Bara mu dan yi magana akan rashin iya girkin Moon. Na saka cewa Moon ba ta iya girki ba ne saboda ina son in nuna wa mazan da suke karanta littafin nan dama matan cewa 'nobody is perfect' babu, kar ka saka ran zaka auri mace kyakykyawa mai ilimi mai addini mai tsafta mai son mutane mai ladabi da biyayya mai iya kula da miji, mai iya kula da miji a other room kuma mai iya girki, NO, ba zai yiwu ba, kamar yadda shima namijin ba za'a samu wanda yake 100% complete ba. Tabbas akwai matan da basa son girki, kamar yadda akwai matan da basa son shara da wanke wanke, kamar yadda akwai mazan da basa son kallon ball. Girki is a hobby, sometimes yana zama necessity, to idan ya zama both shine ake samun matar da ta iya girki sosai. Idan kuma aka samu matar da bata da interest akan girki amma kuma ya zame mata dole to sai azo a samu matsala, saboda hakkin kula da abincin miji da 'ya'ya yana hannun mu mu mata. Idan kinsan bakya son girki to kiyi kokari ki fara son shi, saboda ba zaki koya ba har sai kina son ki koya din, make it a hobby, make it a challenge, ki fara da kadan kadan a hankali zaki ga kin fara son sa. Nan gaba zaku kara fahimtar abinda nake nufi.
Har mota muka raka Amira da Amir, suna tafiya nayi gaba na bar Sultan dan har yanzu ba hucewa nayi ba. Daki na na tafi nayi kwanciya ta, ko minti biyu banyi ba kuwa ya shigo, na juya bayana na rufe ido. Ya zagayo ta gabana ya zauna akan gadon "wai kar dai ki ce min maganar abincin nan ce baki manta ba?", na turo baki, ya mintsini bakin nayi kara na sake juya masa baya. Ya hau kan gadon sosai yace " to wai bana baki hakuri bane ba. I never meant anything by it. I don't want a good cook, I want you. Idan abinci ne I can get it anywhere amma ke guda daya ne, there is no one like you" ya juyo dani yace "please kiyi murmushi mana in gani" ina so inyi murmushin amma na kara bata rai nace "just promise me ba zaka kara cin abincin ta ba" yace "abincin wa?" Nace "ita dai" yace "ni bansan wa kike magana akai ba, I don't know anyone bayan ke" ya dora goshinsa akan nawa "now smile" nayi murmushi tare da zagayo hannayena a wuyansa, yace "that's what am talking about" na saka fuskata a wuyansa irin yadda yake min nace "I will learn how to cook, for you" yace "NO, I don't want you stressing yourself out akan abinci, I will get a cook for us, ko ba a kasar nan bane ba" nace "na riga na kira Mommy ai, tace zata bani aron ma'u for sometime" ya jawo fuskata ya rike a hannunsa yace "dakin bar musu asma'un su mu ba sai mu samu tamu ba?". A haka dai muka kare har magrib sannan ya tashi ya tafi masjid.
Washegari tunda safe ya ce min zamu je mu gaishe da Yaya da Nani. Nace masa Hajiya fa? Yace sai Takawa ya dawo, baya kasar, in ya dawo sai muje mu gaishe su gaba daya. Muna gama breakfast na shirya cikin doguwar rigar lace, budaddiya, na gyara fuskata amma babu kwalliya sosai, na dauko jeweleries na zuba, na daura dankwali sannan na yafa babban mayafi, na kalli kai na a madubi, ni kaina sai da nayi mamakin chanzawar da nayi in few days, lallai aure daban ne, that little girl is gone, am a woman now, matar aure. Sultan ya shigo ya same ni a tsaye gaban madubi, yazo ya tsaya a bayana muna kallon kan mu ta cikin mirror din. Ya sunkuyo a hankali yayi kissing kuncina yace "you look beautiful, Darling" na daga hannuna na shafa fuskarsa ina kallonsa ta cikin madubin nace "you look handsome too, Darling" a tare muka yi dariya, ya dauko wayarsa yayi mana selfie ta cikin mirror sannan muka tafi. A bayan palace din sabon gurin yake, an kawata gurin sosai dan zaka dauka wani palace din ne daban, ko da yake gidan mahaifiyar sarki ai dole a kawata mata shi. Tun daga bakin gate ake ta gaishe mu, ni har kunya nake ji in naga manyan mutane suna durkusawa har kasa suna gaishe mu, na kalli fuskar sultan naga ya wani hade rai kamar bai taba dariya ba, ni kuwa sai washe baki nake ina amsawa. Direct part din Yaya muka shiga, da kanta ta fito har kofar palo ta tare mu, ta kama hannuna ta jani jikinta ta rungume, sai naji kunyar ta sosai, naja mayafina na rufe fuskata, tana ta dariya tace "ni fa kakar kice ba surukarki ba, ki bude fuskarki ki kalle ni sosai, in kika tsaya wasa sai in kwace mijin, dama ara miki nayi" ina jin Sultan yana cewa "nan gani nan bari Yaya, ai wutsiyar rakumi tayi bala'in nesa da kasa" suna ta wasan su na kaka da jika muka shiga ciki, har cikin bedroom dinta ta zarce damu. Sultan ya samu kan gado ya haye harda harde kafa. Ni kuwa na zauna a kasa kan carpet, Yaya ta zauna kusa dani, na rissina ba gaishe ta ta amsa da fara'arta, tace "ya bakunta? Ina fatan dai bakiyi kewar gida da yawa ba?" Nayi murmushi kawai bance komai ba. Tana ta tsokana ta wai kauyanci nake yi irin na fulani, Sultan dan rashin kunya shine yake ramamin, ta saka aka cika mana gaban mu da kayan ciye ciye. Ni dai na kasa cin komai, sultan kam aka sauko aka fara aikin da aka saba, ci. Da kyar na danci fruits kadan naci dambun nama. Yaya tace "kaga karamin sarki, ka tashi ka tafi ka bar mana ita. Da daddare sai ka dawo ka dauke ta" da sauri sultan yace "what? Amma dai wasa kike yi ko? Ai ba haka muka yi ba, cewa kika yi in kawo ta ku gaisa ba wai in kawo ta ta wuni ba" ta rike baki tace "au yanzu kana nufin ba zaka bar mana ita ta wuni din ba?" Ya girgiza kai yace "gaskiya ba yau ba, sai dai wata rana kuma" na dauko wayata nayi masa text, 'Sultan ka barni in wunin mana, kaga haka ba dadi fa' yana ta zance bai gani ba nayi masa flashing yana dauko wayar na katse, ya duba yayo min reply 'yanzu kina nufin ni kadai zan koma gida?' Na amsa 'it will be for just few hours ne fa, in kuma ba ka son zama kai kadai sai ka zauna anan din kaima, ko kuma ka tafi wani gurin" ya dan kalle ni nayi masa alamar please, ya dauke kai. Yace "OK, Yaya, kinci nasara, zan bar miki ita, saura kuma in na dawo daukanta ace kwana kuma ake so tayi" ya mike yana kallona nace "adawo lafiya" yayi kwafa bai ce komai ba ya tafi, Yaya tace "Allah ya raka taki gona, daga zuwanka har ka saka ni ciwon baki saboda magana". Sai daya dan jima da tafiya sannan Yaya tace "kin ki cin komai maimunatu, kina ganin dai shi yadda yake ta zuba min rashin kunya amma ke abinci na ma kin kasa ci" nace mata "na koshi ne ai" tace "wai menene sirrin ne?" Na kalketa da alamar rashin fahimta tace "ya akayi kika kwace min miji ne wai?" Na sake jin kunya na sunkuyar da kai, tace "gaskiya ni kam babu abinda zan ce miki sai godiya, ko a mafarki ban taba tunanin zan ga karamin sarki yadda na ganshi yau ba. Ban taba ganinsa cikin fara'a, kwanciyar hankali da nutsuwa irin yau ba. Allah ya saka miki da mafificin alkhairi duniya da lahira, yadda kika kawo farin ciki rayuwarsa Allah ya tabbatar miki da farin ciki a cikin taki rayuwar" nace "Ameen" ta cigaba da magana "kullum babu dare babu rana addu'ah ta akan yaron nan take, bam taba gajiyawa ba kuma ban taba fitar da rai ba, gashi Allah ya amshi adduah ta ta hanyar ki maimunatu. Ni kam babu abinda zan saka miki dashi illa in yi miki alkawarin zan yi iya bakin kokarina inga cewa dake dashi kun cigaba da zama cikin farin ciki har abada. Dan haka duk wani abu da kike so, na kudi ko akasin haka, ki gaya min. Duk wani abu da kika ga anyi muku ba dai dai ba shima ki gaya min, kar kice zaki boye har ku zo ku cutu dake dashi. Karamin sarki yasa wahala a rayuwarsa, yanzu farin ciki yazo masa, akwai mutanen da ba zasu so suga wannan farincikin ya dore ba, dan Allah maimunatu kar ki basu dama. Karki yadda wani ya gaya miki wani abu akan mijinki ki yarda, duk abinda aka gayamiki kiyi bincike sosai akansa. Nasan tun kafin ki auri karamin sarki kin san yana shan giya, amma baya neman mata, ban taba samun wannan complain din akansa ba. Duk wadannan mugayen abokan nasa na tabbatar zaki iya raba shi dasu, dan in baki raba shi dasu ba zaki ke yin tubka ne suna warware miki" da tanyi shiru sannan ta cigaba "Maimunatu ke kadai ce hope din mu akan karamin sarki. Ke ce amsar adduar mu" jin ta sake yin shiru ya sa na dago kaina nace "Insha Allahu Yaya komai ya kusa zuwa karshe, insha Allah yanda ki kai kuka akansa kin kusa kiyi dariya" dariya ta fara yi tun yanzu tace "dariya kam ai na fara yin ta maimunatu, ganinsa da nayi yau kadai ya wanke min zuciya ta" wata 'yar karamar budurwa ce ta leko da sallama tana kallon mu daya bayan daya. Yaya ta ce "sai ki shigo ai, dodon naki ya tafi" ta karaso amma kamar bata yarda ba, sai da ta tabbatar innan ta zauna tana dariya ta gaishe ni, na amsa da fara'a tace "ashe ya tafi, ina ta lekowa tun dazu ina son inzo in gaishe ki bana son mu hadu dashi, ni tsoro yake bani wallahi" Yaya tace "Allah ya shirye ki, dan uwan naki kike tsoro" tace "Yaya baki ga yadda jikinsa yake ba ne ba a mummurde, kina ji kuma rannan yace in ya kamani sai ya dake ni" Yaya tace "to ai tsoron nasa da kike ji ne ya saka ya ke miki hakan" ni dai dariya kawai nake yi mata, daga baya nace "kinsan abinda zakiyi ki daina jin tsoron sa? Shiryawa zaki yi mu tafi tare, in kina ganin sa kullum zaki saba dashi ki daina jin tsoronsa" tayi saurin girgiza kai tana zaro ido tace "in kin ganni a gidanki to yayi tafiya. Wai in tambaye ki, yana dariya kuwa?" A raina nace 'lallai Sultan wato tsare gida ne dashi a cikin 'yan'uwansa kenan, dan su Fa'iza ma tambayar da suka fara yi min kenan' nace "yana yi sosai ma, da kin shigo dazu da kin ganshi yana dariyar ai" tace "ban taba ganin sa yana dariya ba"mun jima muna hira da ita, anan na fahimci cewa cousin din sultan ce sunan ta Huda, tana secondary school bata gama ba, a gurin Yaya ta ke zaune. Sai bayan Magrib sultan yazo daukana, bai shigo ba kira na yayi yace in fito, nan kuma Huda ta fara nuna bata son in tafi, Yaya tace ta bari da weekend sai tazo min. Yaya ta saka aka zuba mana abinci a flask muka tafi dashi.
Tun a hanya nake bawa Sultan labarin yadda muka yi da Yaya da kuma Huda, yayi dariya yace "tunda na dawo daga America yariyar nan take jin tsoro na wai na zama kato". Muna shiga palo na ajiye jakata ina kokarin in kira yara su dauko mana abinci a mota, sultan ya zagayo ta bayana ya dauke ni chak ya fara tafiya dani hanyar dakin sa, da mamaki nace "Sultan what are you doing?" Yace "It is pay back time" nace "ka manta yadda tsarin yake ne? Food, bath, and then it?" Yace "No, an chanza tsarin yanzu. Yanzu na samu abinda yafi food dadi, it will comes first, then birth and then food" mukayi dariya a tare sanda muka shiga dakinsa, kan gado ya kaini ya ajiye ni yace "fada min dame dame yaya ta baki" nace "ina ruwanka, sirri ne tsakanin mu" ya tashi yana cire kayansa yana kallona, nayi sauri na rufe idona, ina jinsa yana dariya, naji motsin sa ya hawo kan gadon, ya juya ni ya zuge zip din rigata, ban hana shiba amma ban bude ido na ba, ya zare rigar ya ajiye gefe, ya zare skirt underwear na shima ya ajiye, still naki bude ido na, ya kamo hannuna ya dora a kirjinsa yace "open your eyes" na girgiza kaina, yace "why?" Na hadiye yawu da kyar. Ya sake cewa "open your eyes and look at me" na dan bude ido na na kalleshi, ganin babu komai a jikinsa ya sa na saka hannayena na rufe fuskata, ya sake kama hannayen nawa ya dora a kirjinsa yace "it is OK, Daddy ba zai ce miki No ba Mommy ba zata yi miki fada ba" ya fara yawo da hannuna a jikin sa yace "kin gani baki kama da wuta ba. Nothing will happen idan kin kalle ni ko kin taba ni. I am made of flesh and blood like you, I am not made of glass or fire, in kin taba ni I will not crumble or break down, I drive as much pleasure when you touch me as I do when I touch you" ya cigaba da yawo da hannuna a jikinsa, ji na nake wani iri, ganin hannun yana tafiya wani gurin nayi sauri na kwace hannuna, yana dariya ya jawo ni muka zauna muna facing juna yace "you see?, it is perfectly alright. Try it" na dago hannuna na dora a kafadarsa na fara shafawa a hankali ina jin softness of his skin plus the hardness of his muscles, ya lumshe idonsa yana murmushi yace "do you feel that? Feels good, right?" Yes it does feel good amma ban fada ba, na cigaba da shafa jikinsa a hankali, tun yana guiding hannuna har ya barni na cigaba da kaina, sai da nayi iya yina sannan na dago na kalli fuskarsa, idonsa a rufe, fuskarsa tayi red, red lips dinsa sun kara ja, bakinsa slightly open, na kawo fuskata dai dai tasa na dora lips dina akan nasa na fara kissing dinsa a hankali, he let me, na dan sake shi naja baya kadan amma ko inchi biyu ban matsa ba ya jawo ni da karfi ya mayar da bakin mu ya hade, tun daga rikon da yayi min nasan yau kam sai yadda Allah yayi dani.
Da safe bayan munyi sallar asuba mun koma, karar wayar sultan ce ta tashe mu, ya farka amma bai dauka ba har sai da ta katse, ta sake fara ringing yayi tsaki ya mike zaune sannan ya dauka, a hankali yace "abbas" a take naji baccin ya bar idona, ina jin su suka dan yi magana sai naji sultan yace "OK, zamu shigo an jima" ya kashe wayar ya ajiye ya rike kansa da hannu biyu, na tashi zaune ina jin ciwon jiki duk kuwa da cewa sai da na gasa jikina kafin in kwanta, na dafa shi nace "me yace Abbas din?" Ba tare da ya kalle ni ba yace "Takawa yana kiran mu wai in an jima" nace "ya dawo ne?" Yace "I don't even know ya dawo ma sai yanzu, maybe jiya da daddare ya dawo" ya mike ya shiga toilet. Ina lura dashi har muka zo yin break hankalinsa baya tare dashi, na hada masa tea na bashi amma naga ya zauna yana ta juya shi, na taso na zauna a cinyar sa dauki tea din ina bashi a baki amma still sha yake yi kamar mai shan magani. Sai da ya shanye sannan na ajiye cup din ina shafa fuskarsa nace "what's wrong?" Yana shafa bayana yace "bansan kiran da yake mana ba, bai taba kirana akan abin alkhairi ba" nace "amma dama ai zamu je mu gaishe shi idan ya dawo, tunda anyi bikin mu baya nan maybe albarka zai kira mu ya saka mana" ya danyi murmushin takaici yace "my Daddy is not like your Daddy, my Daddy baya saka min albarka. Am very sure there is something bad a wannan kiran" kawai nima sai naji zuciyata ta tsinke, haka muka shirya duk babu fara'a muka fita. Munayin packing ya fito ya bude min kofa, ina fitowa ya kama hannuna ya rike kam, tamkar wadda za'a kwace mishi ni, nayi kokarin kwacewa amma yaki shikawa, na kalli fuskarsa naga sam babu fara'a, ban taba ganin fuskarsa a haka ba. Muna tafiya mutane suna ta gaishe mu amma ko kallon inda suke bai yi ba ni ma kuma bai bani damar amsa gaisuwar ba saboda yadda yake jana da sauri. Wata katuwar kofa naga mun dosa, muna shiga na saki baki ina kallon haduwar gurin, hatta bangon gurin an kawata shi da zane irin na sarauta, ga manya manyan hotunan sarakuna nan generation by generation, ga bayi nan da dogarai a zazzaune suna ta gaishemu amma bamu amsa gaisuwar kowa ba, muka shiga wata katuwar kofar glass, nan babu kowa amma yafi inda muka baro haduwa, ni dai gabana sai faduwa yake yi kuma har yanzu sultan yaki ya saki hannuna. A bakin wata kofa naga ya tsaya, sai da yayi ajjiyar zuciya sannan yayi knocking ya tura kofar a hankali tare da sallama. Muryar mace naji ta amsa, ya bude kofar gabadaya. Yau ne ranar dana fara ganin Takawa ido da ido, yana zaune ya harde kafafuwansa irin zaman da sultan yake yawan yi, gabansa tray ne da fruits a ciki, fuskarsa babu annuri ko kadan a ciki, kallon fuskarsa kadai ya saka naji hanjin cikina ya kada saboda tsoro. Gefensa da dama Hajiya ce, fuskarta fal da fara'a kamar gonar auduga, kusa da ita saratu da fa'iza. Daga hannun hagun Takawa kuma Abbas ne kansa a kasa dan haka ban karanci tasa fuskar ba. Nayi kokarin karbe hannuna daga cikin na Sultan amma ya kara rikewa, ina kallon idon Takawa ya sauka akan hannayen mu sannan ya kalli fuskokin mu, nayi saurin sauke ido na kasa ina jin bugun zuciyata yana karuwa, a tare muka taka muka karasa gaban sa, muka durkusa a tare, Sultan ne ya fara gaishe shi sannan nima nayi yadda yayi, babu wanda ya amsawa a cikin mu, hakan ya kara sawa naji bugun zuciya ta ya karu, Hajiya ce tace "yaron kirki shiru kuma babu kai babu amarya?" Ko kallon inda take Sultan bai yi ba, na juya ina kokarin gaishe ta naji muryar Takawa kamar a tsakiyar kaina yace "Maimuna" nayi sauri na juyo jiki na yana rawa, kafin in amsa ya jefo min wata envelope gaba na yace "bude" ina kai hannuna zan dauka Sultan ya riga ni dauka ya zaro abinda yake ciki, ji nayi gaba daya jinin jikina ya kafe, wani daci ya taso bakina kamar mai shirin yin amai, hotuna ne a ciki, ranar da aka kawo ni gidan sultan, hoton farko Sultan ne a tsaye da kwalbar giya a hannunsa, gefensa Daniel ne shima da the same kwalba a hannunsa. Hoto na biyu Solomon ne yana mika wa Sultan bindiga, hoto na uku kuma nice, da bindiga a hannuna, sultan a tsaye a kusa dani ga Ibrahim a durkushe a gaban mu. Na kalli sultan naga bani yake kallo ba babansa yake kallo wanda shi kuma ni yake kallo, na mayar da kaina kasa na sunkuyar ina jiran abinda zai biyo baya, Takawa ya fara magana "babanki mutumin kirki ne, abokina ne, babu yadda banyi dashi ba akan kar ya hada auren nan amma ya dage sai ya hada. Na dauka kema mutuniyar kirki ce irin mahaifin ki, ashe ba haka bane ba" fada yake yi sosai yana daga murya. "Bindiga, a cikin gidana? Waye shi wannan da zaku harba din?" Sultan yace "It doesn't matter waye shi, kuma ba laifin ta bane, ni na bata bindigar, ko menene za kayi ni zaka yiwa ba ita ba" da tsawa Takawa yace "shut your mouth, ba da kai nake magana ba, ka sani ba tun yau ba, I don't care ko ma menene zakayi da rayuwar ka. Itama saboda nayi wa baban ta alkawarin kula da ita ne, duk da cewa na gaya masa cewa duk abinda kayi mata shi ya saya da kudinsa. Amma har kana buda baki kana gayamin cewa kai ka bata bindiga da hannunta ka saka ta ta harbi mutum. What kind of a husband are you?" Ya juyo kaina yace "ki sani, zan kira Muhammad in gaya masa halin da kike ciki, Idan kuma shi ba zai dauki mataki ba ni zan dauka, saboda a matsayina na shugaba bazan tsaya ina kallo yarinya kamarki with good potential in life ta rusa rayuwarta saboda yaro kamarsa ba" ya karashe maganar yana nuna sultan. Sultan ya sake kama hannuna ya rike yace a hankali "we will leave, we will leave the palace, we will leave the town in ma kasar kake so mu bar maka zamu bar maka, you will never hear from us again..." Ya katse shi yace "you will leave the town dai, amma babu inda zaka tafi musu da yarinya, in kaga dama ka tafi karshen duniya ma babu wanda ya damu, but she will remain here" da sauri sultan yace "she is my wife" Takawa yace "and yet, nace babu inda zaka je da ita, in kuma baka yarda ba try me kaga abinda zai faru" tunda suka fara maganar nake kallon fuskar Takawa ina tattaro dukkan ilimi na na psychology ina so in karanci mind dinsa amma na kasa, kamar wani blanket ne a idonsa daya rufe emotions dinsa. Sultan ya mike da sauri ya jani, ina jin Hajiya tana cewa "amarya ki shiga ciki mana in na shigo sai mu gaisa sosai" kafin in samu bata amsa Sultan ya jani da sauri muka bar gurin, ni dai kawai binsa nake yi a baya dan ji nake yi kamar zai tashi sama dani, muna zuwa ya bude mota ya jefa ni ciki ya rufe ya zagayo ya shiga ya tayar, yana yin reverse ya daki lamp post amma bai tsaya ba ya figi motar mukayi hanyar gurin mu. Har mukaje bai ce min komai ba nima ban ce masa ba, yana yin packing ya fito da sauri nima na biyo shi a baya harda dan gudu na dan in kamo shi, ta kofar part dinsa ya shiga na bishi a baya, yana shiga ya dauki coffee table dinsa ya buga shi a jikin bango ya tarwatse, na saka hannuna na toshe kunne na ina ambaton sunan Allah, ban taba ganin bacin ran sultan ba irin na yau, idonsa yayi duhu hancinsa yana budewa alamar yana shakar numfashi da sauri, nayi kokarin in rike shi kar ya taka glass din ya yanke amma ya kwace ya jawo wani frame ya doka a jikin glass din window duk suka hadu suka tarwatse. Na kira sunan sa da karfi "Sultan, look at me, me kake yi ne haka?" Ya juyo yana kallona sai kuma ya kwabe fuska kamar zaiyi kuka amma kuma babu hawayen, yace "He is going to take you away, I should have known dama ba zai taba bari na cikin farin ciki ba. What did I ever do to him" na karasa na rungume shi ina jin bugun zuciyarsa tamkar a kirjina, a hankali nace "babu mai rabaka dani mijina, am yours, forever and ever" ya zagayo hannayensa a jikina yana sauke ajjiyar zuciya sanna ya sake cewa "what did I ever do to him?"
