Wawan mari Talatu taji an dauketa dashi. Mommy ta sake daga hannu Hajiya ta riketa yi hakuri Salma muji abinda ya hadasu. Rosie cikin kukan makirci tace Talatu ce ta fito zata sha iska tace dakin yana tayar mata da zuciya. Tana fitowa wannan yarinyar ta nuna Hafsi, mommy kuwa ta make hannun karki sake nuna min yarinya da yatsa wallahi. Rosie ta share ta cigaba da magana kawai tana ganin Talatu sai tace mata zanga yadda zaki haifi dan shege a gidannan. Tray din da plates din da ke kai duk ta tura mata a ciki. Hajiya ko kadan bata gaskata zancen ba ganin yadda Hafsi ke kuka tace mamana me ya faru. Hafsi ta fadi iya abinda ta sani. Mommy ta kama hannunta su koma falo ayi maganar.
Sai a lokacin suka kula da yadda jini ke bin kafar Hafsi ta dama Mommy tace maza a kira mata Junaid yazo ya kaita asibiti.
Da fara'arsa ya shigo falon. Mommy daga nasa yarki dafa min indomie sai ace in kaita asibiti. Ko ta kitse albarka. Gunjin kukan Tilly yaji daga bayansa ya juya da sauri lafiya? Rosie hade rai ka tambayi matarka da take son zubar wa Talatu da ciki. Yace au ashe sunanta Talatu ai na zata Tilly ne. Muryar Mommy yaji tana kiransa. Ya zan aika a kira ka sai kazo kana wani zancen daban. Ka dauko key mukai yarinyar nan asibiti nace. Ya kalle Hafsi duk fuskarta hawaye yayi saurin karasawa gabanta. Me ya faru Hafsi garin yaya kika ji jiwo? Mommy tace ka tashi mana ka zauna kana mata tambayoyi.
Suna shiga motar Nafisa na isowa Hajiya tace ta debo su Rosie su taho tare. Amma ta taho da security don kada su zama su kadai. A motar Junaid kuwa Mommy tana ta balai ya dauko musu masifa har gida. In Allah Ya yarda sai cikin ya zube. Ga Hafsi nan ki saki jiki kiyi ta zuba masa 'ya'ya tunda su yake so. Hajiyan dangi ta gama waya da senator ta sanar dashi halin da ake ciki sannan ta dubi mommy tana bata hakuri. Junaid kuwa banda sannu babu abinda yake fadawa Hafsi. Hawaye ne wani ke bin wani a idanunta don ita kadai tasan me take ji musamman a cikinta. Ga babban mayafi ta yafa wani karin zafin a cikin.
Suna isa asibiti Junaid daukarta yayi don ganin yadda kafar taki dena jini. Emergency aka shige da ita da Tilly. Kururuwa kawai Tilly take yi ita tasan danta ya mutu. Ai kuwa basu dade ba nurse ta fito tace Tilly tayi bari. Nafisa ta rike baki cike da mamaki wato don sunji yau zaayi scanning suka bullo da wannan abin. Dariya tayi tana gyada kai sai tayi maganin mutanen nan.
Junaid yana tsaye doctor ya zare glass dinda ya shige kafar Hafsi yana ta mata sannu. Bayan an gama cirewa ansa plaster ya lura ta kasa kwanciya da kyau yace Hafsi akwai inda yake miki ciwo bayan kafar ne? A hankali ta daga kanta tace cikina. Fatar ta daye. WHAT??? Shima ya gama tsorata yayi saurin cire mayafin ya nunawa doctor din. Da almakashi ya yanke barin rigar daya kwanta akan cikin yace yi hakuri fatar bata cire ba. Ya dauko magani zai saka mata Junaid ya karba don tuni ya kule da kallon da yake mata. Dr bai ma san me yake ba ya nuna masa yadda zai shafa ya fita.
Ba karamin tausayi ta bashi ba yana shafawa tana runtse ido duk hawaye. Sai da ya gama ya duka yana hura mata cikin tuni ta hadiye kukan. Ya dago kansa sannu kinji Hafsi rabin raina. Ashe tsautsayi ne yasa nasa ki girki. Amma me ya hadaki da waccan. Fada masa komai tayi yace ba komai. Allah Yayi mana jagora.
