Kowa a gurin sakin baki yayi yana kallon Sultan, hatta daddy rasa mai zaice masa yayi, ya jima yana kallon sa shi kuma Sultan ya sunkuyar da kansa kasa, a zuciyarsa yana wishing ina ma dai zai iya kuka, maybe in hawaye ya fito masa zai ji sanyi a zuciyarsa, wannan mutumin da yake tsaye a kansa is his only chance to happiness, idan yace yes to shi kam ya samu duk wani buri nasa na rayuwa, in yace no kuma tamkar a saka full stop ne a rayuwar sultan. Daddy ya sauke ajjiyar zuciya yace "wannan shine dalilin ka na shigo min gida ka tayar min da hayaniya? Wannan shine dalilinka na dukan securities dina?" Sultan ya kuma sunkuyar da kansa yana jin bugun zuciyarsa yana karuwa. Daddy yace "tambayarka nake yi fa?" Sultan ya dago kai ya kalli daddy da jajayen idanunsa yace "daddy ba zasu bar ni in ganka ba ne. And I must see you. Tun a England muka shirya da Moon za ta kawo ni gurinka, bamu samu dama ba, anan ma muka sake shirin zuwa ganin ka shima still bamu dace ba. This is the only way for me to see you" da mamaki daddy yace "ita moon dince ta amince maka kazo gurina ka nemi auren ta?" Sultan ya gyada kansa yace "yes daddy, kuma yanzu I don't even know where she is" daddy ya jinjina maganar a ransa, in dai har Moon ce ta turo shi gurinsa then she must have her reasons, maybe reasons dinta yana daga cikin dalilan da yasa mommy ta dauke ta. Ya juya ya kalli Walid a gefensa yace "Walid shigo dashi ciki" ya juya ya koma palo, walid ya bishi da kallon mamaki amma shi yasan bai isa yayi masa musu ba, yiwa iyaye musu baya daga cikin tarbiyyar da aka basu. Ya mika wa sultan hannu da niyar ya taimaka nasa ya tashi tsaye, sultan ya watsa masa harara ya mike a hankali yadda su biyu kadai zasu ji yace "zan dawo kanka ne" bai jira walid yayi masa jagora ba ya bi bayan daddy. Ya tarar palo babu kowa, da alama daddy sama ya hau, akan carpet ya zauna ya harde kafafunsa ya zabga tagumi. He is ready to wait to awa nawa ne, ko kwana nawa ne, indai har at last daddy zai saurare shi. Walid ya shigo ya samu guri can nesa da Sultan ya zauna, babu wanda yace wa kowa komai har daddy ya sauko, ya yi wanka ya chanza kaya sai kamshi yake, Sultan ya kalli kayan jikinsa, sun chukurkude saboda fadan da yayi da securities, babu abinda yake sai warin gumi, ya daga kafada bai damu ba.
Daddy ya zauna akan kujera yana studying Sultan. He is a perfect mixture of his father and mother. Fuskarsa sak ta Khairat sai dai kawai shi namiji ne ita mace, sai kuma duhun fata da ya fita saboda yayi mix da duhun fatar babansa, kirar jikinsa kuma sak na babansa lokacin yana age dinsa. Daddy yana hango su a idonsa suna wayo tare ko'ina a Oxford. What has gone wrong tsakanin su? Yayi gyaran murya yace "bismillah malan Abubakar, fara daga farko, a ina ka hadu da 'yata kuma menene a tsakanin ku?" Sultan ya danyi shiru yana controlling emotions dinsa sannan ya fara bada labari, komai sai da ya fada wa daddy, da boye boyen da suke yi saboda tana tsoron kawo shi gida, rayuwar su a England da America, amma duk bluntness din sultan bai bada labarin toilet experience dinsu ba, ya bada labarin plans din da suka ringa hadawa na zuwa ganin daddy amma ana samun sabani, ya bada labarin matsalar da suka samu akan project dinta da fushin da yayi ya tafi bar ita kuma ta bi Amir ya kaita gurin shi, ganin da munir yayi musu da zuwan Walid. Sai da ya gama kaf sannan yace "dan Allah daddy kar ka raba mu wallahi mutuwa zanyi, I have no body a duniyar nan sai ita" daddy ya kalle shi a nutse yace "you look like your mother" Sultan ya dago kansa da sauri ya kalli daddy yana tunanin anya kunnen sa ba karya yayi masa ba, sam babu wasa a fuskar daddy, ya sake cewa "kamar ku daya, sai dai ta fika fari, ta fika kuma hankali da nutsuwa" da rarrafe sultan ya karaso gaban daddy ya rike kafarsa yace "you know my mother?" Daddy ya gyara zama yana kallonsa yace "ba sosai ba, dan bamu taba magana da ita ba, amma na san ta kuma ina ganin ka nasan dan ta ne kai. Oxford sukayi karatu ita da babanka, lokacin yana kamar ka. Baban ka was exactly like you, he was a rogue also. A gang leader na 'ya'yan masu kudi" daddy yayi murmushi yana tuno rayuwarsu ta makaranta yacigaba da cewa "ni lokacin dan talakawa ne dan haka bana cikin su, ina dai hangen su suna yawo da motoci a cikin makaranta. He was so energetic, so stubborn like you. Duk sanda na ganshi a TV yanzu sai inyi ta mamakin yadda akayi ya koma haka" sultan ya saki baki yana mamaki, bai taba tsammanin cewa da akwai wani abu na halayya daya dangantashi da babansa ba. A hankali yace da daddy, "please tell me about my mother" daddy yace "kamar yadda na gaya maka, ban santa sosai ba, nasan dai sunanta khairat, and i always say, she is the most beautiful woman I have ever seen. She is full blood Arab. Tana da nutsuwa sosai, kuma daga ganin ta daga babban gida ta fito. They were so much in love ita da Sadiq. I remember always thinking they look odd, ita so fair shi kuma so dark, ita gentle shi stubborn, ita Arab shi Hausa. Amma duk 'ya'yan masu kudi. Muna gama PhD suka bar Oxford, ni kuma na zauna na kama lecturing a can. Ban taba dauka sun rabu ba. Shi yasa nayi mamaki da kace min baka san mamanka ba, and you said something about your father hating you. Ban gane me kake nufi ba. Why will your father hate you?" Sultan ya girgiza kansa yace "nima ban sani ba fa" nan ya fara bawa daddy labarin rayuwarsa tun sanda yayi wayo har zuwa haduwarsa da Moon. Duk abin ya daure wa daddy kai. He needs time to think about it. Sultan ji yayi kamar zai hadiye daddy, tunda yake babu wanda ya taba bashi labarin mahaifiyarsa, he only know her name shima kuma a birth certificate dinsa ya gani, yanzu yasan she is Arab, yayi murmushi, he always have a thing for Arabs, duk da ba wai iya larabcin yayi ba amma duk sanda yayi sai aji kamar a bakinsa aka rada shi ashe its in his blood. Ina ma dai one day zai ganta? Sai kuma ya cire maganar daga ransa, tunda har ta iya cire shi daga jikinta ta ajiye shi ta tafi without a second look to shima dan me zai nemeta. Suna tare da daddy har magrib sannan suka je masjid tare suka yi sallah daga nan daddy yace masa "kaje gida sultan, give Walid your number, I will think about maganar ka and I will call you" daga haka ya shige gida, Sultan yaji babu dadi, he don't want to go home, to menene a gidan ma in yaje? Shi da daddy zai barshi ma anan gidan zai zauna, it will make him feel closer to Moon and also to his Mom.
Tunda mommy taga Daddy ya shigo da Sultan palo ta hau sama ta shige bedroom din ta, this is exactly abinda yasa ta dauke moon, tasan halin daddy, he is soft hearted like moon, da mutum ya zauna ya tsara su ya nuna musu cewa shi abin tausayi ne shikenan. People are not to be trusted, especially people like sultan. Dan haka ta yanke shawarar ba zata gaya wa kowa inda Moon ta ke ba har sai daddy ya fahimci cewa Sultan is totally not to be trusted. A bangaren daddy kuwa bayan sun rabu da sultan ya hau samansa ya tarar da abinci sa a dining dinsa, an jera komai amma babu mommy a gurin, bata taba yi masa haka ba kullum tare suke cin abinci in dai yana gari dan haka abincin kadan yaci yaji ya koshi. Ya kira wayarta taki dauka, mata kenan, shi a ganinsa itace fa mai laifi, ita ta boye masa yarinya amma kuma itace mai yin fushi? Shi me yayi mata? Abu daya ya saka zai rabu da ita shine yasan babu yadda za'ayi tayi harming Moon dan haka kamar yadda tace she is safe ya yarda she is safe din. Maganganunsu da Sultan ya fara dawowa dasu baya yana bin su daya bayan daya, maganar farko daya kamata yayi looking into itace ta yadda Moon ta zabi Sultan har tace ya zo yaga babanta, yasan halin Moon kuma ya yadda da ita, in dai har tace ta zabi sultan than there is something about him da ta gani, something good. Ya shiga bedroom dinsa ya dauko laptop dinsa ya kunna, the first place da ake samun information ya shiga, internet, amma duk abinda ya gani akan Sultan are not good, but why will Moon choose him? Shi abinda ya gani ma zai iya cewa gwara Munir akan Sultan, ya girgiza kansa, hakkin ubane ya samo wa 'yarsa miji na gari, yes Sultan indai labarin daya bashi gaskiya ne to negligence ya jawo ya zama abinda ya zama, amma wannan ba zai saka shi kuma ya dauki 'yarsa ya bashi ba. Emails dinsa ya duba yaga sun taru, kwana biyun nan he was very busy baya samun duba mails dinsa. Ya tashi yaje yayi sallah isha ya dawo, daya bayan daya ya fara bin emails din yana karantawa, bai jima ba yazo kan nata, "please daddy look into this" ya duba date din ya ga ranar da tabi Sultan bar ne amma da safe, ya bude document din data yi attaching, it is an amazing write up akan sultan, ta fara da tarihinsa, almost duk labarin da sultan ya bashi sazu, tayi bayanin duk bad characters dinsa, so she knows duk mugayen halayensa amma ta zabe shi? Sai kuma ta fara wani bayanin da daddy bai gane ba, a totally different side of Sultan, tana bayanin wadansu halayen wanda babu wanda zaice sultan yana dasu, tana dauko kowanne mugun hali data fada a baya tana justifying abinda yasa ya zama haka, tayi bayani akan yadda yayi rayuwa a america da irin yawan mutanen da ya rike tun a lokacin da ya kamata shi kansa ace rike shi ake yi, she then mentioned the orphanages, anguwannin talakawa a Abuja da Sultan ya rike, he is a hero to them, mutanen da ya samarwa aiki, yaran da ya saka a makaranta, talakawan da yake ciyarwa kuma duk ba tare daya nemi ko da godiya ne daga gare su ba, tace "he told me that doing something good makes him feel good, and that's what he wants, not people's praises" a karshen rubutun kuma tace "I believe this character a good person, but this life conditions makes him look bad in his eyes and the eyes of other people, but deep inside him he is good, very good"
Daddy ya zama speechless, ya rasa tunanin me zaiyi, internet ya koma ya fara searching abubuwan data fada akan sultan amma bai ga ko daya ba, me hakan yake nufi? Amma yasan 'yarsa, she will not lie like this, especially not to him, amma me yasa babu wanda yasan sultan da wadannan halayen data lissafa sai ita kadai? Sai kuma yayi tunanin halin mutane, they only see what's on the surface, dan haka kallo daya zasu yi wa Sultan suyi tagging dinsa as a bad person shi kenan kuma, su kuma wadanda yake good to mutane ne da basu da say a cikin al'umma, dadin dadawa kuma shi kansa sultan din bai yarda cewa shi mutumin kirki bane kuma he is set on anything da zai bata wa babansa suna. Sai da kan daddy ya fara ciwo sannan ya tashi ya je ya kwanta, har yanzu mommy bata zo ba, ya yanke shawarar he is going to ignore her for now, har sai ya gama binciken sa akan sultan.
Washe gari sai 12 ya sauko saboda jiya bai yi wani baccin kirki ba. Kuma yau ma tunda ya tashi yake making phone calls na meeting din daya shirya, yana yin breakfast ya dauki Walid a mota suka fita. Farko court din da mommy ta shigar da kara ya fara zuwa yace an janye karar dama misunderstanding ne kuma an samu fahimta. Private investigators ya hada har mutum goma, task din su shine yana son sanin komai akan Sultan, komai, including labarin rabuwar iyayensa. Sun charging dinsa kudi da yawa amma money is nothing to daddy dan haka ya signing musu check, half now half kuma sai sun gama aikin. Exactly one week aka kawo masa report dinsa, ranar har gari ya waye bai runtsa ba, hatta school report din duk kanin makarantun da Sultan yayi sai da aka kawo wa daddy. Komai na Sultan sai da daddy ya sani har abubuwan da ita kanta Moon bata sani ba. Sanda ya karanta ainahin dalilin rabuwar iyayen Sultan sai da ya dafe kansa yace "ya Salaam" gari na wayewa ya kira Walid yace "ka kira Sultan kace ina son ganin sa da yamma"
A bangaren sultan kuwa tun da ya bar gurin daddy gida ya koma ya shiga part dinsa ya kori kowa ya rufe kofa, he misses Moon sosai, dama zai samu ko muryarta yaji da yaji dadi, amma babu abinda zai yi dole ya jira kamar yadda daddy yace masa, tunda yace he will call then he will call din tunda baiyi kama da karamin mutun ba. Matsalar daya ce shine bai san abinda zai gaya masa in ya kira shi din ba, it will either be the end of his life or the beginning of his life. Jiran kuma anan za'a samu matsala, jira bashi da dadi ballantana ga mutum mai zuciya irin ta sultan. Kwana daya kawai duk yabi ya tayar da hankalinsa, he badly want a drink amma yana tsoron kar yasha daddy kuma ya kira shi, ko kuma ace moon tazo, ya tuna rokon da tayi masa akan kar yasha, menene ma abinda tace masa yayi instead? Ce masa tayi ya karanta alqurani. Ya tashi a hankali ya bude drawer da yake zuba books dinsa, anan yake aje alquranin sa tun wanda kakansa ya bashi, yana yawan daukoshi ya karkade ya mayar ya ajiye, karantawar ne dai baya yi. Ya dauko ya dawo kan gado ya zauna ya bude page din farko ya karanta fatiha. Ita kadai ya karanta yaji wani dadi a ransa, ya tuno sanda yana yaro a gurin kakansa wani lokacin tare suke karatu saboda kullum kakansa yana ce masa yana son yaji yana karatu saboda yadda yake lankwasa harshensa irin na larabawa. Ya ajiye al'quranin ya shiga toilet ya yo alwala ya zo ya shimfida sallaya yayi sallah raka'a biyu, sai kawai ya samu kansa da yin addu'a, abinda da ba yayi, ya roki Allah ya kawo haske a cikin rayuwarsa duniya da lahira, ya kuma yiwa Moon addu'a Allah ya kare ta a duk inda take sannan kuma Allah ya sa allkhairi a al'amuran su baki daya, daga nan ya jawo alquraninsa duk surorin saman sun bace masa duk da cewa da ya iya amma rashin karantawa yasa duk sun zube, na kasan dai ya iya su sosai saboda kullum yana karantawa a sallah. Nutsuwar da ya samu sai yaji tafi wacce yake samu idan yasa giya, ji yake kamar wani assurance na cewa everything will be OK. Tun daga ranar ya samu abinyi, baya zuwa ko ina yana daki sai dai a kawo masa abincinsa nan, kullum sai Amir ya shigo ya duba shi su dan taba hira ya fita, sosai Amir yaji dadin changin abokin nasa dan bai dauka zai taba zama calm akan rabuwarsu da Moon ba, Sultan ya bawa Amir labarin duk yadda sukayi da daddy nan suka hadu zaman jiran kiran daddy. Sai da akayi kwana takwas sannan kiran ya shigo, lokacin amir yana game da wayar Sultan, wayar ta fara ringing amir yace "wow, is this who I think it is?" Sultan ya kalli screen din yaga 'Walid' da sauri ya warce wayar ya daga da sallama, ba tare da Walid ya amsa ba yace "Daddy says to come after Asr" daga nan a katse wayar. Sultan ya jima yana kallon wayar a hannunsa, duk jiran da yake yi kuma sai yaji gabansa yana faduwa. Ya gayawa Amir abinda walid yace, ya tashi ya fara neman kayan sakawa, sai yau yayi nadamar rashin dinka manyan kayan da bayayi, da sam bai damu da duk irin shigar da yake yi ba amma yau sai yaji yana son yayi shigar kirki, da kyar ya samu kaya wadanda basu kama jikin sa ba. Amir yace zai rakashi, nan sultan ya kora masa warning kar ya saka matsatstsun kaya kuma ya tabbatar baya warin sigari, baki kawai Amir ya saki yana kallon Sultan, he is really changing, yace "since when did you care wanne kayan na saka?" Sultan ya bata rai yace "just do as I say kuma ka tabbatar ka cire wannan sarkar in ba haka ba bazan tafi da kai ba"
Da yamma suka je gidan, a palon baki aka sauke su aka kawo musu drinks da snacks, sultan da baya barin abinci amma yau sai ya samu kansa da kasa cin komai, so yake kawai daddy yazo yaji abinda zai ce masa. Basu jima ba daddyn ya fito cikin shiga ta alfarma kamar kullum, yana shigowa suka mike tsaye duk har sai da ya zauna sannan suka zauna suma tare da gaishe sa, ya amsa ba yabo ba fallasa sannan ya kalli Amir yace "Amir ko?" Amir ya gyada kansa, haka kawai yaga daddyn yayi masa kwarjini. Shima daddy ya karanta labarinsa da duk abinda Sultan yayi masa. Ya jima yana kallon Sultan wanda ya sunkuyar da kansa yana jiran abinda zaice, can daddy ya bude baki yace "Sultan, zaka iya dawowa nan gidan ka zauna a gurina?"
