***Tana kwance tana sharbar kuka kamar wacce aka daka haka suka shiga suka tarar da ita,wuri Khalil ya samu ya zauna bayan yacewa Aryan yaje wurin umma ya gaidata saboda yau bai sauka downstairs ba kwata kwata,
Dan bude idanuwansa yayi akanta yana kallon yanda take kuka duk tabi ta cika masa kunne domin kukan yana dan fitane da sauti,
"Me yafaru kike kuka....?" Ya tambayeta idanuwanshi na zagaya dakin yana kallonsa komai dai neat ya ganshi babu Kaya awarwargaje,jin muryar sa yasata rage kukanta amma ta kasa magana sai shassheka take yi,
"Bakya jine? Ina tambayar ki me aka yimiki kike kuka? Ko ciwon Marar ne?" Yasake fada cikin fada kadan domin shi ya tsani kuka babu gaira ba dan dalili musamman ma na karamin yaro ko mace mutane biyun nan yana da weakness akansu,
"Babu komai..." Ta bashi amsa tana jan hanci amma acikin zuciyarta ji take inama zata iya da ta ce masa "sonka da kaunar ka ne" Sai dai amma tasan abune da bazata taba iya furta masa ba duk kuwa da cewa yana azabtar da zuciyarta,
"Kukan jin dadi kike yi?" Taji ya fada kuma wannan karon idanuwanshi suna kanta kyarr hakan yasa ta kasa bashi amsa saima sake tukunkune kanta da tayi,
"Duniyar ce tayi miki dadi shine kika zauna kina yiwa mutane kuka?"
Mikewa tsaye yayi har yana shirin fita idonsa ya sauka kan maganinta da ke ajiye saman mirror wanda hajiya ta bada akawo mata, karasawa yayi ya dauka yana dubawa,
"Meye wannan kuma?"
Daga idanuwanta tayi wadanda suke jajur ta kalleshi,
"Maganin laulayi nane..."
Juyawa yayi ya kalleta cike da mamaki har bai san lokacin da yafurta,
"Laulayi?"
"Ehh mana,ba ana bawa masu ciki maganin tsayar da amai da tara yawu ba shine nima aka kawo min nikuma na ajiye kafin infara....."
Sosai maganganun ta suka bashi mamaki har baima san lokacin da yayi murmushi ba unexpected murmushin ya subuce masa "lallai yarinyar nan yar drama ce" yafada acikin ransa amma afili sai ya ajiye maganin ya kalleta,
"Kin kyauta...."
Daga haka yafita daga cikin dakin yana mamakin bakin Hanan wato magana ta fada masa kenan ko yaya?
Itama mamakin kanta da kanta take yi yanda ta iya bude baki ta fada masa haka amma ai gara da ta fada masa tunda ai shine yayiwa su hajiyan karyar wai tana da ciki saboda kar su zargeshi da tauye mata hakki,
Tashi tayi ta shiga toilet tayi wanka da ruwan dumi sannan tafito ta zira doguwar riga ta koma ta kwanta yau ita haushin kowa take ji shiyasa ma bata fita ba tunda ta tashi adaki yau tayi rayuwarta umma barira ma da taji shiru sai dakin ta biyota tana tambayar ta ko lafiya bata fito ba yau? Cewa tayi babu komai kawai dai bata jin dadin jikinta ne,
"Sai hakuri ai,rainon ciki haka yake sai anhada da hakuri idan ba haifeshi akayi ba lafiya bata fiya samuwa dari bisa dari ba......"
Shiru tayi tana sauraren umma kuma tana jin tausayin su acikin ranta saboda su duk sun zaci cikinne da ita dagaske basu san gadar zare ce Khalil ya shirya musu ba. Haka taci gaba da zaman takura wanda ba kowa ne ya takurata ba itace kawai ke takura kanta.
***
Mujahid
Duk da cewa idan yayiwa Hanan text massage yanzu bata kulashi hakan baisa ya daina ba, sannan baya jin zai karbi bukatar sumayya har ya amince yafara soyayya da ita,
Rashin kulashin da Hanan keyi shi yafi komai daga masa hankali ahalin yanzu duk da dai dama bawai kalaman soyayya yake tura mata ba gashi ko ta WhatsApp bata kulashi daga baya ma sai yaga kamar tayi blocking dinshi nan abu ya sake hadar masa goma da ashirin,
Sumayya kuwa ganin tana ta faman shassharreshi tana dauke masa kai ba kamar yadda ta saba ba ada hakan ko ajikinsa sai dai wani lokacin sai yakanji babu dadi irin yanda yarinyar ko kallo bai isheta ba gaisuwa ma sai ta gadama take gaisheshi,
Yau da yake weekend ne yana kwance falon mami da remote hannunshi yana kallon kwallon kafa ta bude kofa ta shigo bata ko kalleshi ba tawuce sai yaji hakan ya kona masa rai fiye da tunaninsa,har shi zata zo ta wuce bata gaisar ba?
Bai gama hucewa daga wannan fushin ba yadawo daga masallaci sallar azahar yazo ya tarar dasu ita da mami tana cemata taje dakinshi ta dauko mata bedsheet dinshi zata hada cikin kayan wanki budar bakinta sai cewa tayi,
"Mami ni bana shiga dakinsa yanzu sai dai intura mai aiki ta dauko miki...."
"Yaushe kika daina shiga dakin yayan naki sumayya? Dan uwanki ne fa"
Kafin tasake magana ya sako kai yashigo dama yana tsaye yana ji, yarinyar nan bata taba bashi haushi irin na yau ba,
"Ke je ki zubo min abinci idan kin gadama...." Yafada yana kishingida saman kujera,kamar bata so haka ta tashi ta wuce kitchen tana ta turo baki alamar dole aka yimata,kwafa yayi da karfi ya kalli mami yace,
"Wallahi na kusa balla yarinyar nan tunda bata da kunya,wai ni ban isa ta gaida ni ba? Dazu fa ina zaune tazo ta wuce kamar bata ganni ba...."
Murmushi mami tayi tace, "To me yakawo maganar ballawa dan kawai bata gaida ka ba.."
"Ai dama mami duk kece kike goyon bayanta wallahi"
Daidai lokacin sumayya ta fito rike da plate din Brown rice with prawn, mango and avocado salad,ajiye masa tayi agabansa tajuya zata tafi tana sake turo baki,
"Ke zo nan...dauko min juice adakina cikin fridge...."
Tana sake turo baki tajuya ta wuce,dariya mami tayi tana fadin "To nima sai ki taho min da nawa aiken da nayi miki dazu kika turje wai ke bakya shiga sai kace dakin surukinki".
***
Kwanci tashi yanzu saura wata daya su Hanan su kammala service dinsu,rabon da ta sa Khalil a idonta kuwa anfi sati domin shi baya ma nan yaje k'asar Cameroon kwananshi shida acan sai jiya da daddare yadawo,
Cikin sanyin jiki da damuwa take shiryawa tana ta sakin dan karamin tsaki ada bata da burin da yawuce taganta sanye da kayan NYSC tana yin service amma yanzu da tafiya tayi tafiya bata da babban buri wanda yawuce taga tacire wadannan kayan ta karbi certificate dinta a hannu,
"Mtswwww wallahi na tsani lectures dinnan na tsiya haka kawai dan kar abar mutum yahuta...... Kaki zuwa kuma suce zasu baka query"
Wani tsakin ta sake ja sannan ta mike tasa kakinta, farin hijabi ta dauka tafito ta tsuke cikin kayanta na NYSC harda takalmi jungle boot a kafarta ta rataya hijabinta a kafada tana saukowa daga sama zuwa downstairs,itafa yanzu duk NYSC dinnan ta fita ranta ji takeyi kamar ta janyo ranar P. O. P dinnan nasu ayi ayi a bata kwalinta amma haka kawai sai gayyar lectures din dole,
Tana saukowa shi kuma yana fitowa daga bedroom din umma,tsayawa sukayi dukkaninsu suna kallon juna na tsawon wasu yan mintuna,
"Ina kwana....?" Ta fada cikin duburburcewa sakamakon hada idanuwa da suka yi,
"Lafiya lau....." Daga haka ya gegeta yawuce ya haura sama,binsa tayi da kallo har sai da ya bacewa ganinta,kai ai dole ma ta lalace bata taba sanin cewa so cuta ne ba sai yanzu,ashe dama haka mutum yake ji idan yakamu da son wanda bai damu dashi ba? Haka masoyin da ake nunawa halin ko inkula yake kasancewa cikin damuwa da bacin rai?
Tun daga lokacin bata kara sakashi a idonta ba sai ranar wata laraba taga text dinshi wai ta shirya zasuje gombe kuma aranar zasu dawo anyi haihuwa, Laila ta haihu yar abban London hajiya ce tace masa lallai lallai yakai matarsa itama tayi barka ko kuma taje suna da hakane zata san dangi suma su santa,
Da yake ranar aikine Aryan baya nan yana school,shiryawa tayi taci kwalliya cikin atamfa exclusive koriya dinkin riga da skirt kamar yadda ta saba dinkunanta, green din mayafi ta yafa sannan ta dauki handbag wadda ta dace da shigarta haka ma takalminta, tana falon k'asa zaune ita da umma tana jiransa amma har azahar shiru wai meeting yakeyi da mr president daga k'arshe dai sai PA yaturo wai yazo ya dauketa yakaita office dinshi sai su wuce ta can basai yadawo gida ba,
Office din nashi yayi masifar haduwa kamar kar ka fita daga ciki dan tsabar kyau baya ciki yana can meeting dan haka ta shiga ciki ta zauna a inda aka kebance dan baki na musamman, kamar yanda yake babu hayaniya to haka office din nasa shima babu wasu takarcen hayaniya aciki,komai atsare kuma ashirye,kan table dinsa kuwa kambun girmamawa ne sunfi abinda suka fi irin wadanda ake bashi sannan ga hotunanshi nan manya manya kafe acikin office din wani shi kadai wasu kuma tare da mutane,wasu kuma tare da matasa yan kwallo,kan teburinshi kuwa wani dan karamin frame ne mai dauke da hoton Aryan ajiki,
"Ohh ni Sa'adatu wannan bawan Allah yana kaunar d'an nan nasa...... Har a office dinma?"
Tana nan zaune tana zaman jiransa duk tagama kosawa duk da cewa ga kayan kallo nan tv katuwa nata faman aiki ankamo tashar labarai ga fridge can kuma shima gefe guda dama kishin ruwa take ji dan haka ta mike ta nufi fridge din da kanta tana zuwa ta budeshi nan ta ganshi tafare da kayan sanyaya makoshi iri iri sai dai kuma abinda idanuwanta suka gane mata sune suka yi sanadiyyar tsayawar numfashinta cakk take ta firfito da ido kamar zasu fado kasa dan tsananin firgici da tsoro.....................鉁嶏笍
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:12 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*
*30*
***Jikinta rawa yashiga yi babu bata lokaci cikin hanzari ta mayar da fridge din ta rufe ta koma ta zauna tana al'ajabin wannan lamari me neman sakata cikin wasi wasi,
"Giya?..... Dama minister mashayin giya ne? Kai anya kuwa iyayensa da abbanta sun sani? Kai ko iyayenshi sun sani abbanta bai saniba dan idan har yana da masaniyar haka to babu abinda zaisa ya dauki auren yarsa ya baiwa mashayi..... Innalillahi" Ta fada acikin zuciyarta tana mai rafka tagumi saboda takaici da nadamar fadawa tarkon sonshi da suka lullubeta lokaci guda,
Gaba daya ma ta rasa abinda zatayi taji sanyi acikin ranta,gaskiya Abban Aryan yayi bala'in bata kunya,ohh Allah kowa dai ka gani kabarshi ayanda ka ganshi domin Allah kadai shine yasan sirrin cikinsa da wajensa,ai ko cikin mafarki bata taba kawowa kanta cewa wannan bawan Allahn zai sha giya ba ashe ashe,
Zaman jiransa taci gaba dayi duk zaman yasoma gundurarta domin ta gaji da jira,ta saka ta warware ahaka yashigo office din tare da wasu mutum biyar wadanda take kyautata zaton cewa bakinsa ne, kasancewar tana wuri daya babu wanda yayi mata magana saida yagama dasu ya sallamesu sannan yamike daga kan kujerarsa ita kuma sai daure fuska take yi kamar me,
"Muje ko....." Daga haka yayi gaba itama ta mike tabishi abaya securities suka dafa musu baya,
Har acikin mota babu wanda yace uffan saida suka fara tafiya sannan yayi magana hankalinsa yana kan wayar dake hannunsa,
"Me zaki kai mata?" Shine tambayar da taji yayi mata idanuwanshi akan screen din wayarsa,saida ta dan yi jimm sannan tabashi amsa,
"Duk abinda yasamu...."
