Ahankali ya buɗe bakinsa yana mai faɗin " nanny ahaɗa mata ruwa tayi wanka saita sake wannan kayan" ya faɗa yana kallon nanny dake kusa da fattu tana faɗin" ke ƴar nan !wannan ƙamshin fa?tunda kuka dosa part ɗin nan nake jin ƙamshin,turaren magajin faɗa,ashe ajikinki yake"cewar nanny Tana mai kallon fattu,kafin ta dawo da kallonta kan Adeeb tana mai cewa" ai dole ma tayi wanka dan wannan turaren yayi yawa ajikinta,kasan shi kuma turare shu'umin abune,yanzu zai saka cikin wani hali,barin ma wannan turare naka mai sanyi ƙamshi, ga yara irin su Rashad birjik afada" nanny ta faɗa tana mai kama hannun fattu suka nufi toilet.
Shiru Adeeb yayi yana kallon ƙofar da suka shiga,lallai dole ma ya hana fattu sanya turare dan maganar nanny gaskiya ce,shi kansa cikin wani irin shauƙi yake jinsa,hakanan tunda ya shaƙi ƙamshin ajikin fattu.
Tashi yayi cikin nutsuwa ya fice daga É—akin.
Dakin ammi ya nufa lokacin tana zaune gaban wani ƙaton akwati mai ruwan gwal ,sai sheƙi yake da ɗaukar ido,ba komai bane cikin akwatin sai sarƙoƙinta na gwal kala -kala.
Wata yar ƙaramar akwatin ce ahannunta tana mai kallon sarkar fattu data adana aciki.
Murmushi tayi tare da faɗin"nayi alƙawarin keda haɗuwa da ahalinki saidai alahira,zanyi ƙoƙarin toshe duk wata hanya da zata sadaki dasu,domin cike burina" ammi ta faɗa cikin zuciyarta tana mai murmushi da ƙarewa kyakyakywar sarƙar kallo.
Kamar daga sama ta tsinkayo sallar Adeeb .dan haka cikin azama ta maida sarƙar cikin dan akwatin tare da rufe babban ta maida shi ajiyarsa.
Zama Adeeb yayi kusa da ita ,ba tare da yaga abinda tayi ba.cikin zafin zuciya yake magana da harshen larabci" ammi zan ɗauki mataki mai tsanani akan Rashad da mahaifiyarsa ,Dan kuwa sun ƙetare iyakarsu" Adeeb ya faɗa yana huci cikin ɓaci rai.
Wani daÉ—ine ya mamaye zuciyar ammi ,amma a zahiri da sauri ta kamo hannun Adeeb tana mai marairaice fuska tace " haba habeebee ,me yayi zafi ?me sukayi maka?Indai akan wannan maganar ce ,to kabar komai ahannuna zanyi wa tubkar hanci,bazai kara zuwa gurin ta ba"Ammi ta faÉ—a tana mai shafa bayan hannun Adeeb É—in.
Girgiza kai yayi cike da jin tsanar Rashad da Amma,kafin yace " ba wannan maganar bace,ammi Rashad ya ɗauke sarƙar da zata zama makamin da zai sada yarinyar da mahifanta,kuma nasan wannan tabbas shirin Amma ne, Ammi na rasa me kika tsarewa matar nan ta Tsaneki da ahalinki baki ɗaya,kullum burinta ta ganmu cikin tashin hankali ,why Ammi ?" Adeeb ya faɗa cikin mugun damuwa da tausayin Ammin nashi.
Sosai Ammi ta marairaice fuska kamar zatayi kuka ,kafin ta fara magana" habeebee nima bansani ba ,duk yadda nake ƙaunarta da iyalinta,amma sam bata gani tun kana yaro take ƙoƙarin saita ga bayanka ,amma Allah bai bata Sa'a ba, kai dai karvi gaba da haƙuri, sannan kabi komai cikin lumana.kuma awannan karon na goyi bayan ka ɗauki mataki akansu har sai sun bayyana sarƙar nan" Ammi ta faɗa cikin ƙarfafa gwuiwa ga Adeeb . Jinjina kai yayi cike da gamsu da shawarar ammin nashi.sun jima suna tattaunawa akan al'amarin ,ba abinda ammi ke yi sai tunzura Adeeb cikin cikima da basira.
Amma kuwa tana zaune abakin dagon Rashad,yayin da take shafa masa maganin zafi aciwonsa bayan yayi wanka da ruwan dumi.sosai take jin zafin abinda Adeeb yayiwa Rashad,kalli yadda yaji masa ciwo kamar wani marar gata?lallai saita É—auki mataki,dan bazata yarda da wannan cin mutuncin ba.
Kallon Rashad tayi wanda yake É—an runtse ido idan ta shafa masa maganin
zafin.
"Haƙiƙa Adeeb yana wuri gona da iri masarautar nan,kaima fa ɗane ba bawa ba,dan me zaiyi maka irin wannan dukan?saikace ya sami yaronsa, haƙiƙa bazan amince ba ,dole mai martaba ya shiga maganar nan,kuma wllh nayi alƙawarin sainaga bayan Ammi ,dan kuwa ita ke daure masa....yake abinda yaga dama.haka kawai an maidamu kamar wasu matasa iko agida,bazai yiwuba ,sam bazan laminci wannan abun ba" Amma ta kai ƙarshen zancen ta cikin fushi sosai da bacin rai.
Kallonta Rashad yayi shima cikin É“aci rai,yana mai faÉ—in "amma kibar wannan maganar atsakanin mu ,kar ki bari mai martaba yaji,dan kuwa da kaina zan É—auki mataki,wllh saina yi masa abinda sai yayi dana sanin aikata min wannan abun akan wata bare,ke dai kawai ki zubamin ido" Rashad ya faÉ—a yana mai kitsa abubuwa cikin ransa.
Wannan kenan.
Baƙi sun fara zuwa ta ko ina ,manyan sarakai da yan siyasa na ƙasar Misra, ko ina acikin gidan jama'ane keta kaiwa da kawowa,dan kuwa yau ne za'a gudanar da ƙayatacciyar walimar murnar dawowar prince Adeeb gida,daga ɓangaren Amma baƙi sunzo sosai,matan sarakuna na ƙasashe da dama,da matan manyan masu kudi da yan siyasa.dan haka hadimai sai kaiwa da kawowa suke dan kula da baki.
Yayin da bangaren Ammi kuwa ,ba magana ,dan kuwa itace uwar taro ,mai gayya mai aiki kenan,sosai ta tara manyan matan sarakuna dana yan siyasa ,da matan manyan attajiran larabawa,kai harda na ƙasashen Afrika .
Ammi taci uwar kwalliya cikin kaya na alfarma ,tayi ado da gwala-gwalai sai ƙamari take bugawa tana cikin matan data gayyata suna ta hira kafin a fara gudanar da taro.
Busar sarewace ta karfe fadar ,alamun da ke nuna wasu baƙin sarakan sun sami hallara,murmushi Ammi tayi dan kuwa ta gane busar ko ta wace ƙasace, ba kowa bace bace ƴar uwarta gimbiya Zulaihat ,wacce ke auren Sarkin gana.dan haka cikin farin ciki ta mike tare da cewa matan tana zuwa.kafin ta fice zuwa farfajiyar da aka ware musamman dan tarbar baƙin ta ,gurine ƙayatacce wanda yasha ado ,aka wadatashi da komai na jin dadi.
Tana tafe haɗimanta na biye da ita ,murmushine ɗauke akan fuskarta wanda ya ƙara ƙasa ta fuskar tata.
Wata farar mace ce kyakyakywar gaske ta fito daga cikin lafiyayyar motar da aka bude,masha Allah matar ta ko ina ta hadu ,fuskarta ɗauke da murmushi mai ƙayatarwa,idanunta na kan Ammi rungume juna sukayi cikin farin ciki,ammi keyiwa matar Barka da zuwa.
Wasu kyawawan yara ne su biyu suka fito daga É—aya gefen,da ala'ma yaran tagwayene duba da yadda suke tsananin kama da juna.yaran zasu kai shekara goma ,saidai yanayin jin dadi da hutu,yasa zaka yi tunanin sun wuce hakan,suna sanye da kaya iri É—aya ,cikin shiga ta ya'yan sarakai.
Gurinsu ammi suna nufo cike da murna suka rungume Ammi,ita cikin jin daÉ—i ta rungumesu tare da sunbatar gishinsu,tana mai faÉ—in," yazeed and zayyad my children" ammi ta faÉ—a tana shafa kansu.
Part É—in ammi suka nufa gaba É—ayansu,cike da murna.
Adeeb ne zaune bakin gado yayin da tareeÆ™ ke gefensa ,yana tashi shiryawa,shi dama Adeeb baida aboki ,tareeÆ™ kaÉ—ai ne abokinsa kuma yaronsa,dashi yake ko wace irin shawara ,dan haka ya zuma suna zaune suna shiryawa,dan Adeeb baya barin kowa ya shigo masa part É—insa, shi fa akan dole yake abubuwan masarauta, dan sam sarauta bata burgeshi, yafi son kasuwancinsa.
Kallon tareeƙ yayi yana mai faɗin,"tareeƙ nufa na gaji da wannan shirin Please ya isa haka" ya faɗa yana ɗan kwaɓe fuska cikin salon shagwaba.
Murmushi tareeƙ yayi yana mai ɗaurawa Adeeb wani agogon azurfa ahannunsa kafin yace " yallaɓai yaufa dole kayi haƙuri ,dan kuwa saikayi shiga irin ta yarima sosai " tareeƙ ya faɗa yana ɗan danne dariyarsa ganin yadda Adeeb ya wani marairaice kamar zaiyi kuka.harararsa Adeeb yayi yana mai faɗin" dariya ma zakayimin ko?ai kaima mugune nasani ,shiyasa kake ta lodamin kaya haka kamar wani dan dako"
Dariya sosai tareeÆ™ ya sanya yana mai faÉ—in" yallabai kasan fa yau sauka gaji da ganin yan mata ,dan zasu yi ta kawo maka hari ne,Suda iyayensu,dan haka dole kayi adon da zaka rikitasu" tare ya faÉ—a yana kallon yanayin Adeeb É—in.
HaÉ—e rai Adeeb yayi yana mai gwabe baki yace " aikuwa zasu wahalar da kansu ne kawai,dan duk ba wacce zata burgeni acikinsu" ya faÉ—a yana mai mikewa tare da gyara kwalar rigarsa.
Murmushi tareeƙ yayi kafin yace "amma yallaɓai yau idan Madam ta ganka zaiyi wahala ta gane ka ,dan kuwa kayi matuƙar kyau Masha Allah,yau lafiya ayarimanka sai" tareeƙ ya faɗa yana mikawa Adeeb wani takobi ,wanda ke matukar gyalli da ɗaukar ido.
Murmushi ne yakub cewa adeeb,jin tareeÆ™ ya ambaci Madam,kallon kansa ya karayi cikin madubi,masha Allah,ko aljanu ya kalli Adeeb to tabbas dole saiya yaba kyau da Allah yayiwa adeeb.
" Kasan bata da lafiya ma,kuma bazata je gurin taron nan ba,zata zauna tare da nanny ,acikin gida,dan haka muyi sauri muje In dubawa sai mu wuce " Adeeb ya faÉ—a yana mai rataya takobin.
Murmushi tareeƙ yayi yana mai jin dadi cikin zuciyarsa,tabbas hasashensa yana neman zama gaskiya,dan kuwa ya kula Adeeb ya faɗa kogin SOYAYYA ,wanda hakan yayi masa daɗi,fattu itace daidai da Adeeb." Yallaɓai kayi kama da mai son zuwa ganin budurwarsa fa" tareeƙ ya faɗa yana ɗan sosa kansa.
Ƙeyarsa adeeb ya ɗan buga kafin yace " ka manta dai ba budurwa ba ,mata zakace ,kuma kasan hakkin ta ne induba lafiyarta ,kafin na sawwaƙe mata,iya muje" Adeeb ya faɗa yana mai kamo hannun tareeƙ.
Murmushi tareeƙ yayi yana mai cewa " zaka dawo hanya ma yallaɓai" ya faɗa cikin zuciyarsa.
Suna fitowa kuwa hadiman da suke ƙofar part ɗin suka ɗauka kirari da bushe bushe irin na larabawa,runtse ido Adeeb yayi cike da damuwa,dan shikam wannan bushe bushe baya so ,dan dai ba yadda zaiyine.
Cikin takun izza da isa yake takawa ,tareeÆ™ yan gefensa sai hadiman dake binsa baya suna busa.
Kai tsaye ya wuce part É—in ammi,da gudu su zayyad suka taho suka rungume ,Adeeb cike da murna ,dan kuwa sun saba dashi sosai.dagsu yayi daya bayan É—aya yana dariya ,
Gimbiya suhaimat ma cike da murmushi take kallon Adeeb,yaron yana burgeni sosai,yana da nutsuwa ga don yara,har ƙasa ya durƙusa ya gaida gimbiya suhaimat,da amminsa, sosai ammi ke yaba kyan da Adeeb ɗin yayi,wani lambu ta ɗauko na na zinare ta sanya masa hannunsa ,tare da wani turare mai kanshi daɗi.
Murmushi yayi tare da mata godiya sosai,kafin ya É—an juyo yana kallon gimbiya suhaimat,haka kawai yaji gabansa ya fadi sosai ,wani tunanine ya É—arsu cikin zuciyarsa ,saidai da sauri ya kawar da batun daga ransa,ya yayi waje .yana gab da ficewa saiga gimbiya Zulaihat ta shigo part É—in ,taci uban ado kamar wacce zata gasar sarautar kyau.
Kallo daya Adeeb yayi mata ya kauda kansa tare da haÉ—e fuska.
Ita kuwa neman gigicewa tayi da yadda taga Adeeb yayi kyau,cikin hanzari ta tari gabansa tare da kamo hannunsa tana mai jin kamar ta rungume shi.
Wani shegen kallo da Adeeb ya watsa mata ,bata san lokacin datayi saurin sakin hannunsa ba ," kayi kyau my prince"ta faɗa tana wani narkar da fuska cike da tsantsar ƙaunar Adeeb ɗin.
Harara ya watsa mata tare da tsaki kafin ya bar gurin cikin sauri.
Kai tsaye part É—in nanny suka shige ,tana zaune afalo ,gefen ta kuma ,wani É—an karamin akwatine mai kyau da É—aukar ido.
Zama sukayi shida tareeÆ™ suka sata atsakiya, gaida ta sukayi,ta amsa cikin farin ciki tana mai shafa kan Adeeb,akwatin nan ta buÉ—e tare da É—auko wani zobe mai kyau sosai ta zira masa ayatsansa na dama.
Murmushi yayi tare da sumbatar zoben kafin yace " tana ina " ya faÉ—a cikin salonsa yana É—an yamutse fuska.
"Tana ciki magajin faÉ—a " nanny ta faÉ—a .
Tashi yayi cikin nutsuwa ya nufi dakin da fattu ke zaune.....
Masu karatu ina barar addu'ar ku,iftila'in rusau ne ya faru agarinmu,wllh gidaje sai rushewa suke,,dan Allah ku samu cikin addu'a bayin Allah suna cikin damuwa sosai ,shiyasa kukajini shiru kwana biyu,abin ya taɓa har anguwar da mahaifiyata take
Muna buƙatar addu'ar ku.
Na gode
Mrs babi ce💘💘
29/08/2022, 10:59 am - Khadijah Salisu Fari: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄
MACIJI NE🪱🪱🪱
Na mammy kabeer
(Anty mammy)
Elegant online writers📚📚
Free book
Page 49/50
_______________Tashi Adeeb yayi cikin nutsuwa, da takunsa irin na jaruman maza ,ya nufi É—akin da fattu ke ciki.
Fattu na zaune abakin gado, tayi shiru kamar mai tunanin wani abu,Adeeb ya turo ƙofar da sallama ɗauke abakinsa,saidai idan ba ka kasa kunne ba ,to bazakaji me yake faɗi ba.
Dago Kai fattu tayi jin muryar Adeeb datayi,baki buɗe take kallon Adeeb ,tunda take arayuwarta,zata iya cewa bata taɓa ganin mutum mai kyau irin na Adeeb ba ."masha Allah"fattu ta faɗa tana mai mikewa tsaye fuskarta ɗauke da murmushi,ta ƙure Adeeb da ido kamar yau ta taɓa ganinsa.
Ƙarasowa Adeeb yayi cikin ɗakin,shima idonsa na kanta ,dan haka kawai yaga tayi masa kyau shima .
ÆŠan harararta yayi kafin yace " Please karki cinyeni da kallo mana"ya faÉ—a yana É—an wani gwabe fuska cikin shagwabar da baisan yayi ba.
Da sauri fattu ta sanya hannu tare da rufe fuskarta tana É—an dariya ,dan kunya taji da yadda yayi salon maganar tasa.
"Hamma kayi kyau sosai ,kai mai kyaune" fattu ta faɗa kanta a ƙasa tana ɗan mirza hannunta.
Wani irin sanyi ne yake ratsa zuciyar Adeeb, sosai yaji daɗin maganar fattu ,dan haka cikin wani irin shauƙi ya mika hannunsa tare da dago habarta .kallon juna suke ido cikin ido,murmushi Adeeb yayi kafin yace "kin tabbata nayi kyau a idonki?wankana yayi miki kyau?" Ya faɗa yana mai kallon lips ɗin fattu ,wanda yake ji kamar ya cinyesu.
