Motsi kadan sai ta daga labule ko zata ga shigowarsa amma shiru. Dawowa tayi falo ta shimfida abin sallah don tana gudun kada ya dawo ya shige daki bata sani ba. Tayi raka'a takwas duk biyu tayi sallama ta sake tashi ta daga leka wajen, wannan karon ruwa akeyi kamar da bakin kwarya tayi ajiyar zuciya...daya daga cikin lokutan amsar addua kenan sai ta koma kan abin sallar ta fara addua. Tana yi tana kuka bukatar tata bata wuce Allah Ya shirya mata Junaid ba. Jin alamar shigowar mota gidan yasa tayi saurin kashe fitilar falon ta koma gefe ta tsaya. Bata dade ba taji ya bude kofar a hankali ya shigo da sanda kamar wani barawo. Mamaki ne ya kamata yadda yake da key din kofar bayan ta rufe ta sannan ta kwashe duka keys din. Yana kokarin hawa sama ne yaji ta haske masa fuska da touch light din wayarta....wane dan kut....maganar ce ta makale a bakinsa ganinta a tsaye fuskar nan kamar bata taba dariya ba. Duk da a buge yake amma sai da gabansa ya fadi.
Saukowa yayi yace Mommy ina wuni...wunin uwarka Junaid? Nace wunin uwarka. Matsowa tayi ta cire hannu ta kwada masa mari har sau uku sannan ta koma ta zauna idanunta cike da hawaye.
Bai iya cewa komai ba don yasan bashi da gaskiya. Yana kallo tana masa kukan nan da ya tsana har cikin zuciyarsa yake jin abin. Mommy ya kira ta a hankali bata ko kulashi ba sai da tayi mai isarta ta tashi ta haska masa agogon bango. Karfe nawa yanzu ta tambayeshi. Hudu da minti ashirin ya bata amsa kansa a kasa. Mu je kayi wanka kawai tace masa. Ba musu ya hau sama tana bayansa yana tangadi amma yana iyaka kokarin dannewa wai kada tace ya sha wani abu. Suna zuwa kofar dakin tace idan kayi wanka kayi alwala ka sauko ina jiranka.
Daki ta wuce ta kalli maigidanta da yake ta uban minshari ta ja dogon tsaki. Ita kam kudi bai zamu musu komai ba sai silar watsewar tarbiyar yaronta. Allah Yasa ma yaran basu da yawa su uku ne. Babbar Nafisa tayi aure itama mai bin Junaid din
Hamida tana gidan mijinta. Shi kadai namiji ya zame mata jarabawa a gidan duniya. Mijinta Senator Rufai Bukar ya rike mukamai da dama har zuwa lokacin da ya fara siyasa yanzu haka karo na biyu kenan da aka sake zabarsa sanata. Ko kadan bashi da lokacin iyalinsa saboda tafiye tafiye idan yana kasar kuwa daga office sai bacci. Baya taba bincikar halin da yaransa ke ciki amma duk karshen wata zasu ji alert mai kauri a account dinsu. Gaba daya lalacewar tarbiyar Junaid bata gabansa. Alwala ta sake sannan ta tashe shi ya sauko suyi sallah a kasa tare da maaikatan gidan tunda ana ruwa.
A falon kasan ta tarar da shi yana nafila tace cikin takaici ko kunya baka ji ka gama aikin sabo ka zo ka tsaya gaban Allah kana neman biyan bukata. Masu aikata laifi bisa kuskure ma suna tsoron haduwa da Allah amma kai naka lamarin kana sane kake takewa. Alhaji dake saukowa daga bene a lokacin yace ni kuwa bana so yaro yana kokarin shiryuwa kina sagar masa da gwiwa... Alhaji kenan ta fada tana shimfida abin sallah wallahi ina dada baku shawara kai da Junaid kuji tsoron Allah. Akwai ranar kin dillaci ranar da dukiya bata da wani amfani. Daga mata hannu yayi to malama naji zan masa fada ince dai shikenan ko.
*********************
Hafsi! Hafsi!! Hafsi!!! Dagewa tayi ta sakar mata duka a baya. A gigice ta dago kai Ummati lafiya kika doke ni. Kujera ta jawo ta zauna kusa da aminiyarta, naga kin zurfafa a tunani ne. Tunda ansa rana ya kamata ki rage tunanin Saif haka. Ki kwantar da hankalinki kamar tsumma a cikin randa. Ke ko tunanin exams kike? Nima da tawa 'yar brain din ban tsorata ba sai ke. Ajiyar zuciya Hafsi tayi ta kalli kawarta Ummati wai kinsan ya mukayi da Saif kuwa jiya? Me ya faru ta tambaya cike da zumudi. Ita dai soyayyar Hafsi da Saif tana burge ta. kamar abin arziki ya nuna min hotunan wasu abokansa da sukayi da matan da zasu aura sai daga baya yace ai tunda ansa rana muma yana son muje muyi. Dadina dake sokonci kin manta mun taba hirar dake lokacin da muka ga na Aliya Yunusa duk muka ce muna so. Ke kanki kin yaba da kyan da suka yi. Gara da kika ce yabawa kinsan ko da wasa bazan iya tambayar Mama ba ma balle Baffa. Bazasu taba barina naje ba shiyasa ma na cire abin a raina, amma ina fada masa haka da fushi ya tashi rai a bace.