Bai sake magana ba itama haka asalima dauke kanta tayi zuwa glass din motar tana kallon birnin abuja domin bata taba zuwa nan haka ba sai yau,awani katafaren supermarket taga sun tsaya,dan karkacewa yayi yana laluba aljihunsa duka guda biyun,
"Ohh Allah ashema kudin nawa sun kare...." Yafada yana kokarin ciro yan canjin da suka rage masa ajikinsa domin duk ya rabar da kudin mawa masu neman taimako da bakin da suke zuwa office gaisuwa,
Sabbin yan dubu dubu taga ya mika mata amma bai kai rafa guda ba sai dai da dan yawanshi badai zata iya kiyasta ko nawane adadinsu ba,
"Gashi ki siyo mata abinda kika ga yadace..... Karki zauna ki bata min lokaci inada abinyi"
Hannu biyu ta saka ta karba sannan tafita wasu daga cikin securities din suka take mata baya har zuwa cikin supermarket din,duba abunda yadace ta siya tafara saboda nafarko dai tasan tunda danginsu masu kudi ne idan ta siyi atamfa watakila arena ko akushe dan haka sai kawai ta yanke shawarar siyan kayan babies,
Hadaddun rigunan jarirai ta siya guda biyar masu tsada sannan ta siyi takalma da socks dinsu set daya sannan ta kara da kayan shafe shafen yara irinsu sabulun wankansu,turare,man shafawa,powder da sauransu shima set daya, atakaice dai tayi siyayya ta kusan fin dubu hamsin,kuma kayan bawani dayawa fal bane ba a'a kawai dai da yake masu tsada ne shiyasa,
Tana shiga mota aka mika mata kayan ta ajiye atsakiyarsu, "Gashi...."
Sannan ta mika masa canjinsa da yayi saura wanda shima bata san ko nawa bane,
"Ga guntun canjinka"
"Ajiye awurinki" Yabata amsa atakaice yana kokarin kara wayarshi a kunnenshi,
"Na'am Aryan..... Andawo daga school ko?...... Kaci abinci?......Ka koshi sosai?...... Yawwa lovely son......ok bye bye.....i love u too"
Tana jinsa har yayi wayar tashi yagama,yana gamawa ya mayar da ita aljihunsa ya ajiye ya sake ciro dayar itama yashiga latsawa,yanda ya manta da lamarinta itama haka ta manta da nashi ta jinginar da kanta jikin kujera bayan ta lumshe idanuwanta cike da takaicinsa duk kamshinsa yabi ya rikitata ya cika mata hanci,ba dan kar tayi karya ba to da zata iya cewa tunda take bata taba jin kamshi mai dadi mai sanyaya rai da zuciya kuma mai saka nutsuwa kwatankwacin nasa ba,wato kamshin nasa ne na dabanne ko acikin dubbai. Har suka hari gombe zaman kurame suke yi sai shi da yake yin waya jifa jifa dan daga tahowarsu zuwa yanzu taji yayi waya yakai sau goma, lallai mulki ba sauki ne dan koda amsa waya aka barka anbarka da aiki tuk'uru,
Basu suka shiga garin gombe ba sai la'asar,gidan Laila suka fara zuwa wato mai jego,tare suka shiga ciki ita dashi dan shine ma yayi mata jagora saboda ita ba taba zuwa tayi ba wancan karon da suka je barka da salla basu samu damar zuwa gidan laila dinba dayake sunyi yawo da yawa ranar,
Yanayin yanda taga gidan ya tabbatar mata da cewa itama Laila din wani hamshakin take aure dan gidanta kadai abin kallo ne,a falo aka yi musu masauki mai dauke da kayan alatu,suna zaune tana kan kujerar da take kusa dashi laila tafito rike da jaririnta wanda ke nannade cikin towel mai laushi,
"Oyoyo yaya Khalil..... Sannunku da zuwa" Laila ta fada fuskarta dauke da fara'a lokacin da tayi ido biyu dasu,
"Laila maman 3" Ya fada yana murmushi, karasawa tayi ta mika masa jaririn tana yiwa Hanan barka da zuwa,zama tayi da kyar tana dan ciccije baki, Khalil ta fara gaisarwa sannan ta juya suka gaisa da Hanan cikin sakin fuska,
Basu fi mintuna goma ba agidan suka fito dan ruwa kadai suka sha suka yimata sallama suka fita bayan Hanan ta ajiye mata kayan barkar da ta tafi mata dashi,
Daga can gidan su Khalil suka wuce acan suka yi sallar la'asar suka ci abinci hajiya sai kaffa kaffa take yi da Hanan tana ta tambayar ta wai ko akwai abinda take so? Shi kam shiru yayi yana saurarensu yarasa wanne irin so hajiya ke yiwa yarinyar nan dan tunda taji zasu zo tayi musu tanadi shiyasa da zasu tafi harda su garin kubewa busasshiya da garin kuka da su daddawa ga kindirmo mai kyau da sauran kayan gargajiya wai tasan mata masu juna biyu akwai kwadaye kwadaye to gashi nan ko zata bukaci wani abu aciki ta huta nema,duk yadda Khalil yaso dakewa kasawa yayi dan saida ta kaishi da yin murmushi yawuce yabarsu suna sallama,
Kofar gidansu lokacin da suka fito cike yake dam da mutane yara da manya da matasa,hakuri yace abasu zuwa nanda kwana biyu zai dawo,gaskiya yan gombe suna yinsa kuma suna kaunar sa sai yau ta sake tabbatar da hakan domin har suka bar cikin garin mutane suna biye dasu sunyi convoy ashe dama kusan duk lokacin da zaizo haka suke yimasa sai sun rakashi har gida idan kuma zai tafi nanma sai sun rakashi wajen gari sannan suke komawa. Wannan karonma kamar dazu haka tafiyar tasu ta kasance baya da amsa waya babu wani abu da yake yi,ita kam duk zuciyarta babu dadi inbanda kuna babu abinda take yi,bacin ran abinda ta gani dazu yaki gogewa cikin zuciyarta,
Bayan sallar magriba suka shiga garin Abuja wanda ke dauke da daddadar iska tana kadawa garin lullube da ni'imar ubangiji,ajiyeta suka yi daga nan ko gidan bai shiga ba suka sake juyawa zasu koma office a wannan lokacin,
A dakin umma ta samu Aryan da umman yana kwance yayi pillow da cinyarta yana game a wayarshi sai shagwaba yake tayi umma nata shan kansa tana lallaba shi yaci abinci wai sai yagama game, shigowar Hanan ta sashi zabura ya yar da wayar yatashi yaje ya rungumeta yana yimata oyoyo,itama rungumeshi tayi tana shafa kumatunsa,
"Cutie"
"Mommy sannu da zuwa"
"Yawwa cutie nah"
"Sannu da zuwa,to kaga shikenan ma tunda ga ummanka ta dawo nima sai inhuta" inji umma barira,
Dariya Hanan tayi ta kama hannunsa,
"Au umma haka zakice? Mai gidane fa"
"Wannan mai gidan ai rigimamme ne kyaleshi"
Dariya Hanan tayi taja Aryan suka hau sama domin ko salla bata yiba,sai da ta kammala sallolinta sannan suka koma dakin umma can suka raba dare suna hira dan har 11 lokacin tuni Aryan yajima da yin bacci,
Saida ta kaishi dakinshi ta kwantar dashi sannan ta wuce zuwa nata,sam babu alamar bacci acikin idonta tunani ne kawai keta mutsuttsukar zuciyarta,ta rasa dalilin da yasa abun ya tsaye mata arai har haka ko dan tana yimasa kallon mutumin kirki na arziki ne shiyasa yanzu abun ke damunta? Tasan watakila yanzu ya shigo gidan tunda 12 tayi,text massage ta rubuta ta tura masa,
Fitowarsa daga wanka kenan yana saka kayan baccinsa yaji shigowar text dinta,karasa shiryawa yayi ya dauki wayar yazauna gefen gado,
_Dan Allah ina son yin magana dakai Abban Aryan amma ina so kayi min kyakkyawar fahimta...._
Shine abinda yaga Hanan ta turo masa,dan yatsanshi yakai bakinsa yana shafa lips dinsa,magana to wacce irin magana take son yi dashi? Kodai har yanzu bata saduda bane ta rungumi k'addarar ubangiji,
_Ok,ina jinki._
Dama tasan amsar dai bazata wuce haka ba tunda shi kamar dogon bayani wahala yake bashi,sake gyara kwanciyar ta tayi ta tura masa da reply kamar haka,
_Dan Allah kana shan giya ne?._
Ganin sakonta yasashi bude idanuwanshi sosai sannan ya tura mata da,
_Zo ina son ganinki._
Gabanta ne taji yafara faduwa jin wai tazo yana kiranta,a tsorace tasaka rigar saman kayan baccinta sannan ta yafa mayafi ta fita,wata iskace mai sanyi da dadi ke kadawa sannan ga sararin samaniya yayi kyau taurari sun kara masa ado da k'awa, ta samu damar ganin hakanne dalilin fitarta kuma dan gaban corridor din da zai sadaka da sashen Khalil open ne babu roofing awurin shiyasa zaka samu damar ganin sararin samaniya,
Tamkar marar gaskiya haka ta shiga falon nasa wanda yake shiru dan babu kowa aciki,Allah ya sota ta taho da wayar ta da bata san yanda zatayi ba,text ta tura masa cewar gata tazo tana falo,kimanin mintuna biyu taji motsin fitowarsa,kallo daya tayi masa ta sunkuyar da kanta kasa, sanye yake da kayan bacci na maza white colour riga da wando masu santsin gaske,
Zama yayi a opposite dinta yana rike da wayarshi,
"Kika ce ina shan giya ko me?"
Shiru tayi tana wasa da yan yatsunta,
"Ba kiji ne?"
Dago kai tayi ta kalleshi nan taga idanuwanshi kyarr akanta ya tallafe kumatunsa gaba daya da hannuwanshi,
"Ina ji...."
"Waye yafada miki ina shan giya...?"
"Babu kowa..."
"To meyasa kika yimin wannan tambayar?"
Duburburcewa taso yi saboda tambayoyin nasa na neman yimata yawa to abunka da kwararren tsohon dan jarida,
"Meyasa kika yimin wannan tambayar? Kin taba ganina ina Shane ko kin taba ganina acikin maye?"
Girgiza kai tayi alamar a'a,
"To why did you asked?"
"Gani dama nayi dazu a office dinka acikin fridge...."