Lumshe ido fattu tayi tare da jinjina kai tace " Hamma bantaɓa ganin mutum mai kyan ka ba,kuma Ni kullum ma kyau kakemin" ta faɗa tana ɗan riƙe lips ɗin ta na ƙasa da haƙoranta.
Wani irin abu Adeeb yaji yana masa yawo ajikinsa,sosai yake jin yana son rungumar fattu ajikinsa ,duk lokacin da yake tare da ita yakan tsinci kansa cikin wani irin shauƙin son kasancewa da ita .
Murmushi yayi tare da shafa gefen fuskarta yace " to me zaki bani matsayin kyautar dazan fita gurin taro da ita?" Ya faÉ—a idanunsa akan lips É—in ta.
Shiru fattu tayi tana É—an rarraba ido,to ita me take dashi ma ?dazata ba Hamma?
"Hamma Ni bani da komai fa ,bansan me zan baka ba.
Kallonta yake baya ko ƙiftawa ,ajiyar zuciya ya sauke yana faɗin " shikenan tunda ba abinda zaki bani,zan tafi,amma karki fito ko ina kinji?ki kwanta kiyi barci da zaran mun tashi daga gurin taro zanzo in ganki "Adeeb ya faɗa yana mai kallon fuskarta.
Jinjina kai fattu tayi tana mai kallon Adeeb É—in,sai taji bataji daÉ—i ba ,ace ya tambaye ta wani abu ita kuma bata bashi ba,kuma duk abinda take dashi ma ai shine ya siya mata,to mezata bashi?fattu ta faÉ—a cikin zuciyarta ,fuskarta É—auke da yanayin damuwa.
Ahankali Adeeb ya fara takawa zuwa bakin ƙofar fita daga ɗakin haka kawai yake jinsa wani iri, sam baya don rabuwa da fattu yau ɗin nan.ganin yana neman fita yasa Fattu ta tako da sauri tare da rungumeshi ta baya.
Dammm!dammmmm!!dammmm!!!gaban Adeeb ya bada wani sauti na bugawa.
Cikin hanzari ya runtse idanunsa,dan yadda yaji fattun ajikinsa ,abin yazo masa cikin bazata.
"Hamma kayi haƙuri wllh bani da abinda zan baka ,amma indai na tara kuɗina zan siya maka cin-cin burodi,nima baffa ke siyomin idan yaje gari, ka fadi abinda kake so nayi maka yanzun" ta faɗa tana mai gyara kanta dake kwance tsakiyar bayan Adeeb.
Cikin dauriya da jarumta Adeeb ya sanya hannunsa ya jawo fattu zuwa gabansa.bude idanunsa yayi dasuka fara rinewa sai wani lumshewa da budewa yake .
Ido ya ƙura mata na wani lokaci,kafin ya matso da fuskarsa zuwa gareta,ta yadda numfashinsa ke sauka akan Tata fuskar.
"Kin amince Ni na É—auki Abinda nake ganin yayi amatsayin kyauta ta " Adeeb ya faÉ—a cikin voice É—insa mai kama da yana mata raÉ—a.
Da sauri fattu ta gyada kanta ,dan yadda yayi maganar saiya sata jin wani iri atare da ita.
Lips É—inta Adeeb ya kalla cike da tsantsar son jinsu cikin bakinsa.bai jira komai ba ya É—ora nasa lips É—in nata.
Gaba É—ayansu sun shiga wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa ,cikin salo da narkar da zuciyar mace Adeeb ke kissing fattu ,yayi da ita kuma take jin abin da yake mata har cikin ranta.idonsu alumshe yake sun lula wata duniyar ,dan tuni Adeeb ya mance da batun taro ,ya sami lips É—in fattu kamar ya sami lollipop.
Bugun da akeyiwa ƙofar ne yasa Adeeb saurin dawowa cikin hayyacinsa,ahankali ya zare lips ɗin sa daga bakin fattu yana kallonta .har lokacin idanunta alumshe suke ,sai sauke numfashi take cikin sauri,jikinta yana bari.
Bakin gado Adeeb ya zaunar da ita,tare da shafa gefen fuskarta yace " wannan ma ya isheni nishaÉ—i har agama taron ,antee sururi Hulwa" Adeeb ya faÉ—a yana mai juyawa ya bar É—akin.
Saƙare fattu ta zauna abakin gadon kamar wata butumbutumi,haƙiƙa tana jin Hamma har cikin ranta,wani irin shauƙi takeji game dashi,sannan ko kaɗan bata jin damuwa idan tana tare dashi,lallai Hammanta shine farin cikinta,ga shi aduk lokacin da Hamman nata ke sha mata baki tanajin wani irin nishaɗi sosai,ko me yasa ma yake sha mata bakin oho?
Murmushi tayi tare da shafa lips É—in ta ,tanaji kamar har yanzu hamman na shan lips É—in nata.
Taro yayi taro ta ko ina ka ƙalla jama'ane Malik a haɗaɗden dakin taron dake cikin masarautar,abie na zaune kan wata kyakykyawar kujera ta zinare, yayinda Adeeb ke gefensa shima zaune kan wata kujera mai shegen kyau da ɗaukar hankali.
Gaba É—aya yan gidansu Adeeb suna zaune kan kujeru masu kyau,sai baki sarakuna da matayensu,kowa kagani yayi ado na kece raini,
Yan mata sai kaiwa Adeeb hari suke da idanuwansu da jikinsu, amma ba wacce ta ishe shi kallo acikinsu.
Anata jawabai da taya abie murnar dawowar É—ansa bayan tsawon lokaci da aka dauka ana nemansa.
Ammi na zaune ita da tawagarta,yayinda gimbiya suhaimat ke kusa da ita ,sai sauran baƙinta, hakama amma na zaune tare da Tata tawagar cikin ado mai kyau.wata matace zaune agefenta tana ɗan kallon ammi,kafin ta juyo da kallonta ga amma tace " Dole saikinyi da gaske kafin ki gama da matar can,makircin ta yayi yawa,ina tsoron kaidinta"
Kallon ammi itama amma keyi kafin ta sauke ajiyar zuciya tace " karki damu Maryam,ninasan ta inda zan bullowa al'amarin nan,akwai Abinda ke É—auremin kai sosai,game da gimbiya suhaimat,
ina don gano asalin gaskiyar abin kafin nayiwa ammi kwaf É—aya,amma zanyi bincike sosai akan lamarin.
"Shikenan zan ci gaba da baki goyon baya ,Abdul lokacin da kike buƙatar taimakona ƙofa abude take" cewar matar.
Godiya amma tayi mata cikin murmushi,
Nan dai suka ci gaba da tattauna akan yadda zasu ga bayan ammi.
Rashad na hango zaune cikin wani kaya masu kyau irin na sarauta,fuskarsa ɗauke da murmushi,ya kafe Adeeb da ido baya ko kiftawa.wayarsace tayi ƙara dan haka ya ɗauka tare da karawa akunnensa, har lokacin idonsa na kan Adeeb,wanda shima hankalinsa yayo kan Rashad ɗin,kallonsa yake cike da tsana, tun lokacin da ya zaune yake kallon Rashad ɗin yana kula da duk wani motsinsa.
Dan kwata-kwata zuciyarsa bata yarda da Rashad ɗin ba,gani yake kamar akwai wani makircin da yake ƙullawa.
Dan haka ya sa tareeÆ™ ya kula da Rashad sosai.
"Ya kamata fa kaje ka aiwatar da abinda zakayi, kafin lokaci ya ƙure " ammi ta faɗa tana ɗan kallon gefen da Rashad ke zaune,waya kange akunnenta,da alam ita ta kira Rashad ɗin.
Wata dariya Rashad yayi kafin yace " ammina ta kaina ,ina sane da lokaci,yanzu zan tashi domin cike burina, yau saina hana Adeeb barci da irin aika -aikar da zanyi masa" Rashad ya faɗa idanunsa ƙur akan Adeeb, wanda ya Dan rangwafo kusa da mai martaba ,da alama suna magana ne.
Kashe wayar ammi tayi tare da sauke wata ajiyar zuciya mai ƙarfi,kafin ta kalli gimbiya suhaimat tace " Ni kuwa suhaimat ina wannan sarƙar taku ta ahali, bana gajiya da kallonta ko kaɗan ,naga banganta atare da ke ba" ammi ta faɗa tana mai kallon gimbiya suhaimat.
Murmushi matar tayi kafin tace " har abada bazan taɓa rabuwa da wannan sarƙar ba,dan kuwa itace shaidar dazata sadani da ƴata, Aduk inda take,ina ji ajikina mun kusa haduwa da juna kuma nayi alƙawarin saina ɗauki fansar rabani da ita da akayi na tsawon shekaru,akan koma waye keda hannu cikin al'amarin " ta faɗa idanunta cike da kwallah.kafin ta ɗan daga mayafin jikinta ,saiga sarƙar ta bayyana ,ƙurawa sarƙar idanu ammi tayi,tabbas wannan irin sarƙar wuyan yarinyar can ce ,hakan na nufin fattu itace ɗiyar suhaimat da suka rasa shekarun baya?innalillahi wa'inna ilaihir raji'un.banga ta zama ba. Cewar ammi cikin zuciyarta.
Da sauri ta miƙe tana mai faɗin "suhaimat ina zuwa "bata jira amsar taba tayi gaba.
Rashad ma ganin ammi ta mike yayi saurin bin bayanta dan zuwa ga fattu,yau kam za'ayi ta ta ƙare.
Zulaihat dake zaune cikin ƙawayenta tana ta zuba izza da iyawa ,ganin su duka biyun sunyi waje hakan yasa itama ta mike cikin sauri ta rufa musu baya, dan kuwa tare zasu aikata mugun nufin nasu akan fattu, tana son ganin komai ya wakana akan idonta ,
Ko ina zasu kuma oho?
Muje zuwa masu karatu,
Manage please har yanzu muna cike da alhini.
Na gode sosai da addu'ar ku garemu,waÉ—anda suka kirani,da waÉ—anda sukayi min ta waya.
ðŸ™ðŸ™
Anty mammy ce
Mrs babi💘💘
Share and comment fisabilillah.
29/08/2022, 11:00 am - Khadijah Salisu Fari: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄
MACIJI NE🪱🪱🪱
Na mammy kabeer
(Anty mammy)
Elegant online writers📚📚
Free book
Page 51/53
_________________Abakin ƙofar hall ɗin Zulaihat ta tarar da Rashad ,yana tsaye da waya ahannunsa ,da alama kira yake ƙoƙarin yi,saidai yana ganinta ya maida wayar cikin aljihunsa yana mai faɗin,"yawwa dama ke nake ƙoƙarin kira,sai gaki kin fito.
Ƙarasowa Zulaihat tayi kusa dashi ta tsaya" ya ake ciki ne ?" Ta faɗa tana ɗan waigen bayanta.
"Yau burina zai cika ,zan sami abinda ke hanani barci,kuma zanyiwa Adeeb illah,saina rama dukan da yayi min akan yarinyar da yake iƙirarin yar amanar da ce,bayan kuma Ni nasan dadironsa ce ,kawai kishine da mugunta sukayi masa yawa,shine ya hanani Nima in ɗana"cewar Rashad yana mai kallon Zulaihat.
"Kaga Rashad karka ƙara cewa dadiron my Prince ce,karkayi masa sharri,dan kuwa nasan halinsa nasan koshi waye,wllh bazai taba ajiye yarinyar nan dan biyan buƙatarsa ba,mutumin da har maganin sha'awa nake saka masa alemo,dan kawai yayi tarayya dani,amma duk yadda ya galabaita bazai koda rungumeni ba.
Dama dai kaine akace ka ajiye ta dan biyan buƙatarka,to wannan kam na yarda dan nasan kai din namamajo ne " Zulaihat ta faɗa tana mai galla masa harara,dan taji haushin sharrin da yayiwa adeeb,ita da take burin ace itace zata fara bude Adeeb aledarsa ina zataso jin wannan batu.
Wani shegen kallo Rashad ya watsa mata kafin yace " banza yar tasha ,ke har Ni zaki cewa na mamajo? Ai duk iskancina ban kaki ba,kefa Æ´ar maye ce sannan jarababbiya, Ni kaina sau nawa ina taimaka miki ?ina ce wataran har guduwa nake saboda jarabarki ?zaki raina min hankali wawiya kawai" Rashad ya faÉ—a cikin faÉ—a.
Haushi sosai ya kama Zulaihat ,ranta ya É“aci da kalaman Rashad gareta ,wato har gori zaiyi mata ,dan ta neme shi kusan sau uku ?ba komai zai gane kurensa wllh.
"Ni kakeyiwa gori Rashad ?to wllh kasani bazan taimaka maka akan ƙudirinka na yauba ,saidai kayi kai kadai ,banza marar mutunci" Zulaihat ta faɗa cikin ɓaci rai tana mai barin gurin cikin sauri.
Tsaki Rashad yayi yana mai faɗin"aikin banza ,da me zaki iyamin agurin banda kema kice kina so intaimaka miki ,Ni kuwa ranata ta yau duka ta fine baby ce,yar ƙwaya kawai " ya faɗa yana mai nufar part ɗin ammi.
Ammi kuwa tana zuwa part ɗinta cikin ɗakinta ta nufa ,ƙullewa tayi tare da zama bakin gado,tana tunani iri iri cikin ranta, wata akwati ta ɗauko dake can ƙasan gadon ta tare da budewa,
Tana buɗewa wani hayaƙi yayo sama baƙiƙirin dashi,banda wari ba abinda ke tashi cikin hayaƙin nan,da sauri ammi ta toshe hancinta, tana mai zaro ido waje,abayyane ta furta " na shiga ukuna ba dai kwalbar nan ta fashe ba? Shikenan ta faru ta ƙare ,dama nasan hakan zata faru wayyo Allah na" ammi ta faɗa tana mai bin wata kwalba yar gajeriya da ta tarwatseda ido,wani farin abu mai kauri yana ta motsi kamar tsutsa.
Bugun ƙofar da ammi tajine yasata saurin rufe akwatin ta tura can kasan gado,saita kanta tayi cikin ɗauriya ta nufi ƙofar .
Rashad ta gani tsaye abakin ƙofar ,"ammi ya ake ciki ne ?ta yaya zan ɗauki yarinyar ne ?kinsan ba aɗakin ta zan aiwatar da ƙudirina ba,dan wancan mayen zai iya zuwa ya cin mini" ya faɗa yana kallon fuskar ammi .
"Ka tafi can É—ayan part É—ina ka jira zan kawo maka ita da kaina ,ina son kayi mata abinda nan da wata guda ma bazata san inda kanta yake ba,bana son ka tausaya mata ko kaÉ—an"ammi ta fada fuskarta ahaÉ—e.
"Kada ku damu ammi bazan taɓa baki kunya ba,nayi alƙawarin saina yi mata abinda Bama ki tsammata ba"Rashad ya faɗa yana wani irin killer smile.
Ficewa ammi tayi tare da nufar part ɗin su fattu.ba kowa afalon,dan kuwa nanny ta ɗan leƙe gurin taron ,ganin fattu kwance tana barci.
Cikin É—akin ammi ta shiga ,tsaye tayi agaban gadon da fattu ke kwance ,idanunta arufe kamar mai barci,amma idanunta biyu,hammanta kawai take tunani.
Kusan minti uku ammi tayi tana kallon fattu dake kwance ,tabbas ko tantama batayi ,wannan yarinyar gimbiya suhaimat ce ,dan kuwa sai yanzu take ganin tsantsar kamannin dake tsakaninsu,amma ta yaya suka haÉ—u da Adeeb?har ya taho da ita nan?wannan shine abinda take son sani.
Ganin fattu ta É—an motsa ne yasa ammi ta É—an kira sunanta " fateema tashi"
Ammi ta faÉ—a tana É—an shafa kan fattu.
Ahankali cikin nutsuwa fattu ta tashi zaune tana É—an mika ,dan ta jima akwance.
Murmushi tayiwa ammi tare da sunkuyar da kanta ƙasa cikin kunya .
"Fateema Sarkin kunya,ke kadaice aÉ—akin ne"ammi ta faÉ—a cikin Hausa ,dan kuwa ta iya Hausa sosai itama.
Jinjina kai fattu tayi tana wasa da Æ´an yatsunta.
Murmushi ammi tayi tana shafa kan fattu kafin tace " to ya jikin naki,?"
" Da sauƙi inna"fattu ta faɗa cikin yar karamar muryarsa mai dadi.
"Kinga bai kamata ki zauna ke kaÉ—ai anan ba kowa ba,dan haka maza ki tashi ki koma can É—aya part É—in sauki kwanta kiyi barcinki kinji?kafin tashi daga taron" ammi ta faÉ—a tana mai kamo hannun fattu cikin nata ,suka fice daga É—akin.
Binta fattu tayi ba tare da ta musaba, dan tana tsananin jin kunyar ammi,saidai haka kawai taji gabanta na faÉ—uwa,gashi hammanta yace karta fita ko ina ,karya dawo bai ganta ba ransa ya É“aci.
Haka dai tabi ammi har zuwa wancan part É—in da Rashad take ciki.
Wani É—aki ammi ta kaita tare da zaunar da ita akan kado,tace cikin murmushi"ki zamanki anan kinji,idan kina jin barci saiki kwanta,akwai abubuwan ci ,acikin fridge idan kinji bukatar ci" ammi ta faÉ—a tana mai kallon fattu ,fuskarta É—auke da murmushi.
Jinjina kai fattu tayi kafin tace "inna !Hamma yace karbaje ko ina ,karya dawo kuma bai ganni ba"ta faɗa kanta aƙasa.
