Sai around 11pm muka bar club din, muna tafiya a hankali kamar yadda ya saba, ya tambaye ni "so, anything you want to ask me?" Na danyi shiru for some seconds sannan nace "why do you join the gang bang?" Sai da yayi dariya sannan yace "ke baki ji yadda sunan yake ba? It sounds dangerous, duk wanda aka ce dan wani gang ne mutane zasu ke tsoronsa, tsoro kuma yana kara wa mutum kwarjini, irin bad boy dinnan" nayi dariya nima nace "kai kuma burinka shine mutane suce maka bad boy right?" Yayi shiru bai ce komai ba, sai ya chanza maganar yace "waye ya baki labarin gang bang?" Nace "Amira, she told me about the rape case" ga mamaki na sai naga yana dariya, yace "dama wannan Amirar daga ganinta zatayi surutu da tsegumi" na hade rai nace "ba abin dariya bane ba ai, how can you get involved with those kind of people? Duk wandanda zasu hadu suyi raping yarinya karama kamata yayi ka nisanta kanka dasu ba wai ka kirasu friends ba" ya daina dariyar yace "no body raped anybody fa, it is all politics. Shi yaron da akayi case din akansa Daniel, lokacin babansa yana takarar governor a Nassarawa. Yarinyar da ake magana akanta tsohuwar budurwarsa ce fa, dama sun saba harkarsu kuma she is not a girl dan banbancinta da karuwa kawai dan ita a gaban iyayenta take, she knows duk sunayen friends din Daniel, lucky for me bata san ni ba, kawai rana daya aka zo aka bawa iyayenta kudi da ita kudi suka ce wai Daniel da friends dinsa sun zo har gida sunyi raping dinta" na katse shi nace "maybe kai a yadda kaji labarin kenan, mutane irin su fa babu abinda basa iya aikatawa" shima ya katse ni yace "OK, she mentioned Amir's name, kuma ranar da tace abin ya faru tare muka wuni muka kwana da Amir, sai dai in a cikin bacci yayi raping din nata. Abubuwa da yawa yadda ake bada labarin su ba haka suke ba, kawai ke dai believe what you see, duk wani abinda wani ya gaya miki kar kiyi believing"
Sai da yayi packing sannan na lura how late it is, few minutes to one, ni da a gida nake na isa in kai karfe goma ma a waje? Sai kawai naji guilty feeling. Ya zagayo ya bude min kofa na fito muka yi sallama sannan ya koma mota amma yaki tafiya, nasan sai yaga na shiga gida zai tafi dan haka na tafi na fara kokarin bude kofa, ji nayi kamar ana kallona, na waiga baya da sauri sai naga Mahdi can nesa damu a gurin flowers, duk da cewa gurin da akwai duhu amma hasken fatarsa ya tona masa asiri. Ban nuna na ganshi ba saboda Sultan will not take it lightly, na bude kofa na shiga nayi waving at Sultan sannan na rufe. Da jikin kofar na jingina zuciya ta tana bugawa, is Mahdi stalking me? Mahdi yasan daddy na kuma yana sona dan haka yana kishin mu'amala ta da Sultan, nasan babu abinda zai hana shi zuwa ya bawa daddy labarin Sultan. Menene abinyi yanzu? To ko zuwa zanyi in same shi muyi magana ta fuskantar juna? Zuciya ta naji duk babu dadi, na mike na shiga toilet nayi wanka nayi alwala, nazo nayi shirin kwanciya, ina kwanciya na fara lissafin abubuwan da suka fari yau ina rewinding dinsu daya bayan daya ina kara fahimta, yau na sake fahimtar abubuwa da yawa akan sultan, kuma naji dadin mafi yawa daga abubuwan dana fahimta. Na dago hannuna daya saka min ring ina kalla. Wani nishadi naji yana shigata, kawai na fara murmushi ni kadai like an idiot.
Kwanci tashi har muka kammala duk abubuwan da suka kawo mu America muka fara shirye2n komawa England. Ana gobe zamu tafi Sultan ya kuma dauka na yawo, wannan karan cewa yayi zai nuna min abubuwan da yake yi for fun sanda yana America. Farko race track muka je kallon car race. Daga nan muka tafi bayan gari wajen wani ranch yace mu hau dokuna, ni kam ban iya hawa ba dan haka sai na dauko camera nake yi masa video. Sosai ya burgeni yadda ya iya sukuwa a doki danni har tsoro yake bani dan gani nake kamar zai fado, shi kuwa kamar wadda nake kara zuga shi har mike wa tsaye yake yi, yadda iska take diban gashin dokin tana wasa dashi haka take diban na Sultan shi ma. A mota ma bayan mun bar gurin videon na cigaba da yi masa yana ta tsokana ta wai ni matsoraciya ce nace na yarda din. Daga nan yace "I want to show you one last thing kafin in mayar dake gida" tafiya muka sake yi mai nisa sannan muka zo gurin wasu duwatsu, sam babu mutane a gurin, muka fara hawa wani dutse mai tsaho dan ni kam da kyar na kai duk na gaji. Muna zuwa na kunna camera ta na cigaba da video, ya nuna min gurin da zan tsaya shi kuma ya koma baya, sai da yayi kusan rabin dutsen sannan ya kwallo min magana yace "get ready" ni dai bansan me zai yi ba kuma, nayi zooming dinsa ta camerar naga ya cire shirt din jikinsa ya bar singlet kadai, ya durkusa kamar me shirin gudu, kar dai Sultan yace min da gudu zai hawo dutsen nan, ina kallon fuskarsa yayi taking deep breaths sannan ya fara hawowa a guje, wow , shine kadai abinda na iya fada, na saki baki ina kallonsa ta screen din camerar, dukkan jikinsa a mummurde yake musamman yanzu da ya cire rigarsa, yadda muscles dinsa suke rippling ne ya saka nayi sauri na runtse idona, I shouldn't be looking at this kamar yadda I shouldn't be doing abubuwa da yawa da nake yi. Iskar gudunsa kawai naji tazo ta wuce ni sannan na bude ido na naga ya doshi clip din dutsen kuma bashi da niyyar tsayawa, yana zuwa karshe naga ya doka tsalle ya fada. Zuciya ta ce naji kamar ta fado kasa, a rikice na yadda camerar hannuna na tafi inda ya fada da gudu ina kiran sunan sa. Ina zuwa karshen dutsen na leka kasa tare da durkutsewa a gurin. Sultan na hango a cikin ruwa yana kyalkyala min dariya. Ashe ruwa ne a gurin ni dai har lokacin kirjina bai daina bugawa ba. Ina kallonsa ya fito daga ruwan yana yi min magana amma bana jin me yake cewa saboda nisan gurin. Har ya zagayo ya kuma hawowa kan dutsen ina zaune a gurin, naga ya chanja kaya daga alama dama ya taho da wadansu a mota. Yana zuwa na mike tsaye nace masa "don't ever do that again" na wuce nayi tafiya ta na barshi. Shi sam bai damu da rayuwarsa ba. Har muka koma gida ina fushi akan tsoron daya bani, ranar da wuri muka koma saboda in karasa shirin tafiya gobe, already an sallame mu, wadansu ma sun tafi tun yau amma mu jirgin gobe Sultan yayi mana booking, nayi waya da 'yan gida na gaya musu gobe zan dawo. Tun dare na gama hada kayana kaf, sai wadanda zan saka goben na bari a waje. Sai da na gama shiryawa kaf sannan naci abinci nayi shirin kwanciya na kwanta. Ina kwanciya na dauko camera ta ina kallon pictures da videos din dana yi mana ni da Sultan ina ta murmushi. Text dinsa ne ya shigo waya ta, na dauka na karanta " I want you to know that these past few days are the happiest days of my life " nayi replying "me too" Har bacci ya fara daukata na tuna bansan time din da jirgin mu zai tashi ba, na kira Sultan wanda naji kamar cikin bacci yake magana yace min 10am.
Da assuba na tashi nayi sallah naga babu abinda zanyi tunda na kammala duk shiri na dan haka na saka alarm 8:30am nasan one hour ta ishe ni in shirya, kafin 30min kuma munje airport. Dan haka na koma baccina.
Kamar cikin bacci naji waya ta tana ringing da tone din Sultan, na duba agogo naga 7am, ne wannan mutumin yake so kuma? Zai hanani bacci kuma a jirgi ma ba lallai ne ya barni inyi baccin ba. Na juya na cigaba da bacci na. Waya ta ce ta sake ringing, Sultan again, na danyi karamin tsaki ba dauka. Da sauri yake magana "kiyi sauri ki shirya, jiya nayi mistake flight din mu ba 10 bane 8 ne" ai ban karasa jin maganar ba naji baccin ya wartsake, na mike da sauri ina kallon dakin dan in tabbatar ban manta komai ba, na cire kayana da sauri na daura bath robe na shiga toilet. Cikin shower na shiga na sakar wa kaina ruwa, sai a lokacin na fahimci har yanzu jikina ciwo yake saboda hawan dutsen da muka yi jiya. Na jima ina jin dadin zubar ruwan a jikina sannan na tuna cewa sauri fa nake yi, na kashe shower da dauko shower gel na fara shafawa a jikina har na hada kumfa a jikina.
Sultan
Bayan yayi sallar asuba yaji sam ya kasa bacci, yayi ta juyi yana ta lissafe2, ji yake kamar kar su koma England, duk da acan ma yana ganinta amma ba kamar nan ba, lokaci yayi daya kamata suyi taking next step a relationship dinsu, he is ready, amma ita har yanzu yaga kamar tana tsoro kuma baiyi blaming dinta ba, her family is a very decent family shi kuma he is what he is. Ya mike tsaye yana karasa hada kayansa, akan bed side ya ga flight tickets dinsu ya dauka yana dubawa "shit" 8am ya gani "shit" ya akayi yayi wannan mistake din? Yanzu yasan da wahala su samu flight din nan tunda sai yaje ya dauko ta sannan su tafi airport. Ya dauko wayarsa ya yi dialing number dinta, no answer, damn it yanzu haka ma bacci ta ke yi, ya duba agogo, 7:05, ya sake kiranta sai da ta kusa katsewa sannan ta dauka, da sauri ya fara mata bayani ta amsa in alarm ta kashe wayar, good at least yasan zata shirya kafin ya karaso, da sauri shima ya shirya ya dauki jakarsa ya fita yana waya da Steve. Gudu yayi ta tsalawa a mota yana ta addu'ar Allah yasa ta gama shiryawa. 7:30 yayi packing ya dau waya yana kiranta, ni answer, Good Lord, yarinyar nan ina ta shiga ne? Ya fita da sauri ya bude apartment din nata ya shiga, babu kowa a dakin sai jakarta a ajjiye, babu motsi a toilet, to ko ta fita waje ne? Har ya yi hanyar fita sai kuma ya dawo ya kama handle din toilet yaji shi a bude, on impulse, kawai ya tura kofar ya bude, a lokacin ne ya ganta, and his world froze.
Moon
Sai da na tabbatar na gama hada kumfa a jikina sannan na kai hannuna zan kunna shower, a lokacin naji kamar motsi a dakin, kar dai ace har Sultan yazo, gaba na ne ya fadi da na tuna a bude nabar kofar toilet din, wani side na zuciya ta yace min ya za ayi ya neme ki a toilet? Ina murda shower din naji karar bude kofa, a razane na juyo, a take idona ya fada cikin nasa, and I froze for some seconds. Wani irin adrenaline rush ne yazo min wanda har sai da naji daci a bakina, da wani irin sauri na mika hannuna da niyar daukar bath robe dina amma kafin hannuna ya kai kan robe din naji an rike su, a firgice na kalle shi dan bansan ya akayi ya taho daga bakin kofa ba har zuwa inda nake saboda akwai yar tazara tsakani. Abinda na gani a idonsa shi ya kara tsorata ni, lust ne, the kind of which I have never seen. "Sultan look at me, Sultan No, No" amma sam sultan ba fuskata yake kalloba, he is looking at something else, wannan Sultan din ba wanda na sani bane, idansa ya chanza daga light brown ya koma black, na fara kokarin kwace hannuna wanda hakan yasa ya hada ni da jikinsa ya rike gam, duk kumfar da take jikina ya goge ta a kayansa, na sake gwada yi masa magana "Sultan me kake son aikatawa ne haka, Sultan ka dawo cikin hayyacinka dan Allah" tashin hankalin da nake ciki yafi karfin hawaye, sai a lokacin yayi magana "please please please only now, only today" daga haka ya hade bakin mu guri daya ya fara kissing dina fiercely. Ji nayi komai ya tsaya min, dukkan emotions din da nake gani a idon sultan su yake zuba min, his sadness, loneliness, anger and his love for me. And I find myself responding back. Daga ni har shi karkarwa muke yi tamkar wadanda ake karkadawa. Babu abinda muke yi sai ajjiyar zuciya one after the other. I feel my senses slipping away from me. A lokacin da za'a tambayeni sunana ma ban sani ba. Hannun Sultan daya ya zagaye kuguna dashi ya matseni a jikinsa daya hannun kuma yana yawo dashi a jikina yana shafa duk inda hannunsa zai iya kaiwa. Allah ne kadai yasan time din da muka dauka a haka dan ni dai kam ban sani ba. Ajiyar zuciya Sultan ya sake yi wacce tayi vibrating a jikinsa gaba daya, a lokacin naji pulsing daga kasansa, wannan shi ya fara dawo min da sense dina, what in God's name is happening? What the hell are we doing? Another pulsing followed. Dukkan senses dina sun dawo kuma yanzu. What have I gotten myself into. Na fara tunanin daddy da mommy, idan suna kallona yanzu mai zasu ce min. Duk tarbiyyar da suka bani. Duk da cewa muna rayuwar kasar waje amma mommy ta bamu tarbiyyar da ko a family muna daga cikin wadanda ake yabawa. And all of it will be for nothing in the next few minutes. Na janye hannuna daga wuyansa na tattaro dukkan karfina na tura shi baya, inda ace dutse na tura to iyakacin response din da zan samu kenan. Na kara gwada tureshi ina kokarin raba bakina da nasa. Still no response. Ya raba bakina da nasa yace "please please don't fight" naji abinda yace kuma na gane me yake nufi. Karfina dana Sultan tamkar a gwada karfin kaza ne dana doki, lol, in dai har nace zan gwada masa karfi to shima dole zai saka min nasa karfin kuma in dai yasa min karfi to kashina ya bushe dan fata fata zai yi dani. Mafita ta daya ce itace inyi using brain dina, fata na daya ne Allah yasa kwakwalwar tawa tana aiki dan sosai jikina yake karbar sakonnin Sultan. Nabi toilet din da kallo a hankali, na hango kofa a gefen inda muke, a hankali na fara tafiya da baya yayinda Sultan shi kuma ya biyoni tamkar magnet har sai da bayana ya hadu da bangon toilet din kusa da kofa, ina jin sultan ya sauke wata ajjiyar zuciyar da na kuma jinta a kasa tare da kara matse jikinsa a nawa. Ta gefen idona na karewa kofar kallo, naga hook din da ake rataye towel a jikin kofar, good, very good. A hankali na saka hannuna a kan handle din kofar na murda, naji dadi da kofar bata yi kara ba duk da ma ko tayi ba lallai ne sultan yaji ba, na bude kofar kadan sannan na saka hannuna ta waje na rike handle din waje, na dakata ina jiran chance dina kuma ina addu'ar Allah yasa kada jikina yayi giving up kafin in samu chance din, ban jima ba kuwa sai ga chance dina ya fado, Sultan ya chire bakinsa daga nawa ya dago kansa da niyyar mayar dashi wani gurin daban. Na bude kofar da dukkanin karfina. Lissafina yayi dai dai dan hanger towel din ta samu Sultan a gefen kansa. Gaf. Da sauri ya sakeni ya rike kansa da hannu biyu. Next second a waje yayi min, ina fita na rufo kofar tare da murda key din sau biyu.
A bakin toilet din na durkushe ina karkarwa, har yanzu na kasa tantance takamaimai me ya faru. I feel lower than the lowest rat, I feel cheaper than a common prostitute. Sai a lokacin sannan wani kuka yazo min wanda ban taba irinsa ba a rayuwata.
# This chapter is for you in kinsan kina bin saurayi ba tare da sanin iyayenki ba. This chapter is for you in kinsan ba zaki iya cewa saurayinki a'a ba duk inda yace ki bishi zaki bishi. This chapter is for you in kinsan kina barin maza ko da kuwa ba samarinki ba suna shiga har dakinki. Ba fata nake miki ba amma zaki iya fuskantar abinda yafi na Moon, ba lallai ne ki zama as smart as she is ba, ba kuma lallai ne ki iya controlling jikin ki kamar yadda tayi controlling na ta ba. Sannan kuma ba lallai ne ya zamanto saurayin naki yana sonki kamar yadda Sultan yake son Moon ba. Zai same ki ne a banza kuma daga ranar ba lallai ne ya kara kallon ki ba. Allah ya raba mu da aikata aikin da zamuyi nadama har karshen rayuwar mu Allahumma Ameen.
Episode Forty Six : The Repentance
Gaba daya jikina karkarwa yake yi saboda irin kukan da na keyi, ba me sound sosai bane sosai amma irin wanda karfinsa yake jijjiga jikin mutun din nan ne. What just happened to us? Ji nayi na tsani kaina gaba daya saboda ina ganin duk abinda ya faru laifina ne. I shouldn't have let Sultan come to America with me tunda nasan ni kadai ce ba kowa a tare dani. Daya biyoni din ma I should have stand my ground in nuna masa limit dinsa. Amma na barshi kusan komai tare muke yi, shi ba muharramina ba sannan ga strong attraction da yake a tsakanin mu. Na tuna lokacin da ya fara cewa yana sona, cemin yayi he has nothing yana so inyi sharing what I have with him. Nothing din da yace bayana nufin kudi ba, yana nufin many things da yayi lacking including tarbiyya, amma maimakon inyi sharing tarbiyyata with him sai na biye masa muka zama marassa tarbiyyar gaba daya. Na tuno maganar Amira da take cemin ita character is contagious, idan ni ban gyara shiba shi zai iya lalata ni, gashi kuwa ta tabbata, ni nasan abubuwan da na aikata zuwana America ko a mafarki akace min zan aikata something like that zance karya ne. Ni nasan wannan abinda ya faru dani har da alhakin iyaye na a ciki. Sunyi iyakacin kokarinsu gurin bani tarbiyya amma nake cin amanar su ina bin Sultan, na tuno abinda na ke yi a abuja da England, sai inyi wa mommy karyar zanje unguwa mu fito da driver sai inyi ditching drivern in bi sultan, instead of in yace min inzo muje yawo in ce masa a'a in yana son gani na yazo ya same ni a gidan mu. Na tuna irin kallon da colleagues dina suke min tinda muka zo America suka ganni tare da Sultan, a lokacin sam ban damu ba, gani nake what people think about me doesn't matter, tunda kullum abinda sultan yake ce min kenan, na manta cewa ita shedar mutane itace shaidar da take bin mutun har kabarinsa. Nan tunanin mutuwa yazo min. Yanzu da zan mutu na tabbatar wuta zanje, annabi saw cewa yayi damu 'kada ku kusanci zina' amma ni exactly opposite abinda yace min nayi. Nan take wani irin tsoron Allah ya fara shigata, kukana ya tsananta, cikin kukan na fara kiran astagfirullah, astagfirullah har sai da murya ta da dashe ni kaina bana jin me nake cewa. Wani sanyi naji yana ratsani sannan na tuna har yanzu babu kaya a jikina, bedsheet din kan gadon na jawo na kudinduna ina karkarwa, a hankali naji na daina jin sanyin, kukan ma ya tsaya sai ajjiyar zuciya. Na sa hannuna na shafa fuskata ina goge hawayena, anan na taba lips dina da suka kumbura, tun da na mallaki hankali na babu wani namijin daya taba koda rike hannuna ne, but Sultan has kissed me today kuma wannan ba shine abinda nafi regretting ba kamar the fact that I kissed him back. I should have control myself but I didn't, I am too weak, too soft.
Na kalli hannuna naga zoben da Sultan ya bani last week. Sai a lokacin na tuna dashi a toilet, duk da abinda ya faru sai naji ina wondering is he OK? Ba motsi sam a toilet din, what if I hit him too hard? Na mike a hankali na dauki kayana dana ajiye na fara sakawa, sai a lokacin na tuna cewa na saba kumfa a jikina ban dauraye ba, na kalli jikina naga babu kumfa babu alamarta. Na saka kayana ba tare da ko mai na shafa a jikina ba, turare ma sai dai yayi hakuri yau kam. A madubi na kalli fuskata naga tayi fari tas tamkar babu jini. Idona ya kumbura sosai saboda kukan da nayi, na dauko glass a cikin handbag dina na saka, na tuna Sultan ne ya saya mana rannan iri daya ni dashi. A kwatina kawai naja nayi gaba, har nakai bakin kofa sai na tsaya ina kallon kofar toilet, har yanzu babu motsi a ciki, na karasa gurin na zare key din daga jikin kofar na tsugunna a hankali na tura shi ta kasan kofar. Still banji motsi ba. Hankali na naji bai kwanta ba, na leka ta keyhole, a zaune na ganshi ya jingina da bango yana facing kofar, idonsa a lumshe, side din fuskarsa daya da jini alamar karfen yaji masa ciwo, na jima ina kallonsa sannan na lura kirjinsa yana dagawa alamar numfashi, sai a lokacin na lura cewa kayan jikinsa complete suke har da takalmi da agogo, sai dai yanzu gaba daya kayan sun jike da kumfar jikina. Ba abinda ya zo gurina yayi kenan ba, zuwa yayi ya kaini airport, he has been good, more than good, how did this happened. Na sake masa one last look sannan na bude kofar apartment din na fita. Na duba agogo naga 12:30, yaushe time ya wuce har haka? Sai da anje gate din hospital din sannan na samu taxi nace ta kaini airport, ina zuwa na sake sayan wani sabon ticket for the next flight to England. Wanda suka ce min sai 6 na yamma zai tashi, I will wait, dan da in koma apartment dina gwara in kwana anan ina jira. Waiting room dinsu na shiga na zauna, na tuna ko breakfast banyi ba amma na share. Ina zaune har lokacin sallar Zuhr yayi na tashi na shiga toilet nayo alwala na dauko potable sallaya ta mai hade da compass na shimfida can gefe na tayar da sallah, sai da nakai sujjadar karshe inda anan na saba gabatar da adduoi na amma yau na kasa addu'ar komai, am a sinner, ta yaya zan roki Allah bukatuna bayan na saba masa, sai kuka, da kyar na dago daga sujjadar na kammala sallar sannan na dinkule a kan sallayar na cigaba da kuka na. Anan na wuni ko ruwa na kasa sha, ina ganin missed calls din mommy, nasan sunje daukana basu ganni ba, bazan iya magana ba shi yasa ban dauka ba. Karfe 6 jirgin mu ya tashi, na zauna a seat dina temperature ta tana hawa, flight attendant na kira nayi requesting a bani bargo, haka na kudunduna ina ta juya zoben sultan a hannuna. Is he OK? Ko ya fito daga toilet din? Duk da abinda ya faru tsakanin mu amma sam har yanzu banji haushinsa ba, nafi jin haushin kaina. Ina nan a kwance har jirgin mu ya sauka around 11:30 na dare, na kunna waya ta na fita reception na kwanta na kudunduna a cikin hijab dina ina karkarwa. Bana son zuwa gida sam saboda gani nake kamar abinda na aikata yana rubuce a goshina ina zuwa gida zasu gane. Number din Hafsat nayi dialing tana dauka nace "Hafsat ina airport bani da lafiya, dan Allah ku zo ku dauke ni" da sauri ta amsa jin yanayin muryata. Ba'afi 20 minutes ba sai gasu ita da Zayed, Hafsat tana taba jikina tace asibiti, Zayed yace "No, mu kaita gida kawai tasha magani ta kwanta, zuwa gobe in babu sauki sai a kaita asibitin" sai da muka je gidan Hafsat sannan ta kira mommy ta gaya mata gani nan a gidansu babu lafiya, nan da nan mommy ta daga hankalinta tace zuwa zatayi ta ganni da kyar daddy ya hana ta yace ta bari sai da safe, tunda daga Zayed har Hafsat duk likitoci ne yasan zasu kula dani. Magunguna zayed ya bani na sha sannan Hafsat ta dama min oats shima na sha, gana nan suka tafi suka barni suka ce in kwanta inyi bacci. Suna fita na tashi na shiga toilet nayo alwala na gabatar da sallah Magrib da Isha, sannan na zauna na fara jero salloli a duk sujjada ina kuka ina neman gafarar Allah, kawai sai na samu kaina da yiwa sultan adduah. Na tuno da maganar da Steve ya gayamin lokacin da na tambayeshi ko sultan yana shan giya, he said only when he is frustrated, yanzu kuwa nasan sultan is as frustrated as frustration goes. Sai da aka fara kiran sallar asuba Hafsat ta shigo da niyyar tashina sai ta ganni already akan sallaya sai ta koma. Sai da na idar da Sallah asuba sannan na kwanta, ji nayi kamar an dauke min wani nauyi daga kaina. A take bacci yayi awon gaba dani.
