Na mammy kabeer
(Anty mammy)
Elegant online writers📚📚
Free book
Page 1
Bismillahir rahmanir rahim,Ina godiya ga Allah daya bani damar fara wannan littafi ,bayan kammala littafin soyayyata.Allah kasa yadda na fara lafiya naga bayansa lafiya ameen.
Gargadi banyarda wani ko wata ya juyamin wannnan littafi ta kowace sigar ba.
_______________Wata kyakkyawar yarinya na hango sanye da kaya irin na Fulani ,wato rigar saki dakuma zaninta,duka duka rigar da kadan ta wuce cibiyar ta,saidai kuma ta daura zanin ya rufe mata cikinta ta yadda ba wanda zai ga jikinta awaje.
Farace irin mai sirkin yallow -yellow din nan,tana da doguwar fuska mai kyan tsari dauke da dogon siririn hanci har baka,bakinta dan karami kamar gidan tsutsa,tana da irin manyan idanunnan masu kamar tana jin barci,ga gashin ido zara -zara.
Girarta kuwa ,kamar wacce aka dora Mata ita dan saiti,gaban goshinta wasu yan kananan gashine kwance lub lub kamar na jarirai.
Masha Allah yarinyar ta ko ina ta hadu ,dan doguwace marar jiki saidai fa Allah ya hore mata hips Kai kace wata babbar macece Sannan akwai alamun girma akirjinta , ma'ana dai akwai dukiyar Fulani dasuka fara tasawa akirjin nata.
Duka duka wannan yarinyar bata wuce shekara 15/16 ba ,amma kallo daya zaka yi mata kasan Allah yayi halitta agurin.
Sandace irin ta Fulani ahannunta tana dagawa sama ,da alama tana son hada kan wasu tarin sha'nun dake kiwone wani kayataccen jeji ,dan kuwa ciyawace agurin Kore sharr da ita ,sha'nun suna ta cin abarsu .
Tafiya ta farayi gurin shanun dake dan nesa da ita ,dan ita tana daga jikin wata bishiya ne tana kallon yadda suke kiwo abinsu.
Kanta ta daga ta kalli yadda garin ke hada wani irin hadari baki kirin dashi ,kuma da alama koda yaushe ruwa na iya saukowa.
"Kuzo mu tai gida abokaina kada ruwan nan ya sauko ya taba mu banin son nai mura aradu"
Cikin Yaren fulatanci take musu magana ,tana daga sandarta .aikuwa kamar wanda suke jin me take fadi suka fara yin hanyar gida .
Murmushi tayi tana mai binsu tana kara daga sandarta .
Tafiya suke cikin jajen ita kadai daga ita sai wadannan garken shanun ,sam ba alamun tsoro tattare da ita,yar wakar tama take tana daga sandar sama.
Kusan tafiyar minti biyar sukayi ,sannan na fara hango bukkokinsu dake can gaba kadan .
AHankali naga duk wani annurin dake kan fuskar yarinyar ya dauke ,nan da nan damuwa ta maye gurbin nishadi da take ,sosai naga jikinta yayi sanyi har suka karasa wata bukka dake farkon rigar da alama nan ne gidansu.
Garken shanun ta fara zuwa ta daure su tsaf sannan ta nufi cikin gidan,bakinta dauke da sallama.
Lokacin har anfara yayyafi .
Ba kowa a tsakar gidan nasu ,hakan yasa ta sauke ajiyar zuciya tare da nufar wata bukka cikin sauri.
Saidai kafin ta karasa kofar bukkar aka daka mata wata uwar tsakar da saida sandar hannunta ta fadi kasa.
Afirgice ta juyi jikinta na rawa sosai kamar dan mazari.da sauri ta karaso gurin matar data daka mata tsawar,
"Gani gwagwgo"ta fada cikin rawar murya. Kallon matar nayi sai na tarar da
matar farace saidai kuma kazanta da rashin kulawa yasa tayi wani irin baki baki fari fari,sannan tana da jiki sosai sam fuskar ta ba alamun rahama a cikinta.
Tana tsaye a kofar bukkar ta tana hararar yarinyar dake durkushe gabanta.
Cikin masifa da bala'i matar ta fara magana da hausarta marar kyau.
"Da kake kokarin shigewa dakin,ubankane zai debi ruwan?
Ko kin ajiye bawanki ne a gidan?matar ta fada cikin zaro ido.
Kan yarinyar akasa jikinta na rawa ta fara magana
"Allah hukkumu hakuri gwagwgo naga ruwa na don sauka ne shiyasa ban deboba"ta fada cikin rawar murya da tsoro.
Wani wawan mari matar ta kai mata cikin rashin imani da tausayi cewar yanzu ta dawo daga kiwo kuma ko abinci bata ci amma take kokarin sake turata rafi.
"Shegen yaro mai bakin hali wllh yanzu koke kidobo min ruwan nan dan ubanki karuwa kawai"matar ta fada tana mai hankade yarinyar .
Faduwa tayi sosai hannunta ya bugu da wani dutse dake ajiye tsakar gidan da alama na zama ne.
Kara ta saka cikin azaba tana mai dafe hannunta dake mata wata irin azabtar zafi.
"Wayyo handi É—in boni lalashewa gwagwgo hannu na ta É“alle" ya rinyar ta faÉ—a cikin azaba.
"Shege wllh dama zai karye danafi kowa jin dadi yarinya kamar aljana,ace kinfi kowa kyau arugarnan? Na tsaneka fatto saina bata wannan shegen fuskan baki.maza ki tashi kona shakeki agurin ki mutu kowa ya huta" cewar matar cikin bala'i da tsantsar nuna tsana ga dattin.
Cikin hanzarin ta mike ta zari wani boket din roba ta fice tana kuka sosai.
Tafiya mai nisa tayi kafin tazo rafin, har zuwa lokacin kuka take hannunta sai zogi yake mata, ruwan ta debo cike da sauri dan kuwa ruwan da ake ya fara karfi.
Saidai me ?tana juyawa tayi arba da wani murtukeken maciji katon gaske ya fasa kai yana huci.
Wani irin mugun tsorone ya kamata nan da nan jikinta ya kama rawa har batasan lokacin da boket É—in ya fadi kasa ya fashe ba.
Tashin hankali kenan wanda ba'a sa masa rana ,iyakar rushewa da tashin hankali yarinyar nan ta shiga.
Hannu ta ɗora aka tana mai kara ƙarfin kukanta.
"Wayyo ni fattu bukar na mutu na lalashe ya zanyi da rayuwata nashi zai karni wayyo baffana wayyo Allah ,taimaka min"
Ta faÉ—a tana kallon boket É—in dake tarwatsa,dama kuma rana ta gama cin ubansa.
Shi kuwa macijin nan ganin yadda ta tsaya tana kallon sa kuma tana kallon fasashshen boket É—in ta ,sai taga kamar neman makami take ,dan haka afusace yayi kanta
Ihu ta kwalla mai karfin gaske tare da zubewa agurin sumammiya dan ganin yadda macijin nan yayi kanta baki bude.
Masu karatu ya kukaji?
Meye ra'ayinku akan wannan Nobel É—in?
Ina bukatar comment dinku idan buk din nan yayi muku dadi muci gaba.
Takuce har kullum anty mammy
Msr babi💘💘
29/08/2022, 10:43 am - Khadijah Salisu Fari: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄
MACIJINE SHI🪱🪱🪱
Na mammy kabeer
(Anty mammy)
Elegant online writers📚📚
Free book
Page 2
_______________Ihu ta kwalla mai ƙarfin gaske ,tare da zubewa agurin sumammiya,dan ganin yadda macijin nan yayo kanta baki buɗe .
Hakan ba ƙaramin tsorata ta yayi ba .
Dai dai lokacin ne kuma wani katon macijin ya nufo wannan macijin da gudun gaske ,yana zuwa ya sarkeshi suka fara kaiwa juna sara .hakan shi ya hana wannan katon macijin ya sami damar karasawa inda fattun ke kwance asume.
Sosai macizan nan ke kaiwa junansu sara suna murdewa cikin jikin juna.ko wanne na ƙoƙarin illata dan uwansa.
Ahankali fattu ta fara bude idanunta da sukayi mata mugun nauyi tana kuma lumshesu,hannunta ta daga da nufin dafe kan nata,saidai wani azababben zafi da radadin ga wani irin zugi dataji hannun yana mata ,shine ya sanyata sanya kara tare da fashewa da kuka."washhhh hannuna wayyo kaina"ta fada cikin kukan tana mai dafe kan da dayan hannun marar ciwon.
Sai kuma ta zabura cikin azama ta zauna tana mai zare idanu da rarraba su,sakamakon tunowa da katon macijin da yayo kanta dazu.saidai kuma can ta hangi macizan biyu suna ta artabu,gaba daya sun jima kansu ciwo jini yana ta zuba akikkunansu,amma sunki daina fadan.
Tsoro ,fargaba ,tashin hankali da rudewa suka saka fattu kurma wani uban ihu tare da yunkurawa ta felle da mugun gudu tana ihu cikin rudewa dan ganin macizan sun zama biyu wato har fada suke akan waye zai cinyeta.
Duk da irin ruwan da ake zugawa mai ƙarfi ga iska ,haka tayi ta cin uban gudu ko gabanta bata gani.ikon Allah ne kawai ya kawota gidansu lafiya.
Kai tsaye ta danna cikin gidan da gudu ta shige dan dakin dayake amatsayin nata,cikin rawar jiki ta janyo wasu karare dogaye guda hudu ta kara a kofar,dan sune
Matsayin murfin kofar tata.
Dakin ba komai sai wata yar yaloluwar taburma ,wacce kallo daya zaka mata kasan cewa taga duniya,dan gaba daya ta ciccinye kuma tayi lakwam da ita.sai wani zani dake gefe daure ,da alama kayanta ne acikin.
Tana tsaye atsakar dakin ,har lokacin jikin ta rawa yake ,ga ruwa sai zuba yake ajikinta yararara!!!
Kallo daya zaka mata kasancewa afirgice take sai kif-kifta ido take tana kallon kofa,gani take kamar macizan nan zasu biyota.tayi kusan minti biyar acikin wannan halin ,kafin ta fara cire kayan jiki ta dake yararin ruwa."masha Allah nace,sakamakon ganin wani uban dogon bakin gashi mai santsi akanta,lokacin da take zame dan kwalin dake kanta .an raba kan biyu an daure ko wanne bangare sai kuma aka nannade ko wanne abarinsa kamar gammo.hakan da akayi shine ya hana mu ganin gashin nata tun farko.
Daurarren zanin nan ta kwance ta dauko wani zanin irin wanda ta cire da rigarsa ,saidai kayan fa sun sha jiki sosai ,sun kode sun jeme sunyi wani fari,sai wata hula baka irin ta sanyin nan ta dauko ta ajiye kusa da kayan ,sannan ta mike tsaye ta cire rigarta ta ajiye ta gefen ta barmar ahankali ta warware tsangalallen zanin shima ta ajiye gefe,ya zama daga ita sai wani kodadden pant Wanda kana gani kasan shima yaga rayuwa.kallonta nayi tun daga sama har kasa kawai nace Masha Allah.dan sura kam Allah ya halicce ta agurin fattu jikintahar wani sheki yake kamar yar masu kudi wacce ke rayuwa cikin jin dadi.
Haka ta dauki kayan ta saka ajikinta tanayi tana kuka abin kwanon ban tausayi.
Bayan ta kammala sanya kayan ne kuma saita dauki wanda ta cire ta matse sannan ta makalasu ajikin karan dake jingine akofar dakinta.
Zama tayi akan yar tabarmarta ta dukunkune jikinta tana kuka.abubuwa dayawa ke dakinta ahalin yanzu,na farko tsantsar tsoron macizan data gani dan bata taba ganin irin wadannan macizan ba,dan dayan kam jikinsa mai matukar shekine da kyau,sai kuma hannunta dake mata azabar ciwo uwa uba kuma yunwa,rabonta da abinci tun safe data sha nono har kawo yanzu da magrib ta sanyin kai ba abinda taci.
Sosai take tausayi rayuwarta, tabbas rashin uwa babbar gibine arayuwa,yanzu da innarta na kusa da ita data rungumeta ta fada mata damuwarta,amma rashin dace ta daya shine sam batasan koda fuskar innarta ba ,bata sani Bama kotana raye koya mutu Allah shine masani.
Tana cikin wannan halin taji an ture kararan data rufe dakinta dashi.
Azabure ta mike tsaye tana shirin sanya ihu.
"Ke fattu nutsu mana nine fa ,nine baffanki"wani dattijo ne fari mai dan tsayi yake maganar,yana sanye da riga da wando na wani yadi mai arha sai takalmin sau ciki na roba,da hula irin mai malafar nan.ya shigo cikin dakin da wani kwano hannunsa.
Ajiyar zuciya ta sauke sakamakon ganin baffan nata ,da sauri ta karasa kusa dashi tace "baffan usee wollahi na tsorata ne"ta fada idonta akan kwanon dake hannunsa.
Murmushi yayi yace "hoo fattu akwai tsoro,sannu maza karbi wannan tuwon ka shinye nasan kanajin yunwa,kayi sauri kar hansai ta gani"yana fadin haka ya mika mata kwanon yayi saurin fita,dan kar matar tasa ta fito ta ganshi ya shiga uku.
Cikin sauri _sauri fattu ke cin tuwon nan kamar zata kware, tas kuwa ta cinye ta side kwanan, da sanda tafice tsakar gidan ta wanke kwanon ta ajiye akicin sannan ta sha ruwa tayi alwala ta koma daki.
Sallar la'asar tayi da magrib dan tuni an kira.
Har zuwa lokacin ruwa ake saidai bai kai ƙarfin na farko ba.tana zaune cikin zullumin matakin da gwogwgo zata dauka akanta ,na fasa mata boket har akayi ishsha tayi salla sannan ta kwanta tana mai karanta addu'a ,nan da nan barci yayi gaba da ita,har baffanta ya shigo ya duba ta yaga tayi barci addu'a yayi mata cikin tausaya wa halin kuncin da take ciki kafin yayi saurin fita.
Gwagwgo kuwa tana daki ita da yaranta suna ta hira suna cin gyada ,ba ruwansu da wane halin fattu ke ciki,shin ta dawo gidanma ko yaya taci abinci ko bata ciba?sam ba wanda ya damu ,kuma ba wanda yayi Sallah a cikinsu.
Can cikin dare fattu na barcinta damuwa da tsoro dan kuwa mafarkin macijin nan take ,saidai kuma ba na farkon bane yazo mata yanzu wannan mai kyakyakywan jikin ne,saidai gaba daya jikinsa jini yake zubarwa,ga wani irin hayaki da tururi dake fita ajikinsa, sai burkima yake yana wani irin kuka da wata murya mai amon sauti,kuma yana nufota da ƙoƙarin hawa jikinta .
Wani razanannen ihu ta kwalla tare da mikewa zaune afirgice ,tana mai waige waige,ba abinda take iya gani saboda duhun dakin ,hakan yasa tayi saurin komawa ta kwanta tare da karanta addu'a kala_kala,hannu ta mika dan janyo zaninta ta rufe jikinta dashi ,saidai kuma hannun nata taji ya sauka akan wani abu mai dan karen sanyi da santsi.
Cikin tsoro take shafa abun dan jin ko menene,tabbas MACIJINE dan kuwa ta tabo har kansa ....
Masu karatu badai macijin ne ya biyo fattu da gaske ba?
Wane hali fattu zata shiga ?
Muje zuwa yaki ce dai anty mammy
Mrs babi💘💘💘
Share and comment fisabilillah.
More comment
More typing.
29/08/2022, 10:43 am - Khadijah Salisu Fari: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄
MACIJINE SHI🪱🪱🪱
Na mammy kabeer
(Anty mammy)
Elegant online writers📚📚
Free book
Page 3/4
________________Cikin tsoro take shafa dogon abun dan jin ko menene,tabbas MACIJINE dan kuwa har kansa ta taɓo.
Aikuwa da hanzari ta janye hannunta cikin kidima ta fara ja baya tare da fasa wani irin gigitaccen ƙara,
"Ahhhhhhhh wayyo Allah baffa maciji!maciji !!maciji!!!"gaba É—aya ta kidime abinda take iya faÉ—i kenan jikinta na rawa kamar É—an mazari.
Allah Sarki baffa dama ba wani barci yake yi ba ,dan yana kula da ɗakin fattu ,kasancewar ɗakin yana gaf da ƙofane,dan haka jin ihunta da yayi ,yasa shi tashi agigice ya nufi ɗakin nata.
Haskawa yayi da tocila can ya hangota jikin bangon ɗakin ta duƙunƙu ne tana ta ihu,da alama batama cikin hayyacinta.
