fantama ta wataya to amma ina k'addara tariga fata.
Rasa abinda zatayi tai daga karshe tasaka wayarta a charge tabi lafiyar kujera ta hakimce tana sake bin falon nata da kallo to kenan ma har kayan dakin shi minister dinne yayi amma dai zata iya yuyuwa shima abbanta yayi mata,to aure ne babu shiri dududu ko wata daya fa ba ayiba da maganar akayi aure shiyasa komai babu shiri,
Dan sakin ranta tayi sakamakon kiranta da mutane keta faman yi awaya suna yimata Allah yasanya alkhairi wasu kuma suna yimata korafin kin sanar dasu bikin nata da batai ba ita dai bata cewa komai sai dai tayi shiru ko ance Allah yabada zaman lafiya bata cewa amin, su Khadija kuwa wadanda sukayi zaman camp tare sunce insha Allah zata gansu tunda dai tana Abuja.
Wuni guda ta kwashe tana shan baccinta salla kawai ke tada ita,bayan tayi sallar la'asar ta yi wanka ta sake shiryawa cikin atamfa exclusive irin na cikin lefenta,dinkin riga da zani ne pieces simple daurin dan kwali tayi sannan ta shafa turare,tun safe rabonta da abinci shiyasa ta nufi downstairs domin cin abinci ai kuwa gashi nan jere an ajiye wurin kala biyar,shinkafa fara da plantain sauce,sai amala da miyar yauki,ga gasasshen kifi wanda yaji vegetables washa washa ga jalop cous cous,sai farfesun kaza da wasu ganyayyaki wadanda bata gane Wadanne bane,
Shinkafar ta diba a plate tafara ci tana hadawa da gasasshen kifin,wato daga safe zuwa yanzu shine har aka kara zuba wasu abubuwan cikin show glass dinnan domin da safe iya dishes ne da ire irensu aciki amma yanzu harda kayan hada shayi irinsu madara, corn flakes, golden moon,da biskit kala kala wanda ake hadasu da tea asha,
Tana daf da gamawa taji karar kararrawa abakin kofar falon wato door bell,tana yunkurin tashi aka sake dannawa,mikewa tayi ta nufi bakin kofar dan ganin waye dukda babu hijabi ko mayafi ajikinta amma tasan kayan jikinta basu da matsala.................鉁嶐煆?
*_Ummi A'isha_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:07 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*
*15*
***Cikin nutsuwa take takawa har ta isa bakin kofar daidai lokacin aka sake dannawa, budewa tayi ta dan ja baya,umma barira ce da nura PA yana dauke da Aryan a kafadarshi da alama ma Aryan dinne ke ta faman daddanna door bell din,
Kasancewar ita ba saninsu tayiba yasa ta dan saki fuska tana yimusu sannu da zuwa, Aryan kuwa sauka yayi daga hannun PA ya ruga jikinta ya rungume ta, bata da zabin da yawuce itama ta rungumeshi din amma bawai dan son ranta ba,
Kaya aka rinka shigowa dashi wanda yake mallakin su umma bariran da Aryan,sai lokacin ta fahimci ko suwaye domin dama taji Zaid yana waya yana fadar cewa zasu dawo gidan da zarar sun kammala shirya kayansu nan suka sake sabuwar gaisuwa da umma barira ta tsugunna har kasa ta gaida umman,
Suna zaune a falo PA nata shigarwa da umma kayanta cikin daya daga cikin bedroom din dake kasa bayan angama kaiwa Aryan nasa dake sama,
Sosai take ankare da yaron wato Aryan wanda yayi dare dare kan cinyar umma barira sai game din Angry run yake ta faman yi awata waya hadaddiya wacce bata da masaniyar ko ta waye,
"Umma kema akai miki kayanki upstairs....." Taji Aryan din yafada yana turo baki alamun shagwaba,
"A'a Aryan ni ina kasa yaushe zan hau sama intakura muku"
Jin abinda tace yayi wurgi da wayar yasoma rigima shi ala dole itama umma sai ta hau sama,wani irin haushin yaron Hanan keji gaba daya anbi anbata yaro an sangartashi dan kawai uwarshi ta mutu? Yaro sai tabarar tsiya duk anbarshi babu gwaba?
