*12:30pm.*
Ya gama shirin sa na zuwa Office, yana sanye cikin wandon jeans blue, sai baƙar riga me gajeren hannu da ya sake fito da hasken skin ɗin sa sosai ya kuma ƙara masa kyau ainun, kwantaccen baƙin gashin sa sai shaining yake yi zuwa siririn sajen sa, babu abinda yake tashi ajikin sa sai sassanyan ƙamshi me tsananin daɗi ga duk wanda ya shiga hancin sa
Wrest watch yake ɗaura wa a tsintsiyan hannun sa me haske sosai da yalwan gashi, fuskarsa babu alamun fara'a ko kaɗan, har ya gama sakawa kafin ya zauna gefen gado ya soma saka Combat ɗin sa da ya kasance Blue Colour da igiyan sa suka kasance baƙi, bayan ya gama saka wa sai ya miƙe ya ɗau briafcase ɗin sa ya fito cikin ɗakin yana rufe wa
Babu kowa cikin parlour'n, sai ya nufi ɗakin Hajiya yayi Nocking yana jiran izni
Hajiya dake zaune kan gado wanda fitowar ta kenan daga Toilet ta ba da iznin shigo wa
Tura ƙofan yayi yana motsa bakin sa idanun sa a kan ta
Kamar yanda itama ta zuba masa idanu tana kallon sa
Takowa yayi a hankali har zuwa gaban ta kafin ya zauna gefen gadon, shiru yayi yana murza hannun jakan dake riƙe cikin fararen tafin hannun sa
Tsawon mintuna biyu Hajiya tana jiran taji yayi magana amma sai taga be da alaman yi, hakan yasa tace, "har ka shirya my son?"
Gyaɗa mata kai yayi yana kallon ta
She smiled and said, "God bless you and good luck."
"Ameen". Yafaɗa a hankali wanda a laɓɓan sa ta fahimci abinda yace
Miƙe wa yayi ya taka ya fice cikin ɗakin yana duba agogon hannun sa.
Yana fita wajen motan sa ya buɗe ya shiga ya zauna sannan ya rufe, tada motan yayi yaja ya nufi bakin Gate
Tun daga nesa da me gadi ya hango zuwan sa ya miƙe da sauri ya buɗe masa Gate ɗin, yana fita ya ƙara Speed, cikin mintuna ƙalilan ya'isa haraban Hospital ɗin
Ɓude ƙofan yayi ya ziro ƙafafun sa a hankali sannan ya fito ya rufe, ya juya ya soma tafiya cikin taƙama da izza wanda zaka san a jinin sa ne.
Shakira da Ayush dake tsaye jikin motan Shakiran, Ayush tana faɗa mata yanda suka yi da Baffa sai idanun ta ya faɗa kan Usman dake doso cikin asibitin, baki buɗe take bin shi da kallo
Hakan yasa itama Shakira ta mayar da hankalin ta inda Ayush ɗin take kallo, nan ta hangi Usman har ya shige
Ajiyan zuciyan da Ayush ta saki me ƙarfi ya saka Shakira take kallon ta cike da mamakin ta
"Lafiyan ki kuwa?" Ta tsinkayi muryan Shakiran da ta sake dawo da ita hayyacin ta
"Hmm ba lafiya ba, wane ne wannan Handsome Guy ɗin da naga kamar yana kama da Familyn ku?" Ayush tayi maganar tana tsare Shakira da idanu
Taɓe baki ita kuma tayi tace, "Yaya Usman ne".
"Kaiii amma wlh ya haɗu, Ni zan iya ce miki ban taɓa ganin mutumin da ya tafi da imani na a second ɗaya ba irin wannan, kai wlh ban taɓa ganin wanda komi nashi ya dace dashi ba sai wannan guy ɗin, Kai Amma wlh ban taɓa.."
"Ke dallah ya isa mana, meye haka kike zuba min hauka? ko dai hankalin ki ya gushe ne?" Shakira ta katse ta tana kallon ta cike da takaici
"Wlh baza ki gane bane, amma wlh yayi Ni dai ya gama dani".
Shakira tace, "to shikenan yanzu kenan baki yi da Yaya na sai wannan ko? Ko kin manta alƙawarin da ki kai min?".
Murmushin yaƙe Ayush ta saki tace, "laa I don't mean that. I'm just saying my opinion on this, but I'm not saying I'm better than Baffa, I like Baff.." Sai kuma tayi shiru ganin zata saki layi
Shakira da hankalin ta ma ba ya ga Ayush ɗin, tana kallon Fadila da tazo wuce su tayi saurin kwaɗa mata kira
Fadila dake tafiya waya a kunnen ta tajuya ta kallo su, sai kuma ta soma takowa wajen su har a lokacin tana ci gaba da wayan ta, sai da tazo dai-dai gun su sannan ta kashe wayan tana ɗago kai ta kalle su
Shakira murmushi tayi tace, "manyan gari wai ke idan ba an neme ki bane ba kya neman mu ko?"
Guntun murmushi kawai Fadila ta saki ba tare da tace komi ba illa gyara zaman jakan ta da take yi
"Yanzu muka gama magana da mutumiyar ki a kan ki ma". Shakira ta sake faɗan hakan still tana Murmushi
Kallon ta Fadila tayi da rashin fahimta kafin tace, "who?"
Shakira tace, "Ɗahira, ai ita nake nufi, kullum kuma idan na ganta sai na ce ta gaishe min da ke, Allah yasa tana faɗa miki don nasan halin ta ba wai son ki take yi ba?"
Numfashi Fadila taja sannan tayi murmushi tace, "haka ne.. to Ni zan tafi kin ga nayi late yau ban shigo da wuri ba". Sai kuma ta ɗan ɗago wayan ta tana duba time kafin ta juya ta tafi ba tare da ta sake furta komi ba
Daga Ayush da tun zuwan Fadilan take kallon ta har Shakira bin bayan ta da kallo suka yi har ta ɓace ma ganin su
Tsaki ne ya biyo bayan shirun nasu
Ayush ta kalle ta da mamaki tace, "mene ne ƙawata?"
Sai da Shakira tayi ƙwafa kafin ta buɗe motan tace, "Allah Fadila tana baƙanta min rai idan nayi mata maganar Ɗahira take nuna halin ko in kula wanda Ni ba hakan nake so ba".
Dariya Ayush tayi duk da bata fahimci me take nufi ba, ta nufi ɗayan side ɗin ta buɗe ta shiga, itama Shakiran shiga tayi ta rufe ƙofan tare da jan motan suka bar haraban Hospital ɗin.
⚫⚫⚫
Kai tsaye hawa na uku ya wuce inda a nan ne office ɗin sa yake, Office ɗin na kallon na Ɗahira ne
Buɗe wa yayi ya shiga ya rufe, kallon ko ina yake yi da idanu fuskar sa babu fara'a, ko kaɗan ba ya farin ciki da kasancewar sa a nan ɗin, jin sa kawai yake yi cikin takura kuma hakan ne ya ƙara ɓata masa rai sosai
Duk da office ɗin yana da girma, ga shi ya haɗu tako ina amma shi be burge shi ba ko kaɗan tunda ko kwatan nashi na ƙasan Turkey be yi ba
A hankali ya soma takawa ya nufi kan kujeran ya zauna yana kwantar da kansa jikin kujeran, ya lumshe idanun sa yana jujjuya wa cikin kujeran, numfashi kawai yake sauke wa ba tare da ya motsa ba tsawon lokaci, sai da wayan sa ta soma ringing ne sannan ya buɗe idanun sa yana ɗago kai yabi wayan da kallo a inda ya'ajiye saman table, ganin sunan Dady na yawo a screan ɗin wayan hakan yasa shi sanya hannu ya ɗauka ya kanga a kunne bayan yayi peacking call ɗin, shiru yayi yana sauraron sa kafin ya buɗe baki a hankali yace, "Eh na zo".
Kallon files ɗin gaban sa yayi, sannan ya yamutsa fuska yace, "ok".
Sai ya cire wayan a kunnen sa yana ajiye wa, ya sake maida kansa jikin kujeran ya rufe idanun sa
Bayan mintuna biyar ya jiyo Nocking, iznin shigowa ya bayar ba tare da ya motsa ba
Ɗaya daga cikin staff's ɗin asibitin ne ta shigo, ta gaishe sa but ko amsa ta be yi ba, kamar ma be san da wanzuwar ta ba
"Dr Noor told me to bring this to you."
