***Sake tsare Aryan yayi da idanuwanshi yana son gano dalilin da yasa yaron yashiga cikin damuwa kwana biyu tunda ya tambayeshi yaki fada masa damuwarsa,
Kama hannunshi yayi yana murza diamond ring din dake yatsanshi,
"Aryan me mommy din take yimaka? Tana dukanka ne?"
Girgiza kai yayi alamar a'a,
"Tana zaginka ko?"
Nan dinma girgiza kan yayi wai a'a,
"To me take yimaka? Fada min bazan fada mata ba"
"Nidai uncle umma tadawo....umma nake so"
"Umma zata dawo ayau dinnan ma kuwa Aryan amma matsalar baka fada min abinda mommy din keyi maka ba,ko baka son inje umarah dakai bana?"
Kwantar da kanshi yayi jikin uban yana murza idanuwa,
"Ina so..."
"To me take yimaka?"
"Babu komai"
"To shikenan,bari nakira PA yazo maza yatafi gombe yanzu yaje ya dauko umman"
Tunda Aryan yaji haka yashiga murna umma zata dawo wanda har abin yaso bawa Khalil mamaki to ko dama rashin umman ne ke sashi cikin wannan damuwar? Babu mamaki saboda umma bata nanne yasa yaketa wadannan shiriritar tunda da ita yasaba,
Kasancewar shima Khalil din fita zaiyi yanada ganawa ta musamman da shugaban kasa yasashi bawa PA Aryan akan yakaishi gida amma Aryan ya tubure akan shi lallai lallai sai yabi nura dauko umma,cewa nura yayi su tafi taren amma dan Allah kar suyi dare ahanya.
Hanan na gida bata san abinda ke faruwa ba ita dai taga Aryan bai dawo gida ba daga baya kuma sai malamin islamiyyarshi da yazo yana jiranshi yace PA ya kirashi yace yatafi wai Aryan na tare da babanshi a office ita sai a lokacin ma taji abinda ake ciki,
Tabe baki tayi ta zuba abincin ta a plate tawuce sama ta shiga falonta tana ta jan tsaki ita kadai,
"Haka kawai kun dauki son duniya kun dorawa yaro kamar akanka aka fara haihuwa,bama dole yaro ya sangarce ba tunda ba a tsawatar masa...."
Saida tagama cin abincin sannan ta zage tafara gyara falon saboda da alama masu aiki iya kasa kadai suke gyarawa sai ko dakin Aryan amma ita nata basa ko shigowa ma shiyasa ta dage ta shareshi tsaff duk da ba wani datti yayiba tayi mopping ta kunna turaren wuta a burner take falon ya dauki kamshi kamar me, toilet ta shiga ta yi wanka tafito bayan ta shirya cikin doguwar riga yar kanti marar nauyi dark blue ta dauko wayarta ta kira number mujahid kamar a mafarki sai taji ta shiga amma har tayi ta katse bai dauka ba sake kira tayi nan dinma har ta tsinke bai daga ba,
Kwalla ce taji tafara zubo mata daga idanuwanta dan wallahi har yanzu bata ji alamar sonshi yaragu daga cikin ranta ba kuma bata jin zata iya daina kaunarsa a rayuwar da zata gabatar agaba,
Text massage ne yashigo wayarta nan ta dauka ta duba mujahid ne yaturo mata,
_Hanan dan Allah kiyi hakuri ki yafe min sannan ki zauna da mijinki lafiya wannan itace alfarmar da nake bukata kadai daga gareki._
Wasu hawayen ta sake jin suna kokarin zubo mata wai kowa sai yace ta zauna da mijinta lafiya bayan mijin ko sanin kamanninsa ma bata yiba ita yanzu da zasu hadu a hanya tasan sai yawuce ta wuce dan dukkansu ba sanin fuskokin juna suka yiba ita wallahi wannan mutumin yagama cutarta,kamar dama wacce take jira nan tasha kukanta tagama sannan ta sauka kasa har lokacin Aryan bai dawo ba babu shi babu alamarsa amma tunda dai ance tare yake da babanshi shikenan. Haka tayita kaiwa da kawowarta ita kadai acikin gidan har magriba tayi tunda ta shiga daki kuma bata sake fitowa ba har akayi sallar ishah,saida ta tashi ta gabatar da ishah din sannan tafita falonta dake sama,tv ta kunna ta kamo tashar da ake nuna fina finan India sabbi da tsofi bugu da kari akwai fina finai masu dogon zango da tashar ke nunawa dan debe kewa,
Zama tayi zaman dirsham tana kallon film din da suke nunawa a wannan lokacin mai suna Viva,kallon shine ya dauke mata kewa dan ko tashi bata son yi har saida taga karshen film din nan ta kalli agogo domin yunwa take ji tana dan sunkurinta haba ashe dole taji yunwa domin karfe 10 daidai yanzu lallai tajima azaune dama karatu da kallo haka suke idan suka dauke maka hankali sai ka raba dare batare da kasani ba,
Tashi tayi da niyyar zuwa kasa domin zubo abinci wanda zata dan sakawa cikinta,duk da dare ne saida ta yafa mayafi ajikinta sannan ta sauka,gidan shiru kamar koda yaushe sai ko uban hasken fitilu tarwal tamkar rana dan ko allurarka ce ta fadi to babu shakka zaka ganta hankali kwance,falon sai tashin kamshi yake yi kamar koda yaushe kan dining table din kuwa jere yake da abinci reras kamar yadda John yasaba shiryashi,
Tuwon semovita tagani miyar okra,sai sphagettee with beef stew,fish and yam stew sannan ga balangu jalop,fish and yam stew ta zuba a plate sannan ta debi balangun taje fridge ta dauki ruwa da juice takoma sama ta cigaba da kallonta tana tsakurar abincin ta ahaka har ta cinye,ita dai gashi ahaka kamar babu abinda ta rasa amma azuciyarta tana jin tabbas ta rasa wani muhimmin abu atare da ita mai mutukar muhimmanci,
K'arfe 10:30 su umma barira suka dawo lokacin kam tuni Aryan yajima da yin bacci dan lokacin da suka shigo ma PA ne ya daukoshi yashigo dashi falon kasa ita kuma umma ta karasa dashi dakinsa ta kwantar dashi bayan ta canja masa kayan jikinsa,
Falon Hanan ta nufa a karon farko dan ba taba shigarshi tayi ba sai yau,har lokacin Hanan na zaune ta kurawa tv na mujiya amma fa acan zahiri bawai kallon take yi ba kawai tunanin yanda rayuwarta ta sauya a lokaci kankani take yi,ita da tajima tana lissafin sai tagama karatu tagama NYSC sannan zatayi aure ashe abin ba haka yake ba,
Jin ana yin knocking yasa ta dan firgita sai kuma tajiyo muryar umma tana cewa "Ko har matar gidan ta kwanta ne?"
Mikewa tayi taje ta budewa umma kofa fuskarta dauke da murmushi,
"A'a wallahi umma idona biyu ashe kune kuka dawo...."
Karasa shiga cikin falon umma tayi tana cewa,
"Ehh wallahi ai mutumin nawa ne yatada rikici sai da akaje aka dawo dani,basu ma sameni anan cikin gombe dinba ina can Billiri gidan dan uwana ziyara acan suka je suka rakato ni..."
"Allah sarki,ai gara da kika dawo umma amma kin tafi ki barmu?"
"Ai ba tafiya nayi ba 'yarnan,zuwa nayi indawo"
"To ai shikenan umma barka da dawowa ya mutanen gida? Kin baro kowa lafiya?"
"Lafiya lau,suna agaggaisheki"
"Ina amsawa"
Kasancewar umma ta gaji daga haka ta tashi ta tafi taje tayi shirin bacci ta kwanta. Ita kuwa Hanan batayi bacci da wuriba yau tasamu kallo saida takai 1 na dare tana kallo a d'akinta,daga k'arshe ta kashe ta kwanta,
Daidai lokacin kuma Khalil yashigo gidan bai shiga ko inaba sai dakin Aryan kadai daga nan yafito ya dan zazzaga gidan sannan yatafi domin agajiye yake shima.
Washe gari misalin karfe 8 yashiga gidan lokacin har ankai Aryan makaranta,dakin umma yashiga kamar koda yaushe yana sanye da farar shadda kar tasha aiki da coffee colour din zare yadora hula itama coffee yar bama sai kamshin turaren gentleman yake yi wanda yake fita daga jikinshi,
Zama yayi suka gaisa da umma sannan cikin fara'a yace, "umma sai kuma kika ga anje andauko ki...... Wallahi Aryan ne yakasa sakewa da bakya nan"
"Ehh mu'azzamu haka nura ya sanar dani,amma ai da kun barni na danyi koda kwana biyu ne itama matar gidan ta dan sake"
Dariya yayi saboda jin abinda ta fada dama yasan dalilin da yasa ta tafi kenan ganin yadawo ne, "A'a umma ai babu komai kiyi zamanki wallahi,nima kaduna zanje yanzu amma sai na fara zuwa office tukunna zan gana da manema labarai"
"To Allah ya kiyaye hanya yabada sa'a,sai ka dawo"
"Amin umma,mutumin yatafi makaranta ko?"
"Tun dazu ai yajima acan,yatafi yana ta rikicin wai sai anhada masa harda wannan lemon madarar da ka hana abashi cikin lunch box dinsa"
"Kar arinka bashi umma saboda rana wallahi"
"Ehh ai shiyasa ban bashi ba nadai lallabashi nabashi dayan"
Fita yayi yatafi abinshi bai ko nemi inda matar gidan takeba kai to ai shi da zaka saka wuyansa gaba gabas bazaice maka ga kalar amaryar nan ba, ita kuwa umma har yau bata san ba agidan yake kwana ba duk d'aukarta agidan yake.
Hanan sai wurin karfe 11 sannan tafito bayan tayi wanka ta shirya cikin wani jan swiss material dinkin doguwar riga,umma ta iske tana falo tana sak'a muficin roba da alama jiya ta taho da kayan yin,
Tea ta hado ta dawo wurin umman ta zauna suna hira,
"Ashe maigidan kaduna zaije ko? Ai kullum baya rabo da tafiye tafiye,ayi mutum kullum da inda zaije bashida ranar hutu? Wannan aiki nasu da wahala yake"
Jin abinda umma tace yasa Hanan fuskarta akan baban Aryan umman ke magana, murmushin yake tayi amma bata nuna cewa bata saniba,
"Wai nikam umma meyasa auren da yafi na yanzu kwanciyar hankali ne dan Allah? Auren yanzu da yawa wallahi ana dai zaune ne kawai amma bawai dan ana jin dadinsa ba", ita kanta bata san lokacin da tayiwa umma wannan tambayar ba kawai dai kun san abinda ke ran mutum wani lokacin sai ya amayar dashi yake jin dadi,
"To ai mu ada kinga akwai biyayya mijin ma ba saninsa kayiba shima bai sanka ba iyayene zasu hada kuma baka isa kace kai bahaka ba koda kuwa kana da naka zabin haka zaka hakura ka karbi nasu,ka isama kace kai ga wanda kake so? Ai idan kayi haka kayi rashin kunya,haka zaka yi hakuri kuma sai kiga nasu zabin yafi nakan"
"Amma dan Allah umma ya kuke ji idan akayi muku auren dolen nan lokacin"
"Wallahi bama jin komai 'yarnan tunda dama abune da aka riga aka saba sannan kin san mutanen da akwai biyayya ba irin na yanzu bane,dan ni kinga lokacin da aka kaini daki wallahi ban taba ganin mijinba sai lokacin shima haka kuma haka muka zauna acan muka saba muka so juna har lokacin da mutuwa ta raba,amma ku yanzu mazajen da kuke so din kuke aura amma babu zaman lafiya,mu hadamu akeyi hadin iyaye amma Sai mu zauna lafiya ba fada ba yaji bare aje garin saki da yawa mutuwa ce ke rabawa amma ku yanzu aure wata biyu wata uku sai afara yaji ko ma auren yamutu gaba daya,mu ada bamu san wannan ba,miji yana girmamaki yana girmama iyayenki kema kuma haka sannan kina yimasa biyayya babu reni amma yanzu ku auren ma yazama na zamani..."
Sosai yau Hanan suka sha hira da umma wacce ke zaune tana ta sak'ar muficinta to babu abinyi idan kuma kafiya kwanciya jikinka sai yayi ciwo. Har lokacin da Aryan yadawo suna tare umma nata bata labarin auren da, Aryan baiko nufeta ba umma yanufa dama da ita yasaba shima kuma yaro yasan mai yimasa inda ake kaffa kaffa dashi yake zuwa shiyasa Aryan baya ko rabarta.
Aranar da yamma su Khadija suka yimata waya wai zasu zo tabasu address din gidan,itama saida ta dan tambaya sannan ta tura musu,tana falo ita da umma shikuma Aryan yana can ana koya masa karatu wani mopol yashigo falon da kayansa na aiki ya tsuke harda bindiga rataye ajikinsa,
Dan russunawa yayi sannan yace "madam kina da baki kin san da zuwansu?"
Ita wallahi sai yau tasan dan zakayi bako sai ka sanarwa securities,mantawa ma take yi da agidan da take nan dai tace masa ehh tasan da zuwansu,fita yayi yaje yashigo dasu sannan yajuya yasake fita,
Mamaki ne yaso kashe su hajara saboda ganin irin aljannar duniyar da Hanan ke ciki haba ai ko haka Allah yabarka sai ka gode masa domin ya daga darajar ka,gaisawa sukayi da umma daga nan takaisu sama falonta ai sai suka sake zama kauyawa sunata yimata murna ita kuwa sai tabe baki take yi bayan tagama cika musu gabansu da kayan ciye ciye da abinci da fruits da juice kala kala,
Ita haushi ma take ji yanda suke ta ikirarin wai tayi sa'a tayi dace,ita da ta auri tsoho komai kudinsa wallahi gara ta auri yaro sun mutu cikin talauci, dariya hajara tayi tace,
"Lallai yarinya baki san talauci ba,wallahi yau da gobe tafi karfin wasa,ai inda kudi bacin ranki kadanne koda bakya sonshi amma komai son da kake yiwa mutum mutukar akwai babu tofa babu zaman lafiya wallahi talauci shi yafi komai hana aure ya zauna lafiya"
"Ki kyaleta hajara,ke nidai ki taimaka min ki hadani da wani acikin abokanshi nima infaso...." Khadija tafada tana kashe ido daya dan ita har zuciyarta dagaske take ita kuwa Hanan wallahi duk haushi suke bata haba me za ayi da auren tsoho ai wallahi akwai matsala yanzu ko abune yatashi na friends kowacce zataje da dan mijinta yaro mai jini ajika kai sai aganka da tsoho? Tsohonma wai abokin babanka,ai ita dai wannan minister ya cuceta wallahi,
Duk maganganun da su hajara keyi ta bayan kunnenta yake shiga har suka gama suka tafi bayan ta cika musu leda da kayan kwalliya,ita dai yanzu alla alla take takoma school taci gaba da zuwa PPA dinta ko ta samu abinyi........................鉁嶏笍
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:08 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*
*18*
***Haka rayuwa taci gaba da tafiya kullum Hanan cikin kunci take sam bata jin dadin zaman gidan minister amma na waje koda yaushe cikin tayata murna suke ana cewa tayi sa'a kuma tayi dacen gidan miji, duk da suna zaune da umma lafiya kuma cikin mutunta juna amma wani sa'ilin ji take yi kamar ta dora hannu aka ta fasa ihu dan tsabar takaici,saida hutunta yakare ta soma zuwa school sannan ta dan fara samun nutsuwa domin kullum idan ta fita bata dawowa sai 2 na rana duk ta zama busy bata samun zama sai weekend Aryan kuwa tare suke tafiya school dashi kullum amma babu ruwanta dashi sam bata sakar masa fuska bare ya kawo mata wargi,
A bangaren oga Khalil shi dinma hakan take domin har yau bai san ko kalar Matar da ya aura ba dama kuma shi ba mazauni bane kullum yana da inda zaije baya shigowa gidan sai dare darenma ba na kusa ba da yazo zaiga Aryan shikenan sai yayi tafiyarsa yakoma tsohon gida amma bai taba kwana a wannan sabon gidan ba umma kuwa yakan zo wani time din da sassafe ya gaishe da ita sannan yawuce bai taba neman hanan ba kuma bazai taba nemanta ba domin bashida matsala da ita shi yanzu matsalar shi ciwon cikin da ke neman zame masa karfen kafa domin kusan kullum cikinsa yake kuma gashi yasha magani yasha magani har yagoda Allah.
Hanan har yau bata ji son mujahid yaragu daga cikin zuciyarta ba kusan kullum sai tayi masa text massage amma baya yimata reply ita kuma kamar yanda kasan asiri yayi mata haka ta makale masa.
***
Mujahid
Dauriya kawai yake yi amma tun ranar da Hanan ta sanar dashi maganar bikinta hankalinsa yayi masifar tashi domin akanta yafara yin soyayya kuma ita yake so bai taba son wata mace ba sai ita,bacci wannan baya iyawa yanda ya kamata,
Yana zaune cikin falon mami mahaifiyar shi ya rafka uban tagumi yasaka abinci agaba amma tsabar damuwa ya kasa ci ahaka mamin tazo ta iskeshi idanuwanshi jajur yakasa cin abinci sai faman tunani yake yi,zama mami tayi ta dafashi tana son jin damuwarsa,
"Mujahid meke damunka ne? Kwana biyun nan duk baka da kuzari lafiya kuwa?"
"Babu komai mami...."
Ya fada yana kokarin hadiye kwallar dake kokarin sauko masa,
"A'a wanne irin babu komai bayan gashi nan ina ganin damuwa baro baro atare dakai,ka fada min abinda ke damunka,idan baka fada minba wa zaka fadawa?"
Tallafe kumatunsa yayi da hannuwanshi guda biyu,
"Mami Hanan din da nake baki labarinta itace aka yi mata aure....."
"Aure? Aure fa kace, yaushe?"
" tun sati biyu da suka wuce nikuma wallahi narasa yadda zanyi indaina sonta"
Shiru mami tayi tana nazari amma tunda yafada mata cewa wai anyiwa Hanan aure tasamu kanta cikin bacin rai domin mujahid din yana tsananin son wannan yarinyar amma shine zata yaudarar mata yaro tasashi cikin matsala da damuwa alhalin ita kuma tana can tana more tata rayuwar,
Shafa kansa tayi acikin ranta tana tunanin abinda yadace tayi domin bazata taba zura idanu tilon danta yashiga cikin matsala ba akan wata,
"Dauki abincin kaci mujahid..... Insha Allah sai Allah yayi maka sakayya,dauki kaci..."
Ba dan yana so ba haka yadauki abincin yafara ci sai dai ko lauma uku kwakkwara baiyi ba yaji wani azababben amai yana taso masa babu shiri yabar abincin yatashi yanufi bedroom din mami yashiga toilet dinta yasoma yunkurin yin amai wanda ke fitowa dakyar harda jini jini,ai hankalin mami wacce ke biye dashi idan yayi dubu saida ya tashi babu shiri ta kira driver suka tafi asibiti mujahid rai a hannun Allah,
Saida yashafe fiye da sati daya a asibitin yana samun kulawa daga ma'aikatan jinya sannan yafara samun lafiya,kullum yana ganin kiran Hanan da sakonninta amma baya bi ta kai saboda yanzu matar aure take bai kamata yarinka kulata ba amma shima kawai danne tashi zuciyar yayi bawai dan yadaina jinta acikin ranshi ba.