Aduk sanda bawa ya aikata laifi, babban abinda ubangiji yake so shine bawa ya tuba, taubatan nasuha, ka tuba da niyyar ba zaka sake aikata laifin irin wannan ba. Shi Allah mai gafara ne kuma mai rahama. In dai har ka tuba ga Allah, kai kanka ba sai an gaya maka cewa tubanka ya karbu ba, ajikin ka zakaji, saboda shi zunubi nauyi ne dashi, zakaji kunchi a zuciyar ka amma da zarar ka tuba zakaji kunchin ya yaye. Allah yasa mu dace.
Sultan
Jinsa yake kamar wanda yake yawo a gajimare, bai taba jin feeling irin wannan ba saboda bai taba bin wannan hanyar ba. Ji yake yi kamar ya bar duniyar nan mai cike da kuncin rayuwa ya kama hanyar wata mai cike da soyayya, gaba yake kara yi ko waiwaye baya yi burinsa kawai ya isa destination dinsa. Kamar daga sama yaji saukar karfe a gefen kansa. Ba shiri ya sake ta, ba wai zafin dukan yaji ba a'a it took him by surprise ne kawai, irin ba zato ba tsammani din nan. Ya rike gurin yana tunanin me ya faru, next thing da yaji shine karar rufe kofa. Sai a lokacin ya bude idonsa, ga mamakinsa sai ya ganshi a tsaye a toilet, toilet din apartment din Moon. "What the hell am I doing here" ya kalli kayan jiki sa yaga duk sun jike da ruwa, what happened, shi dai yasan ya taho da sauri zai dauki Moon zasu tafi airport, ya tuno ya shigo dakin yana nemanta, ya tuno sanda ya murda kofar toilet din, he remember seeing her. He then remember everything. Wani irin jiri yaji ya taso masa yayi baya ya hadu da jikin bango sannan ya durkushe a gurin. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. What have I done? A hankali ya fara jiyo saurin kukanta daga cikin dakin, jin kukan yake yi tamkar saukar ruwan kibiyoyi a kirjinsa. Ya runtse idonsa yana fatan Allah ya dauki ransa anan. Abu daya ne zai hana shi kashe kansa ayau, saboda yasan duk wanda ya kashe kansa wuta zashi, shi kuma yana da burin samun lahirar sa, tunda bai samu farinciki a duniya ba ko Allah zai nufe shi da rahama ya samu lahira. Sai da ya hadu da ita sannan ya fara tunanin maybe zai iya samun farin ciki a duniyar ma, amma yanzu after doing what he did, he knows that he lost his dunya sai dai kuma lahirar. Tun farko yasan cewa he is playing with fire, saboda yadda yake jinta is beyond explanation, amma gani yake ai zai iya daurewa, saboda yana ganin tunda bai taba aikatawa ba bai san dadin abun ba, yana ganin he can control himself, sai yanzu ya gane cewa ashe shayi ma ruwa ne. Har yanzu kukan take yi har muryarta ta dashe. Da ace wani ne ya sakata kukan nan da sai inda karfinsa ya kare amma gashi shi da kansa ya saka ta kuka kuma ko rarrashinta ba zai iya ba saboda baya jin zai kuma iya hada ido da ita. A hankali ya furta "am a monster" . Jin dadinsa kawai shine the things stopped halfway, da ace yayi destroying dinta completely da baisan yadda zai yi da ransa ba. "I should have know that I will never amount to anything good, iyayena ma sunyi abandoning dina saboda sunsan cewa am a monster" a take ya fara nadamar saninta a rayuwarsa, da basu hadu ba da shikenan something like this ba zai taba faruwa da ita ba, she is the most decent girl daya taba sani a rayuwarsa. Now she is crying because him. Ta daina kukan yanzu amma yasan kukan fili ta daina na zuci kuwa zata cigaba dayi har abada. Yana jinta tana shiryawa, tafiya zatayi, yana so ya sake ganinta, one last look, amma yasan ba zai iya ba, abinda yayi mata is unforgivable, ya jingina kansa a jikin bango tare da runtse idonsa. Ya jima a haka kafin yaji an bude kofar apartment din sannan aka rufe, she is gone, gone from his life. A hankali ya mike daga inda yake zaune a karasa gaban mirror yana kallon fuskarsa, jinin da yake fuskarsa har ya bushe. Bai damu da shi ba dan haushin kansa yake ji sosai, ya dunkule hannu ya naushi reflection dinsa, mirron ya tarwatse duk ya yanke shi a hannu "fuck" ba fada yana karkada hannunsa saboda da gaske yaji zafin buguwar. Ya kunna fanfo ya wanke hannun sannan ya wanke fuskarsa. A kasa yaga robe dinta, ya tuna sanda ya kwace ta daga hannunta, ya sunkuya ya dauka ya cusa fuskarsa a ciki yana shakar kamshinta, ya jima a haka sannan ya rataya robe din a ruyansa yayi hanyar kofa, ya murda handle din yaji a rufe, damn, wato he was as bad as sai da ta rufe shi a toilet, I am truly a monster, ya sake fada a hankali. Yayi bending yana studying lock din, sannan ya ciro belt din jikinsa ya zare pin din ya dan lankwasa shi kadan ya zura a keyhole din, bai jima ba ya bude kofar, tun yana yaro ya iya bude locks saboda tsabar yawan rufe shi da ake yi a daki. A Lagos kuwa hatta locks masu pins sai da ya koyi yadda ake budesu. Sai da ya jawo kofar sannan yaga key din a ajjiye a kasan kofar, wani abu yaji ya tokare shi a kirji, she loves him so much, tayi locking dinsa amma kuma sai ta ajjiye masa key saboda ya bude kansa, bayan duk abinda yayi mata, she loves him and that hurts him alot, he let her down bayan kuma shi yayi mata alkawari yace "I will never let you down " . Yasa kai ya fita ya kalli dakin yaga babu abinda ta dauka sai jakar kayanta, hatta kayan da ta chire suna kan gado. Yayi deciding he will have to come back later ya hada mata sauran kayanta ya aika mata dasu, da kayan da ya saya mata na tsaraba, amma shi kam yasan bazai kuma iya hada ido da ita ba.
Moon
Sai wajen 12 na tashi daga bacci, shima kuma yunwa ce ta tashe ni, a hankali na tashi zaune. Abubuwan duk da suka faru suna nan tas a raina amma kuma fes nake jin zuciya ta, na bude kofa na fita palo, mommy na gani zaune ita da Hafsat, sai a lokacin na lura da kibar da Hafsat tayi, she is pregnant, mommy ta tashi da sauri ta karaso inda nake "Moon ya jikin naki? Kinga yadda kika rame kuwa? It is my fault, dana sani na biki American nan in yaso ko hotel sai mu kama mu zauna har ki gama, zaman kadaici ne ya saka miki ciwon ba komai ba" na danyi murmushi a raina nace "I was never alone mom, but you will never know" na rungume ta ina jin dadi har cikin raina, mother is above everyone. Har wajen Zuhr mommy tana nan, sun sani a gaba ina ta basu labarin America da abubuwan da na koya, amma ko da wasa banyi mentioning sunan Sultan ba. Sai da daddy yayi ta kira sannam mommy ta tafi, ni kuma nace sai gobe zan dawo gida. A raina ina son magana da Hafsat ne. Sai da daddare muna bedroom din Hafsat sannan nace mata ina son magana da ita, ta samu guri ta zauna ta bani attention dinta, tiryan tiryan na fara fara bata labarin bina da sultan yayi america har abinda ya faru jiya ban boye mata komai ba, sai da na kai karshe sannan na sauke idona kasa nayi shiru. Saukar mari naji a kunci na na hagu, naji zafin marin sosai a raina nace "I deserve it " wani marin na kuma ji a kuncin dama, wannan karon har sai da kwalla ta kawo a idona, da sauri Hafsat ta mike ta fita, ni nasan kuka zata je tayi.
Follow my New facebook Group @ Maman Maama Novels.
Episode Forty Seven : Amir
Na jima ina shafa fuskata dan da gaske marin ya shige ni. I deserve it. I deserved everything that happened to me. Bawai na gaya wa Hafsat abinda ya faru bane dan tayi min fada ko wani abu ba, na gaya mata ne saboda ta bani shawara akan abinda ya kamata inyi yanzu. Hausawa sunce mai neman shawara sirri sa baya rufuwa amma kuma aikinsa baya baci. Na jima anan a zaune ina ta lissafe lissafe a raina, ina juya zoben Sultan a hannuna. I desperately want to know how he is, amma kuma bazan iya kiransa ba. Nasan kuma shima yana son yaji daga gareni, amma ba zai iya kirana ba. I just want someone to act as intermediary. Har nayi shirin kwanciya na kwanta babu Hafsat babu labarinta. A raina nace tayi fushi dani. Da safe na tashi na yi wanka na shirya sannan na fita, a kitchen na same ta ita da maid dinta suna hada breakfast, ko kallon inda nake bata yi ba har suka gama aikin ina zaune ina kallonsu, suka shirya dining sannan ta tafi yin wanka. Naje na zauna nayi serving kaina ina cikin ci sai ga Zayed nan, daga yadda yake yi min magana na fahimci cewa Hafsat bata gaya masa maganar da mukayi ba, wannan yana daga cikin dalilan da yasa na iya gaya mata, baza ta gaya wa kowa ba. Muna breakfast muna hira sai gata ta fito kamar amarya, tun kafin ta karaso Zayed ya mike ya taro ta suka fara zuba soyayya ni dai ina ta kallonsu. Ko wata rana ni ma zan samu wannan farin cikin? Da sauri sauri ya gama ya shirya ya fita asibiti. Nan muka zauna awkwardly ni da Hafsat, maid dinta tana cleaning table din. Can dai tace "yanzu how do I even know you are intact?" Na harare ta nace "ko in bude miki ki gani?" tayi ajjiyar zuciya tace "yanzu me kike so daga gareni" nace "so nake ki bani shawarar abinda ya kamata inyi" ta bude baki da mamaki tace "yanzu ke har sai na baki shawara? Kina nufin kice min da akwai sauran alaka a tsakanin ku? After what he did to you?" Na sunkuyar da kaina a hankali nace "I love him" tace "you are crazy" a raina nace "maybe I am" can ta sake cewa "yanzu in na baki shawarar ki rabu dashi, zaki rabu dashi?" Na girgiza kaina va tare dana kalleta ba. A fusace tace "then what do you want from me?" Na dan jawo kujera ta kusa da ita nace "yanzu so nake in san ta wacce hanya zamu yi moving forward, abinda ya faru ya riga ya faru, it is in the past. Amma matsalar itace bansan ta yadda zamuyi communicating da shi ba, I can't call him and he can't call me. So nake at least in baki number dinsa ki kira shi kuyi magana, at least to know how he is doing. He is a really good guy, he is not what people think he is. I don't want abinda ya faru tsakanin mu yayi affecting dinsa negatively. Please Hafsat" na gama kamar zanyi mata kuka, amma banga alamar tausayi sam a fuskar ta ba, sai ma tsabagen mamaki na da take yi, cikin mamaki tace "You want me to call him? In kira shi ince masa me for God's sake? Thank you for trying to rape my sister kike so ince masa ko me?" Na dakatar da ita da sauri nace "He did not try to rape me, what happened wasn't entirely his fault, ni ma da laifi na a ciki" kafin in karasa ta mike da sauri kamar wadda ta manta wani abu, taje bakin kofar palo ta bude kofa ta juyo tana kallo na cike da tsantsar takaici tace "get out of my house" banyi mata musu ba na koma bedroom dinta na jayo akwatina wanda dama ko bude shi banyi ba kayan ta nake sakawa, nazo na fice daga ni har ita babu wanda ya kalli wani. Ina fita na tari taxi nace ya kaini Nigerian embassy.
Ina zuwa gida zan iya cewa kusan na manta da komai saboda farin cikin ganin family na. Sai wani ji dani suke yi kamar zasu goyani. Kwana na biyu na warware sosai ina ta harkoki na amma ta ciki na ciki dan dai dai da second daya ban manta da Sultan ba. I terrible miss him. Kullum zan budo number dinsa a waya ta inyi ta kallonta. Duk sanda kuwa naji kira ya shigo waya ta sai naji gabana ya fadi ina tunanin ko shine amma shiru makatau. Last seen dinsa a Whatsaap shine a day to barowa ta America. One week ya wuce, two weeks ma haka. Ni kadai nasan yadda nake ji a zuciya ta tunda babu wanda zan gaya wa in ji dadi. Har aka yi mana fixing ranar defence na project din mu. Meaning mun gama karatu kenan. Na zama busy sosai ina tsara yadda zan presenting project dina, neurology zan fara sannan a week later in yi psychology. Duk sanda tunanin Sultan ya dame ni sai in dauko waya ta inyi ta kallon pictures din mu, wani inyi kuka wani dariya. Ko na dauko waya ta zan kira shi sai in tuna abinda ya faru sai in kashe, kunyarsa nake ji sosai. Ana gobe zanyi defense dina daddy ya tara mu a palo yayi min addu'ah sosai ta samun nasara, dan it is not easy kayi facing professors komai ilimin ka kuwa. Alhamdulillah washegari nayi defense dina successfully na gama. Sosai akayi celebrating a gida amma ni sam hankali na ba'a kansu yake ba dan yau kam da gaske nayi missing sultan saboda kusan tare dashi muka rubuta project din. Ranar har Hafsat tazo gida ita da Zayed sun kawo min gifts. Sai da muka kebe ni da Hafsat sannan ta tambayeni "so... Do you call him?" Na girgiza kaina da sauri, sai kuma hawaye suka fara zuba nace "I can't" ta gyada kanta tace "He is stronger than you, he is suppose to call you first in dai har yana so ku dawo tare" na gyada kaina ina goge hawayena, sai kuma ta rungume ni tana dan bubbuga bayana a hankali, tace "be strong little sister, am sure God have something special for you" Ranar da daddare na dauki wayata da niyyar kiran Sultan ina ajiyewa ya kai sau goma, daga karshe dai na kashe wayar na jefa a cikin jaka na rufe. Har na kwanta kuma sai na tashi na dauko camera ta na kunna videos din da nayi mana ana gobe zan taho, wajen horse race da inda ya hau dutse a guje ya fada cikin ruwa. Kuka na zauna sosai nayi.
Washegari muna zaune palo yaya Walid yace "Wai Moon ina saurayin nan naki da kuke yawan waya dashi? Tunda kika dawo daga America naji shi shiru" Mommy tayi sauri tace "kaima dai Walidi ka fada, nima naji shiru, kinsan dai almost karatunki ya kammala, daga miki kafar da baffa zai yi kawai shine idan ba'a gaya masa kin gama ba, shima kuma delay din da za'ayi kawai zuwa sanda result dinku zai fito ne. Gara kisan me kike ciki Moon. Nima kuma office din mu a Abuja sun fara damuna akan lallai ya kamata in koma aiki in ba haka ba sai dai inyi resigning, so nake muyi magana da daddyn ku kawai mu koma gida haka nan. Faruk ne kawai bai gama karatunsa ba shima kuma zai iya zama shi da daddyn ku zuwa sanda zai karasa" ina sauraronta ina lissafin in dai muka koma Nigeria to ni kam na kade har ganyena. Masifar Hajja da jarabar Munir kadai ta ishe ni. Su familyn mu gani suke yi kamar nayi girma da yawa, musamman yanzu dana gama karatun likita, gani suke ya za'ayi ace har na zama doctor babu aure bayan a zahirin gaskiya am just 22 years, 16 years na gama sec sch yanzu kuma after 6 years na gama first degree na. Har dare ina ta lissafin what to do. Na dauko report dina na psychology ina karantawa, it contains everything about Sultan, sai kawai naji ya kamata in dan kara masa armashi, kamar make-up. Na dan yi tunani kadan sai na mike na tafi part din su yaya walid, na debo kayan drawing dinsa na dawo dakina. I am not a good artist but I am going to try my best. Na zauna a nutse na fara zane, sai da na dauki 3 hours sannan na gama, na tafi palo na dauko fresh milk na dawo na zauna ina duba zanen da nayi. Sultan ne a tsaye, da sleeveless riga a jikinsa da three quaters wando. Ya zura hannayensa a aljihunsa ya dan juya kansa yana kallon side daya. Fuskarsa babu fara'a. Yayi kyau sosai kamanninsa sun fito dan duk wanda ya sanshi in yaga zanen zai gane shi. A jikinsa nayi rubuce rubuce akan behaviours din sa da mutane suka san shi dasu. The drunk, arrogant spoilt rotten prince. Daga bayansa sai na sake wani zanen something like his shadow, a jikinta kuma sai na yi rubutu kanana akan dukkan abubuwan da nayi learning na kyawawan halayensa, saboda yawan abubuwan da na rubuta har sai da gurin ya cika na rubuta etc. Kuma wadannan iyakacin abinda na sani ne kawai, dan na tabbatar da akwai wadanda ban sani ba. Na kalli zanen inajin wani dadi har cikin raina, ina ma mutane zasu ga wannan zanen nawa? Tabbas da sun so sultan kamar yadda nake son sa. I wish one day I will be able to show it to the world. Amma bazan yi hakan ba sai da amincewar Sultan. ( naso ace na iya zane dana zana muku. Lol ).
Ranar da zanyi presenting ita ce kuma final day dina a Oxford. Tun safe na shiga makaranta ina ta practicing abinda zanyi. A ka'idar makarantar malamai kadai ake presenting to, duk sauran guest suna waje. Ana kira na na shiga na kafe zane na a jikin board. Tun daga yadda malaman suke kallon zanen nasan ya samu karbuwa, wannan shi ya kara min confidence. Katardun hannuna na ajiye a gefe, i don't need them, I am going to talk about Sultan and I know him like the back of my hands. Nan na fara kararo bayani akan rayuwarsa, yadda yake rayuwa with two personalities, as a hero and as a villain. Tun da na fara maganar murmushi ne a fuskata. Ina gamawa daya daga cikin lecturers din yace min "who is this man to you?" nace mishi "he is my boyfriend sir" gaba dayan su sai da sukayi murmushi.
Ina fitowa da gudu na karasa gurin su mommy na rungume ta ina murna, nan muka ta daukan pictures dan har daddy yazo gurin duk suna waje. Muna cikin haka na hango motar Sultan, gaba na ne yayi wata irin faduwa, mutun na gani a tsaye a jikin ta yana kallon inda muke, Amir, nayi sauri na dauke kaina kamar ban ganshi ba amma kuma duk hankali na ya tafi gurinsa, ko tare suke da Sultan? Har muka gama yana nan a tsaye a inda yake, an kawo motoci zamu tafi nace musu "ku tafi kawai ni zan taho daga baya, akwai friends dina da nake so muyi sallama dasu" daddy ya kalleni da tsokana yace "friend ko boyfriend" na shagwabe fuska ina bubbuga kafa nace "daddy" yayi dariya yace "is alright, a driver will come back for you". Suna tafiya na juya na tafi gurin Amir. Nayi masa sallama, ya amsa fuskar sa da murmushi. Yana sanye da geans da sweater ya saka hannunsa a aljihun sweater kamar mai jin sanyi. Yace "can I talk to you for a minute?" Ya fada yana nuna cikin motar, Na girgiza kaina dan na fahimci shi kadai ne babu Sultan nace "akwai gurin zama a can, mu karasa sai mu zauna" ya daga kafada dan ya gane bazan shiga motar ba. Muka danyi tafiya kadan sannan muka karasa wata rumfa da akayi dan students, na jawo mana kujeru muka zauna. Sai a lokacin na kare masa kallo, baki ne amma very handsome, yana da manyan ido, fuskarsa irin mai natural murmushin nan ce. Na gaishe shi ya amsa. Sannan ya fara magana "kin ganni a England ko? Na rasa yadda zanyi muyi magana ne shi yasa dole na taho nan" nace da sauri "wait, kana nufin takanas ka taho daga Nigeria saboda kayi magana da ni?" Ya gyada kai yace "Sultan is my only family, I can do anything for him. I guess ya gaya miki labari na ko?" Na gyada kai, yace "you are very special to him you know, Sultan baya magana akan kansa amma daga dukkan alama kinsan komai akansa. Sultan mutum ne na musamman wanda ni kaina bazan iya kwatanta miki shi ba. Tunda ya hadu dake ya soma chanzawa. Ya daina shiga trouble, I was happy for him, very happy. But now...... " ya dago yana kallona, he looks very sad, ya ce "what happened?" Nace "bai yaga maka ba?" Ya girgiza kai yace "the fact that bai gaya min mai ya faru ba shi yafi daga min hankali. Bai taba boyemin wani abu ba. Amma yanzu all he keeps saying is that he is a monster, and that he is taking himself as far away from you as possible. Ranar da yace min zaku dawo England na kira shi sai yace min yayi missing flight, that something he never did, Sultan mutum ne mai kula da time, sai yace min kuma ke kin taho, daga nan na gane something is wrong saboda ba zai taba barin ki ki taho ke kadai ba, in ma missing flight dinne sai dai kuyi tare. Daga nan duk sanda na kira sai in tarar still yana America. Rannan Steve ya kira ni yace police sun kama sultan ya kwana a station, anan nake tambayar Steve me yake faruwa yace min everything is wrong, bai san me ya faru ba but yana ganin it has to do with you. Bayan an fito dashi daga station na kira nayi2 dashi ya gayamin me yake faruwa yaki. Yace he is never going back to Nigeria and he is also not coming to England. A america zai zauna. Tun daga nan na yi tunanin dole in neme ki, yaki ya bani number dinki and that your ugly faced friend itama taki bani. Things are going very badly for Sultan, dole na taho England gurin ki. I need your help" na runtse idona hawaye yana sauka akan kuncina. Yaci gaba da cewa "he is back on the bottle. Kin san rabonsa da alcohol?" Na girgiza kaina yace "tun ranar da kuka hadu a Hilton. Ranar sunyi rigima da Takawa as usual, he got drunk and I had to go out and leave him a gida, after he sober up shine ya fita kuka hadu. He told me that he got something better than alcohol, he said he got love" kuka nake yanzu sosai, ya cigaba "please Maimunatu dan girman Allah, call him" ya fada shima kaman zaiyi kukan, nace "but why should I be the one to call him? Mai yasa shi ba zai kira ni ba?" Yayi murmushi yace "because you are the light to his darkness"
Episode Forty Eight : Awkward
Ranar duk ban karasa ta da nishadi ba, today is my graduation day, I am suppose to be happy. Da naje gida ma yake kawai na ringa yi daga baya na tafi daki nace na gaji bacci zanyi. Na kwanta amma na kasa bacci. So Sultan thinks he is tough right? He thinks he can just give me up instead of facing me? Lets see how tough he can be. Wato ni nice soft one din shine Amir zai wani zo yace in kira shi ko? Na ga dai baccin ba zai yiwu ba na mike na fara abinda na saba duk sanda wani abu ya dameni ko wani al'amari ya shige min duhu, na tashi na fara gaya wa Allah. Nayi adduoi sosai akai na da kan Sultan ina nema mishi guidance na ubangiji. Sai a lokacin na fara wani tunani, addu'ar iyaye itace addua mafi inganci a gurin 'ya'ya, Sultan baya samun wannan, shi kansa ba lallai ne yana yiwa kansa da kansa addu'ar ba. Duk da dai adan zaman da nai dashi na lura baya barin sallah. Na gama adduoi na na kwanta akan sallayar nayi baccina.
