***Tafiya yake yana hada hanya har yasamu ya cimma lafiyayyen gadonshi wanda yasha shimfidu masu laushi sannan ga pillows nan sama da guda goma manya da kanana kuma kaloli daban daban,
Zama yayi akai sannan ahankali ya zame ya kwanta yana jin jikinsa duk asanyaye, agogon dake ajiye kan bedside drawer dinshi ya kalla nan yaga karfe 11:30 yasan dare yayi amma yazama dole ya kira Khalid acikin daren nan ba sai zuwa gobe ba,yana da bukatar neman shawarar sa da kuma jin ta bakinsa kafin ya zartar da hukuncin da yake ganin shine daidai.
Kiran layin Khalid yasoma yi yana jin zuciyarsa kamar zata fashe dan tsabar nauyin da tayi masa,cikin dan magagin bacci Khalid ya daga wayar,
"Khalid zan saketa...." Shine abinda kunnuwan Khalid suka jiye masa ai bai san lokacin da ya wartsake ba yayi zunbur ya tashi yabar cikin bedroom dinsu gudun kada ya tada Muneerat,a falo ya zauna sannan cikin damuwa yace,
"Khalil what are you saying?...... Me ya faru?"
"Khalid zan saki yarinyar nan kawai inaga hakan zai fi...."
"Wai meya faru? Wani abun tayi maka mai girma har haka?"
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya tashi zaune ya dafe kanshi da hannunshi guda daya,
"Babu abinda tayi min kawai dai naga kamar na shiga hakkinta ne kuma na zalunceta domin na kawota gidana na rabata da wanda take so...."
"Itace ta fada maka haka?" Khalid ya bukata,
"Ba ita ta fada minba amma dai kamar alamun hakan sun bayyana atattare da ita...."
"Kaga malam wannan ba hujja bace, bai kamata ka yi haka ba kaifa babban mutum ne Khalil karka manta, yanzu gaba daya idanuwa akanka suke da zarar kayi abinda bai kamata ba za afara yadawa ana yin yamididi da kai.... Ai gara ka ci gaba da zama da ita har zuwa ranar da zata mance da masoyin nata akan ka saketa ka mayar da ita yar karamar bazawara..... Khalil kasan zawarci kuwa? Kasan radadin da iyaye ke ji aduk lokacin da aka sakar musu yaya? To Wallahi duk amincin da ke tsakaninku da mahaifin ta daga ranar da ka sakar masa 'ya shikenan sai wani kadari na Allah kuma.... Kayi tunani"
Shiru ya dan yi na wani lokaci tabbas yasan abinda Khalid yafada gaskiya ne to amma ya zaiyi da halin damuwar da ya jefata? Idan har ya zama silar rugujewar farin cikinta bazai taba yafewa kansa ba,
"Kayi hakuri ka kwanta ka manta da kowacce irin damuwa ka samu bacci brain dinka ta huta inyaso gobe sai mu karasa magana....."
"Shikenan Khalid thank you, thank you for always being with me.... Indeed I have no words to thank you.... Sai da safe"
"Don't mention it Khalil,you are always welcome...."
Katse wayar Khalil yayi sannan cikin karfin hali yasamu yayi addu'ar bacci ya kwanta wai ko Allah zai sa yasamu bacci,duk tunane tunanen da ke zuwar masa cikin rai a daidai wannan lokaci kin yi yayi da haka yasamu bacci yayi gaba dashi.
***
Sosai sumayya taga alfanun daukar shawarar muhibba da tayi,ita kanta bata taba sanin tana da kwarin gwiwar iya yin haka ba sai yanzu,gaba daya ta fita sabgar mujahid babu ruwanta dashi wani lokacin ma shine zai yita takalarta har yasamu suyi fada,fada kam yanzu tsakaninsu kullum ne babu ranar banza da zata zo ta wuce basuyi wannan fadan nasu na sabo ba,
Sai dai kwana biyun nan yanzu ba sosai yake ganinta ba sakamakon exams da suka fara a makaranta,kullum tana cikin makaranta suna karatu bata dawowa gida da wuri,ranar da suka gama exams kuwa aranar ta tattara ta tafi katsina gidan iyayenta, mujahid duk sai yaji gidan babu dadi musamman ma idan yana son abu to sai dai yasaka yar aiki ko kuma yayi da kansa haka ma aikin nata da take yi wani lokacin mami shi take sawa yanzu yauma shi yayiwa mami guga ya goge mata kayanta duk gugar gashi babu dadi stones everywhere injishi da fada,tun yana daukar abun da wasa har yaga bafa na wasa bane,dan haka yacewa mami wai zaije ya dauko sumayya a katsina,ranar da safe ya shirya yatafi bayan yasha manyan kayansa brown colour din shadda da hularta,baisha wahalar samun gidanba saboda dama ya sanshi suna zuwa tare da mami,har ciki yayi sallama ya shiga sumayya na ta shan bacci a falo tana kan doguwar kujera,kafarta ya buga nan tayi firgigit ta juyo kamar a mafarki taganshi tsaye,
"Tashi mu tafi....."
Mutsuttsuke idonta tayi tana son gasgata shin dagaske mujahid ne ko kuwa mafarki take yi?
"Nine nan daina wani kallo na"
Dan turo baki tayi ta zuro kafafunta kasa tana harararsa.
***
Kamar yadda Khalid yafada masa washe gari wasai yatashi zuciyarsa babu wani sauran damuwa ko gurbataccen tunani haka itama murar tashi yau ya danji dama dama shiyasa ma ya shirya yafita office,ita kuma Hanan da damuwa ta wayi gari duk abunda takeyi tana yinsa ne cikin rashin walwala, wai meyasa ya kasa fahimtar ta ne? Meyasa yakasa gane son da take yimasa duk nauyinsa? Ranar dai haka ta wuni babu farin ciki dan adaki ma ta wuni taki fitowa,
Tsawon Kwana biyu basu hadu da Khalil ba gashi ita kuma gaskiya ganin gida ta ke son taje tayi domin zamanta anan bata ga abinda take tsinanawa ba inbanda zaman kashe wando babu abinda take yi. Waya suka yi da anty badi'a nan take fada mata cewa tana son ta dan shiga makarantar koyon abubuwa irinsu hada sabulai,turaren wuta da sauransu koda kuwa irin na online dinnan da akeyi ne shine anty badi'a ta hada ta da wata mata wai ita hajja hasinah kwararriya wurin koyar da mata abubuwa daban daban,kuma wani abun dadi ma kina zaune daga gida zaki koyi abubuwa masu tarin yawa matsawar kin maida hankali. Zunzuruntun kudi ta biya har naira dubu ishirin tayi registration saboda online classes ne nan hajja hasinah ta sakata a cikin group inda aka fara gudanar da lectures,irin tsarin yanda ake koyarwar abun yayi mutukar burgeta domin ana yin komai dalla dalla yanda zaka gane kuma ka fahimta,
Yanzu kam zaman banza ya ragu domin koda yaushe tana rike da wayarta da littafin da ta tanada musamman dan rubuta muhimman abubuwan da aka koyar gudun kada ta manta tunda shi dai WhatsApp baida tabbas,
Ganin yanda take bobboye kanta a daki yanzu bata fitowa falo sosai sannan bata biye Aryan suyi wasa sosai sai Khalil yafara zargin to ko dai dan ya hanata zuwa ganin gidane shine abin yake damunta? May be hakane zuciyarshi ta raya masa saboda duk lokacin da zaiga Aryan yana wasa a falon kasa ko falon sama shi kadai yake gani bai fi ita yaganta sau daya ko sau biyu ba,
Yau garin Abekuta yaje inda matasan yankin suka shirya masa wasan kwallon kafa da kambun girmamawa da zasu bashi kuma bashi yadawo Abuja ba sai misalin 11 harda rabi na dare,acikin daren saida ya je office yayi signing wasu mails da aka aiko masa sannan yanufi gida,wanka yayi ya sha coffee mai zafi sannan ya nufi part din Hanan,yayi mamaki lokacin da yaga haske dal tako ina acikin sashen nata wannan alamu ne dake nuna cewa batayi bacci ba idonta biyu,
Zaune take kan gadonta tana rubuta abubuwan da aka koyar dasu yau wanda bata samu damar rubutawa ba sakamakon baccin rana da tayi kuma koda ta tashi da yamma garden suka shiga ita da Aryan suka je suka shantake acan har magriba,
Knocking yayi wanda yasa Hanan taji tsoro ya shigeta,shiru yaji ba a amsa ba dan haka ya sake bugawa, ahankali ta sauko daga kan gadon cikin sanda sadaf sadaf tazo bakin kofar zata leka, bude kofar yayi nan taga cewa shine, kallon kallo suka tsaya suna yi dan rabon da suga juna face to face tun ranar nan,
"Sannu da zuwa" ta fada tana sunkuyar da kanta kasa,
"Yawwa...."
Tsaye suka yi awurin cirko cirko shi dai bai shiga cikiba haka kuma bai koma waje ba,
"Ki shirya jibi zaki je ganin gida......"
Da mamakinsa sai yaga ta dago fuskarta cike da farin ciki ta kalleshi,
"Nagode"
Baice komai ba yajuya yatafi nan tabishi da kallo yauma dai fararen kayanne na gado farar riga t shirt mai gajeren hannu da farin wando,cike da murna taje ta fada saman gado ta rungume pillow cike da farin ciki ranar dai tsabar murna bacci kadan tayi,washe gari kuma ta fara hada kayanta akwati guda kamar wacce zata yi watanni ko shekara,ranar wuni tayi tana fara'a kamar anyi mata albishir da kujerar hajji,
Washe gari da safe bayan Aryan yatafi makaranta itama suka kama hanyar kanon dabo,karfe 11 da kusan rabi suka isa kano ai Hanan kamar zata tashi sama haka take ji dan tsananin farin ciki,
Lokacin da suka je gidansu kaya taga ana ta fitowa dasu ana shigarwa,kayan abinci ne,atamfofi bandir bandir da shaddodi na maza, "wadannan kuma na menene?" Ta tambayi kanta dan Khalil bai fada mata ba,
Da tsallenta da gudunta ta shiga gidan taje ta rungume mamaye tana murna,shamsu dake tsaye shikam matsawa yayi yana fadin,
"A'a karki kada ni ki jamin zama wuri daya"
Bakinta yau yaki rufuwa kuma ta kasa zama wuri daya ta shiga nan ta fita nan haka ta rinka yi saboda bakuwa ta zama agidan,har Abba yadawo bata samu zama ba sai lokacin ne suka zauna,
"Uwar masu gida ina kuma kika baro dan naki Sulaimanu?"