Da sauri ya nufeta yana kiran sunanta"fadimatu !ke fadimatu menene ?ya isa haka gani akusa dake baffanki ne kinji daina ihun "baffa ya faɗa cikin ƙasa ƙasa da murya dan karya ƙara tsorata ta.
Ita kuwa gaba É—aya ta rikice kawai kira take "baffa maciji zai sareni baffa wayyo Allah na"
Ganin halin da take ciki ne yasa baffa ya fara tofa mata addu'a ,cikin minti biyu kuwa tayi shiru sai rawa da jikinta ke famanyi,ahankali ta daga kanta ta sauƙe kyawawan idanunta akan baffan nata,kawai saita saki kuka tana mai cewa"baffa MACIJINE yake son sarina aradu da idonsa na ganshi anan"ta faɗa tana nuna masa gurin dataga macijin.
Kallon gurin baffa yayi ,shifa ba abinda ya gani agurin ,kawai yana tunanin ko mugun mafarki tayi,dan haka cikin ƙokarin kwantar mata da hankali yace "shike nan fattu ya tafi maza koma ki kwonta kiyi addu'a ba abinda zai sameka kinji"ya faɗa cikin yanayin Hausar su ta Fulani.
Cikin kuka take girgiza masa kai "aradu baffa dawowa zaiyi tun daga rafi suke son cinyeni baffa ,bazan iya kwonshiya Ni kaɗai ba"ta ƙarasa tana mai matsowa kusa da baffan.
Shiru yayi yana tunanin mai ya kamata yayi,dan gaskiya yaga ta tsorata da yawa,dan haka cikin ƙarfin hali yace "tashi muje gurin hansai saiki kwonta shan ko"ya faɗa cikin tausaya wa.
Ai kafin ma ya rufe bakinsa ta kai ƙofa,dan ita kam babban burinta ta bar ɗakin nan,tama manta da gurin wa baffan yace taje.
Ahankali baffa cikin É—an tsoro yake tura murfin É—akin na hansai harya buÉ—e shi duka.suna kwance abinsu kan gado ita da yaranta su uku,na miji É—aya sai mata biyu Dukansu basu kai fattu shekaruba, da alama na mijin zaiyi shekara sha uku,matan kuma basu fi sha daya ba.
Kuma dan rashin tsari irin na goggo hansai da ita da yaranta duka suke kan gadon ,har na mijin.
Ahankali baffa ya karasa yana dan bubbuga fillon da hansai ke kwance ,sai uban munshari take zabgawa,banda wari ba abinda dakin keyi.
"Hansai!hansai!!"baffa ya faÉ—a cikin Muryar tsoro,dan yasan idan ta farka saitayi masa bala'in ya tashe ta tana barci.
Juyi tayi tare da goge yawun barcin dake zuba abakinta taci gaba da barcinta.ahankali ya fara kiran sunanta da É—an karfi "Hansai ! Hansai!!" Har sau biyu.
Buɗe ido tayi ahankali ta sauke su akan baffa dake tsaye ,buɗe idon tayi sosai cikin bala'in ta tace "to jarabarce ta motsa haka da cikin dare zakazo ka dameni?to wllh garama ka koma inda ka fito dan ba abinda zaka samu agurina ,wannan jaraba dame tayi kama ,ko sati biyu bakayi da saukemin jarabarka ba shine yanzu ka ƙara jajiɓo jiki kazo ka sake ko ?to wllh banda lokacinka kaficemin daga ɗaki"ta faɗa cikin masifa tana juya masa baya.
Girgiza kai yayi cikin jin kunyar fattu ,dan yasan taji abinda gwogwgo take faÉ—i ,kuma ai ita ba yarinya bace bare ace bata san me hakan ke nufi ba,tunda tana karatun addini.
Cikin sanyin murya yace "ashsha Hansai ba wannan ta kawoni ba ,dama ina neman alfarmar fattu ta kwana anan ne daku,dan bazata iya kwana ita kadai ba ,atsorace take "ya faÉ—a cikin shakkun zata amince ko yaya.
"Kan ubannan yau kuma da wannan sabon munafurcin kuka zo ?fattu ta kwana aÉ—akina ,lallai in baka mutu ba zakaga ikon Allah,da can da ubanwa take kwana? sai yau zakace ta kwana aÉ—akina?yarinyar mayya wato cikin dare ta lashemu ko?kai baka da asara,to ku ficemin aÉ—aki ,Allah yasa abinda yake tsoratatan ya cinyeta ta mutu kowa ya huta "tana gama faÉ—in haka ta juya taci gaba da barcinta.
Sosai maganganunta suka É“atawa baffa rai ,saidai bashi da damar magana ,kai kawai ya girgiza yace "muje fattu"
Kuka sosai fattu keyi na tausayin su ita da baffanta ga wannan matsalar dake ƙoƙarin Kunno mata kai ,basu da gata sai Allah kawai.
Suna fita baffa yace "shiga É—akina ki kwanta fattu,Ni bari na je É—akin naki kinji"ya faÉ—a cikin sanyin murya.
Girgiza kai tayi tace "baffa Zan koma É—akin nawa In kwanta kaima kaje É—akinka ,idan gwagwgo tasan na kwana aÉ—akinka yanka Ni zata yi,dan ta hanani shiga É—akin"ta faÉ—a tana mai share hawayenta tare da nufar É—akin nata ,gabanta naci gaba da bugawa.
"Kiyi hakuri fattu komai yana da iyaka kinji,Allah zai miki sauyi Na alkairi"baffa ya faÉ—a yana mai mika mata tocila ya ce ki haska ki kwanta kinji ,kiyi addu'a"
Karba tayi tare da É—aga masa kai ta koma cikin É—akin.
Daga bakin ƙofa ta tsaya tare da haska ɗakin ko ina ,ba abinda tagani aɗakin ,hakan yasa tayi zamanta bakin ƙofar ɗakin da tocilan ɗin ta ko yaya taji motsi saita zabura ta haska .
Sam awannan daren bata sami damar runtsawa ba ,ga sanyi da garin ya É—auka sakamakon ruwan da aka zabga jiya.
Sai gabannin asuba sannan barci É“arawo ya saceta.
Wani irin azababben sanyi daya ratsa ƙasusuwan tane sakamakon ruwan sanyin da gwagwgo ta kwara mata ,shine ya sanyata zabura ta miƙe da sauri tana haki,kafin ta gama dawowa cikin hayyacinta kuma taji duka yana sauƙa ajikinta ta ko ina ,ihu ta fara tana neman taimako amma ba wanda yazo dan taimakon nata,dan baffa yana masallaci kasancewar shine limamin rugar,
"Wayyo Allah na gwogwgo kiyi haƙuri wllh bazan ƙara ba ,tsautsayine yasa na fashe miki bokati, dan Allah kiyi haƙuri gwogwgo"abinda fattu ke daɗi kenan cikin azaba dan ko ina na jikinta ciwo yake mata barin ma hannunta daya kumbura sosai ,alamun tayi targaɗe a hannun kenan.
"Wllh yau saina kasheni Shegiyar yarinya muguwa, kafin baƙin cikinki ya kasheni ,na Tsaneki fattu bana ƙaunar ganinki arayuwata, kinsan nawa nasai bokatin nawa?kika je kika fashemin shi? Murtala huɗu da nairagoma fa na siya,wllh saina daki kuɗina kuma kije duk inda zaki samo min kuɗin bokatina ki samomin dan bazan ɗauki asarar ba"gwogwgo ta faɗa tana haki,kuma bata daina jibgar fattu ba ,kamar ta sami jaka.
"Wayyo gwogwgo dan Allah kimin rai hannuna zai karye, wllh bada gangan na fashe miki bokati ba,macizaine suka biyo ni zasu cinyeni shine na gudu amma bada gangan nayi ba wllh"ta faɗa cikin azaba dan tuni ƙarfinta ya kare ko iya ɗaga hannunta bata yi.
"Allah ya tsine muku keda mashizan shegen yaro karuwa ,ina ruwana da macizai ?dama sun cinyeki kowa ya huta mai baƙin hali marar farin jini har yanzu kin kasa auruwa ,dama shegun macizan sun.......kasa ƙarasa magannarta tayi sakamakon wani ƙaton abu dataji ya faɗo kanta jifff !!!kamar buhun hatsi.
"Wayyo Ni Hansai menene wannan ɗin yake zagayemin jiki?ta faɗa cikin firgici da tashin hankali tana mai jefar da iccen hannunta.aikuwa carab idanunta suka sauka akan ƙaton macijin daya nannaɗeta ko motsi bata iya yi,kuma ya fasa kai a saitin fuskarta sai huci yake yana Filato da harshe.
"Wayyo Allah na Ni hansai yau me zan gani ?na shiga ukuna malam kazo fattu ta min ture maciji zai kasheni ka taimakeni, handi ɗin bonu lalashewa ni yar nan wayyo malam"ta faɗa cin tsantsar tsoro da razani da ƙyar take magana dan ba ƙaramin shaƙar mata jiki macijin yayi ba har wuyanta.
Tsoro,fargaba da tashin hankali sune suka daɗa kashewa Fattu jiki ,dan faɗuwa tayi ƙasa warwas ko motsin kirki bata iya yi,shikenan Tata ta ƙare yana gamawa da gwogwgo tasan kanta zaiyo ,Allah Sarki innarta ,yanzu shikenan zata mutu bataga innarta ba,batasan ya fuskarta take ba ?bare tasan dangin innarta?,amma Gara ta mutumma ta huta da wannan baƙar azabar da take sha agurin gwogwgo.
Shikuwa macijin nan ƙara matse gwogwgo yake sosai ,gaba ɗaya ta fice daga hayyacinta,dan ko magana ma ta kasa ,idanunta sunyi jajur sai nishi take numfashinta na ƙoƙarin ɗauke wa.
Saida macijin nan yaga gwogwgo bata motsi alamun ta suma,kafin ya sake ta ta hanyar janye jikinsa daga gareta.
Da gudu kuma yayi kan fattu wacce ke kwance cikin tashin hankali ganin yadda macijin nan ya kashe gwogwgo.runtse ido tayi da mugun ƙarfi tana salati da sallama da duniya,ko motsin kirki batayi ,dan da kyar take iya jan numfashi ma.
Shikuwa macijin nan yana zuwa gareta ya tsaya saitin fuskarta ya fasa kai yana huci,sai kuma ya fara zagayeta cikin sauri da sassarfa, kafin kuma ya fara hayewa kan ruwan cikinta........
Masu karatu mezai faru da fattu ?
Me macijin nan yake nufi da ita ne?
Anya ma macijin ne shi?
Saimun haÉ—e next page in Sha Allah taku har kullum anty mammy
Mrs babi💘💘💘
Share and comment fisabilillah.
More comment
More typing.
29/08/2022, 10:44 am - Khadijah Salisu Fari: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄
MACIJINE SHI🪱🪱🪱
Na manya kabeer
(Anty mammy)
Elegant online writers📚📚
Free book
Page 5/6
________________Hawa macijin nan yayi kan ruwan cikin fattu ,daidai kan fuskarta ya tsaya tare da fasa kansa ,ya tsaya ƙuri yana kallon fuskar Tata, wacce tuni idanun fattu ke rufe tayi mutuwar kwance ko nunfashi ta kasa shaƙa cikin salama.
Shikuwa macijin nan ganin bata koda motsi saiya sauƙo daga ruwan cikinta ya tsaya saitin fuskar tata tare da fasa kansa yana huci ,.matsowa yayi sosai jikin fuskar tata yana hura mata iska daga bakinsa,sannan ya ɗan ja da baya ya tsaya yana kallon ta.
Ahankali fattu ta ɗan buɗe idanunta dan ganin shin me kuma macijin nan ke shiryawa ?ta yaya yake tsara kasheta itama,saidai tana buɗe idanta suka sauka akan na macijin nan ya ƙureta da idanunsa.
Cike da tsoro da fargaba fattu ta kafe shi da nata idanun,dan tsintar kanta tayi da kasa daina kallonsa,abubuwan mamaki take gani tare da macijin,sam kwayar idanunsa ba irin ta macizai bace,sak!irin ta mutane ce saidai gurin farin yayi wani irin kala kala , blue yellow pink ,Amma asalin kwayar baƙace ƙirin.
Sai kuma taga hawaye na zubowa daga idanun macijin kamar mutum yana kuka.
"Innalillahi wa'inna ilahirin raji'un, Allahumma ajirni fi musibati waaklifni kairan minha,la'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin"shine abinda fattu ta fara karantawa cikin zuciyarta jikinta na wani irin tsuma da karkarwa, tunda take bata taɓa ganin irin wannan macijin ba sai yau,ya maciji zai kasance da idanun mutane? sannan kuma jikinsa akwai banbanci sosai dana macizai,dan shi yana da wani irin jiki mai ban mamaki yadda kalar idanunsa ta kasance haka shima jikinsa yake .sannan kuma bai kai girma irin na macijin jiyan nan ba amma yana da girma shima sosai,kuma dogone na gaske.
Kallon kallo kawai ake tsakanin fattu da macijin nan,inda ahankali ya fara hucewa daga kumbura da fasa kan da yayi ,fattu na kallonsu harya koma normal jikinsa ya daidaita ,sannan ya fara ƙoƙarin barin ɗakin ta wata yar hanya dake jikin katangar karan ,wacce ita fattu sam bama tasan da ita ba sai yau,da alama dai shi yayiwa kansa hanyar.
Saida yaje gab da hanyar tasa saikuma ya juyo da kansa yana kallon fattun,shi bai tafiya ba kuma bai dawo ciki ba.
Sosai jikin fattu ke rawa tana zubda hawaye ,dan yau kam lamarin ya kulle mata kai ,wai wannan wane irin MACIJINE ?shin macijin ne ma kokuma wata halittar?sannan maiyasa yaƙi yi mata komai,sai dai ƙoƙarin ceto ta da yake atsammaninsa na ko bata numfashi?haƙiƙa akwai abin dubawa dan gane da wannan macijin.
"Fattu ! fattu!!kin tashine kinyi sallar lokaci yana ja fa"ta tsinkayo Muryar baffa daga wajen É—akin yana mata magana .
Jin muryar baffa da fattu tayi sai hankalinta ya É—an kwanta cikin É—aga murya tace "baffa kazo ka taimaka min gwogwgo bata motsi"ta faÉ—a cikin Muryar kuka tana kallon macijin.
Cikin sauri da azama baffa ya shigo É—akin yana faÉ—in"subhanallah me kuma ya sami Hansai din?
Cikin kuka fattu ta kalli baffa sannan ta kalli inda macijin nan yake ,har lokacin yana tsaye yana kallon ta,
"Baffa bansani ba kawai ta shigo tana dukana sainaga ta faɗi ƙasa"abinda fattu ta tsinci kanta kenan da faɗa murya na rawa.
Ahankali macijin nan ya juyar da kansa ya bi ta yar ƙofar nan ya fice.
Sai lokacin hankali fattu da nutsuwarta suka dawo jikinta ,cikin ƙarfin hali ta yunƙura ta tashi zaune ,har lokacin akwai alamun tsoro da firgici akan fuskarta,dan jikinta sai rawa yake.
"Washhhh hannuna"ta faÉ—a ahankali tana mai runtse ido,dan sosai hannun ke mata mugun ciwo.
Ruwa baffa ya É—ebo mai sanyi wanda ya taru na sama,yana zuwa ya kwarawa gwogwgo ruwan cikin moÉ—a .aikuwa azabure ta tashi zaune tana ihu"wayyo Allah na maciji zai kasheni malam kawo É—auki ,fattu tayiminn turen maciji,wayyo wuyana ,wayyo hannuna na shiga uku na lalace"abinda gwogwgo hansai ta farka dashi kenan,maimakon ambaton sunan Allah .
"Kayya hansai ki nutsu ba wani maciji ana fa nine bukar wannan kuma fattu ce ɗiyarki"cewar baffa kenan a ƙoƙarin sa na kwantar mata da hankali.buɗe ido gwogwgo tayi sosai ta kallesu kafin tace "kuturin bala'i Allah ya kiyaye wannan sheɗaniyar ta zama ƴata mayyace fa,wllh ture tayimin yanzun na wani maciji ya kusan hallakani,wllh sainaga bayan yarinyar nan Shegiya may.......wayyo Allah na ya dawo ya dawo"gwogwgo hansai ta faɗa sakamakon hango kan macijin nan da tayi ,ai da gudun gaske ta fice daga ɗakin tana ihu .
Girgiza kai baffa yayi yana Allah wadai da halin matar tasa ,sam baiyi dacen mata ba.kallon Fattu yayi wacce take riƙe da hannunta mai ciwon, hawaye na zuba a idanunta na azaba.
