Na jima a haka ina kuka mai tsuma zuciya, jikina har rawa yake yi. Why is my life almost so complicated, me yasa komai ni baya zuwa min da sauki. I hate hurting Ibrahim. Ya sha wahala sosai akan soyayyata, he deserves happiness from me now, but I can't give it to him because it is not mine, it belongs to somebody else. Ina jin wayata tana ta ringing, kira na wajan goma kenan, amma ba zan iya dauka ba saboda ba zan iya magana ba. Da zuciya ta da kaina gabaki daya sun toshe kaina sam babu wani abinda yake fahimta, abinda nake tunawa shine naga Ibrahim, kuma soyayyata da na gani a idonsa ta ninka wacce na san yana yi mini a da kafin mu rabu. A hankali na fara abinda na saba yi indai ina so in saisaita tunani na, na fara kiran sunayen Allah daya bayan daya idona a runtse, a hankali nutsuwa ta fara shigomin kuka na ya fara tsayawa. Na bude ido na ina kallon titi, gari ya fara duhu dan tini anyi sallar magrib. Na fara tunani straight. So Ibrahim did came back like he promised he would. Saura kwana goma bikina, bikina da Sultan. Ibrahim har yanzu yana so na, yana sona fiye da yadda ya soni a baya. But ya dawo rayuwata a little bit too late. My heart already belongs to another. I loved him before. Nayi masa son da a lokacin nake tunanin ba zan taba yiwa wani irin sa ba. But it is all gone now. Sultan ya cike dukkanin guraben da suke a zuciyata. Ibrahim Yace Allah ya hada mu ne a yau saboda we have a future together, in haka be kuwa to ba zabi na bane kenan. Even if da akwai sauran son Ibrahim a raina to yana can kasan zuciya ta wanda tono shi sai an dauki lokaci, and time is what we don't have. Even if an tono soyayyar Ibrahim a raina ta yaya zan iya facing iyayena ince musu na fasa auren Sultan wani kuma daban nake so? Komai sanyin Daddy na tabbatar sai naga bacin ransa ballantana Mommy da inajin sai ta kaini psychiatric hospital. I can't even imaging tunkarar Sultan da maganar wai na fasa aurensa saboda wani tsohon saurayina da muka rabu kusan seven years back. Duk wanda yaje ya gaya wa sultan wannan maganar will be committing suicide. I can't even imaging my life without Sultan. Choosing Sultan over Ibrahim is not a choice, it is a necessity. Kamar yadda Ibrahim ya fada hakane, God have reasons for everything He did. Tunda Allah ya hada mu yau to da akwai wani abu daya boye a cikin haduwar tamu, ko da kuwa ba aure bane. I just hope that whatever God has planned for us zai kawo happiness a rayuwar Ibrahim sannan kuma ba zai wargaza rayuwar ta da Sultan ba.
Waya ta ta cigaba da ringing, na dauka ina kallon sunan sultan har ta katse, a cikin dictionary din sultan babu wata kalma wai ita giving up, he never gave up, yanzu kiran nan da ya ke yi min zai yi ta yi ne har sai na dauka ko kuma sai charging wayar ya kare. Na duba missed calls naga 23, amma 5 daga Mommy ne, sauran kuma nashi. Na fara tunanin abinda zance musu tunda duk cikin su babu wanda zan iya gayawa gaskiyar abinda ya faru yau. Mommy na fara kira, bugu daya ta dauka tace "ina kika shiga? Sai da nace muku fa kar ku kai magrib gashi har after seven baki dawo gida ba?" A nutse nace "Mommy mun dan samu matsala ne shagon, Amira ce suka dan samu sabani da wata cashier shine abin yayi delaying din mu, kuma nabar wayata a mota shi yasa ban san kuna ta kira na haka ba" ta dan rage fadan da take yi tace "to amma ai da ko wayar ita Amiran sai ki karba ki kira ki fada mana halin da kuke ciki, ni ba sai inzo da kaina ko in turo wani yaji matsalar da aka samu ba? Na kira wancan yaron ma yace shima yana ta kiranki baki dauka ba, duk kin tayar mana da hankali wallahi" na danyi murmushi a raina nace 'I love you too Mommy' nace "gani nan zuwa yanzu, zan kai Amira gida ne kawai in taho" da sauri tace "NO, duhu yayi kuma unguwar su Amira akwai nisa. Ku tsaya a inda kuke ki kira shi sai ya kai ki ya dawo dake gida" nace "yes mother" na kashe. Ina kashewa kiran Sultan yana shigowa, sai da nayi bismillah sannan na dauka, ina dauka yace "damn it, where have you been?" Cikin sanyin murya nace "am sorry Sultan, na manta waya ta ne a cikin mota, muna cikin wani supermarket ne kuma muka samu wata 'yar matsala, duk everything is Ok yanzu na kai Amira gida zan taho gida nima" kamar sun hada baki da Mommy yace "no, ki zauna bara inzo in dauko ki, dare yayi kuma hannunki bai yi kwari ba" nace "yes sir" ya sauke ajjiyar zuciyar da har sai da naji ta ta cikin wayar yace "you almost gave me a heart attack. Gaba na yana ta faduwa, kuma ina ta kiran wayarki tana ta ringing baki dauka ba. Please don't ever do this again in ba so kike zuciya ta ta buga in mutu ba" kalmar mutun da ya fada ce ta saka ni nayi murmushi nace "kar ka zama ragon maza mana, ko three hours fa ba muyi da waya ba" yace "anything can happen ai a cikin three hours din, kin san babu abinda ban aiyana a raina ba? Har sai da na hango ki a kasan tirela" nayi dariya, yanzu shikenan date din na mu ya wargaje? Har nayi musu waya nace suyi mana reserving table " nace "am sorry, in sha Allahu I will make it up to you. Yanzu Mommy tana can tana jirana in muka tafi fada zata yi. Insha Allahu zan lallabata ta sake bari na fita sai muje" ya shagwabe murya yace "baki ga kwalliyar da nayi miki ba fa" nayi murmushi nace "really?, show me, I want to see" yace "how?" Nace "kayi snapping picture ka turo min yanzu" yayi dariya yace "no, it is kind of special, in kina so ki gani sai dai kisan yadda zaki samar mana fita da wuri. Yanzu cirewa zanyi ma in boye" mukayi sallama yace gashi nan tahowa. Na tayar da mota, I have one stop to make, gidan su Amira. A hankali nake tuki sabida hasken fitulu da yake kashe min ido, addu'ah ta Allah ya kaini lafiya kuma Allah yasa kada Sultan ya riga ni zuwa. Cikin sa'a naje na tarar bai zo ba. Na debi kayan ta data siya ta bari a motar na shiga. Mama ce kadai a palo tana cin abinci, na gaishe ta ta amsa cikin kulawa tace "ya akayi kika zo da daddaren nan bayan dazu ta dawo daga gurinki itama?" Nace "wani sako na manta bance ta taho min dashi ba, kuma gobe zan yi amfani dashi" tace "da fatan dai ba ke kadai kika taho ba" nace "a'a kawo ni akayi" tace "kin ga yanzu tsayawarki ta shiga daki amma tunda ta dawo tana kwance a palon nan, tace bata jin dadine, ki shiga tana ciki" na mike na shiga dakin. Ina bude kofa ita kuma tana shigewa toilet. Na rufe kofar na karasa bakin toilet din na zauna a kasa. A hankali na fara magana "why? Me yasa kika yi min haka? Me tasa kika kasance me son kanki da yawa? Me nayi miki da nayi deserving wannan cin amanar daga gareki?" Shiru babu amsa. Na cigaba "ban taba koda jin labarin mutum marar imani marar tausayi irin ki ba. Nayi miki soyayya ta hakika amma ke ashe duk duniya babu wanda kika tsana irina. Amira babu abinda baki sani ba na wahalar da nasha akan soyayyar Ibrahim amma ashe ko sau daya baki taba tausaya min ba, maybe ma dariya kike min a bayan idona, Amira kina kallona a kan gadon asibiti amma ashe kina da maganin ciwo na kika boye kika hanani. To ki sani, ni babu abinda zan yi miki, na barki da Allah, kuma na tabbata Allah sai ya sakamin cin amana ta da kika yi. Kuma ki sani, kanki kika yiwa. Shi wanda kike claiming kina so shi yafi kowa wahala a cikin duk abinda ya faru, shine kuma still har yanzu a cikin wahalar bani ba. Kuma ki sani, duk da Allah ya kaddaro babu aure a tsakanina da Ibrahim to kema ba zaki same shi ba, saboda Ibrahim baya sonki kuma bai taba sonki ba, kuma ba zai taba sonki ba, especially yanzu daya gano gaskiyar makircin ki, he hates you and I hate you also. Kuma ina gargadinki da kiyi hankali da dosar inda yake saboda yace in dai ya ganki sai na lahira ya fiki jin dadi. Ina fatan zaki halarci bikina nan da kwana goma, ina so kizo saboda ki gani da idonki irin farin cikin da zan kasance a ciki, ina so ki gani da idonki irin sakayyar da Allah yayi min tun a duniya kafin muje can. Ga kayanki nan da kika bari a motar mijina" na mike tsaye, ina jiyo sheshshekar kukanta a cikin toilet na fice, nayi sallama da maman su na fita. Ina fita ana sauke Sultan a taxi. Da sauri ya fito yana bani hakurin ya dade, ya karbi key muka tafi. Muna daukan hanya, ga mamaki na sai naji yace "what's wrong?" Nace masa "me ka gani?" Yace "you look and sound different, kamar akwai wani abu a ranki" na tattaro dukkan charms dina nace "Hey, I am suppose to be the psychologist ba kai ba" yayi murmushi yace "kin san ance zama da madaukin kanwa" nace "to babu abinda yake damuna, kawai dai na gaji ne, kwana biyu bana fita kuma yau mun dan yi yawo, gashi ni nake driving" yace "sorry, kuma gaki dama da son jiki ko? Wannan duk sanda aka fara bikin nan bansan ya zaki ke yi ba" nayi dariya nace "ai wadansu events din skipping zan ringa yi, na gaya muku bana son big wedding kun dage sai anyi" yace "karki damu after the wedding zaki huta sosai, I will be there to help you rest" na harareshi duk da babi haske, dariyar mugunta yake min ban ce masa komai ba, yace "ya kika yi shiru?" Nace "oho maka, kai ka sani" Muna zuwa gida yace wai shi lallai sai dai mu zauna a mota muyi ta hira ba zan shiga gida ba, ni kuwa nasan dan dai gidan da akwai baki ne yasa har yanzu Mommy bata kuma kirana ba amma tana sane da cewa ban dawo ba. Da kyar na samu da lallabashi na gudu. Ina shiga bayan na gaishe da Mommy na tafi dakin Hafsat, kawai so nake in samu in gaya wa wani abin da yake raina ko na dan ji sanyi.
Ina shiga na tarar tana lallaba little khairat, tayi min alama da inyi shiru, na rufe kofar na jingina da jikin kofar ina kallon su, sai da ta kwantar da ita sannan ta juyo tana kallona da murmushi tace "rigimammiya, wai ita lallai a jikina zata yi bacci ba zata kwanta ba" sai kuma ta kura min ido tace "lafiya na ganki kamar wacce aka koro?" Direct nace mata "I saw Ibrahim today" ta dan tsorata da maganar sai kuma tayi sauri tayi getting composure dinta tace "what? A ina? I really hope baki kula shi ba ko baki tsaya kin saurare shi ba" na karaso dakin na zauna a bakin gado ina kallon fuskar khairat da take ta baccin ta peacefully, nace "na tsaya na saurare shi, ba dan komai ba sai don ina son inji dalilin da yasa yayi abinda yayi" Hafsat ta watso min kallon tuhuma tace "and? I really don't like inda maganar ki take dosa Moon" nayi murmushi nace "inda kike tunani ba nan na dosa ba, I am not going back to Ibrahim, but he will always have a special place in my heart" daga nan na bata labarin duk abinda ya faru tsakanina da Ibrahim da Amira, bata ce komai ba har na kammala, ina gamawa naga ta mike ta na kokarin saka hijab, nace "ina zaki je?" Tace "I am going to kill that conniving bitch" nayi murmushi nace "shi yace zai kasheta ke kince zaki kasheta, a cikin ku bansan waye zai yi nasara ba amma nasan cewa koma me zakuyi mata ta riga ta aikata abinda ta aikata, kuma duk hukuncin da zaku dauka akanta ba zai dawo mana da hannun agogo baya ba, the past doesn't matter, what matters is the future. Ibrahim is my past, I have a great future to look forward to, I have Sultan" Hafsat ta yarda hijab din hannunta tazo ta rungume ni, I needed the hug, nima na rungume ta inajin zuciya ta tana sanyi a hankali. Mun jima a haka sannan ta sake ni tace "now, what are you going to do?" Nace mata "I don't know. Abinda na sani shine Ibrahim yana son in dakatar da bikina in bashi chance, which I told him I can't. Ya sha wahala akaina sosai kuma har yanzu yana sona, bana son inyi abinda zai kara masa bacin rai fiye da wanda yake ciki yanzu, kuma ni ba zan iya abinda yake so in yi ba. I don't know what to do. Na tabbatar kuma tunda har yanzu yasan bani da aure to zai zo gidan nan, it is a wonder ma da bai zo ba already, ina tsoron haduwar su da Sultan, Sultan is as unstable as a person can be, kuma bai san da labarin Ibrahim ba" Hafsat ta saki baki da mamaki tace "kina nufin baki gaya wa Sultan labarin Ibrahim ba?" Na daga kafada nace "ban taba tsammanin zan kuma haduwa da Ibrahim ba, so I thought there is no need in gaya masa, there is no point in tone tonen abinda yake a binne" ta kalleni da mamaki tace "Moon when will you stop keeping secrets? Duk abinda ya faru bakiyi learning lessons dinki ba. Kin boye wa iyayen mu Ibrahim, kin boye wa Ibrahim gaskiyar su waye iyayen mu, wannan shine asalin dalilin rabuwar ku da Ibrahim. Ki kazo kika boyewa iyayen mu Sultan sannan kika boyewa sultan zancen project dinki, akazo ba'a kare ta dadi ba. Yanzu kuma you are keeping Ibrahim a secret from Sultan? Again?" Nayi shiru ina jinjina maganarta a raina, she is right, nace "I guess it has all being my fault, it is because i have always been afraid of loosing those I love" tace "gaya wa Sultan labarim Ibrahim ba zai saka Sultan ya rabu dake ba. Kin gaya masa sai yafi bata masa rai akan gaya masa" nace "amma ba kya ganin yanzu it is late? In na gaya masa zai ga kamar dan mun hadu da Ibrahim dinne , ya dauka kamar dan ina son komawa gurin Ibrahim ne ko wani abu. Baki san halin Sultan ba, he is unpredictable, kullum gani yake kamar zan iya cewa na fasa aurensa, ko ya ya samu wani hint na wani abu ban san me zai aikata ba" Hafsat ta sake shiru sannan tace "what do you want to do?" Nace "so nake inyi iya kacin kokarina inga Sultan basu hadu da Ibrahim ba har bayan daurin aure, sannan sai in gaya masa, at least by then ya san dai na zama tasa already. Shi kuma Ibrahim ina so ya fahimceni ba tare da bacin rai ba"
Episode Sixty Four : The Visitors
Ina mika ta'aziyya a madadi na da sauran fans din Maimoon zuwa ga 'yar'uwar mu Nafisa Saleh, admin ta WhatsApp group din mu na mata, a bisa rashin yayanta da tayi sanadiyyar hatsarin mota, Allah yaji kansa ya gafartamasa, Allah ya yafeasa zunuban sa da namu baki daya. Allahumma Ameen.
Nine Days to the D-Day
Ban tashi da wuri ba saboda ban samu isheshshen bacci ba, kuma na tashi da ciwon kai. Amina da sauran cousins din mu na 'yalleman ne suka takura min da sututu a dakina dan haka na fito kan balcony na rufe kofar daga waje na zauna akan kujera ina jin dadin fresh air din gurin. Na jawo waya na kira Sultan, yana dagawa nace "hey busy body, ya kamata ka dauki leave ka samu ka huta, kar azo ana taro ka fadi ka hada mu da aikin dauko ka" yayi dariya yace "sai kace ke? An gaya miki kowa ma rago ne irin ki?" Nace "am serious, ya kamata ka huta" yace "alright amarya, yadda duk kika ce haka za'ayi. Besides, I need my energy for what is about to come" nayi kaman ban gane inda maganar sa ta dosa ba, nace "ina Amir?" Yace "baki bani amsa ta ba ai" nace "baka da amsa. Ina Amir?" Yace "OK, one day zaki buda baki sosai ki bani amsa. Amir ya dan fita, kina neman sa ne?" Nace "No, ka gaya masa kawai Amira bata jin dadi, so ya nemi Amina su cigaba da shirye shiryen da ita" ya dan yi shiru sannan yace "me ya sameta? I thought you guys were together jiya" nace "tun jiyan dama bata jin dadi, yau ta kira ni tace ba zata samu zuwa ba" muka yi sallama na kashe wayar, I feel bad duk sanda nayi wa Sultan karya, saboda shi baya min, baya taba boye min wani abu daya shafe shi. Amma ina jin tsoron gaya masa labarin Ibrahim. A ranar da yamma mai mun gyaran jiki ta zo mukayi, bayan mun gama tace min baza ta kuma dawowa ba sai ranar Saturday, wanda ita ce ranar daurin aure da kai amarya. Ta saka a ka fito mata da duk kayana da daddy ya dinka min wanda zan tafi dasu gidan sultan, dan babu abinda aka taba a lefe na duk already an kai su can ance in naje na dinka a can. Wani katon kasko ta hada turaren wuta take turare kayan nawa dashi, tace duk wankin da zan yi musu kamshin ba zai fita ba, ita shine nata gudunmawar bikin. Nayi mata godiya sosai. Ranar Tuesday za'a fara bikin, za'a fara ne da kunshi sannan da daddare a yi bridal shower, Wednesday za'a kamu da walima, Tuesday mother's eve da dinner, friday luncheon da daddary su sultan suyi bachelor's night dinsu, Saturday 12 na rana za'a daura aure da la'asar akai amarya, da daddare kuma za'ayi bridal welcome party wanda Amir ya shirya mana. Shikenan.
Eight Days to....
Gidan kam a cike yake yanzu da mutane, daga maza har mata, munir bai zo ba kuma naji dadi, dan bana son yazo ya kara min wani tension din. Mamansa dai da sisters dinsa sunzo, suna zuwa suka ishe ni da iyayin suna so suga angon, nasan abinda suke nufi, so suke suga waye ya kasa yayansu, babu bata lokaci kuwa na hada su dashi, tunda suka ganshi suka yi kus, babu wacce ta sake magana a cikin su.
Da yamma na fita balcony, nan ne gurin zama na yanzu indai ina son in jini ni kadai ko in ina son muyi waya da sultan. Na dafa railer na dauko wayata ina kokarin kiran sultan kawai ina daga ido na na hango shi, duk da cewa da akwai distance a tsakanin mu kuma gari ya fara duhu amma na gane shi, yayi packing dan nesa da gidan mu kadan yana tsaye ya jingina da jikin mota ya rungume hannayensa a kirjinsa. Wata irin muguwar faduwa gaba na yayi, Allah kenan, babu yadda baya juya lamarin sa, da akwai lokacin da kullum nake tsayawa a balcony din nan ina kallon waje hoping zan ganshi amma yau gashi ina kallonsa amma maimakon inji dadi sai faduwar gaba da ji. Allah ne kadai yasan dadewarsa a gurin, Allah ne kuma kadai yasan dawa yayi magana. Nasan Sultan dai bai dawo gida ba, baya zuwa yanzu sai dare yayi sosai saboda mutane. Kamar ance ya dago ido sai ga idonsa a cikin nawa, da sauri yayi kamar me shirin tahowa ni kuma nayi sauri naja da baya yanda zai daina ganina. Saboda faduwar gaba har daci nake ji a bakina, na shiga uku, na leka a hankali naga har yanzu balcony din yake kallo. Na koma daki da sauri na shiga toilet, sai da nayi calming down sannan na kira sultan. Yace "Hello love" nace "hey kana ina ne?" Yace "naje karbo mana sauran dinkunan mune. What's up?" Nace "babu komai. Kawai da ina so inji ya kake ne" yayi dariya yace "thanks love, ko in taho ne?" Nace "I would appreciate that amma kasan gidan yanda yake yanzu, ballantana yanzu da yamma" yace "right, nima daga nan zanje wajan Daniel ne yazo gari, so sai dare zan shigo gidan, hope ba za kiyi bacci ba kafin inzo" nace "yeah, bazan yi ba sai kazo, bye" muna gama wayar na koma na leka balcony naga har yanzu Ibrahim yana tsaye. Da sauri na sauka kasa dakin Hafsat na same tana shirya kayan khairat, tace "lafiya? Waye ya koro ki?" Nace "Hafsat Ibrahim ne yazo yana waje" tace "and? Kina nufin fita zakiyi gurin sa?" Nace "no, ke nake so kije" ta yatsina fuska tace "ni? Allah ya tsari gatari da saran shuka" nace "Dan Allah Hafsat kije kiyi masa magana, make him understand abinda yake so ba zai yiwu ba" tace "in baki shawara? Ki kira David ki hada shi da shi, nayi miki alkawarin ba zaki kara ganin sa ba" na girgiza kai da sauri, Hafsat ba zata fahimci abinda nake nufi ba, babu wanda zai fahimci situation dina sai wanda ya taba shiga irinsa. Ma zauna a bakin gadon ta nace "I don't want to hurt him, I don't want to hurt Sultan. Please help me" ta dan jima tana kallona sai kuma ta dauki hijab ta saka tace "amma kin san dama can ni ba shiri muke yi da shi ba, dan haka ba lallai ne yanzu ma mu fahimci juna ba" tana fita na koma sama da sauri na kuma shiga balcony, ya baro jikin motar ya dawo dai dai opposite din gidan mu, ina kallon Hafsat ta bude gate ta fita. Yana ganin ta yayi saurin karaso wa wajanta, bana hango su sosai yanzu, sun jima suna magana sannan daga baya naga ya juya ya tafi wajan motarsa, kafin ya bude motar ya sake juyowa ya kallo balcony din sannan ya shiga ya tafi. Na dawo daki na zauna ina sauke ajjiyar Zuciya, ina jin kuma babu dadi a cikin raina, but haka Allah ya tsara mana ni da shi, we are not destined to be together. Ina nan zaune har Hafsat ta shigo, ta jefo min wani complimentary card tace "gashi nan yace a baki, he is so hot headed sai da na kusa loosing temper dina, he believes hada ku aure akayi da Sultan, yace yaji labarin dan sarkin garin nan ne, shi a ganin sa kin yarda da auren ne saboda babu shi. Yayi yayi in bashi number dinki na hana shi shine ya bani card dinsa yace in baki ki kira shi, yace in baki kira shi ba zai sake dawowa gobe" ta zauna a kusa dani tace "Moon, ki kira Sultan ki gaya masa halinda kike ciki, he will know what to do" na girgiza kaina nace "Sultan will definitely hurt Ibrahim in na gaya masa" tace "to ki fada wa David ya hana shi zuwa gidan nan" nan ma na girgiza kai "securities will treat him badly and I don't want that" ta mike a fusace tace "to hada kayan ki ki kirashi yazo ya dauke ki ku gudu tare a fasa auren" ta fice a fusace ta bugu min kofa. Kwalla ce ta taru a idona ina jin zafi a raina. Na sunkuya na dauki card din nasa, kallo daya nayi wa number din na haddace ta na jefa card din a waste bin. Ina bukatar inyi addu'ar sosai in nemi Allah's guidance. Ranar kam da daddare haka na tashi nayi ta jero adduoi akan Allah ya fitar dani daga matsalar da nake ciki, Allah ya saka wa Ibrahim dangana ya fahimci cewa ni ba matar sa bace ba.
Seven days....