Episode Seventy Six : The Visitors
Ina dan bubbuga bayansa kadan nace "Nothing Sultan, You did nothing" yace "me yasa ya tsane ni to? Me yasa basu zubar da cikina ba tunda sun san basa sona?" Nace "Suna sonka Sultan, kawai dai basa nuna maka ne, amma deep down suna sonka sosai, maybe more than yadda nake son ka ma" ya sakeni yana kallon fuskata yace "don't say that, in kina son kwantar min da hankali na say something else amma ba wannan ba, cos nasan basa sona, tun kafin in san menene so nasan basa sona. They hate me and I don't know why, wannan shi yafi komai bata min rai, why do they hate me so?" Bance masa komai ba saboda bansan me zance masa din ba. Ya zauna akan kujera ya zaunar dani a kusa dashi yace "tunda ya fara wannan maganar ba zai bar ta ba har sai yaga ya raba mu, I know him, zan shirya mana barin kasar nan, shine kadai hanyar da zamu bi mu tsira daga gare shi" na girgiza kaina nace "Sultan barin kasa ba shine mafita ba, iyayen mu ne, we are nothing without them and we can't runaway from them. Mafita shine mu zauna muyi facing din su mu yi duk abinda suka ce mu bar duk abinda suka hana mu. In mukayi haka to Takawa will have no reason da zai sa ya takura mana ko yayi tunanin raba mu. Amma in dai muka ce zamuyi retaliating ko kuma zamu bar kasar to anan ne zamu bashi damar yi mana duk abinda yake so" ya girgiza kansa yace "baki san halinsa ba, he will not stop, baya bukatar reasons, in dai yana son yayi min abu to tabbas zai yi min ne ko nayi laifi ko banyi laifi ba, ballantana yanzu yana ganin yana da dalili a hannunsa. Yanzu nasan Daddy zai kira ya nuna masa picture dinki da bindiga ya kuma gaya masa cewa nace nine na baki. The next thing you will know Daddy zai zo yace ki fito ku tafi an gama auren kenan" nace "then you don't really know Daddy. Daddy ba zai taba yanke hukunci ba tare da bincike ba, ni kuma in ya tambaye ni zan san yadda nayi nayi masa bayani yadda zai gane, kuma nasan zai gane din ma. Yanzu abinda nake so muyi magana akai shine; wa kake tunanin ya kaiwa Takawa pictures din nan?" Wani murmushin takaici yayi yace "tunani? Am sure it is Abbas, ba yau ya fara ba ai, but this will be the last time da zai shiga harkata, dan wallahi sai jikin sa ya gaya masa. He shouldn't have touch you" yadda ransa yake a bace na tabbatar idan ya kama Abbas sai dai wani bashi ba. Na kama hannunsa ina shafa gashin hannun a hankali nace "wannan shine exactly abinda Abbas yake so kayi, so yake ka taba shi yadda Takawa zai sake samun karin dalilin raba ka dani. He got your weak point, me. Yasan cewa you will react exactly like this, yasan cewa in Takawa yayi maka magana zakace zaka dauke ni mubar musu kasar, yasan kuma Takawa zai ce ba zaka tafi dani ba. Ya lissafa cewa duk abinda ya faru shine mai riba, in ka tafi kabar kasar dani shikenan he got rid if you, in kuma bamu tafi ba zaku yi ta rigima da Takawa shima nan shine da riba" He seems calmer now, yana sauraro na sosai, yayi ajjiyar zuciya yace "yanzu mai kike ganin zamuyi?" Nace "kar mu bawa Abbas abinda yake nema. Kar muce zamu je ko'ina. Kuma kar kace zaka dauki fansa akan Abbas, just let him be, duk abinda zai yi kar ka kula shi. Sai kuma muyi taka tsantsan, kar mu yarda muyi wani abinda muka sam Takawa baya so. You already got your job, ka cigaba da abin ka, duk sanda kake bukatar fatherly care ko wata shawara, go to Daddy. The last and the most important thing shine mu dage da addu'ah. I believe Allah yana tare damu kuma yana ganin duk abinda yake faruwa kuma ba zai taba barin mu ba as long as muma bamu barsa ba. Yadda ba zamu bar Allah ba kuma shine ta hanyar ibada da addu'a. Kuma ka saka a ranka cewa I will never leave you, Ever. Duk ma wani abinda zai faru, we will face it together" na dago hannunsa na kai baki na nayi kissing, nace a hankali "I love you" ga mamaki na sai naga yayi murmushi, genuine murmushi, yace "I love you too".
A ranar Asma'u tazo, da gudu naje na rungume ta ina murna, itama murnar take yi, tace " me sunan daada in dai girki kike so ki koya to ki tabbatar kin samu, dan bazan bar gidan nan ba sai na tabbatar babu wani abincin da baki iya ba" na nuna mata kitchen ta shiga tayi surveying ta fito ta fara lissafamin abubuwan da babu ina rubutawa, muna gama wa na bata kudi isassu nace taje ta siyo, shatar taxi ta dauko daga kasuwar saboda yawan kayan da ta siyo, ni dai ina ta mamakin wai duk wadannan kayan a ciki za'a zuba su. A ranar tare mukayi lunch da ita da sauran yara na, banyi aikin ba ina dai zaune ina kallon su suna tayi amma asma'u tana yi min bayanin komai da suke yi da dalilin da yasa suke yin komai. Har aka gama aka shirya table, for the first time yau anyi abinci a gidana, duk da cewa bani nayi ba amma naji dadi, nayi feeling cewa nayi gaining wani abu. Sam na manta ma da Takawa da Abbas and their problems. Sultan ma naga ya saki ransa. Da yamma muka fita muka tafi orphanage gurin surprise party din mu, a hanya muka tsara muka saya musu gifts, kowa sai da muka sai masa toy, mata baby dolls maza bindiga, yan kananan kuma mota, shigar mu cikin yaran ya kara saka wa muka manta da komai. Sunyi organizing abin sosai, harda drama da sport suka yi mana, aka kawo mana cake muka yanka sannan na zauna na yayyanka na bisu na bawa kowa a baki. Nan take naji yaran sun kwanta min a raina, na sake sosai a cikin su mukayi ta wasa, sultan har mamaki na yake yi saboda ganin bamu da yara a gidan mu. Bamu dawo gida ba sai bayan magrib, muna zuwa dama a gajiye muke, dan da kyar muka ci abinci, na fara shirin wanka kenan aka zo aka ce min wai nayi ba'ki, na kalli agogo naga 8:30, nace "wadanne irin ba'ki ne kuma yanzu?" Yarinyar tace min "Hajiya ce, tare da wadansu mata" wata irin faduwa naji gabana yayi, a daki na nake, sultan ya tafi nasa. Nace yarinyar ta shigo dasu palo na tace musu ina zuwa, fasa wankan nayi sauri na zura doguwar bakar riga nayi rolling veil na fesa turare na fito. Su uku ne na tarar a zaune suna karewa palon kallo, Hajiya, sai wata mata kusan sa'arta sai kuma khulsum. Na tattaro murmushi na shimfida a fuskata na karasa gurin su, na tarar already an kawo musu drinks da snacks da fruits, na durkusa na fara gaishe da Hajiya sannan na gaishe da daya matar dana lura suna kama, suka amsa min duk da fara'a a fuskarsu. Na juya na kalli khulsum nace "nayi fushi, sai yau zaki zo gidan nan" ba tare data mayar min murmushina ba tace "abubuwa ne suka yi min yawa. Kuma yanzu ba gashi nazo ba" Hajiya tace "dazu kuma nace ki tsaya sai da na fito na tarar ba kya nan" na sunkuyar da kaina bance komai ba, ta cigaba "ko da yake nasan ba laifin ki bane, yaron nawa ne sai a hankali, amma ace kwana nawa da bikin nan bai kai ki kin gaishe mu ba, sai da Takawa ya kira ku da kansa, sannan kuma ace kunje din ma bamu samu mun gaisa ba. Shi yasa na taho yanzu da kaina ni inzo mu gaisa din, in ga dakinki kuma in saka muku albarka" daya matar dana fahimci kamar 'yar uwartace tace "to yanzu 'ya'yan zamani ne sai a hankali, dan da ka haifa ma yaya ka kare dashi ballantana dan da yake ganin ba kai ka haife shi ba. Ke dai kawai Allah ya saka miki da alkhairi na abinda kike yi masa, dan ko uwar data haife shi iyakacin abinda zata yi masa kenan" Hajiya tace "Ameen dai" ta juyo gurina "ina yake ne? Kar dai kice daga gama biki har ya cigaba da yawon daren nasa? Wannan yaro na rasa yadda zanyi in raba shi da wannan yawon daren. Kullum ya fita hankali na a tashe yake saboda bansan me yake aikatawa a wajen ba" ban katse taba sai da na bari takai aya sannan nace "yana daki" suka kalle ni sannan suka kalli junansu sannan Hajiya tace "to kirawo shi mu gaisa" na tashi na tafi part din sultan. Ya fito daga wanka yana shafa mai, na shiga da sallama, ya juyo yana kallona, ya kalli kayan jiki na yace "why are you all dress up sai kace fita zakiyi" nace "we have guests" ya kalli agogo yace "su waye?" Nace "Hajiya" take yanayin fuskarsa ya chanza, ya ajiye tiraren hannunsa yace "me suka zo yi?" Na karaso na dauki tiraren ina fesa masa nace "zuwa sukayi mu gaisa suga gidan mu si saka mana albarka" yace "bull shit" na shiga closet na dauko masa wata doguwar riga na taimaka masa ya saka, sannan nace "please sultan, don't give them abinda sukazo nema. Kaje kawai ka gaishe su sai kayi dawowarka daki". Da kyar na samu ya biyo ni hannunsa cikin nawa, muna shiga palon duk suka juyo suna kallon mu, nima kallon nasu nake daya bayan daya ina studying din kowannen su. Khulsum kallo daya tayi mana ta dauke kai, she obviously still loves sultan and is jealous, matar da suke tare da hajiya ta danyi blushing alamar taji kunyar ganin hannuna ha sultan ya rike, Hajiya kuma gaba daya hakoranta a waje tana murmushi, tace "yaron kirki, da fatan bamu tashe ka daga bacci ba" yayi kamar bazai amsa ba sai kuma yace "ban kwanta ba ai dama" ya zauna a kasa na zauna a gefensa, yace "barkan ku da yamma" suka amsa su biyi a tare, bai kalli inda khulsun take ba, Hajiya ta fara masa jawabin abinda ya kawo su, ni kuma nayi using wannan opportunity din na fara studying dinta, she looks so calm and happy on the outside, duk wanda ya ganta zai dauka duniya babu wanda take so sama da sultan, but inside she is full with hatred, she is boiling witj bakin cikin ganin mu tare da sultan, a lokacin na kara fahimtar komai. Hajiya may not be responsible for rabuwar iyayen sultan, amma ta tsane shi, tsana ta sosai, she may not be dalilin daya raba sultan da mahaifinsa in da first place but tana da hannu wajan kara huruwar wutar al'amarin. She succeeded so far, amma yanzu na shigo cikin rayiwar sultan kuma sam bata jin dadin changes din da sultan yake samu, tana kallona a matsayin wacce tazo zata tarwatsa mata plans dinta. Tasan ba zata samu nasara akan sultan ba sai ta raba shi dani, and she plans on doing that. Sai kawai na samu kaina ina murmushi, nayi studying psychology ne saboda haushin yaudarar da nake tunanin Ibrahim yayi min, amma sai gashi ilimin nawa ba akan Ibrahim yake min amfani ba akan Sultan ne. Allah mai tsara lamarin sa yadda yaso kuma a lokacin da yaso. Na dawo da hankalina kan maganar da take cewa naji har yanzu fada take yi mana akan mu zauna lafiya mu bawa marada kunya. Tana gamaws daya matar itama tayi nata, daga ni har sultan babu wanda yace musu komai. Suna gamawa sultan ya mike yayi musu sallama ya koma part dinsa. Bayan ya tafi matar da suka zo tare ta kalli khulsum tace "me yasa baki gaishe shi ba? Ba mun gaya miki cewa maganar nan ta wuce ba? Ya kamata ki manta da komai ku cigaba da zumuncin ku" gaba na ne ya fadi saboda nasan wata maganar suke son fada min kuma daga dukkan alama ba zata yi min dadi ba, ban dago kaina ba ballantana in nemi ba'asin me take nufi da maganar ta. Jin bance komai ba sai ta cigaba da cewa "Maimunatu gwara kiji daga bakin mu kar wani ya gaya miki kiga kamar mun boye miki. Tun khulsum tana yarinya karama sultan yake son ta, babu yadda baiyi ba abashi aurenta iyayen mu suka ki saboda a ganin su babu uban da zai yarda ya hada 'yarshi aure da yaro irin sultan. Hajiya babu yadda batayi ba akan iyayen mu su yarda da auren amma suka ki. Bakin cikin abin ne ya saka shi ya fara shaye shaye. Daga baya da yaga da gaske ake ba za'a aura masa ita ba shine yayi kokarin bata mata rayiwarta, Allah ya taimake ta bai ci nasara ba" kallonta kawai nake yi ina tunanin how can someone, mai shekaru kamarta, lie like that? Murmushi na tattaro na dora akan fuskata nace "na sani, ya gaya min komai daya faru tsakanin su, and I still love him".
N
Episode Seventy Seven : Amina
Kadan ya rage dariya bata kubce min ba saboda ganin reaction din fuskokin su. Sam ba haka suka yi tsammani, su a tunanin su babu matar da za'a gaya mata irin wannan maganar ta hadiye sannan ta bayar da amsa irin wacce na bayar. Hajiya tace "kin sani? Kina nufin ya gaya miki exactly wannan maganar?" Ita kanta tasan cewa nasan karya suke yi, Nace mata "eh ya gaya min, ai baya boye min komai. Ya gaya min komai na labarin sa har labarin asalin fara shan giyarsa" a take naga kalar idonta ya chanza, murmushin fuskarta ya kau. I got her exactly where I want her. Na gyara zamana na harde kafafuwa na irin zaman da Sultan yake yi, na cigaba da cewa "nasan komai akansa, nasan duk abinda ya aikata a baya nasan kuma wanda bai aikata ba, nasan kuma abinda zai aikata nasan kuma abinda bazai aikata ba" daya matar tace "kuma duk kinsan halayensa kika yarda kika aure shi? Shi fa aure ba abu ne na wasa ba, in kika auri mutum kamar kin zabe shi ne ya zama uban 'ya'yan ki" nayi mata murmushi nace "ai in kana so kasan mutum, ranki ya dade, ba wajansa zaka kalla ba, ko kuma abinda mutane suke fada akan sa ba. Abinda zaka kalla shine his inner self, deep down waye shi. Sultan deep down is a good person, very good person, ni na gani kuma nayi niyyar fito da wannan goodness din nasa waje yadda kowa zai gani. Alhamdulillah, na fara samun nasara, dan duk wanda yasan sultan shekara daya data wuce in ya ganshi yanzu yasan da akwai banbanci. Wata rana ina fatan kuma zaku ganshi kamar yadda nake ganinsa." Sai a sannan Khulsum tayi magana bayan tayi tsaki tace "tana magana kamar wata psychologist" na juya na kalle ta nace "I am a psychologist, I have a first class degree in psychology from the second best university in the world. I know exactly when someone is lying to me. I can read your mind as well as I can read time from an analog clock" na bi fuskokin su da kallo, kamar an tsiyaye musu jinin su daga jikinsu, na hango kiyayyata karara a rubuce akan fuskokin su. Kusan minti biyu babu wanda ya sake cewa komai a cikin mu. Hajiya ce ta kirkiro murmushi tace "ku tashi mu tafi, mun bar ango yana ta jiran amaryarsa" Khulsum ce ta fara tashi ta fita ba tare da ta kalli inda nake zaune ba. Har mota na raka su na daga musu hannu sannan suka tafi. At least nasan yanzu tsakanin mu is clear, babu munafunci babu yaudara. Ba zasu sake zuwa su ce zasu gaya min wata magana akan Sultan ba, amma kuma nasan na kunno wata wutar kuma. Na gaya musu nasan secrets din su dan haka na kara wutar kiyayyarda suke yi min. But am ready, Allah yana tare dani and am not scared. Na yarda da Allah na yarda da kaddara, nasan su basu isa suyi min komai ba, duk abinda ya same ni daga Allah ne ba daga gare su ba. Kuma komai nisan jifa kasa zai dawo, duk kuma abinda ka shuka shi zaka girba, in khairan khairan in sharran sharran.
Ina komawa cikin gida na koma part dina nayi wankan da ban samu nayi ba, ba fito na shafa special mai na, na kuma fesa turaruka daban daban. Na shiga closet dina, na jima ina neman kayan da zan saka, daga baya na dauko wasu deep red kaya, robber, three quaters wando da half vest. Na saka su ba tare dana saka komai a ciki ba. Ni kaina dana kalli madubi sai da naji kunyar kaina, kayan sun bi jikina like a second skin, kalar ta kara fito da haske da kuma kyan fatar jikina. Na dauko deep red lip stick na shafa a lips dina. Na dauko dogon hijab har kasa na saka, sannan na fita. A palon sa na tarar dashi, yana zaune da fararen singlet da gajeran wando a jikinsa, ya kunna TV ya rike remote a hannunsa amma kuma ba kallon yake ba, yayi nisa a tunani yana kallon sama. Na jima a tsaye ina kallonsa amma bai ma san na shigo dakin ba. Na dan daga murya nace "wanne film kake kallo ne?" yayi sauri ya kalle ni sannan ya kalli TV din, ya daga kafada yace "I don't even know wanne film suke yi. Ba'kin naki sun tafi ne?" Ban bashi amsa ba, ya fara kokarin chanza station, na chire hijab din jikina a yar a gefe nace "pss" ya juyo da sauri yana kallona, a hankali remote din hannunsa ya zame ya fadi kan carpet, ina kallon idonsa naga duk wani tunani da wata damuwar sa suna disappearing har sai da ya zamanto babu saura. Ya saki ido da baki da hanci duk yana kallona, a hankali ya furta "ya Ilahi save me, wannan rayinyar so take ta haukata ni" sai kuma naji kunya nadan rufe idona kadan da hannayena wadanda suka sha jan lalle tun na biki na. Yace "come here" babu musu na taka naje gabansa na tsaya, tun daga fuskata ya fara kallona har 'yan yatsun kafata. Ya hadiye wani mugun yawu daya sa na kara jin kunyar sa. Ya gyara zamansa yace "sit here" yana nuna min cinyarsa, nan ma babu musu na zauna. Ina zama na fahimci sako na ya samu karbuwa dan message din yaje har inda nake so yaje, na danyi dariya kadan, ya saka hannu yana shafa bare fatar cikina, murya can kasa yace "dariya kike yi min ko? Zan rama ne nima" na saka hannayena duk biyun na zagaye wuyansa sannan nace "sai dai ka rame" yayi murmushin gefen baki yace "really? Wanna bet?" Nace "yes" ya dora hannunsa akan kirjina ya fara shafawa a hankali, na lumshe ido na jikina yana amsar sakonsa na bude su akan fuskarsa mai dauke da murmushin mugunta yace "you still wanna bet?" Wannan karon ban bashi amsa ba, ya cigaba da abinda yake yi, nace cikin sarkewar murya, "ka takura musu da yawa fa" ya dan bata fuska yace nine na takura musu ko sune suka takura min?" Ya saka both hannayensa ya kama straps din half vest dina ya jawo ta kasa ya dawo da ita kan cikina, yace "better, yanzu sai muga waye ya takura wa wani a tsakanin ni da su" ina kallon cikin rinannun idonsa nace "in suka rame bashi kenan ba" yayi replacing half vest din da hannayensa yana kara lumshe ido, yace "wa yace miki ramewa zasuyi? A cikin 'yan kwanakin nan baki ga har girma suka kara ba sabida kulawar da suke samu? Nine dai nake ramewa saboda takura min da suke yi, sun hanani sakat, sam bana iya dauke ido na daga kansu, bana samun nutsuwa sai ina tare dasu, in ido na biyi tunanin su nake, in bacci nake mafarkin su nake......" Tun ina jin abinda yake cewa ina kuma fahimta har na daina fahimtar abinda yake cewa, na daina fahimtar komai, shima kansa mai maganar bana jin yana fahimtar me yake cewa, daga baya ma maganar ta gagara gaba daya. Mun manta da duk abinda ya faru a ranar, babu Takawa and his threats, babu Hajiya and her hypocrisy, babu khulsum and her food, a lokacin hatta Mommy da Daddy basa gabana, Sultan ne kadai a gabana, only him existed in my world kamar yadda shima ni kadai ce a tasa world din. Sai da akayi first round aka zauna break sannan na bashi labarin yadda mukayi dasu Hajiya, ban boye masa komai ba na gaya masa duk abinda suka ce min da amsar dana basu. Kamar yadda nayi tsammani, bai nuna damuwar sa koya tada hankalinsa ba sam, sai nuna min jin dadinsa da yayi akan yadda nayi tackling maganar da kuma trusting dinsa da nayi. Daga nan muka bar maganar muka cigaba daga inda muka tsaya. Hint ga matan aure, irin wannan time din shine best time discussing sensitive issue da mai gida, especially mai gidan da yake da temper ko kuma wanda baya daukan shawara, a lokacin he is relaxed, in body and in spirit, kan sa is fresh,and he is very excited, da wahala ki fadi abinda zai bata masa rai a lokacin. Amma fa bance ayi using time din wajan roko ba, ko kai tsegumin kishiya ba, gwara ayi amfani da time din gurin bawa mai gida shawara mai kyau wacce zata kara kafa miki fadar ku a gurinsa.
Washegari kamar yadda Sultan ya saba, in ya tafi masallachi baya dawowa sai gari ya waye, wanda na lura yana zama ne acan yayi karatun al'qurani, ni kuma wannan time din nake using in gyara dakunan sa, mostly daga nan bacci muke koma wa amma yau kitchen na tafi na barshi, yana ta mita wai shi bai ga amfanin in ce sai na koyi girki ba, tunda dai shi zan ke yiwa girkin nan kuma yace baya so ba shikenan ba sai in hakura. Ina shiga kitchen na tarar already Asma'u tana ciki, yau ma cewa tayi in cigaba da watching and learning, tana yin komai tana yi min bayani, ni kuma na bude kaina sosai ina fahimta, in naga abin tambaya in tambaya, har muka gama komai muka jera a dining sannan na tafi zanyi wanka. Ina shiga dakina wayata tana fara ringing na duba naga Daddy. Duk da cewa tun da nazo gidan kullum sai ya kirani ko kuma ni in kira shi mu gaisa amma yau sai da naji gaba na ya fadi. Nayi bismillah na dauki yawar, muryarsa naji wasai babu alamar damuwa a cikin ta, na sauke ajjiyar zuciya na gaishe shi, mun jima muna hira yana gaya min gobe zai tafi England kuma zai dan jima kafin ya dawo, nayi masa addu'ar fatan alkhairi, sai da muka gama maganganun mu sannan yace "jiya da daddare ai nazo palace, mai martaba sarki ya kira ni akan maganar ku, ya nuna min wasu pictures da banji dadin su ba, amma abinda na sani shine na yarda dake, tunda har baki kira ni kin gaya min menene ya faru ranar nan ba hakan na nufin kina ganin zaki iya handling koma menene, amma ina so ki sani, as much as I like sultan I like you more, amma hakan ba wai yana nufin bana son sultan ba, ina sonsa sosai kuma ina alfahari da abinda kike yi a rayuwarsa, but be very careful my daughter, your picture with a gun almost give me a heart attack, idan kinga abin yana kokarin yafi karfin ki just give me a call, ko ina kasar nan ko bana kasar nan I will always be there for you. Idan wani abin ya same ki a dalilin auren nan I will never forgive myself, saboda ni na amince ba saka ki a ciki duk kuwa da sanin sarkakiyar da take ciki. Zan yi yawa da Sultan din shima zamuyi magana dashi." A hankali nace "to Daddy, nagode. Allah ya saka maka da mafificin alkhairi" yace "Ameen" na jima a zaune a gurin bayan mun gama wayar, kawai sai naji hawaye suna zubomin bansan dalilin su ba. A duniya mutum bazai taba samun mai sonsa ba sama da iyayensa, kuma babban dace a duniya bayan kasancewarka musulmi shine samun iyaye na gari. Iyaye na gari sune ginshikin samun rayuwa ta gari.