Da assuba na tashi nayi sallah, har na koma zan kwanta naji still raina babu dadi, na dauko waya ta a jaka na kunna na nemo number din Sultan nayi dialing, sai da ta kusa katsewa sannan ya dauka, amma bai ce komai ba, naji takaici ya kamani, why did I even called? Na katse kiran kaman zanyi kuka. Ina ajjiye wayar kiransa yana shigowa. I let it ring. Ya sake kira naki dagawa. Message ya shigo. "Answer the call please" nayi reply "why didn't you call me sai da na kira ka?" "Am sorry, please pick up the phone" wani kiran ya shigo, it has been a month rabona da Sultan, rabon da inji muryarsa. Na dauka tare da sallama. Ajjiyar zuciya naji ya sauke. An awkward moment followed. Nace "look, idan ba zaka yi magana ba zan ajjiye wayar" a hankali yace "how are you?" sai da naji muryarsa sannan na fahimci how much I have missed him. cikin rawar murya Nace "I missed you" ya dan jima sannan yace " I have more than missed you, i have no word for what I felt" "amma me yasa baka kira ni ba? It hurt me sosai, how can you just give me up just like that?" A nutse ya fara magana "you have no idea how much I love you, do you? Bawai nayi giving up on you bane, I am a bad person Moon, You are good, more than good, bana son in bata miki rayuwarki. Ina sonki son da zan iya rabuwa dake even if it kills me, in dai har zaki samu kyakykyawar rayuwa" na katse shi da muryar kuka nace "and who says I want a good life? Huhh? All I want is a life with you. Just tell me idan har kai ka daina sona ne kawai ka gayamin ka daina min wani boye2. You keep saying you are a bad boy, you can never be good in dai har kana tunanin you are bad" yadda na rufe shi da fada ne yasa yayi shiru ya kasa magana. Nima dana gama fada na nayi shiru. Sannan nace "when are you going back to Nigeria?" Yace "I have nothing to go back to Nigeria for" nace a hankali "you can come to England, you have me here, right? Besides, ina son kazo ka gaishe da daddy" ya danyi jim sannan yace "are you sure?" Nace "yes, am sure. Kai na zaba a matsayin mijina, whether you are good or bad, kai nake so" sosai magana ta ta taba zuciyar Sultan dan har a muryarsa naji, shi abinda ya cigaba da insisting shine wai am too good for him, baya so ya sake letting dina down. Daga karshe dai na gaya masa cewa nan da about a month zamu koma Nigeria kuma muna zuwa aure za'a yi min da Munir, whom I despise, dan haka zabi ya rage nasa, is either ya zauna a America ya cigaba da playing bad boy role dinsa ni kuma a aura min munir ko kuma ya dawo yayi facing daddy ya karbi aurena. Ina fadin haka na katse wayar, ko minti daya ba'a yi ba ya kira, na katse kiran na kashe wayar gaba daya. Na san na kunna masa wuta. Dole ya dawo cikin sense dinsa yasan abinyi.
Ranar da yamma naje na samu mommy a dakin daddy tana gyara masa kaya. Na zauna a kusa da ita nace "Mommy wannan da kuke zance ke da yaya Walid rannan, sunansa Abbakar, dan garin Abuja ne, he is an architecture, iyayensa manyan mutane ne sosai a garin abuja. Ina son kiyi wa daddy maganar sa dan cikin satin nan na keso zaizo England ya gaishe da ku" mommy ta kalleni fuskarta kamar gonar auduga tace "kai Alhamdulillah, he is your final choice kenan ko?" Na gyada kai tace "Allah ya kawo shi lafiya" nace "Amin" har na mike sai kuma tace "Moon, kash, kinga har naso in manta, daddynku gobe zai yi tafiya, president ne ya tura shi wani summit a South Korea kuma zasu dan jima a can, dan yace ma maybe sai dai mu hadu a Nigeria tunda mu zamu tafi da wuri kinsan maganar bikin Nuraddeen ya tashi" na danyi jim ina jin babu dadi, dan da karfi na nazo so nake ayi wacce za'a yi a cikin satin nan a gama. Nace "OK, shikenan sa hadu da daddy a Nigeria, in yazo kawai sai ya gaishe ki ke" mommy tayi dariya, na tsaya ina kallonta dan ni banga abin dariya a cikin magana ta ba, tace "Moon kenan, ina kika taba ganin saurayi yazo ya gaishe da uwa?" Sai da ta fada sannan nima nayi dariyar abin, tace "kawai kice masa yayi zamansa a Nigeria za muzo mu same shi" nace "ai baya Nigeria yana America, dama munyi dashi ne zai biyo ta England sannan ya karasa Nigeria" mommy tace "babu wani abu ai, yazo kawai ku gaisa, in yaso sa hadu da daddyn ku a Nigeria" daga haka na koma part din mu ina lissafin ba haka naso ba ni kam. Amma Allah yasa jinkirin ya zamar mana alkhairi. Dan nasan ba karamin takaici zan sha ba a wajen bikin nuraddeen, a lokacin kowa zai san na gama makaranta.
Sai da daddare na kunna wayata. Messages ne suka fara rige rigen shigowa waya ta, nace a raina 'waya gaya maka barno gabas take ne da, dan kaga ina wani lallabaka shine zakake daga min kai. Na fara karantawa "shine kika kashe wayar ko?" "Please karki kuma mentioning wani munir or else.... I don't even know what I will do" "OK, i will come, pick me up in the airport tomorrow morning" nayi murmushi a raina nace 'na gano lagonka ai yanzu, kishi.
Amina ce ta shigo tanata kumbure2, nace "ke kuma ke da wa kike bata rai" tace "wai Nigeria zamu tafi bikin Nuraddeen, ni wallahi banson zuwa, ina zuwa gida yanzu zancen aure za'a fara yi min, duk an bi an saka min ido a gida kamar ni nafi kowa girma" dariya nayi sosai nace "that makes the two of us, at least ke ba'ayi miki mijin bama, ni yana nan an ajiye min dan haka bani da bakin cewa ai mijin ne bai zo ba" ta zauna a kusa dani tace "yanzu muyi shawara, ki lallaba mana mommy ta bar mu anan, sai mu zauna a gidan Hafsat su suyi tafiyarsu" na harare ta nace "you are joking, right? Mommy n ce zata tafi ta barmu a gidan Hafsat? Ai in mafarki kike ma yanzu ki farka" ta sake bata rai "to ni yanzu ya zanyi, ni ba samari nake yi ba kema kin sani, kuma ni gaskiya bana son a yi min auren family wallahi, ni nafi son in samu miji na da kaina wanda nake so shima kuma yake sona" murmushi nayi jin ta ambaci kalmar so, tace "this is not a laughing matter oo, ke ma fa ba son munir kike ba na sani" nace mata "wai waye yake maganar wani munir ne dan Allah? Akwai wanda zai zo kasar nan gobe, shine wanda zan aura, zan hada ku ku gaisa" tace "kina nufin baffa zai bari? Duk wannan zaman jiran naki da munir yayi?" Nace "matsalarsa ce kuma wannan, babu wanda ya matsa masa yace lallai sai ya jira, ni dai abinda na sani shine baffa yace in na gama karatu ban sami miji ba za'a hada ni da munir, to na samu, babu sauran maganar munir kuma".
Sai da nazo kwanciya bacci sannan na kira sultan, bugu daya ya dauka nace "na dauka kayi fushi ai" yayi ajjiyar zuciya yace "ni na isa? Bayan kinsa yau na wuni da waya a hannuna saboda ina tsoron kar in ajiye ki kira ban gani ba" daga nan na bashi labarin cewa ba zai samu ganin daddy ba sai nan da kamar 3-4 weeks a Abuja. Muka gama plan din zuwansa gobe, ban ankara ba kawai sai gani nayi har karfe biyun dare tayi muna ta hira ba tare da lura da time ba.
Washegari ya kira ni ya gaya min sun taso. Sai a lokacin naji gaba na yana faduwa, can I really face sultan? A wayar ma da yaya ballantana ido da ido. This is going to be very awkward. Nayi wa kaina alkawarin na daina munafuntar iyayena dan haka na tafi gurin mommy nace mata "Mommy Abdallah yau zai zo, kuma yace yana so inje in dauko shi a airport" tace "to shikenan ai babu wani abu, sai ki dauki driver ya kaiki. Allah ya sa albarka a ciki" nace "Ameen, nagode mommy" wannan shine abinda muka yi lacking da a relationship din mu, albarkar iyaye, ko da yaushe in iyayenka suna saka maka albarka to ba zaka taba tabewa ba. Na rasa inyi kwalliya ne ko kar inyi? Wanne kayan zan saka? Karshe dai na gayawa Amina nace dan Allah tazo ta rakani, ina ganin kamar in tare muke kunya ta sata yi sauki. Amina ce ta matsamin wai lallai sai nayi kwalliya, wai ai ba haka ake zuwa taryan saurayi ba, ita ta dauka wani sabon saurayi ne, bata san Sultan babu abinda bai sani nawa ba. 😂. Sai da na nemi Hijab din da yafi kowanne girma a cikin hijabai na sannan na saka. Tsaki Amina tayi tace "wallahi baki isa ba, koni da na girma a 'yalleman ba zan saka wannan hijab din inje gurin saurayi ba" ta dauko min gyale nima nace bata isa ba, a karshe dai wani hijab din na dauko wanda bai kai wancan girma ba na saka. Muka yiwa mommy sallama muka tafi. Karfe 12 jirgin su ya sauka. Ni dai tunda naji announcement na sunkuyar da kaina kasa. Can naji Amina tace "gashi nan ya taho" ban dago kaina ba nace mata "ya akayi kika san shine?" Tace "ko yadda yake kallonki ma ai dole a gane. Kai amma fa ya hadu, a ina kika samo shi? Dan Allah ki samo min irinsa nima". Sallamarsa ce ta hana ni karasa kai mata dukan da nayi niyya, ai babu shiri na juya baya na, ga mamaki na sai naji yana dariya, Amina ma ta biye masa suka yi tayi, yace "chafdi, kice akwai rigima kenan" Amina tace "ba karama ba kuwa, kaga kuma yadda ta zauna take ta koda min kai? Wai kyakykyawa, ga ilimi da hankali, shine ta dauko ni wai lallai sai nazo na ganka" dukan da nayi niyar yi mata dazu shina karasa yi mata yanzu, ta matsa daga kusa dani tana dariya, shi kuma ya matso har sai da naji dumin numfashinsa a jikina "please ki juyo mana in ga fuskarki, you have no idea how much I have missed you" ya ga bani da niyyar juyowa sai ya zagayo, ai muna hada ido nayi sauri na rufe fuskata da hannayena, nima kuma zuciya ta tana son ganin tasa fuskar daurewa kawai nake yi. Wayyo ni kam naga ta kaina. Dariya suke yi min sosai shida Amina. Lallai namiji bashi da kunya, wato shi ko a jikinsa ko? Da sauri nayi gaba na tafi gurin motoci, ina zuwa na shiga na zauna. Anan na samu damar kallonsa kafin su karaso, ya rame, ya tara gashi a fuskarsa but he still looks more handsome to me than duk mutanen da suke gurin. Suna tafiya shida Amina tana ta zuba masa zance, Allah ne kadai yasan yawan karerayin da take shirga masa. Suna karasowa ga mamaki na sai naga ya bude wa Amina gaba shi kuma ya shigo baya kusa dani. Ai kuwa na dunkule a guri daya kamar zan shige cikin kujerar, yana shigowa ya kalleni ya kyalkyale da dariya yace "Amina juyo kiga 'yar kauyen 'yalleman" tana juyowa tace "a'a wannan ai kauyancin ta ya wuce nan, maybe daga wata rugar da bamu sani ba ta taho" ni dai ina jin su bance komai ba. Can Sultan yace "kinsan Allah, ko ki ware daga wannan nannadewar da kikayi kamar macijiya ko kuma..... " sai kuma yayi shiru, na leko ta cikin hijab dina nace masa "ko kuma me?" Ya dauke kansa yace "zaki sani ne duk ranar da na kamaki" what? Me wannan mutumin yake nufi? Driver ne ya katse min tunani na yana tambayar ina zai kaimu. Nayi sauri nace masa "take us to the nearest saloon" Sultan ya kalleni yace "mai zakiyi a saloon kuma?" Nace "not me, you. You really need a haircut" yayi sauki ya shafa fuskarsa yace "damn" it is my turn to laugh now, dan haka nima na rama dariyar da yayi min, ya harare ni yace "how do I look?" Nace "terrible". Wani hadadden barbing saloon yayi wa driver kwatance, muka je ya shiga ciki ya bar mu a waje, nan Amina ta zagayo baya ta fara min barin hakora, "gaskiya gayen nan ya hadu, dan Allah dan ina ne?" Nace mata "Abuja" tace "gaskiya ni kam har yafi min kyau akan Zayed din Hafsat" nace "laa, wannan maganar kamar a kunnen Hafsat dan sai na gaya mata" yana fitowa naga ya koma sak Sultan dina, da murmushi a fuskarsa ya shigo yace "to yanzu fa?" Nace "like the Sultan I know" daga nan gidan Takawa inda Sultan yake sauka muka je, kiri2 yaki fita daga motar wai bai gama gani na ba. Sai da nace masa ina gayyatarsa dinner yau da daddare a gida sannan ya sauka. Muka tafi Amina tana ta santin sa, ni kuwa bata san haushi take bani ba. Dama saurin da muke dan mu samu muyi sallama da Daddy ne, muna zuwa kuwa muka tarar ana fito da kayansa, nan muka sake komawa airport muka rakashi, sai da ya bimu daya bayan daya yayi hugging din mu sannan ya tafi.
Muna komawa gida na gayawa mommy Abbakar zai zo dinner da daddare, nan ta fara yi min mitar ban iya girki ba "idan da ace kinyi spending koda quarter of time din da kika yi spending kina karatu a kitchen, da yanzu kin zama chef. Amma ke ba zaki yi girki ba. To yanzu ni kike so inyi masa abincin? Go to the kitchen jare, a haka zaki koya ai" na bata fuska nace "mommy idan kuma abincin bai yi dadi ba fa?" Tace "matsalarki ce kuma wannan" na kara shagwabe fuska "please mommy" tace "zan yi masa amma ba dan ke ba, dan shi" a raina nace "oho dai". Ana magrib Sultan yazo, wa yaga gandoki, anan masjid din embassy yayi sallah sannan ya kira woni. Yaya Walid tare suka tafi da Daddy, yaya Habeeb kuwa tun last week yana Nigeria, sune abokan nuraddeen ana ta shirin biki, dan haka a palon su na sauki Sultan, wata kyalliyar amina ta kuma zama tayi min tana yi tana cewa "irin wadannan samarin in baka kwalliya yanzu sai wata ta kwace maka shi" ni kuwa jinta nake yi kawai dan nasan mai kwatar sultan a hannuna sai ta shirya, kuma sultan ba kwalliya ta yake so ba, ni yake so. Already mommy ta aika an shirya wa Sultan dining din palon, dan haka ina shiryawa kawai can na wuce. Ina shiga palon na hangoshi dare2 akan dining yana serving kansa a raina nace 'oh Sultan da abinci, at least dai ai ka bari azo ayi maka bismillah ko' ina shiga ya dago yana kallona yace "bismillah, zo muci abinci" shi ko kwalliyar da Amina ta zauna ta tsara min ma bai gani ba, shi ta cikinsa yake yi. Na zauna a kan kujerar da take facing dinsa na rafka tagumi ina kallonsa yana lodawa cikinsa abinci, no wonder yake so energetic, lallai akwai aiki a gabana. Sai da cikin sa ya fara cika sannan ya dago yana kallona, sai kuma ya dan saki baki yace "menene wannan a saman idonki?" Nace "it's called an eye shadow" yace "menene amfaninsa?" Nace "kwalliya" ya saki baki yana kallona, yace "Amina ce tayi miki ko?" Na gyada kai nace "I look terrible, right" yayi dariya yace "no my love, you look beautiful, with or without make up, you are always beautiful" nace "thank you" suddenly na jefe shi da tambayar da take raina tun sanda muka dauko shi daga airport. "Sultan, me yasa kake shan giya" lemon da yake bakinsa ya fesar kan dining din saboda kwarewar da yayi, wanda yake hannunsa kuma ya zame ya zube a kasa, ya dago dara daran idansa yana kallona da mamaki, sam bai san na san da wannan side din nasa ba.
Episode Forty Nine : Ya Habeeb
"What?" Ya tambaya da mamaki, ban maimaita tambayata ba sai ruwa dana zuba a cup na mika masa, bai karba ba, na ajiye a gabansa. Ya sake tambayata "me kika ce?" Na kalle shi cikin ido nace "cewa nayi me yasa kake shan giya" ya bata rai sosai yace "who told you that?" Nayi shiru ban kalle shi ba, can yace "damn it, it's Steve, isn't it?" Nace "tun kafin muyi magana da Steve na sani" ruwan dana ajiye masa ya dauka ya shanye sannan ya mike ya bar dining area din ya koma cikin palon, nima na mike na bi bayansa, na zauna kujerar kusa dashi. Jin bashi da niyyar yin magana yasa na sake cewa "baka ce komai ba fa?" Ya juyo yana facing dina ya wani bata rai yace "can we please just drop this? I really don't want to talk about it now" nima na bata rai nace "why not? Sai bayan anyi bikin mu tukunna zamuyi maganar? Look Sultan da ace zan rabu dakai saboda kana shan giya da tuni na rabu da kai, amma ba wai hakan yana nufin nayi na'am da dabi'ar ba, ina dai saka ran cewa zaka daina. Nayi maka maganar ne yanzu saboda naga har mun fara maganar zuwanka gurin daddy dan haka ya kamata duk wani personal issues din mu muyi solving" na dan yi shiru ina studying dinsa, he looks really disturbed, ya saka duk kan hannayensa a cikin gashin sa, na cigaba "nasan kusan 70% na troubles dinka with the police are related to your drinking habit, saboda fadar annabi ne cewa ita giya itace shugabar dukkan alkaba'i, zata iya saka mutum yayi sata, zina, har ma kisan kai. Sultan zanyi tolerating komai akan ka amma banda drunk husband, what if one day ka dawo a buge kayi min duka?" Da sauri ya kalloni yace "I will never hurt you" nace "you can't be sure, duk sanda kasha u will lost control of yourself, maybe ma ba zaka gane koni wacece ba" alamun bacin raine karara a fuskarsa yace "please ki daina wannan maganar mana, wai what has come over you ne today? Ke fa baki san komai akan maganar nan ba kuma banyi niyyar ki sani ba har abada, yadda kika dauki abin sam ba haka yake ba. Amma na miki alkawarin one day zamuyi maganar but not today. You have no idea what I was going through kafin in hadu dake, and you also have no idea how much I have changed bayan na hadu dake" nace "na yarda, i don't understand and I may never understand. Ni yanzu dai please so nake kayi min alkawari guda daya. Promise me that you will never touch alcohol again" ya jingina da jikin kujerar ya zubo min idanuwansa, a hankali yace "I will do anything for you" na girgiza kaina nace "and that's where you are wrong a duk changes din da kake kokarin yi tunda muka hadu, you are trying to change for me, what I want is for you to change for YOU. Ka gyara ba dan ni ba sai dan kanka, dan ka gyara tsakaninka da ubangijin ka. Idan Allah ya duba niyyar ka yaga cewa dan shi kake komarin gyara rayuwarka sai ya taimaka maka, amma idan ya ga cewa danni kake kokarin gyarawa sai ya barka dani ko kuma ma ya hana ka ni din gaba daya" sai yanzu naga tension din fuskarsa ya ragu, a hankali ya fara murmushi idonsa a cikin nawa yace "thank you for loving me so much. I love you too. Na miki alkawarin one day zamu zauna zan baki labari akan my drinking habit, yadda na fara da struggles din da nayi akai" na lumshe idona inajin tausayinsa a raina, oh dear sultan, what other dark secret are you hiding?" Ya sake langwabar da kai gefe yace "please mu bar maganar nan haka, OK? Dan Allah kiyi min murmushi in ga dimples dinki mana" na rufe fuskata da hannayena ina jin kunyar kallon da yake min. Daga nan muka bar maganar muka koma plans na rayuwar mu, dan yanzu gaba dayan mu munyi shirin taryan koma menene zai faru. Sultan ya yanke shawarar ba zai gaya wa babansa ba saboda yasan ba zai shiga maganar ba. Ya yanke shawarar samun uncle din shi Galadima, amma first sai ya fara ganawa da daddy na. Ni kuma na yanke shawarar samun uncle Aliyu in yi masa bayanin komai akan sultan, na yanke wannan shawarar ne saboda sanin halin daddy na, he is too smart, idan nace shi zan yiwa bayani har sai ya tono abinda bai kamata ya sani ba. Sai after ten sannan Sultan ya tafi. Ina shiga gida na tarar da mommy da Amina jigum jigum a palo sun saka uban kaya a gabansu, na karasa nima ina kallon kayan, kayan da sultan ya lodo min a America ne, dama yace zai yi shipping dinsu nan, ashe ya riga ya turo su shine yanzu ya aiko dasu cikin gida ba tare daya gaya min ba. Na samu guri na zauna ina lissafin ta ina zan fara bayani. Mommy ta ce "shi Abbakar din naki ce masa akayi in za'a zo zance tare da kayan lefe ake tahowa?" Daga ni har Amina dariya muka yi, nace "mommy kayan lefe kuma?" Tace "to in ba lefe ba wadannan uban kayan na menene? Ki kirawo shi tun kafin yayi nisa kice ya dawo ya dauki kayansa. Kema kinsan in daddyn ku yana nan ko da wasa babu wanda zai shigo masa da wadannan kayan cikin gidansa" na lankwasar da kai nace "mommy tsaraba ce fa ya taho min da ita daga America. Kuma yanzu idan na mayar masa shi namiji yaya zai yi da kayan mata? Kuma ba'a nan kasar ya saya ba ballan tana ya mayar musu" ta kalle ni tace "wato tare kuka hada plan din ku kenan. Ke kika ce ya sayo miki kenan?" Nayi dariya nace "wallahi mommy bani na roke shi ba, kuma ni bansan ma ya aiko da kayan nan cikin gidan nan ba, ko gaya min bai yi ba" ta sake kallon kayan tace "to yanzu ya kike so ayi dasu?" Amina ce tayi zumbur tace "ni dai bara in fara zaban rabona" nan ta baje kayan tana zaba, nace da mommy "kinga yanzu na huta da siyan kayan tsaraba in zamu tafi Nigeria" dama mommy ta san halina na kyauta, duk sanda zamu je Nigeria sai na kusan yiwa account dina tas saboda kowa sai na sai masa wani abu, tun daga kan tsofaffi zuwa kan jarirai, Hafsat har mamaki take yi yadda akayi nasan kowa a familyn mu duk kuwa da cewa ba tare muke ba.