Hannu ya nuna mata alamun ta ajiye a table
Don haka babu musu tayi yanda yace mata sannan ta juya ta fice
A ƙalla ya ɗau tsawon mintuna goma kafin ya buɗe idanun sa ya ɗago kai yana kallon files ɗin gaban sa, numfashi yaja me ƙarfi sannan kuma ya ɗaura kansa saman table ya sake rufe idanun sa be da alaman yin abinda ya kawo sa.
⚫⚫⚫
Hannun yarinyan ta riƙe tana kallon ta cike da tsantsan tausayi, wai yarinya ƙarama kamar wannan ace an yi mata Fyaɗe, kee duniya ina zaki damu ne? Mene mutane suke nema a kan ƙaramar yarinyan da bata fi shekara biyar ba?
Numfashi taja tana sanya hannun ta kan yarinyan ta soma shafa mata gashi, ko kaɗan yarinyan ba ta motsi, ba ma zaka san tana da numfashi ba sai idan ka ƙura mata idanu sosai zaka ga tana fitar dashi ɗai-ɗai ta cikin Oxgyen ɗin da aka sanya mata
Ta jima tana kallon yarinyan wanda a baɗini tunani ta lula a kan abinda ke faruwa a ƙasar mu, wanda Fyaɗe ya zama ruwan dare a wannan zamanin
Hannun ta tajanye ta miƙe daga kan gadon ta fito waje
Matar dake zaune bakin ƙofan a ƙasa tana kuka ta ɗago kai da sauri tana kallon Ɗahira, sai kuma ta miƙe cikin rawan baki tace, "Likita.."
Kuka ne yaci ƙarfin ta dole tayi shiru
Ƙwallan da ya cika mata idanu na tsaban tausayin matar da ƴarta ta share sannan ta dubi matar a tsanake tace, "Calm down, she will be relieved by God's will, but follow ME and we will talk".
Kallon ta Matar tayi alamun kamar bata fahimta ba
Hakan yasa Ɗahira ta sake maimaita mata da Hausa, "ki kwantar da hankalin ki zata samu sauƙi da yardan Allah, amma ki biyo NI ofiice muyi magana".
Gyaɗa kanta tayi tana saka gefen zanin ta ta share hawayen ta da suka haɗe da majina, sannan tabi bayan Ɗahira da har ta soma tafiya
Office ɗin ta suka zarce, sai da suka zauna sannan Ɗahira ta kalle ta tace, "zan so ki bani bayani a kan abinda ya faru, sam abun be min daɗi ba kuma tabbas dole ne hukuma ta ɗau mata fansa".
Numfashi taja kafin taci gaba, "Mun rigada mun cire spain ɗin waɗanda sukai mata wannan aika-aikan, kuma insha Allahu idan result ya fito zamu miƙa case ɗin ga hukuma domin abi mata haƙƙin ta".
Cikin kuka Matar ta soma magana da faɗin, "Likita mun rigada mun bar su da Allah, sam baza mu iya Shari'a dasu ba domin kuwa waɗanda suka aikata mata hakan sun fi ƙarfin mu nesa ba kusa ba, Ni fata na Allah ya tashi kafaɗun ƴar mu domin kuwa ban san me zance wa Mahaifin ta ba idan ya dawo ya tarda abinda ya faru.." Sai ta fashe da kuka tana ɗaura hannun ta ɗaya saman fuskarta
Kallon ta kawai Ɗahira take yi na tsawon lokaci kafin tace, "kar ki damu dole ne mu miƙa wannan case ɗin ga hukuma, domin a yanzu zancen da nake miki Human right sun shiga zancen nan, kuma ya kamata ki kira mijin naki duk inda yake yazo ya ga abinda ya faru hakan shi ne maslaha, sannan ina so muyi magana dashi". Taƙarike maganar tana janyo Pepper gaban ta taɗau Bairo ta soma rubutu
Matar bata ce komi ba sai kukan ta da take yi
Miƙa mata Peppern da ta gama rubutu tayi, "Ki je ki siyo wannan alluran ina buƙatar su yanzu".
Hannu ta saka ta'amsa tana jan majina, "Na gode Likita Allah ya saka da alheri".
Murmushi kawai Ɗahira tayi mata bata ce komi ba, tana bin ta da kallo har ta fice sannan ta kau da kanta tana sauke ajiyan zuciya, hannu biyu ta saka ta tallabo haɓan ta bayan ta ɗaura gwiwowin hannun saman table, sosai take cikin damuwa akan abin da ke faruwa da yaran mutane
"Wai shin mene ne matsalan hakan? Meke jawo yawan Fyaɗe a wannan lokacin? Sannan mene ne mafita?"
Nocking ɗin da aka yi yasaka ta dawowa hayyacin ta, numfashi taja tana kallon Baffa da ya turo ƙofan ya shigo.
[5/28, 8:08 PM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTORS*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏼
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
```( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_
*EPISODE Eighteen*
"Yayana baka tafi ba?"
Murmushi yayi ya tako ya zauna yana cewa, "yanzu na tashi nace bari inzo inga ƙanwa ta".
"Allah Sarki Yayana, ina to budurwan taka ko ta tafi ne?" Tayi maganar tana dariya
Shima dariyan yayi yace, "kai sis yaushe nace miki budurwa ta ce?"
Ɗage kafaɗa tayi tana taɓe baki tace, "Ni naga alama ne ai".
"Serious ba budurwa ta bace freindship ne kawai a tsakanin mu".
"Anya Yaya ban yarda ba?"
Langaɓe kansa yayi yace, "shikenan tunda baza ki yarda ba?"
Ɗahira dariya tayi tace, "na yarda to, yaushe ne kuma zaka haɗa ni da budurwan ka ko sai ka kawo ta gida ne zamu ganta?".
"Very soon lokaci nake jira ai".
Ɓata fuska tayi tana shirin magana aka yi Nocking
"Yess come in". Tafaɗa idanun ta a kan ƙofan
Matar da ta fita ɗazu ne ta dawo
"Sis bari in tafi sai mun haɗu a gida". Baffa yafaɗa yana miƙe wa
"Ok Byeee Yaya".
Sannan ta kalli matar tace zauna
Zama tayi kamar yanda ta buƙata sannan ta miƙa mata alluran da ta siyo
Amsa Ɗahira tayi ta duba kafin ta kalli matar tace, "Shin Mijin naki ya zo?"
Girgiza kanta tayi sannan tace, "yana Zaria ne a yanzu haka, sai dai kuma na faɗa masa yace min yana kan hanyan dawo wa".
Gyaɗa kanta tayi kafin tace, "to ki je ki kula da ita, Dr. Rahab zata riƙa zuwa ta duba ta, idan ya ƙariso sai ku taho tare ina son ganin ku".
Jinjina kanta matar tayi sannan ta miƙe tayi hanyar ƙofa ta fice
Waya ta ɗauka tayi kira sannan ta kara a kunne
"Ki zo ina son ganin ki". Abun da tafaɗa kenan kafin ta'ajiye wayan taci gaba da duba files ɗin gaban ta
Babu jima wa wata Nurse ta shigo bayan tayi Nocking an ba ta izni
"Gani Doctor" Nurse ɗin tace hakan bayan ta tsaya a gaban table ɗin Ɗahiran
Lokacin ne ta ɗago kai ta kalle ta, sannan taɗau alluran ta miƙo mata tace, "Yauwa Sister ga shi ki je ɗakin da yarinyan nan da aka kawo jiya take kwance kiyi mata alluran nan, Please yanzu zaki yi mata Dr. Rahab bata kusa ne Ni kuma ban yi sallah ba lokaci ya ƙure, ki kula da ita zuwa sanda zata dawo sabida ako yaushe zata iya farka wa kinji?"
Murmusawa Nurse ɗin tayi sannan tasaka hannu ta'amsa alluran a lokaci ɗaya take faɗin "insha Allahu doctor". Sannan ta juya ta fice
Ita kuma Ɗahira miƙe wa tayi ta cire Labcoat ɗin ta; ta rataye a Hanger, sannan ta zare Eyeglasess ɗin ta tare da agogon hannun ta ta'ajiye ta nufi cikin Toilet ɗauro alwala.
⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫
Sai da suka gama kitumurmuran su na abin da suke ƙulla wa a kan Baffa da Ɗahira kafin Shakiran ta sauke ta a bakin gidan su sannan taja motan ta tatafi
Ayush bata shiga gidan ba sai ta nufi cikin anguwan, gidan ƙawarta Rumanatu
Rumanatu ƙawa ce wajen Ayush tun na yarinta, da gidan su Ayush ɗin da gidan su Rumanatu gida ɗaya yaraba su, sun taso makaranta tare komi nasu tare har zuwa matakin da suka kai NCE, inda daga nan ne Rumanatu ta dakata da karatun nata, yanzu haka shekara biyu kenan da auren ta, ta taɓa haihuwa ɗan nata na da wata bakwai ya rasu
Gidan ba wani babba bane gidan Rumanatun but gida ne na masu hali tunda mijin ta yana da ƙumban Susa, shima a anguwan yake da zama da iyayen sa
Ƙofar gidan ta ƙwanƙwasa tunda a rufe yake daga ciki, babu jima wa aka zo aka buɗe mata
Rumanatun ce da kanta, ganin Ayush a gaban gidan ta sai ta kwantsama ihu tana rungume ta tare da faɗin, "Ayushhhh".
Dariya Ayush tayi itama tana rungume ta ɗin, kafin suka saki juna suka shige ta rufo ƙofan, cikin gidan suka shiga suka yaɗa zango a parlour
"Waiii wata sabon gani ai nayi fushi wlh". Cewar Rumanatu tana ajiye mata farantin silver da ta ciko da drinks
Dariya Ayush tayi bata ce komi ba ta ɗauki Robbern Coke tana buɗe wa
Rumanatun ta sake cewa, "tunda kin zama big girl me amsar Albashi duk wata ai dole ki guje mu".
Still dariyan Ayush ta sake yi kafin tace, "wlh kema kin san ba haka bane, tsakani da Allah idan zaki faɗa gaskiya kema kin san bazan taɓa juya miki baya ba, ai ke kin fi ƙarfin haka a waje na".
Kanta ta ɗaga tana taɓe baki tace, "da dai ban san daɗin bakin ki bane, kar fa ki raina min hankali".
Kwashe wa da dariya Ayush tayi har da ɗan buga ƙafafun ta
Rumanatu ta harare ta tana faɗin, "ke dai kika sani".
Ɗan langaɓe kai tayi cikin muryan tausayi tace, "na rantse da Allah ki yarda dani My Ruman, wlh aiki ne ya ɓoye Ni but kiyi haƙuri ban sake wa".
"To ya na iya, yanzu wuni kika zo min ko kuwa?" Rumanatu tace hakan tana tsare ta da idanuwan ta
Sai da ta yatsina fuska kafin tace, "daga wajen aiki nayo nan fa, wlh damuwa ce dani nake neman me bani shawara".
"Shegiya ashe ba don Ni kika zo ba matsalan ki takawo ki? ke wlh baki da mutunci Ayush". Tafaɗa tana dariya
"Ke dai bani shawara kawai ki ajiye wannan a gefe, babban matsala ce dani wlh".
"To ina jin ki fesa min naji".
Sai da ta sauke numfashi kafin tace, "wlh wani Guy ne nake faɗa miki na kamu da mahaukacin ƙaunar sa, don bazan iya ce miki son da nake masa me hankali bane, yau rana ɗaya na gansa amma wlh baki ga yanda na kasa samun nutsuwar zuciya ba".
Dariya Rumanatu ta sheƙe dashi har da tafa hannayen ta, "Wayyo Allah ki ce yau kin samu wanda ya susutar dake? tirƙashi zamu sha biki kenan".
"Ke ba nan matsalan take ba, bari dai in warware miki komi don ki fahimce ni da kyau". Ayush taƙarishe maganar tana muskuta zaman ta
Tiryan-tiryan tafaɗa mata komi har shirin su da Shakira
Sai da ta gama Rumanatu tace, "lallai kin taro match baki da ƴan wasa, amma kinga Ni shawaran da zan baki tunda har kin samu Baffa ta hanya me sauƙi haka, ga shi har kun zama friend soyayya ce kawai ta rage wanda hakan ba wani matsala bane a wurin ki na sani, to me zai hana ki ƙyale shi wannan Guy ɗin da kika gani, kinga fa kince min Familyn su ɗaya, kar ki je kiyi saki na dafe".
Izuwa yanzu fuskar Ayush ya sauya da matsanancin damuwa, cikin sanyin murya tace, "wlh nima haka na gani Ruman, sai dai kuma matsalan yanda zuciyata ta kamu da ƙaunar Usman na haƙiƙa fiye da Baffa, wlh a yanda nake ji a yanzu dai zan iya rasa komi nawa don in mallake sa, Usman ba irin mazajen nan da mata zasu gansa su ƙyale bane, wlh kinji na rantse miki ya wuce gaban kwatance, amma baza ki gane hakan ba sai idan kinyi ido biyu dashi zaki gane irin su ne mazan nan da samun su babban nasara ne a duniyar mu, kin san me? Wlh kyau dai Usman bazai nuna wa Baffa ba, fari ne kaɗai zan iya cewa Usman ya ɗara Baffa domin babu maraban su, amma kuma wayewan su tasha bamban matuƙa, duk da Baffa shima wayayyen saurayi ne wanda duk macen da ta same sa ta gama Sa'a, sai dai abinda yafi jan hankali na akan Usman kasancewar sa yayi rayuwan out side, that's why dole su bambanta nesa ba kusa ba, uhmmm baza ki gane ba amma wlh zuciyata ta kamu, domin ko wacce zuciya da abun da tafi ƙauna, Ni shi nake so ba wanin sa ba". Ayush taƙarishe maganar da dafe setting ƙirjin ta
Jinjina kanta Rumanatu tayi tana kallon Ƙawar nata cike da tausayi, domin ba kaɗan ba ta bata tausayi don sosai ta hango iya gaskiyar ta a idanun ta, so babban cuta ne ga duk wanda ya kamu da ita dole ya zama abar tausayawa
"Gaskiya kina cikin wani hali Ayush dole in tausaya miki, domin kuwa nima na shiga wannan halin kafin in auri Musbahu, amma Ni abinda nake ganin ya dace kiyi yanzu, ta yanda kika bi da Baffan ta nan zaki bi da Usman ɗin.."
Tun kafin ta gama kai aya a zancen ta Ayush ta katse ta da faɗin, "Ruman yanda nake faɗa miki Usman ya bambanta da Baffa nesa ba kusa ba, a halayyan su daban ne sosai, a yanda Shakira ta faɗa min ta ce mugun me zafin kai ne, yana da tsananin miskilanci fiye da tunanin mutum, be da harka ko kaɗan, wlh Ni kaina da na ganshi na yarda da hakan don banga alamun zai iya saurarona ta wannan hanyan ba". Sai kuma ta girgiza kanta taci gaba da faɗin, "Inaa! kwarjinin sa ma bazai bar Ni inje ba".
Numfashi Rumanatu ta saki tana kallon Ayush ɗin, "To yanzu ya kike so ayi?".
"I don't know Ruman, shawaran ki nake nema".
"Ok Ni dai shawarana a nan kawai kibi sa a social media, idan har ya kula ki sai ki faɗa masa abinda ke zuciyar ki, kar ki tsaya tamkar na wannan ki ce zaki ƙi sanar masa, duk da haka ki bani time sai mu san abun yi ko? Ai shawara bazai gagara ba za mu samu mafita".
Murmushi Ayush tayi tace, "Yauwa my Ruman shiyasa nake son ki, I know zaki iya wlh, yanzu ki bani Numban ki so that mu riƙa communicate, wancan Numban taki idan na kira ba ta shiga".
"Wlh kuwa, wayan faɗi tayi shiyasa ai". Rumanatu taƙarishe maganar nata tana amsar wayan Ayush ɗin ta soma ƙoƙarin saka mata Numban
Daga nan hira suka soma yi don Ayush tace mata "ba yanzu zata wuce ba," don haka Rumanatun ta miƙe domin ta girka mata wani abun, tare suka shiga kichen ɗin tana taya ta.
⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫
Ƙarfe 06:01pm. Ɗahira ta gama komi nata ta haɗa kan files ɗin dake gaban ta, sannan ta ɗau jakan ta tare da files ɗin ta fito cikin Office ɗin nata, rufewa tayi tana juyowa shima Usman ya fito daga office ɗin sa riƙe da kai yana yamutsa fuska
Idanun su ne suka haɗe waje ɗaya yayinda gaban ko wannen su yayi mummunan faɗuwa, musamman ma na Usman wanda ya kasa jurewa har sai da ya runtse idanun sa zuciyar sa na masa wani irin ƙunci
Ya tsani wannan yanayin a koda yaushe da yake rinskan sa, that's why ya tsani ganin Ɗahira sabida duk idan idanun sa zasu shiga nata to tabbas sai ya rasa nutsuwar sa tare da bugawar zuciya
Buɗe idanun sa yayi tare da sake tamke fuska yana kallon bayan ta da har ta buɗe Office ɗin kusa da ita ta shige
Dogon tsaki yaja ya janyo ƙofan sa yayi gaba cikin tafiyan sa na taƙama.
Office ɗin Dr. Rahab abokiyar aikin ta tashiga, files ɗin dake hannun ta takai mata ta fito ta nufi hanyan da zai sada ta da Lifter
Usman na ciki yana ƙoƙarin danna numbobi ta'iso wajen, idanun su ne suka sake haɗe wa waje ɗaya, yayinda suka bi junan su da wani irin kallo me cike da tsantsan tsana
Duk da yanayin da yake ji da ganin wannan idanuwan nata masu matuƙar faɗar masa da gaba but yaƙi ya ɗauke nasa idanun a kan ta, illa aika mata da saƙon tsanar da yake yi
Har sai da ƙofan ta kusa rufe wa kafin Ɗahira ta janye idanun ta taci gaba da tafiya ta nufi Steps, ta gummaci ta ɓata time ɗin ta wajen sauka ta bene da ta haɗa hanya da mutumin da zuciyarta tafi tsana a rayuwan ta
Ko kaɗan ba ta ƙaunar haɗuwa dashi a rayuwan ta, musamman yanzu da ta ganshi ya fito a Office ɗin dake kallon nata wanda ta tabbatar da cewa nasa ne, wani irin baƙin cikin hakan taji a ran ta
Tsaki ta dinga jerawa har ta sauka ƙasa ta fita daga cikin Hospital ɗin ta nufi parcking lot, motan ta tashiga taja tabar asibitin gaba ɗaya.
[5/29, 6:40 AM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTORS*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏼
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
```( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. *GOMA'S FAMILY*_
*EPISODE Nineteen*
Horn tayi a bakin tanƙamemen Gate ɗin gidan su
Babu ɓata lokaci me gadi ya buɗe mata
Ta kutsa hancin motan cikin gidan, yayinda ta nufi parcking space Direct ta faka motar, jakar ta; ta ɗauka da wayan ta tafito ta rufe ƙofan motan tare da saka mata keey, mayafin ta tagyara kana ta nufi cikin gidan cikin tafiyan ta na tsantsan yanga wanda ya zame mata jiki
Usman dake cikin motan sa yana amsa Call yabi ta da kallo time ɗin da tazo ta gifta shi, kallon ta kawai yake yi har ta ɓace wa ganin sa kafin ya ɗauke kansa, a ransa kuwa yana jan tsaki cike da jin haushin kallon ta da yayi, shi mamaki ma take bashi ta yanda take irin wannan tafiyan tamkar baza ta taka ƙasa ba, kai da gani kasan tana ji da tashen ƙuruciya da tsantsan yanga, wanda shi a ganin sa iya Shege ne, be san cewa Nature ɗin ta bane hakan, ya riga ya zama jinin jikin ta, har a maganar ta da komi nata cikin yanga take yin sa tare da sanyin jiki sosai, shiyasa komi nata daban ne, she has a very classy class.
Wayan sa ya janye daga kunnen sa ya fito cikin motan ya rufe, jin ana kiran sallah sai ya nufi bakin famfo na can wajen masu gadi yayi alwala ya fice a gidan zuwa masallaci.
⚫⚫⚫
Ɗahira na shiga cikin parlour'n su da sallama a bakin ta, babu kowa cikin parlour'n don haka Direct cikin ɗakin su ta nufa
Tana shiga bata zauna ba ta shige Toilet bayan ta ajiye jakar ta da wayan ta, alwala ta ɗauro ta fito
Time ɗin ne itama Fadila ta shigo cikin ɗakin don itama dawowar ta kenan, itama jakar ta ta'ajiye ta nufi Toilet ta ɗauro alwala, tazo ta shimfiɗa sallaya kusa da na Ɗahira ta tada sallah.
Ɗahira ta soma idar wa, don haka ta miƙe ta fice cikin ɗakin, ɗakin Maman ta tanufa
Tana zaune a kan sallaya tana azkar, sallaman da Ɗahiran tayi ta amsa mata tana bin ta da kallo
A kan sofa ta zauna tana kallon Maman nata har ta ida azkar ɗin
Sannu da gida Ɗahira tayi mata
Ta amsa mata tana tambayan ta "har kun dawo?"
"Eh Mama".
"So Masha Allah, what is your job? Is there no problem?"
She smiled Ɗahira and said, "It's all right, Mama."
Gyaɗa kanta ta ɗan yi kafin tace, "Then go to the kitchen and get some food, and if you leave it later, then."
Gyara kwanciyar ta Ɗahira tayi saman dogon kujeran tana ɗaura hannun ta saman kanta tace, "I'll eat later."
Aunty Amarya bata sake cewa komi ba taci gaba da addu'o'in ta, har sanda ta gama ta tashi ta fice cikin ɗakin.
Ita kuwa Ɗahira tana nan kwance tana tunane-tunane cikin ranta, kuma duk tunanin nata akan Masoyin ta ya ƙare, zuciyar ta na ƙwaɗaita mata son ganin shi matuƙa, tana son sanin ko wane ne but ya ƙi amince wa su haɗu, Allah ya gani tana ƙaunar sa itama, zata so su haɗu ko dan ya nuna mata soyayyar da yake mata a zahiri ba a cikin waya ba, har yanzu ba su taɓa yin waya ba, ko ta kira ba ya shiga, amma kuma idan ta tura text babu daɗe wa yake turo mata reply.
Numfashi taja tana juya kwanciyar nata fuskarta ƙunshe da murmushi.
Aunty Amarya da ta shigo tana kallon ta, kaɗa kai kawai tayi bata ce mata komi ba, sai da ta daidaita kanta a sallaya sannan ta sake duban ta tace, "To idan kin gama murmushin da saƙar zucin; ki tashi ki je kiyi sallah, Abbun ku ya dawo ma yana neman ki".
Murmushi kawai Ɗahira tayi tana kallon Maman nata da har ta soma sallan ta tamkar ba ita ce tayi maganar ba, tashi tayi tana sosa kanta cike da kunya da ya kama ta jin abinda tafaɗa mata, ta fice a ɗakin.
Bayan kowa ya idar da sallan sa fitowa suka yi suka hallara a kan dainning, cike da nishaɗi suke gudanar da dinnern su, kai da gani kasan suna farin ciki, musamman yanda Abbu ke ta jan su da hira yana tsokanar su don shi dama al'adan sa ne tsokanar ƴaƴan sa, yana da son yara kuma ba ya da ɗaurewar fuska ga iyalan sa.
A haka har suka gama cin abincin suka dawo Parlour suka yi zaman hira, in ka ɗauke Fadila da tuni ta shige ɗaki abun ta, don ita bata cika zaman hiran ba ne sai ta ga dama, kuma ko ta zauna baza ta ce uffan ba, wayan ta ko t.v su ne kaɗai abokan hiran ta, wani lokacin kuma idan an sako ta takan saka musu baki ko tayi murmushi, babu me damuwa da halin nata tunda ba baƙon abu bane a gidan nasu, ba ita kaɗai ba gaba ɗayan su hakan a jinin su yake, sai dai nata abun ya girmama ne, to zan iya cewa halin su ɗaya da Usman domin miskilancin ya girmama.
⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫
*Ƙarfe 11:30pm.*
Lokacin ne Hajja Fatu ta tura ƙofan ɗakin mijin ta tashiga da sallama
Be ɗago kai daga aikin da yake yi cikin Laptop ba ya amsa mata
Taho wa tayi ta samu wuri gefen gadon kamar yanda shima yake zaune, ta zauna tana kallon Laptop ɗin, duk da kuwa ba ta ganin abinda yake yi a ciki amma hakan be sa ta ɗauke kanta ba, illa ma ƙoƙarin leƙa wa da take son yi
Shi kuma jin tayi shiru sai ya ɗan ɗago kansa kaɗan ya kalle ta, ganin tana leƙa masa Laptop sai yace, "lafiya dai Hajjaju, what do you want to see?"
