Ibrahim ya cika alkawarinsa, mun bar soyayyar mu very low, ban da occasional smiles babu wani abu da zai nuna maka cewa akwai wani abu a tsakanin mu. Har muka gama second term muka koma third term. Muna shirye shiryen rubuta qualifying exams ne rannan a class ake zancen in mun tafi hutu baza mu dawo mu tarar da coppers ba, sai dai maybe mu tarar an kawo wasu. Sam na manta cewa shekara daya ake yi ana service, nan take naji kaina yana juyawa. Amma Ibrahim bai taba min wannan maganar ba, dole in zauna inyi tunani. Wato shi nufinsa sai dai kawai in mun dawo in neme shi in rasa ko? Amma dai bara in ga gudun ruwansa tukun.
Wasa wasa har saura one week muyi hutu Ibrahim bai ce min komai ba. Ranar akayi taro akan shirye shiryen saukar alqur'ani da zamu yi, an saka ranar hutu ranar za'ayi bikin sauka. Duk an tura wa iyayen mu IV. Ana cikin taron ina kallon Ibrahim yana ta kallona yana yimin murmushi amma na hade rai naki mayar masa. Hafsat sa ido tana lura dashi tace min "yau da alama tsimin ya tashi" nayi banza na rabu da ita. Ana tashi daga taron ya taho gurin mu yace min " I want to see you, please" nace masa "OK, ai gani ko" ya sunkuyo saitin fuskata yace "alone" daga haka ya juya ya fice daga hall din. A raina nace lallai wannan mutumin, amma bance komai a fili ba saboda su Hafsat 'yan bani na iya 😎..Bayan sa nabi na tarar dashi a staff room a zaune shi kadai saboda duk malaman are busy. Ya nuna min kujera na zauna ina ta shan kanshi ni lallai fishi nake yi. Yace "wai wannan fushin na menene Maimunatu?" Na kara tsuke fuskata ina turo baki, dariya ma abin ya bashi yace "ni dai bansan abinda nayi ba, duk dokokin da aka kafa min ina binsu, to me nayi ne ni Ibrahim?" Na kalle shi da fada nace "sai yaushe kake planning zaka gaya min in ka tafi gida ba dawowa zakayi ba?" Nan take murmushin fuskarsa ya bace. Ya taso ya dawo kusa dani ya zauna yace "maimunatu ina so muyi maganar amma so nake in tsaida tsayayyiyar magana tukun" nace "bangane ba" yace "bana son komawa Ibadan, ina son in nemi aiki anan ko cikin abuja ko school dinnan, inda dai zan ringa ganin ki. To nayi wa principal dinku maganar inda akwai vacancy inaso amma bata bani amsa ba tukun, to ni tunda nazo ba shiga cikin gari nake yi ba sosai sai last two weeks muka fara zuwa da victor muna raba CV din mu. In har na samu job a Abuja zan dawo nan da zama saboda ke, in ban samu ba kuma babu yadda zanyi maimunatu dole in koma Ibadan" naji dadin maganar sa har cikin raina, cewa zai iya dawo wa Abuja da zama saboda ni alhalin family dinsa suna Ibadan. Nace "amma familyn ka fa? Don't you want to go back to them" yace "family na ina zuwa ganin su ai duk weekend. Bature yace home is where the heart is, and u are my heart maimunatu. I want to be with you" na sunkuyar da kaina kasa ina lissafin maganar sa. Tabbas ina son zamansa a abuja saboda bana son yayi nisa dani amma kuma family dinsa fa? Nayi musu adalci? Amma kuma ta wani bangaren samun aikin sa a abuja ai cigaban sane, duk da bansan salaryn sa na Ibadan ba amma nasan nan nan sai yafi na can. Wata idea ce tazo min raina kuma nayi alkawarin zanyi trying. Muna zaune wasu staff suka shigo suna kallon mu, sai kawai naji ban damu ba. It doesn't matter tunda barin school din ma zaiyi. Tun daga ranar kullum muna tare da Ibrahim gani nake kamar in muka rabu bazan sake ganin saba, shi kuma kullum yana assuring dina da cewa koda bai samu aiki a abuja ba to kullum zai ke zama a hanyar zuwa gurina.
Ana saura kwana biyu hutu mun fito daga exams muna zaune akan veranda ni da Ibrahim muna ta hirar mu muna dariya, yanzu ban damu kowa ya ganmu tare ba tunda it's almost over. Sai nake tambayar shi maganar auren sister dinshi Hadiza, yace "Hadiza ta jama kanta ai, yanzu wani cousin din mu za'a aura mata kuma bata so, data hakura da wancan ta fito da wani da shikenan ai" na sunkuyar da kaina nace "do u think it is easy?" Yace "what?" Nace "idan kana son wata kuma parents dinka suka ce no, do u think it will be that easy ka hakura da ita ka samu wata?' Yanzu ya fahimci cewa ba maganar Hadiza nake yi ba, ina magana ne akan abunda zamu iya fuskanta anan gaba. Yayi shiru bai ce min komai ba, har nayi tunanin ba zai amsa ba sai kuma yace "they will not say no. Maganar Hadiza is different, wanda take so ba mutumin kirki bane. They only need to get to know you zasu soki sosai" nayi murmushi a raina ina cewa naka mai sauki ne Ibrahim nawa nake ji, a fili kuma sai nace "idan kuma basu soni ba fa?" Yace "they will" na sake cewa "what if they don't?" Kamar wanda aka mintsina sai ya mike tsaye yace "dan Allah ki bar maganar nan, we will cross that bridge when we come to it " a raina nace Allah ya bamu ikon tsallake wa lafiya.
Dama da akwai plan din da nake shiryawa na abinda zanyi. Na jawo school bag dinsa da ya ajiye a tsakanin mu na bude na fara yi masa bincike, ya dawo ya zauna yana cewa "me kike nema a jakar tawa kuma" nace "wasikar budurwar ka nake nema" yayi dariya yace "ai ba"a nan zaki samu ba, kin ganta a nan" ya fada yana zaro pink and purple handkerchief dina daga aljihunsa. Nasa hannu na rufe fuskata ina dariya nace "kai yanzu ajiye shi kai?" Yace "eh mana, kuma ajjiyarsa zanyi tayi as a reminder" nayi shiru ban bashi amsa ba, yace "seriously, what are u looking for a jaka ta?" Nace "CV dinka nake nema" yace "me zakiyi da CV dina" nace "ajiyewa zanyi nima as a reminder" yayi dariya yana karbe jakarsa daga hannuna. Nace masa "da gaske so nake in ajiye duk sanda na tashi rubuta CV sai in duba taka" ya jima yana kallona da alama bai yarda da bayani na ba sai kuma ya daga kafada ya dauko ya miko min, na karba nace "nace thank you " "you are welcome"
Ranar hutu daga ni har shi kamar marasa lafiya muka zama, tun da sassafe na fito muna tare dashi har akayi assembly aka fara shigo wa daukan students. Yace min "kina da number dana baki" nace "yes" yace "you can call me anytime" nace "to" duk mun rasa kalaman da zamuyi sallama dasu kawai dai muna enjoying company din each other. Ina ta addu'ah a raina Allah yasa kar azo daukan mu da wuri sai na hango motar gidan mu tana shigowa, gaba na ne ya fadi saboda naga motar mommy ce sabuwar benz dinta, bana son Ibrahim ya ga motar tunda har yanzu bai san gidan mu muna da kudi sosai ba. Nace "ga daddyn mu chan yazo, would you like to meet him?" Nan da nan naga fuskarsa ta chanza alamar tsoro, yace "no, not now" dama nasan haka zaice shi yasa na gayyace shi din. Yace "look at me " na daga kai ina kallon cikin idonsa da yayi kalar tausayi, yace "please in kinje gida call me, da akwai abubuwa da nake so in gaya miki" nace masa to amma still ya kasa tafiya nima kuma na kasa tafiya, sai ga Hafsat nan tazo tana kirana, dole na dauke ido na daga cikin nasa na dau hanyar gate ina hadiye kuka na. Ina jiyo shi yana bawa Hafsat amana ta, ga mamakina sai naji ta biye masa har da dariya.
Episode Twenty: The New Job
Bayan mun koma gida da sati daya daddy ya zo. Ranar duk mun hadu a main falo muna kallo, ina kwance a cinyar mommy tana yi min tsifa, Hafsat kuma suna playing chess ita da Ya Habeeb wanda yanzu ya gama SSCE dinsa yana jiran result, da Faruk. Ya Walid ne kadai baya nan tunda su basu samu hutu ba. News aka fara daddy ya karo volume muma duk sai hankalin mu ya karkata akan TV din. Titi aka nuno chike da hold off ana ta hayaniya can gaba kuma wasu motoci ne guda biyu suka yi crossing suka rufe titin ruf babu hanyar wucewa. A kusa da motocin kuma wasu samari ne sun takarkare suna ta jubgar junansu kamar Allah ne ya aiko su. Camera tayi zooming fuskokinsu ga mamakina sai naga daya daga cikin su dariya yake yi shi kamar game ne abin a gurinsa, dayan kuma sai huci yake yi da alama dariyar dayan ce take kara kular dashi kuma daga dukkan alama me dariyar yafi shi karfi. Daddy ne yayi gyaran murya yace "Habeeb wannan ba Sultan ba ne?" Ya Habeeb ya dan kalli TV yace "Hmm shine fa daddy, yana nan sai abinda ya kara gaba" mommy tace "ai dan baka zama sosai ne, mu yanzu ai mun saba da labarai akan Sultan, kusan kullum zancen kenan. Ni na rasa wanne irin yaro ne wannan. Daga yau a kama shi da drunk driving, gobe fada akan titi ya kama yaran mutane yayi ta jubga, jibi kuma sai kaji ance yaje yayi terrorizing unguwa. Kuma wai an rasa mai daukan mataki akan sa, wannan wacce irin rayuwa ce" daddy yace "ba laifin sa bane, laifin maimartaba ne. Ni bansan yaushe ya chanza hali ba, mutum ne shi mai zafi sanda muna makaranta" da sauri muka hada baki ni da Hafsat "daddy dama sarki abokin kane" yayi dariya yace "ba abokina bane, kawai dai munyi makaranta tare, department din mu daya dashi a Oxford, first degree da second, amma ba abokina bane, tunda ni talaka ne a lokacin su kuma 'ya'yan masu kudi ne. Muna haduwa dai in za'ayi taron Nigerian students. Ni lokacin tsoro yake bani, wato kato ne gashi baki ga zafin zuciya" duk mu ka kwashe da dariya. Ya Habeeb yace "ah bara mu je mu siyo alkyabba, ai ni daga yau na zama dan sarauta tunda babana sunyi makaranta daya da sarki" nan ma dariyar muka same yi, bayan anyi shiru daddy ya shigaba da cewa "bayan mun gama masters ne, munyi applying for PhD sai na daina ganin sa, na tambaya akace sun dan samu problem ne da babansa akan yarinyar da yake so, shine uban ya chire shi yace a daina karatun. Nasan yarinyar dan ina yawan ganin su tare, balarabiya ce, I can remember in na gansu har dariya nake yi, shi bakikkirin ita fara tas, kyakykyawa ce sosai" muka yi dariya ganin yadda mommy ta turo baki kamar yarinya. Na juya na sake kallon screen din TV naga police sun zo scene din an raba fadan, wanda aka kira da Sultan ya kama police guda daya da kokawa sai da suka taru akan sa sannan suka saka masa ankwa, He was still grinning. Anan camera ta tsayar da hotonsa, reporter ta fara lissafo irin crimes dinsa amma da an kama shi za'a sake shi saboda dan sarki ne. Na kura masa ido ina kallonsa. Kyakykyawa ne first class, kana ganin sa kaga half caste, fatar sa golden brown mai kwalli da daukar ido. Idanun sa dara dara farare tas, hankinsa kamar an auna da fuskarsa, lips dinsa tamkar ya shafa jan baki. Bashi da tsaho sosai amma fa a murde yake dan sai da police uku suka hadu sannan suka iya rike shi. Na dauke kaina ina aiyana yadda rayuwar sa take. What is his story? Kawai na samu kaina da tambayar daddy "daddy to an yi auran?" Yace "auran wa?" "Auran balarabiyar, naga wannan kamar halfcast ne" daddy yayi shiru yana kallon hoton sultan a TV sannan yace "gaskiya I can't say ko anyi auran ko ba'ayi ba" mommy tace " anya kuwa anyi? Dan na taba shiga fadar amma matar sarkin da na gani bahaushiya ce, and she is far from being beautiful, kuma na lura Sultan din dan ta ne dan lokacin tana ta fada wai an tafi dauko shi daga airport da wrong car, specifically ya fada yace ga motar da yake so a dauko shi amma aka ki. Gaskiya ina ganin kamar itace ta bata sultan" daddy ya girgiza kai yace "Allah ya kyauta".
Washe gari da sassafe na tashi, na shiga kitchen naga cook din mu tana ta kokarin hada breakfast. Pancakes na yi irin yadda naga mommy tana yiwa dadday, na hada masa coffee shima irin yadda yake so. Na hada da cup da komai akan tray na hau saman daddy. A balcony dinsa nagan shi kamar yadda nayi tsammani. Yana zaune yana karatun news paper. Na durkusa na gaishe shi sannan na koma falonsa na dauko stool na dawo na dora masa tray din da na kawo akai. Na zauna a kasa a gefen sa. Sai da ya fara shan coffee dinsa sannan yace "ya akayi ne maimunatu?" Na sunkuyar da kaina na kasa magana. Ya ajiye cup din hannunsa ya bani dukkan attention dinsa yace "You know I can do anything for you, in dai bai sabawa addini ba, just say it and it will be done" a hankali na fara magana "daddy ba akai na bane" "OK, akan waye?" "Dama wani copper ne a makarantarmu" sai kuma nayi shiru "ina jinki" "dama wani copper ne a makarantar mu, to sun gama service dinsu wannan watan, to daddy mun saba dashi sosai kuma yana taimaka mana sosai, gashi soon zamu fara SSCE" na sake yin shiru kirjina yana bugawa, saboda is simple amma baya tolerating nonsense, bai ce komai ba amma ni yake kallo, naci gaba "daddy so nake yi ko zaka saka baki a bashi aiki a school din mu" yayi shiru yana cigaba da shan coffee dinsa, na daga kaina naga idonsa yana kaina, da alama studying dina yake yi. Can ya nisa yace "maimunatu shi copper din shi yace miki yana son aiki a school din ku?" Nayi sauri nace "eh daddy shi yace yana so" "kuma yace ki nema masa?" Na girgiza kaina, " yace dai yayi wa pc din mu magana in da akwai vacancy yana so" "then that's all, in suna da vacancy, in he is as good as you said he is, za su bashi ba sai nayi magana ba" nayi shiru kuma naki tashi daga durkushen da nake, daddy yace "menene qualifications dinsa?" Nayi sauri na zaro CV din Ibrahim dana boye a jikin rigata, daddy ya karba da mamaki a fuskarsa yace " How did you get his CV?" Nan fa ido na ya raina fa ta, idonsa har yanzu a kaina yake kuma ni kaina nasan nayi alamar rashin gaskiya. Ya sake tambaya "Maimunatu how did you get his CV?" Nace " He just mentioned it in class cewa yana neman aiki a school din mu, to rannan na ari book dinsa sai naga CV din a ciki shine nayi tunanin in kawo maka ko zaka taimaka masa" na fada bakina yana rawa, a nutse daddy yace min "you are lying" wani daci naji a cikin bakina, nan danan zuciyata ta fara bugawa a cikin makogwaro na. "What tribe is he?" A sanyaye nace "he is a Muslim dad" yace "OK, naji musulmine, what tribe is he" can kasan makoshina nace "yaroba" kalmar yaroban kamar wani garwashi naji ta a bakina. Daddy ya ninke takardar dana bashi ya ajiye sannan yace "Hafsat ta tashi?" Nace "a'a" yace " tashi ki tafi, in Hafsat ta tashk ki turo min ita" jiki a sanyaye na tashi na koma saman mu. Ina shiga toilet na shiga na rufe kaina, nan da nan hawayen da nake rikewa suka fara zuba. I was a fool to think I can fool daddy. Shikenan tawa ta kare, yanzu da Hafsat taje zai tambayeta ita kuma zata gaya masa gaskiya, shikenan mommy tana zuwa zai gaya mata ita kuma zata sakani a turmi da daka. Hafsat ce tayi knocking kofar tana jira na, na wanke fuskata na fito ina sussunne fuska. Tana kallona tace "kuka kuma da sassafen nan?" Nayi banza na rabu da ita. Sai da ta fito tana saka kaya na gaya mata kiran daddy, ta zura hijab dinta zata fita na sha gabanta nan da nan wani kukan ya taho min tace "lafiyar ki kuwa Moon?" Cikin kuka nace "Hafsat please, akan maganar Ibrahim daddy zai tambaye ki, dan Allah kar kice komai" tana kallona da mamaki tace "saboda me?" Tambayar ta ta bani mamaki nima, ban gane saboda me ba? Ita ai tasan saboda menene. Tacigaba da cewa "bakya ganin cewa it will be easier for you both in aka gayawa daddy in za'ayi yace eh in kuma baza'ayi ba yace a'a? The longer kuka jira the more painful it will be in aka hana ku aure, ni bazan ce da daddy komai ba, it is not my call, amma shawara ce nake baki" daga haka ta juya tayi tafiyar ta. Sam Hafsat bata gaya min yadda suka yi da daddy ba kuma shima bai ce min komai ba. Washegari muna breakfast daddy yace min "Moon na duba takardun copper din ku, naga yana da first class a maths kuma yana da experience a teaching, zan kira PC dinku in suna da vacancy zanyi endorsing dinsa" daga haka bai kuma cewa komai ba, Hafsat ta mintsine ni a bom bom nayi kara muka saka dariya muna godewa daddy. Mommy ta tsaya tana kallon mu tace "maganar me kuke yi ne?" Hafsat ce tayi mata bayani, mommy tace "ok, wanda kuke extra lessons dashi?" Nace mata "eh" tace "OK, Allah ya sanya alkhairi, adaiyi hankali, the youth of nowadays are not to be trusted" daddy ya kalleta yace "extra lessons kuma?" Nan mommy ta bashi labarin yadda suka yi da pc din mu. Daddy ya kallemu da serious face yace "I want the extra lessons to stop, in zai maku lesson yayi fixing kuyi a class da sauran dalibai, bana son any special treatment a tsakanin ku, da banyi niyyar ne ma masa aikin ba sai da Hafsat tace min shi ya roke ku a class akan duk wacce tasan baban ta zai iya samar masa aiki ta kai masa takardunsa" nayi sauri na kalli Hafsat ita kuma ta daga kafada. Har cikin raina banji dadin abinda Hafsat ta gayawa daddy ba, Ibrahim is a very proud person amma ta ce wai shi ya roke mu mu samar masa aiki. Daddy ya cigaba da cewa "zan taimaka masa ne saboda bana son in discouraging dinku akan taimako, amma no strings will be attached, shi yasa zance da pc din kar ta gaya masa baban ku ne, saboda bana son wani special something. Allah yayi muku albarka baki daya" muka ce amin.
Kamar yadda al'adar makarantar mu take, duk second day na first term ake yin speech and prize giving. Wannan session din ma haka. Muna shiga hall na tuna cewa shekara guda kenan da haduwa ta da Ibrahim. Muka gaida su mommy muka zauna. Yana shigowa idona ya sauka akan sa, ya saka complete yaroba attire har wannan hular tasu. Ina binsa da kallo har ya zauna a side din baki. Muna ta karbar gift duk gift din da za'a bani sai na kalleshi shi kuma sai yayi min 👍 har aka tashi. Ban je gurinsa ba na wuce gurin su mommy muka basu gifts din mu suka tafi gida. Ina komawa hall din naga students sun zagaye shi ana ta tambayarsa me ya dawo dashi. Na tsaya daga gefe kawai ina kallonsa. Yana gani na ta taso ya kara so inda nake bakinsa har kunne. Sai kuma muka rasa abin cewa "you didn't call me" yace yana dan bata fuska, na rufe tawa fuskar nace "sorry". Muka sake yin shiru nace "ashe baka manta yau speech and prize giving ba" yace "I wouldn't miss it for the world, ko da kuwa da rarrafe zan taho" nayi dariya nace "thank You". Can ya sake cewa "I also wanted to tell you, principal din ku tace next week inzo interview, wai wani ambassador ne ya nema min aikin, bansan ko waye ba" na kirkiro mamakin karya nace "congratulations, amma naji dadi sosai" shima yace min "thank You " sannan yace "by the way, Happy Anniversary to Us" na saka hijab dina na rufe fuskata na tafi na bar shi a gurin.