Tun daga ranar kullum anan gidan Sultan yake dinner kuma sosai muke kara shakuwa da juna ni dashi, ban taba tunanin cewa wani mutun zai iya yiwa wani irin son da muke yiwa juna ni da Sultan ba. Wani lokacin a gidan Hafsat muke haduwa amma sam yanzu na daina binshi yawo, ko zamu fita ma sai dai tare da Amina ko kuma da driver. A duk sanda muka hadu a gidan Hafsat in dai Zayed yana nan sai ya ta yiwa Sultan tambayoyi akan a ina yayi karatu kuma a ina yake aiki da dai sauransu. Ni har kunya nake ji tunda anyi tambayar nan ba sau daya ba ba sau biyu ba amma Sultan sam baya nuna damuwar sa sai dai yayi ta bashi amsa. Rannan dai bayan sultan ya fita sai Hafsat tace "Darling wai me yasa kake ta yiwa Sultan wadannan tambayoyin ne?" Zayed yace "wallahi na rasa dalili, kullum na ganshi sai inji tamkar na sanshi, kuma na rasa a inda na sanshi, sam babu wani guri da muka gadu dashi" Hafsat tace "kasan wadansu haka suke, kama ce kawai, maybe kasan wani mai kama dashi ne" Zayed ya girgiza kansa yace "I know him or someone that looks like him from somewhere, I just cant place my finger on it" .
Kwanci tashi har lokacin bikin nuraddeen yazo. Nan muka shirya inamu2 sai Nigeria, Sultan ya riga mu yin gaba saboda wani aiki daya taso masa. Kwana biyu muka yi a Abuja muka wuce 'yalleman. Abinda nake tunani kuwa shi ya faru dani dan kowa muka hadu sai ya tambaye ni "yaushe ne naku bikin?" Ni dai kawai da dariya nake bin su. Munir kuwa kamar jela haka yake bina duk inda nayi, mutane kuwa da sun ganmu sai suce "our next amarya da ango" ni kuwa haushi kamar ya kashe ni. Kuma wai duk da muna tare amma haka nake ganin sa a gurin 'yammata, da karya da akuya kowa ya gani indai da skirt a jikinta to sai ya bita, sai dai in ya ganni ya maze kamar bashi bane ba. Sultan kuwa rikice min yayi wai lallai sai ya taho gurin bikin, a cewarsa ai shikenan sai ya gaida duk uncles dina kuma 'yan'uwana ma duk sai su gan shi, da kyar na hana shi, kuma nasan abinda yake damunsa shine yasan dole muna tare da munir, sau da yawa in muna waya in yaji muryar namiji sai ya tambayeni "waye wannan?" Sultan akwai kishi, ni har tsoro yake bani, na hana shi bina 'yalleman saboda bana son haduwarsu da munir dan ba za'a kwashe da dadi ba, na fison sai naje gurin iyayena formally kafin su hadu. Masha Allah anyi biki lafiya an gama lafiya, nayi ta yiwa 'yan'uwa rabon kaya kamar yadda na saba, nuraddeen ya gina gidansa mai kyau anan 'yalleman din inda nan zasu zauna shida amaryarsa, muna zuwa ganin gida kuwa na saba da amaryar dan itama mai son mutane ce, nan muka yi exchange din number. Ana gama biki uncle Aliyu ya kira ni palon waje, ni nasan kwanan zancen kuma na shirya. Ina shiga na ganshi shida uncle Rufa'i na gaishe su na zauna a kasa. Uncle Aliyu yace "maimunatu kinsan dalilin kiranki da nayi?" Na gyada kaina. Yace "to ya muke ciki?" Nace "Uncle da akwai wani, ina son kusa masa rana yazo ya gaishe ku. Na so ya gaida daddy tun a England amma kuma basu hadu ba, insha Allah daddy yana dawowa zai je ya same shi sai kuma yazo gurin ku kuma" Uncle Rufa'i yace "madalla, Allah ya sanya alkhairi. In yazo mun ganshi kuma zamu saka ayi bincike a kansa. Kin tabbatar shi kike so" na sunkuyar da kaina bance komai ba, yace "to Alhamdulillah. Shi kuma munir ya kuke ciki dashi?" Nace "Uncle shi Munir ai na riga na gaya masa, shi ne dai yaki hakura har yau. Ni dai uncle wannan din dai..... " yace "wannan din dai shi kike so?" Nayi shiru. Uncle Aliyu yace "kar ki damu Maimunatu, babu wanda zai miki auren dole, maganar munir zamu san yadda zamuyi da ita yadda ba za ta bata zumunci ba. Shi wannan da kike magana akansa ya sunan sa? A ina yake? Dan waye shi?" Nace "sunansa Abbakar Sadiq, A abuja yake" na danyi shiru sannan nace "dan sarkin Abuja ne" uncle rufa'i yace " ah, kice da princess muke magana" na rufe fuskata ina dariya. Uncle Aliyu yace "ban san 'ya'ya nawa ke ga maimartaba ba, amma nasan akwai wani dan sa fitinanne. Whatever dai ki kai shi gurin yaya ambassador din in ya dawo, tunda shi ya fini sanin kan Abujan. Allah yayi miki albarka" nace "Ameen, nagode uncle" .
Bamu bar 'yalleman ba sai da su daddy da yaya Walid suka zo tukunna, kwanan su biyu sannan muka koma Abuja gaba daya. Ranar da muka koma a ranar Sultan ya zo. Duk gidan a hargitse yake saboda ana general cleaning da ake yi dan haka a mota naga Sultan. Ina shiga da sallama yace "look what you have done to me" na kalle shi sama da kasa nace "me nayi kuma?" Ya nuna min wuyansa, baki ga ramar da kika saka ni nayi ba" nayi dariya nace "ni banga wata rama da kayi ba Sultan, gashi nan kayi wani fresh da kai har da ajjiye tumbi" da sauri ya shafa cikinsa, ganin yana kokarin daga shirt dinsa nayi sauri na dauke kaina ina dariya, yace "please dan Allah tumbi nayi?" Nace "wasa nake maka fa" ya wani bata fuska "amma wannan ai mugun wasa ne, kinsan kuwa yadda bana son tumbi? Amma ke kinga yadda ki ka yi kiba kuwa? Dama ku fulanin nan haka kuke da wayo,sai ku tafi ruga kuje kuyi ta cin dadi,kuci kaji,kuci zabbi, kusha nono" nace "kuma muci kwai ba. Karka damu indai 'yalleman ce har sai ka gaji da zuwanta" daga nan muka koma hirar yaushe gamo, na bashi labarin yadda muka yi da uncle Aliyu, yace "daddy fa?" Nace "tare da shi muke yanzu, zan tunawa mommy ta gaya masa, sai ya baka rana ka zo" shi kuma ya bani labarin ya samu maigirma galadima da maganar, yaji dadi sosai kuma yace in dai ance ya turo iyayensa to yazo direct ya gaya masa, shi zai yi masa komai. It's like everything is falling in place, matsalata daya yadda zanyi convincing daddy ya karbi Sultan, amma shima na samu solution, project din da na rubuta akan sultan zan bashi, in yaki yadda kuma ince masa yayi bincike.
Da daddare na samu mommy na tuna mata maganar Sultan nace ta gayawa daddy, tace zata gaya masa amma yace mata gobe zai koma England, da akwai wadansu takardu da zai cike amma ba zai dade ba zai dawo. Naji babu dadi amma we are ready to wait. Washegari tunda na tashi nake jin zuciya ta babu dadi. Irin feeling din da mutun yake ji idan something is wrong, nayi ta tunani ko zan tuno wani abu da nayi ba dai dai ba amma na kasa tunawa, sultan na kira na tambaye shi if he is alright, kuma daga muryarsa na gane bashi da wata matsala, jin yadda nake jin babu dadi yasa yace zai zo da yamma. Yamma nayi na shirya cikin doguwar riga purple mai ratsin pink nayi rolling pink veil, ina gama shiryawa sultan ya kira ni yace yazo, part din su ya Walid na saka aka bude masa ya shiga sannan na fita, ina shiga palon na tarar dashi ya bude fridge ya dauko drink yana sha, na tsaya ina kallonsa nace "wannan wanne irin bako ne? Daga zuwa zai bude wa masu daki fridge" ya juyo ya kalleni dan bai san ma na shigo ba, yace "waye bakon? Ni a gidan nan ai sai dai in sauki wadansu" na shiga na zauna tare da gaishe shi, ya amsa sannan ya zauna akan center table din gurin yana kallona, yace "so... What's the problem?" Nace "I don't know, kawai dai ina jin ba dadi ne, I just want to confirm if you are alright" yayi murmushin nuna jin dadin sa yace "am OK, I really am. Maybe akan tafiyar daddy ne kike feeling bad, tunda ba dade wa zaiyi ba ai babu problem ko?" Na kirkiro murmushi nayi masa. Nan ya zauna yake ta bani labarai da zasu saka ni farin ciki, in no time kuwa sai gani na ware ina dariya sosai. Yana cikin bani labarin Amir yayi wata budurwa kanuri sai kawai ji muka yi an bude kofar palon, a tare muka dago kai muka kalli kofa, ya Habeeb ne a tsaye, yadda muke kallon sa shima haka yake kallon mu, Sultan ya mike da murmushi ya doshe shi yana mika masa hannu, kallo daya yayi masa ya wuce shi ya karaso inda nake zaune a daskare, ya nuna sultan ya hannu yace "Moon me wannan yake yi a gidan nan?" Na bude baki amma na kasa cewa komai ganin yadda kamannin yaya Habeeb suka juye "I asked you a question, me wannan yake yi a gidan nan" murya na rawa nace "gurina yazo" na kalli sultan naga mixed expression a fuskarsa, na sake mayar da kallona kan yaya Habeeb wanda har yanzu ni yake kallo, yace "amma ya muka yi dake, you told me he is not your type that you are just using him for your project, ko? Rasa amsar da zan bashi nayi, na sake kallon Sultan, he is getting angry, nace "yaya Habeeb please don't do this" yace "don't do what? Ke fa kika cemin da kin gama using dinshi for the project zakiyi masa kafa, that's exactly what you told me, kuma yanzu kin gama so banga dalilin da yasa zaki cigaba da ganin sa ba, i see no reason why you should waste his time any longer" yana fadin haka ya juya ya koma gaban sultan ya tsaya yace "look man, this should be the last time da zan ganka tare da kanwata, you are not her type, ita da kanta ta fada, she was just using you for her project kuma ta gama, so ala raka taki gona" gaba ki daya kamannin sultan sun chanza, idonsa ya rikide ya zama jajawur, bai ce da yaya Habeeb komai ba sai ya karaso inda nake, da sauri na mike tsaye nace "Sultan listen to me, abinda ya fada ba haka bane, you of all people know I love you" ya Habeeb yace "bullshit" wani irin juyi sultan yayi ya danki wuyan ya Habeeb yayi baya dashi ya hada shi da bango, a zabure na karasa gurin na fara kokarin kwace yaya Habeeb nan da nan hawaye suka fara zuba a idona, hawayen da Sultan ya gani a idona ne yasa ya saki Ya Habeeb shi kuma duk da shakar da yasha amma bakinsa bai mutu ba, yace "kai kana tunanin kowa mahaukaci ne irinka? Waye kake ganin zai dauki 'yarsa ya baka?" Ya juyo kaina yace "ke kuma ki sani, am going straight to mommy" daga haka ya juya ya fice.
Kujera na samu na zauna na rufe fuskata da hannayena ina kuka, ina jin Sultan ya kuma dawowa ya zauna akan center table din gaba na. Yace "Maimunatu me mutumin can yake cewa ne? Do you really told him cewa am not your type?" Na bude fuskata amma ban kalle shi cikin ido ba, ya sake cewa "what project was he talking about? Did you really write a project on me?" Nace "Sultan listen to me, duk yadda ka dauki maganar nan ba haka take ba... " ya katse ni "did you write a project on me? Yes or No" nace "yes, but... " da sauri ya mike yasa kafa ya daki kujerar kusa dani, nima na mike nace "Sultan ka saurare ni mana, I never meant to hurt you, ina taso in gaya maka ban san yadda zaka dauki maganar ba" ya juyo yana kallona, a hankali ya karaso inda nake tsaye, ya matso sosai har sai da ya hade goshin mu guri daya sannan cikin murya mai kama da rada yace "fuck you, and fuck your damn project" rintse idona kawai nayi hawaye yana zuba dan nasan babu abinda zan ce masa ya saurare ni. Ban bude idona ba sai da naji rufe kofar sa. Da sauri nabi bayan sa, kafin in fita daga palon har ya shiga motarsa ya tayar, a guje ya fincike ta dan Allah ne kadai ya taimaki mai gadin mu dan sauran kadan sultan yayi ciki dashi.
Episode Fifty : Munir 2
Nabi motar da kallo har ta fice, ji kaina nake a cushe cos babu wani tunanin da yake tafiyar min dai dai. Kamar daga sama naji kara mai kama da accident din mota a waje, ko ba'a gaya min ba na san Sultan ne, bansan lokacin da naje bakin gate ba kawai nima gani na nayi a gurin, motar Sultan na gani ta daki bishiyar da take opposite din gidan mu, ji nayi tamkar zuciya ta ta fado kasa, ina ganin masu gadi suna tafiya gurin amma ni ji nayi kamar an daskarar dani, ga mamaki na sai naji ya yi wa motar key yayi reverse da ita tare da tarwatsa mutanen da suka tafi kayo masa dauki, gaba daya gaban motar yayi damage amma a haka ya sake figarta ya yau titi. Yana tafiya masu gadi suka fara surutu, 'wai yaron nan me yake kawoshi unguwar nan ne kwanannan? Kar fa yazo ya tattaka mana yara a banza kuma babu mai daukan mataki a kansa" ni dai jiki a sanyaye na koma gida. Sai da na kama hannun kofar shiga palo sannan na tuno da ya Habeeb da kuma alkawarinsa na gaya wa mommy. Ga mamaki na sai naji babu wani tsoro a zuciya ta, gwara a yi ta ta kare kowa ma ya huta, dan ni yanzu ban damu da kome za'ayi min ba, nafi damuwa da halin da Sultan yake ciki, I fear he might hurt himself, ni kuwa nasan ba za'a taba yimin wani physical damage ba. Na murda kofar na shiga da sallama, babu kowa a palon sai ya Habeeb, fuskarsa sam babu rahama a cikin ta, kallo daya nayi masa nayi hanyar kitchen, haushinsa nake ji sosai duk da cewa deep down nasan ba laifin sa bane ba laifi nane, he was only trying to protect me. A kitchen na samu Asma'u, cook din gidan nace "Ma'u ina mommy?" Tace "Mommy taje unguwa, lokacin kina gurin bakon ki, tace in gaya miki sai dare zata dawo" banji dadi ba cos I don't want to delay this any longer. Na sake fito wa na wuce ta gaban yaya Habeeb na hau stairs din part dina. Direct balcony na wuce na saka kujera na zauna. Kamar yau ne na tsaya a gurin nan ina kallon Ibrahim ya fita daga gidan nan ruwan sama yana dukansa. Can't believe it has already been six years. History is repeating it self today. Amma yanzu a shirye nake, I am no longer sixteen years old, I am twenty two. Yanzu ba yarinyar nan bace da ta gama secondary school, wannan double degree ne da ita a second best university in the world. Ba wai zama zan yi in jira abubuwa suke faruwa ba kamar yadda na zauna nayi ta jiran Ibrahim, this time I am going to make things happen. Tashi nayi na koma daki na dauko laptop dina na kunna, email na shiga na rubuta wa daddy sako kamar haka "please daddy check this out" sai nayi masa attaching da duk rubuce2n da nayi akan sultan, na tura masa. Nayi missing Hafsat, da at least in na gaya mata zan dan samu sassaucin radadin da ziciya ta take yi. Na dauko wayata nayi dialing number din sultan, matar mtn ce ta fara yi min bayanin is switched off. Wani murmushin takai ci nayi, exactly haka nayi ta kiran Ibrahim is switched off, it is funny sometimes yadda rayuwa take zuwa wa mutum. Wani tunani ne ya fado min, this is my chance na ganin sultan in tabbatar masa da cewa abinda ya dauka ba haka bane, and most importantly to find out if he is Ok. Dan nasan mommy tana shigowa gidan nan suka hadu da yaya Habeeb to ni da in kara fita sai wani ikon Allahn kuma. Kuma nasan duk bayanin da zan mata ba zata fahimta ba da taji bayanin abbakar din da nake gaya mata Sultan ne shikenan zata toshe kunnuwanta daga dukkan baya ni na. Amma still it will be better in ni na fara gaya mata. Na dauko waya ta nayi dialing number ta, ta dauka suna ta hayaniya a gurin tace "Moon ya akayi ina gurin taro ne, akwai wani abu ne?" Nace "mommy akwai maganar da nake so muyi ne" tace "am very busy yanzu, can't it wait sai na dawo?" Nace "Ok mommy, sai kin dawo din" na ajiye wayar a raina nace "why is everyone not available when I needed them the most?" Ina daki har aka kira magrib ina ta kiran sultan har yanzu switched off, in ma nace zan fita neman sa bansan inda zan same shi ba, to ko gidan su zanje? Tunda gidan babba ne maybe har in fito babu wanda zai san na shiga? Amma fa ni ban taba shiga palace ba, in naje ma bansan inda zan dosa ba. Na tashi nayi alwala nayi sallah na zauna ina adduoi na naji karar wayata, ban dauka ba sai da na kammala, na dauka baga bakuwar number, ina kokarin dialing wani kiran ya sake shigowa, na daga da sallama. "Maimunatu Amir ne, kina ina?' Ji nayi gaba daya yawun bakina ya kafe nace "Amir ina Sultan?" Ya sake cewa "kina ina?" Nace "ina gida, me yake faruwa?" Ya danyi shiru sannan yace "ina gida dazu wani friend din mu ya kirani yake gayamin yaga Sultan a bar, he seems to be injured, to shine naje gurin na same shi, he is injured kuma yaki tashi in kaishi asibiti" da sauri nace "how bad is it?" Yace "not that bad, kawai dai kafarsa ce, kuma tana bleeding har yanzu. Sultan taurin kai ne dashi, ban sani ba ko ke in kika yi mishi magana zai tashi, he has been drinking also" a raina nace "nasan za'a rina, an saci zanin mahaukaciya" ya katse min tunani na da cewa "can you come, please?" Na ce "of cause I will come. Kuna ina?" Yayi min kwatance, nace amma kuma fa ban iya driving ba, bana so kuma in dau driver, ko kuma zuwa zakayi ka dauke ni?" Yace "alright gani nan zuwa" tashi nayi da sauri na chanja kaya zuwa wani material simple doguwar riga, nayi rolling veil sai kuma na saka dogon jihab, na sauka kasa, yaya Habeeb ya tashi daga inda yake dazu ina jin masallaci ya tafi, na samu Asma'u tana shirya dining nace mata "Ma'u kinga kaina ne yake ciwo, na sha magani yanzu zan kwanta, please in mommy ta dawo ki gaya mata ina kwance banjin dadi" da sauri tazo ta dafa goshina, "oh oh, sannu mai sunan daada, gashi nan kuwa jikin ki ya fara zafi, Allah ya sawake" nace "Ameen" na koma kamar na hau sama sai nabi ta kofar baya na fita, ina fita Amir ya kirawo ni yace gashi ya zo, na zagaya ina buda securities, dama in daddy baya nan basu da yawa, guda biyu kawai na hango tare da baba Habu a can gefe a zaune, sai da na zagaya ta side din da ba zasu ganni ba sannan na shige seat din baya na durkusa a kasa yadda wanda yake waje in dai ba lekowa yayi ba ba zai ganni ba. Ina jin baba Habu yana tambayar Amir "har ka karbi sakon?" Shi kuma yace masa eh sannan muka fita. Sai da muka hau titi sannan na zauna sosai ina tambayar Amir "ya jikin Sultan" ya yi murmushi mai sauti yace "He is lucky to have you. Da sauki jikinsa, so nake kawai ya tashi in kaishi ayi dressing kafar kar ciwon ya zama infected kuma a tsayar da jinin" nayi shiru ina lissafi, wannan fitar da nayi ni kaina nasan I am playing a very dangerous game, saboda na bawa mommy damar yadda da duk abinda za'a gaya mata, amma kuma bazan iya barin Sultan ba alhalin yana bukata ta. Wani hotel muka shiga, sannan muka bi ta bayan building din muka tsaya a wani karamin packing space. Ga wanda bai san gurin ba zai dauka babu komai a gurin, amma sai naga mun doshi wata kofa, Amir yayi knocking wani ya leko ya kare mana kallo sannan ya bude muka shiga, wani dogon corridor muka bi muka sake shiga wata kofar sai gamu a wani katon guri. Ga mutane nan birjik kowa yana abinda yaga dama, kowa ka gani da kwalba da cup a hannunsa, wasu da 'yammata wasu kuma su kadai. Fitulun gurin duk dim ne marasa haske. Oh ni maimunatu wai yau nice a gidan giya? Lallai soyayya babu abinda bata sakawa.