Dariya tayi aranta tana cewa Allah sarki Aryan,
"Abba suna nan lafiya duk suna gaisheku"
Har dare bata san ma'anar wadannan kayan da tazo dasu ba,text tayiwa Khalil tana tambayar shi wad'annan kayan da ya hadota dasu na menene? Sai lokacin ya tuna ashefa baiyi mata bayani ba shi yasaba duk lokacin da Ramlat zata je gida yana yimata tsaraba wadda zata kaiwa yan uwa da abokan arziki, reply ya mayar mata dashi,
_Tsaraba_
Shine kadai abinda ya rubuta,tambayarsa ta sake yi wai to kwana nawa zatayi nan ya dawo mata da reply wai sati daya marairaicewa tayi kamar yana ganinta wai dan Allah tayi sati biyu shi kuma yace A'a,damunsa Aryan yayita yi shi kuma wai zaiyi waya da mommy,saida ya kira masa ita sannan yabarshi,tashi yayi ya wuce bedroom dinshi.
Tana kwance suna shan hirar yaushe gamo da mamaye tana ta zuba shagwaba wai mamaye bata je gidanta ba, gashi ankusa shekara tana cikin yin wannan mitar kira yashigo cikin wayarta nan ta dauka tun kafin tayi magana taji muryar Aryan,
"Hello mommy...."
Murmushi tayi ta amsa masa ko gaisheta baiyi ba yasoma bata labari yadawo daga makaranta umma tabashi abinci yaci kuma yaje islamiyya,uncle yadawo daga office ya kawo masa shawarma da tsire,labarai dai kala kala,
"Ina uncle din yake?"
"Yana daki yace kar na dameshi da surutu"
Dariya tayi saboda abisa dukkan alamu kam Khalil ba mai son hayaniya bane sai wacce ta zama dole shiyasa take mamakin yanda yake yi da bakin matasa a office duk lokacin da suka kawo masa ziyara kila wannan dalilinne yasa baya rabuwa da ciwon kai kullum cikinsa yake,
Sun jima suna waya da Aryan har saida Khalil yafito nan tajiyo muryar shi yana tambayar Aryan wai har yanzu basu gama hirar da mommyn ba?lumshe idanuwa tayi tana murmushi sakamakon jin muryar sa da tayi tasan yanzu yana can sanye da farar t shirt da bakin wando ko fari tunda shigar tashi kenan kullum babu sauyi, sallama sukayi da Aryan ta kashe wayar.
Sabo turken wawa bata taba sanin cewa tayi mugun sabo da gadonta ba sai yau domin kasa bacci tayi sai juye juye kadai taketa faman yi tana tuno abun kaunarta, fuskarsa, muryar shi da dukkan yanda yake gudanar da komai nashi cikin jan aji da nutsuwa, murmushi tayi ta rungume pillow ahankali cikin rada ta furta "I love you minister"........................鉁嶐煆?
*Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:13 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*
*37*
***Baccin yau tayi shi ne cike da nutsuwa,kewa da kuma shauki,hakanne ma yazama silar faruwar wani mafarki mai dadi acikin baccinta,
Khalil ta gani zaune akan wasu duwatsu agaban bakin wani tafkeken kogi,shi kansa ruwan yana da daukar hankalin duk wani ma'abocin kallonsa ko kuma wanda yasamu kansa a wurin. K'ananan duwatsu yake ta dauka yana cillawa cikin ruwan,yana sanye da farar t shirt da bakin trouser fuskarshi boye cikin bakin gilashin da ya karbeshi yayi masa kyau ainun,ita kuma tana zaune gefe daya can nesa dashi itama sanye cikin farar doguwar riga amma kuma tana ta kuka tsawon lokaci shi kuma yaki ya ko kulata bare ya bata hakuri,
Tsawon wani lokaci bai juya ya ko kalleta ba sai tajiyo wata kara daga bayanta kafin ta juya tuni yayi kukan kura yayi tsalle yazo ya fizgota jikinshi ya rungume yana kakkareta alamar baya son wani abu ya sameta ko ya tabata,zuwa cann bayan dan wani lokaci ya dago kanta yana kallon kwayar idonta sai dai ita bata iya ganin nashi idon sakamakon bakin gilashin dake sanye a fuskar tashi,cikin muryar shi mai taushi da dadin saurare yace,
"Sa'adah...... Kin zaci bana sonki ko?..... Gashi ke kuma kina sona.... Shi so sirri ne dake boye cikin zuciya...... Wani mutumin yana mutukar kaunar ka amma yakan boye hakan acikin ransa batare da ya bayyana maka ba....."
Sakinta taga yayi ya durkusa akan gwiwowinsa irin yanda indiyawa keyi hannunshi guda daya yakai ya kamo nata yayi kissing dinshi sannan ya bude baki cikin salo mai burgewa yace,
"Nima ina sonki......! I love you sa'adah......"
Wata iskace mai karfi da dadi ta taso wacce ke barazanar yin awon gaba da ita cak taji ya dagata yasata cikin jikinsa ya lullube ta da yalwataccen kirjinsa,
Juyi kawai take yi daga kwancen da take saboda har lokacin cikin mafarki take tana rungume a kirjinsa suna juyawa iska na kadasu tana shakar kamshin jikinsa mai saukar da nutsuwa,
"Hanan..... Hanan...."
Ahankali ta bude idonta nan taga mamaye tsaye da carbi a hannunta gari har yayi haske alamar ta makara,
"Wai kinyi sallah ma kuwa?"
Girgiza kai tayi ta sauka daga kan gadon tana jin wani sabon shaukin kaunarsa acikin zuciyarta. Kamar mahauciya ko sabon kamu haka ta zama ranar domin wuni tayi tana murmushi bata da aiki sai murmushi ita kadai,da zarar ta tuno wannan mafarkin da tayi sai murmushi ya kufce mata haka tayi ta fama tana buri tare da fatan mafarkin ya zama gaske,
Yauma sunyi waya da Aryan kuma sun jima yana yimata surutu dan har da sanar da ita wai Daddy bashi da lafiya yana yin ciwon ido dayake yau khalil da ciwon ido ya tashi gaba daya idanuwan sunyi jajur kuma suna yimasa radadi ga dan kunbura da sukayi,
Bayan sun gama waya da Aryan sun gaisa da umma barira ta katse wayar tana tunanin taya yadace ta duba Khalil? Shin kiransa zatayi ko text massage zata tura masa? Ita fa gaba daya Khalil dinne kunyarsa take ji idan ta tuna irin diban albarkar da tayi masa abaya, shiyasa ba kyau saurin yanke hukunci ita dai gashi yanzu zuciya ta kaita ta barota aruwa,shiru tayi tana nazari to idan ta kirashi me zata ce masa? Kawai gara tayi text din zaifi sauki dama dadin text massage kenan zaka iya fadawa mutum abinda kake so wanda bazaka iya fada ba idan waya kuke, shawarar zuciyarta tabi ta tura masa massage din.
Khalil yana zaune kan gadonsa da laptop a cinyarshi gefe daya kuma Aryan ne shima yayi matashin kai da kafarshi idanuwanshi sanye da farin glass sakonta ya shigo bai samu damar budewa ba saboda yana aikine mai muhimmanci,sai bayan da ya gama ya dauki Aryan yaje ya kwantar dashi a dakinsa ya shiga kitchen ya hado coffee mai zafi sannan ya koma bangaren sa, glass din idonshi yacire saboda dama saboda hasken system din shiyasa yasaka,wayar ya dauka yana zaune kan sofa yana kurbar coffee dinshi bude sakon yayi nan yaga daga Hanan ne wani dan kyakkyawan greeting card pic yagani mai kyau mai dauke da flowers jajaye ajiki sannan anyi rubutu kamar haka,
_If these flowers were wishes, then my wish for you is to get well soon._
Shiru yayi kamar wanda yake kokarin gano wani abu daga jikin sakon zuwa can yasaki ajiyar zuciya sannan yatura mata da reply, _Thanks_,bata damuba saboda dama tasan halinsa sakonshi bai wuce ok, alright, thanks etc.
***
Cike da mamaki sumayya ke kallon mujahid tun bayan da suka kamo hanyar kanon dabo tumbin giwa koda me kazo anfika, Wai yau itace mujahid yaje tahowa da ita takanas har garin katsina,hannu takai kan radio din cikin motar zata kunna,
"Karki kunna min...."
Fasa kunnawa tayi ta kawar da kanta tana hararar gefe,
"Ke haka akeyi sai ki wani taho gida ki nemi wurin zama ki shantake..... Kinma manta da mutane gaba daya"
Sai lokacin ta kalleshi tana kokarin turo masa baki,
"Suwaye mutanen? Mami ce kuma kullum muna gaisawa ta waya"
"Ohh mami kadai kika sani? Idan kika kara turo min bakin nan sai kinga yanda zanyi dake...."
Bata kara magana ba taja mayafi ta rufe fuskarta zatayi bacci,
"Karki yarda kiyi min bacci a mota,ki bude idonki kar ki jamin ace satoki nayi...."
Gaba daya ita mamaki mujahid ke bata wai shine yaketa takalarta da janta da surutu haka mujahid din da ada ko magana tayi masa sai ya gadama yake amsawa idan kuma bai gadama ba harara ce ke rabasu amma wai yau shine keta janta haka,har suka je kano yana janta da magana,agaban wani dan karamin restaurant ya tsaya ya fita yana cewa ta jirashi idan kuma tafito ta bata to babu ruwanshi, murmushi tayi ta dauke kanta bayan wasu yan mintuna yadawo dauke da wata yar kyakkyawar leda wadda aka zubo masa snacks aciki harda drinks guda biyu,
"Amshi kici yar kauye dake kawai...."