Ɗan ja da baya tayi cikin basarwa duk da kuwa taji kunyan kama ta da yayi, sai lanƙwaye murya da tayi tace, "to Abban Baffa laifi ne don na leƙa naga me kake yi? Don't forget that I am also a doctor."
"Eh ke doctor CE sai aka yi ya ya? Ko an ce miki wannan aikin Hospital ne?" Yayi maganar yana yatsina fuska
"Uhmm Abban Baffa why are you like this to me? Mene ne dalilin ka na son ɓoye min sirrin ku? Kar ka manta fa Ni matar ka ce kuma uwar ƴaƴan ka, sannan a duk matan gidan nan Ni kaɗai ce wacce tayi ilmi me zurfi har kuma take ci da gumin ta, idan baku saka Ni a al'amuran ku na taimaka muku ba; to wa zaku saka? Wlh ba na jin daɗin abinda kake min kwata-kwata, na kula ko kaɗan kana ɗauka ta wata aba ce daban saɓanin yanda ni na ɗauke ka". Hajja Fatu taƙarishe maganar nata cikin tsantsan damuwa da ya nuna a muryan ta, tabbatan dai abinda mijin nata yake mata ba ya mata daɗi
Murmushi Abba ya saki cike da mamakin matar tasa, shi be ga abinda yake mata ba da koda yaushe idan taga yana aiki sai tayi ƙorafi, musamman idan ya nuna mata aikin be shafe ta ba duk lokacin da ta buƙaci taya sa, to shi me zai saka ya bata bayan wannan sirrin Business ɗin su ne da ƴan uwan sa, don tana aiki a Hospital ɗin ai ba yana nufin tasan sirrin su bane, da me tafi sauran matan gidan ne?...
"Abban Baffa, I am talking and you are listening because you have made Me nothing." Maganar ta takatse masa tunanin sa
Still murmushin yayi yace, "kin fiye rigima ke kam Hajjaju, kin ga na nemi taimakon ki ne? Meyasaka baza ki ji da naki aikin ba? Ko da ma abinda ya shafi aikin asibiti ne ai ba ɓangaren mu ɗaya ba bare ki taya ni, ki je abun ki na gode".
A fusace Hajja Fatu take kallon sa, cikin takaici da halin mijin nata da har yanzu ya ƙi ya gane tace, "haka kace ko Alhaji? Well shikenan God help".
Da gama maganar; ta miƙe ta nufi ƙofa don ficewa, duk da har aranta ta nuna masa fushin ta ne don ta san halin sa zai iya dawowa da ita, daga nan ma ya faɗa mata abinda yake yi, ita kuma ta samu damar shiga jikin sa har tasan sirrin komi nasu
Amma kuma ga mamakin ta har ta buɗe ƙofan be ce mata komi ba, ɗan juyo wa tayi ta kalle sa sai taga aikin sa ma yaci gaba dayi tamkar ma be san da ita wajen ba, hakan ya ƙara tunzura ta; ta fice tana bugo ƙofan cike da tsantsan takaici
Murmushi Abba yayi yana bin ƙofan da kallo, kana ya girgiza kansa yana maida kansa yaci gaba da abinda ke gaban sa.
Fitowan Hajja Fatu itama Shakira ta fito a ɗakin ta, kallon Mahaifiyar nata tayi cike da nazarin ta kafin kuma tace, "Lafiya Hajja me ya faru ne?"
Huro hanci tayi tana ɗaga idanun ta ta sauke kan Shakiran dake tsaye tana jiran amsar nata tace, "It's me and your father. Let's talk about it tomorrow. I'm not feeling well. What are you doing here?" Ta sauya maganar da tambayan ta
Shakira tace, "I just came out to drink water, har na fara barci ishin ruwa ya tado ni".
Bata ce mata komi ba ta nufi ɗakin ta tabuɗe ta shige
Da kallo Shakira tabi ta dashi, har sai da ta shige kafin ta janye idanun ta tanufi bakin Fridge, buɗe wa tayi ta ciro goran ruwa tasha sosai, sannan ta mayar ta rufe ta koma ɗakin ta.
.
_plz I don't get a lot of comments, if you don't like it please tell me in Dena, don ba nan kaɗai nake yi ba, can da suka fi buƙata sai in riƙa musu su kaɗai, ta comments ɗin ku kawai zan san kuna so aci gaba._
_kar ku manta Vote and share._
[5/29, 8:48 PM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR'S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL._
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* 🧝🏼
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
```( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
𝗝𝗜𝗞𝗔𝗥 𝗟𝗔𝗪𝗔𝗟𝗜 𝗖𝗘✍️
𝗪𝗮𝘁𝘁𝗽𝗮𝗱: 𝗨𝗺𝗺𝘂𝗗𝗮𝗵𝗶𝗿𝗮𝗵👈
𝗦𝗔𝗗𝗔𝗨𝗞𝗔𝗥𝗪𝗔
𝑁𝑎 𝑠𝑎𝑑𝑎𝑢𝑘𝑎𝑟 𝑔𝑎 𝐹𝑎𝑚𝑖𝑙𝑦 𝑛𝑎 𝑔𝑎𝑏𝑎 ɗ𝑎𝑦𝑎. 𝗚𝗢𝗠𝗔'𝗦 𝗙𝗔𝗠𝗜𝗟𝗬.
*EPISODE Twenty*
Da sannu rayuwa taci gaba da gudana, zuwa wannan lokacin Familyn Dr. Al'ameen suna ta shirye-shiryen zuwa Kano ne Bikin Salma (Ƴar Hajiya Laila), yanzu haka saura wata ɗaya
Kaka da kansa ya ba da odan kaya ya raba musu, wai wanda zasu ci biki dashi, matan kaɗai, daga iyaye har ƴan matan, har da su Aunty Zainab da Aunty Zulaiha sai da ya saka aka aika musu dashi, kala bibbiyu ne atamfa da Swiss less, kuɗin su kuwa zai kai dubu ɗari ko wanne, daga gani kasan kayan masu uban tsada ne, sun yi murna matuƙa, nan da nan kowa yakai ɗinki inda zai iya kai wa
Kafin ranan bikin kuwa tuni an amso musu, ranan Alhamis ƴan matan suka shirya tafiya, matan gidan kuma sai gobe juma'a za su taho, su kuma su Big Dady ranan ɗaurin auren asabar za su je, gaba ɗaya har dasu Usman, sannan kuma su dawo a ranan.
Tun 11:00am. Suka gama shirin su, ko wacce da jakan ta a hannu, har haraban gidan iyayen su mata suka rako su
Drever ya amsa jakunan nasu ya saka a bayan mota
Yusra ce ta shiga gaba, su kuma su uku a baya, drever'n yaja motan suka ɗau hanya cike da ɗoki
To dama ba wai sun saba zuwa sosai bane, kasancewar Boarding school suka yi a A.B.U Zaria, shiyasa ba su da lokacin kansu bare su riƙa ziyarce-ziyarcen ƴan uwa, kuma suna gamawa suka soma aiki, wannan dalilin ne yasa sun daɗe rabon da su je Kano, gwara-gwara ma Katsina, hutun ƙarshe da suka samu kafin su gama school a can suka yi, sai kuma suka ƙarisa sauran a Maiduguri, Kano ne dai sun shafe kusan shekaru biyar rabon da su je.
Zuwa ƙarfe 02:00pm. Tayi musu a Kano, Direct family house ɗin *General Isah Basheer Isah (Walid)* suka nufa, wanda a yanzu ake kiran sa da Granny
Gate aka wangale musu drever yaja motan zuwa ciki, be tsaya ba sai a ɓangaren su Salma, kasancewar gidan babba ne me Part-part, da ƴaƴan sa guda hudu maza da jikokin sa waɗanda suka yi aure su wajen uku duk a cikin gidan suke da zama, kuma kowa da na shi Part ɗin, sai na Granny ɗin da matar sa da suke ce mata INNA Haja.