Dr Sunusi yana fita Nafisa ta ja shi suka yi magana tace dr ina jin yarinyar nan cikin karya gareta. Yace ya akayi kika sani tace yar uwarmuce ce daga garinmu ina jin karya take ta matsu ne ta haihu sai tayi ta kiran cikin karya gashi kwanaki tayi bari baa wanke cikin ba. So nake don Allah kayi mata wankin ciki zan biya ko nawa ne. Bani da burin da ya wuce Talatu ta sami haihuwa. Ta dan matse hawaye. Dr Sunusi yace ba komai Hajiya ki kwantar da hankalinki. Yana fita Nafisa tace shegiya ai karen bana shike maganin zomon bana.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐31
Senator Rufai ranshi duk a bace da aka sanar dashi result din test din. Ya kalli Hajiya ni yanzu ya zanyi da Hafsatu? Duk irin abinda ya faru kafin a bashi aurenta gashi kuma baaje ko ina ba rayuwarsa ta baya tun kafin yayi aure tana dawo musu. Hajiya tace ni dai idan zaka dauki shawarata Rufai kabari yarinyar nan ta tare. Kullum mu kwana mu tashi da ita bata san makomar aurenta ba ai kaga ba dadi. Irin wannan ne idan iyayenta suka sani lamarin sai ya baci fiye da yanzu. Mommy tace anya Hajiya a bar shi da yar mutane kuwa? Bafa kowacce mace bace zata yarda ta zauna da mutumin da yake da da a waje ba. Wata ko dan kishiya bata so bare dan kafin fatiha. Senator yace to ku bani zuwa wata asabar din sai a kaita. Kisa su Hamida su tambayeta irin kalar motar da take so ma. Mtsw Ya danyi tsaki yaron nan bai min adalci ba wallahi. Gara tun da sauran mutumci na naje har gida muyi magana da babanta.
Zaman dakin duk ya isheta tana ta canja tashoshi babu wani abin kallo ta mike ta daga labule tana kallon waje. Tun jiya da su Nafisa suka zo da nurse bata sake fita daga dakin ba, Nafisa dai ta fada mata zasu dawo ta kai Talatu scanning. Tun dazu take jiran zuwansu ko ta sami abokin hira. Su mommy suna iya kokarinsu wurin debe mata kewa sai dai kuma suna cikin damuwar maganar cikin nan. Tana dan tunaninta ne ta kalli kasa suka hada ido da Junaid. Wani abu ne ya ratsa mata zuciya har kafarta. Murmushi yayi mata tayi saurin sakin labulen. Ta koma ta zauna bakin gado. Meyasa take saurin rikicewa ne akan Junaid..abinda take tambayar zuciyarta kenan.
Meyasa zata masa rowar kyakkyawar fuskarta ne. Su Hajiya suna masa gashin kuma gashi yanzu yana cikin jindadin kallonta ta gudu. Girman laifinsa yasa ya danne zuciyarsa bai dami iyayen nasa akan a bashi matarsa ba. Itama yana jin nauyinta sosai a ransa. Ina amfanin badi ba rai? Karamar yarinya tana masa kwarjini saboda ya zubar da girmansa a waje. Ga su Rosie sunyi kane kane a gidansu. Fasa shiga gidan nasa yayi ya koma main house. Mai aikatan gidan suna ta gaishe shi ya haye sama da sauri. Addua yake kada kowa ya ganshi a hanyarsa ta zuwa dakin Hafsi.
Rub da ciki tayi tana karanta wani littafin tarihin Annabawa da Hajiya ta bata taji an bude kofar. Duk a zatonta Nafisa ce tayi saurin juyuwa babbar yaya ina ta jiranki tun dazu yau bani da....kallon da yake mata bayan ta juyu yasa tayi shiru. Ya zaka shigo min ba sallama? Ni da dakin matata har sai nayi sallama? Ya kara kallonta ita duk kayan jikinta suna mata kyau. Dinkin yau ma riga da skirt ne fitted sunyi mata kyau sosai abinka da yar Mama tela. Ya jawo kujerar dressing mirror banda gulma duk wannan kwalliyar kice babbar yaya kike jira? Fada min gaskiya dai ni kika yiwa wannan kwalliyar ko. Bargo ta jawo ta rufe jikinta da sauri ni ba kai nayiwa ba. Kan gadon ya dawo ya zauna a gefenta ya rage murya are you sure? Har fa zuwa kika yi bakin window don na ganki kuma na gani. Daga cikin bargon tace ni Allah ba kai nayiwa ba. Ji tayi kamar ya tashi daga kan gadon sai dai kuma har fuskarta ta rufe yace malaiku na jinki kina cewa yar miji kika yiwa kwalliya ba shi ba. Yau littafinki sai cika da rubutu amma fa daga na hagun. Muryar nan ta shagwaba ta fara yi ni ba haka nake nufi ba...kafin ta karasa magana taji ya daga bargon daga wurin kafafunta ya shigo ciki. Hannuwansa yasa ya danne duka sides din don kada ta bude. Tuni idanunta suka raina fata, they were so close suna shakar numfashin juna. Ya kashe mata ido daya ina jinki wa ma kika yiwa wannan kwalliyar? Ki fadi abinda nake son ji sai na fita salin alin. Kanta a kasa tace kai. Malama ni banji ba fa. Ta sake cewa kai a hankali. Bari na sake matsowa kusa kila zanfi ji. Da karfi tace kai nayiwa. Good girl to ki dan bani chance mana na yaba kwalliyar. Bata ankara ba taji ya janyota ya rungume. Yana shafa mata gashi a hankali. Wata ajiyar zuciya yayi Hafsi Hafsi ki tayani addua yau nayi interview har biyu ta neman aiki. Nasan nayi laifi da yawa shiyasa su Mommy basu da time dina amma don Allah zaki zama friend dina kuma special adviser dina. Dago kanta tayi tayi masa murmushi eh. Thank you so much. Ya mike yau zaki min girki? Ban iya ba ta bashi amsa. Au kin manta da malaikun ne? Itama mikewar tayi na iya, me zaka ci? Kallonta ya sake yi gaskiya kayan nan naki fa suna...kodayake ba komai ki dai rufe jikinki kafin kije kitchen din. Indomie da kwai nake so ina sonta sosai. Idan kin gama ki kirani. Wayarta ya dauka yasa mata number dinsa. Duk ta tsufa anma dena yayin irinta. Itama Gwaggo Zainab ce ta siyo mata irin second hand dinnan. Ki taho dashi daki zanzo na karba. To kawai tace ya fita. Tayi tsaki meyasa idan taga Junaid take zama wata wawiya ne. Ko dan jan ajinma sai ya nemi ya gagareta.