"Yan kauye dai"
"Keda wa?" Ya bukata yana kokarin yiwa motar key,
"Nida kai tunda duk tushenmu daya..."
Murmushi yayi ya harareta, "ke dai yarinya"
Lumshe idanuwanta tayi ta jingina da jikin kujera tana yiwa Allah godiya acikin ranta da yakawo mata wannan rana cikin sauki batare da tasha doguwar wahala ba.
***
Kullum sai sunyi waya da Aryan da umma barira haka shima Khalil tana kokarin tura masa massage tana tambayar idanunshi domin har yanzu bai samu lafiya ba sai dai da sauki za ace,
Acikin gidajen dangi da yan uwa da sauran abokan arziki babu inda bata je ba kuma duk inda taje sai takai turamen atamfofi da shadda ita kanta tana jin farin ciki da dadin abinda tayi domin ta dadadawa mutane da yawa ta hanyar basu wannan shaddar da atamfar,gidan anty salaha kuwa kwana biyu tayi acan anty salaha sai mitar uwar ramar da tayi take tayi tana cewa taki ta kwantar da hankalinta ta zauna lafiya agidan mijinta tayi kiba bayan bata rasa komai na jin dadin rayuwa ba idan kuma saboda tsufan minister ne take sawa ranta damuwa ai akwai matan da suka auri mijin da yafi nata tsufa, murmushi Hanan tayi sannan tace,
"Ai anty bama tsoho bane wallahi,matashi ne mai jini ajika son kowa kin wadda ta rasa.... Bari ki ganshi fa"
Hotunanshi da tayi saving a Instagram ta budewa anty salaha ta mika mata wayar tafara gani daya bayan daya,
"Ikon Allah.... Hanan yar baiwa.... Ke yanzu dama wannan balaraben ne mijin naki? Allah mai yadda yaso.... Hanan ki godewa Allah"
Haka anty salaha keta faman santin Khalil ai da taga pic din Aryan sai ta sake rudewa tana cewa sai kace jinin larabawa? Ita dai hanan dariya take yi saboda itama farkon ganinsu tayi wannan santin da rudewar amma ta boyewa anty salaha halin da take ciki na tsananin son Khalil wanda shikuma abisa dukkan alamu bai ma san tanayi ba. Satinta daya agida PA yaje ya daukota kamar yadda Khalil ya fada mata,harda kukanta itada mamaye ita tanayi mamaye nayi, tsakanin d'a da mahaifi,
K'arfe biyar na yamma suka shiga garin Abuja lokacin anyi ruwa an dauke amma garin awadace yake da ni'ima mai yalwa ga iska mai dadi tana kadawa, lumshe ido tayi ta bude lokacin da suka shiga unguwar su tana zaune ta kame a owners corner,unguwar shiru babu hayaniyar komai ga shuke shuke sunyi shar shar luf luf dasu, tangamemen gidansu suka shiga har bakin kofar shiga PA yakaita yayi parking, tunda Aryan ya hangota yabaro malamin islamiyyarshi yataho yana yimata oyoyo karatun da bai koma ba kenan,murna da umma barira da Aryan kamar sayi me saboda gidan duk sororo yayi musu lokacin da bata nan itama umma ba abokin zance sai kayan kallo da radio,har dare suna tare a dakin umma ga tsarabar da ta kawo musu nan iri iri da na ciye ciye da kayan amfanin gida,
Bayan sallar ishah tafito daga wanka ta shirya cikin riga da wando na bacci blue colour,yau jin kanta take yi wata iska na shigarta sakamakon kitson da tayi kafin ta taho dan rabonta da kitso tun kafin bikinta dan tunda tazo Abuja ba ayi mata kitso ba ita dai umma ita keyi mata tunda ta dan iya, Aryan ne yashigo rike da balloon yana son hurawa ya kasa yabata wai ta hura masa awurin Daddy ya karbo,karba tayi ta kama hannunsa suka koma kasa wurin umma,itace har 12 saura adakin umma suna hira daga k'arshe tayiwa umma sallama ta tashi dama tun dazu takai Aryan dakinshi,
Tun da ta shawo kwana iskar dake kadawa tafara kawo mata kamshinsa cikin hancinta ai kuwa tana taka kafar bene tajiyo takunshi shikuma yana kokarin saukowa,sai da ta lumshe idanuwanta sannan ta budesu daidai lokacin ta hangoshi yana sanye da farar t shirt da bakin dogon wando hannunshi rike da dan karamin coffee flask yana kurba idanuwanshi sanye da bakin glass...........................鉁嶐煆?
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:13 AM - Ummi Tandama: 38
***Ahankali take hawa steps din shikuma yana saukowa cikin kwarjini da cikar haiba,yana kara dosota kamshinsa na kara kusanto ta kasala na kara lullubeta,
Dan sunkuyar da kanta tayi lokacin da suka zo kusa da juna,
"Ina yini uncle?" Ta fada muryar ta na dan sassarkewa wanda ita kanta ba zatace ga dalili ba kawai dai abinda ta sani shine kusan duk lokacin da zata ganshi to sai ta tsinci kanta cikin wannan halin koma fiye da haka domin nutsuwarta tafiya take tabarta har sai baya nan sannan take dawowa gareta,
"Lafiya lau.... Ya mutanen gida?" Ya amsa yana cigaba da tafiyarsa batare da ya tsaya ba,
"Suna lafiya,ya jiki?"
"Alhamdulillahi...." Yabata amsa lokacin har ya dan gota ta,
"Allah ya kara sauki" Ta sake fada duk da bata da tabbaccin ko zai jiyo abinda ta fada,ahankali taci gaba da tafiya cikin ranta tana jin wani abu yana tsirgawa cikin magudanar jininta,kamar wannan shigar da yayi sak ita taganshi da ita cikin mafarkin da tayi kwanaki biyar da suka wuce,
Bedroom dinta ta shiga ta sulale gefen gado asanyaye ta kwanta tana jin damuwa na lullube farin cikin da take tare dashi yanzu,da ace Khalil na sonta ko yana jin wani abu agame da ita da yanzu suna can tare amma sai dai kash ba itace a gaban sa ba abisa dukkan alamu.
Washe gari haka ta tashi sukuku danma dai online classes dinsu na dan debe mata kewa domin abubuwan da take koya a group din Allah yayi yawa dasu ko a fannin girke girke ta koyi girki kala kala wadanda ba zasu lissafu ba ita kuma dama Allah ya dora mata jarabar son girki dan sam bata ganin wahalar sa amma abun haushi tun da tazo gidan Khalil iya farfesu kawai ta taba girkawa komai kuku ke dafa musu,wuni tayi adaki tana tsara abubuwan da zata bada a sissiyo mata domin hada turaren wanka da humrah wadanda hajja hasinah ta koyar musu,ita nata take son tayi daban mai kamshi na musamman wanda duk wanda yaji zai so,
Zuwa yamma ta bawa Emah driver yatafi kasuwa domin harhado mata kayan,daga nan falon kasa ta zauna wurin umma barira dake zaune tana sakar maficin roba anan take jin wai Khalil yau minna yatafi gaisuwa,dan tabe baki tayi cike da bacin rai amma bata nunuwa umma ba.
Zuwa dare Khalil yadawo kuma yau da wuri yadawo sakamakon takurawar da idonshi yayi masa wani irin radadi da zugi yake yimasa ta ciki,
Yana zaune falonsa jikinsa sanye da jallabiya umma barira da Aryan da Hanan suka shiga domin dubashi,waya suka iske shi yana yi yana cewa,
"Khalid kace mata nifa bana cin mike..... Ehhh...to shikenan muna zuba ido....ok thank you"
Jin sunan wanda ya ambata yasake tabbatar musu cewa da Khalid yake yin waya nan Aryan ya tubure yahau rigimar shi sai anbashi yayi magana dasu Nawwar,mika masa wayar Khalil yayi sannan ya maida hankalinsa ga su Hanan wadanda ke zaune ita umma tana saman kujera ita kuma Hanan tana k'asa kan Rug. Da umma suka fara gaisawa tana tambayar ya idon nashi saboda yau da sassafe yafita, tissue ya yaga yana dan goge idon nashi sannan ya dagosu jajur yana kallon umma ita kuma Hanan tana kallonsa tana ganin yanda idanuwanshi suka yi ja,
"Wallahi umma idonne ma ya takura min nadawo gida amma ban gama aikiba a office kawai dai tahowa nayi.... Ina saka masa magani amma kamar bana sakawa"
"Ai likitan ido ya kamata ka gani mu'azzam..."
"Ai shi nagani umma, Dr Al'amin ne ma ya hada ni dashi..."
Sai da Hanan tajira suka gama da umma sannan ta gaishe shi,sau daya kurum ya kalleta daga nan bai kara ba sun dan jima wurinsa suna hira da umma sannan suka fita,
Washe gari da burin yin aiki ta tashi tana son hada humrah da turaren wanka kuma cikin nasara ta yisu kamar dama can tajima tana yi,gaba daya sashenta gaurayewa yayi da kamshi kamar me ita kanta kamshin take yi saboda kayan hadin da tayi amfani dasu masu kyau ne da tsada sannan ta dan kakkara da wasu turarukan wanda ma hajja hasinah bata saka musu suba, lokacin da ta kammala saida ta yiyyi wa kayan hotuna sannan ta turawa hajja hasinah,kowa na gidan saida ta diba masa ta saka masa acikin toilet daga Aryan har umma har Khalil shi amma Khalil a toilet dinshi na falo ta ajiye masa dan ba taba shiga master bedroom dinshi ma tayiba har yau bata san kalar bedroom dinsa ba ita kuma humrar dama kanta ta hadawa shiyasa bata bawa kowa ba,ji tayi idanuwanta suna yi mata kekayi nan ta sosa kamar kuma dama jira suke suka fara yimata radadi sai kuma hawaye kafin dare itama tuni har ido ya ruruce yahau ciwo ya kada yayi jajur, lokacin da umma tagani cewa tayi to awurin Khalil ta dauka sai akira mata likita itama yadubata, itama tasan awurin nashi ta dauka dama tun lokacin da sukaje falonsa ta kalli kwayar idanuwanshi tafara jin nata kwayar idon suna dan tsikarinta kadan,
Har 12 dare bata yi bacci ba sakamakon ciwon da idanuwanta keyi ganin babu haza yasata yimasa text wai bata da lafiya ciwon ido ke damunta ko zai taimaka ya Kira mata Dr? Reply taga yayi mata da wai tazo,
Tashi tayi ta sauka daga kan gadon ta saka hijabinta da silifas tafita,yana kishingide akan kujera kafarshi daya saman center table yana kallon CNN ta bude kofar ta shiga bakinta dauke da sallama, idanuwanshi akan TV ya amsa batare da ya kalleta ba. Wuri ta samu ta zauna can nesa dashi sosai amma duk da haka sai da hancinsa ya jiyo masa masifaffen kamshin humrar dake tashi jikinta,shiru yayi ya dan lumshe idanuwanshi na dan wani lokaci sannan ya kalleta da lumsassun idanuwanshi wadanda suka kara yin jaa,saurin kawar idonta tayi daga kanshi dan tunda ta zauna take kallonsa kamar zata cinyeshi,
" Me kika ce....?" Taji ya tambayeta bayan ya dauke idonshi daga kanta,
"Idanuwana ke ciwo..." Tabashi amsa tana wasa da bakin hijab din jikinta,
"Me yasamu idon?" Ya sake tambaya,
"Awurinka na dauka..."