Episode Fifty Six : What You Sow
Sultan ji yayi maganar wani iri, sam ba abinda yayi tsammani ba. Ya jima kansa a kasa kafin yace "daddy bansan me zance ba" daddy ya gyada kai yace "I understand. Kafin ince zan baka Moon ko ba zan baka ita ba, dole ina so inga how far you can change, dan haka nake son chanza maka environment zuwa gurina. Amma da akwai sharadi, indai har ka amince zaka dawo gidannan dole zaka bi sharuddan zaman gidan nan, na farko babu yawo, zaka iya fita iyakacin cikin gari amma in dai zaka bar gari sai na sani kuma sai na amince, a cikin garin ma duk inda kake in lokacin cin abinci yayi zaka dawo gida saboda tare muke cin abinci a gidannan breakfast lunch dinner duk tare muke ci, kuma duk inda kake 9pm tayi maka a gida, babu wayon dare. Sanna the most important thing, ba zanyi tolerating koda single drop of alcohol a gidan nan ba, kuma koda a waje kasha ba'a gidan nan ba zan sani kuma ni kadai nasan hukuncin da zan yanke maka. I also want a total change of friends daga gareka, Amir will still be your friend of cause amma shima in naga bashi da niyyar chanza hali dole zan raba ka dashi, ga Walid nan shine sabon friend dinka zan kuma gaya masa kar inji kuma kar in gani a tsakanin ku. Abu na gaba kuma gida na ba gidan 'yan dambe bane, ko da wasa kar inji ance ka daki wani a cikin 'yan aikin gidan nan, tsakanin ka dasu ya zama girmamawa da mutunta juna. Next thing is you will need a change of wardrobe, saboda kamar yadda nake yawo da Walid haka zan ke yawo da kai kuma ba zan ke shiga da kai cikin mutane da wannan shigar a jikin ka ba. Wadannan sune sharudai na, in kaga zaka iya yarda dasu then you are one step to getting Moon, in kuma kaga ba za ka iya ba shikenan sai ka chire ta a ranka Allah ya hada kowa da rabonsa" da sauri sultan ya dago yana kallon daddy wanda shi kuma ya dora kafa daya kan daya ya daiki jarida yana kokarin budewa, alamar ya gama magana kenan. Sultan wani iri yake jinsa, wani irin feeling mixed with kunya, tunda yake ba'a taba ce masa 'yi kaza ko kar kayi kaza ba' amma yau gashi daddy ya wanke shi tas kuma a matsayinsa na surukinsa to be. Da sauri Sultan yace "daddy na yarda, ni kam na yarda da duk sharudan" daddy ya ajiye jaridar yace "madallah da wannan hukunci, gobe da safe zanje fada da kaina zan nemi alfarmar dawowarka gidan nan a gurin mai martaba sarki" Sultan ya girgiza kai yace "ba zai ce komai ba, ba zai noticing ma bana gidan ba" daddy yace "whatever, hakkin sane a gaya masa, kuma ni da kaina zan gaya masa. Yadda muka yi dashi Walid zai kira ka ya gaya maka. You can go now" Sultan ya kasa tashi, shi maganar bata ishe shi ba, shi da za'ayi ta masa fada so yake yi, can ya dan taba Amir yayi masa rada "ask him ina Moon take" Amir ya dan yi gyaran murya yace "daddy ko zamu samu ganin Moon kuwa" ba tare da ya kallesu ba yace "you will see her when the time is right" still sultan bai tashi ba, he have one more question, ya matsa gaban daddy sosai yace a hankali "daddy, dan Allah a cikin informations din da kake dasu, I want to know, did my parents.... " sai kuma ya kasa karasa maganar, daddy ya ajiye takardar hannunsa sa yace "ina jinka" sultan ya hadiye yawu yace "did my parents marry before...... Did they marry kafin su haife ni?" Daddy ya jima yana kallonsa ya kasa magana, tausayin yake ji har cikin ransa, jin daddy bai yi magana ba yasa Sultan ya mike tare da cewa "thank you daddy, dama ina so ne kawai in sani, I always thought wannan shine dalilin da yasa babana baya sona" daga haka yayi hanyar fita, har ya kai bakin kofa daddy ya kira sunan sa, ya tsaya ba tare da ya juyo ba saboda wani irin zafi da yake ji a ransa, daddy yace "sultan iyayenka sunyi aure kafin su haife ka, you are a legitimate child, abinda ke tsakanin ka da babanka is totally different from haihuwarka" Hmmm
Kamar yadda daddy ya fada haka ya aikata, washegari yaje fada akayi masa iso gaban mai martaba sarki, bai yi tsammanin zai gane shi ba amma sai yaga ya tare shi sosai da fara'a da wasa da dariya yace "Muhammad baka da kirki, ace kana garin nan da iyalinka amma ba ka zuwa mu gaisa? Kasan ni nauyi yayi min yawa bazan iya ziyarar abokanai ba" daddy yayi murmushi yace "Allah ya taimake ka ai ni ma ba zaman garin nake sosai ba, kuma in dai nazo to abubuwa sukan yi min yawa har sai na koma. Amma ayi min afuwa, in sha Allah zan ke lekowa lokaci zuwa lokaci" Har palon da yake barkar manyan bakin sa ya saka aka shiga da daddy, nan suka zauna gaba dayan su akan carpet suka fara hirar yaushe gamo da labarin karatun su da friends dinsu wadanda yanzu kowa ya kama gabansa. Daddy yayi mamaki sosai yadda yaga takawa ya zage sosai yana hira da dariya, saboda shi ya dauka maganar da zasuyi formally zasu yi ta maybe a gaban mutane ma, ashe dai Sadiq din is still the same person da ya sani kawai dai nauyi ne ya hau kansa yanzu. Anan suka zauna har aka kawo musu lunch sam daddy bai lura da yadda lokaci ya tura haka ba, he totally can't believe cewa wannan elegant mutumin shi yayi raising Sultan. Da kansa mai martaba yayi serving dinsu a plate daya suka ci, suna cikin ci Abbas ya shigo a nutse yazo ya gaishe su sosai sannan ya fada wa babansa sako cikin girmamawa ya fita. Daddy yayi noticing wani abu, Abbas totally baya kama da Sultan, ba zaka taba cewa 'yan uwa ne ba. Sai da suka gama sannan daddy ya gyara zama yace "Allah ya taimaki sarki magana ce ta kawo ni. Akan dan mu Sultan" daddy ya fada yana kallon fuskar takawa, abinda yayi tsammani kuwa shi ya tarar, just mentioning sunan sultan ya goge dukkan fara'ar dake fuskar takawa, komawa yayi kamar bai taba dariya ba. Yace "Wani abun yayi?" Daddy yace "babu abinda yayi ran sarki ya dade, ina neman alfarma ne in da hali ina so ya koma gida na da zama" Takawa yace "saboda me?" Daddy yace "ba wani abu kawai mun hadu da shine sai naga kusan sa'an yaron wajena ne walid shine sai naga ina sha'awar in hada su a gurina for sometimes, in ka amince of cause" Takawa yayi shiru yana shan lemon hannunsa, har daddy ya fitar da ran cewa ba zai yi magana ba sai kuma yace "you can do with him as you wish. Kawai dai ka tabbatar duk abinda ya aikata maka kai ka jawo mu babu hannun mu a ciki, kuma ka tabbatar duk abinda yayi kar ka danganta shi da mu" daga haka ya ajiye cup din hannunsa ya mike tsaye yace "in ka kammala da akwai servants a waje zasu raka ka motar ka. Na gode da ziyara Allah ya bar zumunci"
I
Da yamma Sultan yaji wayar Walid da sakon sarki ya masa maganar daddy, Sultan sam ya kasa tantance me yakeji a ransa, few things dinsa ya dauka ban da kayan sawa tunda daddy yace baya son irin su. To shi yanzu ina zai iya saka wata shadda ko yadi ne kam. Bashi ma da tailor. Yana zuwa gidan ya tarar da walid da Habeeb suna jiransa a compound, direct part dinsu suka wuce dashi fuskokinsu babu yabo babu fallasa dan sukam sam basa murna da wannan hukuncin na daddy. Four bedrooms ne dama a part din, sai palo mai hade da dining duk da dai ba mafani suke da dining din ba sai dai in bakon da ba za'a shiga dashi main palo ba. Walid ya bawa sultan key din daki daya da kuma spare key din palon. Sultan ya bude dakin ya shiga, ba laifi yana da girma, da gado da dan karamin closet sannan sai toilet. Yana gama duba dakin ya fita yana tambayar ina masu share share aka nuna masa su yace "dan Allah aron kayan cleaning nake so" da mamaki suke kallonsa, suka ce "ai mu zamu gyara maka" ya girgiza kai yace "thank you, zanyi, ba wani abu" Sultan sam bai yarda wani ya gyara masa dakin saba saboda gani yake ba za'a taba yi masa dai dai ba, tunda ya fara aiki bai gama ba har magrib, sannan ya shiga toilet yayi wanka ya chanza kaya ya fito da sauri, yana fitowa yaji dad yana cewa a kirashi su tafi masallaci, tare suka yi sallah suka dawo gida, suna zuwa suka zarce main palo, shi dai Sultan duk wani iri yake jin sa, yana zuwa masallaci wani lokacin amma bai taba zuwa tare da mahaifinsa ba ballantana ace wai harda siblings. A palon suka tarar an jera abinci a dining amma sam babu mommy, basu yi magana ba saboda kwana biyun nan haka take yi, kuma daddy ma baya son su hadu da Sultan har sai yayi mata magana da kansa. Suka zazzauna a dining din suna kallon kallo, can daddy yace "Sultan ai sai kayi representing Moon, kayi serving din mu" nan da nan sultan ya washe baki har kunne, ance yayi representing Moon, ya mike har da nade hannayen riga ya fara lafta musu abinci, walid yayi dariya yace "wannan uban abincin duk kana tunanin zamu cinye?" Sultan yace "why not?" Sai da kowa ya rage nasa abincin amma sultan ya chinye nasa tas. Daddy ne ya fara tashi ya koma palo, sultan ne na karshen gamawa, nan ya fara kokarin kwashe kaya, Habeeb yace masa "ka bar shi fa, za'a kwashe ai" shi Sultan ya saba da yiwa kansa komai, tunda aka kaishi america shi yake yiwa kansa komai, daya dawo Nigeria ma haka. Ya karaso palon, har zai zauna sai kuma yaji ajikinsa kamar zai shiga hurumin da ba nasa ba, sai ya mike zai fita, yana jin ba dadi a ransa, daddy ya kira shi ya dawo ya zauna yace "ina maganar kayan sawa da muka yi da kai?" Sultan ya dan bata rai yace "daddy ni ban taba dinki ba, ban masan inda ake saida yadikan ba ballantana wani tailor, amma in na samu zanyi" daddy ya kalli walid yace "gobe ka kai shi gurin tailor din mu ya auna shi, sai kuma ku shiga kasuwa kuyi siyayya" sai kuma ya juya gurin sultan yace "zaka iya ci gaba da saka kananan kayan ka a gida, amma duk sanda zamu fita ina so in ganka da manyan kaya da hula" sultan ya shafa kansa, lallai akwai rigima kenan, shi kam rabon da ya saka traditional hula tun kakansa yana da rai. Daddy ya juya kan su walid yace "ga Sultan nan, ina so ku rike shi tamkar shima dana ne da baya gurin mu amma yanzu yazo, kar inji kar in gani a tsakanin ku" duk suka amsa. Daddy ya sake cewa da Sultan "yi min bayani akan yadda kake gudanar da aikin ka" nan sultan yayi masa bayanin yadda yake yi, daddy yace "abinda za ayi yanzu shine, head office zaka bude, ka dauki ma'aikata sosai, ka saka wa gurin suna yadda zaka ke samun contract sosai. Na duba ayyukan ka naga suna da kyau sosai dan haka nima zan kara yi maka advertising dan kake samun contract a projects din government. Ina ganin hakan shi zai kara rage kama yawo, in ka samu abinyi zaka fi zama a guri daya" sosai sultan yaji dadi, babu wanda ya taba bashi shawara akan me zaiyi da rayuwarsa ko aikinsa. Ji yake yi wata soyayyar daddy tana shigarsa. Daga nan suka fara hirar su abin sha'awa, a tsokani wannan2, har mamaki sultan yake dama haka family yake? Dama haka uba yake a cikin 'ya'yansa?
Bayan sun tashi daga hirar sunyi sallah isha daddy ya hau saman su, dakin mommy ya shiga ya tura kofa, tana zaune tana aiki a computer, taji shigowarsa sarai amma bata dago ta kalleshi ba, a ransa yace 'wai ita menene problem dinta ne?' A bakin kofar ya tsaya yace "Fatima, ina so in sanar miki cewa Sultan ya dawo gidan nan da zama" zumbur ta mike har tana ball da system din gabanta ta karaso kua dashi da sauri tace "Sultan fa kace?" Sai kuma hawaye "haba dear, ya zaka dauko yaro kamarsa ka hada shi da yaran mu, so kake suma ya bata mana su kamar yadda ya so ya bata Moon? Dan Allah kayi hakuri idan purnishing dina kake dan na daukr Moon, wallahi zan dawo da ita, please ka kore shi daga gidan nan" daddy ya girgiza kansa yace "bazan taba korarsa ba sai dai in shine da kansa yace zai tafi, wanda bana jin zai ce haka, kuma badan kinyi min laifi bane yasa na kawo shi nan ba, a'a nayi haka ne dan naga wani chance ne na samun lada Allah ya dora akan cinyata, shi da na kowa ne, baka san wane ne zai ji kanka ba wata rana, kuma ita rayuwa duk abinda ka shuka shine zaka girba, ina so in shuka alkhairi yadda ko bayan raina zuri'ata zasu girbi alkhairi na. Ban gaya miki ba har sai da ya dawo saboda ina son kini zafin da naji nima sanda baki gayamin kin dauke moon ba har sai da kika aikata din. Yanzu bazan matsa miki cewa ki dawo da ita ba har sai na tabbatar da changes din da nake so in gani agurin sultan tukunna" daga haka ya juya yayi tafiyarsa. Mommy ji tayi gaba daya duniya tayi mata zafi, lallai daddy is even softer and weaker than she thought. Amma babu komai, ta tabbatar cewa Sultan will teach him a lesson. Ita kuma ba zata dawo da Moon ba har sai daddy ya yi learning lesson a gurin sultan tukunna.
Cikin sati daya Sultan ya warware a gidan Ambassador MD. Ba laifi sun fara sabawa da su Walid, in da suke jinjina masa akan tsaftarsa dan gaba daya part dinsu ya chanza fasali kamar ba shi ba, har palon sai da yayi rearranging ya chanja labilaye da carpet. Daddy ya samo masa building din da zai bude head office dinsa, wanda ya fara dauka aiki shine Amir, tunda dama tare suke aikin su, nan da nan ya zama busy wajen gyaran gurin da interviewing maaikata, sai yanzu ya kuma gane abinda daddy yake nufi, dan in yana aiki sam mantawa yake yi da komai ballantana har yayi tunanin shan giya, ko a gida kuma har yanzu yana bin shawarar moon ta karatun Alqurani duk sanda ya ji yana son alcohol. Shi kansa yana jin chanji akansa, dan nutsuwarsa ta karu sosai. In dar har baya wajen aiki to suna tare da daddy, dan duk inda daddy zaije tare suke zuwa dashi da walid, har gurin manyan mutane, nan ya fara koyon saka manyan kaya da yadda ake gaishe da manyan mutane. Rannan har gurin president suka je, kuma he found it very interesting dan babu wanda yayi masa kallon wulakanci babu wani security daya hana shi shiga ballantana suyi rigima. Kuma wani abu da daddy yake yi shine, duk inda suka je sai ya gabatar da sultan a matsayin babban dan sarkin abuja, duk sai sultan yaji banbarakwai in yaga mutane suna bashi respect
A gida kuma malami daddy ya dauko na karatun addini, bai ce saboda Sultan ya dauko ba sai yace yaga duk kowa a gidan ya watsar da islamiyya dan haka ga malami nan duk weekend zai ke zuwa za'ake karatu, har maaikatan gidan duk haduwa ake ana daukan karatu. Nan sultan yaga chance dinsa ya dauko alquranin sa ya fito, surorin daya manta nan duk suke bi suna tilawa tare da malam. A hankali karatunsa yake dawowa. In akayi dori ranar assabar ran lahadi kuma sai ayi tafsir, ko ayi karatin sauran littattafan addini, sai abin ya koma kamar discussion, kowa ya fadi abinda ya sani ayi masa gyara, in mutum yana da tambaya yayi. Sultan kam ya bude kunnuwansa sosai yana daukar karatu. Matsalar sultan yanzu daya ce, he terribly misses Moon. Kullum yana so ya tambayi daddy labarin ta amma baya so daddyn ya bata rai ko yaga gazawarsa. Kullum da daddare sai ya dauko bathrobe dinta daya dauka a toilet a america, da ita yake bacci yana jin kamshinta. Idan yana zaune shi kadai kuwa sai dai yayi ta kallon pictures dinsu da videos dinsu yana ta murmushi. She really is a Moon, her arrival in his life have brought light to his darkness.
Ina ma iyayen mu zasu zama kaman daddy? Allahumma Ameen.
Episode Fifty Seven : What You Sow 2
A 'yalleman kuwa tunda Munir yayi wa Hajja waya da sassafe ya hada mata karya da gaskiya ya gaya mata. Suna gama wayar ta fita daga part dinta ta tsaya a compound ta rafka wani uban salati "na shiga uku ni zuwaira yau wanne mugun labari zanji haka" a tare da baffa da inna suka fito daga part dinsa suna tambayarta "lfy? Me ya faru? Waye ya mutu?" Ita kuwa kuka take tana fyace majina da bakin zanin ta, "dama babu abinda ban fada ba aka ki daukan magana ta saboda bani na haifi muhammadu ba kuma shine dan gatan gidan nan, dama gata ai mugun abu ne, babu abinda yake haifarwa sai nadama. Wanda duk baiji bari ba ko ai zai ji oh'oh" inna tana jin zancen muhammadu ta ja da baya ta tsaya tana jiran taji alkaba'in da zai biyo baya. Baffa ma bari yayi sai da hajja ta gama sambatun ta sannan ya kuma tambayarta "me ya faru da muhammad din" Hajja ta duba taga duk yaran gida sun taru a compound suna sauraren abinda ake yi sannan tace "yaran nan babu yadda banyi ba akan ayi musu aure akaki, aka nuna min ban isa ba, to yanzu gashi nan abinda ake gudu ya faru. Manniru ne yayo min waya dazu hankalinsa a tashe, yace tunda yarinyar nan ta dawo kasar nan ta juya masa baya, in yaje gidan nasu sam ba'a barin shi ya ganta, in ya kira ta a waya bata dauka, to jiya da daddare wajan karfe daya ya fita neman abinci saboda yaje gidan sun hana shi abinci shi kuma yunwa ta dame shi, kawai yaga yarinyar nan a titin Allah tana yawo da dan skirt, ta sha giya tayi mankas ko tafiya bata iyayi sai wadansu maza ne suka rirriketa, shima kansa da kyar ya gane ta, kuma ya kira walid ya gaya masa, ashe sun riga sun san halin da yarinyar take ciki shi yasa basa barin ya ganta. Daya bisu gidan ya na tada maganar saboda ayi wa tubkar hanci sai walid da habibu suka taru suka yi masa dukan tsiya suka ce in dai ya sake ya fada wa mutane sai sun nakasa shi" wani irin jiri inna taji yana neman daukan ta, wannan wanne irin sharri ne munir ya shirya wa maimunatu? Palon ta ta koma ta zauna kanta yana bala'in sara mata, yaran gidan kuwa tunda suka gama jin abinda hajja tace suka fara fita daya bayan daya suna shiga makota kai rahoto, baffa kasa cewa komai yayi dan shima jirin ne yake dibansa, Ma'aruf dan autan hajja wanda kuma shi kadai ne ya rage a gidan ne yayi saurin dauko kujera ya zaunar da baffa. Sai da baffa ya mayar da numfashin sa sannan yace "hajja kin tabbatar munir ba karya yayi miki ba?" Hajja ta matso kusa dashi tace "yaya zaiyiwa yarinyar da yake so karya? Ita fa ya zaba ta zama uwar 'ya'yansa ta yaya zai yi mata sharri kuma? Ban taba ganin so na gaskiya irin wanda yaron nan yake yiwa yarinyar nan ba, duk da abinda ya gani da idanuwansa fa cewa yayi shi so yake ma a gaggauta auren ko Allah zai sa auren ya gyara ta" still zuciyar baffa taki yarda da maganganun hajja, yana kallon fuskar maimunatu a zuciyarsa, duk acikin jikokinsa yana son 'ya'yan muhammadu, kuma duk a 'ya'yan muhammadu maimunatu ta daban ce, ga tarbiyya, ga ladabi, ga fara'a, ga shiga ran mutane sannan uwa uba ga son 'yan'uwanta. Sam bata da girman kan wai babanta wani ne, duk sanda tazo sai ta zaga 'yan'uwa kai hatta 'yan aikin gidan nan kawayenta ne dan wani lokacin a cikin su zai ganta tana wasa. Hajja ta tankwashe kafar ta ta cigaba da zuba zance "ya gayamin ai ba laifin ta bane, wani yaro ta hadu dashi lalatacce shine ya bata ta, su kuma iyayen sun dauki son duniya sun dora mata shi yasa suka kasa raba su, dan ce musu tayi ko yanka ta za suyi ba zata rabu da yaron ba. Ni dai shawara ta shine, ka kira muhammadu ka gaya masa zama maza ya kawo mana yarinyar nan gurin mu, tana zuwa sai mu sata a lalle ayi auren nan kowa ya huta. Shi kuma wannan yaron da yace yaji ya gani zai aure ta a haka Allah yayi masa albarka" baffa da har yanzu kansa bai gama juya masa ba ya aika ma'aruf ya dauko masa wayarsa, amma maimakon ya kira muhammadu kamar yadda hajja tace, sai ya kira Aliyu, aliyu yana dauka ko gaisawa basu yi ba yace "Aliyu kaga abinda ka jawo mana ko? Taurin kanka ne ya hana ayi auren nan da yanzu duk wannan abin bai faru ba, to kasani ni babu ruwana, tunda kai ka jawo sai kasan yadda zakayi ka warware" yana kaiwa nan ya kashe wayar ya mike ya shige dakinsa, hajja ba haka taso ba dan tasan Aliyu sam ba zai taba goyon bayan munir ba, saboda kamar yadda take fada tace ya tsane shi saboda ba uwarsu daya da wanda ya haife shi ba. A bangaren inna kuwa tana shiga dakinta ta dauko wayarta ta kira mommy, sai da ta katse ta sake kira sannan mommy n ta dauka, itama ba tare da sun gaisa ba tace "Fatima me ya faru tsakanin manniru da maimunatu?" Cikin inda inda mommy tace "inna babu komai wani abu akace ya faru?" Inna ta bata rai sosai tace "Fatima dani fa kike magana ba da wani ba, cewa nayi me ya faru tsakanin munir da moon?" Mommy kuma sai kuka, sai da tayi me isarta sannan ta bawa inna labarin duk abinda ya faru a lokacin. Inna salati ta saka tace "amma fatima ya za'ayi ace yarinya tana tare da saurayi har tsahon shekara guda amma ke a matsayinki na mahaifiyarta baki sani ba?"Mommy tace "inna wallahi nasan tana tare da wani, amma bansan ko waye shi ba, da nasan yaron nan ne wallahi da tuni na raba su. Ita yarinyar nan kinsan halinta, har cikin zuciyarta gani take taimaka masa take yi" nan inna ta gaya mata duk abinda hajja take fada, mommy sai da ta sake wani kukan sannan tace "wallahi inna ba haka akai ba" kafin ta cigaba da magana inna ta katseta tace "na sani ai, ni nasan maimunatu, nasan abinda zata aikata da wanda ba zata yi ba. Yanzu dai zamu jira muji abinda baffa zai ce" Suna gama wayar uncle Aliyu yana kiran inna, saboda kiran da baffa yayi masa, tambayarta ya shiga yi akan menene ya faru, nan inna tayi masa bayani, nan take ransa ya baci yace sai ya babballa munir, da kyar inna ta lallabashi, maganar yaron da akace suna tare da moon kuma yace zaije har abujan yayi bincike yaji me ake ciki, saboda yasan da maganar yaron da moon tace masa tana so, tace masa dan sarki ne, kuma yasan akwai dan sarkin abuja tantiri. Da kadan da kadan magana take watsuwa ya a garin yalleman, amma ga mamakin hajja duk wanda aka gayawa maganar tun kafin a karasa ma yake cewa karya munir yake yi, da yawa daga cikin 'yanuwa cewa suke yi dan yaga har yanzu bata sonsa ne shi yasa zai yi mata sharri dan ayi mata dole, kowa yasan halin maimunatu kuma kowa yasan halin munir, shi halinka kuma shine jarinka, mutane kuma sune rahamarka. Shi yasa bature yake cewa 'it is good to be good' ni kuma nace 'it pays to be good'
Uncle Aliyu bai samu zuwa abuja ba saboda aiyuka da suka yi masa yawa sai bayan sati biyu, yana zuwa baije gidan ba ya sauka a hotel, yaje unguwar a wayance yake tambayar mutane abinda suka sani tsakanin sultan da moon, amsoshin da yake samu sam basu yi masa dadi ba. A karshe dai ya kira ambassador inda shi kuma ya gaya masa ai yana gari ma. Da yamma yaje gidan, a compound ya tarar da ambassador tare da walid da kuma wani kyakykyawan yaro sun saka kaya iri daya shi da walid, har ya zauna yana kallon yaron dan sam bai san shi ba, suka gaishe shi tare shi da walid, uncle Aliyu ya dan tsokani walid sannan suka shiga gida. Sai a lokacin ya gaishe da yayan nasa, sannan yace "wannan yaron kuma fa yaya a ina ka samo shi?" Fuskar ambassador dauke da murmushi yace "Sultan sunan sa, shine babban dan mai martaba sarkin Abuja" da mamaki uncle Aliyu ya kalleshi yace "Sultan? Sultan din moon?" Daddy shima da mamaki yace "kasan shi ne?" Uncle aliyu yace "a'a bansan shi ba. Amma maganar sa ce ta kawo ni abuja. Sai dai kuma yadda ake gaya min labarinsa ba haka na ganshi ba" daddy ya gyada kai cikin gamsuwa yace "ai ba haka din yake ba, yanzu ne ya zama haka" nan ya fara bashi labarin sultan dalla dalla, a karshe yace "labarin yaron ne ya saka naji tausayinsa kuma nayi alkawarin gyara masa yaruwarsa" uncle Aliyu yanu tausayin rayuwar sultan sosai, amma duk da haka sai yace "gaskiya yaron abin tausayi ne, amma duk da haka yaya kana ganin ya dace mu dauki maimunati mu bawa yaron da yake da past kamar nashi?" Daddy ya gyara zama yace "shi aure wannan nufin Allah ne, yanzu ba maganar auren su ake ba tukunna, maganar chanzawa yaron yaruwa ake yi. Kuma ni sam ba domin maimunatu nake yi ba, ko da ace a yanzu sultan zai ce ya fasa auren moon to ba zan fasa ko daya daga cikin abubuwan da nayi niyyar yi masa ba". Suna cikin maganar sai ga sultan ya fito daga part dinsu, ya chanza wanka, yazo kusa da daddy ya durkusa yana shafa kansa yace "daddy zan dan fita" daddy yace "OK, Allah ya tsare. Make sure ka dawo kafin dinner" sultan yayi dariya yace "I won't miss it for the world" shima daddyn dariya yayi sanin halin sultan akan abinci, Sultan yayi wa uncle Aliyu sallama sannan ya fita. Har lokacin dinner uncle Aliyu yana nan, sosai yaji yana missing moon amma daddy yace kar ya kula mommy akan maganar ta, a dinner din duk su Habeeb har daddy suka saka sultan a gaba da tsokana shi kuwa ko a jikinsa sai zuba lomarsa yake yana kuma zuba surutu, sai dai in sun hada ido da uncle Aliyu ya dan sunkuyar da kai alamar kunya. Nan take uncle Aliyu yaji sultan ya shiga ransa saboda Sultan yana da shiga rai kamar Moon.
Daga Abuja direct yalleman uncle Aliyu ya koma, ya samu baffa ya tabbatar masa da cewa duk maganganun Munir karya ne, yace masa kawai yayi mata sharri ne dan yana so a tirsasa ta ta aure shi. Ai kuwa da baffa ya tisa munir a gaba da fada kamar zai dake shi da kansa, dan har hajja sai da fadan ya shafe ta. Shi dai munir yasan ba duk maganar sa ce karya ba, akwai 'yar gaskiya a ciki, amma fur kowa yaki sauraronsa. Yana fita waje kuwa suka kwashi 'yan kallo da nuraddeen wanda tun da yaji maganar yace wallahi duk sanda munir ya shigo gari sai jikinsa ya gaya masa tunda yayi wa Moon sharri irin wannan. Kaikayi ya koma kan mashekiya.