***
Zaman Hanan agidan minister har yau jiya iyau domin babu wani sauyi sannan bata taba ganinsa ba shima haka shi dai Khalil akwai ranar da yashigo da sassafe ita kuma ranar zata fita CDS tana sanye da uniform ya hango shigarta mota shikuma yana cikin motarshi mai dauke da bakaken gilasai yana kishingide a owners corner kamar koda yaushe,suna yin parking ita kuma motarsu na fita daga cikin gidan dama yanzu anware musu motarsu ita da Aryan mutumin nata wanda har yau baya ganin dariyarta kullum cikin cimasa magani take shiyasa yake bala'in jin tsoronta wanda har yau babanshi bai saniba dan da ace yasani da tuni yajima da daukar matakin da yadace.
Kasancewar tana jin haushin uban shiyasa shima dan take jin haushinsa ga shegen surutu da shagwaba awurin wannan yaron amma uban baya gani bini bini zaka ji yakira dan awaya yana tambayar sa ko akwai wani abu? Ita kanta wayar Aryan din ta dubunnan kudice kuma ba uwar komai yake yi da itaba sai game sai waya da uban ita dai wallahi tana jin haushin wannan abu amma tunda ba danta bane ido ne nata,gashi da yadawo daga makaranta zai shiga dakin da kayan wasanshi suke a kasa yayi kaca kaca dasu yahau na hawa ya bata na batawa.
Yau kam ta kama weekend tunda asuba Khalil yatafi gombe zai halarci wani daurin aure da yaso yatafi da Aryan to kuma yasan time din bai tashi daga barci ba,
Hanan kuwa tun da tatashi ranta abace yake saboda weekend ne yanzu zata yita zaman wuri daya daga nan har monday,gashi tunda tazo garin nan batayi kitso ba kanta atsefe tagaji dashi kuma ahaka,text massage ta turawa minister akan tana son fita kitso,shi kam da yake yana can gombe kuma tare da mutane bai ko samu zarafin duba wayar ba saboda jama'ar da yake tare dasu daga wadannan sun fita wadannan zasu shigo kuma duk lokacin da yaje gombe hakane,zakayi mamakin irin mutanen dake tururuwar zuwa wurinshi duk ranar da yaje garin.
Shirun da Hanan taji yayi mata sai tasake kufula ta tunzura dama ta jima da yimasa zargin girman kai wato yanada wulakanci da girman kai anata tunanin dan ko massage sai ya gadama yake amsawa,shiyasa a kule ta wuni ranar da rana ma saida yunwa ta ciyota tazama weak sannan ta sauko kasa Aryan na zaune falon yabaza kayan wasa baja baja yanata wasanshi umma kuma na bedroom tana dan taba baccin kalula,
Kan dining Hanan ta hau ta zuba alalan kwai mai dauke da kayan lambu da sos tana ci,
Aryan ne yacika falon da wata irin kara sakamakon bindigar wasanshi da ya kunna kai sai ka rantse karar bindigar gaske ne nan yacikawa Hanan kunne da kara ita kuma dama a kule take,
"Kai......kashe karar nan" Ta fada cikin fada amma bai kasheba saboda shi bai jita ba sau kusan uku tana yimasa magana amma bai jiba ita kuma ta zaci yana jinta ya kyaleta dan haka ta tashi afusace ta nufe shi tana zuwa ta daka masa wata gigitacciyar tsawa da ba ataba yimasa irinta ba,
"Kai...... Kashe wannan abun naka duk kabi ka wani cikawa mutane kunne shashasha kawai...."
Dama Aryan tsoronta yake hakan da tayi masa sai yasake tsorata da sauri ya kashe jikinsa na rawa,
"Bar nan....fice daga nan"
Tashi yayi da sauri garin yabar wurin yataka wani abu daga cikin kayan wasan nasa santsin tiles yajashi suuu yatafi ya fadi kansa ya bugu da kujera ji kake gummm shikenan ya fadi awurin babu numfashi....................鉁嶏笍
_*Ummi Shatu*_馃憣馃徎
8/14/20, 10:08 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*
*20*
***Da hasken wayarshi ta hannu yayi amfani wacce ke cikin aljihun gaban rigarsa,caan ya hangosu kwance saman gado sunyi kai da kafa,sake lumshe idanuwanshi yayi sannan yasoma takawa ahankali har ya isa gaban gadon,kamshin dakin nata sai yaji ya banbanta da irin wanda falon nata keyi, bai tsaya kallonta ba yayi abinda yakaishi kawai wato kallon sha lelensa Aryan,ita kam gaba daya lullube take da duvet tun daga kafafuwanta har zuwa kanta dan haka babu abinda zaka iya gani atare da ita sabanin Aryan da dama tun can asali baya son a lullubeshi idan yana bacci sai ko idan baccin nasa yayi nisa,
Shafa fuskar Aryan din yayi sannan yayi kissing dinsa a goshinsa shima ya lullubeshi, ahankali yajuya yafita daga cikin bedroom din amma can kasan ranshi wani dadi ne ke ziyartarsa ganin irin kulawar da Hanan ke bawa Aryan, Allah sarki ashe ya dauki hakkin yarinyar ne da har ada yafara zargin ko itace ke takurawa dan gaban goshin nasa,ashe ba haka bane ita tayashi ma sonshi takeyi,
Zuciyarshi fes yabar gidan yanufi tsohon gidansa inda karfi da yaji can yake rayuwarsa shi daya,wanka yafara yi sannan yahada coffee yasha duk jikinsa jinsa yake yi yana yimasa ciwo kamar wanda ya wuni yana yin aikin karfi, shiyasa ma yau bai samu zarafin yin tsaiwar dare ba kawai dai ya zauna ya karanta abinda ya sawwaka cikin littafi mai tsarki daga nan yayi alwala ya kwanta.
Su Hanan kuwa babu wanda acikinsu yasan cewa wai Khalil yazo gidan sai da suka fito da safe sannan suka ga tsarabar da yakawo musu adaren jiya wato fura da nono sai fruits kala kala harda apple mango irin manya manyan mangoes dinnan, ita umma barira har yau bata san cewa ba agidan yake rayuwarsa ba kuma bata san akwai wata akasa tsakaninsa da Hanan ba da za ta tsawatar musu kuma ta dauki mataki.
Yau ita dai hanan da farin ciki ta tashi,ruwan wanka ta hadawa Aryan sannan ta d'aukeshi duk da bai tashi ba ta nufi cikin toilet dashi tana sakashi cikin bahon wanka mai dauke da ruwan dumi ya bude manyan idanuwanshi irin na ubanshi domin babu ta inda yabar babanshi a kamanni,
"Mommy....."
"Good morning cutie"
Kwantar da kanshi yayi acikin ruwan nan tayi saurin rikeshi tana dariya, ahaka tayi masa wankan suka fita, direct dakinshi ta wuce dashi domin shiryashi, saida tafara jona masa wayarshi a jikin charge sannan ta zauna ta shafa masa mai ta fesa masa turare sannan ta saka masa uniform, ahankali take taje masa kanshi wanda ke mutukar bata sha'awa, ohh duniya kenan Allah baya barin wani dan wani yanzu gashi shi Aryan uwar ta tafi ta barshi bai ko santa ba shiyasa bahaushe ke cewa da na kowa ne saboda sai ka haifeshi amma baka mora ba wanda zai mora daban,insha Allah tayiwa kanta alkawarin kula da rayuwar Aryan ko dan lalurar dake tattare dashi kuma insha Allah zata soshi zata kula dashi fiyeda yanda zata kula da dan cikinta,
K'asa suka sauka ta bashi breakfast yana ci sai lokacin umma barira tafito ganinsu cikin shiri suna karyawa yasata yin murmushin jin dadi sannan cikin farin ciki tace,
"A'a d'a da uwa har anshirya ne anfito?"
"Wallahi kuwa umma ai idan muka zauna sanya sai mu makara azo ana tare mu"
"Ahh gaskiya kam,kai dan albarka yau babu magana? Zanfa daina mijin dakai"
"Ai sai muma mu samo wata umma"
Dariya sukayi dukkaninsu cike da raha suka rabo bayan Aryan ya gaisa da abbanshi wanda ke can gida kwance har lokacin bai fita ba saboda gajiyar daren jiya bata sakeshi ba har yanzu shiyasa bai bar gida ba yau sai 10.
***
Mujahid yajima yana jinyar son Hanan acikin zuciyarsa,kullum baida aiki sai dai ya tisa hotonta agaba yana kallo duk yabi ya susuce yafita hayyacinsa,ada ya zaci zai iya daurewa ashe abin ba haka yake ba sai yanzu yagane gaskiyar son da yake yimata,
Kullum idan yaga sakonta sai yaji kamar ya mayar mata da amsa domin yanda take ji shima fa hakan yake ji acikin ransa koma fiye da haka,nan dai zuciya ta soma zugashi akan kawai ya fara kula Hanan suje suyi rayuwarsu, gashi akwai yar uwarsa mai sonshi sumayya amma shi hankalinsa baya kanta yana kan Hanan kuma tajima tana sonshi tun yana jami'a agidansu take kasancewar shi kadai ne awurin iyayensa shiyasa suka dauki sumayya suke rikewa,
Zaman asibitin da yayi ma tare sukayi jinyarsa da mami amma har yafara samun lafiya baya sakar mata fuska saboda shifa ba sonta yake ba,yau ma yana zaune a falonshi yana kallon hoton Hanan sumayya tabude kofa tashigo tana sanye da Arabian gown maroon colour,sake hade rai yayi kamar yaga mutuwarsa domin aduniya yaki jinin wannan yarinyar sumayya,
Kayan breakfast din dake hannunta ta ajiye masa tana sussunkuyar da kai alamun kunya,
"Yaya mujahid ga breakfast dinka inji mami..... sannan tace....tace wai ka daure ka kaini school..."
Idan kujerar da yake kai ta amsa to shima ya amsa mata,tafi minti biyar atsaye awurin baice mata uffan ba daga karshe yaja wani dogon tsaki yawuce cikin bedroom dinshi batare da ya ko kalleta ba,jagwab ta tafi ta zauna bisa kujerar da yatashi tana dafe kanta wanda yafara sara mata wasu hawaye ne suka shiga kai komo akan kuncinta wanda ko tantama babu na bakin cikine,inama tana iyawa da ta cire son ya mujahid daga cikin zuciyarta amma tasan hakan bamai yuyuwa bane tunda ba ita ta dorawa kanta ba.
***
Lokaci kankani shakuwa da soyayya mai tsanani ta shiga zukatan Hanan da Aryan,yanzu yaron yasaba da ita sosai kuma yana sakewa da ita kamar umma, dukkan al'amuransa wadanda ada umma ce keyi masa ayanzu Hanan ce ke yimasa,itace wankansa, shiryashi zuwa makaranta,yanke masa farce itace ke bashi abinci abaki yanzu komai ita keyi masa kuma har cikin zuciyarta yanzu tana son Aryan kamar zata lasheshi dan so,shima Aryan din yanzu ya shaku da ita komai ita yake nufa,
A yanzu kam tana jin dadin zaman gidan fiye da farkon zuwanta dama gidane babban gida babu abinda babu na fannin more rayuwa babu ce kawai babu agidan amma komai da kasani akwaishi ga swimming pool,ga wani daki mai dauke da kayan motsa jiki ga library babba mai dauke da littattafai iri iri, can ta kofar baya kuma idan kabi akwai hadadden garden dan debe kewa mai dauke da tsintsaye aciki ga Giggs da dawisu dake sake kawata wurin,agaskiya gidan akwai abubuwan dauke kewa da kadaici sai dai har lokacin tana kewar gida dan duk bayan kwana bibbiyu take kiran mamaye da Abba su gaisa shi kuwa yaya shamsu kusan kullum suna hade ta online.
Har tsawon wannan lokacin Khalil da Hanan basu taba ganin juna ba saboda shi baya shigowa gidan sai sunyi bacci kuma idan yaje ma iyakarshi dakin Aryan da yaje yaganshi zai tafi idan kuma awayane tashi hanan take yi tabar wurin amma tsakaninta da Aryan yanzu akwai kauna mai girman gaske dan har shi Khalil din yafara fuskantar hakan saboda komai sai yaji Aryan yace mommy ce tayi masa idan abu yaci sai yace itace tabashi yaci,tsakaninsa da ita sai dai yaji sunanta abakin Aryan amma ko awaya bai taba jin muryar taba itama haka shi kuma dama ba mazauni ba yau yana wancan gari gobe yana waccan k'asa.
Tana kwance a d'akinta bayan ta idar da sallar la'asar tana karanta wani novel din turanci (Tiers of betrayal) gaba daya hankalinta yatafi ga karatun da take yi taji Aryan ya fada kanta,
Ajiye wayar tayi tana rungumoshi jikinta, "Cutie what happened?"
Kiss yayi mata agoshi sannan ya rungume ta,
"Uncle yace ba gobeba wata goben birthday dina kuma Uncle Zaid zaizo yakaimu aje ayi party..."
"Woww.....my boy zai kara girma"
Rungumeshi tayi tana tambayar shi me yafi so wanda zata bashi a matsayin gift da yake yaro akwai shirme wai sai yace cake yake so,dariya tayi tace insha Allah zata yimasa cake,
Khalil kuwa washe garin ranar yatafi kasar Italy kuma aranar da yamma sai ga Zaid yazo saboda wai shine zai kai Aryan wurin birthday dinshi idan ranar tayi,
Sai yau Hanan ta taba ganin Zaid saboda ranar bikinta bata samu damar ganinsa ba tana kunshe cikin mayafi,tunda Aryan yaga Zaid ya makale masa suna ta tafawa da yin games kamar wani abokinsa,shima Zaid yanada haske amma ba sosai can ba kana dai ganinsa kaga bufulatani,gaba daya tana ta tunanin abunda yadace ta bawa Aryan amatsayin birthday gift dinshi amma ta rasa me zata bashi daga karshe dai sai ta turawa da Khalil text message,
_Ina son zan fita zuwa super market nida Aryan_
Shine abinda yaga ta turo masa, lokacin da yaga sakon nata yana daki ya idar da salla, reply yatura mata,
_me akeyi a supermarket din? Ki kular min da yaro saboda ban fiya barinsa yana fita any how ba._
Yana gama tura mata yakira Zaid yace yakaisu supermarket din sannan dan Allah ya kula da Aryan Sosai,
Shiryawa Hanan tayi tasha bakar doguwar riga mai stones tayi rolling tafita kasa inda Aryan da Zaid ke jiranta,umma suka yiwa sallama sannan suka tafi supermarket din,duk abinda Aryan keso barinsa tayi ya dauka sai da yagama jidar abubuwan da yake so sannan taje wurin biya ta ciro ATM card dinta tabasu suka cire kudinsu ta POS,duk kayan ciye ciye da zaki Aryan ya diba dan harda su ice cream,daga can kai tsaye gida suka wuce dama Khalil sai kiran Zaid yake awaya yana tambaya yaji ko sun koma gida saboda shi duk lokacin da aka fita da Aryan hankalinsa baya kwanciya har sai yaji sun koma gida.
Washe gari yakama ranar birthday din aryan kuma tun safe Zaid yafita karfe 2 yakira Aryan awaya yace wai mommyn shi ta shiryashi zaizo masa da kayan da zai saka,suna bedroom dinshi bayan tayi masa wanka Zaid yashigo ya kawo masa wasu tsadaddun kaya shi ba yadi ba kuma ba shadda ba yasha dinki na musamman kalar kayan ash colour ne amma anyi masa kwalliya da baki,ga takalminsa shima baki Aryan yayi kyau kamar babu gobe,
Itama Hanan shiryawa tayi cikin doguwar riga mai shegen kyau ja tayi rolling kamar abun shiri sai kuma mararta tafara yimata wani azababben ciwo dole sai hakura tayi tace suje,
Zaid ne yadebesu a mota banda umma ita kam cewa tayi adawo lafiya,daga shi sai Aryan suka tafi excellent square garden acan ne aka shirya party din cikin wani kayataccen hall mai masifar kyau, Hall din yasha decoration tako ina ga cakes nan manya manya wurin guda hudu kowanne kalarshi daban amma ajiki anrubuta HBD Aryan,yara da manyan dake wurin kwata kwata basu fi guda goma ba nan akayi aka gama saboda Khalil yanata yiwa Zaid takarar wai karsu yarda sukai dare shiyasa ana yin magriba suka tashi bayan anyanka cake anci ansha.
Har suka dawo Hanan na kwance adaki tana fama da kanta saida taji dawowarsu ne ma sannan ta samu dan karfin fita dan ganin gifts din da aka kakkawowa Aryan wadanda ke zube afalonta Zaid yashigo dasu, gifts ne sama da guda goma ko wanne anyi raping dinshi da raping sheet mai kyalli sannan ga manya manyan cakes dinshi nan wasu an yanka wasu kuma ko tabawa ba ayiba banda sauran snacks da drinks, PA ne yazo falon kasa yakira zaid yabashi wani sungumemen gift din shima anyi raping dinshi wai inji oga wato Khalil,
Hanan na zaune da Aryan akan cinyarta suna cin cake Zaid yakawo sakon,itace tafara budewa gift din Khalil din tana cewa Aryan, "Bari mufara ganin na Daddy ko"
Da wani dan karamin greeting card tafara cin karo wanda ajiki aka rubuta,
_Hope your birthday blossoms into lots of dreams come true! May today be filled with laughter and love. Happy Birthday and many happy returns of the day._
Murmushi tayi bayan ta gama karanta masa,wani babban enlargement din hoto tagani mai dauke da hoton Aryan atsakiya yayi kyau sosai ajiki anrubuta HBD boy,sai kuma wani dan karamin akwati koda ta bude agogon diamond ne kirar carat watch sai walwali yake aciki anninke wata yar karamar farar takarda ce wadda ajiki akayi rubutu da biro kamar haka,
_I may not be celebrating your special day with you but I want you to know that I am thinking of you & wishing you a HAPPY BIRTHDAY._
_papa_
Murmushi tayi ta daura masa agogon wanda kamar angwada da hannunsa,gaskiya babansa rikakken dan boko ne jibi rubutu kamar ba hannune yayi ba sai kace injine ya rubuta,raba dare sukayi suna santin gifts din da Aryan yasamu musamman ma na wurin Dad dinshi ga kuma na sauran mutane dan wasu ma ko budesu basu yiba..................鉁嶏笍
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:08 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*
*19*
***Duk da cikin bacin rai take sai da hankalinta yayi mugun tashi domin gani tayi Aryan yayi wanwars baya ko motsi wanda da alama suma yayi ko kuma rai ne yayi halinsa,
Rasa ma inda zata dosa tayi waje ko ciki? Da gudu ta nufi kofar da zata sadata da waje amma sai takasa bude kofar ma da yake arude take sai kokarin budewa take amma ta kasa,kamar daga sama Allah ya kawo mata security guda daya wanda yanufo cikin gidan,cikin rudu da rikicewa dan ko maganar ma ta kasa tafara nuna masa Aryan wanda ke can cikin falo asheme kamar wanda ya mutu,
A mutukar hanzarce suka shiga ya daukoshi,umma na can daki tana bacci bata san abinda ke faruwa ba har suka tafi asibiti,suna zuwa Dr Al'amin ya karbeshi dama shine family Dr dinsu nan yashiga bashi agajin gaggawa ita kuwa Hanan na waje ta rasa inda zata tsoma ranta tun daga yanzu tafara nadamar abinda ta aikata, bawai matakin da minister zai dauka shine tsoronta ba a'a shi dama tasan dole ne ya daureta har igiya tayi rara amma tsoronta kashe dan mutum da tayi,
Tafi awa tana kaiwa da komowa tasan idan minister yaji abinda yafaru ai yau sai kwanan prison tunda ta tabo shalele,yaron da yake jinsa kamar ransa, tana nan tsaye tana ta faman kaiwa da kawowa saiga umma barira da daya daga cikin securities din gidan itama ya kawota hankali atashe,
"Sa'adatu..... Me yasamu Aryan din? Ni natashi daga bacci na duba naduba ban ganshi ba sai da nafito nemansa wai ko yafita karatu sai suke fada min kun taho asibiti, me yasameshi?"