"Ashsha ashsha fattu kiyi haƙuri kinji,komai yayi farko zaiyo ƙarshe ,Allah yana sane da halin da kike ciki in sha Allahu zakiyi dariya anan gaba"baffa ya faɗa cikin sanyin murya da ƙoƙarin kwantar mata da hankali.
Ahankali ta sanya hannu ta share hawaye idanunta ,kafin tace "baffa hannu na ciwo yake min"ta faÉ—a tana nuna masa hannun dayake mata ciwon.
Kallon hannun yayi yanda ya kumbura yayi suntum dashi ,cikin tausaya wa yace "ayya faɗimatu sannu. Kinji maza daure kiyi sallah saina duba miki hannu kiyi haƙuri, Allah yayi miji albarka"ya faɗa yana mai taimaka mata ta miki tsaye.
"Ameen baffa "ta faɗa tana ficewa daga ɗakin .bayi ta shiga ta kama ruwa sannan tayi alwala cikin dabara kafin ta fito ta koma ɗakin ,Sallah tayi tare da karatun alƙur'ani mai girma ,da ka take karatun dan da ahaka aka koya mata ,bayan ta idar ne baffa ya shigo ɗakin ɗauke da kwarya ahannunsa ,
" Sannu fattu karɓi wannan madarar Kisha kinji,saina duba miki hannun"baffa ya faɗa yana miƙa mata kwaryar.karɓa tayi ahankali tayi Bismillah ta kafa kanta,saida ta shanye kafin ta ajiye kwaryar .
Allah Sarki fattu tasha wahala sosai lokacin da baffa ke gyara mata hannun ,dan yayi tsami sosai ,kuka harda majina,haka baffa ya gyara mata yana mata sannu.bayan ya gama gyara mata ne yace ta kwanta ta huta kafin garin ya gama wayewa.haka ta kwanta tana ajiyar zuciya ,ba jimawa kuwa barci yayi gaba da ita ,abinka da wanda bai sami barci ba dama.
Ficewa baffa yayi daga ɗakin ya nufi nashi cike da tausayin ƴar tashi dayake matuƙar ƙauna.
Ko minti talatin batayi ba tana barcin ta tsinkayo muryar gwogwgo tana kiranta "Ke gantalalliya mayya fito dan ubanki ,ko uwarki ce zata miki aikin?Shegiyar yarinya aljana wllh bakici bulusba yadda kika sa macijin nan ya lagartamin jiki to wllh saina rama ,fito ki É—ebomin ruwa yanzun nan .
Afirgice fattu ta tashi daga barcin ta fito da gudu tazo tana rawar jiki ,Dan bala'in tsoron gwogwgo take kamar ranta."gwogwgo dame zan É—ebo ruwan "ta faÉ—a kanta asunkuye.
Da ubanki zaki ɗebo ruwan kinji ?kije ki nemomin kuɗin da zaki biyani bokatina inyaso ki ɗebomin ruwan aciki"gwogwgo ta faɗa tana daga ɗaki,dan taƙi fitowa waje kartaje macijin nan ko ajikin fattun yake.
Masu karatu har zuwa wannan lokacin fa yaran gwogwgo hansai suna kwance aÉ—aki suna barci.
Amma take ƙoƙarin tura fattu ɗiban ruwa da wannan safiya,alhalin bata da lafiya.dan lokacin da baffa ke gyara mata hannun tana jin ihunta.lokacin tana kwance akan gado tana hucin azabar da macijin nan ya gana mata,"Shegiyar yarinya Gara kemaki ɗandana azabar dana sha ,Allah yasa hannun ya karye ma kowa ya huta.
"Dan Allah gwogwgo kiyi haƙuri wllh bansan inda zan samo kuɗin ba kiyimin rai "fattu ta faɗa cikin kuka.
"Dan kan ubanki tashi ki É“acemin da gani,wllh kome zakije kiyi bai dameni ba Indai zaki kawomin murtala uku da raina gomata."ta faÉ—a tana rarumo wani busasshen kwanon tuwo aÉ—akin ta cillowa fattu shi.
Allah ne ya kare fattu da tuni kwanon ya sauƙa akanta ,tayi saurin ficewa da gudu daga gidan.
"Shegiya da kin tsaya ai"cewar gwogwgo tana mai kwanciya ba ko sallar safiya.
Koda fattu ta fita daga gidan kuka take sosai ,batasan inda zata nufa ba ,ina zata samo Murtala uku da Naira goma?waye zai bata waɗannan iyayen kuɗin? Kodai gurin jauro zataje tace ya taimaka mata da Murtala uku da Naira goman?kai a'a bazataje ba, dan jauro ba mutumin kirki bane ,ranar nan ma hannunta yake ƙoƙarin kamawa wai yana sonta,kuma baffa yace maiyin hakan ba mutumin kirki bane.
Kusan minti biyar tana saƙa da warwara,kafin ta yanke shawarar kawai ta tafi bakin rafin ta zauna ko Allah zai sa ta sami abun ɗiban ruwan.
Tafiya take ahankali ,wanda kallo É—aya zaka mata kasan batajin daÉ—i,hannunta mai ciwon kuwa ta rikeshi da É—ayan hannun.haka ta nufi rafin dake can bayan gari cikin jeji.
"Hai jauro wai kuwa kaga Abinda nake gani"?
Cewar haroji kenan wanda suke zaune akan wata bishiya shida jauro can kusa da rafin da fattu ta nufa.
"Wanda aka kira da jauron ne ya ɗago kanshi dake duƙe yana zuƙar sigari yace "me ka gano mana"?
"Wllh fattu ce kuma ita kaÉ—ai kaganta can ta nufi rafi"ya faÉ—a cikin É—oki da zumuÉ—i.
Da sauri jauro ya kalli gurin da harojin ke nuna masa ,aikuwa fattu ya hango ,cikin hanzari ya fito daga kan bishiyar yace "wayyeee huuhuuu ,yau kam mun fito asa'a dan wllh saimun aikata mata ,wllh saina kusan cinye fattu yau "ya faɗa cikin murna da farin ciki yana mai bin hanyar da fattu ke tafiya,harta kusan ƙarasawa rafin.
Da sauri haroji yabiyo bayansa yana faÉ—in"ai wllh nima saina É—ana yau É—innan inka gama saika birmin siÉ—i"
Da sauri suke tafiya dan haka cikin ƙanƙanin lokaci suka cimma ta.kawai sai gani tayi sun sata atsakiya.
Kallonsu tayi cikin tsoro da fargaba,tace"meye hakan jauro ku bani hanya in wuce"ta faÉ—a cikin dakiya da nuna alamun bata tsoro su.
Dariya suka kyalkyale da ita ,kafin jauro yace "wllh fattu yau saina kusan shinyeki gaba É—ayanki Allah ne ya kawo mana ke dan haka maza kwanta "ya faÉ—a cikin jahilci da rashin imani.
Cikin tsoro da fargaba fattu ta fara ja baya tace"jauro me na maka zaka cinyeni?dan Allah kayi haƙuri wllh bana son mutuwa yanzu ina son ganin innarta"ta faɗa lokacin harta fara zubar da hawaye.
Dariya suka saka sakawa suna tafa hannu kafin haroji yace"jauro kawai kamata da shegen ƙarfi dan bazata kwanta ba ,kuma fa kamar bata san me kake nufi ba " aikuwa jin haka sai jauro ya cakumo fattu yana faɗin aikuwa yanzu zata san me nake nufi ,yarinya kin cika kin batse amma ba mai amfana dake" nan da nan suka fara kokawa,yana ƙoƙarin Kaita ƙasa ,ita kuma tana Turkewa da ƙoƙarin kwatar kanta. kasancewarsa namiji tuni yaci ƙarfinta dan har ya Kaita ƙasa,ga ciwon hannu.
Daram ya zauna akan ruwan cikinta yana ƙoƙarin cire mata riga.dan tuni shikan ya cire wandonsa daga shi sai wata yar Shara ajikinsa banda wari ba abinda yake yi .haroji kuwa yana tsaye ya juya baya yana gane musu koda me tahowa.
Ihu fattu take cikin tsantsar tsoro da tashin hankali ,tayi mugun razana da ganin abinda jauro ke ƙoƙarin tura mata a bakinta yana fadin"maza Kisha fattu haka ake mana lagus sha maza kiji akwai daɗi"ya faɗa yana ƙoƙarin tura mata jauronsa abakinta wacce ganinta kaɗai ya mugun tsorata fattu.dan bata taɓa ganin wannan ƙaton abun mai numfashi haka ba sai yau.
"Wayyo Allah na shiga uku jauro menene wannan kake ƙoƙarin bani abakina ka bari bana so wayyo hannuna ,wayyo baffa zan mutu" ta faɗa tana wani irin kakkafewa jikinta na wani irin ɓari.
"Wllh yau ko zaki mutu fattu saina kusan cinyeki dan na jima da yunwarki araina, yau kuwa ba mai hanani yin.......wayyo Allah menene wannan haroji maza zoka taimakeni"jauro ya faɗa lokacin da yaji wani gibgegen abu ya fado kansa ya duƙunƙune shi sannan yasa baki ya cafke aliyarsa.
Ihu jauro ya kurma mai ƙarfin gaske ya daɗi can gefe guda........
Masu karatu,menene wannan ya faÉ—owa jauro?
Me zai faru nan gaba?ku biyoni next page in Sha Allah,taku anty mammy
Mrs babi💘💘💘
Share and comment
Fisabilillah.
More comment
More typing.
29/08/2022, 10:44 am - Khadijah Salisu Fari: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LsrDragdsZn2UMCRLPA7uv
Banda maza Please mata kawai .
By mammy kabeer
🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄
MACIJINE SHI 🪱🪱🪱
Na mammy kabeer
(Anty mammy)
Elegant online writers📚📚
Free book
Page 7/8
________________Ihu jauro ya kurma mai ƙarfin gaske ya faɗi can gefe yana burbura tare da rikan "wayyo haroji jaurota zai cinyemin ka taimakeni zan mutu wayyo maciji "ya ƙarasa faɗa da kyar sakamakon wata danƙa mai ƙarfi da macijin nan yayiwa jauronsa har saida numfashinsa ya ɗauke .
Haroji kuwa ya mugun tsorata ganin halin da jauro ke ciki,ga wannan ƙaton macijin daya kanannadeshi yana ƙoƙarin karya masa ƙasusuwa.
Cikin kiɗima ya rarumo wani ƙaton dutse yayi kan jauro da wannan macijin,yana zuwa baiyi wata wata ba ya ɗaga dutsen ya kwaɗawa macijin nan abayansa.
Aikuwa nan da nan bayan macijin ya fashe jini yayi tsartuwa har kan fuskar haroji,wani ihu haroji ya kwala ,sakamakon sauƙar jinin macijin nan akan fuskarsa ji yayi kamar an watsa masa ruwan batir,nan da nan gurin ya sale kamar wanda ya ƙone sai turiri gurin yake.
Jifa haroji yayi da dutsen hannunsa yana ihu yana faÉ—in"wayyo Allah idona bana gani wayyo kwayar idona ta zazzage na shiga ukuna "abinda yake daÉ—i kenan yana ihu da tsalle.
Shikuwa macijin nan silalewa yayi daga jikin jauro ya koma gefe guda tare da kwantar da kansa akasa ,dan kuwa sosai haroji ya kwada masa dutsen nan,kuma da alama ya shige shi .
Gaba ɗayan abinda ke faruwa akan idanun fattu ,tana kwance tana kallon ikon Allah,tabbas zuwa yanzu ta gama yarda cewa macijin nan bashi da biyar cutar da ita ,saima taimakon ta da yake,shin wanene wanan macijin?meye alaƙarta da shi?me yake nema agurinta?anya ma MACIJINE wannan ?kodai aljanine yake zuwa mata asiffar macijin? Wadanna sune tarin tambayoyin da fattu ke yiwa kanta tana daga kwancen wanda bata da amsarsu.
Saidai kuma gaba ɗaya hankalinta ya tashi ganin yadda macijin nan ya kwanta lamo kamar ya mutu.nan da nan tsoro ya mamaye zuciyarta ,cikin dauriya da jarumta ta yunƙura ta miƙe tsaye tana yamutse fuska,hannunta mai ciwon yana riƙe aɗaya mai lafiyar.
Gurin macijin ta nufa gabanta na ci gaba da faɗuwa,dan tsoro take kar ita kuma yayi mata wani abu.tana ƙara sawa ta durƙusa ahankali dai dai inda haroji ya buga masa wannan dutsen ,hannu ta sanya ahankali ,cikin karkarwa jiki ta ɗan shafa gurin ciwon.ai tana ɗora hannunta agurin macijin nan yayi wata irin juyowa tare da fasa kai kamar zai sareta, cikin tsoro da fargaba ta cire hannunta tare da matsawa baya da sauri tana zare ido tana kallon macijin.
Shima yana juyowa yaga fattu ce ,sai ya tsaya yana kallon ta,tare da komawa yadda yake ,wato ya sassauta fusatar da yayi ,kawai ya tsaya yana kallon ta.
Itama kallonsa take cikin tsoro da bugawar zuciya,ahankali macijin ya fara tahowa ,har ya zo gareta ,runtse idanu tayi tana karanta addu'ar Allah ya tsareta.
Ga mamakinta kawai saitaji macijin ya hau kan cinyarta ya kanannaÉ—e jikinsa ya dora kansa a saman gammon da yayi da jikinsa.
Ahankali ta buÉ—e idanunta tana kallonsa,shima ita yake kallo saidai idanunsa na zubar da hawaye kuma na jini .
Jikinta kawai rawa yake cike take da tsantsar tsoron abinda zai faru .juyawa tayi tana kallon haroji dake ta faman ihu yana yaÉ—uwa kasa.sannan ta kalli jauro wanda yake kwance ba alamun numfashi atare dashi,ga jauronsa nan tayi wani irin kumbura na ban mamaki sai jini ke zuba .
Tsorone ya ƙara kamata cikin azama ta yunƙura tare da mikewa tsaye, ture macijin tayi daga jikinta ta kwasa da gudu tayi gida tana kuka .
Koda taje gidan, da sanÉ—a tayi saurin shiga É—akinta tana kuka,zama tayi akan tabarmarta tare da kife kanta a tsakanin cinyoyinta tana kuka.damuwace fal cikin ranta,wai meke shirin faruwa ne da rayuwarta?wacece mahaifiyarta?waye wannan macijin da yake É—aukan hukunci akan duk wanda yayi nufin cutar da ita?tanasan sanin wannan macijin waye shi,kokuma waye ya aikoshi gareta.tana cikin kukanta ne kawai taji abu yana hawa jikinta silililili!!! Afirgice ta É—ago kanta tana kallon macijin daya gama hawa jikin nata. kansa ya É—ora akan wuyanta yana fidda wani irin huci ,shiru tayi tana sauraron yadda macijin ke huci,sanan jikinsa yayi wani irin zafi sosai.duk yadda akayi bashi da lafiya ,kuma dukan da haroji yayi masane solar hakan.
Tausayinsane taji yayi mugun kamata,ahankali cikin tsoro ta miƙa hannunta tare da riƙo saitin wuyansa ahankali ta janyoshi, ko motsi baiyi ba bare ya hanata abinda yake yi ɗin.
Akan tabarmar ta ɗorashi tare da ci gaba da kallonsa,cikin muryar kuka tace "bawan Allah kai waye?meke tafe dakai?waya aikoka zuwa gareni?meyasa kake ƙoƙarin daukar mataki akan duk wanda ya zalumceni?dan Allah karka cutar dani, bani da kowa sai baffana,dan Allah kayi tafiyarki ,idan mutanen garin na suka farga da kai zasu kasheka ,bazan so hakan ba dan Allah na roƙeka ka tafi"ta ƙarasa maganar tana haɗa hannunta cikin kuka.
Shidai macijin nan ko motsi baiyi ba sai huci da yake yi sosai,
Ahankali ta kalli gurin da yaji ciwo dazu sai taga gurin yana turiri kuma yayi wani fari fat.shiru tayi tana kallonshi ,yanzu ya zata yi masa ne?dan da alama fa yana jin jikine, data rasa abinyi kawai saita lulluba zanin sallarta ta fara karatun Alqur'ani mai girma.cikin abinda bai wuce sakwan biyar da fara karatunta ba kawai macijin nan ya fara wata irin murmurɗewa yana sauya kala, da farko yayi jajur dashi,sai kuma yazo yayi baƙiƙirin sosai ,wani irin hayaƙi na fita daga jikinsa .
Duk abinda yake sam fattu bata kulaba ,dan ta É—aga kanta sama ne tana karatun ,kuma idanunta na zubda kwalla.
