Ajiye handrayern tayi bayan ta gama ta soma shafa Lotions ajikin ta, tana gamawa tayi Light makeup a baby face ɗin ta, sai ta miƙe ta ciro kayan ta tasaka
Doguwar riga ce robber kalan ruwan hanta, babu kwalliya a rigan ko ɗaya sai dai wuyan V yake dashi wanda aka saka masa bakin less white colour, haka ma dogon hannun a ƙarshen an saka masa bakin less, Hula ta saka fari wanda ya kasance na rigan ne, tayi kyau sosai kasancewar ta kyakykyawar
Wayan ta kawai ta ɗauka ta fito Parlour.
Fadila na zaune tana cin abinci at the same time tana latsa wayan ta
She Sit on the One sitter next to Fadila on the Two sitter
Ɗan kallon ta kawai tayi sai ta ɗauke kanta ta mayar kan plasma t.v dake aiki babu me kallo, shiru tayi na ɗan wani lokaci sai kuma ta ɗago wayan ta ta soma latsawa
Da text ɗin da ya shigo wayan ta ɗazu ta fara cin karo, har zata wuce kuma sai ta ga kamar da number akayi mata Text ɗin wanda ada azaton ta MTN ne su kayi mata
Buɗe wa tayi da mamaki take kallon text ɗin, har sake murza idanuwan ta tayi tana sake ƙura manyan idanun nata, jikin ta na rawa ta soma karanta wa:
_"Aslm alaikum ya ke kyakykyawa abar so ga kowa, za kiyi mamakin ganin wannan text ɗin nawa aduk lokacin da ya riske ki, amma ba abun mamaki bane domin an ce me son ɗan tsuntsu shi ke bin sa da ji fa, Ɗahira na daɗe da ƙaunar ki cikin zuciya ta, sai dai har yanzu na kasa fitowa fili na sanar miki, ba don komai ba sai don ban san ya zaki amshe Ni a matsayin Masoyi ba, but know that I love you and I will continue to love you until my breath goes out, I Love You .. I love You with all my heart."_
_MASOYIN KI✍️_
Ta maimaita text ɗin ya fi sau biyar, gaba ɗaya ta ruɗe domin abin da bata taɓa gani bane a gare ta, tunda take babu wanda ya taɓa nuna yana son ta kuma babu wanda ya taɓa tura mata text da sunan masoyin ta, hakan ne ya saka ta shiga wannan ruɗun tare da bugawar zuciya me tsanani
Zumbur ta miƙe ta nufi ɗakin su
Fadila tabi bayan ta da kallo cike da mamakin sauyawan ta lokaci ɗaya, amma sai dai bata ce komi ba ta maida hankalin ta kan wayan ta.
Tana shiga ta nufi kan gadon ta ta zauna, sake ɗago wayan nata tayi ta sake karan ta text ɗin
"Anya wanda ya turo text ɗin nan ba mistake yayi ba?" Tafaɗa cikin sanyin murya tana bin wayan nata da kallo
Ƙure Numban tayi da idanu ko za ta san me irin shi but ko kaɗan bata taɓa ganin ma irin Numban ba, domin kuwa sabon Numban da MTN suka fito dashi ne me 091
Har ta latsa da ninyan kira taji ko wane ne sai kuma ta yanke da sauri don bata san me zata ce ɗin ba ko da an ɗauka, zuciyarta ta bata shawaran kar ta sake ta kira wataƙil mistake ne aka yi, kuma be kamata ta kira ɗin ba, da haka ta'ajiye wayan ta kwanta tana tsira wa waje ɗaya idanu cike da tunani
Da sauri kuma ta tashi zaune tana faɗin, "amma kuma ya kira suna na ai, Of course I am. This text is for me, but who is it?"
Duk yanda taso yin tunanin gano wanda zai iya mata amma ta kasa, koma wa tayi ta kwanta tana ajiyan zuciya.
⚫⚫⚫
Yana kwance saman kujeran sa yana faman latsa wayan sa yana murmushi
Wayan ce ta soma ringing hakan ya saka ya dakata da abinda yake yi yana kallon baƙuwar Numban da aka kira sa, shiru yayi na ɗan wani lokaci kafin yayi peacking call ɗin ya saka a kunne
Daga can ɓangaren muryan mace ce ta doki dodon kunnen sa
"Aslm alaikum".
"Wa'alaikis salam". Slowly he gets up and sits up
She smiled and said, "Do you know who Dr. Al'ameen Abubakar Al'ameen is?"
Baffa da yayi tsimi yana sauraron muryan ta sai be ce komi ba
Hakan ya bata damar ci gaba da faɗin, "My name is Dr. Ayush Abdulkarim and I work at your Family Hospital." Sai kuma tayi shiru tana tunanin abinda zata ce
Baffa yace, "to Allah yasa dai lafiya? But I don't know you."
She smiled and said, "Yes, you will never know me because I have just started working at the hospital, but idan har ka bani dama zan iya bayyana maka kai na domin mu san juna, tunda ina son alaƙar mu tayi nisa ne, that's why." so I asked for your number and I called you ".
Shiru yayi cike da mamakin ta
"To me zai sa ta so ƙulla alaƙa dashi?.."
Be gama guntun tunanin sa ba ta katse sa da faɗin, "I'll meet you tomorrow insha Allah, I'll come to your office. Byee Take care." Bata jira me zai ce ba ta kashe wayan
Shi kuma ya ciro wayan yana kallo, ya jima a haka yana tunani kafin ya'ajiye wayan ya miƙe ya shige toilet don ɗauro alwala.
⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫
Dariya suka kwashe dashi har da tafa wa
"Wow gaskiya kin yi ƙoƙari Ayush, amma kina ganin zaki iya jawo hankalin shi gare ki har ya manta da wancan shashashan?"
Murmushi me ma'anoni da dama Ayush ta saki tana kallon Shakira tace, "ke dai ki zuba idanu ki gani, da zaran mun haɗu ma zan sanar masa ina ƙaunar sa don ma ya sani tun yanzu".
Dariya Shakira tayi tace, "Thanks.. sai kuma mu jira muga shirin namu zai yi aiki ko kuwa.."
"Idan ma bazai yi ba sai mu sauya salo". Ayush tafaɗa itama tana dariyan
Jinjina kanta Shakira tayi cike da jindaɗi sannan tace, "Is it tomorrow when we meet?"
"Yeah insha Allah". Cewar Ayush tana ɗaukan jakan ta sannan ta buɗe murfin motan
Daga nan sallama su kayi ta fito cikin motan, ita kuma Shakira taja tabar ƙofar gidan su Ayush ɗin
Tana nan tsaye tana ɗaga mata hannu har ta ɓace ma ganin ta, murmushi ta saki tana faɗin, "Uhmm Dama ta biyu kenan, yanzu komi zai soma min daɗi, tabbas Buri na zai yi saurin cika, da wannan shirin naki Ni kuma zan cika tawa Burin".
Dariya tayi ta shige gidan su
Babban gida ne me sasa biyu, na farkon shi ne na mahaifin ta, inda akwai ɗakuna Huɗu da kichen a bakin ƙofan gidan; sai kuma bayi dake can ƙuryan sasan wanda aka rufe sa da fale-fale
Ƴaƴan Baban su su goma ne maza da mata kuma itace ta Biyar, sannan duk mahaifiyar su ɗaya.
Ɗayan sasan kuma Ƙanin Baban su ne ke zaune da matar sa, yaran sa shida shima maza da mata.