"Umma faduwa yayi yabuge da kujera,wallahi babu abinda ya sameshi bayan wannan...."
Kafin umman tasake magana sai ga Dr Al'amin yafito,
"Insha Allah nan da anjima ko zuwa dare zamu iya barinku ku tafi gida saboda ya farfado dama ba wani abu bane furgici ne da tsoro da ya shigeshi shi ya haifar masa da wannan suman amma insha Allah babu komai zai tashi normal..."
Sai lokacin Hanan taji hankalinta ya dan kwanta ta samu yar nutsuwa da taji cewa bai mutuba yana numfashi,umma kuwa ai arikice take dan kallo daya kadai zaka yimata ka fahimci hakan,tana dai tsaye ne kawai amma hankalinta yagama tashi,
Wurin Aryan din suka shiga suka iskeshi yana bacci amma ga numfashinsa nan yana fita yanda ake bukata, dukkansu jugum suka yi babu wanda yake cewa uffan har tsawon wani lokaci. Koda Aryan din ya tashi jikin umma yaje ya boye yana leken Hanan cike da jin tsoronta, murmushi Hanan tayi masa idanuwanta jajur sanadiyyar kukan da tayi,
Hannu ta mika masa, "Zo mana cutie"
Kin zuwa yayi har suka tafi gida yana nanuke da umma suna zuwa gida suka iske miss calls din Khalil yafi abinda yafi yakira Aryan yakira umma saboda tunda yakira Aryan yaji bai sameshi ba yakira umma yaji ko lafiya ita dinma shirun yaji,
Hanan kam sai sake shiga jikin Aryan take tayi tana son yaron yasaba da ita yadaina tsoronta yasake da ita kamar kowa tunda lalura tashigo ciki dan a mota har suka zo gida umma nabata labarin dama haka yake yi tun yana jariri idan yayi kuka yayi kuka sai kajishi difff yasuma shiyasa uban baya son bacin ransa,
Chocolate ta debo masa irin wadan taga umma na bashi idan zai tafi makaranta, "Cutie zaka sha wannan?" Girgiza mata kai yayi alamar a'a da tace yazo yakarba sai ya makale kafada yahaye kan cinyar umma,
Bata hakura ba taje ta zubo masa tuwon semovita miyar egusi wanda ke cikin fridge a ajiye saida ta dumama masa sannan ta zubo cikin plate ta kawo inda yake zaune yana ta danne danne awayarsa yaran yanzu kamar da ilmin danna waya ake haifarsu saboda yanda yaketa latsa wayar sai ka rantse babba ne,
"Cutie zo inbaka tuwo kaci kaji...."
Kallon umma yayi sannan ya kalleta,make kafada yayi,
"Ni umma ce zata bani"
"A'a ni zan baka yaron kirki dan babansa,zo kaci kaji,akwai dadifa tuwone ko incinye abuna? Kaga zan cinye to..."
Kamar baya son zuwa haka ya sauka daga kan cinyar umma wacce ke cemasa maza yaje yaci,tafiya yake kamar yana taka kwalba ahaka yaje wurinta,murmushi tayi ta dorashi kan cinyar ta tafara bashi abaki yana ci,tashi umma tayi tabarsu tashiga daki tana waya da Khalil wanda ya kara kiranta tana dauka tajishi arikice,
"Umma meya samu Aryan ne? Na kira aka ce mun kunje asibiti..."
"Waye yafada maka Aryan muka kai? Matarka muka raka kanta na ciwo kuma tasamu sauki"
Ajiyar zuciya taji yasaki mai karfi,
"Allah yabata lafiya,yanzu ina Aryan din?"
"Gashi can tare da ita afalo tana bashi abinci"
"Ok to bari na kirashi"
Suna zaune tana ta bashi tuwon yana ci yana game din Disney magic awayarshi amma yafi maida hankali kan game din haka dai take ta lallaba shi tana bashi,kiran Khalil ne yashigo sai jinsa tayi yana fadin,
"Papa...."
"Na'am Aryan...."
Bata jiyo maganar uban ta iya Aryan take ji kawai,
"Ina kaje dazu na kiraka baka nan?" Khalil ya tambaya dan son tabbatar da gaskiyar abinda daya daga cikin securities din yasanar dashi,
"Munje asibiti nida umma da Mommy"
Wani sanyi Hanan taji jin ya kirata da mommy ashe haka iyaye ke jin dadi idan 'yaya suka kirasu da wannan sunan?
"Shikenan naje gombe idan zan dawo me zan kawo maka?"
"Yogurt....."
"To shikenan sai nadawo"
Katse wayar yayi yajuya ya kalleta, "Na koshi"
Murmushi tayi ta shafa kansa, "Daure ka cinye dai cutie nah"
Karba yayi taci gaba da bashi har sai da ya cinye din sannan ta d'aukeshi suka haura sama, dakinshi ta kaishi tayi masa wanka ta sake daukoshi zuwa cikin dakin ta zauna ta shirya shi yasha turare,pink din riga t shirt ta saka masa da bakin jeans ta daura masa belt,akan cinyarta ta dorashi tana gyara masa sumarshi,
"Kai wai ba a yimaka aski ne cutie?"
Jijjiga mata kai yayi alamar a'a baya so,dariya tayi ta d'aukeshi suka fita zuwa falonta,carton ta kunna masa a tv dinta itama tashiga ta watsa ruwa ta fito, doguwar riga ta saka marar nauyi sannan ta dawo wurinsa bayan ta dauko robar ruwa,
"Mommy Daddy yace min kin mutu...."
Cak ta tsaya daga shan ruwan da takeyi ta kalleshi tabbas yataba fada mata haka,
"Yaushe Daddyn ya fada maka" ta tambayeshi tana janyoshi jikinta,
"Da dadewa ya nuna min wani hoto yace na mamata ne awurin haihuwata ta mutu bayan an fito dani mu biyu sai dayan ya mutu itama mommyn sai ta mutu sai ni dashi kadai....."
Hawaye taji yana kokarin zubo mata wanda bata san ko na menene ba amma tausayin yaron taji akaro na farko sannan taji tana nadamar abubuwan da tayiwa yaron na rashin jansa ajikinta da sakar masa fuska, Allah sarki maraya,
"Kuma sai naganki a school...."
Shafa kansa taci gaba dayi cikeda tausayinsa tana jin kaunar yaron na sake shigarta ta ko wacce kafa. Ranar tare dashi suka kasance har lokacin bacci yanata bata labari da yake yaro ne mai wayo da surutu,bacci ma adakinta yau yayi ta kwantar dashi
Misalin karfe 1:30 Khalil yadawo daga gombe kuma basu zarce ko inaba sai sabon gida domin yazowa da Aryan da tsarabar da yace yakawo masa. Agajiye yake lilis dan kana kallonsa ma zaka fahimci hakan,cikin fridge yasaka masa su fura da nonon daya kawo masa sauran kayan kuma sai yadora musu kan dining,duk da yasan Aryan din yayi bacci amma haka yanufi dakinsa,amma yana shiga yaga wayam baya ciki,gabansa ne yaji ya fadi nan yafita agigice da kamar yashiga dakin umma sai kuma yasake komawa sama ya nufi falon Hanan wanda bai taba shiga ba sai yau,
Wani kamshi ne mai sanyaya zuciya da narkar da ita gamida saukar mata da nutsuwa ya bakunci hancinsa dayake turaren wutar da take amfani dashi mai masifar kamshi ne daya daga cikin irin gudunmawar da anty badi'a ta kakkawo mata,sai da ya lumshe idanuwanshi sakamakon irin kasalar da kamshi da sanyin falon ya haifar masa dashi, kofar bedroom din nata yabude zai shiga amma duhu didim babu haske ko kadan...................鉁嶏笍
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:08 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*
*22*
***Bai kokalleta ba kai da alama ma kamar bai san tashigo cikin dakinba domin shi ta lafiyar dansa yake yi gaba daya hankalinsa na kansa,
Tana tsaye tana kallonsu shida Dr Al'amin wanda keta kokarin kwantar masa da hankali ta hanyar yimasa bayanin cewa wai jikin Aryan dinma ai da sauki akan yanda aka kawo shi,shi dai Khalil duk bai gamsu ba domin irin yanda yaga ramar da yaron yayi sannan duk yafige yayi wani iri kamar wanda ya shekara yana jinya gara kawai yafita dashi waje aje can adubashi, sakin hannun Aryan din yayi yajuya suka fita shida Dr Al'amin domin Aryan bacci yake tayi. Awaje ya tsaya wurin su umma da hajiya yana yimusu bayanin gaskiya daga yau zuwa gobe zai fita da Aryan k'asar chairo ko India domin lalurar yaron ta tayar masa da hankali,wuri hanan tasamu ta zauna kamar wata munafuka sai faman rabe rabe takeyi,
"Banki ta takaba Khalil amma da dai ka dan sake basu lokaci nan din tukunna dan ni wallahi bana son harka da turawan nan,nan dinma likitocinmu babu abinda basa yi sai dai ko da yake ku kuna dashi shiyasa fitar bata yimuku wahala...."
"Shikenan hajiya amma fa duk kiduba kiga yanda Aryan yakoma..."
"Hakane,mudai muyi fatan Allah yabashi lafiya"
"Amin hajiya,bari naga Dr Al'amin"
A office ya iske Dr Al'amin yanata yan rubuce rubuce ajikin file din Aryan,abunku da dan jarida zama yayi ya tsare Dr Al'amin da tambayoyinsa masu zafi wadanda sunfi guda goma daga wannan sai wannan daga karshe yatashi yafita yasake komawa wurin Aryan, Hanan na zaune gefensa ta rafka uban tagumi,atsaye ya tsaya kyamm yanata faman safa da marwa hannuwanshi goye a bayansa,ta gefen ido take kallonsa wallahi ba dan kar tayi karya ba sai tace bata taba cin karo da halittar da ta dauki hankalinta kamar tashi ba,bata taba ganin namiji mai kyau da kwarjini da kuma cikar haiba kamarsa ba. Gaba daya ta raja'a a kallonshi bata ko kiftawa yayinda shi kuma hankalinsa kacokan ya tafi kan abinda yadace yayi wurin samowa Aryan lafiya baima san tanayi ba domin hankalinsa ba akanta yake ba dan baiko san da itaba awurinma,
Tunda yazo bai matsa ko nan da canba salla kawai ke fitar dashi,har lokacin magriba yayi,lokacin su hajiya suka dawo asibitin itada Zaid ita kuma Hanan suka tafi gida ita da umma barira,tun acikin mota take jin zuciyarta na addabarta da tunaninshi wanda bata taba jin irin hakanba akan wani namiji a iya tsawon rayuwarta,daga kallo daya da tayi masa duk tabi ta rikice ta gigice ta kuma dimauce,
Kasa katabus tayi kamar wacce aka zarewa laka daga jikinta motsi kadan sai taga fuskarshi ko shi kanshi yana kaiwa da kawowa cikeda damuwa a dakin da Aryan yake,ji take yi kamar ta koma taje taci gaba da kallonsa babu ko kiftawa,haka dai tasamu tayi bacci sama sama amma bawai cikakken bacci mai cike da nutsuwa ba,washe gari da sassafe ta tashi ta shirya ta hada breakfast din da John yashirya acikin basket wanda zata tafi dashi asibiti ita da umma, Arabian gown ta saka pink colour tayi rolling tasa hill sannan suka tafi PA yajasu, tunda suka shiga suka san abu yasake rikicewa domin Aryan sai razana yake kamar wadanda Aljanu suka shafa abun dai babu dadin ji gaba daya uban yashiga wani hali.
Abu kullum gaba yake kara yi duk Aryan yabi yayi wani irin baki kamar bashi ba,cikin sati daya kacal yazama duk wani iri baya ko iya tashi zaune ga firgita da yake ta faman yi ko bacci yake yi sai aga yanata firgita hakan yasa hajiya cewa su tattara su koma gida dan da alama wannan ciwon ba ciwon asibiti bane dan haka suje gida ayi magani,suna komawa gida aka fara maganin gida amma duk shi dinma jiya iyau Khalil kam ba acewa komai domin karshen tashin hankali ya shigeshi,
Waya Hanan tayiwa abbanta ta sanar dashi lalurar Aryan nan yafada mata duk abubuwan da yadace tayi kafin yasamu yazo,
Dakin Aryan ta nufa bayan tagama wayar da abbanta ta iske Khalil zaune gefen Aryan wanda ke kwance yayi baki sosai, tunda yazo k'asar ko kalma daya bata taba hadasu ba sai yau dinnan,
Durkusawa tayi agabansa kanta a kasa tace,
"Abban Aryan nayi waya da abbanmu kuma na fada masa irin lalurar da Aryan ke ciki yace asamo ruwan zamzam sai ahada da ruwa inkaranta masa ayoyin warware sihiri sai abashi yasha sannan ashafe masa jikinsa dashi dan abisa dukkan alamu sihiri ne....."
Baice mata komai ba sai kai da ya daga mata,nan take yaciro wayarshi ya turawa da Zaid massage akan yaje yasamo pure zam zam mai kyau ba fake ba,tashi hanan tayi takoma bedroom dinta taje ta dauko littafin ta na ayatusshifah,tana zaune tana duddubawa Zaid ya leko yasanar da ita yakawo zamzam din, magunguna kam Aryan na shansu dan gasu nan jarka jarka anata kawowa daga wurare daban daban,
Cikin babban jug ta zuba zamzam din ta hada da normal bottle water ta dauka ta kakkaranta ayoyin karya sihiri kamar yadda Abba yasanar da ita bayan ta gama ta mikawa Zaid, shida Khalil suka daga Aryan suka bashi yasha sannan suka shafe masa jikinsa dashi tas,tun atake awurin suka fara ganin alamar sauki domin yabude idonsa harda yin magana yana kiran Daddyn sa duk da maganar bata wani fita sosai. Tunda Hanan taga haka sai suka mayar da ruwan wannan addu'ar yazama shine ruwan shan Aryan kuma alhamdulillah sauki yana samuwa dan ana ganinsa,bayan kwana biyu Abban Hanan yazo duba Aryan sannan yataho masa da wasu magungunan irin na musulunci musamman na karya sihiri,dama yan dubiya kam suna shansu dan kullum gidan baya rabo da baki yan zuwa dubiya danginsu Khalil kuwa kusan babu wanda baizo ba,
Mamaki ne ya lullube Hanan saboda ganin yanda abbanta da Khalil keyi tamkar wasu abokai,yau shine karo nafarko da zata shiga sashen Khalil wanda tun bayan dawowarsu daga asibiti yakoma can tunda dama ashirye yake babu abinda ba asaka ba shine dai kawai baiga damar dawowa ba sai yanzu da Aryan baida lafiya sannan yadawo dan aganinsa Menene amfanin shi yana gabas dansa yana yamma baya ganin motsinsa,
Fruits da drinks ta jera cikin farantin silver ta dauka ta nufi sashen oga,suna daga ciki suna hangota tana tahowa amma ita bata ganosu sakamakon daga waje glass din mai duhu ne taciki kuma mai haske ne sosai kana kallon na waje tsaff,riga da zani ne ajikinta na atamfa tasaka hijabi,hanan taso tayi kauyanci domin bata san ta yanda zata bude kofar falon nashi ba tana tsaye da faranti a hannunta yataso da kansa yazo ya bude mata bata hanya yayi tawuce ciki sannan ya rufe kofar yabi bayanta,agaban abbanta ta dire farantin tana jin wani farin ciki yana mamaye ta tare da kaunar mahaifin ta wanda tasan har duniya tatashi banda Allah babu wanda zaiyi mata ko rabin gatan da yayi mata,tashi tayi tanufi kofar fita tana zuwa ta danyi tsamm da ranta tana kallon madannan dake gefen kofar bawai dan ta saniba kawai tayi shahada ta danna green din nan take taga kofar ta bude,kasa ta sauka taje ta harhado abinci kala daban daban wadanda John ya dafa saida ta dauko komai sannan ta sake komawa, yanzun ma shine yataso yasake bude mata sannan ta shiga, fruits din da ta kai musu ta iske suna sha da fork kowannensu,
Sunkuyar da kai tayi ta soma gaida abbanta wanda fuskarshi ta cika da fara'a dan bakinsa yaki rufuwa,
"Lafiya kalau uwar masu gida,mun sameku lafiya ko? Ya jikin yaron naki? Allah yabashi lafiya, Allah yasa takin arzikine"
"Amin Abba"
Magungunan da yazo dasu yafirfito dasu wadanda yawancinsu da zuma da zaitun da habbatussauda aka hada yana yimusu bayanin yanda zasu yiwa Aryan amfani dasu,sai bayan da yagama yimusu bayanin sannan ya kalli Khalil wanda ke sanye da farin yadi tsadadde dinkin boda yace,
"Dama ahar kullum ina fada maka yaron nan sai shima ka kula dashi da addu'o'i da zikirin safiya da maraice,wani abun idan kai anyi maka aka ga bai sameka ba to za a iya komawa ayiwa danka,kai kam bani da jaa akanka kana da kariya sosai atare dakai saboda duk wanda yayi riko da ibada ya tsaida salla kuma ya kiyayeta sannan yake yawaita tsayuwar dare da sadaka kuma yabi iyayensa to babu mahalukin da zaiyi nasara akansa sai dai makiya su gaji su barshi dan yafi karfinsu to amma shi sulaimanu ai kaga yarone dole sai ankula dashi, Allah yabashi lafiya kuma insha Allah nasamo bakin zaren,insha Allah zai samu waraka,sihiri ne akayi masa kuma mace ce tayi amma idan nace gata to nayi karya,amma tabbas mace ce dan naganta acikin mafarki,wato kasan wani sihirin akwai addu'ar da akeyi ayi salla raka'a biyu to Allah yana haskawa mutum inda aka yimasa sihirin idanma binnewa akayi duk za anuna maka wurin...."
Daga Hanan har Khalil jikinsu ne yayi sanyi Sosai, Hanan aranta cewa takeyi wannan wanne irin rashin imani ne da mutum zai nemi halaka dan tahalikin yaron da baiyi masa laifin komai ba? Ita kuwa wannan matar me Khalil yayi mata da har take kokarin hucewa akan dansa? Kwalla taji ta ciko mata ido bata gogeba saida tabarta ta sauka,
Shi kam Khalil shiru yayi yana tunanin to wacece wannan? Zuwa caan ya sauke ajiyar zuciya ya tankwashe kafafuwanshi yana lankwasa yan yatsun kafarshi domin yagano ko wacece, Abba ne ya kalli Hanan sannan yace,
"Yanzu kiyi azamar zuwa kibashi magungunan nan yasha sannan ki shafe masa jikinsa da wadannan mayukan,insha Allah zai samu waraka"
"Toh Abba"
Tashi tayi ta dauki maganin tafita,sai bayan da ta fita sannan Khalil ya kalli Abba yace,
"Nagode madallah malam, Allah yasaka maka da alkhairi,kuma ba dan kar kace nayi zargi ba wallahi har nagano wadda tayi min wannan abun...., bazai wuce yesmin ba,tajima tana bibiyata kuma ita ba da aure take sona ba a'a da sabon Allah nikuma ba halina bane,babu wanda bai san zaman kanta take yiba...., Yanzu last zuwan da nayi Denmark sai da tabini hotel din da nasauka....."
"Ai shiyasa nake fada maka dole sai ka dage da addu'a da rokon Allah saboda mata iri iri zasuyi ta kawo maka farmaki sai dai Allah ya tsareka ya kareka daga kaidinsu...."