Wannan kenan;
Sultan yana kwance a daki daddy ya kira shi, ya daga da sallama, daddy yace masa "Maza ka shirya ka fito zamu tafi Niger mu dauko Moon" rasa masar da zai bayar yayi dan ji yayi komai ya tsaya masa, sai da daddy yace "kaji abinda nace kuwa?" Da sauri yace "yes, daddy" ya mike yana tunanin anya yaji abinda yace din kuwa? Ya daiji kamar ance Niger kuma ance Moon, sai a lokacin tunanin shi ya dawo, Moon zadu je su dauko a Niger, what? It means yau zai ganta kenan? Wani tsalle yayi ya sauko daga kan gado ya fito palo yana neman walid dan yayi confirming maganar, yana fitowa walid yana shigowa da sauri, ya kalle shi yace "a haka zaka je dauko amaryar taka" Sultan ji yayi kamar kafafuwan sa ba zasu dauke shi ba, da gudu ya koma daki, sai kuma gashi ya sake fitowa da gudu yace wa walid "yau zamu dawo ko kwana zamu yi?" Walid ya duba agogonsa yace "sai dai mu kwana ai, it is already late, dan dai daddy ya matsa tafiyar nan ne amma da mun bari kawai sai da safe" Sultan bai ji karashen maganar ba ya koma dakin, ba'afi minti biyar ba sai gashi ya fito ya shirya da jaka a hannunsa, babu walid a palon dan haka ya fita waje ya saka kayansa a motar da zata kai su airport, ji yake kamar yaje ya chichchibo duk wanda za'ayi tafiyar dasu suzo su tafi, gani yake kamar duk suna sane suke lakaki. It seems like eternity kafin su mommy su fito, yana ganin ta yaji jikinsa yayi sanyi, bata taba yi masa magana ba kuma ko sun hadu a compound in ya gaishe ta bata amsawa, bai kuma taba ganin ta a palo ba shi kuma bai taba tambayar dalili ba. Yaji dadi da ba mota daya zasu shiga ba, shi da daddy, ita kuma da Walid. Sai gab da magrib suka je airport, private jet din daddy suka hau, kafin isha suka sauka a Niamey, aka kai su wani gida shi da walid suka sauka, shi dai kawai jira yake yi suje gurin moon, sai da zasu kwanta walid yake masa bayanin moon fa ba'a nan take ba, tana agadaz amma sun taho suna hanya, goben ma sai wajen azahar zasu karaso. Ranar sultan yadda yaga rana haka yaga dare, wani irin farin ciki yake ji da wani irin son Moon a ransa, sannan kuma da fargaba, what if yanzu kuma tace bata son shi? Tunda shi ya jawo mata duk wannan wahalar da ta sha, yasan tana cewa bata son shi kuma daddy zai kore shi daga gidansa. He will then be back to square one. Washegari tunda yayi breakfast yake zaune, gabansa ne kawai yake ta faduwa, sai can bayan azahar Walid ya shigo yana dariya, sultan yasan me zai ce masa "sun zo, baka je kayi mata oyoyo ba" Sultan ya zauna akan kujera yana rikr kansa, Walid yayi dariya yace "jarumtar kenan? Kar ka bani kunya mana, ni da na saka ran zaka fita a guje kaje ka ture daddy ka rungumeta?" Hararar sa kawai Sultan yayi dan shi kadai yasan me yake ji a ransa. Walid ya sake cewa "kaga ni na fita yawo, in ga kama ragwantar ka fita driver zai kaika inda suke, zan same ku a can" Sultan bai iya fita ba har sai da daddy ya kira shi a waya yace sun kusa gama wa fa, su zo su same su. Da sauri ya dan watsa ruwa ko zaiji garau, ya chanja kaya yana kallon kansa a mudubi, maybe ma cewa zata yi bai yi kyau ba, ya chire hular ya ajiye sai kuma ya sake dauka ya dora. Sai kuma yaji haushin kansa, me yasa yake nin tsoron wannan 'yar mitsitsiyar yarinyar ne. Koma me zata ce ta fada din. Ya fita aka kai shi can gidan, ya fito ya jingina da jikin mota yana jiran fitowar su, wayarsa ya dauko yana daddan nawa amma sam ba wai yasan abinda yake yi bane, ji yayi ana kallon sa, kuma har cikin jinin jikin sa yasan cewa itace kuma yasan daga wanne side take, a hankali ya daga kansa, cikin idonta ya tsinci nasa. Ya Allah. He had no idea how much he missed her sai da ya ganta. Karfin zuciya ne kawai ya saka ya tsaya a inda yake, ji yayi kamar yayi abinda walid yace, yaje ya rungume ta, amma kuma anya rungume budurwa a gidan surukai dai dai ne? Ta rame, sosai, Allah ne kadai yasan abinda zai yiwa wanda duk ya takura mata da zai ganshi. Sama sama yaji daddy yana magana amma bai fahimci me yake cewa ba, sai da ya sake maimaitawa sannan ya fahimta, wayarsa ya dauko ya kira walid ya gaya masa sakon daddy sannan ya bude wa daddyn kofa ya shiga ya rufe da sauri ya juyo inda take tsaye, Allah yasa bata bace ba, tana nan kuwa tamkar wadda aka dasa, cikin kwayar idonta ya kalla ya fahimci cewa he have nothing to fear, kujerar mulkinsa tana nan daram a zuciyarta. Da sauri ta bar gurin ta tafi daya motar ta shiga, sai bayan data shiga sannan ya lura daddy ya sauke glass din window dinsa yana kallon shi, ya shafa kansa da sauri yana sunkuyar da kai kamar munafiki sannan ya shiga gaban motar ya zauna. Walid ya karaso suka hau hanyar airport.
Episode Fifty Eight : I Missed You
Na lumshe idona ina addu'ar Allah yasa shi dinne ya gani ba wai gizo yake yi min ba, dan ganin nasa ya taba min wani guri a zuciya ta wanda bansan yadda zanyi ba idan ba shi bane. Muna zuwa airport muka fito, mommy ce ta fara shigewa jirgi, daddy ya tsaya suna sallama da mutane, sai lokacin na samu damar ganawa da yaya Walid dan a mota tsoron mommy ya hana ni magana, na rungume shi tsam a jikina ina ajjiyar zuciya "I missed you" ya rabani da jikinsa yace "I missed you too sweetie pie" ta gefen idona na hango sultan yana tahowa gurin da muke, kara kankame yaya Walid nayi ina runtse idona, 'Oh Allah, give me the strength kar inje inji kunya a gaban mutane' na kasa kallon inda yake dan nasan zan iya loosing control, muryarsa naji yana cewa "to cika ta haka, ai an gama oyoyon" shi dinne dai, dan muryar sa ce wannan. Ya walid ya dafa kafaduna da hannayensa duk biyun yace "anki din, sai ka bari in an daura muku auren sai kayi min iko akanta amma yanzu tawa ce. Ni ban taba ganin ma suruki marar kunya irin kaba sultan, babban wa ai uba ne, ni ne fa madaurin auren ta, inna ga dama sai ince bazan bayar ba" yaushe Sultan suka fara wasa da Ya Walid? Last time I check ya Walid ya mari sultan. Wata dariya sultan yayi yace "kayi kadan yaro, ni iya kacin sanina na girme ka, dan haka kai ya kamata ka ke yi min biyayya" ya walid ya kama hannuna muka tafi jirgi, har yanzu na kasa kallon sultan, sai da muka fara hawa steps din sannan na juyo ina tunanin kar mu tafi mu barshi, ina juyo wa muka hada ido, nayi sauri na dauke kaina.
Chamber biyu ne da jirgin sai gurin pilots, daddy da mommy suna chamber din farko, mu kuma mu uku muna chamber ta biyu. Tunda na zauna har jirgin ya tashi ban daga kaina ba, duk jina nake a takure saboda idanuwan da sultan ya dora a kaina ko kiftawa baya yi. Ji nayi kallon yayi yawa na dan daga kaina kadan sai naga ashe ido hudu ne a kaina ba biyu ba, yau naga ta kaina zasu chinye ni danya. Ya walid yace "kin ganki kuwa? Wannan ai kece ifritu minal jinni. Wannan irin rama haka? Me Aunty Zaliha take miki?" Ni dai bance komai ba na rufe fuskata da hijab dina. Ina jin Sultan yana ce masa ya tashi ya koma gurin su Daddy, ya Walid yace "saboda me? Duk abinda zaka gaya mata ka gaya mata a gabana. Suma wadancan din couple ne, gwara ma ku ba aure ne da ku ba, babu wani abu da zakuyi wanda ba zan iya gani ba" su kayi ta maganganun su ina jinsu bance musu komai ba, shi Sultan yana ta insisting sai Walid ya tashi ya bamu guri shi kuma yaki. Nadan bude fuskata kadan na kallesu naga basa kallona sai na gyara zamana na bude fuskata sosai. A hankali nace ina kallon sultan "how is your leg?" Duk suka jiyo suna kallona da mamaki Sultan yace "What?" Na sake maimaitawa ina kallon kafarsa. Still bai gane mai nake nufi ba, nace "kafarka da kaji ciwo rannan, how is it?" Dariya yayi sosai, da alama yama manta da cewa yaji ciwon, yace "ta warke ai, tun tuni. Abinda ya kamata ki tambayeni shine how is my heart" ya Walid ya harare shi, ni kuma nayi murmushi ina sunkuyar da kai na kasa. Har muka sauka a Nigeria bamu samu munyi wata magana da Sultan ba, muna sauka muka tarar da motoci suna jiran mu, muka shiga sai gida. Tunda da na fito daga mota nake jin idanuwan sultan a kaina amma baki kallon inda yake da sauri na shige cikin gida. Ina shiga palo na tarar da yaran gida kowa sai murnar dawowa ta suke, nan na sha runguma har sai da jikina ya fara ciwo, da wayo na gudu na hau sama na shiga dakina, a gyare na tarar da dakin sai kamshi yake yi, na fada kan gado tare da lumshe idona, home sweet home, da sauri kuma na mike naje na bude window ina leken waje ko zan ganshi amma naga bayanan, to ko ya tafi gidan su? Toilet na shiga na kunna ruwa a tub na hada kumfa sosai, when was the last time I had a real bath? Na cire kayana na shiga ina sauke ajjiyar zuciya. Na lissafo irin wahalar da nasha, kuma duk akan Sultan amma yanzu wai gani gashi na kasa yi masa kwakwkwarar magana. Sai kuma na fara yiwa kaina tambayoyin me ya faru da bana nan? Ya akayi har su daddy suka karbi sultan har ya saba dasu sosai? Jin ana kiran sallar isha yasa na tuna ko magrib banyi ba, na dauraye jikina na fito, na bude kayana naga sunanan yadda na tafi na barsu sai dai daga alama an dan karkade su an sake gyaramin, na saka wasu riga da skirt ga mamaki na sai naga wuyan rigar yayi min yawa skirt din kuma yana zamewa, chafdi, gaskiya na rame da yawa, dole na saka doguwar riga nayi rolling mayafi na fita. Ina saukowa daga sama na tsaya da mamaki, Sultan again, dare dare a kan kujera a palo suna ta zabga musu da ya Habeeb, a tare suka juyo suka kalle ni, dif sultan ya dauke wuta ya daina magana, ya Habeeb kuma ya taso da sauri gurina yana cewa "welcome home, my parrot" nayi murmushi na karasa gurinsa, sai kuma ya rike hannuna yana kallon fuskata, dariya yayi yace "kinga yadda kika yi baki kuwa?" Na juya idona nace "tubarkallah, wannan yace da rame wannan yace nayi baki in ba so kuke ku chinye ni ba ai ya kamata ku kyaleni haka" daddy ne ya shigo Walid yana biye dashi a baya, duk muka gaishe da daddy ya hau sama, har lokacin sultan bai ce min komai ba sai kallo kamar zai chinye ni, dole na tashi na tafi kitchen na zauna ina kallon ana ta fita da kayan abinci, sai da naji daddy ya kuma saukowa sannan na kuma palon, still Sultan yana nan, muka tafi dining har dashi, sai kawai naga ya tashi yana serving din mu, what is happening ne ni maimunatu? Someone should start explaining. Har ya zuba min abincin kuma sai ya dauke ya sake karo min ba tare da ya kalleni ba yace "ki chinye wannan a karo miki wani" ji nayi duk suna dariya ni bansan dariyar me suke yi ba, daddy yace "yes, kina bukatar alot of food da kuma bacci ko kya yi kyan gani" a raina nace Daddy kaima harda kai ko? Allah ne kadai yasan shi kuma Sultan me zai ce min. Na dan fara cin abincin kamar bana so kuma sai naji taste din abincin ba zan iya resisting ba, nayi missing home da duk wani abu na home din, ya Habeeb yace "to 'yar agadaz, bamu labarin agadaz" na yi murmushi nace "sai dai in baka labarin anty Zaliha da samarin 'ya'yanta, dan su kadai na gani tunda naje agadaz din, ko kofar gate ban taba zuwa ba" nan aka koma hirar Niger da zafin garin, suna cewa zafin ne ya sakani baki. Tunda muke hirar Sultan baice mana komai ba abincinsa kawai yake ci, har ya gama yasha lemo ya mike tsaye, ina kallonsa muka hada ido nayi sauri na dauke kaina. Yace da Daddy "Daddy sai da safe" Daddy yace "Allah ya bamu alkhairi" ya dan jima a tsaye kuma sai ya tafi, naji bude kofar palo amma banji rufewa ba. Yaya habeeb ne ya fara taba ni yana nuna min hanyar waje, nayi kamar ban ganshi ba, ina jin yaya Walid yana yin dariya kasa kasa, sai kuma ya dan daga murya yace "na'am? Tana zuwa" sai ya ce a hankali "kamar naji sultan yana kiranki ko?" Shima yi nayi kamar bansan me yake yi ba amma fa ta ciki na ciki, a hankali Daddy yace "tashi kije" nace "yes Daddy" na mike a hankali kamar bana so nayi hanyar waje, amma fa a xuciya ta ji nake kamar in kwasa a guje. Ina zuwa kofar falon na ganta a bude, na fita na mayar da ita na rufe. Kafin inyi taku daya naji ni a jikin sa, duk da banga fuskarsaba amma nasan shine, na danyi kokarin raba jiki na da nashi amma ya rike ni tsam, nima kuma I need the hug, dan haka na kwantar da kaina, a tare muka sauke ajjiyar zuciya, ina jin bugawar zuciyar sa kamar a kirjina take bugawa, mun jima a haka sannan ya kawo bakinsa dai dai kunne na yace "I missed you" na kara narkewa a jikinsa dan ni inajin ba zan iya cewa ma i missed you din ba. Sai da hankali na ya fara dawowa jikina na tuna anytime wani, ko kuma ma Daddy da kansa zai iya bude kofar palon ya fito. Na dan zame daga jikinsa amma ina jin kamar na bar wani part of me a tare da shi. Yana kallona yace "come, let me show you something" yayi gaba na bishi a baya da sauri, naga yayi hanyar part din su ya Habeeb, ni dai binsa nake, ya bude kofar yayi min alama da in shiga, ina shiga naga gurin gaba daya ya chanza min, wani kamshi mai dadi yana tashi, kamshin Sultan, irin kamshin da kullum motarsa take yi kuma irin kamshin da naji a apartment dinsa na newyork, ya tsaya a bayana yace "welcome to my humble home" na juyo ina kallonsa da mamaki, ya jawo ni ya zaunar dani akan kujera shi kuma ya zauna a gaba na ya harde kafafuwansa yace 'I have a story to tell you" nan fa ya fara bani labarin abubuwan da sula faru tun tafiya ta, duk irin abubuwan da Daddy yayi masa, dawowarsa gidan mu hatta zancen sabon kamfaninsa daya bude sai da ya gayamin, nayi mamakin yadda al'amarin ya kasance sannan na jinjinawa Daddy na, na kuma gode wa Allah da samun uba na gari da nayi, dan iyaye na gari sune ginshikin rayuwar 'ya'ya, sannan kuma na kara imani da kuma godiya ga Allah, dan nasan duk abinda ya faru ya faru ne saboda karfin addu'ah. Ni kam babu abinda zance sai Alhamdulillah. Nan ni kuma na zauna na fara bashi labarin nima abinda ya faru dani tun sanda ya Walid ya dauko ni daga gurinsa, tafiyar mu niger da duk abinda ya faru acan har taimakon da musbahu yayi min na samu na kira daddy na. Nace "yanzu Mommy ce kadai matsala, ita ma kuma insha Allah zata sauko" na sauko daga kan kujerar nima nayi irin zaman da yayi na cigaba da bashi shawarwari akan sabon companyn sa, na bashi shawarar ya bude branch a New York tunda yana da mutane sosai acan, naga alamar yaji dadin shawarar, nan yace in zabarwa companyn suna wai dama ni yake ta jira in dawo in fadi sunan da nake so, nace zan zaba amma ba yanzu ba sai nayi tunani. Nan kuma na sake bashi shawarar yake zuwa palace yana gaishe da babanshi, ya dan bata fuska yace "why?" Nace "because he is your father" Ya Habeeb ne ya shigo palon, ya tsaya yana kallon mu da mamaki yace "wai ke har yanzu kina nan? Mu duk mun dauka kinyi bacci by now?" Na kalli wall clock din palon 12:49, da sauri na mike ina rufe bakina da hannu, na shiga uku, duk dariya suke min, Allah yasa Mommy bata shiga dakina ba, dan tunda muka dawo gidan ban kuma ganinta ba, kar in kara wani laifin akan wani. Ya Habeeb yace "soyayya dadi, wayo ku baku ma san lokacin ya tafi ba ko?" Da sauri nayi hanyar waje ina jin Sultan ya biyo bayana yana kirana, a bakin kofa na tsaya ya karaso ya miko min wani abu a leda, na kalle shi da alamar tambaya yace "it is a phone, ba zan iya hakura da jin muryar ki ba, dazu na siyo na yi miki charge dinta na saka miki sabon sim" na dan yi shiru amma kuma nima ina son muke wayar ai. Na karba nace "thank you" bai ce komai ba, na juya na cigaba da tafiya ya sake biyoni ya sha gabana yana tafiya da baya da baya yana kallona kamar wacce zan gudu, har muka je kofar palon mu, na kama handle din kofar yace a hankali "love" na juyo na kalleshi, a hankali ya sake cewa "thank you for loving me" bance komai ba sai murmushi da nayi, shima murmushin yayi min, and in that moment ji nayi duk hawalar da nasha is nothing, for him, I can do it all over again, ko da wacce tafi ta baya ce ma.
A bangaren Mommy kuwa tunda suka dawo ta shiga dakinta ta rufe kofa, ta kwanta a kan gado zuciyarta tana yi mata zafi, mai yasa wai kowa ba zai fahimce ta ba? Wannan yaron ba yaron kirki bane, bai dace da Moon dinta ba, her perfect daughter deserves someone like her. Wannan yaron is too strong for her daughter, in anyi auren ma cin zalinta zai tayi yana lallabata ita kuma da raguwar zuciya tayi ta yafe masa. That's is ko da ace ya gyaru ma, in kuma bai shiryu ba yaje ya sha giyarsa yazo ya lakada mata dukan tsiya. Ta runtse idonta, bama zata iya tunanin 'yarta wani katon gardi yana dukanta ba. Ta tashi ta dan daga labule ta leka waje, shi ta fara gani akan mota tare da habibin ta, ta rasa wanne irin charm yayi using akan 'ya'yanta da mijinta, ita yanzu abin kunya ne ma kawayenta su shigo su ganshi a gidanta bayan duk irin maganganun da suke yi a office akansa, da akwai cases dinsa da yawa da ake kawo musu amma sai kuma azo a janye saboda iyayensa sun bata shi, ita ta kasa gane wanne irin so iyayensa suke masa da har suka barshi ya lalace haka, wannan ai ba soyayya bace. Ta shiga toilet tayi wanka ta fito tana shiryawa, wai har ita yau dear ya zauna ya wanke ta agaban iyayenta, abinda bai taba yi mata ba kuma duk akan wancan shegen ruwa biyun. Ta saka kayanta ta fita ta leka dakin Moon ta jita a bandaki tana wanka, ita kunyar 'yar tata ma take ji, me zata ce mata bayan tayi failing, yanzu ga yaron nan an kawo shi har gida yadda zaiji dadin lalata mata 'ya a gidan ubanta. Ta sauka kasa tana bada order abincin da za'a dafa, a kitchen din ta zauna kamar yadda ta saba akayi aikin abincin tare da ita, sai da ta tabbatar komai ya kammala sannan ta koma sama tace akawo mata nata sama, bata son wannan tsageran yaron ya shigo ya same ta a kasa, da wasu idanunsa a tsatstsaye irin na marasa kunya. Ta koma dakinta tayi sallolinta sannan ta jawo abincinta taci, duk abincin ma babu dadi, sam yanzu bata iya cin wani abin kirki, she is suppose to be downstairs with her family, kamata yayi ace tana can ta tabbatar Moon taci abinci ta ko shi. Amma sam dear yaki sauraronta, ita ba zata iya zama da yaron nan ba, shi kuma direct ya gaya mata shi fa ba zai kore shi daga gidan saba sai ranar da shi da kansa yace zai tafi. Kuma yaran ma babu wanda ya hawo yayi mata magana, irin Mommy mai yasa ba kya saukowa mu ci abinci tare? Ji tayi wani hawaye ya zu bo mata, ta goge tare da jawo wayarta ta duba time, safiya ce yanzu a England, tayi dialing number din Hafsat.