Dan karamin tsaki taja tana kallonsu umma nata kokarin rarrashinsa amma yana ta botsarewa,cigaba tayi da kallon dramar tasu amma fa yaron akwai masifar kyau ko tantama batayi tasan mahaifiyar shi ya iyo dan wallahi kamar dan larabawa yake ko turawa,
Dakyar umma ta rarrasheshi ya hakura ita dai Hanan haushi ne ya hanata magana domin dama haushinsa take ji tunda ta sanadiyyar shi ne ubansa yaje ya aurota har da su kafa mata dokoki akansa. Har lokacin sallar magriba yayi suna babban falon kasa zaune lokaci zuwa lokaci suna dan taba hira shikuma Aryan na kwance yayi pillow da cinyar umma yanata game dinshi,ganin lokacin salla na neman wucewa yasa umma barira fadin,
"To kai sulaimanu dagani inje daki inyi salla karka karasa min k'afar"
Mikewa umma tayi domin shiga daki shikuma Aryan yana cewa,
"Ni bazan bikiba mommy zanbi"
"Ehh kuje umma ta gaida Aysha" umma tafada tana wucewa daki,ita kam Hanan bata kulashi ba da taga zai biyota ma harara ta zabga masa jikinsa yana rawa yabi bayan umma yafasa binta,sama ta hau tana ta faman mita,
"Haka kawai kunbi duk kun bata yaro kamar shi kadaine maraya mtswwww nidai wallahi bazanyi tolerating wannan nonsense dinba"
Bedroom dinta ta shiga tayi alwala tafito aranta tana cewa idan uban naka yaji haushi ya sallame ni inbar muku gidanku sai yaci gaba da lallaba ka yana tattalinka. Aryan kuwa da kuka yashiga dakin umma wacce ke kan rug din salla tana yi,shi tunda yafado duniya bai san wani abu waishi takura ko kiyayya ba,kowa cikin nuna masa so yake da kauna ko harara bai santa ba sai yau da yaga Hanan tayi masa shiyasa tun daga lokacin yafara jin tsoronta,saida umma ta idar da salla sannan tasoma rarrashinsa daga karshe taci nasara bayan tace masa suje tabashi tuwo yaci dama akwai shi da son tuwo yana mutukar kaunar tuwo yaron yafi sonshi fiyeda komai adangin cima,
Saida umma ta sake masa kayan jikinsa daga jeans da t shirt zuwa riga armless da gajeren wando sannan suka fita,akasa suka zauna bayan umma ta zubo tuwon nan tafara bashi abaki yana ci tana hada masa da ruwa amma shi hankalinsa gaba daya yana kan wayar dake hannunshi,ahaka Hanan ta sauko ta samesu tana sanye da babban hijabi hannunta rike da casbaha tana ja ahankali,zama tayi akan kujera tana kallonsu kamar tasamu tv domin sai umma ta dan rarrashesa sannan yake yarda yana karbar tuwon,
Kamar a mafarki kuma sai taga yana murna yana dariya yana fadin,
"Papa..... Daddy"
"Yes son how you? Me kaka cine haka?" Khalil yafada wanda ke kwance kan gado yana kallon Aryan da umma agefenshi ta video call din da yakira,
"Daddy tuwo umma take bani.... Kuma da dad'i"
Dariya Khalil yayi yana kallon fuskar Aryan Sosai,
"Boy meyasa kayi kuka? Waye ya taba min kai?"