Amina
Tun ranar da tabar gidan Moon kullum sai ta kira number din Ibrahim sau ba adadi amma har yanzu bai dauka ba. Wani lokacin sai ta ji haushi ta jefar da wayar tace yayi wa kansa, amma kuma in ta huce sai ta kuma dauka ta kira shi, still no response, kuma karin jin haushinta shine number din tana shiga dauka ne ba'a yi. In tayi tunanin ta rabu dashi kawai sai kuma ta yi tunanin to ko bashi da lafiya ne, he might be dying on a hospital bed ko kuma alone a gida for all she knows. Ranar dai da akayi kwana biyar ta shirya da niyyar yau dai zata yi finding out ko ma menene ya same shi. Ta shirya tsaf ta hau sama dakin Mommy ta gaya mata zata fita tana son siyan wasu 'yan kaya, Mommy ta bata kudi tace kuma ta dauki driver amma kar ta dade. Tana shiga mota ta gayawa driver supermarket din Ibrahim, tasan dole zata samu labarin sa a gurin staff din gurin. Tana shiga ta danyi 'yar siyayyar ta kadan tazo gurin cashier ta biya sannan tace "please manager dinku kuwa yana nan? I am a friend of his ina son ganinsa" matar ta danyi jim tana tunanin me zatace sannan tace "eh yana nan ma'am, amma I don't know ko zai ganki, in kina da number dinsa ki kirashi mana in yace ki shiga kinga shikenan" Amina tace "ai number din nasa bata shiga ne, I would have call him, just ki je kice masa Amina tazo tana son magana dashi" matar tayi saurin girgiza kanta "am sorry ma'am, bana son inyi laifi" Amina tace "OK, just show me ina office din nasa yake sai inje ni kadai" nan matar tayi mata kwatance. Ta hau saman benen da aka nuna mata tana kallon kofar offices din da suke a jere, a kofa ta uku taga an rubuta "manager" sai data sauke ajjiyar zuciya sannan tayi knocking, babu response, ta sake yi sannan ta murda hannun kofar, ga mamakin ta sai ta ji kofar a bude, ta tura ta shiga da sallama. Yana zaune akan kujerar sa yana danna laptop din gabansa. Looking as handsome as ever. Ya dago idanunsa ya dora akanta, sanyin AC office din ya saka ta dan rungume hannayenta tana shakar daddadan kamshin sa. Bai ce mata komai ba kawai ya zuba mata idanu. Ta dan kirkiro murmushi ta karaso gaban desk din sa, tace "Can I sit down?" Nan ma babu amsa, ta dan zauna tana kallon haduwar office din, ta na feeling nervous, damn you Moon da kika saka nayi miki wannan alkawarin. Kamar daga sama taji yace "What do you want?" Ta juyo a tsorace tana kallonsa, babu dariya sam a fuskarsa, zuciyar ta taji ta fara tafasa, a ranta tace "what am I even doing here? In Moon tana son ta san halin da yake ciki she should come by herself" ta mike tsaye cikin zafin rai tace "am sorry I bother you" da sauri ta fice daga office din kamar zata tashi sama. Har ta fara sauka stairs din sai kuma tayi wani tunani, wannan mutumin kar fa ya dauka wai ta damu da shine ya saka take ta kiran sa a waya kuma har tazo office dinsa, da sauri ta koma saman, ba tare da sallama ba ta kuma bude kofar ta tsaya a bakin kofar tana kallonsa tace "ba wai dan na damu da kai nake kiranka a waya ba, ba kuma wai dan na damu da kai nazo office dinka ba har da zaka wulakanta ni. Moon ce ta roke ni inyi haka, har kasa ta durkusa akan guiwoyinta sannan na yarda zan yi, dan haka save your arrogance for her not me, ka tattara duk wani guntun wulakancin ka and shove it up your handsome face" tana gama fadin haka ta buga kofar da karfi ta juya ta tafi tana murmushin jin dadin ta rama wulakancin da yayi mata, sosai taga yadda expression din fuskarsa ya chanza sanda ta ambaci sunan Moon, ita wannan soyayyar mamaki take bata. Ji tayi ya bude kofar da sauri ya biyo ta, bata waiga ba taci gaba da sauka stairs din yace "Amina wait please" ta juyo tana kallonsa tace "saboda me? Saboda kaji nace sakon Moon ne zan gaya maka? Wait, ya akayi ma kasan sunana? Ka yiwa kanka ai, zan koma in gaya mata kace baka son jin komai daga gareta" ta juya ta cigaba da sauka, tana jin sa ya biyo bayan ta yana kiranta amma bata waiga ba, tana gama sauko wa tayi hanyar fita, sai da takai bakin kofa sannan ta juyo, bai biyo ta ba, the mighty manager ba zai zubar da ajinsa a gaban yaran sa ba. Ta fita ta shiga mota suka koma gida. Tana ta tunani a ranta, wannan wacce irin soyayyace haka, wanne irin so ne Ibrahim yake yiwa Moon, duk da cewa kiri kiri moon ta zabi Sultan, duk irin abinda ya faru ranar nan amma har yanzu mare ambaton sunan ta ya chanza masa lissafi. Ita kam bata jin zata iya yiwa wani irin wannan son. Ta fara tunanin abinda ya faru ranar da aka kai Moon, bata taba tsammanin wai maganar zata wuce shikenan kamar ba'a yi ba, amma Moon wai ko Daddy ta hana a gaya wa, wanne irin so ne haka itama Moon take yi wa Sultan?.
Tana shiga gida ta dauko wayar ta, 6 missed calls from Ibrahim. Dariya tayi a bayyane, she got him right where she wants him, sai ta rama duk abinda yayi mata, sai ta ja ajinta san ranta. Kwanan su biyu a haka, ya turo messages sunfi a kirga, ya kira ta sau ba adadi amma bata kula shiba. Ranar kwana na ukun dai ya gaji, zuciyar sa tana ta yi masa sake saken menene sakon Moon din da Amina zata bashi? Is she OK? Kar dai ace wani abun ya faru da ita ranar nan bayan tafiyarsa. Yana tashi daga office ya biya ta restaurant ya ci abinci daga nan gidan su Moon ya wuce, direct ya doshi gate din gidan yayi horn, mai gadi ya leko ya ga motar bai bude gate din ba ya fito ya taho gurin sa, ya sauke glass din sa yana kallon mai gadin yace "Amina tana na kuwa" mai gadi yace "eh tana nan" ya cigaba da kallonsa, Ibrahim yace "zan iya shiga in ganta ko kuma in tsaya anan za'a kirawo min ita?" Da da sauri mai gadin yace "a'a bara a bude maka ka shiga ciki" still amma yana kallon Ibrahim, sai kuma ya dan yi gaba kamar zai tafi ya kuma juyowa ya kalli Ibrahim, sai ya dawo da baya, yace "ni kuwa bawan Allah kamar kaine ka taba zuwa nan a shekarun baya ka bani sako in bawa maimunatu" Ibrahim yaji yawun bakin sa ya bushe, yace "eh nine baba, ashe baka manta ni ba" baba habu ya washe baki yace "yauwa har naji dadi, ai bana manta fuska, in dai naga mutum ko mai tsahon shekaru ina iya gane shi" ya danyi shiru sannan yace "abinda yasa kaga na tambaye ka shine, bayan na bata sakon, lokacin zasu tafi England, ta bani wata katarda tace in baka. Tunda kuwa suka tafi kusan kullum sai ta kira ni ta tambaye ni kazo? Daga baya ni nace mata ta hakura ta daina kira, in kazo da kaina zan kira ta in baka ita kuyi magana" Ibrahim ya jingina kansa a jikin kujerar motar ya runtse idonsa yana jin zafi a ransa, baba habu ya cigaba da cewa "ina fatan dai ba wajan ta kazo ba yanzu ba, saboda anyi auren ta satin daya wuce" Ibrahim ya bude idonsa yace "No, ba wajanta nazo ba, wajan Amina nazo, nasan anyi bikinta. Amma baba takardar da ta baka tana nan kuwa har yanzu?" Baba habu ya danyi tunani yace "ai shekarun ne da yawa, amma zan duba maka, inna ganta kafin ka tafi sai in baka" daga nan ya bude wa Ibrahim gate ya shiga sannan ya tafi kiran Amina. Tun da Ibrahim yayi packing idonsa yake rufe yana jin dachi a ransa. She trusted that he will come back shi yasa har ta bayar da letter tace a bashi idan yazo, amma bai zo din ba, he imagine her pain, calling day after day tana tambayar ko yazo? Amma kullum amsar shine bai zo ba. Tace masa five years tayi tana jiran sa, a cikin five years din nan bata taba yin ko da saurayi ba, shi take jira duk kuwa da tasan cewa shi yayi aure. Ya dafe kansa da yaji yana sara masa. Ya bude ido yana kallon gidan, wannan shine karo na biyu daya shigo gidan nan, ya tuna abubuwan da suka faru a zuwansa na farko, a karshe ya juya ya tafi ya bar hawaye yana zuba a idon maimunatu. Ji yayi duk ya tsani kansa. Ta madubi ya hango ta ta fito tana kalle kalle, gabansa yaji ya fadi, she looks so much like Moon, but she isn't Moon. Ya danna horn ta juyo ta kalli inda yake, tana zuwa dai dai window dinsa ta bata rai ganin shine, ya rike kugu tace "what do you want?" Exactly abinda ya gaya mata a office dinsa, bai bata amsa ba ya turo ko fa ya fito, ya jingina da motar ya rungume hannayensa a kirjinsa ya zu ba mata ido. Sai kuma ta kasa kallonsa ta juya tana kallon gefe, sai da ya gama tsare ta da ido sannan yace "na horu haka, ayi min afuwa, nayi kuskure ba zan sake ba" ta juyo tana kallonsa tace "me kayi?" Yace "laifuffuka na ai suna da yawa, na farko I used you to get into Moon's home, na biyu I ignored your calls, na uku I treated you badly a office dina" Ta dan so tayi murmushi amma ta maze tace "shine abinda ya kawo ka? Ai na dauka kazo kaji sakon da Moon ta bani in gaya maka ne. To tunda ka gama fadar abinda zaka fada ni bara in koma gida" yayi sauri ya tari gabanta yace "to ai baki ce kin hakura ba" ta murguda masa baki ta sake yin gaba, sai kuma ta juyo "au ba zaka tambaye ni sakon Moon din ba" ya girgiza kansa yace "just tell me if she is OK" tace "she is more than OK. Amarya ce fa ko ka manta" daga haka tayi komawar ta gida. Ya danyi murmushi yana jin dadi a ransa, at least maimunatu is OK, she loves mijin da ta aura, abinda ya faru ranar ya tabbatar masa da haka, abinda ba shi da tabbaci a kai shine idan shi mijin nata yana son ta kamar yadda take son sa. Ya koma motar sa ya tayar ya koma bakin gate, yana zuwa baba habu ya kawo masa wata 'ya karamar envelope, yace "ka ganta kuwa na gani" ya karba yayi godiya ya saka a aljihun sa ya tafi. Bai bude letter din ba sai da yaje gida ya gama duk abinda zaiyi yayi shirin kwanciya sannan ya dauko takardar ya bude;
Dearest Ibrahim
I may not be around when you come back. Please give the man who gave you this letter your new phone number and I will call you.
I miss you
Maimunatu.
Ya ajiye takardar ya dafe kansa da hannayensa biyu yana jin garin yana juya masa. Ya tuna yawan zurga zurgar da ya ringa yi zuwa unguwar su maimunatu, amma Allah bai taba bashi ikon karasawa gurin mai gadin su ba, all this while wannan wasikar tana ajjiye, da ace ya karasa gurin mai gadin ya karbi wasikar ya karanta da duk wata karya ta Amira ta kare. Ba Amira ce ta raba shi da Maimunatu ba, Allah ne ya raba su, saboda ya riga ya kaddara cewa babu aure a tsakanin su. Ya jingina kansa a jikin frame din gadon for some time, sannan ya mike zaune ya dauko wayarsa yayi dialing number din Amina, ga mamakin sa sai yaji ta dauka, bata gaishe shi ba tace "what do you want?" Yace "har zan kwanta na tina baki ce kin yafe min ba har yanzu" tace "to sai na fada? Tunda kazo gidan mu kaga na fito ai na hakuran kenan ko" yace "thank you" tace "good night then" yace "wait. In really kin hakura can we be friends then?" Ta danyi shiru sannan tace a hankali "am not Moon" yace "I know" tace "ok, friends then" yace "to kiyi min dariya mana inji sai in yarda mun zama friends din" tace "I don't have dimples" yace "I know".
Episode Seventy Eight : The Storm
Bayan Wata Uku
Rayuwa tana tafiyar mana sosai cikin jin dadi. Dan ni kam a bangare na bani da problem. Su Hajiya tun ranar da suka zo na kora musu bayani basu sake dawowa ba, su fa'iza su na dan zuwa kadan kuma sam ban taba daure musu fuska ba. Amira ma ta dawo twice, mu kan danyi hira kadan amma sam ba kasa sake wa da ita kamar da, mun koma kamar strangers. Kullum kuma in tazo bata da zance sai na aure, ta gaji da zaman gida yanzu aure take so dan yanzu kullum suna cikin samun sabani da mamanta. A bangaren Sultan kuma tunda ya koma aiki ya zama busy, dan kullum sai dai akai masa lunch dinsa office, sai bayan la'asar yake dawowa, amma kuma in ya dawo din in ba dole ba baya fita ko kofar gida sai dai in zashi masjid, kullum company sa kara habaka yake yi, dan yanzu da kansa yake karbar kwangilar gine gine yana yi, na government ko kuma na private mutane. Sultan ya rike addini sosai dan har mamaki yake bani yanzu, karatun qur'ani kam kullum sai yayi safe da yamma, wani lokacin na yamman muyi tare. Ni kuma babu abinda nake yi a gida sai koyon girki, dan a yanzu Asma'u tafara bari na ina yin abincin da kaina, sai dai ta dan ci gyarana kadan, a raina nakan ce 'ashe ma abin babu wahala, kawai sa kai ne' tun daga kan main dishes, snacks, drinks babu abinda asma'u bata koya min, tace so take yi in na fara yi wa Sultan girki duk abincin da yaci idan ba nawa bane ya ji ci salam. Duk abinda kuwa na dafa ko sultan baya nan sai na ajiye masa na bashi yayi tasting, Sultan kam ko abin bai yi dadi ba cewa yake yi yayi dadi duk da nasan wani lokacin alkunya kawai yake yi min. Soyayya tsakanin mu kuwa kullum karuwa take yi, ni da na dauka da anyi na dokin aure shikenan amma ashe ba haka abin yake ba, stamina din Sultan har mamaki take bani, dole na na yawo jakar magungunan daada na cigaba da amfani dasu. Mun je gida ranar da Daddy ya dawo daga England, tunda akayi biki na sai ranar naje gida, da gudu naje na rungume Mommy, ita kam kallo na kawai take yi dan gaba daya na chanja, nayi kiba na kara chika, fata ta har wani yellow take yi saboda haske. Sau da yawa in kawayena suka zo sukan tsokane ni suce ko ciki ne dani, amma ni nasan bani da komai, dan cikin wata ukun nan ko tsallaken period ban taba yi ba. Ranar a gida Sultan ya barni na wuni. A lokacin ne Amina take bani labarin yadda suka kare da Ibrahim, naji dadi duk da dai tace min yace bayason jin labarin sultan, kawai shi fatansa in am OK shikenan, nan take min complaint cewa he is becoming a little bit touchy, nayi dariya nace "then it is going more than I expected" ta bata rai tace "ya zaki ce haka, ina gaya miki cewa yana yawan tabani kuma kice min kina murna?" Nace "yi hakuri Amina ta, abinda nake so ki gane shine, Ibrahim was born and raised in yaroba land, they are Muslims and then they are yarobas, su a gurinsu it is nothing dan saurayi ya rike hannun budurwarsa" ta harare ni tace "waye yace miki saurayi na ne? We are just friends" Nace "OK let me rephrase my statement, su a gurinsu it is nothing dan aboki ya rike hannun abokiyarsa" yadda na fadi kalmar abokiyar ya saka mukayi dariya gaba daya, nace "nasan ki fa Amina, kuma nasan tun ranar da kika fara ganin sa kika zo kina santinsa" ta tabe baki tace "lokacin ai bansan waye shi a gurinki ba" nace "he is nothing a gurina yanzu, not even my friend, but he will soon be my brother in-law" tace "in ya daina taba ni ba" nace "ai ke zaki hana shi, next time ya rike miki hannu ki bata rai ki ce kar ya kuma ba kya so, daga ranar ba zai kara ba". Sai dare Sultan yazo daukana. Kamar ba zan fito ba saboda duk su yaya Walid suna gida ana ta hira da dariya, a nan na fara matsar kwalla wai ni dan Allah sultan ya barni in kwana sai gobe na koma, ni kaina da nake fada nasan it is impossible, dan in dai zan kwana a gida to tabbas sultan zai biyo ni mu kwana tare. Mommy ce ta rakani har mota amma ita ma kamar ba zata barni in tafi ba, muna jan mota na dora hannu aka na rusa kuka wai ni ya mayar dani gidan mu. Gefen titi ya samu yayi packing sai da ya tsotse hawayen fuskar tas sannan ya dashi motar muka tafi kuma yace in dai na sake wani kukan abinda yafi haka zai yi min ba ruwansa da cewa a titi muke. Na san zai iya aikatawa dan haka nayi shiru da baki na. Muna zuwa gida sai da ya tabbatar ya mantar dani 'yan gidan mu sannan ya rabu dani.
Ranar wata Friday muna zaune palo da asma'u da baba gaji da wasu daga 'yammata na, baba gaji tana ta bamu labaran abin dariya muna ta darawa without a care in the world, ina yi amma ina kallon agogo, nasan sultan yana hanya by now, ai kuwa ba'a jima ba sai ga shi ya shigo. Yana shigowa duk suka nutsu, haka nan sultan yake da wannan kwarjinin, duk inda ya shiga sai kaga mutane suna shakkarsa ko da kuwa bai yi musu magana ba. Ya zauna a kujera, duk suka gaishe shi sannan suka fita, nayi masa sannu da zuwa, ya amsa a hankali yana jingina kansa a bayan kujerar, na tashi na dauko masa pineapple drink din dana hada dazu, na kawo na zuba masa a cup na mika masa, bai karba ba ya zauna yana kallona, nasan me yake nufi nayi murmushi na zauna a cinyarsa na dafa kafadar sa da hannu daya daya hannun kuma na dauki cup din drink din na fara bashi a baki, sai da ya shanye cup din tas sannan ya dauke kansa, na karo masa wani na sake bashi, wannan karon a hannunsa ya karba yace "let me guess, ki kika hada wannan drink din" na washe baki nayi fari da ido nace "you guess right, this drink was made by yours truly, Asma'u bata ma san nayi ba" yace "wow, wannan matar fa so kike ki fi asma'u iya girki, kuma it is like duk abinda kikayi yana da wani unique taste na musamman" naji dadi sosai nace "thank you Darling" ya juya wuyansa, kashin wuyan yayi kara alamar gajiya, nace "you are overworking yourself honey, ya kamata ka ke rage aikin nan kana hutawa fa" ya kwantar da kansa a kirjina yace "I know, shi yasa nake shirya mana tafiya zuwa Maldives, karshen watan nan in sha Allahu" na tashi tsaye na fara tsallen murna yana ta yi mini dariya, sai da na gama murna ta na zagayo bayansa na saka hannayena biyu akan kafadarsa na fara yi masa tausa, he feels so tense, a hankali nake matsa masa kafadunsa zuwa wuyansa, yayi ajjiyar zuciya yace "God, that feels so good" na cigaba dayi masa tausar har sai da naga yayi relaxing sannan na daina na zagayo gabansa naga kamar wani abu yana damunsa, nayi kneel down a gabansa na dora hannayena akan cinyarsa nace "me ya faru ne a office din yau? Ya dan saki ransa yana murmushi yace "why did I marry a psychologist?" Nace "because you are lucky" ya shafa fuskata yace "you are damn right I am" kamar ba zai cigaba da magana ba kuma sai yace "uncle galadima ne yazo office dina dazu. Dama tun dadewa yake cewa zai kawo min ziyara. To yau yazo muka zagaya dashi yaga gurin sannan aka zauna akayi addu'ah" yayi shiru, nace "then what's the problem?" Yace "kafin ya tafi ya kirani gefe yake ce min yana son in ringa zuwa fada ana zama tare dani, wai I belong there, a kusa da Takawa. Ni kuma na gaya masa NO, I am happy now, I have you, I have my job, bani da wani problem. He still insisted wai inje inyi tunani akai" na dan jinjina maganar a raina kafin nace "to yanzu wacce shawara ka yanke?" Yace "my answer is still no. Yanzu ina zaune lafiya Takawa ya dauke idonsa daga kaina, maybe ma ya manta da existence dina, amma ina zuwa kusa dashi shikenan na zama nama, ba lallai ne ma ya barni in shiga ba, zai yi disgracing dina ne a gaban mutane kuma ni na jawowa kai na. Besides, ina shiga gurin people will think kamar I want the throne" dariya na fara yi a hankali, ya tsaya yana kallona fuskarsa da mamaki, yace "menene abin dariya kuma?" Nace "since when did Sultan care about me mutane suke tunani akan sa?" Shima dariyar ya fara yi a hankali ina taya shi, sannan yace "na chanza da yawa ko?" Na mike na koma na zauna a cinyarsa ina shafa fuskarsa nace "yes ka chanza my Darling, and I am so proud of you. Amma yanzu ka ajiye Takawa a gefe, ka ajiye abinda mutane zasu ce a gefe, tell me what you really want" ya jima yana kallon gefe yana tunani sannan ya juyo yana kallona yace "lokacin da ina yaro, lokacin kakana yana da rai, there is nothing I want more than the throne. Kullum abinda yake gayamin shine the throne is mine, kullum idan yana zaune a fada zai saka ni in zauna a gabansa, telling me to learn, saying that one day I will rule. Wannan yana daya daga cikin abinda yasa na zama so furious lokacin da babana ya daina zuwa fada dani, a lokacin ina tunanin sarauta is what I was born for dan haka karbarta kamar an cire min purpose na rayuwata ne, amma as I grow up, musamman bayan haduwa ta da ke, na fahimci cewa there is more to rayuwata than sarauta, and now I don't want it, har cikin zuciyata" tun daya fara maganar nake kallonsa kuma na fahimci har cikin zuciyarsa abinda yake fada haka ne. Nace "tunda haka kake so then that's exactly abinda zaka yi. Amma ni ina ganin no matter how much kake so kayi ditching sarauta it is in your blood. In kana ganin zaka iya why not kake zuwa once a week, kamar on Fridays, just ka gaishe shi da sauran mutanen gurin ka fito, Amir zai iya kula da companyn ka a lokacin. At least kaga galadima ba zai ga kamar ka ki daukan shawarar sa ba" ya danyi murmushi yace "in dai hakan shine abinda my Queen tace to hakan zanyi. But not Amir, sai dai in sami wani, Amir hasn't been himself lately" naji babu dadi nace "why? Me ya faru dashi?" Yace "akan wata yarinya ne da yake nema. Sunanta Aisha, 'yar maiduguri ce, tazo bikin cousin dinta garin nan suka hadu suka fara soyayya, bayan ta koma gida har maiduguri yake zuwa gurinta, wajan shekarar su daya kenan tare. To yanzu sai iyayenta suka ce ta fito da miji ita kuma tace shi take so, aka aiko wa aunty din ta tanan garin akan ta bincika waye shi, the first thing da tayi finding out shine babu wanda yasan iyayensa, a kofar orphanage aka tsince shi ko cibiyarsa ba'a yanke ba. Suna jin haka suka aiko masa cewa kar ya sake zuwa gurin 'yarsu, su ba zasu bada 'yarsu ga wanda bashi da asali ba. And that break him down, bai taba nuna damuwarsa ga rashin iyayensa ba sai yanzu, lokuta da yawa yana mayar da maganar kamar wasa amma yanzu he is devastated, it hurts me that there is nothing I can do for him" naji kamar zanyi kuka, naji tausayin Amir sosai, how can some parents be so cruel, ki haifi da da kanki sannan ki je ki jefar dashi? Shi yaron menene laifinsa? Shi yace ki haife shi? Ana samu kuma har da masu kashewa, wadansu su jefa a toilet, ni dai a ganina wannan shine extreme of cruelty. Allah ya shirya mu baki daya.
