Tun daga ranar mahdi ya zama best friend dina, in har ina cikin asibiti to muna tare dashi, rannan muna zaune dashi nace "dan Allah Mahdi in tambayeka" ya cire glasses dinsa yana kallona yace "ina jinki" nace "dan Allah da gaske kai bahaushe ne? I mean biologically?" Straight yace min "no, babana adopting dina yayi" da sauri nace "yes!! I knew it" dariya yayi sosai har yana buga kafa sannan yace "wasa fa nake miki, serious ni bahaushe ne, why do you doubt it?" Sai naji kunya kuma nace "kawai dai ba kayi kama da hausawa ba" yayi shiru sannan yace "my mother was shuwa arab, ni kadai ta haifa Allah yayi mata rasuwa, so.... I am different duk a family, wannan shi yasa na taho kasar waje karatu, I want to feel like I belong, a gida kullum kamar alien nake ji na a cikin siblings dina" na sunkuyar da kaina inajin ba dadi, ace ka zama kamar bare a cikin 'yan'uwanka babu dadi, nace "am sorry about your mom, am sorry I asked you" yayi murmushi yace "chill, ba komai, it is better that you know".
Har gida na kai Mahdi ya gaishe da daddy, take daddy ya gane shi kuma yayi masa fada akan baya zuwa yana gaishe shi. Karatun mu muke yi sosai gar muka gama first year din mu a clinical, sanda muka je hutu gida kamar za'a chinye mu danyu, babu shiri daddy ya sako mu a jirgi muka dawo England. Munir da ya ganni kamar zai yi hauka, lallai ai shi baffa yayi masa alkawarin aure na. Inna da daada ma yanzu sun fara mita, a cewarsu ya kamata by now ace muna da tsayayyun samarin da muna gama makaranta sai aure. Four years kenan rabona da Ibrahim, tabbas har yanzu ina jinsa a raina amma sosai na rage tunaninsa. Sometimes na kan yi lissafin ko me yake yi yanzu? Sai kuma in yi sauri in kawar da tunanin saboda bana son in dawo wa da kaina aiki baya. Sai da muka shiga final year din clinical sannan na fara fahimtar cewa Mahdi is gradually falling in love with me. Yawan kira na a waya, kullum da weekend yana hanyar embassy gurina, ga yawan compliment, duk kayan da na saka sai yace nayi kyau, ko kuma yayi ta kallona a sace in mun hada ido ya yi sauri a dauke kai. He is really a nice guy and I really don't want to hurt him, amma sam ni bana jin sonsa a raina, I like him, but I don't love him.
Rannan muna daki da Hafsat da Amina, sai Amina ta dau waya ta tana ganin pictures kawai sai taga hotona da Mahdi. Tace "wow, moon wannan gayen fa?, gaskiya ya hadu ba karya" nace "wa kenan?" Ta juyo min screen din naga Mahdi nace "ohh, he is my friend, sunan sa Mahdi" tace "wait, don't tell me bahaushe ne" nace "dan kano ma kuwa, kanon ma cikin badala" ta bude baki tana kallona da mamaki sannan ta sake kallonsa, sai kuma tayi murmushi tace "something is really cooking here, wannan din za ki ce min wani friend din ki? Mu dai a fada mana ba sai tayi tsami ba" nayi dariya nace "am serious, we are just friends" tace "then something is definitely wrong with you, anya kuwa kina da lafiya, anya kuwa female hormones estrogen and progesterone suna aiki a jikin ki kuwa?" Nayi dariya kawai na share maganar ta, amma kuwa maganar ta tsaya min a rai, ba maganar Mahdi ba, maza in general, sam bani da interest a kan su, sam bana jin wani feeling idan naga wani namiji me kyau ko kuma in muna tare da wani namiji ballantana Mahdi wanda jinsa nake kamar Hafsa. Na tuna sanda muna tare da Ibrahim yadda nake jin attraction a tsakanin mu, why is it now gone? Yanzu dana kara girma ma ya kamata ace libido na ya karu amma it's like I have none. Na zauna ina lissafo Mahdi, komai bashi is perfect, sai kawai naji a raina ina comparing dinsa da Ibrahim. Mahdi is far more handsome than Ibrahim, more educated, more richer, his family is well known, kuma a kyawun dabi'a ma ban taba kama Mahdi da hali marar kyau ba, dan tunda muke bai taba taba ni ba. Amma why is it that in na tuna shi bana jin komai amma in na tuna Ibrahim nake jin pang a zuciyata, why must love be so cruel? Da haka na yanke shawarar cewa i must do something about Mahdi tun kafin inyi hurting dinsa.
Rannan yazo gida gurina kawai sai nace masa "ni kuwa Mahdi baka taba fada min wacce irin mata kake son aure ba" kamar wanda na sosa masa inda yake yi masa kaikayi nan ya fara lissafo min duk siffofi na da halaye na yana murmushi, yace duk sune abinda yake bukata a gurin matarsa. Ji nayi kamar hawaye zai zubomin dan na tabbatar da cewa she is head over heal in love with me. Sai da ya gama tsarinsa sannan yace "ke kuma fa" na kakalo murmushi nace "OK, inason namiji baki, kakkarfa, mai ilmi, mai addini.. " ya katseni yace "baki kuma? Why?" Na sake yin wani murmushin nace "tun ina yarinya haka kawai sai nake ganin kamar dark color is for men and fair color is for women, to har girma na sai ya kasance I am more attracted to darker men then fair men" murmushin fuskarsa naga yana subucewa, nayi sauri nace da alamar mamaki "oh God am so sorry Mahdi, you are very handsome the way you are, it's just my short coming and it's not as if you are in love with me, right? Na tambayeshi zuciyata na bugawa, ya sunkuyar da kansa kasa sannan ya girgiza kai yace "you are right, i just find it weird cewa ba kya son maza farare" ya hadiye wani abu a makogwaronsa yace "bara in tafi, see you tomorrow " bayan ya tafi na jima a gurin a zaune, I hated hurting him amma it's better this way, na dafe kaina nace "ohh Ibrahim, what have you done to me? Kai kana can kayi auren ka ni kuma I can't even have a boyfriend"
Tun daga ranar muka koma 'yar wasan buya da Mahdi, duk sai naji na takura saboda ban saba da haka ba.
Cikin 'yan kwanaki naga Hafsat ta fara zama mysterious, nasan da abinda take boyewa amma na kyale ta nace in tayi tsami maji. Rannan kuwa na dawo daga asibiti kawai sai na hango ta a mota ita da wani, can nesa da gate din gidan mu, na saka driver ya sauke ni a gate, ni ma yau sai na gwada mata sa'do irin wanda take yi wa mutane. Ina karasa wa kuwa na tabbatar ita din ce da wani, harara ta watso min, na dauke ido na daga kanta na kalli wanda suke tare, ai bansan sanda na bude ido, baki, hanci kai har da kunne ina kallonsa ba. Dariya yake yimin wholeheartedly sannan yace "so, the beautiful one is here" Hafsat tace min da fulatanci "to rufe bakin haka" na mayar da bakina kuwa na rufe, nace mata nima da fulatanci "kamar balarabe nake gani?" Bata bani amsa ba ta shareni. Tabbas sanda nace duk saurayin da Hafsat tace tana so to azo a ganshi da gaske nake, amma sam banyi tsammanin irin wannan ba. Balarabe ne, kuma daga ganin shi full blood balarabe ne, ga gayu da cikar kamala irin na larabawa, zai kai around thirty something years. Fuskarsa cike da kyau da annuri irinna larabawa. Yasa hannu ya bude min kofar baya yace cikin kyakykyawan turancin sa "shigo, waje akwai zafi sosai" ba musu na zagaya na zauna. Ina zama yace "my name is Zayed, and i am going to be your brother in law insha Allah" na ce excitedly "Ameen, sunana... " ya katse ni "Maimunatu, ana ce miki Moon, shekara daya Hafsat ta baki and you are her only sister... " nan yayi ta bani labari akaina har abubuwan da nake so da wanda bana so, nace " ya akayi ka sani?" Ya kalli Hafsat yace "kullum sai anyi min hirar ki, Moon this, Moon that, kullum maganar kenan, inama zan samu asoni kamar yadda ake sanki" Hafsat ta dafe kanta tace "ohh God, am out of here" na bude motar sannan tace min, "to parrot, in kin gama surutun ki shigo gida" ko kallon sa bata yi ba ta rufe kofar ta kama hanyar gida. Tana tafiya nima na fito, amma maimakon inyi hanyar gida nima sai na zagayo na dawo seat din gaba in da ta tashi na zauna, nan muka kama hira dashi, na fahimci shima yana da surutu da tsokana. Ya gaya min cewa shi mutumin saudi arabia ne, aiki ne ya kawo shi England, shine director na pediatric department na asibitin da muke clinical, wato ogan Hafsat ne, be taba aure ba saboda be taba ganin wacce tayi masa completely ba sai akan Hafsat. Nan nima nace masa "kasan kuwa Hafsat bata taba saurayi ba, ko da kuwa saurayin wasa ne" yace "really?, please bani labarin ta? Nan na gyara zama na fara kwararo masa labarin Hafsat tun muna yara, muna nan har aka kira sallar magrib, sam bai gaji da hirar ba nima kuma ban gaji ba, a karshe nace masa "the bottom line is, she is very annoying but she is the best sister that I could ever ask for"
Tun daga ranar kullum Zayed yazo sai ya neme ni munyi hira, tun Hafsat tana tashi in nazo har ta hakura take zama. Na fahimci cewa suna matukar san junan su kuma ni a idona sunyi bala'in dacewa. Zayed yayi min a matsayin brother in law.
Muna kokarin gama clinical din mu ne rannan da weekend naga Hafsat kamar hankalinta a tashe, nayi niyyar in rabu da ita sai kuma dai na kasa, na tambayeta, har ta shareni sai kuma ta dawo kusa dani ta zauna. Tace "Zayed ne zai zo ya gaishe da daddy yau" nan da nan na washe baki na da murna nace "Allah?, to kuma menene abin bata ran ke da zakiyi murna" tace "I am scared moon, gani nake kamar za'a samu matsala, and I really love Zayed you know" sosai na gane yadda take ji saboda nima na taba kasancewa a irin exact position din ta, nan na shiga lallabata ina cewa "daddy ba zai taba kin someone like Zayed ba". Wajen yamma yazo, Hafsat kasa fita tayi dan gabaki daya jikin ta karkarwa yake yi. Sai ni na fita na shigo dashi main palo sannan naje na gayawa daddy yayi bako a palo, sai da daddyn ya fito sannan na tashi na dawo daki, akan sallaya na tarar da Hafsat tana ta faman jan charbi, har dariya taso ta bani amma na dake, kawai na tuno ranar da Ibrahim yazo gidan mu a Abuja yadda securities suka ringa maltreating dinsa, Zayed kuwa yanzu yana zuwa har wani bashi guri suke yi suna gaishe shi, a raina nace rayuwa kenan, if you have money you have everything. Muna nan zaman jiran sakamako ni har na fara bacci naji Hafsat tana kiran sunana, na tashi na hango ta akusa da window, nima naje na leka, Zayed, daddy da ya Walid muka hango suna tafiya hanyar gate, daga ganin yadda suke cikin nishadi kasan an samu nasara, Zayed bakinsa har kunne. Hafsat ta rungume ni itama tana murna, kawai sak naji kwalla a idona. Inama Ibrahim ne muma hakan ta kasance damu. Su daddy basu jima da dawowa cikin gida ba ya kirani a waya yace muzo ni da Hafsat. Hafsat duk kunya ta ishe ta. Muna zuwa kuwa kowa ya fara tsokanarta wai ta dauko balarabe dan take yin aikin Hajji da umra a free. Sai da akayi shiru sannan daddy yace " Hafsat naga sakon ki, kuma ni dai a ra'ayina ni da mommyn ki munyi na'am da zabin ki. Amma na gaya masa in kun gama wannan session din zamu je Nigeria sai ya saka time ya turo magabatan sa sune 'yalleman su gaida baffa da kawunnan ki, su zasu bada auren ki bani ba, suma kuma ina saran insha Allah ba za'a samu matsala dasu ba. Allah ya sanya alkhairi" gaba daya muka ce "Ameen" ya Walid ya kalleni yace "saura ke" nayi sauri na sunkuyar da kaina. Daddy yace "eh Maimunatu saura ke. Ya kuke ciki ne da wannan farin yaron dan Datti Sufyan?" Nayi sauri na dago kaina nace cikin in ina "ba.. ba komai daddy" yace "bangane babu komai ba, dama ba saurayin ki bane?" Na girgiza kaina, yace " to maimunatu, kinsan dai akwai maganar Munnir har yanzu, kuma ni Allah ya sani bana son hadin ku da munnir, amma babu yadda zanyi indai har baki fito da miji ba kafin nan kafin ku kammala karatunku" Mommy tayi ajiyar zuciya tace "ni na rasa gane kan Moon wallahi, kamar wadda take gudun samarin, who would have thought Hafsat zata riga Moon samun miji
Episode Thirty Four : Back to Square One
Daddy ya tashi ya shige daki. Yana shiga Hafsat ta mike ta fada cinyar mommy ita kuma ta rungume ta suna dariya, nima dariyar nake yi amma ta yaqe ce, maganar daddy ce take yi min yawo aka, tabbas nasan munir bashi da niyyar hakura, kuma nasan in har na gama school bani da wani sauran excuse, ballantana yanzu idan iyayen Zayed suka je neman auren Hafsat kowa kuma hankalinsa dawo wa kaina zaiyi. Ina cikin wannan lissafin naji maganar mommy wacce ta sake daga min hankali "ai naji yace ma indai har su baffan sun amince acikin hutun nan naku yake so ayi komai a gama, in yaso kya karasa project dinki a gidan sa, kinga nan da baifi wata biyar ko shida ba za'a gama komai" Hafsat ta boye fuskar ta a cinyar mommy wai ita kunya, su yaya Habeeb suna ta tsokanarta da amarya, ni kuwa, shock din maganar ne ya daskarar dani a inda nake zaune, mommy ta kara da cewa "ni dai kam ni aka tasa a tsaye, lokacin yayi min kadan gaskiya, saboda ni plan dina shine nan da kamar shekara biyu masu zuwa, so nayi yadda kuka taso tare ke da moon in hada ku rana daya in aurar daku shikenan" I have heard enough, na mike zuciya ta tayi min nauyi na kama hanyar fita, ina jiyo su suna ta making plans, mommy ta kira daada tana gaya mata. Ina fita part dinmu na shiga, sai kuma na rasa me zan dauka, sai kawai na dauki hijab dina na saka na kama hanyar gate. Ni kaina bansan inda zani ba, I just want to get away for a while. Baifi saura wata biyu ya rage mana muyi hutu ba, muna yin hutu zamu tafi Nigeria. Allah ne kadai yasan irin abinda zan fuskanta a can. Dan jiki na yana bani baffa zai iya cewa a hada aure na dana Hafsat, da zarar nace bani da saurayi kuwa za'a ce ai ga munnir nan yana ta zaman jira. Allah ya gani bazan iya auran munnir ba. I despise him. To ko Mahdi zan lallaba ne? But I don't love him and I will end up hurting him. Ya Ilahi. Ina fita gate na hango motar Zayed a gurin da yake tsayawa in yazo gurin Hafsat. Na juya na fara tafiya in opposite direction, ina jinsa yana horn kuma nasan dani yake amma naki juyowa. Ban ankara ba sai ganin mota nayi a gaba na, yayi winding glass din motar ya kalle ni da murmushi a fuskar sa "beautiful one ina zaki je ne haka ke kadai kuma a kafa?" Nayi niyyar inyi banza in rabu dashi tunda duk shi ya ja min daya dauko maganar auren Hafsat amma kuma sai na kasa, it is not in my nature wulakanta mutane. Na karasa kusa da motar sa nace "nan baya zan je ba nisa" daga yadda yake kallona nasan bai yarda da maganata ba, ya bude kofar motar yace "shigo in kai ki" na danyi jim sai kuma na shiga. Ina zama yace "What is wrong" kawai sai jin hawaye nayi yana zubo min, nayi sauri na rufe fuskata da hannuna na fara kuka. Ya gyara packing din motar ya zauna, bai ce min komai ba, bai kuma rarrasheni ba, sai da nayi kuka na me isa ta sannan na dube fuskata ina goge idona da hannuna, ya miko min box din tissues, sannan ya sake tambayata "what's wrong?" Nan take na fara bashi labarin tun farkon haduwar mu da Ibrahim, aikin da na saka daddy ya samo masa, graduation din mu, yadda ta kasance ranar da yazo gidan mu da tafiyarsa, dawowarmu England da labarin aurensa,na kara da cewa "har yau babu shi babu labarinsa, he might be dead for all I know. Amma na kasa chire shi daga raina, na rage tunaninsa amma na kasa mantawa dashi, I can't fall in love again" sannan sai na bashi labarin Munnir, na kuma bashi labarin Mahdi. Na kara da cewa "yanzu muna zuwa Nigeria aka fara maganar ku da Hafsat, shikenan hankalin kowa zai dawo kaina, ko dai in fito da miji, which I don't have, ko kuma a aura min Munnir, who I don't love". Nayi shiru idona a lumshe ina sauraren yadda zuciyata take bugawa. Zayed yayi gyaran murya yace "do u want the truth?" Ba tare da na kalle shi ba na gyada kaina. A hankali yace "He is not coming back" na juyo da sauri na kalleshi ya gyada min kai tare da maimaitawa "he is not coming back" na dauke kaina na daina kallonsa, yacigaba da cewa "he left because he weak and unsure of himself, yes, sanda ya tafi maybe yana da niyyar dawowa sanda yaji he is strong enough, auren sa ya kara rage chances dinsa of coming back to you saboda matarsa zata yi iya kokarinta wajan janye hankalinsa daga kanki, da zarar ta haihu kuma shikenan hankalinsa zai kara karkata kan 'ya'yansa. After almost five years kuwa his chance of coming back to you is zero percent. Dole ki saka a zuciyarki kuma ki yadda da fact that he is not coming back. Abu na farko kenan. Abu na biyu shine, dole kiyi opening heart dinki for another man. Love at first sight is very rear dan haka idan guy yace yana sonki kamata yayi ki bashi chance, get to know him sannan zaki san cewa you can love him or not. You are very young and very beautiful Moon, your life is just starting, kar ki bar wani can da maybe ya manta dake yayi ruining happiness dinki. Open your heart to both Munnir and Mahadi and whoever else comes your way. Kina jina Moon?" Na gyada kaina yayinda wasu siraran hawaye suka biyo kuncina. Ya cigaba "daga duk kan stories dinki da nake ji a gun Hafsat, na fahimci cewa you have a good heart, mutane like you, I mean people with good heart sun fi kowa facing challenges a rayuwa akan harkar aure, kasuwanci da sauran al'amuran rayuwa saboda Allah yana testing din su yaga how good they are saboda He is saving something good for them"
Idan kana ta samun matsala a rayuwa, kuma ka tabbatar baka da hakkin kowa akan ka, ka tabbatar kana bin iyayenka kuma kana da zuciya mai kyau wacce babu hassada babu ganin kyashi babu kwadayi ko zalunci a ciki, to ka tabbatar cewa jarabawa ce daga Allah kuma in har kaci jarabawarka to sakamakon ka zai zamo something very good aduniya da kuma lahira. Allah ya bamu dacewa, Ameen.
Tunda muka yi magana da Zayed sai naji tamkar an sauke min wani nauyi daga kaina, maybe dama I needed someone to talk to. Naji na samu confidence na facing ko menene yake tahowa gareni ko da kuwa auren munnir ne. Kafin mu rabu ranar sai da ya saka nayi masa alkawarin duk halin da nake ciki zan ke zuwa ina gaya masa. Ina zuwa asibiti na samu Mahdi bace masa ni fa bana jin dadin yadda muke yi yanzu, ina so mu koma kamar da, ya nuna min cewa komai ya wuce, nan muka cigaba da al'amuran mu kamar da. A gida kuwa mommy sai shirye shirye take yi, daddy kuma yayi waya Nigerian embassy da ke UAE ya basu information din Zayed ya saka suyi masa bincike akan sa da family dinsa. Hafsat da Zayed kuwa sun dage sai diga soyayya suke kamar zasu chinye juna, inna gan su sai inyi ta sha'awarsu, both gentle, kuma Hafsat duk rashin kunyar ta in suna tare sai inga tayi laushi, dan ko harara ta zata yi sai taga baya kallonta tukun.
Mun kallama clinicals din mu an sallamemu daga asibiti muka koma school, inda acan ne aka bamu project topics wanda kowa ake so ya kammala acikin shekara daya. A bangaren psychology da nake yi ne coordinator din mu ta bani wani strange topic. Abinda tace shine "kowanne mutum yana da sides guda biyu, da akwai side din da yake in the light da akwai kuma side din da yake inda dark. Shi light side din shine wanda mutum yake nunawa kowa yana gani, ma'ana, dabi'unsa da kowa ya san sa dasu. Shi kuma dark side din shine wanda mutun yake boyewa, ma'ana, dabi'unsa wadanda ba kowa ne ya sansa dasu ba. Wannan side din shi ta kira da shadow, kowa yana dashi amma ba'a ganin sa sai mutun ya fito cikin haske. Naturally da akwai mutanen da suke iya boye dark side dinsu yadda babu wanda yake gani, even if you are a psychologist you have to look very deep kafin ka gani. Compused? Kar ku damu kawai dai an bani project a psychology. Task dina shine in samo irin wadannan mutanen in binciko shadow side dinsu, ba tare da sunsan ina bincike akan su ba. Hint din da ta bani shine, most of them are attention seekers, saboda suna son su nunawa mutane light side dinsu yadda ba za a ga shadow side din su ba. Don't worry, zaku gane later.