Kasa ta sauka babu kowa sai masu aiki ta dafa masa indomie biyu da daffafen kwai biyu. Tana shiga kitchen Rosie ta hangota ta koma daki da sauri ke Tilly tashi mu jirata a hanya. Akan tray ta dora zata fito wata mai aiki tace madam bari na kai miki Hafsi tayi dariya ai ba nauyi Chinwe nagode. Tana tafiya kamar daga sama Tilly tazo ta bangaje abincin ya zube a kasa plate din ya fashe kawai sai ji tayi Tilly na ihu wayyo Allah cikina.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐 33
Tana kwance suna hira cikin nishadi nurse din ta dawo. To angama komai ina kudina? Rosie ta dauko dubu ashirin a jakar Tilly ta mika mata. Ki dai tabbatar babu wani cikin wadanda suka kawo mu babu wanda ya shigo. Nurse Talle ta washe baki tana murna ta ce angama ranki ya dade. Bata dade da fita ba Dr Sunusi ya shigo dakin tare da wata nurse din. File ya bude yana dubawa, ya dan dago kai kece Talatu Jibo ko? Eh ta amsa da kyar tana ta rike ciki ita a dole mara lafiya. Yanzu likita na rasa baby na kenan? Kiyi hakuri mana ki dena kukan Rosie ta fada tana rarrashinta. Dr yace ya naga kina rike ciki ne ko bai gama fita bane? Saurin sakin cikin tayi ya fita duka ni dai ku sallameni kawai na tafi. Ya kalli nurse din kinga ki gyara min dakin can zanyi mata wankin ciki, ya maida kallonsa ga su Tilly. Ai kada ki damu idan nayi miki wankin cikin before you know it zaki sami wani. Yadda kike rike cikin nasan akwai saura. Wannan karon kukan gaske ta saka masa kayiwa Allah likita kada kayi min wallahi cikin baya ciwo ko kadan. Yace ai dalilin wankin kenan idan akayi bari ba ciwo nan ma akwai serious problem. Tana kuka yace a kawo wheelchair a kaita dakin da zai mata a can.
Kankame Rosie tayi bazata tafi ba. Rosie tace kiyi hakuri Tilly kada asirinmu ya tuno. Saboda tsabar kwadayin daya kawo su Tilly tana ji tana gani akayi mata D and C. Likita dai yasha zagi ta uwa ta uba.
Sai dare aka sallamosu duka a gidan suka hadu da Hamida suna jiransu da Senator. Ko daki basu shiga ba Rosie tace yallabai munyi waya da kawu na baban Talatu yace gobe zaizo gari don na fada masa abinda ya faru. Anyi mata fyade kuma anyi sanadin zubar da cikin. Wallahi maganar nan har yan jarida sai na fadawa. Kowa kallonta kawai yake tana rashin kunya Senator ya hanasu magana a cewarsa dansa ne ya ja masa. Tana gamawa yace idan sunzo goben zaa daura musu aure da Junaid. Yana gama magana ya juya zai haye sama zuciyarsa na kona saboda bacin rai. Ta sake cewa ita kuma wadda ta zubar da cikin idan zaayi adalci sai a saketa ko a dau mataki. Hamida tace uban kuturu kuma yayi kadan in fada miki. Hafsi mutu ka raba da Junaid. Hajiya tace ku wuce ku tafi gidajenku Allah Ya bamu alkhairi.