Nace "but da na dauka yana son Amira ne ai, har na fara tunanin idan abin yazo zan yiwa Daddy magana ya shigar masa tunda akwai sanayya abin zai zo da sauki" Sultan yace "gaskiya bai taba yi min maganar Amira ba, kullum ina tsokanarsa akanta saboda inji ta bakinsa amma bai taba cewa komai ba, wannan Aishan dai ita ce a gabansa" nace "Allah sarki Amir, Allah ya kawo masa mafita" yace "Ameen".
Tun daga lokacin Sultan ya fara zuwa fada duk ranar Fridays, ranar farko da zai je haka na zauna nayi ta addu'ar Allah ya dora shi akan mahaifinsa kar ya wulakanta shi a cikin mutane, dan nasan zuciyar Sultan, in dai Takawa ya kore shi to kuwa ba zai sake zuwa ba, tunda yanzun ma ba wai a son ransa yaje ba. Cikin ikon Allah kuwa babu abinda ya faru, sai dai kamar kullum da ya gaishe shi bai amsa ba, Sultan bai nuna ya damu ba ya gaishe da sauran mutane ya dan zauna for one hour sannan ya tashi yayi tafiyar sa. Kiri kiri ya hango bacin rai a fuskar Abbas amma bai kula shi ba, sai ya nuna kamar bai san yana yi ba. Ranar ina zaune ina jiran sultan ya dawo daga office sai ga sako daga Abbas, alkyabba da rawani, wai a bawa sultan inji shi a ce masa in dai yana son zaman fada he should dress like dan fada, nasan tsokanar fada ne, dan haka na nuna wa dan aiken kamar Sultan yana dakin sa, na shiga na fito na dawo masa da kayan nace sultan yace a gaya wa Abbas ya gode sosai, amma ya riga yayo order nasa kayan daga saudiyya, idan sun iso ma har shi zai aikowa, tunda dai hakkin yaya ne ya jagoranci gida ya kuma kula da kannensa. Ni nasan na kunna wuta a zuciyar Abbas ranar nan, Sultan yana zuwa na bashi labarin abinda ya faru, muka yi ta dariya tare dashi na kuma cigaba da rokon sa akan dan Allah duk abinda Abbas zai yi masa kar ya kula shi, dariya kawai sultan yayi bai ce komai ba.
A kwana a tashi na fahimci shigar ciki a jikina, sam babu laulayi dan ko sau daya ban taba amai ba ko zazzabi, lokacin period dina yana zuwa naga bata zo ba dan haka na tabbatar da zargina, Sultan kam da yaga babu period shi murnar sa ta daban yake yi dan kwata kwata banga alamar yayi linking abin da ciki ba. Babu laulayi a ciki na sai dan karen kwadayi, kullum ina kitchen, in soya wancan inci, in gasa wannan inci, in tafasa wannan inci. Tunda sultan baya wuni a gida dan haka sam bai san me nake yi ba, da daddare kuwa yawo nake masa in gudu daga dakinsa in tafi kitchen in ci abinda zanci in dawo. Ina ta tunanin yadda zan yi in gaya masa, duk da bamu taba yin zancen haihuwa dashi ba amma nasan yadda yake son 'ya'yansa na orphanage dan haka nasan Allah ne kadai yasan irin son da zai yiwa nasa dan ko 'yar.
Ranar wata Wednesday tun da safe nake son chocolate, sauran wadda nake da ita a gida na shanye amma kamar tayar min da kwadayi ta kuma yi, sultan yana dawo wa daga office na saka shi a gaba sai ya kaini mall na sayo chocolate, da kyar na barshi yayi wanka ya dan huta, ana yin sallar magrib na dauko bakar after dress na dora akan riga da zanin jikina, nayi rolling viel na dauki key din mota na tsaya ina kallon Sultan, ya langwabe kai yace "please Love, ki bari muci abinci mana" na girgiza kai nace "in mun dawo ma ci, yanzu fa zamu je mu dawo, ko 30 minutes ba za muyi ba. Yayi ajjiyar zuciya ya mike yace " amma ki sani, ina binki bashi, in mun dawo zan karba" a raina nace 'oho dai, ko ka kaini ko baka kaini ba dama nasan sai ka karba din'. Muna fita nace "sahad zamu je" ya dan bata rai yace "why? Kin san bana son zuwa sahad, it is too crowded" nace "naga yafi kusa ne ai, kuma ba wani special abu zan saya ba kawai chocolate ne" ya daga kafada yace "OK, bara muje can din".
Ibrahim
Tun da safe yace da Amina zai zo gurinta da yamma, dan haka yana tashi daga office gida ya tafi yayi wanka ya shirya, yana yin sallar magrib ya fito ya dau hanyar gidan su, yana shan kwanar gidan ya hango ta tana tahowa bakin titi, bakar after dress ce a jikin ta, tayi rolling mayafin rigar, kamar kullum duk sanda ya ganta sai gabansa ya fadi saboda gani yake kamar Moon ce sai ta matso kusa sai yaga ba ita bace. Yayi slowing down ya barta ta karaso inda yake sannan ya sauke glass dinsa yace "ina zuwa ne haka?" Ta dan tsorata kadan, yayi dariya ita kuma ta bata rai "tun dazu kace min zaka zo ina ta jiranka shiru" ya hada hannuwansa biyu yace "am very sorry, ban tashi da wuri bane ba kuma naga it is already late, shine na tsaya na jira bayan magrib sannan na taho. But ina zaki je kuma?" Ta dan kara bata rai tace "Mommy ce ta aike ni sahad, kuma drivers din duk basa nan" yace "to ga wani drivern yazo, common in" ba musu ta zagaya ta shiga suka tafi. A hanya yace mata "but why sahad? Ba zaki zo gurina kiyi siyayyar ba?" Tayi dariya tace "are you jealous?" Yace "of cause I am" tace "let me tell you why. Shi sahad tsohon guri ne, akwai wasu specific abubuwan da ba'a samu a wani gurin, misali sababbin guri irin naka, sai acan. Dan haka Mommy ta fada min exactly abinda take so bata son substitute, dan haka gwara inje can din direct nasan zan samu" yace "OK, zan kaiki sahad ne kawai saboda inyi proving cewa you are wrong, babu abinda suka fi mu dashi, sai abubuwan da muka fi su dashi ma" tace "OK, we will see". Suna shiga cikin sahad motar su Moon tayi packing suma suka fito duka shiga, amma kowa da side din daya nufa. Ya dauko mata basket suka fara zagaye tare tana duna list din Mommy, ya karbi list din ya duba yayi tsaki yace "babu abinda bani dashi anan wallahi" ta karbi basket din tace "ka ga in kasan zaka dame ni da mita yi tafiyar ka wani gurin, in na gama sai in neme ka" da kamar ba zai tafi ba kuma sai ya tuna cewa a matsayinsa na dan kasuwa ya shigo gurin abokin competition dinsa gwara yayi using chance din ya zagaya yaga abinda suke dashi wanda shi bashi dashi, dan haka ya sakar mata basket din yace "OK, call me when you are done". Ya tafi yana zagaya gurin, har ya fama zagayensa bata kira shi ba, yayi tsaki, su dai mata in suka shiga kasuwa sai ka rasa me sukeyi, shi kuma bai ga abinda wannan gurin yafi nasa ba. Ya juya ya koma ya fara neman ta, ko bata gama bama fita zasuyi, ko me take so suje gurin sa ta dauka.
Moon
Muna shiga direct gurin sweets na tafi, na dauki basket na mika wa sultan ya rike min, na fara chocolate verities iri daban daban ina zubawa a basket din, Sultan kawai kallona yake yi da mamaki yace "wai yaushe kika zama shazumamu ne ban sani ba? Duk wannan chocolate din me zaki yi da ita? A matsayin ki na doctor ai kinsan illar zaki ga lafiyar ki ko?" Na juyo na murguda masa baki na juya na cigaba da abinda nake yi, yace "ni ko? Zaki yi bayani ne in mun koma gida?" Mun jima ina ta diban alawa, in dau wannan in ajiye in koma baya in dauko wata, Sultan ya gaji, kuma ina sane nake kara delaying din mu, a raina ina cewa 'bani kadai zan sha wahalar cikin nan ba kai ma sai kasha' duk kuwa da cewa har yau bai san da cikin ba. Ya ajiye basket din yace "bara in zagaya wajan perfumes, da akwai wani turare da nake ne ma ban sani ba ko zan samu anan" nasan babu wani turare da yake nema, ya gaji ne so yake in ce masa ai na gama mu tafi, na juyo nace masa "OK" ya saki baki da mamaki yana kallona yace "kin yarda in barki anan ke kadai" nace "I am 23 years old, ba zan bata ba" ya juya ya tafi, har yakai karshen lane din ya juyo, nayi masa alamar bye2 ya girgiza kansa ya sha kwana. Na juya ina dariya, a raina ina tunanin maybe tonight in gaya masa labarin cikin nan, I can't wait to see his reaction. Nayi murmushi na cigaba da kwasar sweets dina.
Kamar daga sama naji an kama hannuna an fara jana da sauri, "let's go, babu wani abinda ba zaki samu ba a gurina, menene anan din wanda ni bani dashi?" Duk da banga fuskar wanda ya rike ni ba amma muryar sa ta saka na gane shi, hakan kuma ya saka ni wata irin faduwar gaban da har sai da naji daci a bakina, wani amai naji yana neman taso min, nayi kokarin kwace hannuna amma bai sake ni ba kuma bai kalle ni ba, cikin muryar fada amma kuma cikin rada saboda bana son inyi calling attention din mutane zuwa garemu nace "what are you doing?" Yayi sauri ya sake ni, lokacin har mun kai karshen lane din, a razane yake kallona, hakan ya tabbatar min ba wai yana sane ya aikata abin da yayi ba, murya kasa kasa shima yace "Maimunatu what are you doing here? Am very sorry na dauka Amina ce, tare muka zo da ita kuma itama bakar riga ta saka. Am very sorry" nace "am here with my husband, go away bana son ya gan mu tare" ya dan bata fuska yace "you look scared, why are you scared of your husband, is he mistreating you" by then gaba daya hankali na ya tashi, na juyo da sauri na matsa daga inda yake amma sai ya kuma zagayo wa gaba na, fuskarsa fal da concern, yace "Maimunatu please tell me if you are not OK" numfashi na ne gaba daya naji yana neman daukewa, Sultan na hango a farkon lane din a tsaye, da kwalbar turare a hannun sa, tun daga inda nake na hango jijiyoyi sun fito rado rado a goshinsa, farin idonsa ya kada yayi jajawur light brown din ciki kuma yayi bakikkirin, mara ta ce ta daure kamar zan yi fitsari, a hankali na furta "innalillahi wa inna ilaihir rajiun".
Winter is really coming
Episode Seventy Nine : The Lightening and The Thunder
Ibrahim ya juya shima da sauri yana kallon inda nake kalla, yace "ya salam" yayi two steps gefe, Sultan ya fara takowa a hankali yana tahowa inda muke, idanuwansa a kaina har ya karaso gabana ya tsaya, ko kallon inda Ibrahim yake tsaye bai yi ba, ga mamaki na sai naga yayi murmushi, amma murmushinsa bai rage min ko kadan daga cikin faduwar da gabana yake yi ba sai ma karuwa da yayi, I know that smile very well. Ya miko min turaren hannunsa yace "see, I got it" ban karba ba kuma bance masa komai ba, kawai kallonsa nake yi ina jiran bomb din ya tashi. Ya sali kwalbar turaren ta fadi kasa ta fashe, har yanzu murmushin yakeyi, jajayen idanunwansa har kwalli suke yi, yace "kin gama sayen chocolate din? Naga kamar basket din bai cika ba. Let me help you fill it up, in ma gaba daya sweets din gurin kike so sai in saya miki" a hankali nace "sultan not here, let's go home" yace "oh let's go home? Kin gama kenan ashe, oh na tuna fa ashe dama ba sayen sweets kika zo yi ba kin zo ne ki ganshi, kuma kin riga kin ganshi, mission accomplished, so let's go home" jin maganganunsa nake tamkar wuta a kirjina, na juya na kalli inda Ibrahim yake tsaye naga bayanan, na dawo da ido na kan sultan, yana kallona yace "baya nan ai, ya gudu, ko baki gaji da ganin sa bane inje in kira wo miki shi? Am sure bai bar building din nan ba by now" mutane sun fara tsayawa suna kallon mu, na ajiye basket din hannuna na juya nayi hanyar fita daga gurin, tafiya kawai nake amma bana ganin gaba na sosai, how can Sultan even think that? Babu komai a hannuna dan ko waya ta ban dauko ba ballan tana in hau taxi. Na tsaya a packing space din na rufe fuskata da hannayena ina kokarin dai dai ta numfashi na, kaina ya chunkushe bana iya tunanin komai. Tsayuwar mota naji a gaba na, na bude ido na naga Sultan ya fito daga seat din driver ya zagayo ya bude seat din gaba, ba tare da yace min komai ba ya chusa ni a ciki ya mayar da kofar ya rufe, ya zagaya seat dinsa ya shiga ya ja motar a guje muka bar gurin. Na hadiye dacin da nake yi a bakina nace "how can you even think that Sultan? How can you hurt me like this?" Ba tare da ya kalle ni ba yace "what do you want me to think ehh? Ke kika matsa lallai sai mun fito yanzu and you also insisted sai munzo sahad, wai zaki sayi chocolate, since when did you start eating chocolate? You also kept delaying us unnecessarily. And I also saw you holding hands and whispering to each other. Tell me what do you want me to think?" Da hannu daya yake driving din kuma a guje yake tafiya yana ta overtaking motoci. Na lumshe idona saboda kaina da naji yana bala'in sara wa nace "ya kamata a ce kasan ni by now, Sultan ya kamata a ce by now kasan me zan aikata da kuma menene bazan aikata ba" yace "I tot I know you, but when it comes to him am not sure where I stand. He is your first love, har hawan jini kika samu sanda ya gudu ya barki saboda irin son da kike masa, you waited for him years after years, sanda ya dawo it is already days to our wedding, ko kince kin fasa aure na ma kinsan it is impossible Daddy ya fasa....." Na katse shi nima cikin daga murya nace "duk wannan tsahon lokacin dama abinda kake tunani kenan?" Shima ya daga tasa muryar "what do you want me to think? Kullum mutane suna gaya min you are too good for me, and I also know you are too good for me, you always kept secrets from me..." Na juyo ina facing dinsa sosai nace "kasan dalilin da yasa nake keeping maka secrets? Kasan babban dalilin da yasa tun farko ban baka labarin Ibrahim ba? Because I know you will act exactly the way you are acting now. You always let your temper get in your head and stop you from thinking clearly. Kawai ganina kayi tare dashi, baka tambayeni nayi maka bayani ba, you just conclude and start making accusations, a cikin mutane a cikin kasuwa Sultan, I don't think koma menene nayi I deserve something like that from you, you make a fool of me and you make a fool of yourself" ban taba jin raina ya baci irin na yau ba, sam na manta da mijina nake magana, na koma na kwanta akan kujerar na dafe kaina da nake ji kamar zai tsage gida biyu, I can feel my blood pressure rising. Can kasan muryarsa naji yace "she now calls me a fool" a hankali nace "am sorry. Ban taba jin raina ya baci irin na yau ba, ban taba zaton a ranka za kayi tunanin ina son wani bayan kai ba. Yazo gurina ya rike hannuna ne saboda ya dauka Amina ce, tare suka zo gurin da ita, ba wai da gan gan yayi haka ba, bayan ya gane ni ce ya bani hakuri, he saw that I got scared and was wondering me yasa zan ji tsoron ka" da sauri ya kalle ni yace "are you afraid of me?" Nace "No sultan am not afraid of you, am afraid of your anger. In ranka ya baci you are not yourself, nasan gani na tare dashi zai sa ranka ya baci, I was afraid of what you will do" na dora hannuna akan mara ta nace "Sultan so kake ka zama mijin da matarsa take jin tsoron sa? So kake ka zama uban da 'ya'yansa suke guduwa idan sunji muryarsa?" Na juya na kalleshi amma sai naga hankalinsa baya kaina, he is busy looking at the central mirror, yace "can you now tell me why he is following us? Idan a store yayi miki magana saboda ya dauka Amina ce yanzu kuma ya biyo mu ne saboda ya dauka Amina na dauko a mota ta?" Na juya da sauri na kalli bayan mu, a las, motar Ibrahim ce a bayan tamu, na dawo da hankali na kan Sultan naga his rage is coming back, jan idon daya fara raguwa ya dawo yanzu, ya kara gudun motar, nace "Sultan please stop the car" ko kallo na baiyi ba, na koma na kwanta a kan kujerar na saka hannu daya na dafe kaina dayan kuma na dafe marata da nake jin kamar zata tsage gida biyu, a cikin zuciyata nace "hang in there baby, everything is going to be alright" na fara jero sunanyen Allah a hankali ina neman ya kawo min agaji, na jima a haka sannan na bude idona na kalli inda muke, mun dau hanyar barin gari, har yanzu gudu sultan yake yi a motar, duhu yayi sosai dan haka few motoci ne akan hanyar na juya na sake kallon bayan mu, motar Ibrahim tana bayan mu still, oh dear God, what is Ibrahim thinking, na kalli Sultan nace cikin dasashshiyar murya, "Sultan ko ma menene kake tunanin yi please don't, annabi ya hane mu da yanke hukunci idan muna cikin fushi, Sultan please don't do something da zakayi regretting for the rest of your life" bai kalle ni ba ya miko hannunsa ya saka min seat belt sannan shima ya saka nasa, danshi na fara ji a kasa na na rintse idona hawaye suna bin kuncina, yanzu titin ya zama babu kowa sai motocin mu guda biyu, suddenly Sultan ya daga handbrake din motar, a take ta fara katantanwa a tsakiyar titin, da karfi ta daki motar Ibrahim da take dab damu, motar tasa tayi adungure sau biyu akan titi sannan ta gangara gefen titin, sultan ya taka burki motar mu ta tsaya chak a tsakiyar titin, na juya ina kallon motar Ibrahim da har yanzu take ta adungure, a karshe ta fada cikin wani katon rami dake gefen titin, na juyo na kalli sultan wanda shima motar yake kallo, fuskarsa babu dariya ko kadan, a hankali yace "die, you bastard". Kara na fara ji kamar daga nesa da murya kamar tawa, amma kuma kamar bani nake karar ba, can nesa naji kamar muryar sultan yana kwalla min kira, a hankali na fara ganin duhu a idona, daga baya na daina ganin komai.
A hankali na fara dawowa haiyacina, sanyin AC naji yana ratsani. Nayi kokarin bude idona naji yayi min nauyi sosai, na motsa hannayena kadan ina son in dawo da karfin jikina, muryar Mommy naji tace " Maimoon? Maimunatu kina ji na?" Na dan bude ido na kadan na kalleta, da sauri ta taho ta rike hannuna fuskarta tayi ja alamar tayi kuka, na danyi kokarin yi mata murmushi amma ciwon da kai na yake min yasa murmushin ya zama kamar gyatsine. Na fara duba dakin da nake, asibiti ne, ga drip a hannuna, Mommy tana zaune gefena, Daddy yana tsaye a gefenta, Sultan yana daga can baya ya jingina da jikin bango, tsantsar tashin hankali ne a rubuce a fuskarsa. Motar Ibrahim na tuno yadda tayi ta adungure kafin ta fada cikin ramin. A take hawaye ya fara kwaranyowa daga idona, innalillahi wa inna ilaihirrajiun, Allah kasa mafarki nake yi yanzu za'a ce min ba gaske bane ba, amma yanayin fuskar sultan ka dai ya tabbatar min da cewa ba mafarki nake yi ba, Sultan yayi kisan kai a gaba na, Sultan ya kashe Ibrahim. Allah sarki Ibrahim why? Menene kake tunani me yasa ka biyo mu? Nasan bacin ran daya gani a fuskar sultan da yadda sultan ya fara acting a cikin store din shi ya saka ya biyo mu, he was looking out for me, amma banda abin Ibrahim koma me Sultan zaiyi min ai munfi kusa ni da shi, ballantana ma Sultan babu abinda zai iya yi min. Yanzu shikenan Ibrahim ya bar duniya, because of me, Sultan yayi kisan kai, because of me, na tuna da little Moon, na tuno fuskarta a hotonta dana gani a office din Ibrahim, she looks so happy, yanzu ta zama marainiya babu uwa babu uba because of me, sultan da yake ta faman kula da marayu kullum maganar shi bata wuce ta marayu yau muguwar zuciyarsa da bakin kishinsa ya nawo yayi making marainiya da kansa. Kuka nake yi sosai inajin ciwon kaina yana karuwa. Muryar Mommy naji tana cewa "Haba Moon, kukan menene kuma wannan? Daga rashin lafiya sai kuka? BP dinki ne fa ya hau idan baki daina kuka ba kuma tayaya zai sauka?" Daddy ya kalli sultan yace "kace a kitchen ta fadi ko?" Sultan ya dan kalleni kadan sannan ya gyada kansa ba tare da yayi magana ba, Daddy yace"amma menene zai sa BP dinta yayi wannan hawan haka? Bai taba hawa kamar haka ba" Sultan ya sunkuyar da kansa fuskarsa kamar zai yi kuka amma sultan never cries, Mommy tace "may be zafin kitchen ne dear, dama masu hawan jini ba'a so su ringa kusa da wuta sosai" Daddy ya karaso ya rike hannuna yace "maimunatu kukan me kike yi?" Kafin inyi magana sai ga doctor ya shigo, yana murmushi yace "finally ta farka ashe, ya jikin?" A hankali nace "da sauki" yace "menene kuma na kuka? The pregnancy is intact ai, munyi nasarar tsayar dashi bai fita ba" a tare Mommy da Daddy suka ce "pregnancy?" Na juyo na kalli sultan naga gaba daya fuskarsa tayi fari tas kamar babu jini, ya juyo da sauri ya kalle ni, na kalli su mommy naga gaba daya hankalinsu yana kan doctor yana musu bayani, na gyada masa kai nace "shi yasa nace ina son chocolate din" hannu biyu ya saka ya rike kansa, Mommy naji tana magana cike da fara'a tace "I suspected as much, bana son in saka rai ne ko ba haka bane inzo inji babu dadi shi yasa na dora wa zafin kitchen" doctor din ya gama yi musu congratulations ya fita, Sultan har yanzu kallona kawai yake yi sannan da sauri kamar wanda aka jawo ya taho gurina, kara na saka da duk dan karfin da ya rage min, wannan ya jawo hankalin Mommy da Daddy kaina, Mommy ta taho da sauri kusa dani tace "lafiyar ki kuwa? Ciwon kan ne?" Na nuna Sultan nace "kar ka karaso inda nake, it is over between us" cikin muryar abin tausayi yace "Moon dan Allah kar kice haka, bazan iya rayuwa in babu ke ba mutuwa zanyi please" nace "then so be it" bai hakura ba ya sake taku daya, na dunkule hannuna na daga dai dai kan mara ta nace "kana kara wani takun zan fitar da abinda yake cikina in baka kayanka" a tsorace ya tsaya, he looks scared, I have never see Sultan scared tunda na san shi. Mommy ta rike hannuna da sauri tace "baki da hankali maimunatu? Me ya hada ku haka?" Fuska ta babu alamar wasa kwata kwata, na kwace hannuna daga hannun Mommy na kuma dagawa a saman mara ta, da sauri sultan ya ja baya, yanayin fuskarsa kadai ya isa ya saka mai karamar zuciya ya fashe da kuka. Daddy ya tafi kusa dashi yana cewa "Sultan me ya faru?" Bai amsa ba ya juya da sauri ya fice daga dakin.