Shikuwa macijin nan burburwa ya ci gaba dayi yana murɗewa jikinsa na turiri tare da sauya kala.can kuma ya fara wani irin ƙara mai kama da gurnanin zaki.cikin tsoro fattu ta dawo da kanta ƙasa tana kallon macijin , sakamakon wannan sautin ƙara da taji yanayi.sai lokacin hankalinta ya kai kanshi taga abinda ke faruwa.
Tsorone ya kamata ƙarara "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un"shikenan ta tabbata wannan ba maciji bane tabbas aljanine ,ko kuma aljanine ya shiga jiki sa,na shiga uku ni fattu ya zanyi da rayuwata?meke shirin faruwa dani" ta faɗa cikin muryar tsoro da shiga ruɗu.
Shikuwa macijin nan tana daina karatun saiya daina burburwar da wanann gurnanin,ahankali kuma jikinsa ya dawo yadda yake . Ya jima kwance lamo kafin ya fara motsi,kansa ya ɗago tare da fasa kan yana kallon fattu,gaba ɗaya idanunsa sun koma baƙiƙirin dasu sannan wasu irin ƙananan layoyi suka bayyana kusan guda uku aƙasan kanshi, sai wani irin motsi suke kamar ya'yan tsutsa.
Karkarwa jikin fattu keyi kamar an saka mata shokin, lamarin ya matukar bata tsoro ,meye wannan É—in haka suka bayyana jikin macijin nan? Me yasa daga fara karatun Alqur'ani gaba daya ya sauya kama?tabbas akwai wani boyayyen al'amari game da wannan halittar dake gabanta,kuma zata ci gaba da bibiyar macijin nan sannu kan hankali har saita gano menene tattare dashi.
Tana nan maƙale jikin katangar karanta kamar ƙadangaruwa dan tsabar tsoro da shiga shock ,idanunta ƙuri akan macijin ,wanda shima ita yake kallo ,kusan minti biyar suna haka ,taga macijin ya sulale ya bar ɗakin ta wannan hanyar tashi.
Rarraba idanu ta farayi tana dafe da ƙirjinta ,yau kam tana ganin ikon Allah kala kala ,anya kuwa bata janyowa kanta masifa ba?waima meye alaƙarta da wannan halittar ne?ko dai baffanta zata sanarwa halin da ake ciki ne?kai a'a ba yanzu ba tukunna ,ya kamata ta zama jaruma tayi wanann aikin koba komai zata taimaki rayuwar macijin,dan ta fahimci akwai boyayyen al'amari atareda shi.
Su haroji kuwa gaba ɗaya ya fice daga hayyacinsa sai ihu yake yana faɗuwa ƙasa ,ahaka ya nufi gidan lamiɗon garin ,wanda shine mahaifin jauro ,yana ihu yana tumami, har yaje gaban lamiɗo ya faɗi yana "wayyo idanuna ,wayyo fuskata lamiɗo ka taimaka min.
Ruɗewa lamiɗo yayi wanda yake tsaye jikin wata sanuwa yana bata ciyawa, lamiɗo bashi da imani ,azalumine sosai ,kuma mutanen garin suna matuƙar tsoronsa, dan haka yake mulki na zalumci agarina,ganin halinda haroji yake ciki"kai haroji menene hakan ?ina jauro?me yasameka?sune tambayoyin da lamiɗo ya jerowa haroji
Cikin azabar ciwo da fitar hankali haroji yace "jauro ya mutu maciji ya cinye masa jauronsa yana bakin rafi"
Ai dajin wannan batu hankalin lamiɗo ya tashi ,nan da nan yayi kan haroji yana faɗin wane macijin ?me kake cewa ?jauro ya mutu?ƙaryane badai agarina ba ,ba wanda ya isa ya zo garina ya kashe min ɗana."lamiɗo na gama faɗin haka ya kira mazan garin ,ya sanar dasu maza aje bakin rafi ataho da jauro.
Aikuwa cikin ƙanƙanin lokaci aka ɗauko shi kamar gawa .
Nan da nan lamiÉ—o ya nemi haroji ya sanar dasu abinda ya faru .
Nan ya sanar dasu iya abinda idanunsa suka gani,dan shima yana cikin mugun halin mutuwa ko rayuwa dan tuni gurin da jinin nan na macijin ya taɓa ajikinsa yayi wani irin kore shar yana zubar da wani yallow ɗin ruwa .
"LamiÉ—o fattu ce ta Turo mana macijin nan ,shine ya kashe jauro"abinda haroji ya faÉ—a kenan ya sume.
Nan da nan mutanen gurin suka fara maganganu Suna faÉ—in da "da hansai ta faÉ—a tace mayyace yarinyar ,tunda har ta fara kashe mutane ba zasu yarda ba sai an hukunta itama.
Ran lamiɗo ya ɓaci sosai ,dan dama yana jin haushi yarinyar da ubanta,ya shirya neman aurenta amma sam taƙi yarda wai karatu take,yanzu kuwa dama tasameshi da zai hukunta su ita da tsohon nata.dan haka cikin bada umarni yace lallai lallai aje ataho da fattu da ubanta .
Nan da nan fusatattun maza suka nufi gidan malam bukar dan aiwatar da ƙudurin lamiɗo........
Masu karatu meke shirin faruwa ne ?
Wane hukuncin lamiÉ—o zai zartar akansu fattu?
Mai zai far nan gaba?
Muje zuwa yaki ce dai anty mammy
Mrs babi💘💘💘
Share and comments fisabilillah.
More comments
More typing.
29/08/2022, 10:45 am - Khadijah Salisu Fari: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄
MACIJINE 🪱🪱🪱
Na mammy kabeer
(Anty mammy)
Elegant online writers📚📚
Page 9/10
__________________Nan da nan fusatattun rugar suka nufi gidan malam bukar ,dan aiwatar da ƙudirin lamiɗo.
Allah Sarki fattu kuwa a wanann lokacin tana ɗakinta cikin jimami da tunanin abinda ta gani yau ɗin nan,haka nan ta tsinci kanta da son sanin menene wannan abubuwan dake motsi aƙasan wuyan maciji? wanda tun daɗewa bata taɓa ganinsu ba sai yau,waya sani ma ko wani akayiwa asiri ajikin macijin ?tabbas zatayi iya ƙoƙarin ta dan ganin ta raba macijin nan da wannan abubuwan ,ta yadda koda wani aka yiwa asiri ta hanyar macijin, to asirin zai karye .sannan tana fargabar gwogwgo ta gano cewar tana gidan kuma bata ɗebo ruwan ba.kuma ahalin da ake ciki yanzu bazata iya komawa rafin nan ba ,.dan ta tsorata dasu jauro .
Hayaniyar mutane ce ta cika gidan nasu fattu ,wanda haka yasa gwogwgo hansai fitowa dole badan ta soba, Dan har lokacin nan ita da yaranta ba wanda yayi sallar asuba.
"Kai su waye haka suka zo suka cika mana gida da ihu kamar ana yaƙi?"cewar gwogwgo hansai tana gyara daurin ƙirjinta dake ƙoƙarin kuncewa bayan ta fito daga ɗakin.
"Aa meye hakan arÉ—o ?lafiya na Ganku da yawanku kun shigo?ta tambaya lokacin da idanunta ya sauka akan mutanen da suka cika gidan,kusan duk mazan garin ne.
Cikin masifa wanda aka kira da arÉ—o yace "wllh yau saimun É—auki mataki akan bukar da fattu ,haka kawai yarinya ta fara kashe mutane ,kuma ta rasa ta kan wa zata fara sai É—an gidan lamiÉ—o ?wllh yau sai mun kashe Shegiyar yarinyar nan"ya faÉ—a yana wani zazzaro idanu kamar zararre.
Eh wllh afito mana da ita kawai mukaita gurin lamiɗo ya bamu izini mu kashe mayya.gaba ɗayan mutanen gurin suka faɗi haka cikin nuna fusata da ƙosawa abasu fattun .
Wani irin farin ciki da jin daɗine ya kama gwogwgo hansai ,shikenan zata rabu da alaƙaƙai cikin sauƙi Allah yasa akasheta kowa ya huta ,dama su haɗa da bukar ɗin da yake ɗaurewa fattu gindi ,koba komai shanunsa sun zama nata.gwogwgo hansai ta faɗa cikin ranta.kafin ta kalli arɗo da sauran mutanen tace "aikuwa idan aka kasheta an kyauta ,dan nima nan wllh so take ta cinyeni nida yarana, jiya da kyar mukasha data maƙuremin wuya wai saita cinyeni, ku ɗan jira kaɗan yanzu zaku ganta shegiya gantalalliya,banma san inda ta tafiba, dama haka takeyi kullum inta fice yawon iskanci bata dawowa da wuri,tana can gurin maza"gwogwgo hansai ta ƙarasa maganarta tana mai buga hannu acinya.
"Aikuwa yanzu zamuje mu nemota ko ina ta shiga,wasu sutafi bakin rafin wasu sushiga jeji, mukuma zamu jira ana "cewar arÉ—o kenan yana kafe sandarsa akasa,sannan ya gyara tsayuwarsa.
Duk wannan abunda ke faruwa akan kunnen fattu, tana jin komai ,saidai tashin hankali,firgici tsoro da kuma ruÉ—ewa sun hanata koda yin kwakwkwaran motsine .
Numfashinta ma da ƙyar yake fita tsabar ruɗewa.
Ta shiga uku !shikenan yanzu kasheta za'ayi?laifin me tayi da za'a kasheta?me baffanta yayi ake nemansa shima? Dama jauron mutuwa yayi ? innalillahi !!!yanzu ya zatayi.
Wani kukane ya kubce mata cikin sauri ta toshe bakinta tana kuka sosai kamar ranta zai fita,ji take dama tana da ikon É“acewa, tabbas da ba abinda zai hanata É“acewa ta bar duniyar ma gaba É—aya.
Ahankali ta miƙe cikin sanɗa ta leƙo da kanta ,ba ƙaramin tsoro tajiba lokacin da taga mutanen da suka zo tafiya da ita.shikena kawai ta mutu,yanzu shikenan bazata cika burinta na ganin innarta ba?wayyo "Allah ka kawomin ɗauki "ta faɗa cikin raunananiyar muryarta mai cike da tsantsar tsoro.
Ahankali ta ƙara leƙo da kanta waje ,cikin rashin Sa'a kuwa sukayi ido huɗu da dan gidan gwogwgo hansai umaru.wanda hayaniyar mutane tasa suma suka farka.
"Laaaah aradu gwogwgo ga fattun can cikin ɗakinta tana leƙowa"ya faɗa yana nuna ɗakin da Fattu ke ciki
.cikin hanzari fattu ta koma cikin ɗakin tana mai runtse idonta ,tare da dafe ƙirjinta."shikenan sun ganni wayyo Allah na baffa,wayyo MACIJINA kana ina kazo ka taimakeni zasu kasheni wayyo ni fattu"fattu ta faɗa tana mai leƙa hanyar nan da macijin Kebi idan zai bar ɗakin nata inya zo kamar Zariya haka take bankada hanyar macijin da hannunta.
"Munafuka ,mayya dama kina ji ana neman ki shine kika ɓuya nan?to fito yau dubunki ta cika ,mutuwa zakiyi wllh saikin bar duniyar nan yau nima na huta da ganinki ,maza arɗo zoka tafi ta ita gata nan"gwogwgo hansai ke faɗin wannan maganar tana daga bakin ƙofar dakin Fattu,dan tun lokacin nan da tasha matsa agurin maciji bata ƙara shiga ɗakin Fattun ba.
Aikuwa kafin ta rufe baki su arÉ—o sukayo kan Fattu suna janta.
"Wayyo Allah gwogwgo karki bari su tafi dani zasu kasheni ,wllh ban aikata komai ba wayyo Allah na gwogwgo ki taimaka min"abinda Fattu ke faɗi kenan tana miƙawa gwogwgo hannu cikin kuka mai tsanani.
"Ai wllh dana taimakeki gara hannuna ya karye Shegiyar yarinya ,kutafi da ita can ku kashe banza" gwogwgo ta faÉ—a tana kaÉ—a hannu irin yadda ake korar kaji ,cikin farin ciki take maganar.
Ihu Fattu keyi tana kuka,amma haka suke janta kamar akuya aƙasa, suna cikin tafiya ne ,saiga baffa aguje yazo gabansuu ya tsaya riƙe da sanda yana ta haki,dan yana can bayan gari ya sami labarin abinda ke faruwa acikin garin da gidansa,shine ya rugo yazo .
Aikuwa Fattu na ganin baffa ta ƙara fasa ihu tana cewa" wayyo baffana ka taimakeni zasu kasheni" ta faɗa tana miƙa masa hannu,abin tausayi dukta susuce tayi buju buju da jiƙaƙkiyar ƙasa.kallonta baffa yayi
Cikin bacin rai mai tsanani ya ce.
"Sakarmin yarinya arɗo, kona rotsa maka sandar nan akanka" baffa ya faɗa cikin hargowa da ƙaraji,
Kasancewar baffa kowa ya sanshi arugar mutumin kirki ne ,sam ba ruwansa da shiga harkar wani,sanan kuma shine ke ja musu jam'i ,hakan yasa suke ɗan ganin girma da mutuncinsa, dan haka cikin Turo baki da hura hanci arɗo yasaki hannun Fattu wanda ke mata azabar ciwo da raɗaɗi,yana mai cewa"ato lamiɗo ne dai yace mu taho daku,dan haka ya zama dole ayiwa lamiɗo biyayya"ya faɗa yana hararar gefensa, dan yaji haushin sakin wannan hannun na Fattu mai shegen laushi da daɗin taɓawa da baffa yasa yayi.lol
Fattu kuwa yana sakar mata hannu ,da rarrafe ta ƙara so gurin baffa ta rirriƙe shi tana kuka da faɗin"wllh baffa ba abinda na aikata,ban kashe jauro ba " ta faɗa cikin matsanancin kuka da tsoro, jikin ta sai rawa yake.
Riƙota baffa yayi cikin tausayawa yace "na sani Fattuna,baki kashe jauro ba ,kuma ba wanda zai kasheki, Allah na tare dake kinji"?ya faɗa cikin sigar rarashi,sannan ya kalli arɗo yace"kai arɗo ka kiyayeni ,karka ƙara ƙoƙarin sake aikata irin wannan dabbacin akan ƴata, saboda baka da hankali shine zaka rinƙa janta aƙasa. Kamar wata dabba ?jahilan banza jahilin hofi,muje gurin mai garin zanji idan shiyasaka wannan ɗanyen aikin"baffa ya faɗa cikin mugun bacin rai yana mai riƙe Fattu suka nufi faɗa.
LamiÉ—o na hangosu ya fara lasar baki ya kure fattu da idanu kamar maye , yana kissima abubuwa da dama cikin ransa....
Manage please yau ina busy,Dan banyi niyar typing bama yau wllh.
Masu karatu me lamiÉ—o ke nufine shima?
Hmmmmmm kubiyoni mu hade bayan sallah danjin yadda zata kaya.
Kafin nan ina mana fatan yin salla lafiya,sannan aci Nama ahankali kar azo ana .......
Taku anty mammy
Mrs babi,💘💘💘
29/08/2022, 10:45 am - Khadijah Salisu Fari: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄
MACIJINE 🪱🪱🪱
Na mammy kabeer
(Anty mammy)
Elegant online writers📚📚
Free book
Page 11/12
Ta ƙabbalallahu Minna waninkum.
Slm, ƴan uwa masoyan littafin MACIJINE, ina miƙo gaisuwa tare da Barka da Sallah ,Allah ya maimaita mana,yasa munyi karɓaɓɓiyar
Ibada.
________________Kai tsaye su baffa suka nufi gurin lamiɗo,hannunsa riƙe da na fattu ,wacce ke tafiya ahankali cikin azabar raɗaɗin da hannunta keyi,dakuma ciwon jiki.yayinda su arɗo ke mara musu baya burinsu kawai suga wane irin hukunci lamiɗo zai ɗauka akansu fattu ,cikin zuciyarsa arɗo yake fatan inama lamiɗo ya kori su fattu daga rugar ,inyaso su bisu hanya suyiwa fattun fyaɗe,dan su kashe ƙishirwarta dake cin ransu.
Shikuwa mai gari tun daga nesa ya hango su fattu,gaba ɗaya nutsuwarsa ta bar jikinsa,ƙureta yayi da ido guri!!yana haɗiyar yawu da lasar leɓe kamar tsohon maye.
Kallonta yake yana ji kamar yaje ya kamota yayi É—aka da ita.
haba malam ,yarinya bul-bul da ita kamar nunannen tumatur,lallai yau zai sha shagali.lamiÉ—o ya faÉ—a cikin ransa yana mai kallon fattun.