Ummati ta dafa kafadar Hafsi bari mu fito daga exam dinnan sai muyi shawara. Karatu suka cigaba har malamansu suka shigo ajin aka fara jarabawa.
Suna tsaye a bakin gate din makarantarsu Health Technology dake cikin birnin Kanon dabo. Ummati ta zunguri Hafsi tana waigowa ta danyi murmushin yake. Kana ganinta kasan tana cikin damuwa. Ke na samo mana mafita fa. Nan take hankalinta Hafsi ya kwanta har suka samu adaidaita sahu suka tafi gida.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐 2
A tsakar gida ta tarar da mamanta tana dinki. Bayan sun gaisa Mama ta tambayetajarabawa. Alhamdulillah tayi sauki sosai. Hmmm kinji ki wai tayi sauki sosai to a bita da addua dai. In sha Allah ta bata amsa tare da shigewa daki. Tunani kawai take yi na yadda zata gabatar da plan din da suka yi da Ummati idan ba haka ba sai dai Saif yayi hakuri. Amma tasan halinsa sarai na fushi. Gado ta fada tana juyi. Idan akwai abinda ta tsana bai wuce fushin Saif dinta ba. Ina ma dai yayi hakuri har zuwa lokacin aurensu sai ayi kowanne hoto yake so ta fada a ranta.
Sauransu jarabawa uku su gama makarantar gaba daya sai dai har yau ta kasa fadawa Mama. Hafsi ta rasa me yake mata dadi domin kuwa daren jiya da Saif yazo baram baram suka rabu. A cewarsa bai taba tambayarta komai ba sai wannan ta gagara yi masa. Da bacin ransa tayi bacci 'yar wayar daren ma da suke yi yaki kiranta da ta kira kuma yaki dauka.
Shewar Ummati ta jiyo tare da kannenta Amira da Anisa. Da sauri ta fito ta jawo hannunta suka koma daki. Ummati ta kalle ta to sarauniyar masoya yau kuma me ya faru? Tunda naji muryarki kamar zaki yi min kuka nasan an taba zuciyar. Ba kya ma tausayina wallahi naga abin har dariya yake baki. Plate din abincin da Hafsi ta zuba amma tunani yasa ta kasa ci shi Ummati ta dauka tana ci...bakinta cike da abinci tace bana tausayinki zan zo yau. Ai don nasan Baffa yana gida yau ba aiki ne ba bari zaiyi ki fito ba. Ni fada min me ya faru. Hafsi ta zauna kan dadduma tace akan zuwa daukan hoton nan ne fa. Kwarewa Ummati tayi tana kokarin yin magana. Amma dai ke anyi banza wallahi Hafsi, ina ce tun last week muka rufe zancen nan. Ajiye plate din tayi ta tashi ina zuwa...ganin zata fita Hafsi ta bita da gudu tsaya don Allah ina zaki. Ko sauraronta bata yi ba ta shige kitchen wurin mama. Mama kinga Hafsi ko...dago kanta tayi daga tsintar waken da take yi me tayi miki kuma ku da ba kwa rabo da fada. Wai nace mata ranar da muka gama exams tunda ta safe gare mu ranar tazo muje daukan hoto shine tace wai bazata ba. Mama tun shekaranjiya nake mata magana tana kin bani amsa shine nace bari nazo kawai na fada miki. Kun fiye shirme ke da yar uwar taki meye abin fada a nan. Kinsan halin Baffanku sarai baya son fice fice ba gaira babu dalili nasan abinda take tsoro kenan. Ummati wadda ta zauna a kasa tana taya ta tsintar waken tace Mama dama wai na tarihi nake son muyi ranar tunda kinga ni Bauchi zan....karasa mana bauchi zamu kaiki ko. Tashi tayi zata gudu Mama tace ba komai zan fada masa ranar da ku ka gama din sai kuje kuyi hoton shikenan ko. Nagode nagode nagode abinda ummati take ta fada kenan har ta fita daga kitchen din. Ita kuwa Mama dariya take sai dai bata san me yaran ke kullawa ba.
********************
Kwance yake kan makeken gadonsa yana zukar wata irin taba mai kauri da tsaho, bai ankara ba kawai sai ganinta ya yi a tsaye bakin gadon. Ah sis saukar yaushe...harara ta galla masa kafin ta fizge tabar. A jikin wandonsa ta kashe ta ai kuwa ba shiri yayi ihu tare da mikewa yana kokarin cire dogon wandon. Sis don mugunta sai ki kona ni me nayi miki kuma daga zuwanki. Ko da ya cire wandon saman gwiwarsa ya fara alamun tashi. Ta zauna ai kadan ma ka gani wutar can tafi wannan. Jin yanayin maganarta yasan mommy ta kai shi kara wurinta ne. Daure fuska yayi yace to idan kinzo ganewa idonki ne kinyi sa'ar gani sai ki fita....rayuwa kowa da tasa so please let me be. Duk ranar da na gaji ke zan fara sanarwa. Yana gama magana ya shige toilet tare da banko kofar da kafa daya. Har zuciyarta taji sautin ta mike a sanyaye. Zuwan Junaid America certificate kala kala ya samu banda na school harda na shaye shaye, neman mata da tsabar kin ji. Baya ganin kowa da gashi ciki kuwa harda mahaifin nasu da ya dage sai dansa yayi karatu mai tsada.