Wata uwar harara ammi ta bankawa fattu,kuji yar iyayi shegiya mai kama da aljanu,zaki gane kurenki, ne yau zaki yabawa aya zaƙinta,dagake har Adeeb ɗin.
Da sauri ta saki fuska tana murmushi,ganin fattu ta É—ago kai tana kallonta,"karki damu habeebtee zan sanar da Adeeb nina kawoki nan kinji?"ammi ta faÉ—a tana sumbatar goshin fattu .kafin ta fice daga É—akin.
Rashad ta ci karo dashi abakin ƙofar ,daga shi sai wando iya gwuiwa da singlet,kallonsa ammi tayi cike da murmushi,tana mai faɗin"Rashad kenan,wannan zumuɗin haka?,nidai ka kula da maganata banson asami matsala" ammi ta faɗa tana mai kamo kunnensa.
Murmushi yayi yace "baki da matsala ammina,ke dai kawai kijira sakamako"ya faÉ—a yana mai murmushin mugunta.
"Amma ka jira sai an jima kadan,zan kulle ƙofar ta baya,inka gama sauka fice ta ɗayan ƙofar" jinjina kai Rashad yayi cikin zaƙuwa da son ammi tayi ta fice daga ɗakin.
Adeeb yana zaune kusa da abie ,saidai haka kawai yakejin gabansa na faɗuwa ,sosai yake jin faduwar gaban.fattu kawai yake tunani yana ji cikin ransa yana buƙatar ganinta ahalin yanzu.
Kallonsa ya kai inda Rashad ke zaune,saidai ba alamunsa agurin.gabansa ne ya ƙara mugun faɗuwa,ina Rashad ya nufa?yaushe ya bar gurin?
Da sauri ya yunƙura zai mike,dan zuwa ya duba fattu,saidai gurin taron ne ya kara de da kiran sunansa Adeeb,ana buƙatar yayi jawabin godiya ga baki .
Kallon abie yayi cikin yanayi na marairaita ,amma abin ya jinjina masa kai alamun yaje yayi jawabin.
Haka Adeeb ya karbi lasifikar nan badan ransa yaso ba,burinsa kawai yaje gurin fattu.
Adaidai wannan lokacin kuma Rashad ya kulle ƙofofin ɗakin daga falon har zuwa toilet duka,ɗakin da fattu ke ciki kawai ya bari abuɗe .kai tsaye ya kunna kansa cikin ɗakin.
Fattu na zaune abakin gadon inda ammi ta zaunar da ita,zuciyarta sam bata aminta da zaman É—akin nan ba, sai kalle kalle take,
Da sauri ta juyo atsorace jin kamar mutum atsaye akanta.
Ido huɗu sukayi da Rashad tsaye abakin ƙofa yana kallonta ,fuskarsa ɗauke da murmushi irin na yan duniya,
Da sauri fattu ta miƙe tsaye jikinta na rawa,me wannan mutum yake yi anan kuma?ba innar Hamma tace nan ma ɗalibta bane?innalillahi,wayyo hammana kana ina?fattu ta faɗa cikin ranta jikinta na rawa matuƙa.
Murmushi Rashad keta famanyi,yana takowa cikin ɗakin bayan ya kulle ƙofar,cikin harshen larabci yake faɗin"yan mata meye na tsorata haka?nimafa nazone nayi miki abinda wancan wawan yayan nawa ke miki,ki nutsu yarinya musha daɗinmu tare ,dan kuwa yau wllh ko mutuwa zakiyi saina kwashi daɗi" ya faɗa yana mai karasowa bakin gadon.
Kuka fattu ta fara tana mai yarfe hannu, dan kuwa sosai take fahimtar yaren yanzu,dan haka ta fahimci da dama abubuwan daya faÉ—a,
"Wayyo Allah na kayi hakuri dan Allah ,wllh niba yar iska bace ,kuma Hamma baya min komai,kayi min rai dan Allah"fattu ta faÉ—a cikin kuka sosai tana ja da baya.
Zagaye suka fara ita da Rashad,yana ƙoƙarin kamota,ita kuma tana zillewa cikin kuka tana masa magiya,akan ya barta karya mata komai.
Ganin zata É“ata masa lokaci ne kawai yayi wani tsalle tare da damko gashin kanta cikin fushi ya wanka mata mari tare da hankaÉ—ata kan gadon.
"Dan ubanki ki nutsu wllh idan kika É“atamin lokaci,saina yi miki fata-fata anan gurin,kina abu kamar baki san me nake sanyi ba ,ko irin baki taba yi É—in nan ba,shi wancan wawan idan yazo haka kike masa?Rashad ya faÉ—a cikin tsawa yana mai haurowa kan gadon.
Cikin azama fattu ta mirgina can karshen gadon tana kuka,tare da kiran "wayyo hammana kazo ,Hamma kazo ka taimakeni"
Ran Rashad ne ya ƙara ɓaci ganin zata ɓata masa lokaci,da sauri shima ya bita ya damko gashin kanta,ya ƙara wanke ta da mari, nan da nan gefen bakinta ya fashe jini ya fara zuba.
Ihu fattu ta kwalla cikin azaba tana kuka tare da riƙe hannunsa daya damko gashin kanta .
Ƙoƙarin Rashad yake ya haɗe bakinsa dana fattu ,amma sai kauda kai take tana kuka tare da juya kai.
Bakinta Rashad ta matse da karfin gaske ,gaba ɗaya kamaninsa sun sauya ,ba abinda yake so da buri illa yabiya buƙatarsa da fattu.gashi sai neman bashi matsala take.
Hannunsa ɗayan ya ɗora akan ƙirjin fattu ,zaro ido fattu tayi cikin tsantsar razana da jin hannunsa inda ba wanda ya taba ɗorawa,da karfi ta dunkule hannunta tare da buga masa aciki.
Ihu Rashad ya kwalla Dan kuwa ta bugeshi sosai acikinsa.
HankaÉ—ata yayi jikin bango ,aikuwa ta buga kanta ajikin bangon ,ji kake gummm!!ta gwara kanta.
Ihu ta kwalla cikin azaba tana mai dafe goshinta da jini ya wanke ,tsabar azaba numfashinta har É—auke wa yake.
Ko tashi ta kasayi,da rarrafe ta nufi bakin ƙofa jini na zuba agoshinta.
Cikin mugun bacin rai Rashad ya nufota, rigarta ya kamo ta baya ya fizgota baya.
Mari yayi ta sauƙe mata har guda hudu,sannan ya cilla ta kan gadon,
Gaba É—aya fattu ta fita daga hayyacinta ,ko hannunta bata iya dagawa,numfashinta sai kaiwa da kawowa yake,
Rashad kuwa cikin rashin imani ya zare wando sa tare da singlet yayi kan fattu gadan -gadan ,yana zuwa ya janye gadon tare da kama rigar fattu ya yagatadaga sama har ƙasa ,sannan ya...........
Wayyo fattu ,Hamma kana ina kazo ka ceci fattunka,shikenan Rashad zai cutar da fattunka .
Da gudu na fice dan nemo inda Adeeb yake .saiki biyoni muje nemansa tare.
Taku ce anty mammy Mrs babi💘💘
Share and comment fisabilillah
More comment
More typing.
29/08/2022, 11:02 am - Khadijah Salisu Fari: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄
MACIJI NE🪱🪱🪱
Na mammy kabeer
(Anty mammy)
Elegant online writers📚📚
Free book
Page 53/54
________________Gaba ɗaya Rashad ya zama kamar wani mahaukaci,ba abinda ke gabansa face biyan buƙatarsa.
Gaban rigar fattu ya kama da karfin tsiya ya tsargeta ,tun daga sama har ƙasa.
Nan da nan farar best ɗin fattu da baƙin skin tite ɗin ta suka bayya, Allah ma yasa wandon har ƙasa yake.
" Wllh yau ko da zaki mutu ,saina ida nufina akanki,banga wanda zai iya karbarki daga hannuna ba" Rashad ya faÉ—a cikin wata irin murya ta azzalumai,waÉ—anda suka manta da cewar Allah yana kallonsu duk abinda suke aikatawa.
Da gyar fattu ta iya buÉ—e rinannun idanunta ,wanda tsabar mari da kuka suka sanya idanun kumbura sosai.
Ahankali take daga lips ɗin ta magana take amma saiƙa kura mata ido zaka fahimci me take cewa."wallahu galibun ala amrina" shine abinda take ta maimaitawa abakinta.
Ƙoƙarin zare skin tite ɗin Rashad keyi amma sam ya kasa,jikinsa sai rawa yake,yana jin kamar wanda ake jona masa shocking,Amma tsabar masifa da jaraba ,yaki fasa abinda yakeyi,
Cikin haushi,ya ƙara kaiwa kumatun fattu mari mai zafi da shiga jiki."Dan ubanki me kikasa ajikinki?idan na taɓaki nakejin kamar ana zuƙemin jini?"Rashad ya faɗa yana mai kai fuskarsa saitin Tata,bakinsa ya ɗora akan na fattu,aikuwa ba wata wata fattu ta gartsa masa cizo alips ɗinsa.kara ya kwalla yana mai komawa gefe dafe da lips ɗin sa na ƙasa "kai -kai -kai Ni kika ciza Dan uwarki?zaki gane kurenki ,wllh yau saina kusan kasheki Shegiyar yarinya mai taurin kai"Rashad ya faɗa yana mai danƙo gashin fattu ,wanda yayi buju-buju.
Fattu fa ko motsin kirki bata iyayi,gaba ɗaya jikinta ya saki,tunda take a rayuwarta,bata taɓa shiga tashin hankali da azaba irin na yauba.
Sunan Allah kawai take ambata cikin ranta.
Adeeb kuwa cikin gaggawa yayi jawabinsa tare da godiya ga baƙin da suka zo dan tayashi murnar dawowa gida cikin ƙoshin lafiya.sosai ƙirjinsa ke mugun bugawa zuciyarsa kamar zata fito waje,idanunsa sunyi jajur dasu,wani irin ɗaci yakeji cikin zuciyarsa,sannan ko dana second ɗaya ne fattu taƙi barin tunaninsa.
Gefen da Rashad ke zaune Adeeb ya ƙara kai dubansa, baya gurin har zuwa yanzu,kai gaskiya akwai Abinda ke faruwa ,dole yaje ya duba Hulwa.
Dan haka cikin hanzari ya mike tsaye ,kallonsa abie yayi tare da tambayar ina zashi haka ?ya mike cikin hanzari,sanar da abie yayi cewar kansa ke ciwo yana son yaje ya kwanta.
Sanin da abie yayi cewar ,sam Adeeb yana son hayaniyane,yasa shi cewa yaje ya kwanta sannan yasha magani,akwai maganar da zasu yi zuwa dare.
Cikin sauri da sassarfa Adeeb ya nufi ƙofar barin hall ɗin,yana ɗan kallon gefen da tareeƙ ke zaune,saidai baiga tareeƙ agurin ba.dan haka ficewa yayi daga hall ɗin yana mai takawa da sauri sosai.
Bangaren nanny ya nufa kai tsaye,yana shiga ya tarar da tareeƙ da nanny atsaye cirko -cirko,gabansa ne ya ƙara faɗuwa ,da sauri ya karasa gurin nanny yana kallonta,"nanny Ina Hulwa?"ya faɗa cikin muryar damuwa.
Kallonsa nanny tayi itama da alamun damuwa akan fuskarta tace " to magajin fada,nan da ka ganmu wllh ita muke nema,naje gurin taron can kenan,na barta tana barci,kuma ina dawowa naga bata É—akin,na duba ko ina cikin bangaren nan banganta ba,saiga tareeÆ™ kuma yana tambayar ko Rashad ya shigo nan"
Da sauri Adeeb ya nufi ɗakin da fattu ke zaune gabansa naci gaba da bugawa da ƙarfi.
Ko ina ya duba amma bata nan,to ina taje?yasan dai ba yawo takeyi ba ,ba inda ta sani cikin fadar nan,ko part É—in sa ma sau É—aya ya kaita,da sauri ya juyo yana kallon tareeÆ™," Ina Rashad yayi?"ya tambayi tareeÆ™ cikin wata irin murya mai kama da ta basawa.
"Yallaɓai ina zaune naga lokacin da Rashad ke waya,kuma saiya fito waje,hankalina bai kwanta da fitowar sa ba,dan haka saina biyoshi,ina fitowa na hangesu shida Zulaihat,dan haka na buya ina sauraron me zasuce,yallaɓai amma banji me suke tattaunawa ba,saidai ga dukkan alamu akwai abunda suka ƙulla tare, sai dai kuma basu sami jituwa ba,dan kuwa cikin fushi suka rabu.
Nayi ƙoƙarin bin Rashad Dan ganin inda ya nufa amma ban ganshi ba" tareeƙ ya faɗa yana kallon Adeeb cikin damuwa.
Dafe kai Adeeb yayi zuciyarsa na masa zafi,lallai idan har wani abu Rashad ke ƙoƙarin aikatawa akan Hulwa ,to zai gane kurensa wllh azeem,saiya ɗanɗani kudarsa.
Cikin sauri Adeeb ya nufi ƙofar fita daga part ɗin,tareeƙ ya na biye dashi,ganin zasu fice yasa nanny tayi saurin bin bayansu dan bazata iya zama ba.
Suna fita daga part din, kai tsaye Adeeb part din ammi ya nufa,ko fattu can ta tafi,saidai suna gab da shiga ya tsinkayi Muryar ammi na kiran sa,tsayawa yayi harta ƙaraso,"lafiya na ganku haka afujajan?gashi ka bar gurin taro ba'atashi ba?"ammi ta faɗa tana karantar yanayin Adeeb.
Ahankali Adeeb ya sauke wata ajiyar zuciya mai zafi,tare da lumshe idanu kana yace "ammi mun rasa inda yarinyar nan tayi ne ,shine zamu duba ko tana party É—inki" Adeeb ya faÉ—a cikin yamutsar fuska kamar zaiyi kuka.
"Hmmmmm ji dan Allah wai akan wannan Shegiyar yarinyar suka tada hankalinsu haka,dan kawai basu ganta ba.
Tukunnama wllh sai kunga yadda rayuwarta ta koma yanzu,dan nasan Rashad ya kammala aikinsa"ammi ta faÉ—a cikin zuciyarta,amma azahiri,
Cikin hanzari ta riƙo hannun Adeeb tana mai zaro ido." Ikon Allah ina kuma ta nufa?dan gaskiya bata part ɗina, sai dai kuma ɗazu naga Rashad yana shawagi tsakanin part ɗina Dana nanny,Allah yasa bashine yayi mata wani abu ba" cewar ammi tana mai dafe kai cikin nuna tsantsar tashin hankali.
Gaban Adeeb ne ya fadi ,shikenan dama yasan hakan zata iya kasancewa, dan kuwa sam yau bai yarda da Rashad ba dama ,"innalillahi "Adeeb ya faÉ—a cikin ruÉ—u da tashin hankali.
Da sauri ya kunna kansa cikin part É—in na ammi,suka rufa masa baya.
Saidai nan ma sunyi iya bincike su amma bata nan,wasa -wasa fa sune har part É—in Rashad Amma bashi ba Hulwa,zuwa wannan lokacin Adeeb ya shiga tsantsar tashin hankalin da bazai misaltuba,gaba É—aya fuskarsa tayi jaaa kamar manja, idanunsa sun koma kala kalan nan,idan ya buÉ—e baki har wani turiri zakaga yana fitowa daga bakin nasa.
Hankali kowa ya tashi,tsakanin ammi ,tareeÆ™ ,nanny dakuma amma ,wacce ta tsincesu abangaren Rashad,Dan itama nemansa tayi ta rasa agurin taron,shine tazo dubawa ko part É—in sa ya dawo.
Sai kuma ta riskesu suna dubansa.sosai tashiga tashin hankali,karfa Rashad ya janyo mata wata sabuwar matsalar,amma tasan ma bai zama lallai abinda suke zargi ya kasance ba.
Cikin wani irin voice Adeeb ya juyo yana kallon amma tare da fara magana " wllh !wllh!!wllh!!! idan wani abu ya sami hulwa ta silar ɗank,i nayi alƙawarin saina illatashi,ta yadda ke kanki bazaki so ganinsa ba" Adeeb ya faɗa yana mai nuna amma da ɗan yatsanshi, tsabar masifa da bala'i kumatunsa har rawa suke.
Cikin tsoro amma ta ja baya tana mai dafe ƙirjinta ,dan kuwa ta tsorata da yanayin na Adeeb,tana kuma fatan Allah yasa ba hannun Rashad aɓatan fattu.
Can kuwa wajen taro ,anyi addu'oi,kuma anci ansha taro ya tashi lafita,abie yana ta tunanin ina iyalin nashi suka nufa ,dan baiga kowa agurin taron ba,zuciyarsa na raya masa akwai Abinda ke faruwa ,dan haka kai tsaye bayan ya sallami baƙinsa ya nufi bangaren sa ,jakadiyarsa ya tura cikin gida dan ta gano masa ko lafiya.
Adeeb yana gama korawa ammi warning yayi waje cikin zazzafar zuciya da jin jikinsa yana masa wani irin rawa,idanunsa gaba ɗaya ya rine zuwa kalar na macizai.tsoro sosai ya kama su ammi da nanny,hatta tareeƙ atsorace yake,dan bai taba ganin yallaɓan nashi cikin wannan yanayin ba.