Junaid da Hafsi basu san abinda ke faruwa ba saboda ya wuce pharmacy da ita neman wani magani. Ac ya ware mata ya ja mayafinta can baya yadda cikin zaisha iska. Motar ko radio bai kunna ba yana ta kallon yadda Hafsi take ta zumbure zumbure. Yasan itama laifinsa take gani ya jawo musu masifa har gida an rasa yadda zaayi dasu saboda gudun abinda zaije ya dawo tunda babansa dan siyasa ne. Tarkace da yawa ya siyo mata na kwadayi bayan ya siyo maganin. Ganin bata da niyar kula shi yace Hafsi Hafsi kiyi hakuri akan abinda ya faru. Bansan dalilinta nayi miki sharri ba amma zanyi maganin abin. Tsautsayi ne ya kaini ga saninta amma kisa a ranki wallahi bazan aureta ba don nasan ko wacece Tilly. Cikin takaici yake maganar Hafsi tayi biris dashi. Ba komai ke damunta ba face yadda aka kasa gano karyarsu kuma ita bata da wani shaida akan abinda taji. Tasan Nafisa ta yarda da ita amma idan basuyi wani abun ba suna kallo Senator zai sa Junaid ya auri wannan matar. Wai ma ya akayi suka yarda bari tayi ne? Ko dai da cikin gasken? Ita ta gama zama confused. Har ta fara kokonto akan abinda kunnenta ya jiye mata
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐35
Washegari wayar Junaid ce ta tasheta daga bacci da asuba. Ko da ta dau wayar sai taga an rubuta J dear. Lallaima wato har wani saving sunansa yayi a haka. Ta daga cikin muryar bacci tace waye ne waya da asussuba kamar me karbar bashi. Murmushi yayi yana shafa kansa ai zaki biya bashi ne Hafsi Hafsi amma not now. Yanzu dai ya kika kwana? Ya jikin? Da sauki ta ams itama murmushin take. Wani son Junaid takeji yana ratsa ta. Amma babu yadda zatayi yanzu sai sun kawar da su Talatu daga gidan.
Karfe 9 na safe aka sanar da su Mommy zuwan baban Talatu Mal Jibo da kannensa biyu. Senator ta tayar daga baccin da sai bayan asuba ya sami runtsawa saboda tunani. Doguwar riga ya saka ya mike. Ki aika a kira min Junaid tun jiya ban sanar dashi maganar auren ba saboda kada ya daga min hankali. Shi ya jawo matsalar nan so he has to deal with it. Mommy tace amma yallabai baka ganin kara dulmiya shi zamuyi kaga baya sonta kuma basu da kamanin mutumci. Hannu ya daga ya dakatar da ita...haba Salma duk shi baiyi tunanin haka ba sanda yake bin duk macen da ya gani. Ai duk rayuwar da mutum yayi kafin aure indai ba Allah Ya kare ba sai kiga tana bibiyarsa. Ko kadan ita dai abin baiyi mata dadi ba amma dole tayiwa mijinta biyayya. Haka suka sauka kasa ya fita wani falo ya tarar dasu a zaune sun kusa cinye duk abinda aka kawo musu na tarar baki. Bayan doguwar muhawara Senator Rufai wanda rashin son tonon asiri yasa babu wanda ya iya sanarwa halin da ake ciki cikin abokansa da yan uwa ya tsayar da magana akan zaa daura auren Junaid da Talatu nan da sati biyu. Mal Jibon karya yace ranka ya dade ni dai gara a daura auren nan asabar mai zuwa saboda kada ya lallaba ya sake banka mata wani cikin. Wata irin tsawa Senator Rufai ya daka masa ya mike tsaye...kada ka dauki saukin kaina a matsayin shashanci mana. Ina binku ne a hankali kawai don in tayaku sayawa yarku mutumci. Idan kuka shige gonar da ba taku ba wallahi ina da karfin da zansa duk a neme ku a rasa. Duk abinda nake yi saboda girman Allah nake yi so be careful , be very careful. Yana gama magana ya fita Tanimu yace kai baaba kaji yadda hantar cikina ke kadawa kuwa. Baaba yace ai sai da nayi dana sanin magana ma. Wallahi idan Rosie bata biyamu da kyau ba jikinta ne zai fada mata. Kaga yadda yake muzurai kuwa. GG dake gefe yace ai ni na fiku tsurewa yadda yace zai batar damu gani nake kamar ya gama gane mu ma.
Baffa ya dauki wayarsa dake faman ringing tun yana sallar walha ya duba sai yaya sirikinsa ne. Bayan sun gama gaisawa Senator ya labarta masa dukkan abinda ke faruwa a gidan nasa. Mal Aminu dai yau ya rasa bakin magana saboda takaici yanzu irin gidan da Hafsan sa ta tare kenan. Senator ya cigaba da bashi hakuri da neman shawara. Mal Aminu duk yadda ransa ke kuna yace dole ayi abinda ya dace don a rufa asiri kuma shi yanzu kullum Junaid yana kiransa kuma ya yarda da irin shiryuwar da yake ji tare dashi. Haka suka yi ta shawara Senator yace idan ba damuwa ko zaku iya zuwa zuwa Jumaa kai da Alh Bashir saboda bani da wanda zan iya tonawa sirrina. Lallai rayuwa babu yadda bata zuwa ga bawa. Allah Ya kara rufa mana asiri. Daga nan Senator ya nemi dansa ya sanar dashi shawarar daya yanke. Junaid mikewa yayi cikin rudani yana daga murya...wallahi wallahi Alhaji bazan auri Tilly ba, karuwa ce fa.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐34
Yadda tayi zurfi a tunani yasa Junaid kare mata kallo. Wayarta ce ta hau tsitsi shi ya dawo da ita daga dogon tunaninta. Da sauri ta dauka ganin baffanta ne. Tana masa sallama yace Hafsa ya jikin? Dazu babanku yayi min waya kinji ciwo. Ince ko babu wani mugun rauni..dariya tayi ashe kana sona dai Baffa. Yayi dan gyaran murya kaniyarki wasa nake dake ne. Ta sake wata dariyar baffa babu ciwo sosai glass ne ya shige min kafa amma an cire. To sannu Allah Ya kara sauki, amma ki rinka kula kinji ko. Ga Mamanki duk ta damu itama. Sun dade suna hira da mama da kannenta kowa yana mata sannu. Bayan ta gama wayar yace yanzu tun dazu ina magana kina share ni sai da kika ji muryar su baffa kika yi dariya ko. Yadan bata fuska kamar zaiyi kuka Allah Sarki Junaid babu mai sonka. Har tissue yasa yana goge ido , bata san lokacin da dariya ta kubuce mata ba. Wayarta ya dauka yana juyawa. Ni na gaji da ganin wannan toy din. Idan munje gida kizo ki karbi sabuwar dana siya miki. I hope you will like it.