Tun kafin mu karasa inda yake na gane shi duk kuwa da juya bayansa da yayi yana kallon bango, light blue din wandonsa yayi staining da jini, a hankali na karasa na jawo kujerar kusa dashi na zauna. Da sauri ya juyo ya kalleni sai kuma ya dauki kofin gabansa ya shanye abinda yake ciki sannan yace a hankali "damn you Amir" ya janyo kwalbar da take gefensa ya sake cika kofinsa sannan yace ba tare da ya kalleni ba "what are you doing here, this is no place for a girl like you" nace "it is also no place for someone like you, dan kai nazo kuma na tabbatar ba zaka bari wani abu ya same ni ba" murmushi yayi me kama dana takaici sannan yace "what do you want?" Nace "first ina so in gaya maka cewa I love you, all of you, sannan na biyu ina so in gaya maka cewa wannan mutumin da yake zaune a gaba na yana shan alcohol is not sultan, it is what you think you are but it is not who you really are" yace "ta ya akayi kika sani? Kinfi ni sanin kaina ne? This is what I am, this is what I have always been" na girgiza kaina nace "no, ba haka bane, wannan shine abinda mutane suka saka ka mayar da kanka" ya danyi shiru sannan ya sake daga kofin gabansa yayi masa kurba daya yana yamutsa fuska. He looks calm, so peaceful, fuskarsa sam babu damuwa, muryarsa kuma a nutse yake magana. Sai da ya ajiye cup din sannan yace "kin san wani abu?, ranar da muka hadu dake na dauki alkawarin bazan taba barin kisan ina shan giya ba, ballantana har ki ganni ina sha" ya daga kafada yace "I was a fool, ban taba wishing for something na samu ba amma na saka ran cewa zan samu wannan wish din. Now here we are" na hadiye wani abu da ya tsaya min a makogwaro nace "wannan bai chanza komai ba a tsakanin mu, kamar yadda nake so abinda ya faru dazu kar ya kasance ya chanza wani abu a gurinka" ya juyo yana kallon cikin idona yace "idan da akwai wani abu da nake da tabbas dinsa a rayuwa shine I will love you, till my dying day. Amma nasan you are just another dream a gurina, and my dreams never come true" nace "wannan mafarkin zai tabbata Sultan, I will fight for us, amma ina bukatar kaima kayi fighting for us. Abinda zaka fara yanzu shine ka ajiye kwalbar hannunka, ka tashi muje a duba kafarka" bai ajiye dinba kuma bai tashin ba, har zan sake magana sai yace "me yasa baki gaya min zancen project dinki ba?" Na sunkuyar da kaina kasa na fara magana "lokacin da aka bani project din ban sanka ba, daga baya muka hadu dakai, ranar da ka fara kaini gidan su Amira muka biya ta wata unguwa har na samu labarin orphanages din da ka gina kuma kake running da kuma irin taimakon da kake wa marasa hali sai naga kafi fitting topic dina, a lokacin na fara rubutu na, I was already in love with you then, nayi tunanin yin rubutun akanka zai sa in kara fahimtar ka sosai, I never meant to hurt you. Ina ta so in gaya maka kullum but ina tsoron yadda zaka dauki abin. You are not an easy person, you easily lost your temper" ya dakatar dani yace "have I ever loose my temper with you?" Na girgiza kaina dan ko mugun kallo Sultan bai taba yi min ba. Na cigaba "tun ranar dinner din Hafsat da ka je Ya Habeeb ya gan mu tare yayi min warning kar ya sake gani na da kai, a lokacin nace masa 'u are not my type' saboda ni kaina a lokacin bansan zan so ka ba saboda a lokacin ban sanka ba. A England ma ya sake ganin mu a Oxford, he threatened me cewa zai gaya wa mommy kuma nasan in har ya gayawa mommy ba za'a barni in sake ganin ka ba. Na ce masa 'I was using you for my project' ne saboda in kara samar mana lokaci together" sai kuma na kasa ci gaba da maganar na rufe fuskata da hannuna ina hawaye sanin lokacin da na samar mana ya kare yau, dan maybe already mommy ta koma gida by now, maybe already sunyi magana da yaya Habeeb. Bai rarrashe ni ba sai ya sake kiran bartender ya karo masa wata kwalbar, yana ajiyewa na dauke na ture ta gefe nace "please Sultan me kake son yi ne? So kake ka kashe kanka?" Idanunsa sunyi jajur, amma abin mamaki banda jan idon babu wani abu da zai nuna maka cewa a buge yake, he seems totally in control of himself. Bai karba ba ya kara zama yace "rannan na miki alkawarin zan baki labarin yadda na far shan giya" ban amsa ba shima bai jira amsa ta ba ya cigaba da magana "ina da shekara goma kakana ya rasu, bayan an yi nadin sarauta babana, Hajiya da sauran siblings dina suka dawo palace, su kuma su yaya da sauran matan kakana sai akayi musu sababbin gini a bayan palace din suka koma can. Ina jin labarin tarewa a sabon waje na fara tattara kayana nima saboda nayi zaton dani za'a tafi, tunda dasu yaya na saba, ban saba da Hajiya da su Abbas ba. Amma ranar tarewa tana zuwa sai akace ban dani, wai Hajiya tace a barni saboda in saba da 'yan'uwana, nan na dasa rigima lallai ni ba zan zauna dasu ba. Sai da Yaya ta kirani ta zaunar dani tayi min bayanin cewa an ce in zauna ne saboda in saba da babana nima yake kula ni kamar yadda nake so, ina jin haka na fara murna nima zanyi family. Sai daga baya na fahimci ba haka bane, ba wai rashin sabo ne ya saka baya kulani ba a'a ni din ne baya so. Gaisuwata da safe baya amsawa, baya cin abinci dani kamar yadda yake ci da abbas, ko dariya yake dana zo gurin zai bata rai. A lokacin abinda ya fi komai bata min rai shine, kullum in zaije fada zai saka a shirya Abbas, a saka masa manyan kaya da rawani da alkyabba, su tafi tare, amma ni bai taba ko tunani zuwa dani ba. Kullum in aka dauki abbas aka barni sai na hargitsa gidan nan dan bacin rai, in farfasa glasses din windows da duk abinda tsaho na zai kai, next thing duka ne zai biyo baya, ko kuma a sakani a daki a kulle ni. In nayi buge2na na gaji sai in zauna in hada kai da gwuiwa inyi ta kuka, I am four years older than Abbas, ni a gani na ni ya kamata baban mu ya kai fada ba Abbas ba, duk sanda aka saka mishi kayan sai inyi ta sha'awa dan nawa wanda nake sakawa sanda kakana yana da rai ma duk Hajiya ta karbe ta bashi tace min sunyi min kadan za'a sayo min sababbi, har yau ba'a sayo min ba. Wata rana ina ta gursheken kukana Hajiya ta aiko akayi kirana dakinta, cikin bedroom dinta, ta tambaye ni tace in gaya mata me nake so, nace mata inaso babana ya soni kamar yadda yake son Abbas, tace min to zata bani maganin da zan ke sha wanda zai saka ya soni fiye da Abbas din ma. Ta dauko shi a kwanba ta zuba min a kofi tace in sha, na dauka da murna ta na shanye, babu dadi amma haka nasha saboda ina son Takawa ya soni, banji dadin taste din ba amma naji dadin feeling din da ya saka naji, zuciya ta naji tayi min dadi, babu bakin ciki ko bacin rai sam, sai wani nishadi da nake ji, I felt very calm and happy. Tun daga nan kullum sai ta aiko naje nasha, ni kuma ina jin dadin yadda nake ji in nasha din, daga baya ma sai ya zama ni nake zuwa da kaina in raina ya baci ince ta bani magani insha, tace min inyi mata alkawarin ba zan gayawa kowa ba ni kuma nayi mata. A hankali na fara zama less active, kullum sai bacci ko kuma in zauna inyi ta kallo ko tv game, wanda da ba halina bane cos I was very energetic child, Amir ne ya fara lura sai ya gayawa Hajiya yace akaini asibiti fa, bani da lafiya tace masa to amma yaga shiru ba'a kainin ba, hakan yasa ya shirya ya tafi gurin yaya ya gaya mata cewa bani da lafiya kuma anki kaini asibiti, babu shiri yaya ta taho cikin gida tazo ta tarar dani ina bacci, jikina babu zazzabi amma nayi weak babu karfin da ta sanni dashi da. Nan ta samu hajiya ta tambaye ta sai tace ai na samu kulawa ne da tarbiyya shi yasa na nutsu, ita kam yaya bata yadda ba saboda tasan yaro mai fitina daban yake da yaro quite, I was never quite and calm dan haka lokaci daya ba zan zama ba. Ta daukeni ta tafi dani gurinsu da sunan zanyi week end acan, kwana na daya na rikice musu suka rasa kaina, daga baya dai nace ni aje gurin Hajiya a karbo min magani na, nan yaya ta saka ni a gaba da tambayar wanne irin magani har dai na gaya mata. I was young then, ba zan iya tuna duk abubuwan da suka faru ba amma dai nasan an yi rigima sosai da yaya, ni dai rigima ta daya ce, a bani magani na. Hajiya ta daina bani, but I was already addicted to it. Ita kadai take calming dina down duk sanda nake tantrums dina. It still does. Duk sanda raina ya baci ita nake sha inji zuciya ta tayi sanyi. Ba abinda rannan kike cewa bane rannan, it doesn't make me do things, it calm me down and stop me from doing things. A lagos kuma su masu kula da mu su nake bribing su kawo min, wani lokacin ma da kansu suke bani saboda in nayi bacci shikenan sun huta da fitina ta. Sanda aka kaini America kuwa tamkar an bani ticket ne, hankali na kwance babu me cemin kar inyi. Sai da na shiga university sannan na fahimci tana hanani karatu, ni kuma a lokacin ina son karatu saboda in faranta ran babana. A lokacin na fara ragewa dan kaina, ya zama bana sha sai in na zama really frustrated yadda ba zan iya controlling anger dina ba. Bayan na hadi dake kuma I cut it down to zero, saboda in raina ya baci da munyi waya dake zan manta da bakin ciki na, I returned to it sanda muka rabu a America but tunda muka dawo ban kuma sha ba sai yau." yayi shiru yana kallon cup din hannunsa kamar mai studying dinsa.
Na saka hannayena na juyo da fuskarsa gurina, still ban cika fuskar ba nace "alcohol doesn't give you calmness sultan, it makes you think it gives you calmness. Haka giya take, shi yasa take addiction ce, zata baka feeling din da kake so saboda ka cigaba da shan ta. Do you believe in destiny Sultan?" Bai bani amsa ba kallona kawai yake yi, nace "I know you do, I strongly believe that we are destined to be together. Zayed ya taba gaya min wata magana rannan wacce kuma na yarda da ita, yace people with good heart da suke suffering a rayuwa are destined for greatness, suffering din da suke yi is like a test da Allah yake musu dan yaga how good they are. Sultan I strongly believe that you are destined for something great" kallona kawai yake yi da jajayen idonsa, amsar daya bani itace "can I kiss you now?" a raina nace 'he is really drunk' a fili nace "no" ya daga kafada yace "OK" sai ya kifa kansa akan table din gabansa. It is time for me to get him out of here, na tabbata mommy ta dawo yanzu, hope dina kawai in taji bani da lafiya maybe ta bar maganar sai safe. Na fara waige waigen Amir wanda sai yanzu na tuna dashi, babu shi babu alamar sa, na bar waya ta a gida ballantana in kira shi, ina Amir when I need him the most? Na tambayi Sultan "ina wayarka?" Idonsa a rufe yace min "Amir" haka ne da ita muka yi waya da Amir. Nace "Sultan tashi mu tafi, am getting you out of here" ya dago kansa idonsa sun kara ja yace "can't stand" tashin hankali, ta yaya zan iya daga sultan, I really need to go back home kuma ba zan iya tafiya in bar sultan a haka ba. Dole somehow in fita dashi waje, fresh air zata danyi clearing head dinsa, daga nan sai in samar masa taxi a kaishi gida, nima kuma in nemi taxi zuwa gida. Na saka hannu a aljihunsa na dauko kudi, roll ne na 1000 notes, na dau guda biyu na mayar masa da sauran. "Sultan try standing up please" ya gwada, nasan kafarsa tayi tsami yanzu, da kyar ya dafa table din ya mike yana cije lebe, yanzu saura tafiya kuma, na a side din kafarsa mai ciwon na ce masa ya dafani mu tafi. Sai da muka fara tafiya sannan nayi nadama, he is very heavy, gashi duk ya sakar min jiki kaman ma naya sane. Sai na muka huta sau bixu kafin mu zo gate. Muna fita gate din na fara rarraba idon inda zanga taxi, nace "Sultan zan saka ka a taxi za'a kaika gida, inna je gida zan kira Amir in gaya masa ya kira doctor ya duba kafar ka sosai. Ana barin taxi ta shiga palace?" Uhmm kawai yace, good, tunda yana gane me nake cewa.
Wata mota ce ta wuce mu har na fara daga hannu sai na lura ba taxi bace na sauke hannuna. Har tayi gaba sai tayo baya kuma, good, maybe it's Amir, tayi packing a gaban mu aka bude kofar da sauri aka fito. "Moon? Is that you?" Na saki baki ina kallon me maganar, Munir. Na kasa rufe baki na ballantana in yi magana. Ya karaso gaban mu, da sauri ya toshe hancinsa. "Moon waye wannan? Me kike yi a gurin nan da daddaren nan? Are u drunk?" Tambayoyin da ya jero min kenan. Sai a lokacin na fahimci what we looked like, kusan rabin sultan a jiki na yake, gaba dayansa warin giya yake dan haka nima warin nake, yadda muke tafiya kuma babu wanda zai ce ba'a buge muke ba gaba dayan mu. A hankali nace "listen Munir, this is not what you are thinking" Sultan naji daga gefena yace "Munir? "
Episode Fifty one : Mommy
Nayi kokarin raba jikina dana Sultan wanda da kyar ya tsaya. Munir ya kara matsowa yana kare mana kallo, dogon hijab dina duk ya chukuikuye yayi squeezing yace "dama abinda kike aikata wa kenan shi yasa ko waya nayi miki ba kya dauka, haka ne fa ya saka na shirya na taho abujan da kaina dan inga me yake faruwa. Ashe abinda kike aikatawa kenan har ake yi min gorin baza 'a bani ke ba dan kin fini tarbiyya? Ina tarbiyyar take anan? I wish uncle Aliyu zai ganki a yanzu sai ya gane tsakani na dake wa ye marar tarbiyyar" da kyar na bude baki nace "Munir kar ka adar da batun da baka tabbatar ba, I was only trying to help him, shi kenan taimako kuma sai ya zama laifi?" Yace "waye shi? Menene tsakanin ki da shi?" Nace a fusace "what is your problem with that?" Sultan ne naji yace "I am her husband to be, ko kana da abinda zaka yi akai?" Wata harara Munir ya watsa masa yace "da masu hankali nake magana ba da bugaggu ba" da sauri Sultan ya yunkura zai kai masa duka nayi sauri na rike shi, nasan a yadda sultan yake a yanzu Munir duka zai yi masa dan gaba daya alcohol din ta zuke karfin sultan. A fusace Munir yace "cikashi kizo mu tafi" nace "am not leaving him here" da mamaki kawai ya tsaya yana kallona yama rasa me zai ce min. Wata taxi ce ta tsaya a gaban mu Amir ya fito da sauri ya karaso in da muke, yace "Moon ya akayi kuka fito nan, what if someone sees you?" Sai kuma ya juya ya kalli munir yace "waye wannan kuma?" Takaici bai barni na bashi amsa ba, nace "ina ka tafi? Dare yayi sosai, I needed to go home, ba zan iya tafiya in bar shi ba, babu wanda na sani a ciki ballan tana in nemi taimako, ina ka tafi?" Kamar zaiyi kuka yace "am so sorry Moon, na dauki motar da Sultan yayi accident da ita niyya ta in kaita gida sai in dawo in dauke shi a mota ta, na hadu da police a hanya sunga damage din da motar tayi suka tare ni suna ta yimin tambayoyi, sai da naje station nayi cike cike sannan suka barni na tafi, I thought zaki kira ni a waya ma, dan Allah kiyi hakuri" nace masa "ai babu waya a hannuna, wayar sultan kuma tana hannunka" ya kuma kallon munir da har yanzu yake tsaye yana sauraren mu yace "waye shi?" Da takaici nace "shine wanda akayi alkawarin za'a aura min a gida" Amir ya dora hannunsa aka yace "ya Salam, am so sorry Moon" Munir yace "are you guys done? Saboda na matsu muje gida inji bayanin da zaki yi musu" nace "ni ba zan shiga motar kaba, ai ba tare muka zo ba, kayi tafiyarka kawai" wani murmushin mugunta yayi sannan ya dauko wayarsa ya fara dannawa yace "in ba zaki shiga mota taba, bara in kira wanda dole ki shiga tasa" kafin inyi wani yunkuri naji yana cewa "Hello Walid kana ina? Guess wa na gani yanzu? Moon. Au dama nemanta kume yi? a buge na ganta a hannun wani gardi suna ta marisa a gefen titi. To shikenan in baka yarda ba kazo ka gani da idonka." Daga nan ya fada masa inda muke ya kashe wayar. Har yanzu murmushin nake yace min "mu zuba ni da ke mu gani, lets see idan gobe ba'a daura mana aure ba" Kaina naji yana wani irin juyawa, idona har wani dishi dishi nake gani. Wata zuciyar tace min in kwashi takalma na a hannuna in fita a guje, wata kuma tace min in dauki halin Sultan in rufe Munir da duka. Na juya na kalli Sultan idona cike da kwalla, daga ganin sa kasan zuciyarsa tafasa kawai take yi amma babu karfin yin wani abu akai, a raina nace 'daga yau zaka fara fahimtar illar shan giya'. Amir kam gaba daya hankalinsa ya tashi, da sauri sauri ya wuce ya shiga cikin hotel din can sai gashi ya dawo da motar sa. Ya bude kofa yazo zai kama Sultan amma sultan ya tubure yaki tafiya, nace "Sultan ku tafi gida kafin yaya walid yazo ya same ku" na juya gurin Amir nace "Amir ka kira doctor din palace sai ku hadu dashi a can ayi dressing kafar" Sultan ya rike hannuna yace cikin gaskararriyar murya "I am not leaving you here, gurin nan bashi da kyau, and am not leaving you tare da wannan mutumin" na rike hannunsa nima, a raina ina jin tamkar wannan shine gani na karshe da zan yi masa a rayuwata. Sam babu kwalla a idona nace "Sultan kayi min alkawarin ko ina nan ko bana nan wannan itace rana ta karshe da zaka kuma shan giya, kayi min alkawarin duk sanda ranka ya baci zaka rungumi alqur'ani not alcohol. Sultan please promise me that you will fight for us, bawai fada zaka yi ba, show people your true self wannan shi kadai zai saka a baka ni. Please sultan, ka manta da zancen destroying family name dinka, koda ba za kayi dan kanka ba, do it for me and for our unborn children, tunda in dai na aureka shi family name din naka shi ne dai sunan da zamu yi bearing ni da 'ya'yan mu" ya saki hannuna daya ya jawo ni jikinsa, ina jin yadda zuciyarsa take bugawa da karfi a kirjinsa, a kunne na ya rada min "please don't leave me, let's runaway together, let's go back to America" nayi kokarin kwace jikina ya kara rikeni "please, I can't live without you" na zame jikina ina girgiza kaina nace "no Sultan, guduwa ba shine solution ba, solution shine mu samu albarkar iyayen mu, in muka gudu ba zamu taba ganin dai dai ba a rayuwar mu" duk da irin son da nake wa Sultan, bazan taba iya guduwa daga gurin iyayena ba, duk da nasan irin abinda yake jira na a gida amma nasan abinda zan fuskanta inna gudu sai yafi wannan, ni ina ji a jikina cewa fitowar da nayi ba tare da sanin iyayena ba shi ya zawo komai ya kara chakude min. A ganina worse abu da 'ya zata yiwa iyayenta shine ta gudu ta barsu, duk duniya babu wanda yake son ki ko kuma wanda zai soki sama dasu, in kika gudu kika bar su kullum zasu zamo cikin tashin hankalin rashin sanin halin da kike ciki, wannan tashin hankalin nasu kuma ba karamin bala'i bane a gurin ki.
Tun daga nesa na hango motar ya Walid ta shigo layin, Sultan ya kara rikon da yayi wa hannu na, na kalli Amir nace "take care of him please". Yana zuwa yayi packing ya fito yana bin mu da kallo daya bayan daya, idonsa ya sauka akan hannayen mu ni da sultan. Munir ya karasa gurinsa yana cewa "kaga ni ko? Yanzu ka yarda da abinda na gaya maka? A rungume take a jikinsa ma ganin ka ne ya saka ya sake ta" ya Walid bai ce masa komai ba ya karaso in da muke tsaye ni da sultan, kallo daya yayi wa Sultan ya dawo da kallonsa kaina, muna hada ido na sauke kaina kasa amma na kasa cika hannun Sultan. Wani wawan marin da ban taba tsammanin ya Walid zai min ba shi ya sakar min, sai da na dena gani for some seconds, taste din jini naji a bakina, ina dago kaina naga ya sake daga hannu zai kara min wani, na runtse idona ina jiran saukar marin, wannan karon nasan completely zan karasa makancewa. Jin marin bai karaso ba yasa na bude idona dan ganin abinda ya tare shi. Hannun Sultan na gani rike da na yaya Walid, ba zan iya kwatanta expression din fuskar saba, murya can cikin makogwaro yace "don't you dare hit her again" da dayan hannun ya Walid ya wanka wa Sultan shima na shi rabon, daga ganin marin nasan yafi nawa karfi dan sai da sultan yayi baya kamar zai fadi Amir ya rike shi, sannan yaya Walid ya nuna shi da hannunsa yace "an dake ta din, me zakayi akai?" A raina nace 'ayyah ya Walid, dan dai Sultan ba dai dai yake ba da yau sai ka kwanta a asibiti' ban dawo daga tunani na ba naji ya Walid ya damki gashina ta cikin hijab daga baya ya fara jana, wata azaba naji tamkar zan saki fitsari a wando, a haka ya jani har mota, inajin Sultan yana kwalla min kira amma zafin rikon da ya Walid yayi min ya hanani magana, kafin mu karasa mota Munir ya bude kofar baya, ya Walid ya watsa ni ciki tamkar kayan wanki ya mayar da kofa ya rufe, ina jinsa ya tada motar ya ja muka tafi. Sam babu hawaye a idona sai fuskata data kumbura side daya. Muna tafiya wayarsa tayi kara ya dauka yace "Hello mommy gamu nan mun taho, she is OK but sai munzo dai" Ina jinsa yayi horn aka bude mana gate muka shiga gida, yana packing ya zagayo ya bude kofar baya ya ya fito dani, he half drag me zuwa palo, muna shiga ya watsar dani flat a tsakiyar palon. Ban dago kaina ba ballanta na in san suwaye a palon. Muryar mommy naji tana magana a nutse tace "ka gayawa daddyn ku?" Ya Walid yace "a'a, naga yanzu a can cikin dare ne shi yasa na bari sai da safe tukun na" mommy tace "ka barshi, ni zan gaya masa" yace "Ok mommy" yadda take maganar a nutse ne ya bani mamaki sabida nayi zaton kafin muzo zan tarar ta hargitsa gidan gaba daya. Na dago kaina ina kare musu kallo, mommy tana tsaye a tsakiyar palon ta rungume hannayenta, daga can gefe daada a kan kujera tana ta sharbanen majina, Ya walid yana tsaye shima a kusa da mommy, ya Habeeb yana zaune daga bayana. Mommy ta kura min ido tana kallona sannan tace "kai ka dake ta ne?" Ya Walid yace "eh" sannan tace "Habibi kira David kace asa muna bukatar karin securities a gidan nan, kace masa nace munyi receiving threats, duk wanda suka ga zai hauro mana su harbe shi" wata muguwar faduwa gaba na yayi, na mike zaune daga kwancen da nake. Ta cigaba da magana tana zagaya palon, tace "ina da labarai da yawa akan yaron nan, he is capable of doing anything, nasan zai iya yayi attempting shigowa ya dauke ta. Yazo har gida ya dakar min da, sannan ya dawo yayi kidnapping yarinya ta, in ya sake dawowa for the third time ina da right din da zan saka a harbeshi in self defense" cikin rawar murya nace "mommy he did not kidnap me" marin da dazu yaya Walid bai karasa min ba shi yayi min yanzu, wannan karon kunnena ne naji ya dena ji, sanda na dawo hayyacina a kwance na ganni again. Daada ta kara sautin kukanta kamar ita aka mara. Sama sama naji mommy tana yiwa ya Walid fadan kar ya sake dukana, tace "duka is not a solution to kangararrun yara" kalmar kangararruce ta tsaya min a raina, wato nima yanzu na shiga layin kangararru kenan. Na kuma tashi na zauna ina jinsu suna ta plans na security, a raina nace 'indai sultan yayi niyyar shigowa gidan nan sai ya shigo, but I don't think he is coming, not today' Mommy ta kalleni tace "tashi ki tafi daki" na mike sum sum2 nayi hanyar stairs sai kuma tace "ah ah ah, bani wayoyinki" na nuna mata hannayena nace "ban fita dasu ba dama" tace "Habeeb bita ta baka ka kawo min, manyan wayoyinta guda biyu da karamar Nokia, da laptops dinta biyu, ta hado maka da ATM cards dinta guda biyu suma. Kayi locking kofar balcony dinta sannan in ka fito ka rufe kofar dakin daga waje ka taho min da keys din" mommy is surely harder than steel, tun ina yarinya nasan she is thorough a duk al'amuranta. Muna shiga daki na bawa yaya Habeeb duk abinda mommy tace, bai ce min komai ba ya rufe kofar balcony ya zare key din, ko kallo na baiyi ba ya kwashi kayan ya fita sannan yayi locking kofar daga waje.