Kafin Aryan yayi magana umma tayi karaf tace, "Rigimar tashi ce kawai ta motsa kasan halin mutumin idan yan rikicin suna kusa,muma ai gamu asabon wuri Masha Allah wallahi wuri yayi kyau mu'azzam Allah yasanya albarka"
Duk abubuwan da akeyi Hanan na saman kujera tana kallo amma ita bata jiyo maganar Khalil din tunda ba akusa take ba. Sunfi mintuna talatin suna wannan wayar dan har Hanan ta ci abinci tagama tawuce sama tabarsu har lokacin Aryan yanata hira da Abban nashi, lallai Allah kadai yasan irin son da wannan mutumin ke yiwa Aryan gaba daya parlors din gidan hotunan yaronne akakkafe wanda sam da bata lura dasu ba kun san ance hankali shine gani ita dai dakinta ta koma tayi sallar ishah tayi wanka tayi shirin bacci tabi lafiyar gado.
Washe gari kasancewar da akwai makaranta kafin ma tafito tuni har anshirya Aryan antafi kaishi shiyasa lokacin da ta fito iya umma kadai ta tarar tana karyawa,gaisheta tayi sannan itama tawuce kan table tana ta mamakin wai su ma'aikatan gidan nan ba aganinsu ne sai dai kawai kafito ka tarar da aiki angama? Dan hatta shara dasu mopping duk anyi ansaka turaren kamsasa daki sai faman tashi yake,bayan tagama takoma wurin umma anan ma take tambayar ta ma'aikatan gidan nan umma tafara bata labari ai su da asubah suke aikinsu suyi su gama,sun jima tare da umma suna shan hira wanda hakan ba karamin debe mata kewa yayi ba,suna tare Khalil yakira umma suka gaisa cikin fara'a umma ke cemasa mutumin ai yatafi makaranta sai anjima za aje adaukoshi,tana jin lokacin da umman ke cemasa amarya fa ko abata waya? Sai yace a'a itama zai kirata ita kuwa Hanan tasan ba kiran nata zaiyi ba shiyasa da umma ta fada mata acikin zuciyarta tace yarike kiransa itama ba nema take yiba. Sun jima tare da umma suna hira daga daren jiya izuwa yau kadai taji ta saki jiki da matar kuma har sabo yashiga tsakaninsu kamar dama can sun dade tare,wurin azahar ta koma sama tayi wanka tayi salla ta dan kwanta ita fa gaba daya ta kosa hutunta yakare ta koma school saboda bazata iya wannan kwanciyar ba ace mutum babu abinda zaiyi sai dai yaci ya kwanta? Tunda fa tazo gidan nan babu abinda take yi daga gyaran d'akinta sai gyaran falo da toilet shikenan aikin sai kwanciya alhali ita bata saba wannan rayuwar ba,ita tasaba ta wuni tana aiki tana kujiba kujiba takai can ta kawo nan amma yanzu wani lokaci yazo mata wanda bata duk wadannan abubuwan.
K'arfe 2 na rana tasake sauka k'asa lokacin tuni har Aryan yadawo daga makaranta PA yaje ya daukoshi yana zaune a falo daga shi sai gajeren wando duk uniform din nashi da takalmi da school bag duk ya zubarsu anan, harararshi tayi bayan ta zauna nan yashiga taitayinshi yadaina abinda ta sameshi yana yi wato baza kayan wasanshi irin fruits din roba dinnan na wasan yara harda su wuka wacce ake yanyankawa to su ta iskeshi yana barbazawa duk yana neman hargitsa falon,kalar tausayi yayi ya rakube jikin kujera yana wasa da wayarshi,
Jin motsi a dining area yasata waiwayawa nan taga kuku yana shirya abinci dama tunda ta sauko take jin kamshi ya cika falon,yau dai taga ma'aikacin gidan guda daya, muryar kukun tajiyo yana gaidata nan ta amsa cikin harshen turanci domin bai iya hausa ba sunanshi John,tana ji yanata jan Aryan da wasa amma baiyi magana ba Aryan din bayan kuma surutu ne da yaron kamar aku,
Tana can tana faman kallon yanda john ke shirya table cikin kwarewa da sanin makamar aiki Khalil yakira Aryan kuri yayi yana kallon yaron saboda sam babu fara'a atare dashi fuskarshi kamar zaiyi kuka tambayar shi yafara yi wai waye ya tabashi? Ko yunwa yake ji? Yaci abinci? Ina umma barira?