"Amin" yafada yana sunkuyar da kanshi kasa,shi dai Abba cigaba da bashi shawarwari yayi ta yi yanda zai cigaba da neman tsari daga kowacce irin mace. Hanan na zuwa dakin Aryan ta samu hajiya da umma atare dashi,sune suka taimaka mata tabawa Aryan magungunan yasha sannan ta shafe masa jikinsa da wadanda abba yace mata na shafawa ne,kuma sauki kam ana samu sai godiyar Allah dan ko minti 20 baiyi da shan maganin ba yace zaici abinci wanda rabon da yaci anjima,abinda yake son ci Hanan ta tambayeshi yace shinkafa dama akwai shinkafa acikin abubuwan da John yadafa yau dan haka ta sauka da sauri taje ta zubo masa a plate ta kawo,itace ta zauna ta bashi abaki kuma babu laifi ya dan ci dayawa daga nan bacci yakoma ita kuma tafita taje d'akinta tayi wanka sannan tayi sallar la'asar,wurin Aryan ta sake komawa tasamu suma su umma har lokacin suna tare dashi yatashi daga baccin da yake yi yanata game a wayarshi, gefenshi ta samu ta zauna ta dora kanshi saman cinyarta tana tofa masa addu'a ahaka Khalil yabude kofa yashigo ya samesu ganin Aryan yana game yaji dan sanyi sanyi acikin ransa,hannu yakai saman goshin Aryan yace,
"Sannu abba na,jiki yafara sauki ko?"
Kai Aryan ya daga sannan yace,
"Uncle zaka tafi dani Italy ko?"
"Zanje dakai duk inda kake so abbana, Allah dai yabaka lafiya"
Daga haka yajuya yafita yakoma wurin Abban Hanan wanda ke can yana jiranshi, ita kuwa Hanan tana wurin Aryan har magriba tayi dan anan ma dakin Aryan tayi sallah tana idarwa taji shigowar text cikin wayarta,
_Kizo abbanki na kiranki._
Shine abinda taga minister yaturo mata tashi tayi tafita saida tafara shiga bedroom dinta ta shafa turare sannan tafita tana sanye da doguwar riga yar kanti da farin hijab ajikinta, tsayawa tayi bakin kofar tana wurwurga ido shin ina zata taba? Jan ta danna sai kuwa kofa tabude,ahankali cikin nutsuwa take takawa har zuwa cikin hadadden falon nashi wanda yafi kowanne falo dake gidan haduwa,komai nashi farine tas babu sirki,hatta Rug din dake shimfide a tsakiyar falon farine sai dai an diddiga masa kalar baki dan sake fito dashi,falon tafkeke ne na gaske amma sai dai babu tarkace masu yawa acikinsa,iya kujeru ne wato (Turkish Sofas) farare guda biyar sai glass tables manya da kanana an a'ajjiye su a muhallin da yadace dasu sannan ga kayan kallo manya manya sai fridge acan gefe daya sannan ga dining table da yan kujerunsa kwaya hudu shima farare acan gefen dama,daga gefen hagu kuma wasu fararen kujerunne kwaya biyu masu laushi an ajiyesu da farin Rug dan karami a tsakiyar su sai center table atsakiya,kai falon dai yayi ba karya kuma ya hadu karshen haduwa,ga toilet nan aciki sannan sai kofar bedroom dinshi agefe ta can bangare daya kuma kofar da zata sadaka da valcony ce wadda aka shiryata domin hutawa dan yanzun ma haka su abba acan suke suna hira,
Hanan tsaye tayi domin bata san inda zata nufaba, maganar su tajiyo suna kokarin shigowa,
"A'a ashe ma ga mai babban sunan har ta karaso"
Tajiyo muryar Abba yana fada cikin raha shi dai minister bata ji me yace ba, Abban ne yafara shigowa ya nemi wuri ya zauna sannan itama ta zauna akasa tana sunkuyar da kanta,
Sake sabuwar gaisuwa sukayi da abba sannan suka cigaba da hirar gida wanda ba karamin dadin hakan Hanan tajiba shi kuwa Khalil har har lokacin yana valcony yana shan iska daga Allah bai shigo falonba sai da yaji ana kiran sallar ishah, Hanan tasake sosai da abbanta yashigo,dan satar kallonsa tayi taganshi sanye cikin wasu kayan wadanda ba na dazu ba saboda yanzu milk colour din shadda ce ajikinsa sai kyalli takeyi dinkin half jamfa yayi kyau yayi kyau har ya gaji,
"Bari muyi salla ko..." Taji abbanta yafada,tashi tayi tana fadin,
"To Abba,bari naje na kawo muku abinci"
Fita tayi sukuma nan cikin falon suka tada kabbarar sallarsu ita kuma tawuce kitchen taje ta zuzzubo musu abincin da aka shirya na dare,suna salla duk ta kawo ta ajiye musu sannan tafita.
Bata sake komawa sashen minister ba sai wurin karfe 9 shi lokacin ma yana d'akin Aryan tare dashi dasu hajiya yadora Aryan din asaman cinyarsa yana yin game awayarsa,bata ga abbanta ba sai kayan kawai ta debo ta fito dasu tasan watakila abban yana masaukinsa dan dakyar ma ya yarda zai kwana da cewa yayi ayau zai koma,
Dakin Aryan ta shiga inda su hajiya ke ciki itada umma dakin gauraye da kamshin turaren Khalil na no 1 wanda ya mamaye dakin gaba daya,sai bayan da ta rufe kofar dakin sannan idanuwanta sukayi arangama dashi zaune dare dare bisa kan gadon Aryan ga kuma Aryan din akan cinyarshi,zama tayi gefen umma tana satar kallon Khalil wanda ke cikin blue din riga ta polo sai dogon blue din wando mai santsi,kamar lokacin da tafara ganinsa yanzu ma shagala tayi da kallonsa yana ta yiwa Aryan wasa wanda ke yin game,
"Mommy zan sha ruwa..." Taji Aryan yafada,
Tashi tayi ta dauko masa ruwan maganinsa wato ruwan addu'a taje ta mika masa,karba yayi yatashi zaune yasha sannan yakoma ya kwanta,ayanda ta lura Khalil ba mai yawan magana bane domin idan aka bata dama tsaf zata kirge adadin maganarsa tun shigowar ta dakin,iya umma da hajiya ne kawai ke ta hirarsu. Sai da Aryan yayi bacci sannan Khalil yafita,bayan fitarsa da yan mintuna itama tafita ta nufi bedroom dinta,shirin bacci tayi ta kwanta tana lumshe idanuwanta cike da begen Khalil....................鉁嶏笍
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:08 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*
*21*
***Khalil na kwance kan gadonshi adakin hotel din da yasauka yana kallon pics din birthday din Aryan duk da baya nan aka gabatar da party din amma zaid yayi kokari kamar yana nan saboda yanda aka shirya abin cikin kyau da tsari bugu da kari kuma gashi yaga fuskar Aryan cikin farin ciki sosai hakan kadai da yagani yaji inama shima yana wurin ko kuma inama zai iya yin fuffuke yatashi da yaje anyi dashi,har yagama kallon pics din baiga Hanan ba koda yake ai ba saninta yayiba kuma ta yuyuma babu ita awurin.
Hanan kam har washe gari ma bata samu fitaba dan har lokacin bata jin dadin jikinta tadai shirya Aryan ta hada masa komai yatafi school,kuma har yaje yadawo tana kwance a bedroom dinta tana kallon hotunanshi dake cikin wayarshi wadanda sunfi dari,kuma duka nashi ne shi kadai bata ga na babanshi ba duk shi kadai ne akasashe daban daban gaskiya yaron nan ya zagaya duniya domin tun baifi shekara biyu ba ta ga uban yafiffitar dashi manya manyan k'asashen labarawa da na turawa dan wasu hotunan ga larabawa nan wani kuma turawa zaka gani gasu nan dai burjik wani kuma a saudiyya ne dan ga ka'aba nan da sauran kyawawan wurare dake cikin birnin k'asar,ta shagala sosai da kallon hotunan shiyasa har Aryan yadawo bata saniba tana ta kallon hotunanshi shida wasu yara kyawawa suma guda biyu kamarshi mace da namiji taji shigowar Aryan yana zuwa ya haye kanta kamar yadda yasaba, rikeshi tayi tana murmushi,
"Welcome back my Cutie..."
Kankameta yayi suna dariya pic dinshi da yaran nan ta nuna masa tana tambayarshi suwaye wadannan sai yace mata wai nawwar ne da Naina yaran Abba Khalid wai yan uwanshi ne, lallabawa tayi ta tashi taje tayi masa wanka bayan ta cire masa uniform dinshi tabashi abinci yaci sannan yafita islamiyya wurin malaminsa.
Bayan birthday din Aryan da kwana biyu Zaid yakoma gombe yanzu gida yarage sai iya Hanan da Aryan da umma barira,duk wani abu da yashafi Aryan yanzu Hanan ce keyi masa itama shagwabashi yanzu takeyi sosai wanda har Khalil yasan da haka dan komai sai Aryan yace masa wai mommyn shi ce tayi masa idan abinci ne sai yace itace tabashi shi kansa yasan tana kulawa da yaron Sosai ba kadan ba.
***
Har yanzu sumayya bata samu ta shawo kan mujahid ba domin kullum cikin wulakantata yake yauma hakance tafaru tana daki tana ta sharbar kuka mami ta shigo ta zauna gefenta,cikin lallashi tace,
"Sumayya daina kuka kinji,yi hakuri,ki daina sakawa kanki damuwa akan mujahid kedai kawai kici gaba da addu'a idan har mijinki ne babu makawa sai ya aureki....kiyi shiru kinji"
Kai ta daga alamun to,haka mami taci gaba da rarrashinta daga karshe ta tashi tafita,tana fita ta dauki wayarta ta kira k'awarta muhibba ta zayyane mata dukkan abunda yake faruwa sannan cikin kuka ta karasa maganar tata da fadin,
"Muhibba da me Hanan tafini da yake wulakanta ni akanta bayan ma tayi aurenta ita ta manta dashi amma shi kullum cikin kallon hotonta yake...."
"Babu da abinda tafiki sumy,ki kwantar da hankalinki kiji abinda zan fada miki....."
"Ina jinki muhibba"
"Yawwa kema ki shareshi ki fita harkarsa kuma ki daina kulashi,ki nuna masa idan dashi ko babu shi zaki iya rayuwa,ki shareshi fa sosai dan shima yana sonki bawai ke kadai ke haukan sonshi ba saboda duk wanda kake so wallahi shima yana sonka sai dai ko wani dalili ya hanashi bayyanawa amma dan so shima yana sonki,ki danne zuciyarki ki shareshi shi da kansa zai sauko"
Shawarwari sosai muhibba tabata kan yanda zata share ya mujahid har sai yakawo kansa da kanshi,ita dai sumayya ji take yi kamar bazata iya ba saboda irin yanda a kullum wutar son mujahid ke ruruwa a cikin zuciyarta gashi shi kuma yayita disgata agaban kowaye babu ruwansa dazu fa agaban yan aikin gidan yayi mata rashin mutunci dan kawai tashiga dakinsa abinda yasata kuka kenan amma insha Allah zata danne zuciyarta tabata hakuri ta gwada aiki da shawarar muhibba.
***
Bayan birthday din Aryan da sati daya Khalil yadawo nan yakawowa Aryan tsaraba mai tarin yawa ta takalma da jeans da t shirts masu tsada,
Kullum baya shiga gidan sai cikin dare misalin karfe 1 ko 2 wani lokacinma har 3 dan sai kowa yayi bacci agidan,bai jima da dawowa ba yasake komawa k'asar Italy amma kullum suna makale awaya shida Aryan wanda ada yamakale masa wai sai yabishi dakyar ya shawo kansa ta hanyar cemasa ankusa yin hutun makaranta ana yin hutu zai fita dashi duk k'asar da yake so.
Khalil baifi sati daya da tafiya ba Aryan yawayi gari da wani zazzabi mai zafi ga tari da ciwon kirji babu shiri aka kira Dr Al'amin yana zuwa da yadubashi yace su tafi asibiti dan dole sai ya kwantar dashi,
Asibitin suka tafi dukkaninsu cike da damuwa da tashin hankali ita kam umma ma kashe wayarta tayi dan kar Khalil yakirata haka ta Aryan dinma arufe take,kwantar dashi Dr Al'amin yayi yafara bashi taimakon gaggawa,
Aranar da yamma sai ga Zaid yazo kamar yanada masaniyar abinda ke faruwa,can asibitin yabisu dan ajikinsa ma aka debi jinin da aka karawa Aryan din,
Khalil shi bai san abinda yake faruwa ba amma haka kawai yaji jikinsa duk babu dadi kamar irin baida lafiya dinnan alhalin kuma shi lafiyar sa kalau amma dai jikinsa yayi masa wani irin sanyi kalau haka dai ya daure yaci gaba da al'amuransa wadanda suka kaishi,
Yana ta kiran Aryan awaya kuma baya samunshi haka itama wayar umma bata shiga daga karshe sai Zaid ya nema dan jin meke faruwa amma sai Zaid ya ce masa wai babu komai da ya tambayi Aryan sai yace bacci yake yi,cewa yayi to ya gaidashi shida umma sukayi sallama,
Duk dangi kuwa babu wanda bai san rashin lafiyar Aryan ba Khalil kadai aka boyewa saboda ba ason afada masa saboda kar hawan jininsa ya motsa,tun a washe garin ranar da aka kai Aryan asibiti hajiya tazo Abuja suna tare a asibitin suna kula dashi,
Zaid kuwa sai hanya hanya yake yiwa Khalil idan ya kirashi yace ya hadashi da Aryan sai yace yana toilet ko yace yana bacci ko kuma yace wai yana makaranta,da Khalil ya tambayeshi to me yasamu wayar Aryan din da yasa baya samu idan yakira sai yace wai ai swimming pool tafada a hannun Aryan shiyasa ta daina yi nan Khalil yace masa to idan yadawo ya daukeshi suje wurin siyar da wayoyi ya siyo mishi duk wacce yakeso komai tsadarta da toh Zaid ya amsa masa sukayi sallama suna yin sallama yakashe shima tashi wayar gaba daya.
Yau kam tashin hankalinsu yafi na kullum domin tunda garin Allah yawaye Aryan yake ta faman suma daga safe zuwa yamma ya suma yafi sau biyar,shi kansa Dr Al'amin yagama shiga tashin hankali saboda yanda jikin Aryan yarikice Sosai,
Hanan shawara tayi da zuciyarta bata sanarwa da kowaba aranta tace gara ta fadawa Khalil abinda ke faruwa tunda boyewar bata da amfani da afada masa mutuwar dansa gara afada masa rashin lafiyarsa yazo ya ganshi kar aje yamutu,
Text massage ta tura masa tana turawa ta kashe wayarta itama, Khalil na kwance yakasa bacci dan a yan kwanakin nan sam baya iya bacci gashi dai lafiyarshi kalau amma kamar baida lafiya yake jinsa,jin shigowar sako yasashi kallon agogo,karfe 3 da kusan kwata dan asubah ma ta kusa,daukar wayar yayi yabude sakon nan yaganshi kamar haka,
_Abban Aryan kazo gida domin Aryan ba lafiya muna asibitin Dr Al'amin._
Yana gama karantawa yaji yashiga cikin tashin hankali,acikin wannan daren yafita akayi cuku cukun jirgin da zai tashi da asubah zuwa Nigeria,bai dauki komai ba sai wayoyinshi yanufi Nigeria.
Kamar yadda babu wanda yasanar dashi rashin lafiyar Aryan shima babu wanda ya fadawa cewa yabaro Florence yataho Nigeria har saida jirginsu ya sauka sannan yakira PA yace yazo ya d'aukeshi,
Kai tsaye asibitin suka wuce PA ne agaba sai securities dinshi abaya shi kuma yana tsakiyarsu,
"Ni wallahi bana son yaron nan Khalil yaji maganar nan saboda hawan jininsa" umma barira tafada cikin damuwa domin dukkansu suna waje su hudun zaune kofar dakin da Aryan ke ciki kan wasu kujerun karfe wadanda aka tanada awurin domin zama,
"Ai gashi nan ma dan halak" Zaid yafada yana mikewa tsaye,
Hanan kam kanta asunkuye yake ta dunkufar dashi bayan tasha kukanta ta more dan har idanuwanta sunyi jajur ga shi sunyi luhu luhu,wani arnan kamshi ne yafara kaiwa kofofin hancinta sumame wanda ya tilastata ta dago kanta domin ganin mamallakin wannan kamshi,
Dakatar da securities din nashi yayi yakarasa wurinsu umma shi kadai,ai Hanan ji tayi tai suman zaune, dama wannan shine minister? Shine mahaifin Aryan? Shine abokin Abbanta? Mamaki ne ya mamaye dukkan ilahirin zuciyarta domin bata taba zaton zata ganshi hakaba kyakkyawa mai cikar halitta da kwarjini ba,kamarshi daya da Aryan da Zaid amma duk ya kere su a kyau domin farine kal dogo Sosai dan har ya dan rankwafa ma'abocin bakar suma wuluk mai matsakaicin jiki, fuskarshi dauke take da manyan eye balls farare tas ga hanci kamar biro bakinshi kuwa dauke yake da lips masu taushi suba red ba kuma su ba pink ba akwai saje a fuskar tashi wanda yataho har zuwa habarshi yahade da dan kyakkyawan gemunsa amma bawai buzu buzu da yawa ba a'a dan gwanin sha'awa dashi kuma shine ya karawa fuskar tashi kyau da annuri, kuruciyarshi afili dan sam babu maganar tsufa atare dashi sannan jin dadi da hutu sun sake fito da kuruciyarshi da kyakkyawar halittar shi dan duk da yana yawace yawace baya zama wuri daya amma hakan bai samu nasarar hana jin dadi da hutun da yake ciki bayyana agareshi ba,bafulatani ne na usul daga kallonsa zaka fahimci hakan,samun kanta tayi da nadamar yimasa rashin kunya da tayi abaya ita wallahi ta zaci zata ganshi tsoho kuma mummuna ashe abin bahaka yake ba sai gashi ta ganshi mai kyakkyawar halitta ma'abocin cikar haiba da kwarjini,shagala tayi da kallonsa domin tunda yazo ya dauke mata hankali wanda bata farga ba har saida yagama gaisawa dasu umma yanufi dakin da Aryan ke ciki batare da yako kalleta ba dan shi hankalinsa ma bai kai kanta ba, firgigit tayi daga duniyar da tatafi kamar kazar da kwai ya fashe mata aciki haka ta mike jiki babu kwari tabishi cikin dakin...........鉁嶏笍
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:08 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*
*23*
***Juyi tayi ta dauki karamin pillow guda daya ta rungume acikin zuciyarta tana hango kyakkyawar fuskarshi, murmushi ta saki ita kadai kamar wata tababbiya saboda tuno rashin son hayaniyar shi da tayi ga masifar jan ajin tsiya kamar wata mace wanda hakan ba karamin kyau da kwarji yake kara masa ba,wai meke shirin faruwa da itane? Ta tambayi kanta bayan ta tashi zaune,
"He's cute....." Tafada ahankali bayan ta koma ta kwanta tasake rungume pillow,
"Ban taba ganin namiji dan gayu handsome kamar shi ba" ta sake fada afili tana sakin murmushi,gaskiya Khalil yahadu yahadu irin haduwar da tafi gaban kwatance domin sai wanda idanuwansa yagane masa kawai,juye juye tayita faman yi takasa bacci sai Khalil da take ta faman gani a idon zuci dakyar tasamu bacci ya lallabo ya saceta.