Episode Twenty one: Amira
Ibrahim ya kawo mana kaya babu lefi, kayan tea, biscuits, cosmetics da drinks. It must have cost him dukkan albashinsa. Yazo yayi interview din, kuma bayan wata daya aka aika masa da offer dinsa har ibadan. A week after that, ya tattaro ta dawo abuja. An bashi gida a staff quarters. Nan take ya fara siyayyar kayan gida, kusan komai ya saya sai ya gayamin ni kuma sai in gaya masa menene next abinda ya kamata ya saya. I wanted to help him with money amma nasan ba zai karba ba, kuma bama nason yasan financial status din family na. Farko sai aka bashi ss2 shi kuma ya dage lallai baya so shi ss3 yake so, a cewar sa ya saba damu tunda mu ya dauka sanda yana service. Sai da kyar suka bashi SS3 din, ranar bakinsa har kunne yana murna yazo yake gaya mana, sannan kuma an bashi sports master. Yanzu kam da yawa daga 'yan ajin mu sun san alaka ta da Ibrahim tunda sam yanzu baya boye abinda yake ranshi, ni ce dai nake dan ja da baya.A haka har muka yi hutun first term. A cikin hutun abubuwa da yawa sun faru, na farko Allah yayi wa baban Amira rasuwa.
Asalin su Amira 'yan kano ne, baban ta babban mutum ne sosai, yana da manyan 'ya'ya a kano sai aiki ya mayar dashi Abuja, ita kuma uwargidansa tace sam ba zata koma Abuja da zama ba tunda ta tara iyali a kano. Nan 'yan'uwansa suka hada musu auren zumunci da maman Amira ya taho da ita Abuja. Amira ce kadai 'ya a tsakanin su tunda shekarunsa sunja sosai. Sam 'yan uwan Amira babu wanda ya damu da ita balle mahaifiyarta, dan haka sai mutuwar tayi musu zafi sosai. Maman Amira bata san komai na dukiyar baba ba sai gidan da suke ciki a abuja, duk harkokinsa da manyan 'ya'yansa yake yi. Matarsa ta kano ta dage lallai sai a sayar da gidan na Abuja a hada kudin da sauran dukiyar sa ta kano sannan a raba gadon. Ita kuma maman Amira bata son sayar da gidan saboda bata son tashi daga abuja tunda nan ta saba dashi, daga ita har Amira. Mommy ce tayi tsayin daka akan maganar tunda ita lawyer ce har sai da taga an bar musu gidan a matsayin gadonsu, bayan gidan kuwa babu abinda suka tsira dashi, hatta motar da maman take hawa sai da aka karbe. Maman Amira sec sch kadai tayi, dan haka babu zancen neman aiki, ga Amira ita ko sec din bata gama ba. Mommy ce ta biya wa Amira school fees na second and third term sannan ta biya mata kudin SSCE din da zamu yi nan bada jimawa ba.
Muna komawa pc tayi taron Muslim students ta sanar mana cewa akwai musabaka da federal government take shiryawa, ance a bada daliba guda daya da zatayi representing din school din mu, dan haka mu zaba a tsakanin mu wa muke ganin zata iya. Nan take muka zabi Amira, kuma tace ta yarda zatayi, muna ta murna sai pc tace zata hada ta da malami guda daya wanda za su ke yin tilawa tare kafin likacin musabakar. Muka tashi daga taron muna ta yiwa amira murna.
Da daddare after islamiyya sai Ibrahim yace da Amira ta tsaya yana son ganinta, inajin haka nasan shi akace yayi coaching dinta. Amira ta ja hannuna muka tsaya tare. Sai da aka gama tafiya sannan yazo yace mata "congratulations Amira, naji abin alkhairi, Allah ya bada sa'a" muka ce amin. Nan suka fara tsara yadda zasuke karatun ni kuma ina jinsu ina dan bada tawa shawarar. A karshe suka yanke shawarar zasu keyi daga magrib zuwa isha. Haka kuwa akayi, kullum in munyi sallar magrib sai Amira ta zauna a masallaci tare da Ibrahim har sai munzo sallah isha tukunna mu tafi ialamiyya tare.
A bangare na kuma lokaci daya girma razo min, ni kaina bansan yaushe ba sai gani nayi kayana duk sunyi min kadan. Kirjina kullum kara chika yake haka hips dina, har saida nakai ga komawa aron kayan Hafsat ina sakawa ita kuma tace sam ba zata yiwu ba sai dai in aika gida akawo min wasu kayan. Ina aika wa kuwa sai ga kaya akwati guda duk size din Hafsat kuma dana saka sai naga duk sunyi min dai dai. Wata ranar sport muka saka sport wears kamar yadda muka saba muka fita. Ni dama basketball nake yi tun jss1 haka Ibrahim ma, duk ranar sport tare muke yi dashi kuma ya iya sosai saboda yana da tsaho. Ina zuwa na tarar dashi already a field da wadansu staff su biyu tare da students wadanda mostly 'yan kallo ne. Ban yi wata wata ba na shiga muka fara bugawa, amma sai na lura Ibrahim hankalinsa sam baya kam ball din, duk ya zama distracted, ya kasa scoring ko kwallo daya, gashi anaso ayi mana game, nan na tafi gurinsa da niyyar in tambayeshi mai yake damunsa sai na lura gaba daya ransa a bace yake. Ina zuwa kusa dashi sai kawai naga ya chire jacket din daya daura a kugunsa ya kama kokawar saka min, na kwace daga hannunsa cikin fada nace "what is wrong with you?" ya dora min jacket din akan kirjina yace "just go and play table tennis or snooker, ai ba sai lallai kinyi basketball din ba" raina naji ya fara baci, nace "saboda me? Kullum ba basketball din nake playing ba? Dan me yau zaka ce wai inje inyi snooker bayan kai ne ma kake bata mana game din" wani kallo da yayi wa kirjina yasa naji kafafuwana duk sun sage, kallon kawai yayi min na gane ma'anar me yake nufi, wata kunya ce naji kamar zan narke a gurin. Bai ce min komai ba ya juya ya bar field din. Daga baya na naji wasu sababbin coppers suna cewa "wannan Ibrahim din dan bakin ciki ne wallahi" wani hawayen takaici naji yana taho min, nayi sauri na mayar dashi. Da sauri sauri na zura jacket din Ibrahim na bar gurin. Ina jin wata tana kwalla min kira na rabu da ita. Can kasan wata bishiya na hango hafsat tana zaune akan kujera da novel a hannunta tana karantawa, ta dora kafa daya kan daya. Itama sport wears din ne a jikin ta amma tayi rolling farin vail har saman kirjinta. Na tsaya a gabanta nace "why didn't you tell me?" Ta kalleni da rashin fahimta tace "tell you what?" Na zauna kusa da ita nace "ba za kiyi min fada kice kayan jikina are showing ba, kika barni na fito mutane suna kallona?" Dariya tayi ni kuma na kara kuluwa, sannan tace "kusan shekaru biyu da suka wuce na taba fada miki magana akan Ibrahim sai kika ce min you are old enough to make decisions for yourself, to dan me yanzu kuma zan yi miki magana, tunda you are not blind. Yanzu ai kin dauki darasi ko?" Na kara bata rai bance mata komai ba. Kamar daga sama naji yana cewa "barka da hutawa big sister" duk muka kalleshi Hafsat tana dariya tace "ni fa bana son big sister dinnan, sai inji duk tsufa ya kamani" suka yi dariyar su su kadai. Ya zauna kusa dani naja kujera ta na matsa yace min "am sorry, bai kamata inyi miki magana a cikin mutane ba, amma bazan iya hakura mutane suna kallonki ba" Hafsat tayi gyaran murya tace "Hello, ina nan fa" ya kalleta yace "in ba zaki tashi ba to ki toshe kunnuwanki" ni dai bance musu komai ba dan duk haushi suke bani. Tun daga ranar na koma saka dogon hijab irin na Hafsat, 'yan sport din mu kuwa tun suna nemana har suka hakura.
Muna gab da fara SSCE Amira tace min sun daina karatu da Ibrahim. Na tambayeta dalili tace babu komai kawai tana ganin ta iya duk abinda ya kamata ta iya. Washe gari muna class aka kira ta a staff room, shiru shiru bata dawl ba sai na tashi na bi bayanta. A hanya muka hadu da ita. Abinda na gani a fuskarta ya bani tsoro, na tambayeta "Amira lafiya, ko a gida ne wani abu ya faru?" Wani kallo ta yi min wanda naji tamkar ta doka min guduma aka, cikin sarkewar murya tace "me kika biyo ni kiyi min kuma, nace na fasa karatun dashi ba shikenan ba? To yanzu na fasa musabakar ma gaba daya, kije kiyi na bar miki, besides you are the golden one ai, you are so perfect that you must have everything that you want. You can have him, you can have the musabaka and everything else" ta bangaje ni da kafadar ta ta wuce. Ni sam ban gabe ina maganganun Amira suka dosa ba dan ni a iya sanina banyi mata komai ba. Tana tafiya sai naga Ibrahim ya fito daga office din PC muka hada ido ya girgiza min kai alamar kar inyi magana ya tafi.
Tunda muka shiga class Amira ta kifa kanta a desk take kuka, kowa ya tambayeta sai tace babu komai. Hafsat tace a rabu da ita, dama tun mutuwar babanta she has not being herself maybe mutuwar ta tuna. Ana tashi Ibrahim yazo ya kira ni ya tambayeni ko zan iya yin musabakar? Da mamaki nace masa "Amira fa" yace "tace ta fasa" na tambayeshi dalili yace bai sani ba. Muna zuwa hostel nayi wa Hafsat bayanin duk abinda ya faru. Tayi shiru sannan tace "Are u sure babu wani abun a tsakanin su?" Naji maganar ta kamar kibiya a zuciyata amma sai na maze nace "wani abu kamar me fa?" Ta kalleni da nutsuwa tace "Amira ba haka take ba, in har ta gaya miki wadannan maganganu to da akwai dalili, kuma they have been spending a lot of time together lately, maybe something happened".
Maganar Hafsat ta shige ni kuma nayi niyyar zan samu Ibrahim inji daga bakinsa. Dama yanzu mun daina lectures sai dai revisions ko kuma muyi ta tutorial. Dan haka muna zuwa class na tafi staff room na cewa Ibrahim ina son ganin sa. Mu ka fito tare muna tafiya, direct na tambayeshi nace "Me ya hada ka da Amira?" Ya tsaya yana kallona yace " bangane ba, wani abun tace nace mata" nan na fada masa duk maganganun da Amira ta gaya min, yayi shiru bai ce komai ba. Direct na sake tambayar sa "is Amira in love with you?" Yace da sauri "what? Me yasa zaki fadi haka" na sake cewa "are you in love with Amira?" Da karfi yace "hell no!!" Nayi shiru saboda naga yana son yayi min ihu a cikin mutane. Sai da muka jima a tsaye muna kallon kallo sannan ya fara magana "OK, na jima da sanin cewa amira tana so na, tana dannewa saboda she is your friend, ni ma kuma ban taba nuna mata na sani ba, but I know the signs. Yanzu da muka fara karatu da ita sai ya fara zama worst har bata concentrating akan karatun sai dai tayi ta tambata things about me and other stuffs, to sai nayi suggesting cewa mu gayyato ki kizo muke yin karatun tare, shine taji haushi tace ta fasa karatun, na gaya wa pc kuma shine tace ta fasa musabakar gabadaya, sai dai ke kiyi tunda nace dake nake so muyi karatu" tun daya fara maganar nake sauraron shi ina jin wani daci yana taso min a baki na, ji nayi kamar in rufe shi da duka, amma dana kalleshi sai naga iyakacin gaskiyarsa yake fada min. Na juya da sauri zan bar gurin ya kamo hannuna, wani mugun kallo na jefa masa nan da nan ya sake ni nayi gaba. Ina jinsa yace "maimunatu 🙏please "
Episode Twenty Two: Efisowa
Ina zuwa class Hafsat ta taso take tambayata "well, what did he said?" Na kalleta da jajayen ido nace "it's none of your business" ta jima tsaye a kaina sannan ta daga kafada tace "OK, in tayi tsami maji" da ace ana sayar da maganin sa ido da saina sayo na bawa Hafsat. Two days suka wuce, zuciya ta fara sanyi amma har yanzu ban huce ba. Ibrahim duk ya gama rikicewa saboda silent treatment da nake bashi. Amira kuma ta ja baya da komai, ta zama wata irin silent ba ta yiwa kowa magana, musamman ma ni. On the third day muna aji a zaune sai ga Ibrahim nan yazo, ya taho direct gurina ya tsaya a gabana yace da karfi yadda kowa a class din zaiji "nace miki I don't love her, what more do you want from me?" Gabadaya ajin kowa yayi shiru yana kallon mu ballantana su Hafsat sa ido. Nayi kasa da murya nace "what are you doing?" Ya kara daga murya yace "am telling everyone bana son ta ni ke nake so, ke kadai nake so" Wata jamila tace "sir wacece? A ajin nan take? Cewa tayi tana sonka?" Na dan saci kallon amira sai naga ta juya ma class din baya tana kallon waje, sai kawai naji zuciya ta ta karye, na dauki wani katon textbook na fara dukan Ibrahim da shi ina korar sa waje, amma yaki tafiya yace lallai saina fada masa cewa maganar ta wuce sannan zai fita, su kuwa 'yan aji sai kara tambayarsa suke ya basu labari. Da naga dai Ibrahim da gaske yake so yake yayi wa Amira tonon silili sai nace masa na yarda, maganar ta wuce, yace "kinyi alkawarin ba zaki kara tayar da maganar ba?" Nace "I promise" sannan ya juya ya fita. Yana fita Hafsat tace "well3, dama nace in tayi tsami zanji, 'yan class din nan duk mai son yaji wacece yazo in gaya masa" nan da nan duk suka tafi gurin Hafsat, na kalli Amira naga alamar tsoro a fuskarta, nayi sauri naje gurin Hafsat nace "Hafsat dan Allah ki bar maganar nan" tace "sai kinyi min alkawarin daga yau anti Hafsat zaki ke ce min" nace "done, anti Hafsat from today".
Sai da muka je hostel sannan Hafsat tace "ni daga ke har Amira kun bani mamaki wallahi, ni banga abin so a jikin wannan dogon mutumin ba" nayi dariya kawai ba rabu da ita, amma maganar ta ta tsaya min a rai. A lokuta da dama mutum ba shi yake zabar wanda zuciyarsa zata so ba, kawai haka kawai zakaji kana son mutum, wani lokacin kuma daga kaga mutum sai kaji baka son sa, ba tare da yayi maka komai ba. Kamar yadda lokaci daya na ji zuciya ta tana son Ibrahim duk da irin banbancin da yake tsakanin mu, babu wani dalili da zance saboda abu kaza nake sonsa, kawai dai nasan ina son sa. Da nayi considering Amira sai naga itama haka ne a wurinta, kawai taji tana sonsa ne amma saboda kusancina da ita ya saka ta boye a ranta har sai yanzu da suke spending time together sannan ta fara nuna masa, it must be hard on her, especially yanzu da yayi declaring a gaban kowa cewa baya sonta, sannan gashi gandantakar mu ta shekaru kusan shida tana so ta baci saboda kawai ta kasa controlling zuciyar ta. She deserves a break from me. Ina yin wanka na shirya sai na tafi dakinsu Amira, na tarar da ita a kwance idonta a rufe kamar mai bacci amma kana ganinta kasan ba baccin take yi ba. Na daka mata duka a cinya nace "sleepy heads, ki tashi mu tafi karatu" ta bude idonta tana kallona da mamaki. Ita tasan na sani. A hankali tace "bana jin dadi ne" nace "yeah right, in kika fita zaki warke" a haka na takura ta tayi wanka muka fita. Tun daga nan muka cigaba da kawancen mu da Amira, amma duk abinda muke yi da Ibrahim yazo gurin zata tashi, ni ma kuma bana cewa ta tsaya saboda ta ciki na ciki daurewa kawai nake yi.
Soyayya sabowa muke shimfidawa da Ibrahim. Gani nake tunda na shiga SS3 ai I am old enough, shima kuma dama kiris yake jira. Sam Ibrahim baya kunyar nuna min soyayya ko a gaban waye ma kuwa, ni dai duk sai kunya ta rufe ni. Rannan a class ya zo yana cewa wai ya kasa bacci jiya kawai sai yaji muryata yake so yaji, wai saura kadan ya taho hostel, su kuma 'yan ajin sai su biye masa suyi ta tsokana ta, inna ga sun dame ni sai in tashi in bar musu ajin.
Anan nake so inja hankalin iyayen yara musamman 'yan mata akan mu kula da tarbiyyar 'ya'yan mu. Yanzu makarantu sun baci, da yawa malamai suna soyayya da daliban su mata. Kuma da yawa daga cikin su basa nufin alkhairi, musamman a boarding schools. Kuma school management suna basa kula tunda shi kansa principal din ko vice ba zai rasa budurwa ba, musamman a private school inda yaran suke da budaddan ido. Mu tabbatar mun bawa yaran mu tarbiyya sannan kullum muke yi musu addu'ah dan babu abinda yafi addu'ah iyaye kariya a gurin 'ya'yansu. Allah yayi wa zuri'ar mu albarka baki daya.
Rannan muna a gaban chemistry lab muna duba past questions and answers na WAEC sai muka hango Ibrahim da wasu mata su biyu a gaban staff room, Hasiya ce ta taba ni tace "kinga mutumin ki can, ko suwa ya samu kuma" ina dubawa naga mata ne su biyu da kaya a hannun daya, dayar daga gani babbar macece dayar kuma budurwa, budurwar da hijab matar kuma da babban mayafi, sun jima a tsaye suna magana sai naga ya karbi kayan hannun budurwar ya wuce gaba suna binsa a baya suka tafi staff quarters. Har dare ban kuma ganinsa ba kuma ina ta tunanin ko su waye wadan nan? Washe gari da safe sai gashi yazo yace min inzo, muna fita waje sai yace "there is someone here that wants to see you" gaba na ya fadi nace "who?" Yace "my mother" nan da nan naji wani tashin hankali yazo min, he wants me to meet his mother, this is serious. To ni yanzu da wacce fuskar zan je mata? Kuma me zance mata? Nace masa "Ibrahim am sorry, I can't" ya bata fuska yace "why can't you?" Nace "tsoro nake ji" dariya yayi yace "tsoron me kuma? Bata cin mutane, besides tare zamu je, just ku gaisa shikenan" na kalli kayan jikina, uniform ne a wanke a goge, hijab dina ya rufe har bom2 dina, fuskata babu kwalliya, dama ba kwalliyar nake yi ba. Na sake kallonsa har yanzu da dariya a fuskarsa. Yace "you look great, let's go" yana fadin haka ya shige gaba, na bishi a baya kamar wadda kwai ya fashewa a ciki. Direct visitors room muka je, ya dan tsaya yana kallona yace "are u ready" na girgiza kaina alamar no, yayi dariya kawai ya bude kofar da sallama. Nima nayi sallama na shiga. Su biyu ne kamar jiya da babba da karama. Ina kallon babbar nasan ita ta haifi Ibrahim sai dai bata kaishi tsaho ba, karamar kuma sam basa kama dan ta fishi hasken fata sosai, dan da kadan zan nuna mata fari, sai dai ita fuskarta duk kuraje yayin da tawa take tas. Kana ganin maman su Ibrahim kaga typical yaroba woman. Da daurin zanin ta akan riga, da goggoron akan ta. Ibrahim ya zauna a kusa da ita ni kuma na durkusa daga nesa a kasa na gaisheta da turanci. Ta amsa min amma daga gani turancin na isar ta yayi ba. A raina nace oho dai ni ba iya yarabanci nayi ba sai dai mu tsaya daga gaisuwar. Na gaishe da dayar tunda daga ganinta nasan ta girme ni. Ta amsa tana dariya, na dago kai sai naga Ibrahim ne yake hararar ta, ya wani dora kafa daya akan daya. Maman su kuwa idonta yana kaina. Sai da muka dan jima a haka sannan Ibrahim yace "Maimunatu this is my mother, and that girl over there is my sister" da saurin ta tace "his step sister" na dago kai na kalleta sai naga idonta a kansa, bansan dalili ba sai naji hankali na bai kwanta ba da kallon da take masa. Mamansu naji ta fara magana da gurbataccen turancinta "kullum na kira Ibrahim zancen sa Maimunatu tace kaza maimunatu tayi kaza, inna yi masa complain akan baya zuwa mana weekend sai yace ai muna karatu da Maimunatu sun kusa fara exams, kullum zancen kenan, shine nace bara inzo inga maimunatun nan dai da ido na" naja hijab dina na rufe fuskata, inaji tana masa magana da yarabanci, naji dai tace fulani a ciki, sai naji yace "mu fa yaroba ba'a wani kunyar suruka, in zaki bude ido ki bude, dan duk randa kika haihu ita zata yi miki wanka" na kara dunkule wa a guri daya a raina ina cewa kai Ibrahim mai ya kawo zancen haihuwa kuma? Gaba daya suka yi dariya. 'Yar budurwar ce tayi magana tace "let me introduce myself properly, ni step sister dinsa ce, ma'ana babana ne mijin mamansa, sunana Efisowa amma zaki iya kira na Efi, nazo in taya shi assessing sabida nasan ba iya zabe yayi ba. Dama tunda naji mama tace Fulani nace sai nazo nagani da kaina, gashi kuma naga kinyi kankanta da yawa" Ibrahim yace mata "shut off" sannan yayi mata magana da yarabanci itama ta mayar masa, sai maman tayi musu magana duk sukayi shiru. A hankali maman tace min "ina parents dinki?" Nace mata "suna cikin garin abuja" tace "ku 'yan Abuja ne" nace "'yan jigawa ne mu" kawai sai naji matar tayi min, yadda take magana a hankali irin maganar Ibrahim. Efi ce dai hankali na bai kwanta da ita ba, duk na damu ganin ta kasa dauke idonta daga kan Ibrahim. Ibrahim ne yace zai mayar dani class dan muna karatu, Efi ta sake yin magana da yarabanci shi kuma ya sake ce mata shut off maman tayi tsaki tana kallon efi alamar warning. Tunda muka fito bamu yi magana ba sai da muka dan yi nisa sannan yace "how do you like my mother" nace "she is OK, you look like her but taller" yace "no, she always say da baban mu nake kama" Har nayi tunanin kar in tambayeshi akan efi amma sai zuciya ta ta kasa jurewa, nace "Your sister doesn't like me" yayi dariya yace "yours doesn't like me either" nima nayi dariya sannan nace "but this is different, i feel like there is some tension between you two" yayi shiru bai bani amsa ba, wannan ya tabbatar min da zargina. Nan take naji raina yana kuna. Sai da muka kusa zuwa class sannan yace "koma menene da a tsakanina da efi is over tun tuni, abinda yake tsakanin mu sam bashi da dangantaka da efi. A mincewar mama da baba kawai nake bukata. Please Maimunatu don't screw this thing off. Mama tazo takanas saboda ta ganki, please show her your best behavior yadda in taje zata bawa baba labari shima zai yaba dake, please don't let Efi get in your head, that is exactly what she wants" muna zuwa gaban class din mu nayi shigewa ta ba tare da nace masa komai ba. Har na zauna yana tsaye a gaban class din ya rungume hannayensa fuskarsa da alamar damuwa.