Dakin mommy ta shiga ta zauna a gefen gado tayi tagumi tana jira mommyn ta idar da sallah. Ya dai Nafisa kunyi magana da kanin naki. Hmm mommy ai lamarinsa sai addua kawai ta fada tana tabe baki. Nan ta labarta mata yadda suka yi. Mommy tace to ni dai na gaji zan sanar da Hajiyan Dangi halin da ake ciki kafin yaron nan ya dauko mana magana. Zaro idanu Nafisa tayi cikin tsoro tace Hajiyan Dangi....wai .
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐 3
Cike da murna Hafsi ta kira Saif ta sanar da shi an bata izini a gida amma sai ta gama exams. Yayi matukar farinciki da jin hakan. Hafsi kyakkyawa ce ga kyan jiki. Tun farkon haduwarsu yayi ta fama da samarin da ke sonta kala kala Allah Ya taimake shi ta zabe shi kuma yayi saa mahaifinta bashi da wasa wurin sa ido akan lamuran 'ya'yansa. Duk da kasancewarta ba fara ba saboda babanta mutumin maiduguri ne amma yanayin fatarta mai kyau ne kamar 'yar hutu. Duk wanda ya kalle ta sai ya kara saboda haka Saif yake godewa Allah da wannan tsaleliyar budurwar take sonsa.
'Yan ajinsu suna ta faman rokonta su tsaya ayi hoton tarihi ciki kuwa harda Ummati amma ita duk hankalinta yayi gaba. Gefe ta jawo kawar tata. Ummati wai kin manta da abinda ke gabanmu ne yau kin tsaya sai hira kike yi. To sarkin azarbabi ko dan jan aji ai kya yi masa yasan kema kina ji da haduwa. Ki bari muyi sallama da mutane cikin mutumci. Da kyar Hafsi ta bari sukayi hotuna sannan suka wuce gida. Cike da doki tayi wanka ta debo kayan sallarta da wasu kaya masu kyau har kala hudu ta zuba a leda. Tana cikin shiryawa Saif ya kirata. Tana dauka ya suma magana.
(Matar baku shirya bane? Na kusa karasowa gidanku fa)
Ji tayi gabanta ya fadi don bata fada masa da yadda aka barta ba. Kashe murya tayi cike da shagwaba.
( Saif kada ka zo please Baffa zaiyi fada. Ka jira mu a bayan layin su Ummati idan ka iso yanzu zan fito nima.)
(Ai duk yadda kika ce haka za'ayi matar. See you soon)
A gaggauce ta fito ta ce Mama zan je gidansu Ummati daga can zamu wuce. To Allah Ya kiyaye amma don Allah banda bude jiki gaban mai hoto. To kawai ta amsa tana sauri ta fita. Hafsa! Taji mama ta kira ta ....a hankali ta juyu tace baki karbi kudin hoton ba da kudin mota ko duk saurin ne. Da gudu gudu ta koma ciki ta karbi kudin tayi godiya sannan ta fita.
Tana zaune gaban motar Saif suna ta hira sai dai gaba daya ta kasa sakin jiki sosai saboda basu gama fita daga unguwarsu ba. Karshe dai fakewa tayi ta duba kasan takalminta ta sunkuyar da kanta har sai da taji sun hau titi sosai. A gaban wani sabon gidan hoto da ake ji dashi a kano Treasures suka tsaya. Zata bude kofa ta fita Saif yace haba matar ai nine mai bude miki kofa daga yau, tunda gashi nayi sa'a kin shiga motata. Ummati da ke baya tayi shewa lallai ma Saif wato ni ko oho. To Allah bazan fito ba sai nima wani cikin ku ya bude min ai nima ina da nawa rabin ran. Dariya duk suka yi sannan suka shige ciki. Zama suka yi a reception ya gama magana da receptionist sannan yayi joining dinsu kafin azo kansu. Wai Saif yau babu aiki ne ka fito yanzu? Matar kenan Lukman na bari ya kama min kafin mu gama. Dayake aikin sa kai ne ba. Da haka nan nace ka zo a wannan lokacin cewa zaka yi aiki aiki. Ledar hanunta ya kala yayi saurin dafe kai kinsan har na manta ba taho da kayan canjawa ba. Bata fuska tayi don Allah da gaske kake? Dariya yayi mata sannan yace ina son shagwabarki matar kinga yadda kika yi kyau kuwa...buga kafa tayi a kasa ni fa da gaske nake yi Saif....nima da gaske nake yi Hafsah ya kwaikwayeta. Zanyu kuka fa dariya yakeyi sosai sanan ya tashi ke wasa nake yi suna mota just give me a minute.
