Ɗahira ce tsaye gaban mirror ta buɗe locker ta ɗau ɗan siririn glass ɗin ta tasanya a idanuwan ta sannan ta juya ta ɗau jakan ta ta fice, Direct ɗakin Maman ta ta nufa, tana shiga ita kuma tana fitowa daga Toilet
Kallon ta tayi tace, "Ke har yanzu ashe baki tafi ba?"
Ɗahira tace, "Eh Mama ban gama shiryawa bane yanzu zan tafi".
Aunty Amarya tace, "to ki kula sosai abinda ya kai ki shi za kiyi, Allah ya tsare".
Murmushi Ɗahira tayi tace, "Ameen Mama na tafi bye".
Ta juya ta fice, a parlour ta tarar da Umma tana zaune
"Umma sai mun dawo".
Umma kallon ta tayi sannan tace, "to adawo lafiya".
Amsa mata kawai tayi ta fice cikin sauri, parcking space ta nufa ta buɗe motan ta da ta kasance ash colour ta shige tabar gidan
Mintuna 15 ya ɗauke ta kafin takai Babban Hospital ɗin wato *AL'AMEEN FAMILY HOSPITAL* tana shiga tayi parcking motan sannan ta ɗau jakan ta tare da rigan aikin ta tafito, rufe motan tayi kafin ta juya ta doshi cikin Asibitin cikin tafiyan ta na yanga, Lifter ta hau yakai ta hawa na uku kasancewar anan ne Office ɗin ta yake, ko wani Doctors akwai sunan sa agaban office ɗin sa, itama haka an saka Dr. Ɗahira Al'ameen Al'ameen, sai da ta kalli sunan nata tasaki kyakykyawar murmushin ta kafin ta buɗe tashiga ciki, ahankali ta taka har ta'isa kan kujera ta zauna tana ajiye jakan ta tare da rigan aikin ta, files ɗin da ta gani azube akan table ta soma buɗe wa tana dubawa, sai kuma ta miƙe tsaye da nufin fita taji anyi nocking
"Yes come in". Tafaɗa tana kallon ƙofan
Baffa ne ya shigo hannun sa riƙe da wasu files, murmushi suka sakarwa juna kafin ya'iso ciki ya zauna, itama ɗin komawa tayi ta zauna tana cewa
"yayana Barka da safiya".
"Yauwa my sweet sister, hope dai kina enjoyed aikin?"
Murmushi tasaki cike da farin ciki tace, "Yes sai dai ban fara ba zuwana kenan".
Shima murmushin yasaki cike da ƙaunarta a ran sa yace, "Ok ga wasu files ɗin; su ne waɗanda zaki duba anjima da ƙarfe 10:00am, waɗannan kuma na gaban ki na petiens ɗin ki ne Big Dady ya kawo miki, idan kin shirya sai muje in nuna miki Rooms ɗin da suke".
Ɗahira kallon sa tayi har alokacin da murmushi a face ɗin ta tace, "Tom muje".
Miƙewa yayi itama ta miƙe tana ɗaukan farar rigan aikin ta tasaka, sosai rigan yayi mata matuƙar kyau fiye da tunanin me karatu, eyeglasess ɗin ta tagyara tana me bin bayan sa
bayan sun fito atare suka jera suna tafiya suna hira sai zuba murmushi duk kan su suke yi.
⚫⚫⚫
. Buɗe ƙofan tayi ta shigo bayan da Shakira ta bata umarnin shigowa, ahankali ta ƙariso ciki tana karairaya cike da son burgewa ta samu waje ta zauna tana kallon Shakira da itama ta zuba mata idanu tana kallon ta, murmushi ne kwance a face ɗin ta tace
"Suna na Dr. Ayush Abdulkarim, Ni ce office ɗina ke kusa da naki kuma nima ɗin ina cikin wanda Hospital ɗin nan suka ɗauke ni aiki ranan Waliman ku, am.. shine nace bari na shigo mu gaisa".
Sai alokacin Shakira tasaki fuskarta tace, "ok Ni kuma Dr. Shakira Abubakar Al'ameen".
Murmushi Ayush tayi tace, "idan babu damuwa zan so mu zama Friends coz tun alokacin Walima naga kin burge ni".
"Why not". Shakira tafaɗa tana ɗage kafaɗa
"Thank you, bari inje zan sake dawowa idan na gama aiki".
Murmushi Shakira tayi mata tace, "ok babu damuwa".
Tashi Ayush tayi ta fice tana me rufo mata ƙofar, murmushi ta saki tana cije leɓe afili ta furta
"Da sannu Burina zai cika, da sannu mafarki na zai zama gaske, tabbas sai na cika burin zuciyata".
Juyawa tayi ta shige office ɗin ta dake kusa da na Shakira.
⚫⚫⚫
Ɗahira bayan ta gama duba petiens ɗin ta ne ta juyo ta nufi office ɗin ta, ta zo karya kwana kenan su kayi karo da wata matashiyar budurwa har files ɗin hannunta suka zube, cikin sauri atare suka ce
"Sorry".
Sai kuma su kayi murmushi sannan Ɗahira tariga ta cewa
"Kiyi haƙuri fa".
Budurwan me suna Safna tace, "no babu komi".
Sannan ta duƙa ta soma kwaso ma Ɗahira files ɗin, itama duƙawa tayi ta taya ta har suka gama kafin ta'amsa na hannun ta ta wuce
Bayan ta Safna tabi da kallo har ta ƙule sannan ta saki ajiyan zuciya tana murmusawa a ranta tace, "Tana da sauƙin kai ba kamar wancan bugaggiyar da mu kayi karo da ita ba".
Juyawa tayi taci gaba da tafiyan ta har ta'iso wajen lifter ta buɗe zata shiga, ji tayi an bangaje ta an shige, tana ɗago kai taga Yusra, a ran ta tana mamakin halinta, yanzu suka gama karo da ita ta balbale ta da tsiya but gashi yanzu ta buge ta bata ce mata tayi haƙuri ba. ɗauke kai kawai Safna tayi ta shige ciki tare da danna Number liftern ta rufe.