Yana fita na kifa kaina akan pillow na fara rera kuka, Allah kai kasan me kake nufi damu, Allah ka shiga lamarin mu. Ko kadan abinda Sultan ya aikata bai chire min ko digo na soyayyarsa daga raina ba. Amma abinda na fahimta shine; Sultan is too hard for me to break, diamond ne shi kafin a narka shi sai anyi amfani da ice da fire, I have used the ice bai yi min amfani ba, now I have to use the fire. Daddy ne yazo ya zauna kusa dani yana shafa kaina yace "Maimunatu talk to me" na dago kaina naga Mommy tana ta sharar kwalla, na runtse idona ina tuna duk abubuwan da suka faru a ranar, na kwalli agogon bangon dakin naga 3:30 na dare, hakan yana nufin an dauki hours da yin abin, hakan yana nufin Ibrahim yayi spending hours a cikin ramin day fada, wani kukan ne ya taso min, na dora kaina a kafadar Daddy nayi mai isa ta sannan na share hawaye na, tiryan tiryan na basu labarin duk abinda ya faru, na karasheda wani kukan "yanzu Daddy sultan ya kashe Ibrahim, ya zanyi? Shima hukuncin kisa ne akansa in aka san maganar nan, idan kuma nayi shiru ban fada ba kuma kamar na daure wa cin zali gindi kenan, ya zanyi Daddy? Mommy ki taimaka min" Mommy ta jawo ni ta rungume ni tana kuka tana salati "mun shiga uku mun lalace ni Fatima" Daddy kuma cike da mamaki yace "waye shi Ibrahim din ne?" Mommy tace "wannan copper din da yake sonta da a makaranta" Daddy yace "That yaroba guy?" Kai kawai na gyada masa, yace "a dai dai ina abin ya faru? Kamata yayi muje first mu dauko shi, maybe yana da rai yana bukatar taimako, in ma bashi da ran kamata yayi ai muje mu dauko shi" nayi musa kwatance ya mike yace "bara in nemi sultan shima inji me yake ciki, I don't want him hurting himself kuma" na girgiza kaina nace "he won't. He would want to see his child".
Tunda Daddy ya fita babu wanda yayi magana ni da Mommy, kowa da abinda yake zuciyarsa. Mun jima sannan naji Mommy ta fara yi min magana, ga mamaki na maimakon inji tana fadan abinda Sultan yayi sai naji tana addi'ar Allah yasa babu abinda ya sami Ibrahim. Muna cikin haka wayar ta tayi kara, ta dauka tace " wannan number ce ma babu suna, waye zai kira ni cikin daren nan kuma" ta daga tare da sallama, take naga yanayin fuskarta ya chanza, tace "Amina slow down kiyi min bayani yadda zan gane. Kina ina?" Ta jima tana sauraron Amina tana kuma kallona, na mike zaune ina jiran inji abinda ake gaya mata, tace "OK, kinyi kokari sosai Amina, ki zauna anan inda kike bara in kira daddyn ku in gaya masa" ta kashe wayar, bata yi min magana ba sai tayi dialing number din Daddy tace "ba sai kunje gurin ba dear, su Amina sun dauko shi sun tafi dashi general hospital. Yes, he is alive, zan yi maka bayani later" ta kashe tana kallona, wata ajjiyar zuciya na saki na koma na kwanta, duk da bansan details din me ya faru ba amma na fahimci cewa Ibrahim is alive, wannan information din kadai ya isa ya kwantar min da hankali. At least Sultan is safe now, amma kuma dole zai fuskanci hukunci daga gurina, sam ba zan yi masa da wasa ba, he must learn to control his temper especially yanzu da zamu fara ajjiye zuri'a. Daga baya Mommy tayi min bayanin cewa ashe duk abinda ya faru a store Amina ta gani, taga fitowa ta da kuma fitowar Sultan, bayan ta fito itama waje sai taga tafiyar mu a guje, sai kuma taga Ibrahim ya biyo bayan mu shima a guje, shine taji tsoron kar wani abin ya faru ta hau taxi tace yabi yaban mu, munyi musu nisa dan haka basu ga sanda abin ya faru ba amma sunga motar mu tana juyowa amma bata ga ta Ibrahim ba, suna zuwa gurin suka ga alamar anyi accident, ita da mai taxi suka fito sannan suka ga inda motar Ibrahim ta fada, mutane masu wucewa ne suka taimaka masu aka fito da Ibrahim, lucky for him shima ya saka seatbelt kuma motar sa akwai airbag dan haka bai wani ji mugun ciwo ba amma still he is unconscious, sun kai shi asibiti an kaishi emergency.
Gari yana wayewa Daddy ya shigo, ya gaya mana cewa har lokacin Ibrahim bai farfado ba amma doctors din sunce he is stable. Sultan daga bakin kofa ya tsaya yana kallona, kallo daya nayi masa na dauke kaina gefe, ya gaji da tsayiwa ya juya ya fita. Da la'asar aka sallame ni, direct gida aka nufa dani, naji dadin haka dan dama ina ta addu'ar Allah yasa kar Daddy yace a mayar dani gidan Sultan. Shima kansa Daddyn naga ya hade wa Sultan rai sosai. Muna zuwa gida Daddy ya saka ni a gaba yace "zaki dan zauna a gida Moon, hakan ba yana nufin zan raba ki da mijinki ba, a'a, so nake mijinki ya gane cewa abinda yayi ba dai dai bane, for him to think cewa zai iya daukan ran mutum koma me mutumin yayi masa is very bad. Zaki koma amma sai na tabbatar da cewa something like this will not happen again" na share hawayen ido na nace "na gode Daddy" yace "yanzu so nake dake ki nuna masa kuskurensa sosai, kar ki raga masa ko kadan. Ke ce abinda yake so fiye da komai a duniya, kuma yana takama ne cewa kina sonsa, show him you can leave him in dai har ba zai iya controlling kansa ba" na gyada kai na sake cewa "na gode Daddy".
Dakina aka gyara min, na shiga ina karewa dakin kallon, I never thought zan kuma dawowa dakin in kwana a ciki. Dare yana yi nayo alwala nazo na fara jero salloli ina godewa Allah daya ta kaita abin, sannan kuma ina sake neman guidance dinsa akan abin da na saka a gaba na. Na duba agogo naga karfe daya da rabi na dare, na kashe fitila na zauna akan gado ina kallon kofar balcony, I know he is coming, and I pray for God to give me the strength to do what I plan to do. Ban jima a zaune ba naji ana taba kofar, sannan aka bude ta, duk da cewa dakin da duhu bai hana ni gane shi ba, ya jima a tsaye yana kallona amma ya kasa cewa komai, nace "me kazo yi nan?" A hankali ya karasa shigowa dakin yace "Maimunatu dan Allah ki tsaya kiji abinda zan gaya miki" nace "me zaka gaya min, a gaba na kayi kokarin kashe mutum, you almost make me miscarry our child" da sauri yace "how can you say that, ke ma kinsan bansan dashi ba" nace "how can you say naje store ne dan in hadu da Ibrahim bayan bansan yana gurin ba" yace "am so sorry" nace "don't be. Rayuwa ta da taka ba iri daya bace ba. Ka tafi, ni bazan iya zama da mutumin da yake ganin cewa it is OK yayi kisan kai ba, bazan iya haifar 'ya'ya da kai ba, wannan ma da yake cikina in naga baka chanza ba I will make sure cewa bai san kaine babansa ba" da gaske magana ta ta shige shi dan fuskarsa koma wa tayi kamar an chire masa spirit din jikinsa, na mike tsaye nace "now get out of my room" ko motsi bai yi ba, na kunna fitilar dakin, yanayin da naga fuskarsa yasa nayi saurin dauke idona daga kansa tun kafin zuciyata ta karaya, na sake cewa "ka fita ko in kira security su fitar min da kai" a hankali yace "you won't" ban kuma ce masa komai ba naje na danna security button, ba'a jima ba sai ga David da wasu guda biyu sun shigo dakin, David da bindiga a hannunsa. Na nuna Sultan nace "ku fitar mun dashi daga nan" David yace "with pleasure ma'am" dama har yanzu David yana da grudges for sultan saboda dukan daya yi masa rannan ya kunyata shi a gaban yaransa. Ga mamakina ko motsi sultan baiyi ba ballantana yace zai yi fada dasu, suka kama shi suka fita dashi ta gabana, na dauke kaina ban kalle suba, amma suna fita na bi bayansu na tsaya a kofar dakina ina kallon yadda suke jansa akan stairs, ji nake tamkar zuciyata suka fito da ita waje suke ja a kasa, ina kallon su har suka bude kofar palo suka fita dashi waje. Na hango Daddy a kofar dakinsa shima yana kallon su. Na koma dakina da sauri na bude kofar balcony na shiga na cigaba da kallonsu suna jansa a kasa kamar babu rai a jikinsa, har suka bude gate suka fita dashi waje, a gaban gida na biyu bayan namu na hango motar sa, nan suka nufa dashi suka jefar dashi a gaban motar suka juyo, na tsaya ina kallon duhun inda yake a kwance a kasa, a raina ina cewa 'get up sultan' amma shiru bai tashi ba, bayan kamar 20 minutes na koma dakina na dauko waya na dawo balcony din, na kira wayar Amir, yana dauka nace "Kazo gidan mu yanzu, your friend needs you" na kashe wayar, ban bar gurin ba har sai da naga shigowar Amir unguwar mu, har ya wuce inda Sultan yake sai kuma yayi reverse, ya fita da sauri yana taba sultan, sannan ya daga shi, naji wani dadi a rauna ganin sultan din yana kokarin tafiya da kansa, a bayan mota Amir ya saka shi sannan ya koma ya rurrufe motar sultan din sannan suka tafi. Na rufe fuskata da hannayena ina kuka, I really hope cewa abinda nayi is the right thing to do. Waya tace ta fara kara, duk a tunani na Amir ne amma sai naga sunan Hafsat. Nace a raina 'har ta samu labari kenan' na dauka nayi mata sallama cikin sarkakkiyar murya, excitedly ta fara magana "Moon am sorry na kira ki yanzu nasan dare yayi sosai a Nigeria, what ever you are doing ki ajiye ki hau WhatsApp na turo miki hoton wata auntyn zayed, she looks exactly like Sultan, her name is Khairat, Moon I think she is his mother".
*when everything seems lost, have hope and trust in Allah, He will always find a way out for you. Remember, there is always darkness before dawn.*
Episode Eighty : The Skeleton in The Closet
A lokacin da su David suka ajiye shi a kusa da motar sa, kasa tashi yayi daga gurin, jira yake mutuwa ta karaso ta dauke shi, dan shi a ganinsa bashi kuma da sauran rayuwa a gaba. To menene sauran rayuwa in babu Moon? Dama itace farin watan data haskakae rayuwar ta sa da hasken ta, to yanzu tunda babu ita kuma menene yayi saura in banda duhu, a cikin duhun zai yi ta lalube har yaje ya afka ga halaka, he is sure that he will be lost without her. Yana kwance yaji tsayuwar mota a kusa dashi, a tunanin sa ma robbers ne kuma he didn't care. Sama sama yaji muryar Amir yana yi masa magana, ya dan bude idonsa ya kalle shi ya mayar da idon ya rufe. What is this man doing here? Me ya kawo shi? Yana jin Amir ya fara kokarin tashin sa, ya kwace, Amir yace masa "Sultan menene hakan kake yi wai? Moon ta kira ni tace inzo gurin ka, me ya faru? I really hope you are not drunk kuma? Sultan ya bude ido ya kalle shi sosai sannan yace cikin murya kamar ba tasa ba "Moon ce tace kazo nan?" Amir yace "eh, me ya faru haka" Sultan ya fara kokarin tashi Amir ya taimaka masa ya bude masa mota ya shiga suka tafi. Me yasa Moon ta kira Amir? Shin hakan yana nufin she still care about him ko kuma just tana so a dauke mata shi daga kofar gida saboda bata son ganin sa?. Ya lumshe idonsa yana tunanin abubuwan dasu ka faru tsakanin su, she even said zata tabbatar da cewa dan da yake cikin ta bai san cewa shine mahaifinsa ba, she hates him that much kuma bai ga laifin ta ba, koma menene ya faru laifinsa ne. Na farko ta ya akayi ma zuciyarsa ta raya masa cewa Moon sun hada plan da Ibrahim zasu hadu? How can he even think that? Kishinsa ya rufe masa ido kawai ya fadi magana without thinking kuma wannan maganar ita ce tafi komai bata wa Moon rai. Shi shine mai bad past, amma ita ko yaushe tana kyautata masa tsammani, ya tuna case din khulsum, tun kafin ma moon ta tuntubeshi da maganar har ta yanke hukuncin karya suke masa, amma shi bai showing mata the same courtesy ba. Wannan shine babbar nadamar sa ba wai ture Ibrahim ba, that bastard, he deserve that, uban wa yace ya biyo su? Har cikin gidansa ya shiga gurin matarsa and he let him go, sannan kirikiri ya ganshi ya rike hannun matar sa a cikin store and he still ignore him, duk da cewa da kyar ya danne zuciyar tasa ya yi ignoring din nasa, dan a lokacin babu abinda zai bashi satisfaction irin ya ga ya zubar masa da hakoran da yake using yake smiling at his wife, amma ya danne zuciyar sa saboda a lokacin yana ganin laifin moon ne kamar ita ce ta bada hanya, bayan sun fita kuma ya biyo su, why will he follow them in ba rainin hankali ba, waye suna tafiya da matarsa zai ga tsohon saurayinta yana binsu a baya kuma ace ransa ba zai baci ba? Laifin sa daya a lokacin, bai kamata yayi playing with rayuwar moon ba, kamata yayi yayi packing motar ya fito da Ibrahim da ga tasa motar ya babballashi ya zubar a gurin sannan suyi tafiyarsu.
Suna zuwa gida a part din Amir suka tsaya. Amir ya fito ya zagayo ya fito da sultan sannan suka shiga ciki, shi Amir duk a tunanin sa Sultan a buge yake, yana zuwa ya kwantar dashi a kan gado sannan ya debo ruwa mai sanyi ya kawo masa, yana fara sha yaji ruwan kamar madaci, ya furzar ya ajiye cup din a gefe. Amir ya zauba a gefensa yace "Sultan why do you do it? Ka samu good life with Moon why will you throw it all away saboda giya?" Wani takaici sultan yaji ya kama shi yace "fuck off amir" ya juya masa baya yayi kwanciyarsa. Amma babu bacci babu alamarsa sam, yadda jiya baiyi bacci ba haka yau ma da alama va zai yi baccin ba. Wata biyar kenan da aurensu da moon amma bai taba kwanciya ba tare da ita ba sai yau, bai taba tunanin kuma zai kwanta ba tare da ita dinba, amma yau gashi basa tare kuma duk suna raye, suna kuma gari daya. She even call the security on him tasa suka fita dashi ko kallon sa kuma bata yi ba, wannan ya tabbatar masa da cewa she means what she said, rabuwa zatayi dashi kamar yadda wadda ta haife shi ta rabu dashi, kamar yadda wanda ya haife shi ya rabu dashi, bai damu ba ko ya mutu ko yayi rai. Daddy daya ke kallo a matsayin sabon uba ma ya hade masa rai, daya gaishe shi kin amsawa yayi kamar yadda in ya gaishe da takawa baya amsawa. It is all over. He was a fool to even think it will work. Moon was right, rayuwarsu ba daya bace, they care about everyone hatta wanda ya bata musu, shi kuma va haka yake ba, they expect him to do the same, instead sai gashi ya kusa aikata kisan kai. He is a monster, shi ya riga ya dade da sanin hakan, idan zuciyarsa ta debe shi shi kansa abinda yake aikatawa sai daga baya yayi mamaki. Amma kuma yanzu har acikin zuciyarsa bai ji yayi nadamar abinda yayi wa Ibrahim ba, the bastard. Yanzu haka ma da zai ganshi da sai ya karasa shi, tunda shine yayi sanadin duk wannan abinda ya faru.
Shi kam yasan rayuwarsa ta kare, a kan gadon nan zaiyi ta kwanciya har sai mala'ikan mutuwa ya tuno dashi yazo ya dauke shi. Sai kuma ya tuno da halittar da take cikin marar Moon, wani nauyi yaji zuciyar sa tayi masa, his baby, yaci burin ya haifi 'ya'ya ya nuna musu soyayyar shi da ba'a nuna masa ba. Amma kuma Moon ta gaya masa cewa idan bai chanza zafin zuciyarsa ba 'ya'yansa ma gudunsa zasu ringa yi. Yaji wani irin daci a zuciyarsa, just the thought of his children resenting him ya saukar masa da wani mugun zazzabi. Ya jawo bargo ya kudunduna, maybe the baby will be better off without him.
Tun da assuba Amir ya taba shi yaji irin zafin da jikinsa yayi, da kyar ya tashi yayi sallah ya koma ya kwanta. Gaba daya hankalin Amir ya tashi, ya manta rabon da yaka Sultan a kwance babu lafiya, tun wata rashin lafiya da yayi suna America, sultan has always been healthy and energetic. Zuwa karfe goman safe yaga zagin jikin karuwa yake yi, duk uban bargunan daya loda masa amma karkarwa kawai yake yi hakoransa suna haduwa guri daya, a hankali yaji yana magana kasa kasa, ya sunkuyo da kansa dai dai fuskarsa yaji yana cewa "Moon am sorry, moon am sorry, dan Allah kiyi hakuri ba zan sake ba" wani irin tausayin abokin nasa yaji yana ratsa shi. Menene kuwa zai hada shi da Moon har haka? Shi yasan a rayuwarsa bai taba ganin soyayya irin ta Sultan da Moon ba, to menene kuwa zai saka su bata?. Ya dauko wayarsa yayi dialing number din Moon amma wayar a rufe, ya kuma kira har five times amma bai samu ba, yayi mata text "Sultan babu lafiya, kuma ke yake nema" ya tura mata. Daga nan ya kira number din doctor din gidan ya gaya masa halin da sultan yake ciki. Ba'ayi awa daya ba doctor din yazo ya duba sultan, shi kansa yayi mamakin zafin jikin sultan a take ya saka Amir ya taya shi suka cire masa bargonan daya lulluba suka cire masa riga da wandonsa suka barshi da singlet da gajeren wando sannan suka yi ta goge masa jikin sa da jikakken towel, amma suna dora towel din sai suga ya bushe saboda zafin jikin, a haka dai uka samu da kyar jikin ya danyi sanyi kadan, idan sultan gaba daya ya juye kamar ba nasa ba, doctor din da sauri yace a saka shi a mota su tafi dashi asibiti, suna zuwa aka tafi dashi private room likitoci suka hau kansa, Amir ya zauna anan shi kadai a waiting room, kawai ji yayi hawaye yana zubo masa, a ce mutum mai gata irin sultan, a Prince, da uwarsa da ubansa da matarsa a duniya amma an kawo shi asibiti babu kowa a gurin sai shi? Yana nan yana ta kukansa har doctor ya fito yana kallonsa yace "Haba Amir, kar ka badani mana, kana namiji kana kuka?" Amir bai kula da tsokanar da yake masa ba yace "doctor how is Sultan?" Yace "da sauki zamu ce. Fear dina shine brain dinsa, zazzabinsa yayi zafi da yawa in tsoron kar ya taba kwakwalwarsa, kuma yana tunani da yawa, wannan shi ya saka muka kasa stabilizing bp dinsa, amma for now mun yi masa allurar bacci, za mu jira kuma muga sanda zai farka. But please do your best ka ga ka kawo masa abinda zai faranta masa idan ya tashi daga baccin" Amir yayi masa godiya sannan ya shiga da sauri inda sultan yake kwance, tun kafin ya karasa kusa dashi ya hango irin ramewar da yayi da kuma farin da yayi, fatar bakinsa tayi purple alamar babu isashshen jini a jikinsa, kuma zazzabin ne ya kona jinin. Ya karasa ya rike hannunsa da yaji yayi sanyi kalau yanzu alamar zazzabin ya sauka, a hankali ya fara magana "Sultan ya zanyi? Me zanyi maka ka samu lafiya sultan?" Sai kuma ya mike kamar wanda aka tsikare shi yayi kissing hannun sultan ya fita da sauri, direct gidan su Moon ya dosa, tun daga bakin gate David ya tsayar dashi fuskar nan babu rahama a cikin ta ga bindiga a kugunsa yace "you are no longer welcome here" Amir yace "ba shiga zanyi ba ai, Moon nake son gani" David yace "bata son ganin ka ita" wata zuciya ta debi amir amma ya danne yace "ya akayi kasan bata son ganina, ka shiga ka gaya mata nine nazo zata fito" David yace "itace tace in kazo kar a barka ka ganta" Amir ya sake cewa "can you at least tell her that her husband is sick kuma yana bukatar ganin ta? Am sure in ka gaya mata haka zata ganni" ko kula shi David baiyi ba ya koma kofar gidan kawai ya tsaya yana kallonsa hannunsa a rike da bindigar sa. Amir yayi wishing ina ma yana da karfi irin na sultan da sai ya farfasawa david baki ya shiga gidan ya dauko moon aka ya kaiwa sultan ita. Amma babu damar yin hakan dan yasan tunkarar David will be like a suicide, kuma yasan bashi kadai bane akwai sauran a ciki. Dole ya koma yaja motarsa ya tafi, yanzu ya zaiyi kenan? Ya zaiyi da Sultan idan ya tashi? Wani tunani ne yazo masa, ya juya kan motar sai palace, yana shiga fada ya tafi direct, mutanen gurin sai kallonsa suke yi, sun san shi amma kuma basu taba ganin shi a fadar ba, ya tsaya yana facing Takawa da yake harde akan karaga, ga Abbas a zaune a hannun daman sa, ga sauran hakimai duk kowa ya juyo yana kallon Amir, da karfi amir yace "Your son is dying, yana asibiti kuma yana nemanka" kafin ya rufe bakinsa fadawa sukayi kansa, suka jashi suka fitar dashi waje, amma ko babu komai Amir ya isar da sakon sa. Ana fita da Amir Hakiman gurin suka fara magana, 'dama Sultan bashi da lafiya?' 'Me ya same shi?' 'Allah sarki yaron ya nutsu sosai wallahi' 'ni kam kwanan nan kullum na ganshi sai yayi ta bani sha'awa' da sarkin bai da makama, da madaki, wadanda sune ake kira da king makers, suka kalli juna suka mike a tare suka durkusa a gaban sarki "Allah ya taimaki sarki ai ya kamata muje muga jikin nasa" idon takawa ya kada yayi ja saboda bakin ciki, a ransa yana cewa "wannan yaron Amir yake kowa? Zaman sa ya kare a gidan nan" amma kuma a fili ba zai iya musa wa hakiman sa ba, musamman king makers, sune kamar shugabanni dan dattijai ne sosai, sune suka nada babansa, suka nada shi, sune suke da alhakin zaba da nada sarki. Dole Takawa ya mike, gab daya sauran hakimai suka mike, Galadima ne akan gaba. Amir yana ganin su yasan tarkon sa yayi kamu, ya shiga motarsa yayi gaba su kuma duk suka biyo bayansa. Gaba daya mutanen asibitin ranar sai da suka fito kallo, ga sarki da hakimansa gaba daya sunzo dubiya, direct dakin da sultan yake kwance suka nufa. Dakin bai dauke su gaba daya ba dan haka wasu ta taga suka leka suna gano sultan a kwance har yanzu yana bacci, Amir yaje kusa dashi yana shafa kansa yace "Sultan ka tashi ga Takawa yazo duba ka" a hankali idon Sultan ya fara budewa kadan kadan yace murya can kasa "Daddy? My Daddy?" Galadima ya rike hannusa yace "eh Sultan, babanka ne yazo ya ganka. Ya jikin nasa" Sultan ya kalle shi, ya dan hadiye yawu sannan ya fara kallon mutanen dakin, idonsa ya tsaya akan Takawa da yayi kicin kicin da fuska, ya karbe hannu sa daga na galadima ya mika gurin sarki yace "Daddy?" Gaba ki daya kowa idonsa yana kan Takawa dole ya karasa ya kama hannun sultan ya rike, hawayene ya fara gangarowa a idon Sultan, amir yaji wani iri a jikinsa, tun da suka girma, tun sanda aka kaisu lagos, bai taba ganin hawayen sultan ba sai yau, masu raguwar zuciya a gurin sai da suka taya sultan kokawa saboda babu wanda bai san kiyayyar da sarki yake yiwa sultan ba kuma babu wanda yasan dalili, a hankali sultan ya fara kukan kuma sai kukan ya fara karuwa har da sheshsheka, ya rike hannun Takawa yaki chikawa. Wani abu takawa yaji ya tsaya masa a zuciyarsa ya tokare, ya kasa hadiye koma menene, ya kasa fahimtar me yake ji. Muryar sultan yaji yace "Ummee na, Ummee na". Kan Takawa ne yayi bala'in sarawa, ya cika hannun sultan ya rike kansa da hannu biyu yana ambaton sunan Allah, ummee na, ummee na, a ina ya taba jin wadannan kalmomin, wani dan karanin yaro ya hango a idanuwansa wanda bazai wuce shekara biyu ba a hannun baba gaji yana ta zunduma kuka yana miko masa hannu yana cewa "Daddy na, Daddy na, ummee na, ummee na" a lokaci daya komai daya faru ya dawo masa tas a cikin kansa, take ya yanke jiki ya fadi sumamme a gaban gadon da sultan yake a kwance.