Tun kafin ma su fito daga motan su Salma suka fito tarban su, dayake sun san da zuwan su, ƴan mata ne kusan su goma kuma duk jikokin Granny ne, a ciki har da ƴaƴan yaran sa mata da sukai aure a wani wajen
Sai kuma Shamsiyya da itama tazo tun jiya
Nan da nan suka karaɗe ɓangaren da murna da ihun ganin juna, daga baya kuma suka ɗunguma zuwa ciki
Hajiya Laila na zaune a parlour'n ta tana jiran isowar su, ganin su yasa ta washe bakin ta kafin ta fara musu maraba
Gaba ɗaya wajen ta suka isa suna gaishe ta cike da tsananin farin ciki a fuskokin su
Bayan sun gama gaishe-gaishen ne ta tashi taba su waje, nan kuwa suka ƙara ɓarke wa da Surutu ana hiran yaushe gamo, Sarkin surutu Firdausi tuni ta soma zuba ko haɗiye miyau ba tayi, tana ɗire aya take ɗaukan wani
Yau har da Fadila ba'a bar ta a baya ba, domin tayi zaman ta cikin ƴan uwa ana ta hiran da ita
Sai daga baya ne ma da Hajiya Lailan ta fito, take musu tsiya "ko abinci basu ci ba sun zauna suna ta zuba zance"
Salma ita da su Shamsiyya suka tashi suka haɗo musu abincin, duk sun baje a parlour'n suna ci suna ci gaba da hiran su cike da nishaɗi.
Ƴaƴan Hajiya Lailan ne guda biyu maza, Bashir (Abba) da kuma Yaseer suka shigo cikin parlour'n, yanzu haka ko wannen su da iyalan sa, shi Abban ne babban jikan gidan
Gaishe su suka yi cikin girmamawa, su ma suka amsa cike da fara'a da nuna farin cikin su na ganin su, har da tambayan su Baffa da Usman tare da sauran ƴan gida, duk suka amsa musu da "lafiya lau sun ce a gaishe su," daga nan suka wuce ɗakin Mahaifiyar su suka bar su nan suna ci gaba da hiran su
Ɗahira ce ta kalli Fardausi da ta cika su da Surutu, don ita ce ma ƙarfin hiran, cikin tsokana take ce mata, "Ni wlh da an haɗa ku gaba ɗaya Dady ya aurar daku, ko gidan ma sun huta da surutun ki, yarinya ko haɗiye yawu ba ta yi".
Dariya gaba ɗaya aka kwashe dashi
Ita kuma Firdausin gyara zaman ta tayi har da karkace ɗankwalin kanta tana faɗin, "me kuke ci na baka na zuba? Ai wlh marriage is time and I'm here to do, amma wlh bazan yarda a haɗa Ni da Salma ba, dole sai na zauna nima na taɓa ƴan matanci na Ni kaɗai, haka kawai ai bazai yiwu ba".
Hararan ta Salma tayi tace, "dalla yi mana shiru, Ni wlh ban san ma meyasa Dady ya ƙi tilasta miki fiddo da mijin ba, uwar ma me zaki sauna yi musu bayan ba kya cas ba kya as".
Itama dai Firdausin hararan nata tayi tace, "eh naji dai, baza ai mana auren tare ba ƴar baƙin ciki, wlh nima yanda kika fara aiki kafin kiyi aure, nima bazan yi ba sai na soma aiki na".
Tsaki kawai Salma taja tana sake kwaɗa mata harara
Firdausin ramawa ta kuma yi, har da murguɗa baki
Dama sun saba kasancewar saƙo da saƙo suke, bare kuma dama Salma tana jin haushi an ce ta fito da miji a haɗa da na sauran yayyin su biyu maza da za ayi musu aure, ita kuma Firdausi da sauran ƴan matan ba'a ce musu ba, hakan yasa take jin haushi tunda ba'a haɗa su gaba ɗaya ba
Su dai sauran sai dariya suke musu, basu tashi ba sai da aka kira sallan la'asar, sai ma lokacin ne su Ɗahiran suka tuna basu yi azahar ba, ganin ƴan uwa da hira ya shagaltar dasu
Ɗakin su Salma suka wuce, wasu daga cikin su kuma suka koma nasu Part ɗin, sallan suka gabatar kafin Ɗahira ta miƙe tana kallon Firdausi dake zaune kan sallaya, tana latsa wayan ta da aka kira time ɗin tana sallah
"Fido tashi ki raka Ni mukai gaisuwa wajen Granny da ƴar tsohuwar matar sa, tun kafin ma ya aiko".
Ɗago kai Firdausi tayi tana dariya tace, "wlh nima dai naga haƙurin sa da be aiko a kira ki ba".
"Ko dai be san ta zo bane?" Cewar Haneefa dake zaune itama kan dadduman
"He knows, tunda Ni naje na shafa masa labari har ɗakin sa yau za su zo".
Ɗahira ta murmusa tana faɗin, "Let's go. Please, I'm too tired to see him, because I'm missing him."
Salma tace, "oh wa yaga Ɗahira matar tsofaffi, Ni na kula ma tsofaffin nan duk sun fi son ki, Anya ba da ɗaya za ayi ba between Kaka and Granny?"
Dariya suka kwashe dashi sauran cike da shaƙiyanci.
Fadila da Shakira ma duk tashi suka yi suka bi bayan su Ɗahira don su gaida Granny ɗin, a Parlour suka tarar da Yusra dake zaune ita da Hajiya Laila, nan suka yi mata bayanin "za su je gaishe da Granny ne daga nan su je sauran ɓangaren su gaishe su," har da Yusran suka tarkata suka tafi.
Part ɗin Granny suka soma zuwa, lokacin Inna Haja na sallah a ɗakin ta
Koda suka leƙa suka ga tana sallah ne sai suka nufi ɗakin Granny, yana zaune kuwa yana duba ƙur'ani, shima idar da sallan sa kenan, dayake ba ya iya fita sabida ciwon ƙafa da yake fama dashi, duk da ba'a Wheel chair yake zaune ba, kuma yana iya tafiya amma ba me nisa ba
General Isah Basheer Isah (Walid) kenan, tsoho me ran ƙarfe, kai da gani kasan an zuba ƙaƙƙarfan jarumi sanda yake matashi, har yanzu kuma idan ka kalle sa zaka ga zubin jarumtar sa, don daga gani kasan da sauran ƙarfin sa sosai, sai dai kawai tsufa ne da yayi, ga furfura da duk ya cika masa kai, kasancewar sa ba me barin gemu ba shiyasa babu komi a wajen sai ƙananun gashi farare kaɗan-kaɗan.
Shigowar su yasaka ya ajiye ƙur'anin yana ɗago kansa tare da cire medical Glass ɗin sa, fuskar sa yalwace da murmushi yake amsa gaisuwar da suke masa tare da bin su ɗaya bayan ɗaya yana kallo
Cikin tsokana Firdausi tace, "wai kuwa ka gane su Granny? Ko sai na maka bayani tunda naga idanun naka sun tsufa da yawa?"
Dariya yayi kafin yace, "ke kam baki da kirki Nana Firdausi, yo idan har bazan gane su ba kema ai bazan iya gane ki ba".
Gaba ɗaya fashe wa da dariya suka yi, ban da Firdausi da ta kwaɓe fuska tana ma Granny shagwaɓa.
Nan ya soma tsokanar su Ɗahira bayan ya tambaye su mutanen gida, suka zauna suka biye masa suna ta kwasan dariya
Itama Inna Haja da ta idar da sallan, ɗakin ta shigo ta zauna ana yi da ita.
Sai da suka daɗe a nan shashin kafin suka wuce sauran sasukan, suka gaishe da su, a Part ɗin Baba ƙarami suka shantake sukai ta kwasan hiran su.
Washe gari da safe sai ga Hajiya Ikram ta bugo sammako, ita da ƙannin Shamsiyya, sai Babban ƴar ta wacce take aure a Katsinan Aunty Mimi da nata yaran sun taho tare
Zuwa wajen sha ɗaya su Aunty Zulaiha da Aunty Zainab su ma suka zo, gida sai sake cika yake yi kowa ya hallara.
Da yamma sai ga su Aunty Amarya, Hajiya da Umma sun taho, ban da Hajja Fatu, ita zata biyo su Big Dady ne washe gari ranan auren, idan kuma za su koma su Big Dadyn sai su Hajiya su bi su, ita kuma Hajja Fatu za su dawo ranan Lahadi tare da su Ɗahira.