Yusra ta soma sauka kasancewar office ɗin ta a hawa na biyu yake sannan ita kuma Safna ta sake latsa number yakai ta ƙasa, wasu files taje ta'amso a reception sannan ta sake hawa ya maida ita block 4 inda anan ne office ɗin ta yake, tana ɗaya daga cikin waɗanda aka ɗauka sabbi.
⚫⚫⚫
Ƙarfe 01:00pm. Ta gama duba marasa lafiyan ta, miƙewa tayi ta shiga Toilet ɗin cikin office ɗinta ta ɗauro alwala ta fito, sallaya ta shimfiɗa ta gabatar da Sallah sannan ta miƙe ta ɗau duk abinda take buƙata ta zuba cikin jaka ta fito ta rufe office ɗin, lifter ta hau ya kaita upstairs na 5 inda anan ne office ɗin mahaifin ta yake, Direct office ɗin ta nufa tayi nocking aka bata iznin shiga, tura ƙofan tayi ta shige da sallama a laɓɓanta
Abbu ganin ƴar shi da yafi ƙauna cikin ƴaƴan shi a office ɗin sa yayi matuƙar saka shi farin ciki, cike da fara'a ya'amsa mata yana cewa, "Mama na".
Ɗahira da itama take faman doka murmushin ta ƙariso ta zauna tana cewa, "Abbu Barka da aiki".
"Yauwa Mama na ya naki aikin?"
"Alhmadulillah Abbu".
Abbu yace, "masha Allah haka ake so, har kin tashi kenan?"
"Eh Abbu, nazo ganin ka ne sai mu wuce tare".
Murmushi yayi yace, "Mamana kenan ai ban tashi ba, ina ga yanzu sai zuwa 04:00pm.".
Gyara zaman ta tayi tace, "to Abbu bari in jira ka sai mu tafi tare".
"A'a tashi kije gida ki huta Mamana ba na son ki zauna nan, kin ma ci abinci?"
"A'a Abbu".
Coolarn dake kan desk ɗinsa ya turo mata yace, "ɗauka ki ci".
Duk da ba ta jin yunwa bata yi masa musu ba ta ɗauka ta soma ci, kaɗan taci ta tsame hannun ta ta shiga Toilet ɗinsa ta wanko hannu ta dawo
Lokacin ne Abbu ya ɗago kai daga rubutun da yake yi yace, "Kin ƙoshi kenan?".
Gyaɗa masa kai tayi sai kuma tace, "Abbu ko ma ban ƙoshi ba idan na koma gidan zan sake ci ai".
"To shikenan Allah ya miki albarka ki kula kinji".
"To Abbu byee".
Ta ɗaga masa hannu sannan ta fice tana murmusa wa, tana fita haraban asibitin ta shige motan ta taja tayi gida, bayan tayi parcking ta fito ta nufi Part ɗin su, sai da ta soma shiga ɗakin Mamanta ta sanar mata dawowar ta sannan ta nufi ɗakin su, wanka ta soma yi ta shirya cikin wata koriyar atamfa ɗinkin Buba ta ɗaura ɗankwalin shi, eyeglasses ɗin ta tasanya ta fito ta nufi kichen, abinci ta ɗiba ɗan kaɗan ta fito parlour ta zauna tana ci, lokacin ne itama Fadila ta dawo
Ɗahira amsa mata sallaman ta kawai tayi taci gaba da cin abincin ta idanuwan ta na kan t.v, bayan ta gama ta tashi tamayar da plate ɗin kana ta wuce ɗakin Mamanta, tana tura ƙofan da sallama Aunty Amarya ta ɗago kanta daga karatun Hisnul Muslim da take yi, ta kalle ta tana amsa mata sallaman
"Mama bari inje wajen Kaka".
Gyaɗa mata kai kawai Maman tayi ta maida hankalin ta kan littafin ta, ita kuma Ɗahira ta fice.
[5/23, 8:53 AM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTORS*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* 🧝🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
```( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_
*NASIHA*
_Sallar natsatstsu ba ta samuwa sai an kare sallar daga duk wani abu mai shagaltar wa, a kuma yi ta cikin lokatai waɗanda ba su hana yin Sallah da zuciya ɗaya kuma ba su zama shamaki tsakanin zuciyar sa daga kome ban da tunanin Allah, sai Allah ya haskaka masa zuciyar sa, ya sami basira ya ji daɗin saduwa da Ubangiji. Daga nan sai ka ga Bawa kullum yana mayar da hankali sosai ga wanda yake ganawa da shi. Wannan ma ya fi ƙarfi cikin sujada domin kuwa Bawa ya fi kusa da mahaliccin sa lokacin da yake cikin wannan hali. Don more wa shi wannan muƙami an ji Manzon Allah yana cewa, "Bawa ya fi kusanta ga Ubangiji. Saboda haka ya yawaita addu'a."_
*EPISODE Nine*
Cikin siririyan muryan ta tayi sallama tana shiga ciki
Kaka dake zaune saman Wheel chair ɗin sa yana karatun jarida ya ɗago yana kallon ta, sannan ya'amsa mata sallaman yana cewa, "Maraba lale da matata abar ƙaunata, yau ga matata ta zo gare Ni".
Murmushi me burgewa Ɗahira ta saki tana takowa wajen sa ta zauna a gefen gadon sa tana cewa, "Kakus kenan baka rabo da tsokana ta, sai kace ka daɗe rabon da ka ganni".
Smile yayi yace, "Matata kenan ke baki san yanda nake ji dake bane, yau gaba ɗaya ba na jin daɗin rasa ki kusa dani, Allah da ba don kar in so kaina da yawa ba, da sai ince ki zauna a gida abinki ba sai kinyi aiki ba, tunda gani Mijin ki Ina son ki kusa dani".
Dariya sosai Ɗahira tayi kana tace, "Kaka kenan hmm Mijin kwali ko, don dai a kan ka dai bazan iya ajiye aiki na inzo in tare a wajen ka ba".
Zaro idanu yayi yace, "au kina nufin ban kai matsayin da zan iya auren ki bane na zama na ƙarfen?".
Sai kuma ya girgiza kansa yana dariya yace, "to bari kiji Ni ɗin Ni ne dai Mijin ki da zaki yi alfahari dashi nan gaba don babu wanda zai so ki fiye da yanda nake ƙaunar ki, har da wanda kike son min gori akan sa".