Ba wani kuɗi suke dashi ba amma suna da rufin asiri dai-dai gwargwado, mahaifin su yana ɗauke musu duk wani nauyi da ya rataya akan sa
A cikin ƴaƴan sa mata Ayush ce kaɗai tayi karatu me zurfi har matakin Doctoring, Wanda hakan shi ne burin ta, don tasan shine hanya ta farko da zata iya bi wajen cin ma babban burin ta, wato auren me kuɗi
Tun tana yarinya ta taso tana jin labarin Familyn Dr. Al'ameen Abubakar Khabeer Cindo, kuma sosai take jin labarin Hospital ɗin sa da ya shahara a faɗin Nigeria, wanda idan har za'a yi kwatance, to, da shi ake yi. Wannan dalilin ne ya saka ta ɗaukar ma kanta alƙawarin sai tayi aiki a cikin asibitin sabida ta nuna wa ƙawayen ta da ƴan uwanta tafi su
Zuwan ta asibitin da yanda taga tsaruwan Hospital ɗin tare da Familyn gaba ɗaya sai tayi sha'awar kasancewar ta cikin FAMILYN, burin ta a yanzu shi ne ko ta halin ƙaƙa ta shiga gidan itama ta zama ɗaya daga cikin familyn da su kayi Suna a faɗin Nageria; kuma suke ji da kuɗi da Izza
Binciken Farko da tayi shi ne sanin mutanen gidan, duk da bata samu labari sosai ga jama'an gidan ba amma ta gano Maza biyu ne kaɗai a cikin gidan kuma duk basu yi aure ba, ɗayan yana Aiki a ƙasar Turkey, ɗayan kuma yana aiki a Hospital ɗin su
Sai ta yanke shawaran fara shiga jikin ƴan gidan don samun damar kusanci gare su, abun kuma sai yazo mata da sauƙi office ɗin ta na kusa dana Ƙanwar Baffa ne wato Shakira, don haka ta nemi ƙawance da ita lokaci ɗaya kuma Shakira ta'amince.
A yau ɗin kuma sai ga Shakira ta zo mata da wani aiki akan jan hankalin Baffa ya faɗa tarkon ta duk a sabida a raba shi da Ɗahira, ba tare da Shakiran ta san da cewa Ayush ɗin dama tana neman hanyan da zata shiga jikin ɗaya daga cikin samarin gidan bane; don ta samu ta aure sa.
_plz kuyi *Vote* da Comments._
[5/24, 6:49 PM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTORS*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
```( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_
*EPISODE Thirteen*
Ahankali ta buɗe kyawawan idanun ta tana sake lumshewa cike da kasala, hannu biyu ta sanya ta riƙe kanta dake faman sara mata a hankali, tayi wajen mintuna biyar kafin ta soma yunƙurin tashi zaune tana jingina bayan ta da jikin gadon, sake lumshe idanun ta tayi tana soka hannu ƙasan pilon ta tazaro wayan ta ta kunna, sai da tasan ya gama kunnuwa kafin ta buɗe idanun ta tana kallon screan ɗin wayan, agogo ta duba taga ƙarfe 07:45am.
Ajiye wayan tayi tana sakin hamma kafin ta zuro ƙafafuwan ta ƙasa tana shirin sauka taji ƙarar shigowan text message, wayan ta ɗauka ta duba taga Numban jiya ne da aka yi mata Text dashi, da sauri ta buɗe jikin ta na rawa ta soma karanta wa
_ "Aslm alaikum Good morning Sweetie, I hope you are well? Take care of yourself God bless you then work" _
_MASOYIN KI✍️_
Jujjuya maganar take yi cikin ranta cike da tunani kala-kala, sosai take mamakin wannan mutumin da yake iƙirarin shi ɗin masoyin ta ne
"Ko dai ya San ni ne? But who is he? Why bazai fito fili ya nuna min kan sa ba?" Tafaɗa maganar a fili
Ajiye wayan tayi tana ninyan tashi sai kuma ta dawo ta zauna tana ɗaukan wayan tayi dialling Numban, Amma kuma a kashe yake
Shiru tayi tana riƙe da wayan a hannu, ta daɗe tana nan zaune tana faman tunani tare da son gano wanda ke mata wannan text ɗin, ganin zata ɓata lokacin ta tamiƙe ta shige Toilet, wanke bakin ta tayi ta fito ta ɗau ɗan ƙaramin Hijabin ta tasaka a saman kayan barcin ta masu taushi ta fice
Gaba ɗayan su suna zaune a dainning suna breakfast, Abbu ne kaɗai ya miƙe tsaye yana goge bakin sa da tissue alamun ya gama nashi breakfast ɗin
"Abbu Good morning". Tafaɗi hakan lokacin da ta'iso wajen tana kallon sa da murmushi
Shima murmushin yayi yana kallon ta ya'amsa mata cike da kulawa, sannan ya tambayi "Ya ya ta tashi?"
Ta'amsa mishi tana zama kan kujera kafin ta gaishe da Mahaifiyar ta da Umma
Abbu said, "Fadil, get up and let me drop you off."
"To Abbu". Cewar Fadil ɗin yana miƙewa ya nufi ɗakin Umma don ɗauko School Bag ɗin sa
Duk a dawo lafiya sukai ma Abbu ɗin kafin ya fice, Fadil shima ya fito ya bi bayan sa da sauri
Fadila ta soma tashi a cikin su ta nufi saman sofa ta zauna, daga baya kuma Umma da Aunty Amarya su ma suka tashi aka bar Ɗahira ita kaɗai tana karyawa
Bayan ta gama itama miƙewa tayi ta shiga ɗakin su, tana shiga ta cire kayan ta tashiga wanka, bata jima ba ta fito tana ɗaure da Showel a jikin ta
Ƙarisawa tayi ta ɗau wayan ta dake faman ruri, sai da ta zauna kan stool dake gaban mirror kafin ta'amsa call ɗin
"Aslm alaikum Yayana na kaina".
Sautin murmushin sa ne ya doki kunnen ta kafin yace, "Wa'alaikis salam My dear Sister, kin tashi lafiya?"
"Lafiya lau yaya, kaifa ya kake?"
"Alhmadulillah My dear, har kin fito?"
Girgiza kanta tayi kamar yana ganin ta kafin tace, "a'a Yaya yanzu dai zan shirya in fito".
Baffa yace, "ok Ni na rigada na fita tun 07:00am. Ina da Theater, but my sister ki je ɗaki na ki ɗauko min takardu dana manta ban ɗauka ba, suna nan akan drower na ajiye su".
"To Yaya amma ka kulle ɗakin ne?"
"Eh na kulle kiyi amfani da keey ɗin wajen ki".
Ɗahira tace, "to Yaya".
"Allah ya kawo min ke lafiya ki kula da tuƙi kin ji?"
Murmushi ta saki cike da jindaɗi kafin tace, "insha Allah Yaya bye".
Daga nan katse wayan yayi ita kuma ta'ajiye wayan ta soma shafe-shafen ta.
⚫⚫⚫
Yana sauke wayan a kunnen sa ya'ajiye saman table yaci gaba da aikin sa cikin Computer
Nocking yaji ana masa, be ɗago kai ba ya ba da umarnin shigo wa
Buɗe ƙofan tayi ta shigo da siririn sallama me haɗe da kisisina
Hakan ya saka ya ɗago kansa yana sauke idanun sa a kanta, sannan ne ya'amsa mata yana ci gaba da kallon ta
Murmushi tayi wanda ta san yana narkar da duk namijin da ya gani, cikin takun ta da son burge sa ta'iso wajen tana kallon sa still tana murmusawa tace, "Dr. Al'ameen Abubakar Al'ameen".
Baffa da ya sauke kansa ƙasa yaci gaba da aikin sa, jin ta kira sunan sa sai ya sake ɗago kansa yana kallon ta
Bata bari yayi magana ba tariga sa da cewa, "Can I sit down?"