A gaban gado na durkushe fuskata tana min radadin marin da nasha. Na kusa kaina a tsakanin kafafu wana ina neman kuka amma yaki zuwa. Wani zafi nake yi a kirjina. Kamar yadda na saba duk sanda nake jin irin wannan yanayin sai na fara kiran sunayen Allah 99 a fili amma a hankali, kafin in kai karshe naji raina ya danyi sanyi. Hijab din jikina wanda gaba daya warin giya yake na cire na shiga toilet nayo alwala nazo na yi sallar isha sannan na dauko alqurani na na fara karantawa a hankali, wata nutsuwa ce take shigata a hankali, kamar some kind of assurance cewa everything is going to be alright. Sai da naji muryata ta fara dashewa sannan na rufe alqur'anin na kwanta a kusa dashi, na ki barin zuciyata tayi tunanin sultan saboda kaina ba zai iya dauka ba. A hankali bacci ya fara daukana. Ana kiran assuba na tashi na fara kawo nafiloli sannan da akayi assalatu nayi sallar assuba amma da nazo yin addu'ah sai na rasa me zance, what if Sultan ba shine alkhairi a gare ni ba, ko kuma nima ba nice alkhairi a gare shi ba? Dan haka kawai sai na yi addu'ar Allah ya bamu ikon cin dukkanin jarabawar da zai yi mana, ya bamu karfin zuciyar daukan ko menene zai taho mana kuma ya zaba mana mafi alkhairi a duniya da kuma lahira.
Da gari ya waye ina kwance a gado naji an bude kofar dakin, nayi sauri na mike zaune, mommy ce ta shigo sai mai aiki a bayanta, a ajiye tray da abinci a ciki ta fita, na ce "mommy good morning" ba tare data kalleni ba tace "ki tashi ki ci abinci" daga haka ta fice tare da rufe kofar. Tunda nazo duniya yauce rana ta farko da na gaida mommy bata amsa ba, It feels really bad, wato haka Sultan yake ji kenan tunda yazo duniya. Ban kalli in da abincin yake ba na cigaba da kwanciyata har zuhr tayi. Ina zaune a kan sallaya aka sake bude kafar, wannn karon Asma'u ce, tajiye trayn hannunta ta kalli na safen da ko taba wa banyi ba. Tace "mai sunan daada ki ci abinci mana? Ya za'ayi mutun ya zauna babu abinci?, murmushi kawai nayi mata na cigaba da jan charbi na. Bata dade da fita ba aka sake bude kofar, wannan karon mommy ce ita kadai. Ta zauna akan bedside drower sannan tace "tashi kici abinci" banyi mata musu ba na dauko trayn ba bude na zuba abincin na fara ci, sam ji nake abincin babu taste amma haka nake hadiyewa da kyar, ina gama cin abincin ta dauke trayn ta fita ta rufe kofa. Sai da akayi la'asar sannan ta dawo, yanzu ma ina kan sallaya ta zauna akan bedside tace "zo nan" na mike naje gabanta na tsugunna, tace "tashi ki zauna a kan gado, ba musu na tashi na zauna ina kallon kasa tace "Maimoon ina so ki gaya min gaskiya, in kika yi min karya abinda zanyi miki sai yafi wanda nayi niyya" a hankali nace "to mommy" tace "tun yaushe kuke tare da Sultan?" Nace "tun bikin Hafsat" tace "shekara daya kenan?" Nace "eh" ta gyada kai tace "good, yaushe ne kuma ya fara koya miki shaye shaye?" Da sauri na dago kaina ina kallonta "mommy nice fa, Moon ce fa mommy" ta dauke kanta tace "I don't know you anymore, Moon din dana sani ba zata bi saurayi gidan giya ba, Moon din dana haifa na raina ba ita ce wannan a gaba na ba. Just answer the question" sai yanzu sannan hawaye suka zo idona, na rufe fuskata da hannayena ina kuka, ta sake cewa "just answer the question, tun yaushe yake kaiki bar?" Nace "wallahi mommy ban tana shan komai ba. In baki yarda ba kisa ayi min drug test" tace "OK, ina son ki gaya min komai and I mean everything da ya faru tsakanin ku" nan na fara bata labarin tun haduwar mu dashi a abuja har komawar mu England shima ya bi mu, sannan na bata labarin bina da yayi America da duk abinda ya mu kayi a can amma na cire labarin abinda ya faru ranar da zan dawo, oh no I can never tell her that, sannan na bata labarin dawowar mu Nigeria da plans din mu na kai maganar gaban iyayen mu, na gaya mata kuma abinda ya faru tsakanin su da yaya Habeeb da kuma bin Amir da nayi zuwa gurin sultan. Na kara da cewa "mother, he is not a bad person, he is a good person. Dan Allah ku tsaya ku fahimce shi" ta yi ajjiyar zuciya tace "you are not as smart as we all thought you are, moon he is playing you. Mutane irinsa abinda suke yi kenan, su samu yarinya kamarki su yaudare ta su bata mata rayuwa suyi dumping dinta. Tunanin ki bai taba baki cewa duk wadanda suke zuwa suke baki labari akansa shi ya ke turo su ba?" Na girgiza kaina nace "mother this is for real, wallahi da gaske ne, I trust him" ta mike tsaye tare da ajjiyar zuciya tace "Maimoon, you are no longer allowed to see or talk to Sultan in dai na isa dake" na fado daga kan gadon na rike kafafuwanta, ina kuka nace "Mommy kiyi min rai, mommy wallahi in kika raba ni dashi mutuwa zanyi, purnish me duk yadda kike so dan Allah karki raba mu" ta kwace kafarta taje bakin kofa tace "you really have no idea about your situation. Already munir yayi waya 'yalleman ya gaya musu abinda ya gani jiya, it is just a matter of time kafin baffa ya turo a bincika masa, so you really understand why I want you as far away from sultan as possible? He is who he is and you are who you are" ta bude kofa ta fita ta barni a durkushe a gurin. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Allahumma ajirni fi musibati wa aklifni khairan min ha. I can only imagine yadda Hajja zatayi ta yawo da maganar nan. Allah ne kadai yasan irin karyar da munir ya kara akan abinda ya gani din. Na dafe kaina daya fara sara min.
Washe gari da assuba mommy ta shigo da breakfast a hannunta ta saka ni a gaba na ci, sannan tace in tashi inyi wanka, naje naji na fito na tarar ta ajiye min kaya har da underwears akan gado tace in saka, a raina nace ina zamu je kuma da sassafen nan? Ni dai na shirya na zauna ina kallonta, ta kalleni cikin ido tace "you are going on a journey, ke da daada, ba za ku dawo ba har sai kin manta da Sultan" na durkushe a gabanta nan da nan na fara kuka ina rokonta, ko saurare na bata yi ba, tace it's for my own good, a karshe dai nace mata "mommy, ina son magana da daddy" tace "mun riga munyi maganar dashi, shine ma ya bada wannan shawarar" mommy is a bad liar, in dai tayi karya sai an gane, ina kallon fuskarta nasan daddy bai san maganar tafiyar nan ba. Zata tura ni wani gurin da Allah ne kadai yasan inane, ba tare da sanin daddy ba ballantana wani dan haka Allah ne kadai yasan ranar dawowata. Allah gani gare ka.
When everything seems lost, always have hope. Have faith that God is planning something for you. Believe that God's plan is the best.
Episode Fifty Two : The Journey
Munir, ni mai nayi wa Munir a rayuwa? Kawai dan nace bana son sa? Ai ba yaudarar sa nayi ba, tun farko na gaya masa bana sonsa kuma ni ban saka shi lallai sai ya jirani ba shi yaga dama. Na gane mugun nufinsa so yake yayi ruining reputation dina yadda lallai koda na dage bana donsa sai iyayen mu sun tilasta min na aure shi. Ni kam ban masan me zanyi ba in aka aura min Munir. Ina nan a durkushe a gurin ina hawaye har ta dawo, daga bakin kofa ta tsaya tace "let's go" na kuma rike kafarta "mommy dan girman Allah ki bani wayata, wallahi ba sultan zan kira ba, mommy dan Allah ko Hafsat ki barni inyi magana da ita" ta hade rai tace "am not stupid Moon, ni na haife ki ba ke kika haife ni ba, in dai har zan baki waya menene amfanin kaiki wani gurin. Tunda har kika san ki fita daga gidan nan ki tafi gurin saurayi ai zaki iya komai moon. Moon daga bar fa aka dauko min ke kina warin giya. Moon kece fa har da daukar saurayi ku tafi wani kasar. Duk abinda nayi miki har kina da bakin rokona mercy. In dai har ni na haife kiba zaki kara ganin yaron nan ba har abada. Kuma in dai har ni lawyer ce sai na tabbatar yaron nan yayi jail time saboda ya zama darasi a gare shi da sauran masu hali irin nasa" sautin kukana na kara, tashin hankali na shine jin tace sai ta rufe sultan, sanin halin mommy i know she is not bragging. "Mommy kiyi min rai dan Allah karki taba Sultan, dan Allah ni kiyi min komai, laifi nane, ni naje gurinsa bashi yazo gurina ba, he needs help mommy not more suffering. He will loose himself completely idan ya rasa ni kuma aka rufe shi" ta karaso inda nake tana kallona, ni kuma na sunkuyar da idona kasa tace "did you have sex with him?" Na dora hannayena aka na rusa wani sabon kukan tace "answer me, did you? How many times?" Kuka kawai nake na kasa bata amsa, mommy ta riga tayi nisa duk abinda zance mata ba zata saurare ni ba. Tace "ba zaki amsamin ba sai na kira Walid ya nakasa min ke tukunna? Did you?" Na girgiza kaina da sauri "no mommy, never" ta jima tana kallona kafin tayi deciding gaskiya nake fada, tace "tashi mu tafi" nace "ban dau kaya ba ai" tace "no need, na hada miki already" na juyo na kare wa dakina kallo, sannan na fita ta biyo ni a baya. Babu kowa a palo, haka ta tisa keyata muka fita waje, daada na gani a tsaye gaban motar mommy, baya mommy ta saka na ta rufe kofar ta zagaya zata shiga drivers seat. Yaya Habeeb na hango ya fito daga part dinsu da gajeran wando da singlet, daga dukkan alama jogging zai fita, tsayawa yayi da sakakken baki yana kallon mu muna shiga mota, wannan shi ya tabbatar min da cewa suma basu san da wannan tafiyar ba, da sauri ya karaso "Moon ina zaku je" bani da amsar da zan bashi sai kawai na daga masa hannu alamar 'oho' ya karasa gurin mommy tun kafin ya karasa ta watsa masa harara, ya juyo ya sake kallo na sai kuma ya juya da sairi yana kwalla wa ya Walid kira, tun kafin ya shiga part din nasu mommy ta ja motar dan haka ya tsaya kawai yana kallon mu, munje gate na juyo naga ya Walid ya fito shima ya tsaya yana kallon mu fuskarsa dauke da mamaki.
Titi babu kowa dan haka mommy ta ke kwarara gudu san ranta, ta gaban palace muka wuce, na kalli gate din ina lissafin ko Sultan yana ciki? Na lumshe idona knowing this is the closest I can get to him. Airport muka je, a raina nace kasar zamu bari kenan gaba daya. Muna zuwa muka fito muka shiga waiting room muka zauna, ni dai bance musu komai ba, sai da aka fara kiran flight naji an kira Niamey sai naga sun mike, zuciyata naji tayi min fari kal, dan dai Niamey ai bani da problem, wato mommy gidan su zata kaini kenan, ina zuwa zan karbi waya a gurin cousins dina na can in kira daddy in kira Sultan. Na mike da kwarin jikina, amma ban saku fuskata ba dan kar ta gane ban damu da zuwa Niamey ba. Wata jaka ta miko min tace "ga magungunan ki nan kullum zaki rinka shan dai dai" na duba naga magungunan hawan jini nane, watk mommy tasan sai jini na ya hau shine ta dauki precautions. Na rungume ta ina hawaye nace "am sorry I failed you mother" ta dan shafi bayana kadan sannan tace "it's ok, Allah ya kiyaye hanya" daganan ko fuskata bata kalla ba ta juya ta fice daga gurin. A jirgi hankali na a kwance muke tafiya, ni ce har da bacci, dan nasan 'yan Niamey sosai dan haka bani da matsala. I will come back to Nigeria in less than a week. Hmm
11 na safe a Niamey tayi mana, muka dauko kayan mu muka fito, muna fito wa na fara wara idon ganin motar da zata dauke mu, dan nasan duk sanda muka je Niamey wani cousin din mommy ne yake zuwa daukan mu, babu shi babu alamar sa. Taxi naga daada tana tsayarwa, na karasa gurinta naji suna magana da mai taxi din da yaren da ban sani ba, abinda na fahimta kawaj shine kudin da ya gaya mata, kudi ne masu yawan gaske, ya fito ya fara zuba kayan mu a mota, nace "daada ina zamuje ne?" Tace "zaki gani ne ai" nace "daada ko ma ina zamuje mu fara zuwa gidan su Ahmodou mana mu gaisa, kinga sai mu huta acan" bata kulani ba ta tura keyata cikin mota sannan itama ta shigo. Tun muna tafiya ina gane titunan da muke bi har muka fara shiga inda ban sani ba, daga baya muka dau hanyar barin gari, ni maimunatu na shiga uku, ina zamuje ne? Ni in banda Niamey ban taba zuwa wani gari a Niger ba, na sake cewa "daada ina zamu je ne?" Direct tace min "Tahoua" na kwantar da kaina a jikin window ina kallon jefi jefin bishiyoyi suna wucewa, Tahoua, nasan sunan garin amma a iyakacin sani na bamu da 'yan'uwa acan. Lallai mommy da gaske take, na danyi murmushin takaici nace a raina 'tace bazan dawo ba sai na manta da Sultan. Bata san sai da ya dauke ni shekara biyar ba kafin in chire Ibrahim daga raina ba? Sultan kuwa nasan kuwa nasan zan tafi dashi ne a raina zuwa kabari na' a haka bacci ya dauke ni, can naji daada tana tashina, na dauka munzo ashe tsayawa mukayi sallah, cikin sahara, dan gurin da muka tsaya ko 'yan bishiyoyin babu, ni dai a tsorace nayi sallar na koma mota. Bayan mun kuma daukan hanya daada ta dauko wata food warmer da soyayyun kaji a ciki ta hado min da ruwa da lemo ta miko min, na diba na zubawa drivern na mika masa. Ni lemon kawai nasha dan sam bakina babu taste.
Sai bayan magrib muka isa Tahoua. It is worse than I imagine. Gidan da muka je gidan kasa ne rufin azara, cikin wata chakudaddiyar unguwa. Ji nayi gaba daya hankali na ya kuma tashi, yanzu mommy tana nufin anan zan zauna har sai ranar da ta waiwayoni? Muna shiga muka tarar da wata tsohuwa tana kirki a itace, da mamaki ta taso ta tari daada, suka rungume juna suna ta murna, ni dai 'yar kallo ce, ta kaimu wani daki mai dan girma wanda ko siminti babu sai kasa. Ta shimfida mana tabarmar karauni muka zauna na gaisheta tana kallona tace "tubarkallah, daada ina kika samo 'yar kyakykyawar yarinya haka?" Daada tace "diyar bintou ce fa" tace "hidijan, yanzu bintou ke da diya kamar wagga?" Daada tace "laa wagga ita atta hudu" matar tace "alqur'an daada wagga ya kamata a amra mata dan'uwa ta zamna a Niger" ina jika na mike nace "ina ne bandaki zan zagaya?" Matar ta taso ta rakani, shaddar kasa, na kasa tsugunnawa na fito nayi alwala nazo na tayar da Sallah. Ina yin sallar isha na shimfida zanina na kwanta na lulluba da hijab dina, ba bacci nake ba, so nake inji hirar su daada dan insan halin da nake ciki, ga mamakina ko zance na basu yiba, labarurrukan da kawai suke yi suna dariya. A cikin hirar naji daada tace ai akan hanya muke, tsayawa mukayi mu huta, Agadaz zamu je. Zumbur na mike daga kwancen da nake nace "Agadaz daada? Daada Agadaz fa karshen duniya kenan?" Cos haka muke cewa sanda muna yara. Daada ta harare ni tace "dama ba bacci kike ba ko?" Nace "dan Allah daada Agadaz zamu? Wa muke dashi a Agadaz? Mommy ma da kanta tace bata taba zuwa ba saboda nisan garin? Daada me laifi na har ya kai girman haka?" Sai kuma kuka. Ina jin matar tana ta yiwa daada tambayoyi amma bata ce mata komai ba, aka kawomin abinci naki ci, daada ta dauko min magani na ta bani tasa lallai sai da na sha. Ranar sam banyi bacci ba, ga gajiya ga tunani, da zarar baccin ya daukeni kuwa zanyi ta mafarke mafarke, most of them na Sultan ne kuma duk basu da dadi. Daga karshe dai na tashi zaunr na hade kai da gwuiwa nayi ta rera kuka na. Babu abinda ba zan iya bayarwa ba a lokacin dan insan halin da Sultan yake ciki. Ni kaina ina tsoron zuciyarsa. Sai ya hargitsa garin Abuja gaba daya. Sai gab da assuba sannan nayi bacci, cikin baccin naga sultan a cikin gidan mu yana bi daki daki yana nemana, yana bude dakin mommy ta dauko bindiga ta harbe shi. Na farka a tsorace ina ta jero adduoi. Naji ana kiran sallah na tashi nayo alwala nazo na fara nafiloli ina ta jero wa Sultan addua, ni ban damu da kaina ba, duk abinda mommy zatayi min nasan ba zata taba chuta ta ba, amma shi bashi da kowa sai Allah. Mommy lawyer ce, zata iya creating case against him wanda dole alkalin ya dauke kansa daga ganin cewa dan sarki ne ya rufe shi, babansa kuwa ko dan yatsa ba zai daga ba ballantana ya damu. Hope dina kadai shine daddy, shi kadai ne zai taka wa mommy burki. Amma bansan shi kuma yadda zai dauki al'amarin ba, saboda shi daddy baka ta ba gane inda ya sa gaba saboda kwarjinin sa. Ana yin assalatu na tashi daada sannan na tayar da sallar, na idar ina azkar naji tana gayawa matar ta aika a samo mana mota shata. Karfe shida muka shiga motar, kawar daada ta hado mu da kunu da kosai wai ma ci a hanya. Motar hilux ce saboda sahara. Muna baya ni da daada kayan mu kuma suna gaba tare da driver. Tun karfe shida muke tafiya har karfe uku na yamma sannan muka tsaya muka yi Sallar azahar da la'asar muka cigaba da tafiya. Lallai Agadaz akwai nisa, nayi baccin har na gaji, nayi tunanin har kaina yana neman bugawa. Ko bishiyoyin ma babu, inka leka ta window yashi kawai zakayi ta gani babu iyaka. Daada tayi tayi dani inci abinci naki ci. Rabona da abinci tun wanda mommy ta takura min naci ranar da zamu taho. Mun daga nesa na hango garin. Babban gari ne babu laifi amma ko irin 'yan kauyukan kan hanya din nan babu kawai sai dai ka ganshi a gabanka a tsakiyar sahara. Muna shiga garin daada ta gaya wa drivern in da zai tsaya, ya tsaya amma maimakon inga mun fito sai naga mun zauna a mota muna jira, can sai ga wata katuwar Jeep ash color ta tsaya a kusa damu, wani saurayi ne ya fito ya kara so windon da nake yace "baki daga Nigeria?" Hausar shi tas kamar dan kano. Na dauke kaina kamar ban ji shi ba dan ni kowa ma haushi yake bani. Daada ce ta amsa masa da murmushinta tace "eh mune, mustapha ne ko musbahu?" Yayi dariya yace mata "Mustapha ne daada" ya kalleni yace "Hafsat ko Moon" ya sake bawa iska ajjiyarsa. Daada ta kama fada ni bama abinda take cewa nake ji ba, ya bude min kofa shima yana magana amma bana gane me yake cewa. Ina fitowa daga motar jiri ya debe ni sai kasa. Da sauri ya zo zai rike ni na daga masa hannu nace "Don't touch me" ni na manta ma 'yan Niger basa turanci, amma ga mamakina sai naga ya ja baya yace "just trying to help" daada ta zagayo da sauri ta rike ni muka tashi tsaye, muna tashi kuwa nayi mata wanka da amai, babu komai a cikin aman nawa sai ruwa. Sama sama nake jinsu suna ta yi min sannu. Daada tana cewa "bata taba yin tafiya me nisa irin wannan ba ne shi yasa, kai wannan gari naku da nisa yake" ni dai aka sakani a mota na kwanta ina jin dadin sanyin ACn motar. Ina jin alamar muna tafiya amma babu damar in dago kai in kalli gari saboda jirin da nake ji. Naji horn kuma naji an bude gate, daganan naji mun tsaya. Daada ta riko ni muka fito tare, inajin saurayin yana yiwa wata yarinya French sai naga tazo ta kamani itama muka shiga cikin gidan. A palo suka kwantar dani akan doguwar kujera. Mustapha ya sake aiken yarinyar sai gata da cup din tea mai zafi ta kawomin, na karba nace "graciers" na ringa kurba a hankali har sai da na sanye. Sai a lokacin na samu idon kallon palon. Yana da girma kuma an cika shi da kayan alatu, daga dukkan alama mutanen gidan basu da matsalar kudi. Daada ta shigo daga alama sallah tayi. Mustapha shima ya shigo daga masallaci. Nan aka nuna min inda zanyi sallah na shiga nayi. Daki ne babba da katon gado da wardrobe a ciki, sai toilet shina babu lefi mai kyau. Kayan mu na gani a dakin, anan kenan zamu zauna. Ina idarwa yarinyar ta dawo tayi min alama da ana kira na. A palon na tarar dasu suna cin abinci, daada da wata mata da maza samari su uku. Na karasa na zauna daga dan nesa dasu. Matar ta dago ta kalleni fuskarta a hade babu murmushi. Na gane ta. Aunty Zaliha. Kawar mommy ce tun muna yara, gurin aikin su daya da mommy. Tana zuwa gidan mu muma kuma muna zuwa gidanta tare da mommy, muna secondary school mommy tace mana sun tashi daga Nigeria amma sam bamu san Niger suka dawo ba ballantana insaka ran ganinta a agadaz. Tana da yara maza uku. Twins, Mustapha da Musbahu, sai kuma gambon su Musaddiq. Musaddiq shine sa'an Hafsat su kuma twins din sa'annin yaya Walid ne.