In ban da dariya babu abinda Ɗahira take tiƙawa, sosai Kaka yake ba ta dariya idan suna zancen nan, kuma sai ya fuske tamkar da gaske ne maganar tasa
"Hmm ci gaba da min dariya, ban da abinki ma ni fa taimakon ki zan yi, kin san Real Matata tafi ki komi baza ki haɗa kanki da ita ba".
Wannan karon murmushi tayi tace, "Kakus nawa Ni kaɗai, kaima ban da abun ka me zan yi da tsoho irin ka, idan har matarka ta fi ni komi ai nima Mijina ya fi ka komi, kuma idan kace ƙarya zan kawo maka shi ka ganshi".
Cike da jin daɗi Kakan yace, "yauwa Jabun Matata ki kawo min shi dama na daɗe ina burin ganin sa, kin ga sai a gwada aga wanda yafi kyau cikin mu, ke kaɗai ce dama ban san saurayin ki ba, amma kin ga su rasa kunya ɓeran tanka duk sun kawo min su na gani".
Numfashi Ɗahira taja tana kallon sa don ita bata san ma me zata ce mishi ba, ita da bata taɓa yin saurayi ba taya zata kawo masa wanda zata aura?
"You are silent my wife? I love to see who you will marry more than the other children. Burina kenan inga Mijin ki inga wanda zai iya riƙe min ƴar ƙwai na da amana". Kaka ya ƙarike maganar tasa yana kallon ta da alamun dagaske yake yi
Hannu ta saka ta dafa Wheel chair ɗin sa tana kallon sa, cikin murmushi tace, "to karka damu Kaka, idan ma tsoro kake ji karka mutu baka ga aure na ba ka kwantar da hankalin ka, zan roƙa maka Allah ya barka da ranka har zuwa ranan da zaka ga aure na, me kake ci na baka na zuba Tsoho na?"
Kaka dariya yayi yana jan hancin ta yace, "ja'ira kin ganki".
dariya tayi itama tana kai hannun ta kan hancin nata
"To ki nuna min shi ko a hoto ne mana".
Zaro idanu tayi tace, "kaiii Kaka is so expensive, wannan dalilin ya saka na hana sa yin hoto kar ma wata ta mallaki hoton a rashin sani, don shi ɗin yafi ƙarfin ko wace mace idan ba Ni ba, but idan kana son in ɓurɓusa maka wani abu daga cikin labarin sa nima sai ka bani labari me daɗi ta yanda zanji daɗin baka labarin shi".
"To shikenan yanzu bari in Baki labarin Matata abar alfahari na".
Murmusawa Ɗahira tayi ta gyara zaman ta da kyau har da buga tagumi tace, "to ina ji bani nasha".
Sai da yayi dariya kafin yace, "to tashi ki buɗe drowern can ki ɗauko min jakan ciki, ga ɗan mukullin acikin locker".
Yayi mata nuni da Lockern dressing mirror
Ɗahira da har ta tashi tsaye tanufi wajen ta buɗe ta ɗauko keeys ta kawo masa, shi ya cire mata na drowern ta'amsa taje ta buɗe ta ɗauko masa jakan ta dawo
Zuge jakan yayi hotuna ne da yawa aciki, ya zaro ɗaya daga ciki ya nuna mata
"You see this".
Amsa tayi tana kallo, shi ne tare da Baby a manne da juna, ga duk kan alamu anyi hoton ne lokacin da ake party, murmusawa tayi tana shafa hoton ta ɗago kai tana kallon sa tace, "Wow Kaka gaskiya kun yi kyau sanda kuke Matasa".
Murmushi yayi yace, "ke ma kin faɗa ai, mun yi hoton nan ne lokacin da ake Dinnern bikin mu, hmm bazan taɓa manta wannan lokacin ba, Matata har yanzu na kasa manta ta har yanzu kuma ƙaunar ta na nan daram cikin raina batare da ko ɗigo ya fita ba duk da kuwa ba ta a raye, kin san kowa da irin ƙaddaran da Allah yake jarabtan bawan sa dashi, to Ni soyayyarta shine ƙaddara ta, na so ta matuƙa fiye da tunanin mutum, haka zalika taso Ni fiye da tunanin me tunani, Allah Sarki Baby".
Sai ya saki murmushi yana komar da hawayen idon sa
"I will never forget her in my life. har yanzu zanen halin ta na nan daram cikin raina".
Murmushi kawai Ɗahira take yi tana kallon Kakan nata, sai da ya dasa aya a maganar nasa sannan tace, "Grandpa tell me about the day you first met her".
Sai ko Kaka ya saki dariya me sauti, ga duk kan alamu ya tuna wani abu ne, cikin murmusawa yake cewa, , "This is the day I will never forget in my life, ranan da na haɗu da Babyna matata abar ƙauna ta, lokacin da naje Hospital ɗin da nake aiki, a bakin Hospital ɗin na kusa bige ta da motata, hakan ya saka ta tsorata har ta faɗi taji ciwo a hannu sannan kuma nayi mata asaran shinkafan da take siyarwa".
Ƙwalalo idanu Ɗahira tayi tace, "Kaakaa Talla?"
Dariya yayi yace, "eh Talla, ai talla naga take yi lokacin da muka fara haɗuwa, Hmm my Baby taga rayuwa duk da kasancewar ta ƴar gata don mahaifin ta me kuɗin gaske ne.."
"To amma Kaka ya akayi ta koma yin talla?" Ɗahira ta katse sa da tambayan nan
"Ƙaddara, ko ince canjin rayuwa".
"To Kaka ya kuka ƙare da ita kuma wani kalma ta soma shiga tsakanin ku? And kuma lokacin ne ka soma sonta?" ta sake tambayan sa cike da zumuɗi da son jin labarin
Murmushi Kaka yayi yana lumshe idanun sa, sai ya buɗe a kanta yace, "kalman da ta soma fitowa a baki na shine haƙuri na bata, sannan ne ta ɗago ta kalle ni, tabbas kallon farko da nayi mata na kamu da matsananciyar ƙaunar ta, kuma sai na nemi alfarman tabi ni inyi mata dressing hannun, da farko bata da ninyan bi na but mutanen da suka taru wajen ne suka saka ta taje, kalman da na soma ji a bakin ta har ta tafi sunan ta kaɗai ta faɗa min".