Na tashi zucita ta fes kamar babu abinda yake damuna. Muna ta harkikin mu da 'yammata Amir ya aiko kiran Amina zasu je su gano venue din dinner. Muna zaune sai ga kungiya guda nan ta kawayen mu na sec sch, nan fa guri ya kuma hargitse wa, muna ta hira sai ga hasiya nan ta shigo daga baya, tana zuwa tace "guess wa na gani a waje yanzu?" Tun kafin ta fada nasan waye, nan take cikina ya kada tace "uncle Ibrahim" nan da nan suka kuma rude wa "yana ina?" "Moon dama kuna da contact dashi?" "Ko sallama yazo?" Duk ban basu amsa ba, hasiya tace "yana waje wallahi, ina ganin sa na gane shi, kunga yadda ya kara kyau kuwa? Ya goge sosai ya zama dan gayu fiye da yadda kuka san shi a baya" Walida tace "ke Hasiya, kina matar aure kike kallon wani ko? To wannan maganar kamar a kunnen abban Na'im" duk muka yi dariya tacigaba da cewa "da muka gaisa ma bai gane ni ba fa, wai yasan fuskar a cikin kawayen Moon amma ya kasa tuna sunan, sai da na gaya masa tukunna ya tuna. Yace yaji labarin bikin Moon shine yazo yayi mata Allah ya sanya alkhairi amma ya rasa wanda zai aika ya kirawo ta, nace masa in na shigo sai inyi mata magana sai yace kawai ma sauri yake yanzu in bashi number dinta zai kira ta, shine na bashi" hannu biyu na dora aka nace "kin bashi number ta fa kikace?" Ta kalle ni da mamakin yadda na rude tace "eh na bashi, Murna fa zaiyi miki shikenan, kuma ba'a daura ba ballantana kice kin zama matar wani ba zaki yi waya da wani ba" a raina nace "Hasiya had killed me" na tuna dramar da mukayi da Sultan akan musbahu ballantana Ibrahim. Duk abinda muke yi Hafsat tana jin mu baya tanka ba, sai kawai naji tace "'yan 'uwa ku matso in baku wani labari" duk suka juyo suna kallonta, tacigaba "kun tuna rannan a makaranta da Ibrahim yace wata a ajin mu tana sonsa amma shi baya sonta?" Duk suka ce eh, tace "a lokacin nace muku zan fada muku wacece amma moon ta hana, to yau zan fada muku kuma har ba bonus na labarin duk abinda tayi" da sauri nace "Hafsat no, please don't do this" bata jira abinda nake cewa ba ta kwashe labarin Amira kaf ta gaya musu" ta cigaba da cewa "sai shekaran jiya sannan Allah ya toni asirinta suka hadu a supermarket, kun ga ikon Allah ko? Da Allah ya tashi kamata ita da kanta ta kai Moon har office din Ibrahim" nan take gurin ya hargitse da hayaniya, daga masu dure2n ashar sai masu Allah wadaran halin Amira, Hafsat ta cigaba da cewa "na fada muku wannan ne saboda idan da akwai wacce take da saurayi to tayi musu katanga da Amira, mai miji ma haka, dan bamu san kan wanda zata koma ba kuma" Zulaihat ce dama masifaffiyar ciki ta mike tace "waye zai je gidan su Amira ya koya mata hankali?" Nan take duk suka mike har da Hafsat, dama ita tun shekaran jiya take son zuwa na hanata, na mike na sha gabansu, "dan Allah ku bar maganar nan, na riga na samu mijina wanda yafi Ibrahim a wajena ita kuma ta rasa Ibrahim din bashi kenan ba, shima Allah ya bashi matar data fini" ture ni sukayi gefe suna kumfar baki suka fice, Hafsat ce ta tsaya tana kallona tace "at least this will teach her a lesson tasan cewa tayi ba dai dai ba, amma in dai aka barta zata ga kamar taci riba ne ai, this will serve as a lesson to her da duk masu hali irin nata" ni dai anan na durkushe a bakin kofa ina hawaye, Amira was a good friend to me, she was my best friend for about 13 years, ni in ta nine ma zan so Ibrahim ya aure ta amma nasan ba zai aure ta din ba. Maman ta kuma kawar Mommy ce, naso rigimar mu ta tsaya a tsakanin mu bana so iyaye suji. Waya ta naji tana kara na duba, number din Ibrahim na gani, na san za'a rina dama, na ajiye ban dauka ba, ya cigana da kira kusan missed calls biyar sannan ya hakura, message naji ya shigo, shima ban dauka na karantaba. Sai can bayan la'asar sannan su Hafsat suka dawo suna ta dariya "dan Allah kuyi hakuri, ku bawa Moon hakuri dan Allah" wai haka Amira take cewa, kawai hawaye naji yana taho min, nace "da Amira ta raba mu da Ibrahim da kar ta raba mu, Allah ya riga ya kaddaro ba miji na bane ba" sukace "ke ai sanyin zuciya ne dake, da ace wani zai kashe ki ki sake dawo wa duniya ya baki hakuri cewa zaki yi kin hakura" sai kuma suka koma gulmar Ibrahim, "kin san har yanzu yana waje?" Nace "oho muku ku kuka sani" Hasiya tace "ni wallahi tausayinsa nake ji, Moon yana sonki da yawa wallahi" na harare ta nace "to bara in hada su shida Sultan in aura kawai". Hafsat ta gama tsara musu yadda events din bikin zai kasance sannan suka tafi suka barmu ni da Hafsat da Hamidda. Gab da magrib sai ga Amina ta shigo, fuskarta kamar gonar auduga, tana shigowa tayi tsalle ta fada kan gadon tana birgima. Muka bita da kallo da sakakken baki, sai da ta gama haukanta sannan tace "Albishirin ku" muka ce "goro" tace "at last yau wani yayi noticing cewa ni kyakykyawa ce" tsaki muka ja a tare ni da Hafsat, Hafsat tace "Allah ya shirye ki Amina" ta tashi zaune tace "am serious fa, anan waje muka hadu dashi bayan Amir ya sauke ni, ya taho da sauri yana yi min magana wai ya dauka ke ce" ta fada tana nuna ni, guiwata naji tayi sanyi na zauna akan stool, ta cigaba "ni ban san me yasa mutane suke hada kyakykyawar mace kamar ni da something like Moon ba, ni banga wani kama da muke yi ba" nayi dariya nace "shi yasa aka kasa noticing kyan naki ake noticing nawa" Hafsat tace "uhum, me yace miki kuma" ta cigaba "cewa yayi he is a friend of Moon, yaxo yana son ganin tane, daya ganni ya dauka itace shine ta taso. Yace muna kama sosai ko ni 'yar'uwarta ce, sai nace masa ni yayarta ce, shine yace shi Hafsat kadai ya sani yayarta, nace masa aini ba'a nan na taso ba a England na taso. Ya bani number sa yace in na shigo in kira shi sai in baki. Oh my God Moon ya hadu da yawa" na mike na shige toilet na rufe kaina, a fanfon sink na tara fuskata nabar ruwan yana ta zuba. Dai da naji numfashina yana neman daukewa sannan na cire kaina na goge fuskata da towel na koma dakin, ina shiga naga ta danna wayar ta ta miko min tace gashi, na jima ina kallonta sannan na karba, tace bara taje tayi sallah ta fita. Na zauna a bakin gado na saka wayar a kunne na naji already ya dauka, nace "assalamu alaikum" sai da ya sauke ajjiyar zuciya sannan ya amsa. Nayi shiru. Yace haka.u gaisuwa?" Nace "good afternoon" yace "yauwa ko ke fa, at least dai ai nayi deserving gaisuwa daga gare ki. Please Moon why are you doing this to us? Please don't punish me like this. Ba laifi na bane ba. I was led to believe kinyi aure. Kuma ko da hakan ma sonki bai ragu daga zuciyata ba sai ma karuwa da yayi. I know u love me too. I saw it in your eyes a office dina. You just have to tell Daddy cewa wanda kike so is here, a ajiye maganar wannan Sultan of a thing din" a hankali nace "Sultan is not my parents choice, he is mine. In fact daga farko ma parent dina basa sonsa nina matsa cewa shi nake so sannan suka yarda" yayi sauri yace "saboda bana nan ne yasa kika zabe shi Maimunatu. I am back now. Mun sha wahala Maimunatu kar kiyi mana haka. Abinda Hafsat tayi ta cewa kenan wai ke kika zabe shi. Whatever you think you feel for this man, believe me it is not love." Nace "Ibrahim, please don't make this harder than it already is. I know you are hurting and believe me, bana jin dadin haka sam. Amma abinda kake nema daga gare ni is just not possible. Ko da ace Sultan ba zabi na bane ba vazan iya tunkarar iyayena at the dying minute in ce musu na fasa auren nan ba. Ballantana ni na zabe shi. Put your self in his position, ace kana da budurwa kunyi maganar aure da ita, you went through alot together, kun sha wahala kuka yi convincing iyayen ku, an gama komai hatta jere anyi sai kuma few days to daurin auren ku sai tace ta fasa auren ka, how will that feel?" Yayi shiru for some seconds sannan yace "very bad" nace "good, to believe me it will feel more than very bad to Sultan, it will destroy him completely" yace "me yasa nasa zaifi na kowa zafi?" Nace "because he is kind of special" da sauri yace "ouch, that hurts" na danyi dariya nace "sorry" ya dan jima baiyi magana ba, sannan yace "do you think you will be happy with him?" A hankali nace "yes" muryarsa very deep with emotions yace "then I will be happy for you" wasu hawaye masu zafi naji sun taru a idona. Muka sake shiru sannan yace "Can I at least see you one last time?" Na danyi jim ina tunani, nace "not now, sultan zai iya zuwa anytime" yace "OK, I understand. Nagode for at least talking to me. Good night" ya katse wayar. Na ajiye ina jin zuciyata babu dadi.
Six days to....
Duk an gama shirye shirye. 'Yammata ana ta rigima da tailors din da basu gama dinkuna ba, ni kam duk kayana sun kammala kuma suna dakin Sultan, nace ya barsu a can saboda cikin gidan duk a hargitse yake kar inzo in rasa wani abun ranar da nake bukatar sa. Wajan 12 na rana aka ce inzo nayi baki a palo, na sauko na ga 'yammata su uku a zaune, already an riga an cika musu gaban su da kayan ciye ciye, ban gane ko daya daga cikin su ba amma daga ganin su kasan 'ya'yan manya ne, biyu bakake daya fara, amma jikina ya bani cewa farin mai ne. Na zauna da murmushi na ce musu "sannun ku da zuwa" kallo kawai suka bini dashi sannan suka kalli juna, sai suka sake kallona, daya daga cikin su tace "Amaryar ta mu ce?" Na sake murmushi nace "sunana maimunatu" suka sake kallon juna sannan dayar tace "eh haka muka gani a jikin IV. Ita din ce kuwa. But you are younger than we expected. An ce mana medical doctor ce" nayi dariya nace "I am a neurologist and also a psychologist. Karatu ai ba shine shekaru ba, in dai ka fara da wuri shikenan" bakaken biyu suka yi dariya, daya tace "sunana Fa'iza, wannan kuma kanwata ce Saratu. Mu kannen ki ne" ban gane ba, tace "if you know you know" sai yanzu na fahimta, kannen sultan ne, he never talk about them kamar basu yi existing ba. Na kara fadin murmushi na nace "sai yau kuka tuna dani? Nayi fushi" saratu tace "sorry big sister, ba laifin mu bane, mu bamu san ma dake ba sai kawai IV aka kawo mana, ko ince sai IV muka gani, dan mu yaya Sultan ko gayyatar mu bai yi ba, maimakon ace mune masu gayyata ma amma sai a gari muke ji" nace "to kusha kurumin ku, har sai kun gayyaci wasu ma" suka yi dariya, nace "and who do we have here?" Na nuna wacce suka zo tare, fa'iza tace "antin mu ce, umma khulsum" ban nuna komai a fuskata ba nace "sannu da zuwa aunty" da alamar tsokana, ta bata rai tace "in kika ce min aunty ai sai ki mayar dani kamar tsohuwa" muka yi dariya. Bayan sun dan motsa bakin su na tafi dasu sama dakina, har bayan azahar suna nan, tare mukayi lunch dasu, kowa sai da na nuna masa kannan Sultan. Ina lura dasu suna ta kallon gidan, ni kuwa nasan ba 'ya'yan sarki ba, ko 'ya'yan waye karya suke su kushe mana gida. Tunda suka zo suke ta yi mini tambayoyi akan sultan, wai yana dariya kuwa? Har da tambayar is he romantic, nace sosai kuwa. Around 3pm aka zo aka dauke su, na hada musu kayan kyalliya masu tsada da turaruka na basu tare da katinan kowanne event na bikin.
Na koma gida nayi wanka na shirya, nayi sallar la'asar aka sake cewa nayi bako kuma, na sako hijab dina na fito ni da Amina, a tsaye muka ganshi a jikin motar sa. Yayi kwalliya kamar babu gobe. Daga ganin sa kasan hutu ya zauna masa. Ina ganin da na gane shi. Abbas ne, muka karasa muka gaishe shi ya amsa yana tsokanar mu "wacce ce yayar tawa ne a ciki?" Na nuna Amina, yace "to tunda kika nuna ta ke ce" muka yi dariya yace "ya shirye shirye?" Amina tace "Alhamdulillah' nayi kokarin a kaishi palon su ya Habeeb amma yace sauri yake, yace karar Sultan ya kawo min, wai bai saka shi a cikin harkar bikin ba kwata kwata, shida ya kamata ace shi yake organizing bikin amma sai dai yake gani ana yin abubuwa babu shi, nayi masa alkawarin zanyi wa sultan magana akan hakan. Ya sake cewa " sai magana ta gaba, ina so in shirya masa hawan angwanci a matsayin wedding gift dina amma yace baya so, ni ban taba ganin inda akayi bikin dan sarki babu hawan angwanci ba" na jinjina maganar, nasan Sultan ba zai yi ba, tunda yake babansa bai taba hawan sallah dashi ba, kuma ko a magana ban taba jin yana maganar yin hawan angwanci ba, da yana so kuwa da zai ce zaiyi. Nace masa "insha Allah zanyi masa maganar shima, amma babu guarantee zai yi, in ba zai yi ba kawai ka rabu dashi", ya daga kafada yace "it's OK, ina son kuma cards saboda friends dina" na tura Amina ta dauko masa da yawa ta kawo masa. Shima muka yi sallama ya tafi.
Da daddare Sultan bai samu zuwa gida da wuri ba saboda friends dinsa na America da suka zo, yana can nema musu masauki da entertaining dinsu, dan haka bamu hadu ba sai waya mukayi. Na gaya masa bakin da nayi yau da yadda muka yi dasu duk, yace "what? Munafukan yaran nan karya suke yi, babu abinda ban basu ba, su dai kawai tsegumi suka zo yi" nayi murmushi nace "it is OK ai. Tom Abbas kuma yace ka ki sakashi a organisers" yace "Abbas ba zai iya organising komai ba, bai san ni ba bai san me nake so da wanda bana so ba, role din Amir yake so in bashi kuma bazan bashi ba" nace "but at least involve him in something, tunda ya nuna yana so karka sace masa guiwa" yace "moon baki san halin yaron nan bane ba. But whatever, zan gaya wa Amir in da akwai wani abu ya bashi. Zancen hawan angwanci kuma bazan yi ba, I already told him bazanyi ba, he is trying me" jin ya fara daukan zafi nayi shiru, sai da naji ya huce nace "tell me something nice" daga muryar sa kadai nasan ya ware yace "what's nice without you. Sai yanxu nake nadama big wedding din nan, da na sani kawai daurin aure akayi aka kaimin amaryata" nace "tukunna ma, sai jibi in an fara ido zai raina fata" yace "ohh jibi za'a fara ko? Gaskiya ya kamata gobe ki san yadda zakiyi maganar date din nan. I really want to see you wallahi" nace "insha Allah tomorrow zamu fita. Kar ka manta da kwalliyar da ka yi min alkawari, I want to see it" yace "baki da problem. Thanks , Love"
Episode Sixty Six : The Wedding
So...... The long awaited episode is here.
Monday
Washegari tun Mommy tana dakinta kafin ta fito naje na sameta, na gaisheta ta amsa. Sai kuma nayi shiru, ta kalleni tace "akwai abinda kike so ne?" Na danyi shiru ina tsoron kar ta hanani, tace "in ba zaki yi magana ba I have so many things to do" nace "Mommy dama zamu dan fita ne in an jima da Sultan" tace "in an jima kamar yaushe kenan?" Nace "kamar bayan magrib" tace "duk tsahon ranar nan bata ishe ku ku fita ba sai da daddare?" Nayi shiru a raina ina cewa 'shikenan, baza ta barni ba' tace "kun san dai gidan nan a cike yake da 'yan sa'ido da tsegumi bana don ku jawo mana wata maganar kuma" nace "to Mommy" tace "Allah ya kaimu, kuje, amma duk inda kukaje kar ku kai karfe goma" na ji wani dadi a raina, da sauri nace "thank you mother" ta harare ni, ni dai na tashi na fita tun kafin ta chanza ra'ayi. Bayan munyi break muka tafi saloon akayi mana gyaran gashi, kusan duk 'yammatan tare muka tafi har Hafsat, acan akayi mana manicure da pedicure, bamu dawo ba sai la'asar. Tun la'asar Sultan ya kira ni yace mu hadu acan. Naji haushin me ya saka ba zaizo ya dauke ni ba. Ina yin sallar magrib nayi wanka na dauko wani bakin material dina da aka dinka min a cikin kayan fitar biki na saka, riga da skirt ne anyi masa ado da golden, na gyara fuskata da light make up, ni kaina nayi mamakin irin kyan da nayi, na dauko golden mayafi karami nayi rolling, mayafin ya sauko ya rufe kirjina, na fesa turare na fita, dakin Mommy na fara shiga na ce mata na tafi, ta kalle ni sama da kasa tace "wannan mayafin yayi karami, ki daura dankwalin kayan sai ki saka babban mayafi, nace "yes mother" na koma dakina na dauko dan kwalin ina kallonsa, ni ban iya daurin dankwali ba shi yasa da wahala kagan ni da dankwali sai dai inyi rolling mayafi. Dole na nemo Amina, nan ta sakani a gaba wai sai ta kara min kwalliya wai wacce nayi tayi kadan, ta zauna ta tsara min kwalliya sannan tayi min daurin dankwalin shima, ina kallon kaina naga kamar ba ni ba, na juyo nace mata "Amina ba'a fara bikin ba fa, wannan kalliyar ai sai mutane suyi ta kallona" tace "to zauna kar mutane su kalle ki, ke da ba'a yi miki abin arziki" nace "thank you" ta kofar baya na fita, motar Mommy na gani a farko dan haka ita na shiga. Wajan 7:30 na isa Hilton, na kira sultan a waya yace "am sorry love, ki shiga nayi mana reserving table, gani nan zuwa, ki bani five minutes" na sake jin haushi nace "yanzu ni da nake mace ni zan je in jira ka? Maimakon ace already kana jira na acan?" Ji nayi bai wani damu da bacin raina ba yace "Sorry, yanzu ba zaki gane ba sai nazo tukunna" na kashe wayar ina tsaki a raina, na shiga ciki.
Ina shiga naga wata waitress tazo ta tare ni ta tayi min jagora zuwa wani table a can corner din gurin, ga mamaki na sai naga the same table ne da muka zauna ranar da muka hadu. Na zauna akan the same seat din da na zauna ina kallon bakin kofa. A take na fahimci abinda sultan yake nufi, so yake abin yayi looking exactly kamar ranar da muka hadu, nayi murmushi, wannan shine dalilin da yasa yayi insisting in taho ni kadai kuma yace in shigo in jira shi, na kalli wajan naga babu abinda ya chanza. Ina zaune kawai naga waitress ta kawo min tea ta ajiye, na sake murmushi, wato ya tuno da tean da nake sha san da ya shigo. Na dauki tea din na fara kurba ina tina ranar, ranar bridal shower din Hafsat, Munir ya takura min, kawayen mu ma sun takura min da tambayar ina Ibrahim, I was so pissed up a lokacin na fito kawai na taho nan saboda ina son inji ni ni kadai, ashe destiny ne yake kirana. Na kai cup din tea din bakina zan kurba kenan na hangoshi ya shigo, kasa shan tean nayi na ajiye cup din tare da sakin baki ina kallonsa. Dark blue wandone a jikin sa three quarter da kuma light brown body hug short sleeved shirt, rigar tayi squeezing. Exactly kayan da suke jikin sa ranar da na fara ganin sa, gashin kansa a hargitse. Ya dan tsaya a bakin kofar yana karewa gurin kallo hannunsa a cikin aljihunsa. Tsayuwar da yayi exactly yadda na zana shi a project dina, except for murmushin da yake yi. Ya juyo ya kalli side din da nake zaune. Idon mu suka hadu, bansan sanda na mike tsaye daga zaman da nake ba. A hankali ya fara tahowa inda nake tsaye fuskarsa da murmushi, yace "Assalamu Alaikum" ban iya na amsa masa ba, yace "Mind if I join?" Sai a lokacin na rufe bakina na gyada masa kai ina dariya kasa kasa, maimakon ya zauna sai ya zagayo bayana ya rike min kujerata na zauna first sannan ya zagaya ya zauna a exact kujerar da ya zauna almost two years ago. Yana kallona yace "kinyi more than kyau, bama zan iya fassara yadda kike looking ba, kawai dai kinyi kyau" nayi dariya tare da dan shagwabe fuska nace "ba kai bane kace zakayi min special kwalliya shine nima kasa ni nayi kwalliya ashe kai abinda kake planning da ban" yayi dariya yace "kar dai kice kwalliya ta bata burge ki ba, da ita fa nazo na siye zuciyar ki" nace "waye yace maka a lokacin ka sayi zuciyata?" Yace "to yaushe na saya?" Na danyi tunani sannan Nace "nima ban sani ba. Kawai dai naga ta zama taka ce, ban masan sanda aka yi ciniki ba ballantana in san sanda na sayar maka" yace "hummm, ni kuma kinsan sanda kika sayi tawa? The first moment dana dora idona a kanki nasan cewa I am hooked for life, tun daga ranar kuma har yau ke kike controlling dinta" a lokacin aka fara serving din mu abinci, muka fara ci muna hira muna dariya, it's like mu kadai ne a duniyar, babu tunanin kowa babu tunanin komai a zukatan mu sai mu kadai. Yace "gwara fa ki samu kici abinci fa sosai, dan after today ba lallai bane ki samu damar cin decent meal ba kuma sai a gidan ki" nace "that goes also for you" yace "wa? Ni akwai wani abu da zai hanani cin abinci a kuwa? Amma nasan abinda zan ke yi miki in an fara bikin nan, kullum dura zan ke zuwa ina yi miki, kar azo a gama biki kuma ki kare da zuwa asibiti a bar ni da tagumi" na harare shi bance komai ba. Mun jima muna cin abinci sannan muka gama, ko bayan da muka gama ma aka gyara table din bamu tashi ba muka cigaba da hirar mu. Yana ta bani labarin friends dinsa da suka zo. A lokacin ne yake gaya min cewa 'yan gang bang duk sunzo, hotel daya duk suka kama suka sauka. Sai naji babu dadi, ni har na manta ma da zancen su, na dan bata rai, yace "what's wrong?" Nace "I thought ka rabu dasu, me suke yi kuma a bikin ka?" Yace "It's just biki kawai, kuma we have been friends shekara da shekaru, yanzu ba zai yiwu ace bikina yazo kawai sai dai suji labari ba" nace "why not? Ni dai sam bana son su wallahi, I don't want you with them" ya jawo kujerar sa kusa dani ya langwabar da kai yace "baby, I can't just send them away, babu dadi ai. Yaushe rabona dasu ma, yanzu fa duk mun girma kowa ya kama gabansa, in ba abu irin wannan ba bama haduwa. Yanzu kuma in aka gama bikin nan ba lallai ne mu kuma haduwa ba sai bikin wani kuma" na kalleshi cikin ido nace "ba zaka je bikin kowa ba" dariya yayi yace "yes ma'am, an gama. Please ki dan saki ranki mana" nayi murmushi yace "yauwa, ko ke fa" hannun da ya rike naji ya fara shafawa a hankali yana kallona, nayi sauri na kwace hannuna naja kujera ta baya, ina kallon fuskarsa yana so yayi dariya amma ya maze nace "wato tsokanata ma kake yi ko?" Ya dan bata fuska yace "ni din? Ni na isa in tsokane ki?" Nayi kwafa nace "as if I don't know you. Na san ka fa Sultan. Babu abinda ban sani naka ba" yace "really kin sanni?" Nace "yes, like the back of my hand. Na san ka ciki da bai" devilish smile dinsa ya fara, a take na fahimci so yake ya juya min magana ta, na bata rai, bai damu ba yace "yanzu da gaske kina nufin kinsan Sultan? Baby girl I let you know only what I want you to know. There is a part of me that you don't know, there is a part of me that even I don't know. Amma kar ki samu damuwa, we will soon explore that part very soon. But I think rannan mun dan buda page daya na wannan chapter din" ya sunkuyo saitin kunne na yace a hankali "In America" ji nayi tamkar kasar gurin ta tsage in shige ciki, wato abinda Hafsat ta fada gaskiya nr bai manta ba. Ina jinsa yana dariya kasa kasa ganin yadda fuskata tayi ja saboda kunya, ba tare da na kalle shi ba na saka hannu na dauki jaka ta na mike, yayi saurin rike hannuna na kwace na yi gaba da sauri kamar zan tashi sama. Da kyar na samu na dauko key din motar saboda yadda hannu na yake karkarwa. Ina bude motar yana karaso wa gurin "am sorry Love, ki tsaya in kaiki gida dare yayi" ban ko kalli inda yake ba na shiga motar zan rufe kofar ya rike yace "please ki bari in karki gida, I promise ko magana ba zan yi miki ba" har yanzu da akwai alamar dariya a muryar sa, ya zaiyi yayi wasa da wannan maganar? Amma kuma nasan ba iya tukin dare nayi ba kuma Mommy bata san ma na daukar mata mota ba dan duk a tunanin ta tare muka fita. Na fito na zagaya na shiga seat din baya na zauna, har yanzu dariya yake ya tayar da motar muka tafi. Har muka je gida ba wanda yayi magana. Muna packing na fito, ya fito shima ya sha gabana yace "thank you for today, I really had I great time" bai samu amsa ba na zagaye shi na shige gida. Seriously ni Sultan tsoro yake bani.
Tuesday
Yaune kunshi da bridal shower. Tun sassafe akayi shimfidu a compound, madu kunshi suka zo, ni kam sam bacci bai ishe ni ba haka aka taso ni wai lallai ta kaina za'a fara kunshin. Jan lalle aka fara yi min, ana fara wa 'yammata suka zagaye ni aka fara wakar gada ana tafi. Hannu da kafa duk akayi min, ni kaina lallen yayi min kyau musamman saboda gyaran da fata ta tasha. Ana gamawa nace Amina ta daukar min shi a hoto ta turawa Sultan, tana ta dariya nace tayi shiru kar mutane suji. Tana tura masa ya turo min reply din kisses. A baki Hafsat ta zauna taba bani abinci ina ci har na koshi. Nan akayi ba'ki shima akan jan. Ai fa nan take na fito amarya ta sak. Tsofaffi sai guda, 'yammata sai waka. Ana gama wa dani aka koma kan sauran 'yammata. Mai kunshin ce ta dawo gurina tace "bara inyi miki wani abu as my wedding gift" nace "me fa?" Tace "wait and see" riga ta ta daga tana min wani abu a kasan kafada ta, ni dai dariya nake yi har ta gama, Amina nasa ta dauko min hoton gurin in gani, ina dubawa naga wani design tayi da bakin lalle mai kyau, a tsakiya ta rubuta S & M. Yayi kyau sosai, nayi mata godiya. Sai wajen la'asar aka gama kunshin dan har su daada dai da aka yiwa, wai suma sai sunyi gayu,lol. Ni dai ana cire min nawa na tafi daki nayi wanka na shirya cikin wata doguwar riga ta ta lace orange color, tayi bala'in yi min kyau dan kana gani na ba sai an gaya maka ba kasan nice amaryar. Dakina a cike yake da 'yammata ana ta shirye shiryen bridal Shower, su Hafsat kuwa ana waje ana making arrangements na gurin da za'a yi event din. A garden din gidan mu za'ayi, decorators already sun shirya gurin sai dan abinda ba'a rasa ba. Ana sallar magrib mai kwalliya tazo, Fauziyya tace "to ina kayan da amaryar zata saka ne wai?" Amina ta tabe baki tace "oho, sai ku tambaye ta, nima ban sani ba" na kira sultan nace ya aiko min da kayan yau, duk suka saki baki suna kallona, Hamidda tace "wai kina nufin kayan da zaki saka suna gurin angon?" Nace "yep" basu karasa mamaki ba sai da Maryam ta shigo da kayan a 'yar karamar jaka, suka buda duna kallo, doguwar riga ce fara tas, mai hannun vest, wuyanta ya shiga ciki sosai both gaba da baya, sai wani dogon siririn veil mai kamar jela irin wanda ake nannadawa a wuya ash color, takalmi da jaka ta ma duk ash ne, suna fito da kayan sai ga brazier da pant a kasa, a tare suka saka salati, ni kaina sai da nayi dariya, suka juyo suna kallona nace "wallahi ban san ya siyo da underwears ba" Hasiya tace "amma wannan angon shine number one a marasa kunyar Nigeria" Amina tace "Ai in da akwai number zero to Sultan ne" Sai da nayi sallah sannan ta fara yi min, a kawayena har da masu recording kwalliyar a video. Na saka kayana sannan muka fita ta kofar baya gurin event din, muna zuwa Hafsat ta dora min crown a kaina sannan ta rataya min tag da aka rubuta 'Bride' a jikinsa. Ni nayi shigar fari tas sauran duk mutanen da suke gurin kuma sunyi shigar baki, kowa a ganni a ranar sai ya sake kallo. An saka securities sun tare hanyar garden din babu namijin da zai shiga. Gaskiya tun a ranar nasan ina da kawaye masha Allah, dan har wadanda ban saka ran zasu zo ba sun zo. Ina jin waya ta tana ta kara a cikin jaka kuma nasan Sultan ne amma naki dauka na rabu dashi. Aka kawo min cake dina shima fari da kwalliyar baki, Hafsat ta taya ni muka yanka, akayi ta pictures daga nan kuma aka fara dancewa. Muna ta enjoying kan mu bamu san lokaci yaja ba sai da Mommy ta aiko tace ya kamata a tashi haka tunda da akwai masu nisa, sannan muka duba time muka ga after 11. Mommy ta saka drivers din gidan suka yi ta jigilar kai mutane gida.