Be ce mata komi ba illa nuna mata kujera da yayi da hannu
Zama tayi tana kallon sa cike da wani irin salo tace, "nasan baka gane Ni ba ko? I am Dr. Ayush Abdulkarim and I called you yesterday".
Sai a lokacin Baffa ya ɗan saki fuskar sa kafin yace, "Allah Sarki ai ban gane ki ba, amma fa bakin ki ya riƙe suna na da yawa".
Ayush cike da yanga tace, "ai ba baki na bane ya riƙe sunan ka ba, sunan ka ne ya zauna a baki na, daɗin sunan ka ke sakawa ba na gajiya da faɗin sunan ko da kuwa na so bari".
Murmushi kawai yayi yana kallon ta
Ita kuma sai ta gyara zaman ta da kyau tana sake kafe sa da idanu tare da son burge sa tace, "kayi haƙuri da kiran da nayi maka jiya amma zuciyata ce ta kasa haƙuri da son ƙulla alaƙa da kai, idan har baza ka damu ba zan so mu zama friends duk da kuwa nasan nayi maka katsalandan cikin rayuwa, amma gaskiya bazan ɓoye maka ba ka burge Ni ne sosai shiyasa nake son wata alaƙa me ƙarfi ta shiga tsakanin mu".
Numfashi Baffa ya sauke yana kawar da kansa kafin yace, "naji bayanan ki A'isha duk da kuwa Ni ɗin ba na abota da mata, sai dai bazan iya watsa miki ƙasa a idanu ba musamman yanda kika yabe Ni kuma kike son ƙulla alaƙa dani, babu damuwa". Yaƙarike maganar yana kallon ta
Murmushi tayi tace, "gaskiya kana da sauƙin kai ba kamar yanda nayi zato ba, naji daɗi da ka amshe Ni hannu bibbiyu Allah yasa hakan shi yafi alkhairi".
Baffa smiled and said, "ameen no worries".
Ayush miƙe wa tayi tana kallon sa tace, "Let me go and see you next time, friend?"
"Ok Thanks friend". Yayi maganar cikin kwaikwayon muryan ta
Sai suka yi dariya gaba ɗaya cike da nishaɗi
Ɗaga masa hannu tayi tana murmushi kafin ta juya ta nufi ƙofa ta buɗe
Dai-dai lokacin itama Ɗahira ta saka hannu za tayi Nocking
Ganin an buɗe ƙofan shiyasa ta janye hannun ta tana kallon Ayush da itama ta kafe ta da nata idanun tana ci gaba da murmushin ta
Kallon kallo sukai wa juna na ɗan sakonni kafin Ɗahira ta janye jikin ta a hanya don Ayush ɗin ta wuce
Fito wa Ayush tayi still tana kallon Ɗahira da ita kuma ta cire nata idanun akan ta tana gyara zaman Eyeglasess ɗin ta, sai kuma ta sake kallon ta har yanzu Ayush ɗin itama kallon ta take yi, hakan yasa Ɗahira ɗan sakar mata murmushi cikin sanyin muryan ta me daɗi tace
"Sannu ko".
"Yauwa sannu". Cewar Ayush itama tana faɗaɗa murmushin ta
Ɗahira bata sake cewa komi ba ta buɗe ƙofar ta shige tabar Ayush nan tsaye tana bin ta da kallo kamar t.v
Tana shiga ta sauke idanun ta kan Baffa da shima har yanzu yana murmushi be ci gaba da aikin ba
Yana ganin ta ya sake faɗaɗa murmushin sa yace, "welcome my dear Sister".
Murmusawa tayi kafin ta soma takowa ta'iso wajen; ta zauna a kan kujeran da Ayush ta tashi
"Dear Brother Welcome to work". Sai kuma ta'ajiye takardun hannun ta a saman table ɗin tana faɗin "ga shi Yaya".
Ɗauka yayi yana dubawa cike da jindaɗi ya sake kallon ta yace, "yauwa my dear wlh Sam na manta, kuma Abba ne yace na taho masa dasu ashe na barsu a gida, yanzu bari inje in Kai masa".
Ya miƙe tsaye riƙe da takardun a hannu
Itama miƙewan tayi tana gyara zaman jakar ta a kafaɗa tace, "nima bari in wuce sai anjima".
Za gayowa yayi suka jera suka nufi bakin ƙofan, shi ya buɗe ƙofan ya matsa mata ta wuce sannan shima yafita.
⚫⚫⚫
Kallon sa Hajja Fatu tayi cikin ƙasa-ƙasa da murya tace, "Dr. Zubairu idan har ka yi min aikin nan tabbas Ni da kai yanzu muka ƙulla, duk abinda kake so zan taimaka maka da shi, da kuma yarda na zaka ci gaba da shigo da kayan ka ba tare da ka sami wata matsala ba, Ni dai kawai fata na ka shiga jikin su sosai ta yanda zaka gano min duk wani sirri na cikin asibitin nan, kai Ni ban cire maka Mijina ba har shi ina so ka shiga jikin sa, idan har..."
Maganar nata ne ya maƙale sakamakon turo ƙofan da aka yi, idanuwan ta kamar za su faɗo ƙasa haka take bin ƙofan da kallo, ganin wacce ta shigo ɗin ne ya saka ta daka mata tsawa cikin fusata tace, "Are you going to come into my office without my permission?"
Cikin rawan murya Safna da ta ƙame a bakin ƙofan tace, "don Allah Dr. Kiyi haƙuri wlh nayi Nocking naji shiru shi ne na shigo".
Harara ta balla mata tace, "uban Nocking kika yi, kin yi Nocking ɗin ne zamu kasa ji? Shashashan yarinya kawai".
Safna saukar da kanta ƙasa tayi duk jikin ta rawa yake yi
Dogon tsaki Hajja Fatu tayi tace, "uban me ya kawo ki to?".
Da sauri Safna said, "These are the files that Dr. Abubakar told me to bring to you, in the Female ward to check on the Patiens brought in, and then one needs an emergency theatre".
Tsakin Hajja ta kuma ja kafin ta sake balla mata harara tace, "dalla bani ki ɓace anan".
Kamar dama jira take yi ta'iso da saurin ta tazuba files ɗin gaban ta ta juya ta fice da mugun sauri, tana fita ta sauke ajiyan zuciya cike da tsoro, sai da ta sake juya kanta ta kalli ƙofan kafin ta sake sauke wani ajiyan zuciyan, cikin ranta take cewa, "waii! wannan matar shegiyar mata ce wlh duk ta tsorata Ni da wannan uban tsawar nata, ko ma uban meye suke tattaunawa da ba ta so inji? Munafuka kawai".
Sai ta sake kallon ƙofan sannan kuma ta juya tayi gaba da sauri, Office ɗinta babu nisa da wajen tayi saurin shige wa.
Fadila da ta fito cikin office ɗin ta kusa dana Safnan; tana sanye da labcoat ɗin ta a jiki ta nufi office ɗin Hajja Fatu
Hajja Fatu wacce taci gaba da yin ma Dr. Zubairu bayani ta sake jin anyi Nocking, cak ta tsai da maganar ta tana kallon ƙofan
while shima Dr. Zubairun yabi sahun ta
Siririn tsaki taja tana ba da umarnin shigowa
Fadila opened the door and walked in
Ganin Fadila ce hankalin Hajja Fatu ya ɗan kwanta har da ƙirƙirar murmushi tana yafa ma fuskarta
Cikin miskilancin ta Fadila tace, "Hajja Drugs ɗin nan zaki bani".
Hajja bata ce komi ba ta buɗe drowan table ɗin ta ta ɗauko keeys ta miƙa mata tana faɗin, "Take" look at the Sif there and pick it up."