Bayan ya dawo suka shiga aka bar ummati tana jiransu idan an gama na masoya sai ayi na kawaye kamar yadda ta fada.
Suna shiga mai hoton ya ce da Hafsi cikin hausar da bata gama zama a bakinsa ba zaka yi cire wanan veil ko yana nuna mayafinta. Saif ta kalla da alamar tambaya yace ta cire akwai wanda zasuyi nan gaba da mayafin. Nan fa aka rinka hotuna kala kala...babu wanda jikinsu baya taba na juna tun Hafsi tana dan jin kunya har ta saki jikinta. Sunyi kusan kala goma suna canja kaya dama ga ta gwanar kwalliya da daurin dankwali. Mai hoto yace da Saif, Alaji ba zakiyi na english wears ba amarya? Dariya Hafsi tayi tace kaji min mutum baza muyi ba. Saif yace ni nayi tunanin zaki zo dasu fa matar. Juya masa idanu tayi mai hoto yana kallonsu wannan sai bayan biki. To na yarda ya amsa mata sai tana shirin daukan mayafinta sai kawai taji saif ya cire mata dankwali ya kuma fizge mayafin ki dan baza gashinki sai muyi a haka a madadin kananan kayan tunda naga wannan rigar ta kama ki yadda yake maganar wani kasa kasa. Daure fuska tayi sosai Saif meye haka ya zaayi nayi hoto a haka. Ita saboda ma yanayin rigar bata yadda sunyi hoto da kayan ba mayafi ba. Fitted gown ce a jikinta wadda ta bude daga kasa. Saman kuwa ya kama mata kirji sosai gashi gaban yana da dan zurfi ana ganin saman kirjinta.
Shi kanshi Saif ya kadu da ganin surarta banda mai hoto da yake gefe yana ganin bati. Please matar ko daya ne ki bari muyi please, please. Bata son bata masa rai amma ba karamin haushi taji ba. A haka ta bari aka yi guda daya da kyar ta tsaya gabansa bayanta a jikin kirjinsa ya sakalo hannuwansa duka biyu ya ta gaban cikinta. Wani irin yanayi duka suka tsinci kansu shi da kansa yace ya isa guda dayan.
Da rashin fara'ar nan aka dauke su tare da Ummati wanda zasu nuna a gida. Bayan an wanke musu ya bada wayarsa aka tura masa. Ita Hafsi dama tata wayar ba wata mai tsada bace tace bata so. Wanda aka wanke ma cewa tayi ya rike duka a wajensa. Ganin duk ta bata rai bayan sun shiga mota yace Ummati ta bata hakuri. Ko da ummati taga dalilin fushin duka ta kai mata a baya shegiya Hafsi irin wannan pose haka ko ni da Lawal bamuyi irinsa ba. Hawayen da take kokarin boyewa ne suka sakko ba shiri. Saif na gani ya tsaya da ribas din da yake shirin yi da mota.... matar don Allah kiyi hakuri nima sai da nace muyi abin duk ya dameni. Bani da niyar wulakanta ki, ummati ki sa baki mana. Haka suka yi ta bata hakuri har ta dena kukan amma a zuciyarta ba karamin tsanar kanta tayi ba da ta biye masa irin wannan runguma haka kamar an shafa fatiha. Ga wani bakon feelings da takeji tunda ta hada jiki da Saif abinda ko hannunta bai taba rikewa ba. Anya tayi wa kanta adalci kuwa. Da wannan tambayar a ranta suka isa unguwarsu.
Kamar yadda suka tafi yanzu ma a bayan layi suka sauka. Haka ta shiga gida sukuku kannenta suka karbi hotunan da tayi da Ummati suna gani. Baffa ne ya kula da yanayinta Hafsa me ya faru ne duk kinyi wani iri. Kago murmushi tayi Baffa kaina ke ciwo. Daki ya shiga ya samo mata magani Mama tace sannu ai abin ne da yawa ga karatu, kinyi jarabawa sannan kuma baki huta ba kin sake fita. Ai zan baki hutun kwana biyu kafin ki cigaba da tayani dinki kinga sun taro. Baffa ya harareta nifa na gaji duk kin mayar min da yara teloli. Kowa dariya yayi harda Hafsi da ta kakalo ta dole.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐 4
A hankali yake tuki kamar yana tausayin kasa. Fitsararrun matasan Abuja ne suka cika wurin maza da mata wanda abin takaici 'ya'yan musulmi ne mafiya yawan cikinsu. Kallo ne ya koma kan hadaddiyar motar da ya shigo da ita tun kafin a gane waye a ciki. Wuri ya samu yayi parking yana fitowa aka fara ihu da tafi
Juni! Juni!! Juni!!!
Junaid ji yayi kansa ya kara fashewa. Sanye yake da wani matsatstsen jeans baki da bakin takalmi mai kyau. Farar riga ce a jikinsa mai dogon hannu amma bai balle maballi ko daya ba ana ganin bakar singlet din da yayi zanzaro da ita. Hannunsa wani agogo ne mai tsada ga bandana ya daura a kansa wanda ya tara gashi ya aski gefen hagu da dama. Kana ganinsa kaga yaron da ke ji da kudi, kyau da tsabar rashin tarbiya ko rashin sanin ciwon kai.