Bayan na zauna sai nayi tunanin ban kyauta wa Ibrahim ba, kuma gaskiya ya fada cewa this is our chance, ya kamata inyi kokari inyi probing to his mother cewa I am good enough, inna bari kishin Efi ya shiga raina tun yanzu to ina da problem.
Anan zan tsaya inja hankalin 'yammata har ma da matan auren, idan mace ta nuna tana son mijin ki, musamman idan shi mijin ko saurayin baya son ta, don't make an enemy out of her, ki jata a jikin ki kiyi mata kirki sosai, make sure duk sanda saurayin ko mijin yake around kun nuna mata irin soyayyar da kuke yiwa junan ku, ita da kanta zata ji kunya ta ja baya, amma idan kika kama fishi da fada kamar kina tura shi gurinta ne. Ke kuma budurwa da kike neman miji, kar kiga wata da nata kiyi sha'awa kice lallai sai kin raba. In dai har soyayyar tsakani da Allah yake yi mata to ba zasu rabu bafa.
Washe gari da yamma muna kofar library da Amira da wasu kawayen mu sai ga Ibrahim sun taho gurin mu shida Efi, tun daga nesa nake kallon yadda take ta shishshige masa, gaba daya kowa ya tsaya yana kallon su har suka kara so. Kallo daya nayi masa nasan ransa a bace yake. Suna zuwa yayi introducing dinta generally, sannan yace "she said she wants to look around the school" nayi sauri nace "she is welcome" tare da miko mata hannu, ta kalle ni sannan ta kalli Ibrahim kamar me neman izni shi kuma ya dauke kansa ya juya ya tafi, tayi masa magana da yarabanci bai amsa mata ba, ya saka hannayensa a aljihun wandon sa yayi tafiyarsa. Yana tafiya na fara yi mata hira, nayi mata introducing duk friends dina da suke gurin. Amira ko kallon ta bata yi ba. Daga nan nace tazo in showing her around, tun daga classes, labs, kitchen, dining hall duk sai da na kaita, sannan na kaita hostel.
Hafsat tana kwance muka shiga, ta bimu da kallo, sannan tace min da fulatanci "wannan kuma a ina kika samota?" Na amsa mata da turanci "she is Ibrahim's step sister" sannan na kalli Efi nace "this is my Sister, Hafsat" Efi tace "oh my God she is so beautiful, nice to meet you" ta mika wa Hafsat hannu, kirikiri Hafsat ta ki bata hannu tace da fulatanci "ni bazan taba hannunki ba, kurwata kur" nayi dariya, Efi tace "what did she said?" Nace mata cewa tayi "ai kin fita kyau ma" nan da nan ta washe baki tace "thank u" Hafsat ta harare ni. Nan da nan Efi ta fara santin dakin mu, wai wannan ai ko a gida sai haka, ita in tana nan ai ba zata so ayi hutu bama. Nan da nan na chika mata gabanta da kayan chiye2 muka zauna muka yi ta hira, tana bani labarin gidan su. Amma ni bance mata komai ba akan namu gidan. Har akayi sallar magrib muna tare can sai Ibrahim ya kira ta yace ta fito su koma gida, haka kawai sai na samu kaina da jin babu dadi saboda ya kira ta a waya. Na dauko wani set din toiletries na mu na dove na saka mata a keda na bata. Tayi ta mamaki wai ina student har nake kyautar kaya?
Washe gari Ibrahim yace min zasu tafi, na hado sweets da biscuits madu yawa a leda na boye a hijab dina saboda 'yan sa ido, yazo ya kira ni muyi sallama da mama. Ina shiga na gaishe ta, ta amsa min da sakakkiyar fuska sosai tayi min fada akan karatu, naji dadi har raina, na dauko leda ta na bata nace a kaiwa Abdullahi da Abdulrahman, kananan kannen Ibrahim. Taki karba na ajiye mata a gabanta na tafi.
Da daddare Ibrahim yazo yana ta fada wai me yasa na kashe kudi na sayo kaya? In ina son in basu basai inyi masa magana shi ya sayo musu ba? Shi ya dauka siyowa nayi. Bayan kwana biyu sai gashi da kaya niki niki ya kawo min.
Sanda muka fara SSCE kullum in mun shiga exam Ibrahim zai zauna a kofar hall din ya jira ni, har sai na fito ya tambayeni ya paper sannan zai tafi. A lokacin ya koya min jin kida, zai kunna slow music ya saka ear piece a kunne daya ni ma in saka kunne daya muna ji tare. Shakuwa ce sosai kullum take kara shiga tsakanin mu. Har tararradin ranar da zamu gama paper nake yi. A week to gama papers din mu PC ta kira ni tace federal government ta aiko a bada sunan best student za' a biya mata scholarship zuwa university of her choice. Dan haka tana sanar min cewa sunana zasu bayar. Nayi shiru ina tunani. I don't need the scholarship, daddy zai iya biya min karatu zuwa kowacce kasa nake so. Scholarship is meant for bright students din da iyayensu ba zasu iya biya musu school fees ba. Kawai sai Amira ta fado min a rai. Nan take nace da pc na barwa Amira, asaka sunan ta instead of sunana. PC ta nuna bata ji dadi ba, I am the best student that they ever had a school din. Nace mata to tayi contacting daddy ta sanar masa, duk abinda yace shikenan.
Ana gobe zamu yi graduating Ibrahim ya kira ni yace zamuyi magana. Muna zama na lura he is serious. Yace "Maimunatu in kunje gida ina so zanzo in nemi iznin neman auren ki a gurin daddyn ku" zuciya ta ta buga da karfi na kalle yace "yes, ina so in samu permission dinsu saboda insan in da na dosa, just pray for us"
I hope you enjoy this episode. Put on your seat belts because the next episode is going to blow u away.
Episode Twenty three: The Break up 💔
Alright this is another long episode, nayi deciding zan ke yi da yawa ne saboda we have a long way to go.
Na yi shiru na zuba mishi idanu kamar yadda shima ya zuba min. Can ya dan yi murmushi yace "are you scared?" Na gyada kaina alamar eh. Yayi dariya yace "I am scared too, amma dole muyi haka, saboda inaso in kun koma gida in ke zuwa gurin ki kuma kinga bazan ke zuwa bada iznin daddy ba, it's not right" na sunkuyar da kaina nace Allah ya kai mu.
Washe gari har mukamuka fitar da kayan mu bakin gate banga Ibrahim ba, mun dawo hostel muna sallama da mutane sai gashi yazo bakin gate, daga ganin sa nasan cewa he is not OK. Hafsat ce ta tambaye shi "sir, baka da lafiya ne?" Yace mata "wallahi kwana nayi da zazzabi" nan Hafsat ta saka shi a gaba da tsokana wai dan zamu tafi ne, nima kaina zazzabin nake ji. Muka je bakin gate yace shi ba zai karasa ba, wai ko wanka bai yi ba baya son ya shiga gurin mutane. Nan Hafsat ta barmu ta karasa gate. Tana tafiya ya matso kusa dani yace a hankali "so, finally dai zaki tafi ki barni" nace "ba kace zaka ke zuwa ba" yace "ba dole in zo ba, dan ke fa nake zaune a garin nan, only for you, yanzu ma tunanin yadda zanke yin spending days with out you nake yi." Nace masa "ai zamu ke yin waya" yace "bayan ke baki da waya? Kuma in kinje gidan bakya kirana da wata wayar" nace "ai zan kira ka yanzu" "ban yarda ba, ki bani number mommy kawai" "laa to in ka kira ta me zaka ce mata?' "Sai ince mata son in law dinta ne" nayi dariya, a raina nace lallai wannan bai san wacece mommy ba. A fili kuma nace "Allah da gaske nake zan kira ka" ya marairaice fuska "yanzu tafiya zaki yi ki barni?" Nayi dariya ganin yadda yayi da fuskarsa, yace "au dariya ma kike yi min ko? Duk sanda daddy ya bani permission kullum sai nazo" nace "Allah ya kaimu lokacin" Hafsat naji tana kwala min kira, naga tana dago min hannu, nasan anzo daukar mu kenan. Naki tafiya, sai gata tazo tace in ba zaki tafi ba zanyi tafiya ta wallahi, na kalle ta na dauke kai. Sai tace au kuka zakuyi? Bani phone dinka inyi muku hoton tarihi, kawai sai ya fito da phone din ya mika mata, ta karba ta bude camera ta dauke mu. Na dan kwantar da kaina a kafadarsa shi kuma ya juyo da kansa yana kallona. Hoton yayi kyau sosai. Daga haka Hafsat ta figi hannuna muka tafi, ina jinshi a hankali yace "Maimunatu" amma ban juyo ba ballantana in amsa masa.
Muna zuwa gida muka tarar daddy da mommy sun shirya mana surprise party na graduation, duk kowa yana nan har neighbours an gayyato, ga cake kato da hotunan mu a jiki ni da Hafsat. Nan da nan muka chanja kaya zuwa dogayen rigunan da mommy ta bamu as gift din ta, ta Hafsat pink tawa red. Munyi kyau ba kadan ba, mommy tayi mana light make up. Muka fito muka yanka cake tare da daukar hotuna, nan take naji duk na manta da wani rabuwa da Ibrahim. Muna gamawa daddy ya kawo mana nashi gift din. Muna unwrapping muka ga wayoyi ne sababbi fil kirar Samsung galaxy edge ta Hafsat pink tawa red. Ai ji nayi kamar daddy ya saka ni a aljanna. Muka rungume shi muna murna tare da cewa "thank you daddy". Bayan an tashi daga party muka dawo main palo muka dasa sabuwar hira, muna ta basu labarin makaranta su kuma suna bamu labarin abubuwan da suka faro sanda bama nan. Hafiz ya samu admission shima a Oxford inda zai karanci accounting. Anan daddy yake ce min sunyi waya da PC din mu akan scholarship dina, "is that what you really want" nace eh, yace "to shikenan zance a bata din, Allah yasa haka ya zamar miki sadaqatujjariya" nace "amin daddy" nan ya kara yi mana nasiha akan tausayawa na kasa damu da duk wanda muka ga yana bukatar taimako, wanda duk ya taimaki wani Allah zai taimake shi.
Muna komawa daki da daddare mu ka dauko wayoyin mu muka kunna, dama already an saka mana sim cards a ciki. Hafsat ta dauko address book din da muka karbi numbers din friends din mu ta fara saving a wayar ta, ni kuma number da nake so inyi saving tana cikin kaina. Na zauna nayi dialing, bugu daya ya dauka, sai kuma na kasa magana, yayi ta hello3 can yace "maimunatu talk now, ko so kike zuciya ta ta buga ne" da mamaki nace "ya akayi kasan ni ce?" Yayi dariya yace "nasan babu wanda zai kira ni yayi shiru, wato wayo zaki yi min ko? Ke kina jin murya ta amma ni kinyi min rowar taki ko?" Nace "a'a ba haka bane ba fa. Dama so nake ince maka daddy ya saya min waya" da sauri yace "haba? Amma daddy ya gama yi min komai" nace "ya jikin naka?" Yace "na warke yanzu tunda naji muryarki" na lumshe ido na ina jin dadin kalamansa. Dama Ibrahim da magana a hankali balle kuma ana tsara budurwa a waya. Na kwanta lamo a kan gado na rungume pillow, ina ganin Hafsat tana harara ta ni kuma na murguda mata baki. Kalamai Ibrahim yayi ta tsaro min wadanda nake jin su har 'yan yatsun kafata. A haka har bacci ya dauke ni. Da assuba karar waya ta tashe ni, da kyar na bude ido na na duba naga number Ibrahim, tunda banyi saving ba. Ina dagawa yace "a tashi ayi sallah sleepy head" cikin bacci nace "na tashi ai" yace "aa, ban yarda ba, ki shiga toilet ki kunna ruwa inji tikunna" na tashi na shiga toilet na daga sink sannan ya kashe wayar.
Haka rayuwa tacigaba da kasance mana ni da Ibrahim, kullum muna makale a waya. Wannan yasa na rage zaman falo sai bedroom. Da naji mommy ta taho kuwa sai in kashe wayar. Babu abinda Ibrahim bai tsara min ba, ya gama tsara mana rayuwar mu kaf, tun daga design din gidan da zamu zauna, 'ya'yan da zamu haifa, yace duk so yake su yi kama dani amma mazan suyi tsahon sa. Ni dai sai dai inyi dariya ko ince masa to. Wani lokacin yakan sakj layi ya koma bedroom secrets ni kuma da naji haka sai in kashe wayar.
Munyi three weeks da dawowa Ibrahim yace yana son zuwa, yana son in gaya masa ranar da zai samu daddy a gida. Na gaya masa yace to in jira shi.
Ranar da zaizo tun safe na tashi da mutuwar jiki. Muka yi waya da Ibrahim na ce masa ya bari sai yamma tunda yanzu daddy baya gida. Nayi masa text din address. Allah ya soni mommy tana office tun safe, dan haka na shiga kitchen na gaya wa cook abinda nake so ta hada min zanyi bako. Tana dariya take tsokana ta "it is about time, ya kamata mu fara ganin samari a gidan nan" nima nayi dariya nace "asma'u ba fa saurayi na bane, just nace miki zanyi bako sai kice saurayi?" Ta tabe baki tace "ai ku 'yan boko haka kuke, sai kuce baku isa aure ba" da naga dai magana take nema sai na fice na bata guri, dan banajin dadi sosai. Nayi wanka na na saka wata blue din atamfa mai pink flowers, riga da skirt, na gyara fuskata da powder da wet lips, na fesa turaruka na masu dadin kamshi. Hafsat tana kwance tana kallona tace "finally yau zai zo gidannan, I salute his courage" na ce mata "shut your mouth, saidinawa masu bacci da ido daya" na fita na kira wani daga cikin yaran gidan nace ya saka min kujeru a garden. Na dawo falo na zauna nayi folding hannuna zuciyata tana bugawa.
Har five daddy bai dawo ba, Ibrahim bai zo ba. Hafsat ta sauko tana kallona tace "you look pale moon, relax" nace mata "baki san mai nake ji ba Hafsat" waya ta ce tayi kara na duba naga Ibrahim ne, na dauka yace "Am here, ina gate, your security won't let me in" tun daga muryarsa na gane he is somehow not happy" nayi sauri na dauki gale na pink na fita, ina jin Hafsat tana cewa "good luck". Ina fita wani security ya karaso guri na yana min bayanin wani yazo gurina, nace masa su bude masa gate, nima na yi hanyar gate din da sauri. Yana shigowa wani security ya zo da bomb detector yana shafa masa, da sauri na daga masa hannu nayi masa alama da ya matsa daga gurin. Na karasa da sauri ina kakaro murmushi, shima murmushin yayi min da side daya, da alamar bacin rai a fuskarsa. Complete yaroba attire ya saka. Riga bubu three quater da wando mai fadi, sai hula da aka dinka da yadin shaddar, ya lankwasa hular zuwa side din fuskarsa. Nayi masa sannu da zuwa na wuce gaba da dan sauri shi kuma ya biyo bayana. Kamar daga sama naji ance "hey!! Where are u going?" Na juyo naga chief security din gidan ne yake wa Ibrahim tsawa. Zuciya ta naji ta buga da karfi. Na juyo a fusace na kama yi masa masifa shi kuma yana bani hakuri cewa bai san tare muke ba. Yadda yake kallon Ibrahim kadai zaka gane assessing kayan jikin sa yake yi. Banyi aune ba sai ji nayi gate ya bude, lokaci daya Royce Rossey din daddy ta danno kai harabar gidan. Ji nayi kamar kafata ba zata dauke ni ba, ni kame kam a gurin da nake haka ma Ibrahim. A hankali motar take gangarowa har tazo dai dai saitin mu sannan glass din ya fara sauka kasa. Innalillahi wa inna ilaihir raji'un kawai nake ambata a zuciya ta dan bakina bazai iya furta komai ba. Fuskar daddy ce ta baiyana cike da kwarjini da kyau da kasaita irin na fulani. A hankali ya chire glass din idonsa yana kallona sannan ya mayar da kallonsa kan Ibrahim. Daga ni har Ibrahim babu wanda yace komai. Ya mayar da glass din idonsa sannan glass din motar shima yayi sama a hankali har ya rufe sannan motar ta mirgina tayi gaba. Ajiyar zuciya mai karfi na sauke, sannan na fara jin wanj sanyi yana shigata alamar zazzabi.
Na juya na kalli Ibrahim wanda har yanzu motar yake kallo. Nasan idan ba a movie ba Ibrahim bai taba ganin RR ba, dan very few people ne suke da ita a Nigeria. Nace masa "let's go" amma bai motsa ba. A hankali yace "I guess that is your father, the man I am suppose to meet today" kaina a kasa nace yes. Da haka na juya na nufi hanyar garden. Sai da nayi nisa sannan ya biyo bayana muka karasa tare. Muna zuwa na nuna masa kujera amma sai ya tsaya ya fara safa da marwa. Ni dai na zauna na zuba masa ido. Dan kansa kuma yazo ya zauna yace "why didn't you tell me" nace "me fa?" Ya kalleni bacin rai karara a fuskarsa yace "you clearly know what" nace "me kaso ace na gaya maka? Cewa babana ambassador ne? Muna da katon gida mai cike da securities?" Ya katse ni da cewa "hell yes!! Exactly like that, da kin gaya min haka da nasan mai zan fuskanta ai" nace "it doesn't change anything" yace "it changes everything, ni maimunatun da na sani is a simple daliba, wannan kuwa is a princess living in a castle guided by a bunch of dragons" ta gefen ido na na hango driver yana fito da motar yaya Walid daga garage, da alama fita zai yi. Na dawo da hankali na kan Ibrahim nace masa "I am still me" ya mike tsaye ya cigaba ba safa da marwa "ta yaya kike tsammanin mutun kamar ni zaije gurin mutun kamar babanki yace masa yana neman auren 'yarsa? Daya kalleni abinda zai gani shine some stupid yaroba parasite da zaiyi feeding on his daughter, he will take one look at me and ask his security to throw me out" zafin zuciyata naji ya karo, na mike tsaye ni ma "don't talk about my father that way, baka san shiba, ba haka yake ba. Don't judge him without knowing him" gani yayi da gaske raina ya baci, sai ya tsaya yace "am sorry maimunatu, am just not myself" na zauna shima ya zauna. Ta gefen idona na hango Ya Walid ya fito daga gida ya nufi motarsa. A cikin zuciya ta nake cewa "karka juyo, karka juyo" amma kamar wanda na takarkare na kwalla masa kira sai gani nayi ya juyo din kuwa, ya dan dakata yana kallon mu, har da saka hannunsa ya kare hasken rana. Har ya bude kofar motarsa sai kuma ya rufe ya sake kallon inda muke, na kalli Ibrahim naga shima shi yake kallo. Kawai sai naga ya nufo inda muke zaune. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun kawai nake ta maimaitawa a raina. Ibrahim yace "I guess this is your brother" nace "yes". Duk gidan mu Ya Walid ya fi mu hasken fata, fari ne tas dan har yalo fatarsa take yi. A kyau kuwa ba daga nan ba. Dan gayu ne na ajin karshe, ballantana kuma yau kamar fitar musamman za'ayi. Shirt da wando a jikinsa 'yan gaske, kansa babu hula sai gyaran da gashin sa ya sha sai daukan ido yake, takalminsa da agogon hannunsa kadai abin kallo ne. Ya karaso gurin mu idonsa a kaina, sannan ya kalli Ibrahim da alamar tambaya a fuskarsa. Ya bawa Ibrahim hannu suka gaisa. Da fulatanci ya ce min "Moon a inda za'a kare kenan?" Na bata fuska yayi dariya, sannan yace da turanci "idan mommy ta dawo kice mata na fita" sai a lokacin na tuno cewa mommy tana iya shigowa a kowanne lokaci. Na gyada masa kai kawai. Ya juya yayi taku biyu sai yayi juyi 180 ya dawo yace "baki yi introducing din mu ba kuma" nayi murmushin yake nace "Ibrahim wannan shine yaya Walid, babban yayan mu, Ya Walid wannan shine Ibrahim my.... " Ibrahim yayi sauri yace "her former teacher" nayi sauri na kalleshi amma sai naga bani yake kallo ba. Ya Walid ya dan jinjina kai yana dan turo baki, sai kuma ya juya zai tafi, two steps ya sake tsayawa a raina nace "oh dear God, what now" ya juyo fuskarsa da alamar tambaya ya sake kallon Ibrahim sannan yace min da turanci "Ohh ko shine wanda kwanan baya kika sa daddy ya samo wa aiki?" Zuciya ta naji ta bug sau biyu a tare sai kuma ta tsaya chak, jini yayi draining daga fuskata. Ya Walid ya lura da chanzawar yanayi na sai ya daga kafada yace "what did I said?" Daga haka ya juya ya nufi motarsa kirar Ferrari wacce ba'a dadr da saya masa ba. Ta bata wuta, ya kunna kida ya figa a guje a fice.