Duk wadannan tambayoyin babu wanda ya amsa sai murza ido da yake ta faman yi yana son yin kuka,kasa da murya Khalil yayi yace,
"To albishirinka lovely son.... Gobe zata zama rana ta musamman agareka.... Ai kasan babu school gobe ko? Gobe zanyi surprising dinka da wani abu,maza jeka ka kaiwa umma wayar.."
Tashi Aryan yayi da gudu yana murna yahau sama nan Hanan tabishi da kallo, dakinshi dake sama yashiga wanda sam Hanan bata ma san dashi ba can ya iske umma tagama gyara masa dakin tana karasa shirya masa kayansa cikin drawer,wayar yabata yana ta murna,
Bayan umma tagaisa da Khalil cikin damuwa Khalil din yace mata, "Umma ni kwana biyun nan haka haka nake ganin yaron nan babu walwala kamar yana cikin damuwa ko baida lafiya ne?"
"A'a lafiyar shi kalau wallahi kuma babu abinda ke damunshi kai dai ka saki ranka ka kwantar da hankalinka wuri daya"
Bazaiyi musu da umma ba shiyasa yayi shiru amma ko jiya fa da yaga yaron da daddare saida jikinsa yabashi cewa kuka yayi yau kuma gashi yaganshi yazama wani soo silent kamar wanda aka takure wuri daya, sallama sukayi umma ta mikawa Aryan wayar suka ci gaba da magana da tsohonshi Khalil sai janshi yake da hira tun bai sake ba har yasake yafara nuna masa dakinshi da umma tagama gyara masa yana ta murna yana cewa Khalil dakinshi na yanzu yafi na tsohon gida kyau ahaka Hanan ta shigo ta samesu saboda taji shirun yayi yawa kuma agabanta Aryan ya iyo sama da gudu shine da taji shiru tabiyo bayanshi, kasancewar yabar kofar dakin abude shiyasa tagane inda ya shiga,koda ta shigo cikin dakin sakin baki tayi kawai ta tsaya cak tana kallon ikon Allah domin abinda idanuwanta suka gane mata yayi bala'in bata mamaki.....................鉁嶏笍
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:08 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*
*16*
***Sakin baki kawai Hanan tayi tana kallon irin uwar dukiyar da aka narkar wurin shiryawa Aryan dakinsa,dakin ya hadu ne yasha furnitures masu tsada da burgewa irin yanda ake shirya dakunan yara akasar turai ko India,
Wani dan karamin gado ne hadadde pink & purple colour da drawers dinsa sai mirrior wanda aka daurashi a jikin bango gashi gaba daya bangon dakin an zaneshi da zanen su butterfly da sauran zane na daukar hankalin yara da kaloli daban daban har da wurin karatunshi acan gefe ansaka table da yar karamar kujera kai dakin dai yagama haduwa karshe,
Tsabar mamaki kasa magana tayi sai faman bin ko ina na cikin dakin take yi da kallo yayinda ita kuma umma barira ke kokarin karasa shirya masa takalmansa saman shoe rack,
"Masha Allah Aryan wannan dakin naka na yanzu yafi na tsohon gida kyau ko?" Umma ta tambayeshi cikin tsokana,yana rike da wayarshi yaturo baki,
"Uhm uhmm ni nafi son wancan"
"To basai kaje ka koma ba dan nema,ni katashi ma inshiryaka maza malamin islamiyya zaizo yanzu kar yazo baka shirya ba..."
Ita dai hanan wuri tasamu ta zauna tana kallon wannan ikon Allah yaro karami amma dan daurewa karya kugu shine harda wani dakinsa kuma dakin ma ba ashiryashi da wasa ba dagaske aka shiryashi domin anci mutuncin naira dagaske ba kadan ba. Agabanta umma ta buda drawer din kayan shi domin ciro masa kayan da zata saka masa,kayane iya ganinka wani kayanma wannan sai yafi shekara bai maimaita shi ba saboda tsabar yawansu dan hatta uniform din makarantarshi gashi nan yafi set goma,gaskiya yaron nan dan gata ne na ajin karshe ubanshi naji dashi kuma yana nuna masa tsantsar so shi ko tunanin gaba ma bayayi?