Junaid Rufai Bukar kenan dan senate president din Nigeria wanda yake fantamawa son ransa saboda kudi da kuruciya da ke cinsa.
Tun shigowarsa harabar club din take kallonsa kamar tsohuwar mayyar da ta kwana da yunwa. Tana son namiji mai kyau a rayuwarta gashi tun da ta fara zuwa club din bata taba ganinsa ba. Yana ta gaisawa da maza da mata tana binsa da ido har ya shige ciki. Itama binsa tayi ta sami wuri a gefe ta zauna don matan da sukayi kansa suna da yawa. Sai da taga an fara rawa ta je kusa da shi suka gaisa. Amma ke bakuwa ce ko ya tambaya yana mika mata cup cike da juice wanda aka sirka da kayan maye. Yes ta bashi amsa. Matar ta hadu don ba ya kirata yarinya ba, yasan da kyar idan bata girme shi ba. My name is Tilly beauty...sunan ya dace da ke kuwa. Ni suna na Junaid. Hmm amma naji ana kiranka Juni. Cire glasses dinsa ya yi kana mata wani shuumin kallo Juni friends dina ke kirana. Nima ina son zama daya daga cikinsu. Then you can call me Juni. Haka hira ta balle tsakaninsu karshe da suka fara buguwa da kyar suka karasa daya daga cikin dakunan da ake bayarwa haya a cikin club din.
Ganin baccinsa yayi nisa ta dauki kayanta ta saka ta kare masa kallo gaskiya Juni yana da kyau ga kudi...just what she needed. Takarda ta samu ta rubuta sunanta da phone number ta ajiye masa sannan ta fita. A waje ta hadu da kawarta Rosie suna haduwa suka tafa. Aiki yayi kyau Rosie sai munji daga gareshi. Shegiya Tilly baki da kyau fa Rosie ta fada tana dariya.
*******************
Da kyar ta samu Baffa ya barta taje gidan yayarta Hadiza kwana uku bayan ta gama exams. Suna kitchen sai hira suke yi Saif ya kira Hafsi a waya. Tashi tayi ta koma daki Hadiza tana ta yi mata tsiyar ta gudu kada aji hirarsu.
Kan gado ta kwanta sannan ta amsa wayar.
(Hello matar kin wuni lafiya?)
(Lafiya kalau ya aiki?)
(Ba dadi gaskiya. Ni missing dinki nake yi sosai yau.)
Yar dariya tayi domin itama kwana ukun da basu hadu ba tun ranar da suka je daukan hoto bata ji dadi ba. Babu abinda yafi damunta kamar yadda ta kwadaitu da son sake jin ya taba ko da hannunta ne. Ya Allah Ka kara tsare mana imaninmu.
(Ina gidan Yaya yanzu amma anjima bayan laasar zan tafi.)
dadi yaji har ransa domin kamar yadda take son kasancewa tare dashi abin yafi daga wurinsa. Karshe dai yace zaizo ya dauketa.
Bayan ta idar da sallah ta zauna gaban mudubi fuskar nan tasha fenti. Hadiza ta kalleta Hafsi amma dai kinsan bai kamata ki fita da irin wannan adon kan titi ba ko. Saurin mikewa tayi to yi hakuri Yaya na yau ne kawai nayi shaawa. Saif na zuwa yayi mata waya tayi sallama da yayarta wadda har kudin mota ta kara mata. Tana rufe gate din gidan ta tsaya ta feshe jikinta da turare mai kamshi abinda bata saba ba domin tasan rashin dacewar mace ta tsaya gaban saurayi tana kamshi irin wannan banda zunubi a addinance. Sai dai ita kanta ta rasa gane dalilinta na yin hakan. Annabi SAW yayi gaskiya da ya fada mana cewa shaidan yana gudu a jikin mutum kamar yadda jini yake gudu. Shi aikin sabo da kadan muke farawa sai a hankali ya zame mana jiki. Mu kiyaye don Allah da yadda muke langabewa jikin maza ayi hoto wai da sunan pre-wedding pictures. 'Yar uwa idan baki aure shi ba meye makomar rungume rungumen da ku ka yi duk da sunan wayewa?
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐5
A mota Hafsi ta sami Saif yana jiranta. Tana shiga wani kamshi mai dadi ya bakunci hancinta tare da sanyin AC. A kunyace ta zauna tare da gaishe shi. Matar kinyi kyau sosai ga kamshi mai dadi da kike yi. Fari tayi masa da ido har na kai ka kamshi Saif? Har kin fini ya bata amsa yana dariya.
Yana tuki suna hira bata ankara ba taji ya kama mata hannu ya dora akan gear ya hada ya rike. Tana kokarin kwacewa ya matar kina son muyi accident ne kike neman canza min gear? Cikin muryar shagwabar da ta saba magana tace da hannuna fa ka hada Saif. Au hannunki ne ma ba nawa ba. Naka ne mana amma ba'a gama baka ba sai an daura aure. Ku mata komai sai an daura aure ne? Ko kin manta ansa mana rana. Ai yanzu abinda ya rage tsakaninmu kadan ne.