Shiru yayi yana kallonta baice komai ba har saida ta fitar da tsammanin zaice wani abu sai kuma taji yace,
"To abinda kika gani ba giya bane,lemo kika gani saboda ni babu abinda ya hadani da giya banko taba dandanata ba bare insha,ki rinka tabbatar da ingancin magana kafin kiyi comment akanshi...... Bakauyiya kawai kinga lemo kince giya"
Duk da bata gane ayanayin da yayi maganar ba shin cikin bacin raine ko sabanin haka ita dai hakuri ta fara bashi,
"Kayi hakuri bazan kara ba"
Sai da ta sake maimaitawa sannan yamike yana fadin,
"Is alright"
Fita yayi tabi bayansa,shi dakin Aryan ya hara ita kuma ta wuce nata tana jin nutsuwa na saukar mata, murmushi tayi da tuno sunan da ya kirata dashi wai bakauyiya gaskiya taji kunya dan tabbas kam bata karanta sunan lemon ba kawai dai taga kwalba kuma green an kawatata,ashe dan Allah wai lemo ne dole ne yace da ita yar kauye.
***
Yau ne su Hanan ke yin Pop dinsu ranta fari tass taje ta karbo certificate dinta wahala dai ta kare hutu zai samu zata huta da wannan gayyar fita PPA da CDs dinnan masu hana mutum isasshen bacci,hotuna suka sha Sosai ita da friends dinta yan batch dinsu wadanda suka gama tare da ta dawo gida ma sunyi da Aryan yafi kala ashirin,shima uban gayyar lokacin da takai masa certificate din "congratulations" yace da ita kadai.
Bayan kwana biyu da gamawar su kuma duk sai taji babu dadi domin tayi bacci har ya isheta wuni take yi tana bacci yanzu har takai minzalin da ko baccinma bai fiya daukarta sosai ba,
Satinsu biyu da gama service tana daki tana gyara wardrobe dinta umma ta shigo mata agigice cikin tashin hankali da dimuwa hannunta aka......................鉁嶏笍
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:12 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*
*31*
***Sake gigicewa tayi ta rikice ganin umma na hawaye tuni jikinta ya dauki rawa dan tasan babu ko tantama mutuwa akayi kuma abu mai yuyuwane kila ace minister ne ya mutu,
"Umma waye ya mutu? Shikenan ya mutu...."
Goge hawayenta umma tayi cikin damuwa da yanayin dimuwa tace,
"Ba mutuwa bace amma har gara mutuwar Allah na tuba, Aryan ne ba aganshi ba tunda aka tashi daga makaranta wai ance wasu ne sukaje suka daukoshi daga makarantar wadanda ba asan ko su waye ba....."
"Innalillahi....." Hanan ta fada gaba daya idanuwanta awaje,haba shiyasa taji shiru bai dawoba aranta har tana cewa ko kuma dai yadawo ita dince bai shigo wurinta ba,
Hawaye take son yi amma tashin hankali ya hanata sai yau ta tabbatar da cewa yaron yashiga ranta fiye da tunanin ta domin jin numfashinta take yi kamar zai dauke,
Fita umma tayi ita kuma ta samu gefen gado ta zube bayan ta kifa kanta, innalillahi kawai take ambata ahaka taji anbanko kofar d'akinta anshigo kafin ta daga kai taga waye taji anshakota,
Khalil tagani tamkar wani mahaukaci saboda yanda duk ya furgice ya rude, bata taba sanin haka ya iya fada da daga murya ba sai yau,
"Da sa hannunki acikin b'atan d'ana ko babu.....?" Yafada yana jijjigata kamar zai ballata idanuwanshi aburkice kamar wanda yasha wani abu,sake rikicewa tayi ta gigice tama rasa amsar da zata bashi,
"Dake nake magana,nace da sa hannunki cikin batan yarona?" Yasake fada cikin karaji,
Girgiza kai tashiga yi muryarta na rawa,
"Wallahi tallahi ban san komai ba akai Abban Aryan, wallahi babu hannuna, taya za ahada baki dani acutar da Aryan...."
Sake wujujjugata yayi sannan cikin kausashasshiyar murya yace, "Wallahi idan har bincike na ysnuna min cewa akwai sa hannunki sai na kasheki....."
Daga haka ya hankadata kan gado yajuya yafita da sauri gudu gudu,sai lokacin ta samu damar fashewa da kuka ai daga ganin yanda yakeyi kasan yashiga rudu jifa harda maganar kisa,kuka take yi sosai,
Shima Khalil yana can anbaza jami'an tsaro kowanne lungu da sako dake cikin garin, yan gombe kuwa tuni labari yaje musu wai ansace Aryan,sai wayar umma da Hanan ake kira amma duka wayoyinsu akashe shi kuwa dama Khalil ba asamu call forwarded wayarshi ke nunawa.
Har magriba gidan tsit kowa yana cikin daki abun duniya ya isheshi daga ita har umma babu wanda yaci koda kwayar abinci haka shima Khalil yana can yanata yawo daga nan sai nan har gidansu principal din Aryan yaje yace Wallahi idan dansa bai fitoba sai yarufe wannan makarantar tunda har cikin makaranta akaje aka sace Aryan bawai fitowa yayi wajeba,shi dai principal hakuri kawai yake bashi yana cewa insha Allah Aryan zai bayyana,masu gadin makarantar kuwa da securities sunsha tambayoyi kamar babu gobe dan tambayoyin da Khalil ya tsaresu yana yimusu ko agaban alkali ba lallai ayi musu itaba,Emah kuwa ranar yaga tashin hankali saboda shine drivern Aryan shine ke kaishi school yadawo dashi saboda shi PA abubuwan sunyi masa yawa, Emah sai da yaji kamar ya gudu kauyensu dake can anambra state kawai dai dan yasan ko ya gudune oga sai ya nemoshi shiyasa ya zauna amma daga lokacin da yaje dauko Aryan bai ganshi ba zuwa yanzu ya zagaya bandaki yafi sau goma.
Hanan tana d'akinta ta idar da sallar ishah lokacin misalin karfe 11 na dare umma ta shigo wai tazo suje asibiti ankwantar da Khalil baida lafiya hawan jininsa ya kada shi,
Wani tashin hankalin hankula suka sake shiga domin Khalil baya ko gane wanda yake kansa dayake hawan jini shima akwai kisan mummuke,daren yau dai yanda suka ga rana haka suka ganshi Hanan tayi kuka har ta gaji,
Washe gari da sassafe su hajiya suka bayyana a asibitin kowa jikinsa a sanyaye kuma fuskarsa dauke da alhini,kamar masu zaman makoki haka suka zama,shi kuwa Khalil yana can Dr Al'amin yana fama dashi dan acewar Dr nisan kwana ne da Khalil amma da ace mai kararren kwana wannan ciwon yasamu to da yanzu wani labarin akeyi ba wannan ba,
Kwanansa biyu a asibitin sannan ya dan farfado duk da baya gani yadda ya kamata haka kuma jinsa ma ya danyi kasa amma ahakan yake son wai sai yatashi yatafi neman Aryan, Zaid ne ya rirrikeshi yace yayi hakuri shi zaije neman nasa yanzu, Zaid yana fita yasake yunkurin tashi ta hanyar riko Hanan wacce ke zaune gefe,
"Karki barshi yatashi.... Idan yatashi faduwa zaiyi" Anty saudat ta fada sannan ta fita daga cikin dakin,
Riskeshi Hanan tayi ta mayar dashi ta kwantar kwalla tana fita daga cikin idanuwanta,
"Kayi hakuri Abban Aryan insha Allah, Allah zai bayyana shi,mutane sunata addu'a suma kuma jami'an tsaro suna iyakar bakin kokarin su dan ko dazu saida ministan tsaro yazo yace afada maka ka kwantar da hankalinka kaci gaba da addu'a insha Allah suna gab da samo Aryan......"
Lumshe idanuwanshi yayi wasu zafafan hawaye suka zubo masa duk sai Hanan taji tausayinsa ya kamata saboda duk abinda zaka ga babba yana kuka to abin ba karami bane, lallabashi aka yita yi har yasamu bacci,
Aranar abbanta shima yazo ya jajanta musu dama kuma mutane nata zuwa kamar anyi musu busa,asibitin kullum cika yake dam da matasa da manyan mutane sai yanzu ta sake tabbatarwa da cewa Khalil mai jama'a ne kuma ana sonsa shiyasa idan Allah yabaka dama to kayi iya bakin kokarin ka wurin kyautatawa mutane dan tayuyu zaka bukacesu agaba sai suma su taimakeka a lokacin da kake neman taimakon da kudinka baza suyi maka ba dan wani taimakon kudi bai isa yayi ba sai dai jama'a ce zasuyi maka.
Kullum cikin garin Abuja sake baza jami'an tsaro ake sannan gaba daya kafafan yada labarai koda yaushe maganar batan Aryan ne to abunku da dan masu abun,shi kuwa Khalil ya dan fara samun sauki sakamakon ruwan zamzam da Abban Hanan yasa aka nemo ya hada masa maganin hawan jini na musulunci gaskiya zamzam maganine sosai kuma sadidan. Cikin Kashi dari kashi 70 na hawan jininsa ya sauka dan tangararau yake ganin komai yanzu sannan kuma yana jin komai radau kamar da sai dai tarin damuwa dake sakashi zubar da hawaye da rashin cin abinci,idan yatuno Aryan yana hannun wadanda ba asan ko su waye ba sai yaji kamar ya hadiyi zuciya ya mutu dan bacin rai, damuwarsa bai san inda yaronsa yakeba bai san wanne hali yake cikiba sannan bai saniba ko yana raye ko ya mutu shi idanma mutuwarce to har gara Aryan ya mutu agabanshi yakaishi ya binne hankalinsa zaifi kwanciya akan ace bata yayi gaba daya, wannan al'amari shi yake sake daga masa hankali har baya kunyar zubar da hawayensa agaban koma waye dan da yan jarida suka zo asibitin domin ganawa dashi kasa cewa komai yayi inbanda kwalla da yayita fitarwa sai fitar da yan jaridar akayi daga dakin,gashi ko bacci baya samu sai idan allura Dr Al'amin yayi masa shine zai dan samu bacci akalla na awa shida zuwa bakwai,
Yau kam saida safe yasamu baccin saboda jiya da daddare kasawa yayi duk da cewa anyi masa allurar, Hanan na zaune kasa kan sallaya tana kallonsa wallahi duk tausayi yake bata idan ta kalleshi dama shi ba jiki ba kuma gashi yasake ramewa cikin kwanaki hudu kacal,yana sanye da farar t shirt da bakin jeans duk yasake zama yaro sakamakon ramar da yayi,ahankali taga ya bude idanuwansa sai kuma taga ya mayar dasu ya rufe hawaye na zirarowa ta gefen idonshi,
Tashi tayi ta matsa gaban gadon ta durkusa akan gwiwowinta ta kai hannu kan nashi wanda ke soke da cannula ajiki,bai bude idonsa ba kuma bai motsa ba,kwantar da murya tayi koda yake dama muryar tata akwance take sakamakon kukan da itama ta shassha,
"Dan Allah Abban Aryan kayi hakuri muci gaba da addu'a insha Allah Aryan zai bayyana kuma baza su samu ikon cutar dashi ba domin yana tare da kariyar ubangiji....."
Shiru tayi tana sake zuba masa ido ji take yi kamar ta rungume shi ajikinta taci gaba da rarrashinsa kamar jariri,jin za abude kofa ashigo yasata dan matsawa, Khalid ne yashigo shima hankalinsa duk yatashi dan shi bai san hakan tafaru ba sai jiya da daddare dama matsalar zaman nesa kenan sai ayi abu agida kai baza ka ji ba shiyasa har gobe yake takaicin zaman Calabar dinnan da yakeyi domin abubuwa da dama baya sanin anyi sai yazo yake ji,
Zuwan Khalid dinnema yasa Khalil ya dan samu saukin damuwarsa kasancewar wani lokacin childhood friend dinka yana da abubuwa daban daban wad'anda zai yimaka har yasamo kanka,duk da dai akwai damuwar amma ya dan ji saukinta.