Tabe baki tayi ta tashi tafita bayan ta fadawa umma dama sawun Aryan din tabiyo da taji shiru bai koma ba, k'asa ta sauka ta hau kan table domin cin abinci, spaghetti and cheese bagels taga ni sai egusi soup and eba ga kuma jalop rice with jerk chicken salad, sannan ga goat meat pepe soup,
Eba din ta zuba da miyar egusi tasoma ci tana yi tana hadawa da juice mai sanyi,gefe daya kuma tana mamakin yadda akayi wannan kukun ya iya girki har haka sai kace yaje catering school dan ko mace bazata nuna masa kwarewa wurin girki ba,tun kafin ta kalli wurin tasan sun sauko domin tana jiyo karadinsa da karar takalminsa, gaskiya umma barira na da hakuri dan wannan Aryan din dan rigima ne,
Su dinma kan dining din suka hau umma nata rigima dashi akan sai yaci abinci saboda baya son cin abinci dan wani lokacin ma lunch box dinshi yanda yatafi dashi school haka zai dawo dashi bai ko buda ba,
Tana jin umma nata lallaminsa har aka samu yaci eba ta hada masa da karamin juice na kwali sannan yafita domin tuni malaminsa yazo yana can yana jiransa. Ita dai tana son tayiwa umma barira magana akan Aryan amma kuma bata san ta inda yadace tafara ba domin irin wannan wani lokacin kai zakayi magana da zuciya daya kuma gaskiya zaka fada amma sai aga kamar da biyu ka fada saboda ba kai ka haifi yaroba shiyasa ma kawai taja bakinta tayi shiru suka yi wata hirar ba wannan ba,
Suna zaune cikin falo bayan sun gama cin abinci nura PA yashigo dauke da kayan wasan Aryan wanda yabaro a tsohon gida wai Aryan dinne yace akawo masa kayansa shine fa akaje aka debosu cikin mota Hilux guda ahakan ma ba duka ya debo ba yabar wasu acan,
Daki guda taga anbude anan k'asa kusa da na umma barira ciki nura keta kai kayan ashe dama akwai wasu aciki kiriga guda sababbi babu abinda babu,motoci ne,babur,jirgi,bindiga,duk na roba gasu nan jingim kamar dakin wasan yara,ganin haka sai ta kara shan jinin jikinta akan lamarin daga karshe ma tashi tayi takoma sama bata san lokacin da aka gama shigowa da kayanba.
Washe gari bayan tafito da safe misalin karfe 11 iya umma kadai tasamu kishingide cikin d'akinta tana jan charbi,shiga tayi suka gaisa sannan umman ta kara da cewa,
"Nima yanzun nan nashigo ai mutumin na raka yashiga mota babanshi ya iyo waya tunda asuba wai ashirya shi za akaishi wurin faretin yara yana son gani wai yau babu makaranta ranar yarace...."
"Allah sarki shi faretin yake so? Ko harda shi a masu yi?"
"A'a gani kawai zaije yayi ai uban yahana shi yi da harda shi ake zaba sai uban yace bazai yiba kin san hutsu ne wani lokacin..."