A gajiye na shiga daki na fada kan gado duk jikina yana min ciwo. Gashi banyi sallar isha ba, wanka na fara yi sannan nayo alwala na fito nayi sallah sannan nayi shirin kwanciya. Sai da na kwanta sannan na dauko waya na kira sultan, yace "wato yau wannan matar kin manta dani ko?" Nace "ni na isa? Gurin da hayaniya in ma na dauka ba zaka jini ba" yace "to kuma shine ni ko a nuna min kwalliyar ko?" Nayi dariya nace "wannan kwalliyar ta yau tafi karfin idonka, ka bari zan ajiye maka pictures, randa duk ka kai matsayin gani sai in nuna maka" yayi ajjiyar zuciya yace "I can't wait" ban bashi amsa ba nace "good night Sultan" yace "fi amanillah"
Wednesday
Bacci nayi sosai da safe na huta, Sultan ne ya tashe ni da waya wai lallai yana son ganina kafin ya fita, da sauri sauri muka gaisa ya fita saboda mutane. Ranar anti Zaliha tazo, na gaisheta tace "Moon an samu abinda ake so ko? To baza muyi miki baki ba, Allah ya sanya alkhairi" sum sum na tashi na fice daga dakin. Rumfar motocin gidan aka gyara aka kwashe motocin gidan, anan za'ayi kamu. Ranar shigar atamfa nayi purple mai adon pink, sosai kalar atamfar ta kara haska fata ta, plain zani ne, na daura shi akan rigar, ana gama yi min kwalliya na shiga toilet na saka shower cap na rufe gashina tsaf da ita sannan aka daura min dankwali aka saka net aka rufe fuskata. Suna ta mamakin me yasa na saka shower cap a kaina ni kuwa nasan dalili. Nani ce tazo tare da mata da yawa daga fada. Dubu dari biyu suka ajiye da akwati guda na turaruka, sannan suka feshe ni da turare, daga nan aka bude fuskar amarya aka tayi min ruwan kudi, both dangin sultan da nawa. Sai da aka kusa gamawa sannan Hajja tazo tace sam kamu bai yi ba tunda ba'a zuba min nono ba, ai ni bafulatana ce dan haka da nono za'a kama ni. Kamar yadda tayi alkawarin sai tayi min wanka da nono haka tayi min, Mommy ta kule kamar zata yi kuka ni kuwa dariya ma nake yi abina, sai yanzu kawayena suka gane amfanin shower cap din dana saka. Ana gamawa direct toilet na shiga nayi wanka da special sabulu na, babu wani sauran karni daya rage a jikina. Bayan munyi sallar magrib kuma aka shirya tafiya walima. Doguwar riga na saka yellow mai adon golden stones, na saka jaka da takalmi suma golden, ina shiryawa na kira Sultan video call na nuna masa kwalliya ta, nan fa yace shi baiga dalilin da za'ace babu maza a walima ba, ai suma suna bukatar ayi musu wa'azin yadda zasu rike matan su, nace masa ai anayi amma suma du kadai banda mata, da kyar muka rabu wai bai gaji da ganina ba.
A abuja national mosque akayi walimar, anyi wa'azi sosai da nasihohi masu ratsa jiki kuma duk akan zaman aure, da kuma sirrika na rike miji bisa sunna. Naji wa'azin sosai dan jikina gaba daya dai da yayi sanyi. Muna dawowa gida na tarar Sultan yana jira na waishi lallai bai gama ganin kwaiya ta a waya ba sai ya gani a fili. A mota muka zauna ya fito mana da fura da nono mai sanyi da tsire, muna ci muna hira, ni har na manta ma bikin mu ake yi dai da amina ta kira ni tace "kinsan dai in baki yi bacci ba zaki tashi da kumburaren ido, kuma kwalliyar ki ba zata yi kyau ba" a raina nace 'oh Amina ko passion design kika karanta sai haka'
Episode Sixty Seven : The Wedding 2
Thursday
Tunda na tashi da assuba na koma na cigaba da baccina, cikin baccin naji kida na tashi kamar a tsakiyar kaina, na dauko pillow na dora a kaina na toshe kunnena amma a banza. Na mike a fusace ina mita "wai ba mother's eve aka ce ba? A bari sai evening din mana. Ni wallahi bacci bai ishe ni ba" Amina da ta fito daga wanka tana shiryawa tace "to ke da wa ya aike ki ki zauna hira da Sultan har karfe dayan dare? Dama ta yaya bacci zai ishe ki? Ai kawai hakura zaki yi ki tashi haka" na mike ina tsaki, na leka ta window na ga DJ ne ya baje kayan kidan sa a dai dai gaban tagar dakina. Na kara wani tsakin ina duba agogo, 11:30, kamar zan yi kuka nace "fi sabilillahi karfe goma sha daya za'a dasa min kida aka? Ni dai kam an shiga hakkina" Hafsat ta shigo cikin kwalliya tana kallona tace "wai yanxu kika tashi? Har Mommy tana cewa a kira ki ku gaisa da mutane?" Na kara bata rai na shige toilet. Ruwa na hada a tub na cire kayana na shiga na mayar da idona na rufe, take wani baccin ya sake dauke ni. Knocking kofar da akayi shiya farkar dani, ni ban ma san nayi baccin ba, muryar Mommy naji tana fada "uwar me kike yi a toilet din nan da har yanzu baki fito ba kin bar mutane suna ta jiranki?" Da sauri na tashi na kammala wankan ina mita a raina 'duk Sultan ne ya jawo min wallahi'. Ina fitowa na tarar mai kyalliyata tazo dan haka mai kawai na shafa na zauna muka fara, Hafsat ta shigo ta zauna tana feeding Khairat sai ga Mommy ta shigo itama, ta zauna akan bed side tana kallona tace "me ya hada ku da Amira?" Gaba nane ya fadi duk da dama nasan wannan tambayar tana nan zuwa, nayi shiru bance komai ba, ta sake cewa "fada kukayi ko?" Hafsat ce ta bata amsa tace "eh Mommy, fada suka yi" Mommy ta danyi shiru sannan tace "akan me?" Nan Hafsat ta zauna ta bawa Mommy labarin duk abinda ya faru, har ta gama Mommy bata ce komai ba. Sai da ta gama sannan Mommy tace "Maimoon3. Sau nawa na kira ki?" Murya can kasa nace "sai uku" tace "you are not to see that man again. Kinji ni ko baki ji ni ba?" Nace "Naji" ta kuma cewa "I am very serious in na sake jin maganar sa sai nayi mugun saba miki. Yanzu ace few days to daurin auren ki har kuma kina fada da best friend dinki a kan wani saurayi daban?" Nace "Mommy ni ba akan Ibrahim bane ba, akan tayi betraying dina ne, kuma ni ban hana ta zuwa gurin bikin nan ba, ita taga dama ta ki zuwa" Mommy tace "whatever, ni dai nace bana son sake jin maganar nan. Ok?" Nace "yes mother" tace "ita kuma Amira zata zo ta same ni ne, haka kawai akan wani saurayin da ko damuwa bai yi da ita ba zata watsar da rayuwarta kuma ta yi loosing best friend dinta" ta dauko wayarta tayi dialing ta fara magana "Hajiya salamatu lafiya kuwa? Jiya anyi kamu babu ke babu Amira yau ma kuma gashi har yanzu baku zo ba?" Ta danyi shiru tace "kani kuma? Me ya faru? Aa gaskiya ku dawo, please ko jirgi ku shigo ni zan biya ko baku samu mother's eve din ba ku sami dinner. Ok na gode sai kun zo din" ta kashe wayar ta fita.
Da yamma akayi mother's eve, ranar naga gatan iyaye da 'yan'uwa, gidan taf ya cika da mutane kuma wai kowa saboda ni yazo, su fa'iza ma sunzo tare dasu akayi komai. Har magrib sannan aka watse. Sallah kawai mukayi kuma muka fara shirin tafiya dinner. Na aika aka karbo min kayan dinner a gurin Sultan naxo na sake wanka na dan kwanta na huta zuwa isha sannan na tashi nayi sallar isha aka fara shiryani. Yadi ne cotton cream color doguwar riga data kamani daga sama sannan ta bude sosai daga kasa, daga baya kuma tana jan kasa sosai kuma anyi mata adon stones masu kyalli, ta gaba kuma anyi mata aiki kalar golden brown. Head dina, jaka ta da takalmina duk golden brown ne da adon stones cream. An gyara min gashina ya sauko har saman bayana an jera masa stones cream color sannan aka tubke shi da golden brown ribbon. Ni kaina dana kalli kaina a madubi sai da nayi mamakin irin kyan da nayi, a zuciyata nayi tasbihi ina godewa Allah. Around 8:00pm muka isa hall din taron, already kowa ya shiga ya zauna amarya da ango ake jira. Sultan da tawagarsa ne suka fara shiga, aka saka musu kidan su aka gama cheering, sannan akace mu shigo, na juya na kalli tawagar kawayena duk sun saka ankon su na jan lace da yellow head, ga Hafsat a kusa dani ita kuma da yellow kace da jan head a matsayinta na maid of honour. A hankali muka fara tafiya, flower girls dina na gabana su biyar da fararen kayansu suna tafiya suna watsa flowers, sai ni da Hafsat na rikr hannunta kamar zan balla shi, sai kuma sauran kawayen mu a baya. An saka mana namu kidan da ban na musamman, muna shiga kowa a gurin ya mike tsaye muka fara tafiya akan red carpet din da aka shimfida mana direct zuwa high table. Straight idona ya shiga cikin nasa, a hankali na saki hannun Hafsat dana rike. Irin yadin jikina shine a jikin sa shima amma nashi color golden brown ne da aikin cream, wato kayansa kalar aikin kayana ne kayana kuma kalar aikin nasa. Yayi kyau sosai, for the first time ya gyara gashinsa ya kwantar dashi baya ya dora hularsa da tasha adon stones. Murmushin fuskarsa from ear to ear. Nima murmushin na mayar masa. Sultan bai iya jira mun karaso gurin sa ba ya sauko daga stage din ya taho gurin mu, nan take gurin ya dauki ihu da tafi, yazo ya miko min hannunsa na kama muka karasa high table tare. Sai da muka zauna sannan kowa ya zauna. Aka fara gabatar da addu'ar sannan aka fara programs. Anyi abubuwa da yawa, jokes, speeches da sauran su. Amina da Amir ne suka ce suna da surprise for us, nan suka fara displaying pictures din mu ni da sultan tun muna yara, Sultan dan lukuti abin dariya, har da picture dina da Pampers fuskata duk chocolate, aka cigaba da nuno mu muna girma har zuwa yanzu, akayi ta saka pictures din mu tare, da wadanda muka yi a America da na England da na nan. Abin yayi kyau sosai. Sultan yayi introducing dina to most if his friends da suka zo gurin including the gang bang, ina ganin su na ga basu yi min ba sam amma da dake nayi musu murmushi muka gaisa suka tsokane ni suka wuce. MC ne yace zamuyi playing game wanda zai nuna how much do we know each other. Handkerchiefs aka saka aka rufe mana idanun mu, sannan aka chire mana takalman mu, aka bani daya nawa daya nasa a kowanne hannu, shima aka bashi. Daga nan mc ya fara yi mana tambayoyi yace min in amsar Sultan ne sai in daga takalmin sultan in kuma Moon ne sai in daga takalmina. Ya fada wa Sultan ma the same thing. Daga nan ya fara jero mana tambayoyi kamar; waye yafi fara'a a cikin ku? Na daga takalmina, waye yafi tsafta? Na daga takalmin Sultan, who is the smartest? Na daga takalmina, who is the best cook? Na daga takalmin sultan, who love food the most, nan ma sultan na daga. Haka yayi ta mana tambayoyi ni dai ina amsawa amma bansan amsar da sultan yake bayarwa ba tunda idona a rufe yake. Ga mamaki na duk amsar dana bayar sai inji hall din ya dau ihu da tafi, anan na fahimci cewa the same answer muke bayarwa ni da sultan, it is like mind din mu tana working a tare, har mc ya gama tambayoyin daya rubuta ya koma karawa up head amma ba muyi missing ko answer daya ba. Gaba dayan mu dariya muke yi, we know our selves so much we are like two bodies with one soul. Finally, MC yace final questions, a cikin mu waye yafi son wani the most? Gaba daya gurin yayi shiru ana jiran amsar mu, muma kuma mukayi shiru din, sai daga baya a tare muka daga hannu, ni na daga takalmina ina nufin son da nake wa sultan yafi wanda yake min shi kuma ya daga nasa yana nufin son da yake min yafi wanda nake masa. Lol. Ai kuwa gaba daya hall din ya hargitse. MCn ma kasa magana yayi, sai daga baya yace "this means that the love is equal" daga baya aka bude mana idon mu. Bayan an nutsu aka kawo mana cake muka yanka. Akayi hotuna da family da friends Sai kuma aka ci abinci aka rufe taro da adduah.
Friday
A gajiye nake likis dan har saida nasha paracetamol sannan na danji dai dai, luncheon din da akayi is very brief and not as grand as dinner din jiya. Muna gurin luncheon din ne Amira tazo, ta zo guri na tace "hi" nima nace mata "hi" tace "kinyi kyau" nace "thank you" ina lura da sultan yana kallon mu ganin irin yadda muke magana casually amma bai ce komai ba, ta sauka ta tafi can wata corner ta zauna ita kadai saboda ba zata iya shiga cikin kawayen mu ba.
Babu kyau baccin bayan la'asar amma ranar sai da nayi, muna zuwa gida nayi sallah kawai na kwanta na rufe kofa nace kar wanda ya tashe ni, ban farka ba sai ana kiran magrib sannan na tashi na bude kofa nayi sallah na kira sultan muka dan taba hira sannan na sauka kasa. Ji nake yi duk jikina babu dadi saboda ina tunanin yau ce rana ta ta karshe a gidan mu, duk sanda zanzo sai dai inzo a matsayin bakuwa. A kasa muka zauna gaba dayan mu tun daga kan daddy har faruk, suma kamar masu yi min farewell, anan mukayi dinner tare suna ta tsokana ta, sai da suka ga na fara musu kuka sannan suka rabu dani. Daddy da Mommy suka tashi suka tafi suka bar mu. Muna ta hira har sallar isha, su yaya walid suka fita mosque suka dawo, can nace musu "wai ku ba za kuje bachelor's night din bane" yaya Habeeb yace "Allah ya kiyaye. Wannan night din ai yafi karfin mu" ban gane me yake nufi ba nace "saboda me?" Ya walid yace "kin san menene bachelor's night ma kuwa?" Nace "I thought kawai it is just a funny guys' thing. Just to have fun" yace "exactly" nace "to menene laifi? Don't you want to have fun?" Yace "ya danganta da irin fun din da za ai having" nayi shiru ina kallonsa yace "look parrot, wadanda suka shirya wa Sultan bachelor's night dinsa are not my kind of people, dan haka yana yi min magana nace ba zamu je ba"
Ban sake cewa komai ba nayi shiru ina tunani, su waye suka shirya masa? Take na samu amsata, the gang bang. Lokaci daya naji hankali na ya tashi. Tun da na dawo daga Niger ban kuma ganin sultan a buge ba, kuma bana jin ko a bayan idona yana sha duk da bamu taba maganar ba. Har karfe goma ina zaune a palon amma sam hankali na baya tare dani. Only God knows a ina sultan yake kuma me yake yi. Na tashi nayi musu sallama na tafi daki, na kira wayar sultan tana ta ringing babu answer. Ko da ace Sultan ya daina shan giya amma temptation fa? Musamman idan ya ga ana sha, ballantana nasan zasu iya bashi su ce sai yasha. A automatic redial na saka wayar na kuma saka ta a speaker na kwanta, kiran yana ta shiga har wajan 30minutes bai dauka ba, ina cikin haka Amina ta shigo, ta kalleni tace "ba dai Sultan kike kira ba? Ke ma kinsan kina bata lokacin ki da battery din wayarki ne a banza amma ba dauka zai yi ba" ina kallonta ta gama shirin kwanciya ta hawo kan gado ta kwanta, nace "Amina, what do you think maza sunayi a bachelor's night?" Tace "hmm, a England an taba bikin wani dan ajin mu, mazan suka shirya masa bachelor's night, washegari very few ne suka zo makaranta, saboda sauran all got drunk the other night ba zasu iya zuwa ba. Na tambayi wani a cikin su,why?, sai yace ai suna celebrating last day of freedom din su ne, in suka yi aure kamar they are bond to their wives babu sauran sakewa suyi abinda suke so. So duk abinda namiji yafi enjoying shi zai yi a daren, in mashayi ne in manemin mata ne sai yayi kayan sa one last time" tayi sauri tace "amma fa ba ina cewa abinda sultan yake yi kenan yanzu ba, it depends on mutun. Ke kinsan Sultan kinsan me zaiyi kinsan kuma menene ba zai yi ba" bance mata komai ba amma zuciyata in ban da zafi babu abinda take yi, har yanzu kira nake kuma har yanzu bai dauka ba. Ba'a jima ba Amina tayi baccinta ta barni, har na fitar da ran zai dauka kawai naji ya dauka, gurin da yake hayaniya ne kawai da kida yake tashi a gurin, yace "Hello, love, bakiyi bacci ba" nace "sultan where are you?" Yace "muna gidan Solomon, wani abu ne?" A hankali nace "Sultan I want you to come back home" yace "why? The party hasn't even started yet" ina jin wani a gurin yana cewa "chafdi, Sultan wannan amaryar taka in aka gama bikin nan ko kofar gida ba zata ke barin ka kana fitowa ba" duk suka kwashe da dariya, Sultan ya dan matsa daga gurin su yace "why?" Nace "ni kawai bana sonka da mutanen nan wallahi" yace "Moon, this is my party, saboda ni suka shirya shi. I can't just leave" naji wani abu ya tsaya min a makogwaro na. Kafin in san me zance masa wani a cikin su ya karbe wayar yace "look amarya, we are going to get your ango drunk today, he is even lucky he don't do women, amma shima in kika sake kiransa we will make him do it even if we have to tied him to the bed" Sultan ya warce yawar yana ce masa "fuck you" da sauri yace min "Moon" ban jira abinda zai kuma cewa ba na kashe wayata. Kafin in ajiye ta ya kira, ban dauka ba, ya sake kira na kuma share shi. Zafi nake ji sosai a raina. Sai da yayi five missed calls sannan ua hakura. Na runtse idona ina addu'ar Allah yasa in iya bacci amma sam babu bacci a idona. Ina tsakiyar tunani na naji wayata ta cigaba da kara, nayi niyyar in sake rabuwa dashi amma na daure na dauka, bance komai ba yace "kinyi fushi ko?" Naji inda yake babu hayaniya, amma duk da haka bance masa komai ba, ya sake cewa "gani a balcony dinki, ki bude min kofa"
I hope duk wacce take karanta littafin nan zata so saurayinta/mijinta kamar yadda Moon take son Sultan, duk wanda yake karantawa kuma shima zaiso budurwarsa/matarsa kamar yadda Sultan yake son Moon. Remember, Love is the strongest magic of all.
Stay loved.
Episode Sixty Eight : The Wedding Night
Na kashe wayar na mike da sauri na zura dogon hijab dina na bude kofar balcony. Yana tsaye ya jingina a jikin railer yana murmushi. Wandon jeans ne a jikin sa army green da farar singlet yayi stocking dinta a cikin wandon ya daure da belt, sai light green din top wadda ya balle duk maballayenta ya barta a bude, iskar da ake kadawa a gurin tana ta diban rigar tasa kamar zata chire ta. Na dan bata rai nace "Sultan me kake yi anan cikin daren nan" shima bata ran yayi yace "to tunda kin hanani zama acan ba sai in taho nan ba. Ni nasan kona kwanta yau ba zan iya bacci ba, ba gwara in taho nan ki tayani hira ba" naji dadi har raina dana fahimci ya bar gurin partyn saboda nace bana so, nasan it was a hard decision but a good one. Na jawo kofar na rufe saboda tinawa da nayi cewa Amina tana cikin dakin, na karaso inda yake na jingina da railer nima ina kallon kasa nace "thank you" yayi ajjiyar zuciya yace "I will never do any of those things da Daniel yake fada" nayi shiri ban ce komai ba, ya danyi dariya yace "they will kill me in suka kamani gobe da safe, dan duk cikin su babu wanda yasan na fito, sai daga baya zasu lura bana nan" ya dauko wayarsa a aljihu yayi switching off ya mayar aljihun sa. Ya kalleni ya fara murmushin muginta yace "but there is a price for everything, tunda kika hana ni kwana a gurin party na to yau a dakinki zan kwana" nima murmushin muguntar na mayar masa nace "bismillah, ina nuna kofa" babu musu yaje ya bude kofar, sai yayi sauri ya rufe ya dawo da baya, dariya nayi sosai nace "ka shiga mana, wallahi in ta fara ihu sai duk mutanen gidan nan sun tashi daga bacci" ya dan jima yana tunani sai kuma ya sake bude kofar, ina hango yadda Amina ta kudundune a cikin bargo tana baccinta, hannu ya saka ta bayan kofar ya zare key din jiki sannan ya mayar da kofar ya rufe yayi locking ta waje ya saka key din a aljihunsa yace "then we will sleep here" da mamaki nace "you are not serious are you?" Yace "sa ido kiyi kallo" daga haka ya tafi ya kwanta rigingine a kan carpet din da yake gurin. Tsayawa kawai nayi ina kallonshi naga yayi pillow da hannunshi ya rufe ido, gaba daya rigar ta bar jikinsa sai singlet din kawai. Nayi sauri na dauke kaina na daina kallonsa na koma ina analysing situation din, nayi tsaki a raina ina cewa 'Sultan, wannan fa shine baccina na karshe kafin aure a gidan mu amma ba zaka barni in kwanta a gado na ba'. A kwai security light sosai a compound din gidan amma duk waje suke haskawa, wannan ne ya kara wa balcony din duhu, ma'a na babu wanda zai hango mu daga waje amma mu zamu ke ganin su. Amma Amina da take daki zata iya farkawa kowanne lokaci taga bana nan. Already jikina ciwo yake min saboda gajiya amma kuma ace zan kwana akan carpet. Amma kuma gwara haka da ace Sultan ya kwana a gurin wadannan mutanen. Sai dai ni ban yarda inje kawai in kwanta a kusa da Sultan ba. Na zauna akan kujerar da take gurin na kudunduna a cikin hijab dina, kadan kadan nake kallon sultan har daga baya bacci ya dauke ni.
Cikin bacci naji ana shafa lips dina, a hankali na bude idona da suka yi min nauyi saboda bacci, fuskar Sultan na gani dab da tawa yana kallon fuskata. A hankali tunani na ya fara dawowa, nayi sauri na mike zaune amma maimakon in ganni a kan kujerar dana kwanta sai na ganni a kasa a kan carpet nayi pillow da damtsen hannun Sultan. Na juya na kalli sultan naga ya chire rigarsa complete yayi pillow da ita sai singlet dinsa kawai. Nayi sauri na kalli nawa jikin naga hijab dina yana nan amma duk da haka ban yarda ba sai da nayi ta taba jikina wai ko zanji wani chanji. Duk abinda nake sultan kallona kawai yake yi yana dariya, sai da ya gama dariyar sa sannan yace "Don't worry yau ne ba gobe ba. And when I touch you ko tashi zaune ba zaki iya ba" na bata rai nace "wa yace ka dauko ni daga inda na kwanta? Ka hana ni kwanciya akan gado na kuma kan kujerar ma sai da ka raba ni da ita" ba tare dana jira amsar saba na mike tsaye ina kallon waje, I don't know the time but nasan assuba ta kusa, ya mike shima yana zuwa rigarsa ya karaso kusa dani yace "zanje in shirya, karfe shida zamu bar nan saboda muje akan lokaci" ban bashi amsa ba ya kara matsowa kusa dani yace "are you scared?" A hankali nace "yes" yace "me too. I am scared I might fail you as a husband. Na sani kamar yadda mutane suke ta fada min koda yaushe cewa I don't deserve you. Ni kaina bansan dalilin da yasa Allah ya bani ke ba, kin fi karfi na nesa ba kusa ba. Amma abinda na sani without doubt shine ke alkhairi ce a gare ni" ya riko fuskata da hannayensa yana kallon cikin idona yace "I promise you like I always did, I will never let you down. Abinda nake bukata daga gareki shine ki kara hakuri dani. I promise you you will never regret marrying me" na lunshe idona ina jin dadin maganganunsa sannan a hankali na bude ina kallonsa nace "kar kake cewa bakayi deserving dina ba sultan, you deserve more than me. Dan haka ni ya kamata inji tsoron kar inyi failing dinka, kar in gaza baka farin cikin da kayi deserving. And I promise you, I will never regret marrying you". Expression din fuskar sa is very clouded, irin yanayin da bana iya karantar sa, ya jawo ni da sauri ya rungume a jikinsa, ban hana shi ba, ya jima sannan ya sake ni ya kamo sannuna ya saka min key din kofar sannan ya haura railer ya juyo yana kallona yace "see you on the other side wife" daga nan ya dirga kasa. Ina kallonsa ya yi hanyar part dinsu da sauri.