Da haka muka tattara ina mu ina mu sai Naija. Muna zuwa Nigeria kamar yadda aka tsara haka ce ta kasance, an bawa su Zayed rana kuma sunzo, a Abuja suka sauka daga nan daddy zai saka a raka su 'yalleman. Babu yadda daddy bai yi dasu ba akan su sauka a gidan mu amma suka ki, suka sauka a hotel. Shi kuwa Zayed dama direct nan ya taho, ko kunya baya ji, ya sauka a dakin ya Walid, nan Hafsat aka hau hidimar yi masa girki kala-kala. Kwanan su daya a Abuja suka tafi 'yalleman da ya Walid da wadansu abokan daddy su biyu. Ranar da suka tafi Hafsat kwana akayi ana sallah. Washegari Amira tazo muka hadu muka saka Hafsat a gaba da tsokana. Nayi mamaki da naji Amira ko mentioning Ibrahim bata yi ba. Zuwa wajen la'asar Zayed ya kirani a waya yace "congratulations, I am going to be your brother inlaw in the next two months" nan na yar da wayar ina ihu, Amira da Amina suka biye min Hafsat kuwa ta shige toilet ta rufe kanta
Episode Thirty Five : When Destiny Calls.
Shirye2 ake yi sosai na bikin Hafsat, tun ana saura sati biyu gidan mu ya fara cika, mutanen Niger sunzo sun sauka a part din daada. Amira kusan kullum sai ta zo mun yi namu plans din, ita kuwa Hafsat ba abinda ya dame ta na shirin biki, soyayyarta kawai take zubawa. Zayed ya kira ni ya tambaye ni yadda al'adar mu take na harkar biki, nayi masa bayani dai dai misali, nan ya saka ni na yi gaya masa size din kayan Hafsat dan yasan ita ba fada zata yi ba. Duk wanda yazo gidan sai yace "dama tare aka hada da Moon da shikenan an huta" araina sai ince "in kun kawo min mijin ba sai kuyi min auren ba". Mommy ta zage dantse sai siyayya take yiwa Hafsat kamar babu gobe, kayan fitar biki akwati set guda mommy tayi mata, nima kai na da ba amarya ba na sha kaya har sai da na gode Allah. Mun tsara mu kawaye za muyi bridal shower da dinner, mommy zasu yi kamu, kunshi da mother's evening, daga nan kuma sai ayi daurin aure. Familyn Zayed suma sun shirya bridal welcome dinner wacce za'ayi a can England in an kai amarya. Tun maganganun mutane basa damuna akan Hafsat zatayi aure ta barni har suka fara damuna, ga hidimomi sunyi min yawa, ga surutun mutane. To rob salt to my wound sai ga Munnir nan yazo tun biki saura sati daya. Ina daki ya kira ni naki dauka, sai ya kira Amina, ina jinsu suna magana sannan tace min "Moon angonki yazo" ji nayi kamar ta watsa min ruwan zafi, nace "in kin gaji da ganin sa babu aure ke ba sai ki aure shi ba" tayi dariya tace "mai da wukar, ni 'yar aike ce. Allah da gaske nake yace kije yana compound" nayi tsaki na gyara kwanciyata a raina nace "ai gidan ba bakonsa bane, kuma shi ba makaho bane" shikenan kuma yanzu mutane zasu kara takura min, shima kuma zai kara takura min, duk burin da naci na bikin nan bana jin zan ji dadinsa, na sake tsaki na ja bargo ina neman bacci amma yaki zuwa. Tun sanda mukayi magana da Zayed nake kokarin inga ko yaya ne na saka son Munnir a raina amma na kasa, tun ina yarinya bana son sa duk abinda yayi haushi yake bani, He is so arrogant and selfish. A hankali bacci ya fara dauka na. Kamar daga sama naji ance "out all of you" nayi sauri na bude ido na saboda naji muryar tayi kama data munnir. Na mike zaune da sauri kawai na ganshi a tsaye a tsakiyar dakin yana korar Amina da Amira. Ina ma Hafsat tana nan dan nasan bazata fita ba. Da sauri na fara neman abinda zan rufe jikina dashi, suna fita yayi locking kofa lokacin na samo hijab ina kokarin saka wa, cikin taku biyu ya karaso inda nake ya warce hijab din yana tsareni da ido, cikin gadara yace "dan baki da kunya shine na kira ki kika ki dauka, na aiko ace kizo kika ki zuwa ko? Who the hell do you think you are? Kin manta akwai alkawarin aure na a kanki? Badan wannan stupid uncle Aliyun ya hana ba da tare baffa yace ayi dana Hafsat, ni dai Allah ma ya sani ana shiga hakkina" na tattaro duk bravery dina nace "to in an shiga hakkin ka ka nemi wata matar ka aura mana? Ko ni kadai ce mace a duniya? Ba lallai ba dole kayi hanyar ka inyi tawa" yana kallona da mamaki yace "me yasa ba kya sona wai" direct nace "baka yi min ba" maimakon yaji haushi kamar yadda nayi tsammani sai naga yana murmushin mugunta "don't worry, I will surely change that duk ranar da aka kai min ke, you will begin to like me then" ya fada yana lasar lebensa, nayi sauri na dauke ido na daga kansa ina kallon kasa, ji nayi bai sake magana ba na dago na kalleshi, idansa na gani kyar akan kirjina, ba shiri na mike nayi hanyar toilet, kafin in karasa naji ya kamoni ya hada da jikin bango ya hada jikina da nasa, na zazzaro idanuwa cikin tsoro yayi sauri ya saka hannu ya toshe bakina, a kunne na ya rada min "ko yanzu ya kamata in fara making changes din ne? Kinga dole ki aure ni tunda ba wanda zai karbi second" Sai kuma ya maida kallonsa akan abinda ya tsokane masa ido yana murmushin mugunta ya fara kokarin dora fuskarsa akan saman kirjina daya fito ta wuyan rigata, hannun daya toshe bakina dashi na gantsarawa cizo, babu shiri ya bude min baki, na dage da duk karfin da Allah ya hore min na kwalla ihu, da sauri ya sake ni ya ja baya yana kalle2, na kuma dage wa nace "daadddyy, moommmyy, Haafsaaat,... " kafin in kai karshe ya bude kofar ya fice da saurinsa. Nan na durkushe jiki na yana ta karkarwa. Da yake kofofin gidan sound proof ne sai ya kasance babu wanda yaji ihu na, ni kadai nasan abinda ya faru. How can I marry a man like that?.
Ranar Wednesday ita ta kama ranar da za'a fara biki, ranar ce ake yin kunshi da bridal shower, Thursday za'ayi mother's eve da kamu, friday su Zayed za su zo shi da friends dinsa za muyi dinner, Saturday da safe za'a daura aure daga nan za'a tafi a akai amarya. Amarya kam tasha gyara ciki da waje, from head to toe, nima kuwa banda gyaran cikin, duk wani gyara da akayiwa Hafsat na waje to anyi min nima, dan haka jin mu muke yi on top of the world. Tun safe 'yan yalleman suka fara zuwa, duk wadanda suka zo sai sun bata min rai "amaryar Manniru, amaryar Manniru" duk sai inji farin cikin da nake ciki ya kau, dan ma dai ni ba mai iya bacin rai bace. Tun safe masu kunshi suka zo duk aka fito compound din gidan ana ta kunshi, ja da baki, Amarya aka fara yiwa nata sannan mu, sannan sauran mutane. Anata hidimar kunshi har yamma sannan mu kuma muka fara hidimar bridal shower din mu. Abin ya tsaru sosai domin Amira akwai iya tsari, amarya tayi kyau a cikin gown lemon green ta rike pink roses an dora mata pink crown akanta, mu kuma duk munsa gown light pink da light green din jaka da takalmi. Ana tsaka da hidima naji karar waya ta ina dubawa naga uncle Aliyu. Gaba na ya fadi, na koma can gefe inda babu haya niya na dauka na gaishe shi, ya amsa min cikin kulawa sannan yace "Maimunatu tunda aka kawo zancen maganar auren Hafsat gabadaya gida ya hargitse akan maganar auren ki kema, Hajja ta dage akan lallai sai an hada anyi auren ku tare" numfashina ne gaba daya yake neman daukewa, jiri naji yana dibana, "ya Allah" na furta a hankali, yace "ki kwantar da hankalinki, na samu na shawo kan baffa, nayi masa bayanin cewa ita Hafsat mijinta acan England din yake da zama, ke kuma in akayi miki aure za'a dora miki nauyin aure ne har tsahon shekara guda kafin ki tare da mijinki. Na samu ya yarda sai next year in kin gama project din ki" wata ajiyar zuciya na sauke wacce karfinta sai da yasa na durkushe a gurin, ya cigaba da cewa "Moon kar ki bani kunya don Allah, kinga na kara nema miki lokaci, ki daure kafin lokacin ki ya cika ki fito da mijin aure, kin san halin munnir ba sai na gaya miki ba, Munnir ya wuce duk inda kike tsammani, daga ni har yaya Ambassador bama son hadin nan amma in har kika gama makaranta ba tare da wani tsayayye ba to dole mu bari a aura miki shi".
Gaba daya naji taron ya fita daga kaina, muka yi sallama dashi na koma gurin taro amma sam hankali na baya jiki na. Na tsaya kusa da Hafsat kenan muna yin pictures naji hayaniya ta karu, ina juyowa naga Munnir ya doso inda muke fuskarsa dauke da wannan murmushin nasa da yake karamin tsanarsa. Ideally maza basa zuwa bridal shower saboda kayan da ake sakawa masu bayyana jiki ne, to shi in banda iskancinsa mai ya kawo shi? Yana zuwa kusa dani ya bude rafar yan 1000 yana watsa min, ya gama abinsa yace "kinyi kyau, my darling" sannan ya juya ya fita yana wani takun bada fadi wai shi yana ganin ya hadu. Wani tukuki naji a raina saboda ganin duk gurin ni ake kallo daga masu dariya kasa kasa sai masu rada a tsakanin su. A hankali na janye jikina na shige cikin gida. Direct dakin mu na shiga na zauna bakin gado na rufe fuskata da hannayena "Ya Allah, ka bani yadda zan yakice wannan bawan naka daga gareni, Allah ka kawo min mafita. Ina haka naji hayaniya ana hawowa, cousins din mu ne wajan su biyar suka shigo, ciki har da kannen munnir su biyu, suna shigowa Nusaiba tace "Maimuna ta Munniru, Maimuna ta Munniru" nan take sauran suka dauka suma. Da ace ina da bindiga zan iya harbe su amma su sunki su gane. Na juya da nufin fita kenan aka bude kofar, Amira ce tare da wasu daga cikin kawayen mu na sec sch, suna shigowa Hasiya tace "Moon wai da gaske wannan mutumin zaki aura wai? Ina uncle Ibrahim?" Na juya ba tare da nace mata komai ba, har na kai kofar toilet ta sake cewa "Moon ina Ibrahim?" Na murda kofar toilet din na shiga na rufe. Finally, i am alone. Direct shower na shiga na kunna da complete kaya a jiki na har takalmi na ban cire ba, la lumshe ido na ina addu'a a zuciyata "ya Allah ka bani ikon cin wannan jarabawar, Ya Allah idan wannan shine zabinka a gareni ka bani karfin zuciyar dauka, Allah kaine Allah, Allah kayi min jagora zuwa inda yake mafi alkhairi a gareni" nan na fara amfato sunayen Allah, ban fito daga shower dinba sai da na gama su duka 99 din. Ina fitowa na cire kayan jikina na daura rob na koma dakin, har yanzu a cike yake ana ta hayaniya, kayana na diba na koma toilet, doguwar riga ce ta atamfa purple da white, rigar ta kama jikina daga sama, daga kasa ta bude sosai, ban daura dankwali ba na dauko farin veil na yi rolling, na fesa turare. Ji nayi gaba daya zaman gidan ya ishe ni it is like everyone is against me. Sama sama mukayi magana da mutanen dakin na fice, falo ma a cike yake, compound ma duk samari ne da 'yan mata ana ta tadi, addu'ah nake tayi a raina Allah yasa kar Munnir ya ganni, can na hangoshi ya ritsa wata yarinya amma ban gane fuskar taba, ni dai na wuce da sauri nayi gate, sai ranar nayi nadamar ya akayi ban koyi mota ba, na duba agogon waya ta naga 9:00pm. Ina ta tafiya har na isa bakin titi na tari taxi nace ya kaini Hilton. Ni kaina bansan dalilin da yasa nace akaini can ba. Muna zuwa na zarce restaurant dinsu na samu guri acan wata corner na zauna. Waiter tazo ta kawo min menu nace ta kawo tea kadai.
Banfi minti goma da zama ba ya shigo gurin. Yana fitowa daga revolving doors din ya tsaya yana kalle kalle. Kallo daya nayi masa nasan tabbas nasan wannan fuskar, amma na kasa tuna a ina nasan shi. To ko a England ne? Yana tsayawa naga securities out of nowhere sun bayyana a gurin, amma basu ce masa komai ba, they just look ready. Na cigaba da kallonsa daga inda nake zaune, a half breed, half african half something else. Gashin kansa a hargitse kamar wanda ya tashi daga bacci, rigarsa tayi squeezing, body hug ce wadda ta kama jikinsa sosai ta fito da kakkarfan kirjinsa, damatsensa da suke a bayyane a mummurde suke kamar wanda yake wrestling kullum (who knows?). Bashi da tsaho sosai amma ba za'a ce masa gajere ba. Ya saka hannunsa a cikin gashinsa yana dan sosawa kamar mai tunanin wani abu hakan yasa muscle dinsa yayi flexing, nayi sauri na dauke kaina, zuciya ta naji tana bugawa. Who is this? I know him but where?
Wow, gaskiya yau nayi typing da yawa. Somebody give me a cookie. Lol.
EpisodeThirtySix: Interesting
Na sake daga ido na na kalle shi naga still yana tsaye a inda yake, sai dai ya saka hannayensa a aljihun wandonsa yana karewa gurin kallo, as if he owns the place. Securities ne masu sanye da kaya masu tambarin Hilton suke ta kara shigowa cikin restaurant din, sai a sannan na lura cewa kusan rabin mutanen gurin shi suke kallo amma shi daga dukkan alamu bai ma san anayi ba. Banyi tsammani ba kawai sai ganin idonsa nayi cikin nawa, nayi sauri na dauke kaina na wayance da daukan kofin tea na da ya kusa sandarewa na kurba. A lokacin ne naji wani security a kusa da inda nake zaune yana yin waya "oga mutumin ka ne fa ya shigo yanzu, eh shi kadai ne yallabai, gamu nan duk mun shigo ciki muna observing dinsa in case ko zai yi halin nasa. Ok sir" na tabbatar akan mutumin da ya shigo yanzu ake waya, interesting, so you are a trouble maker. Na sake kallon inda yake tsaye sai naga kamar wanda na kira shi, ya juyo direct ya taho wajan table dina. Nayi sauri na dauki cokali na fara juya tea dina duk da cewa babu abinda na kara a ciki, zuciya ta kamar ta fito waje, na shiga uku, kodai mutumin nan baya son kallo ne kuma yaga ina ta kallonsa shine zaizo ya kwada min mari? Na kasa daga ido na ballantana in tabbatar gurin nawa ya taho. "Assalamu Alaikum" a firgice ba dago kaina na kuwa ganshi a tsaye a gaba na. Duk yadda naso in hana kaina kallonsa amma na kasa dauke ido na daga fuskarsa. Fatarsa chocolate ce mai haske, misali ace ka hada coffee ka zuba masa ishashshiyar madara, tas take cike da alamar kulawa da jin dadi. Tunda nake ban taba ganin idanu masu kyau irin nasa ba, farare ne tas masu maiko, bakin ciki kuma ba baki bane ba, light brown ne, wannan ne ya kara tabbatar min da cewa ya hada jinsi da fararen fata. Girarsa mai yalwar gashi ce, lips dinsa jajawur tamkar ya shafa jan baki mai turuwa. Fuskarsa ba mai tsaho bace ba kuma bata cika fadi ba, tana zagaye da kwantaccen saje wanda ya sha gyara. Gashin kansa a hargitse, amma daga gani kasan ba gashin hausawa bane. Finally na dauke ido na daga kansa na cigaba da aikin juya tea din da yake gabana. Can kasan makoshi na amsa masa "Amin wa alaika as salam" yace "mind if I join?" Mind If I join? Wani ya taba gayamin exactly wadannan words din. Ibrahim, a library, maganar da muka fara yi daga ni sai shi ranar da naki zuwa class dinsa. Na kirkiro murmushi, at least ba mari na yazo yayi ba, nace "bismillah, zauna babu wani abu" sai da ya zauna sannan na tuna cewa har yanzu fa juya tea nake yi. Na dauki kofin na cigaba da sha, da shi da ruwan fanfo basu da maraba sai sugar. Na dan saci kallonsa ta saman kofin hannuna kawai sai muka hada ido shima yana kallona, a tare muka yi sauri muka dauke kai. Ya danyi gyaran murya yace "so.. Me zaki ci?" Na nuna masa kofin hannuna nace "tea nake sha" ya wani bata fuska kamar abin kyankyami yace "tea? Are you telling me kin baro gida kin taho nan dan ki sha tea? In fact restaurant din nan ma basu iya tea mai kyau ba, what is so special about it?" A takaice nace masa "bana jin yinwa ne shi yasa" wani murmushi yayi wanda sai da naji shi har kafafuwa na yace "in kika ga abinda zanci yanzu, dole ki ji yinwa" daga nan ya daga murya yadda nima kaina sai da na dan tsorata "Wai babu waiters ne a gurin nan?" Ya dawo da dubansa kaina yana murmushi mischievously. Wait, I know that smile, sai yanzu na tuna a inda na san sh, a tv, suna fada shi da wani mutun akan titi police suka zo suka yi arresting dinsa. Dan sarkin Abuja, Sultan, yes, haka naji ya Walid ya ce sunansa, a real big time trouble maker, no wonder daga shigowarsa gurin aka cika gurin da securities. Wait, hakan yana nufin ina zaune a table daya da criminal kenan?
Ta gefen idona naga securities guda biyu sun zo gefen mu sun tsaya, sannan sai ga wata waitress nan tazo da sauri ta kawo masa menu ta ajiye a gabansa, daga ganin ta kasan a tsorace take, nima ta ajiye min a gaba na, na daga mata hannu alamar bana bukata, bai dago kai ba yana duba menu din gabansa yace "don't worry, I will order for you. Please don't say no" bance komai ba har ya gama bada order dinsa ta tafi. Ya sauke ajiyar zuciya yace "Allah yasa kar su dade, dan yunwa nake ji sosai kuma bana so kice zaki tafi ba tare da kinci abinda nayi miki order ba" ni dai bance komai ba kawai na cigaba da shan tea dina wanda by now ya tashi daga ruwan fanfo ya koma ruwan fridge. Na ajiye kofin nayi signal na akawo min bill zan tafi, fuska sosai ya bata yana cewa "dan Allah karki tafi" waitress ta taho zaka kawo min bill yayi mata wani kallon banza ba shiri ta koma da sassarfa. Yau na ga ta kaina ni Maimunatu. Na kalleshi with serious note nace "serious tafiya nake so inyi, dare yayi kuma a gida ba'a san na fito ba" ya gyada kai alamar gamsuwa sannan ya sake daga murya "waiter!!" Sai gata ta dawo har tana sassarfa, yace "na fasa cin abinda nayi order, just bring us something simple, a fried rice with chicken perhaps" tace "but sir, already an fara shirya maka wancan order din" ba tare da ya kalleta ba yace "i don't care, bring us fried rice and be very quick about it" har tayi gaba ya sake daga murya "make sure the chicken is not burnt" dariya yake yi kasa2 yace "tsaya kiga wani abu" wayarsa ya zaro ya fara magana da dan karfi "yah Amir kana ina ne? Ina Hilton wallahi yunwa nake ji gashi suna wasting time dina sun wani sa securities sun tsatstsaya a kaina, eh mana, in dai basu kawo min order ta in the next two minutes ba, kuma basu janye securities dinsu ba to abinda zanyi musu sai yafi na last week, kasan halina ai" daga haka ya kashe wayar yana mischievous smile dinsa. Daya bayan daya securities din suka ringa fita, hatta mutanen gurin gani nayi suna tashi suna fita, dariya yayi yace "now a person can eat in peace, amma idan mutane in yayi yawa ma ai mutun ba zai iya cin abinci ba" a raina nace au kasan ana kallonka ashe.
Da sauri waitress din tazo tayi serving din mu, babu musu na kama cin abinci na dama nima din ina dan jin yunwar dan in ana taro sam bana iya cin abinci. Daga dukkan alama kuwa yunwar yake ji dan da gaske yake cin abincinsa. Sai da yaci kusan rabi sannan ya fara magana "kinsan har nayi bacci kawai na farka naji ina jin yunwa? Nasan cikin gida babu abinda zan samu sai tuwo shi yasa na taho nan. Amir ya tafi yawo ya barni, i don't like coming out alone. I hate being alone" a raina nace wannan surutu ne dashi kenan. Ya sake cewa "what's bothering you?" Na kalleshi na dan bata rai nace "me ka gani?" Ya danyi murmushi "a girl all alone in a restaurant, tana shan tea, it is either you are trying to getaway from something or you are or you are waiting for someone" sai kuma ya ajiye spoon din hannunsa ya bude manyan idanuwansa a kaina "ko ni kike jira dama? Maybe we are destine to meet here, har nayi bacci fa na tashi na fito na taho nan, ke kuma only God knows what you were doing kika fito ke kadai kika taho nan" ni ma na ajiye spoon din hannuna ina jin jina maganarsa. He is not my type, too rough for me. Na girgiza kaina nace "it is just a coincidence, i just wanted to be alone shi yasa nazo nan" yayi kasa da murya kamar me rada yace "let me tell you a secret, am a magician, kina gaya min abinda yake damun ki zaki nemi duk matsalolinki ki rasa" yadda yayi maganar ne yasa dariya ta kubuce min, shima dariyar yayi wadda tasa maikon idonsa yayi kyalli, kyawawan hakoransa suka bayyana, shima kallona yake yadda nake dariyar. Sai da muka gama dariyar mu sannan ya sake cewa a hankali "there you go, yanzu kinga ai kinyi dariya har naga dimples din ki" kunya naji na rufe fuskata shi kuma ya cigaba da dariya "wani ya taba gaya miki cewa you are very beautiful? Very unique?" Na bude fuska ta a hankali nace "thank you" har yanzu fuskar tawa yake kallo. Na mike a hankali nace "thank you for the food and the talk" da sauri nayi hanyar fita, yace "wait" ban tsaya ba kuma ban waigo ba, na bude kofa na fice, ina jinshi yana kwalla wa waiter kira. Sai da na fito sannan na tuna cewa ba da mota nazo ba. Na duba agogon hannuna naga after 11.oh God Allah yasa ba'a neme ni a gida ba.