Bayan yayi parking din motar Hafsi ta bude zata fito yace tsaya ina zuwa. Zagayowa yayi ga mamakinta sai kawai taji ya dauketa. Yau karo na uku kenan yana daukarta. Tana ta mutsu mutsu ya ajiyeta kada wani ya gansu ya share. Da kafa ya tura kofar motar bai tsaya ko ina ba sai a side dinsu dake bayan gidan. Ajiyeta yayi ya bude kofar ya sake daukanta, kan doguwar kujerar falo yasauke ta ya duka hannunwansa duka biyu a gwiwoyinsa yana ta nishi. Wai Hafsi haka kike da nauyi...anya baki kai buhun shinkafa biyu ba kuwa. Filon kan kujerar ta jefa masa wallahi bani da nauyi. Kuma ma ai bance ka daukeni ba. Ya sami wuri kusa da ita ya zauna tare da janyota jikinsa. Gaskiya yarinyar nan idan kika hau kaina buzu na zaa dauka. Mintsini yaji a gefen cikinsa tace ya fa isheka ko don kaji ina shiru. Ya kama gefen cikin ke dama haka kike? Don kin kone a ciki nima nakasa ni zakiyi. Ya danyi murmushi me kama da na mugunta kinsan fatar cikinki zata fi dadin mintsini ko. Tana jin haka tayi saurin tashi sai ta fada jikinsa saboda zafin da kafarta tayi. Rungumeta yayi sosai hmmm su Hafsi wayon ki dan ji dumin jikina shine kika wani fado min a jiki. Maganar da tayi niyar yi ce ta makale mata saboda kunya data kama ta. Zata bashi hakuri taji ya hade bakinsu wuri daya. Cikin kankanin lokaci suka tafi wata duniyar sai dai basu dade ba suka ji bugu a bakin kofa tare da sallamar Hamida cikin daga murya.
Tsaki yayi ya amsa mata tare da mikewa. Tace Yaya munji shigowar motarka amma har yanzu Hafsi bata shigo gida ba. Wani tsakin yayi gata nan zuwa kill joy sim dinta zan saka a sabuwar waya. Hafsi dai gintse dariya tayi don yadda taga yana bin Hamida da harara bayan ta rikota zata taimaka mata su koma cikin gida.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐 36
Senator Rufai yace Allah Yasa magajiya ce sai ka aureta. Yau kaine kake kiran wata karuwa? Ka manta irin kukan da mahaifiyarka ta rinka yi lokacin da kake bibiyar matan banza. Yau gashi a sanadiyar hakan Junaid wasu yan iska suna neman bata min suna. Duk rayuwar da nayi a politics ina taka tsantsan saboda abokan gaba. Hajiyan dangi dake zaune a gefe ta dago kai cikin fushi lallai ma Rufai ashe duk abinda kake ba saboda lahirar mu kake yi ba. Dama saboda mutumcin siyasa kake yi. To wallahi ka sa a ranka duk abinda ya sameka kai ka jawo tunda babu abinda kake don Allah. Mommy dai kuka take don abin yayi mata yawa. Hajiya tace Junaidu? Ya amsa mata cikin kuka. Ina so kayi wa babanka biyayya hakan shine shaidar ka shiryu. Kuma da yardar Allah zaka ci jarabawar da Yake yi maka. Tashi ka tafi Allah Yayi maka albarka. Yana fita mommy ta hau rokon a janye maganar aure. Yace kun kasa fahimta ta ne Hajiya. Nasan ina son kare mutumci na amma ki duba ki gani indai yayi mata cikin da gaske kada su sami abin tozarta shi nan gaba. Bani da burin da ya wuce naga iyalina suna zaune cikin kwanciyar hankali amma hakan bazai taba yiwuwa ba sai mun toshe duk wata kofar da wani zai iya samun damar daga mana hankali. Senator yayi iya kokarinsa wurin ganin iyalinsa sun amince da auren don a iya tunaninsa da haka ne kawai zaa iya toshe bakin su Talatu.