Part ɗin sa ya nufa kai tsaye,saidai yana zuwa saitin ɗaya part ɗin na ,ammi yaji zuciyarsa ta tsananta da bugawa ,cak yaja ya tsaya tare da ƙure ƙofar part ɗin da idanunsa.zuciyarsa na raya masa ya shiga ya duba,saidai yana tunanin ammi bata fiye amfani da bangaren nan ba ,kuma me zai kawo Rashad nan ma ?
Idan kuma yazo nan ɗin da Hulwa dan kawar da tunaninka fa ?ɗayar zuciyar ta bashi amsa.dan haka ba bata lokaci ya kama handle ɗin kofar ya murza da zummar shiga,saidai kuma akulle yaji ƙofar ,hakan ya matukar bashi mamaki,dan kuwa kullum part din nan abuɗe yake ,koda ammi bata ciki akwai hadimai acikinsa.amma how comes yau zai kasance akulle haka.nan take zuciyarsa ta bashi lallai Hulwa na cikin part ɗin nan.daidai lokacin su ammi suka ƙara so gurin.kallon tareeƙ yayi cikin wata irin murya yace " na tabbata Hulwa na cikin nan,saidai ina mamakin yadda part ɗin ya kasance akulle karon farko" ya faɗa yana kallon ammi,wacce tayi wiƙi -wiƙi tsoro ya ɗan bayyana akan fuskarta.
Dan kuwa Adeeb ya kafeta da mayun idanunsa.sam ba zargin ta yake ba,kawai yana tunanin yadda aka yaudareta ne itama har akayi amfani da part É—inta.dan baya raba É—aya biyu cewar Rashad na cikin part É—in.
Cikin in-ina ammi tace "habeebe a.a.a...k.wai spy ..kk...eyy " ta faÉ—a cikin jan numfashi.
Kallonta tareeÆ™ yayi cike da zargi,dan shikam harga Allah tun farko ita ya zarga dan yasan bakin nufin ta akan abun daya shafi Adeeb sarai.
Amma ma kallon ammi take cike da tuhuma,karfa tuggu ta haÉ—awa Rashad Dan kawai tana son ganin bayanta?
" Wai wannan wane irin wandone kika sa ?kusan minti nawa ina ƙoƙarin cirewa amma na kasa?wllh idan ma wani siddabarun kikayiwa wandon nan yaƙi fita,to zanyi abuna ahaka, dan ubanki yau ɗin nan nayi alƙawarin ,sai Adeeb yayi kwanan baƙin ciki "Rashad ya faɗa yana hankaɗa fattu kan wani ƙaton tebur dake ajiye gefen gado ,da alama an ajiyeshine ɗan ɗora kofuna ko abinci idan bukatar hakan ta taso.
Aikuwa tana fadawa ta fada kan wani glass cup, nan da nan ya tarwatse gaba ɗaya ya sossoketa aƙirjinta da wuyanta.wani marayan ƙara fattu ta sanya ,wanda koshi Rashad baiji sautin ƙaranba, dan kuwa muryarta tayi mugun dashewa.ahankali idanunta ke lumshewa yana budewa,gaba ɗaya jini ya bata farar best ɗin dake jikinta.amma bako imani bare tausayi haka Rashad yake ƙoƙarin keta mata haddi, ba tare da ya cire koda wannan skin tite ɗin ba.
Wata irin zabura Rashad yayi sakamakon ƙaran da fattu ta kwalla,wanda yayi daidai da ƙarar faduwar kofar dakin .
â€RASHAD!!!!!!............"
Aka kwallah kiran sunan Rashad Wanda saida Rashad É—in ya buge kansa ajikin tebur É—in nan tsabar razana da yayi da wannan kiran sunan nashi da akayi......
Hmmmmm masu karatu,nima tsabar tsoro bansan sanda wayar hannuna ta fadi kasa ba,mutara zuwa gobe idan na É—auki wayar .fatana dai wayata bata fashe ba.
Mrs babi ce💘💘
Share and comment fisabilillah
More comment
More typing.
29/08/2022, 11:05 am - Khadijah Salisu Fari: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄
MACIJI NE 🪱🪱🪱
Na mammy kabeer
(Anty mammy)
Elegant online writers📚📚
Free book
Page 55/56
_________________"RASHAAADDDD"
Aka kwallah kiran sunan Rashad,Wanda saida ɗakin ya amsa.gaba dayan mutanen da suka shigo ɗakin saida suka tsorata ,saboda yadda amon Muryar ya fito da mugun ƙarfi da sauti mai firgitarwa.
Ahankali fattu da ke neman macewa ta buɗe kunburarrun idanunta da gyar,ta saukesu akan fuskar hammanta, wata shashshekar kukace ta zo mata ,numfashinta na hawa da sauƙa ,da gyar ta daga hannunta tana mikawa Adeeb ,
Da wani irin mugun sauri Adeeb yayi kanta yana mika mata nashi hannu,saidai kafin ya ƙara so tuni hannun nata ya koma ƙasa sharaff!! Ahankali kuma idanunta suka kulle ,duk wata jijiya dake jikinta tasaki,ataƙaice dai fattu ta sume.
Wani irin ƙara Adeeb ya kwalla mai matukar firgitarwa ,hayaƙi na fita ta bakinsa da hancinsa, hannun fattu ya kama ya riƙe cikin nashi tare da damkewa kamar zai balla hannun nata.
Jikinsa gaba É—aya rawa yake kamar ana kaÉ—a masa gangi,É—ago da kansa yayi afusace ya sauke idanunsa akan Rashad,Wanda tsabar tsoro ya kasa koda matsawa daga kan table É—in gashi tsirara haihuwar uwarsa.
Da sauri Rashad ya runtse idanunsa,numfashinsa na wani irin hawa da sauka kamar shima zai shide tsabar tsoron ganin yadda idanun Adeeb ya koma,ga wani irin bakin hayaƙi daya fara cika ɗakin,
Wani ƙaran Adeeb ya sake kwalla,wanda yafi na farko sanya tsoro da razani,gaba ɗaya dakin yayi wani irin bakiƙirin ,baka ko ganin hannunka bare na kusa dakai.
Su ammi da amma,nanny tareeÆ™ ,jakadiya,da Zulaihat wacce zuwan ta kenan,bangaren dan ta sami labari gurin yan s.i.d É—inta.gaba daya tsoro ,firgici da tsantsar mamakin abinda ke faruwa yasa sun kasa koda motsine agurin ,bare suyi wani abu.
Sun ƙanƙame juna jikinsu yana wani irin bari,nanny Banda sunan Allah ba abinda take ambata"innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, meye wannan ke shirin faruwa haka,tareeƙ kana ina bana ganin komai fa " nanny ta faɗa tana ƙanƙame tareek dake kusa da ita.
Shi kansa tareeÆ™ jikinsa rawa yake ,sam ya kasa magana sai rungume mahaifiyarsa da yayi sosai ajikinsa.
Ƙaran rashad ne ya karaɗe dakin ,cikin wani irin sauti na azaba,wanda kana jinsa kasan wanda ke wannan karan yana cikin azaba da halin ƙunci.
Kuka kawai amma ta sanya ,dan tasan yau kam É—an ta sai abinda hali yayi,shikenan yau abinda ake shukawa agidan ya dawo kansu.
Ahankali É—akin ya fara washewa daga tsantsar duhun da yayi ,kusan minti uku suna cikin halin tsoro da razani kafin ,suka fara ganin komai tar-tar .
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un"shine abinda Dukansu suka haÉ—a baki wajen faÉ—a,sakamakon ganin wani narkeken maciji mai girman gaske nannade da Rashad ,Wanda kallo É—aya zakayiwa Rashad kasan cewa ba alamun numfashi atare dashi.
Kallon kallo ake tsakanin mutanen dake cikin dakin,wanda suka shiga tashin hankali fiye dana farko,dan kuwa ba Adeeb aÉ—akin sai wannan narkeken macijin,wato dai Adeeb shine ya zama wannan macijin.
Jikin nanny Banda rawa ba abinda yake ,haka ammi da amma,jakadiya da Zulaihat wacce tuni ta jiƙa jikinta da fitsari,tana tsaye ƙanƙame da amma wacce itama ta ƙanƙame Zulaihat ɗin.
Sun kasa magana sai kallon ikon Allah suke.
Macijin nan yana tsaye nannade da Rashad ya fasa kai yana wani irin huci da fesar da wani irin bakin abu daga bakinsa.juyi ya farayi da ƙarfi kafin ya maka rashad ajikin bango,ji kake timmmm!!Rashad ya baje akasan tyles,tuni jini ya fara zubowa daga kansa.hakan bai ishi macijin nan ba ya kara zuwa ya nannade Rashad tare da kara makashi jikin bango.
Ihu suka farayi ganin macijin nan na ƙoƙarin tarwatsa kasusuwan Rashad.
Da gudu jakadiya ta juya tayi waje tana ihu ,ta nufi part É—in mai martaba,tana faÉ—uwa tana mikewa,gaba É—aya bata cikin hayyacinta.
Zulaihat ma silalewa tayi agun ba alamun numfashi atare da ita.
"Wayyo jama'a ku taimaka min ,zai kashemin yarona,wayyo Allah na na shiga uku ku taimaka min"amma ta faɗa cikin ficewar hayyaci,dan tsabar tsoro gadan gadan take nufar cikin dakin gurin da Rashad ke kwance ayashe, aikuwa kafin ta ƙarasa kaiwa inda Rashad ke kwance, saijin wani abu tayi mai kama da bulala ya fyadeta a gadon bayanta,wani ihu amma ta kurma tare da faduwa sakamakon azabar raɗaɗin da taji gadon bayanta ya ɗauka.da rarrafe ta koma inda take tsaye. Jikinta na rawa .
Ammi fa tsoro ya gama kasheta,dan ko tsayuwar kirki ta kasayi, sam batayi tsammanin haka abin yake ba,ashe dai da gaske mutum yana iya komawa wata halittar ta hanyar asiri?lallai yau taga abinda ya fi ƙarfinta , sam bata tsammaci abun haka yake ba, amma dole tayi wani abu dan gudun zargi.dan haka cikin bugawar zuciya da tsananin tsoro ta fara takawa zuwa gurin da Adeeb ke tsaye yana zagaya Rashad yana huci.
"A...a.ddd..ee.e.bbb."ammi ta kira sunansa cikin tsinkewar numfashi, shikuwa baiko kalli inda take ba ,burinsa kawai yaga Rashad yayi motsi ya kara karairaya masa inda bai gama lalacewa ba.
"Ka nutsu Adeeb É—ana,.n...i.cce ammin ...ka, ka ...ka...ji."ta faÉ—a tana matsawa cikin tsoro da firgici.
Ai kuwa jin takunta da adeeb yayi ,afusace ya juyo tare da kai mata tsafka, cikin sa'a kuwa ya damketa,ihu ta farayi tana neman taimako,"wayyo Allah na taimako jama'a taimako"ammi ta faÉ—a lokacin da Adeeb ke nannaÉ—eta kamar buhun goro.saida yagama naÉ—eta sannan ya fasa kansa saitin fuskar ammi yana huci.tsabar firgici tuni ammi ta sume ,kura mata ido Adeeb yayi kafin ya fara dakinta ahankali ,ta faÉ—a kan gado.
Gurin fattu ya koma tare da hawa gadon bayanta, nade ta yayi tare da mirgina ta ta juyo rigingine,kallon fuskarta yake wani irin farin Ruwa na zubowa daga idanunsa ,kwanciya yayi akan cikinta yayi lamo yana mai juya kansa ,tare da yin wani irin ƙara yana bude bakinsa.
Al'amarin yayi matuƙar tsorata dukkan wadanda ke cikin dakin,dan nanny ma tuni ta sume ,amma ce kawai mai ƙarfin hali ,dan tana zaune riƙe da bayanta da tasha bulala.
TareeÆ™ kuwa hawayene ke zuba daga idanunsa.yana matukar tausayawa yallabai É—in nasa.
Ana cikin wannan halin ne,abie ya shigo dakin tare da waziri da manyan faɗa ,sai Shaikh lateef ,babban malamine dake koyar da ilimin addini sannan masani akan abinda ya shafi jinya da maganinta, ya ƙware sosai wajen magance abun daya shafi sihiri.
Lokacin da jakadiya ta kaiwa abie labarin,shikuma suna tare da su waziri suna É—an tattauna wata magana mai muhimmanci,shine suka garzayo gaba É—ayansu, É—an ganin abinda ke faruwa.
Ba ƙaramin kaɗuwa abie yayi ba,lokacin da ya wannan kumurcin macijin amatsayin Adeeb ɗinsa,hawaye ne kawai ke zuba cikin idanunsa, ya ƙurawa Adeeb ɗin ido.tunanni kawai yake ,waye wanda yayiwa adeeb wannan aika -aikar?me yatsarewa wanda yayi masa haka?ace yaro mai gata dan sarauta kamar Adeeb yana zama maciji?duk yadda Adeeb ya kasance mai tausayi da taimakon al'umma ,amma ashe wasu suna can suna shirya masa mugunta.lallai dole ya tsaya tsayin daka ,wajen bawa yaronsa abin sonsa kariya ta ko wacce siga.yasan ammi na ƙoƙarin wajen yiwa adeeb addu'a ,kuma tana sawa ayi masa kamar yadda take faɗa amma dole shima ya dage ta bangarensa.
Abie ne ya kalli Shaikh lateef,cikin damuwa da zubar hawaye yace "Shaikh kaga Adeeb ga ,kaga halin da yake ciki,menene abinyi ?abie ya faÉ—a yana mai share kwalla.
Shaikh lateef kuwa wanda tun shigowar su yake kallon Adeeb,kallo na tsinake,sai lokacin yayi ajiyar zuciya kana ya kalli abie,yace" ranka shi daɗe lallai Adeeb yana cikin tsaka mai wuya ,da tuggun maƙiya ,amma In Sha Allah komai yazo ƙarshe,yanzu dai ayi ƙoƙarin diban bayin Allah dake kwance dan akaisu ga likita,sannan sai musan abinda ya kamata muyi"Shaikh lateef ya faɗa yana mai kallon abie.
Nan da nan kuwa aka kwashe su ammi da nanny,Zulaihat ,sai dai ko yaya akayi yunƙirin zuwa inda Rashad ke wance kamar gawa,take macijin nan zaiyo kan mutum afusace.
Ganin haka ya sanya abie cikin ƙarfin hali ya tunkari Adeeb dake fagen fattu yana fasa kai,ya kasa ya tsare,
Ahankali abie ke kallon Adeeb da idanuwansa masu fidda hawaye kafin yace"habeebee kayi hakuri adauke dan uwanda,dan asuba lafiyarsa, koma me yayi maka nine nan,zan ɗaukar maka mataki,bazan taɓa yarda da zalunci ba"Abie ya faɗa cikin sanyin murya yana kallon Adeeb.
Huci kawai Adeeb keyi yana kallon Abie kafin ya maida kansa ga fattu yana kallonta,sannna ya É—ago kai ya kalli abie,
Jinjina kai abie yayi cike da fahimtar Adeeb ɗin yace "na fahimta habeebee,dole zan ramawa yarinyar nan abinda rashad yayi mata,dan kasan ba'a zalumci amasarautata" abie ya faɗa yana mai ƙara sawa kusa da Adeeb ɗin ahankali ya sanya hannunsa yana shafa bayan Adeeb.
Shikuwa Adeeb sai huci yake yana guri da wata iska mai matukar zafi.haka aka samu aka lulluɓawa Rashad Abu ajikinsa kafin kayi waje dashi, amma duk yadda akayi ƙoƙarin ɗauke fattu Adeeb ya hana ,dan hatta mai martaba ,da yayi yunƙurin daukar ta saida Adeeb ya kai masa tsafka.haka suna ji suna gani ba yadda suka iya,sai lulluɓe mata jiki da sukayi itama ,dan kuwa yaƙi barin jikinta ma.
Shaikh lateef ne zaune gaban Adeeb yana karanto wasu addu'oi yana tofa masa,lokaci guda jikin Adeeb yayi laushi, gaba ɗaya baya ko kwakwkwaran motsi,sai huci da yake fiddawa ,ya dora kansa akan ruwan cikin fattu dake lulluɓe,jikinsa sai wani bakin hayaƙi ke fita.
Ci gaba Shaikh lateef yayi da addu'ar sa yana tofawa Adeeb,yayin da su abie ke gefe guda suna kallon ikon , Allah,dan zuwa lokacin murƙususu kawai macijin nan keyi,kafin wannan hayaƙin ya turnuke dakin,baka iya ganin komai tsabar duhu.
Su abie suma addu'a suka fara,lokacin da suka ga wanan hayaƙin,dan Shaikh lateef yace karsuji tsoron komai ,duk abinda zasu gani kawai suyi addu'a.
Can kusan wucewar mintuna biyar suna ta addu'oi ,dakin ya fara haske yana washewa har ya gama washewa tar, kamar ba shine yayi wannan duhun ba.
Adeeb ne durƙushe agaban wannan table ɗin da fattu ke kwance,kansa har lokacin yana kan cikin fattu.
Hamdala Abie da su waziri sukayi,ganin Adeeb ya dawo asalin halittarsa, dan abie yayi matuƙar tsorata, kar ace ahaka Adeeb ɗin zai zauna.
Ahankali Adeeb ke buÉ—e idanunsa ,da har zuwa lokacin basu gama komawa normal ba.
Kanshi ya daga da gyar yana É—an yatsine fuska tare da dafe kan,dan ciwo yake masa sosai.
Sai kuma yayi saurin zabura ya mike tsaye "Hulwa" shine abinda ya faÉ—a cikin daga murya yana waige waige,
" Habeebee ka nutsu kaji ga hulwar taka nan kusa da kai "abie ya faÉ—a yana mai mikewa shima tare da riko kafadun Adeeb.