Hafsat ta gama sallamar Zayed tana shirin shiga wanka taji shigar kira daga Mommy, ta zauna da kyar saboda nauyi da ta fara, ta daga da sallama. Mommy ta amsa da daskararriyar murya, suka gaisa sannan mommyn tace "Moon ta dawo gida" da yake tuntuni Hafsat tasan duk abinda yake faruwa, da sauri Hafsat tace "Haba? Tana ina? Dan Allah Mommy bata mu gaisa" Mommy tace "tana kasa tare da daddyn ku da brothers dinku, da kuma wannan yaron" Hafsat ta gane wa take nufi. Sun jima shiru sannan Mommy tace "Hafsat ke kinfi kowa sanin Moon, dan ina ganin kamar hatta ni da na haife ta kinfi ni sanin ta, please tell me, where did I go wrong a tarbiyyar dana bata? Me yasa tayi choosing ta bakantamin ta tozartani a cikin jama'a? Me yasa ta zabi sultan? Me yasa tun farkon ganin ta dashi ba ta fahimci cewa ba sa'an auren ta bane ba?" Hafsat ta danyi shiru sannan tace "Mommy kaddara ce, destiny, Sultan destiny din Moon ne haka itama Moon destiny din Sultan ce. Allah ya riga ya rubuta cewa sai sun hadu kuma sai hakan ta faru a tsakanin su. Mommy babu inda kikai wrong a tarbiyyar mu dan ba mu kadai ba duk wanda ya san mu yana yabawa da irin tarbiyyar da kika bamu, wannan shi yasa ko da yaushe muke kokarin mu zama perfect saboda kar muyi failing dinki, but no body is perfect. Duk abinda Moon tayi tayi shine because she is afraid of failing you Mommy. Sultan ba shine saurayin Moon na farko ba, tayi Ibrahim, she loved him so much amma haka tayi ta kumbiya2 saboda tasan ba lallai ne in ta kawo muku shi ku karbe shi ba, sanda tayi summoning courage kuma ta kawo shi gida shi kuma ya kasa summoning courage yayi facing Daddy. Sai da tayi spending five years kafin ta cire ran dawowarsa. So you understand why she is holding tightly unto Sultan. Shima haka tayi ta hiding dinsa daga gurinku saboda tasan shima ba zaku amince da shi ba. Tsoron da take yi na cewa zaku rabata dashi shi yasa take going behind your back take ganinsa. Na sha bata shawarar ta kai ku gurinsa but she kept saying she is waiting for the right time, she was afraid, afraid of not being the perfect girl you want her to be. So tayi ta dan gyara shi kafin ta kawo muku shi, amma sai gashi kun ganshi in his worst" tunda ta fara magana Mommy bata ce komai ba, sai da taji tayi shiru sannan tace "yanzu me kike ganin ya kamata inyi" Hafsat ta sake cewa "Mommy ni personally i don't like sultan, but tunda har Moon tayi falling for him, kuma Daddy ya dauko shi ya hada shi da 'ya'yansa gudan jininsa, suma kuma a cikin 'yan watanni har suka saba dashi then there must be something Good about him. Ni ina ganin Mommy give him a chance, you might even like him too"
Bayan sun gama wayar Mommy ta jima a zaune tana digesting maganganun Hafsat, tasan Hafsat tsintar kalmomi tayi wajan yi mata bayani amma abinda take so ta gaya mata shine 'she is too strict' kuma tasan haka ne, takurawar ta da son su zama perfect ne ya saka Moon take zuwa gurin Sultan a boye. Yanzu badan Allah ya kare mata yarinyar bama da sai dai ta ganta da ciki ta rasa a ina sa samu. She was wrong before, but now she is going to correct her mistakes. Ta tashi ta kwashe kayan abincin da ta gama ci ta fita dasu kitchen, babu kowa a palon duk sun fita, ta koma daki ta sake wani wankan tayi shiri na musamman, she is going to take back her family. Tana jin Daddy yazo ya wuce ta gaban dakinta amma ko lekowa bai yi ba, sai da ta bari ya dan jima da shiga sannan ta bi bayansa. Tana shiga taga ya fito daga wanka da towel a jikin sa yana kokarin shiryawa, kallo daya yayi mata ya dauke kansa, ta zagayo gabansa ta dauko mansa ta fara kokarin shafa masa, ya ture ta ya matsa, ta ajjiye man ta dauko turarensa ta biyo shi inda yake kokarin saka pajamas dinsa ta karasa saka masa ta fara fesa masa turaren hannunta, ture ta ya sake yi ya tafi kan gado yana shirin kwanciya, ta saka hannayenta ta baya ta rungumo shi, ya chire hannun nata ya matsa. Ta shagwabe fuskar ta kamar zatayi kuka tace "am sorry fa" bai kula taba ya hau kan gadon, ta bi bayansa ta kwanta a kirjinsa tare da sauke ajjiyar zuciya, sun jima a haka sannan a hankali ya dora hannunsa a bayanta yana shafa ta kamar mage, ita kuma ta kara narkewa a jikin sa, can kasan makogwaronsa a furta "I miss you"
Episode Fifty Eight : For You, Only You
'Yan # teamibrahim ina jin duk abinda ake yi muku, believe me, i will surely reward your loyalty. Bature yace "he who laugh last.......
Washegari da sassafe Sultan ya kira ni yace min ya tafi office, yana da meeting very early, dan haka nima ban tashi da wuri ba, ina jin Mommy kusan shigowarta uku tana dubani, sai kusan karfe 12 na tashi, shima kuma yunwa ce ta tashe ni, nayi wanka na shirya cikin wasu riga da skirt english wears tunda duk kayana sunyi min yawa yanzu, nayi packing gashina a tsakiyar kai na sauko kasa, a kitchen na samu su Mommy already suna aikin abincin lunch, na gaishe da Mommy ta amsa tana kallon kayan da na saka, na jawo kujera na zauna nace "Ma'u ki kawo min taimako, yunwa na ke ji" da sauri Asma'u ta ajiye aikin da take yi ta fara hado min tea, na karba na fara sha sannan ta zubo min farfesun naman ragon da suka gama hadawa ta hado min da bread, na karba ina ci ina santi, Mommy tace "aikin kenan, amma in akace kiyi garki ba zaki yi ba sai dai a girka ciki, ni ban taba ganin macen da bata son girki ba sai ke Moon" Furaira ta karba "kuma gashi gwanin nata gwanin abinci ne ba" a tare muka watsa mata harara ni da Mommy, tayi sauri taja bakinta tayi shiru, can Mommy tace "ke furaira ya akayi kikasan saurayinta ne?" Furaira tace "nima Mommy wallahi a gurin 'yan waje nake ji, shi yake gaya musu" a raina nace "zai aikata" Asma'u tace "kar ki damu mai sunan daada, duk sanda akayi bikin ki gidan ki zan koma inyi ta dafa miki abinci ke da mijin ki" nan itama ta karbi nata rabon hararar daga Mommy" sai da na gama cin abinci na sannan Mommy tace "ku bata suyar friend rice din nan tayi" na fara yarfe hannu ina kallon Mommy kaman zanyi kuka "Mommy wallahi kone wa zanyi, ni kuba ni in yanka muku wani abu, ni zafin wutar ne bana so" asma'u ta biye min "dama wannan jikin naki haka babu tsoka ina zaki iya juya shinkafa? Bara dai in baki ki hada fruit salad" nan na kama murna na zauna dishen a kasa na nade kafa, maryam tace "so take fa ta gudu, ai tana zuwa kitchen zata ce a bata yanka, daga nan zata yanke hannu sai kuma ta tashi ta fita shikenan ba zaki kara ganin taba sai akan dining" duk suka saka dariya, na bata rai nace "ke Maryam har zaki nuna min aiki da wuka? Da likita fa kike magana" daga nan sai na fara basu labarin yaddda muke buda kan mutun mu bude kwakwalwarsa mu yi masa aiki sannan mu mayar mu rufe, ban ankara ba ina ta surutu sai gani nayi ana juye fruit salad din a bowl, har an gama hadawa, na dauko cup aka zuba min na koma gefe na fara sha ina cigaba da labari na. Tsayuwar mota muka ji a waje, Mommy ta kalleni tace "madam ki je ki chanza wadannan kayan na jikin ki, dan wannan tsageran yaron bashi da linzami a gidan nan, har kitchen din nan zai iya shigowa" nace "Mommy kaya na duk sunyi min yawa ne wallahi" tace "to sai ki saka wadanda suka fi wadannan girma ko kuma ki saka dogon hijab" nace "yes Mommy" har zata fita tace "kar ki yadda fa inzo dining in tarar dake da kayan nan sai ranki ya baci" da sauri na mike na riga ta hawa saman. Sai da nayi alwala na saka dogon hijab dina bayi sallah sannan na dan gyara fuskata na sauka kasa, ya Habeeb na tarar a palo, na zauna muka fara hira sai da ga Daddy, ya Walid da Sultan sun dawo, daga gani daga masjid suke. Ko kallon inda Sultan yake banyi ba na gaishe da Daddy, duk da ina jin idanuwansa a kaina. Daddy ya fara yi mana zancen convocation din mu da za'a yi next week, kuma duk tare za'ayi har dasu Faruk. Nan muka kama murna. Saukowar Mommy ce ta katse mana hayaniyar mu, gaba daya muka juya muna kallonta, tasha ado tun daga sama har kasa, tayi kyau sosai dan bazaka kalleta ba kace ta haife ni ma ballantana ya Walid daya doshi 30 years. Tana zuwa ta gaishe da Daddy, su kuma duk suka gaishe ta har Sultan, ta amsa ba tare da ta kalle shi ba, sannan tace "ga abinci nan a dining" ta mike ta tafi, muma duk muka bi bayanta. Muna zama na tashi na fara zubawa kowa abinci, sakara ce da miyar vegetables, fried rice da hadin salad sai farfesun naman rago, sai kuma fruit salad. Kowa farfesu na fara zuba masa sannan kuma sai in tambaye ka me kake so a cikin sakwara da shinkafa sai in zuba maka, amma da nazo kan Sultan ban tambaye shi ba na xuba masa fried rice da salad da yawa amma na ciccire tumatir din cikin salad din, duk abinda nake yi idon kowa akaina yake, ina gamawa yace min "thank you" ban amsa masa ba na koma na zauna. Ya Habeeb ne ya kasa shiru yace "shi Sultan mai yasa ba'a tambaye shi abinda yake so ba? Idan kuma ransa yafi son sakwarar kuma fa?" A hankali nace "baya cin sakwara ai" ya Walid yace "wow, yanzu kai zama kayi kai ta lissafa mata abincin da kake so da wanda baka so?" Daddy yayi gyaran murya duk kowa yayi shiru. Ina lura da Sultan gaba daya a takure yake, kuma nasan ganin Mommy a gurin ne. Daddy ya cigaba da maganar zuwan mu England ita kuma Mommy ta gaya mana cewa in munje zamu taho tare da Hafsat saboda tana son tazo ta haihu a gida, nan muka kara yin wata murnar. Sultan ne ya fara tashi yace wa Daddy zai koma office saboda ya baro aiki sosai a can. Yana tafiya su Daddy da yaya Walid suka fara maganar irin cigaban da company n Sultan yake samu, yaya Habeeb yace "yanzu fa a cikin 'yan watanni har ya fara zancen sayan building din kusa dashi zai kara wasu offices din ya kara expanding din gurin. He is a real hustler. Baya zama sam, baya kuma gajiya da aiki" ni da Mommy kawai jin su muke bamu ce komai ba. Sai da suka gama sannan Mommy tace da ya Habeeb "kai da kake ta celebrating success din wani kai ina taka success din? Tunda aka samar maka aikin nan ka fara ni banga ko hula ka saya wa kanka ba, baka da aiki sai kashewa 'yammata kudi ko? Ka san Allah Habeeb ka fita daga ido na in rufe, kana ganin walid ya sayi filin sa yana kokarin fara gini amma kai ko ajikinka sai ana maganar wani ka iya cewa 'he is a real hustler' bayan kai yanzu da zan duba account dinka babu wani abin kirki a ciki" yadda kokayi maganar ya Habeeb ne saka mu muka yi dariya ni da ya Walid, ta juyo tana hararar ya Walid tace "kai kuma ka iya taya wani murna cewa budurwarsa tasan abinda yake so da wanda baya so amma kai kaki yin budurwar ballantana ka gaya mata kai me kake so din, you are not getting any younger fa, ya kamata kai ma ka san me kake ciki tun kafin hajja ta juyo kanka ta samar maka mata" na rufe bakina ina dariya ganin yadda ya Walid ya bata fuska, ta juyo kaina tace "ke kuma a ina kika samu wannan wayar ta hannun ki?" Cikina ne ya bada kululu, na fara in ina, tace "shine ya baki ko?" Na gyada kai, tace "ce masa akayi ba zamu iya saya miki waya bane ba? Ko kuma ke ce kika roke shi?" Nayi sauri na girgiza kaina tace "to ki tabbatar kin mayar masa da wayarsa, phones din ki suna dakina kije ki dauka, kuma kar ki sake karbar komai nasa" nace "yes Mommy" Daddy yace "saura ni" duk mukayi dariya banda Mommy, yace "to duk kin hada min kan yara kin musu fada ai gwara ki hada dani kawai"
Haka rayuwa ta cigaba da tafiyar mana inda Sultan ya dage da aikinsa ni kuma na fara mayar da kiba ta. Kullum haka muke wuni makale a waya duk da cewa zai zo muyi lunch tare, dinner ma haka, kullum da daddare kuma muna tare a palon su ya Walid har sai Mommy ta kira ni ko kuma in su ya Habeeb sun kora ni gida. Ana gobe zamu tafi england aka dauko Amina daga 'yalleman. Tare duk muka tafi England a jirgin Daddy, a gidan Hafsat na sauka naga tayi nauyi sosai, Sultan ma ba kunya cewa yayi acan zai kwana, dole Zayed ya bude masa guest room din waje, ranar kusan raba dare mukayi hira, da zayed da sultan suka zauna hira har sai da muka gaji ni da Hafsat muka tafi muka kwanta muka barsu. Washegari da sassafe muka tashi muka fara shirin tafiya Oxford, wata tsadaddiyar doguwar riga Sultan ya aiko min da ita yace in saka, ai kuwa kamar an gwada ni dan das ta zauna a jiki na, Hafsat ta kalle ni ta tabe baki tace "to ba dole tayi miki dai dai ba tunda yasan size din komai, ni rashin kunyar ku har mamaki take bani, kun wani maze kamar babu abinda ya faru" na bata rai nace "kai Hafsat, ni kam da na sani ban gaya miki maganar nan ba, ni dashi har mun manta ma amma ke kin kasa mantawa, it is in the past, please move on" ta tabe baki tace "shine yace miki ya manta? An gaya miki duk wannan kallon naki da yake na banza ne? To gwara ma ki sani, bai manta ba, dan haka sai kibi a hankali dashi" ni dai ban kuma ce mata komai ba saboda bana so tayi spoiling mood dina for today. Na dora graduation gown akan doguwar rigar muka fita, sam na kasa hada ido da Sultan sai nake ganin kamar maganar da Hafsat ta fada gaskiya ne. Tun daga gidan Hafsat muka fara pictures, a dole na ware da Sultan muka yi ta pictures sannan muka tafi mkrt, muna zuwa suma 'yan gida suka zo nan guri ya hargitse muka tafi hall din taro, muna shiga muka tarar anyi displaying innovations na graduands, zanen Sultan na gani anyi enlarging dinsa a saka a wall din da take kallon mu, duk kan mu tsayawa mukayi muna kallon zanen, kowa yana cewa "kunga zanen sultan" "yayi kyau" "moon ke kika zana?" Ni dai duk ba wanda na bawa amsa, na juya na kalli sultan a gefe na naga ya saki baki yana kallon zanen, na kasa karanta expression dinsa, can ya juyo ya kalle ni yace "ke kika yi zanen nan?" Na kalle shi cikin ido nace "yes" ya kuma kallon zanen sannan ya sake juyowa yace "dama haka shape din kaina yake kamar mangaro?" Duk gurin kowa sai da yayi dariya nace "you are welcome, dan nasan thank you kake so ka ce" An gama taro lafiya duk muka karbi certificate din mu, I am now officially a neurologist and also a psychologist, Faruk da Amina ma duk sun karbi nasu, daga gurin taron gidan Hafsat muka zarce gaba daya inda Zayed da Hafsat suka shirya mana Walima. Washegari zamu koma Nigeria dan haka Hafsat already ta riga ta gama hada kayanta, Zayed sai bacin rai yake yi, ina jinsa yana gayawa sultan wai shi fa ba'a son ransa ba, kai Sultan maimakon ka bada hakuri sai cewa yayi "chafdi, ai kayi kokari ma, ni kam babu mai rabani da matata dan zata haihu" Hafsat tace "wato kar mu saka rai kenan ko?" Yace "gaskiya kam, kar ma ku saka rai ballantana in na hana kuji haushi"
Washegari muka dawo Nigeria. Motar mu tana shigowa gate na hango mutane cirko2 a tsatstsaye. Da sauri muma muka karasa gurin muka fito. Wata arniyar picanto fara tas an nada mata ribbon alamar gift ce, a jikin plate dinta an rubuta 'Her Royal Highness' ina gani nasan aikin waye wannan, nayi ta nemansa ko sama ko kasa bayanan, a saman motar an ajiye card, na dauka na karanta 'it will be my pleasure if you will let me teach you how to drive' lallai sultan rigima yake so ya debo min a gidan nan. Daddy yana ganin motar shima ya gane aikin waye yace da walid "ina sultan?" Ya Walid yace "a hanya ya sauka bai karaso gida ba" Daddy yace "call him" yana zuwa Daddy ya mika mishi key din motar yace "not now. In zaka koya mata mota akwai motoci a gidan nan ku dauki duk wacce kuke so" Sultan ya dan bata fuska Daddy yace in serious voice "I said NO" dole sultan ya karbi key dinsa. Inaji ina kallo aka saka motar a garage aka rufe.
A kasa aka gyara wa Hafsat daki saboda tace ba zata iya zirga2r hawa sama ba, nayi mamaki sosai yadda naga suna mu'amala da sultan, ta sake dashi sosai, Mommy ma naga yanzu tana dan kulashi kadan, har wani lokacin takan tambaye shi ya office ko kuma ta dan saka shi wani aiki. Shi kuma na lura yana jin nauyin ta sosai, dan in dai tana guri wata nutsuwa ta musamman yake yi. Kwanan mu biyar da dawowa rannan da safe bayan mun gama breakfast duk 'yan mazan sun tafi aiki sai ga Amira da mamanta sunzo, daga ganin fuskarta na san akwai matsala, a palo suka zauna tun kafin mu gaishe da mama ta fara fada "gata nan fatima na kawo miki ita maybe ke in kika yi mata magana zataji, Amira taki aure, na rasa me yake damun yarinyar nan, taki samarin ma ballantana har ta samu na aure. Ni na gaji, gwara in tattara in koma gida in yaso acan a samar mata miji a 'yan'uwanta" nan Mommy ta samu abinda take so, daga yiwa amira fada ta hada har dani tayi mana tas tace kuma tace ta bawa Amira 3 months in bata fitar da miji ba da kanta da kanta zata kaita kano gidansu a aura mata duk wanda yace yana so. Ni dai bance kala ba, maman Amira tace "wani shegen yaro ta hadu dashi ya hana ta kula kowa kuma shi yaki ya fito ayi maganar aure, na rasa yadda zan yi in raba ta dashi. Nan Mommy ta fara tambayar Amira wanda take so din ita sai ta aika a gaya masa idan bai shirya auren taba ya rabu da ita, tambayar duniyar nan Amira taki magana, duk fadan Mommy haka ta hakura ta kyale Amira. Muka tashi muka tafi dakin Hafsat muka zauna, nayi ta tambayar Amita problem din ta amma tace min ita babu abinda yake damunta tace " ita fa mama duk abinda take dauka ba haka bane ba, shi wanda take magana akansa fa ba saurayi na bane, a makaranta muka hadu, he is my friend kuma haka kawai sai inje in ce masa ya fito ya aure ni? Kullum threats dinta shine zata kaini kano dan tasan bana son can to ni ya zanyi? Idan miji bai zo ba ni zan auri kaina ne?" Sai naji tausayinta na rungume ta ina lallashinta, Hafsat ma ta bata hakuri, nan muka zauna hira na bata labarin duk abinda yake faruwa tsakani na da Sultan, na dauka zamuyi rigima akan maganar amma sai naga tayi murmushi tace "Allah ya sa hakan shi yafi alkhairi" gaba daya muka ce "ameen". Mama anan ta tafi tabar amira ta wuni a gurin mu tana bamu labarin aikin data samu a aso rock, da irin kudin fa take samu tana saving, yanzu basu da wani problem na matsalar kudi. Na danyi tunani nace " Amira ni kuwa ina ma zaki gwada Amir abokin Sultan, he is really nice...." Kafin in karasa ta katse ni "Allah ya sawake, ai kwantan nawa bai kai har haka ba, ke dai da kika ga zaki iya da sultan sai kije kiyi tayi" nayi dariya nace "idan kuma Allah yayi mijin ki ne fa?" Tace "ai Allah baya dora wa bawa abinda yasan ba zai iya ba" tare muka yi lunch da ita, Sultan yana ta tsokanar ta wai Amir yana gaisheta. Bayan la'asar ta shirya tafiya muka je zata yiwa Mommy sallama, nace "Mommy zan raka Amira gida" tace "to sai driver ya kai ku" na dan yi shiru nace "Mommy da Sultan ne yace zai kaimu" ta jima tana kallona ni kuma na sunkuyar da kai kasa sannan tace "a dawo lafiya" Na kira Sultan nace an bar mu gamu nan fitowa.
A motar sa muka same shi already yana jiran mu, na shiga gaba Amira ta shiga baya muka tafi, yace "Amira wai yaushe ne bikin kawar ki ne?" Tace "wacce fa?" Yace "wacce ki ka fi damuwa da ita" tace "sai ranar da ka shirya ranar za'ayi" yace "to ai ni already a shirye nake" ina jinsu na rabu dasu nasan neman magana yake yi, naga ya chanza hanya na tambaye shi yace "Amir zamu dauko" da sauri Amira tace "What? Please ku sauke ni in hau taxi, I can't tolerate that man" duk dariya muke mata tace "am serious wallahi, he is so annoying" muna yin packing ya bude ya shiga baya, yana ganin Amira a ciki ya ja tsaki yace "damn it, wannan yarinyar me take yi a motar nan?" Dariya muka sake yi, ni drama dinsu dariya take bani. Daga nan naga mun kuma yin wata hanyar daban, this time banyi magana ba Sultan yace "I want to show you something" Bance komai ba har naga yayi packing a gaban wani katon building duk muka fito na daga kaina naga an rubuta a saman ginin 'MOON CONSTRUCTION AGENCY" na kalle shi da mamaki yace "to ba kin ki gayamin sunan da kike so ba, shi yasa na saka sunan da na fi so" muka shiga gurin suna nuna mana ko'ina suna kuma yi mana bayanin komai,gurin ya tsaru sosai, I trust sultan in dai ta gurin tsari ne, aikin architecture yayi suiting dinsa sosai. Daga nan muka tafi gidan su Amira, a can mukayi magrib sannan muka fito muka kai amir gida shima. Finally daga ni sai shi, nace masa "thank you for the name" yace "I only hope it will shine as bright as you" nayi murmushi. Yace "wai har yanzu Mommy ba ta ce miki komai ba?" Nace "akan me fa?" Ya nuna kansa sannan ya nuna ni yana mischievous smile dinsa. Na gane me yake nufi, na dan bata rai nace "ni ban san akan me kake magana ba" yace "common, how much longer do I have to wait ne wai. Ni aure na ke so seriously" na rufe baki ina dariya nace "kai Sultan, baka jin kunyata kake cemin aure kake so?" Yace "ke din zanji kunya? Ke fa zan aura kuma sai inji kunyarki? Please ki dan tambayi Mommy mana kiji me ake ciki" nace "kai ma wasa kake, me zan ce mata? Mommy yaushe za'ayi min aure?" Yace "exactly" na girgiza kai nace "sai dai kai kaje ka tambayi Daddy" yace "OK, wato ke kina nufin ba kya son auren kenan?" Nace "wai what has come over you ne yau?" A lokacin muka shigo gida, yayi packing amma be kashe motar ba yace "ai na riga ma gaya miki me yake damuna, aure nake so, ai nayi kokari, ya kamata a bani medal ma. Kinga yanxu abinda za'ayi, irin in kuna magana da Mommy sai kike gaya mata ga abinda kike so ayi da bikin ki, zata dauki haske ai sai tayi wa Daddy magana" nace "wai ni na ce maka ina son aure? Kai da kake son auren ba sai ka fada ba?" Ya juyo yana facing fina yace "look into my eyes kice ba kya son aure na" na ki kallonsa, yasa hannu zai juyo fuskata na kara matsawa, yace "kin gani ko? You want it too" na girgiza kaina nace "I don't want anything" yace cikin murya kasa kasa "then look into my eyes and tell me you don't want me" da sauri na bude kofar motar na fita, shima ya bude ya fito ya sha gabana "au guduwa zaki yi ko?" Nace "kafi karfina yau. Yau mood dinka is not for me" yace yana kallon cikin idona "I have always been in this mood, for you, only you. Kawai hakuri nake, please do something. Ni fa idan ba'ayi mana aure kwanan nan ba to akwai rigima." Dariya nake son yi amma shi fuskarsa so serious, can ya fara devilish smile dinsa sannan yace "laugh all you want, baby girl, my time will come, then I will do the laughing and you will do the crying" bansan sanda na daina dariyar ba, da sauri na nayi hanyar gida, ina jinsa yana kira na amma ko waiwayowa banyi ba.