Tun daga bakin titin na jiyo karar cin taya, jikina ya bani shine zai fito kuma na tabbatar nema na yake yi, oh God me yasa banzo da mota ba? Da sauri na kama tafiya ina rufe fuskata da mayafi na, ai kuwa banyi wani nisa ba naji an ci taya a gefena, ban kalleshi ba na cigaba da tafiya ta, ya bude motar ya fito ya sha gabana yana dariya "thank God bada mota kika zo ba da tuni kin gudu, wow, na tsorata da yawa fa" na dago kai na kalleshi, sai yanzu na kara ganin kakkarfan jikin shi. Ya cigaba "ko sunan ki fa baki gaya min ba, and after seeing your face kina tunanin zan iya bacci with out knowing your name?" Direct na bashi amsa "Sunana Hafsat" "I always like the name Hafsat, muje in sauke ki a gida ko?" na girgiza kaina nace "thank you, amma ni ba zan shiga motar ka ba, I don't know you" yace "sunana Sultan, shikenan?" Na sake girgiza kaina. Ya fahimci dai da gaske bazan shiga motar saba sai yace "to dan Allah ki bani address dinki mana" ba musu na bashi address din gidan su Amira, bakinsa har kunne yana dariya yace "ok, saura phone number" ya miko min phone dinsa na karba na saka masa tsohuwar number din Ibrahim da na haddace. Nishadi yake sosai yana jin dadi. Ya tarar min taxi na shiga sannan yazo window yace "it is very nice meeting you Hafsat, i will call you in na je gida" nace masa "ok, nice meeting you too Sultan"
Ga mamaki na sai na samu kaina da waiwayensa bayan motar mu ta ja, yana tsaye yana kallon motar mu ya saka hannayensa a aljihun wandonsa. Sai kawai naji tamkar na bar wani part of me with him. Na runtse ido na "ya ilahi, sultan is not my type, he is a rogue" amma me yasa sanda muke tare dashi naji for the first time na manta da Ibrahim? A lokacin da muka yi dariya ni da shi na manta da duk wadansu problems dina dana fito na bari a gida. Yanzu kam nasan ba lallai ne mu sake haduwa dashi ba, amma kuma nasan bazan taba mantawa da fuskarsa ba.
How do you guys like Sultan?
Masoyan Ibrahim ga rival anyi muku.
Episode Thirty Seven : The Dinner
Gaskiya kalamai ba zasu fayyace muku jin dadi na ba akan yadda labarin nan ya samu karbuwa. Nagode Allah ya bar kauna.
Masoyan Ibrahim kar ku bani kunya mana tun yanzu. Lol
Zaku ga changin yanayin rubutun labarin, nayi haka ne dan a samu fahimta sosai. I hope zakuyi enjoying sabon tsarin. Much love from maman maama 💖
Ya jima yana kallon motar har ta bace. Sannan ya juya ya shiga motar sa ya figa a guje ya dau hanyar palace. Yau dama sam bai yi niyyar fita daga gida ba. Tun daga nesa ya danne horn din motar sa, dama ya saba kullum abinda yake yi kenan, kowa sai yasan sultan ya shigo, ko mutun yayi bacci sai ya tashi. Yana shiga direct part dinsa ya wuce yayi packing a inda yake ajiye motocinsa. Direct bedroom ya nufa, yana shiga ya kalli kansa a cikin mirror sai ya bata rai yana kallon squeezed rigar sa "damn" ya fada kan gado da kayan sa complete har takalmi. Ya lumshe idonsa yana tuno every detail na fuskarta, it is like brain dinsa tayi automatically saving hotonta. "Hafsat" ya furta a hankali. Tunda yake bai taba yin serious budurwa ba, 'yammatan da yake haduwa dasu duk club girls ne da zasu yi rawa tare and that's all. Shi ba manemin mata bane sam, he consider it dirty. Ya dauko wayarsa ya dubo number dinta da yayi saving yana murmushi a ransa yana yabawa kansa dabarar da yayi na karbar number dinta maimakon shi ya bata tashi, dan yasan ba lallai ne ta kira shi ba. Ko ta karasa gida yanzu? No, unguwar da ta yi masa kwatance tana da dan nisa, bara ya bari a dan kara jima wa tukun. Ya ajiye wayar tare da gyara kwanciya. Har after 12 yana kwance a haka kuma baiyi bacci ba, ya sake dauko wayar yayi dialing "The number you are trying to call is currently switched off, please try again later" "damn you MTN" ya fada tare da jan tsaki. A cikin daren ya kira number takai sau goma amma still switch off ake gaya masa, maybe charge dinta ne ya kare, ya fada a ransa, amma baiji dadin haka ba saboda yana son ko yayane ya sake jin muryarta kafin yayi bacci.
Washegari tunda yayi sallar asuba yake zaune yana kallon agogo, jira kawai yake yi yaga gari yayi haske ya kira ta. 8:00 ya sake dialing number ta amma still switched off. Damn it, kar dai ace wrong number ta bashi, in haka ne kuwa to tabbas address din ma wrong ta bashi. Ya mike da sauri ya shiga wanka, nan da nan yayi ya fito. Duk gayun sa yau da sauri ya shirya cikin usual body hug kayansa, yana fitowa ko kallon bayin da suke zazzaune a falo da abincin da aka shirya masa a dining table bai yi ba ya fice. Agogon hannunsa ya duba yaga karfe goma, yasan tunda Takawa yana gari to duk mutan gidan suna falonsa yanzu. Shima direct can ya wuce, duk masu gaishe shi a hanya babu wanda ya kula, yana shiga yaga Takawa a zaune a kan shimfidar da ake masa ta cin abinci a tsakiyar palon, Hajiya tana kusa dashi daga hannun dama Abbas kuma daga hannun hagu, daga gefe kuma saratu ce da Fa'iza. Daga dukkan alamu hira suke suna dariya har Takawan, shigowar Sultan ce tasa Takawa ya hade girar sama data kasa tamkar bai taba dariya ba, Sultan ya karasa gabansa ya durkusa "barka da assuba" bai samu amsa ba kuma dama bai sa ran zai samu ba, ya mike ya koma kusa da Hajiya ya zauna tare da dora kansa akan kafadarta, ta sa hannu tana shafa gashin kansa a hankali "yaron kirki yau kuma da wuri aka tashi haka? Ko wani gurin za'a je ne" ya girgiza kai yace "no Hajiyata, part din Amir zan shiga nace bara in shigo in gaisheku" Abbas yace "yaya Sultan barka da assuba" sultan ya kirkiro murmushi yace "Abbas, ya kake?" Su saratu ma duk suka gaishe shi daga nan sai kowa yayi shiru. Sultan ya danyi jim a zaune sai kuma ya mike yace "Hajiyata bara inje" tace "to yaron kirki, a dawo lafiya" ya karasa gaban Takawa ya sake durkusawa "a huta lafiya" nan ma babu amsa. Sai da ya fita ya turo kofa sannan yaji muryar Takawa sun cigaba da maganar da suke yi da Abbas. Ya runtse idonsa zuciyarsa tana masa zafi sannan kuma ya saka hannayensa a aljihunsa yayi gaba.
Kamar yadda yayi tsammani, rashe rashe ya tarar da Amir yana ta shirgar bacci, Allah ne kadai yasan jiya karfe nawa ya kwanta bacci dan tunda yace Solomon ya zo gari to yasan sai sun raba dare a club. Tsaki yaja ya daddaka masa duka a cinya "kai tashi daga baccin nan haka" Amir ya bude ido cikin bacci yana kallon sa, "what happened naga har ka shirya, ko ta samu ne?" Sultan yace "eh ta samu, babban samu ma kuwa" nan sultan ya zauna ya bashi labarin haduwar su da Moon da yadda wayarta bata shiga, tunda ya fara maganar Amir kawai kallonsa yake yi, sai da ya gama sannan yace "in baka shawara abokina? Kawai kaje kayi ta addu'a dan kuwa ina da tabbacin gamo kayi da aljana" dariya sosai Sultan yayi sannan Amir yace "to in ba aljana ba Sultan ni ban taba ganin ka damu da wata mace ba, daga jiya zuwa yau har kabi ka tayar da hankalinka akanta, tunda har ta baka wrong number ai bata yi da kai ne" Sultan yayi sauri yace "a'a, raka ni zakayi address din mu gani, maybe wayar ta samu problem ne" Amir yace "wai kana nufin yanzu? Haba rankai dade, duk matsuwarka ai ka bari yamma tayi zuwa dare ko? Saboda tsabar kai sabon shiga ne, ka hadu da yarinya jiya da daddare sannan kawai yau da safe kaje gidansu" Sultan ya fada kan gadon kusa da Amir ya lumshe idonsa, a hankali yace "baka san yadda nake ji bane Amir, ba zaka gane ba"
Moon
Tun dana tashi da assuba ban koma bacci ba, muna ta hidimar kamu da mother's eve da za'ayi yau. Sam na manta da wani Sultan duk da jiya da daddare da kyar nayj bacci ina ta tuna abubuwan da suka faru a tsakanin mu. Anyi taro lafiya an gama lafiya babu wata matsala sai rigimar da akayi da Hafsat akan ita fa lallai ba za'a zuba mata nono aka ba, sai da aka rirriketa kamar mai aljanu sannan aka zuba mata, dan muguntar hajja kwarya guda ta juye mata. Mu dai muna ta dariya. Hajja ta juyo tace min "in naki yazo wanka zanyi miki dashi" Munir kam ya zamar min tamkar jela, cikin mata ko cikin maza duk inda nayi sai ya bini kuma sai yayi maganar da zata sa a gane akwai wani abu a tsakanin mu. Washegari da wuri jirgin su Zayed ya sauka shida abokan sa guda biyar, sai Waliyansa su uku. A ranar ne kuma zamuyi dinner da daddare, Zayed ya kawo mana kayan da zamu saka ni da Hafsat, dogayen riguna ne masu kyau, wadanda kuma suka rufe mana jikin mu ruf, iri daya ni nida ita sai dai banbancin color, ta Hafsat golden tawa cream. Ni samun wannan rigar yasa duk na manta da dinkin mu a gurin tailor ni da Amira wanda da muka yi niyyar zamuyi anko ni da ita. Ban tuna ba sai da muna shiryawa ta kira ni tace gata nan zuwa. Ai kuwa ina gaya mata ai ban karbo ba ni na samu wasu kayan ta hau bala'i daga karshe ta kashe wayar gaba daya. Nima nasan ban kyauta mata ba amma abubuwa ne suka yi min yawa shi yasa. Har muka gama shiryawa muka tafi Amira bata zo ba, nayi ta kiran wayarta kuma bata dauka, a karshe na hakura na rabu da ita.
Sultan
A hankali suke bin address din har suka zo gidan. Suna yin packing Amir yace "to munzo, now what?" Sultan ya dan sosa kansa yace "ya akeyi in anzo gurin budurwa?" Amir yayi tsaki yace "ideally kiranta zakayi a waya, to tunda kai baka da number dinta sai ka nemi yaro ka tura shi ya kirata" Sultan ya bude kofar mota ya fito yana ta zagaye ya rasa dan aike, sai da kyar ya samu wani yaro yace masa ya shiga yace ana kiran Hafsat, can yaron ya dawo yace "wai ance babu Hafsat anan gidan" ya juya suka dubi juna shida Amir, Amir ya kyalkyale da dariya yace "sai kazo mu tafi ai, yau dai ka barni inyi bacci tunda ka tabbatar yarinyar nan tayi playing dinka" sultan ya juyo jiki ba kwari ya shiga mota, har zaiyi mata key sai kuma ya dakata yana tunani, can yace "no, bazan hakura ba, tunda har tayi min kwatancen nan gidan to inhar ba gidan su bane ba to gidan 'yan'uwansu ne, ko kuma gidan su kawarta, yes, zan jira inga wanda zai fito daga gidan in tambayeshi ko ya santa" Amir binsa yake da kallo har ya gama sannan yace "you are not serious are you? Kana nufin zama zamuyi tayi a gurin nan har sai wata ta fito mun tambayeta? What if babu wanda ya fito har gobe?" Sultan yace "then I will wait har gobe, in kaga ba zaka jira ba kayi tafiyarka ban hana kaba" tsaki Amir ya sake yi ya kwantar da kujera tare da kunna kida, Sultan kuwa ya fito ya jingina da jikin motar idonsa na kan gidan. Shiru2 har wajan awa daya babu alamar wani zai fito, kuma unguwar shiru babu motsin mutane ballantana su nemi wani information. Amir har yayi baccinsa amma sultan yana tsaye kamar soja. Wannan shine kadai link din da yasan zai same ta dan haka ba zai yi wasa da wannan damar ba. Can kawai yaji motsi daga ciki, sannan yaga an bude karamar kofar gate din. Wata budurwa ce ta fito, doguwa, baka kyakykyawa. Taci kwalliya irin ta kure adaka dinnan, daga gani kasan gidan biki zata je. Suna hada ido da sultan ta danyi baya alamar tsorata sannan kuma ta maze ta rufe kofar tana gyara mayafin ta. Sultan ya karasa kusa da ita yace "Assalamu Alaikum" ta juyo ta watsa masa harara tace "alaikassam, ya akayi" kut, wannan badan information yake nema a gurin taba da sai ya babballata. Ya daure yace "please, wata ce ta bani address din nan gidan tace gidan su ne, sunan ta Hafsat" Amira ta sake yi masa kallon wulakanci tace "ko wacece karya tayi maka, nan babu Hafsat, oyo san inda dare yayi maka" lallai wannan yarinyar bata san hali ba. Daga bayansu suka ji ance "Hey, who do you think you are ana miki magana kina yiwa mutane rashin kunya, da wata mummunar fuskar ki anan, ko ki bashi amsar tambayarsa ko kuma wallahi.. " ta katse shi "ko kuma me Amir? Zaka dake ni ne?" Mamaki ne ya ishe shi yadda ta san sunan shi kuma ta mayar masa da magana ba tsoro. Har ta juya zata tafi Sultan ya sake binta "please, ko cikin kawayenki babu wadda kike tunanin zata bada address dinki?" Kamar ba zata kula shi ba sai kuma ta juyo fuskarta da murmushin mugunta tace "ya kamanninta yake?" Da sauri sultan yace "fara, fulani, very beautiful, tana da dimples manya guda biyu" murmushin mugunta Amira ta sake yi, Amir ya karaso yace "so? Do you know her or not" ba tare data kalleshi ba tace "shut off" Amir ji yayi kamar ya gaggaura mata mari, ko ba yau ba sai ya koya wa yarinyar nan hankali. Ta kalli sultan tace "na gane ta, yanzu ma tana gurin bikin da zanje" wata ajjiyar zuciya Sultan yayi yace "to shigo mota mana mu tafi" ta girgiza kanta tace "no way zan shiga motar ku, Allah ya raba gatari da saran shuka, in kuna son ganinta ku biyo ni" daga haka ta juya tayi gaba. Da sauri sultan ya koma mota ya tayar yana ta yiwa Amir horn dan yayi sauri ya shigo, Amir kuwa bakin ciki ne ya cika shi, wai ba zata shiga motar su ba, wacece ita?. Haka suka yi ta bin Amira a baya har ta fita titi ta samu taxi ta shiga, suka cigaba da bin taxi din har Sheraton. Amir yayi tsaki yace "maimakon kawai tace mana Sheraton, sai ta saka muka ringa binta a baya kamar wasu yaranta. Wannan budurwar taka should better be worth this in ba haka ba akanka zan huce" Sultan yace "believe me, she is worth morethan this" suna fitowa Amira tayi musu nuni da hall din da ake taron tayi shigewar ta ta barsu.
Moon
A matsayina na kanwa kuma babbar kawar amarya nice na ke zaune a kusa da ita a high table, sai Zayed da babban abokin sa Hamad. Ana cikin tsakiyar taron na hango Amira ta shigo, sai da ta gama shawaginta suna gaisawa da mutane sannan ta karaso high table, nan nayi introducing dinta a gurin su Zayed sannan muka dauki hotuna. Sai da muka gama sannan tazo dai dai kunnena tace "I brought a gift for you. Saboda bari na da kikayi babu kayan sawa yau" har ta juya kamar zata tafi nace mata "what gift?" Tace "Sultan, yana bakin kofa" nayi sauri na kalli hanyar shigowa, ga mamaki na kuwa sai naga masu gadin kofar suna ta hayaniya, har mutane sun fara tsayawa kallo. "Damn you Amira"
Episode Thirty Eight : The Shadow
Gaba nane ya fadi da muka hada ido da munnir wanda ya kasa ya tsare yana kallon duk wanda zai yi min magana. Na tabbatar sultan yana shigowa zai hangoni tunda ina kan high table, yana gani na kuwa zai taho, Allah ne kuma kadai yasan abinda zai faru tsakanin sa da Munnir. Na rada wa Hafsat "two minutes, ina zuwa" ta yi sauri ta rike hannuna alamar bata so in tafi in barta, nayi mata alamar yanzu zan dawo. Cikin friends din mu na dan shiga, ina kallon munnir ta gefen idona yana bina da kallo, sai da na tabbatar baya gani na sannan nayi hanyar gate da sauri. Ina zuwa kuwa na ga Sultan ya dunkule hannunsa ya naushi wani mai gadi, nan na nan jini ya fara fita ta hanci ta baki, maybe ma hakori ya fita, wanwar gayen ya fadi a kasa yana gunjin azaba, sultan ya durkusa kusa dashi, na dauka ma hakuri zai bashi, sai naga ya goge jinin daya bata masa hannu a jikin rigar gayen, ya mike tsaye yace "who is next?, dan rainin hankali har ni zanzo ince zan shiga guri ku ce min card admit ne, da card din da admit din duk naci uwarsu gaba daya" da sauri na karaso gurin cikin fada nace "what the hell are you doing" sai a lokacin ya ganni, hannu duk biyun ya saka a cikin gashinsa tare da cewa "shit" na durkusa gurin mai gadin da aka daka wanda har yanzu ya kasa tashi, da sauri sauran guards din suka karaso suka kamashi suka tafi, na mike ina kallon sultan daya kasa hada ido dani nace "what are you doing here?" Ya karaso kusa dani yace "am sorry" sai a lokacin na lura da wanda suke tare, zasuyi kusan tsaho daya da sultan amma bazan tantance kibar saba saboda uban kayan daya loda a jikinsa duk kuwa da yanayin zafin da ake ciki, kansa yasha kwal kwal amma kuma ya bar saje a fuskarsa. Kallo daya nayi masa na maida kallona kan sultan wanda yasha kwalliya dan daga gani wannan shigar ta musammance. Har yanzu ya kasa magana ni kuma na bata rai na tsare shi da ido. Abokinsa ne ce "so, kece Hafsat kenan, kwana biyu wannan sunan har acikin bacci kiransa yake" sai a lokacin na tuno cewa ashe fa ce masa nayi sunana Hafsat. Na sake cewa "uhum, ina jinka, me ya kawoka nan?" Ya sake hargitsa gashin kansa sannan yace "I just wanted to see you ne, please, number da kika bani bata shiga, shine naje address din shima na tarar wrong ne da kyar yarinyar gidan ta kawo munan" nace "OK, ka ganni zaka iya tafiya yanzu" ina fadin haka na juya zan koma ciki, da sauri yasha gaba na, fuskarsa kamar wani abin tausayi "please kar ki koma" nace "serious, bani da lokaci, biki muke yi, na tabbatar yanzu ma nema na akeyi a ciki" da sauri yace "OK, at least ki gaya min sunanki na gaskiya, ki bani number dinki ta gaskiya" ya saka idonsa cikin nawa pleadingly, kawai sai naji na daina jin haushinsa, ya danyi murmushi tare da cewa "pretty please" na danyi murmushi nima kadan. Abokinsa ne yace "OK, lokacin introducing dina yayi" daga ni har sultan babu wanda ya kalleshi, sam ya kasa dauke idonsa daga cikin nawa, ni na fara dauke kaina nace "i really must go inside" yace " OK, sunanki na gaskiya" nace "Maimunatu" ya dauko wayarsa yace " phone number?" Har na fara fada masa sai ya dakatar dani yana karkada hannunsa "not again, an sha ni na warke" ya miko min hannunsa "bani wayarki" na gane me yake nufi dan haka nima nayi dariya tare da mika masa wayar, ya karba ya saka number dinsa yayi dialing, da kiran ya shiga wayarsa sai da ya dauka ya tabbatar shine sannan ya kashe ya miko min waya ta. Ina karba naga an bude kofar hall din an fito, a tsorace na waiga, yaya Habeeb na gani a tsaye yana kallon mu ni da Sultan, sai kuma ya koma ya maida kofar ya rufe. A sauke ajiyar zuciya nace "zan koma kaga already ana nemana" ya gyada kai yace "it is OK, nagode sosai, and please don't block my number" nayi murmushi nace "I won't" na juya na kama hanyar komawa ciki, naji abokin sultan yana cewa "hey, bakayi introducing din mu ba fa" sultan yace "shut up Amir".