Baffa kuwa suna ƙarasowa gaban mai gari ya nemi guri ya zauna tare da zaunar da fattu kusa dashi,wacce gaba ɗaya arikice take ,tsorone ƙarara shinfiɗe akan fuskarta.tayi luƙus ajikin baffanta jikinta sai rawa yake, ta kasa ɗaga kanta ta kalli kowa ,sai hawaye take sharewa.
Kowa yanemi guri ya zauna ,masu tsayuwa suka tsaya , da ƙyar lamiɗo ya iya saita kansa ya aro nutsuwa ya yaɓa akansa, tare da ɓata ransa ya kalli baffa yace "malam bukar kana sane da irin abinda ƴarka take aikatawa awannan garin ?lamiɗo ya faɗa cikin kakkausar murya .
Ahankali baffa ya gyara zama kafin yace ,naji anata wai wai agari cewar Æ´ata tayiwa su jauro turen maciji ,amma sam ban yarda da wannan magana ba,dan kuwa Æ´ata ba mai kashe mutane bace ,sannan ba mayya bace kamar yadda ake faÉ—a"baffa ya faÉ—a cikin É—aure fuska .
Cike da É“aci rai lamiÉ—o ya fara magana.
"To wllh malam bukar bazan É—auki wannan abun agarina ba,yanzu ace abun nata ya wuce kan kowa sai kan É—ana ?sannan kuma kace wai baka
yarda da zancen ba ?kana nufin nayi maka ƙarya ne?to bari kaji dole ne saina ɗauki mataki mai ƙarfi akanka da ƴar taka ,dan ka nuna rashin ɗa'a a gaban fada.bayan kuma kowa yaga abinda ƴarka tayiwa yaranmu,
Dan haka bazan yanke hukunci yanzuba sai zuwa gobe ,idan yaranmu sun sami lafiya,dan haka yanzu za'a shiga da ita cikin gida anan zata zauna cikin wancan bukkar da ake ajiye masu laifi .
Dan haka kowa ya watse sai zuwa gobe da la'asar adawo nan dan jin hukuncin da zan yanke"mai gari yana gama faÉ—in haka ya jingina da jikin kujerar da yake zaune akai.
gaba É—ayan mutanen dake gurin sunyi na'am da wannan hukuncin nacewar fattu ta zauna a gidan mai gari ,dan karta gudu.
Kuka sosai fattu ta sanya tana riƙe hannun baffa "wayyo Allah na baffa ka taimakeni,dan Allah karka bari akulleni adakin hukunci ,wllh bani nayi musu haka ba ,kuma sunzone da nufin keta min haddi baffa ka kalli Yadda ya famamin targaɗe na wllh ba laifi na bane" fattu ta faɗa cikin matsanancin kuka kamar zata shiɗe.
Cikin tashin hankali baffa ya riƙe hannun Fattu ,ji yake kamar ya fasa ihu,aduniya ba abinda ya tsana irin yaga Fattu cikin damuwa,"kiyi haƙuri fattu ba abinda zai sameki,in Sha Allahu Allah zai saka mana dan wannan mugunta ce ake son yi mana ,kuma Allah yana bayan mai gaskiya"yana gama faɗin haka ya juya gurin mai gari yace "lamiɗo ina neman alfarmar abarmin fattu mu tafi gida ,zamu dawo da ita zuwa goben,dan bata da lafiya kuma barinta ita kaɗai akwai matsala" ya faɗa cikin damuwa da alhinin wannan rashin adalci da ake ƙoƙarin aiwatar musu.
Cike da mugunta lamiÉ—o yace "kai bukar ina ganin girmanka karkasa in daina gani ka iya bakinka a faÉ—a kake,kasan idan na riga yanke hukunci ba mai ja dani ,dan haka ka tashi ka bani guri tun kafin raina ya gama É“aci kuma yanzu zansa aje anemomin macijin duk inda ya shiga daga nan zuwa safiya ,"lamiÉ—o ya faÉ—a yana mai kiran wasu matasa yace su shigar da fattu cikin bukkar.
Kuka fattu keyi tana faɗin"wayyo baffana wayyo Allah ka taimakamin zasu tafi dani wayyo Baffa na karka bari su nemo shi zasu kasheshi. "amma haka suka tura ƙeyarta suka tafi da ita ɗakin hukunci.baffa yana ji yana gani ,hawayene masu zafi suka silalo daga idon bawan Allah ,zuciyarsa kamar ta faso ƙirjinsa yakeji, ashe ma ƙoƙarin keta masa haddin ƴa akayi?amma saboda rashin imani da adalci aka ɗora mata sharri,ba komai Allah zai saka musu.
Juyawa yayi ya nufi gida ransa amatukar jagule,yanzu idan wani abun ya sami yarinyar fa?idan wasu suka ƙara yunƙurin cutar da rayuwarta fa?"ya Allah ka karemin yarinyar nan Allah ka duba matsalolin dake kanta da wanda suke shirin samunta.ya Allah ka sauƙaƙa mata ƙalubalen dake gabanta.haka yayi ta mata addu'a harya ƙarasa gida kwata kwata hankalinsa baya jikinsa.
Yana shiga gidan gwogwgo hansai ta sanya dariya cike da mugunta harda riƙe ciki tana nuna baffa da hannu."wllh malam Gara ka cire wannan yarinyar daga zuciyarka, inba haka ba kana tsaye zaka yanke jiki ka faɗi ka mutu.ba ruwa na bani da asara, ai wllh banso lamiɗo ya kyaleta wai har sai gobe ba,daya sani yasa anyanke mata kai yau -yau ɗin nan ,da mun huta da nauyinta akanmu" ta faɗa tana turo wani baƙin ɗan kwalinta mai shegen datti zuwa gaban goshinta.
Kallon ta kawai baffa keyi ,cikin zuciyarsa yake kissima iri saɓawa gwogwgo da zaiyi dan yau zai nuna mata matsayin fattu azuciyarsa ,sai dai yana yunƙurowa da nufin maida mata martani,kawai yaji bakinsa yayi nauyi,wani irin shayinta da tsoro ya mamaye zuciyarsa.kai kawai ya girgiza ya wuce ɗakinsa ,wato itama gidan mai garin taje kenan?ba komai akwai Allah.
Fattu kuwa tunda aka turata cikin É—akin nan banda kuka ba abinda takeyi, ita damuwarta ma yanzu bai wuce na rashin ganin macijinta ba,duk wannan abunda ke faruwa baizo ba.anya kuwa lafiya?kodai wani abu ya sameshi ne?
"Ya Allah ka kare wannan bawan naka ,ka bashi kariya daga sharrin mugayen mutane .
Shikuwa maciji adaidai wannan lokacin yana gidansu fattu yaje nemanta bai ganta ba yayi ta zagaye aɗakinta amma bata nan,tun lokacin datayi masa karatun nan daya fita yaje can jeji ya kwanta ,sam bayajin daɗin jikinsa sosai yake jin ciwo ta ko'ina ajikinsa,sai da lokaci yaja sannan ya nufi gidansu fattu ,ahankali yake tafiya cikin ciyawa da jikin katanga, harya ƙarasa gidansu fattu.
Koda yaje yaga bata nan saiya yi ta zagaye É—akin yana nemanta ,amma bata nan. Kwanciya yayi akan É—aurin kayanta yayi lamo kamar ya mutu.saidai hawayene ke zuba cikin idanunsa .
Can kuwa gidan mai gari ,da misalin ƙarfe bakwai na dare sosai hadari ya haɗu agarin, dan haka kowa ya shige cikin gida dan gudun zubowar ruwan,da akowane lokaci yana iya sauƙa.
Daidai wannan lokacin kuma fattu na duƙunƙune cikin ɗakin hukunci sai kuka take zuciyarta tayi mata ƙunci ga yunwa dake addabar ta rabo ta da abinci tun madarar da baffa ya bata da safe.hannunta sai zagi yake mata.
Ahankali taji ana turo kofar É—akin hukuncin,da alama shigowa za'ayi,ga duhu aÉ—akin.
Zabura tayi cikin sauri ta miƙe tsaye jikinta na karkarwa,kar dai ace su jaurone suka dawo ?wayyo Allah na " ta faɗa tana dafe ƙirjinta ,zuciyarta kamar zata fito dan tsoro da firgici.
Cikin rawar murya tace "wa...w....ayee."
Ahankali cikin murya mai kama da raÉ—a,yace "ke kwantar da hankalinki,nine nan lamiÉ—o"
Ya faÉ—a yana mai haska tocilan É—insa .
Cikin zubar da hawaye tace "dan Allah lamiÉ—o ka fitar dani daga gurin nan ,wllh ban aikata komai ba,bani na kashe jauro ba"ta faÉ—a cikin kuka.
"Kinga ki nutsu jauro bai mutu ba yana raye ,kuma idan kika bani haÉ—in kai muka yi komai cikin sirri ,to zan kyale ki ki tafi gida abinki"lamiÉ—o ya faÉ—a yana matsowa gareta.
Ja tayi da baya cikin sauri tace "me kake so nayi maka ?dan Allah ka gyaleni na tafi gida ,an fara ruwa"ta faÉ—a cikin kuka,dan ta gano manufarsa ,irin tasu jauro ce ,wato fyaÉ—e yake son yi mata.
Matsowa lamiɗo yayi tare da ruƙo hannunta yana mai cewa"Ayya fattu yarinya mai kyau da kyan jiki ki yarda dani mana duka -duka minti nawa ne ba dayawa zanyi ba kinji ki taimaka min"ya faɗa yana mai janyota jikinsa sosai .
"Wayyo Allah na baffa kazo ka taimakeni,dan Allah lamiɗo kayi haƙuri wllh ba kyau kaji tsoron Allah ka tausaya min na roƙeka"fattu ta faɗa cikin rawar jiki da matsanancin kuka,tana mai tureshi daga jikinta,banda warin tsufa ba abinda yake yi.
"Ke dan ubanki ki tsaya ko saina miki ta ƙarfine?Shegiyar yarinya haka zamu zuba miki ido muna kallonki kin cika kinyi tunjum dake amma ba mai morarki,ki tsaya dan ubanki"lamiɗo ya faɗa yana mai ɗauke fattu da wani gigitaccen mari Wanda saida ji da ganinta suka tsaya na wucin gadi.kusan minti biyu kafin kwakwalwar ta ta dawo aiki,kuka ta sake fashewa dashi mai tsananin gaske lokacin da lamiɗon ya Kaita ƙasa yana ƙoƙarin dage yar ficiciyar rigar dake jikinta ,wacce jiƙaƙƙiyar ƙasar nan ta gama bushewa .
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un wayyo Allah na baffa wayyo mai taimako kana ina?kazo gareni,ina buƙatar taimako ka ahhhhhhhh "fattu ta kwalla wani irin ƙara mai ƙarfi lokacin da lamiɗo yayi.........
Tofa masu karatu me lamiÉ—o yayiwa fattu ne ?
Muje zuwa kuci gaba da bin alƙalamin anty mammy.
Mrs babi 💘💘
Share and comment fisabilillah
More comment
More typing.
29/08/2022, 10:47 am - Khadijah Salisu Fari: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄
MACIJINE🪱🪱🪱
Na mammy kabeer
(Anty mammy)
Elegant online writers📚📚
Free book
Page 13/14
____________________"Wayyo Allah na Mai taimako kana ina?kazo gareni,ina buƙatar tallafinka,ahhhhhhhhh !!!fattu ta kwalla ƙara mai tsananin ƙarfi lokacin da taji hannun maigari na ƙoƙarin taɓa mata dukiyar fulani tana mai buge hannunsa daga kan ƙirjinta.
Ɗaga hannu maigari yayi cikin fushi ya sake ɗauke fattu da wani gigitaccen mari,dan ya fuskanci tana ƙoƙarin kawo masa cikas akan ƙudurinsa,shikuwa ya rantse yau bazai bar wannan damar ta wuce shi ba.
"Dan ubanki ki tsaya nayi- nayi abinda ke gabana,wllh yau ko ubankine bukar zai zo gurin nan bai isa ya hanani aiwatar da ƙudirina akanki ba"mai gari ya faɗa yana ƙara ƙoƙarin maida hannunsa gurin dake tsole masa idanu,wato breast ɗin fattu.
Saidai kafin hannunsa ya sauƙa ga inda yayi nufin ,yaji wata irin shaƙa da tunda yake arayuwarsa bai taɓa tsintar kansa cikin irin makamancin wannan shaƙar a aduniya ba.
Ta ko ina yaji shi aɗaure dam-dam kamar ƙullin buhun goro.
Cikin azaba da fizgar magana mai gari yace "wayyo Allah hannuna,na shiga uku wayyo zan mutu" ya faÉ—a idanunsa azazzare kamar zasu fito tsabar azaba.
Cikin hanzari fattu wacce idanunta ke rufe, ta riga ta gama fitar da rai ta sadaƙar cewa yau shikenan ta rasa budurcinta ,dan ta san ba mai zuwa ya ceceta ,koda tayi ihu ba mai jin sautin ihunta,sakamakon ruwan saman da ake tsugawa.ba zato ba tsammani tajiyo ihun maigari lokacin da maciji yayi sama dashi ya cilla shi can gefe guda ,bayan tabbatar da cewa mai gari ya suma.ji kake ƙasss-ƙasss,hannu da ƙafar mai gari na bangaren dama sun karye.
Da sauri fattu ta kalli inda akayo jifa da mai gari dan tabbatar da cewar shiɗin ne kokuma yaya.aikuwa cikin wani irin farin ciki da murna ta yunƙura da ƙyar ta zauna tana kuka da dariya,sai kuma ta tafi gareshi cikin rarrafe tana zuwa inda macijin ke tsaye yana huci ya ƙure mai gari da ido,da alama yana son ganin maigari ko zaiyi wani motsin ne yaje ya ƙarasashi,duba da yadda yake ta uban huci ya kafe mai garin da ido.
Fattu na zuwa ta wani kwaƙume macijin zuwa jikinta ,ta ƙanƙameshi tana kuka kamar ran ta zai fita,kukanta na dalilai biyu ne,dalili na farko shine ganin macijinta na nan araye ba mutuwa yayi ba,kuma masu neman shi basu ganshi ba.na biyu kuma yadda yazo ya kawo mata ɗauki adaidai lokacin da ta fidda rai da cewar zata rasa abu mafi muhimmanci arayuwarta.
"Ina ka shiga mai taimakona?na shiga damuwa na rashin ganinka, naji tsoron ko sun kamaka sun kashe ,dan Allah karka ƙara yin nesa dani na tsawon lokaci irin haka,kalli yadda suke son kawar min da budurcina, bansan me na tsare musu ba ,kowa nufinsa ya cutar dani,kai kadai ke sona,sai baffana ,bana son na rasa ɗaya daga cikinku ,kune rayuwata,farin cikina da jin daɗina,mai taimakona ina sonka har cikin zuciyata, ba ruwana da kasancewarka wata halitta ta daban,Dan kafiyemin halitta irin tawa sau dubu"duk cikin kuka fattu ke faɗin Waɗan nan maganganu,yayi da take ƙanƙame da macijinta kamar zata maida shi cikinta.yadda ta ƙanƙameshi, kai kace uwace ake ƙoƙarin rabata da ɗanta.
Ahankali macijin nan ke sauƙe wani irin numfashi kamar yana hurawa fattu iska mai sanyi ,da alama dai rarrashinta yakeyi,dan yadda yake huro iskar yana wani rufe ido da buɗewa shine zai fahimtar da kai cewar rarrashinta yake .
Zare jikinsa yayi daga ƙwaƙwumar da fattu tayi masa ya zagaye west ɗinta ,Amma Sam bai matseta ba ,sannan ya shigo da kanshi ta ƙirjinta yana kallon fuskarta yadda hawaye yayi faca -faca kan kyakkyawar fuskar tata.kallon -kallo ake tsakanin fattu da macijinta ,kallo yake mata irin na tausayawa dan abin mamaki ne sosai idan kaga yadda ya wani marairaice fuska yana ƙifta idanunsa tare da ɗan matso da kansa saitin fuskarta,sai kuma ya kwantar da kan nashi saitin da hawayenta ke tsiyaya, ta ɓangaren dama, sannan yayiwa ɓangaren hagun ma haka.
"Dariya mai haɗe da kuka fattu take yi cike da tsantsar ƙaunar wannan halitta ,hannu ta sanya ta share hawayen daya ƙara zubowa tace "na daina kukan mai taimako tunda baka so ,bazan ƙara ba ka gani ma ko "ta faɗa tana mai ƙara shafe idanunta ,saidai wasu hawayen na ƙara zubowa.
Zare jikinsa yayi yana mai hawa kan wuyanta zuwa kanta saiya leƙo da kansa ta saman kanta ,idan ta ɗago da nufin kallonsa saiya silale ya koma wuyanta ya ɓoye kansa abayanta.