Amsa kawai Fadila tayi ta nufi wajen sif ɗin ta saka keey ɗin ta buɗe ta ciro wanda zata ɗauka ta rufe ta dawo mata da keeys ɗin, tana amsa ta juya ta fice
Ita kuma Hajja ajiyan zuciya ta sauke tana sake mayar da hankalin ta kan Dr. Zubairu da shima yake kallon ta
"Dr na rigada na gane duk abinda kike nufi, kar ki damu zan miki duk abin da kika ce, kin san dama ban da matsala da Dr. Noor tunda Aboki na ne, to sauran ma ba wahala bane tunda muna mutunci dasu, sai dai kuma gaskiya kafin nasan komi zan ja lokaci da yawa, sai dai mu riƙa bin komi a sannu a hankali".
Washe baki Hajja tayi tace, "Na san da haka Doctor, Ni dai fata na Buri na ya cika, Miji na ko kaɗan ba ya kyauta min matsalan nan duk daga wurin sa yake, idan da ya saka Ni cikin su ai da ba haka ba, amma koda yake.."
Sai kuma tayi shiru tana jan numfashi, cike da takaici tace, "Dr zuwa gobe insha Allahu zan san yanda za'ayi kayan ka su shiga ciki, baka da matsala da wannan".
Dariya yayi yace, "Na san haka Dr. Shiyasa tun farko na zaɓe ki, Allah dai ya cika mana burin mu gaba ɗaya".
"Ameen Doctor". Hajja Fatu tafaɗa tana murmusawa
Tashi yayi yace, "Let it be tomorrow,"
"Ok". tace dashi tana miƙe wa
Sallama suka sake yi kafin ya fice
Ita kuma Files ɗin da Safna ta kawo mata ta ɗauka a ran ta tana ƙorafin mijin nata, sam bata so kawo mata aikin nan da yayi ba tunda lokacin tashin ta yayi, tsaki taja ta ɗau abinda zata ɗauka ta fice.
[5/25, 7:57 AM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTORS*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
```( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_
*EPISODE Fourteen*
Sai da ta gama rubutun da take yi kafin ta ɗago kanta tana kallon matar dake zaune gaban table ɗinta ta cikin farin Glasses ɗin ta, murmushi ta sakar mata tana miƙa mata Peppern tace, "ga shi sai kije ki siyo magungunan ciki, za su rubuta miki yanda zaki riƙa sha".
Matar amsan Peppern tayi sannan tayi mata godiya tana miƙe wa ta fita
Wasu files guda biyu ta janyo ta buɗe na saman tana dubawa
Wayan ta dake ajiye saman Deks ɗin ta yayi ƙaran shigowar Text har sau biyu
Janye idanun ta akan file ɗin da take dubawa tayi ta mayar kan wayan nata, sai kuma ta saka hannu ta ɗauka ta soma buɗe saƙon, mutumin dai da ya soma tura mata text ne daga jiya zuwa yau, saƙon farko an rubuta
_"Aslm laikum I hope you have a good day my beauty? How works?" _
Ɗayan kuma da ta buɗe an rubuta
_"Abu ɗaya da bazai taɓa ƙare wa ba shi ne soyayyar mu da ke, sabida ke kaɗai ce a cikin zuciya ta, ina fata zaki amshe Ni hannu bibbiyu domin in fito fili in bayyana miki tsantsan ƙaunar da nake miki, wlh soyayya ta a gare ki gaskiya ce, ina ƙaunar ki fiye da yanda zan faɗa miki"._
_MASOYIN KI...✍️_
Ɗahira tayi tsawon mintuna goma bata sake wani motsi ba, zuciyar ta ta gaza ɗaukan waɗannan abubuwan dake faruwa da ita, tunani barkatai sun zo sun yi mata diran mikiya sun hana ta saƙat
Daga ƙarshe kiran layin tayi amma a kashe, ajiye wayan tayi ta miƙe tana gyara zaman Labcoat ɗin ta kafin ta ɗau wayan ta saka cikin aljihun Labcoat ɗin, ta kwashe files ɗin a hannu ta nufi ƙofa, fita tayi ta nufi ɗakunan da Patients ɗin ta suke ta soma bi tana duba su
Bayan ta gama ta dawo Office ɗin ta, cire Labcoat ɗin tayi ta rataye a Hanger kafin ta nufi cikin Toilet ta ɗauro alwala ta fito ta gabatar da sallan azahar
Bayan ta idar ta tattara komi nata ta fito ta rufe Office ɗin, ta hau lifter ya kai ta downstairs
Inda motan ta yake fake ta nufa cikin tafiyan ta kamar baza ta taka ƙasa ba, wayan ta na maƙale a kunnen ta suna waya da Baffa
Mota ta gani a bayan nata ta yanda babu yadda za'ayi ta wuce sai an ɗauke, kallon motan tayi, ta gane me shi, sai ta tsaya kawai tana waige-waige tana ci gaba da wayan ta, wajen mintuna 5 kafin su gama call ɗin ta nufi jikin motan ta tatsaya tana kallon hanya, ga rana sosai yana gasa ta
Tsaki taja tana buɗe motan ta shiga tabar ƙafafun ta a waje, shiru tayi tana jingina bayan ta a kujeran, idan zata ce ranta be ɓaci ba ƙarya tayi, tabbas Yusra ta soma shigan mata hanci da ƙudundune, me zai saka ta'ajiye mota a bayan nata tunda tasan koda yaushe zata iya fice wa? kuma ba wai babu sauran wajen parcking bane tsaban iskanci ne da neman magana
Kusan mintuna 20 da zaman ta, har ta gaji ta fito da ninyan zuwa har Office ɗin ta tayi mata magana, sai ta hango ta ta taho tana shirin buɗe motarta ta shige
Kallon ta kawai Ɗahira take yi kuma sarai tasan ta ganta, amma dayike ita ɗin ƴar wulaƙanci ne ta ɗauke kanta tana tamke fuska ta shige taja motar a guje tabar cikin asibitin
Numfashi Ɗahira ta sauke kafin itama ta shige cikin nata motan, tana ji a ranta idan har ta sake mata haka tabbas zata fuskanci fushin ta, ko kaɗan ba ta juran wulaƙanci shiyasa ba ta shiga harkan da ba nata ba
Motan taja itama ta fice cikin Hospital ɗin.
⚫⚫⚫
*ONE MONTH*
A cikin wannan watan abubuwa da dama sun faru.
Ɗahira ta dage sosai wajen aikin ta ko kaɗan ba ta wasa dashi, ta saka abun a ranta don haka sosai ta jajirce wajen taimaka wa Hospital ɗin nasu
A yanzu ta dena komawa gida har zuwa dare take kaiwa, aiki take yi tuƙuru wajen taimakon mara su lafiya
Da farko mahaifin ta yayi mata magana akan ta dena cika ma kanta aiki, tunda dama ita dutyn safe take yi zuwa rana
A cikin su huɗun ita da Shakira da Yusra dutyn safe suke yi, ita kuma Fadila na rana zuwa dare, sannan kuma akwai masu yin dare zuwa safe
Fadila fannin zuciya ne aikin ta, don haka bata cika samun patients ba a farko that's why take komawa gida idan bata da aiki, in ta zo ta duba patients ɗin ta sai ta koma gida
Koda Abbu yayi ma Ɗahira magana a kan ta dena cika ma kanta aiki, sai tace masa "ai zata iya," sannan tana yi ne don taimakon jama'a tunda babu abun da zata yi a gida gwara ta zauna ta taimaka
Hakan yayi musu daɗi sosai, musamman ma Kaka dasu Big dady, kullum saka mata albarka suke yi, sun tabbatar ita ɗin jajirtacciya ce aikin kawai ta saka a gaba
Yanzu ko kaɗan bata da lokacin da suke fita da Baffa sai dai jefi-jefi zai zo ya ɗauke ta su je restaurant su ci abinci
Baffa yanzu sosai suka shaƙu da Ayush don ko yaushe suna tare, a waya ne ko a gida, wasu idan suka gansu suna tunanin ko soyayya suke yi, sai dai shi kawai ya ɗauke ta a friend ne ko kaɗan ba ta ransa, Ɗahira ce har yanzu yake gani a matsayin Masoyiya
Itama ɗin Ɗahiran tana yawan ganin su da Ayush ɗin, sai dai bata taɓa mashi maganar ta ba
Yanzu masoyin ta na Ɓoye sosai kullum sai ya turo mata text ɗin nan, safe, rana da dare, idan ma be turo ba har ba ta jin daɗi, sosai yanzu take jin sa cikin ranta, kuma kullum sai tayi yunƙurin kiran layin amma a kashe, but bata taɓa tunanin itama ta tura masa text ba
Burin ta a yanzu tasan masoyin nata, sabida a yanzu zuciyar ta ta yarda dashi; soyayyar sa ne tsantsa a cikin ran ta.