Tunda na koma na cigaba da activities dina har aka tashi ban kuma tunawa da wani sultan ba ballantana his troubles, bayan an tashi munje gida duk mun sallami friends din mu, zamu hau samanmu kenan sai yaya Habeeb ya kira ni, na juya na koma duk jikina a gajiye, so nake kawai in ganni a kwance. Ina zuwa naga ya bata fuska yace "dazu dawa na ganki a gurin dinner" sai a lokacin na tuno da wani sultan. Nayi ajjiyar zuciya nace "Sultan ne, dan sarkin Abuja" yace "nasan ko shi waye, kece baki san sultan ba shi yasa har kika tsaya dashi. Duk inda kike tunanin sa ya wuce nan. In ana zancen top criminals a Abuja sunan sultan yana daga layin farko" nace "ya Habibi babu komai fa a tsakanin mu, naga cewa idan ban kula shi ba zai iya tayar da rigima a gurin shi yasa na kulashi, but I know he is a trouble maker and all.. " ya Habeeb ya katseni "trouble maker? He is not just a trouble maker Moon, he is a drunk" ji nayi tamkar ya Habeeb ya watsamin ruwan zafi a fuska, a drunk? Har naje dakin mu jikina a sanyaye yake, can kuma nace a raina, me yasa na damu, it is not as if na damu dashi. Direct toilet na shiga na yi wanka nayi shirin bacci, ina fitowa na ga Hafsat har tayi bacci, nima na kwanta nayi addu'ah. A drunk, but how, me yasa ya zabi wannan rayuwar? Me yasa ya zabi abokai irin su Amir? Dan manyan mutane kamarsa, dan Sarki, sarkin ma na federal capital, how can he be what he is? Me yasa iyayensa ba zasu dau mataki a kansa ba? Waya ta naju tayi kara, na dauka na duba screen "my Sultan" naga an rubuta, nayi murmushi, wato haka yayi saving number dinsa a waya ta kenan. Na ajiye ta na barta tayi ta ringing dinta har ta katse, wani kiran ya shigo sannan wani. A drunk, na maimaita a raina. Take na yanke shawarar in dauki wayar in gaya masa cewa bani da interest a kansa yayi hakuri. Tana fara wani ringing din na dauka "Assalamu Alaikum" naji yace. Assalamu Alaikum, peace be unto you. Wannan itace kalmar daya fara fada min ranar da muka hadu a Hilton. Mutane nawa ne a cikin mutanen kirki suke sallama idan sun kira ko an kira su a waya. Mostly hello ko hi ake cewa wanda ba dai dai bane, amma shi a matsayinsa na known criminal me yasa yake yi min sallama. Ko hakan yana nufin some part of him is good?. Wannan kalmomi na Assalamu Alaikum da Sultan yace min sune suka sa na fasa yanke alakar ta dashi. I feel like I want to know him better.
"Assalamu Alaikum" ya sake maimaitawa, sai a lokacin na samu damar amsa masa "ameen, wa alaika assalam" ya sauke ajiyar zuciyar da sai da naji daga cikin wayar, "sorry I kept calling, ina so ne ko yaya in danji muryarki kafin nayi bacci" nayi shiru babu amsa, yace "ya taron? Da fatan baki gaji da yawa ba" nace "gajiya kam akwaita, sai godiyar Allah" "sorry" na danyi murmushi saboda yadda ya furta kalmar sorry din, ya sake cewa "am really sorry akan abinda ya faru dazu, I came to your party uninvited kuma na yi creating commotion, I just can't hold my temper ne most of the times" nace "it is OK, ya wuce, Allah ya kiyaye gaba" "Ameen, thank you for understanding" kasa2 naji suna magana da wani, nace "kai da waye ne?" Da muryar dariya yace "Amir ne, wai koya min zance zaiyi, wai ni ban iya ba" nace " He is funny" yace "yes he is, bari in barki ki huta kin gaji ko? Na gode da daukan waya ta da kika yi, you have no idea how much it means to me" na runtse ido na inajin kalamansa har cikin raina. Nace "good night" yace "fi amanillah" daga nan ya kashe wayar. Na kara runtse idanuna ina jin wani abu yana min yawo a jikina. Na jima banji irin wannan feeling din ba, tun rabo na da Ibrahim. Nayi tsaki na gyara kwanciya ta, ya kamata in nutsu in san me nake yi especially after warning din da yaya Habeeb yayi min cewa sultan is a drunk, but he didn't look or sound drunk to me. Oh dear God, don't let me fall in love with a wrong guy again. Not again. Da kyar na samu bacci ya dauke ni.
Washegari tun safe aka tafi "yalleman daurin aure, mu dai muna abuja muna ta shirye shiryen kai amarya, Zayed ya dage shi lallai babu zancen wani kafi ko gara, su a al'adarsu in kayi aure mata kawai za'a kai maka, shi wai a gurinsa abin kunya ne aga ana shigar da kaya gidansa wai daga gidan surukansa, dan haka daddy ya hada kudin duk da yayi niyyar yiwa Hafsat kayan daki ya saka mata a account dinta yace inta ga dama tayi jari dasu, in bata ga dama ba kuma ta kashe kayanta, kudin kayan gara kuma ya saya wa Zayed dalleliyar mota ya bashi a matsayin wedding gift. Tunda akayo mana waya an daura aure Hafsat take kuka tamkar wacce aka yiwa auren dole, sanda muka zo tafiya airport kuwa cewa tayi ta fasa auren ta shige daki ta rufe kanta, sai da daddy yazo da kansa sannan ta bude kofar. A hanyar zuwa airport na duba waya ta naga 5 missed calls daga sultan da message guda daya "please in kin samu chance call me" sai na samu kaina dayi masa reply cewa yanzu zamu tafi England, in naje zan kira shi da number ta ta can.
Masha Allah, gidan Hafsat ya tsaru iya tsaruwa, tsayawa bayanin gidan bata lokaci ne, likita matar likita, ina kallon gidan ina tunanin cewa some people are so lucky in life, komai yana zuwa musu da sauki. Embassy muka sauka, anan zamu yi kwana biyu sannan mu dawo Nigeria. Ranar da muka baro Hafsat a gidan miji kwana nayi ina juyi, Allah sarki 'yaruwata shi kenan an shiga layin manya. Sai kawai na samu kaina da imagining what will it feel like, ga mamakina kuma a imagination din nawa sai naga Sultan with his muscular body, red lips and shiny brown eyes maimakon Ibrahim da nake gani duk sanda nayi irin wannan tunanin. Nayi sauri na kawar da tunanin daga raina tare da sake sabuwar addu'a amma still babu bacci. Nayi tsaki na jawo wayata na duba time, 12:30am, a Nigeria zai zama around 8:30am kenan. Nayi dialing number dinsa, bugu daya ya dauka kamar mai jira. "Assalamu Alaikum" na amsa masa, sannan yace "God, saura kadan in running mad, ban taba jin haka a rayuwa ta ba, what have you done to me woman?" A raina nace kai zanyi wa wannan tambayar ai, a fili kuma cewa nayi "haba dai, da girman ka?" Yayi dariya yace "nima na dauka am strong, sai yanzu nake ganewa ashe shayi ma ruwa ne" hmm kawai nace, yace "to ya hanya? Ya kuma amarya" nace "lafiya lau, mun kaita mun baro ta, gobe zamu huta jibi mu dawo insha Allah" yace "so, tell me about yourself" nan na bashi labari na in brief, abinda ya shafi family na da karatu na, ko kadan banyi mishi zancen Ibrahim ba, shima ya fara bani labari da cewa "well, as unbelievable as it may sound, babana shine sarkin Abuja, ni ne first born sai Abbas, Saratu sannan fa'iza, nayi primary a Abuja, sec da university duk nayi su a USA. Na karanci architecture first and second degree. I have many friends but Amir shine babban abokina, he is like a brother to me" daga nan yayi shiru, a hankali nace "what about your mother?" Yayi shiru kamar ba zai magana ba, can yace "I don't know who my mother is" duk da ta cikin waya ne sai da na fahimci irin zafin da maganar da ya fada tayi masa a ransa. Ba wai besan babarsa ba, a'a bai ma san wacece babarsa ba.
Episode Thirty Nine : The Shadow 2
Jinjina ta musamman ga masoya Ibrahim. Lallai kun chika masoyan gaskiya da kuka rike soyayya har tsahon shekara biyar. Ina kuma baku hakuri dangane da jin shiru akansa, na tsara labarin ne a haka saboda in kara masa armashi yadda zaku fi jin dadinsa, amma insha Allahu nan ba da dadewa ba zamu ji labarin Ibrahim.
Jinjina ta musamman again ga masoya Sultan tunda har kuke son sa duk da kasancewar sa bad boy wannan itace soyayya ta gaskiya, kaso mutum ba dan halinsa ba.
💖 you loads
Nayi shiru maganar tana sinking a raina, sannan nace "bangane ba, how comes?" Shima shirun yayi kamar baiji abinda nace ba, munfi minti biyu a haka, ina jiyo saukar numfashinsa ta cikin wayar, can yace "can we please not talk about this? In fact yanzu nasan dare yayi sosai a England, gwara in barki kiyi bacci haka ko?" Na gane waccan maganar ce baya son yi amma nasan bani da right din da zan matsa masa dan haka nima ba bar maganar "OK, good night then" "fi amanillah" na jima bayan munyi sallama ina lissafin maganar sa, me yake nufi? What is his story?
Washe gari tun safe nake baccin gajiya har zuhur sannan inna ta tashe ni nayi sallah naci abinci na sake komawa wani baccin. Sai la'asar sannan na tashi nayi wanka na shirya dan zamu je gidan Hafsat muyi mata sallama tunda gobe da safe zamu koma Nigeria. A gidan Hafsat ne su inna da gwoggo rabi babar su nuraddeen suka yi ta yiwa Hafsat nasiha akan zaman gidan miji, nima na zauna naji kuma na karu sosai, bayan sun tashi suna kara zagaya gidan ne na saka Hafsat a gaba da tsokana wai sai ta gaya min abinda ya faru jiya bayan mun tafi, harara tayi ta watsa min daga karshe tace "wai ke yaushe na fara wasa dake ne? In auren kike so ki fada yanzu zaki ganku a gidan munir" wata harara nima na watsa mata, dan ni har mantawa nake yi da wani munir a duniya, dariya itama tayi min tunda ta kashe min baki. Sai da muka zo tafiya kuma sannan ta fara kuka, babu kunya Zayed ya kama rarrashinta a gaban su inna, sum2 suka fice ina ta yi musu dariya. Kaya sosai maman Zayed ta bamu muka tafi dashi. Washegari da safe muka dawo Nigeria. Duk 'yan biki kuma kowa ya watse sai fatan Allah ya sanya alkhairi.
Sai da aka gama watsewa sannan na fara missing Hafsat, gashi Amina ma bata nan ta bi mutanen 'yalleman zata karasa hutun ta acan. Duk gidan ya gundire ni sam babu dadi. Sultan kuwa kullum sai ya kirani a waya, yayi2 in barshi yazo gidan mu naki, saboda ina tsoron abinda zaije ya zo. A raina nasan ya kamata in dakatar da Sultan amma zuciya ta taki barina in yi haka, sosai nake jinsa a raina, dan wani lokacin ma ni da kaina nake kiransa a waya. Ranar da mukayi sati daya da dawowa daga England na tambayi mommy cewa ina so inje gidan su Amira in wuni acan sai dare zan dawo tunda na gaji da zama ni kadai, babu musu mommy ta barni tace driver ya kaini da daddaren sai ya koma ya daukoni. Na shirya cikin riga da skirt na jar atamfa mai adon fari da baki, na yafa farin mayafi, da farin takalmi, na debi wayoyina muka tafi. Muna cikin tafiya munbi ta wata siririyar hanya sai muka tarar da go slow, gurin ya chunkushe mutane sai hayaniya suke yi, nayi mamaki saboda normally gurin babu traffic, driver nane ya fita ya tambaya sai ya dawo yace min wai wani ne yayi blocking hanyar yace yau babu mai wucewa ta nan, sai dai mu koma baya sai mubi ta wata hanyar. Nayi shiru ina tunani, sai na dauko waya ta na kira number din sultan, ya dauka nace masa "kana ina?" Dariya yayi yace "na fita unguwa ne kuma sai na tsaya neman rigima" bance komai ba na kashe wayar nace da drivern ya zauna ina zuwa, na fita na kutsa ta cikin mutane har inda problem din yake, katuwar Jeep Dodge na gani anyi crossing dinta akan titin yadda ta rufe titin completely, duk glasses dinta a tinted dan haka bana hango wanda yake cikin motar, mutane sai hayaniya suke, wani naji yana cewa "to tunda ba zai dauke ba ba sai a kira masa 'yan sanda ba, in yafi karfin mu ai baifi karfin hukuma ba" wani kuma yace "to in an kira 'yansandan ma ya za suyi dashi? In sun kama shima ba zai awa daya ba za'a sake shi, su kansu yanzu sun gaji da kama Sultan" a raina nace da gaske shi din ne. Number motar na duba naga "SULTAN 3" na karasa kusa da motar, inajin wani daga bayana yana cewa "'yan mata kiyi a hankali fa, wannan mutumin is very dangerous".
Na karasa dai dai windown driver nayi knocking a hankali, da sauri ya sauke glass din fuskarsa ta bayyana dauke da murmushin mamaki "Hey, me kike yi anan?" Na daura hannayena akan windown nayi tagumi nace "unguwa zanje kuma an tare min hanya" ya kalli dandazon mutanen da suka taru a gefe sannan yace "lallai kice dara taci gida kenan" nayi dariya nace "dama ai hausawa sunce in zaka gina ramin mugunta ka gina shi gajere, yanzu kaga nice na rufta ciki" shima dariyar yayi yace "da fatan baki balla kafa ba" wani daga bayana yace "baiwar Allah dama kin rabu dashi, wannan mutumin bai san magiya ba, gashi nan an kira police zasu zo suyi mana maganin sa" Sultan ya leko da kansa yace "kafin suzo suyi magani na ni bara inzo inyi maganin ka, dan rainin hankali kawai" ya bude kofar motar ya fito da sauri, sai kuma ya kalleni ya ga yadda na hade rai sai ya koma yana cewa "kaci sa'a, amma na gane fuskarka, zamu hadu wata rana" ni kawai kallonsa nake yi da mamaki, shi babu abinda ya dame shi wai dan mutane suna zaginsa, kamar ma wani enjoying kansa yake yi. Yasa hannu ya bude min kofar kusa dashi yace "shigo in kaiki unguwar" na yi jim ina tunani, anya kuwa in shiga motar Sultan? Anya mutunci nane? Besides ba wani sanin halinshi nayi ba, kuma duk a halayensa da ake gaya min babu wani na kirki. Na sake kallonsa naga shima ni yake kallo pleadingly, oh God, kawai sai na zagaya na shiga. Mutumin da suke fada da Sultan ya saki baki yana kallon mu, ina kallon sultan ya mika hannunsa ta window yayi masa alamar fuck you. Daga nan ya daga windown ya tayar da motar muka tafi. Wani daddadan kamshi ne a cikin motar, irin kamshin nan da yake sa mutum ya lumshe idonsa, da gaske sultan dan gayu ne dan cikin motar tsaf yake, kujerun an lullube su da wani tattausan bargo wanda shi kansa kamshin yake yi. Shi kansa Sultan din gani nayi ya kara yi min kyau da kwarjini, yauma kamar kullum rigarsa body hug ce data kama jikinsa sosai amma yau 3 quarter wando ne a jikinsa, gashin kansa a hargize yake kamar kullum. A 20 yake tafiya da motar kuma gaba daya ba titi yake kallo ba ni yake kallo, har sai da naji kunya na rufe fuskata da mayafina. Motoci sai horn suke yi mana daga baya, duk wanda yazo wucewa kuwa sai yayi bala'i amma sultan ko kallonsu baya yi hankalinsa gaba daya yana kaina. Nace "wai wannan kallon na menene kuma" "duk sanda na ganki sai inga kamar kara kyau kike yi" kamar nima ince masa shima haka sai kuma dai nayi shiru nace "thank you" yace "ina zakije ne?" Sai yanzu na tuna na bar driver da mota a baya, da sauri na dauko waya ta na kira shi nace na tafi, ya danje yawo kadan sai ya koma gida yace ya kaini. A muryarsa naji alamar baiji dadin abin ba amma kuma babu yadda zaiyi. Mun danyi tafiya kadan nace "why do you do it?" Yace " me fa?" Nace "why do you block the road?" Kafin ya bani amsa wani ya danne horn a bayanmu sannan ya zo ya wuce mu a guje yana cewa "malam in ba zaka wuce ba ka bawa mutane hanya su wuce" Sultan yayi dariya yace "that's why" nima dariyar nayi nace "to kai me yasa ba zakayi saurin ba, kana tafiya a cikin abuja a 20 bayan kasan kowa a garin nan sauri yake" ya wani kwantar da kujera kashingida yace "sauri va gurin zuwa ba" da sauri nace "dan Allah ka rufa min asiri ka tashi, ya za'ayi mutum yana driving kuma ya kwanta" sai da yayi dariya sosai sannan ya tashi zaune, ni kuwa duk na rude, yana tashi wani ya yi masa dakuwa daga waje, ai kuwa ya sauke glass sukayi ta zage2 sannan muka wuce. Sai a lokacin na gaya masa inda zanje, yace "OK, inda kika tura mu rannan ko?" Muka yi dariya gaba daya. Muna tafiya a hanya ne yake tambayata me yasa nake yawo da driver? Nace masa "ban iya driving ba" yayi ta min dariya yana tsokana ta wai abin kunya kamata ban iya driving ba, yace "in kin yarda sai in koya miki" nace "not now, sai na gama school tukunna" yace "OK, Allah ya kaimu" mun danyi nisa na sake tambayarsa "yanzu dazu da kayi blocking hanya da mai martaba yazo wucewa fa?" Yace "kinsan kuwa hakan ta taba faruwa" na ware ido nace "haba? Ya akayi kuma?" Yace "kamar yadda nayi dazu, na rufe hanya nace ba shiga ba fita, na rufe glasses din mota na kunna AC na kwantar da kujera ta nayi kwanciyata, mutane suna ta hayaniyarsu da zage2n su, kawai sai ga Takawa nan ni ban sani ba, yana zuwa yaga an tsaya ya tambaya lafiya aka ce ai hanya a rufe take, yace aje a gano me ya faru, aka koma akace masa ai nine na rufe hanya da motata" yayi shiru, nace "me yace kuma?" Yace "dogarai ya aiko yace su farfasa motar su fito da ni suyi min duka su jani a kasa su kaini gida" na rufe baki na ina mamaki nace "ya salam, sunyi din kuma?" Wani murmushi ya jefa min yace "sun fasa mota alright, amma none of them will dare to touch me, duk wanda ya taba ni kuwa sai na kwantar dashi a asibiti kuma ya bar aikin sa kenan" nayi shiru ina jimamin maganar, it seems like there is crisis between the father and the son, does it has to do with Sultan not knowing who his mother is? Ina so in sake tambaya kuma bana so yaga kamar ina bi masa kwakwkwafi. Mun danyi gaba kadan sai naga ya sake hanya yabi wata hanyar daban, nayi sauri nace "ba nan ce hanyar ba fa" bai kalleni ba yace "eh na sani, sayar dake zanje inyi" nayi shiru yace "kinga kuwa zakiyi tsada" ni dai bance masa komai ba, sai a lokacin na fara lissafin babu wanda yasan tare da wa na fita, shi kansa driver din da muka fito dashi baiga sanda na shiga motar sultan ba, what if ya sace ni? Ina kallon shi ta gefen ido na yana min dariyar yadda na takure a gefe daya ina rarraba ido. Wata unguwa muka shiga irin unguwar talakawan nan, a raina nace me yake kawo sultan irin wannan unguwar kuma? I really hope he is not doing drugs kuma? Can gefe ya samu yayi packing yace "please two minutes dan Allah zanje in karbo sako" na gyada masa kai amma a raina ina cewa zaka je ka karbo drugs dinka dai. Ina kallonsa ya fita ya saka hannayensa a aljihu yana tafiya ya shige wani loko. Da sauri na dauko waya ta na kira Amira, "Amira gani na taho amma ba'a motar gida ba, ina motar sultan, in case in na bata a gurinshi zaku neme ni" na kashe wayar ina rarraba ido.