Jin abinda tace yasashi daga ido ya kalleta,
"Awurina kuma?"
"Uhmmmm"
Shiru yayi na dan wasu mintuna sannan cikin rashin daga murya taji yace,
"Shiga bedroom dina zaki ga magani ki dauko...."
Har ta mike bata san me ya tuna ba taji yayi saurin cewa,
"Zauna kawai bari in dauko.."
Daga haka yatashi yawuce cikin bedroom dinshi nan tabishi da kallo farar t shirt ce jikinsa da farin wando wanda da kadan yawuce gwiwarsa shima fa ta lura idan yasamu dama akwai gayu idan zai fita ne kullum cikin manyan kaya,
Koda yashiga cikin dakin sai da yatsaya gaban bedside drawer dinshi wanda ke dauke da hoton Aryan da hoton Ramlat cikin wasu frame kanana guda biyu masu kyau,ya dan jima yana duban hoton kamar mai son gano wani abu aciki sannan ya dauki maganin yafita,
Tana zaune inda yatafi ya barta zama yayi saman kujerar da yake zaune tun farko, sannan ya dora mata maganin kan center table din gabanshi,
"Zo ki dauka"
Anutse ta tashi tazo ta dauka tana kallonsa alamun neman karin bayani,
"Ki disa a idon naki idan zaki kwanta"
"To kai kuma fa?" Ta fada muryarta na rawa kamar wacce ke jin tsoron fada,
"Ba matsala kije dashi"
"Nagode,sai da safe"
Kai kurum ya daga mata ta juya ta fita tana jinjina rashin son magana irin na wannan bawan Allah dan idan yana yinta kamar anyi masa dole.
Kamar ciwon idon nasu layi yake bi washe gari shima Aryan yatashi da shi duk idanuwan nashi a like haka suka yita fama har tsawon sati biyu umma ce kadai bata yi wannan ciwon idon nasu ba,
Abangaren abubuwan da take koyo kuwa yanzu tasake bada himma sosai kuma alhamdulillah ta koyi abubuwa masu yawa kuma tana ma kan koyo wani abun burgewa ma shine ta kan jajurce wurin gwada dukkan abun da aka koyar dasu,
Yauma kamar kullum tana zaune falon kasa itada umma kowa yana aikinsa maganin zaman banza,ita umma tana karasa mificin da take sakawa ita kuma Hanan tana sabulun gyaran jiki wanda hajja hasinah ta koyar dasu cikin satin nan,muryar Aryan tajiyo yana ta zuba surutun nashi ko shida waye oho,
"Kinji d'an naki can ko wa ya samo yabaro karatun islamiyyar tashi kuma?" Umma ta fada tana kokarin bantarar goronta,kafin Hanan tayi magana tuni anbude kofa, dukkansu ita da umma d'aga ido sukayi suka mayar da hankalinsu kan wad'anda ke shigowa,Zaid ne rike da trolley yana janta Aryan na biye dashi shida wata kyakkyawar matashiyar mata sai zuba mata surutu yake yi,
Ganinsu yasa umma fadada fara'arta tana fadin lale marhabun da mutanen gombe,itama Hanan ba abarta abaya ba wurin yimusu barka da zuwa,
Kujera duk suka samu suka zazzauna ana kokarin gaisawa,jin muryar matar yasa Hanan dan sake kallonta lokacin da taji umma tace,
"Maamy mutanen London..... Saukar yaushe?"
"Ai zan kai 3 weeks da dawowa.... Koda yaushe Khalil na mitar wai bana zumunci naki zumunci shiyasa shima ya shareni ko Aryan baya kai min to yanzu gani nazo har gida....."
"Allah sarki ai kuwa kin kyauta.... Sannu da zuwa"
"Ina yini?" Hanan ta fada tana kallon ta,dan murmushi maamy tayi sannan ta amsa cikin fara'a,
"Lafiya lau.... Mun sameku lafiya?"
"Lafiya lau" Hanan ta amsa mata tana tattare kayanta tunda dama ta gama,sama ta haura domin kai kayan bayan sun gaisa da zaid, lokacin da take saukowa tana jiyo muryar Zaid yana cewa umma,
"Ai ni umma kasa gane Anty maamy nayi Yaya Khalil ma nasan dakyar idan zai ganeta dan tafi 4 years rabonta da kasar nan"
Dariya maamy tayi ta cire farin glass din dake idonta,
"Zaid kaima fa baka da dama"
Ita dai hanan samun wuri tayi ta zauna tana kallonsu da sauraren hirar da suke yi yayinda ita kuma Aryan yazo ya haye cinyarta. Kasancewar ga dakuna nan reras agidan daki guda aka warewa anty maamy ta shigar da kayanta lokacin anata kiraye kirayen sallar magriba,suma su Hanan basu zauna ba kowa dakinshi yawuce domin gabatar da salla shikuma Aryan suka fita tare da Zaid,
Hanan bata samu fitowa ba sai bayan sallar ishah saboda tana can dakinta tana chaten da su salaha tana tuttura musu abubuwan da ta gwaggwada na daga cikin wad'anda ta koya,bayan sallar ishah tafita domin cikinta yafara kiran ciroma,tana sanye da dark blue din doguwar riga yar kanti da hijab asama,falon babu kowa hatta umma bata fito ba,zama tayi kan dining bayan ta debi abincin da zata ci,tana tsaka da cin abincinta Zaid suka shigo shida Aryan,suna zama saiga umma itama tafito nan suka cigaba da hirar su suna cin abinci,
K'arfe 9 tabar falon takoma sashenta bata sake fitowa ba sai 11 saura lokacin Khalil yadawo suna can falonshi gaba dayansu harda umma,sashen nashi itama ta nufa jikinta na fitar da wani kamshi mai sanyi,cikin nutsuwa ta bude kofar falon ta shiga abinda idanuwanta suka gane mata shine yasanya ta taji jikinta yayi sanyi cikin rashin kwarin gwiwa ta juya zata koma...........................鉁嶐煆?
_Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din._
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:13 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*
*39*
***Muryar umma tajiyo tana kiranta lokacin da take kokarin komawa,
"Sa'adatu ina kuma zakije.....? Ki karaso mana ayi dake"
Babu musu tafasa fita ta shiga,kujera ta samu ta zauna tana kallon kowa, Khalil ne zaune kan doguwar kujera shida Aryan wanda ke bacci akusa dashi sai Anty maamy dake kujerar kusa dashi tana sanye cikin brown colour din doguwar riga sai Zaid dake kujerar kusa da ita amma shi gaba daya hankalinsa yana ga wayar dake hannunsa yana daddannawa ita kuma na zaune opposite dinsu tana kallonsu,akusa da umma Hanan ta zauna tana yiwa Khalil sannu da zuwa sannan tana sake kallon Anty maamy dan sai yanzu ne ma tayi mata kallon tsaf,doguwa ce sosai dan idanma Khalil zai fita tsayi to da kadan zai fita, fatarta mai haske ce sosai wadda hutu da jin dadi suka sake haskaka ta, siririya ce Sam bata da kiba amma fa kuma tana da masifar kyau kamar ita tayi kanta tana da diri da sura,
Hanan wani abu taji ya tsaya mata arai sakamakon murmushin da taga Khalil nayi lokacin da suke yin hira da Mami,
"Maamy uwar son girma.... Wai dan Allah har yanzu baki daina son girman nan ba? Lokacin da kina yarinya fa har kuka kike yi idan akace kece karama acikinmu...."
Wata dariya mai kayatarwa maamy tayi sannan cikin murmushi tace,
"Woohhh Khalil ka iya bada mutane wallahi,yanzu da girmana kake fada min haka agaban Zaid..... Kana gani na kusa diban surukai,sahla fa jss 3 take Jawad jss 2 faruk ne kadai a primary school"
"To kuma shine me? Kaji yarinyar nan da wata magana,to nida Khalid da ace da wuri mukayi aure da ba tuni mun aurar da 'yaya ba....."
"To wai Khalil da kai da Khalid din da me kuka fini? How many years kuka ban? Da me kwado yafi gaya ne wai?"
Dariya Khalil yayi yasake kishingida jikin kujera alamar yana jin dadin wannan hirar,
"Wai dan Allah shekararki nawa? Fada min"
"Am 39 by the way...."
"Lallai maamy kina da son shekaru,to yarinya ai ko mu bamuyi 39 ba 38 muke har yanzu.... Ke ai ba zaki fi 36 ba ko 35..."