"Ai kuwa dai naga alama" Ta fada acikin zuciyarta amma afili sai tace,
"To Allah yadawo dashi lafiya,bari naje inyi breakfast nima fitowata kenan"
Fita tayi ta hau kan dining domin karyawa,to ko mujahid yasake layi ne dan ko dazu sai da ta kirashi amma wayarshi akashe kamar koda yaushe,tsaki tayi taci gaba da cin abincinta tana jin duk zaman gidan har yafara isarta tun ba aje ko inaba,to zamane wuri daya kuma gashi babu abinda zakayi sai dai kaci kasha ka kwanta daga nan babu wani motsi da zaka yi,ita wallahi son fita ma take yi ta dan ga gari,
A kasalance ta koma sama ta kwanta a falonta wayarta ta dauka ta siyi data wai ko zata dan rage zafi domin ta gaji da zaman shirun nan wai ahakanma dan da su umma, group dinsu na WhatsApp ta duba wato Abuja Kopa kamar yadda sunan group din yake wai ashe anfara clearance tun jiya amma bata saniba kuma babu wanda yafada mata,dan tsaki tayi ta mike tana tunanin ko a ina kakinta ma yake oho dan bata san duniyar da yashiga ba,bata san ta inda yadace tafara nemanshi ba,
Bedroom tashiga tafara dubashi amma sai dakyar ta ganshi duk ya yi squeezing yanzu dole sai angogeshi,fita tayi wurin umma tana tambayar ta a ina zata samu ta dan goge kayanta? Nan umma ta karba tace idan PA yazo zata bashi sai yabawa mai wanki idan angoge za akawo mata, godiya ta yiwa umma sannan ta juya tasake komawa inda ta fito.
K'arfe 2 da kusan rabi na rana su Aryan suka shigo shida PA yana kan kafadar PA ya daukoshi kamar wani yaron goye,zuwa yayi ya haye kan umma barira bayan nura ya saukeshi shikuma yafita,
"Dan albarka andawo? Me ka kawo min?" Inji umma,
"Kayan dadi..."
Shigowar nura ta katse musu hirar da suke yi wanda ke rike da kaya niki niki na kwalam da makulashe cikin manya manyan ledoji masu dauke da tambarin ihsan confectionery,
Uniform din Hanan umma tabaiwa PA yabawa mai wanki ya wanke mata ya goge sai yahado da kayan Aryan ya kawo, nura na shirin fita Hanan ta sauko lokacin umma nata tiriniyar bubbude kayan da PA yashigo dasu,vanilla ice cream ne manya manya sai chocolate suma manya manya da sauran tarkacen kayan ciye ciye da su snacks,fada umma tafara yi tana cewa Aryan,
"Kai ja'iri ba babanka ya hanaka shan wadannan kayan sanyi da zakin ba? Shine shikuma nura ya biyewa son ranka yasiyo maka ko?"
"Umma Papa ne yace asiya min shima yakusa dawowa"
"Karya kake Khalil bazai ce asiya maka wannan kayan zakinba"
Ai jin umma ta ambaci Khalil sai yafara kuka wai danme zata fadi sunan babansa sai dai itama tace Daddy ko Papa,dariya umma tayi ta soma rarrashinsa tana cewa,
"To ai nikuma ba babana bane ba akanme zance masa baba?"
"Babanki ne..."
"To naji baba nane nima shikenan?"
Hanan kallonsu take yi kawai amma acan kasan ranta ji take yi kamar taje ta kwada masa mari saboda b'acin yaron da sangartarshi yayi yawa yanzu meye abin kuka anan daga magana dan anfadi sunan Khalil? Wallahi ba dan tana jin kunyar umma barira ba da sakashi zatayi agaba ta yita fadin sunan uban nashi inyaso yayi kukan jini. Wadannan kayan da yazo dasu su yasha yaki cin abinci umma sai kyaleshi tayi,malamin islamiyyarshi ma da yazo kin fita yayi nanma umman tayita binsa amma yaki harda yimasa barazanar zata fadawa abbansa amma abin mamaki da Khalil din yakira waya umma tana cemasa,
"Ka ganshi nan tunda yadawo daga wannan cindirin de din yaki dadi sai rigima yaketa yi yaki yaci abinci sannan ga malaminsa can yana jira shima yaki zuwa"
Murmushi Khalil din yayi yace da umma,
"Umma children's day fa ake cewa,tunda baya son zuwa karatun yau akyaleshi gobe sai yaje nima insha Allah yau da tsakar dare zan dawo yanzu haka ma ina dan shisshirya kayana da nazo dasu ne"
"Ai kuwa Aryan yafada nazaci ko shirmensa ne,to Allah yadawo daku lafiya"
"Amin umma nagode, bawa Aryan din"
Duk abubuwan da ake yi Hanan dake can karamin falo tana jiyowa amma iya maganar umma kadai take ji, da alama dai shi yake bata yaronshi da kanshi ba umma ba dan umma na iya bakin kokarin ta akan Aryan. Tabe baki tayi aranta tana cewa sudai suka sani ita kam yar kallo ce.