Ta mirror na hango wani mutum yana tahowa wajen motar daga opposite direction din inda Sultan ya tafi, magidanci ne zaikai kamar 45 years, ta side din driver yazo yayi knocking, ina sauke glass din ya fara kokarin durkusawa zai yi gaisuwa sai kuma yaga babu kowa a gurin. Na gaishe shi ya leko ya amsa cikin sakin fuska sannan yace "yallaban baya ciki ashe" nace "ya fita, wai zai karbi sako" ya girgiza kai yace "zai kawo sako dai, tun dazu mukayi waya yace gashi nan zuwa da naji shiru shine na dan fita" sai kawai naji ina son in san sakon menene zai kawo. Nace "sakon menene zai kawo?" Yace "kudin makarantar yara ne, kinsan an kusa komawa sabon session, to nayi masa list na school fees, kudin books da uniform tunda akwai sababbin dauka to shine yace zai kawo min yau" kaina naji ya toshe nace "yara? Wadanna yaran kuma" yace "yaran unguwannin nan mana, ai duk shi yake musu komai na makaranta, mu kam ba abinda zamu ce masa sai sam barka dan da yawa mutanen da suke zaune a unguwannin nan shi yake ciyar dasu, ya ciyar damu ya biya wa yaran mu kudin makaranta ya samarwa matasan mu aikin yi. Kinga wannan sabuwar orphanage din daya gina duk nan unguwar yazo ya dauki ma'aikata maza da mata" cikin cushewar kai nace "orphanage? Sultan din ne ya gina orphanage?" Yayi alamar rufe bakinsa yace "ai na dauka tunda kuna tare kin sani, ai baya so a sani, da nasan vaki sani ba da bazan gaya miki ba" nayi sauri nace "dan Allah baba gayamin, wallahi bazan ce kai ka gayamin ba" ya gyara tsayuwa da alama yana da surutu, ya ce "ai wannan ta biyu ce, waccan babbar ma ta cikin gari ai shi ya gina ta sai mutane suke cewa dan majalissa ne shi kuma sai ya samu dan majalissar yace yace shine yayi. Ai duk unguwannin nan na marasa karfi yana da representative da yake gaya masa duk bukatun mutane kuma in dai an fada to zai bayar, in dai har maganar kudi ce to mukam sai godiya" nayi shiru ina jinjina maganar a cikin raina. Nayi wa mutumin godiya ya tafi hanyar da naga sultan yayi, har Sultan ya dawo ina jinjina maganar mutumin nan a raina. Yana zuwa ya shiga muka tafi yace "sorry na barki kina jira" kai kawai na gyada masa, yace "are you OK? Naga kin chanza?" Nan na kirkiri murmushi nace masa ba komai, bai yarda ba dai yace "bayan na tafi wani yazo nemana?" Na girgiza kai nace "babu wanda yazo nemanka" ina ganin fuskarsa ta chanza alamar yaji dadi. Dole na ware nima dan kar ya fahimci wani abu har muka je gidan su Amira. Tun 10:30 na baro gida amma banje gidan su Amira ba sai 1:30, kamar wacce na tafi kano. Muna yin packing Amira ta fito da sauri kamar dama a bakin gate take. Sultan ya tsatstsare ni da ido wai lallai sai na yarda yazo a maida ni gida. Amira tana bude kofar ta finciki hannuna "fito daga motar nan" Sultan yana dariya yace "check her from head to toe, ban ciri komai ba" ita dai bata kula shi ba sai jana take ni kuma naki fitowa. Sultan yace "please yaushe zan zo in dauke ki" Nace "after magrib" yayi murmushi yace "thank you" na juya zan fita muka hada ido da Amira wacce ta saki baki da hanci tana kallona.
Episode Forty :TheShadow 3
Tunda muka shiga gida Amira take min bala'i. Ni dai kawai dariya nake mata. "Yanzu kinsan kuwa duk wanda ya ganki a motar sultan irin kallon da zaiyi miki? Kin san ma kuwa waye Sultan? Mutumin nan ko magana bai kamata ace ta hada ku dashi ba ballantana har ki shiga motar sa. Yanzu ma tukunna, ina kukaje da kuka dade haka baku karaso ba?" Na harare ta nace "gidan sa ya kaini. Ina ruwanki da inda muka je?" Muka shiga dakin mamanta muka gaisheta sannan muka koma dakin ta. Nan fa ta saka ni a gaba da nasiha, ita lallai gani take shiga motar Sultan din da nayi tamkar wani katon zunubi na aikata. Tace "Yanzu Allah ne kadai yasan irin maganganun da ya gaya miki, duk sai yaje ya hure miki kunne anzo an kasa gane kanki. Ki rufa mana asiri Moon ki rabu da Sultan dinnan" Nace "Saboda me?" Tace "saboda me? Yanzu har tambaya kike yi saboda me? Just look at him zaki gane saboda me. He is a criminal for God's sake. He is spoilt rotten. A gangster. A rogue. A drunk. Duk wadannan dalilan basu ishe ki ba?" Murmushi kawai nake yi ina kallon yadda ta dage tana ta bayani. Nace "yanzu in tambayeki, ya akayi kika san Sultan is a drunk?" Tace "duk garinnan waye bai san dan shaye2 bane? sau nawa ana ganinsa yana yawo a gari a buge" nace "yanzu ke kin taba ganinsa yana shan giya?" Tace "ni ban taba ganin sa ba amma.. " na daga mata hannu nace "amma me? Annabi da kansa ya hana yada jita jita, abinda baka tabbatar ba kar ka fada musamman akan alfasha" Amira ta saki baki tana kallona kamar zata yi kuka tace "are you truly depending him?" Nace "ba wai goyon bayan Sultan nake yi ba, ina goyon bayan gaskiya ne" ta sake matsowa kusa dani desperately tace "yanzu ki duba kiga irin abokansa, ki kalli wannan shegen Amir din ki gani. Kin san kuwa sunan gang dinsu? Gang Bang they call themselves. Gang din 'ya'yan manya ne wadanda suka fi karfin karfin iyayensu. Abuja, kano, kaduna, legos da duk sauran manyan states na Nigeria an sansu, Sultan da Amir sune 'yan Abuja. Moon duk wanda yake cikin gang dinnan is a known criminal kawai dai dan babu yadda za'ayi dasu ne shi yasa. Kinsan kuwa kwanan baya suka yi gang raping wata yarinya a Nassarawa state?" Ji nayi tamkar ta chaka min mashi a kirjina, amma na daure nace "ke a ina kikaji wannan labarin?" Ta daga kafada tace "a radio, a television, a social media, a newspaper ko ina zancen akeyi" nace "ita yarinyarce tace su su kayi raping dinta" tace "eh mana, anyi hira da ita har a gidan radio" na sake cewa "ita yarinyar ce tace da wane da wane da Sultan suka yi raping dinta?" Tace "just because his name wasn't mentioned doesn't mean he didn't do it" na girgiza kai na kawai ina kallonta, tace "Moon kar ki bari son da kike masa ya rufe miki ido ki kasa ganin gaskiya. Dududu yaushe kika sanshi da har zaki tunanin kinsan shi fiye da sauran jama'a? Duk abinda nake gaya miki kamar yana shiga ta wannan kunnen ne yana fita ta wancan. Already har ya riga ya hure miki kunne" ta mike a fusace ta dauko laptop dinta ta ajiye min agaba na tace "in baki yarda dani ba check for yourself, ki duba internet zaki fahimci waye Sultan" daga nan ta fice ta barni a dakin. Na jima ina kallon laptop din ina jimamin abinda bincike na zai gano min. Can na dauka na kunna direct na shiga goggle, nayi typing sultan sai naga amsoshi da yawa wadanda ba sa dangantaka da abinda nake nema. Na goge nayi typing sultan Abuja prince. Nan da nan kuwa naga an watso min hotunan Sultan, wadansu a kasarnan wasu a kasar waje. Duk hotunan babu ko guda daya da yake da manyan kaya a jikin sa, babu kuma ko guda daya da yake tare da babansa. Nayi typing criminal record dinsa, nan ma naga rubutu da hotuna da yawa, can ya daki wancan, nan yayi trashing wancan shagon, yayi causing traffic jam, duk dai labarin daya ne. Nayi shiru ina karanta labaran daya bayan daya, sai wani tunani yazo min, duk cikin labaran banji ance yayi sata ba, banji fashi da makami ba, banji kisan kai ba kuma banji labarin yarinyar ta Amira ta fada ba, asali ma duk hotu an nasa babu inda na ganshi da mace, duk tare da maza ne masu shiga irin tasa. Wani hotonsa ne ya dauki hankali na nayi zooming, Sultan ne fuskarsa dauke da murmushi, rike a hannunsa kwalbar giya ce a daga ta alamar cheers. Na runtse idona ina jin zafi a kirjina. So it's true, yana shan giya. Hawaye naji yana kokarin zubo min na yi sauri na mayar dashi. Nayi typing emir of Abuja, nan ma hotuna na gani ba adadi na mai martaba sarki kuma kusan duk hoton yana tare da second son dinsa Abbas, cikin kima da daraja da kwarjini irin na sarauta, mostly a gurin saukar karatu ko bude masallaci ko musabakar alqurani. Nayi zooming wani hoton mai martaba, kana ganinsa kasan shi ya haifi sultan, idonsu, girarsu da shape din fuskarsu iri daya. Na koma nayi searching prince Abbas, nayi ta bincike amma na kasa ganin single fault nasa, he is like a perfect son, komai tare suke yi da mai martaba, duk inda mai martaba zaije tare suke zuwa. Can naga wank hotonsu shida sultan a america gurin graduation din sultan na masters. Nayi shiru ina tunani, mutane criminals irin sultan basa karatu, most of them da wahala suke gama sec sch, amma sultan masters ne dashi kuma a babban field like architecture. What is happening? What am I missing? What are u sultan? A gurin manyan mutane da masu kudi shi criminal ne, a gurin talakawa da sauran marasa karfi shi hero ne. Wanne dalili ne zai saka mutumin kirki ya mayar da kansa mutumin banza a idon mutane. Har zan rufe laptop din sai na fasa nayi typing the gang bang. Ai kuwa naga rubutu sosai a kansu, Amira tayi gaskiya dan daga 'ya'yan tsofaffin shugabannin kasa sai 'ya'yan gwamnoni da manyan masu kudi, a cikin list din naga an rubuta "the drunk prince of abuja" duk da basu fada ba nasan sultan suke nufi. Na rufe laptop din na kwanta ina tunani. Why will Sultan want people to think he is a bad guy while in reality he is good, very good. Yau kusan 3 hours nayi a motar sa daga ni sai shi amma ko da wasa bai kai hannunsa jikina ba kuma baiyi min wata magana da zata nuna cewa dan iska bane. Dear God, what do I do now. Inanan a kwance Amira tazo ta kawo mana abinci har yanzu fushi take yi dani ita wai lallai naki jin maganar ta. Da kyar na samu na bata hakuri nace tayi min addu'a insha Allah komai zai warware. Muna nan muna ta hira har magrib sai Sultan ya kira ni yace min gashi nan zuwa, tun daga nan Amira ta cigaba da bata fuska, naje zanyi sallama da mama tace min "Maimunatu wai me yake damun kawarki ne?" Nace "mama me ya faru? " tace "sam taki kula samari ballantana har ayi maganar fitar da miji, ta gama degree dinta, tayi service, me kuma yayi saura? Ni na gaji da surutun da iyayenta suke yi min wallahi, ni babu miji ita babu miji amma ita sam bata damu ba, shi wanda naga tana nacewa da ya fara zuwa kamar gaske kuma yanzu shiru, ni ko waya ma yanzu banji suna ji ba, idan ba aurenta zai yi ba sai ta rabu dashi ta samu wani" na kalli Amira da alamarr tambaya saboda ban gane maganar da mama take yi ba, Amira ta daga kafada irin oho din nan, nan dai na bawa mama hakuri nace zamuyi maganar da Amira. Muna fita na tambayeta "wanene mama take magana akansa" ta dauke kai tace "nima bansani bafa, ita dai kawai ta damu sai nayi aure ne kuma ai shi aure lokaci ne, idan mijin baizo ba ni zan auri kaina ne?" Jikina ya bani da akwai abinda Amira take boyewa amma sai na rabu da ita, na san in tana son in sani zata gayamin ne da kanta.
Muna zuwa wajen motar Sultan Amira ta rike hannuna tayi masa knocking, ya sauke glass yasha wani bakin glasses a fuskarsa, Amira ta hade rai sosai tace "gata nan na kawo ta, kuma ka sani wallahi duk abinda ya same ta hukuma ba zata bar ka ba" Sultan ya dan sauke glasses din idonsa kadan yana kallonta ta saman glasses din, sai kuma yayi dariya yace "Thank you Mah, zan bi duk kanin umarnin ki" ina jin Amira tana ta kunkuni tana cewa "banza mai kyan dan miciji kawai" ni dai ina ta kunshe dariya ta naje na shiga muka tafi. Kamar yadda ya kawoni a 20 komawar ma a 20 muke tafiya. Ya chanza wanka yasaka riga mai dogon hannu amma kuma sai ya nannade hannun rigar zuwa gwiwar hannu. Wani irin cikar halitta da kyau ne yake bayyana a jikinsa. Kawai sai ji nayi yace "are you checking me out?" Naji wata kunya ta kama ni saboda bansan yana kallona ba. Yayi dariya yace "Thank you for appreciating me" nayi sauri nace "I didn't" yace "OK ni bara inyi appreciating dinki. Kinga kina da kyau sosai da sosai, kina da komai da yakamata ace mace tana dashi. Sannan kina da nutsuwa sosai da kamun kai. Ga ilimi, you are a potential doctor at a very young age, and that's wow. Zan iya cewa babu abinda kika nema kika rasa. Ina so ko yaya ne kiyi sharing abinda kike dashi with me" ya danyi shiru ni kuma bance komai ba, sai ya cigaba "nasan ni ba kowa bane ba, I am nobody and I have nothing, na san kinfi karfina nesa ba kusa ba kuma nasan abinda nake so in fada kamar selfish ne, amma kuma tun ranar da na fara ganin ki na kasa samun sukuni na zuciya na kasa controlling kaina. I want to spend the rest of my life with you" na lumshe idona na kwantar da kaina akan headrest din kujerar inajin sonsa yana kara huda kirjina. A lokacin Ibrahim cewa nayi idan mommy ta sani zata saka ni a turmi ta daka ni ta mayar dani gari, wannan karon kuwa inajin in ta sani sala sala zatayi da nama na tayi kilishi ta cinye, lol.
Episode Forty One : Born for This.
Jin bance komai ba yasa Sultan yayi ajjiyar zuciya yace "am sorry, maybe it sounded like an insult to you. Allah ya baki hakuri. Kawai dai na fada ne saboda ni bana iya rike abu a raina. I don't deserve you, I know. Kawai dai na dauka for once maybe zan zama lucky" na kalleshi ina girgiza kaina nace "am not saying no Sultan, am just not saying yes. Duk wannan abin yayi sauri da yawa, babu dade da haduwa ba. I don't know you and you don't know me" ya cire glasses din idonsa ya dora akan dash board yace "look ba fa cewa nayi zan turo iyayena ba ko something like that ba, am just asking for your permission to love you" nace "na sani, amma still, indai har soyayya ce dole a kafa ta akan yarda da juna da aminci. Kafin in ce ina sonka ko bana sonka dole sai na sanka first. Sultan I don't even know your real name, babu abinda na sani a tare da kai" guri ya samu a gefen titi yayi packing ya juyo yana kallona sosai, yace "saboda rannan kin tambayeni about my mother shi yasa kike cewa haka ko?" Nace "well, yes, na gaya maka almost everything a kaina amma kai ka kasa gaya min komai, ta yaya kake so in fara relationship da kai ba tare da nasan komai a kanka ba?" Yace "I didn't tell you anything about my mother because I don't know" ya buga hannunsa akan steering alamar ransa ya fara baci. Nayi shiru bance komai ba ina gudun kara bata masa rai. Mun jima a zaune sai ya fara magana "Sunana na gaskiya Abbakar Sadiq Abdallah, for some unknown reason babana ya saka min sunansa, a game da mahaifiyata kuma bansan komai akanta ba, it is as if she didn't exist,babu wanda yake maganar ta, abinda na sani kadai shine sunanta, shima kuma a jikin birth certificate dina na gani. Tun tasowa ta a gidan kakana na taso, kakana wanda ya haifi mahaifina lokacin shine sarki ba Takawa ba. Duk duniya zan iya cewa daga shi sai Amir zan iya nunawa ince wadannan suna sona dan soyayyar da ya nuna min sanda yana da rai ko 'ya'yansa baya nuna wa haka. Tun ina yaro nasan Takawa shine babana amma kuma tun a lokacin nasan baya sona, dan ina tuna lokacin da in yazo gidan zan kama rigarsa in rike ina kuka shi kuma yana ture ni har sai na fadi sannan yayi tafiyarsa. Kakana lokacin shi zai daukeni yayi ta rarrashina. Gata kam a lokacin na gani, duk abinda nake so shi za'a yi min, babu wanda ya isa yayi min tsawa ko fada koda kuwa Yaya ce (yaya itace kakata wacce ta haifi babana), dan haka na taso a sangarce, babu mai sani babu mai hana ni, wani lokacin sai in zauna inyi ta kuka ince ni gurin mommy na da daddy na zanje ko wanne yaro yana gurin iyayensa banda ni, a irin wadannan lokutan ne marigayi sarki ya dauke ni ya kaini orphanage ya nuna min yaran gurin yace 'kaga wadannan yaran su basu san uwarsu ba basu san ubansu ba, basu san kowa a dangin su ba, kai kuma kasan babanka, kasanni ni kakanka, kasan dukkan danginka na gurin babanka to kamata yayi ka godewa Allah', a orphanage din na hadu da Amir" na kalleshi da sauri ya gyada min kai "yes, Amir is an orphan. Babarsa tana haihuwarsa ta dauke shi daga shi har mahaifarsa ko cibiya bata yanke masa ba ta ajiye shi a kofar orphanage ta gudu. Kakana shi ya rada masa sunansa Abdallah shine ake ce masa Amir. Sanda yake kaini orphanage ya hada ni da shi, tun a lokacin muke abota da yake shima fitinanne ne iri na, daga baya in zamu taho sai yayi ta kuka yace sai ya bi mu, sai kawai kakana yayi adopting dinsa ya saka mu a makaranta tare, komai tare muke yi dashi har yau. Lokacin da kakana ya rasu ne rayuwata ta chanza gaba daya, I was ten years old then, nayi ta kuka akayi ta rarrashi na naki hakura, Takawa yana zuwa ya kama ni ya daure min hannu da baki na ya saka ni a dakina ya rufe kofar. Haka na kwana ina kukan zuci babu bakin yin kukan ga uban dauri da nasha, sai washe sannan ya aiko aka kunce ni kuma yace in na sake kuka sai ya kuma daureni. Daga ranar nasan na rasa soyayya a rayuwata. Hankali na bai kuma tashi ba sai da aka nada babana sarki, ya dauko iyalansa wadanda ko saninsu banyi ba tunda baya bari inje gidansa ya dawo palace. Ni na riga na saba duk abinda nake so shi zanyi, tun da ya dawo gidan kuwa sai ya zamana duk abinda nayi no matter how small ba zai yi min fada ko nasihaba sai dai ya saka dogaran sa suyi ta dukana, wani lokacin har Amir za'a hada a daka koda kuwa ni kadai nayi laifin. Daga lokacin muka fara koyon fada ni da Amir, in an saka a dake mu sai ya zamana suna dukan mu muna ramawa. Bayan na karasa primary school, Rannan na tambayi Yaya nace dan Allah ta saka a kaini gurin babata sai tace min itama bata san inda take ba, na tambayeta ko ta san dalilin da yasa iyayena duka rabu? Sai tace min saboda ayi protecting family name. Lokacin ina yarinta ban fahimci maganar ta sosai ba. Lokacin Takawa ya sai wata sabuwar mota kawai sai na dauki fenti na shiga garage dinsa na rubuta 'fuck the family name, I want my mother', nasan abinda na aikata dan haka naje na shirya, na saka duwatsun wuta a cikin safa ta na hada da hannuna wanda na daure da karamin towel na daure, neman kawai wanda zan huce temper ta akansa nake yi, ai kuwa sai dashi an turo wani dogari mai tsautsayi akan ya zo ya dake ni, da na dage na fara naushinsa da hannuna mai duwatsun nan har sai da naga baya motsi, haka aka kwashe shi sai asibiti. Washe gari takawa ya kirawo ni yace "tunda ni ka gagare ni zan tura ka inda za'a koya maka hankali" shikenan abinda yace min, babu Sultan me yasa kayi haka? Babu Sultan ya kamata ka dena haka. Kawai ya saka mu a jirgi ni da Amir sai lagos, gidan kangararru. Wasu iyayen suna ganin gidan kangararru a matsayin gidan da zai gyara musu 'ya'yansu basu san cewa kara kangarar da yara yake yi ba. Sanda ya kaimu na tambayeshi 'why?' Amsar da ya bani shine 'to protect the family name'. Babu abinda ban koya a gidan nan ba, babu abinda ban iya ba, acan na hadu da most of the gang bangs, iyayensu sun kasa basu tarbiyya sun turo su nan. Shekarar mu biyu acan uncle dina galadima yaje a fito damu, yana kawomu gida Takawa kallo daya yayi mana yace ba'a gidan sa ba, a lokacin ne Hajiya ta kira ni dakinta ta ce min zata saka a kaini America a saka ni a makaranta amma sai na mata alkawarin bazan dawo Nigeria ba zanyi zama na acan. Ni a lokacin gani nake yi me zai dawo dani Nigeria tunda babu wani abu da na bari anan, nobody wants me, not even my mother. Sai a lokacin naga birth certificate dina da sunanta a jiki 'Khairat Abdallah' da signature dinta, sai a lokacin nasan cewa a america aka haife ni, dan haka ina zuwa America asibitin da aka haife ni na fara zuwa ina bincike ko zan samu wani information akanta amma ban samu komai ba. Takawa ya saya min gida ya saya min mota ya cika min account dina da kudi. Babu wanda yayi tsammanin zamuyi karatu da gaske ni kuwa na dage da karatu kawai saboda ina sa ran maybe in nayi karatu he will love me, na gama sec sch na shiga jami'a amma ko sau daya bai je ya ganni ba, sai dai duk kudin da nake so zai aika min. San da na gama first degree dina na shigo jirgi na zo Nigeria na kawo masa certificate dina ya karba ya duba, abinda yace min shine "good for you" daga nan ya jefo min takardata, alokacin ne na fahimci cewa ba wai halina ne baya so ba ni din ne baya so, Hajiya tace min ina alkawarinta nacewa bazan dawo Nigeria ba? Dan haka na tattara na koma America na koma makaranta. A lokacin nayi hankali sosai kuma na fahimci cewa duk abinda ya faru a rayuwata ya faru ne saboda babana yana so yayi protecting his family name, ni kuma na sha alwashin sai na bata family name din nasa da yake ji dash, duk tsiya dai shi ya haife ni kuma duk abinda nayi dole sunan nasa da yake ji dashi za'a ambata. Ina zuwa Nigeria hajiya ta fara tambayar alkawarin mu and I told her to fuck off, nasan abinda take so, bata so na a kusa da sarauta saboda tana son abbas yayi sarauta ita kuma bata san sarauta is the last thing on my mind ba, dan haka na fara bribing dinta cewa in dai har tana bani goyon baya ina yin duk abinda nake so to I will leave Abbas alone yayi ta sarautarsa.