Episode Sixty : The Prince
Sultan gaba daya ya rikice min, wai shi lallai sai na fada a gida cewa aure nake so, kaji mutum, kuma shi in nace masa ya fada sai yaki. Dole yanzu na fara rage doguwar hira dashi, a waya ma kuma sakin layi yake. Gaba daya ni yanzu lamarin sa tsoro yake bani, kuma gashi Daddy ko mentioning zancen mu baya yi, ballantana Mommy da ko maganar ma bata so ayi. Da yaga na fara gudunsa sai ya tsiyo da zancen driving lesson, Daddy ya gayawa, daddy kuma yace muke yi da yamma in ya taso daga office. Ni dai nasan ba wani abin arziki za'a koya min ba amma dai haka nake binsa muna fita, in muka je rabi lesson rabi hira. Rannan nace masa "to wai kai me yasa ba zaka je ka tambayi daddyn ba? Ai kun fi kusa dashi, ko kasa yaya Walid ya tambayar maka" yayi shiru yana kallona sannan yace "Daddy has done so much to me ne bana so inyi disappointing dinsa, bana so yaga gazawa ta ko kuma yayi tunanin dama abinda nake after kenan. Nafi so ace shi yayi min magana da kansa. Amma gaskiya na gaji da jira, I don't know how long zai taking kafin yayi min maganar" ya dan bata fuska yana kallona "ke ko ajikin ki ma wallahi, hankalinki kwance ke ko shekara za'ayi a haka babu ruwanki ko?" Nace "wa ya gaya maka haka?" Yace "to ai bakya nuna wa. At least kema ki dan ringa nuna min kina so mana, at least sai in san cewa the feeling is mutual ba wai ni kadai na ke abuna ba" nace "sultan komai fa da lokacin sa, musamman aure, in kaga anyi to lokaci ne yayi ba wai nuna ina so ko rashin nuna inaso bane zai sa ayi. Kai dai kayi ta addu'ah sai kaga komai yazo da sauki"
Sosai muke ta shirye shiryen haihuwar Hafsat, takanas Mommy ta dauko wata midwife suke kwana tare saboda in case ko haihuwar zata zo da daddare. Hafsat kam duk tayi laushi, bata da aiki sai cin abinci sai da yamma inna tafi driving lesson dina ita kuma ta tafi strolling. Kaya kam har dai da aka ware daki guda ake zubawa dan kullum sai an siyo wani abu na baby an ajiye, in dare yayi kuwa bata zaman palo, tana daki makale da zayed a waya har sai tayi bacci. Ni kuma kullum da daddare bayan an gama dinner zamu zauna hira da Sultan, Mommy ta hana hirar palo tace muke zama a compound in da mutane za suke ganin mu, ni ma banyi mata musu ba saboda wannan Sultan din ba na da bane ba, shimq dana gaya masa abinda Mommy tace sai cewa yayi "yauwa, ai gwara ma muke zama inda Daddy zai ke ganin mu yana tunawa da maganar mu"
Rannan ina gyaran kayana a daki kawai sai naga katin da musbahu ya bani a agadaz, shaf na manta dashi ma ni, dan adam kenan. Na dauka na saka number din nayi saving as 'musbahu ngr', sai bayan da nagama aikina kaf sai na dauko wayar na kira number dinsa, ya nayi masa sallama ya amsa yace "sai yau kika tina dani ko Moon?" Nace "lah ya akayi ka gane nice?" Yayi dariya yace "naga number din Nigeria kuma naji muryar mace, I have been expecting your call kuma shiru har na fitar da rai" nace "wallahi na rasa card dinne sai dazu na ganshi, ya su mustapha da sauran 'yan gidan?" Yace "lafiya lau. Ina Sultan?" Nace "au baka manta sunan sa ba?" Yace "It is kind of special ne shi yasa ban manta ba" muka dan taba hira na kashe na ajjiye wayar, ni sam ban kawo wani abu a raina ba sai da daddare muna tare da sultan ya karbi wayata yana kallon pictures din da mukayi dazu wajan koyon mota sai kawai naji an kira ni, na mika hannu ya ban wayata sai naga yanayin fuskarsa ya chanza, ya juyo min screen din na karanta 'musbahu ngr' wayar ta katse aka sake kira har ta sake katsewa bai bani ba kuma bai ce min komai ba. Can dai yace "why is he calling you?" A ina ma ya samu number dinki da zai kira ki" na bata rai nace "dazu na kira shi muka gaisa. Yace in nazo Nigeria in kira shi, tunda nazo kuma ban kira shi dinba saboda nama manta da maganar sa sai dazu" nan take naga yanayin fuskarsa ya chanza "ina ruwanki dashi to da zaki kira shi, yanzu gashi ya samu number dinki kuma har yana da guts din da zai kira ki yanzu da daddare" nace cikin lallashi "Sultan, gaisawa fa kadai muka yi, har tambayata kai sai da yayi, he means nothing, kuma ya taimakamin wallhi, badan shi ba maybe da har yanzu ina agadaz" Sultan yayi chuckling yace "he is fooling you, kuma zancen taimako ke fa kike gayamin kullum cewa komai yana da lokacinsa, dan haka tunda lokacin dawowar ki gida yayi dole sai kin dawo with or without his help" nayi shiru na rabu dashi tunda naga rigima yake ji da ita, jin nayi shiru sai ya cigaba " you called him yaji muryar ki, and now he is calling again saboda ya sake jin muryar ki. Ni da son raina ne in banda 'yan gidanku babu wanda zaki ke yiwa magana ballantana har wani kato yazo yace zai kula ki. Kamar yadda nake ban taba budurwa ba sai you and you are the last haka nake so kema tunda baki taba saurayi ba in zamanto the first and the last" gaba na ne ya fadi dana tuna cewa sultan fa har yanzu bai san labarin Ibrahim ba, nayi sauri na ture maganar daga raina nace there is no need for him to know, tunda dai what you don't know won't hurt you. Ya jefo min wayar kan chinyata yace "block him" na dauki wayar inajin zafin yadda ya dage yake fada akan abinda bai kai ya kawo ba, na mike tsaye nace "I won't block him, tinda ni ba butulu ba ce" da sauri ya mike tsaye shima, kamar zai ce wani abu kuma sai ya fasa, ya saka hannunsa a cikin gashinsa sai ya tafi kamar zaiyi hanyar gate kuma sai ya dawo sai da yazo daf dani ya tsaya, ke gezau banyi ba, ya kalleni cikin ido yace "in har naga kafarsa a gidan nan sai na babballashi wallahi" na hade rai nace " kai yanzu sai ka karya mutum dan ya kulani?" Yace "bazan san sanda zan karya shi ba ai, sai na ganshi a kasa sannan zan san me na aikata. So you better warn him" na juya ina kallonsa har ya fice a kafa daga gidan. Na sauke ajjiyar zuciya, lallai ina da aiki a gaba na, sultan zuciya, sultan kishi, dole sai yayi maganin wadannan abubuwan guda biyu sannan zamu zauna lafiya dashi. Na koma cikin gida, ban kira musbahu ba kuma banyi blocking dinsa ba, sai kuma naji babu dadi a raina, yau munyi fada da Sultan, amma nasan zai sauko na bashi nan da awa daya.
Nayi shirin kwanciya na kwanta, bacci ya fara dauka na kenan naji wayar sultan, har ya sauko, nima yanzu zanyi nawa fushin. Na rabu dashi yayi ta kira na naki dauka, message ya shigo, ina dauka naa emoticon na kuka, ya rubuta 'am sorry love' nayi murmushi a raina nace 'iyakacin zuciyar kenan?' Kafin ya kuma kira na kira shi, bugu daya ya dauka har da sauke ajjiyar zuciya nayi shiru bance masa komai ba, sai na kuma jan aji tukunna. Cikin muryar shagwaba yace "to wai ba nace am sorry bane ba? Dan kinsan ba zan iya bacci banji muryarki ba ko?" Na sake yin shiru yace "please please please haba love, this is so cruel wallahi. Am sorry nayi miki fada, i don't want you talking to any man. Ina kishin ki sosai. Please kar kiyi fushi dani akan haka" a hankali nace "ni ba akan kayi min fada nake fushi ba" yace "to akan menene, tell me, koma menene zan daina" nace "akan baka yadda dani ba" ya danyi shiru sannan yace "bangane ban yarda dake ba" nace "all this while ya kamata ace kasan how much I love You, ba musbahu ba koma waye mu kayi waya dashi ko kuma ka gan mu tare dashi bai kamata ka bata ranka ba, ban san menene a cikin zuciyar musbahu ba amma nasan menene a cikin tawa, and that should be your only concern. Sultan bana ganin wani namiji a gaba na ko a bayana sai kai, my heart is for you, only you, to menene naka na tsayawa kana bata ranka akan nayi magana da wani wanda ba lallai in sake ganin sa ba" jin yayi shiru ya saka na kwalli wayar na dauka duk wannan tsarin da nake yi kiran ya katse, naga seconds suna reading na mayar da phone din kunne na nace a hankali "sultan?" Can kasan makogwaronsa naji yace "I must do something, I really must do something" cikin confusion nace "ban gane ba?" Yace "seriously na gaji da fadar kalmar I love you na kuma gaji da jin kalmar i love you. I want to start giving some actions and receiving some actions. Kalmomin sun kare, I am out of words to show you my love for you. I want to start really showing you my love. I want you" nace "sultan zan kashe wayata" yace "go ahead ki kashe din, ai dai naji muryar ki. Tun ina yaro, if I want something, I go for it, yanzu ma haka, I want you and I will come for You" na katse wayar da sauri, na kashe ta gaba daya. Da sauri na tashi na rufe windows dina da kofar balcony na dawo na zauna akan gado, amma a raina nasan in dai Sultan yayi niyyar shigowa daki na to sai ya shigo, but I don't think he is coming, he is not going to throw away duk abinda ya samu ba.
Da safe yawa ta tana kashe dan haka bamu yi wayar da muka saba yi da safe ba kafin ya fita, bayan munyi breakfast na kira shi naji switched off, har aka zo lunch ban samu wayarsa ba, kuma bai zo cin abinci ba, daddy ya tambayi walid sai walid yace masa sunyi waya yace yau aiki yayi masa yawa ba zai zo ba. Muna gama cin abinci naje na hada masa basket guda na abinci na bawa driver nace ya kai masa office dinsa. Ga mamaki na sai ga drivern ya dawo yace wai ance yau baije office ba, suma nemansa suke yi. To ni maimunatu ina sultan ya tafi. Babu irin tunanin da banyi ba. Har akayi la'asar shiru. Ina kitchen ina zaune ina kallon su asma'u suna ta aiki, yau ko surutun ma bana musu, sai ga maryam ta shigo da sauri tace "kai kuxo ku gani yau baki akayi a gidan nan har da masu rawani da dogarai" da sauri na mike nabi bayansu muka leka ta tagar kitchen amma bama hangowa sosai, na dai hango jama'ar gidan mu sunyi chirko2 a gefe, muna cikin leke Mommy ta shigo kitchen din da sauri tace min "zo ki fita ki tafi daki" da sauri na fice ina jinta tana bada order abinda za'ayi. Dakin hafsat na shiga na tarar tana sana'ar tata ta bacci, na daga labulen window dinta na leka waje, jibga jibgan motoci na gani har guda biyu sai kuma mota mai kalar kayan dogarai, yaya Walid na gani da sauri yaje gurin motar farko ya bude kofar ya durkusa ya gaishe da wanda yake ciki sannan ya matsa ya badu guri suka fito, manyan mutane ne sun sha kayan alfarma na sarauta, duk ban san suba, naga sun tafi palon da Daddy yake saukar manyan bakin sa. Aka matsar da motar gefe aka matso da dayar, matane suka fiyo su biyu, daga ganin su kaga manyan mata, dogarai suka zagaye su har suka shigo kofar palo. Nayi sauri na koma bakin kofa nayi kneeling ina leke ta keyhole, Mommy da mutanen ta suna ta kai kawo a gurin bakin amma bana hango su sosai kuma bana jin me suke cewa. Na zauna anan na jingina da jikin kofar, na kara kiran wayar sultan switched off. Dazan kama matar nan mai cewa switched off a waya da Allah kadai zai raba ni da ita. Ina nan zaune naji kiran Mommy ya shigo, na dauka tace "kina ina ne?" Nace "ina dakin Hafsat" sai a lokacin Hafsat ta tashi ta ganni nayi tsuru2 ta tambaye ni menene na daga mata kafada. Mommy ta shigo tana kallona sannan tace "ki zo ki gaishe su" da sauri na bude kayan Hafsat ina neman kayan sakawa, Mommy tace "NO, kayan ki are OK, kawai ki dan gyara fuskarki sai ki samu babban mayafi ki saka" na shiga toilet da sauri na wanke fuskata, jikina sai rawa yake, inna kama sultan ni kadai nasan me zan yi masa, in less than five minutes na shirya Hafsat ma ta dan gyara muka fita. Tunda muka fita kaina yana kasa amma inajin idonsu a kaina, muka zauna daga can nesa muka gaishe su suka amsa mana da fara'ar su. Daya ta fara magana "Sultan bai kyauta mana ba wallahi, sam bai gaya mana maganar nan ba sai yau. Yanzu gashi ya saka munji kunya bamu kawo mata wani abin kirki ba" wata kuma tace "marar kunyar ba, ni yaushe rabon da in saka shi a idona, kawai sai gashi da sassafe yaje min kamar an koro shi, ni na dauka ma baya kasar" sai kuma ta dawo kaina "Maimunatu kalle ni kinji, ni ba surukar ki bace ba, ni kakar ki ce, Nani sunana, wannan kuma Yaya" ta nuna ta kusa da ita, "wannan ita ce surukarki, matar galadima ce" na kara sunkuyar da kaina ina murmushi, yaya tace "mu kadai muka zo yanzu saboda bai bamu lokaci ba, yace lallai sai munzo yau, mu zuwa muka yi mu ganki mu saka miki albarka sauran kuma magana ta maza ce" Matar galadima ita ma tayi mana addu'ah aka ce mu tashi mu koma. Ina shiga daki na zube a kan gado, gaba ki daya jikina rawa yake yi. Hafsat tace "wai kina nufin bai gaya miki zasu zo ba?" Na girgiza mata kai. Muna nan zaune har suka tafi sannan muka fito palo, kaya muka tarar a gaban Mommy akwati biyu, kayan kwalliya ne kawai dana gyaran jiki. Ina ta jiran inji anyi min wata magana shiru babu wanda yace min komai, har muka yi dinner da Daddy shima bai yi min magana ba. Sultan bai zo ba kuma babu wanda yayi maganar sa. Na gaji da zama na tashi na ce musu sai da safe na hau sama. Na kwanta amma sai juyi nake yi na kasa bacci, me hakan yake nufi? Babu abinda zuciya ta bata ayyana min ba kuma duk marasa dadi. A haka har bacci barawo ya dauke ni.
Cikin bacci naji ana shafa fuskata a hankali, a tsorace na tashi ina rarraba ido, Sultan na gani a zaune a gaban gadona yana dariya, nayi sauri naja bargona lullube jikina duk da cewa dakin da akwai duhu. Nace "Sultan me kake yi anan ne? Na shiga uku, ka tashi ka fita, yanzu in Mommy ta shigo ta ganka fa?" Yana dariya ya saka hannu ya kunna bedside lamp, nayi sauri na kashe, nace "babu kaya fa a jikina dan Allah ka tashi ka fita" ya mike tsaye yace "OK, bara in juya bayana sai ki saka kayan sai in juyo muyi maganar" nace "kowacce magana ce ka bari mana sai da safe mayi, Sultan Mommy nake tsoro, in ta shigo ta ganka a dakina cikin dare me kake tunanin zata ce" ya zagaye gadon yaje bakin kofa yayi locking ya zare key din yace "problem solved" na sake cewa "me kake yi a dakina" yace "zuwa nayi inga amaryata" Hijab dina na nuna masa ya dauko min na saka sannan na fito daga bargon na zauna bakin gadon na kunna fitila. Gabana yazo ya zauna ya harde kafafuwansa yana kallona da murmushi, na bata rai, "shine ka kashe wayarka ko" yace "ramawa nayi, dan kiji yadda nake ji in kin kashe min waya" nace "amma dai at least ka gaya min plans dinka kafin ka aiwatar ko? We are suppose to be a team, kawai sai ganin baki mukayi bamu san da zuwan su ba" yace "I told you I must do something, kuma sanda na hada plan dina kin kashe wayar ki, da safe kuma na ai watar da plan dina. Tunda naga Daddy yaki cewa komai ni kuma bana so in tambayeshi shi yasa na je na gayawa galadima nace yazo ya nema min auren ki a gurin Daddy, munyi rigima dashi sosai kafin ya yarda yazo din, yace na daina zuwa gurinsa na zama dan kaina and all that, ni kuma abinda yasa na daina zuwa gurinsa saboda bana son cigaba da hada su rigima da Takawa, sanda nake zuwa gurinsa kullum sai Takawa yayi masa masifa akaina, so kawai sai na rabu dashi, ashe shi haushi na yake ji. Su kuma su yaya su suka gayyaci kansu, kawai galadima ne yace in je in gaya musu maganar shine sai suka ce lallai sai sunzo sungan ki, fitinannun tsofaffi kawai" ya mike tsaye yace "oh God yunwa nake ji wallahi" nace "to baka fada min ba kuma abinda akayi" ya daga gira daya yace "akayi me?" "Maganar da suka zo yi me akace?" Yace "yarinya tana so tana kaiwa kasuwa, bazan fada din ba sai kin bani abinci naci." Nace "dakai me kake yi ba kazo kaci abincin ba" yace "ina office wallahi ina zane" da mamaki nace "zanen me kuma cikin dare?" Yace "zanen gidan mu, I made all the plans, gobe za'a fara aiki" na saki baki ina kallonsa. Daga tsayen da yake straight ya fado kan gado, nayi sauri na mike nace "Sultan menene haka kuma, tashi min daga gado" yace "nace miki yunwa nake ji, ni bani da energy din tsayawa" nace "amma kana da energy din hawa katanga ka shigo wa mutane daki ta taga ba" ya tashi zaune "please ki samo min abinci inci, Allah yunwa nake ji" na tashi na dauki key na bude dakin, ina fiya na sake rufewa da key ta waje. Duk da saukowar da Mommy ta fara yi, na tabbatar in ta shiga dakina taga sultan a kwance a kan gado to koma menene aka shirya sai an warware shi, maganar aure ta tashi. Na duba kitchen naga duk an yi wanke wanke babu sauran abinci, a fridge na samo masa wata gasashshiyar kaza, na dumama ta a oven na hado masa da fresh milk na taho. Ina shiga daki naga agogo ya nuna 2:19. Ina shiga na kuma rufe kofar, yana kwance ya mike ya zauna ya harde kafa na ajiye masa a gabansa na shiga toilet na kuskure baki na na dawo, yana kallo na yace "menene na wani zuwa ki wanke baki?" Nace "tayaka ci zanyi" na hau gadon na zuba masa madarar na mika masa. Sai da ya fara ci sannan ya fara magana "Daddy yace 'yalleman za'a je, sunyi fixing jibi zamu je tare gurin baffa, shine zai ce ya bayar ko yace ya hana. Amma shi gurin Daddy yace ba matsala" nayi shiru bance komai ba, yace "hey, ya kamata ki bani tukwuici mana" nace "OK, me kake so in baka" yace "a hug will be very much appreciated" na harare shi nace "only in your dreams" yana murmushi yace "it happens only in my dreams now, it will happen in reality very soon" na sauko daga gadon nace "tashi ka fitar min daga daki" ya gyara zama yace "da ace zan yi miki wani abu baby girl, da tun sanda na shigo kina kwance kina ta sharar bacci a lokacin zan miki, so relax, i have waited for so long, saura kadan ya rage min" na zauna a kan bedside ina kallonsa har ya gama cin abincin sa ya tattare kayan sannan koma ya zauna ya dauko wata takarda ya warware yace "come let me show you something" na zauna kusa dashi, ya fara nuna min wani zane yace "this will be our home, anan zamu rayu muyi raising kids dinmu" ya fara min bayani dalla2, na jima da sanin cewa sultan ya kware a aikinsa amma sai yau na gani in reality, gidan ya tsaru iyakacin tsaruwa, kuma katon gaske ne, dan in baifi gidan mu girma ba to zasu yi kai daya. Sai da ya gama yi min bayanin gidan ya ninke takardar sannan yace "baki tambaye ni a ina za'a yi ginin ba?" Nace "a ina" yace "a palace. Nayi magana da galadima zai gayawa Takawa, ba cikin palace din bane ba, daga bayansa ne wani daji ne babu abinda ake yi da gurin, in ya yarda gobe zan aika ayi clearing gurin. Ta gate din palace din za'ake shiga sai kuma a zagaya baya" nayi mamaki sosai, ban taba tsammanin sultan zai yi tunanin zama a cikin palace ba, amma kuma sai na tuna cewa sarauta a jininsa take, yana sonta sosai, kawai dai yana basarwa ne saboda kar ya kara wa kansa bakin ciki, na tuna motar daya siyo min 'Her Royal Highness' it means deep down he is considering himself as 'His Royal Highness' kenan. Banyi masa maganar ba saboda bana son spoiling mood dinsa.
Washegari kamar kullum ya fita da sassafe, sanda ya dawo lunch yake gaya min har ya aika za'a fara clearing din gurin, it means Takawa ya yarda kenan. Daga nan kuma yace galadima yana kiransa, bamu sake magana ba sai da daddare yace ba'a nan zai kwana ba saboda sa sassafe zasu tafi 'yalleman din, ta kano zasu biya su dauki uncle Aliyu shi zai raka su. Washe gari nayi wa Amira waya na gaya mata me yake faruwa sai gata nan tazo zata tayani zaman jira. Muna zaune sai ga message ya shigo min ta WhatsApp daga Sultan, hoto ne, ina budewa na saki baki ina kallonsa. Sultan ne, yaci ado da kayan sarauta, babbar riga, rawani, da alkyabba, maroon color da adon fari, rawanin kuma fari da adon maroon. Yayi kyau karshe, ban taba ganin sultan yayi kyau irin wannan ba, sarauta a jinin sa take, he is a real prince, a kasan hoton ya rubuta 'do u know this man?' Take na chanza dp dina na mayar hoton, sannan nayi masa reply, 'no, i have no idea who he is, but whoever he is tell him that I love him so much" yayi reply "ohh God, am jealous" sannan wani message din 'and I love you too"
Gaskiya ina jin dadin sakonnin ku sosai, jiya nasha dariya musamman a WhatsApp, ansha rigima tsakanin #teamSultam da #teamIbrahim. Da fatan dai ba'aji ciwo ba lol. I love you guys alot, stay blessed.