Bayan sallar la'asar kawai sai ganinsa suka yi yafito daga cikin dakin da yake kwance yana bacci,kowa tashi tsaye yayi har securities dinsa, Khalid ya kalla,
"Bani aron key din motarka zanje wani wuri indawo...."
Kowa dake wurin zaro ido yayi nan aka fara tambayar ina zashi? Hajiya kuwa tiburewa tayi tace babu inda zaije idan kuwa ya dage sai ya tafi to dole yatafi da masu kula dashi shi kuma yace A'a,dafashi Khalid yayi yace,
"Haba Khalil.... Ina zaka je acikin wannan halin kuma? Kafa san yanda kuke koda yaushe mutane suna fakonku..... Dan Allah ka koma ka kwanta"
Hannun Khalid yaja suka shiga dakin mintuna biyu suka sake fitowa,
"Hajiya babu matsala insha Allah kubarshi yaje yadawo din..." Khalid yafada cikin kwantar da hankali,
Duk da haka dai hankula basu kwanta ba da fitarsa shi daya nan suka dunguma suka bishi har harabar asibitin inda yashiga motar Khalid mai dauke da bakaken gilasai,yafita daga cikin asibitin kamar zai tashi sama saboda yanda yake sharara gudu,zuba ya hara cikin kankanin lokaci ya isa yana tuki yana duba wayarshi yana bin direction din da aka bashi har ya isa wani hamshakin tangamemen gida,horn yayi wasu garada su kimanin guda biyar suka zo suka bude dukkaninsu fuskokinsu rufe da mask, ahankali yatura hancin motar tasa ciki sannan yayi parking yafito,
Sakashi suka yi atsakiya suka yimasa jagora har cikin wani kerarren falo mai dauke da Royal furnitures,juyawa sukayi suka fita yarage saura shi daya acikin falon,
Minti biyar yana tsaye hannayensa cikin wandon jeans din dake jikinsa yaji wani azababben kamshi yasoma ziyartar hancinsa ahankali cikin takun jan hankali da kasaita ta bude kofa tafito tana taunar cingum,
Daga idonsa yayi ya kalleta tana sanye cikin kayan bacci na daukar hankali farare tatas wadanda babu abinda suka boye na daga kyakkyawar surar da Allah yayi mata,doguwar rigace iya gwiwa da yar top dinta asama wacce ta tsaya iya kirjinta,
"Yesmin......" Yafurta akan labbansa,
"Barka da zuwa fadata mai girma minister....." Ta fada cikin jan hankali tana kokarin zama kan daya daga cikin kujerun da suka yiwa falon kawanya,
"Yesmin...... Ina kika kai min yaro na?" Ya fada fuskarshi babu rahma ko kadan,
"Karka damu yaronka yana nan cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali..... Babu abinda ya sameshi"
"To me kike nufi da hakan da kikayi? Me kike bukata daga gareni?" Ya bukata cikin bacin rai domin tuni hakan ya bayyana akan fuskarshi,
"Yawwa sai yanzu kazo gabar da najima ina son kazo...." Mikewa tsaye tayi tana karairaya da salo na jan hankalin duk wani da namiji mai cikakkiyar lafiya,
"Abinda najima ina so daga gareka tsawon shekara da shekaru....."
Marairaicewa tayi harda kwallar karya da yaudara,ta matsa dab dashi kamar zata rungumeshi,
"Dan Allah Khalil kaji kaina....,ka taimaka min kada ciwon sonka ya zama ajalina.....pls....pls"
Juya mata baya yayi domin yasan idan yaci gaba da kallonta ahaka za a iya samun matsala domin tausayin ta zai iya shigarshi shi kuma baya son yaji tausayin ta adaidai wannan lokacin,
"Yesmin abinda najima ina fada miki yau ma shi zan sake jaddada miki.... Bana zina ban taba yinta ba kuma bana sha'awar inyi har tsawon karshen rayuwa ta.... Ina yarona yake? Kifito min dashi dan shine yakawo ni bawai bukatar ki ba...."
Dan lumshe idanuwanta tayi sannan ta budesu akanshi wannan fa wani lakani ne aka jima da bata akanshi kuma dole sai yayi zina da ita sannan maganin zaiyi tasiri har yayi aiki gashi wannan itace damarta ta karshe idan har hakanta bai cimma ruwa ba to komai zai rushe,
"Gashi can cikin wancan dakin...."
Ta nuna masa dakin dake kusa da wanda tafito daga cikinsa, Cikin jarumta da rashin tsoro ya dirfafi dakin,
"Sadauki..."
Tafada ahankali tana kokarin bin bayansa wannan yana daya daga cikin abubuwan da ke kara ingizata duniyar son taga ta mallakeshi domin baida tsoro ko kadan ga nuna shi namiji ne agaban ko waye,
Cikin kwarin gwiwa Khalil yabude kofar dakin yashiga mai dauke da duhu dan kamar ba a halicci haske ba aduniya haka dakin yake,laluben makunnar hasken dakin yafara yi amma yarasa sai shashimawa yakeyi yana kiran,
"Aryan..... Aryan"
Haske ne yaga ya gauraye dakin cikin sauri yajuya ya kalli kofa,yesmin yagani tsaye tana rike da key din kofar dakin sannan ta cire yar rigar saman rigar baccinta gaba daya kirjinta yafito fili ta yar raga ragar dake saitin kirjin rigar,
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un...." Yafada yana juya mata baya, murmushi tayi ta kai hannu zuwa ribon dinta dake daure da yalo yalo gashin kanta nan tacire ribom din ta jefar ta baza gashin nata ya sauka saman kafadarta,takawa tafara yi ahankali tana dosarsa maganganun malaminta na sake fado mata "Sai kin yi zina dashi tunda bai taba yin zina ba sannan bukatarki zata biya..." Lumshe idanuwanta tayi cikeda kwarkwasa takai hannu zuwa gareshi......................鉁嶏笍
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:13 AM - Ummi Tandama: Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.
*32*
***Dafa kafadarshi tayi sannan cikin sanyin murya mai dauke da tsantsar yaudara yaji tace,
"Wai meyasa kake guduna ne Ibrahim? Gaka dai ahaka kamar wayayye..... Kana da kudi,kyau, kuruciya uwa uba ga mulki to meyasa bazaka more rayuwarka kaji dadi ba? Sai yaushe ne zaka waye? Idan baka huta yanzu ba sai ka tsufa ko yaya?"
Lumshe idanuwanshi yayi domin tab'ashin da tayi ji yake yi kamar ta watsa masa garwashin wuta ajikinsa,
"Yesmin..... Ki nuna min inda yarona yake kawai domin ni ba wannan ne ya kawoni ba..."
Rigar baccin dake jikinta ta soma sabulewa tana kokarin shan gabansa,
"Me kake ci na baka na zuba? Zaka ga yaronka amma har sai nima ka amince da bukata ta..."
Bude idanuwanshi yayi da zummar balbaleta da fada amma abinda idanuwanshi suka gane masa yasashi saurin runtse idanuwanshi yana furta,
"Wa'iyazubillahi.... Yesmin dama bakida hankali? Ke wacce irin sakarya ce?"
Rabon da yaga sankaceciyar budurwa tsirara har yamanta sai yau da yayi mummunan gani sanadiyyar ta,
Kokarin rungumeshi take yi yayi gaggawar matsawa nan ta sake matsowa yasake matsawa bata hak'ura ba ta sake yunkurin matsowa bai san lokacin da ya dauketa da wani gigitaccen mari ba abunka da bahago bai iya duka ba shiyasa sai da taga wasu taurari sun gilma ta idanuwanta sannan taji jinta ya dauke na dan lokaci, kuncinta ta dafe tana kallonsa cikin mamaki da bacin rai,
"Ibrahim ni ka mara? Dan kawai na nuna soyayya ta agareka?"
"Na mareki..... Ai kadanma kika gani tunda ke wawiya ce dakikiya marar tunani... Ina yarona yake? Wallahi idan baki fito min dashi ba sai nayi miki dukan kawo wuka,sai nayi shari'a dake ke saima na kasheki......sai nayi ajalinki....."
"Ka fita waje zaka samu yaronka acan amma ka sani Wallahi sai kayi nadamar abinda kayi min....sai ka san ka mareni kuma ka wulakanta ni"
Bai sake tanka mata ba yawuce ta yafita tare da bugo kofar dakin da wani mugun karfi,abakin kofa yaga biyu daga cikin garadan nan na dazu masu kama da samudawa,wani mugun kallo yayi musu sannan ya ratsa ta tsakiyarsu yawuce yana kaiwa tsakiyar falon yaga Aryan yataso da gudu yazo ya rungumeshi yana kiran,
"Daddy.... Uncle...."
Rungumeshi shima yayi sannan ya durkusa gwiwowinsa akasa yana dudduba jikin Aryan din,
"Abba na babu abinda suka yimaka? Sunyi maka wani abu?"
Jijjiga kai yayi yana sake makalkale Khalil,daukarsa yayi yajuya ya kalli bakin kofar dakin nan yaga yesmin tsaye tare da garadanta tana yimasa wani kallo mai cike da ma'anoni kala kala,fita yayi yabude motar da yazo da ita ya saka Aryan sannan ya bude side din driver shima yashiga ya zauna yayi reverse da mugun gudu yafita yabar gidan,
"Aryan ya akayi ka bari suka sace ka? Haba Aryan kaida nake ganinka kamar mai wayo ashe bahaka bane...."
"Daddy da aka tashi daga school ne sai naga mota irin tamu kuma wani mai kamada Emah yazo yakama hannuna shine nabishi muka tafi....."
"Kaima dai soko ne Aryan,you are such an idiot....daga ganin mutum sai ka bishi? Suna baka abinci kana ci?"
Kai ya daga babu bakin magana duk ya tsure dan yasan watakila sai Khalil ya zaneshi saboda duk wannan soyayyar da yake yimasa fa idan yayi laifi babba to rufe ido yake ya zaneshi da belt shiyasa tun yanzu tsoro ya darsu a zuciyarsa dan yasan zaisha duka.
Can asibiti kuwa hankula sun sake tashi domin anata kiran wayar Khalil baya dagawa kuma gashi shiru shiru bai dawo ba, hajiya fadi take,
"Sai da nace yaron nan kar yadauki motar nan ya fita amma ina sai da yafice.... Ko meyasa yakeda taurin kai oho"
Suna tsaye carko carko kowa na fadin albarkacin bakinsa Khalid ya koma gefe ya dauki wayar da Khalil ke yimasa,
"Ya andace kuwa?"
"Ehh gashi na taho dashi dagaske ai itace ta saceshi,ku tattaro ku taho gida kawai..."