Na jima a tsaye a gurin ina kallon hanyar da yabi sannan na juya na shiga daki. Direct toilet na shiga nayo alwala nazo na fara sallali ina rokon Allah alkhairan da suke cikin auren nan da kuma tsari daga sharrukan da suke cikinsa, ban jima ba aka fara assalatu, na tashi na kawo raka'atainil fajri sannan na dora da subh. Ina idar wa Mommy ta shigo tace min "kizo inji Daddy n ku" na mike na bita a baya har part din Daddy, ina shiga na tarar dashi a zaune yana shan coffee, ya shirya tsaf daga dukkan alamu daga nan sai gurin daurin aure. Ba zauna a kasa na gaishe shi ya amsa mun fuskar sa a sake. Sai da ya gama shan coffee dinsa sannan ya fara min magana "maimunatu yau Allah yayi insha Allah nan da 'yan awanni zamu daura miki aure da Sultan wanda ke kika zabe shi da kanki mu kuma muka goya miki baya har Allah ya tabbatar mana da abin. To so far dai babu abinda zance sai Alhamdulillah. Na amince zan aura miki Sultan ne saboda abu biyu, na farko ina kwadayin ladan da zamu samu daga ni har ke in har burin mu ya cika na gyara rayuwarsa, abu na biyu kuma saboda tsananin sonki da naga yana yi, nasan wannan soyayyar zata iya saka shi yayi komai, wanda nake saka ran soyayyar ki zata iya saka shi ya chanza rayuwarsa. Auren Sultan da zakiyi tamkar jahadi ne. Duk abinda nayi a rayuwar sultan tamkar sharar fage ne akan wanda ke zaki cigaba dayi bayan auren ku. Sai kin dage sosai maimunatu. Nasan ke yarinya ce mai ibada amma ina so ki kara akan wacce kike yi da, ki dage da adduoi na neman tsari sannan ki tsarkake zuciyar ki daga dukkan sharri. In sha Allahu Allah yana tare da ke kuma bazai barki ki tabe ba. Ina son ki sani cewa dani da Mommy n ki muna tare dake 100% amma hakan ba yana nufin muna so mu san duk wani sabani daya shiga tsakanin ki da mijinki bane, duk abinda ya faru tsakanin ku mun fi son ya kasance ya tsaya a tsakanin ku, sai dai in har kinga yafi karfin ku sannan sai ki kawo mana shi mu kuma zamu yi iyakacin kokarin mu muga an samu maslaha a lamarin. Allah yayi miki albarka Allah, Allah ya baku zaman lafiya dake da mijinki" Mommy tace "Ameen" ya tashi yace "nina tafi" sai da suka fita shida Mommy sannan na lura cewa kuka nake yi ashe, ba goge hawayen idona ina jin alamar jikina yana daukan zafi kamar mai shirin fara zazzabi. Ina nan zaune har Mommy ta dawo daga rakiyar Daddy ta zauna kusa dani ta kamo hannayena tace "kuka kuma maimoon? Wa yace miki yanzu 'yammata suna kukan aure?" Nayi mamakin yadda Mommy take min magana a hankali cikin rarrashi babu fada, nan ta shiga yimin tata nasihar da kuma bani shawarwari akan harkar auratayya, na koma na kwanta akan cinyarta ina sauraronta kuma ina daukan duk abinda take gaya min. Muna a haka Hafsat ta shigo da khairat a hannunta suka hadu ita da Mommy suke ta kwantar min da hankali, Hafsat tana tsokanata da cewa "ke da zaki zauna ma a kusa da gida? Ko ihu kikayi da karfi Mommy zata jiyo ki" na dan yi murmushi kadan. Wayar Mommy tayi kara aka sanar mata mai gyaran jikina tazo, muka sauka kasa mukayi breakfast first sannan aka fara yimin kitso, dama na gaya mata ina son tayi min kitso shi yasa ma tazo da wuri. Kanana kitso ne irin na bare bari akayi min da kitson gaba da matar tayi masa wata tubka wacce ta rufe rabin ido na na hagu. Kowa yaga kitson nan sai sambarka. Bamu gama ba sai wajan sha daya da rabi. Ni dai duk hankali na baya kan wanda suke tare dani kallon agogo kawai nake yi gaba na yana faduwa, har daci nake ji a bakina. Ana gama yi mun kitson na sulale na gudu na tafi dakin daada, duk babu kowa a ciki dan duk suna part din mu, na shige cikin bedroom dinta na kwanta ina jin temperature dina tana kara hawa. 12:00 nayi na runtse ido na ina karanto duk adduoin da aka koya min a islamiyya. Around 12:30 na jiyo guda cikin gidan mu, gaba daya an dauki hayaniya. Nan take hawaye ya balle min. Kuka nake yi sosai amma ni kaina bansan dalilin kukan nawa ba. Shin na murnar na zama matar Sultan ne ko kuma na menene oho. Nasan ana can ana nemana a cikin gida dan ko waya ta ban taho da ita ba dan kar a kira ni. Suwaiba, wata 'yar uwar mu daga Niger ce ta shigo dakin ta ganni around 1:00 da sauri ta fita ina jinta tana bada sanarwar ai gani can a dakin daada. Kan kace kwabo dakin ya cika, tsofaffi da 'yammata sai tsokana ta suke wai azo aga amaryar zamani amma tana kuka, ni kam kamar kara zugani suke yi dan kuka na kawai nake yi bana sauraren su. Umma ce, babar Amina tazo ta fito dani tace su daina tsokana ta, ta shiga dani har dakina itama ta sakani a gaba da nasiha, Amina har da yimin video wai sai ta nuna wa Sultan dan yasan cewa ashe duk I love you din na karya ne bai kai zuci ba. Ina daukan waya ta naga 13 missed calls daga sultan, a raina nace "wasa ma kenan, kai da kaji muryata kuma ai sai dai acan" .
Sallah kadai na samu nayi dan abinci ma kasa saka shi nayi a bakina, aunty zaliha ce ta saka ni a gaba da kyar na iya cin loma biyar nace na koshi. Mommy ta shigo ta kawo min magani na tace in sha, na karba ba musu na shanye. Idon Mommy kawai na kalla nasan itama kukan ta gama. Ina jin Hafsat tana kiran mutane su zo su ga hoton ango a waya, suna ta yaba kyan da yayi amma ni kam na kasa kalla. Daga baya naji suna waya da Hafsat tana gaya masa wai gani nan ina ta kuka, ta miko min naki karba sai ta saka shi a hands free "kiyi hakuri amaryata ki daina kuka, gani nan akan hanya, ina shigowa abuja zan zo in rarrasheki da kaina. Kuma duk wanda ya tsokane ki ki rubuta min sunan sa ni kadai nasan abinda zanyi masa" daga jin yadda yake maganar kasan shima dariyar yake yi, na karbe wayar na kashe, ni banga abin dariya ba dan ina kuka anyi min aure. Mai gyaran jiki na ta hada min ruwa tace inje in shiga, na shiga na kwanta ina lissafin shikenan fa, yau na taka wani stage na daban a rayuwaya, yau wani nauyi babba ya hau kaina, shi kenan na zama matar aure. Bayan an gama yi min wankan na shafe jikina da wannan man da ta bani na musamman, ta hada min turaren da nake tsugunnawa akai shima nayi. Muma gama wa da mai gyaran jiki mai kyalliya tazo muka fara, na gaya mata yau bana son heavy make up light zatayi min dan haka ba mu dade ba ta gama min. Yau shadda na saka fara tas da bakin aiki a jiki, komai da na saka fari ne. Irin shigar da Sultan yayi kenan ta daurin aure. Da dankwalin shaddar aka yi min gwaggwaro. Mommy ta shigo da wani dan karamin box a hannunta ta fito da complete set din sarkar gold, da kanta ta saka min, nan na kara fitowa tar dani. Ina yin sallar la'asar aka saka farin mayafina aka rufe ni ruf har fuska aka saukar dani kasa zuwa dakin Hafsat, karfe biyar 'yan daukan amarya suka zo, ai ina jin zuwansu na kankame Mommy na fara sabon kuka, itama biye min tayi muka yi ta rusa kukan mu, sai da wata kanwar daada tazo sannan ta kama yi wa Mommy fada. Yaya ce da kanta tazo dauka na, inna ce ta bayar dani ta danka hannuna a hannun yaya, ni dai idona a rufe, ji nayi an lullube ni da wani abu mai kauri yana wani kamshi na musamman, ashe alkyabba ce. Babu abinda nake ji sai guda ta ko ina. Haka ina ji ina gani aka fita dani daga gidan mu aka sakani a mota, da jiniya da komai aka tafi dani palace. Yaya da inna su suka saka ni a tsakiya. Tun da nake ban taba shiga palace ba sai yau. Kuma yau din ma fuska ta a rufe take dan haka babu abinda na gani.
Cikin gida aka fara shiga dani direct part din Hajiya. Ina jin muryoyin su Fa'iza suna tsokana ta amma ban kula su ba. Da fara'a da komai Hajiya ta tarye mu. Duk da cewa fuska ta a rufe take amma na fahimci shima gidan a cike yake da mutane. A nan Umma kuma ta bawa Hajiya amana ta ita kuma tace ta karba. Sai da akayi sallar magrib sannan aka tafi dani gidana. Tafiyar kusan unguwa guda ce kafin gidan. Tun daga waje mutane suke kiran masha Allah, inna ta sakani nayi bismillah sannan na shiga da kafar dama. Direct cikin bedroom dina aka wuce dani, gidan gaba daya kamshi yake yi saboda tun safe Mommy ta aiko aka kara gyarashi aka saka fresheners a ko ina. Ko ina an bude a gidan saboda mutane su gani, part din Sultan ne kawai a rufe. A hankali mutane suka fara watsewa, iyayena duk suka zo sukayi min sallama suka tafi, daga karshe ya rage daga ni dai kawayena wadanda zasu zauna saboda partyn da za'ayi in an jima wanda kuma zai yi serving a matsayin siyan baki.
Amina ce ta mintsine ni tace "to sun tafi, sai ki bude fuskar ai" sai da na leko na tabbatar babu wani babba a dakin sannan na bude idona. Hasiya tace "au ashe kukan ma harda na munafunci a ciki" na murguda mata baki nace "eh din" suka saka dariya. Zulaihat tace "Moon gidanki yayi kyau, masha Allah" nace mata "nagode" Hafsat tace "kunji rashin kunyar ko? Ki bar mu muyi godiyar mana". Anan muka yi sallar magrib da bamu samu munyi ba, ina cikin sallah naji wayata tana kara, Amina ta dauka tace "kunga daya marar kunyar ko? Ba karamin aikin Sultan bane yanzu yace an fasa partyn nan kowa ya tafi a bar masa amaryarsa" ta dauka ta gaya masa ina sallah sannan ta kashe. Ina idarwa nace "ke Amina waye ya baki damar yi min magana da mijina" duk suka kwashe da dariya. Hafsay tace "ina tausayawa angwayen nan yanzu fa dawowarsu daga 'yalleman kenan kuma zasu tarar da wata hidimar ta daban". Bayan munyi sallar isha muka shirya zuwa gurin partyn, a wajen swimming pool za ayi, gurin kato ne amma kuma a zagaye yake, dan madaidaicin swimming pool ne a gurin sai kuma kujeru da aka jejjera. An kawata gurin da fitulu masu color wanda yasa ruwan yake yi kamar shi ma different colors din ne. Kayan da na saka musamman Zayed yayi mana order dinsu daga saudiyya a matsayin wedding gift dinsa, kayan larabawa ne na mace dana namiji, kalar light blue mai kyalli. Nayi rolling mayafin yadda ya rufe rabin fuskata tunda ba'a saui baki ba.
Sai da suka gaya mana sun iso sannan muka fita gurin partyn, kawayena a zagaye dani wai lallai babu mai gani na sai an biya kudi. Suka kaini kan kujerata suka zaunar dani. Hayaniyar da naji ne yasa na fahimci gurin a cike yake da maza abokanan Sultan, a raina nace 'sultan akwai kwashe kwashe shi kam' ina jinsu suna ta ciniki na sai kace wata kaza, har suka gama a take Solomon ya rubuta check ya bawa kawayena, sai da aka basu sannan suka matsa daga gabana na fito fili sosai. Ta cikin mayafina nake leken inda zanga Sultan, tunda aka daura ban ganshi ba, can na hangoshi a tsakiyar abokansa suna ta dariya, fuskarsa kamar gonar auduga, yayo kyau sosai da kayan sa irin nawa. Gurin gaba daya ya hargitse da samari da 'yammata, kusan rabin mutanen gurin a tsaye suke. Ina jiyo amir da sultan suna ta musu, Amir yace tunda an sayi baki sai a bude fuskata kowa ya ganni tunda purpose din taron kenan, a taryi amarya, Sultan kam yace sam babu mai gane masa fuskar mata, ai kowa ya ganni a dinner da luncheon.
Ni dai ina zaune kamar gunki. Wani kamshi dana shaka be yasa zuciya ta ta tsaya ta daina bugawa for some seconds, sannan kuma ta fara bugawa da sauri, Hafsat da take zaune a kusa dani naji ta mike tace cikin muryar rada "what are you doing here?" Muryarsa naji yace "I have come for her" a razane na dago fuskata, Ibrahim na gani a tsaye a gabana, wani jiri naji yana neman daukana 'am I hallucinating?' Yawun bakina gaba daya ya kafe. Na kalli gurin da Sultan yake naga ya juyo yana kallon mu. Ji nayi kamar in tashi in fita daga gurin a guje saboda tsoro. Bakina ya kasa motsi ballantana inyi magana, inajin Hafsat tana masa bala'i murya kasa kasa "ka fita tun kafin su ganka, baka san an daura mata aure bane ba, there is nothing more between you two" maimakon ya fita din sai ya durkusa a gaba na, na kuma kallon Sultan da sauri naga gaba daya attention din su shida friends dinsa ya dawo kan mu. Fitsari ne kawai ban saka a wando na ba. Sama sama nake jin muryar Ibrahim yana magana "Maimunatu, nace miki na hakura ne saboda kince min you will be happy with him, a lokacin ban san wanene zaki aura ba, Maimunatu how can you marry someone like him? Is he blackmailing you or your family? Nasan ba dan kudinsa bane because you have all the money you need, kuma yanzu bayan binciken da nayi a kansa na tabbatar ba dan kina sonsa bane, saboda ni na sanki, nasan ba zaki taba son mutum mai hali irin nasa ba. Maimunatu nazo nan a yau, duk da nasan cewa ba lallai ne ya bar ni in fita daga gidan nan da raina ba amma am ready to die for you in dai har hakan zai kawo karshen wannan auren naki ne. I sacrifice my love so that you will be happy, but now after knowing you won't be happy I am willing to sacrifice myself so that you will be free" Tashin hankali ba'a saka masa rana. Poor Ibrahim. You have no idea what you have done. Hannuna naji ya kama ya saka min wani abu a ciki, sannan cikin rada yace "please Moon, run away" ta baya naga an finciki Ibrahim an mikar dashi tsaye, na daga kaina naga Solomon, kyakykyawan mari ya sauke a fuskar Ibrahim. Na mayar da dubana kan Sultan, kofin da yake hannunsa naga ya saki ya fadi kasa, sannan ya fara takowa a hankali idonsa yana kaina, na mike tsaye ina jiran karasowarsa, Hafsat ce tayi sauri tasha gabana, a raina nace "oh no my dear sister, Sultan will never hurt me" chak ya daga ta ya ajiye a gefe, na daga mayafina na karasa bude fuskata ina kallon cikin jajayen idanunsa. Bazan iya cigaba da kallon abinda nake gani a idon sultan ba dan haka na rufe nawa idon, ya dora goshinsa akan nawa yace cikin muryar rada "who is he?" Na kasa cewa komai, ya kara tambayata "who is he?" Da kyar na tattaro yawun bakina daya bushe a hankali nace "please sultan, not here" kamar baiji ni ba ya sake cewa "who is he" kafin in bashi amsa ya kama hannuna ya cire abinda Ibrahim ya saka min a ciki, na bude idona na kalli abin, shima shi yake kallo. Kallo daya nayi masa na gane menene, pink Handkerchief dina ne dana yiwa Ibrahim reply a jiki all those years ago. Sultan ya bude ya karanta rubutun jiki. "I don't know where the path to the future leads, but I want to find out with you"
Hmm
Episode Sixty Nine: The Wedding Night 2
Ibrahim; 9 hours ago
Ya daga kai ya kalli agogonsa da yake kada karfe goma sha biyu na rana. Ya mayar da idonsa ya lumshe yana jin zafi a ransa. Tun safe yake kwance akan gadonsa, ko breakfast bai yi ba. It is time, yasan yau ne yasan kuma yanzu ne daurin auren Maimunatu dan har katin daurin auren yana dashi. Ya dauko katin yana juyawa a hannunsa, sau nawa za'a bashi katin auren maimunatu ne wai? Kamar yadda ya gaya mata ya hakura, he just want her to be happy, kuma indai happiness dinta will come from wannan auren to dole zai hakura da ita ko da kuwa zai cigaba da zama babu aure har karshen rayuwar sa. Amma tun ranar da yace mata ya hakura din bai samu sassauci na radadin da zuciyar sa take masa ba har yau. Why must his destiny be so cruel ne? Da ya rasa ta ya sha wahala after several years kuma sai gata har office dinsa only for her to tell him cewa bata sonsa yanzu wani take so kuma. Ya mike zaune ya jawo wayarsa ya kira yaronsa ya bashi umarnin ya siyo masa abinci ya kawo masa dakinsa. Ya ajiye wayar yana tunanin wannan abin daya same shi yasan duk alhakin Efi ne. Marainiya babu uwa babu uba aka aura masa amma duk da son da tayi masa haka ya rufe idonsa yayi ta gallaza mata sabida baya santa. Lallai alhaki kuikuyo ne, gashi shima wacce yake so din tace bata sonsa kuma duk da cewa ba tayi treating dinsa kamar yadda yayi treating Efi ba amma zuciyar sa ba karamin zafi take yi masa ba. Shin haka Efi taji itama? Ko kuma taji fiye da haka ma? Ya tuna sunan mijin da Moon ta aura, Sultan, a Prince, ya tabbatar ba zata samu matsala ba tunda at least babban gida zata shiga, gidan daraja, she will be respected in the society. By impulse, kawai ya jawo wayarsa ya shiga Facebook saboda yana son ya rage tunani, yana shiga ya fara scrolling through newsfeed, ya jima a haka kawai yaga hoton Moon tare da wani, ya jima yana kallon hoton saboda irin kyan da yaga tayi masa, yayi sauri ya dauke kansa yana kiran "auzubillah" matar wani ce yanzu, ko kallon mijin nata baiyi ba ya bude labarin kasan hoton. Zuciyarsa ce ta buga da karfi har sai da ya mike zaune, jikin sa ya fara karkarwa, ya sake maimaita heading din labarin "The Drunk Prince of Abuja weds Today" a hankali ya fara karanta labarin, an danyi brief magana akan Sultan, irin halayensa da mutane suka sanshi dashi, sai kuma akayi bayanin yadda bikin ya kasance da irin kudin da aka kashe a bikin. Kafin ya gama karantawa gaba daya gumi ya jika jikinsa, ya fara duba comments din mutane, most of them suna cewa suna tausayawa Moon na 'she looks so young' 'iyayenta sun cuceta' 'poor girl' wadanda kuma basu san iyayenta ba suna cewa 'kudi iyayenta suka gani suka bashi' Ibrahim ya ajiye wayar akan gado ya rike kansa da yake sara masa, ya ilahi, me yake faruwa ne? Mai yasa maimunatu ta auri mutum irin wannan? Ba class dinta bane ba. Ya sake daukan yawar yana ta bincike akan Sultan, anan yaga labarin gang bang da irin abubuwan da suke aikatawa a duk fadin Nigeria. No, no, no, kawai yake maimaitawa "no I will not let Maimunatu destroy her life. But why us she doing this?" Gani yake kamar duk abinda ya faru fault dinsa ne, da ace tun farko bai tafi ya barta ba da duk haka bata faru ba. A ganin sa babu wacce zata auri dan giya tace zataji dadin aure, babu kuma wacce zata auri known criminal kamar sultan tace zata ji dadin aure.
Da sauri ya zura rigarsa ya dau key din motar sa ya fice, yama manta da zancen bai ci abinci ba. Supermarket dinsa ya tafi yayi kamar zai shiga sai ya tsaya, mai gadi yazo ya gaishe shi, yace masa "kasan wani dan Sarkin garin nan kuwa da ake bikinsa yanzu?" Da sauri yace "sosai ma kuwa yallabai, ai wannan babu wanda bai san shi ba a garin nan, tun yana yaro ya gagari ubansa, mai martaba sarku da kansa ya kaishi gidan gagararru, acan ya girma, naji labarin ma har kisan kai yayi a gidan shine suma suka ga ba zasu iya ba suka sallamo shi ya dawo" (kunji mutane ko?hmm) Ibrahim yaji yawun bakinsa gaba daya ya dauke, mai gadin yace "Yallabai Allah dai yasa ba wani abun ne ya hada ka dashi ba?" Ibrahim yace "babu komai kawai labarin bikin naji" daga nan bai shiga ba ya fito da motar sa ya kuma hawa titi, tafiya kawai yake bai san inda zashi ba, mai yasa Daddy ya yarda ya aura wa Moon Sultan? Tabbas da akwai wani abu a kasa. Maybe blackmailing Daddy yake yi, tunda Daddy babban mutum ne, Sultan zai iya hada wata karyar yace idan Daddy bai bashi Moon ba zai fada a gari, irin abinda blackmailers suke yi. Wani gurin cin abinci ya tsaya ya shiga, ya duba agogonsa yaga karfe biyu har da rabi, time is running out, he have to think of something. Dan kadan yaci abincin yaji ba zai iya ci ba, ya tashi yaje gurin biyan kudin sai yaga bayarabe ne cashier din, ya tambayeshi da yarabanci "kasan dan sarkin garin nan da aka yiwa aure kuwa?" Mutumin kamar dama jira yake yace "ni kuwa na san shi, ni da suka hana ni bacci jiya da daddare ba dole in san shi ba?" Ibrahim yace "suka hana ka bacci kamar yaya?" Mutumin yace "ai inda suka yi partyn jiya a kusa da gida nane, shi mai gidan, Solomon, is a known criminal in lagos, ya gagari kowa, he is a kidnapper as well as an arm robber. Gida kawai ya saya a garin nan ya ajiye in yayo barna a lagos sai ya taho nan ya zauna kwana biyu sannan sai ya koma. Jiya a gidansa sukayi partyn su har gari yawaye babu wanda yayi bacci a unguwar nan sabida kida, kwalaben giya kuwa da aka ringa shiga dasu ni dai har kallo na fito yi, da safe makocina ya ce min ta window dinsa yaga ana shiga da mata gidan, mata irin wadanda bana mutunci ba, mu dai jiya Allah ne kadai ya saka va'a kife da unguwar mu ba saboda yawan zunuban da aka aikata a ciki" Ibrahim has heard enough, yayi masa godiya ya fito. Direct gida ya koma, kafin ya karasa gida har ya yanke shawarar abinda zai yi a ransa. He is going to break the marriage, even if it takes his life. Yayi murmushi a ransa, maybe wannan shine destiny dinsa, maybe wannan shine dalilin da yasa Allah ya sake hada shi da Moon few days to her wedding. Yana zuwa gida yayi sallah ya bude locker dinsa da yake ajiye muhimman takardunsa ya dauko handkerchief din Moon daya ke ta ajjiye dashi all those years. Ya karanta rubutunta da still yake baro baro a jikin hanky din "I don't know where the path to the future leads to, but I want to find out with you" ya sake yin murmushi. So, this is it, this is the future, their future, and he will be there for her. Da yake late yayi sallar azahar din sai yaji already ana la'asar dan haka ya sake tashi yayi sannan ya dauko wayarsa. Yasan inya kirata ma ba zata dauka ba. Amma wannan 'yar'uwar tata wacce tayi masa karyar cewa ita yayar moon ce, yama sunan ta? He can't remember. Number din ma bai yi saving ba dan haka yayi ta scrolling call history dinsa har yayi tracing number din, yayi dialing, sai da ya kira wajen sau uku sannan ta dauka, kamar yadda yayi tsammani hayaniya ake tayi, tace masa bata jinsa sosai amma bara ta fita waje ta kira shi. Ba'afi ten minutes ba kuwa ta kira shi, suka gaisa sosai ya tambayeta ya biki tace Alhamdulillah, yace "kuma ku bikin naku na rowa ne ko? Ko gayyatar mutane ma bakwayi" tace "ayyah, na dauka Moon ta gayyace ka ai" yace "a'a, ko daurin aure bata gayyace ni ba. Na so kuma inyi attending ko da event daya ne in yi wa ango Allah ya sanya alkhairi, kuma kinga kema ai da mun sake gaisawa sosai ko?" Ta danyi dariya tace "ai ba'a gama ba, yanzu zamu tafi kai amarya, a can gidan nata kuma zamu yi party da daddare" a ransa yace "perfect, then that is what I will attend" a fili kuma yace "to ban sani ba ko za'a iya gayyata ta can din" ta sake dariya tace "why not, ai har da maza abokan ango. Ka taho kawai bayan Sallar isha, tunda biki ake in kazo palace din zasu barka ka shiga, sai a nuna maka part din amaryar, in kaje can sai ka kirani sai in shiga da kai" yace "kai amma naji dadi sosai, jazakillah bil jannah" tace taba dariya "kai sai kace wani abu na baka? Sai kazo din" ya kashe wayar yana murmushi, sam baya jin tsoro ko fargabar abinda zai je ya dawo. Tsoron da yaji ya kasa tunkarar Daddy shine dalilin faruwar komai, he is no longer afraid, he was a fool, but not anymore. Yana yin sallar isha ya shirya, shi kansa bai san taka maimai me zaiyi ba amma yasan zuwansa gurin a matsayinsa na tsohon saurayin Moon zai bata ran mijinta, tunda dan giya ne ma zai dauka ita ta gayyato shi, hakan kuma zai iya zama sanadiyyar mutuwar auren, shi kuma ko menene zai faru dashi bai damu ba, as long as Moon will be free from this marriage.
Bai sha wahala gurin shiga palace din ba saboda gidan a cike yake da mutane, tun daga gate ya tambaya akayi masa kwatancen inda gidan amaryar yake, da dan nisa kafin ya karasa, yana zuwa yaga gurin a cike da motoci, yayi packing ya fito sannan ya kira number din Amina yace mata gashi yazo, ba'a jima ba ta fito suka sake gaisawa sannan tayi masa jagora zuwa ciki. Suna shiga ya hango Moon a zaune a tsakiyar kawayen ta, sparkling like the moon she is. And he feel like his life doesn't matter any more.