Dariya fattu take cikin farin ciki da ganin cewar wai wasa yake mata dan ta sami nutsuwa ta daina kukan ,dan haka lokacin daya ɓoye abayanta sai tace "wayyo ni fattu mai taimakona ya ɓata, ya zanyi da rayuwata ,ina kake abinsona shikenan masu son cutar dani zasu sami dama akaina wayyo ga mai gari nan ya taso"ta faɗa cikin yanayi kamar tana son yin kuka .aikuwa cikin sauri macijin nan ya haye kan cinyarta yana mai fasa kai da wani kalle -kalle ya miƙa kansa can ya dawo dashi can yana huci.
Dariya fattu tayi tace "nima ramawa nayi tunda ka boyemin " ta faɗa cikin shagwaɓa kamar wacce ke gaban baffanta ko innarta.
Juyowa macijin yayi yana kallonta sai kuma ya ɗora kansa daidai saitin zuciyarta yayi lamo ,tare da rufe idanunsa.ahankali ta sanya hannu tana shafa kyakyakywan jikinsa mai matuƙar santsi da laushi.kusan minti biyar suna haka,yayinda ake tafaman zuga ruwan sama ,can gefe kuma mai garine shame shame akwance baya motsi.kallon mai gari fattu tayi ,sai taji tsoro ya cika zuciyarta,kodai shima mutuwa yayi, dan ita tama manta da batunsa aɗakin sam,idan kuma ya farka ya ƙara dawo mata fa ,gara fa su gudu daga ɗakin nan tun kafin jama'a su ankare dasu.
Cikin muryar tsoro tace "mai taimako ya kamata mu gudu gida karya farka ko wani yazo ya gammu dashi ahaka"ta faɗa tana kallon macijin dake kwance akan ƙirjinta,da alama kuma yana jin daɗin kasancewarsa ahakan.
Ahankali ya ɗago kansa tare da silalewa ƙasa yayi hanyar ƙofar fita daga bukkar,wacce mai gari ya barta abuɗe tsabar jaraba na cinsa.
Binsa fattu tayi da sauri ,harta fita saikuma ta dawo ta ɗauke tocilan nan ta mai gari ,dan taga garin yayi baƙi ƙirin kuma har lokacin ruwa ake.
Suna fita fattu ta kama sauri -sauri gudu-gudu ,tana tafe tana haska tocilan É—in nan ,yayinda mai taimako ke biye da ita cikin salon nashi gudun ,saidai suna tafe yana zagayeta ,dan bata kariya ta kowacce kusurwa.
Suna zuwa gida kai tsaye fattu É—akin baffa ta nufa,tana zuwa ta shiga É—akin ahankali tana haska tocilan É—in hannunta.Allah sarki baffa yana kan sallaya ya É—aya hannunsa sama yana ta addu'a,juyowa yayi dan ganin hasken da ake haskowa.
"Waye anan"ya faÉ—a yana kunna tashi tocilan É—in.
Ai da sauri ya miƙe tsaye yayi kan fattu,yana mai cewa"fattu kece alhmdllh fattu na ba abinda ya sameki,?ina mai garin?waye ya fito dake?baffa ya jero mata waɗannan tambayoyin alokaci guda yana mai shafa kanta cikin farin ciki .
Ahankali fattu ta kalli gefenta ta ƙasa inda macijin nan ke nannaɗe ya fasa kansa yana kallon baffa.tace "baffa wannan ne ya taimakeni, kuma shine macijin daya hukunta su jauro "ta faɗa tana haska macijin da tocilan.
Da sauri baffa yaja baya yana faÉ—in"subhanalla fattu wannan ai MACIJINE ,meye haÉ—inki dashi,matsa daga gareshi maza karya cutar dake" baffa ya faÉ—a cikin tsoro yana mai kamo hannun Fattu.
"Baffa ka kwantar da hankalinka ,ba abinda zai min ,domin mun jima tare dashi,zauna baffa in baka labarin haÉ—uwata dashi ,sannan baffa macijin nan yana cikin matsala ,dan da alama anyi amfani dashi wajen yiwa wani asiri.
Zama baffa yayi ahankali kan sallarsa ,idonsa akan macijin nan ,daya matso kusa da fattu wacce ke zaune kusa da baffanta,kallon ikon Allah baffa keyi, yadda macijin nan yayi kane-kane akan cinyar fattunsa ya waniyi lub kamar jariri akan cinyar mahaifiyarsa.
Kallon fattu baffa yayi ,yaga ko ajikinta saima hannu data É—ora akan bayan macijin tana shafawa.
"Ina jinki fattu faÉ—a min komai dan hankalinta ya kwanta"
Nan fattu ta fara bashi labari tun daga farko har kawo yanzu.
Sannan ta É—ora da cewa "baffa dan Allah mu taimaki wannan macijin dan wllh yana cikin matsala ,bakaga yadda ya koma ba lokacin dana ke masa karatu,mu cire masa wannan masifar dake jikinsa"ta faÉ—a tana nunawa baffa waÉ—annan layun dake wuyan macijin.
Cike da mamaki da al'ajabi baffa ke kallon macijin ,wanda ya ƙara kafewa jikin fattu yana kallon baffa da kuma fattu.baffa yace "haƙika akwai wani ɓoyayyen al'amari dangane da wannan macijin ,kuma in sha Allah zamu taimaka masa iyakar ƙarfin mu,tun kafin mai gari ya farfaɗo ya ɗauki matakin kashe macijin nan ,yanzu kije kiyi alwala ki dawo,dan mu fara aiki akansa.
Cike da É—oki fattu ta amsa da" to baffa na ina godiya agareta sosai"sannan ta ajiye macijin gefen baffa tace "mai taimako ai kasan baffana ko?to katsaya agurinsa yan zu zan dawo kaji"ta faÉ—a cikin murmushi tana shafa bayansa.
Kallo ta kawai yayi kafin ya kwantar da kansa ajikin gangar jikinsa dake nannaÉ—e.
Bayan fattu tayi alwala ta dawo dakin ne ta gabatar da sallolin dake kanta ,sannan tayi addu'ar samun nasara akan ceton macijin nan ta shafa.sanna ta juyo gurin baffa wanda ke ta tofa addu'a cikin wata ƙwarya ,zama ta gyara tana mai kallon baffa da jiran ya kammala addu'ar sa.
Shikuwa macijin nan yana ganin fattu ta zauna ya silalo ya dawo kan cinyarta ya kwanta,gaba É—aya jikinsa asanyaye yake,kamar wanda yake tsoron faruwar wani abu.kallonsa fattu tayi tace "mai taimako ba abinda zai sameka ka kwantar da hankalinka ,in Sha Allahu zamu cire maka duk wani sihiri da akayi amfani dakai wajen yinsa"ta faÉ—a tana mai shafa lallausan san jikinsa mai santsi.
Miƙa mata kwaryar nan baffa yayi yace karɓi wannan fattu ki yayyafar masa ajikinsa ,kinayi kina karanta ayatul kursiyyu da falaƙi da nasi, duk abinda zaki gani karki tsorata kinji ?"baffa ya faɗa yana mika mata kwaryar,dan shikam ya gama fahimtar abubuwa da dama aka. Macijin nan.
Karɓa fattu tayi cikin nutsuwa ta fara karatun tana kuma shafa masa ruwan rubutun nan ajikinsa.
Ikon Allah,ai da fara shafa masa ruwan nan ajikinsa ya fara wani irin motsi da jijjiga ,yana murÉ—ewa ,baffa kuma saiya ci gaba da addu'a yana tofa masa.
Ahankali hannun Fattu ya kai kan waɗaɗan na layin dake wuyan macijin nan,aikuwa damƙarsu tayi da Bismillah ta fizge da ƙarfin gaske.
Wata irin ƙara da guguwa ne suka turnike dakin gaba ɗaya baka iya ganin komai sai duhu.....
Masu karatu mutara gaba dan jin ya zata kaya.
Takuce dai Mrs babi💘💘
29/08/2022, 10:48 am - Khadijah Salisu Fari: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄
MACIJI NE🪱🪱🪱
Na mammy kabeer
(Anty mammy)
Elegant online writers📚📚
Free book
Page 15/16
Albishirinku masoya,ga dama ta samu ga mai buƙatar a tallata mata hajarta,to ashirye nake dan tallata mata cikin farashi mai sauƙi,dan haka idan kin shirya sai kiyimin magana .
________________Wata irin ƙara da guguwa ne masu matuƙar ƙarfi da firgitarwa , suka cika dakin.ta yadda koda tafin hannunka baka iya gani tsabar duhun da ɗakin yayi,ga guguwa sai juyawa take aɗakin.
Ko kaɗan hakan bai tsorata baffa ba ,saima cigaba da yayi da karanto ayoyin shifa daga cikin alƙur'ani mai girma yana tofawa asaitin dayasan macijin nan yana gurin ,duk da duhun daya mamaye ɗakin.
Fattu kuwa wani irin tsorone da fargabar suka baibayeta , jin yadda macijin nan yake wata irin murɗewa da sakin wani sautin ƙara mai ban tsoro ,sannna kuma sai takejin yana ƙara mata nauyi sosai akan cinyarta.
Cikin tsoro da ruÉ—ewa ta lalubo hannun baffa tace " wayyo baffa tsoro nakeji,wllh kamar yana rikiÉ—ewa ne zuwa wata halittar ,yayimin nauyi akan cinyata baffa, baffa ina tsoron kar wani abu ya faru"Fattu ta faÉ—a cikin rawar murya mai cike da tsoro.
Hannunta baffa ya riƙe shima cikin yanayi na son kwantar mata da hankali yace"karki damu Fattu ba abinda zai faru sai alkairi,kici gaba da karanto addu'oi kina tofa masa in Sha Allah komai yazo ƙarshe "baffa ya faɗi hakan tare da ci gaba da karanto zafafan addu'oi yana tofawa macijin.
Fattu ma É—aurewa tayi taci gaba da karanto addu'ar tana tofamasa, jikinta sai rawa yake,yadda takejin alamun sauyin halittar da macijin nan keyi.idanunta arufe gam-gam.
Kusan shuÉ—ewar mintina biyar zuwa bakwai, duhun nan ya fara yayewa ,ahankali hasken tocilolin su baffa ya fara gauraye dakin.
Salati baffa ya farayi da ƙarfi da kiran sunayen Allah yana mai kabbara. "La'ilaha illallah muhammadur rasulullahi sallallahu alaihi wasallam,ya Allahu Ya rahmanu ,ya hayyu ,ya ƙayyum,Allahu akbar, Allahu akbar "abinda baffa keta faman faɗi kenan cike da ta'ajibi da jinjina wa ƙudurar Ubangiji,cikin hanzari ya janyo zanin rufuwarsa ya lulluɓawa maciji ,daga cikinsa zuwa ƙasansa dan ba kaya ajikinsa.
Jin yadda baffa ke tafaman kabbara da salati ne ,yasa Fattu buɗe idanunta cikin nutsuwa da kuma jarumta ,har zuwa lokacin bata fasa karanto addu'oi ba.akan fuskar baffa ta sauƙe idanunta ,gaba ɗaya baffa ya shiga al'ajabi da mamakin abinda idanunsa suka gane masa.dan har lokacin yana kallon macijin ne ƙuri kamar ya sami talabijin.
Ahankali Fattu take sauƙe idanunta zuwa kan cinyarta,wata irin bugawa zuciyarta tayi ,lokaci ɗaya komai nata ya tsaya cak. Sai wata irin rawa da jikinta ya kama kamar zata karkarye,ta ɗauki kusan minti biyu cikin wannan halin kafin taja wani dogon numfashi tana mai buɗe baki tace"ba.....f..ff..fa ...mumm.......tttuummm....nnnee.....a..Mamman.cc.....iiii.....sai kawai ta sulale ta faɗi ƙasa daga zaunen da take.
Ba komai bane ya sanya Fattu shiga cikin wannan halin ba , face ganin wani zankaɗeɗen haɗaɗden saurayi ,fari ƙal-ƙal da tayi kwance ya kifa cikinsa akan cinyarta,maimakon macijin dake kwance akan cinyar ta ta.
Kuma wannan shine dalilin salati da baffa keta rafkawa cikin kushu'i da tsarkake baiwa da buwayar mahalicci.lallai duniya ta zama abinda tazama ,yanzu mutum ne aka mayar dashi dabba?maciji?kuma ga dukkan alamu wannan ba É—an yankin nan bane ,dan ko kaÉ—an baiyi kama da mutanen mu ba.
Ahankali baffa yayi kokarin janye shi daga kan cinyar fattu ya kwantar dashi rigingine akan tabarmar.
Hannu baffa ya sanya ya gyara masa zanin daya lulluɓa masa dan rufe masa al'aurarsa.sannan ya ture gashin daya lulluɓe fuskar mutumin.
"Masha Allah ,watabarakallahu fi ahsanil kaliƙin"baffa ya faɗa adaidai lokacin da yayi arba da fuskar kyakyakywan matashin mai cike da haiba da kwarjini,ga kyan zati.
Kallonsa baffa yake ƙuri yana jinjina kai cike da mamaki da alhini,lallai duniya abin tsoroce, rayuwa bata da tabbas,Allah ka karemu,ka rabamu da sharrin maƙiya da mahassada. Baffa ya faɗa acikin zuciyarsa yana kallon bawan Allahn.
Ruwa baffa ya ɗebo ya yayyafawa fattu ,ahankali ta fara motsi tana buɗe idanunta ,tar ta buɗe idanun ta sauƙesu akan baffa, kusan minti biyu tana kallon baffa.
"Sannu Fattu kinji?tashi ki zauna kiga ikon Allah ,tashi kiga taimakon da kikayiwa rayuwar wannan bawan Allahn.
Baffa ya faÉ—a yana nuna mata inda macijinta yake kwance.
Zabura tayi ta tashi zaune cikin tsoro tana kallon inda baffa ya nuna mata,da sauri ta matso kusa da baffa ta riƙe shi gamm! Jikinta sai rawa yake tace "na shiga uku baffa wllh aljani ne wannan ba mutum bane, daga maciji ya koma siffar mutum ,baffa wllh bamu san me zai koma ba nan gaba ,baffa atsorace nake"ta faɗa idanunta yana zubar da hawaye.
Ahankali baffa ya kamo hannunta yace "habaFattun baffa ,kin manta ne?macijin nan ne fa ,wanda yake taimakonki cikin hukuncin ubangiji, shine kuma kikejin tsoro yanzu?kin manta da halaccin sa gareki?meyasa bazaki tsaya tare dashiba?alokacin da yake buƙatar taimakonki kema?ki kwantar da hankalinki Fattu ina ji ajikina wannan bawan Allah shine zai zame miki bango kuma tsanin da zai haɗaki da innarki"baffa ya faɗa cikin yanayi na son kwantar mata da hankali.
Murmushi Fattu tayi cikin kwarin guiwa tace "hakane baffa ,kuma zan kula da bawan Allahn nan in Sha Allahu ,harya sami lafiya"ta faÉ—a cikin kwarin guiwa,saidai har zuwa lokacin tsorone fal cikin ranta.ahankali ta matsa kusa da macijin saidai can nesa kaÉ—an dashi ta zauna .
Kallonsa take cike da mamakin tsantsar kyan da Allah yayiwa wannan bawan nashi, ita kam tunda take arayuwarta, bata taɓa ganin wani mutum mai kyan wannan bawan Allah ba.
Dan duk kyanta da ake faɗa ,tayi imani bata kama koda ƙafar wannan bawan Allahn ba.
Ahankali ya fara motsi yana ɗan juya kansa hagu da dama.sai kuma ya fara ɗan fizge fizge kamar yana ƙoƙarin tuna wani abunne ko kuma yana son farkawa daga wani mummunan mafarkin .
"Baffa kaga abinda yake "Fattu ta faÉ—a cikin zabura tana kallon baffan.
Wata yar jarka baffa ya ɗauko ya buɗe ,ahankali yafara shafa masa ruwan dake cikin jarkar. ahankali maciji ya sauƙe wata ajiyar zuciya mai ƙarfi yana sauƙe numfashi ahankali ahankali.
Addu'oi baffa yake tayi cikin wasu magunguna kala-kala yana shafawa bawan Allah nan da yake kwance ,wanda zuwa yanzu jikinsa yayi sanyi,ba kamar dazu da yayi zafi ƙau-ƙau ba.
Tun daga ƙafafuwansa Fattu ke kallonsa har zuwa fuskarsa,masha Allah.
Wannan mutumin ya haɗu ta ko ina ,anya ma wannan ba haushene?ko bafulatanine irin mu?kai gaskiya wannan bayajin Hausa ko fulatanci,ohhh Ni Fattu yanzu wanann macijina ne haka ?dama da mutum nake ma'amula ashe?waye wannan bawan Allahn?su waye sukayi masa wannan shirin haka?me yayi musu ?inane garinsu?meye sunansa?waɗan nan sune tambayoyin da Fattu ke buƙatar amsarsu ,saidai ba mai bata amsar sai wannan bawan Allah.