*_________________________*
Yau ta kasance Sunday, kuma yau ne taron Familyn su kasancewar duk ƙarshen wata suna taruwa a General parlour aci abinci tare, masu matsaloli su faɗa a magance musu
Breakfast ne kawai kowa ke yi a part ɗin sa, Lunch kuma da dinner sai su haɗu aci tare, haka za su zauna ayi ta hira tunda babu me zuwa aiki a ranan
Wani lokacin ma har su Aunty Zainab suna zuwa, Aunty Zulaiha CE kawai bata cika zuwa ɗin ba sabida tana nesa sosai, amma idan ta sami lokaci tana ziyartan taron
Gaba ɗaya matan gidan suke haɗuwa ayi girki kala-kala da soye-soye, a babban kichen ɗin gidan suke haɗuwa tare da masu aiki su taya su
Yau ma hakan ta kasance duk sun haɗu suna ta girke-girke
Sauran yaran gidan kuma duk suna General parlour suna ta hiran su
Su Big Dady kuma suna ƙaramin parlour'n dake kusa da General parlour, anan suka zauna suna hira da nishaɗi
A cikin yaran in ka cire Fadila dake part ɗin su babu wanda ba shi ciki, ita dama bata cika son zuwa hiran ba, iyakan da an gama abinci zata zo taci ta tafi abun ta
Kaka shima na ɗakin sa yana karatun Jarida be fito ba, be son su ishe sa da surutu that's why ya zauna cikin ɗakin sa
Ɗahira na zaune gefen Baffa suna hira suna kallo cikin waya sai dariya suke yi
Gefe can kuma Yusra da Shakira ne su ma suka buɗe tasu shaftan, Fadil ya zauna tsakiyan su sai zuba musu surutu yake yi, su kuma idan ya'ishe su wannan ta mangare shi ta nan, wancan ta mangaro shi ta nan, kuma yaƙi tashi a wajen shi a dole sai dasu zai yi hira
Yau dai su Aunty Zainab babu wacce tazo cikin su.
.......... .......... .......... .........
Babu jima wa aka soma shigo wa da abincin ana jera wa a dainning table ɗin cikin parlour'n dake can gefe, babba ne me cin a ƙalla mutane ashirin
Bayan an gama an hallara a lokacin ne itama Fadila ta shigo ta zauna cikin su, kowa ya zuba abinda yake so
Ɗahira kuwa tana can cikin Parlour tare da Kaka dake zaune kan Wheel chair ɗin sa, dama haka take yi idan har ba ya son zuwa kan dainning ita take zama kusa dashi tana taya sa hira, idan ta ɗibo masa abinci sai su zauna tana taya sa hira suna ci har su gama
Yau dai shima Baffa ɗauko nashi abincin yayi ya dawo kusa dasu yana ci yana saka musu baki
Haka Familyn suka kasance yau cike da nishaɗi
Bayan kowa yaci ya sha aka dawo parlour aka zauna, nan su Big Dady sukai ta tambayan matsalolin mutane, daga nan kuma Kaka ya soma yabon Ɗahira da ƙoƙarin ta kan aiki, haka su ma su Big Dady sai yaba mata suke yi suna saka mata albarka
Abbu da Aunty Amarya hakan ya saka su farin ciki matuƙa
Hajja Fatu kuwa baƙin ciki kamar ya karta, haka ma Shakira sai dai ko kaɗan basu nuna a fuska ba
Hajiya kam babu ruwan ta duk da itama ba wai yabon yayi mata daɗi bane, Umma ma dai na ciki na ciki
Fuskar Yusra kamar zai fashe saboda baƙin cikin yanda iyayen nasu suke yabon Ɗahira, ko kaɗan ta kasa ɓoye abin da ke zuciyar ta, sai cika take yi tana batse wa babu wanda ya kula da ita
Anan Big Dady yake faɗa musu Usman zai dawo gaba ɗaya gobe, iyayen sun yi farin ciki amma ban da yaran don sun san halin sa ba ya da mutunci bare ɗaukar raini, yanzu zai zo duk ya takura musu
Daga nan aka ci gaba da hira, masu abun yi sun tashi sauran kuma sun zauna
Fadila ce farkon tashi ta koma part ɗin su.
*__________________________*
Ɗahira ce ta shigo cikin ɗakin nasu
Fadila dake waya tabi ta da kallo, sai kuma tayi dariya tana faɗin, "ga ta nan yanzu ta shigo ai".
Cire wayan tayi a kunne tana kallon Ɗahiran da ta nufi wajen gadon ta tace, "Ga shi za ku gaisa da Yaya K.b".
Murmushi Ɗahira tayi ta'iso wajen ta'amshi wayan tana kangawa a kunne kafin ta zauna gefen gadon Fadilan
"Yaya na". Tafaɗa tana dariya
Shima daga can dariyan yayi yana faɗin, "ƴan mata kin ɓuya da yawa fa".
"Haba ko dai ka ɓuya? Kaji min wannan mutumin".
Dariya yayi sosai yana faɗin, "Allah Ni ina nan ke ce dai kika ɓuya".
"Ai dama kai ba ka son laifin ka,
so how are you, how everyone?"
"Alhmadulillah. how about you?"
Ɗahira murmushi tayi tace, "lafiya sumul kamar yanda kuke, ina Shamsiyya?"
"Ai kam yanzu ta tashi anan ta gama min daɗin baki". K.b yafaɗa yana murmushi
"Hmm kai dai ka faɗa gaskiya ko dai kai ne ka gama mata daɗin bakin? Ai nasan hali".
K.B said, " Let me call her and u ask her,"
"A'a Ni bance ba, ka barta nariga dai nasan Shamsiyya baza tayi maka haka ba, ya Ɗan kinibibi ina fatan yana lafiya? Duk da nasan kai dashi baku da zumunci, wai ace anyi Waliman mu amma kuka ƙi zuwa".
K.b dariya yayi yace, "sorry Madam wlh kin san Ni aiki ne yayi min yawa, idan ma wani zai ƙi zuwa ai Ni bazan ƙi ba tunda har da my dear, amma insha Allahu kwanan nan zan zo Garin ma".
Taɓe baki Ɗahira tayi tana kallon Fadila da ta shiga Toilet tace, "Mu dai muna zuba idanu; and Kar ka manta da saƙo na don Allah idan zaka zo".
"Ok insha Allah, ga fa Mutumin naki nan ya shigo in ba shi wayan ne sai ki faɗa masa sunan da kika kira sa dashi?"
Rufe baki Ɗahira tayi cikin waro idanu tace, "don Allah rufa min asiri kar ka haɗa ni dashi".
K.b me zai yi in ba dariya ba
Ita kuwa Ɗahira wayan ta miƙa ma Fadila da ta dawo ta zauna kan gadon tana faɗin
"Riƙe wayan ki naga Yaya K.B yana son yaja min salalan tsiya".