"Kaka kasan me?"
Girgiza mata kai yayi yana kallon ta
Murmushi tayi da ya bayyana ƙananun haƙoran ta tace, "abinda yake bani mamaki da burgewa yanda ka auri Mata har uku masu suna ɗaya, ko a Film da littafai ban taɓa ganin hakan ba, kuma har kayi rayuwa dasu alokaci ɗaya".
Shima murmushin yayi yace, "Allah kenan shi ya ƙaddara hakan, gashi ke kuma kin zo a ta huɗu".
She laughed and said, "Show me the other pictures, ka ga har yanzu bansan sauran matan naka ba ko a hoto ka ƙi ka nuna mana, wancan ƴar uwan taka da tayi aure a ƙauye kawai nasan zan iya tunawa, tunda nasan ta muna yara kafin ta rasu".
Jakan ya buɗe ya kuma zaro wani hoton ya miƙa mata
Hoton ta'amsa tana kallon matashiyar da aƙalla zata kai shekara 19 zuwa 20, fara ce sol kyakykyawar bafulatana, da sauri Ɗahira ta ɗago kai tana kallon Kaka tace, "Laa Kaka wlh wannan sak Big Dady, ba su da maraba kamar tayi kaki ta ajiye".
Murmushi yayi yace, "Matata ta farko kenan *UMMEE NAFEESA,* Mace ƴar aljanna me tsananin haƙuri, dattako da sanin ya kamata, bazan iya fasalta miki kyawawan halayyan ta ba, wannan hoton anyi sa ne gab da zata rasu, Ni na ɗauke ta a waya shine na ba da aka wanko min, Allah Sarki ta rasu da ƙuruciyarta, ta rasu lokacin da nake matuƙar buƙatar ta, ta rasu sanda ta gama naƙudan Noor (Big Dady) batare da ta ganshi ba ta koma ga Allah. Allah ya jiƙan ki da rahma Ummeeta". Kaka ya ƙarike maganar tasa yana share hawaye
Itama Ɗahira har sai da tayi nata hawayen sabida tausayi sannan tace, "ameen Kaka, may Allah have mercy on them all".
Amsan hoton yayi ya maida a jaka, yana shirin rufewa Ɗahira ta saka hannu ta zaro wasu hotunan biyu tana cewa, "Kaka ka bari mana ka gama min bayani, wannan kuma yaron me tsananin kama da kai wanene?"
Ta nuna masa hoton ɗan ƙaramin yaro dake wasa da kayan wasan da aka zube masa da yawa a gaban sa
"Yarona na farko kenan sunan sa Arif, Sunan Kakana yaci Khabeer, amma tun yana ƙarami ya rasu".
Ɗahira tace, "laa Kaka ashe ban da Big Dady dama kayi wani yaron? Wacece maman shi?"
Hoton hannun ta ya nuna mata
"Ga Maman shi nan cikin hoton nan".
Shafa hoton Ɗahira tayi da hannun ta tana murmushi, hoton KAKA ne da Ƙannin sa biyu Baseera da Ihsan sai kuma Nafeesa mahaifiyar Arif".
"Kaka kuna tsananin kama sosai duk kan ku kowa ya gan ku ya san ƴan uwan juna ne".
Murmushi kaɗai yayi ya miƙa hannu ya'amsa hoton sannan yace, "kawo in mayar zanyi sallah".
"So what about the story Kaka?"
"Ki bari duk sanda na sami lokaci zan tara ku gaba ɗaya in baku cikakken labarin aurena dasu".
"Yauwa Kakus ɗin mu, Allah yakai mu to".
Bayan ya zuba hotunan ya bata jakan ta mayar, ita ta tura sa har Toilet ta zuba masa ruwa yayi alwala sannan ta tafi part ɗin su bayan ta bar sa nan cikin ɗaki yana Sallah.
Tana zuwa Parlour'n su da Fadil taci karo yayi ɗai-ɗai yana kallo
"Yauwa Aunty Ɗahira kin bar wayan ki ana ta kira".
Bata ce komi ba ta wuce cikin ɗakin nasu, ƙarar zuban ruwa tajiyo a Toilet ta san Fadila ce, zama tayi ta ɗau wayan tana duba missed calls ɗin da akayi mata, Baffa ne ya kira ta, itama kiran sa tayi but be ɗauka ba, sai ta'ajiye wayan ta ɗau Novel ɗin da take karantawa *JARUMAI* ta gyara zamanta ta soma karanta wa kafin Fadila ta fito daga Toilet tayi alwala.
[5/23, 4:03 PM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTORS*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
```( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_
*EPISODE Ten*
*WASHE GARI*
BAFFA ne jingine jikin motar sa yana duba waya, yana sanye cikin ƙananan kaya kamar yanda ya saba waɗanda suka matse sa sosai, kansa da askin zamani da yayi masa kyau sosai, sai faman shaining yake yi alamun ya sha mayuka masu tsada
Shakira CE tafito cikin shirin ta, tana tafiya ɗai-ɗai kamar baza ta taka ƙasa ba, har ta wuce ta hangi Yayan nata tsaye wajen motan sa, sai ta juyo tana kallon sa taɗan ɗaga murya tace, "Yaya inzo mu tafi tare ne?"
Lokacin ne Baffa ya ɗago kansa yana kallon ta, sai da ta samu harara kafin yace, "Where is your car and I will take you?"
"Here's Yaya, wlh I don't feel good about my body that's why I don't like driving".
Gajeren tsaki ya ja yana ɗauke kai a kanta yace, "babu inda zan kai ki ki nemi drever".