Moon
Na sake rufe ido na ina kokarin saita numfashina tare da kiran "innalillahi wa inna ilaihir rajiun" repeatedly a zuciya ta. Na bude ido na naga har yanzu Sultan ni yake kallo, jijiyoyin wuyansa da goshin sa sun fito rado rado. Na sake hadiyar yawu da kyar nace "Sultan, this is not what you are thinking" ya kalli handkerchief din hannun sa yace cikin shakakkiyar murya "this is your handwriting. Baki bani amsa taba, who is this man to you? What is he doing here today?" Nayi kokarin rike hannunsa ya matsa baya, cikin rawar murya nace "Sultan not here please. Nayi maka laifi, please ka bari muje wani gurin sai inyi naka bayani". Handkerchief din hannunsa ya dunkule ya jefo min a kirjina, ya juya baya ya koma inda yake dazu. Ban taba ganin bacin rai a fuskar sultan irin wanda nake gani yanzu ba. A hankali na juya gurin Hafsat da take tsaye kusa dani na dora kaina a kafadar ta na fara kuka. Muryar Amir naji yana magana "alright ladies and gentlemen, the party is over, we really appreciate your presence but you all need to leave now" na dago kai ina kallon mutane suna ta fita, friends dina ko sallama basu samu damar yi min ba duk Amir ya tisa keyar su suka fice, Amina da Hafsat ne kadai suka ki tafiya, mazan ma duk Amir ya koresu, amma sai na lura da gang bang ko mutun daya bai fita ba, sai kara samun guri suka yi suka zauna. Sultan na hango shi kadai yana tsaye ya juya bayan sa ya dora kafarsa akan kujera yana shan wani abu a cikin kofi. Gaba na ne ya fadi, oh dear God, no. This is all my fault, tun farko dana bawa Sultan labarin Ibrahim da duk haka bata faru ba. A hankali na fara takawa ina tafiya inda Sultan yake tsaye, na karasa bayansa na dora hannuna a kafadarsa nace "am sorry sultan" ya ture hannuna daga jikinsa ya juyo yana kallona da idanunsa da suka fara sauya color zuwa ja, yace cikin daga murya "why? Na sha tambayar ki in akwai wani wanda ya kamata in san da zaman sa amma kika ce min babu" kafin in bashi amsa naji muryar Ibrahim yace "sai ka tambayi kanka me yasa bata ba ka labarina ba, maybe it is because she is still in love with me" nan take idon Sultan ya karasa yin ja kamar garwashin wuta, ya juyo a fusace yace "please somebody should shut up that man for me" tun kafin ya rufe bakin sa kusan mutum biyar suka yi kan Ibrahim suka fara duka, durkushewa nayi a gurin na dora hannu na aka na fara rusa kuka ganin yadda suke ball da Ibrahim ta ko'ina. Banda Solomon wanda yake zaune a gefe ya dora kafa daya kan daya shan abinda yake cikin kofin hannunsa, wanda ko ba'a gaya min ba nasan irin abinda sultan yake sha ne, a cikin gida na ranar da aka kawo ni. Na rike rigar sultan ina kuka guiwowina a kasa "dan Allah Sultan ka kalle ni kaji abinda nake gaya maka, please ka hana su dukansa dan Allah" kamar wanda na kara tunzura shi ya juyo yace min "why? Me yasa ba kya so su dake shi? Saboda abinda ya fada gaskiya ne, saboda still kina sonsa?" Nayi saurin girgiza kaina nace "I don't love him sultan, I Love You, I chose you, I marry you. Menene kuma ya rage?" Cikin fada yace "you marry me sannan kika gayyato tsohon saurayinki cikin gida na?" Ban san sanda na dake shi a kafada ba nace "how can you say that? Come back to your senses Sultan" bai ce min komai ba sai tsayawa da yayi kamar mutum mutumi yana kallona, ta gefen idona na hango Solomon ya taso ya taho inda muke, yana karaso wa ya mika wa sultan kwalbar da take hannunsa, ba musu ya karba, da sauri na na fincike daga hannunsa na zubar da abinda yake ciki a kasa. Solomon ya saki baki yana kallona kafin ya fara magana "ni dama tunda aka bani labarin cewa our sultan has fallen in love with a good girl, nasan cewa we lost him, Sultan din dana sani ba zai zauna ayi masa irin cin mutuncin da aka yi maka ba, this means nan gaba sharing dinta za ka ke yi da sauran samarinta, only God knows su nawa ne, tunda baka san da wannan ba sauran ma ba zaka sanda su ba sai dai ka gansu a kan gadonta" a zuciye sultan ya juya ya kai masa duka yana cewa "shut up, damn you" ya rike hannun sultan yace "in baka son hakan ta faru then end it here, ka nuna min cewa har yanzu baka yi loosing guts dinka ba over a woman" hannunsa ya saka a aljihu ya zaro wani abu, ganin abun kawai ya saka naji wani zazzabi yana neman ya sauko min, Ya Allah intervene. Tunda nake ban taba ganin bindiga ba sai a film amma yau wai gani ga ita a daren farko na na aure. A hannun sultan ya saka bindigar yace a hankali "shoot him between the eyes, in kayi haka sauran babu wanda zai sake zuwa" gaba daya jiki na karkarwa yake yi dan bana jin bakina zai iya budewa har inyi magana. Amir ne ya karaso gurin da sauri fuskarsa cike da tashin hankali yayi kokarin karbar bindigar daga hannun sultan amma Solomon ya ture shi yace "stay out of this" yaje ya jawo Ibrahim wanda akayi wa laga laga, ya ajiye a gaban Sultan yace "Shoot him" na kama hannun sultan daya ke rike da bindigar nace "Sultan no" a hankali sultan ya dago kansa ya kalli Solomon yace calmly "no, I will not shoot him" ya juyo da jajayen idanunsa kaina ya ce "kince min you chose me over him, let's find out in gaskiya kike fada" ya saka min bindigar a hannuna yace "choose again, me or him" kallonshi kawai nake da mamaki, this is not my Sultan, this is someone else's. "Ki zaba, in har kina sonshi then put a bullet in me, in har kuma ni kike so kamar yadda kika fada then put a bullet in him" sama sama na ke jin sauran maganganun, naji Hafsat tana cewa da Sultan "baka da hankali Sultan? Menene hakan kake yi" na daga mata hannu alamar tayi shiru ba tare dana kalleta ba, no body will get hurt again a saboda ni, naji Solomon yana yiwa Sultan masifa "what if she shoots you?" Sultan yace "then so be it" Amir naji a kusa dani yana magana shima "Moon give me the gun" a hankali na fara jero sunayen Allah a zuciya ta, a take naji duk wani tsoro ya kauce min, na fahimci duk hikima ta ubangiji akan abubuwan da suka faru. This is a battle, Sultan's battle, between his good side and his bad side, I am his good side and Solomon and his other bad friends are his bad side. Yanzu na fahimci komai, na fahimci hikimar ubangiji da ya dawo da Ibrahim cikin rayuwata a wannan lokacin. Kamar yadda Ibrahim ya fada hakane, it is destiny amma ba destiny din zamuyi aure ba. Allah ya dawo da Ibrahim rayuwar mu ne saboda yana son yayi amfani dashi yayi testing Sultan, wannan duk jarabawa ce, ni kuma zanyi iya kacin kokarina inga na taimakawa Sultan gurin cin wannan jarabawar. I now understand everything and I know exactly what to do. Na gyara rikon bindigar a hannuna, it is heavier than it looks. A hankali na dago idona ina kallon rinannun idanun sultan, na motsa bakina na furta I Love You amma ba tare da sauti ba amma na tabbatar ya fahimci abinda nace. Na daga bindigar a hankali ina kallonta, cikin second daya na juya ta zuwa kaina sannan na lumshe idona na dora dan yatsa na akan trigger kamar mai niyyar harbawa. Exactly abinda nayi tsammanin zai faru shi ya faru, kafin in dora dan yatsa na akan trigger Sultan yazo gurin ya doke hannun bindigar ta fadi kasa, dama ba wani rikon kirki nayi mata ba, tana faduwa ya kankame ni tamkar zai tsaga kirjinsa ya sakani a ciki, jikinsa gaba daya karkarwa yake yi. This is my chance, a hankali na fara yi masa magana, yadda babu wanda zai ji daga ni sai shi "Na zabe kane saboda ina sonka, na aure ka saboda ina sonka, ban gaya maka labarin saba saboda bana son in bata maka rai, amma ina son ka sani, babu sauran sonsa daya rage min a zuciyata saboda zuciyata taka ce. Bani nace yazo ba kuma bansan menene yasa yazo ba. Na ce maka ka hana dukansa saboda nasan cewa kai mutumin kirki ne, kuma mutanen kirki basa rama sharri da sharri, mutane ne masu afuwa masu tausayi, mutanen da ubangiji yake alfahari dasu. Nayi kokarin hana ka harbin sa not because I care about him but because I care about you. Kisan kai yana daya daga cikin manyan laifuka da Allah baya so, bana son ka dauki zunubin sa akan ka. Na juyar da bindiga kaina ne saboda in nuna maka how much I Love You. I Love you more than my life it self". Ya jima yana rike dani sannan ya sake ni ya juya da sauri gurin da Ibrahim yake yace masa " GO. But I swear to God, in na kara ganin ka ten miles close to my wife I Will Shoot you". Hafsat ce da Amina suka zo gurina, na rungume daya daga cikin su ba tare da nasan ko wacece ba. Ina jin hayaniyar gang bang "Sultan ya za'ayi ka bar shi ya tafi?" "Har cikin gidan ka fa ya shigo gurin matar ka, har yana ce mata ta gudu daha gurinka" "lallai Sultan ka zama nusari, you are no longer one of us" Sultan yace "gida na ne, kuma matata ce, kuma ni nace masa ya tafi. Duk wanda yake da problem da decision dina will settle it with me" ta gefen ido na naga Amir yana fita da Ibrahim da ga gurin, sannan kuma daya bayan daya suka fara fita, Sultan ne na karshen fita.
Gurin ya rage mu uku kadai, ni Hafsat da Amina. Idon Amina kawai na kalla nasan taci kuka ta koshi, tace "Moon dan Allah kiyi hakuri, wallahi bansan da akwai wani abu a tsakanin ku ba, da nasan haka zata faru wallahi da ba zan shigo dashi ba" na dafa kafadar ta nace "it is OK. Komai ya wuce ai. I have won" Hafsat ta dauko wayarta tace "yanzu zan kira daddy in gaya masa, gwara ya san matakin da zai dauka tun yanzu. In auren nan ba zai yiwu ba gwara a fasa shi kawai" na rike hannunta nace "me za'a fasa? Already an riga an daura. Menene amfanin gaya wa Daddy in banda tayar masa da hankali da zaki yi? Tun kafin a daura auren nan daga ni har Daddy mun san challenges din da zanyi facing. Tunda har yau na iya controlling Sultan na hana shi aikata mummunan aiki duk kuwa da cewa yana cikin tsananin fushi, duk da cewa a buge yake, bana jin akwai wani abu nashi da ba zan iya facing ba"
Episode Seventy : The Wedding Night 3
Kafin mu dora a inda muka tsaya, bara mu dan taba magana akan abinda ya faru ranar kai amarya.
Abinda ya faru ba laifin Ibrahim bane gabaki daya, Moon tana da laifi haka zalika Sultan. Laifin Moon anan shine keeping secrets in a relationship. Wannan shine babban abinda yake wargatsa relationships, ko aure ko kafin aure. Idan kinsan ko kasan da akwai wani abu da kake ko kike boyewa partner dinki/ka to ku fito ku fada, ko da kuwa abinda zai bata masa/ta rai ne, gwara ya/ta sani daga gurin ki/ka akan suji daga wani guri, idan ke zaki fada kinsan da kalaman da zaki yi amfani, idan kuma wani ne zai fada zai iya ya kara har da gishiri da maggi kuma babu yadda zaka/ki yi ka/ki kare kanki. Wannan kuma shi zai kawo rashin yarda, ita kuma yarda da juna ita ce ginshikin ko wanne relationship.
Laifin Sultan kuma shine na yarda ayi organising party a cikin gidansa, wannan mistake ne babba. Ba tsohon saurayin matarka ba hatta su kansu abokanan ka basu da hurumin shigo maka gida irin haka. Ni a ra'ayina ina against siyan bakin amarya da abokanan ango suke zuwa yi. Kwanan baya anyi ta samun cases na raping amare, ni ina ganin wannan siyan bakin da kuma yawan kwashe2n abokanai zuwa ganin amarya yana daya daga cikin abinda yake kawo wadan nan cases din. Ballantana wanda yake da abokanai irin na Sultan.
Laifin Ibrahim kuma shine da yabar emotions dinsa sukayi controlling dinsa ya yanke hukunci ba tare da bincike ba. Babban mistake din da mutum zai yi shine ya yarda da maganganun mutane. Hear say. Wannan ya kara gishirinsa, wancan ya kara maggi wancan ya kara onga, before you know it gaba daya maganar zata chanza salo. Believe only what you see da idonka, ko kuma maganar da kaji direct daga mai ita, ba wai wani ya gaya maka yace wane yayi kaza ko kuma wane yace kaza ba.
Please guys, be a little softer on Ibrahim. He has gone through alot akan soyayyar Moon. He really deserves a break. Amma naga kowa dariya yake masa. Lol. Ni kam #teamIbrahim nake yi, na hana shi auren Moon ne kawai saboda a haka ne ma'anar labarin zata fi fitowa. Please, I am on my knees ku dan rangwanta masa mana.
Back to the story.
Mun jima muna tattaunawa akan abinda ya faru, anan ne Hafsat ta bawa Amina labarin alakata da Ibrahim, yadda Amira ta raba mu da kuma labarin rayuwar Sultan, Amina duk jikinta yayi sanyi ta kasa maganar kirki. Na durkusa a gabanta na rike hannunta nace "Amina, sam yanzu bana yiwa Ibrahim soyayyar aure, amma still ina jinsa a raina kamar dan'uwana haka nake jinsa. Na tausayawa rayuwar da yayi bayan rabuwar mu kuma ina tausayin halin da yake ciki a yanzu. He thinks he is doing a good thing. He thinks I am in trouble. He needs an explanation. He needs to know the whole truth. Dan Allah Amina ina son kiyi reaching out to him kiyi masa bayani yadda zai gane sosai cewa ni na zabi sultan duk da halayensa. Kiyi masa bayanin cewa sultan is not as bad as people think ge is. Ki bashi duk wannan labarin da muka baki yanzu ki gaya masa cewa na auri sultan saboda ina sonsa, saboda ina ganin soyayyata zata kawar da duk wani mugun hali nasa, kuma so far I have succeeded. Ki gaya masa kyaleshin da Sultan yayi yau alama ce ta cewa he is no longer who he was before" tunda na fara magana Amina take girgiza kanta alamar ba zata yi ba, ni kuma ban daina maganar ba har saida nazo karshe, tace "No, Moon, bazan iya ba, ba zai saurare ni ba, yaudara ta fa yayi ya saka na shigo dashi har cikin gidan ki" na kara rike hannunta nace "please Amina, you are my only hope akan sa, duk da yadda nake son in taimaka masa ba ni da yadda zanyi sai ta hanyarki kadai, please help me as your sister" da kyar na samu tace maybe zata yi in ta huce saboda taji haushin using dinta da yayi. Muna cikin haka Amir ya dawo yace amina tazo ta taya shi su kwashe abincin partyn da ba'ayi amfani dasu ba, wadanda ba zasu lalace ba suka shiga dasu suka adana, wadanda kuma zasu baci Amir ya aika dasu cikin gida. Ni da Hafsat kuma muka shiga ciki muka koma cikin bedroom dina muna cigaba da jajantawa, kafin su Amina su gama sai around 12:30, dan haka dole kwana ya kamasu a gidan. Hafsat ta kira zayed wanda tunda yazo bikin ya kama hotel, kullum da daddare yake lallabowa ya dauke matarsa sai da safe yake dawo da ita, ta gaya masa zata kwana a gida na saboda dare yayi. Sai da duk mu kayi wanka muka yi shirin kwanciya sannan naga sun tashi suna yi min sallama wai wani dakin zasu tafi su kwanta. Nace "saboda me?" Hafsat ta harare ni tace "oho miki, yau ne fa first night dinki, kawai kuma sai muzo muyi dare dare akan gado? In angon ya shigo kuma fa?"
Na kasa basu amsa har suka fice. A raina nace "wannan angon nawa ai Allah ka dai yasan inda yake" nayi tunanin in kira wayarsa inji ina yake amma kuma kar ya dauka wani abin nake nema. Na kwanta ina kallon dakina, karshen kyau yayi kyau, babba ne sosai dan duk girman gadon baifi quarter din dakin ba, babu ce kawai a kayan da ake bukata a daki Daddy da Mommy basu saka min a dakina ba. Komai yaji, komai da akwai except ango. Ina Sultan ya tafi? Na gyara nayi kwanciyata duk jikina yana yimin ciwon gajiya amma sam babu bacci a ido na, nafi 30 minutes a haka sai kuma na mike zaune na jawo wayata nayi dialing number dinsa, switched off, yayi fushi, nasan he has the right na yin fushi dani amma abinda yafi damuna shine abinda zai aikata a cikin fushin nasa, ya Ilahi give me the strength. Number din Amir na lalubo na kira, bugu daya ya dauka da alama bai kwanta ba, sai kuma na rasa mai zance masa, yace "Moon baku kwanta ba? Ko akwai abinda kuke bukata ne?" Nace "amm babu komai, dama ina son inji ko Sultan yana tare da kai ne?" Yace "No, ban ganshi ba, na dauka kuna tare ai" nace "a'a ai tunda ya fita bai dawo ba" na dan yi jim sai kuma yace "OK bara in duba shi" na zauna akan gado na harde kafata ina jiran tsammani, can Amir ya kira ni yace "naje har gate na tambaya sunce bai fita ba, kuma naga duk motocinsa da suke gidan nan suna nan, yana cikin gidan, kin duba part dinsa" na girgiza kai kamar yana kallona nace "a'a ban duba ba" yace "ok, ki duba can" nace "to na gode" sai kuma yace "Moon, he will be alright, Sultan is a tough guy, ya fuskanci abubuwan da suka fi wannan kuma yayi surviving. Idan kin duba baki ganshi ba just kiyi baccin ki, let him be, mostly in yayi zuciya yana rufe kansa a wani gurin ne ya zauna shi kadai har sai ya huce, you will be surprise in yazo zaki ga kamar ba'ayi komai ba" na ce "OK, thank you Amir, really thank you, for everything" yace "you are welcome". Banje part din Sultan neman sa ba, na dauki shawarar amir, I will let him come back on his own. Na koma na kwanta ina tunanin lamarin duniya, kana taka Allah na nasa, na tuna irin threats din da sultan yake min akan first night din mu, amma gashi ranar tazo, kuma anyi auren , kuma muna gida daya amma kuma zamu kwana a separate bedrooms. Na tuna baccin mu na jiya akan balcony da abinda ya gaya min sanda muka tashi, nayi murmushi ni kadai. I don't know a ina Sultan yake yanzu, but I know one thing for sure, he is not going to sleep tonight.
A hankali na bude ido na, ji nayi kamar yanzu na kwanta, amma kuma ina jin a jikina kamar gari ya waye, nayi sauri na kalli window naga haske yana shigowa. Na mike zaune da sauri na kalli agogo, 8:30, inna lillahi, ko sallar asuba banyi ba, na shiga uku, wannan wanne irin bacci ne kuma ko juyi banyi ba. Da sauri na shiga toilet nayo alwala nazo na gabatar da sallah sannan na tashi na gyara gadon dana kwanta na koma toilet nayi wanka na dawo daki, tun kafin in fara shiryawa na kira wayar sultan, still switched off, na shafa mai na shirya cikin lace coffee color, riga da skirt da suka kama jikina suka zauna sosai, na gyara kitso na, na bayan ya sauko har gadon bayana, na gaban ma na sake tufke shi yabi ta saman idona ya sauka a wuyana. Na fesa turare na na fito ina neman dakin dasu Hafsat suka kwana, dakin kusa da nawa basa ciki, na kalle shi naga kusan irin nawa ne amma nawa yafi shi girma. Na fita ta dan corridon da zai fita dani palo na, anan dakin ba'kina yake, na murda kofar na gansu sun ba rarraje suna kwasar bacci, nayi murmushi a raina nace 'sun gaji' na duba agogo naga kusan karfe goma, ni kam yunwa nake ji, na dan daki kafar Amina "ke ku tashi fa, kun ma yi sallah kuwa?" Hafsat ta sake jan bargo, nayi ajjiyar zuciya dan nasan ko nafi kuda naci Hafsat ba zata tashi ba, Amina na takurawa sai da ta tashi tana ta kunkuni wai ita bacci bai ishe ta ba an takura mata. Nan na barta tana kokarin shiga wanka na fita ina zagaya gida, a raina ina lissafin Sultan ne fa yayi min alkawarin zai zagaya dani, nasan lissafin yadda gidan yake a raina dan haka ban wani sha wahala wajen gano part din Sultan ba, na tura main kofar sa naji a bude take, na shiga palon sa, na jima a tsaye ina shakar kamshinsa, unique kamshin da yake sakani lumshe idona kullum na jishi, a hankali nake tafiya ina karewa palon kallo, kusan irin nawa ne sai dai ban bancin arrangement din kayan ciki, na shiga corridor dinsa, shima two bedrooms ne dashi irin nawa amma shi bashi da dakin bakin da nake dashi a palo, instead sai akayi part din baki maza daban wanda sai ka fita can main palo sannan za ka shiga gurin. Bedroom dinsa na farko bayanan, kamar ma ba'a taba shiga dakin ba, bedroom dinsa na biyu kuma ina shiga naga alamar anyi amfani dashi amma ba'a kwana a ciki ba, har da kayan sa da yaje daurin aure dasu akan gado, daga dukkan alama sauri yake ya shirya ya tashi gurin party kuma daga can bai dawo nan ba. Na juya jikina a sanyaye na fita. Ina sultan ya kwana? A main palo naga Amina ta fito suna zaune da Fa'iza suna ta zuba surutu, ina shigowa suka bini da kallo, fa'iza tace "wow, masha Allah, babbar yaya kinga yadda kikayi kyau kuwa? Kowa ya ganki yasan babu tantama amaryace" sai kuma ta leka bayana kamar mai jiran wani ya biyo bayana, sai kuma ta rage murya tace "ina angon? Ina fatan dai ba nan zai fito ba dan takura mana zai yi da harara da tsawa" nace mata "sha kurumin ki, baya nan, ya fita already" ta bini da kallon mamaki tace "ya fita kuma? Wanne irin ango ne haka zai fice da sassafe?" Nace "kinsan abokanan sa da suka zo bikin nan wadansu ma bada ga kasar nan suke ba, to duk yau zasu tafi shi yasa ya fita da sassafe dan suyi sallama" daga dukkan alamu ta yarda da bayani na, tayi ajjiyar zuciya tace "har naji dadi, na dauka har an fara gwadawa amaryar halin, kinsan fa sai kinyi hakuri wallahi, dan indai yaya Sultan ne sai ya saka miki ciwon zuciya, dan wani lokacin inya fice sai yayi kwana da kwanaki bama a san inda yake ba" dariya na mayar da maganar nace "really? Kice za'a samu chanji kenan yanzu. Kar ki damu daga yau duk sanda kike bukatar ganin yayanki kizo nan zaki ganshi, in kinga bayanan to office ya tafi" ta tabe baki tace "to Allah yasa" sai kuma tace "dama Hajiya naji tace azo a kawo muku breakfast shine nace bara in zo mu gaisa in kuma ga gidan sosai. Ga abincin can akan dining an ajiye" nace mata "mun gode, in kin koma ki mana godiya a gurin Hajiya" tace "laah chafdi, yaya Sultan fa duk gidan nan shine dan lelen Hajiya, kinga shi ba'ayi masa fada, ba'a saka shi ba'a hana shi, duk abinda yake so shi za'ayi masa, dan haka in kika ce zaki yiwa Hajiya godiya har sai baki kin ya gaji" muka kalli juna ni da Amina, Amina tace "ashe sultan dan gata ne mu bamu sani ba. To shi kuma daya brother din naku fa? Shi ba'ayi masa gatan?" Fa'iza tace "shi wannan ai sha wuya kenan. Shi fa ko time din kansa bashi dashi. Kullum yana tare da Takawa bacci ne kadai yake rabasu, komai nasa shi yake yi. Shi wannan ma banajin ko budurwa yana da ita. In kinga kuwa fadan da Hajiya take masa komai kankantar abu sai kinyi mamaki" Amina ta cigaba da bugar cikin ta "abin tausayi, kice ko karatu mai zurfi bai samu yayi ba kenan saboda bashi da lokacin kansa" tace "kamar kin sani kuwa, da kyar ya samu yayi diploma ya hakura, Hajiya tace masa menene amfanin karatun? Ai anayin karatu ne saboda a samu aiki ake samun kudi, shi kuwa he got all the money to last him a lifetime, aiki kuwa dama dashi aka haifeshi" Amina zara cigaba da yi mata tambayoyi na girgiza mata kai, na chanza topic din da cewa "ni fa duk wannan hirar da kuke yi ba jin ku nake yi ba, dan yunwa nake ji" daga nan muka tashi muka tafi cin abinci. Muna cikin ci Hafsat ta fito, taci kwalliya kamar ita ce amaryar, tayi joining din mu muka ci abincin tare. Dankali ne da kwai, sai farfesun kaji da farfesun ganda, sai kunun gyada mai dadi wanda ni shi nayi tasha, dan sam baki na babu taste, Sultan ne kawai a raina. Nace da Hafsat "kiyi waya mana a kawo khairat, kar tayi ta kuka" tace "ba zatayi rigima ba, nayi expressing breast milk da yawa na saka mata a freezer, da anyi warming an bata shi kenan".