Fadila amsar wayan tayi tana maida wa a kunne, sai kuma tayi dariya tana faɗin, "ai har ta fice ma a ɗakin".
Dariya ta sake yi tana gyara zaman ta, daga nan hiran su suka ci gaba da yi.
Kabir K.B shi ne ɗa na uku wajen Hajiya IKRAM, ɗiyar ta na farko Sunan ta Nafisa, suna kiran ta Aunty Mimi, tayi aure har da yara, sai Isma'il, suna ce masa Dady, sannan K.B ɗin, sai kuma Jalil sannan Shamsiyya, sai ƙannin Shamsiyyan guda uku
K.b ke son Fadila har kowa ya rigada ya san da zancen, yanzu kawai lokaci ake jira sanda Kaka zai ce su fito da mazajen aure ayi musu.
[5/25, 10:04 PM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTORS*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* 🧝🏼♀️
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
```( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_
_Wannan shafin naku ne masoyana, kuji daɗin ku._❤️
*EPISODE Fifteen*
Fitan Ɗahira ɗakin sai ta wuce ɗakin Maman ta kai tsaye, babu ita ciki tana can General parlour
Kan gadon ta tanufa ta soma kwashe mata kayan wankin ta dake ajiye an ninke, kwashewa tayi ta kai mata sif ta dawo ta soma gyara ɗakin, ba wani datti yayi ba amma haka ta sake gyarawa har da wanke mata Toilet, ta dawo Kan kujera ta zauna ta soma duba wayan ta, message ɗin da Masoyin ta ya turo mata yanzu babu jimawa ta buɗe
_"Kyakykyawa ta Barka da hantsi da fatan kina lafiya? Ya Weekend Ina fata kina enjoying?"_
Murmushi ta saki, a karo na farko yau tayi tunanin tura masa amsa, sai ta soma typing cikin ƙware wa
_"Alhmadulillah ina fata kaima haka? Please I want to know who?"
Sai tayi sending ɗin shi, tana nan zaune tana jiran ko za'a dawo mata da amsa but babu, sai ta gyara kwanciyar ta tasoma chatting da friends ɗin ta waɗanda sukai school tare
Can kuma sai saƙo ya shigo, da sauri ta buɗe tana murmushi duk farin ciki ya cika ta
_"Hmm kyakykyawa ta Kar ki damu da sannu zaki san ko Ni wane ne, Ni dai fata na in samu soyyayyar ki, don Allah ki so ni ko da kaɗan da yanda nake miki"._
Wani irin farin ciki ne yake mamaye da Ɗahira, sai dai bata mayar mishi da amsa ba tunda bata san me zata ce ɗin ba, sai taci gaba da chatting ɗin ta cike da nishaɗi.
⚫⚫⚫
Buɗo ƙofan Hajiya tayi ta shiga parlour'n da sallama
Yusra dake kwance cikin 3 Sitter tana kallo ta'amsa mata
Zuwa tayi ta zauna tana faɗin, "Yusra, get me some water."
Tashi Yusran tayi ta nufi Fridge tana faɗin, "Hajiya wai don Allah da gaske gobe Yaya zai dawo?"
Hajiya bata amsa mata ba har sanda ta kawo mata ruwan, ta'amsa tasha sannan ta'ajiye sauran kan Centre table tana maida hankalin ta kan t.v
Turo baki Yusra tayi ta zauna gefen ta tana cewa, "Hajiya I am talking to you."
Sai Hajiya ta kalle ta tana hararan ta tace, "dan ƙaniyar ki Dadyn naki ƙarya zai miki? Ina ce a gaban ki ya faɗa?"
Sake bunso baki gaba tayi tace, "to Ni Hajiya gaskiya bazan zauna ba zan koma gidan Aunty Zainab da zama, don wlh bazan zauna anan kullum ina cikin takura ba".
Hajiya tace, "to Ni ban aike ki ba, idan kin tambayi Dadyn ki ya yarda sai ki fi ruwa gudu ma".
"Don Allah Hajiya kiyi masa magana mana wlh bazai yarda ba in Ni ce".
Hajiya bata sake mata magana ba
Ita kuma sai magiya take mata har da ƴar ƙwallan ta
Ko kaɗan ba ta farin ciki da dawowar Yayan nata, tunda sai tafi kowa takura kasancewar Part ɗin su ɗaya, ko kaɗan idan yana nan ba ya ƙaunar kayi ƙwaƙƙwaran motsi a gidan, yanzu sai ya zama laifi a wajen sa
Daga ƙarshe ma Hajiya tashi tayi ta nufi cikin ɗakin ta tabar Yusra nan tana kumbura fuska kamar Flower, ba don ranta ya so ba itama ta tashi ta fice a part ɗin ma gaba ɗaya, duk zuciyarta babu daɗi.
⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫
*TOMORROW MORNING*
Monday tushen aiki ko Bature na tsoron Monday
Gaba ɗaya ahalin gidan sun tafi aikin su, sai su Umma da aka bari su uku a gidan sai kuma masu aiki, sannan Kaka dake Part ɗin sa
Hajiya itama tunda ta tashi ta soma soye-soyen ta wanda zata tarbi Babban ɗanta dashi, yau gaba ɗaya farin ciki ya cika ta Allah-Allah take yi anjima yayi ta ga dawowar sa, dama sun yi waya jirgin ƙarfe 02:00pm. Yace mata zai biyo; don haka komi take yin sa a tsanake, ita da kanta ta shiga ɗakin sa ta gyara masa tayi masa duk abin da ya dace, bayan ta saka airfreshna sannan ta ƙara masa da turaren tsinke ta rufo ɗakin ta koma kichen taci gaba da harkokin ta.
⚫⚫⚫
Ɗahira tunda ta fara duba Patiens ɗin ta take jin kanta na sara mata, amma dayake ita ɗin jajirtacciya ce bata bi takai ba taci gaba da harkokin ta
Bayan ta gama ta nufi
Ward ta duba sauran mara su lafiyan ta sannan ta dawo Office ɗin ta
Tana son yau ta koma gida kamar lokacin tashin ta but ko kaɗan ba ta ƙaunar taje ta haɗu da maƙiyin ta (sunan da ta saka masa kenan)
Tunda Baffa ya shigo ɗazu ya sanar mata da lokacin da zai je ɗauko sa a airport take ta jin ta babu daɗi, sosai kan nata yake ƙara ciwon
Agogon dake ɗaure a tsintsiyan hannun ta takalla taga ƙarfe 01:20pm. Ne yanzu
Tsaki taja ta tashi ta nufi drower ta ciri magani tasha da ruwan Robber dake ajiye saman table ɗin ta, Labcoat ɗin ta tacire ta rataye akan Hanger sannan ta cire Eyeglasess ɗin ta ta'ajiye saman table ɗin ta nufi Toilet
Alwala ta ɗauro ta fito ta tada sallah, har ta'idar tana zaune nan tana lazimi, barci ne ya soma fisgarta don haka ta tashi ta ninke sallayan ta'ajiye ta nufi gaban table ɗin ta taɗau Glasses ɗin tamayar a idanun ta
Hanyan ƙofa ta nufa don zuwa Office ɗin Abbu ta kwanta acan, amma me ta tuna sai ta dawo tana jan tsaki
Ta san idan taje can zai tilasta mata ta koma gida ne, kuma a yau dai ba ta buƙatar ganin ta a gida, shiyasa ta dawo ta zauna kan kujeran ta ta ɗaura kanta a Deks ta rufe idanun ta, dayike barcin ne sosai yake cin ta don haka babu daɗewa ya ɗauke ta.