"Haba haba Ibrahim....haba Ibrahim ya zaka fadi haka? Nice 35 ko 36? Gaskiya nafi haka"
"Au wai ko dan kinga kin hayayyafa kin tara yara shine kike karawa kanki shekaru? Saboda kinga su sahla sun fara girma ko.... To ai ba anan takeba"
Hanan kallonsu kawai take yi dan bata taba sanin cewa Khalil yana iya yin hira doguwa kamar wannan ba sai yau gaskiyar bahaushe da yace kowa da abokin zancensa,yau kam shi cikin nishadi yake da alama dan harda dariya yakeyi Hanan har tambayar kanta take yi wai dama mutumin nan yana hira? Kuma koda wasa bata taba bashi shekaru har 38 ba dan wallahi da za sata agaba ace ta kiyasta shekarunsa da ko tantama bata yi zatace 32 ko 33 domin jikinshi da fuskarshi duk basu nuna yafi hakanba,
"Wai ma yaushe muka daina tsallakar dake kwata ne maamy? Idan kin manta in tuna miki"
"Ibrahim kenan.... Ka manta lokacin da nake tare maka fada ko? Ka manta lokacin?"
Dariya Khalil yayi,
"Gaskiya maamy ki rage son girma dan wallahi duk shekarunki mu dai mun girme miki nida Khalid"
"Da shekara daya da rabin? Shekara daya da rabi ne fa Ibrahim"
"Zan fadawa Khalid ai duk abun da kika ce"
"Shima saida muka yi dashi ai zuwan nan da nayi gidanshi,ku son girma gareku bayan kuma tuni na kwace muku girman,yanzu dole ku bani girmana"
Murmushi Khalil yayi nan suka cigaba da hirar kuruciya har suka gangara suka koma ta duniya su Hanan dai na zaune suna jinsu saida dare ya raba sannan suka fara tafiya daya bayan daya,umma ce ta fara tafiya sannan Zaid,ita kam Hanan tana nan zaune koda za su kwana anan tayi alkawarin sai taga tafiyar maamy sannan zata tafi dan haka kawai taji bata jin dadin yanda Khalil yasake yabiye maamy suna hira duk da tasan yar uwarsa ce amma bata san ta ina suka haduba kuma da alama tare suka yi kuruciya suka tashi tare dan har hirar zuwa makaranta lokacin da suna kanana sukayi. Bayan fitar anty maamy itama tashi tayi ta dauki Aryan tafita sai da tafara kaishi dakinshi tukunna sannan ta wuce nata,bata san dalili ba amma baccinta kadan tayi ko me yasa oho kuma saida ma tajima kafin ta samu ya dauketa saboda tana ta tunane tunane marassa amfani zuciyarta sai faman sake baci take yi,
Washe gari haka ta tashi shima babu walwala ahaka ta shirya Aryan sannan takoma part dinta bayan yatafi makaranta,wanka itama tayi ta shirya cikin atamfa exclusive riga da skirt sannan tasha humrarta da sauran turarurruka masu dadi,fita tayi dan ta sauka k'asa tana fitowa ta hango anty maamy ta glass ta nufi part din Khalil, kamar ta bita amma sai ta nufi kasa tana duba agogon dake daure a hannunta karfe 9 saura wasu mintuna,
A babban falo ta iske umma da Zaid na kokarin yin breakfast Zaid rike da waya a hannunshi yana sakale da earpiece, gaisheta yayi duk da ahaife kamar zai girme mata amma dai yana bata girmanta,ruwan tea kawai ya hada da sauran kayan soye soyen da John yayi ya dauka yawuce dakinsa dake nan k'asa.
Kallon umma barira Hanan tayi bayan Zaid yatashi,
"Umma ina kwana? Ya gajiyar zama wuri daya?"
"Alhamdulillahi Sa'adatu,ya akaji da dawainiyar gida da kulawa da Sulaimanu?"
Murmushi Hanan tayi amma batace komai ba, hira suka cigaba dayi ita da umma jifa jifa har sukaji alamun saukowar Khalil,tare suka jero shida anty maamy wacce ke sanye da doguwar riga ta bacci ta yafa babban mayafi shi kam farin tsadadden boyel ne ajikinsa wanda yasake fito dashi dass kuma ya amsheshi,
Tun kafin ya karaso kamshinsa yafara karasowa, Hanan tun bayan kallo daya da tayi musu bata kara sake kallon su ba,tana ji suna gaisawa da umma yana sanar mata da wai Legos zaije amma by flight kuma insha Allah ayau zai dawo,
"Ranka yadade wannan charger din abar min mana sai ka nemo wata...." Anty maamy tafada tana daga charger din dake hannunta,
"Kinma isa..... Aro nabaki kina gamawa ki mayar min"
"Dan Allah ka nemo wata Ibrahim.."
"A'a indai bada a nemo miki,amma nidai ki mayar min"
"To babu matsala...., Allah yatsare saika dawo"
Har tajuya zata tafi ta sake dawowa,
"Am Khalil dan Allah acikin motocin gidan nan za a ara min daya inaso zan fita anjima....zanje gidan wata friend dita"
"Babu matsala ki fadawa Zaid sai ya d'auko miki...."
Daga haka yafita itama ta wuce daki, Hanan dai sama sama ta yi breakfast dinnan ta tashi ta koma part dinta wanda ita kanta bata san abinda ke damunta ba,
Tunda ta kule acikin part dinta bata fito ba sai la'asar iya umma kadai ce agidan da ta tambayi umma su Zaid fa sai tace ai tun dawowar Aryan suka fita su uku har Aryan din da anty maamy saboda dama yau babu islamiyya tunda alhamis ce,bata kara magana ba taje ta zubo sakwara da miyar egusi ta dawo ta zauna,
"Wai umma meye dangantakar Abban Aryan da anty maamy?"
"Kakanninsu daya,da uban maamy da uban Khalil ai uwa daya uba daya suke.... Dukkaninsu 'yayan moddibo ne,Asalinsu, Ibrahim moddibo haifafen garin Billiri ne dake nan gombe sana'arshi a wannan zamani kiwo domin Allah ya hore masa dabbobi masu tarin yawa kusan yana daya daga cikin mutanen da ake lissafawa wadanda keda tarin arziki a wannan karnin domin yana da yawan shanu,tumaki, da kuma jakuna,matarsa daya maryo da yara hudu Sulaiman shine dan fari sai Idris dake bi masa sannan sai mariya sai kuma karamarsu muzayya,
Duk cikar gombe da batsewarta babu wanda bai san moddibo ba domin mutum ne sananne kuma malami domin lokacin da yaransa suka fara girma yabaro Billiri yadawo cikin garin gombe da zama nan yasake bude tsangayarsa inda almajirai ke taruwa suna karatu,anan 'yayansa duka suka yi karatu na allo da na zamani amma na allon yafi yawa dan iya Idris ne kadai yasamu nasarar yin karatun boko mai yawa amma yayansa Sulaimanu shi iyakacinsa primary,
Anan cikin gombe duk sukayi aure shi Sulaimanu yar gidan sarauta ya aura yar sarki gaba da baya wacce take sonsa dalilin zuwa fada da suke yi tare da mahaifin sa moddibo saboda aminin sarki ne a wancan lokaci dan shine limamin gidan sarki ma ko ina sarki zaije suna tare to kinji inda ita zaituna suka hadu da Sulaimanu mahaifin mijinki har akayi aure kuma aka samesu su biyar da saude dashi ibrahim mijinki da Lubnah da Humaida da kuma zaidu mai sunan kakan hajiya zaituna wato sarki zaidu na uku,Shi kuwa Idris can yawon karatunsa a k'asar borno ya samo tasa matar labibah wacce ta kasance shuwah wanda ana kyautata zaton ma asalinsu larabawan sudan ne zama yakawo su nan k'asar maiduguri suka zo suka zauna,bayan andaura musu aure nan gombe suka dawo suma suka zauna ga dakin zaituna ga na labibah kowacce tana zaune da mijinta lafiya,kuma yanda kan mazajensu yake ahade haka suma suka hada kansu kin san zama irin na da ya banbanta da na yanzu,ita zaituna duk da kasancewar ta yar sarki jikar sarki bata dauki girman kai ta dorawa kanta ba tare suke yin girki da sauran aikin gida ita da labibah har Allah yabawa kowaccensu rabo bayan zaituna ta yaye babbar yarta ta farko saude na biyunne sukayi rainon ciki lokaci daya dan kusan tare suka haihu tsiran na kwana biyar ne kowaccensu ta haifi danta namiji kuma duk aka saka musu sunan moddibo wato ibrahim amma shi Khalil da yake shine babba shi sai moddibo yasa masa Khalil shikuma dayan Khalid to tare suka taso suka yi wasan kasa suka yi komai da kika sani tare shekararsu daya da watanni biyar labibah ta haifi maamy to itace aka sakawa sunan maryo mahaifiyar su Sulaimanu shine suke kiranta da maamy,itama acikinsu Khalil ta taso tare suka tashi har girma,to da yake kin san shi Idris yayi karatun zamani babu laifi to shine yashiga siyasa ka'in da na'in kuma da Allah ya dafa masa sai yasamu karbuwa,jinin moddibo akwai albarka kowa yana son Idris dan har mukamin governor yarike kuma shine yajawo Khalil ajikinsa yadorashi shima aharkar siyasar duk da shi Khalil din bawai dan yana da sha'awar hakanba dan har commissioner na yada labarai yayi masa lokacin mulkinsa shekararsa hudu yana rike da commissioner na yada labarai matasa da wasanni saboda abinda yakaranta kenan a makaranta,to lokacin da aka gyara kundin tsarin mulki akace anbawa yan k'asa da shekara 40 damar rike mukamin ministoci saboda suma yara zasu iya a lokacin Alhaji Idris yatura Khalil kuma da yake Allah ya tsaga da rabonsa kin ganshi nan sai yasamu dan yanzu akalla ba a kasaru ba mun shafe fiye da shekara biyu a nan kadanne bai karasa uku ba,maamy yar uwarsa ce sosai yaranta uku amma yanzu babu auren dan tafi shekara uku ma bata tare da mijinta, zawarci take yi....."
Ajiyar zuciya Hanan ta sauke bayan umma ta kammala bata tarihin su Khalil,to ita yanzu me yadace tayi? Ta ina yadace tafara? Wanne mataki yakamata ta dauka............................??鉁嶐煆?