Tunda safe su Ɗahiran ma suka tafi yawon su, babu inda ba su zagaya ba, ba su nan ba su can, ko zama ba sa yi, sai da dare ne ma da suka dawo daga yawon na su suka ga su Hajiya sun zo.
The following day aka ɗaura auren Amarya Salma, sannan aka wuce gidajen Sauran amaren yayyin su aka ɗaura na su
Biki yayi biki, mutane tamkar tsaki, haka suke ta ɓulɓulo wa, su Yusra ma ko ganin ƙeyan su ba ka yi, ana can ana ta shan biki.
Da dare tare da su aka kai amarya gidan ta, sai dai a cikin su babu wacce ta kwana sai Yusra tunda za'a kwanar ma Amarya, tare da sauran dangi da aka bar mata.
Zuwa washe gari da yamma suka yi haraman tafiya, ƙarfe 06:30pm. Suka shigo Kaduna.
*WASHE GARI*
Monday tushen aiki, tunda Ɗahira ta shiga Office ɗin ta yau bata huta ba, sosai take da Patients waɗanda zata duba, shiyasa tunda ta shiga ta duƙufe take faman aiki, gaba ɗaya ta gama gajiya ga shi taƙi huta wa kanta.
Ƙarfe 05:30pm ta tashi, ta fito daga Office ɗin ta tarufe da keey tayi hanyan Lifter, dayake ta gaji sosai shiyasa tafiyan nata ma sai ya sauya salo, dama gata akwai yanga bare kuma yau me lasisi ne, buɗe Liftern tayi ta shige, tana shirin rufe wa sai ga Usman cikin saurin shima ya shigo, be ma kula da ita ba sai da ya shigo ɗin idanun su suka faɗa na juna, da sauri ko wannen su ya janye nashi suna haɗe rai alokaci ɗaya
Ƙofan fita Ɗahira tayi zata fice, don baza ta iya haɗa hanya dashi ba, sai dai kafin takai ga ficewar sai ji tayi ya jawo ta kiiiiiii.. ta dawo baya, ya jefar da ita wanda tuni ta je ta haɗe da jikin Liftern, saboda azaba ta ƙwalla ƙara tana dafe ƙeyan ta da sauri
Ko a jikin sa sai ma danna number da yayi ya rufe ƙofan, sannan ya tsayar da Liftern cak, yana juyowa gare ta fuska a haɗe..
[5/30, 11:09 PM] Oummu Ɗahirah: 💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
*FAMILY DOCTOR'S*
🩺
💎💎💎💎💎💎💎💎💎💎
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*NAFEESAT RETURN*
🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*MALLAKAR:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL._
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏼
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
```( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
𝗝𝗜𝗞𝗔𝗥 𝗟𝗔𝗪𝗔𝗟𝗜 𝗖𝗘✍️
𝗪𝗮𝘁𝘁𝗽𝗮𝗱: 𝗨𝗺𝗺𝘂𝗗𝗮𝗵𝗶𝗿𝗮𝗵👈
𝗦𝗔𝗗𝗔𝗨𝗞𝗔𝗥𝗪𝗔
𝑁𝑎 𝑠𝑎𝑑𝑎𝑢𝑘𝑎𝑟 𝑔𝑎 𝐹𝑎𝑚𝑖𝑙𝑦 𝑛𝑎 𝑔𝑎𝑏𝑎 ɗ𝑎𝑦𝑎. 𝗚𝗢𝗠𝗔'𝗦 𝗙𝗔𝗠𝗜𝗟𝗬.
*EPISODE Twenty One*
Wani kallon tsana yake aika mata dashi, sai dai ya kasa magana duk da kuwa so yake yi ya faɗi wani abun
Ɗahira a hankali ta ɗago kanta her eyes filled with tears, and she looked at him, yanda ya haɗe rai yasaka ta kasa faɗa masa magana, illa haɗiye yawu da tayi tana aika masa da kallo me cike da tsana gami da haushin sa
Sake haɗe rai yayi, cikin izza irin ta shi yace, "har ke kin isa ki kai ƙara ta wajen iyayena ko? Kina jin kin girma kin zama macen da zaki iya ja da Usman Noor Al'ameen?"
Ɗauke kanta tayi a kansa tana sake dafe ƙeyan ta
Tsawa ya daka mata da faɗin, "Am I not talking? Uban wa ya baki ƙwarin gwiwan da zaki kai ƙara na wajen iyaye na?"
Sosai Ɗahira ta tsorata da yanda ya daka mata tsawa, nan da nan jikin ta ya soma rawa ta ƙanƙame jikin ta tana hawaye
Matsowa kusa da ita yayi yana saka hannu ya jawo kanta ta yanda za su haɗa idanu, sosai ya matse mata kan, wanda ya sa ta dinga zubar da hawaye tare da rufe idanun ta gam
"This is the first and last time you would do such a thing to me again, domin Ni ba abokin wasan ki bane, idan ba haka ba uhmmm".
Sai ya ci je leɓen sa na ƙasa yana sakin kanta, ya juya ya danna Numban Liftern yaci gaba da tafiya, yana kai su downstairs ya buɗe ya fice.
Ɗahira dake durƙushe a ƙasa tana ta shashsheƙan kuka, ko motsin kirki ta kasa yi sabida baƙin ciki da ƙuncin da ya cika ta, ji take yi tamkar ana tsaga magudanan jinin ta ana ƙara rura wutan tsanar da take yi masa
"Shin ta ya ma zata iya bari wani ƙaton banza ya zauna yana mata irin cin mutuncin nan? Kamar ta? Me ta tare masa ne?"
Ta jima a haka kafin ta share hawayen ta tare da gyarawa eyeglasess ɗin ta zaman sa, ta miƙe ta buɗe Liftern ta fice, a hankali ta taka har gaban motan ta tabuɗe ta shige, ja tayi tabar Hospital ɗin.
Tuƙin take yi amma hawaye na kwaranya a kyakkyawar face ɗin ta, maganganun Usman ne ke dawo mata kwanya, a haka har ta kai gida tayi parcking motan, sai dai ta kasa fitowa sai ma sake fashe wa da tayi da sabon kuka, sosai ranta ke suya da abinda yayi mata, ta rasa meyasa tarasa ƙwarin gwiwan da zata iya mayar masa da martani, alhanin tayi wa kanta alƙawarin baza ta sake barin sa yaci mata mutunci ba, ko kaɗan baza ta iya jure wa ba, shiyasa abinda yayi mata yanzu yayi mugun ɓata mata rai
Kifa kanta tayi saman sitiyarin motan tana rufe idanun ta ruf, tunanin abinda zata yi masa ta huce take yi, but ta kasa, don haka ta ɗago kanta ta share fuskarta tare da gyarawa ta fito daga motan, rufewa tayi ta wuce Part ɗin su.
A ranan sukuku ta wuni ta kasa taɓuka komi, duk idan ta saki jikin ta sai ta tuna abinda ya faru ɗazu, sai kuma gaba ɗaya ta rasa fara'an ta
Aunty Amarya da ta kula da yanayin ƴarta, tayi mata magana, but Ɗahira ce mata tayi, "babu komi". Dole ta ƙyale ta don ta san halin ta akwai zurfin ciki wani lokacin.
Washe gari tana tashi daga barci ta kunna wayan ta, ta soma cin karo da saƙon masoyin ta, yawanci duk complain yake mata a kan rashin reply ɗin ta, kasancewar tunda ta dawo daga aiki ta kashe wayan bata sake kunna wa ba
Murmushi kaɗai tayi ta ajiye wayan ta shige Toilet, sai da tayi wanka kafin ta dawo ta mayar masa da reply ɗin, sannan ta shirya cikin doguwar riga abaya fara me kwalliyan stone da ratsin ja, ta yane kanta da gyalen sannan ta fito
Ɗakin Aunty Amarya ta shiga, tayi mata sallama zata tafi, har ta kai bakin ƙofa ta kira ta tana tambayan ta "taci abinci?"
Dayake Ɗahira ba me yawan yin ƙarya bace don bata saba ba, sai tace mata "a'a but zata ci idan taje can".
Hararan ta Aunty Amarya tayi tace, "yi maza je kici abinci kar in saɓa miki"
Dole ba don ta so ba ta'amsa mata da "to". Sannan ta fice
Kan dainning ta wuce ta zauna ta soma haɗa tea, shi ne kaɗai abinda zata iya saka wa a bakin ta don ba daɗin jikin ta take ji ba, ga kanta dake ta faman sara mata sakamakon kukan da tasha jiya.