Episode Sixty One : Save the Date
Afuwan nayi mistake gurin numbering episodes, nayi fifty eight guda biyu, so daya shine fifty nine, daga nan kuma sai sixty.
A episode sixty kar kuji nace Sultan ya shiga dakin Moon ya kwanta a gado wata ta gayyato nata saurayin daki, duk abinda ya faru babu ruwan maman maama. Kai kuma saurayi kar kaji labarin sultan ya shiga dakin Moon ta taga kai ma ka kama katangar gidan su budurwarka ka haura, idan aka kamaka ba zan zo ceto ba, ehe. Remember, this is just a fiction.
Wajan azahar su Sultan sukaje 'yalleman. Sun samu tarya sosai dan an sanar da baffa zancen zuwan su, kusan duk uncles din Moon su zo taryan manyan baki. Kofar gidan baffa kam cika yayi da mutanen gari da suka zo kallon sarki, a cewar su. Hakimai uku ne suka tafi tare da galadima, sultan kuma cousins dinsa guda biyu da amir ne suka raka shi. A palon baffa aka sauke su, aka gabatar da sultan, ya gaishe da baffa, baffa yana ta tsokanar sa, daga nan aka sallame su suka tafi gidan nuraddeen suka bar manya zasu yi magana a tsakanin su. A gidan nuradden suka ci abincin da akayi ta kawo musu kamar babu gobe, Sultan ya zauna yayi ta shan fura yana santi wai dama abinda Moon take sha kenan in tazo 'yalleman shine bata taba gayyatar sa ba. Nan da nan suka saba da nuraddeen, yana ta bashi labarin Moon sanda tana yarinya. Suna zaune Moon ta kira shi, nuraddeen ne ya dauka, "ke wato yau kadai din ma ba zaki bar mana shi ba ko? Sai kin dame mu da waya?" Tayi dariya "kai yaya, kira nayi fa in ce ya bani kai mu gaisa" yayi dariya "ni zaki yiwa yawo ko? Har da wani yaya sai kace da yayan kike ce min" suka yi dariya gaba daya sannan ya bawa sultan, tace "so...how are you?" Yayi murmushi yace "ke dai ki fadi gaskiya, kin kira kiji yadda nake ko kuma kin kira kiji me ake ciki?" Tayi dariya tace "yanxu shikenan bani da right din da zan kira ka? I just want to know ya kuka je" yace "lafiya lau muka zo love, and maganr kuma da kike so kiji ni ma ban sani ba, suna can suna maganganun su" tace "ni ba wannan ne yasa na kira ka ba, so nake inji ya akayi aka saka maka hular rawanin nan da wannan gashin na kanka?" yayi shiru bai bata amsa ba, ta fara dariya, tace "don't tell me aski aka yi maka" ya bata rai yace "don't laugh, give it a week, zai dawo ne. Besides, ba du aka aske ba ai" tace "can I see it?" Yace "never, ba zaki taba gani ba har sai ya dawo yadda yake"
A wajen su baffa kuwa sosai suke ta shan hira abinsu, da yake baffa mutun ne mai barkwanci nan da nan bakin suka saki jiki da shi suke ta hira. Sai bayan sunci abinci sunyi sallah sannan galadima ya gabatar da maganar data kawo su, suna nemawa dansu Abbakar Sadiq Abdullahi auren Maimunatu Muhammad Dikko, daga nan ya aika aka shigo da wata jaka cike da kudi, aka ajiyewa uncle Aliyu aka bude, mint ne 'yan 1000, galadima yace "ga kudin aure nan, muna fatan zaku karba" kowa ya saki baki yana kallon kudin, uncle Aliyu ya kallu kudin da yasan zasuyi daga miliyan biyar zuwa sama, ya saka hannu ya dauki rafa guda biyu ya ajiye a gefen sa yace "mun gode sosai amma wannan ya isa, albarkar auren muke nema, wannan ma mun dauka ne saboda al'ada ne" Tafida ya matso zai yi magana, baffa yace "abinda zamu iya karba kenan. Tun sanda labarin yaron yazo mana na tura Aliyu yaje har Abujan yayi mana bincike akan yaron, kuma yace min ya gamsu da abinda ya samu, dan haka tunda shine waliyinta na yarda da maganarsa. Na bawa Abbakar Sadiq auren Maimunatu, Allah yayi musu albarka baki daya Allah kuma ya sanya alkhairi" gaba daya aka ce "Ameen" uncle Rufa'i yace "to sai maganar sa rana kuma, yaushe kuke ganin za'ayi?" Tafida yace "ni ina ganin kar aja kwanaki da yawa, matsalar dai kawai yaron bai kammala ginin sa ba, dan haka ina ganin a bashi wata biyu, insha Allah kafin nan ya kammala, ita ma amaryar kafin nan ta shirye2n hidimarsu ta al'ada" kowa yace "wannan yayi, Allah ya kaimu" daga nan nan akayi addu'ar neman alkhairi aka tashi. Sultan kam da aka gaya masa me aka yanke ji yayi kamar ya dora hannu aka yayi kuka. Tun a hanya yake mita "wai wata biyu, ko garin abuja zan gine gaba daya ai iyakacin kwanakin da za'a bani kenan, aikin ginin nawa da a cikin sati daya zan gama shi, aikina ne fa" Ahmad, cousin dinsa yace "why are you whining ne Sultan? Tunda ance an baka ba shikenan ba? Me kake yiwa sauri ne wai" Sultan kawai tsaki yayi yace a ransa 'ba zaku gane ba'
A abuja kuwa kiran gaggawa Daddy ya samu daga fada, nan da nan ya tafi, yana zuwa mai martaba sarki ya nemi a basu guri zasu gana, yace "Muhammad dama abinda kake shiryawa kenan? Dama dalilin da yasa ka dauki yaron nan kenan" Daddy yace "Allah ya taimakeka sam ba haka bane, mayar da Sultan gida na daban da alakarsa da yarinyar wajena" Takawa yace "bakasan halin yaron nan ba labarinsa kakeji, duk inda tunanin ka ya kai to ya wuce gurin. Ina tausayawa yarinyar nan, she have no idea what she is in for. Ka taimaka mata ka janye maganar auren nan. Bana son abinda zai bata zumuncin da yake tsakanin mu. Nasamu labarin itin tarbiyyar da ka bawa 'ya'yanka, sam yarinyarka bata dace da yaron nan ba. He don't deserves her" Daddy yayi shiru yana tunanin amsar da zai bayar, sai yace "Allah ya taimake ka ni bani na hada yaran nan ba, hadin Allah ne, kuma magana ba'a hannu na take ba tunda tun dazu suka ce min har sun isa 'yalleman gurin baffa na, yanzu maganar tana hannun sa. Ni ina ganin mu zuba ido kuma muyi addu'ah mu ga zabin da Allah zai yi mana" Takawa yayi shiru kamar ba zai sake magana ba, sannan yace "mu dai mun gayama gaskiya, wanda bai ji bari ba kam tabbas zaiji hoho. Fatan mu shine duk abinda ya faru kar kazo gurin mu. Zaka iya tafiya" Daddy jiki duk ba kwari ya mike ya fito, har yaje gida yana lissafin lallai da akwai wani abu a tsakanin Sultan da babansa wanda duk bincikensa bai sani ba, koma dai menene, it is something big.
Moon
A dakin Hafsat muka zauna, hira kawai muke yi muna dariya abin mu, muna ta labarin Haihuwar Hafsat da irin shagalin da zamu yi ranar suna. Edd dinta ya riga yayi kawai haihuwa ake jira. Hira nake ina dariya amma can kasan raina ina tunanin abinda yake faruwa a 'yallemam. Muna cikin haka naji shigowar kiran Sultan, na daga ina kallon sunan jikin screen din 'my Sultan' na tuna ranar da yayi saving sunan da kansa a waya ta, ranar dinner din Hafsat, a lokacin ban taba tsammanin zan dauki kiran saba ko da ya kirani sai gashi yanzu ya zama tamkar wani sashe na jikina wanda ba zan iya rabuwa da shi ba. Yanzu gashi wai yana kirana ne ya gayamin an bashi aure na ko ba'a bashi ba, sai naji na kasa daukan wayar har ta katse, ya sake kira shima naki dauka. Amira tace "in ba zaki dauka ba bani shi nan, har wani Sultan akewa kunya? Baki san ance kunyar mara kunya asara bace" na mika mata wayar, tana karba aka sake kira, gani nayi ta taba rai ta dawo min da waya ta, na duba screen naga 'Amir" dariya nayi dan nasan drama dinsu da Amir na dauka, yace "wai kunyar amarcin ce za'a fara yi mana tun yanzu?" Nayi murmushi kawai bance komai ba, yace "gamu nan mun taho, amma na san sai dare zamu karaso Abuja, tell that your ugly friend ta shirya mana abinci dan anan zamu fara sauka" nayi kamar banji ba, na saka shi a hands free nace "me kace?" Yace "wannan kawar taki mummuna, bakar nan masifaffiya, kice mata ta dafa mana abinci kafin muzo" ai kuwa Amira ta warce wayar daga hannuna ta kama yi masa masifa "yanzu har kai zaka kalli wani ka kira shi da ugly? Anya kuwa kana kallon fuskar ka a mudubi kuwa? Duk baki na wallahi ni balarabiya ce akan ka" ni dai dariya nake yi Hafsat tana taya ni. Sai bayan isha suka zo, iyakacin samarin ne suka zo nan manya kowa ya kama gabansa, uncle Aliyu ma yazo ya taho da Amina wacce daga jin zancen biki ta rude ta hado kayan ta. A palon su Sultan suka sauka nan aka shiga hidimar kai musu abinci, sai da suka gama sukayi sallolinsu sannan muka je, ni da Amira da Amina. Muna shiga aka fara drama da Sultan dan fir yace babu wanda zai ga fuskata, ai an bashi ni yanzu dan haka i am no longer in tha market. Su Ahmad suka yi ta naci su kuma lallai sai sun ga fuskata tunda takabas dan su ganni suka zo, da kyar dai Sultan ya yadda na bude fuska ta, shima kuma ya kasa ya tsare yace babu dogon kallo, ni dai dariya kawai nake yi musu. Nan fa Amira da Amir suka dora daga inda suka tsaya, Amina ma da yake mai surutu ce sai ta shige cikin su suke tayi. A hankali sultan ya mike ya je bakin kofa sannan yayi min alama da in zo, tsam na zame na bishi ba tare da duk sun lura mun fita ba. Ina fita sai naga ya kama hanyar garden na bishi a baya.
Akan kujera ya zauna nima na karasa na zauna a kusa dashi, ya juyo yana kallo na nayi sauri na sunkuyar da kaina kasa ina murmushi, dariya yayi sosai yace "wai ni kike jin kunya kuma? Tsafdi, lallai kin hadu da aiki" ni dai bance komai ba, ya kamo hannayena duk biyun yana kallon su, sannan a hankali ya shafa zoben sa da har yanzu yake makale a danyatsa na. Sannan yace "wata biyu suka ce, what if something happens a cikin watanni biyun? Na kalle shi naga ya sunkuyar da kansa yana kallon hannayen mu a hade, nace " Sultan, babu abinda zai faru kaji? Kullum muna addu'ar zabin alkhairi, tinda har Allah yasa suka ambaci wata biyu to sune mafi alkhairi a gare mu. What if da ace baffa cewa yayi NO? Ya zakayi kenan?" Ya dago da sauri yana kallon idona yace "then I will definitely be your patient, dan kwakwalwata zata iya bugawa" na same hannu na daga nasa na tallafo fuskarsa dasu ina kallon idonsa nace "babu abinda zai same ka, shi Allah baya taba dorawa bawansa abinda yasan ba zai iya ba" ya katse ni yace "then Allah ba zai raba mu bama, saboda yasan ba zan iya dauka ba" idonsa gaba daya ya chanza kala, nayi saurin chanza maganar nace "Askin ka yayi kyau" Hannu biyu ya saka ya rufe kan sa yace "ash, ya akayi na bari kika gani" nace "really yayi kyau, I like it" ba duk gashin aka aske ba, an rage masa tsaho dai, sai ya fi dacewa da sajen sa, fuskarsa kuma ta kara fitowa sosai. Ya shafa kan yace "thank You" sannan ya cigaba da magana "tom yanzu cikin two months din nan me za muyi?" Nace "kamar me fa?" Yace "to kill the time" nace "as usual, kai already ma ai aiki yayi maka yawa, ga office ga harkar gini, ni kuma I will just be here, waiting" yace "driving lessons din mu fa?" Nace "bayan ba wani abin kirki kake koya min ba, for over one month amma ace har yanzu ban iya driving ba" muna cikin haka muka ji muryar Amir "to in kun gama soyewa sai kuzo muyi sallama mu zamu tafi gida" na tashi ina dan jin kunya, muka fito muka tarar har sun dauko mota mukayi sallama suka tafi, Amir kuma ya dauko motar sultan guda daya, yana zuwa gurin mu nace "Amir dan Allah ga Amira nan ka kaita gida, kaga dare yayi sosai" a tare suke ce "what?" Ni da sultan sai dariya, sultan ya bata rai yace "gaskiya Amira in ba zaki shiga motar Amir ba to sai dai ki hau taxi, dan ni na gaji ba zan kai ki gida ba" Amir yace "to ni an gaya maka ban gaji bane? Ballantana wannan unguwar tasu mai shegen nisa, kuma ni ba ma nason a ganni da ita a mota a daukar ko budurwata ce, ai sai aji na ya zube" nan Amira ta hayayyako "Allah ya kiyaye min shiga motar ka, ni da in shiga motar ka ba gwara na tafi a kafa ba" yace "ai kuwa zaki tafi a kafar" har yaja mota sai kuma yayi reverse, yace "get in" kawai sai muka ga Amira ta zagaya ta bude ta shiga sun tafi, daga ni har sultan duk sakin baki muka yi muna kallon su, Sultan yace "munafukai, a hankali sai asirin ku ya tonu"
Rayuwa ta koma normal, abubuwa suna tafiyar mana yadda muke so, sultan ya dukufa haikan akan aikin gininsa duk da kusan tare muke aikin dan dai ni bana fita field dinne amma komai tare muke tsara shi, komai za'a saka a gidan sai ya kawo min samples na zaba tukunna, ba karamin kudi yake narkar wa a aikin ba dan ni har mamakin inda Sultan yake samun kudi nake yi, gani nake kamar aikin sa ba zai shigo masa da wadannan uban kudaden ba. Rannan mun fita koyon mota sai yace min yana so zamu je wani guri. Hanyar barin gari naga mun dauka amma ban tambaye shi ina jamuje ba. Gani nayi yayi packing, na fito ina kallon gurin da muka zo, orphanage, a kafa muka shiga cikin building din. Babban guri ne sosai, ga dakunan yara, maza daban mata daban, ga gurin wasa, ga kitchen sannan ga offices din staff. Muna shiga ma'aikatan gurin suka fara gaishe mu da girmamawa sosai kamar zasu kwanta a kasa, ni har mamaki nake yi, idonsu kawai zaka kalla kaga tsantsar soyayyar sultan da kuma respect dinsa, ya fara tambaya "where are my kids?" Da sauri wata tace "suna playground suna wasa" muka tafi gurin, ina ta kallonsa naga wani excitement a fuskarsa, real love, ai kuwa muna shiga gurin wasan gaba daya rayan suka taho a guje wasu har suna faduwa suka rungume shi, sai da suka kai shi har kasa yana ta kyalkyala dariya, in ba tare da ni ba ban taba ganin sultan cikin wannan fara'ar ba, da kyar ya samu suka daga shi, ya zauna a zaune suka zagaye shi kowa yana kokarin bashi labari, ga mamakina duk yasan sunan kowa kuma yasan me yake ciki, ni sam bana fahimtar me suke cewa saboda yadda suke magana gaba dayan su a tare. Sai da suka dan numfasa sannan ya tashi ya kamo hannuna yace "na kawo muku bakuwa yau, Mommy zaku ke ce mata, she is going to be my wife" masu wayon cikin su suka kama murna marasa wayo kuma kawai suka tsaya suna kallona, har cikin dakunan su ya shiga dani na gani, ko wanne yaro da gadonsa sai 'yan kanana ne ake musu shimfida a kasa saboda kar su fado, gurin tsaf tsaf babu kazanta, ko wanne yaro da locker din kayansa, ga kuma inda suke cin abinci shima a tsaftace, muka shiga kitchen masu aikin girki suna ta gaishe mu, suka bashi list din abubuwan da suke bukata nan take ya bada kudin yace a saya, muka shiga dan karamin clinic dinsu shima ya nuna min sannan yace yana son ya dan yi musu 'yar karamar makaranta amma sai nan gaba tukunna, yanzu dai van ya saya musu ake kaisu kamaranta kullum ake dawo dasu. Har zamu tafi wani yaro yazo da gudu yana bata fuska yace "Daddy kace in ka dawo zaka kawo min bindiga kuma gashi ka dawo baka kawo min ba" Sultan ya sunkuya har kasa yana shafa kan yaron yace "sorry Halifa, na manta, amma gobe insha Allah zan bawa uncle Amir ya kawo maka" yayi masa kiss a goshi, yaron ya tafi yana ta murna. Ji nayi kwalla ta taru a idona, yanzu na fahimci inda sultan yake samun kudi, as long as kana kyautatawa mutane da dukiyarka, musamman marayu, to Allah zai yi ta ninka maka kofofin arzikin ka, abinda ka bayar sai Allah ya biya ka da dubun sa, mutum kamar sultan ba zai taba talauci ba. Muna shiga mota ya kama hannuna daya ya rike yake tuki da dayan hannun, babu wanda yace komai, can nace masa "da ka gayamin nan zamu zo at least ai da na taho musu da wani abu ko?" Yace "you are welcome, duk sanda kike son zuwa zan kawo ki" na sake yin shiru a raina ina mamakin mutum irin sultan.
Tafiya muke a hankali kamar ba ma son zuwa gida, kowa da tunanin da yake yi, har yanzu kuma yana rike da hannuna, sai da muka yi nisa nace "Sultan ya kamata kaje gurin Takawa kuyi maganar bikin nan dashi" ba tare da ya kalleni ba yace "naje ai" da sauri na kalleshi ina mamakin ya akayi bai gaya min ba, packing yayi sannan yace "Abbas ne ya kira ni a waya ina office yace min inje Takawa yana kirana, da naje gurinsa na gaishe shi bai amsa ba, kin san me yace min?" Na girgiza kaina, yace "check book ya jeho min duk yayi signing pages din yace 'ka dauki duk adadin kudin da kake so kayi duk abinda kake so dashi, amma ina son ka fasa auren yarinyar nan, she doesn't deserve someone like you" yayi shiru fuskarsa tana nuna bacin ransa, a hankali na tambayeshi, "me kace masa kuma" ya daga kafada yace "na ajiye masa check book dinsa na ce masa bana bukatar kudinsa, abinda da nake nema daga gare shi ma yanxu bana bukatar sa" ya juyo yana kallona yace "all I wanted before is love, yanzu na samu daga gare ki, kowa ma yaje ya rike nasa, your love is enough for me" hawaye naji yana fitowa daga idona (is it possible to love someone so much that it makes you cry?) Ya saka hannu yana goge min hawayena yace "just promise me that you will never leave me
Episode Sixty Two : The Manager
Na kalli cikin idonsa nace "I will never leave you, dama parents dina kawai nake ji, tunda yanzu na samu go ahead din su babu abinda zai saka in rabu dakai" a hankali yanayin fuskarsa ya fara chanzawa daga bacin rai zuwa murmushin da ya saka nima na fara murmushi yace "then I don't need anybody else" Mun dau hanyar gida again naji wayata tana ringing, na daga naga Mommy, ina dauka tace "ya akayi har yanzu baku dawo ba? Ku zarto asibiti mun tafi da Hafsat yanzu tana labor" a rikice ta katse wayar ina kallon sultan nace "Hafsat....labor... Hospital" nan take Sultan ya gane abinda nake nufi ya juya kan mota muka tafi asibitin da Hafsat take antinatal. A hanya na dauko wayata ina neman number, sultan yace "wa zaki kira?" Nace "Zayed" yace "No, ki bari sai ta haihu tukunna" na mayar da wayar na ajiye. Muna zuwa da sauri na fita na bar sultan a mota, a waiting room na samu Mommy da Amina, Mommy tana ta faman jan charbi. Na samu guri nima na zauna. Ba'a jima ba aka leko aka ce wata a cikin mu ta shiga ta zauna da ita, da sauri na tashi na shiga. Zan iya cewa tare muka yi laborn da Hafsat, in tana kuka nima sai in kama kukan, in tana addu'ah in taya ta. A haka mukayi ta fama har dare ya raba, Sultan yana ta kira yana tambayar jikin Hafsat, a lokacin na kara jinjinawa mata da irin wahalar da suke sha a gurin haihuwa, a lokacin kuma na kara jin haushin duk matar da zata haihu ta dauki dan taje ta yar, kuma na kara tsanar duk dan da zai ki yiwa iyayensa biyayya. Hafsat ba ta haihu ba sai da alfijir ya fara keyowa, ta rike ni gam tamkar zata ballani sannan ta haifo kyakykyawar 'yarta mace, ana goge yarinyar na karbe ta na rungume ina jinsonta yana shiga zuciya ta, Hafsat ba kunya babu tsoron Allah tana samun kanta tace in bata 'yarta, har nurses din wajan sai da suka yi dariya. Na dora mata ita akan cinyarta ta fara shayar da ita (shayar da baby a wannan lokacin yana taimakawa wajen tsayar da jini da kuma saukin fitar mabiyya, kuma yana taimakawa jariri wajan saurin koyon shan nono da wuri kuma wannan ruwan nonon na farko yana da matukar amfani a gurin jariri). Gari yana wayewa aka fito dasu dakin hutu, nan fa dakin ya cika da 'yan ganin baby, ina ta Allah2 in kira Zayed ashe har Sultan ya riga ni, Mommy da Daddy sai rige rigen daukan baby suke, Hafsat kam cewa tayi ayi mata allurar bacci dan tana son hutawa, tayi kwanciyarta a ciki mu kuma muka taho daya dakin muna ta hayaniyar mu. Bayan azahar sultan ya kirani a waya, ina fita na tarar dashi a mota ya ce min "shigo" ba musu na shiga, naga ya tayar da mota, nace "ina zamuje?" Yace "gida zan kaiki kije ki huta, jiya baki yi bacci ba throughout" nasan gaskiya yake fada dan haka na kira Mommy nace mata zanje gida in anjima zan dawo, ina zuwa kuwa na tafi daki na na kwanta sai bacci, ban koma asibitin ba sai da daddare muka tafi tare dasu asma'u da suka dage sai sunje sun ga baby ba zasu jira su dawo gida ba, muna zuwa Zayed ya kira daddy yake gaya masa cewa ya samu delay din flight dinsa amma dan haka daddy yayi wa baby huduba da sunan Mommy, Fatima Zahra, Mommy kasa rufe baki tayi dan murnar an yi mata takwara, kowa sai murna har Hafsat taji dadi sosai, Daddy ya karbe ta yayi mata huduba ya miko min ita, Amina ce tace "to Hafsat yanzu me zamu ke ce mata kenan, tunda dai ai mu ba zamu kira ta da sunan ta ba" Hafsat ta daga kafada, sai gaba daya suka juyo suna kallona, ni aka barwa zabi kenan, na kalli babyn sosai ina ganin tsantsar kyawunta na larabawa, nayi murmushi nace "Khairat, we will call her Khairat" a tare Daddy da Sultan suka juyo suna kallona, nayi kamar bansan sun gane me nake nufi ba, Mommy tayi dariya tace "perfect, yayi sosai, Allah yasa ta zama sanadin alkhairi a gare mu baki daya" nan kowa yace "Ameen" Hafsat ma murmushi take da alama sunan itama yayi mata dadi, sultan bai yi magana ba sam, ni kuma ban kalle shi ba, sai daga baya na lura ya fice daga dakin. A mota na same shi ya kwantar da kujera ya rufe idonsa kamar mai bacci, na zauna kusa dashi nace "in bacci zakayi ka tafi gida mana" ba tare daya bude idonsa ba yace "why Khairat? Why do you want her when she doesn't want me?" Bance masa komai ba saboda babu abinda zance masa, jin nayi shiru ya saka ya bude idonsa yana kallona yace "yanzu zaki tafi gida ne?" Nace "a'a, anan zan kwana ai" yace "OK, but ki tabbata kinyi bacci sosai, kar ki biye wa little Khairat" nayi murmushi na fita, na tsaya nace "good night" yace "good night love". Washe gari da safe aka sallame mu muka koma gida, a ranar kuma Zayed yazo. Sati yana zagayowa akayi suna, anyi taro sosai, kayan barkan da Sultan ya hado in wani ya gani zai iya tunanin shi aka yiwa haihuwar. Ana gama hidimar suna Mommy ta juyo kaina, tace yawo ya kare, babu inda zan ke zuwa. Shirye shirye ake yi sosai, dan har gyaran gida Daddy yayi, Amira da Amir sune chairman da chairlady din committee n shirye shirye, Sultan yace shi big wedding yake so, a cewarsa it will be the biggest day of his life, dan haka dole yayi celebrating. Ni nafi so ace anyi komai kadan amma mutane sunfi karfi na, dan anko sai Amira ta fitar da kala biyar, wai kowanne event sai anyi masa nasa ankon, kawayen mu na secondary school duk sai da Amira ta je ta gayyato su, ni dai ban samu damar zuwa ba saboda Mommy ta hana ni fita sam. Takanas Mommy ta dauko wata mata daga maiduguri wai zata min gyaran jiki, ni dai kawai jinsu nake dan banga abinda za'a gyara a jikina ba. Ranar farko da matar tazo muka shiga daki da ita, ta shiga toilet ta hada wani ruwa a tub, tace in cire dukkan kayan jikina in shiga ciki sai nayi awa daya tukunna, ina jin haka na dau waya ta da ear piece na je na shiga na kwanta na kira Sultan lokacin yana office muke ta hirar mu, ban ma san sanda awa dayar ta wuce ba, sai ganin matar nayi ta dawo da wani soso a hannunta, na yiwa Sultan sallama nace mata "wannan soson fa?" Tace "dashi zanyi miki wanka yanzu da wannan sabulun" na bata rai nace "ni zaki yiwa wankan?" Tace "eh, ai wannan ruwan da kika shiga kamar jika ki nayi yanzu kuma zan chuda ki ki fita tas" ni dariya ma abin ya bani, wato ana nufin duk wankan da nake yi ba fita nake ba shine yanzu za'a yi min wani. Bana son in gwale matar nace mata "OK, bani soso da sabulun, ni zanyi wankan da kaina" tace "ai ba zaki iya da kanki ba, anfi so wani yayi miki saboda zaki fi fita" yau naga rigima, ni kam babu yadda za'ayi in zauna kamar wata jaririya ayi min wanka. Ganin na dage da gaske nake ba zata yi min ba yasa ta fita ta kirawo Mommy, Mommy tana zuwa ta karba tace ta bata ita zata yimin da kanta, ai kuwa kam nasha durza kamar za'a ciremin fata, ni gani nake duk wahalar da ni suke yi suma suna wahalar da kansu, ban tashi sanin bani da wayo ba sai da na fito na kalli kaina a mudubi, gani nayi kamar wadda aka cire min fata ta aka saka min wata, a hankali nasa danyatsa na taba jikina, wani laushi da santsi naji jikina yayi. Ina fitowa kuma aka hada wani kaskon turaren wuta aka saka na tsuguna akai, wani irin kamshi ne mai tsadadden dadi yake ratsani, bargo matar ta saka ta lullube ni, sai fuska ta ce kawai a waje, sai da nayi 30 minutes a haka. Bayan na tashi kuma ta dauko wani mai ta bani tace duk in daina amfani da mayuka na sai shi kadai har lokacin biki na, kuma tace in na tashi shafawa a duk jikina zan shafa. A haka muka rabu da ita tace bayan kwana uku zata sake dawowa ta sake yi min wani wankan da turaren. A raina nace wannan me kuke so in zama kafin lokacin bikin? Ta kara jaddada min kuma banda fita rana, sam ba'a son rana ta taba ni.