Aikina na architecture yana kawo min kudi sosai, dan haka a yanzu bana bukatar kudin Takawa dan duk abubuwan da nake yi da kudina nakeyi, yanzu ba zai sa a dakeni ba kuma babu yadda zaiyi dani dan haka sai ya koma ignoring dina, nuna wa yake yi kamar bai san dani a duniyar ba amma nasan cewa sakonni na suna isa gurinsa sosai" ya juyo ya kalleni fuskarsa dauke da wani murmushin dana kasa gane kansa yace "to Maimunatu, I opened up to you, babu wanda na taba zama mukayi irin wannan maganar dashi bayan Amir sai ke. This is me. Yanzu zaki iya yin making decisions dinki yes or no" yana gama fadar haka ya mayar da glasses dinsa ya tayar da motar. Har muka je gida babu wanda ya sake cewa komai. Ni a gurina kaina ne ya kulle, I need to digest duk maganganun Sultan kafin inyi fully understanding din labarinsa. Yana packing nayi masa godiya, kai kawai ya daga min na fita. Sai bayan na gama da kowa nayi sallah nayi wanka na kwanta sannan na fara rewinding duk maganganun sultan ina reviewing dinsu. Duk abinda yake yi yana yi ne dan ya bata sunan family dinsa saboda yana ganin basa sonsa kuma sune sanadiyyar gurbacewar rayuwarsa. Yanzu na fahimci dalilin soyayyarsa da yara da taimaka musu ta hanyar gina orphanage da saka su a makaranta, saboda yasan ciwon rashin samun kulawa daga iyaye, yasan maraici duk da shi ba maraya bane. And suddenly I know what sultan wants, what he needs, LOVE.
Na dauki waya ta na duba time na lissafa naga rana ce yanzu a England, nayi dialing number din supervisor na, yana dagawa nace "sir I think I found the subject for my research project"
*what do you guys think is more important, Family or Family name?
Episode Forty Two : Born for This
Sultan ya jima a zaune a cikin motar bayan fitar Moon, shikenan ta faru ta kare, haushin kansa gaba daya yake ji, menene dalilin da yasa ya gayawa Moon labarinsa, yanzu ya tabbatar she will say NO to him, babu wacce zata so ta hada zuri'a dashi. Wannan shine dalilin da tun tuni ya kasa yin budurwa saboda baya jin zuciyarsa zata iya daukan rejection daga budurwa kuma, plan dinsa shine yazo Nigeria yayi destroying name din familyn sa sai ya koma America ya cigaba da rayuwa acan. A plan dinsa babu budurwa ballantana aure, saboda yasan aure zai ruguza masa plan dinsa ne tunda in yayi aure dole zai haihu kuma 'ya'yansa will still bare family name din da yake yaki da. Out of nowhere Moon ta shigo rayuwarsa, kallo daya yayi mata and he is hooked for life dan yanzu baya jin zai iya rayuwa babu ita wanda hakan yasan wani babban yaki ne ya dauko. Yasan babanta sosai, Ambassador M D, a very well respected man, tsakanin sa da ambassador MD tamkar hanyar jirgi ne da ta mota. Koda ace yayi convincing Moon baya jin zasu iya convincing babanta. Babansa kuwa yasan ba zai shiga maganar ba ballantana a duba darajarsa a bashi ita. Ya runtse idanunsa yana jin zafi a zuciyarsa. She means the world to him, he can't loose her. Ya tayar da motar ya fara tafiya. Yayi mamakin kansa dazu, he don't normally talk about himself amma kawai ya zauna ya saki baki yayi ta zuba mata magana kamar wadda tayi masa asiri, yanzu ya yarda da ake cewa Love is the strongest magic of all. Ya tabbatar cewa yau ba zai yi bacci ba.
Ko da yaje gida ya kwanta ma juyi yayi tayi akan gado amma ya kasa bacci. Sanda baccin ya dauke shi kuwa mafarkai yayi tayi na rayuwarsa a baya. Sai wajen assuba sannan a samu bacci mai dadi. Cikin bacci yaji wayarsa tana kara, da magagin bacci ya dauka ya saka a kunnensa ba tare da ya buda number ba "Assalamu Alaikum" yaji ance "wa alaika assalam, a tashi daga baccin nan haka assuba tayi" tuni yaji baccin ya watstsake, ya duba screen din wayar da sauri, Love, ya sake mayarwa kunnen sa yaji an sake cewa "in baka tashi ba zan kashe in sake kiranka har sai ka tashi" a hankali ya furta "Love, is that you?" Daga cikin wayar yaji sautin murmushinta ya lumshe idonsa yana hango fuskarta da dimples dinta, tace "yes it is me, ka tashi kayi sallah assuba tayi" still idanunsa a lumshe ya ce "then you are not dumping me, right?" ta danyi shiru inda bugun zuciyarsa ya karu sannan tace "no Sultan, am not dumping you". Bai san sanda wani murmushi ya bayyana a fuskarsa ba yaji tamkar an cire shi daga ukuba an saka shi a Ni'ima, murya can kasa yace "thank you, i will never let you down".
Na ajiye wayar ina bin screen din wayar da kallo, nasan na debo babban aiki but I can't stop myself, I feel like I was born for this. Jiya na jima banyi bacci ba kuma na yanke shawarwari da yawa, na farko zanyi accepting soyayyar Sultan dan nima ina son shi kuma ina so in chanza masa rayuwarsa in fito da kyawawan halayensa kowa yasan ko waye real sultan, zan bashi abinda ya rasa a rayuwarsa tun kuruciya, soyayya, zan bashi something to care for, me. Zan nuna masa cewa akwai wanda ya damu dashi kuma zan fahimtar dashi cewa idan har bai gyara rayuwarsa ba zai rasa ni. Matsalata daya shine yadda zanyi family na suyi accepting Sultan a matsayin mijina. Daddy na is soft as well as hard, dole in ina son in gabatar da Sultan a gurinsa sai na nemi soft spot dinsa which for now I don't know. Mommy is as hard as steel dan haka bansan ta wanne barin zan shigar mata da sultan ba, wannan dalilin ne ya saka na yanke shawarar zan cigaba da ganin sultan a boye sannan sai in nemi chance dina kuma inyi ta addu'a. Addu'ar ita na tashi nayi da daddaren nayi istikara na nemi zabin Allah, akan sallaya ta anan nayi bacci kuma ina farkawa da assuba Sultan ne ya fara fado min a rai na shi yasa na kira shi na tashe shi yayi sallah.
Tun daga ranar muka dinke ni da sultan, kullum muna tare dashi a waya dan har komawa nayi saka ear piece saboda bazan yi ta rike wayar a hannuna ba. Wani lokacin muna zaune a falo da 'yan gidan mu muna hira at the same time kuma muna waya dashi. Duk sun san cewa nayi sabon saurayi amma basu san ko waye ba saboda bana yadda in kira sunansa a gabansu. In muna so mu hadu kuwa sai in kirkiri fita unguwa, ko ince zanje kasuwa ko gidan kawaye, sai muyi plan din inda zamu hadu dana fito sai in sallami driver na ince ya tafi yawo in na gama zan kira shi, daga nan sai sultan yazo ya dauke ni. Ni kaina nasan abinda nake yi ba dai dai bane amma na kasa samun wata mafitar. A haka har hutun mu ya kare muka fara shirin komawa england. Ranar da na gaya wa Sultan abinda yace shine "kice tafiya England ta kama ni kenan" nace "ban gane ba?" Yace "wai kina nufin zan zauna a Nigeria ke kina England bana ganin ki? You dey craze? Ai bana jin zan iya sati daya ban ganki ba" dariya nayi sosai nace "Sultan aikin ka fa?" Yace "Daga can ma zan iya yi. To in kin tafi ai tunani ma ba zai barni in yi aikin sosai ba" kuma nasan har zuciyarsa yake wannan maganar, yes Sultan loves me that much, wani lokacin har zama nake inyi tunanin me zaj faru in aka ce za'a raba mu? Ni nasan cewa duk ranar da Daddy da mommy suka ce in bar Sultan to kuwa zan barshi har abada duk kuwa da son da nake masa saboda ban taba yi musu gardama ba kuma bana fatan inyi musu, ina son iyayena sama da komai kuma zan rabu da Sultan in sunce in barshi koda kuwa sansa zai zama ajali na. Ana gobe zamu tafi Amira tazo zamuyi sallama nan na bata labarin cewa sultan fa bin mu zai yi. Tace "bangane ba, daki za'a bashi a gidanku ya zauna?" Nayi dariya nace "ke Amira, da akwai gidan babansa acan, anan zai zauna" ta bata rai tace "ni dai Moon Allah ya gani bana son ki da Sultan wallahi, this is a very dangerous game you are playing. Ita behavior is contagious, idan ke baki chanza shi ba shi zai chanza ki tunda ya fiki taurin zuciya plus kina son shi da yawa. He is handsome na sani, but He is as handsome as sin. Duk wani abin zunubi zaki ga kyakykyawa ne, very tempting, dole sai ka kai zuciya nesa zaka hana kanka" nayi shiru ina lissafa maganar ta, but i know what I feel for Sultan is not lust, it is love.
Bayan munje England ma haka ce ta kasance, kullum muna tare da Sultan a makaranta dan komawa yayi kamar shima student din ne. Kullum in muna tare sai nasan yadda nayi nayi masa nasiha ta sigar lumana, ina nuna masa this is right and this is wrong, amma ga mamaki na sai naga in aya na fara janyo masa sai ya karasa min, in hadisi na dauko sai ya gayamin wani irinsa, wato yana sane da duk abinda yake yi kenan. Abinda na kara fahimta a dangane dashi shine yana da zuciya, muguwar zuciya ma, wannan shi ya saka ya ke da fada, dan a makaranta kullum ina cikin rabon fada da Sultan. Allah yaso makarantar tana da girma shi yasa har yanzu siblings dina basu san da zaman sultan ba. Sannan kuma Sultan yana da mugun kishi dan ko kallona wani namiji yayi indai kallon bai gamshe shi ba yanzu zakuji kansa, ni har dariya yake bani dan ni mai mutane ce kowa nawa ne babu mace babu namiji. Haduwar su ta farko da Mahdi nayi introducing dinsu suka gaisa kamar gaske sai bayan mahdi ya tafi sannan Sultan ya bata rai yace "I don't like him" nace "saboda me? He is nice and shine best friend dina a school dinnan" ya tsare ni da ido yace "amma kin san yana sonki" na sunkuyar da kaina nace "yes, but I don't love him, I love you".
Sau da yawa sai in samu kaina da comparing Sultan da Ibrahim. Sam basu da alaka, kamanninsu sun sha ban ban, yayinda Ibrahim yake da sanyi Sultan kuma zafi ne dashi, Ibrahim ustaz ne sultan is the total opposite of ustaz, amma abinda yake bani mamaki shine lokacin da muna tare da ibrahim har rigima mukayi dashi akan taba ni duk da kuwa lokacin ina kwaila amma sultan ko da wasa bai taba kai hannun sa jikina ba. Situation din da muke ciki da Sultan is exactly wanda muka kasance da Ibrahim, yadda yake bina duk inda na tafi, yadda yake sona kamar ya cinye ni, da kuma yadda duk nake boye su daga gurin iyayena. They are totally different but exactly the same.
A hankali ina ganin chanji a halayen Sultan, yana behaving kansa especially if I am around. Kuma har yau ban taba ganin shi a buge ba kuma na kasa tambayar sa saboda bansan yadda zai dauki maganar ba, amma nasan ko da yana shan giya to ba sosai ba saboda shi dan giya ko yayane sai an gane shi. Shakuwa ce sosai take kara shiga tsakanin mu kuma Sultan is an open guy, komai nasa yana gayamin saboda koda yaushe yana gayamin shi baya son secret. Rannan muna zaune a school yace min "tell me Love, akwai wani guy da ya kamata in san da zamansa? Ina nufin akwai wani da kuke tare kafin ni ko akwai wani da yake sonki bayan ni? I want to know" nayi shiru ina auna maganar sa, bana jin zan iya gaya masa labarin Ibrahim, there is no need saboda by now na tabbatar cewa Ibrahim ba zai dawo ba, nace "actually there is one guy, sunanshi munir" nan na gaya masa labarin munir da alkawarin baffa nayi mana aure in na gama makaranta ba tare da miji ba. Sultan ya saka hannu a cikin gashinsa yana hargitsawa, dabi'ar dana lura yana yi duk sanda wani abu ya taba zuciyarsa, shi yasa kullum gashinsa yake a hargitse. Na saka ido na a cikin nasa nace "wannan shi yasa nake son ka nutsu yadda zan kaika gida kafin in gama project dina" ya bata fuska yace "am trying, really trying, but this is me, I can't just change over night" naga maganar tana so ta bata masa rai sai na chanja topic din nace masa "to kai fa? Any girl that I should know of?" Nan take murmushi ya yi replacing damuwar sa yace "No, not Sultan. Ban taba son wata ba sai ke though akwai yarinyar da take sona, Khulsum, kanwar Hajiya ce. Farkon dawowa ta Nigeria na tarar da ita a gida, she is a good cook ni kuma I love food sai take yi min girki kullum then I realized tana da hidden agenda sai nayi ending alakar mu, she might still be in love with me duk da dai mun dade bamu hadu ba" na gyada kaina nace "it's OK" amma cikin raina na dan ji babu dadi especially inda yace ta iya girki, in akwai abinda ban iya ba a rayuwata girki ne, lol.
Bayan kwana biyu nayi deciding zan kai Sultan gidan Hafsat su gaisa. Tun safe na kira ta na gaya mata zanzo kuma zan kawo bako, sannan na gaya mata cewa I also want him to meet Zayed. Da yake ranar Weekend ce sai na gaya wa mommy zanje gidan Hafsat tace a dawo lafiya, dama mun gama plan din inda zamu hadu da sultan dan haka muna fita da driver na gaya masa inda zai kaini, muna zuwa na tarar already Sultan yana jira na dan haka nayi changin mota. Tare muka shiga palon Hafsat da sallama. Suka amsa a tare ita da Zayed. Idan sunyi mamakin ganin Sultan to sun boye dan sam banga alama a fuskar su ba. Muka zauna mu hudu muka yi ta hira, nayi ta sha'awar Hafsat da Zayed, yadda suke abubuwansu, Arabic din Hafsat ya gyaru sosai dan dashi suke magana da Zayed. Zayed yayi ta yiwa Sultan tambayoyi shi kuma yana amsawa truthfully, saboda gaskiya Sultan ba shi da karya ko kadan, bashi da boye2, duk abinda ka tambayeshi zai gaya maka, either ka karba ko ka bari. Tare mu kaci abincin rana bayan munyi sallar Zuhr, daga nan su Sultan suka fita suka barmu. Na kalli Hafsat nace "so... Fadi abinda yake ranki" tace "he loves you, that's for sure. But he is Sultan, kinsan sunan da yayi a Nigeria babu inda babu labarinsa da labarin takadirancin sa. Kema kanki kinsan cewa kin debo da zafi Moon. Kuma na tabbatar cewa har yanzu a gida ba'a san da maganar sa ba ko an sani?" na girgiza kaina, ta cigaba da cewa "you are making the same mistake as you do with Ibrahim. Bana so ki shiga da yawa kamar yadda kika shiga son Ibrahim kuma abin yazo baiyiwu ba kika zo kika shiga wani hali" nace "so nake inga na chanja shi kafin in kaishi gida, He is a good guy, kawai dai ya riga yayi wa kansa ado ne da bakin fenti, I want to have a chance dazan yi presenting dinsa as the good guy he is" Hafsat ta girgiza kanta tace "you may not have that chance, kawai kisa rana ki kai shi, in yes, yes in no, no, shikenan an wuce gurin" ita Hafsat bata fahimci cewa no dinne zuciya ta ba zata iya dauka ba, bayan heart break din dana samu akan Ibrahim bana jin zan iya daukar wani heart break din na rabuwa da sultan. Ina so inyi ta jan lokaci for as long as possible saboda bana son rabu da shi. A hanyar mu ta komawa gida sultan ya lura da changin yanayi na ya tambayeni "me ya faru?" Na girgiza kaina nace "babu komai" ya saka hannunsa a gashin sa yace "she doesn't like me ko?" Nace "no ba haka bane wallahi, ta nuna min ya kamata in kaika gida gurin daddy ni kuma am not ready yanzu" ya hade rai yace "why not? ni am ready, ke kawai nake jira ki kirawo ni" na kalle shi naga da gaske yake babu wasa, he is strong, very strong, stronger than Ibrahim, dan nasan Sultan ba zai taba guduwa ya barni ba, ba zai taba rabuwa dani ba sai dai ni in rabu dashi, wannan kuma shine abinda nake tsoro, tunda Sultan yazo duniya yake shan wahala mutane suke juya masa baya da nuna masa kiyayya, bansan abinda zai faru dashi ba in nima iyayena suka tilastamin na rabu dashi.
Nayi nisa sosai a harkar project dina dan kadan ya rage min in kammala, haka zalika project dina na psychology ma, wanda kachokam akan Sultan nake rubuta shi, ina ware light side dinsa wato behaviors dinsa da mutane suka sani da kuma shadow side dinsa wato behavior dinsa da yake buyewa, wadanda sune hakayensa masu kyau, anan na fahimci cewa halayen Sultan masu kyau sun ninka marasa kyau dan kusan rabin halayensa marasa kyau shaci fadi ne, rabin abubuwan da ake cewa yayi bai yi ba, wadansu abubuwan ma shi yake kirkira ya ce yayi saboda ya kara wa kansa tabo, gashi yanzu tabon shi zai iya jawowa a hana shi aure na. Dama hausawa sunce rana goma ta barawo rana daya ta mai kaya, rannan muna tafiya a makaranta ni da sultan wani bature dan ajinmu ya tsayar dani muna magana, Sultan duk ya gama kulewa sai faman taje kansa yake da hannunsa. Can dai ya gaji yazo ya taba Jack ta baya, ya juyo sultan yace masa "ita wannan da ka sakata a gaba kana kallonta kana mata surutu tayi kama da uwarka ne?" Jack ya bishi da kallo bai san me yace ba, Sultan ya sake cewa "Uwarka nace, shege da fuska kamar danyen kosai" ni dai ina ta kunshe dariyar da take neman kwacemin, kawai kamar daga sama sai ganin yaya Habeeb nayi a gurin yana kallona da mamaki, nan take dariyar ta tafi zuciya ta ta fara lugude a kirjina. Na gaishe shi sannan Sultan shima ya lura dashi ya bashi hannu suka gaisa, bai kuma cemin komai ba ya wuce warsa ya tafi. Tun daga lokacin ban kuma samun walwala ba har na koma gida, nasan yaya Habeeb ya taba kora min warning akan sultan kuma a lokacin nace masa babu komai a tsakanin mu to yanzu gashi ya kuma ganin mu tare kuma a England bama a Nigeria ba. Har dare ina ta sake saken amsar da zan bashi in ya tambayeni. Ina shirin kwanciya kuwa sai ga kiransa a waya, na dauka yace "ki same ni a palo" daga nan ya kashe. Na riga na gama shirya abinda zan gaya masa dan haka da confidence dina na fita gurinsa. Wani mugun kallo yake bina dashi har na zauna yace "me yake yi a garin nan kuma a Oxford kuma a tare dake?" Nayi gyaran murya nace "yaya Habibi" ya katseni "don't yaya Habibi me, ki gaya min gaskiya in ba haka ba straight daga nan sai gurin mommy zan kai ki" nace "yaya Habeeb kasan ina yin psychology, to an bani project topic" kaf na bashi labarin project dina da yadda na lura characters din sultan sun dace da project din nawa nace "to abinda yasa nake tare dashi kenan, idan ban jawoshi a jikina ba bazan iya studying dinsa yadda ya kamata ba. Amma da zarar na kammala aiki na a kansa zan yi masa kafa" naga kamar bayani na bai gamshe shiba na tashi na dauko laptop dina ba bude masa aikin da nake yi akan sultan ya karanta, sai a lokacin naga yayi ajjiyar zuciya yace "OK, but you have to be very careful, guy din is very dangerous" daga nan ya tafi ya barni ina tunani. Anya kuwa abinda nayi dai dai ne? Shi kanshi project din da nake rubutawa har yanzu ban gaya wa Sultan ina rubuta shi ba, gashi kuma nayi wa yayana karya akansa, Sultan ya sha gayamin cewa baya son secret. Amma in banyi haka ba menene a binyi. Kullum ina cikin feeling guilty saboda karyar da nake tayi ina boye boye. Dole in nemi mafita.