Suna shiga unguwar ta fada masa su bi ta bayan layinsu Ummati sai ta sauka. Ba musu layin suka shiga da yake a tsuke yake ba mutane sosai. A nan Saif ya sami damar kebewa da Hafsi don a gidansu akwai idon jama'a. Rikota yayi ya hanata fita....matar ni fa duk kin rikita min lissafi tun ranar saturday da muka yi hoto. To yanzu me kake so ayi. Wayarsa ya dauko yana nuna mata pictures din. Hafsi ta sami tarbiya daidai gwargwado kuma shima Saif din ya fito ne daga gidan mutumci sai dai koyi da tarbiyar nasara yasa idanunsu ke neman rufewa. Ganin hotunan yasa suka fara shiga wani yanayi. Yadda ya riketa kamar ba zai saketa ba yana kokarin hada bakinsa da nata itama kuma bata yi yunkurin hana shi ba.
Tun shigowarsu layin Mal Aminu ya gane motar sai dai bai gane yarinyar da ke gaba ba saboda yadda take ta kokarin rufe fuskarta. Ganin motar ta shige wata kwanar ba hanyar gidansa ba yasa yayi mamaki kamar ya wuce sai yaga anyi parking dinta a karkashin bishiyar darbejiya shiru ba'a bude kofa ba. Karasawa yayi ya tambayeshi gidan wa yake nema tunda dai a iya saninsa gidansa yake zuwa a unguwar.
Jin ya fara kissing dinta jikinta yayi sanyi hankalinta gaba daya ya tashi. Ashe akwai ranar da zata aikata irin abinda take ji a labari tana ganin bakin masu aikatawa. Wai a zamanin yanzu a haka ne kawai masoya zasu nunawa junansu kauna. Wazu hawaye taji sun zubo mata. Hankalin Saif ya tashi...matar kiyi hakuri wallahi rudin shaidan ne amma bani da mugun nufi a kanki. Yana cikin share mata hawaye suka ji an bude kofar gefen da take zaune.....idanu ta bude a tsorace ganin waye a tsaye cikin rawar murya tace BAFFA!.
*******************
Yau ma a cikin maye ya shigo gidan anyi sa'a ma wurin shabiyu da rabi na dare ya shigo. Fito ya shigo yana yi yana karkada keys din hannunsa. Kamar daga sama yaji kira...Junaidu....ba don namiji bane da gabansa sai ya fado kasa yadda ya mugun tsorata. Cak ya tsaya kamar gunki. Don ubanka juyu ka kalleni. Mommy da ke zaune a gefe shiru tayi. Babu wanda baya tsoron Hajiya Ramatu. A kano take aure a gyadigyadi wurin da aka fi sani da dangi, shiyasa ma ake kiranta da Hajiyan Dangi.
Tsawa ta daka masa bazaka zo ba ne. A hankali ya dawo ya zauna a kan kafet. Hajiyan Dangi doguwar macece kamar mahaifisu ga jiki. Ita kadai ce mace a gidansu kuma ita ce babba. Allah bai bata haihuwa ba sai dai ta rike yara da yawa daga danginta har na mijinta. Cikinsu harda Senator Rufai kaninta. Mace ce mai riko da addini kuma mai sa ido akan tarbiya. Yanzu Junaidu wannan wannan rayuwar ka daukarwa kanka? Tana magana ta soma hawaye gidan malamai manyan mutane muka fito amma saboda giyar kudi na dibanka kana neman lalata rayuwarka. Ta kalli Mommy yanzu sai da lamarin ya baci haka kika sanar dani. Mommy dai hakuri ta ba ta. Bandanan kansa Hajiyan dangi ta fizge. Gobe kaje ka aske wannan shegen kan kuma kazo ka nuna min. Ko ci kanka bai ce mata ba haka ya tashi ya basu wuri. Yana shiga daki tabarsa ya kunna ya fara busa hayaki kai ka ce bakinsa salansar mota ne. A haka Junaid ya tuna bai yi sallar laasar, magriba da isha ba. Tsaki ya ja tare da mikewa ya nufi toilet. Haka ya yi alwala irin yadda kwakwalwarsa ta karanta masa sannan yazo ya fara ramuwar sallolin da bai ma san abinda yake karantawa ba.
A dakin da take sauka kuwa Hajiyan Dangi ce ta yanke shawarar ba zata koma kano ba sai kaninta Rufai ya dawo daga Australia sunyi magana akan Junaid. Babu abinda taki jini kamar yaro yaki ya rinka keta dokokin Allah ba tare da an dauki mataki akansa ba.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐6
Jikinta ne ya hau bari kamar wadda akayiwa wanka da ruwan sanyi a watan december. Iya karfinta ta sa ta fito daga motar har tana ture baffan nata. Da gudu ta tafi gida kafarta ko takalmi babu. Saif kasa motsi yayi a cikin motar ya sunkuyar da kansa. Baffa bai ce masa komai ba ya juya ya nufi gidansa.