Har ta buɗe baki da ninyan yin masa magiya sai taga yana kallon hanyan ƙofar shiga gidan yana sakin murmushi, itama juya kai tayi ta kalli wajen
Ɗahira ce ta fito sanye da Jan abaya me kwalliyan Flower's da stones a jiki, tayi Rolling da ɗankwalin Rigan, face ɗin ta sanye da ɗan siririn farin glasses 👓ɗin ta wanda ya ƙara wa Sky Green ɗin cikin idanuwan ta kyawu, tunda ta fito itama take murmushi tana taho wa cikin tafiyar ta na yanga tamkar zata karye
Tana isowa suka sakarwa juna murmushi me bayyana haƙora, sannan ya buɗe mata motan ta shiga, shima zagaya wa yayi ya shige yaja ya nufi Gate
Shakira dake tsaye kamar an dasa ta ta saki baki tana kallon motar har ta fice
"Cab ɗijam.. Kar dai ace hasashe na ya zama gaske? Uhmm idan ko haka ne tabbas akwai matsala, babu yanda za ayi na bar Yayana yaso wannan me kama da mujiyan.. ina sam".
Ƙwafa tayi tana nufan motan ta ta shige taja ta fice a gidan, ko a cikin motan tunanin yanda ta gansu yau ɗin ya tsaya mata arai, duk da ta san cewa babu wanda ya kai Ɗahira da Baffa shaƙuwa a gidan, amma kuma abinda take gani cikin idanun yayan ta yasa yau ta ɗaura zargi akan su.
Har tazo ta wuce motan su Baffa a hanya tana kallon motan ta mirror tana jan tsaki, tana kitstsima abubuwa aranta da yawa.
Su kuwa a cikin motan hira Baffa yake ta mata cike da tsananin ƙaunar ta, ji yake yi ba ya son ko kaɗan tafiyan da suke yi ya ƙare sabida shauƙin da yake ji, shiyasaka yake tafiya a hankali kamar bazai yi ba
Ɗahira kallon sa tayi tana dariyan labarin da yake bata tace, "Yaya don Allah ka bari haka kar cikina ya fashe".
Dariya shima yayi yana kallon ta cike da so yace, "ai Ni nafi son in gan ki kina Farin ciki ne shiyasa nake baki labarin, don haka Ni bazan Dena ba, bari ma in baki wani".
Murmushi tayi me ƙayatarwa cikin ɗauke kai akan sa tace, "to Yaya kabar ni haka dai zuwa anjima sai ka bani".
"Well, my dear Sister, it's over no matter what you want me to do."
Still Murmushi tayi idanun ta akan titi, sau da dama tana mamakin yanda Baffa yake nuna mata kulawa fiye da tunanin ta, kuma yake yin duk abinda take so yake barin duk abinda ba ta so, tasan cewa yayan nata me ƙaunar ta ne tun tana ƙarama don ba ya son ɓacin ranta.
Yana yin parcking a haraban asibitin ya fito ya zo ya buɗe mata yana nuna mata hanya da hannu, cike da murmushi a face ɗin sa yace, "Yauwa Gimbiya fito an kawo".
Sunan da ya kira ta dashi ya saka tayi dariya tana kallon sa cike da farin ciki, zuro ƙafafun ta waje tayi ta fito, sannan ya rufe suka jera sukayi ciki.
⚫⚫⚫
"I told you to come in at 08:00am o'clock. Me ya tsayar da ke?" Doc. Said yayi maganar yana juyawa cikin kujeran sa
Fari tayi da idanun ta sannan tace, "kai ma ban da abun ka ya Docta; kasan ba a raba mu da ɗan shafe-shafe na kwalliya, kuma ka ga 08:00am yayi wuri da yawa".
Murmushi ya saki yana sakar mata wani shu'umin kallo
"Uhmm Sulaima kenan! That's why I love you more sabida wannan kwalliyan naki, ko kaɗan baki wasa da jikin ki wajen kin ga kin fito kin burge kowa, wasu kuwa ko a jikin su be dame su ba". Yaƙarishe maganar da taɓe bakin sa
Dariya tayi tana sake lanƙwashe murya tace, "Ya Dacta kenan! Ni fa nasan da wacce kake yi, kuma kasan zan iya zuwa in faɗa mata".
Waro ido yayi yana dariya yace, "rufa min asiri don Allah karki haɗa ni da ita kin san halin ta, but yaushe Ni zaki bani dama ne wai? Na gaji da wannan kwane-kwanen da kike min".
Sulaima tace, "Ya Dacta Ni fa gaskiya ba na tunanin zan iya harka da kai, ko ka manta kai Mijin Yayata ce? Haba dai ka sauya tunani mana Ni gaskiya bazan iya ba". Taƙarike maganar a shagwaɓe
Lumshe idanu yayi yana sake kallon ta cike da tsananin sha'awar ta, sai da ya ɗago daga jikin kujeran ya ɗaura hannayen sa kan Deks ɗin sa sannan yace, "Sulaima kin san ni; na sanki, why kike son haramta min kan ki? karki manta fa ba wai na ce miki auren ki zan yi ba bare ki kawo wani zancen Ƴar uwan ki, Ni dai don Allah ki bani dama mu more rayuwan mu tare kin san bazan iya haƙura dake ba, kinga matsayin ki daban matsayin ƴar uwanki daban a waje na".
Murmushi tayi tana girgiza kanta cike da yauƙi tace, "ya Dacta let's change our talk, muyi abinda ya kawo ni ka ga ina da inda zan je".
Doc. Said yace, "to shikenan tunda kin fi son haka, amma ki sani ba wai na bar maganar bane kenan, yanzu ya aka yi kika bar ciki ya shiga jikin ki?"
"Hmm tsautsayi mana, wlh nayi mamaki da naje Hospital aka gwada Ni wai ciki ne dani, kuma duk wani matakan tsaron da na saba yi nayi but abun kamar almara".
Ɗage kafaɗa yayi yace, "any way muje ki hau gadon in duba ki mu gani, don Nima Ina da aiki yanzu a gaba na".
Tashi tayi tana cire gyalen jikin ta ta nufi wajen gadon, shima ya tashi ya bi bayan ta.
⚫⚫⚫
Zuwan ta Office ta tarar da patients ɗin ta suna jiran ta, yau bata zo akan lokaci ba hakan yasaka har suka rigata zuwa tunda ƙarfe 10:00am zata soma duba su, yanzu gashi har goma saura
Tana shiga ta saka rigan aikin ta sannan ta zauna taba su umarnin shigowa ɗaya bayan ɗaya tana duba su, tayi wajen awanni biyu tana faman duba su sannan ta gama ta tashi ta shiga Toilet tayi uzurin ta ta fito, wasu files ta ɗauka ta fita ta nufi rooms ɗin patients ɗin ta masu jinya
Tana shiga da gadon farko ta fara, taƙarisa da fara'an ta tana gaishe da matar dake jinyar wata burduwan yarinya, bayan sun gaisa cikin faram-faram sannan Ɗahira tace, "Mama har yanzu bata farka bane?"