Shima Khalil anasa b'angaren bayan yagama nafilfilinsa lokacin da ya kwanta kasa bacci yayi kawai tunanin abinda yesmin tayi masa yake yi wato ta zabi ta kashe masa d'ansa saboda bata samu abinda take so ba daga gareshi,ita sabon Allah take son ya yarda suyi ta yi shikuma hakanne bazai taba iya aikatawa ba,sau da dama tana zuwa office dinsa amma baya saurararta,gashi dai babbar mace ce amma kuma sam bata da nutsuwa dan babu halin mata na kirki atare da ita gashi abanza tana neman illata masa yaro wallahi ba dan Abban Hanan yabashi baki yace yarabu da itaba da sai sunyi shari'a da ita,bacin rai bai barshi ya runtsa ba sai tsakiyar dare.
Washe gari Hanan da farin ciki ta tashi cikin nishadi tayi wankanta ta shirya cikin riga da skirt na English wears sannan ta saka dan madaidaicin pink din hijabi ta fita lokacin umma na kwance adakin Aryan dama tare suke kwana sai da Hanan ta shiga sannan umma tafita,daga Aryan Hanan tayi wanda zata yiwa brush nan taga abunda yayi masifar tsorata ta har ta nufi kofa da gudu dan kiran umma ko hajiya amma tana bude kofar sukayi gware da Khalil wanda ke kokarin shigowa cikin dakin ganinta da yayi kamar a razane yasashi riketa kamar yanda ta rikeshi,
"Menene...?" Itace tambayar da yayi mata,cikin razani ta nuna masa Aryan jikinta na rawa,
"Wani abune a karkashin Aryan"
Sakinta yayi ya nufi Aryan, shima saida abin yaso tsoratashi domin wata sab'a ce daga jikin Aryan din tafita doguwa sambel kamar muciji bakikkkirin da ita,karasa cire masa sabar yayi yafita aransa yana tunanin wato duk wanda yayiwa Aryan wannan abun da niyyar kasheshi watakila yayi kuma sai Allah bai lamunce masa ba,
Ita kam duk tsoro ya isheta sai sannu take yiwa Aryan,bayan tagama yimasa brush ta zubo masa kindirmo cikin cup ta hada masa da maganin da Abba yace ta rinka hadawa da nono tana bashi da sassafe kafin yaci komai saida ya shanye sannan tafita ta nufi kan dining domin hadawa su Abba breakfast tana tafe tana murmushi sakamakon tuno abinda yafaru dazu da tayi, rikon da mutumin nan yayi mata ya tsaya mata arai,hannunsa masu masifar taushi da laushi kamar auduga. Ita kadai take ta sakin murmushi har tasamu ta gama jera musu breakfast din saman babban faranti,
Sama ta hau ta nufi sashen Khalil,kamar jiya suna zaune shida Abba sai hira suke sha fuskokinsu dauke da fara'a,
Tsugunnawa tayi ta fara gaida Abba sannan ta gaishe da Khalil wanda hankalinsa ke kan wayarshi yana turawa secretary dinshi na office sako,
Dan shiru tayi tana sauraren tattaunawarsu da Abba wadda bata shafeta ba su ta shafa domin bata ma gane kan zancen nasu ba, da gefen ido take satar kallon Khalil wanda ke sanye cikin farin yadi mai laushi wato tissue amma kai daga gani kasan naira tayi kuka domin yanayin yadin ma daban yake,
"Uwata tashi maza kema kije ki karya sai ki dawo muyi sallama saboda tafiya zanyi..."
Idanuwanta narai narai ta mike tafita daga khalil har Abba binta sukayi da kallo bakar body hug ce ajikinta sai purple din skirt wacce ta baje daga kasa,
Tana fita wurinsu umma ta wuce wadanda ke dakin Aryan can takai musu kayan karyawar suka ci domin hajiya ita ba ruwanta duk da cewa tana dan kunyar Hanan din,
Suna zaune su umma nata hira ita kuma ta na shirya Aryan wanda tayiwa wanka kuma dayake yau jikin nasa da sauki da kansa ya taka har zuwa cikin bathroom,
Wayar landline dake ajiye gefen gadon Aryan ce tafara rurin neman agaji, Hanan ce ta dauka tana mamakin to ko waye kuma, shiru tayi batace komai ba caan taji muryar Khalil,
"Zo abbanki na kiranki....."
"Tohm ina zuwa.."
Baice komai ba yakatse wayar, hanzartawa tayi ta karasa shirya Aryan sannan ta fita,
Zaune ta samesu shida abbanta saman kujera suna yin magana amma zuwanta yasa suka bar maganar abba ya fuskanceta yana murmushi,
"Uwata ni zanje inkoma sai ayita hakuri da rayuwa kinji...., Ayita hakuri da duk halin da aka samu kai domin rayuwar gaba dayanta hakuri ce kuma kici gaba da yiwa mijinki biyayya banda sabawa umarninsa,kamar yanda na fada miki abaya ban yarda ki saba masa ba mutukar idan umarnin nasa ba shari'a ya sabawa ba...."
Tuni har kwalla ta ciko idanuwan Hanan tun bayan da Abba yasoma yimata wadannan nasihohin,
"Toh Abba insha Allah zanbi umarninka kuma zan kiyaye su...."
"To Allah yayi miki albarka, Allah yabaki zuri'a kema wadanda zasu yimiki ni zanje inkoma....". Juyawa yayi ga Khalil wanda ke zaune ya tallafe kumatunsa da hannunshi guda daya dayan kuma yana lallatsa wayarshi ba komai kuma yake yiba sai game irin games din da Aryan ke yi idan ya karbi wayarshi,ahaka sai kace ba yajin abinda suke fada amma kuma yana sauraronsu sarai,
"To kai moddibo ni zanje inkoma fa,bako zaiyi halinsa"
Kashe wayar yayi sannan ya kalli Abban Hanan wanda ke kokarin mikewa tsaye,
"Ba zaka sake kwana ba,ai mu bamu gaji dakai ba tukunna"
"Duk da haka gara naje na karasa ai idan nace zan zauna har sai lokacin da zaku gaji dani to ai magana ta baci moddibo"
"To muje kaga Aryan sai mu wuce...."
Hanan na jinsu kuma tunda taga abba yamike tafara sharar hawaye kamar wata karamar yarinya,cikin bedroom dinsa yawuce shi kuma Abba yayi hanyar fita,tana nan zaune tana hawaye sai gashi yafito rike da hularshi a hannunshi,ganinta tsaye tana kuka kuma bata fita ba yazo zai wuce,
"Ko zaki bishi ne?" Shine abinda taji yace kuma bai jira amsarta ba yayi waje abunshi.
Itama bin bayanshi tayi abunka da dogo kamin ta fito har yayi mata nisa,a dakin Aryan ta iskesu Abba nayiwa Aryan wasa ya kama hannunsa yana yimusu sallama ita kam har lokacin kuka take yi,akan idonta Abba yayi musu sallama yatafi,yanzu inbanda aure mai zai rabata da abbanta amma gashi yazo yatafi yabarta,
Tunda Khalil yafita bata kara samun damar ganinsa ba domin duk da yana cikin gidan amma baya ganuwa saboda bakin da yaketa faman yi agida,su kansu cikin gidan kullum cikin baki suke yan dubiya dayawa Hanan ba saninsu tayi ba sai su umma ne da hajiya ke yimata bayanin ko su waye,yan makarantar su Aryan ma sunzo sun dubashi daga students har malaman nasu duka. Yau ma haka suka tashi da bakin daga wadannan sun tafi wasu zasu zo, Abba Khalid ne yau kuma yazo da iyalansa da matarsa Muneerat da yaransa guda biyu Nawwar da Nainah,yau kam Hanan taga su Nawwar din da Aryan kullum ke maganar su kuma take ganinsu a hoto tare dashi,suma yaran kyawawa ne kamar ba yaran hausawa ba koda yake maman nasu kamar irin shuwah shuwah dinnan take sai dai bata da sakin jiki da saurin sabo dan ko magana kayi mata sai dai tayi murmushi ita dai Hanan haka ta sauketa tana ta nan nan dasu shi kuwa Aryan ganinsu Nawwar ai tuni yasake warewa dan har yajasu dakin kayan wasanshi suna can suna fama. Bayan sallar la'asar sun gama lunch kenan ita da Muneerat adakinta ta kwaso kayan zata kai kasa tahango Khalid da Khalil awurinsu Aryan wadanda suka fito da kekunan Aryan suna yi acikin falon, Khalid na fadin,
"A'a lallai sauki yasamu,marar lafiyar nake gani akan keke?"
"Ai nafada maka da kunyi zamanku yasamu lafiya fa..." Khalil yabashi amsa,
"A'a sai munzo mun ganshi ai mun jima bamu ganshi ba dama..."
Hanan karasawa wurinsu tayi ita yanzu ne ma taga Khalil amma yau koda wasa bata ganshi ba inbanda yanzu, kamar kullum yana sanye da farar shadda shi kam da alama yana son fararen kaya koda yake farin abu dama na masu tsafta ne dan kazami bai isa ya saba yanzun nan sai aganeshi,dan dukawa tayi ta gaida Khalid wanda ya riko hannun Aryan yana tambayar shi yajiki,dan juyowa yayi yana amsa gaisuwar tata,
"Lafiya lau madam,ya hakurin zama da wannan sarkin yawon?ki rinka bashi query idan yaki zama agida..." Khalid yafada cikin barkwanci,ita dai shiru tayi ta dan saci kallon Kahlil wanda kamar bai san ma abinda suke fada ba yana tsaye ya dauki Nainah yana tambayar ta wai zatazo hutu suyi wasa da Aryan?
"Ya kuma jikin Aryan? Naga ma ai yasamu sauki to Allah yakara masa lafiya"
Sai lokacin ta amsa da "Jiki ai yayi sauki,amin ya Allah,mun gode madallah"
Juyawa tayi ta koma sama wurin Muneerat duk da ba wata hira zasuyi ba babu jimawa saiga su Aryan sunzo suna kiranta wai tazo inji Abba zasu tafi kar suyi dare ahanya,rasa abinda zata bawa Muneerat tayi sai kawai ta diddibar mata irin humra dinta ta aure acikin kwalabe madaidaita,
A babban falon kasa ta iskesu suna yin sallama dasu hajiya sannan ga kayan dubiya nan anata shigowa dasu wanda Khalid din yakawo kwalayen kayan ciye ciye daban daban da katan katan din lemuka jibgi guda,hannu Khalil yasa a aljihu yaciro rafar kudi yan dubu dubu guda biyu ya mikawa su Nawwar wai susha sweet shima Khalid din duk uban wannan kayan da yakawo sai da yabaiwa Aryan kudi wai yasai alawa bayan gata nan yakawo kaya guda, sallama suka yimusu suka tafi kuma tare suka fita da Khalil din........鉁嶏笍
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:09 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*
*24*
***Tun bayan tafiyar su Khalid Hanan bata kara saka Khalil a idonta ba sai washe gari wannan dinma yana kokarin fita ne yashiga wurinsu hajiya ya gaida su daga nan yawuce office wai yana da meeting din gaggawa da shugabnnin wata k'ungiyar matasa, Hanan na dakin zaune itada Aryan suna cin plantain yashigo wanda tun kafin ya karaso kamshinsa na no 1 yariga shi zuwa,
"Mutumin nan dan gayu ne na ajin karshe"
Hanan tafada acikin zuciyarta domin yayi kyau ba karya cikin farin lallausan yadin dake sanye ajikinsa harda hula amma babu babbar riga ajikinsa,zama yayi suka gaisa dasu hajiya sannan ya mikawa Aryan hannu suka gaisa yana amsa gaisuwar Hanan wacce ke gaisheshi kuma dama gaisuwar bata wuce guda biyu daga ina wuni lafiya shikenan,
Bai jima ba adakin yafita,itama hajiya tun aranar tafara Shirin tafiya domin jikin Aryan yayi sauki sosai kuma sannu ahankali duk farinsa da kamanninsa sun fara dawowa har wata yar kiba yafara yi saboda zaman wuri daya sannan ga kulawa da yake samu daga Hanan dasu umma har kumatu yafara yi,
A kowacce rana Hanan cikin tunanin Khalil take ita kanta tana mamakin yanda tafara damuwa dashi har haka bayan shikuma ba ta ita yakeba domin babu ruwanshi da ita ko maganar shi atakaice take sau da dama idan yana gida suna tare dasu umma sai dai su,su umman suyi ta hirarsu shikuma yayi shiru yana jinsu sai ta kama yake saka baki.
***
Shawarar muhibba sumayya ta dauka duk da tana son mujahid amma haka ta daure tafara shareshi,ko sun hadu a kitchen ko falo ko compound din gidan yi take yi kamar bata sanshi ba ko bata ganshi ba sai takai makura sannan suke gaisawa gaba daya tayi watsi dashi duk da wani lokacin har kuka takeyi saboda irin yanayin da ta samu kanta na son maso wani.
Shi kuma abun duniya ne yataru ya dameshi sakamakon daina ganin text din Hanan da yayi,to ko lafiya? Kodai mijinta yaga irin sakonnin da take turo masa kullum ya kwace wayar tata?
Wadannan tambayoyin kullum su yake yiwa kansa gashi yasaba da ganin massage din nata shiyasa yakasa samun nutsuwa yana jin kamar wani abune marar dadi ya gifta ko kuma ya faru da ita,kullum cikin duba wayarsa yake waiko zaiga sakonta idan kuwa yaji k'arar shigowar text jikinsa har rawa yake yi atunaninshi ko itace sai ya duba sai yaga sabanin haka nanfa abun yayita damunsa daga karshe ya yanke shawarar kiranta duk da yasan hakan haramun ne amma haka yarufe ido ya kirata,har wayar tayi ta katse bata dauka ba nan yasake kira nan dinma no answer saida yakira sau biyar sannan ya hakura ya hada Kai da gwiwa ya rafka uban tagumi.
***
Bayan Sati Biyu
Jikin Aryan yayi kyau kusanma za a iya cewa yagama warkewa gaba daya dan har ana maganar zai fara zuwa makaranta domin ana gab da fara exams,ganin yasamu lafiya yasa hajiya komawa gombe itama dama shi Zaid yajima da komawa tun lokacin da Aryan din yafara samun lafiya,ai Hanan ji tayi kamar kada hajiya ta tafi saboda tana mutukar jin dadin zama da ita babu tsangwama babu sa Ido da takurawa irin na wasu surukan,ita abubuwa da yawa ma hajiyan ke matsanta mata akai dan ko abinci ta rinka cewa taje ta zauna taci abinci tabar hidima dasu haka ita kam bazata fadi kiyayyar uwar mijiba duk da zaman nasu baiyi nisaba. Tunda hajiya ta tafi kuma yarage sai su kadai da umma shima Khalil ba ganinsa akeyi ba domin ankoma gidan jiya dan harma yasake fallawa yakoma Florence wato k'asar italy dan dama bawai yagama abinda yaje yi bane lalurar Aryan ce ta dawo dashi amma koda yaushe yanzun ma suna makale awaya,
Ita kam Hanan tana cikin wani hali domin ta samu kanta dumu dumu da tunanin Khalil wanda ke neman tarwatsa kwakwalwarta kullum ita kenan cikin tunani tarasa meke damunta gashi shi bama ya nan kuma koda ace yana nan dinma ba ganinsa take samun yiba sosai sai antaki sa'a,ranar da mujahid yafara kiranta tana gani taki dauka saboda kamar yadda yataba fada mata akan tayiwa iyayenta biyayya ta zauna da mijinta lafiya to ayanzu ta daura aniyar yin hakan idan kuwa hakane to babu bukatar sufara kiran juna awaya yanzu.
Lokuta da dama tana jin Aryan na yin waya da Khalil amma bata tunanin ya t'aba koda tambayar ta amma fa kullum kuma koda yaushe zaka samesu suna video call da d'ansa,ranar da su Aryan suka fara exams ranar yadawo da daddare yasauka a Abuja su PA sukaje suka daukoshi,tana son taje tayi masa sannu da zuwa domin idonta biyu yadawo amma bata son yin abinda ajinta zai zube a idonshi, shiyasa itama ta shareshi kamar yanda shima ya shareta. Washe gari da sassafe suna yin breakfast zasu tafi school sai gashi ya sauko sanye da kananan kaya kuma da alama dasu yayi bacci riga ce jersey fara sol da dogon wando shima fari mai sulbi sunkuyar da kanta tayi aranta tana tunanin wai Wadanne kayane suka fi karbar wannan bawan Allahn? Duk wadanda yasa kyau suke yimasa daga manyan har kananan,bata farga ba taji maganarshi akusa dasu yana yiwa Aryan magana da harshen turanci wai ko bai san yadawo bane yaga bai ganshi yaje bedroom dinshi ba da safe,
Makalkaleshi Aryan yayi yana murna dagashi yayi cancak daga kan kujerar da yake zaune akai ya rungumeshi yana kissing dinshi,
"Uncle ka siyo min abunda nace kasiyo min?"
"Nasiyo maka Abba na,ai dole insiyo maka,kaje school ka dawo zaka ganshi"
"Thank you Papa..."
"You are always welcome lovely son"
Saida tajira suka gama sannan ta gaidashi,kamar kullum adan ciki ciki ya amsa sannan yawuce yafita daga falon yayi waje,ita kanta tsarin rayuwarshi na burgeta saboda baida girman kai irin na wasu masu kudin sannan bai dauki rayuwarsa da zafiba dan ko yanzu da yafita takalmin roba slippers ne akafarshi amma fa yayi kyau yafito sosai ko dan jiya yadawo daga waje ne oho amma yayi kyau,
Suna fita suka shiga mota kasancewar daga bakin kofa ake ajiye musu motar shima Khalil din haka ne anan ake ajiye masa motarshi yana fitowa sai dai yashiga,daga cikin mota ta hangoshi caan nesa da su da mutane sun yanyameshi ko su wanene oho,kwalla taji ta ciko mata ido tayi saurin gogewa dan kada Aryan yagani.
Bayan dawowarsu daga makaranta tana kwance adakinta tana duba scrip din yara tagaji ta ajiyesu gefe ta kwanta tana hutawa Aryan yashigo da gudu hannunshi rike da wata kyakkyawar yar karamar laptop irin wacce ake siyawa students, ash colour ce mai mutukar kyau ashe dama shine sakon da Aryan ke tambayar Khalil da safe,karba tayi tana fadin,
"Woww.... Yaron babanshi yasamu sabuwar laptop,inye,to maza tafi library kaci gaba da karatu sai anjima sai kafito ka huta kayi game na 15 minutes"
Da gudu yafita ita kuma tashi zaune tayi ta bude laptop din tana dubawa babu komai aciki sai games kala kala da cartoons sai kuma pictures, pictures din tafara bi daya bayan daya tana gani duka na Aryan da Khalil ne tun yana rarrafe gasu nan yayiyyi musu selfie,shagala tayi da kallon hotunan domin mafi yawa daga ciki tare suke kuma sunyi shiga iri daya wato dai atakaice anko yake yi musu dan ko kananan kaya ne yasa sai taga shima Aryan din irinsu yasaka masa, tajima akan wani hotonsu duk sunsha bakaken suit da blue din t shirt aciki sun daura necktie rike da hannun juna awani katafaren wurin shakatawa wanda bata san kowacce k'asa ce ba amma duk fuskokinsu cike da fara'a dan har hakoran Aryan sun bayyana wanda ya daga kansa yana kallon uban, kowannensu idanuwanshi sanye da bakin gilashi wanda yasake kara musu kyau,
"Fatabarakallahu ahsanul kaliqin....." Tafada tana sake zooming din hoton,tana zuwa kan na gaba taga ashe na baya ba wani kyau yayiba akan na yanzu domin shi na yanzu bakaken wanduna suka saka da jar t shirt sunsa p cap suna zaune akan wata gada cikin babban birnin k'asar ingila dan gashi nan akasan hoton anrubuta London Vive,haka tayita rudewa tana kasa banbance wacce shiga ce tafi yimusu kyau domin wani shigar manyan kaya sukayi iri daya har hula wani kuma jallabiya ma suka saka iri daya da yar karamar hularta amma yawanci a saudiyya ne suka yi wadannan shigar,
"Aryan dan gata"
Ta furta hakan acan kasan makoshinta sakamakon ganin pic din birthday dinshi na cika shekara biyar da tayi,shima ankon sukayi da uban kowa yasha bakin jeans da maroon din riga suna bawa juna cake abaki duk suna yin dariya.................鉁嶏笍
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:09 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*
*25*
***Har Aryan yadawo bata samu zarafin gama kallon wannan pictures dinba wadanda ke shirin zautar da ita hakika sai yaune ta sake tabbatarwa da kanta cewa Khalil dan kwalisa ne kuma cikakken dan gayu sannan idan har ba fada maka akayiba wallahi baza ka taba cewa Aryan danshi ne na cikinsa ba duk da suna mutukar kama da Aryan din amma fuskar Khalil babu girma atare da ita yarinta ce fal kwance akai,
Jin Aryan yafada kanta yasata ajiye laptop din tana dubanshi,
"Wai har kayi me cutie?"