Yadda ta shigo a firgice yasa Mama saurin tashi. Hafsa lafiyarki? Me ya faru? Me ya sami yayarki? Ko daya cikin tambayoyin bata amsa ba durkusawa kawai tayi a gabanta tana kuka. Amira ce ta kula da kafarta ta dama tana jini. Mama kinga kafar Hafsi jini take yi. Subhanallahi ke ko hatsari ku ka yi a hanya ne? Ana magana kinyi shiru kamar wata bebiya. Cikin Hafsi har wata kara yayi da jin sallamar Baffa. Bai jira an amsa ba yaja hannun Hafsi zuwa dakinsa. Garammm ya banko kofar har gaban su Mama ya fadi. Ihun Hafsi kawai suka ji tana bawa Baffa hakuri. Tuni Mama ta karasa bakin kofar dakin tana bugawa. Su Amira kuwa sai kuka don tun suna jin kukanta har murya ta dashe. Babu irin magiyar da Mama bata yi masa ba amma yaki budewa.
Baffa ya bude kofa Hafsi na kwance a kasa Mama ta shiga dakin hankali a tashe. Baffan yara me ya faru...ke Hafsa me kika yi? Da kyar Baffa ya iya fada mata tana ta kuka. Ita kam Hafsi hawayenta ba na zafin duka bane kawai. A yau tayi dana sanin abinda ta aikata. Tayi Allah wadarai da maza da matan da basa jin komai lokacin da suke hada jikinsu da juna alhali babu aure a tsakaninsu. Yau ina ranar son zuciya da biyewa shaidan da mukarrabansa wadanda suke tallata irin wannan watsewar da sunan wayewa. Mama da bata zagi yau duk wanda yazo bakinta dankarawa 'yar tata take yi. Tashi ki bani wuri mara mutumci tasa kafa ta haure ta. Jiki a sanyaye haka ta fita tana share hawaye.
*******************
Yau kwana biyu kenan Junaid yana wasan boya da Hajiyan Dangi da mommyn sa. Tun sallar asuba yake fita sai tsakar dare yake dawowa. Hajiyan Dangi lamarin ba karamin bata mata rai yake ba. Sai da ta cika sati a gidan Senator Rufai ya dawo. Bayan ya huta cikin dare wuraren karfe tara yaje dakin da yayar tasa ta sauka.
Hajiyarmu babbar Hajiya zama da tashi cikin girma. Kirarin da ya saba yi mata kenan yau ma bayan yayi sallama tun kafin ta amsa ya fara. Murmushi tayi tana kallonsa Rufai bazaka girma ba. Ai indai ina ganinki bazan girma ba Hajiya. A kan kafet ya zauna kusa da ita. Bayan sun gaisa tace Rufai kayi min laifi gaskiya. Nasani Hajiya kiyi hakuri don Allah. Lamarin Junaid ba karamin bata min rai yake yi ba amma na rasa yadda zanyi da yaron nan. Dole ka fadi haka mana tunda aiki yafi maka akan rayuwar iyalinka, wannan karon cikin fushi take maganar. Kana gefe kana turowa yara kudin da yafi karfin aljihunsu dama me kake tsammani ga yaro da kudi. Shiru yayi don sam baya iya mata musu kuma ma yasan gaskiya take fada masa. Tace to ni na yanke shawara ayi masa aure kawai. Tun zuwana garin nan yaron nan yake gudu na. Anya zaka iya haduwa da Allah akan yadda kayi wasarairai da amanar da Ya baka na yara? Ni bama wannan ba Rufai kaga Allah Ya baka matsayi a cikin al'ummar kasar nan kuma ni da kai munsan ba iyawarka bace tasa ka samu. Zabi ne kawai na Allah saboda haka ina dada baka shawara kamar kullum ka tsaftace dukiyarka. Ka kiyaye haram don ita kadai zata wargaza duk wani al'amarinka. Kafin ta gama magana idanun senator sun cika da kwalla. Dukiya kam suna kai suna wasa da ita son ransu. Ya Allah Ka bamu ikon gyarawa ya fada a zuci.
Gyara zama yayi to Hajiya wa kike jin za'a aura masa? Sayyada ta bashi amsa a takaice. Sayyada ya maimaita shima ban gane ta ba. Bama ka santa ba. Yar wajen Atika ce kanwar Baba(maigidanta). Tun da ta gama secondary ta dawo hannuna bana ma zata gama Buk. Yarinyar tana da hankali da nutsuwa kuma bata daukar wulakanci shiyasa nake ganin zata taimaka wajen shawo mana kan Junaidu. Har zuciyarsa yayi murna. Yace Allah Ya shige mana gaba kuma don Allah a taya mu addua.
Junaid yasha fada wurin mommy karshe tace yaje ya bawa Hajiyan Dangi hakuri. Yana zuwa bakin kofar dakin yaji maganar da suke yi da babansa. Wata dariya ce taso kubuce masa...wa yaga Junaid da auren dole. Ai ko zai dena holewarsa a waje zancen aure bai ma taso ba. Juyawa yayi a hankali tare da yankewa kansa shawarar barin garin a washegari daidai lokacin da yaji Alhajinsu yana cewa idan Hajiyan Dangi zata koma kano zasu tafi tare.