Hmm. Things are not always what they seem.
Episode Eighty one : The Skeleton in the Closet 2
A hankali Takawa ya fara dawowa haiyacinsa, ya bude idonsa da sauri yana kokarin ya dai dai ta tunanin sa, ya ilahi wannan wanne irin mugun mafarki yayi haka? A mafarkinsa wai an raba shi da khairat, a mafarkin sa kuma wai baya son Little Love, a mafarkinsa little love shine abinda yafi tsana fiye da komai, kuma wai har anyi shekaru da yawa har Little Love ya girma yayi aure. Oh wannan wanne irin mugun mafarki ne haka? Ya yinkura ya tashi zaune yana duba gefensa dan ya tashi khairat ya bata labarin mafarkin da yayi, amma sai me? Babu khairat a gurin, kuma wannan gadon ba nasa bane ba, ya kalli dakin shima, wannan dakin shima ba dakin sa bane ba, yayi kama da executive dakin asibiti, amma kuma haduwar dakin babu abinda ya raba shi da dakin gida sai drip daya gani a hannunsa. A karshen mafarkinsa an yi forcing dinsa ya je asibiti duba little love daga nan kuma bai san me ya faru ba sai ya farka daga mafarkin, to ko dai still har yanzu mafarki yake yi ne? Ya matsa ledar drip din yaji zafin shigar ruwan, mutum ai baya jin zafi a mafarki. Ya tashi zaune sosai ya cire drip din ya mike tsaye, gaban taga yaje ya daga labulen tagar, tabbas nan asibiti ne. Ya ilahi what is happening? Kofar toilet ya bufe ya shiga dan ya wanke fuskarsa maybe ko zai dawo haiyacinsa sosai, abinda ya gani a cikin madubi shine ya saka ya daskare a bakin kofa, he looks exactly like yadda yake a cikin mafarkinsa, older, thirty years older, ya karasa gaban madubin yana taba fuskarsa, shi din ne dai kuma tabbas wannan ba mafarki bane ba. Inna lillahi wa inna ilaihir rajiun. Yanzu duk abinda ya faru da gaske ya faru kenan? Yanzu shekararsa talatin rabonsa da khairat? Tana ina yanzu, shin tana da rai ko akasin haka? And Little Love, my poor innocent Little Love. A toilet din ya durkushe yana rusar kukan dashi kansa bai san ya iya irinsa ba.
30 years back
Tabbas Prince Sadiq Abdallah yayi soyayya da Khairat Faisal Abdallah a Oxford, England. Khairat full blood balarabiya ce kuma she too is of royal blood, born and raised in Riyadh, Saudi Arabia. Soyayya suka yi mai tsanani wadda har suke ganin cewa kamar they share the same soul but different bodies. Amma duk wannan soyayyar da suke yi iyayensu basu da masaniya a cikin al'amarin, wannan kuma ya faru ne kasancewar khairat balarabiya dan larabawa da wahala su dauki 'yar su su bada ita aure ga bakar fata, bahaushe. Khairat bata taba ganin anyi haka a familyn su ba, in fact a familyn su ma mostly auren dangi ake musu, dan already ma ita da akwai wanda aka riga aka ajiye mata zata aura in ta gama makaranta. Wannan shi yasa duk nacin da Sadiq yake yi mata akan ta barshi yaje gidansu taki yarda. Lalube kawai suke yi a cikin duhu. Sadiq yasan da irin kalubalen da yake gabansu amma shi bashi da tsoro sam, kuma ya riga ya saka a ransa cewa khairat tasa ce ko da kuwa sama da kasa zata hadu babu wanda ya isa ya raba shi da ita. A haka har suka gama makaranta, iyayen Khairat suka zo suka dauke ta suka mayar da ita gida. Wannan ba karamin tayar da hankalin Sadiq yayi ba dan ya san da maganar wancan hadin da ake so ayi mata a gida. Babu shiri shima ya tattaro ya dawo Nigeria gurin sarki Abdallah, ya shigar da maganar yana son sarki Abdullah yaje can Riyadh ya nemo masa auren Khairat. Sarki Abdallah yasan abinda dan nasa yake nema is close to impossible, ba zasu bashi auren khairat ba, musammam tunda an riga an yi mata miji, ba zasu karya alkawari ba, hakan yasa yayi kokarin tausar zuciyar dan nasa akan ya hakura da auren ya dawo gida ya nemi auren ko wacece a Nigeria zai nema masa aurenta, amma Sadiq was as hard as stone, dan haka ya tubure shi lallai ita yake so kuma ita zai aura. Da Sadiq ya fahimci cewa baban nasa bashi da niyyar honoring wish dinsa ga kuma time yana kurewa dan yasan a koda yaushe za'a iya daura wa khairat aure, dan a halin yanzu ma tayo masa waya tana kuka cewa maganar auren ta tashi kuma ta fadawa babanta cewa ita bata son wanda za'a aura mata kuma shi sadiq din take so, tana fadar haka baban ta ya saka aka kaita daki aka rufeta yace ko palo kar a barta ta ta kuma fitowa. Wannan ba karamin tayar da hankalin sadiq yayi ba, dan a lokacin ji yake yi da ace ya rasa khairat gwara ya rasa ransa, sai ya hada kayansa bada sanin iyayensa ba ya gudu daga gida. Riyadh ya tafi ya kama hotel ya zauna yana plan din abinyi, ba'a karbe wayar khairat ba dan haka suna waya da ita, ita take kara encouraging din sa ma akan yazo din, suka shirya plan dinsu sosai, plan A da plan B. Plan A shine zaizo gidan su ya nemi aurenta a gurin uncle dinta. Plan B kuma shine idan plan A yayi failing an hana shi auren nata zai salallabo cikin dare ya sace ta su gudu. Sadiq yasan cewa Saudi Arabia ba Nigeria ba ce ba, suna da tsatstsauran doka, idan aka kama shi zai iya rasa ransa, babu wanda zai kalle shi ya matsayin Prince tunda su a gurinsu he is not a Prince, amma soyayya ta rufe masa ido. Ya shirya tsaf yaje ya aiwatar da plan A, amma ko kyakykyawan kallo bai samu daga uncle din Khairat ba, in fact warning ma ya buga masa kuma yace ya bashi two days yabar kasar in ba haka ba zai turo masa askarawa suyi out dashi. Sadiq zuciya kamar zai mutu dan bakin ciki, wai yanzu saboda tribe dinsa da kalar fatar sa shi yasa za'a hana shi auren wacce yake so? Menene aibun sa? Yana da asali, yana da addini, yana da ilimi, yana da dukiya kuma shi cikakken namiji ne bashi da tawaya ko kadan amma saboda shi bakar fata ne an hana shi aure duk kuwa da cewa yarinyar shi take so. Nan take ya kira khairat ya gaya mata plan A failed, initiating plan B. Khairat ce ta tsara masa duk yadda tsarin gidan nasu yake shi kuma ya zana, tayiasa bayanin dakin da take da komai. Tayi wa mahaifiyar ta dabara ta saci spare key din kofar gidan ta jefa ta window, ta kira sadiq ta gaya masa shi kuma yazo ya dauka, ta kuma gaya masa exactly a inda ake ajiye keys din gidan. Ana gobe daurin auren khairat Sadiq yazo, bai samu matsala ba saboda su a Saudi Arabia babu burglary dan haka ba wani security. Tunda kowa yasan hukunci babu wanda yake shiga gidan wani. Yana zuwa ya bude kofa da key ya shiga ciki, duk gidan suna bacci banda khairat da take yi masa magana ta waya tana kara yi masa bayanin inda zai bi, a haka har yaje har dakin mamanta ya dauko key din dakinta. Ya fito ya tafi dakinta ya bude, already a shirye take dama dan haka ko magana basu yi ba ta biyo shi da sauri suka fita daga gidan suka shiga motar daya zo da ita, a dakinsa na hotel suka karasa kwana, da sassafe dama yayi musu booking plight suka tafi airport, around 7, jirginsu ya tashi zuwa America. Sun zabi America ne saboda it's a free country, babu wanda ya damu da wani, kuma sun san za'ayi wahalar samun su a can saboda girman ta. Plus England shine guri na farko da za'a fara zuwa neman su. Sadiq bai san ya debo da zafi ba, a saudiyya, ka shiga har gida, kuma gidan masu sarauta, ka sace musu yarinyar da za'ayi bikinta gobe, ka gudu da ita ku bar kasar gaba daya. Chafdi.
Kwanan su daya a America, saboda suna gudun sabawa ubangijin su, suka nemi wani imam suka bukaci a daura musu aure, liman ya nemi waliyyanta khairat tace ita marainiya ce bata da kowa a america, daga ita sai iyayenta kuma iyayen yanzu sun mutu kuma bata taba zuwa garin suba ballantana ta san danginta, sadiq ne duk ya tsara mata wannan yace in sunxo ta fada. Imam din ne ya zauna a matsayin waliyyinta, yace duk wani problem da ya tafu da auren ta zo gurinsa, ya zama shine babanta, Sadiq kuma shi ya tsaya a waliyyin kansa, aka daura aure Sadiq ya bada sadaki, mutanen da suke masallacin sune shaidu. Daga nan sukayi signing marriage certificate sun zama islamically and legally married. Daga gurin daurin auren direct airport suka nufa suka shiga jirgi sai Nigeria. Shi sadiq a tunanin sa uban yaki yadda da auren ne saboda yana jin tsoron zuwa neman auren, dan haka yake ganin yanzu tunda yaje ya aikata abinda ya aikata ai shikenan komai ya wuce. Yana zuwa gida da khairat tun kafin yayi wa sarki Abdallah bayani sarkin ya fahimci abinda ya faru, sato khairat sadiq yayi. Sosai hankalin sarki da Yaya ya tashi dan su sunsan menene zai je yazo. Sadiq ya gaya musu cewa ya riga ya auri khairat dan haka iyayenta babu yadda zasuyi dashi, amma sarki ya san cewa auren nata da yayi shi zai kara mayar da case din worst, saboda zasuyi charging dinsa da forced marriage wanda babban laifi ne a saudiyya, sarki Abdallah ya nuna wa Sadiq cewa lallai ya dauki yarinyar mutane ya mayar da ita gidansu, jin haka Sadiq ko amsa bai bashi ba ya kamo hannun khairat suka fice daga palace din. Shi a tunaninsa yama za'a ce ya sake ta ya mayar da ita gida duk uwar wahalar da yasha kafin ya same ta? A gidan wani abokinsa anan Abuja suka kwana, da safe suka kuma hawa jirgi sula koma America. Sun yanke shawarar gwara suyi zamansu su kadai tunda iyayensu sun kasa fahimtar irin son da suke yiwa junan su. Shikenan kuma suna zuwa america aka shiga honeymoon. Rayuwarsu kawai suke yi suna jin su on top of the world, babu mai saka su babu mai hana su, babu abinda suke sai soyayya kamar su chinye junan su, sun zama Americans sosai. Sadiq ya nemi aiki da takardunsa kuma bai sha wahala ba ya samu, suka nemi gidan haya suka kama, khairat taso neman aiki itama amma sadiq ya hana yace albashinsa ya ishe su, su biyu kadai basu ajiye kowa ba.
Wata daya da auren su khairat ta samu ciki, nan fa murna a gurinsu kamar me, Sadiq yana kallon cikin a matsayin hanyar komawarsa gida, idan babansa yaga cewa ya haihu da khairat ai dole ya hakura ya karbe ta da duk wani challenges din da auren nata zai taho dashi. Su biyu suka yi renon cikin su cike da soyayya da kulawa, da watan haihuwar khairat ya kama kuwa sadiq a jiye aikin sa yayi ya dawo gida gurinta yana kula da ita, hana ta yin komai yayi, komai shi yake yi mata, ko ya kuwa yaga ta dan bata fuska sai hankalinsa ya tashi. A haka labor ya zo mata, hankalin sadiq ya tashi sosai gani yake kamar mutuwa zatayi ballan tana da ta fara bashi wasiyyar ya kula da babyn su, ya kaishi gurin 'yan uwanta ya basu hakuri. Kusan akan chinyarsa ta haihu dan zama yayi dirshan akan gadon ya rungume ta yana yi mata alkawarin daha wannan haihuwar ba zai sake bari ta samu ciki ba saboda ba zai sake bari ta sha wannan wahalar ba. Ana haihuwar Sultan sadiq ya karbe shi ya rungume a kirjinsa, ko goge shi ba'a yi ba, dariya kawai yake yi saboda murna, shi a rayuwarsa bai taba ganin kyakykyawan yaro irin wannan ba, ya sunkuyo gurin khairat da ake gyarawa yace "look at our Little Love, He looks just like you". Nan fa suka ninka soyayyar da suke yiwa junan su suka dora akan Little Love dinsu wanda yaci sunan babansa, Abubakar, sukan zauna kawai su saka shi a gaba suna kallo, watan Sultan biyu a duniya Sadiq yaga cewa ya kamata su gwada zuwa gida suga yadda zata kasance, suka shirya amma basu kwashe kayansu ba saboda basu da tabbas din za'a karbe su a gidan. Sadiq ya shiga gida hannunsa na dama dauke da two months old Sultan, hannunsa na hagu kuma rike da Khairat. Da fushi sarki Abdullahi ya taho, yana zuwa Sadiq ya mika masa Sultan wanda a lokacin kwuiya ce dashi amma kawai sai akaga ya tafi gurin sarki yana bangala masa dariya yana ta ba masa fuska, Sarku Abdallah ji yayi ya kasa fadan kuma, niyyarsa yana zuwa ya kora su su koma inda suka fito amma sai ya kasa, wata soyayyar yaron yaji tana ratsa zuciyarsa. Kowa a gurin sai ya koma kallon su, sultan tamkar ya saba da kakan nasa, Khairat da Sadiq sai dariya suke yi suna mamaki. Dole Sarki Abdallah ya karbi surukarsa da jikansa. Aka ware musu dakunan su suka tare, suka tattaro kayansu gaba daya suka dawo gida. Nan take Khairat tayi farinjini a gurin mutane saboda kirkin ta, ba ta iya hausa ba amma koya take har a gurin bayin gidan, bata damu cewa wai ta fita daban a cikin su ba harkokinta kawai take yi tana kula da mijinta da Little Love dinta. Sarki Abdallah ya karbi surukarsa amma a cikin ransa ya san cewa this is not the end of the story. Dole wata rana sai iyayen khairat sun gano inda take, ko kuma ita khairat din da kanta ta nemi zuwa gurin iyayenta. Takanas ya tura kaninsa zuwa Riyadh dan ya bincika masa yaji me iyayen khairat suke ciki, labarin da aka kawo masa sam baiyi masa dadi ba, iyayen khairat sun dauki maganar very serious dan haka ruwa a jallo ake neman sadiq. Charges dinsa suna da yawa, akwai trespassing tunda ya shigar musu gida ba tare da izinin su ba, ga kidnapping tunda basu yarda cewa ita ta bishi ba sun barshi a cewa sace ta yayi, sauran changes din kuma sai an ganta an ga a halin da take ciki, kuma sarki Abdallah ya tabbatar suna ganinta da baby zasu kara da raping da forced marriage, a takaice indai suka kama Sadiq to sai ya biya da ransa. Sarki Abdallah kuwa is not ready to give up his son, tunda dai aikin gama ya riga ya gama. Ya kira Sadiq yayi masa bayanin duk abinda ake ciki, Sadiq ya daga kafada yace "they can't catch me now" sarki Abdallah ya girgiza kansa a ransa yana cewa 'ta yaro mai take bata karko, kuma komai nisan jifa kasa zai fado'. A bangaren khairat kuwa kullum tana tuna iyayenta amma sai tayi sauri ta kawar da tunanin daga ranta, saboda tasan haduwa dasu yana nufin rabuwa da Sadiq da kuma Little Love dinta, wanda bata jin zata iya hakan. Sarki Abdallah yasan tabbas iyayen khairat zasu gano inda take wata rana za kuma su zo neman ta, dan haka kullum yana cikin tararradin zuwan nasu.
Iyayen Khairat basu samu nasarar gano inda take ba sai da Sultan ya shekara biyu a duniya, lokacin shekarar ta kusan uku rabonta da gida. Da daddare suka iso, babanta mahaifi da kanin babanta, a fusace suke gaba dayan su, tun daga bakin gate da suka ce mai martaba sarki suke nema, aka gaya mudu ya kwanta bacci suka ce basu damu ba. Ganin cewa ba kananan mutane bane ya saka daga bakin gate aka yo waya cikin gida aka fada, sarki Abdallah yana ji yasan ko su waye. Da sauri ya fita, yana ganin idan aka bi abin a sannu za'a iya samun maslaha. Amma yana zuwa ya fahimci babu maslaha, dan sun dauki zafi sosai, saboda abin ya bata musu rai da yawa, domin khairat tana daga cikin yara masu tarbiyya a zuri'ar su, wannan nema dalilin da yasa aka barta ta tafi karatu England, suna ganin duk yaron da har ya iya ya hure wa khairat kunne har ta juya wa iyayenta baya to lallai yafi shaidan shaidanci, cewa sukayi sadiq is a devil kuma ya kamata ayi eliminating dinsa a society, bai kamata ace wai shine crown Prince din da zai jagoranci al'umma ba. Sun dau alwashin cewa sai sunyi hanging dinsa sun nuna wa duniya yadda mulki yake a Nigeria, in dai ire iren su ne shugabannin Nigeria to ya kamata a dau mataki a kai. Wannan maganar ta bala'in bata ran sarki Abdallah, dan shi yana ganin cewa dansa ba mutumin banza bane ba, dan duk a cikin 'ya'yansa yafi na'am dashi, his only fault is falling in love with a wrong girl, amma kuma mutane ba zasu duba cewa the girl lead him on ba, in irin wannan case din ya faru koda yaushe laifin namiji ake gani ba'a duba macen, da bata bashi fuska ba da ba zaiyi hakan ba. Da aka taso abdallah da khairat basu san me yake faruwa ba sai da suka shigo gurin tukunna, Khairat da gudu ta juya zata koma uncle dinta ya damketa, kuka take yi kamar ranta zai fita tana kiran sultan da sadiq. Da kyar aka samu masu rike Sadiq saboda neman zauce musu yayi. A lokacin Yaya ta shigo da Sultan ya hannunta wanda bacci yake yi hayaniya ce ta tashe shi, ita Yaya ta shigo da Sultan ne wai tana ganin kamar in suka ga dan zasu hakura su bar masa uwarsa amma sabanin haka, suna ganin sultan suka gane dan Khairat ne dan haka baban khairat yace shima Sultan din tafiya zasuyi dashi, ai Islamically da na uwa ne har sai ya girma sannan zai zaba, wannan kam sarki yace ba'a isa ba, da kansa ya karbi Sultan wanda ya fara kuka ganin ummeen sa tana kuka, Sarki yace babu wanda ya isa ya karbi Sultan, dole suka hakura saboda an fi karfin su. Aka uncle din Khairat ya dauke ta ya fita da ita tana ihu tana kiran Sultan wanda shima kukan yake yana kiran Ummee na, duk da baisan me yake faruwa ba, da sauri sadiq ya kwace daga rikon da akayi masa ya bisu har wajan mota yace "Khairat, I will come for you, no matter what, no matter how long" a take babanta ya juyo ya dawo gaban sadiq yace "then I will hang you, If you ever step on Saudi land, I will hang you" daga haka suka ja mota suka tafi.
Tashin hankali ba'a saka masa rana, inda Allah ya rufa asiri ma da daddare ne duk gidan kowa bacci yake yi. Da kyar aka mayar da Sadiq daki sarki ya saka akayi masa allurar bacci, amma har yayi baccin yana rantsuwa sai yaje ya karbo matarsa. Sultan kuwa bai koma bacci ba dan gaba daya ya rikice shi ummeen sa da daddyn sa. A ranar sarki Abdallah bai koma bacci ba shima, yana lissafin abinda ya kamata yayi. Duk da yasan cewa gaba da gabanta amma kuma ya tabbatar ba zasu iya taba Sadiq a Nigeria ba, amma yana shiga saudiyya ya zama nama. Sannan kuma ya tabbatar cewa sadiq sai yaje.
Tunda assuba ya aika a kirawo masa babban malamin sa da yake saka yayi masa addu'oi idan wani abin ya shige masa duhu a harkar sarautar sa ko kuma a harkar cikin gidansa. Malamin yana zuwa sarki Abdallah ya yi masa bayanin duk halin da ake ciki bai boye masa komai ba. Malamin yayi shiru yana tunani sannan yace "to yanzu Allah ya taimaki sarki mai kake so ayi?" Sarki yace "so nake idan da wani sirri da kake dashi wanda zaka cire masa ita daga zuciyarsa kwata kwata ya manta da ita" malamin yace "akwai Allah ya taimake ka, za'a iya yin hakan. Amma kuma ran sarki ya dade akwai da a tsakanin su, idan an mantar dashi uwar shi kuma dan fa? Duk sanda ya kalli dan dole ya tuna da uwarsa, musamman ma da yake dan da uwar suna kama" sarki ya danyi tunani kadan sannan yace "to ya kake ganin za'ayi? Malamin yace " za'a iya raba su din kamar yadda ka bukata amma kuma ina tsoron abin zai shafi yaron. In akayi aikin, adadin soyayyar da uban yake yiwa dan zai juye ya koma kiyayya. Zai zamanto kamar mun raba da da ubansa ne Allah ya taimake ka, ina tausayin yaron tunda kaga yanzu babu uwa kuma azo ace uba yana tsanarsa ai abin zaiyi masa yawa, tarbiyyar sa nake tunani" Sarki Abdallah ya daga kansa sama yana tunani. Tabbas in aka raba Sadiq da Khairat an shiga rayuwar Sultan. Amma kuma in ba'a raba su bafa? Ya lissafa abubuwan da suke at stake, na farko rayuwar Sadiq din gabadayanta, Sadiq shine sarki yake sa ran zai gaje shi, shine yake sa ran ko bayan ransa zai rike gidan, zai rike sarautar kuma zai rike al'ummar da suke karkashi sa baki daya, ba rayuwar Sadiq ce at stake ba, family name dinsu da family future dinsu gabadaya is at stake, ba family dinsu kadai ba, hatta martabar musulmin Nigeria gabadaya is at stake, ba musulmin Nigeria kadai ba, ita kanta Nigeria martabar ta sai ta ragu a idanun sauran kasashe. Dan in dai suka ka.a Sadiq sai sunyi publishing a international papers cewa ga abinda Nigerian Prince yayi. Sarki ya sauke ajjiyar zuciya ya sunkuyo da kansa yana kallon malamin yace "a yi. Ni kuma nayi alkawarin zan zamarwa Sultan uwa kuma zan zamar masa uba. Zan bashi duk kannin wani gata da ya kamata iyaye su bashi. Insha Allah sultan ba zai yi maraici ba. Ina rokon Allah kuma ya dubi uzurina, ya dubi dalilin da yasa nayi haka, ya yafe min".