Sai lokacin Adeeb ya ga su abie aÉ—akin,kallon abie yayi kafin ya kalli inda abie ke nuna masa,zaro ido yayi ganin hulwarsa kwance kamar gawa,"Hulwa " Adeeb ya faÉ—a yana mai girgiza fattu,amma ina Hulwa tayi nisan zango.
Janyota yayi zuwa jikinsa ya rungumeta tare da fashewa da wani irin kuka mai tsanani ciwo da zafi.irin kukan da Adeeb keyi kaÉ—ai zai fahimtar da kai yadda yake jin Hulwa da kuma ciwo acikin ransa.
"Rashad !
Rashad !!
Rashadddd!!!ka tabka babban kurkuren ƙoƙarin tabamin mata,kayi kurkure,idan Hulwa ta mutu"yayi shiru yana mai goge hawayen dake kwatanta cikin idanunsa,kafin ya ɗago idanunsa da suka yi wani irin mugun jaaa,ya kalli Abie sannan yaci gaba"wllh billahi,saina kashe Rashad ,idan har matata ma mutu sanadin sa"Adeeb ya faɗa cikin karfafa murya da nuna gaskiyar abinda yake fadi har cikin ransa.
Kallonsa kowa keyi acikin É—akin,dan kuwa sun zama speechless,matarsa yake ta kira,kodai yarinyar nan amatsayin matarsa take?ko kuma yana nufin ita zai aura?
Shine abinda yake ta yawo cikin zukatan su Abie.
"Ya kamata akai yarinyar asibiti yanzu,nikuma zanje gida domin yin bincike akan larurar prince ranka shi dade"cewar Shaikh lateef yana mai mikewa tare da shafa kan Adeeb,dan yana tausayawa yaron sosai.
" Haka ne Shaikh bari akaita asibiti yanzun nan " cewar abie yana mai kallon Adeeb dake ƙankame da Hulwa kamar zai maidata cikinsa.
Kafin su ankara tuni Adeeb ya sungumi fattu yayi hanyar barin dakin da ita." Habeebee kayi hakuri akai yarinyar asibiti,kaima fa ba cikakkiyar lafiya gareka ba" cewar abie kenan ,ganin Adeeb na ƙoƙarin ficewa daga ɗakin.
" Ba wanda zai kara tabamin mata abie ,domin itaɗin mallakina ce mata tace ta Sunnah,hakkin kula da ita yana kaina,dan haka bana bukatar taimakon kowa,karka manta ,likitanci bangarenane" yana faɗin haka yayi waje da fattu rungume aƙirjinsa.
Kai tsaye fart ɗinsa ya nufa da fattu ,yana zuwa ya shimfiɗeta akan lafiyayyen gadonsa, kallo yabi jikinta dashi,cikin wani irin zafi da ƙunar zuciya,gaba ɗaya glasses sun maƙale ajikinta ,jini duk ya bata mata jiki.hatta fuskarta baka ganewa.
Gimbiya suhaimat ce tsaye tana bin Adeeb da kallon sabe da yarinya akafadunsa,haka kawai gabanta ke tsananin bugawa,so kawai take taga yarinyar,
Ko menene ya sameta oho?ahankali ta juya taci gaba da tafi zuwa dakin ammi,dan su basu san abinda ke faruwa ba.
Zuciyarta gaba É—aya taki samun nutsuwa ,ba abinda take son gani sama da wannan yarinyar,gaskiya bazata iya jurewa ba dole taje taga yarinyar,sannan ta san meke damunta?me yasame haka gaba É—aya jikinta jini...
Masu karatu ku biyoni dan jin gimbiya suhaimat zata je ganin fattu ne ko yaya?
Taku anty mammy
Mrs babi 💘💘
Share and comment fisabilillah.
More comment more typing
29/08/2022, 11:05 am - Khadijah Salisu Fari: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄
MACIJI NE 🪱🪱🪱
Na mammy kabeer
(Anty mammy)
Elegant online writers📚📚
Free book
Page 57/58
________________Gimbiya suhaimat ta gama tsara cewa data huta zataje part É—in Adeeb dan ganin yarinyar nan,
Saidai shigarta part ɗin ammi da yanayin da taga ammin yasa ta saurin,ƙarasawa cikin dakin ,cikin damuwa take faɗin"ukktee meke damunki? Yana ganki akwance?gimbiya suhaimat ta faɗa tana kamo hannun ammi ,wanda ba'a daura mata ruwa ajikinsa ba.
Ahankali ammi wacce tayi nisa cikin tunani ta buÉ—e idonta tana kallon gimbiya suhaimat,kafin ta sauke ajiyar zuciya tare da lumshe ido ta buÉ—e" ke dai bari suhaimat,yau naga abinda ban taba gani ba arayuwata,nan ta bata labarin abinda ya faru,saidai ta boye mata asalin labarin fattu,sai cewa tayi wata baiwa ce Rashad É—in yayiwa fyade,dan ita atunanninta Rashad yayiwa fattu fyaÉ—en.
Sosai gimbiya suhaimat ta tausayawa yarinyar,sannan tayi Allah wadai da halin Rashad,zuciyarta na tsananin bugawa ,har cikin ranta take jin tausayin yarinya.kuma tayi alwashin ,saitaje taga yarinyar nan kafin ta bar ƙasar.
Rashad kuwa kai tsaye aka wuce dashi,lafiyayyen asibitin dake masarautar,emergency akayi dashi,cikin gaggawa likitoci suka duƙufa akansa dan ceto rayuwarsa.
Dan da dama cikin likitocin , sunyi tunanin hatsari ya samu mai muni.
Karon farko ruwa suka fara É—auka masa,kafin suka fara bincikarsa,karayama kusan biyar ce ajikinsa, bayan munanan raunuka dake jikin sa,sannan since kansa ya bugu ,dole sai sunyi bincike akwakwalwarsa, dan tabbatar da lafiyarta.
Amma kuka take sosai cike da tarin damuwa da baƙin ciki ,meyasa Rashad zaiyi mata haka?me yasa gaba ɗaya halayyar Rashad ta sauya ne?da ɗan ta mai hankaline da nutsuwa ,sannan yana bin maganarta,amma daga baya ya fandare ya zama gagararre,yanzu ga irin abinda ya jama kansa.karaya har biyar ajikin mutum.Nan dai taci kukanta ta ƙoshi,tana zaune gefen ɗan ta.
Nanny ma ta farfaÉ—o ,hankalinta amatukar tashe ,tana zaune hawaye na zuba cikin idanunta,yayin da tareeÆ™ ke rarrashinta cikin kwantar da murya.
"Kayya tareeƙ abinnan na magajin faɗa,ya isheni yaron nan tun yana ƙuruciya yake haɗuwa da tuggun maƙiya,har zuwa girmansa,yaushe ne zai sami salama shima,kadufa wai Adeeb ne ya zama wannan ƙaton macijin,wanda idan awani gurin ka ganshi,sai inda ƙarfi ka ya ƙare wajen ceto rayuwarka.
Yanzu idan haka ta faru dashi awani gurin yunkurin kasheshi fa zasu yi"nanny ta ƙarasa cikin kuka tana fyace majina.
Hannunta tareeƙ ya kara damƙewa cikin nashi,kafin yace " wai ummeee yaushe zasu sanar da gaskiyar da muka jima da sanine?yaushe zamu taimakawa yallaɓai mu haska masa hanya danya gane irin haɗari dake bibiyarsa arayuwa?na gaji da boye gaskiya ummeee kiyi wani abu"tareeƙ ya faɗa cikin damuwa.
"TareeÆ™ baka san masarautar ya take ba,idan baka iya kama É“arawoba ,to shi zai kama ka,dole mubi komai asannu,akwai lokacin bayyana gaskiya kaji?kayi hakuri"nanny ta faÉ—a tana mai shafa kan É—an nata.
Yanzu ya jikin ɗiyata yake ?shikenan yanzu yaron nan ya lalata nata rayuwa?ya karbi budurcinta awulaƙance sannan tana cikin al'ada ?kai ban taba ganin fajiri irin Rashad ba,Allah ya saka miki ɗiyata"nanny ta faɗa cikin kuka sosai,tana tausayawa fattu.
TareeÆ™ ma runtse ido yayi zuciyarsa na masa zafi,dan kuwa yasan ahalin yanzu Adeeb yana can cikin bakin ciki da damuwa,saidai shikam yana ganin kamar Rashad É—in bai sami damar yiwa fattu fyaÉ—en ba suka karaso, yana kuma fatan Allah yasa hasashensa yazama gaskiya.
Akan gado Adeeb ya shimfida fattu,wacce ke kwance kamar gawa,bata ko motsi,gaba ɗaya jini ya wanke mata fuska,jikinta ko ina raunine ,dan kuwa ba ƙaramin azaba Rashad ya gana mata ba,lips ɗin ta sun bushe idanunta ya kumbura sosai.
Runtse ido Adeeb yayi lokacin da idanunsa suka sauka kan wuyanta zuwa ƙirjinta ,fasassun kwalabe duk sun soketa, zama yayi abakin gadon,cikin wata irin karaya da zafin zuciya.ji yake kamar yaje ya kama Rashad yayi gutsin-gutsin dashi,
Hannunta ya kama na dama ,ya riƙe cikin nashi,gam-gam .jikinsa sai rawa yake ,yama kasa aikata komai akanta.wai hulwarsace kwance agabansa kamar gawa.
"Why Rashad ?why ?duk matan dake cikin fadar nan sai matata?me yasa zaka aikata haka agareni?Adeeb ya faÉ—a afili yana mai kaiwa bango naushi, ji yake kamar zuciyarsa zata kama da wuta.
Da sauri ya mike tare da É—auko first aid box É—insa, dan Adeeb cikakken likitane akan fannin lafiya yayi karatunsa .
Farar vest ɗin fattu data yage kaɗan daga sama ya kama,wacce ta rine da jini, ya cire mata ahankali,nan da nan albarkatun ƙirjinta suka bayyana,cikin faduwar gaba Adeeb ya kawar da kansa ga barin kallonsu,zuciyarsa na ci gaba da bugawa. haka ma ya zare wannan dogon wando dake jikinta ya ajiye gefe,ya rage daga ita sai pant Wanda shima gaba ɗaya yayi stairs saboda yadda jini ya ɓalle mata ,tsabar yadda ta shiga ruɗu da razani.
Hannun Adeeb karkarwa yake ya kasa aikata komai,dan haka cikin sauri ya janyo ƙaton bargonsa ya lulluɓe fattu dashi,iya saman ƙirjinta zuwa kanta ya bari abuɗe.
Sosai ya tausayawa fattu lokacin da yake cire mata kwalaben nan,dan kuwa taji ciwo da yawa,ko yaya ya taba gurin da kwalbar take saita zabura kamar zata farfaÉ—o.
Haka dai ya gama cire mata kwalaben nan,tas yayi mata dressing É—in duk inda ya kamata, ya sami ruwan zafi da towel ya goge mata jikinta .sai dai kuma ba wani kayan da pant da kuma pad É—in dazai canja mata.
Dan haka rigarsa ya ɗauko fara ƙal ,doguwar ya zura mata, kafin ya dauko mata kayanta,dan kuwa yana tunanin ta dawo nan part ɗinsa da zama kenan. Ƙarin Ruwa ya sanya mata ,kafin ya nufi ƙofa, kai tsaye ya kulle ƙofar ya fita zuciyarsa kamar wuta haka yake jinsa,ya nufi part ɗin nanny.
"Tareeƙ na roƙeka kada kace zaka sanar da magajin faɗa komai ahalin yanzu,dan kuwa bamu da kwararan hujjoji akan hakan ,ka bari nan da lokaci kankanin shida kansa zai gano komai,zamu nuna masa hanya ta yadda zai fahimci abubuwa da dama" nanny ta faɗa tana rike da hannun tareeeƙ.
Umme wllh zuciyata zafi take,Aduk lokacin dana ga yallaɓai cikin wani halin,yana zagaye da maƙiya ,amma bai sani ba,shi yana zaune dasu zuciya ɗaya ....
"Su waye maƙiyan nawa?sannan wace gaskiyar ce ake boyemin?"
Suka tsinkayo Muryar Adeeb yana faÉ—in haka cikin sautin da ba wasa acikinsa.
Da sauri suka juyo gaba É—ayansu, dan basu tsammanci ganin Adeeb É—in awannan lokacin ba.
"Magajin faÉ—a yaushe ka shigo?ya jikin naka?ina É—iyata take ?"nanny ta faÉ—a cikin inda-inda da son n kawar da zancen.
Ƙura mata ido Adeeb yayi cike da tuhuma ,gaba ɗaya ta daburce.da alama akwai abunda take boyewa ita da tareeƙ .kallonsa ya dawo dashi kan tareeƙ wanda kansa ke ƙasa ,shi yaji dadin jinsu da Adeeb yayi,fatansa ɗaya ayi komai yau akare.
"TareeÆ™, what wrong me kuke É“oyemin? Dama akwai Abinda zaka iya boyemin tareeÆ™ ?na dauke tamkar kanina da muka fito ciki daya,why tareeÆ™?" Adeeb ya faÉ—a yana kallon tareeÆ™.
Kallon nanny tareeÆ™ yayi,yana jin ba dadi cikin ransa,dama yasan watarana hakan zata iya faruwa,shi baiga amfanin biye boyen ba , amma suna haÉ—a ido da nanny tayi saurin girgiza masa kai,alamun karya ce komai.
"Tareeeƙ,am tolking to you me kuke hidden mini?kada kusa na fara zarginku fa,Please nanny,bayan ammina da abie, ku kadaine mutanen dana yarda dasu arayuwata,ku kaɗai ne waɗanda nake ganin bazasu taba cutar dani ba,karki karyamin zuciya nanny, Please me kuke ɓoyemin?" Adeeb ya faɗa cikin wata kalar murya mai cike da tsoron kar ace nanny da tareeƙ suma suna daga cikin maƙiyansa .
"Ka kwantar da hankalinka magajin faɗa,wllh har abada bazamu taba cutar da rayuwarka ba,saidai mu bata kariya, amma kasani akwai mutanen da kake kallo matsayin maƙiyanka,saidai sam,ba haka abin yake ba. azahiri kake ganinsu matsayin maƙiya,amma abaɗini sune masoyanka na haƙika.
Su kuma wadanda kake kallo matsayin masoya,suke son ganin bayanka, sune waɗanda suke cin dunduniyarka,Adeeb ka kula kazamo mai lura da mutanen da kake tare dasu " nanny ta faɗa tana mai riƙe da hannun Adeeb,fuskarta ɗauke da damuwa.
Kallonta kawai Adeeb keyi,tunda ta fara maganarta ,me take nufi kenan?su waye ya yarda dasu ,kuma suke cin dunduniyarsa?
Sannan suwaye yake wa kallon maƙiya ,alhalin sune masoyansa na asali?kallon nanny yayi cike da tarin tambayoyi zuciyarsa na harbawa da gudu.
"Nanny ban fahimceki ba,me kike nufi da kalamanki? Please kiyimin bayanin da zan gane"Adeeb ya faÉ—a yana kallon nanny,idanunsa sun kada sunyi jajur dasu.
Ajiyar zuciya nanny ta sauƙe mai ƙarfin gaske,sannan tace magajin faɗa ,idan baka manta ba,shekaru kusan sha takwas mijina da kuma gimbiya nazli sunyi haɗari suka mutu,sanadiyyar wuta data kama motar da suke ciki,harda yaranta mata su biyu,nanny ta faɗa tana kallon Adeeb,
Runtse ido Adeeb yayi da mugun ƙarfi,har abada bazai taba mantawa da wannan baƙar rana ba ,ranar data zamo mafi muni arayuwarsa.
Bude idonsa yayi wanda suka cika da kwalla yana kallon nanny kafin cikin rawar murya yace " tabbas nanny bazan taɓa mantawa da wannan rana ba,domin itace rana mafi muni arayuwata" ya faɗa yana mai lumshe idanunsa hawaye suka ziraro sharrrt.
"To kasani wannan haÉ—arin ba afkuwa yayi ba ,shiryashi akayi" nanny ta faÉ—a tana mai kallon Adeeb ,
Azabure Adeeb ya bude idanunsa,da suka gama zama jajur dasu,kallon nanny yake cikin kiÉ—ima da ruÉ—ewa" nanny kamar ya ban gane ba,me kike nufi da shiryashi akayi?waye ya shirya?kuma meye dalilin shiryawa?"Adeeb ya faÉ—a aruÉ—e.
Kamo hannunsa nanny tayi ta zaunar dashi akan kujera dan kuwa gaba É—aya jikin sa rawa yake.
"Tareeƙ maza jeka kulle mana ƙofar nan"nanny ta faɗa cikin damuwa.
Ahankali tareeƙ ya nufi ƙofar tare da kullewa, yana jin sanyi aransa,koba komai yau zasu sauke nauyin da yayi musu bake bake acikin zuciya.
" Nanny kiyi saurin sanar dani, domin zuciyata gab,take da tarwatsewa,dan kaɗuwa" Adeeb ya faɗa cikin tsantsar zaƙuwa .
Ajiyar zuciya nanny tayi kafin tace " ina son ka saurari maganata da kunnen basira ,sannan kayi min kyakykyawan fahimta,kasani bazan taɓa cutar da kaiba, kuma duk abinda nayi nayine don tsiratar da rayuwarka" nanny ta faɗa hannunta riƙe dana Adeeb.