"Mommy har nagama karatun"
Kanshi ta shafa sannan tace,
"A'a cutie baka gama ba ka dai fito break ko?"
Kai ya daga mata yana kaiwa babban dan yatsanshi baki hannun ta buge saboda yanzu dabi'ar da ya ke neman koya kenan shan hannu tun bayan rashin lafiyarsa amma da ba haka yake ba,
"Cutie ba na hanaka shan hannu ba? Ka daina kaji yaron kirki..."
Kai ya daga mata yana jan hannunta,tashi tayi tabishi suka sauka k'asa ta kofar baya suka bi suka fita sune har garden gashi garin da alamar hadari kuma yagama haduwa,
Acan ruwan ya iskesu,da gudu suka shigo ciki ita kam cikin ruwan ta shiga ta hanyar shiga cikin wani dan karamin fili dake tsakanin part din Khalil da nata,filine fetal an shuka flowers kala kala awurin amma babu kasa gaba daya rufe yake da interlock an kawatashi yadda yakamata,
Sosai take jin dadin ruwan yanda yake sauka ajikinta, Aryan ne shima yashigo yana ta tsalle acikin ruwan yana jikasu,
Shigowar shi kenan cikin sashensa yashiga bedroom dinshi yasoma rage kayan jikinsa farar t shirt da bakin dogon wando yasaka yana son shiga yayi wanka kamar ance ya kalli window yanufi gaban windown yana shirin rufewa, Hanan ya hango a kasa ita da Aryan cikin ruwa suna ta wasan banza atoh wasan banza mana tunda wasan ruwa suke yi, wannan yarinyar bata da hankali yanzu da taja masa yaro takaishi cikin ruwa idan mura ta kamashi ko zazzabi fa?
Da sauri yabar wurin window din yafita daga dakin ya sauka zuwa kasa a hanzarce,
Sam Hanan bata san cewa yadawo gidan ba saboda lokacin dawowarshi baiyi ba dan sai dare kuma darenma bawai na kusa ba,
"Aryan..... what are you doing there?"
Dukkansu juyawa sukayi wurin da suka jiyo maganar shi,shi dinma tsaye yayi yana kallonsu cike da takaici dan gaba daya sun jike jagaf,kunya da tsoro taji sun rufeta lokaci guda,shi kam kama kunnen Aryan yayi guda daya yana yimasa fada,
"Idan nasake ganin kayi wasan ruwa nida kaine..." Juyawa yayi ga Hanan,
"Nan gaba idan zakiyi wasan ruwanki kiyi ke daya karki sake kai min yaro cikin ruwa..."
Daga haka yahaura sama yana cewa Aryan yaje umma ta sauya masa kayan jikinsa,jan hannunsa Hanan tayi suka je dakinsa ta sauya masa kaya bayan ta goggoge masa jikinsa,kayan sanyi ta saka masa sannan itama tawuce d'akinta taje ta cire nata kayan ta sauya wasu,tun daga wannan lokacin bata sake ganinshi ba shima haka,duk abin duniya ya taru ya isheta yayi mata yawa,haka dai taci gaba da daurewa tana yin al'amuranta amma can kasan ranta akwai damuwa atattare da ita. Kusan kullum sai sun gaisa da yan gidansu musamman ma mamaye haka itama anty salaha jifa jifa suna gaisaw musamman ma ta chat. A kwana atashi har su Aryan sun gama exams dinsu kuma ranar Friday ake sa ran yin hutu, kasancewar hutun azumi za ayi Khalil yana da burin kaisu gombe sai suyi azumi da salla acan shikam duk Ramadan umarah suke tafiya shida Aryan sai ankusa salla suke dawowa wani time dinma sai bayan sallar sannan suke dawowa,
Ranar Friday akayi hutu bayan anrabawa yara results dinsu,tun a makaranta Hanan taga result din Aryan kuma tayi farin ciki sosai domin ya dauki first position kamar yanda yasaba, Khalil kuwa da yagani farin doki yabada aka siyo masa domin Aryan na masifar son doki tun yana dan mitsitsi. Tunda akayi hutu kuma sai zaman gida babu wurin zuwa duk zaman nan yabi ya ishi Hanan,kullum kai kenan agida babu fita sai hira da umma da koyar da Aryan dan dama tun bayan warkewarsa take koya masa littafin (hisnul ad'fal) wato littafi mai dauke da addu'o'in yara wadanda zasu rinka yi dan samun kariya,
Sati daya da yin hutun taga text din Khalil wai ta shirya zasu tafi gombe kuma acan zasu yi azumi,wani dadi taji ya lullube ta domin tasan zaman gombe zaifi na Abuja dadi saboda can akwai mutane ba kamar nan ba,duk wani abu wanda tasan zata bukata ta dauki abinta haka shima Aryan ta shirya masa nasa kayan,ranar asabar da daddare bayan Khalil yadawo daga office suka dauki hanyar gombe, Aryan ne agaba sai shida ita abaya ita kuma umma motarta daban,tunda Hanan ta shiga cikin motar tayi shiru ta kasa ko kwakkwaran motsi amma fa motar ta tafi da ita domin sanyin AC kadai ke shigarta gashi hatta kujerar motar wani azababben laushi gareta wannan motar ita dai aganinta bata da maraba da jirgin sama kawai dan dai shi asama yake ne ita kuma a kasa,tv taga ya kunna wacce ke cikin motar,daga shi har ita babu mai cewa koda uffan sai dai yana ta amsa wayoyi lokaci zuwa lokaci,wani abu da yasake burgeta shine duk inda sukaje check point ba a tsayar dasu da sunzo zasu wuce shiyasa tafiyar tasu tayi sauri gaskiya masu kudi suna cikin ni'ima domin suna fantamawa son ransu ashe shiyasa Khalil bai jin wahalar tafiya kullum yana bisa hanya,
Suna shiga garin gombe duk da cewa dare ne amma mutane sai faman daga musu hannu suke gashi dai na waje ba ganin na ciki yake ba tun daga nan Hanan tasan jama'ar garin na sonsa kuma suna yinsa domin masu babura rakasu suka yi har kofar gida,ita kam ta bude ido tana ganin yanda garin yake domin wannan shine ganinta na farko dan lokacin da aka kawota tana amarya babu abinda ta samu damar gani shiyasa yau take ta baza idanuwa tana kallo. Suna shiga cikin gidan securities suka fito suka bubbude musu kofa ita abinma kusan mamaki yake bata wai yau itace cikin wannan daular ana girmamata kamar wata matar governor,kai tsaye cikin gidan suka shiga tare da umma da Aryan,
Duk yanmatan gidan suna tare da hajiya ana sauraren zuwansu ganin Aryan dake gaba yasa yanmatan rige rigen zuwa daukarshi shi kuma sai ya gudu ya haye kan cinyar hajiya yana boye fuskarshi cikin jikinta,
"Ja'iri ashe dai baka manta dokaka da kasar da suka taba yiba,sarkin wayo" Inji hajiya,
Kowa dake wurin dariya yayi,a kasa Hanan ta zauna tana gaida hajiya,duk da hajiyan tace ta koma kan kujera ta zauna amma taki anan taci gaba da zama zuwa can aka fara shigo musu da kayayyakin su wanda suka zo dashi, ita kuwa Hanan tuni ancika mata gabanta da kayan cima iri iri hajiya tana ta cewa taci abinci taje ta huta, abincin suka ci ita da Aryan sannan suka wuce dakin dake ciki wanda ko lokacin da tana amarya anan aka sauketa,wanka tayiwa Aryan tayi masa shirin bacci ya kwanta sannan itama taje tayi tazo ta kwanta ta san idan ba wani iko na Allah ba sai Khalil yashigo dakin nan komai dare yaga Aryan saboda tun da sukazo basu kara sakashi a idanuwansu ba yana can tare da baki tunda baya rabuwa dasu. Kamar Hanan ta sani kuwa domin tun bayan zuwansu Khalil salla kawai yasamu yayi daga nan yaketa ganawa da baki bai samu kansa ba sai karfe dayan dare saura yan mintuna gashi cikinsa inbanda yunwa babu abinda yake ji,kuma dadin dadawa ma kofa gaisawa da hajiya basuyi ba,
Tunda yaji part din hajiya shiru yasan kowa yayi bacci agidan amma yana shiga ita ya sameta ido biyu tana zaman jiran zuwanshi yaci abinci kuma su gaisa,kansa babu hula ya zauna nan kasa inda Hanan ta zauna dazu,
"Hajiya mun sameku lafiya?"
"Lafiya lau Khalil ya fama da jama'a? Ga abinci zuba kaci"
"Hajiya ai fama da jama'a kam sai godiyar Allah wallahi rabona da abinci tun wani ruwan tea da na sha da safe a office da meatballs guda biyu shikenan,ko gidana sai dazu da zamu taho nasamu naje daga can muka iyo nan.... Kai rayuwar nan tana da wahala babu komai acikinta face gwagwarmaya da fafutuka astagfirullah"
"To ya za ayi Khalil sai dai fatan lafiya da taimakon ubangiji,nauyine Allah yariga da ya dora maka kana yaronka dakai sai dai fatan Allah yabaka ikon saukeshi"
"Amin hajiya,nauyifa mutum da kuruciyarshi da komai wallahi,duk cikin ministocin nan nine yaro wasunsu ma sun kusa haifata ni wallahi banma san ta yadda akayi na zama ba...."
Dariya hajiya tayi ta dan kishingida ajikin kujera,
"To inbanda abinka Khalil shi hukuncin Allah ai ba ruwansa da girma ko shekaru,haka Allah ya tsara maka, Allah dai yabaka ikon sauke nauyin da ya rataya a wuyanka"
"Amin hajiya,shi wannan yayi bacci ko?"
"Ehh Aryan ba,yayi bacci ai tunda jimawa,kuma nace maimakon ka kai matar taka sashenka shikenan sai akawota nan?"
Dan shiru yayi ya shafi kansa sannan ya ce,
"Hajiya wanne bangaren nawa kuma bayan daki dayane aciki,muje muyi zaman takura haka kawai...."
"Idanma babu dakin ba matarka bace? Ko zaman gaban takura zakuyi kuyi mana ai canne yafi dacewa da ita,kuma kasan ai daki dayanne amma ka daukosu kuka taho"
"Gaskiya hajiya daki daya yayi mana kadan"
"To ba sai kasake gina muku waniba tunda kana da halin yi amma dai babu tsari ace kana can matarka tana nan,yanzu idan kana bukatar tayi maka wani abu sai kazo kana tasota daga nan tana tafiya can?"
"Hajiya ni kwana nawa ma zanyi agarinne? Dududu kwana hudu fa zanyi ko biyar mutafi umarah nida Aryan...."
"Kaida Aryan? Ita kuma matar taka fa? Wa zaka barwa ita?"
Shiru yayi yana tunanin abinda yadace yafada wanda hajiya ba zata yimasa fada ba,ruwa ya dan kurba sannan yace,
"Ai hajiya bana visa dince tayi wahala kuma da har ita naso hadawa amma abun ya faskara mukuma ai kinga permanent Visa garemu shiyasa..."
"Ai shikenan amma gaskiya banji dadin tafiya kubarta ita kuma ananba da zakuyi gaskiya...."
"Hajiya kiyi mana addu'ar dai Allah yasa hakanne yafi zama alkhairi"
"To amin, Allah yadawo daku lafiya, Allah yatsareka ya kareka ya tsare maka dukiyarka da zuri'arka, Allah ya rabaka da mugun ji da mugun gani ya shiga lamarinka akoda yaushe...."
"Amin hajiya..."
Saida yakai wurin karfe 2 na dare shida hajiya sannan yatashi yafita ya nufi bangarensa aransa yana tunanin ai kamar fa tunda yazo baiga Zaid ba anya kuwa yana nan? Kai duk yanda akayi zaid baya garin nan dan kuwa da yana nan da yaganshi. Duk jikinsa a gajiye haka ya lallaba ya daure yayi wanka yasaka kayan bacci yahaye gado yana kallon agogo,karfe 3 saura na dare,yanzu hajiya da take cewa ya hada daki da yarinyar can ai da takurashi za ayi haka kawai abanza shi harma mantawa yake yi da wai ita matarsa ce kawai abinda yasani ya kawowa Aryan friend wanda zata rinka debe masa kewa.
Washe gari ya dan samu zarafin komawa baccin safe, Aryan kuwa tunda yatashi Hanan ta shiryashi cikin kananan kaya bakar t shirt ta polo da blue din jeans tasa masa combos shima baki bata sake ganinsa ba dan wurin hajiya yaje ta can ya gudu wurin babansa dan shine ma ya tashi Khalil din, rungumeshi yayi yana shafa sumar kanshi,
"Waye ya yi maka wanka?"
"Momy ce.."
"Uhmm dan gatan mommy..."
"Mommy tana sona..."
Murmushi Khalil yayi ya tashi zaune yana daukar wayarshi domin kira yashigo,
"Hajiya ina kwana...... lafiya lau....gashi muna tare dashi ai......ehhhh....kokon dai hajiya.....to shikenan sai na shigo"
Daga haka ya katse wayar yabawa Aryan shikuma yashiga bathroom domin yin wanka,har yafito ya shirya Aryan na kwance kan gadon yana ta faman matse matse awayar kamar tashi cemasa yayi kar dai ya yarda yayi masa deleting din wani abu garin wannan matse matsen nasa,shiryawa Khalil din yayi cikin wata farar shadda yasha turare,ba dan hajiya tace yajira akawo masa breakfast ba da fita zaiyi.
Hanan tunda ta gama shiryawa tayi zamanta adaki saida hajiya ta turo mufida kiranta sannan tafita,wata dark purple din atamfa ce ajikinta doguwar riga tasha turare mai sanyin kamshi,gaida hajiya tayi sannan hajiya ta nuna mata breakfast din Khalil wai idan tagama karyawa shima taje ta kai masa mufida ta rakata ko zarah,tea ta hada ta sha ta danci awarar da aka soya da kwai sannan ta tashi suka fita ita da zarah dauke da kayan breakfast din Khalil,
Part din nashi dan karami ne bawani babba ba saiko kayan alatu da yasha,suna zaune falo shida Aryan wanda keta waya dasu Nawwar awayar Khalil daga jin Khalid ya kirashi suna magana shikenan yakafa rigimar sai anbashi ana bashi kuma suma su Nawwar din suka karbe kan wayar tun dazu suketa hirar da taki karewa domin sai labari suke ta bawa juna,durkusawa zarah tayi ta gaidashi sannan ta ajiye kayan dake hannunta tafita,itama Hanan din gaisheshi tayi suka gaisa kamar yanda aka saba ina kwana lafiya shikenan,ta mike zata fita taji yace, "Zo nan"
Dawowa tayi ta zauna amma baice da ita komai ba saima kayan breakfast dinshi da yajawo yabude ya tsiyayi koko a cup sannan ya bude flask din soyayyiyar awara da kwai ya diba a plate ya zuba vegetables sos akai yasa spoon yafara ci,duk sai taji ta takura domin basu taba zama haka su biyu ba awuri duk da Aryan yana wurin,
Ganin wayar Aryan ba mai karewa bace yasa Khalil kwace wayar ya kashe yace maza ya zauna suci abinci shi baya son cin abinci sai anyi masa dabara,yanzun ma saida dabarar shima yabashi yaci. Suna zaune shiru amma jifa jifa Aryan na yin surutunshi ahaka akayi knocking a jikin kofa, zaid ne amma ganinsu duka sai yakoma Khalil nata kiransa amma bai dawoba,ita dai duk da tana jin dadin zaman wurin amma ta kosa ta tafi domin zuciyarta kamar zata faso kirjinta tafito dan tsananin bugun da takeyi,saida suka gama sannan yace sutafi cikin gida ita da Aryan,shikuma yafita tun daga nan kuma ganinsa yayi mata wahala dan bata ganinsa sai kowacce safiya da zarar yafita kuma shikenan dan lokacin da yake shigowa da daddare tuni sun kwanta,ita kanta hajiya fadan da take yimasa kenan wai bata ga yana jan matarsa ajiki yana kiranta suna hira ba shi kuma sai cewa yayi wai ai duk sanda taje wurinshi da safe kai masa abinci suna tattaunawa. Kwanansu hudu da zuwa yace ashiryawa Aryan kayansa saboda zasu iya tafiya a kowanne lokaci, lokacin ana saka ran ganin watan Ramadan nan da kwanaki biyu zuwa uku,daren asubar da zasu tashi tana daki kwance har tayi shirin bacci hajiya ta aiko kiranta,koda taje hajiya cewa tayi wai ta je wurin Khalil ta kwana acan suyi sallama, innalillahi ita dai gashi ba damar tayi musu da hajiya gashi bata jin zata iya zuwa gareshi a wannan lokacin,jiki a mace ta tashi takoma dakin da ta sauka tafi minti goma tana tsaye tana kallon Aryan dake kwance yana bacci sannan ta dauki hijabi har kasa tasa ta fita rike da wayarta a hannu,gidan tamkar rana dan tsabar haske baka jin motsin kowa sai karar injin bada wutar lantarki da ke tashi,tana sake kusantar sashen nasa faduwar gabanta na karuwa jikinta na rawa ahaka taje,ta jima tsaye a bakin kofar falonshi tarasa ta yadda zata shiga ciki,dakyar tayi ta maza ta bude kofar ta sa kai tana jin numfashinta yana tsinkewa kamar zai fice gaba daya.....................鉁嶏笍
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:11 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*
*26*
***Kasa daga kafarta tayi daga nan inda take tsaye bayan tashiga cikin falon nasa wanda kamshinsa ke kai komo acikinsa,
Wuri ta samu ta zauna saman kujera tana kallon kowacce kusurwa da lungu dake cikin falon wanda yake dan madaidaici sai dai kuma antsarashi yadda yadace dan yayi mata kyau kamar irin dan bangaren nan na ango da amarya auren saurayi da budurwa, ango da yar amaryar sa ya ishesu rayuwa kafin su tara 'yaya,komai na ciki milk ne and coffee colour gashi tsaf tsaf babu datti babu kura yayi kyau gwanin ban sha'awa. Idonta ne yakai kan wayar Khalil dake kan wani center table na glass dake can gefe daya take ta sake jin faduwar gabanta ta karu da kaso tamanin cikin dari na wadda takeji dazu,
Fitowarsa kenan daga wanka yasaka farar jersey mai ratsin blue agefe da gefenta sai wandon rigar shima fari amma dogone dan har ya rufe gwiwarshi,falo yafita domin dauko daya daga cikin wayarshi da ya ajiye acan,yana fitowa yaganta zaune ta tukunkune cikin hijabi ba dan yasan da zuwanta ba da babu abinda zai hana ya tsorata to dan dai hajiya ta sanar dashi ne dazun nan da yashigo tagama kora masa jawabin wai yakamata matarsa taje suyi sallama kuma yaji ko tana da wata damuwa,
"Kowacce irin sallama hajiya take son muyi oho..."