Hafsat ma kanta ranar dana zauna a kusa da ita sai da ta rinka shanshanani tana cewa ya akayi ita ba'a yi mata irin wannan ba lokacin bikinta, amma tace in dai tayi arba'in itama sai anzo anyi mata. Ranar kam kin zuwa gurin sultan nayi saboda bana son ya saka ni a gaba da tambayar wanne turare na chanza, shima kuma da yake yanzu kullum a gajiye yake sai bai wani matsamin inje ba, a waya dai muka karaci hirar mu. A hankali komai na ginin sultan ya kammala, Hafsat da aunty Maryam kawar Mommy da gwoggo Aisha, matar uncle Aliyu ne suka je suka gano gidan saboda siyayyar kayan daki, tunda suka dawo suke santin kyau da tsarin gidan, Hafsat har dare zancen gidan nan take yi har sai da Mommy tace "ya ishe mu haka, munji yayi gida mai kyau, congratulations to him" sannan Hafsat tayi shiru. Har yanzu Mommy ba wani son sultan take yi sosai ba amma dai ba kamar da ba, duk da yanzu ta daina ce masa tsagera da sauran sunayen da take kiransa dasu amma har yanzu bata ambaton sunan sa, sai dai tace masa wannan yaron. Dama tun tuni ni da Sultan mun tsara colors din da muke so ayi furnishing ko wanne daki dashi, da colors din yayi amfani gurin tiling da fenti, dan haka na zauna na tsara wa Hafsat komai yadda nake so ita kuma ta gaya wa Mommy, a cikin sati daya akayi order komai aka kawo, masu interior decoration aka dauko suka je suka saka komai, suka kuma kara abinda suke ganin ya kamata su kara. Ni kaina nasan Daddy ya narkar da kudi a kaina. Tun ana saura sati uku biki aka gama shirya gidan tas aka rufe.
Saboda tsabar gyaran da jikina yake samu gani nake yi kamar in aka tabani jini ne zai fito, fuskata har wani kalli take yi saboda tas din da tayi, idan na zauna a guri kuwa ko bayan na tashi kamshina yana nan. Dole na kara jan jikina daga gurin Sultan dan sosai yake nuna min kwalamarsa a fili, sau da yawa in yana zaune a kusa dani yayi ta shanshana ni har sai na tashi na gudu. Da kadan da kadan gida ya fara cika da mutane, daada ta iso da jama'ar niger, part dinta aka bude mata suka sauka a can, tana zuwa itama ta fara dura min tsumi, kullum da akwai abinda zata bani in sha, daga farko dariya nake yi mata dan ni gani nake duk wani maganin mata kawai fada ake yi, dan mu a likitance bamu san wannan ba, ban gane bani da wayo ba sai da na fara jin chanji a jikina, babu shiri na daina shan tsumin daada, inta bani sai inzo in ajiye a fridge in yi tafiya, data fahimci me nake yi ta tambaye ni dalili sai nace mata ta ajiye min in anyi bikin sai inke sha acan, sosai ta fahimci abinda nake nufi dan haka ta daina bani, sai da hado min su jaka guda kowanne da bayanin yadda zan yi amfani dashi ta bani tace in tafi dashi can, na karba nayi mata godiya, ni sai inta mamakin daada da Mommy, su da basa son sultan kuma me yasa suke yi tayi masa tanadi haka?.
Saura sati biyu biki aka kawo kayan lefe, akwati set goma aka kawo,different colors, ni har kasa tsayawa nayi in kalla saboda kayan sunyi min yawa, duk kayan kuma Yaya ce tayi su, tace tata gudunmawar kenan, dan haka da Daddy ya saka sultan a gaba da fadan kayan sunyi yawa sai ya gaya masa yace shi ko dan kunne bai saya a ciki ba. Kaya ne masu tsada daga gani kasan cewa akwai class. Sarkokin gold akwatin su daban. Kuma komai size dina, daga gani kuma kasan babu abinda aka saya a Nigeria. 'Yan 'yalleman dama basu zoba sai ranar da aka kawo kayan, daga nan suma suka bude part din su inna suka baje tasu hajar. Hajja kam sai yada magana take tana kunkuni 'ai dama sai da jikina ya bani, kudi suka gani shi yasa suka hana yaron nan, duk abinda kuwa aka saka bidi'a a cikin sa ba zai yi albarka ba. Shima Allah ya bashi arzikin da yafi wannan kuma Allah ya bashi matar da ta fita" babu wanda ya kula ta haka ta gama sumbatunta.
Inna kam tana zuwa ita tsarabar data kawomin shine na adduoi, tace "gidan sarauta zaki je dole kina bukatar tsari sosai, tsari daga sihiri, tsari daga mugun baki, tsari daga dukkan sharri na mutun kona aljan" ta babbani rubutu na sha, ta kuma koya min adduoin tsari sosai, sannan tayi min nasihu masu ratsa jiki akan kula da addini, tsarkake zuciya da iya mu'amala da mutane, tace as long as kana kula da addinin ka sosai, ka kuma tsarkake zuciyar ka baka nufin kowa da sharri to Allah ba zai taba bawa makiyinka nasara akan kaba. Shi kuma iya zama da mutane shi zai kara maka soyayyar miji ya kuma jawo maka soyayyar 'yan uwan miji. Naji dadin nasihohinta sosai, sai nake ganin kamar duk ita tafi kowa bani tsarabar gidan miji.
Kamar yadda akayi bikin Hafsat haka nawa ma zai kasance, su Mommy sun shirya kunshi, kamu da mother's eve, su kuma su Amira da Amir 'yan committee sun shirya bridal shower, luncheon, dinner, sai walima for girls, and bachelor's night for the guys. Sai kuma ranar da aka kai amarya Amir ya shirya mana welcome party anan gidan mu da Sultan. Ni already jina nake a gajiye, I have no idea yaya zan iya duk wadannan events din.
Har yanzu wasan buya muke yi da Siltan, dan sosai nake rikita masa lissafinsa in muka hadu, nima kuma tunda daada ta fara dura min tsumin ta na fara ja baya dashi. Yayi mitar har ya gaji, gashi gidan ya fara cika da mutane balllantana yace zai yi abinda ya saba ya shigo min daki cikin dare. Shima kuma yanzu ya dan fara ja da baya da zaman gidan saboda baki. Wani lokacin sai dare yake zuwa sai dai insa akai masa abinci office, da daddare kuma sai in aika masa dashi dakinsa.
Ten Days To The D- Day
Tun safe Amira tana gidan mu, sun hadu ita da Amina suna ta ware min kayan da zan saka a kowanne event, ni kallo kawai nake bin su dashi saboda already Sultan ya bada dinkunan mu ni dashi na kowanne event, anko zamu ke yi, wanda kuma na mata ne kadai shima ya dinka min abinda zan saka, hatta takalmi da jaka babu wanda bai saya ba, hotunan yake turomin ni kuma ina zaba, tunda yanzu mun zama mage da bera bama zama a guri daya. Sai da suka gama shan wahalar su sannan nace "kun gama?" Suka juyo suna kallona nace "to sai ku mayar min da kaya jikin akwati basu zan saka ba" na gaya musu tsarin mu da Sultan, Amira ta bata rai tace "kuma dan wulakanci shine kika barmu muke ta wahala, amma wannan akwai munafukar amarya, shine zaku ware ke da angonki ku tsara abinku ba zaku fada wa 'yan committee ba" nayi dariya nace "'yan committee manya, wai dan Allah me kuke cewa in kun zauna meeting din ne? Yarinyar nan babu abinda ba tace min akan Amir ba amma yanzu in ka gansu suna kus kus sai ka dauka they are lovers" ta kara bata rai tace "lovers fa kika ce? Allah ya tsari gatari da saran shuka, ni kuwa me zanyi da wannan? Dan Allah yanzu ke a ganin ki mun dace?" Nace "sosai kuwa" tace "to amma kuwa ya kamata kije ayi miki wankin ido" Amina dai dariya take yi tace "Moon kinga yadda kika koma kuwa? Shi yasa yanzu in dai kina guri Sultan ba sosai yake fahimtar magana in an yi masa ba. Oh Allah. My future husband where are you? Am waiting" dariya nayi sosai nace "to ke ki lallaba munir mana?" Ta zaro ido waje "a 'uzubillahi, kije ki wanke bakin ki please. Ai ni da kike gani sabo zan bare a leda. Munir shi kam in aka ce masa gwanjo ma ai an rufa masa asiri" ta jawo ni tazo dai dai kunnena tace cikin rada "gayamin, Sultan sabo ne ko tsoho" na ture ta ta fada kan gado, nace "you will never find out" Amira tace "ni fa har yanxu ban sayi gown din da zan saka ranar bridal shower ba, kowa ya gama shirin sa ban dani, bayan itama da akwai abubuwan da ban saya ba" nayi sauri na zauna kusa da ita nace "kinga kawata, kuje ke da Amina gurin Mommy ku lallabata ta barni in fita, sai muje in kaiki ki siyo, wallahi na gaji da zaman gidan nan. Tunda sunce rana ce basa so in shiga ai yau babu ranar ma" Amira tace "ni kinsan Mommy yanzu ba shiri muke yi da ita sosai ba, sai dai ko Amina" na juya gurin Amina nace "please yaya Amina, kije ki tambayar min" ta bata rai tace "to in kun fita me zaki siyo min?" Nace "duk abinda kike so" nan ta jera min uban list na abubuwan da take so in siyo mata, duk nace naji na yarda. Ta fita muka zauna zaman jira. Sai da tayi wajen minti talatin sannan ta dawo tana bata fuska, har na sare, sai kuma tayi dariya tace "an barki, amma ki saka dogon hijab da nikab" murna kamar in cinye Amina, dan ji nake gaba daya na tsani kaina saboda zaman gida. Na kira Sultan a waya na gaya masa zamu fita da Amira, yace "OK, in kun gama ki yi min magana, nima ina son zamu je wani guri" nayi shiru bance komai ba, yace "please say yes mana, yaushe rabon da in ganki wajan three days" nace "ina zamu je?" Yace "where it all began, ina so muje muci abinci a Hilton, anan na fara ganinki" kawai sai naji ba zan iya ce masa no ba, nace "OK" yana ta murna na kashe wayar. Da sauri na shirya muka fita, har wadanda suke palo basu gane ni ce na fita ba saboda na rufe fuskata, daya daga cikin motocin Sultan na gani na leka naga key a jiki kawai na shiga na tayar, Amira ta shiga muka tafi. A gate mai gadi kin budemin yayi sai da nayi magana yaji muryata sannan ya bude yana dariya. Wani supermarket tayi min kwatance, ni ban taba shigar sa bama ina dai ganinsa a hanya, ita ma tace bata taba zuwa ba an dai ce mata akwai kaya masu kyau a can. Muna zuwa muka yi packing, na chire nikab dina na ajiye a mota, muka shiga, karshen haduwa gurin ya hadu, kaya kam akwai su, ga shi komai a tsare, nan da nan Amira ta fara lodar kaya, ni kam ban sayi komai ba saboda babu abinda nake bukata, a wajen siyan gown tayi ta ruwan ido, nace "wallahi in ba zaki dauka ba zan tafi in barki, Sultan fa yace zamu hadu in anjima" ta tsaya ta saki baki tana kallona, tace "dama rakonin da kika yi na munafunci ne? Dama gurin sultan zaki tafi? Wallahi kinsan ba karamin aiki na bane yanzu in kira Mommy in gaya mata" nayi ta bata hakuri ina lallabata "ba wani gurin zamu je ba fa, abinci kawai zamuje muci a Hilton, kuma motar sa daban mota ta daban" tace ta hakura ba zata fada ba amma sai in barta ta gama siyayyar ta a hankali. Sai da ta gajiyar dani sosai sannan tace ta gama, muka tafi gurin biyan kudi. Da POS ta biya kudin, aka bamu receipt muka fito, muna shiga mota na dauko waya ta da niyyar kiran Sultan naji Amira tace da karfi "what?" Na juyo ina kallonta da waya a hannuna naga wayarta take dubawa, nace "ya akayi?" Ta nuna min screen din wayarta naga alert ne na siyayyar da tayi yanzu nace "menene?" Ta nuna min receipt din, ni har lokacin ban fahimci me take nufi ba, tace "duba ki gani, sun kara min 10k a cikin kudina" nayi ajjiyar zuciya nace "please Amira, let it go, wallahi na gaji" tace "wallahi bazan hakura ba sai sun biya ni kudina, haka kawai dubu goma a banza, zo muje sai sun biya ni kudina" kamar zanyi wa Amira kuka haka na fita na bita muka koma ciki. A gurin cashier ta fara masifar sai an biya ta kudinta "How can you guys be so incompetent, ku kara min kudi har dubi goma?" Cashier kaman zata yi kuka tana bawa Amira hakuri amma Amira ta shafa wa idonta toka tace sai an biya ta, ni dai ina ta kallon agogo naga har karfe biyar, nasan duk inda six tayi Mommy zata kira ni tace in dawo gida, kuma gaskiya bana son missing date din mu da sultan, na karasa gurin rigimar naji cashier din tana cewa da Amira "madam kudin sun riga sun shiga account din shagon nan, ba zamu iya fitar dashi ba sai dai ki dau wani abun na kudin ki" Amira tace "ni na gama siyan duk abinda nake so in saya, babu abinda zan dauka kuma, kawai kudi na kawai nake so a bani" cashier tace "I can't do that madam, only the manager can do that, sai dai in zaki yarda in kaiki gurinsa inyi masa bayani sai ya biya ki kudinki" naga tsoro karara akan fuskar cashier din, daga alama tana tsoron manager din, nace "Amira ki zo mu tafi, ni zan biya ki 10k dinki" tace "wallahi bazan tafi ba chafdi, nasan sauri kike ki tafi gurin Sultan, in ya kira ki bani shi in yi masa magana" ni dai duk raina a bace, tausayin cashier nake yi, mistake tayi muka maybe zata iya loosing job dinta akan haka, da har nayi deciding inyi tafiya ta in bar Amira su karata amma sai na sake tunanin maybe in na bisu gurin manager din zan iya bashi hakuri kar ya kori cashiet din. Sai da ta fara yin waya ta tabbatar yana office sannan tace muzo muje, ta shige gaba muna binta a baya, ta hau stair muka bita zuwa hawa na uku, da kyar na karasa ina ta haki, taje bakin kofar tayi knocking, aka yi magana daga ciki, ta bude tayi mana alamar mu jira a waje sannan ta shiga ciki, Amira kam ba zata jira ba dan haka ta tura kofar ta shige ciki, nima na zo kofar na tsaya.