***
Misalin karfe 3 nadare agogon Nigeria suka sauka afilin tashi da saukar jirage na Nmandi azikiwe international airport dake garin Abuja,kai tsaye tsohon gidanshi yawuce domin shi komai nasa yana can bai dauke ko tsinkenshi zuwa sabon gida ba kuma bai san ranar komawa ba tunda aganinsa mai zaije yayi agidan alhali ba Ramlat ce aciki ba,
Wanka kadai yayi da ruwan dumi sannan yazura farar jallabiya tas yafita yana rike da wani dan karamin akwatin adana zobe amma daga gani kasan yashaki kudi,
Kasancewar ya danci abinci acikin jirgi baya jin yunwa dan haka yashiga mota suka nufi sabon gidanshi dan bazai iya hakuri baiga Aryan ba har gari yawaye,
Nura na gaba yana yimasa jagora har cikin gidan,gidan yayi masa yadda yake so kuma anshirya shi yanda yabada umarni babu ta inda aka kuskure,dakin Aryan yabude yashiga ganinsa yayi yana kwance yana bacci amma ba kamar yadda ya saba ganinsa ba yau sai yaga yaron ya danyi masa wani iri,sumbatar goshinsa yayi da kumatunsa sannan yashafi kansa,akwatin zoben dake hannunsa yabude yaciro wani dan karamin zoben azurfa mai kyawun gaske dan har kana iya hango haskenshi acikin duhun tsabar shekin da yake yi,kama hannunshi na hagu yayi yasaka masa zoben wanda ke dauke da wani farin stone wanda yakara masa kyau da kwarjini,koda yaushe yana ta son yasiyo masa sakamakon wanda ke yatsan Aryan din tun yana jariri tuni yayi masa kadan yacire masa shi to bai samu wanda yayi masa bane sai wannan lokacin,
Tashi yayi ya dan zazzaga yaga yanda dakin Aryan din yake sannan yafita yaja masa kofar bayan ya lullube shi da bargonshi mai tsananin laushi,
Bai sake shiga ko inaba yafita yakoma mota suka bar gidan yanufi tsohon gidansa, kwanciya ya danyi ko zai dan samu bacci kafin asubah ta karasa domin da safe yana da tafiya zaije jihar katsina.
Da safe bayan yashirya yana kokarin saka farin takalminsa sau ciki sakon Hanan yashigo da kamar bazai bi takai ba sai kuma ya duba bayan yagama saka takalmin,
_Zanje clearance NYSC sectariat._
_Ok._
Yatura mata kawai yadauki hularshi yafita yanufi office.
***
Tunda taga reply dinshi taji ranta yabaci, karasa shiryawa tayi tasaka uniform dinta tafito sanye da milk colour din hijabi,
Bata samu kowa ba sai kayan breakfast jere saman table,taosted bread taci da ruwan tea sannan tashiga dakin umma barira wacce ke kwance bayan tagama shirya Aryan yatafi school gaisawa suka yi sannan tacewa umma zataje clearance tadawo ba jimawa zatayi ba,
"To sai kin dawo,ashe mai gidan shima yadawo daren jiya ko... Ai sai dazu Aryan ke nuna min zoben da yazo masa dashi kuma shine kamar gari bazai waye ba aka kasa hakurin bari sai yau... Tunda yadawo nima wajen gobe zanje ingano gida in danyi kwana biyu sai indawo"
Shiru Hanan tayi saboda ita bata san cewa wai minister yadawo ba au ashema yana garin take wani tura masa text massage,dan murmushi ta kakalo tayi sannan tace da umma,
"Umma menene kuma na zuwa gida dan kawai yadawo,dan Allah karki tafi ki zauna muyi zamanmu"
"A'a wallahi ai idan naje can dinma ba dadewa zanyi ba,kwana biyu kurum zanyi indawo"
"To ai shikenan umma,bari naje nadawo"
Fita tayi nan suka yi kicibus da PA wai oga ne yaturoshi tafito yakaita unguwar, batace komai ba tabishi harabar gidan mai dauke da sassa daban daban gaskiya gidan nan katone ga haduwa da yayi securities kuwa abakin gate kamar gidan wani shugaban k'asa sai yau ta taba fitowa shiyasa ta kame a owners corner tana kallon unguwar tasu har suka je bright future ta karbi clearance form daga nan yakaita NYSC sectariate tayi thumbprint sannan ya maido da ita gida sai lokacin yake fada mata wai oga na can office yana jiransu da zarar yakoma zasu tafi unguwa ita dai bata ce komai ba ta bude kofa ta fita.