Tunda ya bar gurin babu wanda yayi magana a tsakanin mu. Can Ibrahim yace "you really are a genius maimunatu, you played me like a fool, and like the fool I am I am madly in love with you. What a foolish fool am I" a hankali nace "I am sorry" ya sake mikewa, "sorry? Do u just say u are sorry? Wato kina ganin bazan iya samarwa kaina aiki ba shine kika je ki ka gayawa daddy ya samomin?" Nima na mike tsaye "ni bance ba zaka iya samarwa kanka aiki ba, ka riga ka kai takardunka ka nemi aikin ka da kanka... " ya katse ni yace "amma ni da ke munsan da baiyi magana ba baza'a bani ba" yayi shiru sannan ya cigaba "PC tace min wani ambassador ne yayi endorsing dina, I should have known, amma da yake I am a fool sai na karba ina murna" magana yake yi da karfi cikin bacin rai. Out of no where naga chief security yazo gurin "ma'am is this man bothering you?" ban san sanda na rufe shi da masifa ba nace idan bai bar gurin ba saina saka ya bar aiki. Bashiri ya bar gurin. Na sake cewa da Ibrahim "am sorry, ban dauka ranka zai baci har haka ba, naga kana son aikin kuma I didn't want to loose you. I love you" na fada ba tare da realizing cewa na fadi L word ba. Murmushi Ibrahim yayi sannan a hankali yace "and I love you too, only too much" ya karaso inda nake tsaye ya saka hannayensa biyu ya riko fuskata yana kallon jajayen idanuna, ya cigaba da cewa "I am going maimunatu, zan dawo in ga daddy amma sai na zama worthy of u, sai na zama worthy of meeting your daddy, sai na zama someone da zaki nuna wa family dinki. Please wait for me, I will come back for you, I promise you" i dona a cikin nasa nace "you are already worthy enough to me" ya dora lips dinsa akan goshina for what seems like eternity sannan ya juya bayansa ya kama hanyar gate. Kamar hadin baki sai ruwan sama ya tsuge. Ina tsaye ina kallonsa har ya isa bakin gate sai kuma na tafi da gudu na shiga gida, direct sama na hau, na wuce dakin mu na bude kofar balcony na fita na hangoshi ya fita daga get din ya dau hanyar fita daga quarters din, hannayensa a cikin aljihun rigarsa, yana tafiya a hankali yayin da ruwan sama ya ke sauka a kansa.
Anan zan dakata inja hankalin samari da 'yan mata a harkar neman aure, in kaga budurwa kana sonta itama tana sonka, in dai har kana da halin yin aure, ma'ana kana da aiki ko sana'a wadda kasan zai iya rike ku to kar kace sai kayi kudi zakayi aure, hakan bashi da ma'ana. Maybe baka da rabon yin kudin. Maybe arzikin ka is linked with her. Fadin ubangiji ne cewa kowacce rai da arzikinta take zuwa duniya, idan baka da arziki sai kaga a sanadiyyar auren da kayi, ko haihuwar da matarka tayi Allah ya baku arziki. Kuma abinda mutanen mu har yanzu bamu gane ba shine, idan kayi aure baka da arziki, kukazo kukayi arzikin tare da matarka to kun fi mutunta juna, ku sha wahala tare kuji dadi tare. Indai har yrinya tace tana sonka, indai har soyayyar Allah da annabi take maka to bata damu da kudinka ko rashin kudinka ba. Wannan wait for me shiriritar bata da ma'ana, kana can kana neman kudin wani zaizo wanda ya fika komai kuma she may fall in love with him, kaga kayi losing kenan, biyu babu.
Next thing da nake so inyi magana akansa, duk da dai sai a next chapter za'a fi fahimtata sosai shine akan judging mutun ba tare da kasan sa ba. Never judge a book by its cover. Yawancin mutane suna da kirki, no matter the tribe, you just need to know them. Masu kudi da masu sarauta, in kaga wulakanci a tare dasu mostly daga gurin na kasansu ne ba daga su bane. You just need to take a deep breath and talk to them...
Next thing shine secrets in a relationship. In kuna so relationship din ku ya dore, never ever keep a secret from each other, never lie to each other.
Ga 'yammata da samarin da suke tsoron relationship dinsu ba zai dore ba saboda banbancin yare, ko social status, do u try to make it work ko kuma a boye kuke yi? Just take a deep breath ku tunkari iyayenku da maganar, it may turn out easier than you imagine. Ita zuciya an halicceta da son wanda yake kyautata mata, ko wanne kabila ne shi, indai har zai juri kyautatawa iyayenki, yana nuna musu best behavior dinsa, ke kuma kullum kina nuna musu how much you love him, insha Allahu zaku ga chanji a gurinsu. But most importantly pray.
Episode Twenty Four: The Heartbreak 💔
Ibrahim has broke many hearts yesterday, especially Moon's.
Na cigaba da kallonsa har ya bace min da gani. Feshin ruwan saman da akeyi yana dukan fuskata amma sam ban damu dashi ba. Zuciya ta tana kuna amma hawaye yaki zuwa ido na balle inji dadi. Motsin mutun naji a baya na, nasan ko wace dan haka ban juya ba. Sai da ta lulluba min towel sannan nasan duk jiki na ya jike da ruwa. A hankali ta jani muka shiga daki ta rufe kofar balcony din. Na zauna a kan stool ina goge ruwan jikina ita kuma ta zauna a gefen gado tana kallona. Tace "what happened Moon?" Na dago kaina na kalleta da busassun idanu na nace "He is gone" "gone?" "Yes, He was mistreated by our security, He saw Daddy and....... Ya walid yazo ya gaya masa cewa daddy ne ya samo masa aiki, he then lost it" Hafsat ta saki hannuna ta rufe bakinta da hannayenta. "Oh my God, me yace kuma" nan na bata labarin duk abinda ya gudana tsakanin mu. Tayi shiru na wani lokaci sannan tace "Moon am so sorry, I really am, amma dama nasan alakar ki dashi ba mai dorewa bace. You are too different from each other. Banbancin da yake tsakanin ku kamar banbancin da yake tsakanin maiduguri ne da lagos, ba zasu taba haduwa ba" na kalleta da murmushin takaici a fuskata nace "you are wrong my dear sister, we are more alike than we are different. Na farko duk kanin mu mutane ne, sannan kuma Africans, must importantly kuma Muslims. As muslims kuma munsan we are all equal a gurin Allah, babu wanda yafi wani sai wanda yafi tsoron Allah. Banbancin da kuke gani a tsakanin mu banbancin kabila ne. Ni a ganina kabilar mutum ba komai bace illar yarensa da al'adunsa. Yanzu misali ke wacce yare ce?" Ta kalleni da mamaki tace "fulani mana" nace "eh, babanki fulani ne amma mamanki buzuwa ce, meaning you are not full blood fulani. Yare yana nufin language, yanzu misali ni, ina jin fulatanci, buzanci, turanci, larabci da hausa. To wanne yare ce ni kenan? Yanzu fulani nawa kika sani wadanda suke full blood fulani amma basu iya fulatancin ba? Wani ko zo bai sani da fulatanci ba amma yana ikirarin shi bafulatani ne. It doesn't make sense to me. In nayi maganar al'ada kuma is much worse than yare, dukkan kabilun Nigeria mun aje al'adun mu a gefe mun dauko na wadansu daban munayi. Then how are we different from each other? Yanzu ke da kika ce ke bafulatana ce duk cikin suturar ki babu ta fulani, babu abinda kika sani na daga al'adar fulani, we are even lucky mun iya yaren ma. This all doesn't make sense to me. Yanzu na tabbata idan aka kawo miki wani bafulatanin wanda bai iya fulatanci ba, aka kawo miki igbo ko yaroba wanda ya iya turanci sai ki fi communicating da igbon ko yaroban akan fulanin" duk maganar da nake Hafsat tayi shiru tana kallona da alamar tana fahimta ta. Can ta nisa tace "Ok, yanzu what will you do?" Na kalleta for some seconds nace "That, my dear sister is what I don't know"
Sati guda kenan chif da zuwan Ibrahim amma har yanzu ban ji sassauci a zafin da zuciya ta keyi min ba, kuma har yanzu ban yanke shawarar menene abinyi next ba. Ina kwance main palo akan kujera, Hafsat tana zaune a gaba na, mommy tana can gefe tana operating system din ta. Waya ta nayi dialing na saka a kunne na "the number you are trying to call is currently switched off, please try again later, thank you" naji wadannan kalmomin ya kai sau dari a cikin satin nan, amma na kasa hakura in daina trying. Na ajiye yawar na lumshe ido na. Muryar Ya Habeeb naji ya shigo da sallama, ya gaida mommy ya zauna kujerar kusa dani. Na dan kalle shi, yayi min murmushi, ban mayar masa ba, na sake mayar da idona na rufe. Wajan five minutes muna zaune a haka babu wanda yayi magana. Can Ya Habeeb yayi tsaki yace "wai menene yake faruwa a gidan nan ne? Duk komai ya zama so dull kwana biyun nan, ni na gaji gaskiya" mommy tayi ajiyar zuciya tace "I don't know Habibi, ni kaina abin ya ishe ni wallahi, dazu nake cewa ko da yamma fita zamuyi ne mu dan zaga gari? Duk gidan babu dadi" Hafsat tace "au wai ku baku san me yake faruwa ba?" Ya Habeeb yace "menene yake faruwa" tace "we are having a lunar eclipse" mommy tace "what? Me kike nufi?" Hafsat tace "our Moob is no longer bright" duk suka juyo suka kalleni. Ya Habeeb yace "tabbas, duk ta zama wata iri kwana biyun nan" mommy tace "ko abincin kirki bata ci fa, kullum na tambayeta ko bata da lafiya sai tace min ita lafiyar ta kalau" duk ina jin abinda suke cewa amma na kasa tanka musu.
Daddy ne ya shigo ya Walid yana binsa a baya. Muka tashi gaba daya muka gaishe shi. Ya amsa mana da fara'arsa kamar yadda ya saba. Ya zauna sannan yace "dama ina son ganin ku gaba dayan ku, to tunda gaku kun hadu shikenan sai muyi maganar" mommy ta rufe system dinta ta dawo kusa da daddy ta zauna, mu kuma duk muka sauka kasa muka zauna a gabansu.
Daddy ya fara magana da cewa "maganar da nake son inyi muku akan Hafsatu ne da Maimunatu. Tunda Allah yasa kun gama secondary school, ina son in san plan din ku for the future. Aure kuke so kuyi ko kuma karatu kuke son yi?" Muka juya muka kalli juna ni da Hafsat, saboda bamu taba tsammanin wannan tambayar daga gare shi ba, mun riga mun yi zeroing mind din mu cewa karatu zaice muyi, la'akari da irin zurfin ilminsa sannan yayun mu suna gama sec sch suke wucewa university. Mommy ma ta saki baki tana kallonsa tace "aure? Aure fa kace Dear?" Ya kalleta da murmushi yace "yes, aure" ta nuna mu da hannu tace yanzu wadannan 'yan babies din za'ayiwa aure?" Dariya sosai daddy yayi yace "kwarai da gaske. Babu wacce zan matsawa a cikin su ince tayi aure, amma duk wacce tace min aure ta ke so to babu shakka auren zanyi mata. It's very wrong abinda mutanen mu suke yi yanzu na cewa ba zasuyi wa 'ya'yansu aure ta sai sunyi karatu mai zurfi. Hakan bashi da ma'ana. Indai har yarinya ta isa aure, ta samu miji, kuma tace tana son auren to abu mafi a'ala shine ayi mata auren. In ba haka ba ka shiga hakkin 'yarka kuma in Allah bai kare taba to zaka jefa ta a halaka" mommy ta tabe baki tace "ni dai 'ya'yana basu isa aure ba" daddy yace "cikin su wacece bata period" duk palon kowa yayi shiru, ya cigaba da cewa "shekara nawa nana Aisha ta tare a gidan annabi SAW? Duk abinda annabi yayi a rayuwarsa yayi ne saboda yana so mu kwaikwayeshi, su Westerners din da muke kwaikwayo basa yiwa 'ya'yansu aure da wuri amma ai basa hana 'ya'yansu tare wa a gidan samari ko? Mu tunda addinin mu ya hana hakan mai yasa ba za muyiwa yaranmu aure in sun isa ba?" Mommy ta sauke ajiyar zuciya ta karya murya tace "amma dear karatun fa?" Daddy yace "aure ai baya hana karatu, su kansu mazan yanzu ai sun waye basa hana matan su karatu. Yanzu misali, Prof Rukayyatu Ahmad Rufa'i tana sec sch akayi mata aure amma sai da takai har matsayin professor. Dan haka indai har mazajen su sun amince to za suyi karatu har sai inda suka gaji" yayi shiru for some time. Kamar daga sama yace "Moon ina saurayin nan naki yaroba?" Da sauri na dago kai na na kalle shi sannan na kalli mommy wacce itama shi take kallo da sakakken baki. Ya cigaba da cewa "yes, I know. Tun sanda kika sa na nemar masa aiki nasan there is something between you two. Na yi miki gargadi akansa ne saboda malamin ki ne a boarding school, babu idon mu a kanku, amma nasan in har da gaske yake son ki zai biyo ki gida, kuma naga ya biyo ki din. I thought zai zo ya ganni ranar sai kuma naga bai zo ba, sai na saka a raina cewar he is not ready" mommy ta fara girgiza kanta tana maimaita "no, no, no, not my daughter, not Moon" daddy ya cigaba da cewa "I know your mother will throw her tantrum, but I can handle her" mommy tayi sauri tace "inna da baffa ma ba za su yarda ba, Moon din za'a aura wa bayarabe? Dama munafikin copper dinnan ashe bana Allah bane?" Daddy ya kalleta with serious face yace "menene matsalarki da shi" tayi sauri tace "bayarabe fa kace? Wannan kadai bai isa matsala ba?" Daddy yace "indai har yana sallah, yana da asali, mutumin kirki ne, kuma yana da halin rike mata shikenan. Wannan shine abinda addini ya gindaya mana akan in zamu zaba wa yayan mu mazaje, addini baice mana mu duba kabila ko yare ba" mommy wacce by now ranta ya gama baci tace "I am not looking forward to having yaroba grandchildren, can u even imagine that?" Daddy ya kashingida akan kujerar da yake kwance yace "kinga shikenan sun huta idan ana tribal crisis" Ya Habeeb yayi dariya mommy ta harare shi. Daddy ya kalleni yace seriously"tell him in da gaske yake yazo ya same ni muyi magana dashi, in kuma bada gaske yake ba kar ya sake zuwa gidan nan" ni dai bance komai ba. Ya juya kan Hafsat yace "Hafsat ke kuma fa? Karatu ko aure?" Hafsat ta gyara zama tace "daddy ni dai nafi son karatu" yace "shikenan, Alhamdulillah. Along the line in kina karatun in kinji kina son auren kuma Allah ya kawo mijin shikenan sai kiyi kayanki" Ya Habeeb ya zunguri Hafsat "to dama ba dole kiyi karatu ba, tunda babu mashinshini?" Ta juya ta murguda masa baki, yace "kinga tsiyar ai, rashin kunyar kima ai bazata bar samarin su zo ba" duk akayi dariya banda mommy. Daddy yace "shikenan, kowa ya tafi harkokinsa, next week zamu sake yin magana" da sauri na mike, dama kaman akan kaya nake zaune. Na hau saman mu, ina shiga daki naji tafiyar Hafsat a baya na. Ta shigo ta rufe kofa. Lokacin ina cire kaya na tace "now what?" Nace "now, my dear sister, I am going to look for him" da haka na shiga wanka. Ina wanka ina tunanin abubuwan da suka faru. Look what Ibrahim almost cost us. The Idiot. Na fada a fili. He don't know daddy amma after one look at him yayi deciding ba zai saurare shi ba. The Fool. Har da wani tafiya wai sai yayi kudi zai dawo, ko ina ruwan daddy da kudinsa? The Idiot. Na fito daga wanka na zura doguwar riga nayi rolling vail. Hafsat naga ta yafa mayafi. Nan muka fita tare. A falon mommy muka same ta a zaune ita kadai har yanzu ranta a bace yake. Ta bimu da kallo. Hafsat tace "mommy zamu danje unguwa mu dawo" wani mugun kallo mommy tayi mata tace "wato dan ance za'ayi muku aure shine zaku fara yawo kuma? Ko neman mazajen zakuje yi?" Hafsat tace "mommy gidan su Amira fa zamu je" "oh zakuje ku bata labarin za'ayi muku aure ko?" Mu kayi shiru bamu ce komai ba. Ta kalle ni tace "Maimuna ki kiyaye ni wallahi, ki fita daga ido na in rufe, ko da wasa na sake jin maganar wannan bayaraben wallahi sai kin san bani da dadi" na makale daga bayan Hafsat. A raina nace "oh mommy, da kinsan yadda nake jin bayaraben nan a raina da baki ce haka ba" mun jima a tsaye sannan tace "kar ku kai magrib" daga nan ta tashi ta shige bedroom dinta.
Muna fita driver ya dauko motar da ake kaimu unguwa. Wani security ya zo ya shiga seat din gaba, take nace masa ya fita. After what happend ba zanje gurin Ibrahim da security ba. Mu ka shiga baya Hafsat tace da driver ya kaimu former school din mu.
Muna zuwa staff room muka wuce. Muna shiga seat dinsa na kalla. Lokaci daya na sandare a inda nake tsaye. Babu shi babu alamar sa. Babu komai akan desk dinsa. Not even a single paper. Babu kowa a staff room din sai wani malami guda daya. Hafsat ta karasa gurinsa ta gaishe shi, yace "well3, didn't expect to see you soon" Hafsat tace "sir, malam Ibrahim fa?" Ya maida kallonsa kaina yace "you didn't know? He is gone. He quite his job five days ago, babu wanda yasan mai ya faru, yayi rashin lafiya for two days aka kwantar dashi a clinic, yana fitowa ya rubuta resignation, a day after that ya kwashe kayansa kaf ya koma ibadan"
sama sama naji Hafsat tana masa godiya, naji ta zo ta kama hannuna tana ja na, naji ta sakani a mota ta rufe kofar ta zagaya ta shiga daya side din. Driver ya ja muka tafi. He is gone, He is really gone. Ban taba tambayarsa address dinsa ba. Ban taba tambayarsa phone number din wani nasa ba. Abinda na sani kawai shine a ibadan yake, where in ibadan I don't know. Hanyar da Ibadan take ma bansani ba.
Ina jin driver din mu yayi horn mai gadi ya bude masa get muka shiga gida. Muna fitowa sai ga mai gadi nan ya taho da saurin sa yana yi min magana. "Mai sunan Daada" duk muka tsaya. Ya zo gurina yace "mai sunan daada kinga na manta wallahi sai yanzu dana ganki. Kwanaku hudu da suka wuce wani yazo ya bani sako yace in baki, yana ta jaddada min kar in manta kinga kuwa sai da na manta din, kinsan tsufa sai a hankali" a nutse nace masa "ina sakon yake?" Da gudu ya sake komawa dakinsa sai gashi da wata brown envelope a hannunsa. Hafsat ce ta karba ta gode masa. Ta bare seal din ta saka hannu a ciki sai gashi ta fito da CD a hannunt. A jikin CD din an rubuta da marker I LOVE YOU. Tsaf na gane rubutun sa.
Hafsat ta shiga gida ni kuma na koma motar da muka fito, na zauna a seat din gaba na kunna radio na zura CD din hannuna sannan na danna play. A hankali wakar ta fara tashi.. ......
I don't know when am coming back. I will be gone for a little while, but I will keep myself for me and you, I will be back for you.
I don't know what the future will brings, but I will want you to be with me. I will hope and pray make you wait for me, cos I will come back for you, darling
You are my life, you are my prize, and I went to the finish line. You will be always on my mind.
I will be so far away, promise you will wait for me, I will think of you everyday, my love.
I may not come today, but I will be with you again. I will pray for you everyday, My Love..........