Kaico, mai martaba sarki babu wanda yasan gawar fari sai Allah.
Episode Eighty Two : The Light
Like I always say and always emphasize, things are not always what they seem. Duk abinda kake zargi, karka yanke hukunci a kansa sai kayi bincike ka tabbatar, duk abinda aka gaya maka akan wani indai har ba kaine da kanka ka gani ba, kar kayi saurin yanke hukunci akai, kayi bincike sosai first. Never and never judge a book by it's cover, in ba haka ba you might spend the rest of your life regretting.
How far will you go to save your family?
Hakan kuwa akayi. Daga nan sarki Abdallah ya saka akaje dakunan da khairat ta zauna aka kwashe duk kanin kayanta aka rufe dakunan. Gari yana waye wa yasa aka tara masa duk mutanen gidan tun daga kan iyalinsa har bayinsa ya ce ya hane su da ko da ambaton sunan khairat ne a gidan ballantana labarin ta ko wata magana data shafeta. A lokacin da Prince Sadiq ya tashi daga bacci jin kansa yayi fresh, babu abinda yake damunsa, kamar bashi da wata matsala a duniya. Ya danganta hakan da bacci mai nauyi daya samu. Yayi wankansa ya shirya ya tafi gurin mahaifinsa, ya tarar dashi yana cin breakfast, ya gaishe shi ya zauna gefe, mahaifin nasa kallonsa kawai yake yana studying dinsa, sannan yace "Sadiq yau baza a fita gurin abokanai ba ne?" Sadiq ya dan shafa kansa yace "Ranka ya dade yau gida zan zauna, sam yau bana son hayaniya" sarki abdallah yaji babu dadi har cikin ransa. Sadiq ne za'a ce masa ya fita gurin abokanai yace shi ya zashi ba? Sadiq din da kullum in yana gari gidan a cike yake da mutane saboda shi? Bayan ya baro mahaifin nasa ne ya tafi cikin gida gurin yaya, yana shiga palon ta yaga wani yaro yana ta kuka a hannun baba gaji, kallo daya ya yiwa yaron yaji wani irin tsanarsa a ransa, ji yake kamar ya hada daga baba gajin har yaron yayi musu duka ya kore su daga palon amma ya daure zuciyar sa ya wuce ciki, tunda ya shiga Yaya take kallonsa da mamaki har ya durkusa ya gaishe ta, ba zai iya jure kallon yaron ba dan haka ya mike ya fice, ga mamakin sa sai yaga yaron yana yunkurin zuwa gurin sa dan haka ya kara sauri ya fita in ba haka ba zai iya kwada wa yaron mari. Babu shiri Yaya ra dau mayafinta ta tafi gurin mai martaba, ta tarar har yanzu abinci yake ji ga Nani a kusa dashi, babu kishi a tsakanin Yaya da Nani dan haka a gabanta tayi magana, "Ranka ya dade me akayi wa yaron nan ne?" Ba tare daya kalle ta ba yace "Abinda yafi alkhairi a tare dashi shine abinda nayi masa" hawaye ya fara zuba a idon Yaya tace "Allah ya taimake ka ko dansa fa bai gane ba ya zakace hakan shi yafi alkhairi a rayuwarsa? Wannan ba Sadiq din mu bane ba, wani ne daban ba dan mu ba" bai ce mata komai ba, nani ta tambaye ta ta fada mata abinda ya faru, itama nanin kukan ta fara yi dan duk sun fahimci abinda mijin nasu ya aikata, nani tace "ayi mana afuwa, amma muna ganin wannan ai ba shine mafita ba, a zaunar da yaron ayi masa nasiha, asaka malamai suyi tayi masa adduoin nutsuwa, babu abinda yafi karfin addu'a, a hankali komai zai warware. Amma yanzu ba khairat aka raba shi da ita ba, rayuwarsa aka raba shi da ita gabadaya" sarki Abdallah ya ajiye chokalin hannunsa ya juyo yana kallonsu, a hankali yace "ku tashi ku bani guri" babu musu suka tashi suka bar gurin, ya jingina kansa a jikin kujerar dake bayansa, har yanzu ya kasa tantance cewa abinda yayi dai dai ne ko ba dai dai bane ba, odds din sunyi yawa, Sadiq yana da taurin kai kuma tunda yace sai yaje to sai yaje din ko me za'ayi masa, yes addua tana maganin komai amma tana taking time, sadiq ba zai jira ba. Yanzu addu'ar da zaiyi shine Allah ya karya abin wata rana, bayan komai ya lafa, yadda ko Sadiq yaje Riyadh maganar ta riga ta wuce. A ranar da yamma ya aika aka kira Sadiq, ya mika masa takardu guda uku yace "wata takarda nake so ka rubuta min, kayi copy uku, daya da larabci, daya da turanci daya da hausa" ba musu sadiq ya dauki takardar da biro ya fara rubuta abinda mahaifin nasa yake fada masa kamar haka "Bismillahir rahmanir rahim. Assalamu Alaikum wa rahmatullah. Ni Sadiq Abdallah, na saki matata Khairat Abdallah saki daya, idan ta sami miji tayi aure. Bissalam" yana gamawa yayi sauran copies din ya mika wa baban nasa, sannan yace "takardun menene wannan ranka ya dade?" Sarki Abdallah yace "sample ne na yadda ake rubuta takardar saki, zamu ajiye a fada saboda harkar shari'a" sadiq ya danyi dariya yace "sunana na gani shi yasa nayi tambayar" sarki yayi dariyar shima yace "da kai akayi sample din ai, kuma kai ai baka da mata khairat ko kana da ita?" Sadiq ya girgiza kansa yace "I never heard the name". Sarki ji yayi kamar zai yi hawaye dan tausayi.
Haka Sadiq ya cigaba da rayuwarsa, kullum yana ganin wannan yaron mostly tare da sarki, kuma ga mamakin sa sai yaji ana nuna kamar dan nasa ne, duk sanda yaji maganar sai yaji wani bakin ciki kamar ya kama yaron ya shake shi ya mutu, to ya akayi ya zama nasa? How comes? Duk sanda yayi wannan tunanin sai yaji kansa gaba daya ya to she ya kasa tuna komai, wannan shi yake kara irritating dinsa a duk lokacin da yaron yayi masa magana ballantana kuma idan yaron ya tambaye shi wacece uwarsa, sai yaji gaba daya kansa ya toshe kwakwalwarsa ta daina aiki, wannan shi yasa kullum yake kara nisanta kansa da yaron.
Present days
Sarki Sadiq ya share hawayen fuskarsa yana jin matsanancin hausin kansa, duk wannan ya faru ne sanadiyyar taurin kansa da rashin jin maganarsa da kuma kin yiwa iyayensa biyayya a lokacin da suka hana shi auren khairat, amma kuma da akwai rabon sultan a tsakanin su, duk da haka da ace yayi biyayya ga mahaifinsa da mahaifin ya nemi hanyar maslaha cikin sauki ba tare da anyi masa abin da akayi masa ba. Taurin kansa cost him 30 years of his life. Ya tuna da auren da akayi masa, a take wani daci ya taso masa a bakin sa, wannan yarinyar zuwaira ya tsane ta tun tana yarinya, sannan kuma ga abinda tayi, what kind of a father will do what his father did to him? Gashi yanzu ba shi da rai ballantana ya tambaye shi why, amma ai da akwai wacce take da rai kuma yadan da sanin ta akayi komai. Aka hada shi aure da yarinyar da an san da a cikin hayyacin sa yake ko daura masa ita akayi a kafa ba zai tafi da ita ba, gashi yanzu har 'ya'yansu biyu together. Ya mike tsaye ya wake fuskarsa a sink ya dauki towel ya goge, ya sauke ajjiyar zuciya yana kallon reflection dinsa ta mirror, he is back, shekaru basu chanja original sadiq ba, from now everything will be alright.
Yana bude kofar dakin mutanen da suke waiting room duk suka tashi tsaye suna kallonsa da mamaki, da yawa daga cikin su basu gane shi ba saboda ko babbar riga babu a jikinsa ballan tana rawani, ya bisu da kallon daya bayan daya har yaxo kan drivern sa, ya mika masa hannu "baki key" da sauri ya miko masa key din, ya fusga da sauri ya fita su kuma suka bishi da ido. It has been a while daya tuka mota amma bai manta yadda akeyi ba, a hankali ya tuka saboda baya son ya jawo hankalin mutane kansa. Direct sabon waje ya zarce ya yi packing ya tafi da sauri dakin Yaya, tana palo a tare da huda da kuma bayinta biyu suna yi mata tausa. Babu sallama ya daga labulen dakin ya tsaya yana kallonta, hatta huda bata gane shiba amma Yaya ba cire manyan kaya ba, ko menene dan nata zaiyi ba zata kasa gane shiba, a hankali ta mike duk da yanayin jikinta na tsufa, ta mike tsaye tana kallonsa kamar yadda shima yake kallonta, duk da baiyi mata magana ba amma tasan menene ya faru, da hannu ta yiwa mutanen gurin alama da su tashi su fita su basu guri. Suna fita yace mata "why?" Cikin nutsuwa tace "bani bace ba, mahaifinka ne, kuma sanda yayi bai shawarce ni ba" sarki ya hadiye daci a bakinsa yace "amma ya gaya miki dalilin da yasa yayi min haka?" Tace "bai gaya min ba amma na sani, yayi ne dan ya kare ka, yayi ne dan ya kare martabar gidan nan, yayi ne dan ya kare martabar kasar nan baki daya" hawaye ne ya fara taruwa a idonsa yace "to aura min zuwaira fa? Wanne irin uba ne shi? Wanne irin uba ne zai aura wa dansa yarinyar da tayi cikin shege? Wannan ma yayi ne saboda ya kare martaba ta ko saboda ya wulakanta martaba ta? Bai san Yaya tazo kusa dashi ba sai kawai saukar mari yaji a fuskarsa, ya rike kuncin yana jin zagi a ransa, cikin tsawa tace " wannan shine babban dalilin daya janyo yayi maka abinda yayi maka, dan bashi da rai hakan ba yana nufin zaka fada masa duk abinda yazo ranka ba. Komai yayi yayi ne to protect his family, you included".
Ya fara tunanin yadda auren ya kasance, zuwairah cousin dinsa ce, tun tana yarinya baya son ta, jinin su bai hadu ba, tana da rashin kunya sosai ga shegen munafunci, duk a family shi baya son 'yan gidansu saboda sun zama wake daya mai bata gari, tun daga shigar su ma zuwa yadda suke mu'amala da mutane zaka gane cewa ba tarbiyya ce dasu ba. Bayan rabuwarsu da khairat da shekara kawai rannan babansa ya kira shi palonsa na ciki, yana zuwa ya tarar da baba Abdullahi, wanda kani ne a gurin babansa, ya gan su cikin tashin hankali, ya gaishe su suka amsa, nan Sarki Abdallah yake gaya masa cewa Zuwaira ce tayi ciki, saurayinta yayi ya yaudare ta da sunan aure yayi mata ciki ya gudu, basa son zubarwa saboda suna gudun hukuncin ubangiji, kuma basa son magana ta fito saboda kar sunan zuri'ar su ya lalace. Shine suke son su hada shi aure da ita, za'ayi fake aure anan fadar, daga nan sai ace sun tafi kasar waje zatayi karatu, za'a tura ta dangin mahaifiyarta ta gama renon ciki ta haihu, shi kuma sai ya tafi wata kasar ya zauna a can, in ta haihu yaron yayi dan wayo sai a sake daura musu aure na gaskiya kuma amma a boye sannan sai su dawo a matsayin miji da mata da kuma dansu. Yana tuna yadda yaji zuciyarsa tana yi masa zafi kamar zata kona kirjinsa amma bashi da spirit din da zai yi musu, ranar kwana yayi yana kwana yayi yana kukan takaici amma da baban ya kira shi da safe zancen buga IV sai yace "to" yana ji yana kallo aka kakaba masa auren ta, both fake and real din, suka dawo gida kuma ya cigaba da zaman aure da ita ya kuma rike mata danta kamar yadda mahaifinsa yayi umarni da yayi.
Ya dago jajayen idanuwansa yana kallon Yaya yace "yanzu da kuka saka ni na rike shege me kuke tunanin zai faru idan bana duniya, kuna nufin zai ci gadona ne ko kuma kuna nufin zai karbi masarautar nan be ya mulka?" Yaya ta girgiza kai tace "babu ko daya, babanka ai ba fool bane ba, ya rubuta a rubuce ya saka hannu cewa duk sanda babu ranka, Sultan shine magajin ka, idan kuma babu ran Sultan to wani daga cikin kannenka ne zai karbi mulki, yace bai yarda da duk 'ya'yan da zuwaira zata haifa ba, ya bada copy din takarda ga dukkan king makers na masarautar nan, maganar gado kuma kuma ya rubuta ya bawa alkalin da yake raba wa familyn nan gado cewa bayan ranka Abbas bashi da gadonka, amma abar maganar a secret, idan babu ran alkalin next alkali shi zai karbi takardar" ya jinjina maganar, his father is really something. Ya tuna da irin rikon da yayi wa Abbas, da irin rikon da Hajiya tayi wa Sultan, ya tuna maganar giyar data rika feeding Sultan kuma Yaya ta gaya masa amma yayi burus da maganar. Ya juya ba tare da ya ce da yaya komai ba ya fice, mota ya shiga ya karasa palace, su kansu masu bude gate basu gane shi ba motar kawai suka gane, direct part din hajiya ya wuce mutane sai kallon sa suke yi sai in sun gane shi suyi saurin zubewa a kasa. A bedroom ya same ta ta fito daga wanka tana shiryawa, bayinta suna ganin sa suka watse, ta juyo da sauri itama tana kallonsa da mamaki, baya shigo wa part din ta ita take shiga nasa part din. Ya tsaya yana kare mata kallo, how can he have marry this? Ya tuna da khairat, da rayuwarsu together, da sauri ya kawar da tunanin daga ransa dan gap yake da hawaye. Ya ce "how dare you? How dare you treat my son like this? Duk abinda nayi miki, duk rike miki danki da nayi amma ke shine kika wulakanta min nawa dan" da tsananin mamaki take kallonsa, cikin rawar murya tace "Ranka ya dade ban gane maganar ka ba? Wanne dan naka? Wanne dan nawa?" Ji yayi kamar yaje ya zabga mata mari amma yasan dukan mace ba girmansa bane ba, yace "kinsan maganar da nake yi ai. An hada ni dake tare da shegen danki na hada na rike ku tikon amana amma ke kika wulakanta min nawa dan, magaji na, me kike so kiyi archiving? Wato plan dinki shine ki lalata rayuwar yaro na yadda naki yaron zai gaje ni ko? Is that your plan? Ke kika zuga ni na kai shi Lagos gidan kangararru saboda kina so ya lalace, ke kuma kika zuga ni na kaishi America tun yana da shekara goma sha biyu a duniya, burinki ya zama tantagaryar dan iska yadda babu yadda za'ayi a bashi sarauta, abinda baki sani ba shine Allah ya fiki, Allah ya kare min shi burinki bai cika ba, kuma ki sani plan dinki duk a banza kike yinsa, babana daya hada auren nan dan ya rufa miki asiri ba jahili bane ba, yasan me yake yi, ya rubuta ya bayar cewa danki ba zai gaje ni ba, dukiya ko sarauta" da baya ta tafi ta zauna akan gado tana rike zanin jikinta, ta shiga uku ta lalace yau menene yake faruwa, me ya samu Sadiq yau kuma? Tunda akayi auren nan bai taba furtawa cewa Abbas ba dan sa bane sai yau, kuma bai taba kiran sultan da sunan dansa ba sai yau. Me ya faru? Ko ma menene ya faru tasan da sa bakin wannan munafukar matar ta sultan, dama tace tana reading minds yanzu haka ma matsafiyace tazo ta tsafe mata miji zata raba su. Cikin rawar murya tace "wacce magana kake yi ne haka yau kuma. Abinda duk akayi a baya baya wuce ba? Ya zaka taso da wannan maganar bayan ga 'ya'ya muna dasu" ya katse ta yace "ta yaya zan tabbatar da cewa su din ma 'ya'ya na ne?" Da sauri tace "wallahi 'ya'yanka ne, wallahi tunda muka yi aure ban kuma kallon wani namiji ba sai kai" ta durkusa a gabansa ta rike kafarsa, zaninta yana neman kwancewa yayi sauri ya dauke kansa, tace "dan Allah baban Abbas ka daina wannan maganar, ka rufa min asiri yadda Allah ya rufa maka naka" yace "ni kuma kika tona min nawa asirin ba? Ki gaya min abinda kika yiwa dana idan ba tonon asiri ba menene?" Ta dago kai tace "to amma dai ai sanda nace a kaishi lagos din baka musa min ba, kai ka fara wulakanta shi ai, me yasa dana ce maka kayi sai kayo ba za ka yi min musu ba? Ko sau daya baka taba nuna wa kana son yaron nan ba to ni menene laifina dan na taya ka kinsa?" Yasan anan kuma ta fishi gaskiya, amma ko kusa da yana cikin haiyacinsa ba zai bi shawarar ta ba. Ta fara share hawaye tana cewa "dan Allah mu bar maganar nan haka, yadda iyayen mu suka rufe ta to kar mu bude ta dan Allah" ya sunkuyo dai dai fuskarta yace "da ace kin rike min dana da mutunci, da babu wanda zai san waye Abbas, da ace kin kula dashi a lokacin da ni na wulakanta shi, da nima yanzu sai in cigaba da kula da naki dan, d'a na kowa ne amma kika nuna nawa ba naki bane ba, dan haka nima yanzu naki ba nawa bane ba" ya mike tsaye yana kallonta cikin ido yace "na sake ki saki biyu, amma in banda ni da waliyan mu babu wanda zai sani in kin ga dama, zaki cigaba da zama a dakunan ki tare da 'ya'yanki. Abbas kuma ki tattara shi ki kaishi gurin ubansa, ki sanar masa bani ne mahaifinsa ba, in ba haka ba ni zan sanar masa da kaina a fada" ya juya ya fice ba tare da ya kuma kallonta ba. Wani relief yake ji a ransa, ya yarda kwallon mangwaro ya huta da kuda. Hajiya kuma mutuwar zaune tayi a gurin, bata taba tsammanin abin yayi zafi haka ba, saki? Ita din? Da girman ta da komai? Yau wacce irin rana ce? Ita yanzu ta ina zata fara fadawa Abbas cewa shi shege ne? Yau ta shiga uku ta lalace.
Ina fatan 'yan'uwana mata mun dauki darasi daga darasin Hajiya. Indai kika bari wani ya lalata ki to shi tafiyarsa zaiyi kamar baiyi komai ba, ke kuwa ke zaki kasance cikin takaicin abin har karshen rayuwarki, dan in kinyi aure ma kullum mijin zargin ki zaike yi. Ballantana ace kinyi cikin shege, in kin zubar alhaki a kanki, in kin barshi kin bar tambari har abada, shi kansa yaron har ya mutu ba zai ji dadin rayuwa ba, gori kullum, sai an tashi aure ma a rasa wanda za'a hada auren dashi tunda kowa yana son auren mai asali. Darasi na biyu kuma shine, d'a na kowa ne, in kika rike dan wata to kuwa tabbas za'a rike miki naki ko kina raye ko kin mutu. Ki sani zaki iya mutuwa a koda yaushe ki bar 'ya'yanki, za kuma ku iya rabuwa da mijinki ki bar 'ya'yan a gurinsa. Mu shuka alkhairi 'yan uwa, in mune yau ba mune gobe ba.