Kamar yadda umma barira ta fada haka ta matsa sai ta tafi gida wai tayi kwana biyu kun san iyayenmu akwai kara da alkunya ita gani take zata shiga hakkinsu ta takura musu tunda amarci zasuyi,shi kansa Khalil din baya nan tunda yadawo daga Spain sau daya suka hadu sai driver yatura mata da mota yaje ya dauketa suka nufi gombe lokacin Aryan yatafi makaranta,
Koda yadawo daga makaranta baiga umma barira ba kuka yafara yi gidan shiru babu wanda yasan ma yanayi haka Hanan ta sauko ta sameshi kallonsa kadai tayi yaron yashiga taitayinsa jikinsa duk yafara rawa,da kansa ta turashi yaje ya cire uniform dinshi sannan ta tayi masa wanka,wani irin mugun tsoronta yaron yake ji domin baiga fuska ba ko abinci tana zuba masa ya dauka yafara ci duk yau babu wannan shagwabar da surutun da yasaba yiwa umma barira da kuwa ummance da sai sunyi daga da ita kafin ya yarda yaci abincin,
Gaba daya Aryan ya takura yazama marayan gaske kalar tausayi,malamin islamiyyarshi na zuwa yatafi yau babu game babu wasa babu kallon carton,sam Hanan bata wasa dashi,washe gari ita tatashi tayi masa shirin makaranta yatafi kuma babansa bai samu zuwa ganinsa ba ranar yadai kirashi awaya,
Cikin kwanaki biyu kacal Aryan yazama abun tausayi aranar da daddare misalin karfe 2 nadare Khalil yashiga gidan dawowarsa kenan daga gombe yaje ya dubo hajiyarsa,gani yayi Aryan duk ya sauya dan ko dazu awaya yayi mamakin yanda yaga yaron ya zama wani silent kamar bashi ba, Aryan ba irin yaran nanne masu kunci ba amma cikin yan kwanakin nan yafara zama haka shiyasa abin ke taba zuciyar Khalil,a lokacin bai tashe shi ba amma yadau alwashin sai ya tambayi yaron abinda ke damunshi,tashi yayi yafita yayi tafiyarsa tsohon gida.
Washe gari bayan antashi daga school office yasa aka kawo masa Aryan ba akaishi gida ba,
Tare ya zuba musu abincin da PA ya karbo musu daga gida saboda Aryan,daukar shi yayi yadora saman cinyarshi suna facing juna gani yayi da alama yauma Aryan yayi kuka,cikin damuwa ya dan girgizashi,
"Abba na meke damunka? Andukeka a makaranta ne?"
Girgiza kai Aryan yayi kamar zaiyi kuka dan har yafara murza ido da hannunshi,
"To meke damunka? Maza fada min,kaida na kawo maka mommy gida,ko baka farin ciki da zuwanta?"
Daga kai yayi alamun ehh tun daga nan Khalil yasa alamar tambaya jikinsa yabashi akwai wani abu dake faruwa...............鉁嶏笍
0 comments:
Post a Comment