A hankali nace "aunty Zaliha?" Tace "eh nice dai, in kin manta ni ma ki tuna ni, kinsan cewa ni ba Fatima bace bana daukan nonsense. Kin bata wayonki wallahi Moon. Kin bani mamaki. Ni ba dan fatima bace ta gaya min ba zan iya rantsewa karya ake miki. Amma babu komai, zaki dawo hankalin ki ne. Ni na bawa Fatiman shawarar ta kawo ki nan gurina har sai komai ya daidaita tukun" kowa yayi shiru ni kam bakin ciki ne ya kamani jin itace ta bada shawarar rabani da Sultan da babana da 'yan'uwana, sai kuma ta cigaba "yarinya kamarki, me kika rasa ke kuwa a rayuwa, mai kika gani a gurin wannan kangararren yaron da bamu tabbatar ma da asalinsa ba? Kina da asalin ki, ilimi, tarbiyya, ga kyau, na tabbatar samari suna nan suna layi wadanda ko yau akace su fito zasu fito din, amma shine kika gwammace ki zibar mana da mutunci a gurin jama'a" fada take tayi da duk karfinta, ni kuma na sunkuyar da kaina kasa amma ta inda fadan nata yake shiga ta nan yake fita. Daada itama ta dauka suka yi tayi. Sai da sukayi mai isarsu sannan sukayi shiru. Wani daga cikin samarin ne ya zubo min abinci ya miko min, na karba tare da yi masa godiya. Aunty Zaliha tayi sauri tace "a'a, no friendliness of any kind. Duk wanda a cikin ku ya sake ya bata wayarsa ko da wasa ne sai na saba masa wallahi. I am dead serious. There is a very bad person a Nigeria da yake son bata rayuwarta, an kawo ta nan ne saboda a raba su. Duk wanda ya taimaka mata to ya sani cutar ta yayi. Did I make myself clear?" Duk suka amsa da yes. Sakani tayi a gaba sai da na chinye abincin da aka zubo min sannan na sha magani na tace inje in kwanta. Gaba daya jikina ciwo yake yi, ina zuwa nayi sallar isha nayi shirin bacci na kwanta. Bacci me nauyi ne ya daukeni, amma daga baya sai mafarkan suka fara dawowa, na farka na kuma kasa komawa. Daada tana gefena tana ta baccin ta, na tashi na shiga toilet nayo alwala nazo na saka goduwar riga ta na dauko al'qurani na na fara karan tawa, ina yi ina zubar da kwalla. Allah ka fini sanin halin da nake ciki, Allah ka fini sanin waye Sultan. Allah ka huci ran mommy da daddy. Allah ka bani dauriya da juriyar daukan duk wani abinda ka kaddara zai sane ni. Allah ka bawa Sultan hakuri na duk abinda ka kaddara masa. Allah ka zaba mana mafi alkhairi a rayuwar mu baki daya.
Kwana daya ya wuce, na biyu ma haka, sati daya ya wuce na biyu ya biyo bayansa, wata daya yazo, haka wata biyu sannan wata na uku yazo shima. Ko bakin gate ban taba zuwa ba ballantana in fita waje. Daga daki sai palo. Kullum da alqurani na a hannuna dan yanzu shine babban abokina, it's the only thing that's keeping me sane. Ko da yaushe daada ko aunty Zaliha suna kallona, ni kam daga gaisuwa babu abinda nake kara cewa kowa. In an bani abinci inci, in an bani magani in sha. Samarin gidan kullum suna son kula ni amma babu hali saboda suna tsoron aunty zaliha sosai. Amma ina ganin tausayina a idon su. Wanda muke magana dashi kawai shine mijin Aunty Zaliha, kullum in ya ganni palo zai ta tsokanata wai bafulatanar daji tazo birni ko yawo bata zuwa saboda kyauyenci. Kullum sai ina jin aunty zaliha ko daada sai sunyi waya da mommy amma bata taba cewa a bani ba, ni kuma ban taba cewa zan karba ba.
Rannan muna palo da aunty zaliha da Musbahu sai mommy ta kira suna magana ta tashi ta shiga daki dan kar inji me suke cewa, dama haka suke yi kullum. Tana shiga musbahu ya matso kusa dani yace "ya sunan sa?" A hankali nace "Sultan" when was the last time I called his name out loud? Yace "am sorry, I know what love feels like" a lokacin muka ji motsin aunty zaliha zata fito, yayi sauri ya matsa. Tana zuwa ta miko min waya "Fatima zata yi magana dake" na karba kawai ina kallon wayar, hannuna har rawa yake yi na saka a kunnena amma na kasa magana, can naji muryarta tace "Moon?" Wasu hawaye masu zafi suka zu bo min, banyi magana ba ta sake cewa " Moon banyi tunanin zaki dade haka ba, banyi tunanin abinda nayi planning zai dau lokaci ba" ta kuma yin shiru. A hankali nace "mommy ina daddy dasu ya Walid? Mommy in Hafsat ta haihu?" Ta jima bata yi magana ba, sanda tayi muryarta tayi alamar kuka, tace "duk lafiya lau suke, Hafsat bata haihu ba" desperately nace "mommy dan Allah ki bar ni ko waya ne inyi dasu" dif naji ta kashe, na saki wayar na rife fuskata da hannuna ina kuka. Jin muryar mommy ya daga min hankali sosai, gida kawai nake son zuwa. Aunty Zaliha ta dauke wayarta ta sake dialing number din mommy ta koma daki. Ina cikin kuka na naji an ajiye min wani abu a kan cinya ta, na dago kaina da sauri naga Musbahu yana min murmushi, na kalli cinya ta naga waya, a hankali yace "call him, but let it be our secret" gaba nane ya fadi sosai, shi kuma ya mike ya fice daga palon. Da sauri na dau wayar na saka a riga ta ina rarraba ido. I got a phone now, what do I do? Kar a kama ni kuma a kaini wani gurin da yake worse than here. Na tashi na shiga daki naga daada a kwance, nima na kwanta a gefenta na rufe idona kamar mai bacci ina ta lissafi a raina, menene yasa mommy kuka? Me ya faru a gidan? Me yasa tace abinda ta shirya is taking time? Ko dai wani abin ta saka aka yiwa Sultan kuma take regretting yanzu. Na shiga uku. Ina nan kwance har naji daada ta tashi ta shiga toilet, ta fito ta jima tana kallona sannan ta fita palo. Tana fita na mike na shiga toilet nayi locking kofar sannan na dauko wayar, babu security a jikin ta ya chire. Na shiga dialer da sauri na saka number din Sultan, na daga hannu zan dialing na kasa, what if something bad has happened to him? My heart can't take it, ya Ilahi. Sai kawai na goge number. Na saka number din daddy, ta gama ringing har ta katse bai dauka ba. Ya Allah. Na sake re-dialing ina lissafo sunayen Allah a ziciyata. Ringing na uku ya dauka "salamu Alaikum" a hankali nace "daddy" ya danyi shiru sai yace "Moon? Is that you?" Sai hawaye na kasa magana, yace "my God, Moon kiyi min magana mana, a ina kike? Ina Fatima ta kai min ke? Are you Ok?" Kuka ne yaci karfina nace "daddy ina Agadaz" yace "what? Agadaz fa kika ce? Yanzu Fatima cikin extreme saharar agadaz ta kai min yarinyar? To uban wa ta sani a agadaz din?" Nace "aunty Zaliha tsohuwar kawarta ta office dinsu" yace "Zaliha? Dama agadaz suka koma? Are they treating you well? Ko tabo na gani a jikin ki sai na dau mataki akai" nace "daddy am OK. Yaron gidan ne ya taimaka min da aron yawarsa. Please daddy kar asan shi ya bani" yace "don't worry about him, I will come and pick you up tomorrow. OK? Kar ki gayawa kowa kin kira ni, OK?" Na gyada kai kamar yana kallona. Har yanzu hawaye bai tsaya a ido na ba. A hankali nace "Daddy how is Sultan?"
Godiya marar adadi ga duk masoyana masu bibiyar lafiyata, Alhamdulillah lafiyata kalau, biki ne dai muke yi shi yasa akaji shiru. Nagode Allah ya bar zumunci.
Na samu labarin wadansu masoyan moon a whatsaap suna shirya riot dan kwato mata 'yancinta, haha, to sai ku shirya zuwa Agadaz, amma sai dai kuje ku kadai dan ni ban shirya zuwa sahara da zafin nan ba. Lol
I love you all 💖
Episode Fifty Three : Daddy
Yace "Don't worry about Sultan. Kar ki bari zaliha tasan kin kirani har sai na nemi contact da mijin ta, dashi zamuyi magana. Badan jirgi baya zuwa agadaz ba Moon da yau zanzo in dauke ki. Amma highest jibi. Ki kwantar da hankaliki kinji?" Na gyada kaina kamar yana kallona sannan nace "I miss you daddy" ya danyi shiru sannan yace "I miss you too, sunshine" daga haka ya kashe wayar. Nayi tunanin in kira Hafsat amma kuma sai na fasa kar ta gayawa mommy na kira ta. Na mayar da wayar cikin jaka ta na fito daga toilet din ina kalle kalle. Babu kowa a dakin. Na dan tsaya ina tunani, a raina nasan kiran daddy da nayi dai dai ne amma kuma duk da haka sai nake jin feeling kamar nayi ba dai dai ba. Na tsaya a gaban mirror, when was the last time dana kalli fuskata? Tunda muka zo na saka wani towel na rufe mirron dakin saboda bana son kallon fuskata. A hankali na bude, ni kaina sai da na tsorata, babu komai a fuskar sai katon hanci da idanuwa kamar na mujiya, dama haka idona yake? Lallai kiba ma rahama ce. Na kalli wuyana naga wani katon kashin da bansan ina dashi a gurin ba, amma kuma kirjina yana nan dam dam, ramar da nayi ma sai ta karawa girman su fitowa, a raina nace 'su basa ramewa ne?' Na mayar da mirror din na rufe na koma na kwanta. Ina kwance daada ta dawo tayo alwala tazo tayi sallah sannan ta tashe ni, har da dan magagi na kamar me baccin gaskiya sannan na mike na shiga toilet nayo alwala nazo nayi sallah ni ma, muka fita falo tare. Musbahu ne kadai a zaune yana kallo, daada ta zauna kusa dashi ya fara labarin film din da yake kalla, hankalinta gaba daya yana kam kallon na zaro wayar na ajiye a kusa dashi na koma gefe na zauna. Ina kallonsa ya dauka ya saka a aljihunsa ba tare daya kalleni ba. Muna zaune a palon har akayi magrib, anan muka yi sallah aka fara kawo abinci. Mun fara zubawa kenan mukaji shigowar abban su Mustapha, gaba na ne ya fadi saboda nasan ba yanzu yake dawowa ba, tun daga compound yake kwalla wa aunty zaliha kira, ta mike tsaye fuskarta da alamar tsorata, yana shigowa ya fara balbalin fada "Zaliha yanzu dama abinda kuke aikatawa kenan ke da Fatima? Kika ce min yarinyar nan hutu tazo yi gidan nan, dama ni ina mamakin tunda tazo ban taba ganin ta fita waje ba, ashe ita nan zaman prison take yi a gidana. Saboda tsabar rashin hankali ku raba yarinya da ubanta da 'yan'uwanta kawai dan saurayin da take so bai yi muku ba?" Kamar zatayi kuka tace "abban musaddiq dan giya ne fa" yace "to amma baku yi tunanin cewa baban ta shima yana da right na zaba mata miji ba? Ko ita Fatima tana ganin cewa tafi ambassador son ta ne? Yanzu kinga ni kinsa naji kunyar mutumin nan, mutumin kirki wallahi, sai da nayi tayi masa rantsuwa cewa babu hannuna a cikin maganar nan. Yanzu da wani ne da sai dai kawai inga 'yan sanda a gidana" ya zo gaba na ya sunkuya yace "Maimunatu kiyi hakuri kinji? Dana san halin da kike ciki da tuni na dau mataki a kai, babanki ya taho already, a daren yau zai sauka a Niamey dan da private jet dinsa ma ya taho, ni kuma ni zan kai ki Niamey da kaina. Ki tashi kije ki shirya" aunty zaliha ta ce da sauri "wai a yanzu zaku tafi?" Ya tashi yayi hanyar dakinsa yana harararta yace "in bamu tafi yanzu ba yaushe zamu isa can?" Yana shiga daki kowa yayi shiru a palon, na mike sum sum zan shiga daki aunty Zaliha ta danko hannuna fuskarta babu rahama tace "uban waye ya baki waya kika kirashi?" Nan da nan hawaye ya kawo idona saboda zafin rikon da tayi min, nace "ni bani na kirashi ba, bansan yadda akayi yasan ina nan ba" ta juya tana kallon 'ya'yanta har yanzu bata cika ni ba tace "cikin ku waye ya bata wayarsa?" Duk sukayi shiru, cikin tsawa tace "ba za'a bani amsa ba?" Nan suka kama rantse rantse banda musbahu da yake ta game dinsa kamar bai san me akeyi ba, tace "Mustapha kai ne ko? Dan na lura da yawan shishshige mata da kake yi?" Mustapha ya kama rantsuwar bashi bane, ko ta kan musbahu bata bi ba dan sam tunda nazo gidan baya kulani, shi dama ko a cikin 'yanuwansa bashi da harka sosai. Ta sake ni tana girgiza kai fuskarta kamar zatayi kuka "poor you, you have no idea what you have done. Sai kije ai, shi baban naki ya aura miki wanda yake so din. Duk abinda fatima tayi, she did it to protect you amma ke gani kike ta takura miki ne saboda bata son ki" ban gane mai take nufi da babana ya aura min wanda yake so ba, ni dai nasan daddy bai zaba min miji ba kuma shi da kansa ya fada cewa baya son Munir. Ta juya ta shigewarta daki, ina shiga daki daada ta biyo bayana, tana ta maganganun ta akan ban kyauta ba ni ko ko kulata banyi ba na dauki iya abinda zan iya dauka na ziba mana a akwatinan mu, sauran na barwa 'yan gidan. Ban bi ta kan daada ba na jayo akwatinan mu na kawo palo, lokacin already gari yayi duhu, abban su mustapha na gani yana cin abinci a palon, yace min "ina daada? Ku zo kuci abinci mu tafi dan kwana zamu yi a hanya" ba musu na zauna na zuba abinci na fara ci, sosai naci na koshi dan nasan wahalar da nasha sanda muka zo. Har muka gama babu aunty zaliha babu labarin ta, muna gamawa abba ya kira musaddiq ya saka mana kayan mu a mota sannan daada ta shiga dakin aunty zaliha nima na bita a baya, tana kwance a kan gado, suka yi sallama da daada nima na matsa kusa nace mata "zamu tafi" ko kallona bata yi ba, tayi fushi, na kara matsawa nace "aunty Zaliha zamu tafi" tace "Allah ya kiyaye hanya" daga haka bata sake cewa komai ba. A waje na samu daada a kusa da mota nima na tsaya, musbahu ne yazo yana murmushi yace min "so... Har taimakon gaggawa yazo kenan?" Nayi murmushi, yace "there you are, gashi har kina murmushi, abinda tunda kika zo banga kinyi ba" sai yanzu nima na tuna yaushe rabona da murmushi? A hankali nace "thank you" bai ce komai ba, daada ta kalleshi cike da zargi tace "kai ka bata wayarka ko" murmushi kawai yayi mata, ya miko min kati yace "call me when you get your phone back, and ki gaida Sultan. Adios for now Moon" nima nace masa "adios" lokacin abba ya fito da sauri ya shiga gaban motar driver dinsa ne zai tuka, mu kuma muna baya. Na kalli gidan ina jin a raina kamar wacce na bar prison na samu freedom. Tun kafin mu fita daga gari na kwanta nayi pillow da cinyar daada na fara bacci. Sai gab da assuba muka isa Tahoua, already abba ya kira wani abokinsa yace gamunan zuwa, dan haka muna zuwa can muka je, ni kam na jima banyi bacci mai dadin na yau ba, muna zuwa muka yi sallah muka huta muka yi breakfast. Karfe tara muka sake daukan hanyar Niamey, da yake hanyar me kyau ce kuma motar lafiyayya ce karfe biyu muka isa, daada ce ta ringa yi masa kwatance har muka zo gidan kawu sharu wanda yake yayane a gurin daada kuma a gidansa muke zama duk sanda muka zo Niamey. Muna packing naga manyan motoci da number din Nigerian embassy na Niamey nasan daddy yazo, da kyar na iya controlling kaina saboda excitement, amma ina shiga compound din gidan naga palon kawu a bude da takalman mutane a bakin kofar, bansan sanda na zubar da takalmana a gurin na shiga dakin a guje ina rarraba ido ina nemansa, yana ganina shima ya mike tsaye ya bude min hannunsa, ai kuwa a guje na karasa na shige ciki na kankame shi tare da sakin wani kuka mai ratsa zuciya. Sai da nayi kuka na na gama sannan ya raba ni da jikinsa yana kallon fuskata, fuskarsa sam babu fara'a, kallona yayi tayi sama da kasa kamar mai tabbatarwa babu abinda aka gutsira a jikina, sannan yace "are you OK?" Kaina kawai na gyada masa. Na juya ina kallon sauran mutanen dakin, sai a lokacin naga mommy, tana zaune a kan carpet ta harde kafafuwanta a guri daya,fuskarta tayi ja, akwai uncles dinta su biyu na gurin uwa dana guri uba, na saki daddy na tafi na fada kan cinyarta, bata cemin komai ba sai dan bubbuga bayana da take yi. Daada ta shigo tare da abba suka gaisa da mutanen gurin. Daddy ne ya soma fada, daga dukkan alamu dama fadan ya keyi kafin mu shigo yanzu cigaba yayi "ta nuna min ni ban isa ba. Ta dauke min yarinyar ba tare da sanina ba kuma nayi nayi ta gayamin inda take taki. Ko wanne laifin yarinyar tayi au kamata yayi ace an gayamin first sannan kuma sai mu hadu ni da ita musan irin hukuncin da zamu yi mata, amma a haka ai ta nuna min ban isa da 'yata va kenan" kawu sharu ne yace "tashi ki shiga cikin gidan Maimoon" daga dukkan alamu daddy ya manta ina gurin. Na tashi na shiga cikin gida amma jikina duk yayi sanyi. Tunda nake a rayuwata ban taba ganin mommy da daddy suna musu ba ballantana fada, dan ina da burin ace wata rana ni da mijina mu kasance tamkar mommy na da daddy na. Har daga cikin gidan ina iya jiyu muryar daddy yana fada, sam ba halinsa bane ba, dan da wahala kaga daddy yana fada, ballantana a gaban surukansa. Ji nayi gaba daya komawa Nigeriar ma ya fita daga kaina. Na zamanto dalilin samun matsala a tsakanin iyayena, kowa a cikin su is trying to put me first. Nasan duk abinda mommy tayi tayi ne dan tana ganin shine dai dai a gareni, amma ni abinda ban fahimta ba shine dalilin ta na kin gayawa daddy bayan kuma nasan komai tayi sai ta gaya masa. Ina nan kwance abin duniya ya ishe ni gwoggo Sa'a ta shigo tace in tashi inyi sallah inci abinci, bayan na gama ne ta tambayeni "Maimoon wai me ke faruwa ne tsakanin mommyn ki da daddyn ki?" A raina nace wannan tsegumi take so kenan, na daga mata kafada alamar bansani ba, daga nan bata sake cewa komai ba. Mommy suka shigo tare da daada, ko kallon inda nake bata yi ba ta shige toilet tayo alwala tazo ta tayar da sallah, daada tana ta 'yan mitocinta "ba shikenan ba, sai kije ai ya aura miki ko ma waye yaga dama, duk abinda ya fari kuma daga baya kar ki zo gurin mu, ki je can ku karata ke da baban naki" ni duk maganganun da take yi ban fahimci me take nufi ba dan haka kawai kallonta nake yi, mommy ta idar da sallah ta mike ta tsaya a bakin window tana kallon waje, muna haka sai ga dan aike daga waje "wai Maimoon tazo su tafi" na mike ina saka hijab dina nace "mommy ance mu fito" ta juyo ta kalleni tace "ance ki fito dai, ko kinji an ambaci sunana?" Na yar da hijab din hannuna na karasa kusa da ita nace cikin rawar murya "mommy ba tare zamu tafi ba?" Ta juya min baya tace "no, am going to stay here for a while, go with your father " na durkushe a gurin duk farin cikin komawa gida ya gushe daga zuciya ta, na rike kafarta nace "mommy ni bazan koma gida ba tare da ke ba, mommy dan Allah kiyi hakuri ki zo mu tafi, mommy in dai akan maganar Sultan ne zaku samu matsala da daddy wallahi ni na hakura da shi. Kun fiye min dubun sultan wallahi. Dan Allah mommy kiyi hakuri kice kin yafe min" kuka nake sosai. Ta dago ni ta rungume ni tace "ni na yafe miki tun tini Moon. I just wanted to clear the mess you created" nayi sauri nace "to in kin hakura kizo mu tafi gida tare" tace "that's not up to me, daddyn kine yayi fishi bani ba" na chika ta da sauri nasaka hijab dina na fita, a compound naga daddy tare dasi kawu, ina fitowa yace "taho da sauri mu tafi dare yana yi" ina zuwa na durkusa akan gwuiyoyina ina hawaye nace "daddy dan Allah kayi hakuri, wallahi ni na hakura da koma menene yasa kuka samu matsala da mommy, it's all my fault. Dan Allah kuyi hakuri mu koma gida gaba daya, ni ba zan iya rayuwa babu mommy ba kuma bazan iya babu kai ba" ya dago ni yace "it is not your fault Moon, kowa akwai destiny dinsa a rayuwa. Ita kuma mommyn ki ita tace tana son ta zauna anan for sometime, bani nace ta zauna ba, if you can get her to go with us then I will be more than happy" na koma ciki da sauri nace "mommy daddy yace ki zo mu tafi tare" tana kallona tace "shi ya gaya miki hakan?" Nace "eh" kafin ta sake magana kawu sharu ya shigo ya kama bambami "ya zaku ke wani abu ne kamar yara Fatima? Kece me laifi kuma kece mai fushi? Shi kenan kuma kinyi laifi sai kice ba za'a yi miki fada ba? Dan kin samu miji mai hakuri ko?" Ya juya kan daada A cigaba "duk kece kike daure mata gindi ai, kin barta sai abinda taga dama take yi, ai ba gata kike mata ba" sai da ya wanke su tass sannan yace mommy ta fito mu tafi. Fuu ta wuce ni tayi gaba, da sauri2 na bita a baya.