Katse wayar Khalid yayi yakoma wurin su hajiya yace suje su tafi gida shima khalil din ya tafi gida ansamo Aryan dan tare suke nan sukaje suka dudduru amota suka nufi gida tare da securities dinsa. Shi kam tun daga zuba yake haduwa da jami'an tsaro amma da zarar sun tsayar dashi yana sauke glass idan sukayi ido hudu sai su matsa gefe suna fadin "sorry sir"
Duk mamakin ganinshi shi kadai sukeyi ba tare da securities ba gashi mugun gudu yake yi dan shi sam bai iya jan mota a hankali ba gudu yake kamar zai tashi sama,
Yana zuwa gidansa kuwa wani uban horn yashiga zubawa duk yabi ya cikawa masu tsaron kofar kunne sukuma basu san shi bane, full light yayi ya haskesu hakan ya kular da ben daya daga cikinsu ya taso da sauri yana gyara zaman bindigarsa akafadarsa alamar zaiyi rashin mutunci,tun kafin ya karasa Khalil ya sauke glass din zuwansa keda wuya yaga Khalil idonshi na kallon gate din yana mamakin wannan lamari wai shi da gidansa amma anbarshi yana jira sai sun gama shuka rashin mutuncinsu sannan zasu bude,
Da gudu ben yaje yabude gate din sannan ya matsa gefe yana neman afuwa, Khalil baiko kulashi ba ya saka hancin motar zuwa cikin gidan,shi kuwa ben alama yarinka yiwa sauran da baki wai ogane fa da kansa a wannan motar,
Yana kokarin fitowa daga cikin motar bayan yayi parking securities din suka karaso suna yimasa sannu da zuwa da tayashi murnar bayyanar Aryan wanda yafito rike da school bag dinshi,
Ciki suka shiga yawuce part dinshi Aryan na biye dashi,
Yana bathroom yana wanka su hajiya suka shigo dukkaninsu sashen Khalil suka shiga har Hanan ganin Aryan aka shiga yiwa juna barka da taya juna murna,a lokacin Hanan taje tayi masa wanka tasako masa kananan Kaya har lokacin suna part din Khalil acikin falonsa sai ciye ciye akeyi cikin farin ciki,
Khalil ta kalla yana sanye da jajayen jersey da dogon wando da juice a hannunshi yana kurba,kan cinyar Khalil Aryan yaje yahaye ya zauna ana shan hira ohhh wai yau sune cikin farin ciki haka kamar ba sune kwanaki biyu da suka gabata suke cikin damuwa da zubar da hawaye ba. Raba dare suka yi a b'angaren Khalil dan ita kam Hanan saima tafiya tayi ta barsu lokacin karfe 11 na dare,wanka tasamu tayi da ruwa mai dan zafi sannan ta saka rigar baccinta ta kwanta,
Su hajiya kuwa har wurin 1 na dare suka kai daga bisani suka tafi suka bar Khalil da Khalid, kallon Khalil Khalid yayi yace,
"Malam ni zo ka nuna min nawa makwancin nima inje insaka hakarkarina dan gobe asubanci zanyi inbar garin nan.... wallahi hutun kwana daya kacal suka bani..."
"Ga bedroom nan kana gani kaje ka kwanta mana..." Khalil ya fada yana nuna masa da hannunshi,
"Dan Allah ni ka kaini dakin da zan kwana,ya zaka nuna min master bedroom dan wulakanci? Idan matarka tazo fa.... Kasan kai babban mutum ne sai dai abiyoka"
"To nidai bani da wani dakin idan ba wannan ba..."
Tashi Khalid yayi yana kokarin cire rigar jikinsa yanufi cikin dakin yana fadin,
"Ni dai nashiga ciki idan zaka takura kuma saika bakunci dakin matarka"
Banza Khalil yayi dashi yaci gaba da danne dannen wayarshi. Bayan wasu mintuna da shigar Khalid shima yatashi yashiga,kwance yasamu Khalid yana waya da matarsa Muneerat sai wani lankwashewa juna murya suke yi tamkar saurayi da budurwa,
Gefen gadon yasamu ya lallaba ya kwanta kanshi yana dan sara masa Allah sarki Ramlat yanzu da tana raye da shima yana da gata irin gatan da duk wani magidanci yake samu idan har ya amsa sunan dan gata awurin matarsa,
Abubuwane suka shiga dawo masa kamar yaune suke faruwa,tuno lokacin da suke samari yashiga yi Khalid haka zai raba dare yana waya da budurwa shi kuma abinda bai iyaba kenan dan sam baida jimirin yin waya sai idan ta zama dole amma zai iya wuni yana chaten ta waya yafi yimasa sauki akan yayita magana,yanata tunane tunanensa shi dai ahaka bacci ya d'aukeshi yabar Khalid yana ta fama, dayake rabon da yasamu bacci mai dadi tun gabannin sace Aryan shiyasa yau ya nutsu yayi daga shi har Khalid din da yake ta kurin zaiyi asubanci duk makara suka yi dan har aka fito daga masallaci basu saniba,koda Khalil ya farka tuni gari yayi haske fayau sai dai shi nasa dakin kamar dare, fitilar dakin ya kunna ya mike yashiga bathroom yayi wanka sannan yayi brush da alwala yafito rike da dan karamin towel yana sake goge jikinsa,
"Khalid...... To sai ka tashi ai kayi salla ko har yanzu ana nan dai hali bai canja ba? Ka raba dare kana soyayya kuma ka kasa tashi sallar asubah..... Kanata cika bakin asubanci zakayi waye waye ni dama kawai jinka nake yi ai"
Tashi Khalid yayi yawuce cikin bathroom,sai da yayi wankan shima sannan yafito saboda ason samunshi yana yin salla zai wuce,jam'i suka yi duk da sun makara bayan sun idar Khalid yace,
"Ranka yadade ni baka karasa sanar dani abinda yafaru ba jiya ina gama waya naga har kayi bacci...."
"Khalid Wallahi yarinyar nan a daki ta sakani ashe wai wayo zata yimin tace Aryan yana ciki ashe karya take,intakaice maka labari dai wallahi niked tayi agabana...... Dakyar na kwaci kaina"
"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun,ai wasu matan hatsabibai ne nake fada maka,makirci dama ta shirya sai dai Allah ya cigaba da tsareka daga sharrinsu...."
"Amin Khalid ni wallahi narasa gane da me nafi sauran naza da kowacce mace ke kawo min farmaki,kaga idan office naje suna biye dani,idan kasar na bari suna biye dani duk inda naje suna bina...... Ni Wallahi mulkin nan duk ya isheni baida wani dadi ko kadan sai tarin stress da wahalhalu"
"A'a ka daina fadin haka,mulki fa Allah ke baiwa wanda ya zaba kuma yaso,kai dai kaci gaba da addu'a... Amma ya kamata ka dauki mataki akan yarinyar nan gaskiya ko dan saboda gaba"
"Ehh akwai matakin da zan dauka amma ina sone inyi magana da lawyer dina first inyaso sai inji shawarar da yake ganin yadace mubi...."
Wayarshi ya dauka yana duba time 6:30, text ya turawa Hanan akan ta kawowa Khalid breakfast tafiya zaiyi,
Allah yaso ta tashi kuma wayarta a kunne take,sauka tayi zuwa kitchen ta samu john na ta aiki yana soya dankali sannan gefe daya yana hada vegetables sos, diban wanda ya tsame tayi sannan ta harhada masa sauran kayan tea ta dauka ta haura sama,a bakin kofa ta jira bayan tayi knocking domin har yanzu bai bude kofar ba,fitowa yayi yazo ya bude mata tawuce ciki yana biye da ita,kan dining table ya nuna mata taje ta dora kayan sannan ta juyo ta dan kalleshi yana kokarin kunna tv da remote a hannunshi,
"Ina kwana?"
"Lafiya lau....."
Juyawa tayi zata fita taji muryar Khalid yana cewa, "Madam mun saki fitowa da sassafe ko?"
"Lahh ai babu komai,ina kwana?"
Suna gama gaisawa tayi waje domin Khalil sai daddaure fuska yake yi dan baya son Khalid yayi masa baran barama ya jawo masa reni,
Aranar suma su hajiya suka tafi gombe,duk da anga Aryan Khalil bai fitaba dan Dr Al'amin har gida yazo ya dubashi yace ya dan bari tukunna har sai yakara warwarewa,
Manena labarai da yan jarida har gida suka biyoshi suka ji ta bakinsa dangane da batan Aryan da kuma yanda akayi aka ganshi,bai fito fili yasanar dasu yanda aka ganshin ba kawai dai ya basu tabbaccin cewa masu yin garkuwa da mutane ne suka saceshi kuma yana kan yin bincike dan gano ko su wanene,bayan tafiyar yan jarida ya kira emah yasake tsareshi da tambayoyi domin Aryan yace wani ne mai kama da Emah din yazo ya kama hannunshi yakaishi mota to shikuma wannan din yake son gano ko waye saboda yanzu duniya ba abar yarda bace kana tare da mutum sai a iya hada baki dashi a cutar dakai, sai da yagama yiwa emah tambayoyi masu kada masa yan hanji sannan ya sallame shi yatafi yana fita ya danko kunnen Aryan guda daya har cikin bedroom dinshi belt ya dauka yana tambayar shi,
"Nan gaba zaka kara bin wanda baka saniba? Zaka kara bin mutumin da baka san ko waye ba?"
Girgiza kai Aryan yayi yana fadin,
"Allah Daddy bazan sake ba...."
Zaneshi yayi sannan ya sakeshi, cikin fad'a yace,
"Get out of here wawa kawai...."
Fita Aryan yayi yana kuka yatafi wurin Hanan, bata taba ganinsa yana kuka haka ba sai yau tunda tazo gidan,daukarsa tayi tafara lallashinsa tana tambayar meya sakashi kuka,
"Uncle ne ya....zaneni...."
Gwalalo ido Hanan tayi dama Khalil yana dukansa? Tohh ashe dai duk soyayyar yana daukar mataki, rarrashinsa taci gaba dayi har yayi shiru bacci ya d'aukeshi. Tana can wurin umma suna hira Aryan yasauko yazo ya hau jikinta duk jikinsa zafi alamar zazzabi, daukar shi tayi ta nufi sashen uban dashi,samunshi tayi zaune da laptop dinshi kan glass table agabanshi yana aiki, wannan mutum dai ko shine agogo sarkin aiki sai haka dan koda yaushe cikin aiki yake,
Daga ido yayi ya kallesu itada Aryan wanda ya kwantar da kai a kafadarta,
"Ka taba jikin Aryan kaji kamar zazzabi yake yi....."
Mika hannu yayi ya karbeshi,
"Na zaneshi ne shiyasa watakila zaiyi zazzabin...."
Shiru tayi bata ce komai ba ta tsaya tana kallon su yana ta tattaba jikin Aryan yana fadin,
"Am sorry lovely son, zazzabi ne ko? Bari inkira Dr yazo yabaka magani kaci abinci?"
"Baici abincin ba,yanzun nan yatashi" Hanan ta bashi amsa dan tasan Aryan cewa zaiyi yaci saboda baya son cin abinci,
"Ok je ki kawo masa"
Fita tayi shikuma yakira Dr Al'amin ita dai tana ta mamakin Khalil saboda a tsananin son da taga yana yiwa Aryan to bata taba tsammanin Wai zai iya saka hannu ya dakeshi ba. Zazzabin kwana biyu Aryan yayi sannan yakoma school domin yawarke garau haka shima uban ya warware domin har ya soma fita office.
A ranar da yamma mummunan labari ya sameta wai wata matashiya takai Khalil kara babbar kotu akan yunkurin yimata fyade adaren ranar larabar da ta gabata..........................鉁嶏笍
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:13 AM - Ummi Tandama: *33*
***Tsoro,mamaki da kuma damuwa sune suka taru suka rufe Hanan lokaci guda,jin wai wata matashiya takai Khalil kara kuma da laifin yunkurin yimata fyade kai jama'a wannan abu da me yayi kama,
Rasa abinda zatayi tayi kawai sai ta nemi wuri ta zauna nan cikin falonta tayi tagumi,to shin dagaske ne kodai sharrine kawai wannan matar take kokarin yimasa dan dukda cewa ita bata wani zauna tare dashi na tsawon lokaci ba amma sai taga kamar baida lokacin aikata hakan,shiru dai tayi da bakinta bata ce komai ba sannan kuma babu wanda ta fadawa ahaka Aryan yashigo ya sameta yadawo daga makarantar yamma wato islamiyya wadda shi agida ake yimasa tashi,
Kafin kace me tuni labari ya karade kafafan yada labarai wai Khalil yayi yunkurin yiwa yesmin fyade agidanta dake can zubah, nanfa wad'anda basu sanshi ba suka fara Allah wadai dashi wadanda suka sanshi kuma suka fara karyatawa suna fadin ai wannan shaci fadine kawai irin na wasu matan marassa tsoron Allah amma Khalil bazai aikata hakaba dan haka wannan labarin baida maraba da kanzon kurege.