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:14 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*
*40*
***Sakin fuskarta tayi bata bari umma barira tagane komai ba dan bata nuna mata cewa tana tare da damuwa ba,har magriba suna tare da umma suna shan hira da yake umman gwanar hira ce,suna kokarin tashi su shiga salla su Anty maamy suka dawo tana rike da hannun Aryan wanda keta tsallen rashin ji,
Damm Hanan tayi tana kallon anty maamy wacce ta hade cikin bakar riga gown mai stones ta dan yafa mayafin rigar akanta kuma hakan ba karamin kyau yayi mata ba sai dai ko hassada irin ta mai ita,
Sannu da zuwa suka yimusu Hanan bata jira komai ba ta tashi ta hau sama tare da Aryan,bayan sun idar da salla acikin dakinta Aryan sai labari yaketa bata na unguwar da suka je dan har abokan wasa yasamu agidan shiyasa fitar tasu tayi masa dadi ita dai hanan saurarenshi take tana jinjina kai amma idan taga fitar tana neman tayi yawa to zata sanarwa ubanshi dan babu abinda yayi mata zafi kar abu yafaru Khalil yazo yana ganin laifinta saboda shi ba sakaka yake bari ana fitar masa da yaro ba dan kullum ma sai yayi wannan takarar yanzu ne ma ya hakura ya daina,
Sai bayan da tayi sallar ishah sannan ta fito nan ta iske umma da su Zaid ana shan hira harda anty maamy,itama zama tayi akayi da ita sune har wurin 11 dan saida Khalil yadawo tukunna sannan hirar ta tashi. Haka dai aka cigaba da lallabawa Zaid kam tuni yakoma gombe yabar anty maamy wanda hakan gaskiya bai yiwa Hanan dadiba domin bata son zaman anty maamy atare dasu bawai dan kasancewar ta bazawara ba a'a sai dan zata rusa mata target dinta,zata bata mata plan dinta,ahalin yanzu ita babban burinta shine ta yanda zata ja mijinta ajiki su shirya yasaki jiki da ita suyi rayuwa irin ta ko wanne ma'aurata shiyasa zaman anty maamy atare dasu kamar karan tsaye ne agareta, gashi kullum suna tare da Khalil idan har yana gida sai dai idan baya nan amma idan yana gida zaka samesu zaune shida maamy suna hira har abinci maamy ke zubo musu tare amma kowa da flate dinsa hakan ba karamin bawa Hanan haushi yake ba,
Yau ma suna zaune a falonshi misalin karfe 10 na dare sai hira suke yi da maamy hirar sharrin da yesmin tayi masa yana bata labarin irin yanda kotu ta wankeshi dan ankusa kawo karshen k'arar,
Dariya maamy tayi sannan cikin tsokana tace,
"To kai ka aureta mana....". Dan rausayar da kai yayi yana wasa da wayar hannunshi,
"Nida ke waye yafi dacewa yayi aure yanzu? Ke yakamata kiyi aure ai maamy"
Dan murmushi mai ban sha'awa tayi sannan ta kalleshi,
"Aure fa kace Khalil..... Hmmm aiki jaa"
"Ba wani aiki ja,kawai acikin zawarawan nan naki ki bawa wani dama,in bahaka ba ni sai infito"
Dariya maamy tayi harda rike ciki,
"To dama dama kai din..... Zaka iya fitowa"
Duk da awasa suka yi maganar sai kuma sannu ahankali take shirin fara zama babba, Hanan bata da masaniyar hakan amma jikinta yana bata kamar akwai wani abu tsakaninsu,
Shi Khalil rabonshi da soyayya ko wani abu mai kama da haka tun Ramlat tana raye,wata kulawa ta musamman maamy ke bashi ko office yafita tana dan yawan kiranshi awaya suna hira tayi masa fatan alkhairi kuma idanma basu samu damar yin wayar ba to tana tura masa da text message idan kuma yadawo gida zasu kasance tare suna hira amma aboye kamar soyayya suke yi saboda dama tun asali tun kuruciya maamy budurwarsa ce itace budurwarsa tafarko a tarihin rayuwarsa irin saurayi da budurwar nan na wasa dan ko abu yaci sai ya rage mata, Khalid kuwa bai isa ya tabata agabanshi ba dan baya mantawa sunsha kai ruwa rana akan hakan sunsha dambe da Khalid akanta idan ya mareta ko ya daketa to lokacin da yake da wuri ake yiwa yara mata aure shiyasa aka aurar da ita dan shi lokacin bai isa aureba kuma iyaye ma basu san sunayi ba amma da ansani ta yuyu asamu mafita lokacin,
Tuna hakan da yayi sai yaga ai gara kawai ya komawa maamy domin dama can akwai tsohuwar soyayya kuma ita ba karamar yarinya bace bare suyi ta samun sabani,da hankalinta tasan menene aure kuma ta san yanda zata zauna dashi da irin kulawar da yadace tabashi,dari bisa dari yaji zuciyarshi ta gamsu da hakan,bai fito fili ya fadawa maamy abinda ke cikin ranshi ba itama haka amma dai suna dan nunawa juna alamu ko kunyar fitowa su sanarwa da junansu sirrin zuciyoyin nasu suke yi oho. Hanan gaba daya ta susuce ta sake tsangwamar kanta sai kara lalacewa take yi dayake ita budurwa ba kamar bazawara ba ai wayon ma ba daya bane haka sanin sharruda da ka'idojin auren ma duk ba daya bane,ita abinda ke sake daga mata hankali shine irin yanda Khalil da maamy suka dinke har wani fita suke yi tare,idan zaije office tace zata bishi akwai inda zasu sauketa tace zataje saloon abubuwa dai iri iri,gaba daya hanan bata da kwanciyar hankali,
Yauma asama ta samesu falonshi suna hira da system akan cinyarshi maamy na zaune kujerar dab dashi irin zaman masoya dinnan,wani abune ya tokare kirjin Hanan rufe idonta tayi taje ta zauna akan kujerar da yake zaune akai ya tankwashe kafarshi daya akan kujerar dayar kuma tana kasa,sanye yake da fararen kananan kaya jeans da t shirt fuskarshi tasha kyau kamar ya shafa mai da powder,
Bata taba sanin cewa zata iya haka ba sai yau saboda Khalil din kwarjini yake yimata dari dari take yi dashi,bata taba attempting zama kusa dashi irin wannan ba sai yau,zama tayi gefen shi gata gashi jikinsu na gogar juna hannunta kan tafin kafarshi dake lankwashe amma wannan bata saniba ta zaci jikin kujerar ne,
Juyawa yayi shima ya kalleta da mamaki acikin ransa, idanuwanshi kuma na nuna neman Karin bayani tunda watakila da abinda tazo fada masa tunda har tayi irin wannan zaman,
"Uncle..... Banda lafiya"
Ta fada tana marerecewa saboda tana masifar jin haushin lankwasa murya da anty maamy keyi idan tana yimasa magana kuma bata son zaman nan da sukeyi tare akujeru makusantan juna,tunda ita matarsa ce ai game din tazo da sauki ita zata iya yimasa abinda ita maamy bata isa tayi ba idanma ta gwada yi to shari'a ce zata hau kanta,
Katse abinda yake yi yayi ya kalleta cikin sanyin muryar sa yace,
"Me ya sameki?"
Dan jimm tayi saboda ta rasa karyar da zata yi masa zuwa can ta tuno da datsewar da Aryan yayiwa dan yatsanta tun shekaran jiya ajikin kofar bathroom dinshi amma bawani sosai bane sai dai wurin ya kunbura kuma yaji ciwo,yatsan ta mika masa tana cewa,
"Ka gani.... Datsewa nayi jikin kofa"
Zai iya cewa this is the second time da ya taba riketa nafarko lokacin da glass ya fashe ya watsu ajikinta sai wannan na yanzu,jan dan yatsan yayi cikin sauri ta shige jikinsa domin wani irin azababben radadi taji kamar yatsan zai cire dan saida tayi nadamar nuna masa,yana kara ja tana sake shiga jikinsa dan har jefar masa da laptop tayi kasa, tsakaninta da Allah take yin kukan da take yi saboda zafi abunka da yan auta shagwababbu kuma sakalai LoL..... Maamy yi tayi kamar bata gansu ba,da yake akwai shekaru da kuma wayewa sai kawai ta mike fuskarta awashe tace,
"Khalil bari inje in kwanta kaina ciwo yake yi yau banyi baccin rana ba,see you tomorrow"
Yana rike da hannun Hanan wacce ke cukwikwiye ajikinsa ya kalli maamy,
"Yau da wuri haka? Alright Allah yabaki lafiya, Allah ya kaimu goben,saida safe"
Anty maamy bata kara cewa komai ba haka bata kallesu ba ta wuce ta fita,maida kallonsa yayi kan Hanan wacce ke sharbar kuka kamar yana kwakwale mata ido,
"Targade fa kika yi...."
Dago jajayen idanuwanta tayi ta kalleshi haba gaskiya mana taji ciwon yaki wucewa kuma bata iya amfani da yatsan,
"Gobe da safe zan fadawa nura ya samo miki mai gyara sai agyara...."
D'aga kai tayi amma takasa ko kwakkwaran motsi domin bata son matsawa daga jikinsa ji take inama zata tabbata ahaka,
"To dagani....." Taji yafada yana kokarin dauko system dinshi dake kasa,
Kunya ce taji ta lullube ta nan ta matsa tana rufe idanuwa da tafukan hannunta,duk da ba hira suke yi ba amma sai da takai 12 saura a wajensa sannan ta tashi ta tafi ta kwanta,kasa baccinma tayi dan haka ta kunna data ta shiga WhatsApp,sakon hajja hasinah tagani ta private tana tambayarta lafiya kuwa 2 days ta daina participating a group? Dan duk abinda za ayi da tana cikin sahun yan gaba gaba masu gwadawa da kuma bada himma amma yanzu shiru kamar bata nan,bata da kawaye na jiki ko aminiya wanda zata fada mata damuwarta anty salaha kuma idan ta fada mata fadane zata sha shi kamar babu gobe har ta goda Allah,anty badi'a kuma yanzu bata da waya a hannunta shiyasa ta yanke shawarar sanar da hajja hasinah watakila zata taimaka mata da shawarwarin da suka dace,nan tayi mata voice note ta tura mata ta zayyane mata matsalar da take tare da ita sannan ta kare maganar da fadin,
"Nikuma wallahi anty ina sonshi tun ranar da na fara ganinsa to kuma shi baya sona hankalinsa da tunaninsa na ga matacciyar matarsa,ga wannan anty maamy din tazo duk tana neman kankane min miji dan Allah kibani shawara"
Kashe data dinta tayi bayan tagama yiwa hajja hasinah bayanin komai,daga nan tayi addu'a ta kwanta.