I will think of you tonight, cos I no dey by your side, just for a little while, but know that am alright, and I will see you soon, make you wait for me my dear
Na runtse idona, sannan for the first time tun tafiyarsa, hawaye suka gangaro kan kuncina
Episode Twenty five: The Eclipse
Kuka nayi sosai ni kadai babu mai rarrashina. Saida nayi na gaji dan kaina nayi shiru. Na kashe radion na chire CD din na fito daga motar. Ta kofar baya na shiga gidan saboda bana son ganin kowa. Direct saman mu na hau na shiga daki na turo kofa. Na zauna a kan gado ina kallon rubutun jikin CD din. I LOVE YOU. Nasan Ibrahim yana sona but how much? Ni a tunani na in kana son mutum zaka so ka kasance tare dashi, ya kamata ace komai runtsi komai tsanani ace muna tare, we can face anything together. Amma yanzu ya tafi, ya kuma kashe wayarsa ma'ana baya son magana da ni, sannan kuma yace min I love you?. What kind of love is this?. Na jawo kafafuwa na na dora akan gadon da dunkule a guri daya. I wish sanda ya fara cewa yana sona nace masa no, da ban saba dashi ba ballantana har inyi kewarsa. Da yanzu bana jin radadin da nake ji a zuciya ta. Na saka hannuna na jawo bargo na kudunduna. Wa yace da Ibrahim na damu da kudinsa ko rashin kudinsa? As long as we are together, that's the only thing I want. A hankali na mayar da idanuna na rufe.
Kaina ne yake bala'in sara min, idanuwa na sunyi min nauyi. Da kyar na motsa ido na ina son in bude su amma na kasa. Muryar mommy naji can nesa tana cewa "Moon3" na motsa bakina amma na kasa magana. Can nesa naji daada tana to fa min adduoi sai kuma naji kukan mommy kasa-kasa. To ita mommy mai ya sakata kuka? Ko har yanzu zancen da daddy yayi mana ne a ranta? Ita kuma daada me ya kawo ta dakin mu? Ita da bata shigowa part din mu in har daddy yana nan. Na tattaro dukkan karfina na bude ido na dan in tabbatar me yake faruwa. Ga mamakina sai naga dakin ya chanza min, ya koma kamar dakin asibiti, ga ledar ruwa nan a sakale a kusa da gadon da nake kuma daga dukkan alama ni ake karawa ruwan saboda igiyar hannuna ta shiga. Mommy tana zaune akan kujera a kusa dani ta jingina kanta a jikin daada wacce take tsaye a kusa da ita tana lallashinta. Dama mommy ta saba, in dai wani a cikin mu bashi da lafiya to ta ringa kuka kenan har sai ya warke. Na kalli daya side din gadon. Hafsat ce a zaune a zabga tagumi fuskar ta da alamar damuwa. To da gaske ni ce bani da lafiyar kenan tunda nice a kwance. A hankali na furta "mommy" ta dago jajayen idanuwanta ta kalleni sannan ta kalli daada wacce itama ni take kallo. Gaba daya suka karaso kusa dani mommy ta rike hannuna mai dauke da drip. Nace "mommy wai bani da lafiya ne?"da sauri mommy tace "lafiyar ki kalau my daughter, kawai zazzabi ne kike yi, maybe ma malaria ce" mommy bata iya karya ba dan haka tana fada na gane ba haka bane. Hafsat ta fita sai gasu sun dawo tare da likita. Dan matashin saurayi ne haka dogo marar kiba. Ina ganin sa gaba na ya fadi. Ibrahim. This is not Ibrahim. Ibrahim is gone. Na rintse idona kaina yana cigaba da sara wa. Doctor din ya auna ni yace "zan sake yi mata allurar bacci saboda ciwon kan, kar a tasheta sai ta tashi da kanta, in ta tashi sai mu sake gwada jinin nata mu gani in ya sauka" what? Me likitan nan yake nufi in jini na ya sauka? Yaushe ya hau ballantana ya sauka? Shigar allura naji a cinyar hannuna daga nan kuma shikenan.
Sanda na sake bude ido na mommy na sake gani a zaune a inda take, amma ta chanza kaya, fuskarta harda kwalliya. Da sauri tazo kusa dani ta zauna tana murmushi. "Sannu Moon, ya jikin naki?" Nima nayi mata murmushi nace "da sauki mommy" ta dauki wayarta tana waya, daga alama Ya Walid ta kira, naji tana ce masa na farka su shigo. Ba'a jima ba sai gasu complete har daddy. Duk sunyi kwalliya kuma kowa da murmushi a fuskarsa. Nan da nan dakin ya hargitse da hayaniya kowa a cikin su na kokarin jawo attention dina zuwa wajensa. Daddy ne ya, dauko wata sabuwar system kirar apple, red colour, yace "surprise!!" Ya miko min, na tashi zaune da sauri, ciwon kan ya ragu sosai, na karba ina godiya, yace "get well soon sunshine" sannan yayi min kiss a goshina, the same spot da Ibrahim yayi min ranar da zamu rabu. Ya Habeeb ya tabe fuska kamar mai shagwaba yace "gaskiya nima bara in zo in fara rashin lafiya tunda har gift ake bawa mutun in bashi da lafiya" gaba daya suka yi dariya, nima nayi murmushi. Mommy ta dauko wayarta ta zagayo ta bayana tace "selfie" nan da nan duk suka taho kowa yana zuro guskarsa, faruk har da hawowa kan gadon da nake ya kwanta a jikina. Mommy ta nuna min hoton tace "look moon, duk ke kika chinye hoton" na karbi wayar na duba, sam banyi kyau ba, bakina duk a bushe, fuskata tayi fari tas kamar babu jini, gashina duk a tarwatse ga idona ya fada ciki kamar nayi sati a kwance. Na kalle su daya bayan daya duk suna min murmushi, na gane me sukeyi, they are trying to cheer me up saboda jini na daya hau ya sauka. They love me so much and I love them too. They mean more to me than Ibrahim ever will.
Har dare suna nan. Anan duk suka ci abincin dare. Sai lokacin na fahimci kwana na biyu a asibitin. Mommy da kanta tayi min wanka da ruwa mai zafi dan inji karfin jikina, ta shafa min mai ta chanza min kaya, ta bani kunun gyada mai zafi ta saka dole sai da na shanye cup daya. Sosai naji dadin jikina. Mommy ce ta kwana a gurina. Da daddare ta saka ni duk saida na rama sallolin da ake bina sanda nake bacci. Washegari da safe doctor yazo ya auna ni yace jinin ya sauka sosai, zasu rikeni zuwa yamma su gani, in bai kuma hawa ba sai su sallameni.
Bayan an sallame ni mun koma gida ma haka ce ta kasance, dan mommy dawowa tayi dakin mu muke kwana tare. Tace barin mu da take yi mu kadai ne ya saka nake tunani har jini na ya hau. Daddy kuma kullum sai ya shigo kafin ya fita, in ya dawo ma sai ya shigo. Kwana na biyu a gida na warke sosai, babu ciwon kan sam kuma tunanin ma ya ragu, dan sam ba'a barina ni kadai. A week after that daddy ya sake kiran mu palonsa. Muna zuwa muka tarar dashi da mommy a zaune, ya Walid da Ya Habeeb ma duk suna zaune a kasa. Muna zama sai ga Faruk shima ya shigo. Ya Walid yayi mana addu'a muka shafa. Daddy yayi gyaran murya yace "kamar yadda na gaya muku wancan zaman cewa zan neme ku bayan sati daya, rashin lafiyar moon ce ta saka har muka yi delaying zaman. Yanzu ina son in gaya miki wani abu moon, ba fa matsa miki nayi nace sai kinyi aure ba, ra'ayinki nake so inji. Kuma gashi naga har yau shi wanda nayi miki magana akansa bai zo ba, kuma ko a asibiti ban ganshi ba. Ina so inji kunyi magana dashi ne? Nayi shiru can na dago kaina nace a nutse "daddy munyi magana dashi amma na fahinci cewa he is not serious akan maganar, dan haka nima na yanke shawarar zan fara karatu na first kafin inyi aure" murmushi ne ya bayyana a fuskar mommy tace "Alhamdulillah, kafin ki gama karatu kuma insha Allah kin samu wani" ni dai na sauke kaina kasa bance komai ba. Daddy yace "to Alhamdulillah, hakan ma yayi, Allah yasa haka shi yafi alkhairi. That been said, ni da mommyn ku mun yanke shawara, tunda Walid da Habibi suna karatu a England, ga Hafsat da Moon suma sunce karatu zasuyi, to zamu tattara gabaki daya zamu koma England da zama. Dama tunda nazo nake ta chuku2n yadda za'ayi min transfer daga kasar da nake yanzu zuwa England kuma Alhamdulillah jiya aka tabbatar min da samuwar transfer di ta, mommyn ku kuwa ta rubuta leave of absence a office dinta har sai ranar da Allah ya sa muka dawo Nigeria. Faruk shi kuma tunda saura shekara daya ya kammala sec school zamu barshi anan shi da daada har sai ya kammala tukun sai ya bi mu can" tunda ya fara maganar komawa England gaba daya palon ya hargitse, kowa murna. Ni ina zaune kawai ina kallonsu suna ta tsalle suna rungume juna, at the same time ina assessing maganar daddy. Tsam na zame jikina na bar palon na hau saman mu, kofar balcony na bude na fita waje na kama railers ina kallon exact gurin da naga Ibrahim last. Dear Ibrahim, when are you coming back? Dole na san sai na bar Nigeria. Tunani na anan shine, what if Ibrahim ya dawo ya tarar bana kasar? Ta yaya zaiyi contacting dina? Na zauna na danyi tunani kadan sai na dauko takarda da biro na fara rubutu kamar haka:
Dearest Ibrahim
I may not be around when you come back. Please give the man who gave you this letter your new phone number and I will call you.
I miss you
Maimunatu.
Na ninke takardar na saka a envelope nayi sealing. Sai da naga babu mutane a compound din gidan sannan na fita na tafi gurin baba Habu mai gadi. Tun da daddy ya gina gidannan ya saka baba Habu gadi kuma har yau shine yake bude gate da rufewa. Ina zuwa na ganshi a zaune a kan benci shi kadai. Na zauna a gefensa na gaishe shi, ya amsa min da fara'arsa. Nace "baba yanzu kuwa zaka iya gane wanda ya kawo maka sako rannan yace ka bani?" Da saurinsa yace "sosai ma kuwa. Ai ina da mantuwa amma kuma ina da gane mutane" na dauko takardar hannuna na mika masa nace "baba dan Allah gashi, duk sanda yazo in bana nan ka bashi kace injini, zai baka sako ka bani. Baba dan Allah kar ka manta" ya kalleni da alamar tambaya a fuskarsa amma ya daure ya ce "in sha Allah mai sunan daada, kar kiji komai" nayi masa godiya na koma cikin gida.
Shirye shirye akeyi sosai na komawar mu England, daddy yace yana so mu je 'yalleman muyi musu sati daya kafin mu tafi, duk da dai zamu ke zuwa Nigeria in mun sami hutu.
Kafin tafiyar mu sai ga sako daga former school din mu ana gayyatar mu taron speech and prize giving day da graduation party da school ta shiryawa 'yan set din mu. Hafsat tana ta murna ni kuma nace bazanje ba. Mommy tayi tayi dani inje saboda da akwai awards da za'a bani kuma ko ba komai ai zanga friends dina za muyi sallama tunda ba lallai mu kuma haduwa da wadansu ba, ga pics da video da za'ayi na tarihi. Hafsat kamar zatayi kuka tana roko na akan inje amma naki nace har yanzu bana jin dadin jikina. Su basu san abinda yasa naki zuwa ba. I don't want to bring back the memories, which is exactly what will happen idan naje. Ina kallo Hafsat taci kalliya kamar ba gobe ta tafi, na bata sakon ta gaishe min da kowa kuma ta karbo min gift dina. Suna tafiya na koma balcony na zauna ina kallon hanyar da Ibrahim yabi. We made so many plans for our graduation party. Ibrahim cewa yayi zai yi mana anko ni da shi mu saka ranar. Nayi murmushin takaici ina tausayin Hafsat akan irin tambayoyin da zata sha a gurin 'yan ajin mu in sunga babu ni babu shi. Haka staff ma, dan kusan kowa yasan abinda yake tsakanina dashi. Na sake yin wani murmushin dana tuno yau shine exactly two years da haduwa ta dashi. Yanzu gashi mun rabu kuma ko hotonsa bani da shi, amma ina da permanent picture dinsa a zuciya ta. A hankali na furta a fili "Happy Anniversary Ibrahim
Episode Twenty Six: A Step Further Away
Basu dawo ba sai daf da Magrib. Suka dawo da kaya niki niki. Hafsat ta zauna tana bani labari kamar zata ari baki "gaskiya Moon kin yi missing, kowa yazo kuma kowa sai ya tambaye ki" nayi murmushi kawai, a raina ina cewa Hafsat ba za ki gane ba. A lokacin ne mommy take cemin an bawa Amira scholarship award dina, na tambayi Hafsat nace "ya Amira tayi kuwa da aka bata?" Hafsat ta tabe baki tace "kema kinsan ya tayi ai, she first said it is a mistake, sai da pc ta kira su ita da maman ta tayi musu bayani cewa it is a gift from you, baki ga maman ba har da hawaye tana yi wa mommy godiya. Ni fa banji dadi ba Moon, you are too soft wallahi, wai duk abinda yarinyar nan tayi miki amma shine zaki wani bar mata scholarship award dinki" mommy ta dan bata rai tace "me Amiran tayi wa Moon?" Hafsat tayi sauri tace "it is nothing mommy, wani small girl issue ne kuma munyi solving tun a school" daga gani kasan mommy ba ta yarda da bayanin Hafsat ba, kawai dai tayi shiru ne. Nan suka dauko min gifts dina suka nuna min. Duk a ciki guda biyu sunfi birgeni, na farko medal din da school ta bani, na glass ne me kauri, a ciki anyi rubutu da golden colour kamar haka:
Award of Excellency
To
Maimoon Muhammad Dikko
For being the most talented student this school has ever had.
Na biyu kuma students ne suka bani, shi kuma da wood suka hada shi, a tsakiya sun yi zanen moon, a kasa kuma suka rubuta:
Thank you Moon for brightening our lives. We will forever miss u.
Kawai sai naji hawaye a ido na. Hafsat ta dauko wayarta ta nuna min video da 'yan set din mu suka yi suka ce a nuna min. Duk sunyi kwalliya kuma they are all laughing and talking at the same time. "Moon ashe baki da lafiya? We miss you today, kinga gifts dinki?...... " ina dariya kuma ina hawaye at the same time, can wata a videon tace "Moon shine kika rike mana uncle kika hana shi zuwa ko? Hafsat tace yana can yana jinyar ki, ki gaishe ki kice we miss him also" na kalli Hafsat ita kuma ta daga kafada. Wato karya tayi musu tace muna tare da Ibrahim shi yasa basu ganshi ba. Class monitor din mu Hamidda ta hada min take away na duk abinda aka ci a gurin party da handwritten note na get well soon.
A ranar da daddare sai ga Amira da mamanta sunzo yimin godiya har gida, mommy ta kaisu gurin daddy shi ma suka yi masa godiya. Daga nan muka tafi dakinmu muna hira, anan muka ba ta labarin tafiyar mu England, yanda tayi da fuskarta kamar zatayi kuka. Nace mata "Amira ni ina ganin ki cike Oxford kawai sai mu tafi tare, kinga sai ki zauna a gidan mu muke zuwa makaranta tare" ta girgiza kanta idonta fal kwalla tace "I can't. Mama bata da kowa a garin nan sai ni. Bazan iya barin Nigeria in barta ita kadai ba. University of Abuja zan saka saboda in zauna a gida. I wish you guys best of luck in England, in kun je please ku kira ni saboda in samu number dinku ta can" nace mata "insha Allah, you will be among the first ones da zan kira" Haka muka yi ta hira har sai da suka zo tafiya. Casually ta tambayeni "ya labarin uncle din mu kuwa? Naga shima baije partyn mu ba" na kalleta sai ta sunkuyar da kai. Hafsat ce ta gaya mata yayi directly "yayi resigning daga aikin sa ya koma Ibadan" ina kallon fuskarta ta chanza kala lokaci daya "but you are in contact right?" Hafsat tayi sauri tace "What is it to you, in suna fa contact?" Na dakatar da Hafsat da naga ta fara daukan zafi, nan na bawa Amira labarin duk abinda ya faru, na kara da cewa "I believe He will come back like he promised" Hafsat ta ja tsaki tace "wahala da rai" tun daga nan Amira bata kara cewa komai ba har suka tafi"
Washegari muka tafi "yalleman, satin mu guda acan kamar yadda daddy yace. Amina cousin din mu da muke kusan sa'anni sati daya na bata, ta dage lallai sai ta bimu England da kyar daddy ya lallabata yace ta bari in ta gama sec sch za'a mayar da ita can. Mun shaku da Amina sosai dan bayan Hafsat, ita ce kamar second sister dina, bayan kasancewar mu sa'anni, muna kama da ita, dan idan naje 'yalleman cemin ake yi Hassanar Amina.
Muna dawowa Abuja muka fara shirin tafiya England. Muka yi sallama ta duk makota, muka hada hada personal kayayyakin mu, duk da dai daddy yace kar mu dauki kayan sawa tunda zamu ke zuwa Nigeria, in mun je can ma sayi wadansu. Duk da cewa na zama busy a kwanakin nan amma komai nakeyi sai inji irin feeling dinnan da mutun yake ji idan ya manta baiyi wani abu mai muhimmanci ba. Ibrahim is always there tugging at my mind. Ranar da zamu tafi muka su Faruk da daada suka raka mu airport, faruk har da kukansa muna ta tsokanarsa. Muka shiga jirgi, mommy tana kusa da daddy, ya Walid da Hafsat, ni da Ya Habeeb. Jirgin mu yana tashi na kalli window, ina kallon Nigeria a hankali gajimare yana rufe ta tana bacewa. "Goodbye Ibrahim". Na fada a hankali knowing now I am a step further away from him. Na saka earpiece, na lumshe ido na na jingina kaina a jikin headrest din seat dina yayin da jirgin mu ya cigaba da lulukawa sararin samaniya. This journey is like a transition in my life
Episode Twenty Eight : University of Oxford
Karfe dayan dare jirgin mu ya sauka a birnin London. Tuni motoci masu dauke da tutar Nigeria masu fenti kalar kayan sojojin Nigeria suna jiran mu. Muna sauka suka dauke mu sai embassy. A cikin embassy din anan gidan da zamu zauna yake. Gate daya ne zaka shiga, sai ka wuce offices din su daddy sannan sai gidan, sai kuma gidajen sauran manyan staff na embassy din. Gidan katon gaske ne, dan kusan girman su daya da gidan mu na Abuja with exception of part din su inna da na daada. Amma wannan gidan yafi wancan haduwa, it makes me wonder dama Nigeria muna da irin wannan arzikin? Ko dan kawai muyi show up ne a duniya a dauka babu talauci a Nigeria? Wato rayuwa a Nigeria kamar kashin dankali ce, manya su suke danne kanana. Komai a gidan computerized ne, ko wacce kofa sai tayi detecting finger print sannan zata bude, dan haka dole a daren akayi uploading finger prints din mu. Part din mu ni da Hafsat kowa da dakinsa, falo daya, kitchen daya amma mommy tace sam sai dai mu rufe daki daya mu zauna tare, kitchen din ma tace a rufe, mu ringa zuwa main dining room muna cin abinci tare dasu. Mommy da daddy part din su daya, ya Walid da ya Habeeb ma haka. Sai kuma main palo wanda yayi connecting duk parts din.
Washegari da yamma muka fita shopping muka siyo kayan amfanin mu kaf, tun daga kan sutura, toiletries, cosmetics da sauran tarkace. Daddy tun yana biyan cash har ya dawo using credit card, daga baya yace "kai yaran nan so kuke kuga gudun ruwa na ko? To ya isa haka" mommy tana yi masa dariya tace "kai fa kace kar su taho da komai zaka saya musu anan, duk wanda ya sayi rariya kuwa ai yasan zata zubar da ruwa" ni da Hafsat dogayen riguna mommy ta sa muka dauka saboda zuwa makaranta, tace bata son shigar english wear, kar muga muna England muce muma mun zama turawa, mun dauki english wears din dai amma saboda sakawa a gida. Mun sayo sababbin sim cards muka saka a wayoyin mu muka cire na Nigeria muka ajiye. Nan muka fara kiran 'yan'uwa da abokan arziki muna basu numbers din mu. Kamar yadda nayi alkawari, Amira tana daga cikin na farkon dana kira.