"Please nanny go street to the point kina kara sani cikin wasi-wasi" Adeeb ya faÉ—a cikin muryar damuwa ,jikinsa na rawa ,ba abinda yake son ji sai wanda ya shirya wanann haÉ—arin.
Mikewa nanny tayi tare da zuwa jikin window ta tsaya ,kallon Adeeb take tare da karantar yanayinsa, kamar yadda shima yake kallonta cike da ƙosawa.
Ahankali ta buÉ—e baki tace"ba kowa bane ya shirya wannan hadarin face ..........
Wayyo masu karatu cajina ya kare ,amma karku damu mu tara anjima,
Nice dai anty mammynku.
Mrs babi💘💘
Share and comment fisabilillah.
More comment
More typing.
29/08/2022, 11:06 am - Khadijah Salisu Fari: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄
MACIJI NE 🪱🪱🪱
Na mammy kabeer
(Anty mammy)
Elegant online writers📚📚
Free book
Page 59/60
________________Ahankali nanny ta ke kallon Adeeb,kafin ta sauke ajiyar zuciya,tunani take ta yadda Adeeb zai karbi wannan magana,ta yaya zata sanar dashi cewar,amminsa itace silar faruwar komai?shin zai amince da abinda zata faÉ—a masa ko yaya? Wane irin kallo zai musu idan yasan cewa amminsa ce ta kashe sarauniya Nazli da yaranta tare da baban tareeÆ™,kuma abakinsu?anya kuwa basu barowa kansu aiki ba?
"Nanny kiyi magana mana kinyi shiru, ki sanar dani wake da hannu akan hadarin nan?"
Da sauri nanny ta dawo daga dogon tunanin data tafi,kallon tareeƙ tayi cike da karayar zuciya ,amma cikin ƙarfafa gwuiwa tareeƙ ya kalli nanny yana mai jinjina kai da nuna alamun ,kwantar da hankali.
Ajiyar zuciya nanny ta sauƙe Tana mai kallon fuskar Adeeb,kafin ta fara magana.
"Magajin fada kamar yadda na faɗa maka,wasu abubuwan muna kallonsu ne ba a yadda suke ba,ka sani abinda zan faɗa maka ba ƙarya ,ba kuma cutarwa.shiru ta ɗanyi tana jinjina maganar kafin taci gaba"ba kowa ya shirya wannan hadarin ba, face Amminka"nanny ta faɗa tana mai kure Adeeb da ido.
Da wani irin slow Adeeb ya mike tsaye bakinsa bude,zuciyarsa na wani irin bugawa kamar guduma, ji yayi kunnensa ya ɗauki wani ƙara ƙuuuuuuuu!!!
Sai yake jin maganar ta nanny Tana rarrabewa,kamar baiji me take faɗi daidai ba,jikinsa rawa ya kama,ta yadda yana mikewa tsayen yaji kamar zai fadi dan haka da sauri ya koma ya zauna,idanunsa ƙuri,akan fuskar nanny,
Cikin in-ina ya ke cewa"na...nan.,...y mek....Ike ..son....f..a...É—..I n..ee." ya faÉ—a numfashinsa na rarrabewa,ji yake kamar zuciyarsa zata fito tsabar yadda take bugawa.
Da sauri nanny ta ƙaraso kusa da Adeeb ta zauna ,cikin nutsuwa take shafa bayansa tare da kallon fuskarsa cikin tausayawa,dole yaji maganar tazo masa kamar saukar aradu."ka nutsu Adeeb domin Abinda nake faɗa maka yana buƙatar nutsuwa,tabbas Amminka itace ta shirya wannan hadari,tare da taimakon wani ma aikaci dake cikin gidan nan,mai kula da harkokin motocin gidan"nanny ta faɗa cikin sanyin murya tana jin zafin rashin mijinta da uwar dakinta kamar yau abin ya faru.
Kallonta Adeeb yake cikin wani irin yanayi na mamaki ,al'ajabi,tsoro,ruɗu dakuma firgici,ji yake kamar zuciyarsa zata iya fashewa ako wane lokaci,wannan wane irin magana nanny keyi?anya kuwa tana cikin hayyacinta?yaushe nanny ta koma maƙiyarsa ta hanyar hade kai da amma?dan su shiga tsakaninsa da amminsa? Dan kuwa yana tabbatar da cewa wannan shirin amma ne,lallai duniya ba tabbas .cikin zuciyarsa yake wannan maganar,kafin a fili ya kalli nanny ,sannan ya kalli tareeƙ,sai kuma yayi murmushi wanda yafi kuka ciwo ,sannan ya miƙe tsaye yana mai sanya hannunsa cikin aljihu,sannan ya fara magana bayan ya juya bayansa yana kallon bango" ban taba tsammanin cewa matar data raineni tun ƙuruciya zata iya hade kai da makiyana,ɗan ganin sun shiga tsakanina da ammina ba ,yau na kara tabbatar da cewa lallai wanda kake kallonsa matsayin masoyi ,to shine makiyinka aboye, amma bantaba tsammanin haka daga gareki ba nanny;Adeeb ya faɗa cikin zazzafar murya yana mai juyowa ,idanunsa sun kada sunyi mugun jaa, kallo ɗaya zaka masa kasan cewa zuciyarsa akaraye take.ci gaba yayi da cewa"nanny why ?why nanny me yasa zaki canja daga yadda na sanki?me yasa zaki so ganina cikin damuwa?na dauke ki tamkar mahaifiyata,duk wani abinda ya dameni ina zuwa gareki dan samun mafita,ammina tana kula dake da duk wani bukatun ki,amma meyasa kika hada kai da maƙiyanta?me yasa kika saida kanki dan bata alaka tsakanin da da mahaifiya?nanny why?tareeƙ me yasa nanny zatayi min haka?Adeeb ya faɗa yana mai riƙe kafadun tareeƙ idanunsa na zubda kwalla ,gaba ɗaya jinsa yake kamar ba shiba, wani sashen na zuciyarsa yana son karbar maganar nanny,saidai sashe mafi rinjaye na zuciyarsa na tunatar dashi wacece ammi agareshi,dan me zai yarda da batun nanny?.
Cikin damuwa da alhini tareeƙ ya kama hannun Adeeb ,cikin murya mai nuna tabbatarwa ,tareeƙ ke fadin, "yallaɓai ka kwantar da hankalinka,kuma kayiwa maganar nanny kyakykyawar fahimta,da sannu zaka gano gaskiyar dake cikin batunta, yallaɓai munsan abubuwa da dama wanda kai baka sansuba,amma da sannu zaka gane da kanka"tareeƙ ya faɗa cikin marairaita yana kallon Adeeb.
Fizge hannunsa Adeeb yayi tare da dafe kansa da yake jinsa kamar zai tarwatse,kafin ya kalli tareeƙ yana mai jinjina kai"well na gane ,na gane tareeƙ kaima kana bin bayan mahaifiyarka ko?da kai aka hada baki,am disappointed tareeƙ" Adeeb ya faɗa yana girgiza kai cikin karayar zuciya,idanunsa na fitar da hawaye mai tsananin zafi da ƙuna.ahankali ya juya ya nufi ƙofa yana dafe kansa .
Cikin damuwa da zubda kwalla nanny ta miƙe da sauri tana kiran Adeeb" magajin fada karkayi saurin yanke hukunci akan maganata kana bukatar nutsuwa da bincike dan Allah ka yarda dani ɗana, bazan taɓa cutar da kaiba."nanny ta fada cikin zubda hawaye .
Ko waiwayowa Adeeb baiyi ba ya fice daga É—akin ,cikin sauri, dan ko ganin fuskar nanny baya sonyi ahalin yanzu.zuciyarsa na tafarfasa ,ji yake kansa kamar zai kama da wuta.kai tsaye part É—in ammi ya nufa ko zai sami salama cikin zuciyarsa.
"Tareeƙ ka gani ko?kaga Abinda nake faɗa maka,Adeeb ya riga ya makance,baya ganin laifin ammi ko kaɗan,yanzu bansan wane kallo zai rinƙa yi mana ba"nanny ta fada cikin kuka.
Kamata tareeƙ yayi ya zaunar da ita akan kujera ,hannunsa ya sanya yana share mata hawayen dake zuba daga idonta,kafin yace " ummee na,ki kwantar da hankalinki,dama shi aikin alheri haka yake,dole saika fuskanci ƙalubale,nasan yallaɓai zaiyi fushinsa na wani lokacin kafin ya sauko,kuma nasan daga yau zai fara bincike akan abinda kika sanar dashi,In Sha Allah muke da nasara ,tunda akan gaskiya muke"tareek ya faɗa cikin yanayin ƙarfafawa mahaifiyar sa gwuiwa.
"In sha Allah tareeÆ™ ,Allah ya datar damu"nanny ta fada tana share hawayenta.
Ameen yace ,kafin suka ci gaba da tattaunawa akan matsalar.
Kai tsaye ya shiga part din na ammi,ko kula gaisauwar da hadimanta keyi baiyi ba,dan zuciyarsa ba abinda take sai tafarfasa,bai taɓa tsammanin haka daga su nanny ba,lallai mutum bashi da tabbas.
Afalo ya ci karo da sarauniya suhaimat,tana zaune da yaranta,suna cin apple da ya'yan itaceya ,gefe guda kuma suna kallo.
Da gudu su zayyad suka taso suka rungume Adeeb suna murnar ganinsa,kansu kawai ya shafa tare da rungumarsu,shima.
Kallonsa sarauniya suhaimat keyi,dan kuwa taga tarin damuwa cikin idanunsa.
"Sannu yarima ,ya jikin naka?dana yarinyar ?"sarauniya suhaimat ta fada cikin yanayi na nuna damuwa .
Lumshe ido Adeeb yayi cikin damuwa da yanayinsa na rashin son magana yace "da sauƙi" atakaice .
"Allah ya bata lafiya " ta fada da yanayi na damuwa.
"Ameen" Adeeb ya faÉ—a ahankali.
"Ammin naka tana ciki"sarauniya suhaimat ta fada cikin kulawa.
Kai kawai Adeeb ya jinjina mata kafin ya wuce zuwa cikin dakin.
" Bangane ba ?kamar ya nayi sakacin da kwalbar ta fashe,bayan irin kulawa da ita da nake?kasan irin kuɗin dana kashe akan akwatin da aka ƙera na sanya kwalbar ciki?
Shiru tayi ,da alama tana sauraron abinda ake faÉ—ane daga can bangaren.
"Shikenan ,yanzu muna cikin alhini ne na wannan abun daya faru,dan haka kajira nan da kwana biyu,zan nemeka,dan awannan karon aiki nakeso ayimin na ban mamaki,bana kuma son asami matsala " ammi ta faÉ—a cikin wani yanayi mai nuna ta shirya mugunta mai zafi cikin ranta.
Gaban Adeeb ne yayi wata irin faɗuwa da har saida ya dafe ƙirjinsa,wane akwati ammi ke magana akai?wace kwalbar ce ta fashe?da wa ammi ke waya?waɗan nan sune tambayoyin da Adeeb ke yiwa kansa,saidai bashi da amsar ko daya daga ciki.
Ganin ammin ta gama wayar kuma tana ƙoƙarin juyowa ne ,dan ta ba ƙofa baya,yasa Adeeb saurin saita kansa yayi sallama tare da shiga.
Da sauri aɗan razane ammi ta juyo tana kallon Adeeb ɗin,dan batayi tsammanin ganinsa yanzu ba, saidai da alama baiji me take faɗi ba,itafa wllh tsoronsa ma ta fara ji yanzu,amma saita maze ta saki murmushi,tare da miƙa masa hannu,alamun ya ƙaraso gareta.
Ahankali Adeeb ke takawa har yaje bakin gadon ya zauna,dan jikinsa sam ba kwari,murmushin ƙarfin hali yayiwa ammi yana kallon fuskarta,
"Habeebee ya jikinka? na tsorata sosai da yanayin dana ganka É—azu"ammi ta faÉ—a tana mai janyo Adeeb zuwa jikinta.
Sam yau Adeeb ji yayi baya wani jin dadin kwanciya akan cinyarta,Dan saiyajisa kamar akan ƙaya, dan haka da sauri ya tashi daga kwanciyar da yayi,kafin ya dan saki murmushi,yana mai cewa"ƙalau nake ammi,kada ki damu,ya naki jikin?"ya faɗa sam fuskarsa ba walwala.
"Shafa kansa tayi kafin tace naji sauki dana karka damu"ta faÉ—a tana kallon fuskarsa ,dan kuwa sam ba haka yake mataba,yau kam ba wannan shaukin da yake nuna mata idan suna tare.
Mikewa yayi yana mai faÉ—in ammi zanje in duba yarinyar can zan dawo anjima" yana faÉ—in haka yayi waje abinsa.
"Yawwa yarima ,ina son in duba yarinyar nan "sarauniya suhaimat ta fada tana mikewa lokacin da Adeeb ya zo zai wuce.
Shiru yayi yana É—an nazari,akwai bukatar ta duba ta ,tunda likita ce itama ,kuma fannin mata ta karanta.
Dan haka yace "ok muje ,tana part É—ina"
Ficewa sukayi tare suka nufi part din Adeeb.
Toh masu karatu ,mubi su Adeeb dan duba Hulwa.
Sai mun hade next page.
Mrs babi ce 💘💘
Share and comment fisabilillah.
More comment
More typing.m
29/08/2022, 11:06 am - Khadijah Salisu Fari: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄
MACIJI NE🪱🪱🪱
Na mammy kabeer
(Anty mammy)
Elegant online writers📚📚
Free book
page 61/62
________________Ficewa sukayi daga part ɗin ammi zuwa na Adeeb, haka kawai gaban sarauniya Nazli ke faduwa,sam ta kasa gane kan wannan faɗuwar gaban nata,saidai kawai ta alaƙa ta hakan da tunanin halin da zata ga yarinyar data sanya tausayi ta cikin zuciyarta.
Su zayyad ma biyo ta sukayi,dan sunce suma son gannin marar lafiyar ,kuma zasuyi wasa agurin uncle Adeeb É—in.
Suna zuwa Adeeb ya dannan lambobin securityn daya sanya lokacin da zai fice,nan take ƙofar ta bude suka shiga.
"Tana cikin daki" Adeeb ya faÉ—a yana kallon sarauniya suhaimat wacce ke tsaye cikin faduwar gaba.
Kallonsa tayi cikin tausayawa, tare da jinjina kai .
sam zuciyarsa Adeeb da jikinsa basa masa daÉ—i, yana cikin matsananciyar damuwa ,abubuwa sunyi masa yawan da har yana rasa me Yakamata yayi.
" Ku zauna anan maza kafin na fito kunji" ta faÉ—a tana shafa kan yaran nata,kafin tabi bayan Adeeb zuwa cikin dakin.
Tana kwance kamar yadda ya barta,ruwan daya É—aura mata ya kusan karewa.
Jiki asanyaye sarauniya suhaimat ta karasa bakin gadon da fattu ke kwance .sosai bugun zuciyar sarauniya suhaimat ya tsananta.
Zama tayi tare da ƙurawa fattu idanu,lokaci guda taji wata masifaffiyar kaunar yarinyar tana ratsa dukkan sannan jikinta,ji take kamar bata taɓa son abu makamancin yadda take jin son yarinyar na shiga lungu da sako na jikinta ba.
Hannun fattu ta kamo tare da riƙewa gam-gam cikin nata,wani sanyi taji yana ratsata lokacin data kama hannun fattun,batare da saninta ba kawai ta rungume hannun fattu aƙirjinta ,tare da runtse idonta.wani irin shauƙi takeji yana shiga jikinta irin na ƙaunar dake tsakanin ɗa da uwa.haƙika takamu da matsananciyar kaunar yarinyar lokaci guda.
Kallon fuskar fattu take bata ko ƙifta idanunta,Adeeb na tsaye agefe guda yana kallonta ,mamakin yadda yaga fuskarta ta nuna so da kaunar fattu yake,koda yake haka Allah ke al'amarinsa.ganin ta kasa cewa komai kawai tana rungume da hannun fattu ta kura mata ido yasa shi sauke ajiyar zuciya yana mai faɗin"anty lafiya kuwa naga kinyi shiru "ya faɗa yana mai kallon fuskar sarauniya suhaimat.
Sai lokacin tadanyi firgigit ta ɗago kai tana kallon Adeeb,ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi kafin tace "wllh Prince haka kawai naji ina kaunar yarinyar har cikin raina ,sosai nake jin tausayinta, yanzu ka dan bamu guri inason na dubawa"ta fada ta na mai shafa kan fattu.
Kallon fattu Adeeb yayi cike da tausayawa,zuciyarsa na masa wani irin É—aci ,kafin ya sauke ajiyar zuciya kana yayi falo gurin su zayyad da yazeed.
Sosai sarauniya suhaimat taji mugun daÉ—i lokacin data gane fattu period ma take,kuma babu alamun Rashad yayi mata wani abu,hamdala tayi ga Allah tana jin zuciyarta wasai, murmushi kwance kan fuskarta take kallon fattu,wacce ta fara dan motsi tana yamutsa fuska.
Hannunta sarauniya suhaimat ta kara riƙewa da kyau tana mai faɗin"princess buɗe idonki ki ,kalleni kinji" tana faɗin haka tana ɗan buga kumatun fattu.
Ahankali fattu ke buɗe idanunta da suka yi wani irin jaaaa kamar jini ya taru a cikinsu,har ta bude idon fess,tare da kafe silin da ido,bata ko ƙiftawa.da alama tana son tuno wani abune, shiru sarauniya suhaimat tayi tana bin idanun fattu da kallo.