Ranar tamkar wanda ake sake yin wani bikin a gidan, dan sosai gidan ya cika da mutane mostly 'yan uwan sultan masu son ganin amarya da kuma dakin amarya. Na gode wa Allah dasu Hafsat basu tafi sun barni ni kadai ba, dan su sukayi ta hidima dasu suna zagayawa dasu daki by daki, kowa kuwa sai ya yaba da tsarin gidan. Duk kuma wanda yazo sai Amina ta zuba musu kayan gara da snacks din partyn jiya da ba'ayi ba ta bashi. Ni kuma akwatin lefe na na kayan kyalliya guda daya na bude nake rabarwa. Har magriba muna abu daya. Hafsat tayi waya gida ta gaya musu sai dare zasu dawo saboda baki sun yi min yawa, nan da nan sai ga yammata biyu Mommy ta sake turo wa, suka taho da katan katan na drinks da chocolate saboda yara. Abinci kuwa daga cikin gida akayi ta aiko mana, dan haka ko tukunya bamu dora ba. Sai da mukayi sallar magrib sannan kafa ta fara daukewa. Har lokacin babu Sultan babu labarin sa. Na kira wayarsa har na gaji amma still switched off. Bayan munyi dinner muka hadu muka gyara gidan tas har fa'iza da yake bata tafi ba. Muna gamawa muka zauna muna hira, hafsat ta lura ina ta danna wayata ta sake tambayata a hankali "har yanzu bai kunna wayar ba?" Kai kawai na gyada mata, tace "ki kira Amir, shirun yayi yawa" na sake dialing number din Amir, ya dauka muka gaisa yace "ai nayi niyyar shigowa dazu kuma na hango gidan a cike na fasa" nace "wallahi kam yau gidan masha Allah" nayi shiru, yace "bai dawo ba?" Nace "eh, kuma wayar a rufe" yace "amma da mamaki, kusan 24 hours fa kenan" naji hankali na ya kuma tashi. Yace " I will know what to do, am sure yana cikin gidan nan tunda duk friends din mu da suka tafi a gaba na suka tafi kuma bai shiga motar kowa ba, sannan all his cars are here. Za muyi organizing search party mu nemo shi duk inda ya shiga" nace "to na gode, duk abinda ake ciki dai sai a sanar mana" ina kallon Fa'iza tana kallona tana son ta san maganar me nake yi. Tace "wai yaya sultan ba zai dawo bane har yanzu? Tun safe fa nake gidan nan amma baya nan" Hafsat tace mata "a cikin mutanen kike so ya shigo ya zauna?" Tace "a'a wai dai ko yaya ne ai a gaisa dashi. Gashi har dare yayi kar mu tafi mu barta ita kadai"
Bayan sallar isha Amir ya shigo, muka gaisa, nasan ganin fa'iza ne ya saka bai ce min komai ba, sai ya zauna kamar mai daddanna waya ya turo min text, 'couldn't find him, think we report to the police?" ina karantawa naji wani daci a bakina, amma kuma ina jin a raina cewa duk inda yake he is OK, dan da ace wani abun ya same shi da na tabbatar zanji a jikina. Na dago kai na kalli Amir naga baya kallona, nayi masa reply "bashi da wani secret hiding place a cikin palace dinnan? Kamar gurin da yake zama if he wants to be alone?" Ya amsa min "nan spot din dama shine gurin zamansa, cikin trees, yanzu kuma ya sare su yayi gida a gurin" ina tunanin abinda zance masa kawai naji wani feeling like someone is watching me, and that someone is Sultan, nayi sauri na dago kaina na kalli direction din da nake ji feeling din, bakin kofa, and there he is. Har yanzu kayan jiya da daddare ne a jikinsa, fuskarsa babu murmushi kuma babu bacin rai, idanuwansa tarwai a kaina. Nayi sauri na dauke idona na sunkuyar da kaina kasa, har lokacin babu wanda yasan ya shigo palon. A hankali ya fara magana, daga jin muryarsa kasan ya dan jima baiyi magana ba. Yace "waye ya baku izinin ku mayar mana da gida dandali?" Duk suka juya suka kalleshi da mamaki, ni kuwa har lokacin ban dagi kaina ba. Amir ya mike kamar zai ji tsalle yace "I think what you want to say is thank you for keeping my house alive and keeping my wife company" bai bawa Amir amsa ba ya juya yana kallon fa'iza yace "ke, tashi ki fita" jiki na rawa ta mike tace "to yaya babu driver a kusa" yace "Amir ya kaiki" ya karaso tsakiyar palon inda Hafsat take ta watsa masa harara, bai kula ta ba sai da fa'iza da Amir suka fita sannan yace "waye yace kuzo ku cika mana gida da surutu?" Ta yatsine fuska tace "gida? Ina gidan yake? Ai kasan tun kafin ayi daran akayi kwandi, tun kafin kusan zaku yi gida ni da mijina muke da gida, sau nawa kuke zuwa kuna zamar mana a gida bamu taba yi muku gori ba?" Yace "eh din, amma dai bamu je ranar da aka kaiki munyi bake bake mun hana Zayed zuwa gurinki ba" tace "to ai mu bamu muka hana ka zuwa ba. In baka sani ba ka sani, da Allah da annabi ta roke mu muka zauna ai, haka kawai ni an raba ni da mijina an zo an kawo ni cikin hayaniya an saka min ciwon kai" sun jima suna bugawa da Hafsat, daga karshe tayi zuciya ta tashi ta tafi daki. Ya juyo kan Amina da take ta dariya yace "ke kuma waye ya baki ikon saka kayan da ba naki ba?" Ta kalli kayan jikinta ta kalleshi tace "Allah yaso ma kayan 'yar'uwata ne ba kayan wani ba" yace "ni kuma kayan matata ne, sai ki gaya min waye yafi kusanci da ita" tace "to ai miji da mata suna iya rabuwa, dan'uwa kuwa har bada naka ne" yace "ba dai wannan miji da matar ba" tace "shi yasa naga ka tafi ka barta jiya, sai mu din dai 'yan'uwan nata mu muka zauna tare da ita" yace "sai kuma gashi na dawo yau kuma nace kowa yasan nayi, I need to be with my wife, alone" ta mike itama a fusace tace "in kaga na sake dawowa gidan nan sai kunje har gida kun bani hakuri" ina jinsa yana dariya kasa kasa, kafin ta karasa kofar shiga part dina sai ga hafsat nan ta fito musu da jakankunan su ta mikawa Amina tata tace "muje, gobe ma rana ce ai" har sunje bakin kofa Hafsat ta juyo tace "kuma ka sani, kamar a kunnen Zayed, sai na gaya masa ka koreni daga gidan ka" ya bita yana "haba babbar yaya matar babban yaya, ni na isa in kore ki" ya bisu kamar mai basu hakuri, suna fita ya jawo kofar yayi locking yana dariya kasa kasa.
Har lokacin ban dago kaina ba, jinsa nayi shiru na dan gado kadan sai muka hada ido, nayi sauri na mayar da kaina kasa. Dariya yayi sosai sannan ya karaso inda nake zaune, ya zauna a kusa dani ya dan kwantar da kansa a kafada ta, gashin kansa yana gogar side din fuskata, ya kamo hannuna ya rike yana wasa da zobe na yace "Am sorry love, please forgive me, na bar zuciyata tayi controlling dina na daga miki murya a cikin mutane, sannan nazo na tafi na barki ke kadai a first night din mu. I don't know what came over me wai har ni ne na saka miki gun a hannunki. Wannan shi ya saka na kasa dawowa mu hada ido dake tun jiya, I am so ashame if myself. I don't know what to do with my temper" kasa ce masa komai nayi saboda ni basan ni ya kamat in bashi hakuri bashi ba, ni ce nayi masa laifi, duk abinda yayi yayi ne saboda ransa ya baci, kuma nice na bata masa ran. Jin bance komai ba sai ya sauko daga kan kujerar ya durkusa a gaba na ya dora fuskarsa akan cinyata yace "nayi kneel down, in still baki hakura ba kuma zan yi frog jump" nayi murmushi a raina nace "this is my sultan" na dora hannuna a hankali akan gashinsa kamar mai shirin taba wuta, a hankali na fara shafawa, it feels very soft, softer than I imaging. Ina jinsa ya sauke ajjiyar zuciya tare da kara pressing kansa a hannuna. Na fara magana nima a hankali "ni ba kayi min komai ba ballantana har ka nemi yafiya ta, nice nayi maka laifi, nice nayi keeping secret from you, duk da cewa kai baka taba boye min komai akan ka ba, u have the right to be angry at me, am sorry" ya dago kansa yana kallon fuskata yace "we are even then" ya mayar da kansa ya kwantar, na dan ture shi nace "it is not over though, ina kaje? A ina ka kwana ka wuni ka barni da tunanin halin da kake ciki, babu inda Amir bai duba ba a gidan nan baka nan" yana dariya yace "shi Amir din ne yace miki ya duba ko'ina? The fool. Ina part dinsa fa, ina guest room dinsa" nima dariyar nayi, sai da muka gama dariyar mu sannan nace "you really need a bath" ya langwabe kai "no, I need food first, then a bath and then you"
Maimoon is now on wattpad, follow me at @MamanMaimoon
Episode Seventy One : The Honeymoon
Hmmm let's talk about something kafin mu ziyarci honeymooners. Abinda nake so inyi magana akai shine auren dole. Dan Allah iyaye mu kula mu rage yiwa 'ya'yanmu auren dole. Ni 100% ina goyon bayan auren soyayya gaskiya. Saboda soyayya ita take kawo sacrifice, forgiveness, juriya da kuma jajircewa a cikin relationship. Idan da akwai soyayya babu abinda mutum ba zai iya yiwa partner din shi ba. Idan kuwa babu soyayya to dama kiris ake jira yanzu zakaji an fara rigima. Soyayyar dake tsakanin Sultan da Moon ita ce ta saka duk abinda ya wakana ranar kawo amarya ya zamo ba komai ba. I cikin kwana daya sun manta da komai, babu tuhuma babu gori, amma imaging auren babu soyayya a ciki, mai kuke tunanin zai faru?
Na danyi shiru ina kallonsa ina lissafin anya kuwa ina da sauran abinci a gidan nan? Dan duk warmers din abincin an mayar dasu cikin gida. Dabara ce ta fado min a raina, na dan bata rai nace "aren't you forgetting something?" Yace "No" nace "kara tunawa dai" ya danyi shiru har yana sosa kansa alamar tunani sannan ya sake cewa "ni babu abinda na manta" na marairaice fuska nace "Kaza" ya maimaita "kaza?" Nace "yes now, ba ango yana shigowa da kaza ya kawowa amarya ba?" shima ya marairaice yace "please don't tell me yanzu sai na fita siyan kaza" nace "sosai ma" ya harde kafafuwansa yana kallona ni kuma na dan bata rai ina kada kafa irin lallai sai anyi min abinda nake so, dariya naji ya dan yi sannan yace "just tell me babu abinci a gidan inje in siyo, ba sai kin wayance da zancen kaza ba, I know u can't cook, but what you are forgetting is that, I can" ya mike tsaye ya miko min hannunsa yace "zo muje muyi girkin tare" babu musu na kama hannun na mike muka tafi kitchen, muna zuwa ya daukeni chalak ya dora akan worktop din kitchen din yace "sit here and watch" sai kuma ya tsaya yana tunani, ya bude fridge ya juyo yana kallona yace "kaza kika ce kina so ko? To kin samu, kazar amarcinki bata siyarwa bace ba, ni zan gasa miki da kaina" ni dai kallonsa kawai nake yi naga ya fito da kaji manya guda biyu, ya wanke su yazo ya hada spices sannan ya shafe su dashi, ya ajiye su a gefe, ya dawo ya dauko attaruhu da albasa ya wanke ya miko min yace "yanka min wadannan kanana kanana" nace "with pleasure" na dauka na fara yayyankawa. Ya kunna gas ya dora ruwa kadan, ya zuba gishiri da mai, yana tafasa ya zuba taliya. Sannan ya dauko kajin ya sakasu a griller ya kunna yaya setting time. Har lokacin yankan attaruhu nake yi, ya tsaya yana kallona, nayi sauri na karasa na mika masa. Nan da nan ya hada sauce, yayi draining taliyar, ni kam ina zaune ina ta zuba masa surutu, ina bashi labarin bakin da suka yi ta zuwa yau. Kafin ya gama tuni kajin sun fara kamshi, na sauko ina leka cikin griller din yace da sauri "karki taba, zaki kone" a raina nace 'ko baka fada bama ba tabawa zanyi ba' danni babban dalilin da yasa bana son kirki shine tsoron kar in kone. Kayan da ya bata na hada na wanke na mayar dasu inda suke, sannan na hada abincin daya gama na kai dining, shi kuma ya biyo bayana da drinks, tare muka shirya dining din sannan yace "zo mu zagaya gidan kafin kajin su karasa" tun daga palo muka fara, muka shiga part dina sannan muka shiga nasa, daga palon sa muka shiga wata kofa zuwa wani dan karamin palo da ya ke kira da coffee room, yace anan zai rinka saukar bakinsa da baya so su shigar masa cikin gida, palon yana da kofa zuwa waje, ta nan muka bi muka fita waje muka zagaya boy's quarters, guda biyu ne, na mata dana maza, amma babu kowa a ciki tunda bamu dauki 'yan aiki ba tukunna. Muka zagayo ta gaban gidan sannan muka koma ta cikin kitchen. Muna zuwa muka tarar kajin mu sun karasa, ya saka hand gloves ya bude griller ya dauko su ya yayyanka kanana akan plate, sannan ya miko min yace "ga kazar ki nan, amarya" ina dariya na karba nace "thank you ango, it looks delicious".
Tare muka ci abincin, tare kuma muka ci kazar, ina ta zuba santi yana yi min dariya, sanda na tashi daga kan kujerar ji nayi cikina yayi min nauyi saboda koshin da nayi, shi kam sai dariyar mugunta yake yi min. Ji nayi ya daina dariyar ya zagayo ta gaba na yana kallona "ko ba zaki iya tafiya ba sai na dauke ki ne?" Nayi sauri na wayance da tattara kayan da muka bata. Ya karaso ya ruko kuguna ta baya ya hada ni da jikinsa, ya dora fuskarsa a wuyana yana goga min sajensa, tsigar jikina naji ta tashi, nayi kokarin matsawa amma ya hana ni, na lumshe ido na ina jin jikina yana amsawa, a hankali nace "Sultan" a daidai kunne na yace "uhmm" nace "zan kwashe kaya fa" yace "uhum" riga ta ya daga sa zura hannunsa yana shafa cikina, nayi sauri na rike hannun, nace "Sultan" ya sake cewa "uhmm" nace "cewa fa kayi food first, then bath and then....." Yace "then what?" Na hadiye yawu da kyar nace "then sleep" dariya yayi irin ta cikin kirjin nan sannan ya juyo dani yana kallon fuskata yace "haka nace miki?" Na gyada kaina, ya kawo fuskarsa dai dai tawa, nayi sauri na rufe idona inajin bugun zuciya ta har cikin kunnena, idanuwan dana rufe yayi kissing sannan naji ya dauke ni ya fara tafiya dani, na kasa bude idona na kwantar da kaina a kirjinsa, ina ji ya bude kofa ya shiga wani guri, na dan bude idona na ganmu a palonsa, na sake rufe idona nace "Sultan" yace "uhmm" nace "dakina fa zanje" bai ce komai ba sai da ya kaini dakinsa ya kwantar dani akan gado, nayi kokarin tashi ya mayar dani baya da jikinsa, fuskarsa babu dariya, kamar zanyi kuka nace "Sultan baka yi wankan ba fa. Kuma nima zanyi wanka. Kabar ni inje dakina please" ya dan daga ni kadan, ina murna sai naji hannunsa a baya na, ban ankara ba naji fitar zip dina, nayi sauri na rike rigar ina kara zaro ido, sai a lokacin yayi murmushi ya dan dungure min kai yace "matsoraciya, ji idonta" daga haka ya mirgina ya sauka daga kan gadon, na samu na mayar da zip dina da sauri na mike na sauko ina rarraba ido, nayi hanyar kofa, ya riga ni zuwa ya murda key ya zare, na marairaice masa "sultan dakina zanje inyi wanka fa, bai ce min komai ba ya fara cire kayansa yana yi min murmushin mugunta, yace "tare zamuyi wankan anan" na kankame jikina kamar mai boye wani abu na kara zaro ido ina girgiza kaina nace "please no" yace "OK, to shiga ki fara yi in kin fito sai in shiga" da sauri nace "to" har na kai kofar toilet din sai kuma na juyo ina kallonsa, murmushin fuskarsa na kalla na fahimci abinda yake nufi, so yake in shiga ya biyo bayana, na juyo nace "no, ka fara shiga in ka fito sai in shiga" dariya yayi sosai yace "OK, if you say so" daga haka ya shige, na zauna akan kujera ina karewa dakin kallo, gadon round ne, dama ya gaya min round bed yake so, amma fa katon gaske ne, komai na dakin ash color ne hakan ya saka dakin yayi haske sosai. Na jima ina zaune ina wasa da zoben hannuna sai naji fitowar sultan, ban dago kaina ba balle in kalle shi, yayi gyaran murya amma maimakon in kalle shi sai nasa hannu na na rufe fuskata, sai da na dan leko ta tsakanin 'yan yatsuna na ganshi da bathrobe a jikinsa yana goge gashinsa da towel, na tashi a hankali nayi hanyar bandakin, ba tare daya kalleni ba yace "kiyi alwala kafin ki fito" bance komai ba na shige. Har na gama wankan jikina rawa yake yi, sosai nake jin tsoron sultan har cikin raina, na shiga uku ni maimunatu yau na kawo kaina, na gama wankan na duba drawer din towel naga duk sai kanana, babu bathrobe kuma. Na tsaya a bakin kofa na rasa inda zan saka kaina, gashi kayan da na cire riga da skirt ne, na dauko wani towel da naga yana da dan girma na daura sai naga iyakacin saman cinyata ya tsaya, sai dabara ta zo min, na daura daya a kugu na na samu daya kuma na daura a kirji, sannan na dauko wani na lullube kaina zuwa kafada ta dashi. Na bude kofar a hankali na fara lekawa, yana zaune akan kujera da waya a hannunsa, ya saka doguwar jallabiya, gaba daya kamshin dakin ya chanza daga na freshner zuwa na turaren sa, ina fitowa ya juyo yana kallona, dariya ce ta kubuce masa ganin yadda na chukurkude a cikin towels, yace "lallai kina da aiki, don't worry, I will remove every trace of kunya yau" naji wani sabon tsoro ya kuma shigata, cikin wayar murya nace "dan Allah sultan ka bude min kofa in tafi dakina, kaga bani da kayan sawa anan" ya nuna min kan gado yace "na dauko miki ai, ga phones dinki nan ma na taho miki dasu" nace "to mai na da zan shafa yana can" yace "zaki iya shafa nawa" nace "nawa special ne" yace "nima nawa haka" na tsaya kawai ina kallon shi yace "don't worry, ki shiryawarki, ba zan taba ki ba nayi alwala kuma bana son in sake taba ruwa, sai anjima. Am just going to watch you" na harare shi kamar zanyi kuka na debi kayan daya ajiye min akan gado, naga doguwar riga ce da hijab, babu underwears kuma nasan yana sane, na dauka na shiga closet dinsa, na samu mai na shafa, na fesa turarensa na saka kayan daya dauko min na debo towels din na fito na tarar dashi yana sallah, ya shimfida min sallaya a bayan sa, sai da na shiga toilet nayi hanging towels din sannan na dawo na zauna a kan sallayar na jira shi ya idar sannan yace min in tashi muyi tare, na tashi muka gabatar da raka'a biyu, bayan mun idar ya jima yana jero mana adduoi akan mu ni da shi, da 'ya'yan da zamu samu, ya koma yayi wa iyayen mu baki daya, hatta mahaifiyarsa sai da yayi mata addu'ar fatan alkhairi duniya da lahira, duk addu'ar da yayi ina amsawa da Ameen. Muka gama muka shafa a tare. Ya juyo yana kallona, na sunkuyar da kaina kasa, ya matso kusa dani na kankame hijab dina, ya danyi dariya sai naji ya dora hannunsa akaina yace "ALLAHUMMA INNI AS'ALUKA MIN KHAIRIHA WA KHAIRI MA JABALTUHA ALAIHI, WA AUZUBIKA MIN SHARRI HA WA SHARRI MA JABALTUHA ALAIHI"
Ni na riga shi tashi na dauke sallayar, shima ya tashi na dauke tashi. Na tsaya ina kallonsa, nace "Sultan dan Allah ka bude min kofa, Allah zan dawo, kayan bacci na zan dauko, kaga bazan iya kwanciya da rigar nan ba" ya taso daga kan gadon ya fara tahowa inda nake tsaye, ni kuma na fara ja da baya ina kara kankame hijab din jikina, idona duk ya ciko da kwallah, bai ce min komai ba har sai da na tarar da bango ya saka hannayensa a bith sides dina yadda bani da hanyar guduwa sannan ya fara magana "me zakiyi da sleeping wear din?" Cikin rawar murya nace "saka wa zanyi in kwanta" yana kallon fuskata yace "you don't need to wear anything tonight" nan take hawaye ya fara fito min nace "ni ba zan iya kwanciya babu kaya ba" yace "don't worry, I will cover you, with my body" kuka na fara yi sosai harda sheshsheka, nasan na shiga hannu, I have no way out, no escape, amma ni ban shirya ba, tsoro nake ji. Babu alamar sassauci a fuskar sultan, abinda nake karantawa a idonsa shine yake kara tsorata ni. 'Yar dariya yayi yace "kuka kuma? Tun yanzu? Me kike wa kukan wai? I did not even kiss you fa" ya dora goshinsa akan nawa yace "me kike wa kuka?" Nace cikin muryar kuka "tsoro nake ji" yace "tsoron me?" Da hannu na nuna shi, ya kara matseni a jikin bangon yace "I promise you I will be gentle, It won't hurt you that much" wani kukan na kara saki, yace "what now? Me kike so kuma?" Nace "ni ka hakura kawai" yayi chuckling yace "impossible" da haka ya dora lips dinsa akan nawa, very lightly ya fara kissing dina, sam ba irin na America bane, this kiss is not pierce but gentle, there is no anger in it, no sadness, just love, lots and lots of love. Amma kuma just like na American, it took away all my senses. Yana raba lips dinsa da nawa na nemi hijab dina na rasa, ya saka hannunsa ya shafa kitson kaina yace "I like this, I like you, all of you" ya mayar da lips din mu ya hade guri daya, next thing da naji shine karar zip din riga ta, a take na dawo hankali na na rike rigar idona kamar zai fado kasa, babu komai a cikin rigar, ya cigaba da zame rigar daga jikina, cikin kuka nace "Sultan please, just switch off the light first" cikin muryar da ba tasa ba yace "No, i want to see you" na mayar da ido na na runtse da karfi yayin da rigar tabi jikina ta sauka kasa, ban kuma bude idona ba naji ya dauke ni chak, ya danyi tafiya kadan sannan naji ya ajiye ni kan gado.