Shi kuwa Khalil bayan yashiga bedroom zai kwanta da misalin karfe 1 miss called din maamy yagani,bai kiraba saboda yasan yanzu kila tayi bacci,kwanciya yayi ya lumshe idanuwansa,ya kamata kawai ya auri maamy domin rabonshi da wata ya mace shekaru kusan bakwai bayan kuma yana da cikakkiyar lafiya sannan sau da dama halin bukatuwar yana damunsa yana takura masa yana hanashi sakat gara kawai yayi auren ai arashin uwa akanyi uwar daki,insha Allah cikin kwanakin nan zai fasawa maamy sirrin dake ranshi.
Da asubah bayan Hanan ta idar da salla take ganin sakon hajja hasinah inda itama ta turo mata da voice note kuma har lokacin tana online,budewa tayi tafara saurara,
"Hanan naji sakonki kuma matsalar ki matsala ce babba kuma ba babba ba,tun farko sakacinki yajawo haka.... Ai baka sallama namiji musamman ma miji irin naki,maza da ake rikesu hannu bibbiyu gudun kada su zame, gaskiya kinyi kuskure babba amma akwai abubuwan da idan kinyi zaki iya gyarasu watakila amma fa dole sai kin dage,sai kuma kin mike tsaye kinyi iyakar iyawarki,yanzu da farko dole sai kin kula da abincin sa,sai kin kula da al'amuransa na yau da kullum sannan uwa uba shimfidarsa wanda wannan shine matakin karshe..... Ki fara sanin wanene ma shi tukunna? Me yafi so? Wadanne abinci yafi so? Me yafi burgeshi? Wacce irin hira ke sakashi nishadi?, Me yafi daukar hankalinsa? Wadannan sune assignment dinki ayanzu kuma sune zaki nemo dan ta nanne kadai zaki samu solution,dan haka ina yimiki fatan nasara dan daga yanzu dinnan zaki fara....."
Wata iska mai zafi hanan ta furzar sannan ta sauke ajiyar zuciya lallai kam wannan babban assignment aka bata mai chaja kwakwalwa da sata nazari gamida tunani,to yanzu ta ina yadace tafara..............................鉁嶐煆?
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:14 AM - Ummi Tandama: *41*
***Tafi mintuna goma zaune batare da tasan ta ina yadace tafara ba ganin wankin hula na shirin kaita tsakar dare yasata mikewa daga zaunen da take ta cire hijabin jikinta tafita tamkar kazar da kwai ya fashewa aciki, kitchen dinta da ke makare da kaya wanda musamman aka tanada dominta a matsayinta na matar gida tayiwa tsinke, to yanzu ita me zata dafa tunda takamaimai bata da masaniyar me yafi so yaci da safe? Amma dai wallahi hajja hasinah ta hadata da assignment me zafi,
Tana nan tsaye harabar kitchen din tana tunanin me yadace dabara ta fado mata,gwara kawai tayi abincin kala biyu daya na gargajiya daya kuma na zamani inyaso duk wanda taga yaci to shi yafi so,
Hakan kuwa tayi nan ta zage ta soma girkinta cikin jin dadi da farin ciki domin girki yana daya daga cikin abubuwan da ke sakata nishadi a lokacin da take gabatar dashi,wainar semovita tayi za aci da suga kuma abarta tayi kyau kamar ta shinkafa tayi laushi libis sai kunun gyada da ta dama haka kuma ta soya dankali da sos wadda taji kwai nasha nasha,
Agaugauce ta je ta shirya Aryan bayan tagama aikin danma dai ba wani mai yawa tayiba shiyasa bai dauki dogon lokaci ba,tana gama shirya Aryan ta kamo hannunshi suka sauko kasa wanda tuni kuku yajima da shirya table, breakfast ta bashi yaci sannan ta shirya masa lunch box dinsa yatafi,yana tafiya takoma sama ta shiga wanka shima bata zauna tajima acikiba tayi tafito aranta tana jinjina kokarin iyaye mata musamman wadanda suka tara 'yaya ko kuma haihuwar tayi musu sammako,ka kula da yara sannan ka kula da ubansu kai gaskiya isn't easy,shiryawa tayi batare da bata lokaci ba cikin orange colour din atamfa mai bala'in kyau,dinkin fitted ne shiyasa yayi mata tsantsam ajikinta,bata yi wani dogon lissafi ba wurin kalmasa dan kwalinta ba kawai dan cokara shi tayi tafita kuma hakan sai yabada style mai kyau,
Yau kam ta shirya baiwa Khalil surprise dan duk abubuwan da ta dafa kwasarsu tayi ta kai sashensa ta jejjera bisa table din cin abinci sannan ta nemi wuri ta zauna nan cikin falon, agogon hannunta ta kalla bayan ta zauna karfe 8 saura mintuna biyar,kai amma gaskiya tayi kokari kuma aikin nata ma yayi sauri sosai,yau kam sai dai anty maamy tazo ta isketa duk sammakonta ehe.
Bata jima zaune afalon ba taji alamun bude kofa, kamshinsa ne yafara sanar da ita fitowarshi kafin shi din ya bayyana,sanye yake cikin farin yadi na maza dandakeke mai mutukar kyau mai laushi shara shara, yana tafe yana kokarin balle hannun rigarshi,mamaki yaji ya kamashi kwarai da gaske sakamakon ganinta da yayi zaune cikin falon,mikewa tsaye tayi daga zaunen da take alamar girmamawa,
Da idonsa yake neman karin bayanin ganinta da yayi a daidai wannan lokaci,kasa tayi da kanta ta dan duka ta gaisheshi,
"Ina kwana?"
"Lafiya lau..."
Ya amsa mata idanuwanshi na kaiwa kan dining, warmers yagani jere akai da sauran kayan karin kumallo,agogon hannunshi ya kalla sannan ya dan yi guntun tsakin da bata san dalilinsa ba,
"Waye ya kawo wancan abincin?" Ya bukata batare da ya kalleta ba domin hankalinsa na kan wayar dake hannunsa,
"Nice....." Ta bashi amsa cike da kwarin gwiwa domin ta dauri aniyar canja komai a tsakaninsu,
Bai kara magana ba ya nufi saman kujera ya zauna yana ta danne dannen waya da alama wani yake nema amma wayar taki shiga dan sai dan guntun tsaki yake ta ja yana kara wayar a kunnensa,zuwa caan taji yafara magana fada fada,
"Wai ina kaje ne inata kiran wayarka tun asubah amma taki shiga?........ Kana jina...... Ya isa...... Yanzu yanzun nan katashi kaje store ka dauki abinci ka kai gidan yaran nan........ Abincinsu yakare tun jiya....... Kawai ka wani kashe waya tun 11 ana ta nemanka wayarka akashe........ Ka tashi yanzu kaje karka bata min lokaci...."
Daga haka ya cire wayar daga kunnenshi yana jin kamar an dauke masa wani nauyi dake kansa, haba har ya dan ji sanyi amma ace anbar yara marayu babu abinci ai akwai matsala,ita dai hanan ba gane kan zancen nashi tayi ba saboda bata san da wanda yake wayar ba kuma bata san akan wanene ba,
Ta glass ta hango anty maamy na tahowa hannunta rike da karamin flask din coffee zata kawowa Khalil mikewa tsamm Hanan tayi ta koma kusa dashi aranta tana cewa ai kuwa yau sai dai ayi wacce za ayi amma Khalil bazai sha wannan coffee dinba breakfast din da ta kawo masa zai ci,
"Ga breakfast din can kar ya huce......." Ta fada cikin marereta, baice komai ba kuma bai tashi ba yaci gaba da danne dannen wayarshi, falon shiru baka jin sautin komai sai kukan dawisu dake tashi daga bayan dakin baccinsa,ahaka anty maamy tashigo nan Hanan ta dan sake matsawa dab dashi wanda har sai da hakan yaso batawa anty maamy rai,
Fuskarta babu yabo babu fallasa ta karasa cikin falon tana dan basarwa,sanye take da doguwar riga ta material multi colour rigar mai burmemen hannu ta yafa siririn bakin mayafi akanta, karasawa tayi ta zauna kujerar gefensu,
"Ibrahim har kafito kenan....."
Daga ido yayi ya kalleta,
"Maamy..... Kin tashi lafiya.... Wallahi nafito..... Zanje kwara state ne"
"Allah ya kiyaye hanya...."
Ajiye masa flask din tayi agabansa,
"Ga coffee din..."
"Ok thank you.... Sai dai ma nafita dashi office nasha acan"
Hanan na jinsu batace ko uffan ba kuma da yake yau yan rashin kirkin na kusa ko gaida anty maamy bata yiba sai wani daddauke kai take yi ita ala dole ankula mijinta,
"Me da me aka kawo kan table din can?" Taji Khalil yana tambayar ta,wata irin mikewa tayi babu zato yaji ta kamo hannunsa mai tsananin taushi,
"Uncle kazo ka gani mana....... Kai fa na dafawa"
Ba Khalil ba ita kanta anty maamy saida taji mamakin wannan lamari,jingina tayi jikin kujera yanda zata cigaba da kallon scene din da kyau,
Duk da baya wani sakar mata fuska mikewa yayi yabi bayanta zuwa kan dining din wanda har lokacin tana rike da hannunshi,wani irin shock take ji kamar anjona mata electric amma ta kasa sakinsa har sai da ya zauna saman table din,
Tea yace ta hada masa rabin cup amma ganin kunun gyadar da tayi sai yace tabar tea din ta zuba masa kunun,da kunun da waina ta saka masa yaci sai wani kwarkwasa take yi wanda hakan ke baiwa anty maamy dariya, lallai yaro yaro ne,yaran yanzu akwai rawar kai da feleke ita ala dole mai miji sai wani karairaya take yi mijin da ba ma lallai ta burgeshi ba,mikewa tsaye anty maamy tayi domin ta gaji da kallon dramar tasu,
"Ibrahim bari naje na kwanta.... Zamuyi waya anjima"
"Ok mammy thank you"
Fita tayi Hanan tabita da harara aranta tana cewa ai wayar ma insha Allah baza ayita ba,shi kam har ga Allah yaji dadin waina da kunun da yasha haba amma ace kullum tea tea babu wani canji,mikewa yayi yawuce cikin bedroom dinshi tana ganin haka tayi wuff ta mike taje ta dauki flask din coffee din da anty maamy ta kawo taje ta tuttuleshi cikin sink din dake dinning area din,
Fitowa yayi tsaf cikin shirinsa na fita sai zuba kamshi yake yi,tsaye take hannuwanta abaya tana wasa dasu,
"Amm........ Am nace...... Maganar mai gyaran targaden da kace....."