Khalil Kam shi bama ya k'asar dan haka baima san abinda yake faruwa ba yana can Seoul babban birnin k'asar Korea, Khalid ne yaci karo da posting din a Instagram shine yayi gaggawar Kiran Khalil yana tambayar sa, murmushin takaici Khalil yayi zuciyarsa na tafarfasa saboda bacin rai,
"Wallahi wannan karon sai na nemi hakkina awurin yarinyar nan...... Text massage fa tayi min Khalid cewa inje inkarbo Aryan wai yana wurinta kuma kar natafi da securities saboda wani dalilinta marar amfani kuma na yarda natafi ahakan ni daya.... Taje tayita kaiwa k'arar dan Allah karta fasa amma nima yanzu zata ga the other side of me...."
Kitt ya kashe wayarsa cikeda bacin rai saboda yasan zubar masa da mutunci kawai yesmin ke sonyi, so take ta goga masa bakin fenti abanza gashi yan media sam basu iya daukar abuba sai ayita yamididi dakai ana nuna ka kamar watan ramadan, tamkar Khalid ya bude kofar kiran Khalil nanfa yan uwa da abokan arziki suke ta go slow din kiransa daga kiran wannan yashigo sai na wannan,
Bai dauki kiran kowa ba sai na anty saudat babbar yayarshi wacce yake bi,yana dagawa yaji ta rufeshi da fada tana cewa abinda yayi ya kyauta kenan? Yanzu yadace da girmansa da komai arinka buga labarinsa a jaridu da mujallun k'asar nan cewar yayi yunkurin ketawa mace hadddinta? Fada anty saudat take yi ta inda tashiga ba ta nan take fita ba dayake itama mafadaciya ce akwai fada babu laifi, kwata kwata taki tabarshi yayi magana sai zuba masa ruwan masifa take dama shima to afusace yake dan haka ya katse kiran dan ta cika masa kunne da fadanta,
Sake kira tayi tana jin ya daga tafara fadin,
"Ibrahim ni kake kashewa waya? Ni ka katse mawa waya saboda na kiraka ina fada maka gaskiya?"
"To danme zaki kirani ki sakani agaba kina wani yimin fada kamar karamin yaro? Ba zaki tambayeni kiji abinda yafaru ba...."
"Anki atambayeka din..."
"To kar Allah yasa ki tambaya din,duk abinda kikaji akaina ance hakane ina shikenan? Ko da...."
"Kaje kayi fin haka ma idan kaso sunan wa zaka bata? Ba sunanka bane...."
Yana jiyowa daga kusa da ita ana yimata magana kan cewa bai kamata ba wannan abun da sukeyi kamar wasu kananan yara yasan bazai wuce mijinta ba dan kamar muryarsa yaji yana cemata tayi shiru,"Ni baka jin abinda yake fada min? Ba kanina bane shi? Akan me zai rinka gaya min kananan maganganu?"
Shi dai katse wayar yayi yana kokarin ajiye ta kiran lawyer dinshi yashigo wato Barrister muhsin nan ya dauka ya zayyanewa barrister duk abunda yafaru sannan yakara da cewa,
"Barrister nima ashigar min da Kara a nema min hakkina na sace min yaro da tayi har tsawon kwana biyar wanda sanadiyyar hakan har saida ta kaini ga kwanciya a gadon asibiti, sannan a nema min hakkina na bata min suna da tayi..."
"Babu matsala ka kwantar da hankalinka insha Allah komai zai daidaita kuma sai tayi nadamar abunda ta aikata,ai bata san me ake kira da shari'a ba shiyasa har tayi saurin kai k'ara...". Barrister muhsin yabashi tabbaci sallama suka yi suna gama waya da barrister ya kashe wayar gaba daya bayan ya sakata a flight mood. Kwana biyu da faruwar lamarin ya dawo Nigeria yaci gaba da gudanar da harkokinsa, Hanan na son tambayar sa dangane da rade radin da ake tayi akansa amma bata ga fuskar yin hakan ba domin Khalil wani kwarjini gareshi na musamman idan har ya tsare gida to sai kaji tsoron tunkararsa ko kai waye dan su kansu yan jarida suna ta son suji ta bakinsa amma abun ya gagara.
Dawowarsa da kwana biyu yatafi gombe saboda anshirya family meeting akansa amma iya manyanne babu yara, Abban su Khalid tsareshi yayi da tambayoyi to amma da yake mutum idan da gaskiyar sa baya tsoron amsa kowacce irin tambaya haka ya amsa musu dukkan abunda suka tambayeshi daga karshe tattaunawar ta tashi bayan kowa ya yarda dashi. Daga wurin family meeting din nasu gidansu yawuce duk da sun hadu da su hajiya acan sai da suka sake zama da hajiya suka tattauna sannan yatafi ya koma abuja,
Haka dai labari yaci gaba da yaduwa har aka fara zaman kotu shi dai baya samun halattar zaman kotun sai lauyansa shine ke ruwa da tsaki domin acewar lauya shi Khalil ayyukansa bazasu bari ya samu damar zuwa ya zauna a kotu ba.
Ita kam Hanan zaman gida da rashin sanin takamaimai abinyi sune suka taru suka sakata agaba,wata zuciyar sai tace mata kodai ta koma masters degree dinta ne koda kuwa online ne,gashi yanzu inbanda kwadayin zuwa gida babu abinda take yi tana ta son taje gidansu dan wani lokacin har mafarki take yi saboda tsabar yanda ta saka abun aranta haba aima tana ganin kamar tayi kokari wata tara fa yanzu rabonta da gida tasan da akusa da gida tayi aure ai da tuni taje gida yafi akirga,tana son tambayar Khalil amma tana jin tsoro dan tunda abun nan yafaru yasake zama wani marar son magana,daurewa dai tayi ta rufe ido tayi masa text wai tana son taje taga yan gida,reply yadawo mata dashi lokacin yana wurin wani taro acan garin yola shida mataimakin shugaban k'asa,
_Me akeyi agidan?_
Shine tambayar da taga yayi mata, murmushi tayi aranta tace "wai shi dai mutumin nan baya rabo da tambaya ne? To kawai sha'awar zuwa gidan nakeyi" hakan kuwa ta tura masa amma sai taga yadawo da reply yace wai ba yanzu ba,ranar Hanan harda kukanta au dama haka mata keji idan suka bukaci futa aka hanasu? Wallahi sai yanzu take nadamar zaman gida da tayi ta rinka kunshe kanta agida bata fita ko ina daga makaranta sai gidan anty salaha dama ita ba kawaye gareta ba sai abokan mutunci balle ta rinka yawon bin gidan kawayen,ranar har yajin cin abinci tayi sai uban kuka da tasha dan har agaban Aryan tayi.
Bayan sallar ishah Khalil yadawo gidan, Aryan na dakinsa yana game din zumah a laptop dinshi khalil yafito daga wanka sanye da rigar wanka ajikinsa,
"Papa..... Mommy yau tayi kuka.... Kuma taki taci abinci..... Bata da lafiya"
Dakatawa yayi da goge kanshi da karamin towel da yake yi ya kalli Aryan,
"Jeka ka kirawo min ita...."
Tashi Aryan yayi ya fella da gudu yafita ita kuma tayiwa Aryan wayone da yake tambayar ta wai meyasa take kuka sai tace bata da lafiya ne,tana zaune falo tana kallon tashar Bollywood inda suke haska wani film _Ek villain_ Aryan yashigo yana kiranta,
"Mommy kizo inji Daddy... Uncle ne yake kiranki"
Daga haka yanda take ta mike tabishi saboda doguwar rigace ajikinta yar kanti da bakin siririn mayafi akanta sai kawai ta cire mayafin ta warwareshi ta yafa akanta,
Lokacin da suka shiga a falo ta tsaya bata bi Aryan zuwa bedroom din Khalil ba,agaban mirror Aryan ya sameshi yana fesa turare hannu daya kuma yana gyara sumar kanshi,
"Unlce tazo..... Taki shigowa"
Murmushi Khalil yayi yace "Abbana baki abun magana,akwai ka da surutu yaron nan kamar zaka sauko da sarki daga kan doki,jeka wurin umma tana kiranka"
Shi dai Aryan daukar laptop dinshi yayi yafice,da yaje falonma bai tsaya ba wai Daddy yace yatafi wurin umma,
Tafi mintuna goma azaune bai fito ba Wallahi wannan mutumin da jan ajin tsiya yake da mulki ta raya hakan aranta,bata gama tunanin hakanba taji motsin fitowarsa,farar riga t shirt ce ajikinsa ta kamfanin Nike sai bakin wando jeans kamar yadda yasaba shigarsa amafi yawan lokuta,gaba daya kamshinsa ya karade farfajiyar cikin falon,
"Ina wuni....?" Ta fada kanta akasa,dan kallonta yayi sannan ya amsa,
"Lafiya lau..."
Daga haka babu wanda yakara magana acikinsu har tsawon wasu mintuna,
"Me ya sameki kike kuka? Bakida lafiya ne?"
Jin tambayar da yayi mata yasata girgiza kai alamar A'a,
"Lafiyar ki lau kika zauna kina yiwa mutane kuka?"
Shiru tayi bata amsa masa ba domin tasan ai yasan dalilin kukanta bashine ya hanata zuwa gida ba da ta tambayeshi,tasan Aryan ne zai fada masa cewa tayi kuka,
Shiru yayi yana dan nazarinta kadan,shi baya son ta tafine tabar Aryan domin akwai shakuwa mai karfi tsakaninsu,yanda ta damu da yaron haka shima ya damu da ita,
"Ko akan na hanaki zuwa gidane? Shikenan bari zan kira Abban naki infada masa...."
Nan dinma shirun tayi duk da taji abinda yace wai zai kira abba yafada masa,bata yi magana ba dan haka yace,
"Tashi kije..."
Tashi tayi tawuce tafita,tana fita kuma kamar daga sama taji wata kara taratsatsaaaa gaba daya glass din wurin ya tarwatse awurin ya watsu jikinta babu shiri ta durkushe awurin saboda azaba, Khalil dake zaune a falonshi shima yajiyo karar tarwatsewar glass dan haka da sauri yatashi yafita domin duba abinda yafaru,yana fita yaganta durkushe ga gilasan nan tarwatse awurin da sauri ya nufeta dan ganin halin da take ciki.......................鉁嶏笍
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:13 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*
*34*
***Kamar acikin mafarki taji ya rikota ya dagota hankalinsa amutukar tashe saboda ganin irin yawan glass din da ya tarwatse,cikin tashin hankali yake furta,
"Ya yanke ki?...... Ya sameki?"