A week after zuwan mu England aka fara maganar school din mu, ni dama daddy yasan me nake so, neurology, Hafsat aka tambayeta tace itama medicine din take so bangaren gynecology. Har daddy yace mu tafi sai nace "daddy, ina so kuma in dau some courses on psychology" yayi shiru kafin yace "anya Moon abin ba zai yi miki yawa ba? Medicine is not easy on it's own sannan kice zaki kara da wani abun kuma?" Nayi shiru bance komai ba, yace "OK, I will see what I can do, normally ba'a barin students su dau courses out of their field, amma tunda psychology is some how related to medicine zan nema miki" nayi godiya muka tashi muka tafi. Muna zuwa falon mu Hafsat ta fara tambayata "ke kuwa me yasa kike son yin psychology?" Nace "I want to know exactly what people are thinking, I want to be able to tell if someone is lying or not" tayi shiru sannan tace "is this about Ibrahim?" Nace "partly, yes"
Tunda muka koma England,duk sati sai na kira baba Habu maigadin mu na Abuja na tambayeshi ko Ibrahim yazo? Kuma duk sati amsar daya ce "bai zo ba tukun" rannan ina kiran sa kafin inyi magana yace "mai sunan daada" gaba na ya fadi nace "na'am baba" yace "indai har da gaske yana sonki zaizo, ni kuma in yazo zan bashi sakonki kuma zan kira ki in gaya miki yazo har in baki shi ma ku gaisa, idan kin ga bai zo ba, to ba son gaskiya yake miki ba ko kuma Allah bai kaddara alakar da take tsakanin ku mai dorewa ce ba, ki kwantar da hankalin ki, ki manta da batun sa, kiyi karatun ki" jikina naji duk yayi sanyi, kirjina yayi nauyi, nasan gaskiya baba Habu ya gaya min amma anya kuwa zan iya? Murya a sanyaye nace "nagode baba" daga nan ya kashe wayar.
Mun kama karatu sosai. Ita kanta makarantar abar kallo ce, dan zan iya cewa gari guda ce, with its ancient buildings, kowanne faculty kamar unguwa guda ne, dan saida daddy ya bamu maps yace muke tafiya dashi saboda kar mu bata. School of medicine duka muke ni da Hafsat, kuma first year komai tare za'ayi mana tunda kamar introductory courses ne, daga third semester kuma zuwa sixth kowa zai dauki individual courses din field dinsa, shekara ta hudu da ta biyar kuma zamuyi clinicals, kamar practical kenan inda zamu tafi asibitoci muna koyon aiki a gurin kwararrun likitoci, shekara ta shida kuma project. Tsarin makarantar tsari ne me kyau, lecturers dinsu sunsan me sukeyi, ga kayan aiki nan kamar banza, a raina nace dole a kira ta da second best university in the world.
Tunda muka fara lectures kawai sai naji nayi loosing interest a karatun, sam bana gane me akeyi. Ina shiga lecture hall zan tafi seat din baya in zauna in yi ta sake sake a raina ina tuno rayuwar sec sch din mu, sai inji gaba daya hankali na ya koma Nigeria. Sometimes sai inke ganin kamar a class din mu muke, Ibrahim zai iya shigowa anytime. Wani lokacin kuma sai inji kamar kamshin turarensa sai inyi ta waige waige. Duk sanda wani yazo yana son yayi min magana sai inji kamar Ibrahim yana kallona da lumsassun idanuwansa. It is like he is watching me. Sau da yawa in mun shiga lectures sai in kwanta inyi ta bacci har sai an gama sannan Hafsat ta tashe ni. Hafsat tayi fadan, tayi nasihar amma ina, sai da tace zata gayawa mommy bacci nake a class sannan na daina baccin amma still attention dina baya gurina. It is a million miles away. Only time da nake zama inji lecture sai a psychology courses dina. In homework aka bayar sai dai Hafsat tayi mana, kullum tayi ta min gori tana yimin bala'i amma bazan yi ba. It is as if spirit dina na karatu is gone.
A haka muka gama first semester, lokacin exams ma da kyar Hafsat ta tirsasa ni na danyi karatu tana koyamin wasu abubuwan. Hutun da aka bamu babu yawa dan haka daddy yace ba zamu je Nigeria ba, ranar har zazzabi nayi, mommy ta ga ciwona yana kokarin tashi ta kwashe mu muka tafi yawo banda daddy sai security daya hada mu dasu. Mune gari gari, duk garin da muka je sai mu samu hotel mu kwana, mune zuwa kallon London bridge, mune har Scotland da Wales. Na saki raina sosai nayi enjoying time dina.
Hutun mu yana karewa muka dawo gida. Muka cigaba da zuwa makaranta. Har yanzu bani da kawa ko aboki, in fact da yawa daga 'yan ajin mu basu sanni ba, wadanda duka sanni ma suna referring to me as Hafsat's sister, dan basu san suna na ba. It is like am afraid to get attached. Duk abinda akeyi daddy bai sani ba, tunda basu kafe result ba sunce sai at the end of the session. Mommy kuma tunda a gida ina nuna bani da wani problem itama bata taba tunanin ina da problem a karatuna ba. Ni dai kullum lissafin sanda zamu yi hutun session nake yi, dan wannan karon nayi alkawarin bincike zanyi sosai sai na nemo Ibrahim na gaya masa daddy yace bai damu ko wanne kabila ne shi ba, bai kuma damu da cewa he is not wealthy ba, gani nake yi hakan ne kawai zai saka ni in maida hankali na akan karatu na.
Second semester tana karewa aka fitar da result na both semesters din. Tunda Hafsat ta gayamin gaba na yake faduwa, nasan ban aikata abin kirki ba. Allah Allah nake mu tafi Nigeria kafin daddy yaga result dina in yaso in mun dawo ayi wacce za'ayi. Adduah ta bata karbu ba dan washegarin da aka kafe result muna main palo muna kallo sai mommy ta kira Hafsat tace muzo daddy yana kiran mu. Muna shiga palon su na san daddy yaga result dina. Bantaba ganin bacin rai a fuskarsa irin na ranar ba. Muna zama su yaya Walid suka shigo da fara'arsu, ganin yanayin fuskar daddy suma suka shiga taitayinsu. Muna zama ya jeho min takardar hannunsa yace "pick it up" hannu na rawa na dauka, yace "bude ki karanta a fili inji" nan na bude na fara karanta sakamakona. Tun daga first semester har second bani da B ballantana A. Mostly C ne har da D. Nan daddy ya fara fada, ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, tun ina daurewa har na fara kuka. Yayi min wankin babban bargo mommy ta dora a inda ya tsaya. Su bakin cikin su shine sunsan ina da kokarin kawai karatun ne suke ganin banyi niyyar yi ba. Nan daddy yace dole ayi punishing dina akan abinda na aikata. Yace "punishment dinki shine, no holiday for you. Zaki zauna ke kadai a England ba zamu tafi dake Nigeria ba. Use the time to think about what you have done to your life. Sannan kiyi karatu so that you can catch up a inda aka barki a baya" daga haka ya mike ya shige cikin bedroom dinsa ya turo kofa
Episode Twenty Nine: The Message
Kowa a palon yayi shiru, hatta ni da nake kuka nayi shiru ina assessing me daddy yace. It then dawn on me suddenly cewa yana nufin bazan je Nigeria ba. Ai kuwa da gudu na mike na nufi kofar dakinsa ina kuka ina "daddy dan girman Allah kayi hakuri, daddy na tuba please" amma ko motsin sa banji ba, nan na durkushe a gurin ina faman gumurzun kuka. Hafsat ce tazo ta kamani ta mayar dani falo. Na zauna a kasa na kifa kaina a cinyoyina ina cigaba da kuka. Hafsat tace "mommy please do something" mommy wacce itama daga dukkan alamu hukuncin na daddy ya bata mamaki, tayj ajjiyar zuciya tace "yayi fushi sosai, and she deserves to be punished" ya Walid yayi sauri yace "amma mommy kunsan fa yarinyar nan ba lafiya ce ta ishe taba, ta yaya za'ace mu tafi mu barta ita kadai thousands of miles away? Ni dai mommy idan daddy yaki yarda a tafi da ita zan zauna anan nima, kice masa ina harkar wani project and I need to stay in town" mommy ta harare shi tace "kana tunanin he will buy that, duk harkar karatunku babu abinda bai sani ba, yasan cewa babu wani project da kake yi" ya Habeeb yace "at least mommy try something, ba za a bar maganar nan kawai ace shikenan ba" ni daj duk ina jinsu bance komai ba, kuma ban daina kuka ba. Mommy ta mike tace "ina zuwa" sai da naji mommy ta shiga dakin daddy sannan na dago kaina ina goge hawayena. Tun muna yara nasan sau da yawa mu na cewa mommy tana da magic, duk sanda ka tambayi daddy wani abu yace no, to in ka samu mommy tace yes, daga ta shiga dakin daddy ta fito shikenan sai kaji shima yace yes din. A lokacin yarinta sai muke cewa magic ne take yi masa. Mun jima a zaune ba wanda yake yin magana, ni dai in banda sunayen Allah babu abinda nake kira "please God intervene, bana jin zuciya ta zata iya daukan wannan hukuncin" it has already been a year rabo na da Nigeria, da Ibrahim, i just want to know if he is ok. Bude kofar mommy ne ya dawo dani daga tunani na. Fuskarta kawai na kalla nasan cewa wannan magic din baiyi nasara ba. Tana zama na rarrafa gurinta na dora kaina a chinyar ta na cigaba da rusa kuka na. Bata rarrashe ni ba ta fara magana. "Moon, you will be left behind. Zaki zauna kiyi karatu for two months, zai shiga makaranta ya karbo miki textbooks na courses din da kuka yi last session wadanda zaki karanta. Kowanne textbook zaki rubuta formal report akansa in mun dawo zaki wa daddyn ki submitting shi kuma zai kai department din ku with hope zaku kara miki grades dinki. Za'a bar securities, you are not to leave this building har sai mun dawo, za'a bar miki david, chief bodyguard din daddy, duk abinda kike so a cikin gari ki gaya masa zai siyo miki. Cooks da sauran servants duk zasu zauna suna kula da ke da gida. Za'a dauko miki nurse din da zata ke zuwa tana kwana dake, kuma zata ke gwada bp dinki three times aday. A clinic din embassy take" ta juya wajan ya Walid tace "bai yarda da zaman ka ba anan. Saboda bai yarda ya barku daga kai sai moon ba. Nima kuma ban yarda ba" tana gama fadin haka ta mike ta shige daki. Knowing mommy, nasan kuka zata je tayi.
Haka abin ya kasance, textbooks kwali biyu daddy ya lode min wai duk ni zan karanta. Ina kallon su suna ta shirye shiryen tafiya banda ni. Da assuba jirgin su zai tashi dan haka tun cikin dare su ka tashi suna ta wanka da shiryawa. Inajin Hafsat ta na shiryawa nayi banza da ita nayi kamar bacci nake yi. Ta zo ta tsaya a gaban gadon da nake tace, "Moon I am going" na kalle ta kawai bance mata komai ba. Ta sha bakaken kaya da wani bakin glass a fuskar ta. Nasan ta saka glass din ne sano da kar inga kukan ta, she is too proud to let me see her tears. Tunda aka haife ni muke tare da Hafsat, bana jin mun taba sati daya ba tare ba. Yanzu gashi zamuyi two months ba tare ba. Tace "zan yi iyakacin kokarina inga na samo miki news" na gane maganar da take yi, a hankali nace "thank you" daga haka ta juya ta fita tare da rufe ko fa. Ina nan dai a kwance naji anyi knocking kofar sannan aka bude a hankali. Kamshin turaren daddy naji nayi sauri na rufe idona. Ya jima a tsaye yana kallona sannan naji ya hawo gadon yayi kissing dina a goshi sai kuma naji ya sauka ya rufe kofa. Hawaye naji yana zuba daga idona masu zafi. Next ya Habeeb ne yazo da dariyar sa yana ta tsokana ta wai daddy so yake na zama prof kafin su dawo. Sai da ya fahimci cewa am not in the mood for wasa sannan ya rabu dani sai ga mommy nan ta shigo itama, complete ta gama shiryawa dan harda handbag dinta a hannunta. Ina ganin ta naje na rungume ta ina cewa "mommy dan Allah kice daddy ya bar ki su su tafi" ta girgiza kanta tace "kema kinsan hakan ba zai yiwu ba, kiyi abinda yace miki shine mafi alkhairi a gareki, kinsan dan yana sonki yayi hakan ba wai dan yana kinki ba, in mun barki ba karatu ai bamuyi miki gata ba. Kuma yace in dai har ba kici 70% a report din da zaki rubuta ba to next holiday ma ba zaki je ba. Take care of yourself, do as u are instructed and you will be fine" daga nan tayi min kiss a cheek dina ta fita. Na durkushe a gurin zuciyata tana yimin zafi, ina jin tashin motar su amma na kasa lekawa har suka tafi.
Tunda suka tafi ko palo ban leka ba har bayan magrib. Ina kwance a kan gado sai dai in tashi inyi sallah in kuma komawa in kwanta. Bayan magrib ne naji ana knocking kofar bedroom din, da sauri na tashi ina tunanin ko daddy ya chanza shawara an bar wani a cikinsu. Ina bude kofar naga wata mata da kayan nurses a jikin ta tana murmushi tace "good evening, my name is... " kafin ta karasa nace cikin tsawa "go away" tare da banko kofar na rufe. Sai wajan karfe goma na bude dakin na fito shima azababbiyar yunwa ce ta dameni, ina fitowa naga abinci a jere akan center table din palon, na wuce na bude fridge na dauko fresh milk na koma daki. Washegari da sassafe yunwa ta addabeni na fito palon na sake ganin breakfast a ajjiye, naje na zauna na fara hada tea, ina cikin sha naji an bude kofar extra dakin da yake kusa da nawa, wannan nurse din ta jiya ce ta fito, kallo daya na yi mata na dauke kai, tazo inda nake tace min "good morning, my name is Victoria, your father asked me to take care of you" nace " OK " ba tare da na kalle ta ba. Har ta juya zata tafi sai kuma naji babu dadi a raina tunda ni ban iya wulakanta mutane ba, kuma ba laifin ta bane aka tafi aka barni ba, na kira ta nace "zo muci abinci" tace ok, tazo mukayi breakfast tare, sannan ta gwada bp na tayi recording, daga nan ta fice ta tafi office dinta. 12 ta dawo da sake gwada bp na ta fita, ina nan dai zaune ni kadai kuma naki bude kwalin books din ballantana in fara karatu, har six din yamma, sai ga Victoria ta shigo tace "I have gift for you" sai ta dauko wadansu CDs na movies har guda biyar ta miko min, tace "since you don't have interest in reading book, i thought maybe you will like watching movies" na karba nayi mata godiya sosai. Nan da nan na fara kallon movies din. Duk kannin su akan likitanci ne, suna koyar da harkar medicine amma a cikin labari, ranar kwana nayi banyi bacci ba ina kallo, sosai naji interest dina yana dawowa akan karatu. Washegari nace ta kawo min wadansu films din, da rana kuwa da zata zo sai gasu ta karo min wasu, sam bata takura min akan inyi karatu ba amma tana ta gayamin amfanin karatun da, dadinsa. As a doctor zaka zama kana saving life din mutane, babu wani feeling din da yafi, dadi akan ace someone is alive because of you. Da yamma ta dawo tace inzo mu fita yawo, muka fita muka zagaya cikin embassy din, duk wanda muka hadu dashi sai sun gaisa sai ta gaya masa ko ni wacece. Ina kallon David yana bin mu duk inda mukayi.
Five days muna tare da Victoria, da yake bani da wahalar sabo nan da nan muka saba. Har yanzu dai ban fara karatu ba amma sosai ina jin son karatun a raina, kuma bp dina is great. Ranar kwana na biyar din ina daki ina kallon daya daga cikin movies din da victoria take kallo sai na ji kamar motsi a main palo, gaba na ya fadi tunda nasan sai 12 Victoria take zuwa. Na tashi a hankali na dan bude kofar palon mu na leka, kawai sai ganin daada nayi a tsaye tana ta kalle kalle, can kuma sai ta takarkare ta rangada sallama "salamu alaikum" ai bansan sanda na fita da gudu na rungume ta ba, kafin in gama recovering daga shock din ganin daada a palo sai ga Faruk da Amina sun shigo suna jan akwatinan su. Nan na saki daada na je na rungume su a tare, har da kwallar murna a ido na.
Sai da muka gama murnar ganin juna sannan daada take gaya min cewa ai bayan su mommy sunje Nigeria ta tuburewa daddy lallai idan bai bar su daada sun taho wajena ba to ita zata dawo. Inna kuwa tana jin labarin abinda ya faru tace lallai ya kira David ya gaya masa ya sako ni a next plight in taho gida, shine yace mata ai ya zai turo su daada su zauna a gurina. Ita kuma Amina tana jin labarin tafiya England tace lallai sai ta biyo su tunda dama daddy yayi mata alkawari, Shine suka taho tare. Naji dadin zuwansu sosai, nan da nan na qara warwarewa, daada ta dage tana ta yimin nigerian dishes da nake missing. Faruk kuwa kullum sai ya fita yawo shi da David, wata rana Amina ta bisu wata rana kuma tayi zamanta. Zuwan su daada bai hana Victoria zuwa ba, ta daina kwana dai amma kullum sai tazo sau biyu ta gwada jinina kuma munyi hira wanda mostly akan harkar karatu ne da kuma harkar medicine. A lokaci daya sai naji hankali na ya karkata a gurin karatu, na zauna na ributa timetable wacce zata bani damar yin karatu for 5hours kullum. Part dinsu daddy nake zuwa inyi karatuna yadda babu wanda zai dameni. Nayi browsing yadda ake rubuta study report, nan take na fara rubutawa.
Sai da su daddy suka yi wata biyu chip a Nigeria sannan suka dawo, ni kuma a lokacin na karantu sosai dan banajin ko Hafsat zata gaya min sanin abubuwan da aka yi mana. Na hada report dina tsaf na kai bedroom din daddy tare da apology letter ina bashi hakurin abin da nayi, da kuma alkawarin bazan sake yi ba.
Ranar da zasu dawo gabadaya muka tafi airport muka taro su, murna a gurina kamar ranar sallah, saboda ba karamin missing din su nayi ba. Ban tambayi Hafsat ko ta samu labarin Ibrahim ba ita ma kuma bata cemin komai ba. Satin su daya da dawowa muka koma school, yanzu an raba mu da Hafsat kowa ya koma bangarensa, amma a yanzu kam Alhamdulillah ina gane karatu na sosai, in an shiga lecture ina zama a gaba kuma ina bada attention dina sosai, kuma sai naji karatun babu wahala tunda duk basic abubuwa na iya su.
A ranar wata Thursday, na riga Hafsat dawowa ina zaune a main palo ni da mommy da Amina sai ga wani security yazo yayi knocking kofa, naje na bude masa sai na ganshi tare da wani mutun. Muka gaisa dasu sai mutumin yace "I have a mail from Nigeria for miss Hafsat" nace masa "bata nan amma zan karba mata" nan ya bani wasu takardu nayi signing sannan ya miko min sakon. Brown envelope ce babba, na shafa ta sai naji kamar takardu ne a ciki. Na koma palo nace da mommy sako aka kawo wa Hafsat amma ban fada mata daga Nigeria bane, hankalinta yana kan kallo dan haka bata kalleni ba, na wuce na shiga part din mu, na ajiye sakon akan bedside table na zauna akan gado, haka kawai sai naji zuciya ta tana ayyana min in bude in ga menene a ciki, can nayi tsaki a raina nace in Hafsat ce aka kawo min sako babu abinda zai hana ta budewa taga menene, dan haka zuciya ta daya na dauko na bare seal din na zazzage contents din akan gado. Wata irin bugawa kirjina yayi saida na dukushe a gurin.
I think this is the longest episode so far. Ko me sakon Hafsat ya qunsa? Me ma i don't know 😝
Episode Thirty : The Final Blow
A hankali na mike na koma kan gadon na zauna ina bin contents din da kallo. Hotuna ne wajan kala ashirin, sai takardu anyi binding dinsu kamar wani project report. Na fara daukan hotunan daya bayan daya ina kalla. Kaina kamar wacce aka shafe min memory na gaba daya, kwakwalwata ta kasa assessing abinda idanu na suke gani. Hoton farko dana fara dauka hoton Ibrahim ne, yana tsaye a kusa da wani masallaci da sallaya a hannunsa, fuskarsa da alamar bacin rai a tare dashi. Na kurawa fuskarsa ido, komai yana nan kamar yadda nasan shi sai duhu da fatar sa tayi, next photo shi dinne dai akan kujera a kofar wani gida a kusa da wani dattijon mutun bayarabe, daga dukkan alamu serious magana suke kuma basu san an dauki hoton ba. Haka nayi ta bin hotunan ina kalla, duk shi ne a ciki, wani shi kadai wani kuma shi da mutane. Na ajiye hoton hannuna kenan idanu na suka gane min wani kati, na dauka a hankali ina karantawa word by word.
Join us in person or in prayer to celebrate the wedding matrimony of our children :
Ibrahim Adeni Oluwaseun
And
Efisowa Olabesi Adebayo
Na duba date din naga about 3 weeks ago. Ido na kafa akan sunan sa kamar mai hopping mistake ne zai automatic correcting kansa, amma ina, it is real, it has happened. And there is nothing I can do about it. Na ajiye card din na dauki sauran pictures din. Wedding pictures ne, picturing Ibrahim and Efi. She is exactly how I remember her, kawai dai ta yi kwalliyar amare ta rufe kurajen fuskarta. Wani hoto na dauka daga shi sai ita da katon cake a gabansu. Sun sha kwalliya. Ita ta saka farar wedding gown mai dogon hannu shi kuma ya saka wata sabuwar shadda dark brown ta sha aiki. Na kalli fuskokin su gaba daya suna dariya. Fuskarsa tana dauke da tsantsar farin ciki. Na kasa daina kallon hoton.