Na yanke shawarar zan daina ganin sultan har sai na samu solution, time is running out. Bani da abinyi a school wannan week din dan haka nayi zamana gida naki fita, wayar duniyar nan sultan yayi min amma naki fitowa nace masa bana jin dadi, wani lokacin sai yayi kamar yayi fushi amma ana jimawa zai kara kirana. Ranar Friday sati guda kenan bamu hadu ba, muna palon mu ni da Amina muna kallo har after 12, daga nan na fara jin bacci nayi mata sallama zanjr in kwanta tunda yanzu mun raba daki ita tana spare dakin part din mu. Ina bude kofar dakina naji kamshin Sultan, nayi sauri na mayar da kofar na rufe ina wara ido, aikuwa ga mamakina shi dinne a tsaye a bakin window. Da sauri na na saka lock a jikin kofar na juyo na rasa ma me zance masa "Sultan how do you get in here" ya nuna min taga, nace "amma duk security din gidan nan ta ya akayi ka wuce get na farko dana biyu, ka zagayo baya, taya akayi ma kasan waccece window na" devilish smile yayi kafin yace "baki san waye Sultan ba har yanzu" lallai sultan ya wuce duk inda nake tunani, tsalle yayo daga inda yake ya fada kan gado na kamar wani karamin yaro, sai da katakon gadon ya amsa, ni maimunatu yau na shiga uku katon gardi akan gadona, yanzu idan mommy ta shigo gurina fa? Ko Amina? Ta yaya zan fara yi musu bayani? Na tabbatar in aka zo aka kama Sultan a dakina to babu wani bayani da zanyi wa daddy ya aura min shi kuma. Nace "Sultan dan Allah ka tafi, this is very dangerous wallahi, idan wani ya ganka fa?" Bai bani amsa ba sai jawo bargo na yayi yana shanshanawa yana wani lumshe ido "hmmmmm I so much miss kamshin ki wallahi" ikon Allah sai kallo, anya sultan kansa daya kuwa. Sai a lokacin na kalli kayan jikina, riga da wando ne na bacci, Allah ya soni dogaye ne sai dai linon ne masu bin jiki. Nayi sauri na dauki hijab din sallata dogo har kasa na saka na bata rai nace "Sultan ka fitar min a daki" ya mike shima ya hade rai ya zo sai tin fuskata yace "if not?" Na kara bata fuska nace "zan danna button din alarm mintu biyu yayi yawa security zasu cika dakin nan har daddy da mommy na" ya kawo fuskarsa dai dai tawa yace "then go ahead and do it" mamaki ne ya cika ni na saki baki ina kallonsa shi kuma ya tsare ni da ido, can yace "nasan ba zaki iya ba because you love me too" murmushin mugunta ya sake yi min sannan ya koma ya yi adungure akan gadona. Ya gyara kwaciya tare da bubbuga gadon yace "zo ki kwanta" na watsa masa harara, yayi dariya yace "I will not touch in abinda kike gudu kenan, ni kaina kishin kaina nake yi akan ki, I can't bring myself to touch you. Zuwa nayi in ganki kuma muyi hira. Me yasa kika ce min baki da lafiya bayan kuma lafiyar ki kalau" na tabe baki nace "in kana son muyi magana ka fitar min daga daki gobe sai mu hadu muyi magana" shima tabe bakin yayi yace "OK then, sai da safe" daga haka ya gyara kwanciya yaja bargo ya lulluba, da sauri na karasa bakin gadon "sultan ka tashi ka fita don Allah" rokonsa nake tayi amma kamar ba dashi nake ba dan ko motsi bai yi ba, idansa a rufe amma nasan bai yi bacci ba. Na tsaya kawai ina kallonsa. Ina bin kowanne feature na fuskarsa da kallo, ban taba kare masa kallo irin haka ba, naga yadda akayi trimming sajensa yayi kyau sosai da yadda sajen ya kwalta akan fatar sa daga dukkan alama zai yi laushi, ji nayi a raina kamar in kai hannu in taba, nayi sauri na mike tsaye na bar gurin na koma bakin kofa ina tunanin abinyi, inna ce zan koma palo in kwanta that means kofar dakin zata zama a bude kenan and I can't take that risk, wani zai iya shigowa yaga sultan, and I can't take the risk of sleeping with sultan saboda I don't trust him and I definitely don't trust myself akansa. Muryarsa naji yace "in kin gama lissafin ki kashe fitila saboda bana iya bacci da haske" wato idonsa biyu ma ashe. Kofar ban daki na bude na shiga ina lissafin ko anan zan kwana ne? Kai gaskiya bazan iya kwana a toilet ba, nayo alwala na fito, ina fitowa na tarar har ya kashe fitilar ya koma yayi kwanciyarsa. Na dauki pillow na koma can bakin kofa na ajiye. Windows din dakin na rufe nayi locking ta ciki sannan na karo karfin AC. Na dauko wani bargon naje inda pillow na yake na shimfida rabi sannan na kwanta na kudunduna ba hijab din jikina sannan na sake lulluba da sauran rabin bargon. Oh ni Maimunatu naga ta kaina, yau zan kwana da gardi a dakina.
*wannan dai kam har da arias nayi muku, I love you guys so much. Stay blessed
Episode Forty Three: America
Na jima sam babu bacci a idona, yanzu mai zan ce wa daddy idan ya kamani da katoton namiji a dakina? Wato sultan shi bai san bari ba ko? Babu ruwan shi da what is right and what is wrong shi dai kawai in zuciyarsa ta raya masa yayi abu shikenan sai yayi kayansa babu ruwansa da consequences. Kunnuwa na baza ina sauraron ko zanji motsi, ko motsin Sultan ko motsin wani daga waje amma shiru banji komai ba, a haka har bacci barawo ya dauke ni. Dai dai sanda na saba tashi kafin assuba na farka, jikina duk sai ciwo yake yi sakamakon kwana a kasa da kuma takurewar da nayi a guri daya. Nayi mika ina addu'ar tashi daga bacci, Sultan ne ya fado min a raina nayi sauri na mike na kalli gadon. Babu shi babu alamunsa, babu alamun ma mutum ya kwana a gadon saboda gadon a gyare yake tsaf, to ko mafarki nayi ne? Kai ba mafarki bane tabbas Sultan ya shigo dakina jiya da daddare, na karasa gaban gadon sannan naka rose flower a ajjiye a saman wata farar takarda, na dauka na bude na karanta "na dade banyi bacci mai dadi irin na jiya ba, thanks for the night" da sauri na yayyaga takarda gaba na yana faduwa, yanzu idan wani ya karanta wannan ai sai yayi tunanin wani abu, lallai sultan, da ace bangani ba na tafi school mommy ko wani ya shigo ya ga wannan takardar kuma fa? Rose flower din na dauka na kai hancina na shanshana ina lumshe ido, kamshinta har cikin kwakwalwata da zuciya ta, na tafi da baya na fada akan gadon irin yadda yayi jiya, gadon naji gabaki daya kamshin sa yake yi. Sultan is special, he took a special place in my heart.
Ina gama shiryawa na fita palo muka yi breakfast da duk family din. Ana yi ana hira amma ni kam hankali na har yanzu ba'a kwance yake ba ina tsoron ko wani yaga sanda Sultan ya hau window na ko kuma anga fitarsa, har muka gama breakfast shiru babu wata magana mai kama da wannan, sai a lokacin na fara sakewa ina dariya. Daddy yace "Moon supervisor din ki ya aiko min da takarda akan project dinki. Yace da akwai wani experiment da zaki yi amma sai kinje John Hopkins hospital ko?" Ni fargabar Sultan ma ta saka na manta da wannan maganar nace "eh daddy, dama ina son inyi maka maganar bansan ya za'ayi ba" mommy ta ajiye spoon din hannunta tace "john Hopkins? Wai kuna nufin America?" Nace "yes mommy" nan da nan mommy ta fara daukar zafi tana girgiza kanta "wanne irin experiment ne ba za kiyi shi a duk girman UK ba sai kinje USA? Wa kika sani a america ma tukunna? Gaskiya dear kayi magana a chanza mata wani experiment din, ai a ko ina ana substitute, gaskiya ni ban yarda kije America ba" daddy kawai kallonta yake yana murmushi ita kuma murmushin nasa ne yake kara kular da ita. Yace "babu abinda zai same ta in taje america, it will be an experience to her, kuma abinda na fahimta shine ba ita kadai bace suna da dan yawan su za'a tura daga makaranta, dan haka in sunje tare zasu yi komai su dawo tare. Shi asibitin John Hopkins shine number one a duniya a harkar neurology dan haka zuwanta can din yana da muhimmanci sosai" mommy dai har yanzu kai take girgizawa alamar bata gamsu ba, daddy ya kuma cewa "look, shi kansa director na pediatric neurology department na assibitin is a friend of mine, Benjamin Carson, kafin su tafi zanyi masa waya, in hada shi da ita, mutumin kirki ne sosai, shi da matarsa Candy, idan ba kya son ta zauna a cikin students sai taje gidansu ta zauna acan, na tabbatar zai kula da ita sosai. Mutum ne mai dimbin ilmi dan yana daga cikin top knowledgeable mutane na America"
Ina bada shawarar duk wanda ya samu dama ya sayi littattafan Ben Carson, Gifted Hands da Think Big, akwai tarin ilmi sosai a cikin su.
Nan dai daddy ya dauko wayarsa yayi wa Ben waya yayi masa bayanin zuwana da irin aikin da zamu yi ya kuma roki dan Allah ya sa idonsa a kaina. Da yake weekend ne shima Ben din yana gida sai bawa matarsa suka gaisa da mommy. Har suka gama wayar dai mommy bata saki fuskarta ba. Daddy yana fita ta saka ni a gaba da tambaya, tare da su wa zamuje? Kwana nawa zamuyi? Nace mata "6-8 weeks" nan ta kara tayar da hankalinta, nace mata "mommy ba gashi nan daddy yace a gidan uncle Ben zan zauna ba? Tunda shine shugaban gurin nan kinga tare zamu ke zuwa asibitin in mun gama abinda zamuyi mu dawo gida tare" mommy tace "Moon mutanen nan fa ba musulmai bane ba, in fact they are very devoted christians, bana son kije gidansu suna kira miki jesus da yesu, kuma duk gidan nasan sun rarrataya cross, malaikum rahama ba zasu shiga ba gashi kema kuma kina ciki" nace "to mommy in hankalinki bai kwanta ba ki barni kawai in zauna a lodge din da za'a bamu, a cikin quaters din asibitin ne, kuma kowa nashi daban ne, mom trust me" ta dan saki fuskar ta kadan sannan tayi tsaki tace "ni dai da zaku fasa tafiyar nan da sai hankali na yafi kwanciya" nayi ajjiyar zuciya a raina nace "nima da zamu fasa tafiyar da sai hankali na yafi kwanciya" tun sanda aka yi mana maganar tafiyar nake tunanin yadda zata kasance, akai na bani da matsala, problem dina Sultan ne, dole in gaya masa zancen tafiyar kuma I am 90% sure sai ya bini, and that's my problem, bana son ya bini, especially after ziyarar da ya kawo min jiya a cikin gidan mu ma kenan wanda yake cike da security ballantana in na tafi wata duniyar ba daddy ba mommy.
Ban gaya wa sultan zancen tafiyar ba sai ana gobe zamu tafi, a tunanina ai in lokaci ya kure ba zai samu chance din bina ba, bawai inason rabuwa dashi bane a'a sam bana jin dadin yadda nake wa iyayena karya akansa sannan kuma har yanzu na kasa samun courage din zuwar musu da maganarsa. Tun da naje school muna tare dashi har aka zo daukana amma na kasa yi mishi maganar, sai bayan nazo gida nayi shirin kwanciya sannan na kira shi a waya, ya dauka da sallama kamar yadda ya saba, na amsa masa sannan yace "are you already missing me, love" nadan yi dariya sannan nace "magana nake so muyi, be serious please" yace "ina jinki" na dan sassauta murya nace "kana ji, dama wani dan course ne daga makaranta aka tura mu zamuyi a US, to gobe zamu tafi insha Allah, shine dama na ke so in gaya maka tun dazu a school kuma na kasa" shiru bai ce komai ba, na cigaba "Sultan dan Allah kar kayi fushi, ina taso in gaya maka wallahi tun tuni bansan yadda zaka dauki maganar ba, ba wani dadewa za muyi sosai ba, please say something" murya a duskure yace "for how long zaku kasance a can din?" Na yi shiru kalmomin sunyi min nauyi, sai da ya maimaita tambayarsa sannan nace "6-8weeks akace mana" nayi sauri na kara da cewa "amma ba lallai ne mu kai hakan ba, da mun gama zamu dawo" shiru bai ce komai ba amma ina jiyo numfashinsa ta wayar, sai da na gaji na kira sunansa "Sultan?" Yace "yaushe zaku tafi" nan ma amsar tawa ba mai dadi bace "gobe" ya maimaita "gobe?" Na daga kaina kamar yana kallona, "wato kina nufin dazu da muka rabu bye bye kika yi min kenan sai nan da wata biyu?" Na danyi dariyar yake nace "wata biyu ne fa kawai Sultan, kuma ai kullum zamu ke yin waya, kuma dana kammala wata biyun nan na gama project dina sai in rubuta report in yi submitting.... " kawai ji nayi ya katse wayar, na tsaya ina kallon wayar a hannuna, sultan dan rigima, text na rubuta masa da kalamai masu dadi cikin sigar bada hakuri na tura masa, shiru2 babu reply, lallai da gaske fishin yake yi, bamu taba fada da sultan ba, bai taba yin fushi dani ba, sai naji rai na duk babu dadi. Washe gari 12 jirgin mu zai tashi dan haka da wuri na tashi na kaya na da zan tafi dasu, bini2 sai in duba waya ta amma babu missed call babu message from sultan. Kudi sosai daddy ya bani kuma ya kira uncle Ben ya sake tuna masa yau ne fa zuwa na. Mommy har lokacin cewa take yi ita fa sam hankalinta bai kwanta da zancen tafiyar nan tawa ba, nima kuma haka, duk jina nake yi jiki a sanyaye ko dan ban taba yin tafiya mai nisa on my own ba. Gaba dayan su ne suka raka ni airport har mommy, har na shiga jirgi ina ta kiran Sultan amma yaki dagawa, duk sai naji kamar in fito ince na fasa tafiyar dan dai kawai babu yadda zanyi ne. Kira after kira nake ta jera wa Sultan kafin passengers su gama shigowa amma still no answer, na kashe wayar na jefa a jakata, hankali na duk ya tashi, anya kuwa nima zan iya jure wadannan satittikan ba tare da sultan ba? Especially in ya cigaba da kin daukan wayata. Muka sassaka seat belt din mu jirgi ya tashi, wani dan tsohon bature ne a kusa dani dan haka muna gaisawa na gyara kwanciyar kujera ta na saka earpiece ina jin karatu na lumshe ido na ina so inyi bacci ko Allah zai sa zuciya ta tayi sanyi. Nasan dole Sultan zai sakko dan kansa dan haka nayi alkawarin ko mun sauka bazan kira shi ba har sai ya kira ni da kansa. Jiki nane ya bani kamar ana kallona, to shi wannan tsohon menene nashi na kallon mutane kuma? Su turawa fa sam basu da kunya wallahi. Mayafi na naja na rufe fuskata ba tare da na dube ido na ba, ji nayi ansa hannu an bude fuskar tawa, da sauri na bude ido na zanyi bala'i amma se me? Sultan na gani zaune a kusa dani yana kunshe dariya "do you miss me, Love?" Na rasa dariya zanyi ko kuka, mamaki da takaici duk suka rufe ni shi kuwa dariya sosai ya ke yi, na dauki magazine din kusa dani na fara dukansa aka da ita, ya saka hannayensa ya kare yana cigaba da dariya, can dai na lura mutane da yawa a jirgin mu suke kallo, nayi sauri na ajiye magazine din hannauna na maze kamar bani ce nake yi ba. Sai da ya gama dariyarsa sannan ya juyo, "kin dauka fushi nayi ko?" Nayi banza na rabu dashi, ya cigaba da "ni na isa inyi fushi dake? Ai kin wuce wannan gurin. New York is not England. Bazan iya barinki ki tafi ke kadai ba, jiya bayan munyi waya na kira airport na tambayi wanne jirgin ne zai tafi America yau kuma karfe nawa zai tafi, sai kawai nayi booking na shirya kayana" nace masa "ya akayi ka samu visa daga jiya zuwa yau?" "Visa kuma? Legally ni dan America ne acan aka haife ni, i don't need a visa to go there" what a fool i have been, shaf na manta da wannan tsarin, na kasa tantancewa farin ciki nayi da zuwan Sultan ko bakin ciki. Earpiece dina guda daya ya cira ya saka a nasa kunnen shima ya kwantar da kujerar sa a haka muka yi bacci tare. Bamu farka ba sai da aka fara announcing jirgin mu zai sauka sannan muka tashi muka saka seatbelts din mu. Direct asibitin muka tafi, muna zuwa muka hadu da sauran students aka bamu keys din dakunan da zamu zauna sannan aka fara zagayawa damu za'a nuna mana duk inda muke bukatar sani, Sultan yazo ya ce in bashi key dina ba musu na mika masa ya tafi. Ina kallon yadda sauran students din suke kallona da alamar tambaya, a raina nace ina ruwanku? Mahdi ya dawo kusa dani yace "so..... I have seen you found your dark skinned man, Allah ya bar kauna" nasan magana yake gayamin dan haka na dauke kaina nace "amin" sai kuma yace "are you guys like living together kenan?" Na kalle shi ya hade rai nace "what do you mean?" Yace "naga ya biyo ki nan, kuma gashi har da wani karbar key din dakinki ya tafi zai shiga, ni dai a sani na ba'a gayyacemu daurin aure ba ballantana muce ai mijinki ne" na katse shi nace "dakata ya isa haka, kaya na ne da na zo dasu a cikin motar daya dauko mana shata daga airport, shima kuma da kayan sa a ciki, ya karbi key dina ne saboda ya sauke min kaya na ya tafi ya kai nasa masaukinsa. I don't even know me yasa nake maka bayani cos I owe no one an explanation" daga nan nayi gaba na barshi. Sai kuma naji a raina babu dadi saboda gaskiya ya fada min, sultan ba muharramina bane he have no business da shiga dakina. Bayan mun gama duk zagayen mu, a gajiye muka koma lodge din mu, one bedrooms ne a jere kowanne da number a jikinsa. Na duba nawa na tarar da a bude an dan saya kofar, a hankali na tura ne leka kaina ina sallama, babu amsa, na shiga ciki nace "sultan" nan ma shiru babu motsi, na sauke ajiyar zuciya sannan na kare wa dakin kallo, an gyara shi tas sai kamshin freshner yake yi, sabon bedsheet din da nazo dashi ne akan gadon tare da bargo, wato Sultan har kayana ya bincika ya dauko kenan ko? Shi sam baisan ma'anar boundary ba. Ya share dakin tas yayi mopping ya gyara gadon ya jera min kaya na a chest of drawers da suke dakin, ina dubawa naga har underwears ya saka su a drawer daban, kunyar duniya ta isheni yau Sultan yaga panties dina da braziers dina. Na duba toilet naga shima a gyare tas yana ta kamshi, sai a lokacin na lura har da karamin carpet ya siyo ya saka a gaban gadon. Tun ba yau ba nasan Sultan yana da tsafta sosai dan har mamakin tsaftar sa nake inna lura da irin yadda ya taso, koda yake ita tsafta a jinin mutum take, dan wani zakaga gidan su masu tsafta ne amma shi a kansa kazami ne. Komawa nayi nayi locking kofar, kayan jikina na chire na shiga wanka na tarar har kayan wanka na ya jera min a toilet din, na fito na shirya cikin riga buba na gyara gashina nayi packing a tsakiya kamar yadda nake yawan yi in ina gida, na fesa turaruka na sannan na saka hijab na fara ramuwar sallolin da ake bina. Ina idarwa naji anyi knocking nace "am coming" kafin in karasa kawai naga an bude kofa an shigo, na tsaya ina bin shi da kallon mamaki ganin key a hannunsa, wato spare key din dakin ya zare ya tafi dashi, as if dakin namu ne mu biyu, na hade rai sosai na rike kugu ina kallonsa, shi kuma yana murmushi, Allah yaso ma ban cire hijab din da nayi sallah dashi ba, "wannan bata ran kuma fa? Ni na kasa banbance yaushe kika fi kyau, in kin bata rai ko kuma in kina dariya" na kare daure fuska na ce "me yasa ka daukar min kex din dakina? Kasan hakan ai ba dai dai bane in kazo gurina sai ka kira ni a waya in fita in same ka ba wai ka shigo min daki ba" yi yayi kamar bada shi nake ba ya karaso dakin ya ajiye ledojin abincin da suke hannunsa sannan ya zauna a bakin gadk yana cewa "wash na gaji da yawa" na kara masa wata hararar nace "malam sauko min daga gadona, kuma ma waye ya baka damar ka bude min kaya? Kasan dai kayan mata sirri ne ko?" Ya sake share ni ya sauko yana bude ledar abincin da akayi sealing dinsa a cikin dan babban container, sai lemuka wanda ban taba ganin irin suba masu sanyi ya ajiye a gefe "malama in zaki zo muci abinci kizo, in kika tsaya iyayi kinsan ni bana wasa da abinci zan chinye ne in barki" daga haka yasa cokali ya fara cin abincinsa, ina kallonshi yana wani lankwasar da wuya yana lumshe ido nima naji yawuna ya tsinke kuma dama yunwa nake ji da gaske, a hankali na tafi kamar wadda ake jana da magnet naje na zauna na dauki cokali na fara ci dadin abincin yana ratsani, sai da muka kusa cin rabin abincin babu wanda yace wa kowa komai, can dai naji babu dadi tunda ni ban iya shiru ba nace "thank you for.... " na nuna dakin da hannuna, ya ajiye spoon din hannunsa yace "you are welcome" na ce "a ina zaka sauka ne kai?" Yana murmushi ya nuna kan gadon, na harare shi yayi dariya yace "relax 'yammata, garin mu fa kika zo, i have a house here duk da dai yanzu da akwai wadansu friends dina a ciki amma acan zan sauka" na gyada kaina alamar gamsuwa, a haka muka gama cin abincin mu yana ta yi min hida, nayi mamakin yawan abincin da naci, da zan sja drink din sai da na duba ingredients dinsa, ina kallon sultan yana yi min dariya na harare shi kawai bance komai ba. Yana gama wa "nace to atashi kuma asan nayi, sai da safe" ya mike yace "ba sai kin kore ni ba nima dama baccin nake ji" har ya kai bakin kofa nace "bani spare key dina" ya jiyo yace "na karfi ne, in kina da karfi ki kwata"
I don't know why inna fara typing bana son tsayawa sai daga baya in ga ashe nayi da yawa. Ya kamata mu koma yi kadan kadan ko?