D'aga kai tayi cikeda azaba sakamakon jin glasan da takeyi acikin jikinta,fuuuu taga ya jata zuwa cikin falonsa kuma tun daga cikin falon yasoma cire dan mayafin dake lullube kanta,
Tiryan tiryan yarinka janta har zuwa cikin bathroom din dake cikin falon domin aganinsa shi yafi kusa fiyeda wanda ke cikin dakinsa duk hankalinsa yagama tashi wanda bata san dalili ba,
Suna shiga cikin bathroom din yasoma cire mata mitsi mitsin gilasan dake wuyanta domin kaifine dasu kamar anfeke ita kanta tana jin radadin shigarsu acikin jikinta kuma sunfi shiga wuyanta da bayanta,lumshe idanuwanta tayi jin yana kokarin cire rigar jikinta,duk sai taji kunya tabi ta dabaibaye ta ganin da gaske cirewar yayi yana cigaba da cire mata glass din,a lokacin da yake kokarin cire mata doguwar rigar jikinta sauran gilasan dake jikin rigar sun zuba cikin farar bra din dake jikinta nan taji shima kirjinta yadauki radadi amma bata fatan azo gabar da zaice nan dinma sai ya cire,shi bama ta jikinta yake yiba ta ganin yarabata da wadannan mitsi mitsin gilasan yake yi domin suna iya kashe mutum har lahira shiyasa bai tsaya wata wata ba yafara kokarin cire bra dinma, hannu biyu tasa ta kare kirjinta bai kulaba yaci gaba da abinda yake yi domin harsu cikin gashin kanta duk gilasan sun shiga kuma ciresu dole saida dabara dan ahakanma gashi nan wurare da dama duk sun dan yanyanketa,
Ganin ya maida hankali kan gashin kanta yana ciccirosu daya bayan daya yasata dan daga ido ta kalleshi nan shima ta hango glass din a wuyansa abinka da farar fata shi har yankan ya bayyana,hannu ta mika tama manta ahalin da take ciki ta zaro glass din, "Kaga ashe kaima ya yankeka...."
Sai da ya tabbatar da ya cire mata su tass sannan ya kalleta cikin sauri ta kare kirjinta da hannunta,kawar da kanshi yayi,
"Kiyi wanka ina zuwa bari zan kira Dr ya dubaki..."
Daga haka yajuya yafita wayarshi ya dauka yabi ta kofar baya yasauka k'asa yana tafe yana yiwa Dr Al'amin text akan yazo cikin sauri yana nemansa,
Securities dinsa na hangoshi lokacin da yake kokarin fitowa nan sukayi saurin mara masa baya,dama shi idan abu yafaru da kansa zaka ganshi yafito,idan kaga Khalil agidanshi zakayi mamakin jin wai shine minister,saboda irin yanda yake gudanar da sabgoginsa da al'amuransa da lokacin da yana tsohon gida sai kaje ka samesu shida Aryan suna yin ball wani lokacin harda yaran neighbors idan sun shigo,
Wurin chief security yaje yarinka yimasa fada yana cewa menene aikinsu agidan idan har abu irin wannan zai rinka faruwa,kenan zamansu bashi da wani amfani matsawar ba zasu rinka kulawa da kyau ba,yanzu gashi nan an iyo jifa ya fasa glass har yasamu Hanan,da Aryan ne ma awurin haka zai sameshi ko shi kansa,shi dai chief security hakuri kawai yake bashi yana cewa insha Allah haka bazata kara faruwa ba kuma yanzunma zai zurfafa bincike har sai yagano musabbabin faruwar hakan,
Wanka Hanan tayi kamar yanda yace ta dauki towel dake rataye cikin bayin ta daura ta kwaso kayanta da ta cire ta fito sadaf sadaf kamar wata marar gaskiya,ganin baya cikin falon yasata fita ta wuce part dinta tana zuwa ta saka doguwar riga mai gajeren hannu ta dauki turare tafesa nan taji kamar tayi kuka sakamakon zafin da taji ajikinta ta manta ashe ta yanyanke, muryar Aryan tajiyo afalo kuma da alama shida umma barira ne dan itama tajiyo maganar ta,dan karamin gyale ta dauka tafita, sannu umma tayi mata tana cewa ashe abinda yafaru kenan yanzu Khalil ke sanar dasu a k'asa,
Suna nan zaune tare da su umma yaturo mata da text wai taje yana kiranta,tashi tayi ta fita nan taga wurin da glass din ya tarwatse har an tattare an share an gyara numfashi ta dan ja ahankali dama ai wannan kasada ne wato siyan mai yarda inbanda kasada taya za ace gaba daya ayi katanga da glass,ace ko ina glass ne ai dole wata rana irin haka ta rinka faruwa,tare da Dr Al'amin ta samesu zaune shi yanata matse matsen waya yana duba posting din da S A na labarai yayi akan yajin aikin da likitoci ke son tafiya,zama tayi ta gaida Dr Al'amin wanda ke murmushi yana fadin,
"Amarya ashe abinda yafaru kenan..... To Allah ya kiyaye gaba,insha Allah zan baki magani saboda jikinki da glass din ya shisshiga"
"Tohm" ta fada batare da ta daga kanta ba saboda ita kunyar hada ido take yi da Khalil, magunguna Dr Al'amin ya harhada mata yabata tana karba ta tashi sim sim ta fita saboda bata son su sake yin ido hudu da Khalil kuma,
Har ta koma sashenta umma barira da Aryan na nan suna jiranta suna kallon tashar MBC 3 inda Aryan ke kallon cartoon sunata drama da umma tana cewa ita wadannan robobin masu kama da aljanu sun isheta ya canja shikuma yaki ya kama remote ya kankame yana zaune daram akan cinyarta,
Abinci ta zubo taci sannan tasha magungunan da Dr Al'amin yabata, Aryan ta dauka takaishi dakinsa ta kwantar sannan ta fito tazo tayi shirin bacci ta kwanta,tunanin Khalil ne yafara yawo acikin kwanyarta yana kaiwa da kawowa, hannayensa masu taushi da laushi duk da rikon da yayi mata dazu bada wata manufa bane amma tajishi har cikin ranta,kuma har yanzu tana jinsa, lumshe idanuwanta tayi tana sakin murmushi ita kadai sakamakon tunowa da tayi yanda dazu ya rude lokacin da abin yafaru,rufe idanuwanta tayi da tafukan hannayenta kamar yana ganinta saboda kunya,
"Yanzu shikenan ya ga jikina"
Da tunaninsa tare da sabuwar kaunarsa fil bacci yazo yayi awon gaba da ita. Khalil bayan fitar Hanan kallon Dr Al'amin yayi yace masa baya jin dadin jikinsa yabashi pills,
Kallon mamaki Dr Al'amin yafara yimasa kafin daga bisani ya cire farin gilashin dake fuskarshi,
"Amma ranka yadade anya kuwa bazaka hakura da shan relief pills dinnan hakaba.... Kar muje kuma ya fara haifar maka da matsala saboda kajima fa kana shan shi for over 5 years..... For how long zaka yita amfani dashi bayan kuma yanzu kana da iyali..... Ai sai ita ka cutar da ita...."
"Wai wadannan suratan duk waye ya tambayeka? Nifa pills kadai na bukata ba dogon bayani ba..."
"Sorry sir...." Dr Al'amin yafada yana kokarin fito masa da pills din,karba yayi sannan ya sallameshi yatafi,saida yasha pills din sannan yashiga bedroom dinsa,kai tsaye bathroom yawuce yacire kayan jikinta ya sakarwa ruwan sanyi,yajima yana kwarawa kansa ruwan sanyi sannan yafito yana daure da towel,zama yayi gefen gadon yana dafe kansa da hannayensa guda biyu,hoton Ramlat kawai yake gani acikin zuciyarsa, Hanan tayi kama da Ramlat dinsa ata wurare da dama,shi ba Hanan dince ta jefashi cikin wannan halinba,matarsa da yatuno shine silar samun kansa cikin wannan yanayi amma ita Hanan tausayi da kuma kaunar da take yiwa Aryan ne yasa shi dazu yaji hankalinsa yatashi lokacin da glass ya fashe kuma ai ko babu komai yanzu a karkashin kulawarsa take dan haka dole ne ya kula da ita,rasa abinda yake yimasa dadi yayi domin ko pills dinma yau ji yayi kamar baisha ba dan babu abinda ya canja na damuwar da yake ciki,kwanciya yayi saman gadonshi mai laushin gaske duk aikin bada sanyin da na'urar sanyaya dakin keyi shi gumi yake yi kamar ana gasashi cikin oven,yau yasha wahala dan saida ya gwammace kida da karatu daga karshe dai ya lallaba yatashi yasa jallabiya da short din wando sannan yafita, kitchen yasauka yaje yaduba fridge cikin sa'a yasamu lemon tsamin da yaje nema nan take ya yanka yashanye guda daya sannan yakoma sama,abin salla ya shimfida yahau yasoma sallar nafila.
Tunda wannan abun yafaru shikenan Hanan ke kunyar sake cin karo da Khalil dama kuma shi ba mazauni bane hakan yakara nisanta fuskokinsu da haduwa da juna,wurin da glass din yafashe kuwa tuni har an dauko ma'aikata sun gyara sun saka sabon glass awurin,
Text ta sake turawa Khalil akan maganar tafiyar ta kano dan gano gida amma sai yayi mata reply da wai ba yanzu ba,to wai sai yaushe zataje gidanne? Ranar ma tayi kuka dan har yafi na waccan ranar da ya hanata zuwa,ita zaman gidanne ma gaba daya ya isheta babu inda mutum zaije ko makota bazai fita ya shiga ba kai wannan zaman baiyiba gaskiya,haka tayita rayawa aranta,ko kuma dan shi baya zaman gidanne shiyasa yake ganin kamar zaman dadinsa sukeji?.
Khalil yau tun yana office yake jin zazzabi yana neman saukar masa amma dai yayita daurewa ga mura dake damunsa tun jiya amma ita bata yi tsanani ba sai yau din yake jin tafara takura masa,
K'arfe 10 yau ya koma gida bayan ya gama ganawa da lauyansa wato barrister muhsin wanda ke cigaba da kareshi akan karar da yesmin ta shigar, barrister muhsin yace masa akwai alamun nasara sosai dan reshe ne ma ke neman juyewa da mujiya duk da ita ce tayi k'arar,
Yana komawa gida ya ajiye wayoyinsa yasaka su a flight mood sannan ya canja kayan jikinsa ya shige bargo ya kwanta domin izuwa yanzu zazzabin yagama rufeshi ga mura wacce ke haddasa masa tari da atishawa harda ciwon kai. Washe gari yakira likita yazo ya dubashi sannan yatafi ita Hanan bata san yana gida ba ranar dan babu inda yafita da yayi bakima hakuri yace abasu saboda bazai iya fita ba,zuwa yamma dai zazzabin ya sauka sai iya murar kadai gashi baya kaunar shan maganin murar nan dan duk sai yabi ya kashe masa jiki kuma yayita sakashi bacci,ko yau dinma wuni yayi yana bacci kamar wani dan kwaya,da suka yi waya da Khalid yake dubashi shine Khalid din yake tsokanarsa wai ayi masa farfesu mana dahuwar kalwa da attaruhu yaci Wallahi da haka zai fatattaki wannan murar, shawarar Khalid ya dauka dan haka da yasamu yatashi yayi wanka yayi salla sai yafita da niyyar yaje k'asa ya sanar da umma dan baya son kunna wayarsa yanzun nan mutane zasu dameshi da kira,ahankali yake takawa saboda jikinsa babu karfi sosai,ta gefen part din Hanan yajiyo k'arar kida dan haka yakoma yabi ta wurin domin dubawa, muryar m Sharif ce ta fara dukan kunnuwanshi cikin wakarsa ta _hafiz_ koda ya leka Hanan ya hango ita da Aryan sun takarkare sai casa rawa suke yi................................鉁嶏笍
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:13 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*
*35*
***Samun wuri yayi ya harde hannuwanshi akirji yayi crossing legs dinsa ya jingina yana kallonsu,daga ita har Aryan din basu san yana tsaye awurin ba har saida wakar ta kare wata ta shiga nan fa hanan tafara bi tana wata irin rawa ahankali idanuwanta arufe "Sabon salon soyayya na kirkiro.... Kai zan yiwa amma sai munje gida.....sabon salo...sabon salo.... Sabon salo"
Juyowar da Hanan zatayi taga mutum jingine yana kallonsu,guduwa tayi ta shige cikin bedroom dinta,sai lokacin shima Aryan ya hangoshi da gudu yatafi ya rungumeshi,
"Papa...."