Cashier na hango tana ta kokarin yin bayani, muryarta sai rawa take yi, na dan shigo daga ciki dan in hango wannan manager da matar take tsoro haka. Ya dan juya side dinsa, dan haka banga idonsa ba, amma tsaf na gane shi. Familiar scent dinsa ne ya kara tabbatar min da cewa shine. Na kara taku daya cikin katon office din. He is still tall but no longer thin. Yayi kiba, jikinsa ya murje sosai, hakan sai ya bashi almost a giant frame. Doguwar fuskarsa ta cika, siririn sajensa ya kara fadi dan ya tafi da fadin da fiskarsa ta dan yi, dan karamin gemon da da yake dashi yanzu babu, meaning the ustaz part of him is gone. Amira naji tayi catching breath dinta very sharply. Fatarsa ta kara haske, tana kara nuna alamar hutun daya samu. He looks so different but still the same. Lokaci daya ya juyo ya kalleni idonsa ya fada cikin nawa dana bude ina kallonsa. His eyes look the same, babu abinda ya chanza. Suna nan a lumsassun idanun da nayi falling in love with all these years ago. Gabadaya yanayin fuskarsa ya chanza lokaci daya. Da sauri na juya na nufi kofa, bansan sanda ya sauko daga kan kujerar saba har ya zagayo table dinsa ba, ina dora hannuna akan doorknob naji nasa hannun akan nawa, ya jawo ni baya da karfi, cikin tsawa naji ya ce da cashier din data kawo mu "out" na fara kokarin kwace hannuna amma maimakon ya saki hannuna sai ya hada ni da kirjinsa ya matse. Na fara kokarin kwace wa amma sosai ya matse ni, kuka na saka sosai, still bai cika ni ba, ban san adadin tsahon lokacin da muka dauka a haka ba dan har sai da nayi kuka na na gaji dan kaina nayi shiru sannan ya sassauta rikon da yayi min. Ina kwacewa na rarumi wani file akan table dinsa na fara dukansa dashi, har sai da takardun ciki suka tarwatse sannan na kuma daukan wani na cigaba da dukansa ina cewa "why? Why? Why?" Bai hana ni ba har sai da dan kaina na gaji da dukansa na durkushe a gurin na sake wani sabon kukan. A hankali a durkusa a baya na yace "am sorry" na juyo a fusace nace "sorry? Abinda zaka ce kenan? Sorry?" ya sunkuyar da idonsa kasa yace "am sorry, i shouldn't have hug you like that, bai kamata in taba ki ba kina matar aure, am sorry i lost control of myself bayan ganin ki after all these years" na juyo da mamaki ina kallonsa dan ban fahimci me yake cewa ba nace "me kake nufi da matar aure kuma?" Yanayin yadda nayi tambayar yasa ya mike tsaye da saurinsa yana kallona gaba daya ya rude yace "ance min kinyi aure a shekarar da muka rabu, kwanan nan akace min kin haifi danki na uku"
Episode Sixty Three : Amira 3
Cikin tsananin mamaki nace "what? Waye ya gaya maka haka" gani nayi yana kallon office din kamar me neman wani abu, nima na taya shi dubawa, sai a lokacin na tuna cewa tare da Amira muka shigo office din, babu ita babi alamar ta. A zuciye naga yayi hanyar kofa yana cewa "I will murder that bitch" jiri naji yana kokarin dibana, nayi sauri na zauna a kujera, nasan da za'a gwada jini na a lokacin za'a tarar ya hau, Amira, why? Me yasa zata yi min haka? I trusted her. Babu abinda banyi mata ba kuma babu abinda ba zan iya yi mata ba. Ina zaune rike da kaina Ibrahim ya dawo cikin office din idonsa kamar garwashin wuta, ya fara zagaye office din da alama jinin yarabawan ne ya motsa. "She told me lokacin da Daddy ya san alakar mu ya hada ki aure da wani cousin dinki a 'yalleman, she even showed me the wedding invitation, after a year ta turomin message tace kin haihu" sosai kaina yake juyawa dan sama sama nake jin maganar sa, lokaci daya kuma naji wani realisations yayi hitting dina, Hafsat, oh dear God no, not Hafsat, i can take betrayal from Amira but not from Hafsat, na juyo na kalleshi nace "kaima ance min kayi aure, ka auri Efi" ya tsaya a zagayen da yake yi, yazo ya tsugunna a gaba na, expression din fuskarsa na kalla naji wani dadi a raina, at least Hafsat gaskiya ta fada. Yace "yes, na auri efi shekara daya bayan rabuwar mu, amma ban karbi auren ta ba sai bayan da na samu labarin kinyi aure tukunna..." Na katse shi nace "and kawai daga Amira ta gaya maka nayi aure you just believe her, ba zaka bincika ba, ask around, ba zaka kira ni ba kayi confirming daga baki na ba" na danyi shiru ina controlling temper dina, sannan na cigaba "you switched off your phone, you didn't even call me, you just left without a second look" Ya mike tsaye ya koma ya zauna akan kujerar da take kallon tawa, har yanzu bai ce komai ba, na dago kai na kalleshi muka hada ido na mayar da ido na kasa, a hankali naji yace "kin chanza sosai, you look more beautiful, more beautiful than I kept imagining you would be" a hankali nima nace "it doesn't matter, abinda nake so kawai in sani shine 'why?' Dama tun farko bada gaske kake sona ba ko kuma bayan ka tafi ne ka chanza ra'ayi?" Ya kara jawo kujerar sa kusa da tawa yace "Maimunatu kema kinsan amsarki, I love You, more than life itself. Ki tsaya ki saurari labarin abinda ya faru bayan tafiya ta, ina tabbatar miki da cewa zaki yadda cewa it hurt me more than it hurts you. I was fooled by your friend, totally fooled" na sake dago ido ina kallon rinannun idanunsa da suke kaina. Nace "OK. Ina jinka, tell me, what happened"
"Bayan na bar gidan ku a ranar nan, na koma makaranta, ina zuwa na kashe wayata na ajiye saboda nasan zaki kira ni, ni kuma a lokacin gani nake yi as long as ina jin muryar ki I cannot stay away from you. I thought i was strong, na dauka zan iya zama babu ke har sai na samu abinda nake nema, har sai nasan na isa in zo in nemi auren ki. I had your number in my memory, dan haka plan dina shine duk sanda naga cewa it's OK to return sai in kira ki. Ranar sam banyi bacci ba, washegari na tashi da rashin lafiyar da har sai da aka kwantar dani a clinic din school. Sati da daya ina jinya sannan na dan samu sauki nace su sallame ni, suna sallamata na shiga office din PC na bata takarda ta ta barin aiki, bana son duk sanda na tashi dawowa neman aurenki ya zamanyo ina jingine da babanki ne. Kayan da suke gidana duk na hada na sayar na dau jakar kayana na fita daga makarantar, gidanku na fara zuwa na bada sakon CD a gurin mai gadi sannan na wuce tasha, .nadabazan iya misalta miki yadda nake jin raina ba a lokacin maimunatu, ina jin haushinki a lokacin sabida kin gaya min gaskiya da kika yi kuma ina jin wani irin sanki a raina, sannan ga alhinin rabuwa dake kuma, ji nake kamar na chire wani bari na jikina na ajiye. I was tempted to call you then, na dauko waya ta na saka sim na kunna, sai kuma na sake kashewa na cire sim din na jefa shi ta window din motar. Kafin muje ibadan zazzabi ya sake rufe ni, da muka je sai mai motar ne ya karbi number din baba a wajena ya kira ya gaya musu halin da nake ciki, nan suka zo suka dauke ni sai asibiti, na jima shima ina rashin lafiya a can, hatta mama bata san abinda yake damuna ba ballantana su Hadiza, na gaya musu na ajiye aikina na Abuja, kawai dai sun fahimci cewa it has something to do with you. Bayan na samu lafiya an sallamoni sai na yanke shawarar tafiya Lagos, da akwai wani uncle dina a can wanda kudin inheritance din mu yake hannunsa yana business dashi, mama taso ace na zauna a ibadan na nemi wani aikin amma naki, gani nake aikin government babu abinda zai kawo min. Ina zuwa lagos uncle dina ya fara koyamin harkar business, cikin 'yan watanni na koya sosai, ya dauki kudaden mu gaba daya ya bani na fara nawa daban. Duk abinda nake yi kowacce rana, kowanne hour, kowanne minute kowanne second kina cikin raina maimunatu. A lokacin na fara trying kiran number dinki da sabuwar number ta, at least duk da cewa ina ganin lokacin dawowata bai yi ba amma ina so in san ya kike, amma ga mamakina your phone was switched off, kullum na kira a kashe, bani da number din kowa kuma a gidan ku sai taki. Tun a sannan na fara zama very frustrated. A haka har shekara ta kusa ta zagayo. Ban wani tara kudin kirki ba amma bazan iya jure zama babu ke ba, a dole na fara shirin tahowa Abuja in neme ki. Kamar hadin baki, ina zuwa ibadan baba ya shigar min da maganar auren Efi, a take nace masa a'a, wannan ba karamin bata ran mama yayi ba, saboda bata taba zaton zan iya cewa da baba a'a ba, tunda ban taba ce masa a'a ba. Ta fara fada baba yace a tambaye ni uzuri na, nan na gaya masa maganar ki, na nuna masa sosai irin yadda nake sonki, shi kuma ya goya min baya yace inzo abuja muyi magana da daddy in ya amince sai inzo in fada su kuma sai suje ayi maganar manya. Washegarin da muka yi maganar dashi na taho Abuja, har a lokacin wayarki bata shiga. Nazo unguwarku naga gidan ku babu alamar movement kamar wancan zuwam nawa, bana son wulakancin securities din ku dan haka na tsallaka gidan opposite dinku na tambayi me gadin kuna nan kuwa? Sai yace min ai kun tashi daga kasar ma gaba daya, sosai hankali na ya tashi, sai a lokacin na fahimci dalilin da yasa wayarku bata shiga. Bansan a gurin wa zan samu labarinki ba ballantana contact dinki. Na tuna da kawarki Amira itama a abuja take da zama kuma nasan tabbas zan samu labarinki a gurinta. Na tafi tsohuwar makarantar ku gurin principal na roke ta ta nemo min file din Amira, a ciki na samu address din gidan su, ina zuwa gidan su na aika a kirata aka cemin ta tafi makaranta, anan na zauna nayi ta jiranta har magrib sannan ta dawo. Sosai tayi mamakin ganina a kofar gidan su, kuma tayi murna sosai. Sai yanzu na fahimci dalilin murnar ta, ta dauka gurinta naje, ni na manta ma da cewa tana da wani feelings for me, na dauka tunda na gaya mata baki da baki cewa bana sonta shikenan magana zata wuce. Bayan mun gaisa ta kawo min ruwa nasha sai na gabatar mata da abinda ya kawo ni gurinta, cewa ina neman hanyar da zan same ki ne ko kuma number dinki. Abinda tace min shine 'au baka sani ba? Na dauka ta gaya maka ai' nace mata 'me fa?' Tace 'zancen auren ta mana, ai ranar da kaje gidan su Daddy n ta ya ganka, kana tafiya ya tambayeta waye kai ta gaya masa yace babu ita babu kai, shi ba zai bawa bayarabe 'yarsa ba, data takura ta daina cin abinci ta daina yiwa kowa magana sai ya dauke ta ya kaita 'yalleman, bata fi two weeks acan ba aka hada auren ta da wani cousin dinta a can' ji nayi tamkar ta zuba min fetur a jiki na ta kyatta a shana. She is your best friend, how can I not trust her words? Besides, nasan dama ba kowanne bafulatani ne zai yadda ya bawa bayarabe auren 'yarsa ba. Ganin irin yadda hankali na ya tashi ne yasa ta fara lallashina, tace in ban yarda ba zata kawo min sample din IV daurin aurenki kafin in bar gari. Ta gaya min cewa duk 'yan gidan ku suna England yanxu ke kuma kina 'yalleman. Anan ta karbi number ta da niyyar zata kawo min IV din. Daga gidan su Amira da kyar na samu taxi ta kaini hotel na kwana, ranar nayi kukan da ban taba yin irinsa ba a rayuwata, na tausaya miki na tausayawa kaina saboda ina ganin soyayyata ce ta jawo miki aka miki auren dole aka kaiki kauye aka katse miki karatun ki, alhalin ga 'yaruwarki can a England tana karatun ta. Washegari da ciwo na tashi dan ko fitowa ban iya yi ba har Amira tazo da yamma ta kawo min IV din, naga sunan ki da sunan wani Abdulaziz a matsayin mijin. Ganin ina kokarin in mutar mata a hannu yasa ta kira mai taxi suka kaini asibiti, a take aka kwantar dani dan sosai nake neman rasa numfashina. Kwana na uka a kwance Amira tana ta dawainiya dani, ranar dana warke nayi mata godiya nace zan tafi, amma dan Allah she should at least call you and let you know cewa I came back like I promised. Ina komawa ibadan na yiwa baba karya nace na samu Daddy yace yanzu kina karatu in bari sai kin gama tukunna. Mama tana gurin ashe ta gane karya nake yi. Rashin lafiyar ce dai bata barni ba dan tunda na koma ina kwance. Ban san ya akayi mama ta bincike kayana taga IV din da Amira ta bani ba. Bata ce min komai ba har na samu sauki na koma lagos. Ashe bayan na tafi ta nuna wa baba IVn ta gaya masa cewa yarinyar da nake so anyi mata aure, kuma wannan shine sanadin duk wannan ciwowwukan da nake. Ba tare da baba ya sake bi ta kaina ba ya yanke shawarar daura min aure da efi, a cewarsa macece kadai zata saka in manta da ke. Sam babu wanda ya gaya min labarin za'a yi min aure har aka daura ban sani ba, sai da uncle dina na Lagos ya je daurin auren ya dawo sannan ya kira ni ya gaya min, ranar naga tashin hankali, na gaya masa sunyi mistake, ni bana son efi ba zan iya zaman aure da ita ba dan a matsayin kanwa na dauke ta. Ya gaya min lallai in shirya in tafi ibadan inje ayi biki in taho da amaryata. A dole na shirya amma maimakon in tafi ibadan sai na zarto Abuja, direct gidan ku naje, wannan karon na tarar gidan da alamar mutane a cikin sa, ban shiga ba wannan karon a waje na tsaya sai da wani yaron gidan ya fito sannan na tambayeshi ko kina nan? Sai ya ce min ke baki zo ba, amma sauran mutan gidan sunzo, abinda na fahimta a lokacin shine mutan gidan sunzo daga England ke kuma baki zo ba tunda kina 'yalleman. Wannan shi ya goge min duk wani sauran doubts akan auren ki. Na tafi gidan su Amira, wannan karon a gida na same ta. Na gaya mata yadda mukayi da yaron gidan ku tace min eh ke kina 'yalleman, 'yan gidan ku ma sunzo suna ne saboda haihuwar da kika yi, har ta nuna min hoton babyn a wayarta. Ta gaya min cewa kunyi magana da ke kince mata in na sake zuwa ta ce min I should move on, ke kinyi moving on nima I should do the same thing. Zancen haihuwarki ba kara min tayar min da hankali ya kuma yi ba dan ina zuwa ibadan na zube wa mama a tsakar daki, mama hannu ta dora aka tana rusa kukan ta shiga uku danta zai mutu. Babane ya saka ni a gaba da nasiha da addu'a da fada har na dan samu na saki raina. Nan aka fara shirye shiryen biki. Sosai baba da mama suka kashe kudi a bikin nan a niyyarsu ta son suga sun faranta min rai. 'Yan uwana duk sun zo daga side din babana, side din baba da kuma side din mama, kowa was there to make me happy. Bana so in nuna musu kamar wahalar banza suke ji dan haka na ware sosai tamkar na karbi auren har aka yi biki aka gama. Bayan an gama biki ne mama tace mu tafi Lagos tare da efi sai nayi mata bayanin cewa bani da gida a lagos nima a gidan uncle dina nake, amma tunda a lokacin kudi suna shigo min sosai, inna koma Lagos zan sayi gida sai inzo in dauke ta, a haka muka rabu dasu na tafi Lagos. Na sayi gidan kamar yadda nace amma fir naki dauko efi. Nace ni bana son in ci zalinta kuma ni bazan iya zaman aure da ita ba. Sai da Efi ta shekara guda da aure akan ta amma tana zaman gida. Kwata kwata ma na daina zuwa ibadan saboda kar ayi min maganar tafiya da ita. Gashi arzikina kullum karuwa yake yi. Rannan kawai akayi min waya cewa baba babu lafiya, ba shiri na tafi ibadan, kwana na daya da zuwa Allah yayi masa rasuwa. A lokacin nasan mutuwar uba tunda sanda mahaifina ya mutu bani da wayo. Bayan komai ya lafa nace zan tafi, mama ta saka ni a gaba har da kukan ta akan lallai in tafi da matata, yanzu bata da kowa, ba uwa ba uba, ga mijin da dashi da babu duk daya, duk ta lalace ta fita daga haiyacinta. Kukan da mama tayi min ne ya saka na tafi lagos da efi".
Muna zuwa lagos na kaita gidan uncle dina na kama gaba na, ban kuma komawa ta kanta ba. Muna yawan yin waya da Amira, nakan kira ta inji ya kike da su Hafsat, kullum tana ce min lafiya lau kuke, tace hankalinki a kwance yake yanzu baki da wani problem. Kullum tana min maganar ya kamata in ajiye maganar ki a gefe in san me nake ciki a rayuwa amma sam na kasa. Ina waya da ita ne saboda she was the closest thing i have to you. Rana daya kawai sai ga mama tazo Lagos, nan naga bacin rai a gurinta data fahimci abinda na aikata. Efi cewa tayi ta hakura da auren, ita a raba auren kawai duk son da take yi min ta hakura. Mama kuma tace ban isa ba tunda bani na haifi kaina ba. Dole efi ta dawo gidana ta tare. Mama ma anan ta zauna tare da mu ta saka mu a gaba" yayi shiru for the first time tunda ya fara magana. Na kalleshi naga yana kallon can gefe. Ya cigaba da cewa "a duk zaman da muka yi da efi bazan iya tuna ranar da na ganta cikin farin ciki a dalili na ba, ta samu gangar jiki na, amma zuciya ta da ruhina ni kaina basa tare da ni ballantana in bata. I kept blaming iyayen mu da suka hada auren duk da cewa sun san bana sonta. Ba kowanne namiji ne zai iya rayuwar aute da matar da baya so ba. Bamu dade tare ba ta samu ciki, cikin yana girma mama ta dauko ta suka dawo ibadan ni kuma nayi zamana a lagos. A ibadan ta haihu, anan kuma Allah ya karbi ranta a gurin haihuwa. Allah yaso zamuyi sallama nazo kawo musu kayan da mama tace in siya, ina xuwa ta fara labour na kaita asibiti, tana haihuwa jini ya balle mata wanda shine sanadin ta. Inda Allah ya taimake ni na nemi gafarar ta kafin ta mutu da nasan alhakin ta bazai taba barina ba. Bayan na koma lagos naji duk zaman garin ya ishe ni, da kadan na fara sayar da business dina ina dawowa nan garin, a hankali na gina wannan gurin na sayi gida sannan na dawo garin nan da zama. Bayan dawowa ta garin nan na fahimci cewa Amira still have something for me sai na yanke alakar dake tsakanin mu saboda ban taba jin son ta a raina ba, ban taba jin son kowacce mace a raina ba bayan ke. Ina yawan bin hanyar gidan ku with hope wai ko wata rana zan ganki koda kuwa daga nesa ne. Rannan kawai naje unguwar sai naga gate din gidan a bude, kamar ana biki a gidan. Nayi packing daga dan nesa ina jin dadin maybe zan ganki. Na kira Amira a waya nace mata nazo gidanku na tarar ana biki, sai tace min bikin Hafsat akeyi. Ta fito ta same ni tace ta gaya miki nazo kince please in tafi kar mijinki ya ganni, tace kince you are happy with your life and I should leave you alone" ya sake yin shiru yana kallona, fuskarsa tana nuna irin bacin ransa. Ya cigaba da cewa "tun daga ranar ban sake zuwa gidan ku ba. Nayi concentrating akan business dina. Amira tasan ina garin nan amma bata san me nake yi ba, she had no idea nan guri nane, dan haka da kuka zo bata taba tsammanin zata ganni anan ba"
Tun da ya fara maganar nake hawaye har ya kammala, ya tashi ya je gurin water despenser ya debo ruwa a cup ya dawo ya miko min na karba na shanye ina jin dadin yadda sanyin ruwan yake sanyaya zuciyata. Maimakon ya zauna a kujerar daya tashi sai ya hau kan table din gabana ya zauna, exactly yadda yake yi sanda muna makaranta. Na dago kai na kalle shi, he was grinning from ear to ear. It is like nothing has changed, but yet, everything has changed. Involuntarily na kai hannuna kan zoben Sultan na fara wasa dashi. A hankali Ibrahim yace "it is alright now, we are together now" a hankali na far girgiza kaina hawayen fuskata yana karuwa, ya saka hannu zai dago fuskata na matsa baya. Nace "married or not married, ba dai dai bane kake taba ni ba, ka sani kuma" yayi dropping hannunsa a sides dinsa, yace "bani naki labarin inji, what have you been doing all these years" a hankali na fara magana nace "I waited for you, for five years, I waited" yace "six, almost seven" nace "I met someone after five years of waiting for you" nayi shiru ina kallon yadda yanayin fuskarsa ya fara chanzawa, yace "what? Who?" Nace "it doesn't matter who" ya sauko daga kan table din ya koma wajan ruwa, this time kansa ya zuba wa yasha, sannan ya tari wani ruwan ya zuba a kansa, ya juyo yana kallona da wani yanayin da bazan iya fassarawa ba, nayi sauri na dauke kaina dan ba zan iya juran kallonsa a haka ba. Yana daga tsayen yace "do you mean to tell me that you are in love with someone else?" Na yi shiru ina jinjina kalmar love, in nace love sai inga kamar na rage darajar what I feel for Sultan, it is more than love, na gyada kaina a hankali nace "yes" da sauri ya karaso gaba na ya durkusa "maimunatu please, please don't say that, zuciya ta zata iya bugawa please" na runtse idona ina jin zafi a raina, I hate to hurt him like this amma dole in gaya masa gaskiya, nace "I loved you, but not anymore" ya mike da sauri ya fara safa da marwa a office din yana cewa "you don't mean that, dan dai bana nan ne, you still love me, i know you do, I just need you to give me a chance in dawo miki da soyayyata" ya sake dawowa gaba na "maimunatu please ki sake bani chance" na sunkuyar da kaina ina kallon zoben Sultan a raina ina ayyanawa idan da ace sultan ya san inda nake kuma yasan tare da wa nake, zai iya harbo igwa ta tarwatsa building din gaba daya, a hankali na sake magana nace "there is no time, bikina saura kwana goma" da karfi yace "what?" Na gyada masa kai, ya sake mike wa ya buga hannun sa a table din yace "NO" da dan karfi. "No Maimunatu, destiny brought us together today. Da Allah baya so mu kasance tare da ba zai kawo ki office din nan yau ba. Da in zamu hadu ma sai da auren ki tukunna. Please call off the wedding" na girgiza kaina da sauri nace masa "not possible. I can't do that. Ko da ma ace bana son wanda zan aura ai bani nake bada kaina ba, an riga an bashi ni, an gama komai, bazan taba zuwa in ce bana son auren sa ba. It doesn't work like that" ya sake tsugunna wa kamar zai dora hannayensa a kan lap dina nayi sauri naja kujera ta baya, ya dora hannayen aka, sannan ya shafo fuskarsa. Idonsa ya sauka akan zoben sultan da nake ta aikin murzawa. Ka kalle ni yace "his ring?" Na gyada masa kai, ya sake cewa "who is he?" Na sake amsa masa "it doesn't matter" kamar amsar tambayar sa sai waya ta ta fara kara, a tare muka kalleta, 'my sultan' a hankali ya furta "sultan" ban dauki wayar ba saboda bazan iya yin magana da Sultan a yanzu ba, har ta gama ringing ta katse ya sake kira, nasan halin Sultan in yaso abu, bazai daina kira na ba har sai na dauka. Na mike tsaye, Ibrahim ma ya mike yace "please don't go" na kalle shi for some seconds sai na juya zan tafi, hijab dina ne ya jawo wani frame din hoto daga kan table din ya fado kasa, na durkusa a hankali na dauki hoton ina kallo, wata yarinya ce zata yi shekara uku a duniya, naga fuskar Efi a fuskarta amma idon Ibrahim, she looks very cute a cikin English wears tana murmushin da yake bayyana cleft chin dinta just like her father's. Nace "she is very beautiful" ya zagayo ta bayana yana kallon hoton yace "yes she is, just like the Moon I named her after" da sauri na juyo na kalleshi, yace "yes, sunan ki na saka mata, maimunatu, and I call her Moon" da sauri na hadiye kukan daya taho min, her mother died giving birth to her, but he named her after me. Daya frame din da yake kan table din na dauka, numfashina ne ya tsaya chak, hoton mu ne nida Ibrahim, duk bama dariya, fuska ta kamar zanyi kuka, yana tsaye a bayan class din mu ni ma ina tsaye a kusa dashi, na dan kwantar da kaina a kafadar sa shi kuma ya juyo kadan yana kallona. I remember sanda aka dauki hoton, Hafsat ce ta dauke mu da wayar ibrahim ranar da zamu bar makaranta. We were so young then, and so much in love. Na kalle shi da sauri naga yana murmushi, it is like nothing has changed, but yet, everything has changed. Na ajjiye pic din da sauri na yi hanyar waje ina jinsa yana cewa "maimunatu please" exactly yadda yake cewa in yana ya son ya lallabani in yi masa wani abu. Da bibbiyu nake hada stairs ina sauka, idona almost a rufe na fita na doshi motar sultan da nazo da ita, na bude na shiga nayi mata key, a lokacin na hango shi ya fito daga building din yana nemana. Nayi baya na fita daga packing lot din ina ganin sa ta mirror yana kallon motar, yayi noticing sunan da aka rubuta a gurin number "Sultan 2" .
Sai da nayi nisa da building din sannan na sauka daga kan titi nayi packing, na kifa kaina akan steering na kama kuka, what hurt me the most is the fact that Amira can betray me like that. Sometimes, the person you trust the most will hurt you the most.
Masoyan Maimoon ina gaishe ku baki daya, nima kuma ina sonku irin sosai dinnan. Ina ganin sakonnin ku ta WhatsApp da Facebook, masu bina private da masu turo wa ta group. Ina so ku fahimci abu biyu. Na farko Moon guda daya ce ba za'a raba ta a bawa kowa ba, dan haka dole wani ya samu kuma dole wani ya rasa. Dan haka at the end dole wani zai ga kamar ba'a kyauta masa ba. Abu na biyu kuma shine, tun kafin in fara rubuta labarin Maimoon na riga na tsara yadda zai kasance, yanzu kawai details din nake filling, kada wani yaga kamar labarin ina rubuta shine yadda zan farantawa wani. Idan kuka cigaba da bin Maimoon na tabbatar muku karshrn labarin zaiyi satisfying kowa insha Allah. Duk da dai ance shi dan adam ba'a iya masa.
I so much love you all
0 comments:
Post a Comment