Baffa ma tunani yake wannan bawan Allah daga ina yake? ,waye yayi masa wannan sihiri?koma dai menene yayi masa maganin da duk sihirin mutum bazai yi tasiri akanshi ba da yardar Allah.
Suna nan zaune jigum jigum, cike da fatan Allah yasa ya farka ba tare da wata matsalar ba,kawai suka ga ya fara motsi karo na biyu,saidai wannan karon ba fizge -fizgen yake ba ,kawai dai ya ɗan riƙe kansa yana kuma yatsina fuska.
Ido suka ƙura masa ba wanda yayi magana ,daga Fattu har baffa,kowa yayi shiru yana kallon ikon Allah.
Ahankali bawan Allahn nan ya fara bude idanunsa yana ɗan lumshesu ,kafin ya buɗe su tar kamar lantarki dan tsananin haske da sheƙin da suke yi.
Ƙur ya ƙure rufi bukkar dakin baffa da idanu,baya ko ƙiftasu,tunani yake ina ne nan?waye ya kawo shi nan?kuma yaushema suka zo nan ɗin?
Yunƙurawa yayi ya tashi zaune ahankali yana cije light pink lips ɗinsa .kallon ɗakin yake cike da mamaki ,har ya juyo zuwa inda su baffa ke zaune shida Fattu sunyi masa ƙuri suna kallonsa,baffa ya fara kalla cike da rashin sani.
"Sannu bawan Allah ka tashi ?meke maka ciwo yanzu ?me kake ji ajikinka" baffa ya faÉ—a lokacin da suka haÉ—a ido da bawan Allahn .
Ahankali bawan Allahn ya lumshe idanunsa tare da jingina da jikin bangon É—akin.yana mai dafe kansa ,dan ciwo yake masa sosai.
"Ayya Fattu inaga fa wannan bayajin hausa ,kuma bayajin filatanci miƙamin wannan kwaryar In bashi magani ,da alama kanshi ke ciwo.
Cewar baffa kenan, dayaji yayi magana amma bawan Allahn bai bashi amsaba.
Ahankali Fattu ta miƙe ta ɗauki kwaryar ta miƙawa baffa ita ,tana mai cewa "baffa gashi,kuma kamar ma yana jin yunwa ko ?kaga yana shafa cikinsa"ta faɗa tana kallon yadda bawan Allah ke shafa cikinsa zuwa ƙirjinsa wanda gashi yayi kwance luf-luf akai.
Ahankali bawan Allah ya É—ago kansa yana kallon saitin dayaji sassanyar muryar Fattu na tashi.
Aikuwa karaf idanunsa suka gauraye cikin na juna ,wata irin faɗuwar gabace ta ziyarcesu alokaci guda, da sauri bawan Allahn ya kawar da kansa yana mai dafe ƙirjinsa,dan sosai ƙirjinsa ya buga.
Bangaren Fattu ma kuwa,wata irin bugawa ƙirjinta yayi, wacce har saida taji numfashinta ya ɗauke ,wani jiri ne ya ɗebeta ,tayi baya luuuuuuu zata faɗi,ƙara ta kwalla cike da jin tsoro tana mai runtse idanunta, saidai kuma kafin ta kai ƙasan taji ta faɗa kan wani lallausan abu mai kama da katifa tsabar laushi.
Ahankali ta buɗe idonta ta sauƙesu akan.........
Muje zuwa masu karatu yanzu muka fara.
Taku ce dai anty mammy
Mrs babi💘💘
Share and comment fisabilillah
More comment
More typing.
29/08/2022, 10:49 am - Khadijah Salisu Fari: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄
MACIJI NE🪱🪱🪱
Na mammy kabeer
(Anty mammy)
Elegant online writers📚📚
Free book
Page 17/18
______________Ƙara fattu ta kwalla cike da tsoro,dan ta saddaƙar kawai ta gama faɗuwa,saidai kuma maimakon tajita akan ƙasa ,saitaji ta faɗa kan wani abu mai matuƙar taushi kamar katifa.
Da sauri ta buÉ—e idanunta dan ganin inda ta faÉ—a,cikin mamaki take kallon bawan Allah nan,dan hannunsa ta faÉ—o, lokacin da yaga tayi baya zata faÉ—i ,bai ma san lokacin daya zabura yayi kanta ba ,tare da tareta ta faÉ—o akan hannunsa .
Kallon kallon sukewa juna basa ko ƙiftawa, yayin da bawan Allah ya zazzaro idanu waje ,irin wanda idan mutum yaga abin tsoro ɗin nan.
Ita kuma fattu mamaki take yaushe ya taso yazo gareta harya tare ta ?bata kai ga faɗuwa ƙasa ba?
Baffa ne yayi gyaran murya tare da faɗin "subhanallah,fattu sannu, Allah ya taƙaita wahala da tuni kin faɗin ƙasa ,bawan Allah sannu kaji,kana fama da kanka amma zuciyarka mai tsafta bazata bari wani ya cituba,ina mai godiya gareka"baffa ya faɗa cike da jinjinawa bawan Allah nan,lallai akwai wani abu da Allah ya ɓoye tsakaninsa da fattunsa, haƙiƙa fattu kam,zuwa yanzu ta sami mai taimako,kuma yanzu ne ya kamata su fara neman dangin Fattu ,dan zuciyarsa na raya masa wannan bawan Allah alkairine ga rayuwar fattunsa.
Ahankali bawan Allah ya miƙar da fattu tsaye ,yana kallon ta sai dai fuskarsa sam ba walwala ,da alama dai irin mutanen nan ne marasa yawan fara'a .
Fattu kuwa da sauri ta juya baya tana mai dafe ƙirji ,dan hango zanin da baffanta ya lulluɓawa mutumin a ƙasa,kuma da alama bai ma san zanin ya daɗi ƙasanba.
Da sauri shima ya ankare cewar ba zanin fa ajikinsa ,wato yana tsaye tsirara ne.cikin azama ya durƙusa ya ɗauki zanin yana cukuikuyewa ajikinsa, idonsa akan fattu yana fatan Allah dai yasa wannan yarinyar bata ganshi haka ba,dan ma dakin ba wani haske sosai.dan tocilolin sun kalli wani direction ɗin ne da ban.
Zama yayi cike da jin haushin yadda zanin jikin nashi ya daÉ—i kasa,wai ma to ina kayansa ne?me yasa y ganshi haka ba kaya ne?
Daga kanshi yayi yana kallon baffa daya miƙa masa kwaryar da fattu ta miƙa dan abashi magani.
Karɓa yayi shikam nadan yasan menene aciki ba , kallo yabo kwaryar dashi,yana jin wani irin tashin zuciya ,dan kwaryar ta tsufa sosai ,tayi baƙi saboda ruwam rubutun da ake zubawa a cikinta.
"Maza ka shanye bawan Allah zakaji sauƙin ciwon kan"baffa ya faɗa yana nuna masa alamun ya sha da hannunsa ,dan gani yake kamar bayajin me suke faɗi.
Kafa kansa yayi yana shan maganin ,bayan ya runtse idanunsa.saida ya ɗansha da yawa kafin ya miƙawa baffa kwaryar.
Saidai ko minti ɗaya baiyi da sha ba ,ya kama yunƙirin amai.aikuwa tasss ya mayar da maganin nan,sannu kawai baffa ke masa.
Juyowa fattu tayi lokacin daya fara aman, dan tunda ta juya musu baya bata ƙara juyowa ba,saida taji yana aman.
Ahankali ta buÉ—e bakinta tace "sannu hamma"ta faÉ—a ahankali.
Kallonta yayi ,tare da kawar da kansa can gefe yana jingina da jikin katangar karan,ba tare da yayi magana ba .itama bata damu da sai yayi maganar ba,dan su tunaninsu bayajin me suke faÉ—i.
Cikin nutsuwa fattu ta gyara gurin da yayi aman,kanta aduke ,har zuwa lokacin gabanta yaɗuwa yake .shi kuwa bawan Allahn nan yana daga jikin bango Ya lumshe idanunsa ,kamar mai barci.saidai duk abinda fattu keyi idonsa na kanta,mamaki yake da irin kyan da yarinyar ke dashi,gata da nutsuwa komai nata gwanin burgewa.tana da hankali bata da rawar kai duk da ƙaranci irin na shekarunta.dan ya san wannan bata wuce 14/15ba amma Masha Allah,tana kyan diri irin na cikakkun mata ,kalli hips ɗinta kamar wanda aka ɗora mata shi Dass abinta. Jikin fattu ne kawai ya bata cewar kallo ta mutumin nan keyi,dan haka ahankali ta ɗago kanta ,shikuwa daidai lokacin ya ɗan ƙara buɗe idanunsa yana kallon ɗan ma dai-dai cin lips ɗin ta, masu taushi , sai sheƙi suke.aikuwa carab ta kama shi yana mata kallon ƙurillah.
ÆŠan hararar ta yayi tare da kawar da kansa ,aransa yace "wannan ta cika kallon mutane "
Kuji fa masu karatu ?ko tsakanin shi da fattun wake kallon wani?
Da sauri fattu ma ta kawar da kanta,azuciyarta tana mai cewa "kuji min mutum shi yana kallon mutane amma kuma baya son akalleshi"
"Abba waye yakawoni nan?kuma me nakeyi anan?sannan kuma ina kayan?
Baffa da fattu suka ci
tsinkayi murya mai shegen daÉ—i da amon sauti cikin nutsuwa.da mamaki gaba É—aya suka bishi da kallon ,ba wanda yayi magana dan sai sukaga kamar bashi yayi maganar ba ,dan yana yadda yake bai ko buÉ—e idonsa ba lokacin da yayi maganar.
Jin sunyi shuri ba wanda yayi magana ne ,yasa bawan Allah buɗe idanunsa da suka ɗan yi ja kaɗan yana kallon baffa,sannan ya ƙara maimaita tambayarsa cikin Hausarsa da bata fita sosai.
"Ashsha -ashsha ikon Allah yaro ashe kana jin Yaren Hausa ?Alhmdllh.sannu kaji bari na baka kaya saika saka,inyaso zuwa wayewar gari nayi magana kaji"baffa ya faɗa yana mai buɗe wata tsohuwar bakonsa ,kaya ya daukowa bawan Allah nan ,waɗanda dasu yake zuwa sallar juma 'a .wani yaɗi ne yollow share dashi ,anyi masa ɗinkin riga da wando dogaye .miƙa masa baffa yayi yace "kasa Waɗan nan tukunna yanzu kaji"
Karɓar kayan yayi yana mai ƙare musu kallo,to ina nashi kayan da za'a bashi Waɗan nan kayan wani iri dasu haka?ɗari kansa yayi ya kalli baffa yana son yayi magana ,amma sam ya kasa,dan ba ɗabi'arsa bace yawan magana ,yana matuƙar jin wahalar yin magana ,shiyasama tun farko yaƙiyi musu magana .
Kallon fattu yayi wacce ke zaune can nesa dasu kanta aduƙe,tana wasa da yatsun hannunta ,sannan ya kalli baffa ,ya kalli kayan hannunsa kuma .
Fahimta baffa yayi cewar ,yana son saka kayan ne ,kuma yana buƙatar fattu ta bar gurin,dan haka baffa yace "fattu muɗan bashi guri ya kimtsa ko"baffa ya faɗa yana mai kama hannun fattun sukayi wajen ɗakin.
Bayan fitarsu daga ɗakin,shikuwa kallon yabo kayan dashi yana juyasu ahannunsa, kusan minti uku kafin ya saka rigar ,dube dube yake ko zaiga boxern sa ,saidai ba alamun boxer aɗakin nan,dan haka ya saka wando yana mai turo baki da ɗan yamutse fuska.sauƙinsa ma ɗaya kayan wanke suke tas ɗasu,sai ƙamshin kilin suke.lol.
Koda ya saka kayan zamansa yayi a inda ya tashi tare da lumshe idanunsa ya faɗa duniyar tunani ,shikam a iya tunaninsa baisan meye dangantakar da da Waɗan nan mutanen ba,abinda zuciyarsa tafi yarda dashi shine,wata ƙila yayi hadarine suka ganshi suka taimakeshi.
Baffa ne yaji shiru baice musu ya kammala saka kayan ba,kuma ga fattu sai rawar É—ari take, dan zuwa wannan lokacin an jima da É—auke ruwan saman da ake tsugawa,dare ya raba sosai.
Dan haka saiya ɗan leƙa cikin ɗakin.aikuwa azaune ya hangoshi ya jingina kansa da jikin katanga ,sannan idanunsa alumshe .
"Ayya ashe ma ya ida shiryawa fattu, shigo daga ciki kar mura ta mamaki naga kinata rawar sanyi,bana so kije ɗakinki ki kwanta saboda hansai idan ta ganki zata je ta sanar da lamiɗo kina nan"baffa ya faɗa yana mai tura ƙofar dakin nashi ya rufeta.
"Sannu bawan Allah"baffa ya faÉ—a cike da tausaya wa.
Jinjina kai kawai bawan Allah yayi ,ba tare da ya buÉ—e idonsa ba.
Zama baffa ya gyara ya ƙara cewa"ko zaka iya tuna wani abu daya danganci rayuwarka"?ya faɗa cike da fatan cewar bawan Allah nan bai manta komai na rayuwarsa ba.
"Ikon Allah ,saikace wanda yayi lossing memery zan manta da rayuwata "bawan Allahn ya faÉ—a cikin ransa,amma a zahiri ,É—an buÉ—e idonsa yayi ya kalli baffa,sannan ya maida idonsa kan fuskar fattu wacce itama shi take kallon kamar ta sami talabijin.
"Kai wannan yarinyar ta cika kallo wllhda wani idanunta masu kama da ruwan Gwale"ya faÉ—a cikin zuciyarsa yana mai hararar fattun ,kafin ya É—auke idanunsa daga kanta ya maida kan baffa .
Saida ya kai kusan minti biyu kafin ya buÉ—e baki ahankali kamar baya so yace "my name is ADEEB
MUHAMMAD ASHRAF "ya faÉ—a yana jinjina kansa tare da kallon baffa.gani yayi baffa yana kallonsa alamun kamar bai fahimceshiba.
Lumshe idonsa yayi cike da gajiya ,sannan yace "sunana ADEEB MUHAMMAD ASHRAF"yana faÉ—in haka ya mayar da kansa ya jingina tare da lumshe idanunsa.
"To- to masha Allah malam Adeeb ina ne garinku ? Baffa ya faÉ—a cikin gamsuwa da jin cewar shiÉ—in musulmine. Dan da yana ta kokwanto shin musulmi ne shi ko arne? Amma zuwa yanzu ya sami nutsuwar jin cewa shiÉ—in musulmine.
Shiru yayi kamar bazai yi magana ba, kafin ya buÉ—e baki yacewa baffa"nidan MISRA ne" ya faÉ—a yana kallon yadda baffa yayi zugum cike da tunanin ina yakejin Misra?
"Ikon Allah malam adeeb duk da dai Ni ba sanin Misra a ina take nayi ba,amma nasan garine mai matuƙar nisa ,to zahiri gaskiya nan kana Nigeria ne ,cikin ƙauyen ƴar ruga dake jahar Gombe"baffa ya faɗa yana kallon Adeeb wanda mamaki ya mamaye ilahirin fuskarsa , Nigeria kuma ?yaushe yazo Nigeria?bayan rabo da da Nigeria tun last year?
"Who brought me hare"?ya faÉ—a cikin mamaki da sanyin murya.sai kuma ya É—an rufe idonsa tare da dage kansa kafin yace "waye ya kawoni nan?
Shiru baffa yayi ba tare da yace komai ba,na tsawon lokaci ,kafin ahankali ya nuna masa fattu yana mai cewa"haƙika wannan yarinyar itace solar haɗuwar mu dakai ,kuma anan garin ta ganka -----nan dai baffa ya bashi labarin abinda ya sani ,da kuma abinda ya faru yanzu harya koma asalin halittar da.
Tunda baffa ke magana Adeeb ya saki baki yana kallo da sauraron baffa,mamaki yake wai shine ya zama maciji?as how ? Me ya faru dashi ?waye ya maida shi hakan?ya Allah who's known how long yake cikin garin nan,ko yaya ƴan gidansu? Ko wane hali suke ciki yanzu?yasan yanzu haka hankalin amminsa yayi matuƙar tashi fiye dana kowa ,lallai dole ya bar garin nan ko ta halin ƙaƙa.