"Sakeni Aryan kar ka kada ni mana,tun jiya baka ganni ba amma shine baka nemana ko?"
Girgiza kai Aryan yayi,"Ina nemanka Daddy"
Kama hannunsa yayi suka sauka k'asa wurin umma barira nan yake sanar mata da bukatar shi na son yimasa farfesu ko wanne iri amma yasha daddawa da attaruhu saboda mura ke damunsa, daga nan sama yakoma shida Aryan yana yiwa Aryan takarar kar ya dameshi da surutu baida lafiya idan kuma ya dameshi koroshi zaiyi, bedroom dinshi suka wuce kai tsaye ya kwanta saman gado shima Aryan yabishi ya kwanta akanshi, murmushi yayi ya rungumeshi yana cemasa,
"Wato duk da nace maka karka dameni shine saida ka fara ko? Zan koraka wurin mommy yanzun nan kuje can kuci gaba da rawarku tunda rawa momyn ke koya maka..."
"Daddy tana koya min karatu ma"
"Me da me take koya maka? Fada min inji"
Kamar Aryan jira yake yafara jero masa irin karatuttukan da Hanan ke koya masa tiryan tiryan,
"Tana zaneka idan bakayi karatu ba ko?"
"A'a bata zaneni....." Yabashi amsa yana sake hawa kanshi wai zaiyi doki. Hanan sai da ta tabbatar da cewa Khalil yatafi sannan tafito ta sauka k'asa,a kitchen ta samu umma tana gyara kaji manya manya wad'anda zata yiwa Khalil farfesu dashi, karba tayi tana tambayar umma saboda tunda tazo gidan bata taba ganin umma barira a kitchen ba tunda akwai kuku,
"Ai kin san mu'azzamun baya jin dadi mura ke damunsa to shine yace ayi masa farfesu mai yaji dahuwar kalwa..."
Dariya Hanan tayi jin umma tace wai dahuwar kalwa,ita kam agida duk lokacin da wani ke yin mura mamaye wani shayi take dafawa na na'a na'a sannan yasha kayan kamshi,
Gyare kajin tayi guda uku manya manya sannan ta hada kayan kamshinta ta dafasu rigib sannan ta dora shayin bayan ta gama ta zuba masa ta zubawa umma nata ta dauka ta nufi dakinsa,suna falo shida Aryan bayan sun idar da salla,shi yana saman kujera shikuma Aryan yana kasa yana wasa akan rug sai burgima yake yi,da sallama a bakinta ta shiga ta jawo glass table din dake gefenshi ta dora masa akai sannan tafara gaisheshi,
"Ina wuni....?"
"Lafiya lau..."
"Ya jiki?"
"Da sauki"
"Allah yakara sauki"
"Amin"
Daga haka ta kwashi yanmatan kafafunta ta fita. Farfesun yabude tun kafin yakai bakinsa yawunshi ya tsinke,kasa ya sauko ya tankwashe kafafuwansa yasoma yaga yana ci dama kuma gashi yadahu sosai irin yanda ake so kuma farfesun yasha kayan kamshi da daddawa sosai,tare da Aryan suka kusa cinye naman dan sai da kowannensu yaji ya koshi sannan suka hakura Khalil ya rufe sauran ya ajiye,shi duk a tunanin sa umma barira ce ta dafa bai taba kawowa Hanan bace,tun bayan da yagama cin farfesun yaketa fama da face facen hanci, Aryan yatura zuwa cikin bedroom dinshi ya dauko masa tissue,babu laifi yaji dadin naman domin yaji yajin da yaci yafara yimasa amfani. Har lokacin bacci yayi suna tare da Aryan wanda tuni shi yajima da yin bacci ma,
Hanan na kwance dakinta abun duniya ya taru yayi mata yawa,inbanda tunani da begen Khalil babu abinda ke damun zuciyarta,tana tsananin sonshi da bukatarshi wanda har bata san yanda zata kwatanta ba,
Tashi tayi daga kwancen da take domin ta kasa yin baccin,kamar wacce akace tafito ta bude kofa tafito sanye da night gown dinta milk colour,gaban corridor taje ta dan jingina da jikin karfen da ke kewaye da wurin tana jin iska tana kadata tamkar zata dauketa,kanta ta daga sama tana kallon taurari wadanda suka yiwa sararin samaniya ado suka kara haskashi,daidai lokacin shikuma Khalil yafito rike da Aryan a kafadarshi zaije ya kwantar dashi acikin dakinsa,har yazo ya wuceta bata sani ba saboda hankalin ta baya wurin yana can wata duniya ta daban mai cike da soyayya, kauna,shauki da kuma bege,babu abinda take son kasancewa tare dashi ahalin yanzu sama da Khalil kuma tasan bazata taba gajiyawa da shiba domin kallonsa kadai zai dauke mata hankali ya debe mata kewa sannan zai nisantata da dukkan damuwa.
Ahankali yake tahowa yana dosota amma bata saniba har yazo inda take tsaye kanta asama idanuwanta kyarr tana kallon sararin samaniya ko kiftawa bata yi,akusa da ita kadan ya tsaya yakai hannunshi yadafa karfen dake wurin shima sannan yakai dubansa izuwa sama dan ganin abinda take kallo wanda ya shagaltar da ita har haka,
Samun kansa shima yayi da jin dadin kallon da yake yiwa saman nan ya lumshe idanuwanshi sannan yabudesu yasake kai dubansa izuwa sama,shi dan soyayya ne kuma ma'abocin sonta akoda yaushe irin wannan yanayin shi ake kira da lovers moment domin idan masoya guda biyu suka samu kansu a irin wannan yanayin sukan manta da kowa da komai, sannan sukan manta da damuwarsu da duk wani abu da ka iya kawo musu cikas acikin duniyar soyayyar su,
Sake lumshe idanuwanshi yayi sakamakon wata irin iska mai dadi da ratsa jiki da ta shigeshi,a wannan lokaci bazai iya fada maka takamaimai halin da gangar jikinsa da ruhinsa ke ciki ba,fata yake inama yabude idanuwansa yaganshi tare da Ramlat,inama ace yaga Ramlat akusa dashi koda cikin mafarki ne,
Saura kadan Hanan ta fasa ihu saboda ganin mutum da tayi akusa da ita wanda sam koda wasa bata ji zuwanshi ba saboda tana can duniyar tunani,
"Abban Aryan...." Ta fada bakinta na dan rawa,juyowa yayi ya jingina ya harde hannuwanshi akirji yana kallon ta bayan yayi crossing legs dinsa kamar yadda ya saba tsayuwarsa,kallonshi take yi daga sama har kasa kamar yaune tafara ganinsa, bakin dogon wando ne ajikinsa na sport sai farar t shirt ta kamfanin Adidas kafarshi sanye da takalmi slippers dama shigarshi kenan kullum fari baida kayan da suka wuce wadannan ko meyasa oho,
"Abban Aryan yaushe kazo nan?" Ta bukata bayan ta rufe bakinta da hannayenta,
"Kina can duniyar tunani...... Tunanin saurayinki wanda na rabaku kike yi ko?"
Sake rufe idanuwanta tayi da dukkanin tafukan hannayenta tana girgiza masa kai alamar A'a,
"Fada min gaskiya karki yimin karya...."
"Hmmmm" tafada tana gyara tsayuwarta,
"Nasan zafin rabuwa da masoyi.... Nasan irin radadi da azabtuwar da zuciya kan shiga aduk lokacin da ka rasa wanda kake so..... Nasan kema acikin wannan yanayin kike rayuwa ahalin yanzu..... Har yanzu kina kukan rabaki da masoyinki da nayi...."
Lumshe idanuwanta tayi take wasu hawaye suka gangaro mata wanda ba na komai bane face na tsantsar soyayyar da take yimasa,inama zata iya,inama tana da dauriya da kwarin gwiwar da zata iya duban kwayar idonshi ta fada masa ita shi take so shi take kauna ba waninsa ba,inama,zata iya kallonsa cikin ido ta sanar dashi akansa ne zuciyarta ke shiga duk wadannan abubuwan da ya zayyana,
Ganin hawaye na bin kumatunta ya sake tabbatarwa da kansa cewa abinda ya fada ko kuma yake hasashe gaskiya ne domin gashi nan har kuka take yi saboda fama mata raunin dake zuciyarta da yayi,
"Hmmmm...... Wai meyasa masoyi bai fiya kasancewa da masoyinsa ba har tsawon lokacin da yadace?..... Me yasa aduk lokacin da kake tare da masoyinka sai wata k'addara ta rabaku?...... Meyasa yawancin masoya basa samun happy ending?......"
Kawar da kansa yayi ya furzar da wata zazzafar iska kwayar idanuwanshi har ta sauya daga launin fari zuwa ja, karfen wurin ya dafa yana jin tamkar ya fashe da kuka,ita kuwa Hanan dama kukan take wanda zata iya kiranshi da kukan bakin ciki wai Khalil shi duk azatonsa kukan soyayyar wani take yi ba soyayyar shi ba,meyasa yakasa ganewa cewa ita shi take so? Wanne irin makaho ne shi da ya gagara gane tsantsar soyayyar da take cikin idanuwanta wanda take yimasa?
"Kiyi hakuri kowa da yadda Allah ke tsara masa rayuwar sa.... Wasu masoyan sukan kasance da juna tamkar tif da taya ko kuma kamar wata da zara amma lokaci guda sai wata k'addara ta rabasu.... Babu abinda yafi zama da masoyi dadi nasani..... Sannan babu abinda yafi rabuwa dashi daci,tashin hankali da shiga damuwa.... Nasan kina cikin damuwa amma ki kara hakuri har zuwa lokacin da Allah zai kawo karshen zamanki atare damu...."
Wata faduwar gaba ce tasoma ziyartarta jin abinda yafito daga bakinsa wai karshen zamansu,ita da take fata da burin kasancewa tare dasu har karshen rayuwar ta amma yana yimata maganar rabuwa da ita,bata san lokacin da kuka ya subuce mata ba.... Dagowar da zatayi taga wayam babu Khalil babu alamarsa har yabar wurin,da kuka ta koma dakinta ta fada kan gado taci gaba da rusar kuka.
Shima Khalil cike da damuwa yashiga sashensa ya yada zango a falonsa ya zauna cikin tsantsar damuwa da radadi,wai ma meyasa yabi ta son ran Aryan ya auro yarinyar nan? Meyasa ya rabata da masoyinta wanda take so dan kawai biyan bukatarshi alhali kuma yasan zafin radadin rabuwa da wanda kake so? Shi dai gashi Ramlat bata raye amma kullum cikin damuwar rashinta yake wani lokacin har zubar da hawaye yake yi to inaga Hanan wacce ita masoyin yana raye amma aka rabata dashi ai dole tayi kuka idanma akwai abinda yafi kuka dole tayi,
Zamewa yayi ya kwanta kan doguwar kujera idanuwanshi suna kallon sama, tambayar kansa yake shin menene mafita?
"Ka saketa kawai...."
Zuciyarshi tabashi amsa tana sake karfafa masa gwiwar aikata hakan domin hakan shi kadai ne mafita kawai,sabanin haka kuwa zai sa yazama azzalumi mai son kansa kuma marar tausayi,tashi yayi dakyar ya nufi cikin daki zuciyarsa na raya masa wani abu..........................鉁嶏笍
0 comments:
Post a Comment