Koda ta farka babu ciwon kan a yanzu, sallan Asar tayi sannan ta saka Labcoat ɗin ta, tana shirin fita ne Beeper ɗin ta ya soma ruri, don haka ta fita da sauri tayi hanyan emargency ward.
⚫⚫⚫
At home, everyone was celebrating Usman's return
Gaba ɗaya matan gidan suna part ɗin Hajiya sun je taya sa murnan dawowa
Sai da kowa ya watse sannan Shakira da Yusra da take Part ɗin su Shakiran yanzu suka nufi sashen Hajiyan don su gaishe sa
Yana zaune a dainning yana cin abincin da Hajiya ta girka masa da kanta
Yayi wanka har ya sauya shigan sa cikin ƙananan kaya kamar yanda ya saba
Koda suka shiga gaishe sa suka yi, ya'amsa musu cikin Izza da taƙama
Basu sake cewa komi ba suka miƙe suka fice don ba shi wuri, Part ɗin su Shakiran suka koma suka dasa hira.
Shi kuma bayan ya gama ɗakin sa ya koma, kwanciya yayi kan Three sitter ya lumshe idanun sa, shi ba barci yake yi ba kawai kwanciyar yayi, sai da aka kira sallan la'asar kafin ya tashi yayi alwala ya fita
A waje suka haɗu da Baffa suka jera har masallacin dake nesa kaɗan da gidan su
Bayan sun dawo a haraban gidan suka haɗu da Abba da Abbu da dawowar su kenan daga aiki
Gaishe su yayi cikin girmamawa, su kuma sai tambayan shi hanya suke yi cike da fara'a, haka ya'amsa musu sannan ya wuce ya nufi babban Parlour
Fadil na zaune a kan kujera yana kallo shi kaɗai ya shigo
Da sauri Fadil ɗin ya gaishe shi
Da kai ya'amsa masa ya nufi hanyan da zai sada shi da ɗakin Kaka
Da idanu Fadil ya bi shi dashi, sai da ya shige sannan ya taɓe baki a ransa yana mitan "miskilin banza! kai da Fadila wlh ban san wanda yafi mugun hali ba".
Sai kuma ya kwaɓe fuska yaci gaba da kallon sa.
Tura ƙofan yayi ya shiga yana motsa bakin sa
Kaka dake zaune kan Wheel chair ɗin sa kamar ko yaushe yana karatun Jarida ya ɗago yana kallon sa, sai kuma ya yalwata fuskar sa da fara'a yace, "Maraba da Jikalle na".
Takowa yayi ya zauna saman kujeran ɗakin yana kallon Kaka, kaɗan ya saki fuskar sa yace,
"Old man are you still alive?"
Sai Kaka ya saki dariya me sauti yace, "ja'iri ka ƙosa na mutu ko? To ina nan babu inda zan je sai na ga auren ka".
Kyakykyawar murmushin sa yayi yana shafa gashin kansa yace, "uhmm Kaka kace da sauran ka kenan tunda Ni dai ba yanzu ba".
"Koma dai me zaka ce sai naga auren ka tukun zan bar duniyar nan, dama tunda nayi muku maganar kai da takwara babu wanda ya haɓɓa sa, kun fi so dai a haɗa da ƙannin ku ko?".
Usman taɓe baki yayi sai dai be ce komi ba
Kakan changed the conversation and asked, "Ya hanya?" Shi kuma ya'amsa masa a taƙaice
Kaka sai zuba masa hira yake yi, shi kuma daga ya'amsa da Eh sai A'a, daga ƙarshe wayan sa ya ciro yana latsawa yana sauraron Kakan, a haka yaja dogon lokaci a ɗakin kafin ya miƙe yayi masa sallama ya fice.
[5/26, 12:54 PM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTORS*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT 🧝🏼*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
```( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_
*EPISODE Sixteen*
Sai ƙarfe 05:45pm. Ɗahira ta koma Office ɗin ta, Jakarta ta ɗauka da abinda zata buƙata ta fito ta rufe Office ɗin ta nufi Lifter
Tana sauka ta fita ta nufi inda motan ta yake ta buɗe ta shiga, rufewa tayi ta'ajiye jakar ta kan Kujeran me zaman banza sannan tayi ma motan keey, sai dai yaƙi tashi, ta daɗe tana gwadawa amma yaƙi ya tashi, guntun tsaki taja tana dafe goshin ta, lumshe idanuwan ta tayi na kusan minti 2 kafin ta buɗe ta sake gwadawa amma ina har yanzu be tashi ba, fitowa tayi tana ɗan waige-waige, sai kuma ta nufi gaban motan ta buɗe Garage ɗin ta soma tattaɓa wa, duk ta duba ko da akwai matsala ne amma ita a fahimtan ta bata ga komi ba
Tana nan tsaye a wajen tana ɗan sake duba wa taji sallama, sai ta ɗago kyawawan idanuwan ta wanda ƙwayan ciki suke ƙyalli sakamakon Hasken fitillun haraban wajen, amsa mishi tayi tana kau da kanta ganin kallon da yake mata tamkar zai haɗiye ta
"Are you all right? I've seen you here before. Are you still gone? What's going on?"
Ɗahira kamar baza tayi magana ba, sai kuma ta ga hakan be dace ba tunda taimakon ta zai yi, bata ɗago ba ta bashi amsa, "Wlh nima ban sani ba, kawai ta ƙi tashi ne".
Dr. Sa'id yace, "ok bari in duba miki mu gani ko?"
Babu musu ta matsa mishi yazo ya soma duba mata, shima ya daɗe yana taɓe-taɓen sa kafin yace mata, "wake up the car".
Shiga tayi tayi ma motar keey amma har yanzu ya ƙi tashi
"Ina ga dai motar ki sai ta ga bakanike coz myb wani matsalan ne babba wanda baza mu iya gane wa ba". Yayi maganar bayan ya rufe mata garejin
"To Nagode". Tace dashi tana ciro jakarta kafin ta rufe motan da keey
"In ba damuwa muje in rage miki hanya mana".
Ta tsinkayi muryan sa da har ta juya baya zata tafi
Jimmm tayi tana tunani domin ita mutumin ko kaɗan be mata ba, coz ta kula kallon tsiya ne dashi tun ganin sa na farko
Murmushi yayi yana takowa wajen ta yace, "don't worry. Ni ba siyar da kanki zanyi ba, ai kin san a nan nake aiki balle kice Ni ɗin baƙo ne, so ni ba baƙo bane babu wanda be San ni ba, My name is Dr. Sa'id Khan".
Kallon sa ta ɗan yi sai kuma tayi guntun murmushi tace, "ba damuwa mu je".
"Yauwa ko ke fa". Yafaɗa yana yin gaba wajen motar sa
Shi ya buɗe mata murfin motan da zumman ta shiga
Sai kawai ta ga abun yayi mata wani iri domin ita idan har ba Baffa ba basu taɓa hakan da wani ba, hakan ko kaɗan be burge ta ba, amma babu yanda zata yi ta shige ta zauna ya rufe mata
Shiga shima yayi yaja motar suka bar asibitin
A cikin motan ma babu wanda yayi magana cikin su, sai da suka ɗan yi tafiya kafin ya soma jan ta da Surutu duk a kan aikin nasu
Ko kaɗan ba ta jindaɗin surutun nasa
Shi kansa ya gane ba ta ƙaunar hiran sa; yanda take amsa masa maganar kamar baza tayi ba, don haka yaja bakin sa yayi shiru yana mamakin yarinyan, shi tunda ya ganta yaji ta burge sa matuƙa kuma yana son ƙulla alaƙa da ita, sai dai ya ga alamun hakan ba me yiwuwa bane duba da yanda take ɗin, da alamun tana da girman kai kuma zata yi wuyan sha'ani, a yanda ya fahimce ta kenan
Har suka kai ƙofar gidan su kafin ya tsai da motan
Kallon sa Ɗahira tayi cikin siririyan muryanta me kamar tana yanga tace,"Thank you, Dr."