Kamar yadda rannan yayi min alkawarin zanyi kuka haka nayi kukan kuwa, dan kaf 'yan gidan mu babu wanda ban kira yazo ya cece ni ba, tun daga kan Daddy har zuwa su Asma'u cook din mu, amma babu wanda yazo. Ranar sai da nayi nadama ina ma dai banyi aure ba inyi zamana a haka. Amma kuma kamar yadda yayi alkawarin zai yi min dariya baiyi dariyar ba, dan taya ni kukan yayi muka hadu muka yi ta kukan mu tare, amma kuma kukan bai hana shi abinda yayi niyya ba. Na durzu iya durzuwa, shi kuma yasha duka da yakushi da cizo amma ko a jikinsa. Finally sanda ya rabu dani babu karfi ko kadan a tare dani, shima kuma daga dukkan alamu hakan take, dan tunda ya kwanta gefena in banda sauke numfashi babu abinda yake yi, sai da yaga ina karkarwar sanyi sannan ya jawo bargo ya lullube mu, ya dan jawo ni ya dora ni jikinsa, nayi kara saboda zafin da naji, na kankameni yace "shshshsh, am sorry I couldn't keep my promise, my body took control of me, am sorry" ni kuwa ko sauraronsa bana yi, dama ashe I Love You din ta karya ce, tunda har zai iya rufe idonsa ya gana min wannan azabar, babu wani kuma dadin bakin da wani sorry din da zaice min. A hankali na fara rufe idona ina sauke ajjiyar zuciya saboda kukan da nasha, ina kuma jin dadin dumin bare skin dinsa, a haka bacci ya dauke ni. Cikin baccin naji ya zame jikinsa ya kwantar dani, sai naji kuma kwanciyar babu dadi, amma bacci ne mai nauyi a kaina dan haka naci gaba da bacci na. Sanyi naji alamar an yaye bargon, na bude ido na ganshi a tsaye da gajeran wando a jikin sa, jikinsa da ruwa alamar wanka yayi, nayi kokarin jawo bargon saboda yadda naga yana kallona, ya rike hannuna yace "babu abinda zan miki fa, wanka zanyi miki" wai wanka sai kace wata jaririya, yana dagani na ji wata azaba har cikin kaina, a tare muka kalli kan gadon, ai kuwa ina gani na kwalla kara, yayi sauri ya toshe min bakina ya tafi dani toilet, kuka nake yi sosai ina cewa "na shiga uku na lalace, wayyo Allah na wayyo Mommy" ashe wani kukan yana gaba, dan yana saka ni a cikin tub na mike na kankame shi sauran kadan in jawo shi ciki shima, zafi naji sosai dan jikina har karkarwa yake yi, kukan ma babu dan hawayen sun kare, da nasan haka auren yake da ko ana bina ana jawo nine da bazan yi ba. Da karfi Sultan ya danna ni cikin ruwan, shima kamar zaiyi kukan sai sannu yake yi min. A hankali na fara jin dadin ruwan na koma na kwanta, sultan har da gyara min headrest, na rufe idona a take bacci ya dauke ni. Bansan tsahon lokacin dana dauka ina baccin ba kawai naji sultan yayi draining ruwan da nake ciki, ya kunna wani, sannan ya ce min "ki tashi kiyi wanka in kaiki daki ki cigaba da baccin, assuba ta kusa" na dan bata rai nace "ni ka barni anan, wanne wanka kuma zanyi?" Yace "kin san wanne wankan ai nake nufi, ki tashi in ba so kike inyi miki ba" na mike zaune, ganin yana kallona yasa nayi saurin juya bayana nace "to ka fita mana ba sai inyi ba" ya danyi dariya ya fita. Ga mamaki na sai naji na danji dadin ciwon, ya ragu ba laifi tunda dana gama wankan da kaina na fito, ina goge jikina sultan ya kuma shigowa, nayi sauri na rufe jikina duk da nasan babu abinda bai haddace ba, bai kula ni ba ya karaso ya karasa goge min jikin ya zura min bathrobe ya kuma daukana ya fita dani, muna zuwa naga ya chanza komai na kan gadon kamar ba'a yi komai ba, ya kwanar dani ya lulluba min bargo sannan yaje ya kashe wutar dakin ya dawo ya hau shima, ya jawo ni jikinsa banyi musu ba na kwanta akan kirjinsa ina jin dadin kamshin. A kunne na yace min "sleep tight, Love"
Episode Seventy Two : My Everything
A hankali na bude ido na ina ji a jiki na kamar assuba tayi ko kuma ma ta wuce. Dakin naga da duhu kamar cikin dare amma jikina yana bani assuba ce. Abinda ya faru da daddare ne ya fara dawo min a raina, sai a lokacin na lura cewa a jikin mutun nake a kwance. Wata muguwar kunya naji ta kamani kamar in tsaga gadon in shige cikinsa, gani nake kamar a mafarki amma kuma nasan ba mafarkin bane. Na daga jikina a hankali da niyyar sauka daga jikinsa, wata 'yar karamar kara na saki na koma na kwanta, gaba daya kafafuwana sunyi tsami, jikina gaba daya ciwo yake yi, na sake gwada kokarin tashi amma shima sai wani karin ciwon ma kamar dadamin ake yi. Na koma na kwanta ina kwalla silently. Motsin Sultan naji alamar ya farka amma na kasa dago kaina saboda bana jin zan iya hada ido dashi yanzu, ya sa hannu a hankali yana kokarin dago fuskata amma naki yarda, ya rabu dani yace "menene kuma? Sai kin kara wa kanki wani ciwon da kukan nan ko?" Banbashi amsa ba naci gaba da kukana, kokarin daga ni daga jikinsa ya fara yi, ai kuwa na saka masa kara, ya cika ni yace "ciwon ne dai?" Na gyada kaina, ya fara shafa bayana a hankali yana noticing temperature dina data fara hawa, yace "am sorry love, bara muyi sallah sai muga ya za'ayi da ciwon nan" cikin kuka nace "ni ka kaini gida gurin Mommy" da sauri yace "what? So kike Mommy ta tsire ni a kasuwa? In na kaiki gida a haka ai kamar na nuna am not responsible. Ki bari inyi sallah sai in duba ciwon in gani, in naga yana bukatar doctor da akwai doctor din gidan nan sai inyi masa magana ya samo mana gynecologist mace sai tazo ta dubaki" na makale kafada, yayi ajjiyar zuciya yace "OK, to ke ki rubutamin magungunan da kike ganin zasu yi miki amfani sai inje in siyo miki" na sake makale kafada, yace "to fada min me kike so, banda zuwa gida" nace "ni dai ka kira min Hafsat" yace "kinsan dai Hafsat tayi fushi ko na kirata ba zata dauka ba" nace "ni ka bani wayata, in na kira ta zata dauka" yace "to dagani in dauko miki wayar" na sake makale kafada, yayi 'yar dariya yace "wannan dai ba ciwon bane kadai har da shagwaba ko?" Nayi shiru bance komai ba yace "bara inyi maganin shagwabar" juyi daya yayi ya mayar dani kasa, na bude baki zanyi kara ya rufe min bakin da nasa, sai da ya tsotse yawun baccin tas sannan ya sakeni, still yana kaina amma ya rage nauyin sa da hannayensa, nace "banyi brush ba fa" yace "nima haka" daga haka ya mike ya shiga toilet, ya fito da alwala, sai da yayi sallah sannan ya dawo inda still nake kwance ba tare daya ce min komai ba ya dauke ni ya kai toilet, da gaske ciwon nake ji ba wai shagwaba bace, dan kafafuwana jinsu nake kamar lagwani, da nayi alwalar ya dawo dani daki ya sakamin doguwar riga ta da hijab dina ya zaunar dani akan sallaya nayi sallah, ina idarwa ya shigo da tea a hannunsa ya zauna ya fara bani, naki sha sai da yace min inna shanye zai kira Hafsat, na sha kamar rabi nace na koshi, kan gado ya sake mayar dani ya lullubeni. Ya dauko min wayata ya dawo kusa dani ya kwanta yace "to kira Hafsan, tunda kince ita kike so" na duba time naga 6:30, na kira number din Hafsat, ringing biyu ta dauka, sai kuma na rasa me zance mata, tace "I know u will call me dama, check your messages, na bar miki sako" daga nan ta kashe. Sultan yace "me tace?" Na gaya masa, ina duba wa kuwa naga message daga Hafsat 'you once asked me what it feels like, yanzu nasan kin sani. Was Sultan gentle? If he isn't please knock his big head for me. I left something a bedside drawer dinki and I also left you farfesu a cikin fridge, for you alone, kar ki bashi ko loma daya' ina gama karantawa na tattaro dan sauran karfin daya rage min na rankwashi Sultan aka, ya rike gurin yace "ouch, me nayi kuma?" na nuna masa message din Hafsat nace "sako ne inji Hafsat" ya shagwabe fuska "was I not gentle?" Nace "you weren't" yace "to ai ba laifi na bane ni kadai, why do you have to be so damn good. I always thought it will be good but did not expect it to be this good" nace "so it is my fault kenan ko?" Yayi dariya bai amsa ba ya mike yace "let me get sakon nata". Few minutes later ya dawo da leda a hannunsa, ya zauna a gaban gadon ya bude, magunguna ne a ciki, mostly pain relievers ne, sai wani farin gari a leda da instruction din a ruwa za'a zuba a shiga ciki, sai kuma wani paste shi kuma na shafawa ne. Yana gama dubawa ya dauki na ruwan ya tafi dashi toilet, nasan ruwa zai hada min dan haka duk na tsorata, nasan zafin dana ji a ruwan jiya, yana dawowa na saka masa kukan ni bana son shiga ruwa, da kyar muka je toilet din, amma shiga ruwan ya gagara, a karshe dai sai tare muka shiga, kayan kuwa sai a cikin ruwan aka cire su. Bansan me yake faruwa ba sai da na gama jin zafin ruwan sannan na lura da yadda muke, ai kuwa nace sai ya fita amma yaki, a dole muka gama zaman cikin ruwan tare muka fito, muna fito wa na rufe ido na wai bazan kalle shi ba tunda babu kaya a jikinsa, yayi ta tsokanata amma still naki bude idon, muna dawowa daki ya dauko na shafawar wai sai ya shafa min, na fara kokawa ya saka hannu daya ya rike ni kuma ya shafa min din. Na kwanta ina kumbure2 ya fita, har na fara bacci sai gashi ya dawo da bowl a hannunsa da kuma kwalin fresh milk, ya tashe ni zaune yace sai naci, ina ta shagwabar ni bacci nake ji amma haka ya matsamin sai da muka ci tare, muna gamawa ya dauko min magungunan wajan Hafsat ya bani nasha sannan na koma na kwanta, ban jima da kwanciya ba naji shi ya kashe fitilar dakin ya hawo gadon shima, ya jawo ni jikinsa kamar zai tsaga kirjinsa ya sakani ciki, nayi 'yar kara, yayi dariya yace "ya jikin?" Nace "da sauki" yace "Maimunatu" nayi mamaki saboda yau ne rana ta farko daya kira ni da wannan sunan, nace "Na'am" yace "thank you, I really mean thank you, for yesterday, for everything, bansan me zance miki, bansan sunan da zan kira ki dashi ba, I will continue calling you my love, saboda you are the love of my life, amma ki sani ba wannan ne kadai matsayinki ba, you are my everything, I was nothing kafin in hadu dake kuma I will be nothing without you" bance komai ba amma ina jin dadin maganganunsa har cikin raina, ina kara jin sansa yana shiga har cikin bargo na, he is mine, and I am his, forever and ever.
Ni na sake riga shi tashi wannan karon ma, na farka naga still dakin duhu, wato shi wannan dakin na sultan koda yaushe a dare yake kenan, sai mutum yayi ta bacci bai san me duniya take ciki ba. Na tashi zaune, ga mamaki na sai naji babu ciwon sam, sai dan ciwon jiki kadan, na kunna bedside lamp, na duba agogon wayata, 1:15, oh my God, nasan mutane sunyi ta zuwa suna ganin gidan a rufe, na juya na kalli sultan da yake bacci a gefe na, sai naji na kasa tashin sa, he looks so handsome, hasken lamp din yana reflecting a golden skin dinsa, na koma na kwanta a side dina ina kallonsa, I have never see him this peaceful before, na tuna maganar hausawa da ake cewa wai angwaye suna kwallin goshi, to ko dai da gaske ne? Na kai dubana kan kirjinsa, Ya dan yaye bargon ya bar kirjinsa a waje, gashin da yake kwance a kirjinsa yafi na fuskarsa kyau da sheki kamar yadda fatar gurin tafi da fuskarsa haske, a hankali na gada hannuna, na sake kallon fuskarsa naga baccin yake yi, I couldn't stop myself, a hankali na sauke hannuna akan gashin na fara shafawa ina jin laushinsa a hannuna, I was so consumed in doing what I was doing kawai naji maganarsa "hey woman, you already had me, if you want more all you have to do is ask" nayi sauri na dauke hannuna na rufe fuskata dashi, ya mirgino ya hade fuskarmu guri daya yace murya can kasa "do you want more?" Na girgiza kaina da sauri, yace "but I do want more" nace "ni fa tashinka zanyi, lokacin sallar azahar ya kusa, kuma kaga ko bude kofa bamuyi ba kar mutane su yi ta zuwa gida a rufe" yace "so what? Duk wanda bai zo jiya ba yayi wa kansa, an gama ganin gidan amarya. Let's not open the door forever, let's not get out of this bed forever" nayi dariya na dan dake shi a kafada nayi kokarin tashi ya sake dawo dani baya nace "Sultan, ka bar ni inje dakina in saka kaya, inje in samar mana abinda za muci kuma, we can't stay here forever" ya saka fuskarsa a wuyana yace "sai kace girkin ta iya da gaske. Za'a kawo abinci, za'ake kawo wa daga cikin gida har nan da seven days, kafin nan sai mu nemi cook. Yau bana son ko tashi inga kinyi, I want to treat you like the queen you are, komai kike so ni zan yi miki, duk abinda kike so shi za'ayi".
Da kyar na samu ya dauko min kayana a dakina na saka, daga nan ya tafi masallachi sallah ni kuma nayi sallah ta anan, miracle maganin Hafsat yayi min amfani sosai dan bama na tuna wa da wani ciwo sai in na yi motsi da sauri. Man sa na shafa na saka tunarensa, banyi kwalliya ba, na zauna akan kujera ina duba messages din wayata, yawanci sakonnin taya murna ne daga mutanen da basu samu damar zuwa bikin ba, anan naga sakon mahdi, yace min ya cigaba da karatunsa bai dawo Nigeria ba, na rufe WhatsApp kenan naga sakon Amira ya shigo, na koma na bude "Moon dan Allah ina so muyi magana, can I come to your house please?" Ban yi mata reply ba Sultan ya shigo, tray din abinci ne a hannunsa amma idonsa yana kaina, na karaso na karba na ajiye, bai ce komai ba ya sake fita ya dawo da still da wani abincin, na kuma karba nace "Sultan wannan abincin ya zamuyi dashi?" Yace "I don't know which one you will like, shi yasa na debo kowanne. Sun kawo abincin yana dining. Da akwai Baba Gaji Yaya ta turo ta gurinki, I told her ba zaki samu ganinta yanzu ba amma ta zauna duk wanda yazo ta raka shi yaga gida amma ta gaya musu amarya is not available" nace "ayyah, da ka barni naje baka san menene sakon Yayan ba" yace "ba zai wuce zancen masu aiki ba" zan kuma yin magana ya jawo nikan cinyarsa yace "me zaki ci?" Mun ci abincin sosai daga ni har shi duk ashe yunwa muke ji, sam ya hanai fita da kayan shi ya dauka ya fita dasu, kafin ya dawo na gyara gurin na kara freshner a dakin, yazo ya jani muka koma gado yace "ya ciwon? In duba in gani? Nayi sauri na hade kafafuwana nace "bai warke ba ai" yace "OK, kin san me za'ayi masa ya warke da wuri? Wani za'a kuma yi, nan da nan zakiga ya warke" na fara matsawa baya ina zaro ido "please Sultan, wallahi mutuwa zanyi, dan Allah karka tabani" dariya yayi sosai yace "harda mutuwa? Am just kidding, amma babu wani mutuwa da zaki yi, an gama mai zafin ai" na sake matsawa baya, ya jawo ni yace "trust me bazan miki wannan ba, I just want to feel your warmth and smell your scent" na dan saki jikina kadan amma kuma ba abinda ya fada kadai yake yi ba, sai da naga yana neman wuce gona da iri sannan na saka masa kuka, ya sakeni ya gyara min rigata sannan ya gyara min kwanciya, har na dauka yayi bacci sai naji yace "tell me about him" duk da bai fada ba nasan wa yake nufi, kuma nasan dama dole zamuyi maganar amma sai naji bakina yayi min nauyi na kasa magana, jin nayi shiru ya sake magana "I just want to know, shi kadai ne ko kuma akwai wani daban da ban sani ba" na girgiza kaina nace "shi kadai ne, sunan sa Ibrahim, he was a copper a sec sch din mu when I was in SS2, I was 14 years then" daga nan na bashi labarin duk rayuwar mu da Ibrahim him, da yadda muka rabu, da irin zaman jiransa dana zauna yi kafin haduwar mu shi (sultan), na bashi labarin har ranar da muka kuma haduwa da Ibrahim da labarin daya bani na rayuwar da yayi bayan rabuwar mu da irin abubuwan da Amira ta kulla mana, ban boye masa komai ba har wayar da mukayi dashi a phone din Amina da duk bayanin dana yi masa ya kuma nuna ya gamsu, na karasa da cewa "bansan me yasa ya aikata abinda ya aikata ranar nan ba. Am sorry na boye maka duk wanan maganar, at first I never thought zamu sake haduwa dan haka nake ganin there is no point in telling you, daga baya kuma bayan mun hadu dashi na kasa gaya maka ne saboda bana son in bata maka rai". Har na gama maganar baice komai ba,har na fara tunanin ko yayi bacci, na kalle shi sai naga yana kallon ceiling, can yace "promise me you will never see or talk to him again, my heart cannot take it" na dago kaina ina kallon cikin idonsa nace "I promise" yayi murmushi yace "thank you" sannan ya jawo fuskata ya hade bakin mu.
Episode Seventy Three : His Father's Son
Washe gari bamuyi missing sallar assuba ba kaman jiya, Sultan ne ya fara tashi, sai da yayi alwala sannan ya tashe ni shi kuma ya fita masjid, ya jima bai dawo ba har nayi sallah na dan taba karatun al'qurani sannan nayi morning azkar dina, ji nayi duk na gaji da kwanciya, I want to do some work, na tashi na gyara dakin na wanke toilet, na dawo palo ina cikin gyarawa ya shigo, ya tsaya yana kallona "wato matar nan kin warke ko? Shine zaki kama aikin da assubar nan ko?" Nace "na gaji da kwanciya ne kawai, I want to do something" ya fara tahowa yana min murmushin mugunta yace "You want to do something? I have got something for you" na ajiye duster din hannuna na fara ja da baya ina jin tsoro har cikin raina dan na warke amma ban manta azabar da nasha ba. Nace "Sultan Allah ban gama warkewa ba, dan Allah kayi hakuri wallahi na daina aikin zan koma in kwanta" ya karaso in da nake yace "really baki warke ba? Can I see?" Nayi saurin girgiza kaina nace "you are not a doctor how will you know if a wound is healed or not?" Yace "am not a doctor but ni mijin doctor ne, dan haka believe me I will know" idonsa kawai na kalla nasan kona roke shi it will be to no avail, jikina har karkarwa yake yi saboda tsoro, me yasa nayi aure ne wai? A kunne na ya rada min "believe me, it will not hurt". And it didn't, at least not as I expected. Yana cikin bacci na zare jikina na tashi, a hankali na lallaba na saka kayana na fice, da sauri na karasa dakina ina shiga nayi locking kofar, finally nazo dakina after two days, da sauri sauri na gyara dakin duk da ba wani datti yayi ba, na shiga toilet na shiga shower ina wanka, at last zanyi wanka without sultan standing and watching. Na fito na zauna na shirya a tsanake cikin atamfa ruwan hoda, nayi 'yar kwalliya kadan na fesa turare na fito. Ina fita palo na tarar da wata tsohuwa a zaune a kan carpet da wadansu 'yammata su biyar daga can bakin kofa, ina fitowa duk suka mike tsaye kansu a kasa, 'yammatan kamar harda tsoro a fuskarsu, sai da na zauna sannan suka durkusa suka fara gaisheni daya bayan daya, na saki fuskata sosai na amsa musu. Babbar matar ce ta matso tace "ranki ya dade, Allah ya taya miki, Allah ya dora ki akan makiyanki duniya da lahira, Allah yaji kan magabata, Allah kuma yasa albarka a zuriya" nace "Ameen" ta cigaba da magana "ranki ya dade ai jiya ma munzo, muna nan har magriba bamu samu ganin ki ba. Dama mai babban daki (yaya) ce ta turo mu, tace tana gaishe ki sosai, kuma tace duk mu shidan nan mu dawo nan gurinki mu zauna muke yi miki hidima. Ni sunana Gaji, tun asalin kakanni na bayi ne a wannan gidan, anan aka haifeni anan na girma nayi aure na hayayyafa, 'ya'yana ma suka yi aure suka haihu duk acikin gidan nan, guda biyu daga cikin 'yammatan nan jikokina ne. Kamar yadda aka kawo 'yammatan nan gurinki yanzu haka aka kaini gurin mai babban daki sanda tana amarya, wannan shi yasa nake daga cikin amintattun bayinta, kuma wannan shi yasa ta zabe ni akan in zo in zauna a gurinki, saboda tasan zan rike mata amana. Suma wadannan duka yaran da kika gani zababbu ne dan ni ta saka in zabo mata masu tarbiyya da rikon amana kuma na zabo su. Insha Allah zamu rike ki da amana Allah kema ya baki ikon rike mu da amana." Kawai naji matar ta kwanta min araina, na tambayi yaran duk sunayensu suka fada min, naga duk sunki sakin jikinsu sai na fara yi musu wasa, ba'a jima ba suka fara dariya. Da kaina na tashi na kaisu har bq din mata na nuna musu komai sannan muka dawo tare. Nace "Ku dauke ni a matsayin yayar ku kunji, dama ni bani da kanne mata kunga shikenan na samu, duk abinda kuke so kuyi min magana in dai ina dashi zan baku, abinda bana so shine kazanta, ku kula da tsaftar gidan nan ku kuma kula da tsaftar jikin ku, ku kame kanku banda shiririta. Allah ya bamu ikon zama lafiya". Sunji dadin yadda na karbe su, kuma daga dukkan alamu sunji dadin bq din dai sai murna suke sunzo gurin 'yan gayu. Nan take baba Gaji ta raba mudu kowa aikinsa, jikokinta guda biyu su ta bawa part dina, sauran kuma sauran parts din gidan. Banda part din Sultan. A take suka tashi suka fara aikin su. Ina zaune sai ga abinci daga cikin gida, suka je suka ajiye a dining room sannan suka zo suka gaishe ni, wai hajiya tace ayi min sannu da jiki, na amsa musu, naga suna ta kallon 'yammatana da Baba Gaji da naga ta hade rai. Na tashi na koma part din Sultan na tarar ya tashi yana wanka, na zauna na jira shi ya fito, yana kallona yace "shine kika gudu ko?" Bance komai ba, ya tsaya yana goge jikinsa, ya juyo ya kalleni muka hada ido nayi sauri ya sunkuyar da kaina, yayi dariya yace "ana so ana kaiwa kasuwa. You are welcome to watch" nace "an kawo abinci, nan za'a kawo ko kuma zaka fito dining?" Yana kokarin shiga closet yace "bara kawai in fito, dama zan dan fita" har ya kai bakin kofa kuma ya tsaya ya juyo "bazaki zo ki tayani shiryawa ba?" Na rufe fuskata da hannuna, yayi dariya "wannan kunyar naga har yanzu da akwai saura, zanyi maganin ta ne" ina nan zaune inda ya bar ni har ya sake fitowa, kananan kaya ne a jikinsa yayi stocking rigar ya saka belt, da comb a hannunsa yana taje kansa, na tashi na karasa inda yake na karbi comb din na cigaba da taje masa, nace "ina zaka je?" Yace "orphanage. Yanzu zan dawo. Tunda aka fara bikin nan banje na gansu ba" na gama gyara masa gashin nace "let's go eat then".
Sai bayan ya tafi sannan na dawo palo gurin baba gaji, ina zama tazo ta fara yi min tausa a kafa ta, naji dadin tausar saboda dama kafar ba dadin ta nake ji ba, cikin girmamawa ta fara yi min magana "ranki ya dade ni kam wadannan masu kawo abincin nan ina ma za'a ce musu su daina kawowa? Mu sai mu ringa yi anan" ban amsa mata ba na lumshe ido na inajin dadin tausar. Ta cigaba da magana "Ranki ya dade sai kinyi a hankali sosai da Hajiya. Mutanen da suke waje kullum suna maganar irin yadda take nuna wa karamin sarki soyayya amma mu da muke cikin gidan nan mun san ba haka abin yake ba" na bude ido na nace "waye karamin sarki?" Tace "maigidanki ranki ya dade, haka mai babban daki take ce masa muma kuma duk haka muke ce masa" na koma na kwanta na sake rufe idona, ta cigaba "bata sonsa ko kadan, kema kuma dole nasan kiyayyarsa zata shafe ki. Kar ki yarda da duk wata magana da zata gaya miki musamman akansa, mu mun san komai" maganar ta ta karshe ce ta saka na bude ido na, 'mu munsan komai' na tashi zaune ina kallonta nace "Baba Gaji, kin san mahaifiyar Sultan?" A hankali naga yanayin fuskarta yana komawa alamar tsoro, ta sunkuyar da kanta kasa, na sake magana "baba gaji kince anan gidan aka haife ki, kince kuma kina tare da Yaya tun tana amarya, haka yana nuffin kinsan mai martaba sarki tun haihuwarsa har girman sa har auren sa, hakan yana nufin kinsan haihuwar Sultan, abinda na tambayeki shine; kin san mahaifiyar sultan?" Gani nayi jikinta ya fara rawa, kanta har yanzu yana kasa ta kasa kallona, tace "ki yi min afuwa ranki ya dade, an hana mu yin magana akan ta, an hana mu ko da ambatar sunan tane" cikin mamaki nace "waye ya hanaku maganar ta? Kuma saboda me?" Ta dago ta kalleni tace "mai martaba sarki, marigayi, mahaifin wannan sarkin" wani mamakin na sake yi nace "kina nufin ba wannan sarkin ba, wancan" ta gyada kai, nace "to saboda me?" Ta girgiza kanta tace "Allah masani" nayi shiru ina tunani, Sultan ya taba ce min "no body talk about her, it is as if she didn't exist" na gyara zamana nace "amma baba gaji shi wanda kike magana akansa shekarar sa ashirin da rasuwa, in kin gaya min taya za'a yi yasan kin gaya min?" Ta girgiza kai, tace "ranki ya dade mu bayi ne, muna biyayya ga iyayen gidan mu koda kuwa bayan mutuwar su ne, bama cin amanarsu, bama ha'intarsu" na mike tsaye na fara zagaye a palon sannan na dawo na zauna nace "sanda wancan sarkin yana nan kina a matsayin baiwar sa, bayan ya mutu kika zama baiwar Yaya, yanzu kuma yaya ta bani ke, in dai har zaki yi masa biyayya har bayan ransa to hakan yana nufin zaki yi min biyayya nima. Ina umartarki daki bani labarin duk da kika sani dangane da mahaifin sultan da kuma mahaifiyarsa" ina kallon yadda duk ta rude, na dan dafa kafadarta nace "nayi miki alkawarin duk maganar da mukayi zata tsaya a tsakanin mu".