Yafada acikin ransa yana kokarin daukar wayarshi,cikin sanyin murya yaji tana gaisheshi nan ya amsa kamar koda yaushe cikin rashin son doguwar magana,ita dai tun kallon farko da tayi masa bata sake kallonshi ba domin yau yasake yimata kwarjini fiye da sauran ranakun baya gashi kayan jikinsa sun dan kamashi. Wuri shima yasamu ya zauna afalon yadora kafa daya akan daya yana duba tulin sakonnin dake cikin wayar wadanda aka turo masa kuma mafi yawa ba sanin wadanda suka turo yayi ba,
Hanan gyangyadi tafara domin tuni 12 ta dan gota ita kuma ba saba dogon zama tayiba karkarinta takai 11 wannan dinma sai da dalili amma wani lokacin 10 tayi baccinta saboda fitar sassafe. Lura yayi da gyangyadin da take yi dan haka yayi mata magana cikin muryar sa mai cike da sanyi,taushi da kuma gardi,
"Shiga ciki ki kwanta..." Taji yafada amma bawai dan yasoba domin harga Allah shifa takurashi akayi da aka turo masa yarinyar nan,yanzu dole sai taje ta hau masa kan gadonsa shikuma abarshi yayi kwanan takura a falo,
Kasancewar itama bawai awani sake take dashi ba yasata girgiza kanta tace,"A'a nanma ya isa"
Iya nan din da ta furta kawai ya iyaji dan haka yaci gaba da abinda yake tsawon mintuna goma yagama yatashi yawuce cikin bedroom dinshi harda rofo kofa,saman gadonshi ya haye yai kwanciyar sa bayan ya kara karfin na'urar sanyaya daki,itama Hanan anan ta bingire kan 3 sitter bacci yayi gaba da ita,ba ita ta tashi ba sai asubah kasancewar tasaba tashi yau dinma lokacin salla nayi ta tashi duk jikinta ciwo yake yimata saboda baccin da tayi a takure shikuwa wuyanta ya kage bata ko iya juyashi Sosai sakamakon pillow da tayi da hannun kujera,fitowarshi taji daga cikin daki,sanye yake da jallabiya kalar ruwan kasa hannunsa rike da casbaha,ganinta zaune alamar ta tashi yasashi wucewa yafita zuwa masallacin da ke cikin gidan,tana ganin haka itama taja jikinta tafice ta nufi bangaren hajiya sadaf sadaf kamar wata marar gaskiya,da sand'a ta shiga dakin da ta sauka tasamu Aryan yanata sharar baccinsa cikin jin dadi da kwanciyar hankali. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta tashi tashiga toilet, brush tayi sannan tayi alwala tafito,nan inda tayi salla anan wani bacci mai shegen dadi yayi awon gaba da ita,cikin baccin ta soma wani mafarki da wata mata wai ita Hanan din tana rike da Aryan suna ta gudu cikin dokar daji ita kuma matar tana binsu wai ala dole sai ta kwace Aryan daga wurinta,gudu take cin karfinta har tazo wani bakin ruwa mai yawa ga kuma matar ta kusan cimmusu firgigit tayi ta tashi sakamakon tashinta da Aryan din ke yi,janshi tayi tana dudduba jikinsa domin taga ko lafiya yake gaba daya ta gama jikewa jagab da gumi,ganinshi tayi ras saima fararen hakoransa da yake washe mata yana nuna mata sabbin kaya yan kanti da hajiya tasaka masa,
Window ta kalla nan taga rana har tafito sosai tayi mamakin irin baccin da tayi daga yar kwanciya, sauri sauri tayi wanka tafito ta shirya ta saka atamfa pink colour dinkin riga da skirt wadanda suka yimata caras cass,tana kokarin fesa turare zarah ta shigo cikin dakin rike da farantin abinci,
"Anty ina kwana? Yau kin makara,ga breakfast dinki inji hajiya"
Da fara'a itama ta juya ta kalli zarah wacce ke kokarin ajiye mata farantin akan rug din dake gaban gado,
"Lafiya lau zarah,wallahi na makara ina kokarin fitowa ma da yanzu,bari to nafara karyawar"
Fita zarah tayi tana murmushi ita kuma Hanan tayi sakare aranta tana fatan Allah yasa dai kar su hajiya su zargi wani abu akan makarar nan tata tunda jiya taje wajen Khalil. Aryan ta kira suka zauna tare suka karya da wainar shinkafa da miyar agushi sai kunun gyada da shinkafa da tea da bread ga kuma wainar kwai agefe,sai da suka koshi damm sannan tafita duk kunya ta cika mata ciki domin aganinta hajiya zata tsammaci dan taje wurin mijine shiyasa ta makara amma koda ta fita hajiya fuska asake kuma awashe ta karbi gaisuwarta har tana cemata umma barira ta tafi funakaye tace afada mata sai nan da sati biyu sannan zata dawo,
Tana zaune tare dasu hajiya Khalil yashigo cikin ash din shadda yau ne kadai Hanan zata ce ta ganshi da wasu kaya sabanin farare tun daga ranar da ta fara ganinsa,
"Hajiya zamuje mu wuce....Sai Allah yadawo damu" Taji yafada yana zama kujerer dake kusa da ta hajiya,
"To mu'azzam Allah yadawo daku lafiya, Allah ya kiyaye hanya"
Tashi hajiya tayi tabasu wuri wai ko zasu tattauna wani abu da matarsa,
"Ina kwana?" Hanan ta fada tana wasa da yan yatsun hannunta kanta akasa,
"Lafiya lau...."
Daga haka bai kara cewa komai ba sai waya da taga ya daga yana magana cikin sanyin murya da rashin hayaniya,
"Kana jina..... Na warewa PA dina komai awurinsa zaka karba,akwai kayan marayu yadina da shaddodi da atamfofi bandir dari biyar biyar na zawarawan da mazajensu suka rasu ma haka da tsoffi,sai kayan abinci shima shinkafa da hatsi da masara da sugar da man gyada shima kowanne guda dari biyar biyar akai musu a rarraba dan Allah.... Idan kuma akwai wani abu da kuke bukata kayi wa PA dina magana zai sanar dani komai...amin....Amin nagode"
Saida ya gama wayar sannan ya juya ga Hanan wacce har lokacin kanta na kasa aranta tana jin dadin abinda taji Khalil din yayi wato taimakon marayu da marassa karfi acikin wata mai falala kuma gashi harda kayan salla gaskiya yayi kokari dole yarinka ganin budi cikin harkokinsa domin taimakawa marayu da yake yi, muryar sa tajiyo yana cemata,
"Idan kina bukatar wani abu ki fadawa hajiya zata baki..."
Ganin yamike yasa itama ta mike tana jijjiga kai,
"Tom, Allah yadawo daku lafiya"
"Amin"
Kai tsaye dakin hajiya yashiga suka fito tare tana rike da Aryan, rungume ta Aryan yayi suka yi sallama sannan suka fita, itama bin sahun masu yimusu rakiya zuwa compound din gidan tayi tana rike da hannun Aryan,sai bayan da suka ga tafiyarsu sannan suka koma cikin gida kowannensu zuciyarshi cike da kewa musamman ma ita wacce tayi mugun sabo da Aryan.
Kamar yanda ta tsammata hakance ta faru wato daren yau sai takasa bacci tunanin Khalil da gudan jininsa Aryan sune suka tsaya mata arai tana jin kamar tayi tsuntsuwa taje garesu,
Haka tayita kewarsu cikin kwanakin har zuwa ranar da Aryan ya kirata lokacin kwanansu hudu da tafiya kuma ranar aka kai azumi na farko,sunsha hira sosai da Aryan da yake gwanin surutu ne,
Haka rayuwa tayi ta tafiya idan tace acikin zaman da takeyi a gidansu Khalil wani yataba sab'a mata ko yayi mata ba daidai ba to tayi karya,kusan kullum suna gaisawa da yan gidansu ranar ma abbanta yake sanar da ita wai Khalil ya aika musu da kayan azumi da na salla ita dai batace komai ba domin rabonta dashi tun ranar da yatafi umarah sabanin d'ansa da kullum sai sun gaisa,hajiyarsa kuwa tana tattalinta kamar me kullum Cikin hidima da ita ake babu abinda take yi sai dai taci ta kwanta dinkin sallah kuwa kaya kala biyar hajiya ta bada aka dinko mata da mayafinsu da takalmi ko kadan hajiya bata yi la'akari da cewa wai anyi mata lefe mai uban yawa ba. Ana saura kwana biyu salla su zarah suka matsanta mata wai dole sai sunje gidan kunshi tare,ita wallahi a budget dinta babu wani maganar yin kunshi amma irin yanda suka bi suka takura mata yasata yarda zasuje din, Khalil tayiwa text cewa zata fita zataje gidan kunshi,kamar koda yaushe ok kawai yace mata hakan ya tabbatar mata da cewa kenan yabarta taje,
Su hudu suka tafi sukaje akayi musu jan k'unshi mai hade da baki kuma tun safe suka bar gidan amma har la'asar suna gidan kunshin hajiya ajima kadan ta kira tace har yanzu ba agama ba saboda Hanan ce kadai keyin azumi acikinsu ranar su dukansu su ukun basa yi ita Sarah dama sam bata ma yin azumi saboda lalurarta ba mai cikakkiyar lafiya bace ita.
Sai da aka kusan shan ruwa sannan suka baro gidan kunshin nan suna dawowa gida ana shan ruwa sai dai fa amma mai kunshin ta iya kwararriya ce sosai domin duk ta rangade musu kafafuwa da hannaye sai yanzu suka fahimci dalilin da yasa kunshinta keda tsada ashe ta iyane sosai,washe gari kuma kitso aka zo aka yimusu har gida mai kitson hajiya itama ta iya babu laifi,
Bayan ansha ruwa an idar da sallar tarawih suna baje falon Hanan tana kwanciyar gajiya saboda azumin yau dinnan tajishi sosai bada wasa ba kamar bazata kai ba gashi wani abun al'ajabi azumin bana bata sha ko daya ba bata taba fashin shan azumi ba sai wannan karon ita wani lokacin ma azumi sai tasha sau biyu farkonshi da karshensa amma wannan karon bata shaba kwata kwata,babu ko dan kwali akanta hancinta yafara jiyo mata kamshinsa na turaren no 1 ai kuwa wannan turare yaci sunansa domin no 1 dinne wurin zama ajikin mutum dan yariga da ya zauna ajikinsa,
Muryarsa tajiyo yana dososu yana yin magana awaya cikin kwantacciyar muryar nan tashi mai ratsa zuciyar duk wani wanda ke sauraronta,
"Ehh wallahi dawowa ta ma kenan yanzun nan muka sauka...... Ai dama ta gombe natafi wannan karon.... Ehh insha Allah anan zamuyi sallah.... Ok har kashigo ne?..... To Allah yakawoku lafiya"
Sam bata yi yunkurin tashiba dan tasan ba iyawa zata yiba,karadin Aryan suka jiyo shida Zaid wanda ke rike da hannunshi,ayanda take akwancen nan haka suka shigo suka isketa sai dan kwali kawai da taja ta rufe kanta duk su zarah sannu da zuwa suka shiga yimasa ita kuma Aryan yazo ya murkusheta yana murna da farin cikin ganinta,ita ma sannu da zuwa tace dashi idonta na kan farar kafarshi dake sanye cikin takalmi half cover fari tatas,da yawwa kawai ya amsa mata yawuce ciki,
Suna nan zaune Aryan yasasu agaba da labari Khalil din yafito tunda yatafi kuma shikenan sai kayansu aka shigo dashi shi kam har yayi wani wurin,tsaraba kam Hanan tasha ta wacce Aryan yakawo mata kuma ba komai bane sai tarin chocolate kala daban daban da dabino shikenan,shi kuwa uban gayyar babu wanda yasiyowa koda tsinke amma ya sissiyo zam zam da su dabino Sosai shi dama haka tafiyar shi take baya iyo tsaraba idan kaga yasiyo abu to Aryan ya tahowa dashi yanzunma ga kayan wasa nan iri iri yatahowa da Aryan,
Washe gari yakama ranar salla, babbar Rana kuma mai bikin daya rana haka kuma mai dogon baya,kowa kagani cikin farin ciki da nishadi yake,ita tayiwa Aryan wanka sannan tayi masa shirin masallaci domin tare da Daddynshi zasu tafi,wata arniyar shadda aka dinka masa skye blue riga da wando da babbar riga harda hula dinkin yar bama,da takalminsa sau ciki baki mai masifar kyau,saida ta fesheshi da turare sannan ta yiyyi masa hotuna daga nan yafice yanufi bangaren mahaifin sa,
Ita kam dama bata da niyyar zuwa masallaci sallar idi wankanta tayi ta shirya cikin leshinta dan ubansu golden colour dinkin bubu wanda yayi mata kyau sosai,daurin dan kwalin maryam babangida tayi sannan ta yafa farin mayafi ta fita,tunda aka sauko daga sallar idi gidan ke daukar baki wasu dayawa ma bata sansu ba gashi sai raye raye da bushe bushe ake ta faman yi agidan abinci kuwa kala kala gashi nan sai wanda ka zaba cikin manya manyan warmers wanda aka iyo musamman dan ranar yau,ita dai tuwon shinkafa taci ta kora da lemon jarka,
Bayan ta dan nutsu ta kira duk yan uwa da abokan arziki tayi musu barka da sallah bayan tagama ta yafa mayafi tafita kanta babu dan kwali sai mayafin da ta lullube kanta dashi tana fita falo idanuwanta suka sarke da nashi wanda ke zaune falon hajiya shida Khalid suna cin abinci wata faduwar gaba ce mai tsanani ta ziyarceta cikin gaggawa ta sauke nata idon k'asa,gaishesu tayi sannan ta juya da niyyar komawa amma sai tajiyo muryar Khalid yana cewa,
"Ahh madam dawo mana mu gama gaisawa..."
Dawowa tayi ta zauna duk atakure tana jinsu sunata hira amma muryar Khalid tafi tashi dan shi Khalil ma kamar adole yake yin maganar,
"Wai kasan yarinyar nan me tace min last time? Wai su Nawwar da Nainah sun isheta bata son ta sake haihuwa ita planning zata yi kaza da kaza ko kasan asatin da ta fara planning din a lokacin ta samu ciki....."
"Baka yi da wasa ba kenan....." Khalil yafada yana dariya ciki ciki,ita Hanan bata ma ji abinda Khalil din yafada ba kawai dai taji Khalid yace,
"Atoh ba kai ka tsaya wasa ba...."
"Kai ai gashi nan kayi dagaske..."
"To anfada maka ni rago ne irinka? Kai a wannan fannin ai lazy ne...."
"Na taba yi agabanka ne ka gani?"
"Ai alamar karfi tana ga mai kiba,madam saifa kin hadawa wannan tuzurun da yan dabaru ko ya samu yarinka yin abin arziki" Khalid ya karasa maganar yana kallon Hanan wacce sam bata fahimci inda zancen nasu ya dosa ba kasancewar bata jin abinda Khalil yake fada domin maganar tashi k'asa k'asa yake yinta yanda bazata jiba,jin Khalid na shirin yimasa b'arin zance yasashi daga manyan idanuwanshi ya kalleta kamar ance ta kalli wurin da yake nan suka hada ido bakinshi kawai taga ya motsa amma bata ji abinda yace ba sai dai jikinta yabata cewar cewa yayi "Tashi daga nan",jikinta yayi lakwas kamar anyi mata duka tayi azamar tashi ta wuce ciki ba tare da jinkirin ko sakwan daya ba....................鉁嶏笍
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:11 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*
*27*
***Kai tsaye daki ta wuce wurinsu zarah wad'anda ke ta faman daukar hotuna kamar babu gobe,zama tayi cikinsu sai dai gaba daya hankalinta yana can tare da Khalil wato yau dinnan mutumin ya tsokano kyau kamar dan shi kadai aka kera shaddar da ke jikinsa wadda ta kasance irin ta Aryan sak domin anko suka yi yahadu yau dinnan karshen haduwa,
Acan falo kuwa bayan Hanan ta tashi tabar wurin Khalid kallon Khalil yayi yace,
"Anya kuwa mutumin nan? Anya kuwa?"
"Anya me?" Khalil ya bukata cikin rashin son maganar tayi nisa,
"Gaskiya Khalil ya kamata ka gyara nidai bazan gaji da fada maka gaskiya ba amma yadai dace kayi abinda yadace a lokacin da ya dace,ina dalilin kullum shekaru na tafiya sannan ka kawo yarinya karama ka ajiye a tangamemen gida amma ka kasa kulawa da da ita...."
"Itace ta fada maka bana bata kulawa?"
"Sai ta fada? Ai basai ta fada minba,haba Khalil wai kai wanne irin mutum ne, wannan abun fa da kake yi hadda zalunci idan baka saniba domin itama tana da hakki akanka amma haka kawai dan wani banzan tunani irin naka da taurin kai ka zauna kana cutar da yarinya.... wallahi kaji tsoron Allah"
Shiru Khalil yayi masa hakan yabawa Khalid damar cigaba daga inda ya tsaya ta inda yake shiga bata nan yake fita ba,
"Kaga malam dan Allah ka rabu dani bana son hayaniya,ko insakar maka ita ka aurane tunda kace ni zaluntarta nake yi? Kai sai ka aureta kayi mata adalci" Khalil yafada yana cigaba da cin abincin dake gabanshi kuma sai ka rantse da Allah bashi ne yayi maganar ba, jijjiga kai Khalid yayi domin yafi kowa sanin Khalil tun kuruciya suke tare, tare suka taso suka yi karatu suka yi komai kuma asalima ai sunansu iri daya shima Khalid din sunanshi na gaskiya Ibrahim duk sunan mutum daya suka ci wato kakansu na wurin uba (moddibo),to dukansu sunanshi aka saka musu tunda 'yayan wa da kani suke amma mahaifin su Khalil shine babba,
"Allah dai yana gani ai..". Inji Khalid,shiru Khalil yayi masa yana duba agogon Rolex dinshi dake daure a hannunshi karfe biyar har da kusan rabi yana son yatura adauko Aryan amma baya son Khalid yaji babu dadi domin Aryan din na can tare da su Nawwar daga karshe dai ya zabi yin shiru zai bari zuwa magriba inyaso sai ya tura Zaid ya daukoshi.
Su Hanan kuwa sake sabon shiri suka yi suka fita kallon wasannin da ake gabatarwa acan filin fada dama kuma babu wani nisa daga nan gidan zuwa filin fadar,basu suka dawo gida ba sai dab da sallar magriba. Suna shiga gidan Zaid na dawowa shida Aryan hango Hanan da yayi da gudu ya balle murfin kofa ya fito yaje ya rungumeta,rikeshi tayi tana dariya,
"Cutie ina ka tafi yau kabarni ne da kewa?"
"Gidansu Nawwar Uncle yakaini"
"Kuma shine babu sallama cutie? Tafiya babu ko sallama?"