Mama tace, "ta farka jiya da daddare, kuma Dacta ɗin da kika ce zata zo ta duba ta ita ta duba ta, ga ma takardan da tace, "in baki". Ta miƙo mata takardan
Ita kuma ta'amsa tana dubawa, sai da ta gama dubawa sannan ta kalli Maman tace, "Mama to ya jikin nata tana samun sauƙi ko?"
"Ai alhmadulillah Dacta ba kamar jiya da safe ba, ta samu sauƙi sosai".
Gyaɗa kai Ɗahira tayi tana rubutu cikin wani file, sai da ta gama ta matso kusa da yarinyan ta soma duba ta sannan ta ɗago tana kallon Maman tace, "Mama insha Allahu komi zai zo da sauƙi, idan ta farka sai ta soma amfani da ruwa me ɗumi ana mata tsarki, daga yau sai a soma mata amfani dashi ko yaushe insha Allahu komi zai zama normal".
"To Dacta mun gode ƙwarai Allah ya saka da alheri".
Murmushi Ɗahira tayi tace, "ameen Mama Babu komi ai, Allah Ubangiji ya bata lafiya".
Mama ta'amsa da "ameen" tana sake mata godiya
Daga nan Ɗahira gadon gaba ta wuce, itama Yarinya ce budurwa, wata shirgegiyar mata take jinyar ta, sai dai yarinyan bata kai wancan shekaru ba don baza ta fi 13yrs ba
Bayan sun gaisa da matar ta tambaye ta jikin yarinyan
Matar cike da sanyin murya kamar za tayi kuka tace, "Doctor babu sauƙi wlh yarinyan nan tana shan wahala sosai, tun jiya farkawar ta biyu, kuma duk idan ta farka a firgice take tashi tai ta ihu tana surutai".
Ɗahira da take bin yarinyan da kallo cike da tsananin tausayin ta ta juyo tana kallon Matar tace, "Mama ki kwantar da hankalin ki insha Allahu zan yi iya bakin ƙoƙari na wajen na ga ta samu lafiya, Allah zai saka mata duk wanda yayi mata wannan abun".
Share hawayen ta matar tayi tace, "ameen Dactor na gode ƙwarai".
Daga nan Ɗahira duba yarinyan ta soma yi, ta jima tana duba ta kafin ta saka mata ruwa tayi mata allura ta cikin ruwan sannan tayi mata sallama ta wuce
Sauran gadon ta nufa ta duba su su ma, sannan taje wasu Rooms ɗin, sai da ta gama ta koma Office ɗin ta.
Tana shiga taga Baffa zaune yana kallon ta yana sakar mata murmushi
Itama murmushin tayi masa ta shigo ta nufi wajen zaman ta ta zauna, cikin muryan ta na yanga take cewa, "Yaya na yaushe ka shigo?"
"I Come in right now, what's your job?"
"Alhmadulillah. How's yours?"
Murmushi yayi yana shafa suman kansa yace, "uhmm sai godiyar Allah my Sister amma babu daɗi".
Dariya Ɗahira tayi tana kallon sa tace, "kai kenan Yaya, kai da ka jima tsawon shekaru kana aiki kake faɗan haka ina ga Ni da jiya na soma? wlh Yaya da wahala sosai aikin nan duk na gaji". Taƙarike maganar ta tana lanƙwashewa ajikin kujeran
Baffa dariya yayi yace, "oh my dear sister ke dai kawai ki ce ke raguwa ce, amma daga fara aiki kice kin soma gajiya?".
Murmusawa kawai tayi tana ɗan lumshe idanuwan nata don tasan halin yayan nata tsokana yake ji, ita kuma ta gaji ko maganar ma daƙyar take amsa masa
Baffa da ya tsare ta da idanun sa yana sakin murmushi me ƙara masa kyau yace, "sis Naga da alamun kin gaji tashi muje muci abinci".
Shiru tayi tana ɗan tunani
Hakan ya saka Baffa yace, "Do you have a job?"
Girgiza masa kanta tayi tana miƙewa ta zare rigan aikin tace, "No let's go".
Tashi yayi shima cike da jindaɗi suka fito suka jera har wajen lifter, shiga suka yi yakai su downstairs, mota suka shiga suka bar cikin asibitin, babu nisa da Resturant ɗin da suka je.
_More Comments more post_🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️
[5/23, 9:05 PM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTORS*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
```( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_
*EPISODE Eleven*
Bayan sun shiga sun zauna ne Baffa ya tambaye ta abinda take so?
and she answered, "Everything she wants to eat".
And he ordered Jallof Rice da ferfesun Kayan ciki with some drinks
and they started eating.
Ɗahira ta kalle sa tana murmusawa tace, "How do you get used to coming to your GirlFriend's restaurant like this?"
Sosai Baffa yayi dariya yana kallon ta yace, "Why did you say that?"
"Uhmm only".
Murmushi yayi a wannan karon yace, "ke dai ki faɗa abinda ke zuciyar ki".
Maƙe kafaɗa tayi cike da yauƙin muryan ta tace, "Yaya Ni dai nasan kana min rowan ta ne shiyasa ma baka taɓa nuna min ita ba ko da a hoto ne, but nasan dai kuna fita irin wajen shaƙatawan nan".
Baffa kallon ta kawai yake yi cike da burgewa, ji yake yi aran sa tamkar yace, "ke ce macen da na taɓa so a *RAYUWATA,* sai kuma ya girgiza kansa still yana murmushi yace, "My sister kenan, idan har zaki yarda wlh ban taɓa yin budurwa ba".
Ƙwalalo idanu tayi tace, "kai Yaya dagaske kake yi ko wasa? How can it be said that Handsome Guy and you have no girlfriend? Ko dai yaya kana ɓoye min ne ba ka son na sani?".