Kamar wanda aka jefo daga sama kawai ganinsa tayi a cikin dakinta. Yar tsiwar data yi niyar yi masa saboda ya shigo mata daki ba sallama ma kasawa tayi saboda wata irin runguma da yayi mata. Cikinta ne ya soma zafin wurin da ta kone ta fara neman ya sake ta. A kunnenta taji yana magana cikin muryar kuka har hawayensa na sauka a kafadarta. Hafsi please dont ever leave me. Dole ta hakura ta tsaya har ya gaji don kansa sannan ya ja hannunta suka zauna a bakin gado. Kansa ya dora kan cinyarta sannan ya fara magana. Alhajinmu yace lallai sai na auri Tilly. Dama tasan haka zata iya faruwa sai dai tayi shiru ganin kamar bai gama magana ba. Na fada masa karya tayi min amma yaki yarda. Hafsi ke kadai kin isheni rayuwa ina tsoron hadaki da kwararriyar yar bariki. You are too innocent bazaki iya kishi da ita ba. Gashin kansa ta shafa indai Alhaji ne ya baka umarni to don Allah kayi masa biyayya. Kada ka manta aljannarka tana tare da farin cikin iyayenka a kanka. Tana gama magana yaga ta share kwalla yayi tashi zaune kingani ko tun yanzu kin fara kuka. Sai kuma ya kashe mata ido ko dai kishi ne ya motsa. Kyakkyawan rankwashi ta sakar masa ya dafe kai yarinya baki sanni ba ko. Sai a lokacin ya kula ashe daga ita sai wani towel iya gwiwa. Yayi wata dariya yau zaki gane nima mugu ne. Towel din ya kama daga daidai kirjinta yana ja tana ja. Muryarta na rawa tace zan maka ihu fa? Ai idan kika ji mace tana zanyi ihu ba yin zata yi ba. Besides ba zaki so a shigo a ganki a haka ba. To naji ta ce masa, don Allah kayi hakuri bazan kara ba. Kallonta ya rinka yi cike da so yace come here. Sake rungume ta yayi yana shakar kamshin jikinta. Shima kansa yana mamakin yadda yake iya kasancewa da ita kuma ya iya hakura ba tare da ya nemi biyan bukatarsa ba. Ya amince wannan shine true love.
Haka suka kasance suna nunawa junansu kulawa har ranar asabar ta zagayo wadda ranar Baffan Hafsi da Alh Bashir zasu iso abuja kuma ranar ne auren Junaid da Talatu Jibo Aka Tilly.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐38
Rosie tace dadina dake ba kya cin ribar abu. Kin fiye rashin hakuri kamar gudawa. Ki zuba ido yau a jikinki zai angwance. Ki dai sha kaya da kyau don ki kara kama shi a hannu.
Hamida ana ta rawar kafa kamar ita ce zata tare. Nasihohi da adduoi Hajiya da mummy suka yi wa Hafsi. Hamida taja hannunta masu aiki suka bi bayansu da akwatunanta. A ciki suka tarar da Nafisa da yaranta 'yan mata biyu Ummu mai sunan mummy da Husna. Suna ganin Hafsi suka kankameta suna murna. Nafisa tayi musu tsawa ku sake ta mana haka kada ku kayar da ita. Husna yar shekara biyar tace Mama Hafsa ni a nan zan zauna tare da ke ko. Hamida tace asheUncle Junaid zai kore ki kuwa. Ai ku da gidan nan sai nan da wata tara. Hafsi ta sunkuyar da kai kasa cike da kunya. Haka suka zauna suna ta hira. Ko kadan basa barinta tayi kewar yan uwanta saboda yadda suke janta a jiki.
Tun daga bakin kofa yake jin kamshi mai dadi sai dai zuciyarshi wani irin kunci take masa. Yana shigowa falon yan uwansa suka fara tsokanarshi. Nafisa tace to ya isa haka ku tashi mu tafi. Duk suka yi mata sai da safe suka fita. Dama tun shigowarsa Hafsi bata yi masa magana ba saboda yadda su Hamida ke tsokanarta. jin bashi da niyyar kawar da shirun dake tsakaninsu tace masa ina yini. Lafiya ya amsa a takaice. Can ya sake cewa tashi mu shiga ciki muyi sallah ko. Dadi hakan yayi mata ta kara tabbatar da cewa Junaid ya fara maida hankali a lamuran addini. Fuskar nan tata a rufe ta bi bayansa. Suna shiga yaji hakurinsa ya soma karewa yace mata kiyi alwala ina zuwa nayi mantuwa a mota.
Cike da damuwa yake tuki ya rasa abinda ke masa dadi. Ace ya rasa abinda zaiyi ta tunani a yau sai Tilly, Why ??? Gidan ya nufa yayi saa suna zaune a falo. Mamaki karara a fuskar Tilly yace hado kayanki ki sameni a mota. Yana fita suka sa shewa da dariya. Tilly ta yi saurin dauko jaka ta watsa kaya kadan a jakar ko sallama babu ta fice. Rosie ta koma daki tana cin farar kasa wadda ta zame mata abinci yanzu. Mayen cikin yaki zubewa ita kuma tana tsoron wankin ciki.