Kusan minti É—aya fattu tana kallon silin ,kafin ta zabura tare da kwalla kara tana kokarin tashi,da sauri sarauniya suhaimat ta cire mata karin ruwan dan dama ya kare .
"Wayyo Allah na ,wayyo hammana kazo ka ceceni,zai lalamin rayuwa,wayyo baffana,wayyo innata kizo ,dan Allah ka bari wllh niba yar iska bace karkamin bana so banaso wayyoooooo!!!" Abinda fattu ke faɗa kenan tana fizge -fizge ,dan gani take kamar lokacin Rashad ke ƙoƙarin yi mata fyade,janyota sarauniya suhaimat tayi da sauri ta rungumeta tsam-tsam ajikinta ,cikin mugun tausayinta,tana faɗin"ki nutsu princess ba kowa buɗe idonki ki gani,nice ba Rashad bane ya tafi kiyi shiru ya isa"abinda take faɗi kenan tana shafa kan fattu ,wacce ilahirin jikinta ke rawa ,ta rufe idanunta ƙam -ƙam taƙi budewa.
Da hanzari Adeeb ya ƙaraso cikin dakinz su zayyad ma bishi sukayi da gudu ,jin ihu da fattu ta kwalla,har neman faduwa Adeeb yake tsabar sauri,yana zuwa ya zauna abakin gadon tare da kamo hannun fattu ,da sauri ta fizge hannunta tana mai sakin ƙara ,"ahhhhhh,wayyo ni kasakeni banaso ,wayyo hammana kana ina? wayyo Hamma kazo ka taimakeni" fattu ta faɗa tana kokarin zamewa daga jikin sarauniya suhaimat.
Cike da damuwa Adeeb ya ƙara kamo hannunta ya rike cikin nashi ,duk yadda take ta ƙoƙarin kwace hannun nata,amma yaƙi saki,
"Hulwa ki nutsu kinji ,nine hammanki,buÉ—e ido ki kalleni ,ba Rashad bane nine Hamma" Adeeb ya faÉ—a cikin sanyin murya yana mai shafa kan fattu.
Jin muryarsa da fattu tayi yasata saurin buÉ—e kunburarrrun idantuna ,ta sauke akan fuskar Adeeb,É—an kafeshi tayi da ido,gabanta na faÉ—uwa kamar zai fado kasa.
"Nine ,hammanki ne Hulwa kalleni ki gani ,nine Hamma Adeeb " ya faÉ—a yana É—an matso da fuskarsa saitin Tata.
Ahankali tace "hammana"
"Na'am Hulwa is me "Adeeb ya faÉ—a yana mika mata hannu.
Da sauri ta fada ƙirjinsa tare da fashewa da wani irin kuka,mai matukar ban tausayi,kukane irin na wanda ke cikin tashin hankali kuma ya sami mai taimakonsa.
"Hamma ina kaje ka barni?wannan mai kama da kai É—inne yazo zaiyi min fyade,Hamma dan baki yarda shine yayi ta dukana,ya fasamin baki,ya bugamin kaina ajikin katanga,Hamma bana sonshi,bana son ganinsa ,dan Allah Hamma ka fitar dani daga gidan nan bana so"fattu ta faÉ—a cikin matsanancin kuka muryarta har wani yankewa take kamar numfashinta zai dauke.
Ƙamm ƙamm,Adeeb ya rungumeta ajikinsa,yana jin wani irin zafi akirjinsa, mugun tausayinta ne yake zaga dukkan wata kofa dake jikinsa,haushin kansa ma yake ji,wai me yasa ma ya tafi gurin taron ya barta anan?me yasa bai tafi tare da itaba?
Ahankali yake shafa kanta,yana mai faɗin"am sorry Hulwa,kiyi haƙuri laifinane,dana tafi na barki,na miki alkawarin ba wanda zai sake ƙoda miki kallon banza ne bare hakan ta kara kasancewa,ki yafemin hulwata ,an sorry "ya faɗa yana kara ruƙunkumeta ajikinsa,wasu hawaye Masu zafi suna zirarowa daga idanunsa.
Zuru su zayyad sukayi suna kallon fattu,dan yazeed ma tuni ya fara kuka ,dan shi yana da mugun tausayi.
Sarauniya suhaimat na zaune ta kura musu ido,cikin tausayi take zubda kwalla itama,ji take kamar yarta akayiwa wannan zalumcin ,Allah Sarki Adeeb ya cika dan halak dan ga dukkan alamu yana kula da yarinyar nan,duk da kasancewarta ma aikaciya agidansu,kuma tabbas taga zallar kaunar yarinyar cikin idanun Adeeb.
Sun jima cikin wannan yanayin,har saida Adeeb ya tabbatar Hulwa ta sami nutsuwa ta hanyar daidaiton da yaji bugun zuciyarta yayi,sannan ya rabata da jikinsa.
"Sannu princess hulwar Adeeb"sarauniya suhaimat ta fada ,fuskarta É—auke da murmushi.
Sai lokacin fattu ta juya tana kallonta .rassa!rassa!!rassa!!! gaban fattu ya yanke ya fadi,ƙurrr ,ta kure sarauniya suhaimat da ido,lokaci guda taji ƙaunar matar na ratsata fiye da yadda tayi tunani,duk kunya irin ta fattu,da bata yarda kuyi ta haɗa ido da ita,amma yau kam ta kafe sarauniya suhaimat da ido bata ko ƙiftawa.
Murmushi sarauniya suhaimat take sakarwa fattu,kafin tace" baki sanni ba ko?
Ta fada cikin yanayi na murmushi.
Kamar wata doluwa haka fattu ta daga kai idonta akan fuskar sarauniya suhaimat.
"Daga yau nice innarki ,danaji kina faÉ—i kinji "ta faÉ—a tana mai shafa kan fattu.
Ahankali fattu ta matsa kusa da ita tare da É—ora kanta akan cinyar sarauniya suhaimat tana mai faÉ—in "innata"ahankali tare da lumshe idonta.
Kallonsu kawai Adeeb keyi,zuciyarsa na darsa masa abubuwa da dama,wannan wane irin shakuwace ta lokaci ɗaya?gaba ɗayansu sun kamu da kaunar juna daga haduwar farko,anya ba wani al'amarine mai ƙarfi atsakinsu ba ?.
Hammmmm mudaije zuwa.
"Sannu anty "zayyad ya faÉ—a cikin tausayawa.
Ahankali fattu ta É—ago kai tana kallon yaran masu tsananin kama,
Lokaci guda yaran suka shiga ranta.
Masha Allah kyawawa dasu.
Jinjina kai tayi tana kallonsu cike da kauna.
"Maza kuje falo ko anty zatayi wanka" cewar suhaimat.
Kama hannunsu Adeeb yayi suka fice zuwa falon.
Saida Sarauniya suhaimat ta taimakawa fattu tayi wanka ta gyara mata jikinta sosai,ta bata abinci taci ta sha magunguna sannan ta kwanta barci .kafin ta bar ɗakin akan zata kara dawowa ta duba ta.har ta kai bakin ƙofa fattu ta ce"innata" da sauri sarauniya suhaimat ta juyo ,dan har cikin ranta taji sunan ya shigeta.
"Zaki dawo "fattu ta faÉ—a tana kallonta .
Jinjina kai tayi tana mai yiwa fattu murmushi tace "tabbas zan dawo Æ´ata"murmushi fattu tayi cikin karfin hali tare da rufe idanunta.ba É“ata lokaci barci yayi gaba da ita.dan kuwa harda maganin barci acikin wanda ta sha.
Koda sarauniya suhaimat ta koma bangaren ammi,zaune ta tarar da ammin ta buga uban tagumi,duk sallamar da take sam ammin bata jiba,dan tayi nisa cikin duniyar tunani,saida ta tabata kafin ta san da zuwanta gurin.
"Suhaimat ina kikaje ?na duba baki afalon?
Ammi ta faÉ—a da kokarin kawar da samuwar dake kan fuskarta.
Zama suhaimat tayi susa da ammi tace ,wllh yarinyar nan da abin nan ya faru da ita naje na gani,dan kuwa sosai lamarinta ya tsayamin araina ji nake kamar inada wata alaƙa da yarinyar" suhaimat ta fada tana mai lumshe idonta.
Azabure ammi ta kalli sarauniya suhaimat tana mai dafe ƙirji"na shiga ukuna ,suhaimat gurin yarinyar kikaje?me kika gani?da wa kikaga tana miki kama?ammi ta faɗa cikin rudewa da tashin hankali,dan bata taba tsammanin suhaimat zataje gurin fattu ba.
Kallon mamaki suhaimat É—in ke bin ammi dashi ,kafin tace "uktee ,yanaga kin rude haka?daga jin cewar naje gurinta?kuma dawa kike tsammanin zanga tana kamar?ta fada cikin mamaki tana kallon ammi,da sai lokacin ta fahimci tayi baran -barama kuma tana son bada kanta.
Cikin sauri ta saita kanta,kafin tace "ai nayi mamakin yadda kika damu da
baiwane,har kikaje dan ganinta"ammi ta faÉ—a cikin basarwa.
Murmushin suhaimat tayi kafin tace "wllh yadda nake jin yarinyar nan cikin raina ,ko su zayyad bana jinsu haka"ta faÉ—a cike da shauki akan fuskarta.
Wani shegen kallon ammi ta jefa mata ,tana mai faɗin ,aikuwa saidai kiyi ta jin wannan shaukin cikin ranki,amma keda ƴarki har abada,bazan ƙara bari ki ganta ba,dan kuwa kashe shegiya zanyi kowa ya huta.ammi ta fada cikin ranta.
Amma afili saitayi murmushi tana faÉ—in,"ke dai suhaimat kina nan da son jama'a har yanzu,sukuwa mutane ba abin yarda bane ,Gara ki kula"
Jinjina kai suhaimat tayi kafin tace "ai idan har kana abu tsakaninka da Allah ,to tabbas Allah zai zama gatanka, kuma bazai taba ba maƙiya Sa'a akanka ba,kuma kinsan shi sharri dan aikene,idan ka cutar da wani to kana zaune zakaga sakayyar Allah"cewar sarauniya suhaimat kenan cikin murmushi take bayaninta.
Kallonta ammi keyi,cike da sanyin jiki,sai take ganin kamar magana suhaimat ke faÉ—a mata afakaice,amma ai tasan suhaimat bata san komai game da halayyar ta ba ,bare tayi mata shagube.dan haka ta Badar da maganar sukaci gaba da hira.
"Ranka ya dade ,hakika al'amarin Adeeb babban abune,wanda Allah shine kadai zai iya kareshi,domin kuwa sihirin da akaiwa yaron nan,badan ƙarfin addu'ar dake tare dashiba, to tabbas mutuwa zaiyi,domin kuwa sihirin anyi shine badan ya rayu ba,saidai akasheshi. Dan haka ba abinda zamuyi face addu'a domin Allah ya kareshi da duk wani mai nemansa da sharri" Shaikh lateef ya faɗa ,yana mai kallon mai martaba ,
Shiru abie yayi cike da tsantsar mamakin waye yayiwa ɗansa wannan aika aikar,kallon ƙaninsa waziri yayi cikin damuwa yace "ɗan uwana kanaji? Kana jin abinda Shaikh ke faɗi, me Adeeb ya tsarewa jama'a ?yaro mai hakuri,hankali da hangen nesa,ba ruwansa da kowa bai tsarewa kowa komai ba,amma ana neman ganin bayansa,Allah ka karemin ɗana ,ka raba shi da sharrin makiya,yanzu Shaikh menene abinyi.
?"abie ya faÉ—a cikin damuwa yana jin kamar ya zubda hawaye.
Jinjina kai Shaikh lateef yayi yana Jan carbinsa dake maƙale adan yatsansa.
"Ranka ya dade ba abinda zamuyi masa daya wuce addu'oi,sannan zan hada masa maganin karya sihiri wanda zai sha yayi wanka dashi,amma fa kasancewar samutum akoda yaushe abune mai matukar wahala,dan kuwa Aduk lokacin da ya shiga yanayi na É“acin rai mai tsanani to tabbas akwai yuwuwar komawarsa macijin " Shaikh ya faÉ—a yana mai kallon abie.
Wazirine ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Shaikh cikin damuwa kafin yace "yanzu ba wata hanya da Ya kamata abi,Dan arabashi da wannan iftila'in?ta yaya za'ace mutum yana komawa wata halittar? Shaikh aduba dai "waziri ya faÉ—a yana kallon Shaikh.
Murmushi Shaikh yayi yana mai girgiza kai,kafin yace ,tabbas da 'ace akwai hanyar da zanbi dan ganin na raba yaron nan da wannan al'amarin ,to danabi ,kamar yadda na faÉ—a muku, anyi amfani da mugayen aljanu waÉ—anda suka samo macizan da ba irinsu afadin duniyar nan,kafin aka hada lakanin da akayi masa sihirin dashi, dan haka addu'a itace kadai mafitarmu"
Ajiyar zuciya abie ya sauke ,zuciyarsa kamar zata fashe tsabar damuwa da É“acin rai,sosai yake jin tausayin Adeeb,waye wanda ke son ganin bayan Adeeb? Me ya tsarewa mutane haka?
Dole ya tsaya sosai ya kula da rayuwar dansa ,ta hanyar bashi kariya ta kowace sigar.
"Shikenan Shaikh Allah ya shige mana gaba ,ya bamu Sa'a akan abinda muke nema"cewar abie yana mai lumshe idonsa lokaci guda damuwarsa ta baya ta dawo masa ,yana tuna abinda ya faru shekarun baya,sam baya son abu makamancin abinda ya faru a baya ya sake faruwa.
"Yanzu ranka shi dade,ina son aturomin yarima zuwa anjima dan akwai abubuwan da zamu tattauna dashi"Shaikh lateef ya faÉ—a yana mai mikewa dan barin dakin.
Bayan fitarsa waziri ya kalli abie wanda yayi shiru fuskarsa gaba É—aya ta sauya ,ta koma kalar damuwa sosai,
"Ranka ya dade ka kwantar da hankalinka,In Sha Allahu komai yazo ƙarshe,ba abinda zai sake samun yarima"waziri ya faɗa cikin kwantar da murya aƙokarinsa na kwantarwa da abie hankali.
"Allah yasa waziri,amma abin yana damuna ,kasan yadda nake son Adeeb ,bana son abinda zai tabashi komai ƙanƙantarsa,domin shine magajina"
"Ba komai ranka ya dade mubar komai hannun allah."cewar waziri.
Jinjina kai abie yayi kafin yace ,sai kuma wannan matsalar ta Rashad,Dole in ɗauki mataki mai ƙarfi akansa,jira nake kawai ya sami lafiya"
"Haka ne yaya dole ahukunta Rashad ,Dan yana don bata mana suna" cewar waziri cikin damuwa.nan dai sukaci gaba da tattaunawa akan matsalar.
Rashad yana nan har yanzu kwance kamar gawa ,ko motsi bayayi, gaba É—aya kamanninsa sun sauya ,abin tausayi,kullum amma cikin kuka take tana tausayawa halin da É—an nata ke ciki,
Gimbiya Zulaihat ma tun daga wannan ranar bata kuma ganin Adeeb ba,dan tsoronsa take ji sosai,amma har lokacin tana nan akan bakanta na son aurensa.
Adeeb kuwa yana dakin da fattu ke kwance tana barci,kallonta yake cike da tausayi,gefe guda kuma wayar da ammi tayi gaba É—aya ta tsaye masa arai,ga maganar da nanny ta fada masa,shi gaba É—aya ma ya shiga ruÉ—u baisan me Yakamata yayi ba,yanzu gurin wa zai je neman shawara?waye zai sanarwa da damuwarsa?yanzu tsoron mutanen fadar nan yake ,dan kuwa cike take da mutane marasa amana da gaskiya.
Ahankali ya shafa gefen fuskar fattu tare da sumbatar goshin ta kafin ya mike tare da ficewa daga É—akin.
Kai tsaye amma ta fito daga part É—in Rashad bayan ta gama kukanta ta koshi,tunani tayi kan cewar ya kamata akawo karshen wannan al'amarin dake dukunkune cikin fadar nan,dan haka tana da bukatar magana da nanny Dole taje tayi magana da ita yanzu .
Dan haka can ta nufa ,cikin sa'a ta tarar da nanny zaune afalo, kallo É—aya zakayi mata kasan tana cikin damuwa da alhini.tana ganin amma ta mike tana mata maraba cikin girmamawa.
Zama amma tayi tare da kallon nanny tace"zauna nanny inason muyi magana dake . "ta fada tana mai kallon nanny ,wacce itama kallonta take.zama nanny tayi jikinta asanyaye kafin tace "wace magana kike son yi dani ranki ya dade?inaga da kin aiko ankirani nazo gurinki dan gudun zargi ,idan aka ganki anan"nanny ta fada cikin damuwa.
"Ajiyar zuciya amma tayi kafin tace ,ya kamata mu daina boye-boye nanny akan abinda muka san menene gaskiyarsa,ki duba halin da ɗana yake ciki ?kuma duk akan wannan makirar matar ,nasan cewa kome ya faru shirinta ne,meyasa zamu zauna mu zuba mata ido tana aikata abinda taga dama?dan haka dole mu kawo ƙarshen zalunci ta"amma ta faɗa cikin ɓacin rai da damuwa.