Kofar dakin naji an banko an shigo da sauri. Ban dago kaina ba amma nasan Hafsat ce saboda kamshin turaren ta da naji. Ta karaso da sauri tana cewa "ina saqo na da akace an....... " bata qarasa maganar taba saboda abinda ta gani. Ta tsaya a bakin gadon tana kallon tarkacen da suke kai. A hankali tasa hannu ta dauki IV din sai naga ta yarda shi ta rufe bakinta da hannunta. Na kalli fuskarta naga kamar wadda idanuwanta zasu fado kasa saboda mamaki. Bata cemin komai ba ta fara kallon hotunan da sauri sauri. Na ajiye hoton hannuna na mike na fara cire kayana. Har a lokacin ba zance ga abinda zuciyata take ji ba. Na daura towel zan shi ga toilet naji Hafsat ta kira sunana a hankali "Moon am so sorry, da na san abinda za'a kawo min kenan da ban saka private investigator ya nemo shi. I thought in kika ji labarin halin da yake ciki zaki nutsu ki koma normal life din ki" bance mata komai ba nayi hanyar toilet, ta sake cewa "moon please let's talk about this" na juyo da sauri nace mata "ba abinda kika yi min Hafsat, in fact I am so grateful naga wannan sakon. I just need to be alone for a while" daga haka na shige toilet. Shower na kunna na shiga ciki nayi zaman dirshen ruwan yana zuba a kaina. So karya yayi min sanda yace min zai dawo, dama bashi da niyyar dawowa. Shekara daya kawai. He got married to Efi. Amma ai cemin yayi baya son Efi, ko duk a cikin karerayin daya shirya min ne. Har hawan jini na samu da yarintata saboda shi, nayi watsi da karatuna saboda tunaninsa amma dame zai saka min ? He got married. Married for God's sake. Zafin da nakeji a zuciya ta yayi yawan da hawaye yaki zuwa idanu na. Ruwa mai sanyi ne yake sauka a jiki na amma zafi nake ji kamar ana hura wuta a kirjina. What hurt me the most is the fact that he looks happy. He is happy ya auri Efi. Maybe idan aka ambaci suna na sai ya yi tunani kafin ya tuno ni. Maybe I am just one of the others. Kuka nake so inyi amma hawayen yaki zuwa. Why Ibrahim? Why do you choose me as one of your victims? Na tashi na kashe shower na goge jikina da towel na daura wani na fita. Hafsat tana nan a inda na barta, ta gama kallon hotunan tana karanta report din. Na shafa mai, na dauko wani wando skin tight 3 quater na saka, na dauko riga itama 3 quater, daga sama ta matse ni daga kasa ta bude na saka. Kananan kalba ce a kaina, na tattare su nayi packing dinsu a tsakiyar kaina suka zubo kan kafaduna. Na dauko turare na feshe jikina dashi. Ban kalli Hafsat ba ballantana pictures din da suke gabanta. Har na yi unlucking kofa na kama handle zan bude Hafsat ta yi min magana "what are you going to do?" Na tsaya amma ban juyo ba. Ta sake cewa "look, a cikin report din nan an nuna cewa takura masa akayi ya aure ta, babanta shine ya rike su shida sisters dinsa tun rasuwar babansu, kuma shine ya matsa masa sai da ya aure ta, in fact yana lagos akayi daurin auren ma kawai kiransa akayi yazo akayi biki" kallonta kawai na ke yi fuskata babu expression, na saki kofar na jingina a jikinta na rungume hannuna a kirjina, kamar yadda Ibrahim yake yi, a hankali nace "does that change the fact that he is married?" A hankali tace "no. I just thought it will make you feel better. Look ni ban damu da Ibrahim ba, in fact I don't even like him. Baki da lafiya already bana son wani abin ya kuma samunki a kansa. Please just read this for yourself" na juya na sake kama handle din kofar sannan na juyo da kaina na kalleta nace " I am a psychologist my dear sister, I don't read words written on some pages, I read people, I read minds and this man... " na dawo cikin dakin da sauri na dauki hoton Ibrahim da Efi suna dariya, na cigaba da cewa "this man here is happy, and that's all that I need to know". Na juya na fice daga dakin.
Kitchen na shiga na tarar da cook tana ta aikin dinner, na dauki vegetables na fara yankawa sai ga mommy ta shigo ta tsaya tana kallona saboda ni bamai son girki bace, sam bana shiga kitchen in ba dole ba. Kit na yanke hannuna da wuka, da sauri mommy tazo zata rike hannuna na ja da baya na fice daga kitchen din, ina jin ta tana kirana na bude kofar main palo na fita hannuna yana jini. Har na dau hanyar gate sai na tuna kayan jikina yadda suke sai na dawo na koma cikin palo, ina jin Amina tana yimin magana itama na rabu da ita. Sam bana so ayi min magana. Extra dakin da yake part din mu na shiga, na shiga toilet na wanke ciwon hannuna, na daure shi da handkerchief. Har dare ina dakin ban fito ba kuma har lokacin hawaye bai zubo a idona ba. Nayi sallar magrib da isha, Hafsat ta kawo min abinci tace ta gayawa mommy bana jin dadi, nace mata na gode. Na kwanta amma bacci ya gagari idona sai juyi kawai nake yi. Cikin dare naga ba bacci babu labarinsa, na tashi nayi alwala nazo na fara sallah. Ni kaina bansan raka'a nawa nayi a ranar ba, kuma duk sujjada sai na roki Allah ya chire min Ibrahim daga raina. Har aka yi sallar asuba, nayi sallah na zauna ina azkar anan bacci ya dauke ni. Mommy ta shigo ta dubani taji jikina yayi zafi, nan ta kama fadan me yasa na kwanta ni kadai? Nan da nan aka kirawo Victoria, tana gwada jini na kuwa tace ya hau. Dama nasan haka zata kasance saboda yadda nake jin wani azababben ciwon kai. Mommy ta saka ni a gaba akan lallai sai na gaya mata menene matsala ta amma nayi shiru, fada take kamar zata ari baki. Ni dai na samu akayi min allurar bacci nayi kwanciyata. Ranar wuni nayi a gida ban je school ba. Washe gari Saturday tun safe nace da daddy ina son zuwa bakin ruwa (beach), ya barni saboda yana ganin fresh air zata taimaka min, amma yace mu tafi tare da Hafsat da Amina. Ban so haka ba saboda so nake in zauna inyi tunani. Muna zuwa bance musu qala ba na dau handbag dina nayi gaba, sai da na samu gurin da babu kowa sannan na zauna a kasa ina kallon ruwan.
When was the last time I had a serious conversation with myself? Me ya faru da ni ne? Ina wannan yarinyar 'yar makaranta who is loved by all? Na tuna da medal din da school din mu ta bani, to the most talented student the school has ever had. Ina dreams dina na zama likita in bude private hospital a Nigeria in ringa taimakawa marasa karfi wadanda ba zasu iya zuwa kasar waje ba? My life was so peaceful before kuma ina so ta koma kamar da. Indai har ina so in koma kamar da i have to let go of Ibrahim. Tabbas ya samu guri a zuciyata yadda bazan taba iya goge shi ba, amma zan iya tura shi baya yadda bazan ke tuno shi ba. Tabbas wani barin na zuciyata is 100% sure cewa Ibrahim yana so na amma mai yasa yayi aure? Nasan maganar Hafsat zata iya zama gaskiya cewa takura masa akayi amma still ya kamata ace ya neme ni ya gayamin abinda ya faru, na bar masa sako a gida kuma nasan da yaje da baba Habu ya kira ni ya gaya min. Tunda har bai neme ni ba yana nufin yayi accepting auren kenan, he looks happy in the wedding picture. Duk da ya taba gayamin cewa baya son Efi amma tana da chance din da zata juyo hankalinsa kanta a matsayinta na matarsa. Duk da bani da shekaru da yawa amma nasan maza suna da one weakness, Sex, cikina naji ya hargitsa wani amai ya taso min, sex, kusan wata guda kenan da auren, they might have already done it by now. Da sauri na tashi na fara kwarara amai, Allah ya soni babu kowa a gurin, sai da na gama amai na sannan hawaye ya zo idona, na zauna na saka kaina a tsakanin cinyoyi na nayi kukana mai isata sannan na tashi, naje bakin ruwa na wanke fuskata da bakina. Na dauko handbag dina na bude na fito da hotunan da takardun da aka kawo wa Hafsat, daya bayan daya na ringa jefasu cikin ruwan suna tafiya, ina kallansu suna tafiya a saman ruwa sannan suka fara nutsewa kasan ruwa. Na dauko waya ta na goge numbersa da na ke ta faman ajjiya, na shiga messages duk na goge messages dinsa da na kasa gogewa da, na saka hannu a handbag din na sake sauko letter dinsa, first letter din da ya fara rubutomin, na bude na sake karantawa sannan itama na jefa ta ruwa, abu na karshe shine CD din daya aiko min, na dauko ina kallon rubutunsa da yayi da permanent marker a jikin CD din, I LOVE YOU, a hankali nace I love you too Ibrahim but I must let you go, na jefa cd din shi ma cikin ruwan
Episode Thirty One: Let it go
Ina kallon cdn ya jima yana floating sannan ya nutse. Na dauke kaina na koma hanyar inda na baro su Hafsat. Tun daga nesa na hango alamar abinci suke ci, sun shimfida blanket suna zaune akansa. Na karasa da sauri nace "ina fatan dai baku cinye sandwich din nan ba" Amina ta kalleni da mamaki tace "au da jira kike yi mu rage miki? Kinga na hannuna shi ne na karshe, sai dai kisha fruits" ban yi wata wata ba na kwace na hannunnata na tura gabaki daya a baki na, ai kuwa ta taso kaina lallai sai ta kwace, suka hadu ita da hafsat suka danne ni, Hafsat ta kama yi min chakulkuli ina dariya Amina ta kwakule sandwich din daga bakina, sai kuma ta jefar dashi a kasa tace "ew, duk ta saka yawu a ciki" Hafsat ta daga ni tana karkade jikinta saboda dan squeezing da kayanta suka yi, na faki idonta na damko kasa cikin hannuna na watsa mata ta cikin wuyan rigarta. Tsayawa kawai tayi tana kallona cike da takaici, Hafsat da shegiyar tsafta, kuma na tabbatar kasar ta shiga har cikin brazier ta. Ta ma rasa me zata ce min duk masifar ta. Sai kawai ta juya baya tana karkade rigarta ni kuma na cigaba da kyalkyala mata dariyar mugunta, banyi aune ba kawai sai jin kasa nayi a fuskata, har cikin baki na dana bude ina dariya. Nan take wani fadan ya kuma rinchabewa kowa yana watsawa kowa kasa. Kasa har cikin gashin mu ranar sai da ta shiga. Sai late evening ranar muka bar beach din gabaki dayan mu munyi kacha kacha. Muna shiga palo mommy ta mike "what in God's name happened" Hafsat ta nuna ni tace "ita ce ta fara" mommy ta juyo da dubanta kaina, kafin tayi magana na yi sauri nace "aga wanda zai fara zuwa toilet" nan muka dau gudu muka yi dakin mu muka bar mommy da sakakken baki.
Tun daga ranar na mayar da hankali na wajan gyara rayuwata, daga naji Ibrahim ya fado min araina sai in fara wani abin da zai dauke hankali na. Addu'ah kuwa kullum sai na yita. Lecturers din mu sunyi marking report din da na rubuta sun turo wa daddy, ya kira ni naje na same shi a zaune shida mommy ya miko min takardar hannun sa yace "karanta a fili inji" na bude hannuna yana rawa na fara karantawa, As da Bs ne duk, ko C babu, na ajiye takardar na rufe bakina ina dariya, daddy shima dariyar yake yi yace "ashe zaki iya, da wato ganin dama ne bakiyi ba ko?" Mommy tace "Moon ai tamkar mai aljanu take, yau fari gobe baki, ni kaina ban san inda ta sa gabanta ba" daddy yace "at least she is doing good yanzu" ya juyo ya kalleni yace "Moon, ina so in cigaba da ganin irin wannan result din, bana son wannan mood swings din naki. Kina da kokari, kiyi amfani da brain din ki yanzu da kike da chance" nace "nagode daddy, insha Allah abinda ya faru a baya ba zai kuma faruwa ba".
Yanzu a makaranta bama tare da Hafsat, dan haka kowa harkar gabansa yake. Amma hakan bai yi affecting dina ba kamar yadda nayi tsammani, na mayar da hankali na sosai akan karatu na, nan da nan na fara sabawa da mutane, lecturers duk sun sanni saboda ni ina da saurin shiga ran mutane. Turawa, blacks da sauran kabilu duk kowa nawa ne, maza da mata. I am very serious akan karatu but I am not boring, I am very friendly.
Rannan muna zaune a daki muna ta shirin kwanciya bacci, sai muka ji knocking a bakin kofa, Amina tace "waye?" Yaya Habeeb yace "ni ne, I am coming in" Hafsat tace "don't come in, we are naked" kawai ya bude kofar ya shigo yana dariya. Hafsat tayi sauri ta ja bargo ta rufe cinyoyinta, Ya habeeb yayi dariya yace "yanzu Hafsat ni kike wani rufe jiki dan na shigo daki? Da yaushe kika gama shan dummy?" Hafsat ta murguda masa baki tace "i was doing you a favor da nace kar ka shigo, now you are doom for life" yana kallonta yace "bangane ba" tace "yanzu ka shigo kaga tsiraicin mu, zaka fara tunanin duk mata irin mu ne, zaka yi ta searching ka kasa samun kamar mu at the end zaka kare da auri saki" duk muka saki baki muna kallon ta ya Habeeb cikin mamaki yace "Hafsat yanzu rashin kunyar ki dama har ta kai wannan stage din? Do you even think you are beautiful? No wonder har yau baki taba yin saurayi ba" Hafsat tace "Na dauka cewa kayi yaushe muka girma, kuma yanzu kana maganar har yanzu banyi saurayi ba, ashe mun girman kenan" rasa amsar da zai bata yayi, ya juya ya fice. Ni dai ina tsaye da towel a jiki na, Amina tace "Hafsat mai yasa kika yi masa rashin kunya" Hafsat tace "Na gaya masa kar ya shigo, specifically na gaya masa cewa we are naked amma ya shigo, nima banji dadi ba da nayi masa rashin kunya amma so nake yasan cewa we are matured enough yanzu, it is not right ya ke shigo mana daki anyhow" maganar Hafsat tayi zafi amma she is right. Ko 'yan biyu ne ku karewar brother and sister da akwai privacy da kowa acikin ku yake bukata. Samari bai dace su ke shiga dakin 'yammata ba, haka zalika suna 'yammata bai dace su ke shiga dakin samari ba, in dai har bada wani uziri ba.
Sai da muka gama second year din mu sannan na samu zuwa Nigeria. Kawai sai naji bana wani murnar zuwa saboda dama wanda nake saka ran zan gani a Nigeria yanzu na tabbatar is no longer mine. Da muka je Nigeria sai muka zama abin kallo a gurin mutane saboda yadda muka zama, ni kaina nasan a cikin wadannan shekaru biyun ba karamin chanji na samu ba, fata ta wani mugun laushi da santsi, nayi kyar kiba ta komai ya cika yayi bulbul, ga kuma uwa uba wayewa, dadin mu daya mommyn mu is very strict, bata son shigar banza, dan haka koda English wear mu ka saka to sai mun rufe jikin mu, bama taba fita waje da matsatstsun kaya. Samari kuwa tun a makaranta har a gida haka muke ta fama dasu, daga ni har Hafsat har Amina babu wacce take kula samari, dan ni a England zobe na saya na saka a ring finger dina, duk wanda yazo naga yana kokarin ya fara nuna min soyayya sai in nuna masa zoben in ce "am married" duk da dai wadansu suna fahimtar karya nake yi amma dole su hakura tinda babu yadda zasu yi dani. Muna zuwa Nigeria ma abinda ya faru da mu kenan, dan ma samarin nan suna dan jin tsoron tunkarar mu amma duk da haka da akwai masu courage, in sunzo nakan tsaya in basu hakuri ince anyi mana miji, Hafsat kuwa ko kwallon inda suke bata yi balle ta kulasu. Rannan Amina tace "ni kam Hafsat zan ga saurayin ki a duniyar nan" nace "gaskiya kam, duk wanda Hafsat ta bude baki tace tana so to ya kamata azo kallonsa" bata kulamu ba saboda in miskilancin Hafsat ya tashi mu din ma bamu ishe ta kallo ba.
Satin mu biyu a Abuja muka tafi 'yalleman. Murna a gurin su inna ba'a magana. Tana ganin mu tace "lah, England din ce haka? Anya ba za abar karatun nan ba kuwa? Kar kuzo wata rana mu kasa gane ku saboda kun zama irin 'yan can" na rungume ta nace "we miss you too innarmu, in mun tashi tafiya next time tare zamu tafi dake saboda kullum kike ganin mu dan karki manta mu" ta rungume ni itama tana cewa "na ki wayon, salon mu tafi da baffa ki kwace min shi da wannan kyan ka kike yi kullum bayan ni tsofewa nake yi" Amina tace "kai inna, ai kamar ku daya ke da Moon"
Naji dadin zuwan mu 'yalleman dan ba kara min missing din su nayi ba. Nan da nan fara bin 'yan'uwan mu gida gida ina gaishe su kuma kowa sai na kai masa kayan tsaraba, har kayan da na siyo musu suka kare na fara diban kayan mu ina rabarwa. Nan take samari kuwa su kace dawa Allah ya hada su ba da ni ba, babu shiri na koma daki kusa da Hafsat na zauna na daina fita, amma duk da haka ban tsira ba saboda har gida ake aiko wa wai ana sallama da maimuna, Hafsat tana ta yi min dariya wai wa ya aike ni futa yawo a garinnnan.
Rannan muna zaune a compound din gidan sai daddy ya shigo zai gaishe da mutan gidan kamar yadda ya saba. Inna ta aika ni na dauko masa carpet a cikin gida aka shimfida masa, duk ya gaishe su mu kuma muka gaishe shi. Sai Hajja tace "ni kuwa muhammadu ina son magana da kai, da Adama naso muyi magana da ita amma sai nayi tunanin kar ta ce bakin ciki nake yi wa jikokinta" ina jin haka nasan maganar mu zatayi masa. Daddy yace "to hajja ina jinki" tace "anya muhammadu yaran nan ba za kayi masu aure haka ba? Yanzu ka debi yara mata ka tafi dasu kasar waje wai da sunan karatu? Wanne karatu mace zatayi wanda ya wuce na dakin aure? Ni dai a shawara ta ka dawo dasu nan, ga 'yan'uwansu nan sai a hada su auren zumunci, ga nuraddeen nan shima in karatun ne ai yayi, ya gama degree dinsa a BUK, ga balarabe, ga manniru duk babu abinda suka rasa. Ni tsoro yaran nan suke bani musamman wannan tsagerar" ta fada tana nuna Hafsat, "yanzu ma tana mana kallon wulakanci ballantana nan gaba in tafi haka? Ai cewa zata yi bata taba ganin mu ba" daddy yayi ajiyar zuciya yace "to hajja, ni ban taba tunanin hana su aure ba, ko yau suka fito da miji aure zanyi musu" Hajja tayi sauri tace "yo ai indai wadannan ne ba zasu fito da miji ba, ai indai ana so ayi wa wadannan aure to sai dai a fito musu da miji" daddy ya sake cewa "shikenan Hajja, yanzu abinda za'ayi ki kira su samarin ki ce su zo suyi magana da su Hafsat din, indai sun fahimci juna a tsakanin su to na miki alkawarin baza mu bar garin nan ba sai da auren su aka".
Chapdi, lallai da rabon Hafsat zata saka wa garin wuta gaba daya. Lol.
I love you all. Thanks for following
Episode Thirty Two : Munnir
Daddy yana gama fadin haka ya mike yayi musu sallama ya fita. Gurin kowa yayi shiru banda Hajja dake ta sambatun ta ita kadai. "Yauwa, yanzu na ji magana, amma abar yara suna so sufi karfin mutane? Yanzu kuwa zan kira 'yan samarin nan duk abinda suke yi su bari su taho gida, azo ayi ta ta kare" tsam mommy ta mike ta shige dakin da muke sauka in munzo, Hafsat ta tashi ta bita a baya, nan Hajja ta sake daukan magana "zasu je suyi kulle kullen yadda za'a fasa, ai kuwa wannan maganar kamar anyi ta an gama ne, yo gida bai koshi ba a bawa jeji?" Duk abinda take yi inna bata tanka ta ba, aikin gabanta kawai take yi. Sai da na gama taya inna juye furar da ta dama a jug na kai kitchen na saka a fridge sannan na shiga dakin mu. Dariya naji tana neman kubucemin saboda ganin yadda akayi upside down da dakin, duk su biyun sun dage suna ta loda kayan mu a akwatinan mu, wadansu kayan ma ba'a ninke suke ba haka ake watsa su. Mommy idonta ya kada yayi jawur, Hafsat kuma fuskarta kamar an aiko mata da mutuwa. Bance musu komai ba suma haka, na samu guri na zauna na zuba wa sarautar Allah ido, nan da nan mommy ta bani aikin kwashe kayan kwalliyar mu da underwears din mu. Muna cikin aikin da bansan na menene ba sai ga inna ta shigo, da mamaki take bin mu da kallo "yanzu Bintou shine kika tisa 'ya'ya a gaba kuke hada kaya zaku gudu?" Maganar guduwar da inna tayi shi ya saka dariyar da nake kunshewa ta fito, Hafsat ta bini da uwar harara hamkar idanunta zasu fado. Mommy ta yar da rigar da take ninkewa ta zauna dabas a bakin gado tace "inna yanzu zama zanyi a yiwa yaran nan auren dole, dududu nawa suke? Girman jiki ne fa kawai dasu amma ba wani shekarun kirki ne dasu ba ballantana ace sunyi kwantai za'a raba wa 'yan'uwa, wai Nuraddeen, har da Mannirun da baya ganin kowa da gashi" inna tace "ke waya ce miki za'ayi musu auren dole? Ya kike abu ne kamar ba kisan halin mijin kiba? Ni dai abinda kunne na ya jiye min yace shine 'za'ayi auren in dai har yaran sun amince a junansu' to menene kuma abin tashin hankali a ciki. Ke kinsan waye Muhammadu, kinsan babu yadda za'ayi yayi wa 'ya'yansa auren dole, amma yanzu kina diban su kuka gudu cewa zai yi ba kya son 'yan'uwansa. Ki zauna kiyi musu addu'ar zabin alkhairi shi yafi miki" tana fadin haka ta juya ta fice daga dakin.