He smiled and looked at her and said, "It's all right."
Buɗe motan tayi ta fito
Dai-dai lokacin su Baffa da Usman suka ƙariso wajen sun dawo sallan magriba
Gaba ɗaya kallon ta suke yi, yayinda Usman ya ɗauke kansa time ɗin da ta juyo zata sauke idanun ta a kansu, cikin gidan ya wuce batare da yayi wa Baffa magana ba
Shi kuma Baffan sai ya nufo ta fuskarsa duk babu walwala yana bin motan Dr. Sa'id da kallo da har ya ja ya tafi
Itama ganin ya taho ɗin ne yasa ta tsaya tana masa murmushi
Yana ƙari so wa idanun sa a kanta yace, "wannan kuma wane ne? ina Motar taki?"
Sai da ta kalli hanyar da Dr. Sa'id yabi kafin ta dawo da ganin ta kanshi tace, "Yaya Motata taƙi tashi ne wlh ban san kuma me ya faru ba, shi ne yace in zo ya rage min hanya".
Gaba ɗaya zuciyar Baffa ba ta mishi daɗi, tsananin kishi ne yake nuƙurƙusan sa a ransa, daƙyar ya"iya saisaita kansa ya sake jeho mata tambaya
"Aina Motar taki ta tsaya da har kuka haɗu dashi?".
"A cikin Hospital ɗin ne fa, kuma shima Dr. Ne cikin asibitin shiyasa ma na yarda na hau, but da farko ban yi ninyan hawa ba".
Murmushi Baffa ya kirƙiro yace, "let's go then".
Babu musu tayi gaba yana bin ta a baya duk da ita bata fahimci musabbabin tambayan nasa ba, amma ta san cewa shi ɗin Yayanta ne yana da right ɗin tambayar ta
Sai da suka shiga ciki kafin suka jera cikin gidan, Part ɗin su Ɗahira suka wuce
Suna shiga da sallama, Aunty Amarya dake zaune ita da Fadil suka amsa musu
"Aaah maraba da Mijina". Aunty Amarya tafaɗa tana yalwata fuskarta da fara'a
Baffa na faman shafa kansa yana murmushi ya ƙariso ya zauna a kan kujeran kafin ya gaishe ta
Ta'amsa masa cike da fara'a tana tambayar sa aiki
Itama Ɗahira sannu da gida tayi mata ta wuce ɗakin su ba tare da ta zauna ba
Su kuma suka ci gaba da hira suna kallo
Daga baya itama Umma ta fito aka ci gaba da hiran da ita
Baffa duk ya ƙosa Ɗahira ta fito amma tunda ta shiga bata sake fitowa ba, shi kuma ya zauna ne don ita amma tunda ta fito ta zuba abinci ta sake shige wa ɗaki, aiki take yi a ciki shiyasaka ta zauna nan ɗin tunda ba ta son hayaniya
Sai da aka kira sallan isha'i kafin Baffa ya miƙe tare da Fadil suka fito
Anan suka ci karo da Fadila itama dawowar ta kenan, gaishe da Baffa tayi
Ya'amsa yana faɗin, "Sarkin miskilanci sai yanzu aka dawo?"
Murmushi tayi tace, "Yaya kana son dai tsokana ta ko?"
Murmusawa yayi shima yana cewa, "ai gaskiya ne, kwana biyu ma gaba ɗaya kamar ba kya nan a gidan, rabon da in ganki na jima sai jiya a wajen meeting".
Fadil dake tsaye yana sauraron su yace, "ai Yaya wlh duk wanda ya auri Aunty Fadila ya bani, shiyasa ma zan ba ma Yaya K.B shawara tun wuri ya sauya ta don baza tayi daɗin zama ba idan ya aure ta, yana ji yana gani zata mayar da waya abokin rayuwanta ta ƙyale shi yay ta surutun sa.."
Kawo masa duka tayi dole yayi shiru yana matsawa gefe da sauri
"Wlh zan ɓalla ka a nan wajen; Ni sa'ar wasan ka ne Fadil?" Tafaɗa tana hararan sa cike da haushi
Baffa dariya yayi yace, "mai da wuƙan don Allah wasa yake miki".
Ƙwafa kawai tayi ta juya ta buɗe ƙofan Part ɗin nasu ta shige, tana jin Baffa yana faɗin
"Babu sallama kuma zaki tafi?"
Amma bata jiyo ta kalle sa ba bare ta tanka masa
Su ma wuce wa suka yi suka tafi, Baffa na shan dariyan Fadil da yaci gaba da maganar Fadilan.
⚫⚫⚫
*08:45pm.*
Suna zaune su huɗu a kan dainning suna cin abinci, babu me magana cikin su sai ƙaran cokula da Plate da ake ji
Kansa na ƙasa yana cakalan abincin kamar bazai ci ba, rabi kuma hankalin sa naga wayan sa yana kallon wani abu da aka tura masa, har kowa ya miƙe suka bar sa nan zaune be ma san sun tashi ɗin ba
Parlour suka koma sukai zaman su, Big Dady da Hajiya suna taɓa hira while Yusra kuma ta mayar da hankalin ta kacokan kan Film ɗin da ake yi a Bollywood, Film ɗin زوجة زوجي searese
A hankali ya miƙe ya taho cikin parlour'n yana shirin wuce wa ɗakin sa
Dady ya tsayar dashi yana faɗin, "Fodio come here we'll talk".
Juyowa yayi ba tare da yace komi ba ya taho ya zauna kan One sitter dake Facing ɗin nasu Dady
Ɗan gyaran murya yayi yana kallon sa kafin yace, "gobe ne zaka soma zuwa Hospital ɗin ko ya?"
Cikin ƙasa da murya kamar wanda yake tsoron yin maganan yace "No .. until Monday".
Jinjina kai Dady yayi kafin yace, "to har yanzu baka shirya aure bane? Tunda ga shi yanzu ka dawo gida Ya kamata ace kun ajiye mata kai da Baffa amma shiru har yanzu baka ce komi ba, kuma idan ban manta ba naji Baba yayi muku magana akan maganar auren ku".
Shiru Usman yayi be ce komi ba, sai ma sad da kansa ƙasa da yayi
Su kuma sun zubo masa ido daga shi har Hajiya suna sauraron abinda zai ce
Yusra dake kallo ma hankalin ta na wajen
Girgiza kansa Dady yayi don yasan halin ɗan nasa, don babu wanda be saba da miskilancin sa ba
"Ya kamata dai kusan kun girma tun kafin mu ce zamu nuna fushin mu a kan ku ku fito da mata, don baza mu zira muku idanu kuyi yanda kuke so ba, ka tashi kaje Allah yayi muku albarka". Dady ya sake faɗan hakan
Miƙewa yayi yana ɗan motsa bakin sa kafin ya nufi hanyan ɗakin sa
Su kuma suka rakasa da kallo har sanda ya gifta ta gaban su ya wuce
Ajiyan zuciya Dady ya saki yana miƙewa ya kalli Hajiya yace, "Let me in. I have a job."
Be jira amsar ta ba ya sake maida kallon sa kan Yusra yana cewa, "Auta ke baza ki je ki kwanta ba sai kin makara ko?"
Kallon sa tayi tana murmushi tace, "Dady zan kwanta yanzu za'a gama wannan sai inje in kwanta".
Gyaɗa kansa yayi kafin yayi gaba yana shigewa ɗaki
Itama Hajiyan bin bayan sa tayi suka bar Yusra ita kaɗai a parlour'n.
0 comments:
Post a Comment