Ajiyar zuciya nanny ta sauke mai ƙarfi kafin tace "ranki ya dade wannan abun fa abune mai matukar hadari ,dakuma tarin ƙalubale,domin nayiwa magajin fada maganar hadarin sarauniya Nazli, na sanar dashi wanda ke da hannu akan hadarin, amma sam bai yarda dani ba yayi fushi mai tsanani.tunda ya fita bai sake dawowa ba.dan haka ina ganin mudan jinkirta zuwa wani lokaci,har wannan abinda ya faru yayi sanyi"
Jinjina kai amma tayi cike da gamsu,tace "wannan gaskiya ne ,dan kuwa nasan mai martaba ma jira yake Rashad ya farfaÉ—o ,kafin ya yanke hukunci akan abinda ya aikata .Allah shine kawai zai fitar damu " ta fada kwalla na cika idonta.
"Kiyi haƙuri ranki ya dade ,komai yayi farko, yana da karshe ina sha Allah muke da nasara"cewar nanny cike da damuwa akan fuskarta.
"Shikenan nanny Bari na koma can gurin Rashad din"Amma ta faÉ—a tana mikewa.
Biyota nanny tayi tana mata sallama ,har farfajiyar gidan suka fito nanny na kara kwantarwa da amma hankali.
Daidai lokacin kuma Adeeb ya fito daga part É—insa ,idonsa ne ya sauka akan nanny tsaye tare da amma.
Kallonsu yayi cike da tsantsar mamaki,da kara tabbatar da zarginsa akansu.
Suma kallonsa suke cikin yanayi na damuwa da rashin jin dadin ganinsu da yayi .
Tafiya amma tayi daga gurin ,ganin irin kallon da Adeeb ke mata.
Nanny kuwa jikinta ne yayi sanyi sosai.da hanzari ta nufi gurin da Adeeb ke tsaye........
Hmmmmm masu karatu muhaÉ—e next page .
Takuce anty mammy
Mrs babi💘💘
Share and comment fisabilillah.
More comment
More typing.
29/08/2022, 11:07 am - Khadijah Salisu Fari: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄
MACIJI NE🪱🪱🪱
Na mammy kabeer
(Anty mammy)
Elegant online writers📚📚
Free book
Page 63/64
_______________Jikin nanny ne yayi sanyi sosai,ganin Adeeb atsaye,kuma ya gansu tare da amma,tasan yanzu kam kome zata faÉ—a masa ,bazai taba yarda da ita ba.ahankali take takawa zuwa gareshi,gaba É—aya jikinta ba kwari,
Shikuwa Adeeb yana tsaye ya kafeta da Mayun idanunsa ,masu sanya mutum yaji shi cikin tsoro da fargaba.
Nanny Tana karasowa tace "magajin fada ,fushi kake dani ko"?
Ta fada cikin sanyi murya da mutuwar jiki.
Lumshe ido Adeeb yayi ,zuciyarsa na masa zafi yana mamakin abinda nanny tayi masa,ace wai nanny ta hada kai da maƙiyarsa tana tayata ƙoƙarin cutar dashi,matar daya ɗauka matsayin uwa ?mutum kenan.
"Ko kaɗan nanny bana fushi dake,kawai ina godiya ga Allah ne ,daya nunamin gaskiya ,na gane irin mutanen da nake tare dasu,na daukeki tamkar mahaifiyata nanny,Amma bansan nayi babban kuskuren yin hakan ba,dan Allah kiyi haƙuri"ya faɗa yana mai haɗe hannayensa guri ɗaya alamun neman afuwa.
Sosai nanny kejin ciwo cikin ranta ,damuwa da taraddadi sun cika mata zuciya,dama tayi wannan tunanin,tasan idan har Adeeb ya gansu tare da amma ,to shikenan,kuma kome zata faÉ—a masa bazai yarda da ita ba,amma Allah shine shaida bata da nufin cutar da Adeeb ko kaÉ—an.
"Magajin fada wllh abinda kake zargi ba haka bane ,kada ganina tare da amma yasa maka kokwanto akaina, wllh nima Ina jinka tamkar tareeƙ bazan taɓa cutar dakaiba magajin fada.
Nanny ta faÉ—a cike da damuwa aranta.
Girgiza kai kawai Adeeb yayi tare da barin gurin,zuciyarsa kamar zata fashe tsabar damuwa .
Kallonsa kawai nanny keyi,tana fatan Allah yasa ya gane gaskiya cikin sauri kafin komai ya daÉ—a lalacewa.
Ba kowa cikin falon ammi,sai ƙamshi dake tashi ta ko'ina ,dan ammi akwai son kamshi,kai tsaye ya nufi dakin kwananta, nocking yayi amma shiru,hakan yasa shi shiga cikin dakin kai tsaye.saidai nan ma ba kowa cikin dakin.
Harya juya zai fice ,sai kuma zuciyarsa ta raya masa ya duba wanann akwatin da yaji ammi na magana akanta.
Dan haka juyowa yayi yana karewa dakin kallo.
Ahankali yake duba dakin dan neman wannan akwatin,amma yayi iyakar dubansa bai ganta ba.
Harya hakura sai kuma ya hango wata akwati mai kyau da É—aukar ido,yasan akwatin Dan acikinta ammi ke ajiye kwalakwalanta ,dan haka sai yayi tunanin ba komai cikinta, har ya juya da nufin barin dakin,sai kuma zuciyarsa ta kwadaitu da son duba akwatin .
Dan haka ahankali ya zauna tare da ɗauko akwatin, danna lanbobin bude akwatin yayi,dan kuwa tuni yasansu, aikuwa saiga akwati ta bude,gwalagwalai ne acikinta iya ganin ka ,masu kyau da ɗaukar hankali,kallo ɗaya zaka musu kasan an zubar da maƙudan kudade wajen mallakar sarkokin.
Dubawa yayi tayi amma baiga komai aciki ba,sai wani dan karamin akwati mai kyau da ya gani,kallon akwatin yake da mamakin meye acikinsa aka wareshi ?lallai yana son ganin abinda ke ciki.dan haka hannu Ya mika tare da É—auko akwatin ya bude.
Mamaki ,al'ajabi ruɗu da kuma faduwar gaba sune suka ziyarci zuciyar Adeeb,sakamakon ganin sarƙar nan ta Hulwa data bace ,cikin wannan akwatin,
Me yakawo sarkar Hulwa cikin kayan ammi?har akayi mata adana ta musamman?me hakan ke nufi,shidai yasan ammi tana da sarkokin da suka ninka kudin wannan bare yayi tunanin ta daukene dan bata da mai tsada kamar wannan ,to me hakan ke nufi kenan?innalillahi meke faruwa ne acikin gidan nan?kodai akwai Abinda ammin nashi ke kullawa da gaske ? Wayyo ina zaisa kansa ?dawa ya kamata ya yarda ne cikin fadar nan? Dauko sarƙar yayi cikin sauri ya maida komai inda yake sannan yayi saurin barin dakin na ammi ya koma part dinsa. Zuciyarsa na zafi kamar zata kama da wuta .
Lokacin daya koma part din nasa fattu ta farka,tana zaune tana kuka,tsoro takeji,har lokacin barin ma dataga ita kadaice cikin dakin,ina Hamma ya tafi ya barta?karfa wannan Rashad din ya dawo mata? Gashi wannan innar ma bata dawo ba,wannan tunanin yasata ƙanƙame jikinta tana kuka.
Adeeb kuwa cikin wani irin yanayi na sarewar zuciya ya shigo cikin dakin,abubuwa sunyi masa yawa cikin zuciyarsa,jinsa yake kamar bashiba, kansa banda ciwo ba abinda yake ,wai meke shirin faruwa da rayuwarsa ne ?me hakan ke nufi ?me amminsa ke nufi da ɗauke sarƙar Hulwa?
Kukan hulwar da yaji Yone yasani saurin ƙarasawa cikin dakin.
Tana jin motsi sa ta zabura atsorace tana mai kallon ƙofar dakin.ganin Adeeb ne ya shigo yasata saurin yunkurawa ta mike da gyar tana kuka tare da kallonsa.
Da saurinsa ya ƙaraso inda take ,yana zuwa ya kamo hannunta tare da shafa gefen fuskarta yace "menene kike kuka?inane yake miki ciwo ?ya faɗa cikin mugun sanyin murya ,wanda har saida fattu ta ɗago kanta ta kalleshi,
Idanunsa sunyi jajur sosai jijiyoyin kansa sun fito rudurudu,fuskarsa tayi jajur ,kana gani kasan yana cikin damuwa da tashin hankali.
Cikin kuka fattu ta faɗa ƙirjinsa ta rungumeshi, tana faɗin "tsoro nakeji Hamma ,ko ina ganin ƙaninka nake yana min gizo Hamma" ta fada cikin kuka tana ƙanƙame Adeeb.
Cike da tarin damuwar da baisan menene mafitarta ba shima ya ƙanƙame fattun ajikinsa yana mai lumshe ido da sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi,
Ahankali yake faɗin"kiyi haƙuri Hulwa , dagani harke muna cikin damuwa, Hulwa komai bayamin dadi na kasa gane dawa ya kamata in amince cikin fadar nan,Hulwa kowa na fadar nan so yake yaga bayana bansan me na tsare musu ba" Adeeb ya faɗa cikin murya mai tattare da karaya da sarewa.
Shiru fattu tayi tana sauraron abinda yake fadi,ita fa sam bata fahimci inda zancen sa ya nufa ba,ahankali tace "Hamma ,su waye ke son kamin bayanka"?
"Shiru yayi yana mai kara rungume fattu ajikinsa,dan sosai yake jin nutsuwa na samunsa sakamakon rungumeta da yayi,zuciyarsa tana yi masa sanyi .shafa gashin kanta kawai yake bai ce komai ba.
Kusan minti biyar suna rungume da juna ,kafin Adeeb yayi karfin halin zareta daga jikinsa ya zaunar da ita abakin gado,kallonta yake ,har zuwa lokacin idanunta basu koma yadda suke ba,akwai kumburi da kuma dan jaa kadan acikinsu.
Hannunta ya kamo cikin nashi ya rike gam-gam yana kallonta.ji yake kamar ita kadai ta rage masa wacce zai fadawa damuwarsa,saidai fattu yarinyace,idan ma ya faÉ—a mata damuwarsa bazata fahimci me yake nufiba.
Kallonsa fattu tayi itama,tabbas akwai Abinda ke damun hamman nata,ko menene oho."Hamma meke danunka?baka da lafiya ne ?ta fada cikin muryar marasa lafiya ,wadanda suka sha kuka.
Ahankali ya koma kusa da ita ya zauna ,kallonta yayi yace "Hulwa abinda ke damuna yana da yawa,ina cikin wata sarkakiya wacce Allah ne kawai zai fitar dani,bani da wanda zan fadawa damuwata ahalin yanzu,bana son sanar da abie na komai,dan gudun ɓacin ransa,saboda tsoron kar ciwonsa ya tashi,kiyi ta min addu'a kinji hulwatee" Adeeb ya faɗa yana mai riƙe habar fattu tare da zuba mata gajiyayyun idanunsa.
Cike da tausayawa fattu ke kallon Adeeb,kafin itama ta sanya hannunta akan fuskarsa tana shafa gefen fuskar tashi, kamar yadda yake mata .sannan tace "Hamma zanyi ta maka addu'a Allah ya yaye maka damuwarka, kuma kaima kayi ta addu'a Allah maji rokon bawansa ne ,Allah ya bawa abie lafiya Hamma,amma me zai hana ka sanar da innarka itama ta tayaka addu'a" fattu ta faÉ—a bayan ta cire hannunta daga kan fuskar Adeeb.
Wata sassanyar ajiyar zuciya Adeeb ya sauke lokacin da fattu ke shafa gefen fuskarsa ,ahankali ya lumshe idanunsa yana jin wani irin sanyi yana Ratsa zuciyarsa.
Ahankali ya bude idonsa lokacin da yaji ta cire hannunta daga kan fuskarsa.kafin yace "Hulwa ammina tana daga cikin mutanen da nake son boyewa damuwata ,ahalin yanzu bazan iya sanar da ita komai daya danganci lamarinaba,ke dai kiyi ta min addu'a kinji"ya faÉ—a cikin murya mai cike da ban tausayi.
Sosai fattu kejin tausayin hamman nata yana Ratsa zuciyarta.ahankali ta É—ora kanta gafen kafadunsa tare da rungumoshi ta gefe.tayi shiru cike da tunanin meke damun hamman nata.
Ahankali shima ya dora kansa akan nata kan yana jinsa tamkar marayan da bai da kowa.
"Hamma wannan innar bazata dawo ba ko?" Ta fada ahankali idanunta alumshe.
Shima idonsa alumshe yake yana shafa kan fattu ,yace "kina so ganinta ne?
"Daga kai tayi alamun eh sannan tace " eh Hamma ina son ganinta ,ina kaunar ta har cikin raina ,kuma tace daga yau itace inna ta"
Ajiyar zuciya Adeeb yayi kafin yace " Hulwa ita kadai kike kauna ? Ni baki kaunata?ya faÉ—a ba tare da yasan ya fadi hakan ba .saida ya faÉ—a sannan ya fahimce me yace .
"A'a Hamma ina ƙaunarka sosai mana,ina sonka,kaidin kamar baffana kake ,bani da kowa saikai, Hamma bana son wani abu ya tab aka ma" ta fada tana ɗago kai tare da kallon Adeeb.
Cikin wani irin farin ciki da jin dadi Adeeb ke kallon fattu,zuciyarsa cike da jin dadi yace "da gaske kike Hulwa?" Ya faÉ—a cikin murmushi yana kallonta.
Jinjina kai tayi itama cikin murmushi tana kallonsa.
Ahankali ya janyota jikinsa ya rungumeta gamm yana mai lumshe ido , sosai yake jin wani irin. DaÉ—i da Nutsuwa cikin zuciyarsa.
"Kina son ɓata min shiri ko ?,kisani wllh idan kikayi wani kuskuren dana rasa damata,kema zaki karbi naki hukuncin ,kin sanni kinsan halina,kuma kinsan abinda zan iya aikatawa ,dan haka ki kula da kanki,komai yana ƙoƙarin lalacewa saboda sakacinki,to bazan laminci wannan abinda kike yiba.wllh zan aikaki gurin da duk wanda zai zamenin matsala nake aikawa.akan wannan karagar zan iya batar da kowa"
Wani mutum ne daya lulluɓe ilahirin fuskarsa ke fadin wannan maganar cikin ɓacin rai yana kallon ammi,wacce ke tsaye cikin tsantsar tsoro ,jikinta sai rawa yake cikin tashin hankali tace "dan Allah kayi hakuri ,wllh ina yin iyakar ƙoƙarina akan wannan abun ,kuma aKwai shirin da nake yi ,karka damu ka kara hakuri "ta fada cikin rawar murya,tana kallon mutumin da baka ganin komai bace kwayar idanunsa.
Cikin fushi mutumin ya damƙi wuyan ammi ya hadata da jikin bango yana faɗin"bana son jin komai daga bakin ki kawai ki aikata abinda nace miki ,ki tabbatar ya bar duniyar nan nanda lokaci kankani,zan kawo miki abinda zaki saka mishi acikin abinci,zai mutu kuma ba wanda zai zargi wani abu,idan kuma aka samu kuskure .yayi shiru tare da sakin wuyan ammi wacce ke kakari tana kokarin shekawa.
Tari sosai ammi keyi,lokacin da mutumin ya saki wuyanta sannan yayi tafiyarsa cikin sauri yana ƙara gyara rufin fuskarsa.
Saida ammi ta samu nutsuwa kafin ta bar gurin ,kai tsaye dakinta ta nufa ,gaba É—aya awahale take,
Bakin gado ta zauna cike da damuwa tana tunani,can dai ta dauko akwatin sarkokinta,abin yayi matuƙar tsorata ta lokacin datayi arba da akwatin sarƙar fattu ba komai acikinta.
Wani dan gajeren ihu ta kwalla cikin tashin hankali,tana dube dube cikin akwatin ,waye ya daukemin sarƙar nan?na shiga ukuna wayyo ni ammi .da sauri suhaimat ta shigo dakin ammi ,dan kuwa taji ihun da ammin ta kwalla."uktee lafiya ?naji kina ihu?suhaimat ta fada cikin damuwa tana rike ammi.
"Ba komai suhaimat na Dan bugene "ammi ta fada cikin tashin hankali.
Kallonta suhaimat keyi cikin rashin yarda da abinda ya fada,amma koma dai menene tunda taki faÉ—a shikenan .
"To mukam muna ta shiri anjima jirginmu zai tashi .zanje in Kara duba yarinyar can "suhaimat ta fada tana kallon ammi.
"Karkije suhaimat ,karkije,na roƙeki,ki rufamin asiri karkije "ammi ta fada cikin tashin hankali tana kama hannun suhaimat.dan tana tsoron kar ace sarƙar ta koma gurin fattu ne kuma suhaimat ta gani ta gane yarta.
Cike da mamaki suhaimat ke kallon ammi,anya kuwa kalau take?ji yadda ta wani rikice daga cewa zani ganin yarinyar can.
Kai gaskiya akwai wani abu aƙasa.
Cikin hade fuska suhaimat tace "uktee ki fadamin menene dalilinki da baki son na haÉ—u da yarinyar can?me kike kullawa akanta ?menene hajjarki ? suhaimat ta fada cikin haÉ—e rai tana kure ammi da ido.
Zato ido ammi tayi tana kallon suhaimat ,kafin cikin in Ina ta fara magana "su...haim..at ......
Hmmmmm muje zuwa masu karatu.
0 comments:
Post a Comment