Fadila ne ta fito itama ta zauna akan dainning ɗin ta hau haɗa abun karin ta, sai da ta gama sannan ta kalli inda Ɗahira take a karo na biyu tun zuwan ta wajen, tun jiya ta kula da yanayin ta kamar tana cikin damuwa, sai dai kuma miskilanci ya hana ta tambayan ta, yanzun ma ganin Ɗahiran ta tafi tunani ta kasa shan tea ɗin ne ta kalle ta tace, "Sister, are you all right? What's wrong with you?"
Ɗago idanuwan ta tayi ta kalli Fadilan kafin ta kau da kai tana sauke numfashi a hankali, ɗaukan tea Cup ɗin tayi tana bata amsa da faɗin, "nothing, I am thinking something".
Fadila bata sake magana ba duk da kuwa bata gamsu ko kaɗan da amsar ta ba, sai ma ci gaba da tayi da yin breakfast ɗin ta.
Miƙe wa Ɗahira tayi tare da ɗaukan jakanta tayi hanyan fice wa, a Steps ta haɗu da Baffa zai yo Part ɗin su, sai ya tsaya yana kallon ta, yayinda itama ɗin ta tsira masa idanu, kafin kuma ta ɗauke nata ganin yanda yake mata kallon ƙurilla, ɗan dai-dai ta fuskarta tayi tana sakin murmushi tace, "Good morning my brother".
Be amsa ta ba illa jeho mata tambaya da yayi, "What is wrong with you, my dear? What happened to your swollen eyes?"
Har a time ɗin murmushin fuskarta be gushe ba tace, "Yaya babu komi.. it's just that I'm not feeling well"
"Shi ne kika yi kuka?" Ya sake jeho mata tambayar
Shiru tayi tana sauke kanta ƙasa
Sake matsowa kusa da ita yayi yana bin ta da kallo, sosai suka yi kusanci da juna, hakan yasa har suna jin hucin junan su
Da sauri ta ɗago kanta ta zuba masa manyan idanuwan ta, sai tayi saurin ja da baya gaban ta na matsanancin faɗuwa da ganin wasu abubuwa cikin idanun sa, wanda ta kasa fassara su illa saka ta a matsanancin faɗuwar gaba da suka yi, saurin runtse idon ta tayi saboda yanda ƙirjin ta ke sake bugawa sosai, ƙarar sahun takalman da taji yasa ta buɗe ido a lokaci ɗaya
Gaba ɗayan su daga ita har Baffa suka bi Usman da kallo, wanda yake dumfaro wajen su shima idon sa a kansu fuska a turɓune
Ɗahira ɗauke kai tayi daga kallon sa, tana mayar da idanun ta gefe
Lokacin har Usman ɗin ya iso wajen suna gaisa wa da Baffa, iyakan gaisuwa ya haɗa su ya wuce ya nufi hanyar Part ɗin Kaka
Idanu Baffa ya aza kan Ɗahira yace, "meyasa kike son min ƙarya ƙanwata? Kin san duk halin da kika shiga dole ne na gane? Sabida kin kasance mace me fara'a, wanda ba komi ne yake ɓata mata rai ba, kin kasance me juriya me ɓoye baƙin cikin ki ga maƙiya, why kike son nuna gazawan ki?"
Itama idanun ta da suka cika taf da hawaye ta mayar kansa
Ganin ƙwalla cikin idanun ta sai hankalin Baffa yayi mugun tashi, nan da nan ya rikice da tambayar ta yana saka hannu ya riƙo mata hannayen ta
Bata yi yunƙurin hana sa ba, illa lumshe idanu da tayi tana matse bakin ta, buɗe idon tayi cikin rawan baki tace, "How can you tell you what is wrong with me? What have I done? How can Yaya Usman hate me? Meyasa yake son muzguna ma rayuwa ta? Shin na taɓa yin masa laifi ne a rashin sani?" Taƙarishe maganar cike da ɗacin zuciya hawayen na silalo mata daga kuncin ta
Sake damƙe hannayen ta yayi cikin nasa, cike da sanyin murya yace, "Ƙanwata ki dena saka damuwa a kan abinda Usman yake miki, babu abinda kika yi masa, kawai Allah ne be haɗa jinin ku ba, amma insha Allahu wata-rana sai yayi alfahri dake a rayuwan sa, tabbas watarana komi zai wuce my dear, ki saka wannan a ranki zaki ce na faɗa miki, duk inda akwai jini dole ne akwai ƙauna, ke ɗin ƴar uwan sa ce, dole zai so ki kuma zai yi nadamar hakan, Plz ƙanwa ta wannan ya dena ɗaga miki hankali, I'm not happy to see you in this situation. wlh ina ji kamar zan mutu duk sanda na ganki a damuwa, ko kaɗan ba na jin daɗi".
Murmushi ta saki hawayen ta na sake silalo wa, cikin farin ciki tace, "haƙiƙa shiyasa nake sake alfahari da kai yaya, wlh billahi kai kaɗai ka ishe Ni a matsayin Yaya, ina son ka yayana ina matuƙar son ka fiye da yanda kake so na! insha Allahu kuma bazan sake damuwa da ko wani abu da ya nuna min ba, domin kai kaɗai ka ishe ni".
Murmushi sosai Baffa yake yi sakamakon jin zantukan ta, tsaban farin cikin jin kalman so a wajen ta, be san sanda ya janyo ta ya rungume ta ba; duk da kuwa ba yau ya soma jin hakan a wajen ta ba
Sosai Ɗahira ta zaro ido da ganin abinda be taɓa faruwa da ita ba, tayi saurin jan jikin ta tana matsawa da sauri
Sai shima a nan ne ya gane abinda ya aikata, yayi saurin saka hannu yana sosa kai cike da murmushi a face ɗin sa yace, "I'm so sorry Ƙanwata, wlh na manta ne".
Murmushi tayi kawai tana kallon sa, sai kuma ta gyaɗa masa kai
Hakan sai yasa yaji daɗi sosai, don be yi tunani hakan daga gare ta ba, a kullum faɗa masa take yi ba ta ƙaunar irin wannan rayuwan, duk da shi a wajen sa ya saba sosai ga friends ɗin sa da yayi school tare da su, irin wannan rayuwan wayewan shi ne Baffa ya taso dashi, babu ruwan sa don ya rungume mace, amma tun sanda Ɗahira ta soma taka masa birki shima ya rage yi, duk wani halayen sa mara su kyau da yasan za su ɓata mata rai, ya dena su, duk sabida farin cikin ta, shiyasa a kullum sake ji yake yi ƙaunar ta na ƙara wanzuwa a cikin ƙalbin sa, idan har ya same ta a matsayin matar sa kuwa; to, tabbas ya gama dace a rayuwan sa, ita ɗin haske ne cikin rayuwan sa, zai so ya kasance da ita har abada a duniyar sa..
"Yaya mu je kar muyi late". Tayi maganar tana kallon Wrest watch ɗin dake ɗaure a hannun ta
Murmushi yayi kafin yace, "tom dear".
A tare suka fita daga gidan.
⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫
Washe gari aka wayi gari Kaka be da lafiya, zazzafan zazzaɓi ya tashi dashi, sosai hankalin iyalan gidan ya tashi, nan da nan aka ɗunguma aka yi asibiti dashi
Su Ɗahira suna can labari ya riske su, ai nan ko wannen su ya kiɗime, domin ba ƙaramin ƙaunar Kaka suke yi ba, ko kaɗan ba sa son abinda zai taɓa sa, duk da kuwa ya tsufa amma suna matuƙar ƙaunar sa; ba sa son su rasa sa, ga shi be cika ciwo ba shiyasa hankalin su ya tashi da ganin yanda jikin sa yayi mugun zafi.
Gaba ɗaya iyalan gidan sun hallara a bakin ƙofar ɗakin da aka shiga da Kaka, kowa hankalin sa a matuƙar tashe, da yawan su sun kasa zama sai zagaye suke yi, irin su Ɗahira kuwa sun kasa jure wa sai sharan hawaye suke yi.
Su Abbu na ciki su ne masu duba shi, su kansu hankalin su ya gaza kwanciya, sabida halin da suka ga Kaka ya shiga, sun kasa shawo matsalar sai faman zufa suke yi.
0 comments:
Post a Comment