Cikin ido yake kallon ta cike da wani irin salo
Hakan yasaka ta ɗauke kanta tana ci gaba da cin abincin ta cike da yanga da ya zamar mata jiki, komi nata hakan take yin sa
Huro iskan bakin sa yayi be ɗauke ido a kanta ba yace, "Da gaske ƙanwata ban taɓa budurwa ba wlh, akwai wacce nake matuƙar ƙauna sai dai har yanzu na kasa sanar mata".
Ɗago kai tayi tana kallon sa da mamaki kafin tace, "why?"
"Saboda kwarjinin ta.."
Dariyan ta ya saka shi yin shiru yana sake ƙure ta da idanun sa, sosai take dariya shi kuma yana bin ta da kallo cike da tsananin ƙaunar ta da burge shi da take yi
Sai da tayi son ranta sannan tace, "Yaya har akwai macen da zaka kasa sanar mata ƙaunar ka gare ta sabida kwarjini? Shin me tafi ka dashi ne? Kyau ko nasaba ko kuwa kuɗi? Ni na tabbata Yayana duk kwarjinin ta baza ta kai ka ba, kai dai kawai kace kana jin tsoron ta; abun kuma da ban san ka dashi ba".
Baffa yace, "baza ki gane bane Sister, duk abinda kika lissafo tana dasu, sai dai kamar yanda nace miki kwarjinin ta da cikan kamalan ta ya zarce duk tunanin namiji ya iya tunkarar ta da soyayya, a kullum idan nayi yunƙurin zuwa gare ta da soyayyata sai inga girman ta da kwarjinin ta bazai bari na sanar mata ba, yanda nake ji a gaban ta da bugawar zuciya da zaran nayi yunƙurin sanar mata sai in kasa, sau ba adadi nayi hakan amma na gaza".
Kallon Yayan nata kawai take yi cike da tausayin sa har yayi shiru, sannan ta ɗaura da cewa, "How can I help you find her love? Why don't you let me know who I am; and I promise to tell her, sannan kuma zan taya ka yaƙi har sai ta amince da kai, Yaya ban ga macen da zata ƙi son ka ba komin kyan ta komi kwarjinin ta kuwa, sai dai idan har baka faɗa mata ba, Yaya ka cire tsoro ko fargaba ka sanar mata don Allah".
Murmushi yayi yace, "na gode ƙanwata, haƙiƙa nasan kina son farin ciki na, sai dai bazan iya faɗa miki ko ita ɗin wace ce ba, but I promise I will try to tell her."
Murmushi tayi kawai ba tare da tayi tunanin matsa masa akan sanin meyasaka be son sanar mata ba? Ita a komi nata tana ma mutum uzuri maybe yana da dalilin hakan ne
"To yaya na gane, but hurry up and tell her because soon Kaka will start talking about your marriage, kuma ka ga idan baka sanar mata ba za'ayi babu kai haka zakai ta zama a Gwauron ka".
Baffa laughed and said, "Well shikenan my sister, but ni nafi son nayi aure lokacin da kema za kiyi".
Zaro idanu tayi tace, "Yaya baka shirya auren ba kenan? Because I don't have a real boyfriend."
"Hmm you're just saying, duk da ban taɓa ganin kin kawo kowa gida ba amma fa ina da tabbacin kina da masoyi don kuwa irin ki ba su rasa masoya".
Shiru kawai tayi a wannan karon tana murmusawa, sai kuma ta duƙar da kanta tana ci gaba da juya spoon ɗin hannun ta cikin abincin
"Talk to us My dear, when will you show me my son-in-law?"
Ɗago kai tayi tana kallon sa tace, "Yaya Ni bani da gwani har yanzu, amma dai ka taya ni da addu'a".
Sanyi yaji cikin ransa, cike da nuna tausayawan sa a fuska yace, "My dear Sister, I promise to help you. I pray to God to bless a good husband who loves you so much, kuma Allah yasa nan kusa za kiyi aure baza kiyi nesa damu ba".
Dariya tayi cike da farin ciki tace, "kamar ka sani Yayana ko kaɗan ba na Son auren nesa sabida ba na Son nayi nesa da ku, sannan ba na son na dena aiki a hospital ɗin mu, Burina yana da nasaba da aiki cikin Hospital ɗin mu, ka ga kuwa ba na so na zama kamar Aunty Zulaiha da tabar aiki lokaci ƙanƙani, tayi nisa babu daman ci gaban ta a nan, nima ina so ayi alfahari dani cikin Family na; ya kasance ina ba da tawa gudunmawa wajen haɓɓaka shi".
Filled with her love Baffa said, "God fulfill your dream My dear sister".
"Ameen my brother, we should hurry back because my waking time is near, and I want to check on my patients."
"To sarkin aiki ba kya gajiya?"
Murmushi tayi kawai tana ɗaukan Holandia tana sha, bayan ta gama ta'ajiye tana kallon sa tace,"Come on, I'm full."
Ɓa ta fuska yayi yana kallon abincin gaban ta yace, "Baki ci da yawa ba ai?"
Marairaice fuskar ta tayi tace, "Yaya na ƙoshi ne".
"Ok to tashi muje nima na ƙoshi tunda kin ƙoshi".
Sai da ya biya kuɗin sannan suka fito suka shige cikin motan yaja suka nufi Hospital ɗin
Suna shiga haraban Hospital ɗin suka fito ya rufe motan suka jera suka nufin cikin asibitin
A reception Ɗahira ta hango aunty Zainab, tayi saurin zuwa wajen ta tana cewa, "Aunty Zainab".
Juyo wa Aunty Zainab tayi tana kallon ta sai ta faɗaɗa fara'an ta tana faɗin "a'a! my sister. I have been asking Fadila Ni kam ban ganki ba tunda kuka fara aiki".
Dariya Ɗahira tayi tana cewa, "wlh kuwa Aunty nayi ninyan zuwa har Office ɗin ki, to, aiki yayi yawa I don't have time."
Aunty Zainab kallon Baffa da ya ƙariso wajen su ya tsaya yana kallon su tayi tace, "oh ka ga masoya! ina kuma kuka je?"
Ɗahira kallon Baffa tayi suka haɗa idanu, sai ta saki dariya tana mayar da idanun ta kan Aunty Zainab tace, "aunty kenan abinci fa muka je ci da Yaya".