In matsala irin wannan ta samu mutun, musamman harkar ta aure, rigima, koke-koke da tuburewa iyaye ba shine zai samar da maslaha ba, abinyi shine ka bisu a yadda suka zo maka sannan daga baya sai ka same su, ko ka samu wani wanda suke jin maganar sa kayi masa bayanin cewa kaifa baka son hadin nan. Sannan abu mafi muhimman ci shine ka yawaita addu'ah, wani baya taba auren matar wani kamar yadda wani baya taba haihuwar dan wani, rayuwar mu gaba daya a rubuce take duk abinda Allah ya rubuta sai ya faru da kai to babu tsimi babu dabara, addu'ah kadai ita ce maganin masifa. In Allah ya rubuta something bad zai faru da kai in kana yawaita addu'ar neman mafi alkhairi sai Allah ya goge ya rubuta maka something better.
Mommy ta fasa tafiya amma daga ganinta kasan ranta a bace yake, Hafsat ta kara hade gida, ni kuwa harkar gaba na nake yi saboda na yarda cewa daddy ba zai taba aura min wanda bana so ba, duk wanda yazo yace yana sona all what I have to do is in ce bana son sa, kalas.
Nuraddeen ne ya fara zuwa, very cheerful and nice guy. A falon inna ya same mu, kallo daya Hafsat tayi masa ta tashi ta shige daki, ni kuwa harda durkusawa ta ina gaishe shi, ya amsa min da fara'arsa yana tambayata labarin England da rayuwar makaranta, nan na zauna na tankwashe kafata na ringa kwararo masa labari yana dariya, shima ya fara bani labarin BUK da irin wahalar da suka sha ina ta mamakin banbancin makarantun mu na gida da kuma na waje. Sai da muka gama hirar mu ya tashi ya daga labulen cikin daki yace "Hafsat ke kuwa ko gaisawa ai kya fito muyi, ni ba cewa zanyi ina son ki ba dan kin fi karfina, in ma zaban zanyi sai dai Moon ita ce mutuniyar kirki, to amma ita kuma na dauke ta kamar kanwa ta" ina jiyo inna tana yi mata fada sannan ta fito ta gaishe shi tana kirkiro murmushin karya. Har ya juya zai fita sai yace "kun taba zuwa hadejia kuwa?" Muka girgiza kai a tare, yace "ku shirya to gobe tunda ina gari sai muje yawo ku gano fadar sarkin mu, kuga river hadejia" da murna ta nace "Allah ya kaimu, mungode Allah ya bar zumunci" daga haka ya juya ya fita, Hafsat tabi bayansa da harara. Yana fita ta kama kunnena ta rike "maza ki zauna kiyi ta wangale musu baki, in aka aura miki daya ni ko gidanki bazan ke zuwa ba" . Washegari kuwa mukaje hadejia da yaya Walid, nuraddeen da kuma mu uku har Amina. Munyi yawo sosai a garin, ya nuna mana duk guraren tarihi, hatta Hafsat ta ware muna ta hirar mu ta zumunci, a hanyar dawowa ne yake bamu labarin budurwarsa 'yar kano, tana karatu a BUK, bai kai maganar gurin iyaye ba saboda yana so sai ta kammala tukun. Hafsat tana jin haka ta sake warewa tana yi masa hira. Da zamu dawo gida ya sayo mana balangu mai uban yawa. Har zamu shiga gida sai ya kirani na dawo, seriousness na gani a fuskar sa nima na nutsu, yace "naji Hajja tace ta kira munnir shima, in yazo kar ki yadda ki sakar, masa fuska, bashi da kirki ko kadan kuma bashi da kunya" na gyada masa kai da sauri alamar na fahimta, daga haka na shige gida. Balarabe bai zo ba, sai yayo waya ta wayar inna wai shi ba zai samu damar zuwa 'yalleman ba sai dai a turo masa hotunan mu ta waya ya zaba. Nan inna ta haushi da bala'i "an gaya maka su atamfofi ne da zaka wani ce a turo maka hotuna ka zaba, aikin banza, ai ba neman kai muke yi dasu ba" ta inda take shiga bata nan take fita ba. Mommy tace "good riddance" nima kaina sai da maganar tasa ta bani haushi, lallai ma wannan mutumin, me ya dauke mune? Duk hajja ce ta jawo mana wannan wulakancin.
Shi ogan bai zo ba sai ana ya gobe zamu tafi, muna dakin inna Hafsat ta shigo tana bata fuska tace "wannan dan iskan ne yazo, I was hoping ba zai zo ba, ganinsa ma kawai yayi spoiling mood dina ballantana yin magana dashi" mommy tana jin haka tace "wai munnir din ne yazo?" Hafsat tace "eh shi fa, yana dakin hajja" mommy ta watsomin wani kallo tace "behave your self" bata ce da Hafsat komai ba saboda tasan halin abarta. Duk muna bedroom din mu ya shigo palon, tun daga daki muka jiyo kamshin turarensa. Hafsat ta kwanta taja bargo. Ina jinsu suna gaisawa da mommy da inna, yana tsokanar inna wai kullum kara kyau take ko ita zai zaba ne. A raina nace "oh ni 'yar nan, me hajja ta mayar damu ne? Kashin dankali?" Naji inna ta kalla mana kira wai muzo mu gaishe shi. Na dauki mayafi na na yafa na kalli Hafsat naga ta rufe ido. Ina fita palon mommy ta tashi ta shige daki tana harara ta, inna ma tace bara taje kitchen ta duba abinci. Kallo daya nayi masa na fahimci abinda Nuraddeen yake nufi da yace inyi a hankali dashi. Kallo daya nayi masa naji sam bai yi min ba. Tun daga sama yake kallona har kasa. Inna tana rufe kofa yace "damn, wai mafarki nake yi ne ko gaske ne Moon ce ta zama haka? Ni da hajja ta kira ni ina mita za'a hada ni da 'yar tsakuwa ashe kin zama dakwalwar kaza?" Binshi kawai nake da kallo, wannan me yake nufi ne? Sai a lokacin nayi nadamar saka mayafi ba hijab ba. Ya nuna min kan handle din kujerar da yake kai yace "come sit with me" lallai wannan duk inda nake tunanin sa ya wuce nan. Na tafi kujerar da take opposite dinsa na zauna ina gyara lullubi na. Tsam naga ya taso ya dawo handle din kujera ta ya zauna yana cewa "meye kuma na wannan uban lullubin, ni da nazo in ganki kuma in kika rufe me zan gani kenan?" Ya fada yana kokarin sauke min lullubi na. Na mike tsaye ina kallonsa. Kyakykyawa ne ba karya, dan gayu ne na azo a gani, haihuwa da rainon legas. Baban su shine babba a gurin baffa, kuma shi yake kula da business din baffa a lagos. Acan aka haifesu duk, kuma acan suka girma. Bafulatani ne gaba da baya. Ya riko gefen rigata "ina zaki je kuma ko gaisawa ba mu yi ba?" Na kalleshi a raina nace "yau dole in dauki page a cikin littafin Hafsat" na watsa masa wata hararar da bansan na iya taba, nace "don't you dare try to touch me again, in kana so mu gaisa ka koma kujerar da ka taso daga kai, in ba haka ba bazan kara second daya anan ba" ya mike yana wani shagwabe fuska yace "i can't help it wallahi, you are so beautiful" na wuce na zauna tare da hade girar sama da ta kasa irin yadda Hafsat take yi nace "ina wuni" cikin wata irin murya yace min "lafiya lau sweetheart, ya England? Nima nace "lafiya" a ta kaice. Daga nan ya fara min labarin irin kudin da yake samu, sabuwar motar da ya saya, irin yadda yake shanawa a lagos, ni dai duk ina jinsa, sai da na gaji na mike nace "bara in kirawo maka Hafsat", shima ya mike tare da cewa "there is no need, I have already made my choice" daga nan ya ajiye rafar 'yan dubu dubu akan santa table, ya sakar min wani kasalallen murmushi ya fice.
Episode Thirty Two : Mahdi
Na jima a tsaye ina kallon kofar da ya rufe bayan ya fita, me wannan mutumin yake nufi ne? Ni wannan ko a kafa aka daura min shi ai na gwammata in dau wuka in datse kafar in huta. Na zauna akan kujera na dafe kaina da hannayena. Dear Ibrahim, is this our destiny? Sai kuma naji haushin kaina, why am I even thinking of Ibrahim now. Me yasa har yanzu na kasa cire shi daga raina? Shekara biyu kenan rabona dashi, shekara daya kuma da yin aurensa, maybe har sun haihu by now. Jiki ba karfi na tashi na shiga daki na kwanta kusa da Hafsat. Tun muna yara dama ni bana son munnir, sam bai yi mun ba, ballantana yanzu da ya kara habaka, I must be strong, I must pray hard, in nemi zabin Allah kuma nasan Allah ba zai zabar min munnir a matsayin miji na ba. Ina nan kwance inna ta shigo take cewa waye ya ajiye kudi a palo? Nace "mata munnir ne" ta ajiye akan dressing mirror sannan ta fara yi mana fadan mun kwanta da la'asar bayan munsan babu kyau.
A ranar da daddare har nayi bacci na fara jin hayaniya sama-sama, na farka sai naji a compound ake yi, na tashi da sauri na fita palo sai naga Hafsat a tsaye a bakin window tana lekawa, na karasa kusa da ita ina tambayar ta "lafiya" ta yi min alama da inyi shiru. Nan muka cigaba da leke tare. Hajja ce take balbalin fada "ai ba haka mukayi dashi ba, ce min yayi ba zasu tafi ba sai an daura aure, kuma yanzu kawai sai ace min wai gobe zasu wuce?" Baffa yace "kai muhammadu mai yasa kayi mata alkawarin da kasan ba zaka iya cikawa ba?" Daddy yace "baffa ni abinda nace shine, in har an samu fahimtar juna a tsakanin yaran to baza mu bar garin nan ba sai an daura aure, kuma ai daga zuwan manniru yau ba za ace har sun fahimci juna shida maimuna ba, abinda nake gani shine kar ayi gaggawar auren nan ya zama an bata zumunci maimakon a gyara shi, a bari idan yaran sun daidaita tsakanin su shikenan" hajja ta katse shi da cewa "yo yaushe zasu daidaita tsakanin su bayan zaka dauke yarinyar ku tafi? Ai in ma so ake su daidaita sai a bar yarinyar anan yadda zasuke ganin juna" kawu Aliyu yace "hajja rayinyar nan fa karatu take yi, ya za'ayi a raba ta da karatun ta? Daga manniru har maimuna 'ya'yan mu ne, ba za mu so mu tauye wa wani hakkinsa ba, tunda yarinyar nan tace bata son shi a rabu da ita, hajja zamani fa ya chanja, yanzu da da ba daya bane, idan da anyiwa yara aure ba tare da son ransu ba suna hakura yaran yanzu zasu zo su bata mana zumuncin mune. Maimuna yarinya ce mai hankali wallahi, Manniru ba shi da kunya sam, kuma ya girme mata nesa ba kusa ba, ni dai baffa ina ganin in akayi wannan hadin an tauyewa yarinyar nan hakkinta kuma zata iya ta kullace mu har abada" a raina nace "God bless uncle Aliyu, Allah ya baka abinda kake so duniya da lahira" na jingina kaina wanda already ya dau zafi a jikin Hafsat ina cigaba da sauraron mahawarar da zata iya chanza rayuwata gabadaya. Baffa naji ya fara magana "kai manniru kana son auren maimuna kace ko?" Nayi sauri na leqa window, munnir na gani a zaune a gefen hajja, murya kasa kasa yace "eh baffa" baffa yace "to shikenan, na baka damar ka cigaba da neman auren ta daga yau har zuwa ranar da zata gama karatun ta, idan kafin nan ta amince tana sonka shikenan" da sauri munnir yace "baffa shekara uku kenan fa nan gaba" tas, naji saukar mari daga hannun uncle Aliyu zuwa fuskar Munnir, inajin Hafsat tana dariya kasa2, nan uncle Aliyu ya rufe shi da fada "baffan kake musawa magana? Rashin kunyar taka takai har haka?" Baffa yace "rabu dashi Ali, idan ba zai jira ba ya nemo wata a aura masa, ni na gama magana" daga nan ya mike yayi hanyar part dinsa. Nan gurin ya hargitse kowa yana fadin albarkacin bakinsa, kuma daga dukkan alama fiye da rabin mutanen gurin basa bayan wannan hadin saboda duk suna yabon halayena tare da kushe da Allah wadaran halayen munnir, inna sam bata cewa komai, hajja kuwa sai kumfar baki take har da cewa duk sanda mukayi kwantai kar a kawo mata. Munnir kuwa tun daga inda nake nake hango yadda ya murtuke fuska yana bin kawunnan mu da mugun kallo.
Washe gari tun assuba muka fara wanka muna fitar da akwatinan mu, inna ta zo ta saka mu a gaba da nasiha "ku kyautata addinin ku, ku bi iyayenku, ku tsarkake zuciyar ku daga mugun nufi akan kowa, in kuka yi haka Allah ba zai munana rayuwar ku ba, kullum in za kuyi addu"a ku nemi zabin Allah, kar kuce 'Allah ka bani kaza ko Allah ka yi min kaza' gwara kuce 'Allah ka zaba min mafi alkhairi a duk al'amurana'. Ku yawaita karatun alqur'ani dan shi kariya ne, musamman ayatulkursiyu, ku mayar da ita tamkar babbar kawarku kullum ta kasance a bakin ku, in zaku kwanta bacci kuyi alwala, na tabbatar muku in kuka rike wannan duk wani mugun nufi na mutun, aljani ko shaidani ba zai same ku ba".
Kiri2 sanda mukaje yiwa Hajja sallama taki kulamu, haka muka taso muka fito, Hafsat tace a hankali "kinyi wa kanki" muna fita waje naga nuraddeen tare dasu ya Walid, muka gaishe su muka wuce. Na shiga gaba Hafsat ta zauna a baya tunda tare zasu zauna da mommy, ba tare da Amina zamu tafi ba, saita karasa hutunta anan zata same mu a Abuja, ya Walid ne zai tuka mu. Ina zama sai ga nuraddeen yazo yana tsokana ta "amaryar yayan mu" sai na samu kaina da daure fuskata, yayi dariya yace "congratulations though, naji yadda aka kare maganar jiya" nayi masa murmushi nace na gode, ya juya yace "gashi nan yazo sallama bara insan inda dare yayi min" sai da ya matsa sannan na hango munnir yana tahowa inda motar mu take, sai a lokacin nayi nadamar fito war mu da wuri, da munsani mun jira mommy dan nasan duk rashin kunyarsa ba zai yi a gaban mommy ba dan zata iya kwakkwada masa mari. Na yi sauri na dauko wani katon bakin glass na saka wanda ya kusa rufe rabin fuskata, yana karaso wa na daga glass din motar, ga mamakina sai naga ya zagayo ta side din driver, ya shigo ya rufe kofar, daga dukkan alama bai san da Hafsat a motar ba, na dauke kaina tamkar ban san ya shigo ba, murya can kasa yace "ba gaisuwa" nayi banza na rabu dashi, ya sake cewa "shine kika ce da kawu ambassador ba kya so na ko?" A zahirin gaskiya ni daddy bai tambayeni ba, asali ma bamu taba maganar dashi ba, nasan ya fadi haka ne saboda shima baya son wannan hadin. Ji yayi bani da niyyar cewa komai ya sake cewa "ina so ki sani, yanzu na fara sonki, kuma zan cigaba da bin wannan tsohon har sai ya amince da maganar nan dan ni yadda nake jinki bazan iya jiran 3 years ba" still no reply from me, na juya kaina ma ina kallon daya side din, kawai sai jin hannunsa nayi a fuskata yana kokarin juyo dani in kalle shi, Hafsat tana daga baya tace "hey, don't" a tsorace ya juya ya kalleta, duk da ban juya ba na tabbatar harararsa take yi, yace "hey, yaushe kika shigo?" Tace "tun kafin ka shigo, naji komai" yace "sa'ido fa babu kyau, musamman a harkar miji da mata" Hafsat tace "not even in your dreams". Suna cikin haka mommy ta fito, da sauri ya juyo gurina yana min blowing kiss tare da cewa "sai munyi waya" ya fice, a tare mukayi tsaki ni da Hafsat. Yana fita gurin mommy ya tafi ya durkusa yana gaisheta, Hafsat tace "chusa kai ba kwarjini" mommy ta amsa masa fuskarta a sake sannan ta karaso mota. Su daddy ma duk suka shiga motar su shida ya Habeeb da faruk, sai motar security a gaba, muka tafi.
Tun daga ranar har muka koma England kullum sai munnir ya kira ni a waya, na rasa a gurin wanda ya samu numberta, muna komawa England muka koma school.
Shakara daya tazo ta wuce muna ta karatu, har shekarar ta wuce babu Ibrahim babu labarinsa, munnir kuwa har yau yaki hakura duk da maimaita masa da nake yi kullum cewa bana son sa. Amira ma muna da contact da ita tana ci gaba da karatun ta a abuja. An tura mu clinicals, daddy ya saka aka tura mu asibiti daya da Hafsat amma ita tana bangaren gynecology ni ina neurology, Amina ma an samar mata admission ita da faruk sun fara karatu, yaya Walid ya gama, ya Habeeb kuma yana project dinsa.
Na koyi abubuwa da dama a asibitin nan, anan na kara sanin irin baiwar da Allah yayi wa bil adama, naga yadda ake bare kan mutun ayi masa aiki a kwakwalwa sannan a mayar a rufe, na koyi yadda ake yin hemisphecrotomy inda ake chire rabin kwakwalwar mutun a bar masa rabi kuma ya tashi lafiya lau. Na koyi abubuwa da yawa wadanda nake sa ran zan dawo Nigeria in yi.
A asibiti na hadu da Mahdi. Nasha ganinsa amma bamu taba magana ba saboda ba daga school daya muka zo ba dan haka ban sanshi ba. Rannan mun fito daga wata theatre ina zaune ina hutawa kawai sai naji anyi min sallama, na daga kaina sai na ganshi, na amsa masa cikin mamakin accent din hausa da naji a bakin sa. Fari ne tas, irin farin da har jaja yake yi kamar in ka taba jini zai fito, kirar jikinsa dai dai misali, komai nasa kamar shi yayi wa kansa, sam bai yi kama da hausawa ba. Ban gama mamaki ba sai ji nayi yace "sunana Mahdi Datti Sufyan, daga university of Michigan, ni dan garin kano ne, unguwar gwauron dutse. Naga kamar kema 'yar Nigeria ce ko?" Sai a lokacin hankali na ya dawo kaina, sannan na fahimci cewa na bude baki ina kallon sa, nayi sauri na rufe bakina nace "wait Datti Sufyan? The name sounds familiar" yayi dariyar data bayyana kyawawan jerarrun hakoransa yace "yah... My father is kind of famous in kano" ya zauna a kusa dani yace "baki gaya min sunan kiba amma" na sake tattaro hankali na nace "sunana Maimoon Muhammad Dikko, I am Nigerian also, I.." Ya katseni "ambassador MD?" Nace "kasanshi ne?" Yace "yeah..... Da akwai sanda baba yazo ya kaini embassy gurinsa, yace in ringa zuwa ina gaishe shi, amma kinsan halin students ban taba zuwa ba. So you are his daughter?" Na gyada kai ina murmushi, yace "nice to meet you Maimoon" nace "nice to meet you too Mahdi"
#ga masu complain cewa Moon bata da kamun kai, ina tuna mana cewa akwai mutane in reality da suke exactly kamarta wadanda sam basu iya bata rai ba, suna da faran faran da saurin sabo da mutane, yawancin su kuma suna da mugun kirki. Hakan ba yana nufin basu da kamun kai ba, kawai nature dinsu ce haka, kuma yawanci mutane suna son su. Fara'a ita take jawo mutane, su kuma mutane rahama ne#
Thank and I love you all.
0 comments:
Post a Comment