Kusan awanni biyu kenan da fitarsa amma taji shiru. Tun tana sharewa har ta kasa hakuri. Lekowa tayi wajen gidan babu daya daga cikin motocin da yake shiga. Komawa tayi ta zauna tana ta sake sake. Gajiya tayi ta tashi tayi sallar isha da nafila ta zauna kan darduma tana karatu.
Hotel ya kama musu don yasan babu mai bashi mukullan gidan da Alhaji ya kama masa kafin ayi masa wani ginin inda zai iya hada matan biyu. Tilly ansha gyara ciki da waje. Ta nuna masa salo salo na kwarewarta a fanin shegantaka. Wayarsa ce tayi kara wurin shadayan dare. Har ya fara bacci Tilly ta dauka taga ansa H dear. Kashe wayar tayi gaba daya tayi tsaki sannan da dariyar mugunta. Yarinya yau zaki bushe ta fada a fili..
Saroro ta tsaya kallon wayar. Yanzu ita Junaid ya kashewa waya? Ko tayi masa laifi ne? A falo ta kwana ranar tana kuka ita wannan wace irin rayuwa ce daga wannan sai wannan kullum. Ta yanke shawarar idan bai dawo ba da safe zata sanar da iyayensa.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐37
Hafsi da Ummati sun kusa rabin awa a waya suna ta shawarwari don yanzu kam Hafsi tasan bazata iya zama haka babu abokin shawara ba duk da cewa su Hamida suna iya kokarinsu. Yayarta Hadiza ma ta bugu sun dade suna magana. Tana wayar Nafisa ta shigo da wata karamar jaka a hannunta ta zauna kan kujera. Hafsi ta gama waya suka gaisa. Nafisa tace kanwata kinga yadda Allah Yake ta jarrabar mu da abubuwa kullum ko? Yauma hakuri dai zan kara baki. Da yar shawara kadan. Kinga wadanan kayan masu tsada ne amma fa idan kika sha baza ayi asarar kudin tara ba. Suna gyara mace sosai sannan ki rika shan fruits musamman kankana. Akwai kunun aya ma da ake hadawa da ita da cucumber, dabino, kaninfari, citta da kwakwa. Zan hada miki da kaina kafin anjima. Munyi magana da Mommy ke zaki fara tarewa sannan bayan sati daya talatu ta tare amma gidanta daban ne. Kiyi iya kokarinki ki zama tamkar karuwa kema a wurin mijinki kinga ya san wasu matan so raba shi da irinsu sai kin dage sosai. Kan Hafsi a kasa duk kunya ta kamata ta kasa magana. Nafisa ta nuna mata yadda zata yi amfani da kayan data kawo mata. Ke ni ki dena jin kunyata bazan taba bari matan banza su rabaki da mijinki ba. Tunda kika auri Junaid kin gama mana komai.
Talatu yar gidan Mal Jibo mai faskare amaryar Junaidu dan sanata. Kirari ne Rosie da ke zaune kan kujera take wa aminiyarta. Tilly tace yanzu fa dole inyi ta amsa sunan Talatu sunan dana manta dashi tun a kauye. Suka tafa sanan rosie ta miko mata kullin magani. Ga wanan kawata ki shafa hannu ne ki taba shegen. Wallahi zaki sha mamaki don watarana ma sai ya gundireki idan ya fara like miki. Wata shewa suka yi tace Rosie ba kyau. Gara tun wuri na fara kiranki Samiranki kada ayi subutar baki a gaban surukai. Hakane, yanzu dai zan kira shi yazo a sunan kina zubar da jini sai ki fara gwada saarki. Bikin ma da akace muyi a garinmu zasu sha mamaki don sai munyi kara'i. Sake tafawa sukayi sannan Tilly wadanda sun koma dakin da Rosie ta kama musu ta dauki waya ta kira shi.
Tun safe ya kasa zaune ya kasa tsaye saboda tsananin farinciki yau Hafsin sa zata tare. Ya fito daga wanka yaji karar waya a zatonsa ma Hafsi ce don tun dare take tsokanarshi da flashing. Tsaki yayi kamar tana gabansa daya ga number din Tilly. Yana dauka Rosie ra kwarma ihu tace yazo Tilly tana ta zubar da jini. Wani tsakin yayi ya ajiye wayar ya cigaba da shiryawa. Sake buguwa suka yi har sau biyar sannan ya dauko a wulakance yace gani nan zuwa. Cikin gidansu ya shigo ya fadawa Mommy inda zashi. Ta tabe baki sai ka dawo. Kada dai ka dade yace to. Shi har a ce masa kada ya dade yadda yake zumudin nan.