Ina fita na kalli motoci guda biyu da suke jiran mu, a lokacin idanuna suka sauka akansa. Yana tsaye ya jingina da jikin mota, light brown eyes dinsa a kaina. Shadda ce doguwar riga da wando dark brown a jikinsa, kalar shaddar ta kara fito da uniqueness din fatarsa, hularsa da takalmin sa light brown kalar idonsa. Yawan sumar kansa ta saka hular bata shiga kan sosai ba. Ya cire hular ya saka hannu ya hargitsa gashin sa sannan ya mayar da hular still idonsa a kaina. Kafafuwana naji kamar ba zasu dauke ni ba, what is he doing here? Muryar daddy naji yana cewa "Sultan ina Walid din kuma ya tafi? Ku zo mu tafi mana, weather din sahara is unpredictable"
Episode Fifty Four : Her Father's Daughter
Hannu na saka na murza ido na, ni dai nasan ba bacci nake ba ballantana in yi tunanin ko mafarki nake, idonsa yana kaina kamar yadda nawa yake kansa. He looks different, but it is still him. Ya rame shima. Ban taba ganin sa da manyan kaya ba maybe shi yasa naga ya kara chanzawa, but God he looks more handsome than ever. Kamar in ruga da gudu in taba shi dan in tabbatar ba hallucination nake ba. Muryar daddy naji kamar daga sama yace "Sultan, da kai nake magana fa" yayi sauri ya dauke idonsa daga kaina tare da sunkuyar da kansa kasa yace "sorry daddy" sannan ya zaro wayarsa yayi dialing ya saka a kunne "kana ina ne? Daddy fa har ya fito, kayi sauri" ya kashe. Muryarsa ce, so it is really him. Ya bude wa daddy kofar baya, bayan daddy ya shiga ya gyara masa rigarsa sannan ya rufe. Yana rufe kofar ya juyo ya sake maida idonsa cikin nawa, with all my psychology amma a lokacin kasa reading dinsa nayi, so clouded. Daddy ne ya sauke glass dinsa yana kallon sultan sannan ya kalleni, wannan karon nice nayi saurin dauke idona na sunkuyar da kaina sannan kuma sumi sumi kamar munafuka na tafi motar da naga mommy ta shiga, na zauna a baya a kusa da ita. Ta window na cigaba da kallonsa duk da yanzu bana ganin fuskarsa, bamu jima ba naga yaya Walid ya taho da dan gudun sa ya shigo gaban motar da muke ciki, ina kallon sultan ya bude gaban motar da daddy yake ciki ya shiga. Tunda muka fara tafiya babu wanda yayi magana, can mommy tace a hankali "yana motar daddyn ku ko?" Ban fahimci me take nufi ba kuma nasan ba dani take magana ba shi yasa nayi shiru, ya Walid ne ya amsa "yes, mommy" tayi kwafa tare da dafe kanta. Ina son in tambaye su maganar wa suke yi saboda in tabbatar wanda na gani shi dinne dai ba wani ba, amma kuma bazan iya ba. Na runtse idona ina so in fahimci me yake faruwa. Wata na uku da sati biyu rabona da Nigeria amma ji nake kamar wadda nayi shekara daya. Me Sultan yake yi tare da daddy na? A iya sanina ko haduwa basu taba yi ba. Me ya faru bayan tafiya ta?
Kafin Moon ta samu amsarta mu bara mu koma baya mu riga ta sani.
Nigeria bayan tafiyar Moon
Walid da Habeeb suka bi bayan motar mommy da kallo. Walid ya juyo ya kalli Habeeb yace "ina zasu je?" Habeeb ya daga kafada yace "oho, nima kawai ganin su nayi suna shiga mota" Walid ya kalli agogon hannunsa, 7 ma bata yi ba, where can they possibly go to at this hour? Jikin sa dai bai bashi dai dai ba. Yace "OK, mu jira su su dawo kawai" ya juya ya koma ciki. Sai around nine mommy ta shigo gidan ita kadai, babu Moon babu Daada, a palo ta same su suna breakfast, ta shige ciki, har ta shirya ta fito suna palon, ta zauna tana hada tea, Habeeb yace "mommy ina su Moon suka tafi ne da sassafe haka?" Ba tare data kalleshi ba tace "inda ka aike su nan suka tafi" daga nan babu wanda ya kuma cewa komai, daya bayan daya suka mike suka bar palon, tabi bayan su da harara. Tana gamawa ta shirya ta tafi office. Sai karfe biyar ta dawo, tana yin packing wayarta tana yin kara, ta duba screen din 'dear' tayi ajjiyar zuciya, tasan maganar dai, tun jiya maganar daya ce, tasan dole zatayi facing wannan challenge din but she is ready. Moon is weak, too soft, tun da aka haife ta haka take, she trust too much, love too much and gives her all in everything she do, she is her father's daughter, shima haka yake, dan haka ita mommy dole ta zama strength din su, ba zata taba barin wani ya yi taking advantage of her sweet daughter's innocence ya cuce ta ba, not that so called Sultan and not that stupid munir. Tasan plan din munir, so yake a tilastawa Moon ta aure shi, ita kam ba zata taba barin ayiwa 'yarta auren dole ba da mutun kamar munir ba, over her dead body, abinda yayi recently ya tabbatar mata da ba son Allah da annabi yake yiwa moon ba, idan da ace yana sonta da ko ita data haife ta ba zata san abinda ya gani ba. Kiran ya sake shigowa wayarta, tayi taking deep breath sannan ta dauka, 'salamu alaikum" da sauri ya amsa sannan yace "ina kika shiga ne haka? Wajen five missed calls?" Ta danyi murmushi tace "kasan aiki yayi min yawa tunda na dawo dinnan. Ina office sai yanzu na dawo gida. Ya kake?" Ya danyi murmushi "am fine mommyn kids, busy body, ya kuke?" "Lafiya lau, just missing you" "wai Moon har yanzu wayarce bata gyara ba? Tun shekaran jiya rabon da muyi magana da ita. Please in tana kusa bata wayar" ta shirya abinda zata ce masa dama "bata gida yanzu, kafin in fita dama tace zata je gidan su Amira, yanzu na tarar bata dawo ba, nima bana son rashin wayar tata amma tace she is taking a time off" ya tare ta "ba wani time off, tell her in ta dawo na turo mata kudi taje ta siyo wani wayar, and also tell her to call me ASAP" tayi dariya sosai tace "to daddy, an gama" shima dariyar yayi, suka dan taba soyayya kadan ta kashe. Ta jima tana kallon wayar, ta san halinsa akan son 'ya'yansa especially moon amma bata yi tsammanin zai tada hankalinsa da wuri haka ba. Ta gyara packing ta shiga gida.
Karfe takwas na dare Munir ya shigo gidan, tunda yazo garin dama hotel ya kama, baya son zaman gidan saboda baya son asaka masa ido, gwara hotel yadda zaiyi abinda yaga dama. Yayi packing tare da dauko wayarsa yayi dialing number din Moon, switched off, ya tabe baki, shi ya rasa dalilin da yasa ya kasa hakura da yarinyar nan, tun ranar daya fara ganinta yasan cewa he must have her, no matter what. Duk da kiyayyarsa da yake gani a idonta amma yaki hakura, she don't love him, she thinks she is too good for him. Bai taba sanin yana da sa'a a rayuwa ba sai shekaran jiya da ya ganta a gaban hotel din daya sauka, ya fito da niyar zuwa neman abokiyar harka kawai ya ganta tare da wannan half breed drunk guy din. Ashe itama A ce bai sani ba? Who would have imagine that the so good daughter of the so good ambassador is a drunk slut? Yayi dariya, yaso ace ya dauki video yadda zai ji dadin nunawa dan afi yarda dashi. Ya bude motar ya fito ya nufi cikin gidan. A palo ya tararda Habeeb shi kadai yana kallo, tunda ya amsa sallamarsa bai kuma kallon saba. Ya dora kafa akan kujera yace "kai ba ka iya gaishe da mutane ba?" Habeeb ya waiwaya ya kare wa palon kallo sannan yace "suna ina mutanen? Ni banga kowa da zan gaisar ba ai" Maimakon munir yaji haushi sai ma murmushi da yayi yace "duk zaku gane kuren ku ne, kuna daga wa mutane hanci kuna ganin kamar kunfi kowa a family ko? Da sannu duk zaku gane kuren ku" ya samu guri ya zauna yace "ina gantalelliyar kanwar taka take? Ko yauma ta fice? Ya kamata kuyi gaggawar saka mata mari ko kuma ku miko min ita nan ni nasan maganin irin su" Habeeb ya mike yace "kaga malam zo ka fita mana a gida, Moon ba gantalalliya bace ba, kuma tafi karfin ka wallahi, kaje kayi ta fadan abinda zaka fada, idan mafadin magana wawane majiyinta ai ba wawa bane. Babu wanda baisan halinka a family ba kuma babu wanda baisan halin Moon ba, babu kuma wanda baisan cewa moon bata son kaba, so go ahead and continue telling the lies, you will end up looking like a fool" a fisace munir ya mike yana nuna Habeeb "kai dama rashin kunyar ka har ta kai haka? Ni zaka cewa makaryaci? Rufa mata asiri fa zanyi in aure ta, bayan abinda tayi wa kake tunanin zai auri ragowar wani?" Kyakykyawan mari Habeeb ya ajiye a fuskar munir, abinka da farar fuska take fuskar tayi ja. Wannan yayi dai dai da saukowar mommy daga sama, munir ya shaki kwalar habeeb ya fara duka, mommy tayi sauri ta danna security alarm, kafin minti daya wajan mutum biyar suka shigo, da kyar suka raba munir da habeeb kowa ya daku a cikin su, mommy tace "ku fita dashi, kar ku sake barinsa ya shigo gidan nan" munir yace "bazan sake zuwa ba sai kun neme ni da kanku, kuma nayi muku alkawarin sai kun neme ni, daga nan 'yalleman na nu fa" ya fincike daga hannun security din ya fice. Mommy ta zauna akan kujera tana dafe kanta da yake neman sara mata, tabbas gwara data dauke Moon daga gidan.
Haka rayuwa ta cigaba da kasance musu har bayan kwana uku, a lokacin daddy is sure cewa something is wrong, tun Moon tana karama bata taba 24hours ba tare da ta yi masa waya ba in dai baya gari ballantana ace yau kwana biyar rabonsa daya yi magana da ita, tun mommy tana masa karya yana yadda har karyar tata ta kare in ya tambaye ta sai tayi shiru. Dole ya ajiye abinda duk yake gabansa ya tafi Nigeria. To him, his family is above everything, har aikinsa. Ya na kokarin handing over to his assistant kira ya shigo wayarsa daga Walid, ya daga da sallama sannan yace "ya akayi?" A hankali Walid yace "daddy you need to come home, something is wrong, Moon is missing" sai da ya jima yana assessing maganar a ransa sannan yace "what? Ban gane Moon is missing ba?" Walid ya bashi labarin duk abinda ya sani, sannan yace "Mommy ta dauke ta tun three days ago, mun tambayeta taki gaya mana inda ta kaita" daddy ya kasa cewa komai, not Moon, not my daughter, something must be wrong somewhere. Yace "OK, I will be home tomorrow, kar ka ce da mommyn ku komai, in nazo zanji duk abinda ake ciki" washegari kuwa ya sauka a abuja a private jet dinsa. Mommy kawai sai ganin shi tayi ya shigo palo, da sauri ta mike tsaye tana twisting fingers dinta, direct yace mata "ina Maimunatu?" Ta bashi amsa "she is safe"
Sultan
Bai taba regretting shan giya irin na ranar ba, yana kallo aka saka moon a mota aka tafi da ita amma ba zai iya yin komai ba saboda bashi da karfi, karfinsa shine babban abinda yake takama dashi, gani yake he is untouchable, amma yanzu gashi anyi touching something that is more precious to him than himself and he couldn't do anything. Da kyar Amir ya chusa shi a motarsa yaja suka nufi gida, babu abinda yake maimaitawa sai "I will kill him, I swear I will kill him" Amir dai bai ce masa komai ba, tun a hanya ya kira family doctor dinsu ya gaya masa su hadu a gida. Da kyar ya kama sultan ya shiga dashi part dinsa, direct bedroom ya kaishi ya kwantar dashi, lokacin jikinsa ya karasa saki gaba daya. Doctor yana zuwa ya duba kafar yaga bayan yankewa da yayi wanda sai anyi masa dinki, ankle dinsa ma ya goce, ya gama masa komai ya gyara masa kafar, yace kar ya taka kafar sai nan da 3days, ya bashi 3days bed rest, zai fita Amir ya kira shi gefe ya roke shi yayi wa Sultan allurar bacci dan yasan ba zai zauna ba, yana watstsake wa zai fita, ba musu doctor ya hada allurar, Sultan ya bude ido yana kallonsa yace "allurar menene kuma wannan?" Doc yace "pain reliever ce" kafin sultan yace wani abu yayi mishi ita. Tun kafin likitan ya fita sultan ya fahimci allurar me akayi masa, cikin magagi yace "I will kill you Amir, shine kasa akayi min allurar bacci ko? Bayan kana kallo yana dukan ta ko? Waya san me zaiyi mata in sunje gida, duk ni na jawo mata kuma sai na rama mata" Amir yana shafa kansa yace "Sultan brother dinta ne fa?" Sultan ya ture hannunsa yace "I don't care koma waye shi, he have no right to hit her" daga haka bacci ya dauke shi.
Har gari ya waye sultan yana bacci, bashi ya tashi ba sai kusan azahar. Yana farka wa Moon ce a ranshi. Ya mike da sauri sannan yaji pain a kafarsa ya tuna ashe yaji ciwo. Ya zauna a bakin gado ya dafe kansa. Jiya baiyi sallah magrib ba baiyi isha ba, ga subh yau sannan zuhr ta taho, baya wasa da sallah, baya yin nafila dai dasu azkar amma baya barin farilla. Zuwa gurin Moon have to wait sai yayi sallah tukunna. Ya tashi yaji zafin ciwon kafarsa har cikin kansa, a hankali yake jan kafar ya shiga toilet, it annoys him, babu abinda ya tsana irin abinda zai takura shi ya hana shi activities dinsa. Ya fara sallolinsa a tsaye amma dole daga karshe a zaune ya karasa sanoda ciwo. Damn it, wannan kafar ba zata barshi yaje yaga moon ba. Yasan ba za'a barta ta fito ba dan haka plan dinsa shine ya haura ya shiga dakinta ta window kamar yadda ya taba yi a England. Dama ya riga ya lura inane dakin ta. Yaji haushin ta akan kin gaya masa zancen project dinta da tayi amma ya yafe mata, ba zai iya yi fushi da ita ba. Ya mike ya koma toilet ya hada ruwan wanka, ya fito yana shiryawa amir ya shigo tare da wata maid dauke da abinci, ta ajiye ta fita, shi ya manta ma da wani abu wai shi abinci, duk soyayyarsa da abinci kuwa, ashe gaba ma akwai gabanta. Amir ya zau a yana kallonsa yace "ya naga kana shiryawa? Ina zaka je kuma? Kasan doctor yace 3 days of bed rest ya baka ko?" Ba tare da sultan ya kalle shi ba yace "fuck the bed and fuck the rest" Amir bai hakura ba yace "at least kafin ka fita eat something, rabon ka da abinci tun jiya da rana" sultan ya sake cewa "fuck the food" ya dauki key din mota ya saka takalmansa yayi hanyar waje, Amir ya bishi da sauri yace "don't do this sultan, zaka saka yarinyar nan in more trouble than she already is" ya juyo ya nuna amir da key din hannunsa yace "fuck you" ya juya ya fice.
Tafiyar da yayi zuwa packing space kadai ita ta tabbatar masa ba zai iya shiga dakin Moon yau ba, har gumi ya hada saboda ciwo, sai da ya zauna a mota ya huta sannan ya tayar da ita ya fita. Daga nesa da gidan yayi packing ya dauko wayarsa yayi dialing number dinta, shi kansa yasan ba zai samu ba dan ya san da ace da waya a hannunta da yanzu ta neme shi, duk three lines dinta are switched off, har layin ta na England sai da ya kira. Ya jefar da wayar akan seat din motar, sai yanzu yayi nadamar kin cin abincin da yayi, da at least ya dan samu karfi ko yayane. He is not going to give up, no, sultan never gives up. Ya tayar da motar ya karasa bakin gate din gidan yayi packing ya fito, ya karasa baking gate fin yayi knocking. Instead of maigadin daya saba gani, wani katon mutum ya gani ya bude kofar yana kallonsa yace "ya akayi?" He itch to punch the man in the face, ya dan kakaro murmushi yace "Moon tana gida kuwa?" Mutumin yace "what is it to you in tana gida?" Control3 sultan yake ta maimaitawa a ransa sannan yace "am... Ina son magana da ita ne" mutumin ya sake hade rai yace "she is not seeing anybody, so get lost" daga haka ya mayar da kofar ya rufe. Hannu sultan ya dunkule ya daki kofar dashi wishing ina ma dai mutumin ya daka da sai yafi hucewa. Ya koma mota kafarsa tana pulsing saboda zafi ya zauna yana tunanin abinyi. Yana hango balcony dinta a rufe. They are her family, yasan ba zasu yi harming dinta ba, he just need to see her dan ya tabbatar she is OK. A karshe ya yanke shawarar ya tafi gida for now, yayi jinyar kafarsa ya samu lafiya, karfinsa ya dawo, and then he is going to take her away, and no body will stop him.
Kwana biyu yana kwance yana jinya, Amir ne mai kula dashi, kaf cikin gida babu wanda ya leko yace masa ya jiki duk kuwa da cewa Amir ya shiga ya fada musu. Yana bin ka'idojin likita sosai saboda yana so ya samu lafiya, on the fourth day ya shirya yau za'ayi ta kare dan har kayan sa ya zuba a mota, ya sayi flight tickets da sunan sa da nata zuwa America. Dare yana yi ya dau mota ya fita, ko Amir bai sani ba, yaje yayi packing a bayan gidan ya fito da kafa ya zagaya, yayi studying katangar da gate din sosai, ya lura akwai shocking saman katangar, gate din kuma yana hade da alarm. Windown dakin mai gadi yaje, a hankali yayi sliding glass din, ya leka dakin yaga babu kowa, daraf ya shige dakin, a ransa yayi tsaki yace 'mai gadi ya tafi yana gadin gate yabar dakinsa unguarded' silently ya fita ta kofa, ya hango mai gadi da securities biyu a bakin gate duna zaune suna hira. Ta cikin inuwar katangar gidan ya ringa bi yana tafiya saboda security light din da aka kunna ta haske gidan gaba daya, a haka har sai da yaje backyard kusa da boys quarters sannan ya koma jikin gidan, a hankali ya ringa neman back door har ya ganta, lock dinta is coded, dama yayi tunanin haka, ya dauko powder a aljihunsa ya hura akan lock din, a take ya gane numbers din 0258 yayi tunani kadan sai yayi murmushi, Moons birthday, a ransa yace 'they should have change it' ya danna da correct arrangement din 25-08, kofar ta bude ya shige ciki. A gaban stairs ya ganshi, bai jira komai ba ya hau, ya san a side din da dakinta yake dan haka nan yabi, yana ganin kofar ya gane itace saboda pink doormat daya gani, she is the only girl in the house, ya kama door knob din yaji a rufe, ya tsugunna yana studying keyhole din sannan ya dauko wani pin a aljihunsa ya zura a ciki, in less than a minute ya bude kofar ya shiga, wayarsa ya dauko ya kunna fitila yana haska dakin, babu kowa, gadon ma ko shimfida babu akai, a gurin ya durkushe, where is she? Haske ya ga ya gauraye dakin, ya dago kai da sauri half hoping to see her standing, mommy ce a tsaye a bakin kofa, da securities guda biyar a gefenta, yayi sauri ya mike tsaye, tace da securities din "take him away, ku kaishi station kuyi charging dinsa with assault, kidnapping and trespassing" ta juya tayi tafiyarta.
Mamaki ne ya hana sultan motsawa har suka saka masa ankwa suka fita dashi, lallai mommy ta nuna masa ta fishi shekaru. Ranar a station ya kwana. Bai damu ba, tunanin sa daya shine ina Moon take. Washe gari da sassafe aka turo daga fada akayi bail dinsa, not because an damu dashi but to protect the family name, yana zuwa gida ya tarar da takardar sammaci a kotu, mommy ta kai shi kara, kuma a takardar ance ya sace Moon, dan haka ana tubumarsa daya fito da ita. Duk abinda yake na glass a part din Sultan ranar sai da ya fasa shi, duk ya jiwa hannunsa ciwo, sai da Amir ya kira galadima sannan ya samu kan sultan. Nan da nan Takawa ya fara neman yadda za'a samu alkalin da aka kaiwa karar a kashe maganar ba tare da yasan 'yar waye ma ake rigima akanta ba. Babu wanda ya kira sultan ya tambayeshi ba'asin mai ya faru ko kuma yayi masa fada. Bayan la'asar Amir ya kira masu gyara suna ta aimin gyaran part din Sultan, Sultan ya sulale ya fice daga gidan, gidan su Moon ya koma, gate din a bude yake kamar gidan a cike yake, yayi packing ya fito direct ya nufi gate din yana shiga David ya tso ya tare shi, David shine chief security din gidan, katon gaske ne dan Moon tun tana rayinya take tsoronsa, amma naushi daya Sultan yayi masa sai ga David akan gwuiwoyinsa yana kokarin dawo da numfashinsa, nan take sauran securities din sukayi kansa.
Hayaniyar da suke yi ce ta jawo hankalin daddy wanda yake tsaye ya tsare mommy da ido bayan ta amsa masa da "she is safe" ya fita da sauri su Walid suna binsa a baya. Scene din da ya gani a compound dinsa ne yasa ya saki baki yana mamaki, already Sultan ya zubar da mutun uku a kasa, yana ganin daddyya fito ya gane shi dan yasha ganin pictures dinsa a wayat Moon, ya karaso gabansa da sauri, yana zuwa ya zube akan gwuiwarsa, yana haki yace "Sunana Abubakar Sadiq Abdallah, I am a drunk, I don't know who my mother is and my father hates me, na taba zama a gidan kangararru, I have a bad temper, I get in trouble most of the times and I have heavy criminal record with the police. Nazo ina neman auren 'yarka, Maimunatu"
0 comments:
Post a Comment