"Na gode sosai da taimakon rayuwata da kuka ,amma bani da wani masaniya akan abinda ya sameni, ina don barin garin nan gobe-dan akwai gagarumin abinda ke gabansa,saidai i promise you I will get you back,zan dawo gareku"ya faÉ—a cikin wani irin yanayi na ban tausayi,dan gaba É—aya jikinsa asanyaye yake ,sannan damuwa ta cika fuskarsa taf! Da gani maganar ta shiga jikinsa sosai .
Cikin murmushi baffa yace ba komai malam Adeeb Allah yayi mana jagora ,saidai ina neman alfarma agareka"baffa ya faÉ—a cikin damuwa.
"Ba komai Abba ka faÉ—i duk abinda kake don faÉ—i and I promise zanyi maka shi"ya faÉ—a cikin sanyin murya mai cike da tarin damuwa.
"So nake ka tafi da ƙanwarka can garin naku ,domin ka taimaka mata wajen saduwa da asalin iyayenta baffa ya faɗa cikin tsantsar damuwa yana mai kallon fattu,wacce taji maganar baffa kamar sauƙar aradu .......
Masu karatu mu tara next page
Taku ce anty mammy Mrs babi💘💘
Share and comment fisabilillah.
29/08/2022, 10:49 am - Khadijah Salisu Fari: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄
MACIJI NE🪱🪱🪱
Na mammy kabeer
(Anty mammy)
Elegant online writers📚📚
Free book
Page 19/20
https://www.facebook.com/groups/1627491150723081/?ref=share_group_link
Masu amfani da face book sai kuyi join wannan group É—in .
_______________"So nake ka tafi da ƙanwarka can garin naku,dan taimaka mata wajen gano iyayenta na asali"baffa ya faɗa yana kallon fattu ,wacce tunda baffa ya fara maganar take jin wani irin matsanancin faɗuwar gaba ,ji tayi maganar tasa ta sauƙa acikin tsakiyar kanta ,kamar sauƙar aradu,"wace irin magana baffa keyi ne haka" anya kuwa yasan me yake faɗi?kai a'a gaskiya bai gane me yake faɗi ba shima.
Fattu ta faɗa cikin zuciyarta,tana mai sauƙe ajiyar zuciya ,dan ta fahimci baffa yana nufin innar ta kenan,saidai kuma bata da wani dalilin bin mutumin da bata sanshi ba,Gara tayi zamanta agurin baffanta ,inyaso innar tata inhar ta damu da ita ,zata zo gareta.
Ahankali fattu ta buɗe bakinta tace "baffa ina ganin babu buƙatar saina bishi wani garin ,dan neman innata,zan zauna anan ɗin idan da rabon zamu gana wata rana zata zo gareni baffa"fattu ta ƙare maganarta cike da mugun bugawar zuciya ,dan har lokacin kalaman baffa na mata yawo akanta.
Ajiyar zuciya baffa ya sauƙe cike da alhini abinda zai faɗa wa fattun ,kafin yace"ayya fattu amm ki saurareni, da kyau ,ki nutsu ,kuma ki sani kowane bawa da yadda ƙaddararsa ke zuwa masa.
Haƙiƙa Ni malam bukar bani ne na haife ki ba na tsincekine tun kina yarinya ƙarama "baffa ya faɗi hakan yana mai sunkuyar da kansa cike da tausayin fattu.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un baffa me kake faɗi ne haka?dan Allah baffa kayi haƙiri idan nayi maka wani laifin ne,amma karka ƙara nesanta alaƙarka dani, baffa bazan iya jura ba,bansan kowa ba sai kai ,kai kaɗai ne gata na baffa dan Allah karka rabu dani "fattu ta faɗa cikin matsanancin kuka marar sauti sosai.
Shide Adeeb kallonsu kawai yake cike da mamaki,how can that be possible ace wai ya tafi da wata yarinya har can ƙasar su ,yace a ina ya samota ?kuma ta yaya ma zai fara neman ahalin yarinyar .shifa gaba ɗayama lamarinsu ɗaure masa kai yake ,basu sanshi ba,ba wata alaƙa atsakaninsu dashi,amma yana ƙoƙarin bashi yarinya ya tafi da ita.
Kallon baffa yayi lokacin dayaji yana magana da cewa"nasan zaki shiga ruɗu da damuwa Aduk lokacin da kika sami wannan labarin fattu,saidai bani da yadda zanyi,yazama dole insanar dake gaskiyar abinda ke wakana,kisani fattu ina ƙaunarki fiye da ƴaƴan dana haifa na cikina dan kin fiyemin su sau dubu.amma son da nake miki bazai sa in cutar dake ba ta hanyar ƙin faɗa miki gaskiya fattu , kisani ahalin yanzu zamanki arugar nan akwai haɗari ,idan mai gari ya farka,kinsan hukuncin da zai zartar akanki bazai mana daɗi ba .dan haka kiyi haƙuri wllh badan cutarwa yasa nace tafi dake ba,saidan ko da baya nan to nayi niyar barin garin nan dake Dan tseratar da rayuwarki"
Baffa ya faÉ—a hawaye na zubowa daga idanunsa.
Kuka fattu kawai take cike da wani irin baƙin ciki marar misaltuwa, wannan wace irin ƙaddara ce ?yanzu shikenan bata ga tsuntsu bata ga tsarki,baffan da take gani matsayin mahaifinta ashe shima ba mahaifinta bane?kenan ita bata da kowa?tunda ta taso take cikin bakin ciki da damuwa ,amma ta kwance zamanta cikin wannan bakin cikin akan zuwan wannan ranar.kuka take irin wanda yake fitowa kai tsaye daga zuciya ba abinda take fata ahalin yanzu kamar ace ta farka taga ashe barci take ,tayi wannan mummunan mafarkin.to suwaye iyayenta?me tayi musu suka yarda ita?shin basa son tane ko yaya?tambayar da take tayiwa zuciyarta kenan,jikinta kuwa nan da nan ya ɗau ɓari,kan kace me tuni zazzaɓi mai zafi ya kamata.
Ahankali Adeeb ya kalli baffa na tsawon lokaci kafin ya buÉ—e baki cikin salonsa na rashin son magana yace "amma Abba ta yaya zaka bani Æ´arka i tafi da ita ?bayan baka Sanni ba,bakasan koni É—in waye ba ,infact baka saniba ma koniÉ—in mugune ,Amma kake don bani Æ´arka in tafi da ita why?Adeeb ya faÉ—a yana kallon baffa.
Dan murmushi baffa yayi,irin wanda yafi kuka ciwon nan,kafin yace "na yarda da kai nasan bazaka taɓa cutar min da fattu ba ,dan tun kana wata halittar wacce ta kasance muguwa kake taimakonta, bare yanzu da kake cikakken mutum.sannan na jima ina addu'a akan Allah ya kawo wanda zai zama silar farin cikin fattu ,sai haka Allah ya kawo ka,alokacin da mu bamuyi tsammani ba,kuma kallo ɗaya nayi maka zuciyata ta aminta da kai ,nasan Allah ne ya karɓi addu'a ta.dan haka bani da wani kokwanto akanka." Baffa ta faɗa cikin nuna yanayi na gamsuwa akan hukuncin daya yanke.
Ahankali fattu ta rarrafe zuwa kusa da baffa ,hannunsa ta kama ta riƙe gamm!cikin nata ,kafin tace "baffa su waye iyayen nawa?me yasa suka yarda Ni?a ina ka tsinceni?ta faɗa cikin kuka tana mai jan majina.
Kallon ta Adeeb yayi cike da tausayawa,dan sosai yaji ta bashi tausayi, she's too young ace ta fuskanci wannan babban ƙalubalen.
Baffa ne ya fara magana da cewa"kafin na auri hansai na auri wata kanwata,yar gidan tayar babata. Inda muka kasance duka marayune daga i har ita.itace matata ta farko ,minyi aurene irin na haɗin zumunci,tana da haƙuri da kawaici ,muna zaune cikin aminci da mutunta juna,har Allah ya bata ciki.
Munyi murna sosai da samun wannan cikin ,tare da addu'ar Allah ya sauƙeta lafiya.
Wata rana kuwa naƙuda ta kamata,ganin yadda take shan wahala ,saina tafi jeji dan ɗebo mata maganin gargajiya tasha,ina cikin tafiya nayi nisa sosai da rugar nan,kwatsam saina fara jiyo kukan jariri,haka nayi ta bin sautin kukan harna cimma gurin.
Kwance na iskeki kinata kuka gaba ɗaya jikinki yayi ƙura, sannan kin kukkurje dan ga jini jini nan ma ajikin rigar dake jikinki,
Addu'a nayi tare da É—aukoki na dawo gida .
Koda na dawo gida na iske matata tana kuka ga gawar jaririya nan gabanta.wato Æ´ar da ta haifa ta koma.
Munyi baƙin ciki sosai da rashin yarinyarmu,amma haka muka haƙura muka mikawa Allah lamarinmu. Nan na bata labarin samoki da nayi,sai naga tana ta murna da farin ciki,batayi wata- wata ba ta karɓe ki ta fara shayar dake,koda nayi magana saitace"Allah ne ya dawo mana da farin cikinmu.dan haka zamu rikeki matsayin ƴarmu da muka rasa,idan kuma munji anyi cigiyarki saimu bada ke.
Nan da nan nima na yarda da shawarar ta ,dan lokaci ɗaya Allah ya samun ƙaunarki raina. Haka na gayyato mutane akayi suturar ƴarmu,yayinda nake faɗawa Mutane cewar ƴan biyu matata ta haifa ,ɗayar ta koma sai ɗayar.
Lokacin da muka tsinceki akwai wani sarƙa awuyanki,wacce da alama zata yi matukar tsada ,dan haka sai muka cire muka ajiyeta haɗe da rigar dana tsinceki da ita.
Munsha tambaya akan ya akayi baki biyo ko ɗaya daga cikinmuba,dan kin kasance kyakyakywa wacce kaf rugar nan ba wanda ya kama ƙafar kyanki,sannan gashinki ba irin namu bane.haka dai muke samun amsar da zamu rufe bakin mutane da ita.
Shekararki biyu a duniya ,Maryama ta koma ga Allah.munyi kuka daga ni harke na rashinta, kafin daga bisani muka haƙura.
Lokacin ne na auri hansai ,wacce ta kasance ba abinda ta iya banda mugunta da baƙin hali,sam bata ƙaunar ki ,da idan tayi miki wani abun nakan yi magana ,saidai daga baya kuma sainake kasa yin maganar,koda na yunƙuro da nufin yin maganar bana iyawa.
Wannan shine taƙaitaccen tarihinki fattu na.amma na tabbata ko ba daɗe ko ba jima zaki haɗu da asalin iyayenki,jikina yana bani kun kusan haɗuwa. Wanda idan har kikaci gaba da zama cikin rugarnan, hakan bazata faru ba.zan nemeki Aduk inda kuke fattu na "baffa ya faɗa cikin kuka abin tausayi.
Fattu ma kuka take sosai kamar ranta zai fita ,"baffa ina sarƙar take "fattu ta faɗa cikin rawar murya irin ta mai zazzaɓi.
Tashi baffa yayi ya buɗe cikin jakarsa ta kaya ya ɗauko wata leda ya kunce,saiga wata sarƙa mai tsananin sheki da ɗaukar ido,sai wata ƴar riga mai kyau fara ta yara.miƙawa fattu kayan baffa yayi .
Ahankali ta karbi kayan ta rungume ajikinta tana kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.
Kallonsu kawai Adeeb yake ,dan zuwa yanzu ya gama ɗaukarwa kansa alƙawarin taimakawa fattu ta kowace fuska ,har saita ga iyayenta.
Baffa kansa kukan yake ,yana jimamim rabuwa da Fattun sa.
Tashi Adeeb yayi ,cikin tafiyarsa ta izza da cike jarumta ya ƙarasa kusa da fattu ,tsugunmawa yayi akusa da ita ,yana kallon fuskarta dake ta faman kuka ,gaba ɗaya tayi jajur da ita.
Hannunsa ya sanya ya ɗago habarta ya kura mata ido,buɗe idanunta tayi itama ta sauƙe cikin nashi,sun ɗauki kusan mintuna uku suna kallon juna,kafin Adeeb ya sauke wani kwauron numfashi ,sannan ya sanya babban ɗan yatsanshi ya share mata hawayen dake zuba a idonta.girgiza mata kai yayi alamun ta daina kuka.amma sam ta kasa dainawa.
Sarƙar hannunta ya karɓa yana kallo,sarkar zallar daimond ce sai sirin kwal,da gani wannan sarƙar ta doshi millions ,koma ina yarinyar nan ta fito to tabbas ƴar gidan manya ce,in Sha Allah zai haɗata da iyayenta na asali.
Sarƙar ya buɗe tare da nufar wuyanta wanda yake nan zafi ƙau da zazzaɓi,ya ɗaura mata sarƙar.nan da nan sarƙar ta ɗauki wani sheƙi da walwali.
Dawo da kallonsa yayi kan baffa wanda yake kallon duk abinda ke faruwa,zuciyarsa tana masa wani irin ƙuna da ciwo.
Saida ya ɗauki kusan minti biyar kafin yace "Abba nayi maka alƙawarin zan taimaka wajen neman asalin iyayen yarinyarka,zamuiyi amfani da wannan sarƙa in Sha Allah everything is gonna be ok"ya faɗa cikin muryar sa mai daɗin amo .
Hannunsa baffa ya kama cikin farin ciki yace "na gode Allah yayi maka albarka,ka kulamin da fattu karka bari ta cutu "
Jinjina kai yayi shima yana mai riƙe hannun baffan, akaro na farko ya ɗanyi murmushi.masha Allah masu karatu bakuga yadda yayi wani sihirtaccen kyau ba,Dan murmushin ba ƙaramin kyau ya ƙara masaba.
Kwanciya fattu tayi akan sallaya ta juya bayanta tana ta kuka da rawar zazzaɓi,shikenan yanzu haka zata bi wannan bawan Allah da batasan koshi waye ba,meyasa iyayenta suka yarda ita?me tayi musu haka da zafi?dama baffa ya fasa ƙidurinsa na cewar saitabi wannan bawan Allah mana.
Baffa ne ya miƙe tsaye da sauri tare da leƙawa ƙofar ɗakinsa, dan tabbas yaga gilmawar mutum,aikuwa yana leƙawa ya hango zanin gwogwgo hansai tana shigewa ɗakinta. Ya Salam kenan taji duk abinda suke tattaunawa ?lallai dole su bar gidan nan kafin gari ya gama wayewa.dan yanzu kam asuba ta kawo kai,
Da sauri ya koma É—akin yace "Adeeb akwai matsala,yanzu yanzu zaku tashi ku dau hanya,dan kuwa hansai taji duk abinda muke tattauna,kuma na tabbata ko bari bazata yi gari ya gama wayewaba zata je ta sanar da mai gari"
Baffa ya faÉ—a cikin tashin hankali da damuwa.
Shikuwa Adeeb ko ajikinsa ƙara gyara zama yayi ,dan bazai iya kwanciya anan gurin ba ,kafin ya kalli baffa ya ɗan taɓe baki yace "and so what idan ta faɗa masa"?
Ya faÉ—a cikin ko in kula.
"Bazaka gane zalumcin lamiɗo ba Adeeb zai iya sawa kashe fattu ,dan Allah ku tashi muje In fitar daku hanya ku tafi, ka taimaka min ka ceci rayuwar yata"baffa ya faɗa cikin kuka yana durƙusa akan gwuiwoyinsa.
Da sauri Adeeb ya tashi ya kama baffa ya miƙar dashi yace "is ok Abba zamu tafi yanzu.ya faɗa yana mai kamo hannun fattu ya miƙar da ita tsaye.
Ita kuwa fattu yadda yake jin zuciyarta bayani ace mai gari yasa a kasheta Bama,koba komai zata huta da ƙuncin zuciya da damuwa.tana mikewa tayi baya zata faɗi,dan gaba ɗaya ba ƙarfi ajikinta.da sauri Adeeb ya tallafi ga zuwa jikinsa,kallon fuskarta yayi wacce ta kumbura ,sai rufe idanu take tana buɗe wa,da gani tana shan jiki sosai.
"Muje bawan Allah ,fattu daure kinji"baffa ya faÉ—a cikin ruÉ—u ,ba abinda yake É“ukata irin yaga sun bar rugar nan.
Ganin fattu zata É“ata musu lokacine yasa Adeeb ya É—agata sama tsak!kamar Æ´ar tsana ya saba akafaÉ—arsa yacewa baffa" muke Abba"
Wata leda Baffa ya dauko,tare da rigar nan ta fattu ya cusa ciki,sannan yayi waje suka rufa masa baya......
Masu karatu me zakuce game da rabuwar baffa da fattu?
0 comments:
Post a Comment