"A'a"
Bata sake yin magana ba tana rike da hannunshi zasu shiga part din umma ta hango abban nashi yafito da alama masallaci zaije domin gashi nan yana gyara hannun rigarshi wanda ya nannade wurin alwala,sakin Aryan tayi dalilin jiyo kiranshi da uban keyi wai yazo suje salla,ita kam kada kanta tayi zuwa ciki.
Daren yau kamar abun hadin baki dukkaninsu su biyun basu samu bacci ba kowa damuwarsa ce ta hanashi runtsawa ita Hanan tunani da begen ganin Khalil ne ya sa bacci ke neman gagarar idanuwanta,bata gajiya da kallon bawan Allahn nan bata san dalili ba koda yake Allah ne ya kamata tunda abaya babu irin fariya da cika baki da rashin kunyar da bata yimasa ba shiyasa akace kar ka raina mutum ko kuma ka wulakantashi musamman ma wanda baka sani ba ko baka taba ganiba dan Allah na iya jarrabarka da kaunarshi bayan kun hadu,duk da ita dai har yau bata gama tabbatarwa da kanta cewa ta kamu da sonshi ba amma ta damu dashi tunanin sa ya sako ta agaba ta yadda bata yin kwakkwaran minti daya ba tare da ta tuna dashi ba to wai meke damunta ne?.
Shi kuma Khalil maganganun da Khalid ya farfada masa sune suka nemi hanashi bacci wai harda cewa yana zaluntar yarinyar mutane dan haka yaji tsoron Allah,
Juyi yayi akan luntsumemen gadonshi sannan yaja dan guntun tsaki ya harde hannuwanshi a kirji,
"Ko me yake son inyi mata oho..." Yafada acikin zuciyarshi yana sake yin wani tsakin,
"Ka bata hakkinta na aure tunda itama mutum ce....." Maganar Khalid ta sake dawo masa tamkar yanzune yake fada masa,
"Inbata hakkinta? Kai gaskiya bazan iyaba...... Ni in rab'i wata mace wadda ba Ramlat ba? Gaskiya bazan iyaba, Ramlat ita kadai ce matar da zan iya wannan rayuwar da ita kuma tunda ta rigada ta tafi ta barni shikenan zan ci gaba da hakuri har zuwa lokacin da nima nawa wa'adin zai cika...." Ya fada yana lumshe idanuwanshi nan kwalla ta ziraro masa ta gefen idonshi,har yau yakasa mantawa da Ramlat dinsa sannan yakasa daina zubar da hawayensa aduk lokacin da ya tunota,yana yiwa Ramlat son da shi kansa bai san wanne iri bane,akan ya je ya hada jiki da wata macen wadda ba Ramlat ba gara ya zauna bukatar hakan ta zama ajalinsa dan ita kadaice daidanshi a wannan bangaren wannan shine hukuncin da ya yankewa kanshi.
Washe gari da safe da dan ciwo ciwon kai kadan kadan Hanan ta tashi sakamakon rashin samun isasshen bacci da bata yiba,tana zaune ita kadai a falon hajiya saboda su Sarah sunbi umma barira Billiri sai zuwa gobe zasu dawo yanzu gidan babu kowa daga ita sai hajiya sai Aryan sai masu aiki shi Aryan ma tun bayan da tayi masa wanka ya tafi wurin abbanshi bai dawo ba har yanzu,
Text ne taga ya shigo wayarta sai da ta dan ja lokaci sannan ta duba saboda ta zaci ko mujahid ne domin shima yanzu baya kwana biyu batare da yaturo mata da sako ba,
_Ki shirya zan fito yanzu zamuje unguwa._
Shine abinda taga Khalil yaturo mata,tashi tayi ta shiga cikin bedroom ta sake gyarawa ta kintsa sannan ta fito yau shigar shadda tayi kalar ruwan shanshanbale wadda tasha aiki dinkin riga da zanine yayi kyau sosai,sarka da dan kunne da abun hannu ta sassaka sannan tayi dauri wanda yadace da zamani kuma dan yayi da ka ganta dai kaga amarya wacce ludayinta ke kan dawu. Tana zaune bakin gado tana yiwa yaran anty salaha voice note ta WhatsApp tajiyo kamshin turaren shi yana gabato ta,
Bude kofar dakin yayi bayan ya danyi knocking sau biyu bai jira tabashi izini ba kuma yabude ya sako kanshi ciki aranta tace to me amfanin knocking din tunda bai jira izini ba?
"Fito mu wuce...."
Daga haka yajuya yana gyara zaman hular dake kansa, hajiya suka yiwa sallama sannan suka fita da ita dashi da Aryan hajiya sai faman fara'a take yi,yau dama kaya yan kanti ta sakawa Aryan yan ubansu jeans da t shirt jeans din baki da belt dinshi sai brown colour din riga t shirt wadda ajiki aka rubuta 123,sai bakin combos sabo dal,shi kuwa uban farar shadda ce ajikinsa zubin dinkin birni yasha hula sai zuba kamshi yake yi,dukkaninsu baya suka shiga shi kuma Aryan ya shiga gaba yana mikewa tsaye saman kujerar,
Gidan Abba Idris suka fara zuwa wanda ke can sabuwar GRA,gidan babban gidane mai dauke da sassa daban daban, bangaren uwar gidan suka fara zuwa wacce ta karbi Hanan hannu bibbiyu da yake mace ce mai fara'a,shi kuma dama uban gayyar yana can wurin Abban suna gaisawa,bayan tafito daga sashen uwar gidan aka rakata na amaryar itama ba laifi tana da karbar baki,tana zaune ita da Aryan da wasu yara agidan wanda tafi kyautata zaton jikokin gidanne dan harda wadda bata d'ara Aryan a shekaru ba aka leko kiranta wai tafito su tafi,kudi matan gidan suka bata da turaruka,har falon Abba kuma aka rakata suka gaisa shima yabawa Aryan kudi wai gashi nan barka da salla shima khalil rabon kudin yayi agidan kowa da nasa sannan suka tafi,gidan anty Fatu kanwar hajiya suka je wannan kam har falonta Khalil yashiga suka gaisa itama yayiwa yaranta rabon kudi sannan suka fito, Hanan ta lura shi mutum ne mai son zumunci da kaunar yan uwansa domin duka kannensa babu gidan wanda basu jeba yakai mata ziyara, ba dan mai zumunci bane ai hakimcewa zaiyi sai dai shi aje asameshi tunda shine babba kuma yana da kudi amma babu ruwansa yakanje ya gaidasu lokaci zuwa lokaci kuma duk sallar duniya karama ko babba indai yana k'asar sai yaje gidajensu yayi musu barka da salla haka idan anyiwa su Aryan hutu shima kaf dangi sai ya zagaya dashi anganshi sannan yake barin k'asar dashi gaskiya ya rike yan uwanshi kuma ya rike girmansa ya zame musu babban wa uba.
Gidan mai martaba suka je wato fada bayan sun fito daga gidan hamida kanwarshi, Hanan aranta tambayar kanta take tayi to ko dai duk cikin gombe yan uwansu Khalil ne? Saboda sunje gidaje sunfi 20 idan lissafawa zata yi,lallai sai yanzu ta yarda da maganar da taji marokin nan nayi ranar daurin aurenta yanata yiwa Khalil kirari wai ya gaji mulki kuma yagaji sarauta ashe kuwa dagaske hakanne dan tagama kamar gaba daya masu arzikin garin danginsu ne,
Bayan fitowarsu daga fada inda aka hado ta da kayan kamshi kaya guda su turaren wuta,turaren kaya,ban daki da na jiki gidan Khalid suka wuce ta fahimci hakanne dalilin waya da taji yana yi da Khalid din yana cewa gasu nan zuwa,
Acan suka yi sallar magriba duk da Muneerat matarshi bata da saurin sabo amma hakan bai damu hanan ba tayi mata uzuri saboda kowa da irin halinshi. Sai da suka ci abinci sannan suka fito domin tafiya,a compound din gidan suka tarar da su Khalil tsaye shida Khalid suna yin magana amma basu san kowacce iri bace saboda basa jiyo abinda suke fada, sallama sukayi musu suka tafi su Nawwar nata yiwa Aryan bye bye wai suma sai sunzo. Tunda suka koma gida hanan tashiga daki ta kwanta ga gajiyar yawon da suka sha ga ciwon mara saboda tsallaken watan da tayi bata yiba shiyasa take dandana kudarta,tana cikin wannan halin taga text din Khalil wai ta shirya gobe zasu koma Abuja,kasa tashi ta shirya kayan tayi ahaka su zarah suka dawo suka sameta wad'anda suka dawo daga Billiri tare da umma barira...........................鉁嶏笍
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:11 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*
*28*
***Tana daga kwancen tana fama da ciwon mara wanda ke nukurkusar ta su zarah suka shigo ita da mufida kowaccensu da alamun gajiya atare da ita,
Cikin wannan hali ta janyo wayarta tana sake duba sakon nashi wanda yarubuto mata,
_ki shirya kayanki gobe da safe zamu wuce Abuja._
"Anty mun dawo..." Mufida ta fada tana kokarin zama gefen gadon nata batayi magana ba sakamakon yawu da ya tarar mata abaki,tashi tayi taje ta zubar ta dawo ta kwanta,
Wasa wasa tashin zuciya ya sako ta agaba ga shegen rashin dadin baki dake damunta kamar wata mai ciki haka yawu zai yita cika mata baki dayake wani lokacin period yana da wannan tsiyar duk sai yamayar dakai mai laulayin dole,zuwa bayan ishah har ta galabaita dan sai da lamarin ya kaita da yin amai,amai tayita kwarawa kuma tana gamawa cikin ta shima ya rude ta sake komawa cikin toilet din ai tuni su mufida suka tafi suka kaiwa hajiya tsegumin ai ga Anty can tana ta amai bata da lafiya,hajiya tare da umma ai da hanzarinsu suka taho kamar zasu tashi sama,
Tana kwance ta sauya kayan jikinta sakamakon wanda ke jikin nata sun baci da aman da tayi,cikin rudu hajiya da umma keyi mata sannu tana daga musu kai tana kokarin yin magana wani aman yasake turnuko mata cikin sauri ta tashi ta nufi toilet taje ta yi acan,
Fita hajiya tayi ta kira Khalil awaya lokacin shi yana can ma tare da baki suna ganawa,
"Mu'azzam kabar duk abinda kake yi maza kazo matarka babu lafiya amma ka fara kiran likita tukunna...."
Abinda yaji hajiya tace kenan sannan ta katse wayar, Zaid ya kira yace yaje ya dauko Dr,
Hanan na kwance saman gado tana ta karkarwar sanyi suka shigo shida Dr din kowa fita yayi yabasu wuri,yana gaba Dr yana biye dashi abaya,ajiye dan first aid box dinsa yayi likitan yana dan yimata tambayoyi,
"Akwai juna biyu ne?"
Girgiza kai tayi idanuwanta arufe,
"When last kika ga al'adarki?"
"Last month banyi ba" Tabashi amsa cikeda kunya saboda Khalil dake tsaye kyam yana sauraren su,
"Dama kina tsallaken wata ne?"
Girgiza masa kai tayi kuma cikin yamutsa fuska tace "A'a"
"Akwai amai?" Kai ta daga masa,
"Akwai ciwon kai?" Girgiza kai tayi alamar babu,
Dafa wuyanta yayi yaji akwai zazzabi sannan ya dan dudduba idanuwanta bayan ya dan bubbudesu. Magani ya soma duba mata yana cigaba da bayanin cewa ai ba wata matsala bace dama dayawan mata sukan samu irin wannan laulaye laulayen lokacin da zasu yi period, Khalil na tsaye yana daddana wayarshi kamar baya jinsu,ganin hankalinsa yana kan waya yasata dan bude idanuwanta ta kalleshi sannan ta mayar dasu ta rufe,saida yagama hada maganin tsaf sannan ya bata yace taci abinci komai kankantarshi sai ta sha magani daga haka suka fita shi Khalil bai ce komai ba,afalo ya tarar dasu hajiya dukkaninsu zaune suna jiran fitowarsu cewa yayi bari ya sallami Dr yadawo,baifi minti biyar da fita ba sai gashi yadawo amma bai samensu ba sai acikin bedroom din da take ciki ya iskesu anata lallabata ana tambayar wai me take son ci akawo mata? Tsayawa yayi ya harde hannuwanshi akirjinsa yana kallon ikon Allah domin su duk atunaninsu juna biyu Hanan tasamu wai dan sunga tana amai basu san lalurar su ce ta mata ba duk wata,
"Ki daure kici wani abu kinji.... Kinga ai yanzu dole sai kin kula,me za akawo miki?" Hajiya ta bukata cikin kulawa,
"Custard powder kadai zan sha itama kar asa sugar....." Ta fada cikin rashin kwarin jiki,
"Ke zarah maza tashi kuje ku hado mata custard..." Inji umma barira,
Shi abinma sai yaso bashi dariya saboda yanda duk su hajiya suka bi suka rude sunata lallabata,sai da tasha custard din tasha magani sannan suka fita suka barta,
Shima yana shirin fita hajiya tazo ta dakatar dashi,
"Khalil nace yaushe matar taka tafara wannan laulayin ne? Idan tana yawan yin aman ai sai insa asamo mata magani,kasan masu juna biyu sai da kula"
"Toh hajiya"
Daga haka yasamu tabarshi yafita,kulawa sosai ake bawa Hanan dan da safe ma kafin su tafi hajiya nata jawa Khalil kunnen yarinka kulawa da Hanan,da tafiyar ma hajiya cewa tayi sai abari wai har Hanan din ta warware sai da Hanan din tace mata ai itama akwai abinda zatayi idan taje Abujan zatayi clearance to jin haka yasa hajiya amincewa suka kama hanya suka tafi tana sake jaddada wai arinka kulawa da Hanan shi dai bai ce ba juna biyun bane yai shiru yana binsu da ido.
Duk da cewa bata baccin mota yau kam ta yi shi dan tunda suka baro gombe take tikar bacci har lokacin da suka shiga garin Abuja lokacin anata sheka uban ruwa dan tun daga farkon abuja ake zubashi,
Har suka shiga cikin compound din gidan Hanan bata saniba domin tana can tana ta sharar baccinta,sai da Aryan ya bude murya yace,
"Mommy ki tashi anzo gida..."
Firgigit tayi ta mike domin kamar acikin mafarki taji maganar tashi,a dan tsorace ta juya ta kalli Khalil wanda ke zaune kusa da ita,tashi tayi tafita ta nufi ciki tana dan dingishi tana zuwa bedroom dinta ta rage kayan jikinta ta sake kwanciya domin a mutukar gajiye jikinta yake tamkar anyi mata dukan tsiya. Ta jima tana bacci dan sai la'asar sannan ta tashi tayi wanka ta fita wurinsu umma da ke babban falon kasa ita da Aryan wanda ke ta wasa da keken sa,itama zama tayi bayan ta zubo abinci dama aikin kenan daga ci sai bacci bayan shi babu abun yi.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya su Aryan tuni sun koma makaranta shi kuma Khalil yakoma kan harkokinsa shima dan ko ganuwa ma bayayi kullum da inda zaije,
Hanan kuwa tun bata damuwa rashin daidaituwar dake tsakaninta da Khalil har tafara damuwa,bata da aiki sai na tunaninsa da mafarke mafarke akansa gaba daya ta rame ta kanjale gata dai a katon gida lafiyayye zata ci zata sha ba aikin komai take yiba amma da yake akwai damuwa acikin zuciyarta shiyasa duk ta zuke dan ko ganinsa ma bata yi tsakaninta dashi text massage ne idan tana son wani abu ko kuma tana son zataje wani wuri kuma duk abinda ta nema ko ta bukata baya hanata yana sawa a kawo mata,
Shima anasa b'angaren har gobe bai daina kukan rashin matarsa ba domin halin da yake ciki yafara damunsa ada yayi tunanin zai iya rike bukatarsa ba tare da shiga wani hali ba amma yanzu ya ga abun yana neman faskara domin kullum cikin shan pills yake wai ko zaiji dama dama gashi yana yin azumin litinin da alhamis amma duk jiya iyau,
Hajiyarshi kuwa duk lokacin da yaje gombe cikin tambayar sa yajikin Hanan take yana dai kulawa da ita ko? Wannan zuwan da yayi last kuwa hajiya harda bashi sassake sassake na gargajiya wai maganin laulayine na masu ciki yana tsayar da amai da sauran su shidai baice komai ba ya karbo yataho dashi da yazo sai yabawa umma saboda su Hanan basa nan suna makaranta ita da Aryan,
"Umma gashi wai maganin Sa'adatu ne idan ta dawo sai kibata....."
"Na menene?" Umma ta tambayeshi,
"Maganin laulayine wai inji hajiya...."
"Au toh toh, Allah yasa adace Allah sarki dama ai yarinyar nan duk ta zuke ta lalace wallahi cikin nan na wahalar da ita... Allah dai yaraba lafiya"
"Amin" ya amsa daga nan yafita,
Bayan su Hanan sun dawo tana falo tana tsara lesson plan dinta umma tazo ta kawo mata maganin da Khalil yakawo karba kawai tayi tace ta gode,kwalla taji ta ciko mata ido sakamakon damuwar dake ranta gashi kullum mujahid cikin turo mata da massage yake amma tayi biris dashi bata kulawa wallahi kallo daya idan kayi mata zaka fahimci tana da damuwa,sau da dama sai taji kamar ta tura masa da text massage ta fada masa sirrin zuciyarta amma sai taga rashin dacewar hakan,idan tayi haka ta disga kanta kuma bata siyawa kanta daraja ba.
Yau dai tana cikin farin ciki saboda zuwan anty salaha yayarta dan rabonta da ita tun bikinta yau watanni shida kenan kuma wata tara da fara service dinta dan saura yan watanni su gama,
Binta da kallo kawai anty salaha keyi saboda yanda taga ta rame tayi kanjal kanjal da ita kamar ba itace cikin wannan daular ba,
"Gaskiya Hanan banji dadin ganinki ba haka, wannan uwar ramar da kikayi duk ta mecece? Baki rasa ciba baki rasa sha ba meyake damunki?"
Dan jimm tayi dan ta rasa me zata cewa anty salaha,ada tana ta kukan bata son minister bata kaunar shi ayanzu kuma kukan tsananin sonshi da kaunar shi take duk da shi nasa hankalin ba akanta yake ba ko ganinsa yanzu bata samun yi,sai tayi sati daya ko fiye da haka bata ganshi ba,da yake bata da abin fada haka taja bakinta tayi shiru tana sauraren fadan da anty salaha keta faman yimata tana cewa yadace dai yanzu ace ta kwantar da hankalinta ta yi zamanta agidan mijinta tunda ita anty salaha bata san abinda ke cikin ranta ba. Kwanan anty salaha biyu sannan ta tafi kuma ko haduwa basuyi da Khalil ba dan baya nan sai kudi da ya aiko PA dashi ya kawowa Hanan dan tayi masa massage cewa anty salaha tazo.
Tun bayan tafiyar anty salaha tasake shiga cikin damuwa sosai kamar wacce ke cikin kurkuku haka take jinta gaba daya yanzu ta rasa abinda zatayi taji dadi,da yake ranar weekend ne kuka kawai ta zauna tanayi adaki ahaka Aryan yaje ya sameta,ganin tana kuka yasashi fita da gudu zuwa part din Khalil dama suna tare tun safe a dakinshi,yana kwance kan gadonshi sanye da kananan kaya yana aiki a system dinshi dalilin da yasa ma bai fita ba kenan sai ganin Aryan yayi yafado yana fada masa wai ga mommy can tana kuka adaki suje yagani,rufe system din yayi yasa slippers dinshi suka fita suka nufi bangarenta.....
0 comments:
Post a Comment