Sai da ta nutsu ta daidaita numfashinta sannan ta fara magana " ina nan aka haifi mai martaba sarki na yanzu, ina nan kuma aka haifi dukkannin kannensa. Duk a cikin su shine yafi dauko halin mahaifinsa; zafin zuciya, taurin rai da kuma tausayi. Yadda kika ga karamin sarki haka yake, kuma shima kakansa haka yake. An gaya mana cewa wannan shine abinda yasa suke zama sarakuna, dan shi mulki sai mutum yana da karfin jiki dana zuciya, sai mutum yana da zafi kuma yana da sanyi. Sanda ya girma ya zama saurayi mu dai munsan yana kasar waje karatu, duk sanda yayi hutu yazo gidan nan haka zai cika gidan nan da abokanan sa har sai ya koma tukunna, wadansu abokan ma daga makarantar suke biyo shi su zo nan suyi hutun tare su koma. Rannan ya dawo gida tare da abokanan sa da yawa, aka shirya musu party ana ta murna, aka gaya mana cewa ai murnar kammala karatunsa akeyi, muma mukayi ta murna muna taya shi farinciki. Bai dade da dawowa ba sai suka samu sabani da mahaifinsa, rana daya muka neme shi muka rasa a gidan nan, ba karamin tayar da hankali mahaifinsa yayi ba saboda kowa ya san duk cikin 'ya'yansa babu wanda yake so kamarsa. Yaya ta tada hankalinta, kullum ana cikin tara malamai da addu'ar Allah ya bayyana shi. Rannan muna zaune da daddare tare da Yaya kawai sai gashi ya shigo palon, hannunsa rike da hannun wata yarinya, balarabiya. Muka tashi da murna amma sai muka ga yaya sam bata murna sai ma tashin hankali da muka gani a tare da ita, aka aika aka gayawa sarki sai gashi ya taho da kansa, mu dai duk muka fita muka basu guri, basu fi awa daya ba sai gashi ya fito rike da hannunta ya bude motarsa ya shiga ya fice daga gidan. Sai daga baya muka samu labarin ainahin abin da ya faru, yarinya ce yake so balarabiya, ya nemi babansa ya nema masa auren ta amma baban yaki, wannan shine dalilin da yasa ya tsallake yayi tafiyarsa yaje ya nemi auren nata da kansa, aka bashi ita aka daura musu aure sannan ya dauko ta ya taho da ita, a tunaninsa tunda ya riga ya aure ta ai dole uban ya karba. Amma da suka zo maimakon uban ya karba sai ya kara tunzura yana ganin kamar ya nuna masa bai isa dashi ba tunda yayi aure ba da sanin sa ba. Hakan ne yasa shi kuma ya dauki matarsa suka yi tafiyarsu. Ba'a kuma jin labarin sa ba sai bayan shekara daya. Shima wannan karon muna zaune sai gashi ya shigo gidan, hannunsa daya rike da wannan balarabiyar, daya hannun kuma yana rungume da dan jariri. Wato tunda ya kawo musu suruka sunki karba shine yanzu ya kawo musu jika. Ai kuwa wannan karon yaci nasara, dan kallo daya kakan yayi wa jikan ya tattara son duniya ya dora masa. Tun daga nan Khairat ta tare a gidan nan. Yarinya ce nutsatstsiya sosai, tana da hankali da girmama mutane. Farkon zuwanta sam bata iya hausa ba, amma a hankali ta fara koya. Duk gidan nan, 'ya'yan gida da mu bayi, dama wadanda suke shigowa su fita, babu wanda baya son khairat, babu kuma wanda bai san irin son da mijinta yake mata ba dan baya boyewa ko a gaban waye kuwa. Shi kuwa wannan dan jaririn wanda daga baya muka fahimci babansa ya saka masa sunan sa saboda tsananin son da yake masa, sai ya zama an kasa ban bance waye yafi sonsa tsakanin iyayensa da kuma kakansa. Tun yana jariri muka fahimci cewa ba sunan babansa kadai yaci ba harda halayensa, duk duk kiriniyar da babansa yayi yana jariri shima ita yake yi, kamar copy dinsa ne aka ajiye, sai dai yafi kama da mahaifiyarsa. Karamin Sarki yana da shekara biyu a duniya rannan kawai muka tashi babu khairat babu alamunta, babu abinda ta dauka a kayanta, ko danta bata dauka ba, kuma babu wanda yace yaga sanda ta fita. Abinda kuma ya fi bamu mamaki a tafiyar tata shine, babu wanda ya neme ta" nayi sauri na katse ta nace "ban gane me kike nufi babu wanda ya neme taba, mijinta fa wanda kika ce yana yi mata soyayya kamar rai?" Tace "shine abin mamakin Allah ya taimakeki, duk zafin ransa, duk, duk taurin zuciyarsa. Mun dauka zai bita amma ko kofar gida bai je ba. Komawa yayi tamkar wanda aka chanza shi da wani, tamkar ba shi ba gaba daya yayi sanyi duk karfin sa babu. Kamar an zare masa ruhinsa an bar gangar jikin. A rana daya aka saka aka kwashe duk kayanta aka rufe dakinta. A ranar aka taramu aka umarcemu da ko sunan ta kada wanda ya sake ambata a gidan. Bamu tambayi dalili ba kawai dai munyi biyayya. Kwana biyu da tafiyar ta karamin sarki ya galabaita da kukan neman ummin sa da daddyn sa, har zazzabi yayi, ranar da safe ina gurin yaya ina ta faman rarrashin karamin sarki sai ga babansa ya shigo, yana shigowa yaron ya fara zamewa daga hannuna yana kokarin tafiya gurinsa amma abin mamaki ko kallon inda yake bai yi ba, tamkar bai san shi ba, ya shiga ya gaishe da mahaifiyarsa ya juya ya fice, yaron yana ta kiran daddy daddy yana kuka. Tun daga ranar abinda ya cigaba da faruwa kenan, kamar yadda aka goge duk wani abu daya shafi mahaifiyar karamin sarki a gidan nan haka ya zamo tamkar an goge duk wani digo na soyayya tsakanin karamin sarki da mahaifinsa" tasa mayafinta tana goge hawayen idonta, nace "amma hajiya fa, an auro ta lokacin?" Ta girgiza kai tace "ai Hajiya sam basu zauna da mahaifiyar karamin sarki ba, sai bayan da suka rabu da shekara biyu ma sannan aka yi aurenta" ji nayi kaina ya daure, saboda all this while abinda nake tunani shine Hajiya ce ta raba maman sultan da babansa, ita ce kuma ta raba tsakanin su ta saka kiyayya a tsakanin su, things are not always what they seem, na sake tambaya "to daga baya kenan Takawa ya hadu davita har suka fara soyayya suka yi aure?" Tace "Ranki ya dade ai babu soyayya, auren hadi ne, 'yar 'uwarsa ce ai, kakansu daya. Kawai kiransa akayi akace masa an hada shi aure da wance yace to, daga nan akayi auren, anayin auren suka tafi kasar waje tare wai itama zata yi karatu, shekarar su daya suka dawo da yarima Abbas yana karami" na danyi digesting maganar kadan, wanne karatu ne akeyinsa a shekara daya?. Taci gaba da labarin Sultan tace "daga nan sai kakansa ya dauke shi, ya mayar dashi dakinsa, hatta kayan sakawarsa a can suke, gata da soyayya sosai ya nuna masa, a haka har yaron ya saki jikinsa ya daina kuka, amma kuma duk da kankantarsa bai manta da mahaifinsa ba, dan duk inda ya ganshi zai tafi gurinsa da gudu, amma ko kallon inda yake baya yi, in yazo ya rike kafarsa sai ya ture shi ya fadi yayi tafiyarsa. A gurin sarkin lokacin kuma babu tamkar karamin sarki, dan har bacci akan gado daya suke yi, ko taba shi babu wanda ya isa yayi hatta su Yaya da Nani, abin ya dami yaya kwarai amma duk sanda tayi magana to ranar kuwa zata ga bacin rai. A haka har yaron ya shekara goma, ya sangarce sosai babu mai saka shi babu mai hana shi, ko tafiya zuwa kasashen waje tare yake tafiya dashi, a fada suna tare, in taro zaije tare zasu tafi. Rannan kawai da safe aka ga basu fito sallar asuba ba, aka shiga za'a tashe su amma sai jikan ne kawai ya tashi, kakan Allah ya karbi ransa a cikin bacci. Wannan mutuwar ta tayar da hankalin kowa a masarautar nan amma babban abin tausayi shine karamin sarki, bai saba da kowa ba sai shi bai san kowa ba sai shi, dan haka rasa wanda zai rarrashe shi akayi, kwata kwata ya hana a yi wa gawar sutura, sanda mahaifinsa yazo muka ji dadi cewa an samu mai rarrashinsa amma yana zuwa sai ya dauke shi chak ya tafi dashi wani tsohon store ya daure masa bakin sa, ya daure masa hannayensa da kafafuwansa ya rufe shi a dakin yayi tafiyarsa. Babu wanda bai tausayawa yaron nan ba, kuka biyu muka yi a lokacin, har yanzu ina iya tuno wani irin gunjin kuka daya ringa yi babu baki, kamar ransa zai fita, wallahi ban dauka yaron nan zai yi rai ba, na dauka zuciyarsa zata buga ya mutu, amma zuciyarsa mai karfi ce. Haka ya kwana anan sai da safe sannan ya fito dashi kuma ya gaya masa in ya kuma yin kuka sai ya kuma daure shi. Bayan anyi sarauta su Hajiya suka dawo nan mu kuma muka koma sabon guri tare dasu Yaya, nan Hajiya tace abar mata Karamin Sarki, Yaya sam bata so hakan ba amma sai ta barshi din wai ko hakan zai sa ya saba da mahaifanan. Mu dai daga nan bamu kuma jin labarin da yake ciki ba sai kawai muka ji labarin wai an kai shi Lagos gidan kangararru, Yaya ta tayar da hankalinta sosai, amma ko ta kira Takawa ta yi masa magana sai ya nuna mata kamar zai aika a dawo dashi amma shiru, sai da ya shekara biyu acan sannan Yaya ta aika galadima ya dauko shi, tace masa ya mayar dashi gidansa ya zauna acan, ai kuwa nan rigima ta tashi dan har saida Yaya tayi sharia tsakanin sarki da galadima akan me yasa galadima ya dauko karamin sarki daga Lagos, wannan shi yasa duk 'yan uwa kowa ya dauke hannunsa daga kan maganar karamin sarki har aka turashi kasar waje karatu babu wanda yayi magana, amma ni nice shaida, duk watan duniyar nan sai Yaya ta saka an sauke masa alqur'ani da niyyar ya zama kariya a gare shi a duk inda yake".
Jin tayi shiru yasa na gyara zamana nace "to yanzu baba gaji, duk gidan nan babu wanda yasan ina ne garin su mahaifiyar Sultan?" Tayi shiru tana tunani, sannan tace "to mu bayi dai kam bana jin akwai wanda ya sani, amma Yaya ba zata kasa sani ba, amma kuma ranki shi dade bana jin zata gaya miki, dan da zata fada da duk tsahon shekarun nan da ta gayawa karamin sarki". Na koma na kwanta na lumshe ido na ina juya maganganun a raina, na samu wasu amsoshin, amma kuma amsoshin sun kuma tayar da wasu tambayoyin. Menene gaskiya dalilin rabuwar iyayen sultan? Menene dalilin da yasa soyayyar mahaifinsa ta koma kiyayya a lokaci daya? Menene kuma dalilin da yasa ake boye labarin mahaifiyar Sultan ba'a so kowa ya sani? Na tuna da labarin da Sultan ya bani na amsar da Yaya ta bashi sanda yayi mata irin wannan tambayar 'to protect the family name' but what kind of protection?
Follow me on wattpad @maman_Maimoon
Episode Seventy Four : The Cook
Ranar ba'kin gidan mu suka zo yi mun sallama, daga 'yan 'yalleman har 'yan niger duk gobe kowa zai tafi gida. Zuwan su ne ya saka na manta da hirar mu da baba gaji. Nan take 'yammata na suka fara hidima dasu, sun iya aiki sosai dan ba sai bace ayi abu ba zanga kawai anyi, da kyar na samu kebewa da Amina nace mata " Amina kin kira Ibrahim din kuwa?" Ta dauke kanta ta bata rai tace "na kira shi once, bai dauka ba, ni kuma na rabu dashi" sai naji ba dadi a raina, it has been three days, ya kamata ace an san halin da yake ciki. Nace "please Amina ya zaki yi haka, gashi gobe zaki tafi and I don't know who else zan saka" ta daga min hannu tace "relax, ba tare zamu tafi dasu ba, Mommy tace in zauna anan for the time been" nayi ajjiyar zuciya nace "please Amina, kema kinsan ai ranar in kika kira shi ba zai dauka ba amma yanzu at least na san ya dan huce zai saurare ki" ta kara tabe baki tace "I will try amma ban miki alkawari ba, in naga yana daga min kai I won't go around chasing him" na yarda a haka. Sai bayan zuhr Sultan ya dawo, tun daga waje yaga motocin gidan mu dan haka sai ya zagaya ta baya ya shiga direct part dinsa sannan ya kira ni a waya ya ce min ya dawo. Ina shiga palon sa na ganshi a zaune ya kunna kallo da remote a hannunsa, na tsaya daga bakin kofa nace "sannu da zuwa" ya juyo yana kallona sai ya nuna min cinyarsa yace "come here" na makale kafada, yace "to ni ma bana cin mike, bana amsa gaisuwa daga nesa" na karasa shigowa na rufe kofar nace "Sultan baki ne a gidan, inna zo nasan ba bari na zakayi in fita da wuri ba" ya bata rai yace "da ni da bakin waye yafi muhimmanci?" Ban bashi amsa ba nace "amma ai su tafiya zasu yi ko? Sallama suka zo yi mana fa" yana kallona kasa kasa yace "OK, just a kiss, shikenan" na karasa gurin sa na tsaya, ya nuna min lips dinsa yace "here" na matso da fuska ta dai dai tasa, ina kallonsa har da lumshe ido wai shi nan za'a yi masa kiss, na cije shi kadan akan hanci na juya da gudu, ina jinsa yace "ouch, zan kama ki ne" na juyo nayi masa gwalo na fice. Sai bayan la'asar baki na suka tafi, sai a lokacin na koma gurin Sultan na tarar yana lunch din da na kai masa tun dazu, nace "au baka ci abincin ba sai yanzu?" Yace "bayan yau wulakanta ni kike yi dan kinga 'yan gidan ku ko? Tun dazu nake jiranki kizo muci abincin shine kika ki zuwa ko?" Na karbi cokalin a hannunsa nace "am sorry, ban dauka zaka jira ni ba, nasan halinka da abinci" na diba na fara bashi a baki, yaji dadin hakan sosai, na tambaye shi "how are the kids?" Take naga fuskarsa ta haska da murmushi yace "they are fine, suna ta tambayarki, wai suna so su shirya mana surprise party" nayi dariya nace "then it is no longer surprise tunda sun gaya maka" yace "kuma bayan gaya min din da akayi har list aka bani na abubuwan da suke bukata for the party" ya dauko wata takarda muka fara karantawa, tarkace ne nasu balloon da ribbons, har da cake, wai suna so a jikin cake din a rubuta 'happy marriage life mom and dad, we love you' muka yi ta dariya nan na kara abubuwan da basu saka ba. Bayan Sallar magrib sai ga Hafsat da Zayed da little khairat suma sunzo mana sallama zasu koma England. A palon Sultan muka zauna dasu muna ta hira. Hafsat da tsegumi har bedroom din sultan ta shiga, yace "Hey lady, me zaki yi min a daki ne? Baki san cewa bedroom dina sirrin mu bane" ba tare data kalleshi ba tace "koma menene ba sirri ba sai na gani, nasan babu abinda zan tarar sai kazanta" ta shige ciki, ta dade kafin ta fito, knowing halin Hafsat nasan har toilet ta shiga, tana fitowa Sultan yace "kin dau bashi, duk sanda naje gidan ku sai na shiga dakinki" mu dai dariya muke musu ni da zayed. A nan Hafsat take gaya min in sun koma England zayed zai dauki leave zasu je saudiyya, dan 'yan'uwansa da yawa basu santa ba ga kuma khairat itama babu wanda ya santa. Tare muka yi dinner ina ta mamakin yadda sultan yake sakewa da zayed duk sanda suka hadu, dan yadda yake yi masa ko yaya Walid da suka saba sosai baya yi masa haka. Sai very late sannan suka tafi, ji nayi kamar zanyi kukan rabuwa da Hafsat tunda ban san kuma ranar da zamu sake haduwa ba in dai ba wani abun ne ya tashi ba. Sai bayan mun kwanta bacci sannan na fara bitar hirar mu da baba gaji, na kalli Sultan naga idonsa a rufe amma nasan ba bacci yake ba, nace "Sultan" yace "uhmm" nace "will you one day like to see your mother?" Yayi shiru kamar baiji abinda nace ba, na daga kai na kalleshi sai naga idonsa a bude yana kallon ceiling ya jima a haka sannan yace "No" da mamaki nace masa "why?" Da murya mai kaushi yace "I don't need her now. Sanda nake bukatar ta a lokacin ta ajiye ni ta tafi. I wish her happiness a ko ina take a duniya but I don't wish to meet her. Me yasa kika tambaye ni akanta yanzu?" Nayi tunanin in gaya masa labarin ta da na samu sai kuma bayi tunanin bani da wata concrete magana for now, zan gaya masa amma sai na sami more answers, nace "babu komai, kawai dai naji ta fado min a rai ne" ya kara jawo ni jikinsa yana saka fuskarsa a wuyana yace "forget about her kinji, itama yanzu ta manta dani, am sure ta haifi wasu 'ya'yan yanzu. I have you, I don't need anybody else".
Washegari ina palo da baba gaji naji sallamar Amir, baba gaji tace ya shigo, ya shigo muka gaisa nace masa " wato kwana biyu ko leke ko" ya rike baki yace "ni da aka kora ina zan kuma dawowa" muka yi dariya yace "tare da bakuwa muke" na kara fadin murmushina nace "really? Tana ina" ya dan sunkuyar da kansa kasa yana shafa kai yace "Amira ce" take murmushin fuskata ya bace, yace "ta gayamin duk abinda ya faru tsakanin ku, tace ta turo miki message cewa tana so ta zo amma baki ce mata komai ba, shine nace bara in kawo ta in taya ta bada hakuri, she made a mistake na sani amma..." Na dakatar dashi nace "it was not a mistake. Mistake shine abinda zakayi daga baya kayi realising cewa kayi ba dai dai ba sai ka bada hakuri kace kayi mistake, amma ita bata yi realising ba har sai da Allah ya tona asirinta, dan haka va wai nadama tayi ba kawai dai an riga an kama tane babu yadda zata yi" ya gyada kai yace "na fahimce ki, amma ina so ki saurareta, ta baki labarin in her own version, na tabbatar zaki yafe mata" na daga kafada nace "ni ai already na yafe wa Amira, abinda bazan yi ba shine ba zan kuma bata space a rayiwata ba ballantana har ta kuma cin amana ta" yace "OK let me call her in now" ya tashi ya fita sai gasu sun dawo tare, fuskarta tamkar ba Amiran dana sani ba, idanuwanta sunyi circle din baki alamar kuka da rashin bacci, bakinta duk a bushe, bana jin ko mai ta shafa ballan tana kwalliya. Tana shigowa nace da baba gaji ta bamu guri, sai da ta fita ta rufo kofar sannan Amira ta karaso inda nake zaune, nace "sannu da zuwa" bata amsa ba sai ta durkusa a gaba na, hawaye ya fara bin fuskarta tace "Moon dan Allah ki yafe min abinda nayi miki. Dan girman Allah. Wallahi nayi nadama ba tun yanzu ba. Son zuciya ne ya saka ni nayi abinda nayi da kuma sharrin shaidan. Tun da dadewa nake so in gaya miki amma na kasa gaya miki saboda bana son ki yanke friendship din mu" nace "Amira ni na yafe miki already, saboda ni ma ina da laifuffuka na a gurin ubangiji kuma ina son idan na nemu yafiyarsa ya gafarta min. Amma hakan ba yana nufin cewa we are back to friends zone bane ba" ta goge hawayen fuskarta tace "ni hakan ma yayi min. Dama can I never deserve to be your friend. Tun sanda aka kawo ku muna jss 1 naga kin burge ni, 'yar karama dake gaki kyakykyawa, sai daga baya na fahimci how smart you are, duk mun fiki girma da shekaru amma kin fimu kokari. I wanted nothing more than to be your friend. Ban dauka zaki kula ni ba, na dauka zaki zamo mai girman kai amma sai naga ba haka bane ba, naga kina da saukin kai fiye da duk sauran mates din mu. Moon you will never know how much I admire you. Sanda aka yi hutu kika bani address din ku nazo sai naga how rich your parents are, you have everything, you are everything I wanted to be. You were my model, I always wanted to be like you but I couldn't. Lokacin da su Ibrahim suka zo, you guys were laughing at them. I liked him kallon farko da na yi masa. In kuna yi masa dariya har haushin ku nake ji a raina amma ba zan iya fada ba saboda bana so in bata miki rai. I didn't know love then, kuma ko da na sani ma I doubt in zan iya fada masa ina son sa. Ban san ya akayi ba kawai sai na ganku tare a matsayin saurayi da budurwa. I was angry as to how can you have everything I wanted and then still have him? Amma babu abinda zan iya yi akai dole na hakura nake kallon ku, lokacin da ya fara yi min lessons din musabaka lokacin soyayyarsa ta kara karuwa a zuciya ta, I guess na kasa boyewa ne har na nuna masa, abinda yace min shine ya daina yi min lesson din sai dai in zamu ke zuwa tare dake, I was so pissed up nace na fasa musabakar ma gaba daya, yaje ya gaya wa pc ta kira ni nace eh na fasa, maimakon ya lallasheni ya bani hakuri sai cewa yayi da pc ai kema zaki iya, a rabu dani a saka ki kiyi kawai. Ranar ne na fara gaya miki maganganu kuma daga baya sai naji babu dadi, it is not your fault that you get everything I wanted. It was not your fault that he loves you not me. Kuma shima banga laifinsa ba, dan babu wanda zai samu someone like you ya ajiye ya dauki someone like me. It was my fault that I couldn't control my heart. Bayan nan yazo har cikin class ya fada a gaban kowa cewa baya so na, duk da dai 'yan ajin basu san dawa yake ba. Na fahimci cewa ya gaya miki abinda ya faru tsakanin mu, amma ga mamaki na sai naga hakan bai sa kin chanza min komai ba, saboda ke din ta daban ce. Daga lokacin har adduah na ringa yi ina rokon Allah ya cire min shi daga raina. Bayan munyi graduation ne rannan kika gaya min cewa he left you sai nan gaba zai dawo, a raina nayi adduar Allah yasa ba zai dawo ba saboda bana son abinda zai bata kawancen mu dake. I never thought nima zan sake ganinsa. Kawai rannan bayan kun tafi England sai gashi a kofar gidan mu, na dawo daga makaranta kawai na ganshi a tsaye yana jirana. He looks so happy to see me, and my stupid heart thought cewa guri na yazo, it was very stupid of me to even think that. I was so happy. So excited. Sai bayan da na shigar dashi gida muka gaisa sosai sannan ya gaya min cewa ke yake nema. It hurt me so much then. I don't even know ma yaushe na kirkiri karyar cewa kinyi aure na gaya masa. Sai da naga expression din fuskarsa sannan na fahimci me nayi. It was already too late to gi back, maganar ta riga ta fito babu yadda zan yi in mayar da ita" ta fara kuka sosai "nasan cewa abinda nake ba dai dai bane ba amma na kasa dawowa baya in warware karyar da nayi. Na saka akayi min fake IV na kai masa. I kept telling myself cewa it will be better in na raba ku din yadda ba zan ke ganin sa ba ballantana har in bata friendship din mu dake. I kept telling myself cewa you will soon forget about him. Wani lokacin kuma in gayawa kaina cewa ko na bar ku ma ba lallai bane daddy ya yarda ya aura miki shi. Ita karya in ka yi ta sau daya to ka ringa karawa kenan kullum saboda kayi covering waccan da kayi. Haka na ringa yi masa karya akan ki. At first na yi masa karya ne saboda I was angry cewa baya so na, daga baya kuma na cigaba dayi masa karya saboda in boye waccan karyar da nayi dan inye saving friendship din mu. Abinda nake so ki fahimta shine, ban raba ki da Ibrahim saboda ni ina so in same shi ba, a'a na raba ku ne saboda ina gudun in yi asarar kawancen mu" na goge hawayen da yake ido na. Yana daga cikin ginshikin imani mutum ya zama mai yarda da kaddara, mai kyau ko marar kyau. Amira have always been a good friend to me. Ina jinta a raina kamar 'yar'uwata. Na mika mata hannu nace ta tashi ta zauna akan kujera. Ta zauna tana ci gaba da kuka. Nace "it's OK. Komai ya wuce in sha Allah" Amir ya taso ya dawo kusa da ita ya zauna yace "To kuma kukan na menene, ba tace ta yafe miki ba? Sai kinje ki sa wa kanki wani ciwon kuma". Muna nan tare dasu Sultan ya shigo, ya rike kugu yana kallon su "shikenan kuma mutum bashi da damar ya dan fita waje sai an zo an cika masa gida. Dole ma muzo mu bar kasar nan wallahi". Sam sultan bai nuna wa Amira yasan wata magana a tsakanin mu ba, ya zauna ya saka su a gaba ita da Amir da tsokana nima ina tayashi. Muna tare dasu har aka kawo lunch aka kai dining na yi musu bismillah, Sultan ne na farkon tashi wai dama yunwa yake ji, a raina nace 'acici'. Muna shiga na dauko plates da spoons, sultan na fara serving, na duba naga farar shinkafa ce da miyar kaji, sai brown macaroni. Na zuba masa shinkafar ina cikin zuba masa miyar naji yace " khulsum bata tafi ba kenan" na tsaya da abinda nake ina kallonsa naga bani yake kallo ba abincin yake kallo, na bata rai nace "me kace?" Still bai kalleni ba yace "khulsum nace bata tafi ba kenan, this is her cooking" na ajiye serving spoon din hannuna na rike kugu ina kallonsa nace "ya akayi ka san cewa this is her cooking?" ya jawo warmer din ya nuna grated carrot din da aka barbada akan shinkafar yace "this is her signature, in dai tayi abinci tana barbada carrot akai as her signature" sai a lokacin ya dago kai yaga yadda na rike kugu na hade rai ina kallonsa yayi dariya yace "common, da ina yawan cin abincinta, she is a chef, the carrot is just her signature kamr yadda mai zane yake signing a kasan zanen sa dan ya nuna cewa shi yayi" na kara hade rai ganin yayi comparing ita as a chef da shi as an architecture, ya gane abinda nake nufi yayi sauri ya gyara yace "ko kuma yadda likita yake signing a kasan prescription dinsa dan asan shi ya rubuta" a zuciye na jawo plate din abincin da na zuba masa na juye a cikin warmer din na kwallawa Hassana, daya daga cikin yarana kira, tana shigowa nace duk ta kwashe abincin ta tafi dashi gurin su su cinye. Na juya na kalli Amir da Amira da suka saki baki suna kallona kowa da cokali a hannu, sultan mamaki ne ya hana shi magana, sai daga baya yace "common Love, yunwa fa muke ji, yanzu kin bayar da abincin me zamu ci kenan?" Nayi hanyar kitchen ina cewa "I will cook you something" ya taso ya biyo ni, yace "yaushe kika iya girkin?" Nace "I will learn today" ina shiga kitchen na jawo apron na saka na kunna gas na dora tukunya da ruwa. Sultan ya karaso kitchen din ya rungume ni ta baya yace "relax, am sorry, dan nace na gane girkin ta doesn't mean anything, nasan ta iya girkin amma ban taba son taba, nasan baki iya girkin ba amma am head over heal in love with you. Ki bari Amir ya fita ya sami mana abinda zamu ci" Amira ce ta shigo kitchen din ya dan sake ni kadan ta karaso tace min "me za'a dafa?" Sultan yace "no ku bar shi kawai bara mu fita mu siyo" tace "ai kafin ku fita ku dawo ma yaci ace mun gama koma menene, yadda gidan nan yake da nisa zuwa gate ma aiki ne" ya dan tsaya yana kallona, na daga kafada yace "OK, cook us something simple" yana fita Amira ta bude freezer, ina kallonta tana fitowa da abubuwan da take bukata, ta miko min nama tace "wanke wannan" ina tabawa naji shi duk kankara nace "yayi sanyi da yawa ba zan iya tabawa ba" ta tsaya tana kallona kawai, sannan ta dauki naman ta zuba masa ruwa ta koma tana gyara kayan miya. Na dauko waya ta na kira Mommy, tana dauka na shagwabe murya kamar zanyi kuka nace "Mommy ban iya girki ba" tace "au ke da baki san baki iya girkin ba sai yanzu? Babu yadda banyi dake ba akan koyon girki ki ka ki, dama nasan wannan ranar tana nan zuwa. Yanzu me kike so inyi miki?" Nace cikin sanyin murya kamar abin tausayi "Mommy Asma'u zaki bani" tace "ita ma'un an gaya miki toy ce da zance kawai na baki ita? Besides nima ina bukatar ta tunda office aiki yayi mana yawa ba zama nake a gida sosai ba. Cooking classes zaki shiga ki koya ki ringa yi da kanki. Su yaran da aka baki duk basu iya girkin ba suma?" Nace "Mommy ni ba zan iya cin abincin su ba, Sultan ma haka. Professional cook muke nema. Kuma Mommy wallahi sultan ba zai barni in shiga cooking class ba" tace "to ai kuwa kwa kare da siyan abinci" nace "Mommy please" ta dan jima sannan tace "zan tambayi ma'un inji ko zata zo, amma da sharadi, in tazo zama zaki ke yi kuna girkin tare da ita kina koya, yaran naki suma duk su ringa koya, duk lokacin dana bukace ta zan aiko ta dawo gida in baki koya ba kafin nan matsalarku ce" cikin murna na fara yi mata godiya, bata saurareni ba ta kashe wayar. Zuciya ta naji tayi min fari tas, duk wani takaicin khulsum da girkin ta na manta dashi. Nima zan koyi abincin nan dai in huta.
0 comments:
Post a Comment