Suna jin tsayuwar motarsa Tilly ta kwanta a kasa tana wai wai. Kudi ya jefa mata yana mata kallon banza gashi nan nasan abinda kike nema kenan. Ganin bashi da niyar taimaka mata ta tashi ta mike ta riko shi. Juni boy ka saki jikinka mana ai an riga an daura. Ina jiranka anjima kazo mu tafi namu gidan don a sannu zansa ka manta wannan kwailar. Hankadeta yayi har ta fadi kamar zaiyi magana ya fasa ya fice. Rosie dake kitchen ta fito da sauri tana mata sannu. Tilly tace aikin banza maganin naki baya komai ji yadda ya ture ni.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐39
Wani azababben ciwon kai ta farka dashi lokacin da taji bugun kofa. Sai bayan asuba bacci ya sace ta, dan goge fuska tayi ta bude kofar. Amaka ce dauke da tray ga wani a kasa shima duk kwanukan abinci ne a ciki. Tace Amariya goodmorning...Hafsi ta dan saki fuska ta amsa tare da daukar tray din kasan suka shigo dashi. Amaka tace Madam say make you tell me wetin you wan chop for lunch. Hafsi tace what? Ita fa bajin pidgin english take ba. Ta dai gane lunch ta ce mata ta tafi kawai zata shigo. Har shabiyu tana jira ganin dai bashi da niyar dawowa gashi wayoyinsa duk ta kasa samu ta fito ta tafi main house. Babu kowa a falon sai akwatuna guda uku daga bakin kujera. Dakin Hajiya ta fara leqawa ta ganta tana daura laffaya. A'a mamana keda kike amarya me ya fito dake kuma. Nima shirin komawa Kano nake yi yanzu Rufai nake jira yazo muyi sallama sai a kaini iyaport. Hafsi tayi dan murmushi tace Hajiya bana son ki tafi. Allah sarki Mamana bakya so naje na gyara nawa auren ne? Tare fa aka kawo mu dake gashi muna neman wata daya. Wasu hawaye masu zafi ne suka sauko mata Hajiya a rude tace haba Hafsatu kada ki karyar min da zuciya mana. Ki kara hakuri in Allah Ya yarda zaku sami zaman lafiya da Junaidu. Kirawo min shi mu yi sallama sannan ki goge idonki kada yace na taba masa mata. Kanta a kasa tace baya nan Hajiya. Dan bata rai tayi ina yaje kuma daga kai masa amarya. Mummy dake tsaye a bakin kofa tace garin yaya kika bari ya fita amarsu. Har kasa ta kai ta gaishe da mummy sannan soma kuka. Duk hankalinsu ya tashi aka suna tambayarta ko lafiya. Da kyar tace musu bai kwana a gida ba. Sai suka fara salati. Mummy ta dauki waya ta kira shi aka yi sa'a a kunne wayar take.
Tilly ta kalli wayar bari na daukar maka Juni boy. Kasan yau rana ta ce so duk mai kira yayi hakuri. Ba musu ya mika mata batare da yasan mai kiran ba. Hello ta fada bayan ta amsa wayar. Mummy a dan razane tace wacece? Ahhh tuni ta gane muryar jarababbiyar babar tashi. Tace matarsa ce Talatu don Allah a dena kira yana bacci ne idan da sako ki fada na gaya masa. Yadda take maganar a ladabce shi yasa Junaid ta kara lafewa jikinta yana mata cakulkuli please ki ajiye wayar anjima na kira. Karaf maganar sai a kunnen mummy tace Junaid da karfi. Tilly bata bare yaji ba ta ajiye wayar ba tare da ta kashe ba tana ta dariya please baby ka bari kaga jiya baka barni na runtsa ba.
Jefa mummy tayi da wayarta tana kuka mai tsuma zuciya. Maganar Junaid ta tabbata karuwa ce yarinyar nan. Suna tare bansan ko a ina ba amma suna tare. Hajiya tace inna lillahi wa inna ilaihi rajiun. Anya zan iya komawa kano kuwa salma? Yarona yana cikin matsala. Mummy tace ki tafi hajiya ai tsuntsun daya ja ruwa shi ruwa zai daka. Rashin jin maganar iyaye yasa ya kwaso mana balai. Bari na tado Yallabai wallahi a nemarwa yarinyar nan saki tun wuri. Ni bazan iya kallon Safiya ba ina kallo dana yana wulakanta musu 'ya.
Tunda suka fara magana Hafsi ke kuka Mummy ta jawota ta rungume. A haka senator Rufai ya samesu. Bayan anyi masa bayanin abinda ke faruwa yace su kwantar da hankalinsu zaisa a nemo shi duk inda yake a kasar.
Wasa wasa sai da suka yi sati biyu a hotel suna shan soyayya. Hutu ya ratsa su da kyau don daga ci sai kwanciya. Ko kadan baya son Tilly amma ji yake idan ya rabu da ita komai na iya faruwa. Kashe mata kudi yake kamar hauka tana karbewa. Rosie master planner ma an manta da ita .A rana ta shabiyar Senator yasa aka yi freezing dukkanin accounts din Junaid. Matsayinsa yasa har aka nuna masa statement of account din dan nasa. Ba karamin barnar kudi yayi ba a iya kwanakin da baya gida. Senator Rufai ya shiga rudani sosai yadda junaid yake neman kara lalacewa.
0 comments:
Post a Comment