Smiling, Aunty Zainab said, "Hmm Na ga alam ai".
Baffa dake faman shafa kansa yace, "kin ji ABU da wata magana don mun fita da ƙanwata za kiyi mana fassara daban?".
Ɗan waro ido tayi tace, "wai laifi ne don nace masoya kaji min yara?"
Yanda tayi maganar yasa su dariya gaba ɗaya
Still Ɗahira na dariyan tace, "Where's Jinior?"
"Shigo wa ta kenan itama Fadila ta shigo shi ne ta'amshe shi".
Baffa kallon Ɗahira yayi yace, "mu je kin ji My sister Kar mu biye mata".
Hararan sa Aunty Zainab tayi tace, "to babu inda zata je.. kaje kai".
Shima hararan ta yayi yana cewa, "ke fa kina son raina ni fa, wai ba tare kika gan mu ba?"
"Eh tare na gan ku amma aiken ta zanyi".
Kafin yayi magana Ɗahira tayi saurin cewa, "Yaya ka je zan zo har Office ɗin ka".
Gyaɗa mata kai kawai yayi jin wayan sa na ringing, zaro wayan yayi cikin aljihu yana yin gaba abin sa bayan ya ɗaga mata hannu alamun ya tafi
"Hmm Ni dai ina mamakin wannan shaƙuwa na ku, anya.. anya.."?
Ƙwalalo idanun ta Ɗahira tayi tana kallon ta tace, "kai Aunty babu daman Yaya ya nuna wa ƙanwar sa kula wa sai da wani abun? Ni fa na ce miki abinci muka je ci".
"To ai nima ba fitar da kuka yi bane nake magana, mu je kawai". Aunty Zainab ɗin taƙarike maganar ta tana yin gaba
Ɗahira tabi bayan ta suna sauya hiran su
Office ɗin Aunty Zainab ɗin suka shiga, bayan sun zauna ta ɗauko mata wasu files ta miƙa mata
"Ga shi don Allah Ɗahira, ki kai wa Dr. Said don ba na son ya sake damu na".
Amsar files ɗin Ɗahira tayi tana kallon ta tace, "Aunty who is Dr. Said?"
"Aff baki san shi ba ashe, yana nan office ɗin sa na kallon nan wajen ta hannun dama".
"Ok sai na sake zuwa kenan Aunty?" Tafaɗa tana miƙewa tsaye
Murmushi Aunty Zainab tayi tace, "Tom My Sister, ki gaishe dasu Kakus me ran ƙarfe".
Dariya tayi tace, "insha Allah zai ji".
Daga haka ta fice bayan sun sake sallama.
Tana fita kamar yanda Aunty Zainab tace mata hakan tayi ta nufi hannun daman ta, tana zuwa ta soma dudduba sunayen Offices ɗin, nan kuwa taci karo da sunan sa a saman nashi Office ɗin, Nocking ta soma yi
Dr. Said dake zaune yana ma wata budurwa bayani yayi saurin ɗago kansa cike da fargaba, kallon Budurwan yayi yace, "Yi maza ki kwashe magungunan nan ki saka a jaka".
Babu musu kuwa ta kwashe ta zuba a jakan ta
Shi kuma ya gyara zaman sa yana rufe Files ɗin dake gaban sa tare da kifa wa sannan ya ba da umarnin shigowa
Turo ƙofan Ɗahira tayi da sallama ta shigo
Idanun sa ƙyar a kan ta ya'amsa mata sallaman yana kallon ta, duk da be santa ba amma ya ga tana masa kama da Familyn Dr. Al'ameen
Ita kuwa ƙariso wa wajen Table ɗin sa tayi ta miƙa masa files ɗin tace, "ga shi Aunty Zainab ta ce in kawo maka".
Sai a lokacin ya ɗan saki fuskar sa yana bin ta da wani irin kallo, cike da murmushi a face ɗin sa ya miƙa hannu ya'amsa yace, "Ok thanks".
Juya wa kawai tayi ta fice ba tare da ta kalli ko budurwan dake zaune ba
Har ta fice yana kallon ta cike da tsananin burge sa da tayi, sosai Ɗahira ta ɗauke masa hankali da kyawun ta da cikan halittan ta, musamman ma da take siririyan mace, domin yana ƙaunar irin su. sai faman doka murmushi yake yi ya kasa ɗauke kai daga ƙofan da ta fice
Sai da budurwan nan ta buga table kafin ya dawo hayyacin sa
Ɗan shafa kan sa yayi yana kallon ta kafin yace, "kin tabbatar cikin nan be wuce 5 Months ba?"
Kallon sa tayi a yatsine kafin tace, "Dr. Na rigada na faɗa maka wata 4 ne".
"Ok bari in zo".
Miƙe wa yayi ya nufi wani dogon sip ya buɗe, ya soma bincika kayan aikin da zai yi mata amfani wajen cire mata cikin.
Wannan shi ne halayyan Dr. Said, yana cire wa ƴan mata ciki ba tare da sanin kowa a cikin a sibitin ba, domin doka ne idan har aka kama ka kana irin wannan cin amanar za'a kore ka, asibitin kwata-kwata basu yarda da aikata wannan zunubin ba.
⚫⚫⚫
Ɗahira sai da ta koma Office ɗin ta tayi sallah kafin taje ta ƙara duba patients ɗin ta, tana dawowa ta haɗa komi nata da abinda zata buƙata ta fito ta rufe office ɗin
Office ɗin Baffa dake hawa na biyu ta nufa, dai-dai zata shige cikin office ɗin Yusra ta fito nata office ɗin dake kallon na Baffa, kallon juna kawai su kayi suka ɗauke kai, Yusra har da wani sake tamke fuska ta wuce abin ta tana jan tsaki
Ɗahira juya kanta tayi tana kallon ta cike da mamakin ta, har yanzu ta rasa meyasaka Yusra take nuna mata tsana
Bata gama tunanin ta ba Baffa ya buɗe ƙofan yana kallon ta
Murmushi ta ƙirƙiro tana kallon sa tace, "Yayana na gama".
"Ok Muje Nima tafiya zan yi na gama na yau kuma".
0 comments:
Post a Comment