Episode forty four : America 2
Yana gama fadin haka ya ficewarsa ya barni. Naje nayi locking kofar amma a raina ina cewa wannan ai bonono ne rufe kofa da barawo. Na dawo na kyara inda muka ci abinci sannan nayi shirin kwanciya, ranar sam na kasa bacci saboda rashin sabo da sabon gurin, kawai na tashi nayi alwala na yita salloli ina rokon Allah ya bani karfin zuciyar da zan iya controlling Sultan shi kuma Allah ya shirya min shi, na tuno da maganar Amira da tace am too soft and Sultan is too hard, in dai har ina so in gyara masa rayuwarsa dole nima in zama hard amma how? I have been soft tunda nazo duniya how can I be hard kuma yanzu?.
Washegari muka fara aikin da ya kawo mu tukuru, aikin shine koyon yadda ake raba twins din da aka haifa a hade ta ka, yadda kowanne daga cikin su zai rayu. Kullum wuni muke yi a lab sai yamma likis sannan zamu dawo, kuma kullum muna dawowa zan tarar da abinci Sultan ya ajiye min, wani lokacin ma har da ruwan zafin wanka, sai yanzu na fahimci dalilin da yasa ya dauki spare key dina kuma inajin dadin yadda yake kula dani sosai, saboda badan shiba gaskiya zaman zai yi min wahala sosai, fita siyan abinci kawai sai ya isheni. Wani abin mamakin shine duk da cewa ni kadai nake zaune yanzu amma Sultan har yau bai taba kai hannunsa jikina ba, ko wani abu zai bani baya barin hannayen mu su hadu, na jinjina masa ta nan gurin sosai dan ba ko wanne namiji ne zai iya haka ba, wani lokacin har tunani nake "to ko he is not attracted to me?" Amma kuma in na kalli idonsa ina gani a ciki, wani lokaci har bana son hada ido dashi saboda irin abubuwan da nake karantowa a ciki, abinka da psychologist, lol. Watan mu daya a America wani aiki ya taso wa Sultan wanda ba zai iya yi tanan ba sai lallai yaje Nigeria, ji nayi kamar zanyi kuka har sai da ya gane yace to ya fasa tafiyar sannan na hakura. Kafin ya tafi sai da ya bada order a restaurant din da yake siyo mana abinci cewa kullum zasu ringa kawomin safe, rana, dare babu fashi. Yana tafiya muka dinke a waya, kudin da Sultan ya kashe a saka credit daga tafiyarsa zuwa dawowarsa Allah ne kadai yasan yawan su, koda yaushe muna tare a waya sai dai in zanyi waya da 'yan gida ince masa ya kashe kuma shima ana jimawa zai sake kira. Satinsa biyu acan ya dawo amma ji nayi kamar yayi wata biyu. Yana dawowa ya shiga lodo min siyayya yana ajiye min wai tsarabar da zan kaiwa 'yan gidan mu, nace "Sultan wannan uban kayan ya zanyi in tafi dasu?" Yace "shipping dinsu zanyi miki ai" na sake cewa "to yanzu in naje dasu gida ince da mommy a ina na samu kudin saye?" Na danyi tunani kadan sannan yace "tell her you won the lottery or something" kawai na saki baki ina kallonsa, shi a ganinsa wannan is a total excuse, shi bai saba in yayi abu a tuhume shi ba dan haka bashi da idea yadda za'a yi wa iyaye karya. Haka yayi ta lodo kaya yana jibgewa.
Sati daya ya rage mana mu dawo England, duk ayyuka sun yi mana sauki dan kusan zan iya cewa mun kammala, ana koya mana ne yadda za'a kula da twins din ana monitoring dinsu har su warware. Sai lokacin sultan ya samu damar fita dani yawon ganin gari, ai kuwa nasha gararamba lungu da sako na New York sai da ya shiga dani. A lokacin ne ya kaini gidan sa ya nuna min. Tun sanda yace min can zamu je na kudurta a raina cewa bazan shiga ba, muna zuwa yayi packing ya zagayo ya bude min kofa naki fitowa, ya tsaya yana kallona "ko sai na fito dake ne?" Nace "no kawai dai bazan shiga bane" in yayi mamaki ma ya boye bai nuna min ba yace "ohh really? Duk zirga2 da nake yi gurinki ke ko shiga ki saka min albarka a gida na baza kiyi ba? Thanks a lot" wani barin na zuciyata yace min, he is trying to control you, don't give in, na daga kafada nace "sorry, kawai dai naga kamar shiga gidan ka is way ahead of limit" shima kafadar ya daga yace "if you think so, amma matsalata guda daya ce, what I plan is in munzo nan zan barki anan zanje wani guri in karbo sako a gurin wani wanda gobe zai bar gari gobe kuma gurin da zamu hadu is no place for a lady especially lady din da ba zata iya shiga gidan fiancé dinta ba" na daga masa hannu nace "technically kai ba fiancé na bane yet" yayi murmushi tare da jingina da jikin motar yace "OK, yanzu ya kike so ayi?" Na kalleshi ya langwabar da kai side daya, na dauke kai a zuciyata ina cewa, don't fall for that, ya sake zagayo wa ta side din dana mayar da fuskata yace "na rasa me yasa har yanzu kin ki trusting dina, if I want something da tuni na karba, you are too precious for that, I just want you to see my house, nan shine inda na zauna for thirteen years, tun ina twelve years nake rayuwa a gidannan har na kai twenty five years" ba fito daga motar ina karewa gidan kallo, madaidaici ne, sama da kasa, da veranda a kofar gidan, gaba daya gidan a kewaye yake da flowers masu kyau. A hankali na tambayeshi "amma kai kadai ka zauna a gidan tun farkon zuwanka? Ina nufin girki da kula da gida" ya daga kafada yace "farkon zuwan mu akwai house help da driver da suke zuwa kullum, daga baya muka kore su muke kayan mu da kanmu, fifteen years na fara driving, Amir ya iya girku sosai, so we managed" na runtse ido na ina jin zafi a raina, sultan tun yana karamin yaro yake zaman kansa kuma a lalatacciyar kasa kamar America. Sultan ne ya dawo dani daga tunani na yace "look in baki yarda dani ba ga key ki bude ki shiga ki rufe kanki, just look around in na dawo sai mu tafi" ba kalleshi da tuhuma nace "how do I know baka da spare key?" Dariya yayi sosai yace "Wallahi bani da spare key, kinji na rantse miki dai" na karbi key din ina kunkuni na matsa baya, ya rufe kofar ya zagaya seat din driver ya shiga ya kunna motar yace "in kin shiga sama zaki hau, kasan anan friend dina yake zama, amma nace masa zamuzo dan haka ya fita" na gyada masa kai sai kuma ya tsaya yana kallona, na daga masa kafada alamar what? Yace "this is New York not Abuja, ki shiga ciki kiyi locking kofar sannan sai in tafi" Na turo baki na juya ina kallonsa yana yi min dariya har na shige cikin gidan na rufe kofa sannan ya tayar da motar ya tafi. Kallo daya na yiwa palon kasa na hau sama. Ina shiga wani katon hoton Sultan ba gani hannunsa rike da guitar fuskarsa da murmushi, akwai yarinta sosai a fuskarsa, na karasa gaban hoton ina kallonsa, na daga hannu a hankali na shafa fuskarsa ina jin wani sabon sonsa a raina, na shiga uku ni Maimunatu ya zanyi duk sanda aka raba ni da Sultan? Ba wani tarkace a palon amma kamar yadda nayi tsammani tas yake ko digon datti babu a ciki, na cigaba da kallon pictures din jikin bango, duk yawancin su shi da Amir ne, wani suna yara wani sun dan girma, gaskiya Allah ne kadai yasan shakuwar da take tsakanin Sultan da Amir. Wanj hoto ne ya dauki hankali na, Sultan ne da school uniform ana bashi gift a makaranta, gashin kansa a hargitse kamar wanda ya dawo daga filin dambe. So you are brilliant also. Na shiga bedroom dinsa naga gado ne kawai sai sif din kayan sa, na bude sif din a raina ina cewa kaima ai bude min kayana kake yi. Anan na saku baki ina kallo, sets din kaya ne sunfi karfin a kirgasu, a jere neatly, takalma, undies, p-caps abin ba'a magana. A raina nace dan gayu. Na koma kitchen naga babu kayan abinci amma akwai kayan electronics iri iri. Gaba na ne ya fadi da naga fridge, ko zan ga giya a ciki, a hankali na bude fridge din kamar mai taba wuta, na duba kaf banga alcoholic drink ba, na sauke ajjiyar zuciya na dauko orange juice na dawo palo na zauna ina sha.
Kamar daga sama naji ance "hello" a tsorace na juya saboda nasan nayi lucking kofa, wani black American na gani kansa ya sha kitso kamar wata budurwa a tsaye a bakin kofar palon. Na mike tsaye a tsorace ina kallonsa. Sosai naga shima ya tsorata yace da American English "Sorry, na dauka kun tafi shi yasa na dawo kuma banga mota ba sai kuma naga sama a bude, na dauka ya manta bai yi locking bane. Am so sorry, please karki fada masa" ajjiyar zuciya na sauke nace masa "babu komai" har ya juya zai tafi sai kawai wani tunani ya fado min a raina, this is my chance to know more about sultan. Da sauri nace masa "wait, at least tun da ka shigo ai ya kamata mu gaisa ko?" Da fara'ar sa ya dawo amma yana dan rarraba ido, daga dukkan alama Sultan ya kora masa warning akan zuwana. Na nuna masa kujera ya zauna nace "my name is Maimoon" yace "I know, sultan talk about nothing else" ya miko min hannunsa yace "I am Steve " nayi ignoring hannun daya miko min nace "so how long do you know Sultan?" Yace "as long as I can remember" na gyada kai nace "to yanzu misali in aka tambaye ka is he good, bad or in between me zaka ce " mamaki ne ya bayyana a fuskarsa yace "Sultan is more than good, he is the best person dana sani a rayuwata, duk wanda ya gaya miki wani abu bayan wannan karya yake yi. Ba dan Sultan va da yanzu ina cikin hoods ina trading drugs, he saw me through sec sch and college, bani kadai ba muna da yawa wadanda sultan ne uban mu a garin nan, cinmu, shan mu, suturar mu duk Sultan ne. Da akwai sanda za'a aiko masa da kudin makaranta daga gida sai ya dauka ya biya mana kudin makarantar mu sai ya aika gida yace kudin sun bata ko sun kare, muna kallo daddynsa zai aiko har gida azo a kama shi a rufe a cell, wani lokacin sai yayi sati sannan a fito dashi. Saboda Sultan ya ciyar damu ya koyi playing guitar, zai dauka ya tafi market square yayi playing ana bashi kudi in ya tara yazo ya siyo mana kayan abinci. Daga baya ya koyi art, sai yaje ya zana mutum ya biya shi kudi yazo ya raba wa mabukata. He once told me saboda orphans yake karatu, duk kudin da zai samu akansu zai karar, in dai yana da rai babu dan da zai yi kukan rashin gata" hawaye naji yana kokarin tahomin nayi sauri na mayar dashi, nace "naji ance kuma yana yin drugs da alcohol" ya bata rai sosai yace "drugs? No, not Sultan, he hates drugs, ko bashi da lafiya sai anyi da gaske yake shan kwaya ballantana haka kawai" na gyada kaina nace "alcohol?" Ya dauke idon sa daga nawa ya kalli gefe, he then shifted from one leg to another, as a psychologist, tin kafin yayi magana nasan amsar da zai bayar, a hankali yace "sometimes, but only when he is frustrated" nayi shiru na kasa yi masa wata tambayar kuma, ya cigaba da magana "he has a bad temper you know, yana da zuciya sosai, wani lokacin in ransa ya baci gaba dayan mu sai jikin mu ya gaya mana, it is his way of releasing his temper, baya harkar mata sam dan babu wanda zai ce ya taba ganin budurwar Sultan duk kuwa da 'yammatan da suke binsa kamar jela cos he is handsome you know and girl fall for his kind but baya kula su" ni dai kawai sauraronsa nake yi ina saving duk maganganunsa a kaina. Nan ya zauna yake ta zuba min labarai na rayuwar Sultan a America, wani inyi dariya wani kuma inji kamar zanyi hawaye. Muna haka mukaji tsayuwar mota, ya tsorata sosai ya mike yana leka window, dariya sosai abin ya bani, wato they respect and fear him at the same time. Nace masa "relax, ba shigowa zai yi ba" ya kalle ni yace "why? shida gidansa?" Nace "nice nace karya shigo" ina kallon sultan ya dauko wayarsa ya kira ni yace in fito mu tafi. Daga gidan bamu koma John Hopkins ba park ya kaini, muka zauna akan bench muka sha ice cream, anan nake tambayarsa "dama kana playing guitar baka taba min naji ba?" Ya danyi murmushi yace "kinga pictures dina kenan. Yes, ina playing guitar da, amma tunda na koma Nigeria na daina, one day zan yi miki kiji" sai gab da magrib sannan ya mayar dani, muna tsayawa yace 'akwai inda nake so in kaiki in an jima please, ki shirya zan zo around 8pm" serious tone din da yayi maganar dashi ne ya saka ni ban masa musu ba. 8 pm dai dai yazo ya kira ni a waya yace in fito, nayi shigar doguwa riga budaddiya, nayi rolling babban veil daya rufe min jikina sosai. Tunda na fito ya dora idonsa a kaina tamkar ba dazu muka rabu ba, nazo gabansa na tsaya nayi gyaran murya "kallon ya ishe ka haka malam" with seriousness yace "hace I ever told you you are beautiful?" Na juya idona nace "only a million times" yace "to bara in kara daya akai, you are very beautiful" yadda yake kallona yasa na rufe fuskata da hannuna nace "thank you" sai da muka yi tafiya ta kusan 30minutes duk da dai ba gudu yake ba, Sultan naturally baya gudu a mota, sannan muka zo inda zamuje. Kallo daya nayi wa gurin na fahimci ina ne, Club, na juyo na kalleshi da bacin rai nace "am not going in there" yace "ba wai na kawo ki nan gurin bane saboda naga kin dace da gurin, na kawo ki ne saboda ina son in nuna miki wani abu kuma inaso in gaya miki wata magana, na kawo ki nan ne saboda ina ganin in kika gani da idonki zaki fi gane manufata" ni dai kawai jinsa nake dan ni banga me zan gani ko ji a club ba amma yadda naga alamar babu wasa a fuskarsa ya saka na fita na bishi. Muna zuwa kofar gurin naga masu gadi sun fara gaishe shi, da sauri suka bude mana kofa, ana budewa naji wata hayaniya da karar kida da warin sigari, ga fitilu masu kala suna kawowa da daukewa. Tsoro ne ya shiga zuciya ta, na shiga uku ni Maimunatu yau ina na kawo kaina? Amma curiosity ya hana ni komawa da baya. Banyi tsammani ba kawai naji hannun sultan a jiki na, abinda bai taba aikawata ba, nayi sauri na ture shi ya sake kamoni yace "stay still, a guri irin wannan someone will just grab a beauty like you daga nan kuma babu babu wanda zai sake jin labarinki" bansan sanda na makalkale hannunsa ba, ina jinsa yana mun dariya ni dai ban kula shi ba, a raina ina cewa kai da kasan haka gurin yake ka kawoni? Wani mutun da nake tunanin ogan gurin ne yazo yana gaishe da sultan kamar zai cinyeshi, daga nan ya buda mana hanya muka bi ta cikin mutanen da kyar muka wuce har muka wuce stage muka zo wani gurin da babu mutane sosai, sai a lokacin na saki hannun Sultan, ya kalleni yana dariya na harare shi. Daga ganin gurin VIP section ne dan kujeru ne masu kyau a gurin, na samu kujera na zauna Sultan ya jawo kujerar kusa dani ya zauna shima, nan take aka cika gabanmu da kwalabe, kallo daya nayi musu na gane menene, na kalli Sultan da alamar tuhuma sai a lokacin ya lura da abinda aka kawo, da sauri yayi wa attendant din daya kawo magana da wani yare da ban gane ba, kafin minti daya an kwashe su an kawo wadansu, still nace ba zan shaba. Nace "sultan what are we doing here?" Ya sake matsowa ya saka idonsa a cikin nawa ya fara magana "Maimoon na kawo ki nan ne saboda ina so inyi miki bayani akan abinda kike ta yi min magana akai. Change. This place is where I practically grew up, kullum for over ten years anan nake raba dare, this people are my family, su kadai na sani a rayuwata" yana magana yana nuna cikin chunkoson mutanen club din, nima na bisu da kallo, irin mutanen da ake kira da ghettos, niggas da babu abinda suka sani sai shaye2, clubbing da crime. Wannan ita ce rayuwar da Sultan ya kasance a ciki for 15 years, it is a miracle ma that he is what he is. Na juyo da idona kansa ya gyafa min kai ya cigaba "farkon zuwana America daga ni sai Amir ne kawai, bamu san kowa ba, sai daga baya muka fara friends, a lokacin na lura kusan 50% na Africans da suke zaune a america basu da muhalli, basu da gata ga kuma tsananin talauci, rana daya na kori driver na na kori house maid dina na debo mutun goma na kawo gidana, daga nan supplies suka fara yi mana kadan saboda kudin da ake aiko mana dashi kawai nawa ne ni da amir, nan muka fara shiga trouble na kudi dan haka dole na fara improvising, ina playing guitar ina kuma making drawings for money, lokacin ban wuce 15 years ba. Kin san duk inda aka tara mutane irin wadannan to dole akwai matsala, my house was always in chaos but I held on, I felt like they are my responsibilities, lokuta da yawa one of them will get in trouble with the police sai in fito ince ni ne, cos nasan babana zai aiko ayi bail dina amma su in sun shiga sun shiga kenan" na gyada kaina murya can kasa nace "I know" yace "what?" Nan na bashi labarin haduwata da Steve a gidansa da duk labaran da ya bani, bai ce komai ba kawai ya sunkuyar da kansa, na cigaba da cewa "I also know about the orphanages" mamaki ne karara ya baiyana a fuskarsa yace "who told you that" nan na bashi labarin haduwa ta da wannan mutumin ranar dana fara shiga motar sa, na tambayeshi " amma me yasa baka son mutane su san cewa kai ka gina?" Ya shafa kansa yace "saboda badan mutane nayi ba, na dora wa kaina alhakin kula da duk wasu yaran da basu da galihu as long as I am alive kuma abinda nake archiving kenan with the orphanage, in dai har yaran sun samu muhalli, abinci, sutura, ilimi da kuma little bit of love, shikenan abinda nake bukata not people's praises" na bude baki zanyi magana yace "damn it, wannan ba shine abinda ya kawo mu nan ba, na kawo ki nan ne saboda ina so in gaya miki cewa I want to change, I want to be the person you want me to be but it will take time, i can't just change overnight, it is not possible, amma nayi miki alkawarin I will always give you my best, amma ina so kema kiyi mini wani alkawari" ya kamo hannayena duk biyun ya rike a cikin nasa, na kalli fuskarsa ina son in karanta idonsa amma emotions din da na gani sunyi yawa, yace "promise me that you will never let go of me, no matter what" hawayen da bansan sanda na fara su ba naji suna bin kunchi na, anya zan iya yi maka wannan alkawarin Sultan? A hankali nace "I promise I will also give you my best" murmushi yayi yace "thank you" sai kuma yace "I have a little something for you" ya saka hannu a aljihu ya dauko wani dan karamin box ya bude, zobe ne a jiki na diamond, a samansa anyi shape din moon, na bude baki kawai ina kallonsa, ya kamo left hand dina ya saka min a ring finger dina, sai kuma kawai ya tsaya yana kallon finger din, nima na kalla naga zoben yayi min kyau sosai kamar an gwada kafin ayi shi. Ya dago kansa yana wata dariya mai kama da sheshshekar kuka, ni ma dariyar nake yi, yace "yayi miki kyau sosai, ashe na fadi size dai dai" na karbe hannuna ganin bashi da niyyar cikawa.
Mutumin daya shigo damu gurin ne naga ya zo gurin mu da wata katuwar guitar a hannunsa ya mika wa Sultan yana masa magana excitedly da wani yare, ya karba yana dariya yace min "wai sun yi missing kida na, suna so inyi musu" da sauri nace masa "nima ina so" ya jima yana kallona sannan yace "then I will play for you" daga haka ya mike tsaye, nan take naga an zagaye gurin kowa na nutsu. Daga ganin yadda ya rataya guitar kasan gwani ne. Idansa cikin nawa ya fara playing guitar yana kuma waka a hankali.
What will I do without your smart mouth.
Drawing Me in and You kicking Me out.
You got my head spinning, no kidding I can't pin down.
What's going on in that beautiful mind,
Am on your magical mystery ride,
And am so dizzy, don't know what hit me, but I will be alright.
My head is under water but am breathing fine.
You're beautiful and am out of my mind.
Cos all of me, loves all of you.
Love your curves and all your edges,
All your perfect imperfections,
Give your all to me, I will give my all to you.
You're my end and my beginning,
Even when I loose am winning,
I will give you all of me, and you will give me all of you, of you
Our cards are on the table and we are both showing hearts,
Risking it although it is hard.
Cos all of me loves all of you..............
How many times do I have to tell you,
Even when you are frowning you are beautiful too,
Even if the world keeps beating you down I will be around through every mood.
You're my downfall, you're my muse, my worse distraction, my rhythm and blue,
Can't stop singing it is ringing in my head for you.....
Cos all of Me loves all You.
0 comments:
Post a Comment