Batul Mamman
TUN KAFIN AURE💐7
Tamkar mujiya haka iyayenta suka mayar da ita. Babu mai kula ta sai kannenta suma a tsorace don sun fuskanci su Mama fushi suke da ita kada abin ya shafe su.
Zaune take kan abin sallah tana addua bayan ta idar da sallar walha. Idanunta duk sun shige ciki ga ramar da tayi saboda rashin cin abinci. Sallamar Mama taji ta dago kai a hankali ta amsa. Ko kallonta bata yi ba ta shige tana tashin Anisa ta sha magani saboda ta kwana da zazzabi. Mama ina kwana, an tashi lafiya? Kau da kai tayi amma har zuciyarta tana tausayin Hafsi. Ta kuma yarda kaddara babu yadda bata zuwa ga bawa domin duk cikin 'ya'yanta ita ce mutum ta karshe da zata yi tsammanin zata aikata abinda tayi. Auta tashi ki sha magani kinji ta fada tana shafa kanta...mama baki ji Hafsi tana gaishe ki ba ne. Tsaki tayi naji...karbi ki sha sai ki koma baccin. Ficewa tayi ta koma dakin Baffa ita ma kukan tayi na tausayin halin da yara harma da manya ke fadawa a wannan zamanin.
Fitar mama kenan Amira ta fito daga toilet ta tsugunna gaban Hafsi. Wai ni don Allah me kika yiwa su Baffa ne Hafsi? Anisa dake kwance tace yanzu ko gaisuwarta ma Mama bata amsa ba. Share hawaye tayi babu komai ku dai cigaba da taya ni addua. Tana gama magana ta tashi ta tafi dora girki don yau duty dinta ne. Ko da ta fita kannenta shawara suka yi karshe suka kira yayarsu Hadiza a waya aka sanar da ita abinda ke faruwa.
*******************
Juni ba wayarka bace take ringing tun dazu. Tsaki yayi ya sha giyar dake hannunsa kyale shi Old Man dina ne. Ai tun shekaranjiya dana bar Abuja yake nemana wai ni zaiyi wa aure...what a joke. Chuks ya kalle shi ku fa hausan nan haka kuke sai ku auri yarinya ku sakata a family way at a very young age. Chai, its disgusting. Karshe ta sami VVF wurin haihuwa kuyi mata saki.
Hannu Juni ya daga masa kai Chuks dakata bana son wulakanci. Gara mu aure muke yi da wuri kai at what age ka fara having sex. Wata irin dariya yayi har mutanen dake cikin club din suka fara kallonsu...my friend I was 13 fa. Wata yarinyar neighbour dinmu ce na ma girmeta. Ita ta koya min. Juni yace ka gani ko ashe kune manyan 'yan iskan. Kun iya bibiyar kananan yara amma idan musulmi sunyi aure sai ku ce child molestation. Hypocrates kawai.
Abeg no insult me Juni.....ai kaine ka fara zagin hausawa nasan karshe kan musulmi zaka koma.
Ha! Kai ai baka son islam Juni you drink like a fish and sleep with every prosti...kafin ya karasa Junaid ya kai masa naushi a baki. Kan kace kwabo bakin Chukwuma ya fara jini nan yan uwansa suka tarar wa Juni ashe akwai 'ya'yan hausawa. Cikin karamin lokaci sai fada ya kaure tsakanin musulmi da kishiyoyinsu na wani addinin. Ana ta fashe fashen kwalaben giya. Karshe dai sai da police suka shigo cikin lamarin duk aka kama su.
Tilly na kwance akan gado tare da wani hamshakin dan kasuwa taji waya. tayi mamakin ganin sunan Juni ta dauka cike da farinciki. Nan yayi mata bayanin yadda suka yi da police amma jin ko dan waye kuma ya jika su da kudi sun sake shi. Karshe dai yana bukatar account number dinta zai turo mata da kudi ta biyoshi Lagos. Ko sallama bata yiwa mutumin da suke tare ba ta tashi bayan taji alert....lallai Juni na ji da kudi.
*******************
Cikin kuka Mama tayiwa Hadiza bayanin abinda Hafsi tayi. Itama kukan take...wallahi Mama yanzu irin wanan masifar ake fama da ita. Ana zance ana shafar juna karshe inda kaddara ayi ciki. Mama tace abin ne ba kama ba don ni na haifi Hafsa ba amma wallahi nayi mata shaidar alkhairi. Allah Yasa mufi karfin zukatanmu. Amin Mama amma don Allah kuyi hakuri don idan muka nesanta kanmu da ita sai tayi wani abin ma babu wanda ya sani.
Hafsi da Ummati suna ta shawarwari Hafsi tace kinsan har yau babu waya ko text din Saif. Idan na kirashi ba waya a kashe abinda ya kara batawa Baffa rai kenan don shi so yake a sanar dashi a matso da bikin. To aje gidansu mana don bai isa ya jawo mana jangwam ya tsallake ya barmu a ciki. Ke ummati kila a tsoro yaji. Ai ni dadi na dake shegen son saurayi. Ni wallahi daga yau kara kama kaina zanyi har sai anyi aure.
Batul Mamman💖
0 comments:
Post a Comment