Shiru ya dan yi na dan wani lokaci kafin ya daga ido ya kalli side din da take,
"Za aturo shi...."
"Nagode..... Adawo lafiya, Allah ya kiyaye hanya...."
"Amin,nagode" Ya fada a takaice sannan yawuce zai fita har yaje bakin kofa yajiyo,
"Yawwa bani wannan flask din wanda maamy ta kawo min coffee"
Dauka tayi ta nufeshi ta mika masa batare da ta nuna wata alama ba wacce zai sa ya zargi tana da masaniya akai,hannu yasa ya karba sai kuma yaji empty,dan jijjigawa yayi yana son ya tabbatar da abinda yaji nan kuwa yaji wayam babu komai,
"Ya najishi empty??" Ya fada ahankali amma kasancewar akusa take dashi taji abinda yace,
"To ko dai dama bata saka maka komai ciki ba?" Ita kanta ta san wannan tambayar da tayi masa ta rainin hankali ce, baice mata komai ba ya mika mata flask din yawuce yafita tana biye dashi abaya kamar wata bodyguard,sai da ta rakashi har kasa suka gaisa da umma barira sannan yafita,sai lokacin tajuya ta koma sama saboda dama bata son ya hadu da anty maamy ne a kasa shiyasa ta zame masa jela,
Falonshi ta gyara masa ta tsaftace shi tas amma bata yi garajen shigar masa cikin bedroom ba,sai dai amma abinda yakama tun daga kan falonshi zuwa bathroom din dake cikin falon da sauran lungu da sako dake harabar sashen nasa duk ta samu nasarar kalkalesu tsaf,
Bayan ta gama gyara nata sashen kasa ta sauka wurin umma wacce ke kishingide a d'akinta,anty maamy kuma na falo tana rike da novel na turanci tana karantawa, tsaki Hanan tayi aranta tace to ko me anty maamy din take jira da taki tafiya ta share daki ta zauna? Shifa Zaid kwata kwata ma kwananshi biyu ya tafi amma ita anty maamy taki tafiya koda yake ai gidan dan uwanta ne ta sake fadin hakan acikin ranta,dakin umma ta shiga bayan ta shigar musu da sauran kayan breakfast din da Khalil yarage,
Zama tayi suka fara cin wainar da ta yiwa Khalil itada umma,umma na sake kara mata haske akan irin kalolin girke girken da Khalil yafi so wanda shi yafi son abincin gargajiya dan bai ki ya yi breakfast da dumamen tuwo ba ko koko da kosai watikil wannan ne dalilin da yasa bai cika cin abinci ba yake zama da yunwa saboda su ma'aikatan gidan sunfi maida hankali wurin girke girken zamani,murna tayi sosai saboda jin wannan daddadan labari daga bakin umma.
Bayan mai gyaran targade yazo yayi mata sama ta koma ta shiga dakinta ta samu dan karamin littafinta da biro ta soma tsara jaddawalin girke girken da zata rinka yi asati duk na gargajiya amma zata dan rinka hadawa da na zamani shima ba wani mai yawa ba,bayan tagama kwanciyar ta tayi ta huta har azahar tana kwance,bayan ta idar da salla sai maganar anty maamy ta fado mata wacce tayiwa Khalil da safe wai sai sunyi waya,
Wayarta ta jawo ta shiga ta tura masa massage tunda dai ita bazata iya kiranba domin koda ta kirashi bata san abinda zata ce masa ba.
Khalil na zaune tare da mukaddashin mai girma gwamnan jihar kwara sakon Hanan yashigo,
_Uncle ya hanya? Ya aiki? Allah yataimaka ya tsareka ya dawo mana dakai gida lafiya._
Mamaki da al'ajabi sakon Hanan suka bashi,to wannan yarinyar lafiyar ta kuwa? Domin daga jiya zuwa yau gaba daya ta sake canjawa fiye da da,sai kace ba itace ta rufe ido a kwanakin baya ta rinka yimasa ruwan tijara da rashin kunya ba,to yanzu kuma ko me ya canjata? Oho,
Reply ya tura mata kamar yanda yasaba da Thanks kawai sannan yaci gaba da harkokinsa.
Hanan kuwa sai la'asar ta shiga kitchen ta shirya lafiyayyen tuwon semovita dinta miyar ganye, sannan ta sake dama kunun gyada wanda yasha lemon tsami sai kamshi yake,
Bayan tagama Aryan taja suka tafi garden suka haye lilo nan suka shantake har magriba sannan suka shiga cikin gida,anty maamy ce kadai a falon kasa tana daddanna waya,ganin Aryan yasata kiransa ita kuma Hanan ta wuce sama bata bi ta kansu ba,salla tayi bayan ta idar ta yi zamanta a daki tana kallon wani kayataccen labari mai dogon zango na hausa,anan Aryan yazo ya sameta suka cigaba da kallon tare.
Misalin karfe 9 Khalil yashigo gidan,babu wanda yasan ma yadawo,wanka yafara yi,yafito yana shiryawa anty maamy ta kirashi,dauka yayi yana tsane jikinsa da dan karamin towel,
"Hello.... Ka shigo ne?"
"Hy mimimi......"
Murmushi anty maamy tayi ta shafi gashin kanta dake bude tana kwance saman gado,
"Kai baka rabo da tsokana Ibrahim,ka dawo dinne?"
"Ehh.... yanzun nan nashigo nayi wanka"
"Ok....to ya? Zamu je dinne?"
"Uhmm bari na shirya,bani 10 minutes"
"Ok"
Katse wayar yayi yaci gaba da shiryawa,mintuna kadan ya karasa shiryawa bama zaka taba ganewa shi bane sai dai idan kayi masa kyakkyawan sani,
Itama Anty maamy dan sake gyarawa tayi sannan ta fito,da motarshi sukayi amfani suka fita PA yana jansu yayinda su kuma suka kame agidan baya bodyguards dinshi na biye dasu,
Wani Park suka je kayatacce ma'abocin sanyi da sanya nutsuwa,zama sukayi suna fuskantar juna da wani dan table a tsakiyar su,
"Maamy...." Yakira sunanta cikin taushin murya,daga idonta tayi ta kalleshi fuskarta cike da annuri,
"Khalil...."
"Maamy bazan boye miki sirrin dake cikin zuciya ta ba..... Ni dake ina kyautata zaton duk abu iri daya muke ji agame da juna....."
Dan murmushi tayi sannan ta tallafi kumatunta da hannunta guda daya tana kallonsa,
"Amma wai me ya rabaki da uban yayanki? Saboda a iya sanina dake ke macece mai hakuri though dai zaman aure yana da banbanci da kowanne irin zama"
Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta dan lumshe idanuwanta ta budesu akansa,
"Khalil mahaifiyar shi ce ta rabamu,bata sona aduk shekarun da muka shafe tare da danta,ni babu abinda ya hadani da Bilal..... Mahaifiyar shi ce bata kaunata kuma ta sanadiyyar ta nabar gidan"
Jijjiga kai yayi sannan yayi murmushi mai dauke hankali,
"To insha Allah yanzu zaki samu uwar mijin da take ji dake take kaunarki kamar ranta...... Maamy shin zaki iya karasa sauran kwanakin da suka rage miki a duniya tare dani?"
Duk da tajima tana zargin jin wad'annan kalaman daga bakinsa amma bata tsammaci zata jisu da gardi da zaki irin haka ba,
Rufe fuskarta tayi da tafukan hannunta cikin farin ciki tana jin iska na kadata kamar tana yawo cikin gajimare,
"Woww........ Khalil..... Wadanne irin dadadan kalamai ne wadannan? Wow....."
Murmushi yayi ya dan kalleta bayan ya rausayar da kanshi gefe daya,
"To ko dai ban samu karbuwa bane?"
Murmushi tayi wanda har fararen hakoranta suka bayyana,
"Hmmmm..... Anya kuwa ban yimaka tsufa ba?"
Harararta yayi hararar dake cike da ma'anoni daban daban,
"Nawa kike da har zaki yimin tsufa,nine ma dai nake tunanin kamar zan iya yimiki tsufa"
Wannan karon dariya tayi sannan ta kalleshi,
"Kai ai har yanzu kamar yaro ne,ban san menene sirrin ba amma baka canjawa"
Murmushi yayi yana wasa da agogon hannunshi,
"Maamy kenan.... Ai kin fini kuruciya,wai dan Allah yaran nan waye zai zaci naki ne? Saifa wanda yasani"
Dariya tayi suka cigaba da koda juna daga bisani ya kalleta,
"Me kike so inbaki a matsayin sadaki...?"
Dan jimm tayi alamar tunani,zuwa can ta kalleshi,
"Ring..."
"Na gold ko na azurfa?"
"Diamond gold"
"Angama ranki yadade,kamar nan da yaushe kika shirya yin auren ne?"
"Ka bari zamuyi wannan maganar daga baya"
Misalin karfe 11 suka koma gida, Hanan tun 10 take jiran dawowarsa taci gayu cikin English wears riga da skirt,kamar wacce akace ta sauka kasa tana saukowa suna shigowa,tsayawa tayi tana kallonsu maamy sanye cikin bakar doguwar riga mai adon stones ja ajiki ta yafa jan mayafi marar nauyi,shi kuma Khalil kananan kaya ne ajikinsa jeans da riga long slif mai dogon hannu da p cap duk bakake,kafarsa sanye da bakin combos,sosai yayi kyau abunka da farin mutum cikin bakin Kaya............................鉁嶐煆?
_Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din._
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:14 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*
0 comments:
Post a Comment