Episode Eighty Three : The News
Moon
Na jima da wayar a kunnena ina lissafa maganar ta amma na kasa bata amsa saboda wani irin shock da naji, har saida tace "Moon kina jina kuwa" nayi sauri nace "ina jinki Hafsat vara in duba picture din" na katse kiran na shiga WhatsApp, hannuna har rawa yake yi "oh dear God, let it be" na fara downloading picture din amma gani nake yi kamar ba zai gama budewa ba, sau biyu yana failing ina sake trying. Finally ya bude, sai da na dauke numfashi na saboda mamaki abinda na gani, hoton balarabiyyar na gani, amma kuma kamar sultan da siffar mata, the eyes, the nose, the lips, the eye brow, the eye lashes duk irin na sultan ne, hatta murmushin da tayi irin na sultan ne, farin fata kawai ta fishi sai kuma kasancewar ta macece, amma kuma anya wannan ce ta haifi sultan? She is too young to be his mother, amma kuma har sunan iri daya. Na kira Hafsat, tana dauka tace "kin ganta ko Moon?" Nace "na ganta Hafsat. A ina kuka hadu?" Ta fara min bayani "Aunt din Zayed ce, kanwar babansa, to irin bata shiga mutane sosai shi yasa tun da muka zo bamu ganta ba, sai dazu baban Zayed yace masa lallai yau ya kaimu gidanta mu gaishe ta. She live alone a gidan nata ma. Wato Moon kudi ne da ita kamar banza, 'yar kasuwa ce sosai, babu da babu jika, babu kuma miji, ina ganinta gabana ya fadi, nayi ta kallonta ina tunanin dawa take yin kama? Kawai sai da tayi murmushi na gane sultan ne, kuma na tuna cewa mamansa balarabiya ce, amma ban tambaye ki sunan ta ba" na sauke ajjiyar zuciya nace "Sunan ta khairat" da sauri Hafsat tace "Allah da gaske? Moon ita ce mamansa kenan?" Nace "I don't know Hafsat, amma baki ganin tayi yarinta da yawa?" Tace "ke dalla can hutu ne fa, kinga sisters dinta data girma kuwa?" Nace "amma me zayed yace miki a dangane ta ita? Ta taba aure a nan ko kuma ya labarinta yake?" Hafsat tace "it is all mysterious Moon, zayed bai san komai a kanta ba, da yake shi kinsan ba'a Riyadh ya tashi ba kawai abinda ya sani shine rayuwar ta take yi ita kadai bata shiga mutane, kuma tunda ya santa bata da aure" na danyi shiru ina tunani nace "please Hafsat can you get her to talk to you?" Hafsat tace "I think so, kinsan hali na da bin kwakwkwafi, kuma daga gani na ta fara sona bansan dalili ba, ga kuma khairat mai sunan ta" sai kuma tayi shiru sannan tace "wai dama sunan ta kika sakawa khairat" na danyi dariya nace "eh sunan ta ne" Hafsat tace "Munafuka, shine kika saka wa yarinya ta sunan surukarki ko?" Nayi dariya nace "to ai gashi nan kema maybe surukar taki ce" Tace "show sultan the picture ki ji abinda zai ce, ni kuma zan fara tambaya inji labarin ta, ko a gurin ummeen zayed ne, daga nan sai mu gane ko ita ce ko ba ita bace ba" na danyi shiru sannan nace "Hafsat bama tare da Sultan yanzu" kamar bata ji sosai ba tace "what?" Na ce ina jin hawaye yana taruwa a gefen idona "ina gida yanzu" tace "subhanallah Moon wannan wanne irin muguwar magana kike fada min hakan? Sultan din tafiya yayi kika zo gida?" Nan hawaye ya balle min nayi tayi, tana jina bata ce min komai ba, sai da na gama dan kaina sannan na fara bata labarin abinda ya faru gaba daya, na kara da cewa "Hafsat ban san ya zanyi ba, Sultan zafin zuciyarsa yayi masa yawa Hafsat, shima Ibrahim ban san me yake so inyi masa ba, nayi aure kuma ina ruwansa dani?" Hafsat tace "to ai ni sultan yayi min dai dai, cin ubansa ya kamata yayi yadda gobe in ya hango ki a guri da gudu zai fita. Yanzu kina nufin akan Ibrahim din kika baro gidan mijinki?" Nace "Hafsat ba'a kan Ibrahim bane ba, akan Sultan ne, akan bakar zuciyarsa, Hafsat kisan kai fa yayi niyyar yi, da Ibrahim ya mutu me kike ganin zai faru da shi? Me kike ganin zai faru dani? Sannan zargin da yayi min shi yafi komai kona min rai, he should have trusted me" Hafsat tace "tayaya kike tunanin zaiyi trusting dinki bayan ko cikin da kike dashi baki gaya masa ba? Idan da ace yasan da cikin da duk haka ba zata faru ba, idan kakar chocolate kike so zai fita ya sayo miki, in ma ya ganki da Ibrahim din yasan ba purposely kika hadu dashi ba. Idan kika yi la'akari da rayuwar sultan dole yana da trust issues, he is scared of loosing you, gani yake yi kamar kowa is against him" nace "amma Hafsat, upon all what we went through together, ya kamata ace by now ya yarda dani" tace "kin bashi reasons din da zai yarda da ke ne? Mun jima muna tattauna wa da Hafsat a waya, ban ankara ba kawai sai naji wayar ta mutu, ban kunna ta ba kwanta ina lissafa maganganun Hafsat a raina, is what happened my fault? Ban boye wa Sultan maganar cikin nan saboda komai ba sai don ina son inyi surprising dinsa, but I get more than what I bargain for. Naji an fara kiraye kirayen sallah dan haka nasan inna ce zan kwanta bacci zanyi missing din sallah asuba, dan haka na saka phone dina a charge nayo alwala nazo na bude al'qurani na na fara karatu, ina nan har akayi assalatu nayi sallah sannan na kwanta, kafin bacci ya dauke ni na yanke shawarar cewa first thing in the morning zan nuna wa Daddy picture din da Hafsat ta turo min, tunda ya san mahaifiyar sultan zai iya tabbatar min idan itace ko a'a, next thing zan kira Sultan inji halin da yake ciki, my heart can't take hurting him. Amma ga mamaki na ban farka ba sai after 11am, kuma nasan physical and mental exhaustion ne ya kawo min dogon baccin. Ina tashi na kunna wayata, ko wanka banyi ba na saka hijab dina na tafi neman Daddy, a palon sa na same shi shida Mommy, na karasa na gaishe su, Mommy tace "yanzu nake tunanin ko tashin ki za'ayi kichi abinci, sai Daddy n ki yace a barki ki tashi da kanki" na danyi murmushi ina searching picture din da Hafsat ta turo a waya ta, food is the last thing on my mind babu abinda nake so irin inga Sultan, maybe I am weaker than I thought in dai akan soyayyar Sultan ne. Ina samo picture din na karasa gaban Daddy na mika masa nace "Daddy kasan wannan?" Ya karbi wayar daga hannuna sannan ya mike zaune daga kashingiden da yake, ya kalleni sannan ya kuma kallon screen din yawar yace "a ina kika samu hoton khairat? An ganta ne?" Ji nayi wani excitement yana taso min tun daga kafafuwana har cikin kaina, nace "Daddy ita ce mahaifiyar Sultan?" Yace "of cause itace mana, baki ga kamar ba?" Da sauri Mommy ta matso tana kallon hoton tace "Allah mai iko, kamar tasu har ta baci" na tashi da sauri na rungume Mommy ina jin dadi, sai kuma naji kunyar ta na sake ta, Daddy ya tambayeni inda na samu hoton nayi masa bayani, nan suka kara wani mamakin, ikon Allah kenan, wai all this while a she sultan da Zayed 'yan uwa ne babu wanda ya sani. Mommy tace "to yanzu menene abinyi? Zaki gaya masa ne ko zaki bari Hafsat tayi bincikenta a can muji dalilin da yasa duk tsahon wannan shekarun bata nemi danta ba?" Na girgiza kaina , a raina nace "not again, na daina boyewa sultan komai insha Allahu" a fili nace "Mommy zan gaya masa, yana da right ya sani, shi zai yanke decision din me ya kamata yayi" Daddy ya amince, yace "amma ai naga jiya kin kore shi, yanzu kiransa zaki yi? Na dan sunkuyar da kaina ina murmushi, Mommy tace " kar dai kice min shikenan har kin gama horon nashi da zaki yi? Duk kurin zubar da ciki da waye har ya kare kenan, kar ki rako mata mana maimunatu" na rufe fuskata da hannayena, Daddy yace "in kin huce ma ni ban huce ba, sai yazo ya bada hakuri kuma yayi min alkawarin irin haka ba zata kuma faruwa ba. Shi kuma wancan har yanzu fa bai dawo haiyacinsa ba, dan haka nasa anyi wa family dinsa waya a can ibadan an gaya musu halin da yake ciki" bance komai ba saboda bazan iya yiwa Daddy musu ba amma ni kam da zai barni da yanzu zan tafi in kira sultan in bashi labarin mahaifiyarsa, maganar Ibrahim kuma naji babu dadi, it is a pity, naji tausayin mamansa da 'yarsa, a raina nayi masa addu'ar samun lafiya, Daddy yace "ko zaki je ki duba jikin nasa?" Nayi saurin girgiza kaina, there is nothing more between me and him, ni yanzu kawai mijina nake son gani.
Jin basu sake cemin komai ba na gane sun gama magana dani kenan, na tashi na tafi palo ina neman abinda zanci, na faki ido naga babu wanda yake kallona na dauko waya ta nayi dialing number din sultan, amma bansan me zance masa in ya dauka ba, tana ta ringing amma ba'a dauka ba, a raina nace yayi fushi shima, nafara duba messages wai ko ya turo min message ban sani ba, babu message din sultan sai na Amir, na buda na fara karantawa "your husband is sick, kuma ke yake nema" wayar ce ta zame daga hannuna ta fadi kasa, nima na bita na zauna dabas a kasa, for seconds kaina ya toshe, sannan kuma cikin karkarwar hannu na dauki wayar zuciyata tana wani irin bugawa na kira number din Amir, bugu biyu ya dauka yace "Moon ina kika shiga tun safe ina ta nemanki wayarki a rufe. Muna asibiti da Sultan fa bashi da lafiya" cikin muryar kuka nace "Amir me ya samu Sultan? Ya jikin nasa? Amir na shiga uku" yace "baki shiga uku ba Moon jikin Sultan da sauki, dazu dai babu yadda yake amma yanzu ya samu relief, please amma ki zo yanzu in ya ganki zai kuma jin dadi" na saki wayar na dora kuka na daga inda na tsaya, Sultan babu lafiya amma ni ina gidan mu bana tare dashi, kuma am 100% sure cewa ciwonsa dalilin maganganun dana gaya masa jiya da daddare ne, ni maimunatu na shiga uku, in wani abun ya sami sultan I will never forgive myself. My Darling Sultan. He calls me his love but I didn't act like love, bashi da kowa sai ni and I too pushed him away. What have I done? Amina ce ta sauko ta ganni ina ta rusar kuka ta karaso da sauri tana tabani tace "Moon lafiya? Jikin ne?" Ban bata amsa ba ta koma sama da sauri sai gasu tare da Mommy, Mommy hankalin ta a tashe tace "Moon lafiya" na share hawayena nace "sultan ne bashi da lafiya, yana asibiti" tace "kuma dai? Astagfirullah, Allah in laifi muka yi maka ka yafe mana".
Da kyar Mommy ta matsa min nasha tea kadan, shima ina gama sha nayo mata amansa, tunda na samu ciki ban taba amai ba sai ranar nan. Ni duk burina inga Sultan in san halin da yake ciki, duk wani abinci da maganar ciki ne dani su biyo baya, a gurina lafiyar sultan itace a sama. Ganin yadda na tashi hankali na ya saka Mommy tace mu tafi tare da Amina, in an jima ita sai su zo tare da Daddy, ai kam ban jira komai ba nayi gaba, Amina ma a mota ta same ni, muna zuwa asibitin Amina ta kira number din amir ta gaya masa munzo, ya fito yayiana jagora zuwa dakin da sultan yake.
Tun daga window na hango shi a kwance yana bacci. Nayi sauri na bude kofar na shiga. Shi kadai ne a dakin, babu riga a jikinsa amma an lulluba masa bargo har saman kirjinsa, gani nayi ya rame sosai, fuskarsa tayi fari tas. Duniya kenan, wai sultan ne ciwon kwana daya yayi masa wannan kayarwar. A hankali na karasa na dauki hannunsa na rike a nawa, muryata har ta dashe saboda kukan da nakeyi. Amina ta karaso ta dafa ni tana bani hakuri amma ko kallonta banyi ba. Ni kadai na san me nake ji a raina. Ba wai ciwon sultan din ne yake saka ni kuka ba, abinda yafi damuna shine kasancewar nice sanadiyyar ciwon nasa shine abinda yafi damuna. Ban san ma Amina ta fita ba sai dubawa nayi naga bata nan. Na fara yi masa magana a hankali "Sultan ka tashi dan Allah, menene hakan ne wai kai sai kace ba namiji ba zaka wani kwanta ka kama rashin lafiya. Kace ba zaka iya rayuwa babu ni ba, to ka sani nima bazan iya rayuwa babu kai ba, dan Allah sultan ka tashi kace ka yafe min, zuciya ta ba zata iya jurar ganinka a kwance ba Sultan zuciya ta bugawa zatayi in mutu, kaine rayuwata, kaini jinin jikina, kaine mijina kuma uban 'ya'yana. Sultan kayi hakuri, duk abinda na gaya maka wallahi ba da gaske nake ba. Dan Allah ka tashi, sickness doesn't suit you, ga babynmu kuma yana nemanka yana so ku gaisa." Na dora hannunsa akan mara ta na cigaba da cewa "ka ji shi ko? Kwanan nan zai fara motsi, he is going to grow up to be stronger than you, shi ba zai kwanta ciwo saboda sunyi fada da matarsa ba" na dawo da hannun sama na dora fuskata akai hawayena yana bin hannun nasa nace "my poor darling sultan, my sweetheart my honey, my angel my heartbeat, my life my happiness, my husband my babies Daddy" a hankali naga ya fara bude idanunsa, ya sauke su a kaina, they are the same most beautiful eyes I have ever seen, amma sun dan fada ciki kadan, murmushin gefen baki yayi min yace "indai wadannan kalaman za'a ke gaya min in bani da lafiya to kuwa kullum sai nayi ciwo" na saki hannun sa da sauri gaba daya na fada kansa na zagaye wuyan da hannayena ina sake wani sabon kukan yace "ouch, karki ballani mana baby girl, baki san kin zama 'yar lukuta ba yanzu?" Na dan dake shi kadan a kafada nace "kaine dai dan lukuti, mai kwanciya ya kama rashin lafiya kawai" ya saka hannu daya ya dago ni yana kallon fuskata yace "to ya isa haka kukan in ba so kike a baki gado a kusa da nawa ba" na tashi ina goge hawayena, har yanzu idonsa na kaina yace "you look terrible, da wasu jajayen kunburarrun idanuwanki" na dan harare shi nace "in kawo maka madubi ka kalli kanka kaga yadda ka zama?" yace "no, I don't want to see" ya daga bargon jikinsa, naga daga shi sai gajeran wando da singlet, yace "come here, zo in sammiki zazzabi na" ba musu naje na shige jikinsa na kwanta, ji nayi kamar wacce tayi tafiya nai nisa ta gaji sannan ta dawo gida, irin feeling din nan na finally I am home, na sauke ajjiyar zuciya na kara shigewa jikinsa ina jin zafin jikinsa yana ratsa ni, ya dora hannunsa akan marata yana shafawa a hankali, nace "am sorry sultan, for not telling you about the baby, I wanted to surprise you" murya can kasa yace "it is OK" a hankali yace "do you mean all what you just said. Da gaske abinda kika fada min a dakin ki ba da gaske kike ba?" Na girgiza kaina da sauri nace "wallahi ba da gaske nake ba. Am so sorry I said those words" yace "NO, I am sorry, ni nayi forcing dinki ai kika fada min hakan. Am sorry about what I did Nace "it is OK, ya wuce" mun jima a haka, na dauka ma ya koma bacci, sai naji yace "something weird happened da zu. Takawa yazo dubani" na daga kaina ina kallon fuskarsa da mamaki nace "what?" Yace "yes, i don't know me ya faru, amma ina tunanin Amir ne yaje ya gaya masa, sai dai bansan ya akayi yazo din ba, I just woke up and he was here, he held my hand and then he fainted" nace "fainted?" Yace "yes. Komai ya faru ne da sauri bansan menene ya faru ba, yazo nan, ya kama hannuna sai kuma ya suma, suka dauke shi suka fita dashi, sai doctor yazo ya saka na koma bacci, am just not sure whether da gaske abin ya faru ko kuma mafarki nayi" na mayar da kaina na kwantar a kirjinsa ina sauraron bugun zuciyarsa, na danyi tunani kadan akan abinda yace, we will have to ask Amir menene ya faru. Ba tare dana kalle shi ba nima na fara magana "something weird also happened jiya da daddare" nayi shiru kuma na kasa yadda zan fada masa, sai da yayi magana yace "what happened?" Sannan na cigaba da magana "Hafsat ta hadu da Ummeen ka a Riyadh" farko yi yayi kamar baiji me nace ba, sai kuma ya mike zaune da sauri, taking me with him, yana kallona fuskarsa babu alamar dariya yace "me kika ce?" Na jawo yawa ta na bude masa hoton mahaifiyarsa na mika masa, "Sultan wannan itace mahaifiyarka, you and zayed are cousins". A hankali ya karbi wayar yana kallon hoton, emotions fal a fuskarsa.
Episode Eighty Four : Little Love
Ya dago ya kalle ni nayi masa murmushi ya sake kallon hoton sannan yace " then she is alive. All this time ina tunanin cewa bata raye shi yasa bata neme ni ba, amma tana raye ashe, kawai ta ajiye ni tayi tafiyarta, without a second thought" nace "please Sultan kar ka ce haka mana. Baka san uzurin ta ba. Ka bari idan ka samu lafiya sai mu tafi har Riyadh din mu same ta acan, ka gabatar mata da kanka, na tabbatar zata yi maka gamsashshen bayani a dangane da wacece ita" tun kafin in karasa maganar yake girgiza kansa, yace "I will not go, babu inda zanje, haka kawai muje ta wulakanta mu? Kamar yadda ta wulakanta ni ta ajiye ni ta tafi? If she wants to see me ai tasan a inda ta barni, in tana son ganina tazo inda nake" nayi sauri nace "sultan uwa ce fa, kar ka fadi mata maganar da Allah zaiyi fishi damu kuma" yace "ko menene nace mata Allah ba zai kama ni ba. I don't know much about love but naji ana cewa mother's love is the purest of love, hakan yana nufin ya kamata ace sonda take min yafi son da nake miki yawa, ni kuma nasan a yanzu yadda nake jinki a raina rabuwa dake will be the end of me. Ita wacce irin zuciya ce da ita?" Sosai naga ransa ya baci na tuna cewa bashi da lafiya, na karbi wayar daga hannunsa nace "sultan baka da lafiya, let's not talk about this now, in ka samu lafiya sai mu san abinda zamuyi akai" ya jawo ni jikinsa muka koma muka kwanta, ya jawo bargo zai rufe mu, temp dinsa naji da zafi na yaye bargon, ya rabu dani bai tanka min ba sai kara matse ni da yayi a jikin sa, yace "tell me something nice" banyi magana ba na dora hannunsa akan mara ta, yayi dariya kadan yace "yeah, that's a nice topic of discussion" ya danyi shiru sannan yace "mace nake so ki haifa, mai kama dake kuma mai halinki, kuma ina son itama take sona kamar yadda kike sona. Maimunatu zan saka mata" nayi sauri na kalle shi nace "maimunatu? Ai sai muyi maka yawa kuma" ya saka dan yatsansa yana zagaye lips dina dashi, abinda yake fara yi lokuta da dama in zai kissing dina, yace "kin taba ganin inda haske yayi wa mutum yawa a rayuwarsa? Gaba daya rayuwata a cikin duhu nake yinta sai da kika zo sannan kika fara haska min hanya, you brought so many blessings to me, uncountable, yanzu ga baby, to menene laifi dan na kira ta da moon itama, kogi ma ai baya kin dadi" naji dadin maganarsa amma nace "idan hasken yayi maka yawa kuma ai sai ya kashe maka ido ka kasa gani sosai" yace "sai in saka sunglasses" a tare muka yi dariya, abinda nayi tsammani shi ya biyo bayan dariyar tamu, hot kiss, wanda naji shi tun daga kafata har kaina, ganin yana neman zarcewa ya saka na ture shi nace "a asibiti fa muke baka da lafiya" ya shagwabe fuska "ni na warke ai" nace "to in ka warke ka bari a sallameka in munje gida koma menene za'ayi sai ayi, amma yanzu in wani ya shigo fa? Besides kai da baka da lafiya so kake ka karar da sauran karfinka ko?" Bai kula ni ba ya koma ya kwanta irin yaji haushin nan. Banyi aune ba kawai bacci ya dauke mu a haka, daga ni har shi.
Karar wayata ce ta tashe ni daga baccin nayi sairi na mike na sauko ina gyara kayana da sukayi squeezing, na dauka naga Amina ce, ni nama manta tare muka zo da ita. Na dauka da sallama tace "Moon dubiyar kenan? To albishirinki wallahi Mommy da Daddy har da Takawa sun shigo sun ganku" nace "na shiga uku Amina dan Allah da gaske kike?" Tace "wallahi Takawa dai ya shigo, su Daddy kuma yanzu suka zo suka turo ni, na ganku na koma, yanzu ni me zance musu" nace "gani nan fitowa, tunda basu ganmu ba da sauki, Takawa kuwa ba haduwa mukeyi ba ballantana in ji kunyarsa" na kalli sultan naga ya tashi yana kallona, nace "su Daddy sunzo suna waje, an ce Takawa ma ya zo amma ban sani ba ko yana nan ko ya koma" ya tashi zaune yace "then dazu ba mafarki nayi ba kenan" nace "yes Sultan, ba mafarki kayi ba". Na nemo rigarsa na saka masa, yana tayi min complain yunwa yake ji, Allah ya taimake ni su Mommy sunzo da abinci, dan haka suna shigowa na bude na fara zuba masa, dama Sultan ba kunyar Daddy yake ji ba, gwara ma Mommy, ya zauna ya fara cin abincinsa nima Mommy ta matsa min lallai saida na zuba naci. Muna nan tare dasu, Sultan ya ware suna ta hira da Daddy wanda shima naga ya dan sakarwa sultan din, Amir ya shigo, ya gaishe dasu Daddy, nan yake bamu labarin yadda yaje ya kira Takawa da abinda ya faru bayan zuwan Takawan, muka kalli juna ni da Sultan, Amir ya cigaba da cewa " kowa yayi mamakin me yasa yayi fainting, the doctor said he need rest wai stress ne, shine aka kaine daki aka kwantar kuma bayan an jima kawai sai gashi ya fito ko manyan kaya babu, ya karbi key din mota ya fice, babu wanda yasan inda yaje sai dazu ya dawo, yazo nan kuma ya koma can inda aka kwantar dashi, yanzu ya aiko akayi kirana yace inzo in yima sultan knocking ince ya tashi ya ci abinci yayi sallah" muka sake kallon juna ni da Sultan, Daddy yace da Amir ya koma ya gaya wa mai martaba sarki cewa sultan ya tashi har yana cin abinci ma, kuma ya gaya masa jikin sultan da sauki ya kwantar da hankalinsa. 'Yar karamar dariya sultan yayi sannan yace "he doesn't care, kawai drama yake playing" nan take Daddy yayi kansa da fada "ba drama ba koma menene yake playing he is your father, dole kayi respecting dinsa" dama Daddy da dan sauran fushin sa akan abinda sultan yayi, nan ya wanke sultan tas da soso da sabulu, Sultan bai sake magana ba. Bamu ankara ba sai ji mukayi anyi knocking kofa an shigo, Takawa ne da kansa a tsaye a bakin kofa, ya saka babbar riga yanzu, da hula a kansa babu rawani. Fuskarsa babu dariya, idonsa akan sultan. Wani kwarjini naga yayi min sosai, lallai sultan anan ya samu kwarjinin sa. Daddy ya fara kokarin gaishe shi amma sai muka ga ya mika wa Daddy hannu sunyi musabaha, ya karaso cikin dakin duk muka tashi muka fara gaishe shi banda sultan da yake kallon kasa, Amina ta kwashe kayan da muka gama cin abinci ta fita Mommy ma ta bita a baya, na tashi nima zan bisu amma Sultan ya rike hannuna ya dawo dani baya, Daddy ya kalle mu bai ce komai ba shima ya fita. Ya zama saura mu uku, na danyi dariya nervously na kuma kokarin fita amma sultan yaki ya saki hannuna kuma har yanzu kasa yake kallo. Takawa yayi gyaran murya yace "Maimunatu dan bamu guri zamuyi magana" Sultan yace "she is not going anywhere, duk abinda zaka fada min ka fada a gabanta" na kalleshi ina tunanin baiji fadan daddy ba kenan, nace "sultan? Takawa ne fa" yace "you are not going anywhere, in ba zaiyi magana a gaban ki ba ya fita" irin rikon da sultan yayi wa hannuna kamar zai balla ni da kuma yadda naga jikinsa yana rawa ya saka na fahimci ba wai ya hana ni fita ne saboda ya bata wa Takawa rai ba, a'a he is nervous, bai taba zama daga shi sai babansa sunyi magana ba, he needs my support. Na zauna akan kujerar gefensa ina kokarin mu hada ido amma yaki bari in kalli cikin idonsa. Takawa ya karaso gaban gadon sultan ya dan tsaya yana kallonsa, sai kuma naga ya zauna a bakin gadon wajan inda kafafuwan Sultan suke, ya saka hannu yadan bude bargon, ya fara shafa kafar sultan a hankali kamar mai matsa masa kafar, ya fara magana "my Little Love, you are just as strong and brave as I thought you will be. Bansan yadda zaka dauki maganganun da zan gaya maka ba amma ina son ka sani, duk abinda zan gaya maka shine gaskiyar abinda ya faru, kuma abinda zan gaya maka shi zai zamanto amsar tambayoyin da kake yiwa kanka kullum a kaina da mahaifiyarka" nan ya fara zayyano mana labarin da ya saka na saki bakina ina kallonsa, babu wanda yayi magana a cikin mu har ya gama maganar sa, tun daga haduwar su da khairat har dauketa daga gidansi da yayi da auren da sukayi a America, har labarin haihuwar sultan da kuma dawowarsu Nigeria, yadda rabuwarsu ta kasance da abinda Sarki Abdallah yayi bayan rabuwar tasu, aurensa da Hajiya da asalin labarin Abbas, yadda ya dawo hankalinsa yau da kuma sakin da yayi wa Hajiya dazu. Ya cigaba da cewa "ka sani Sultan, ba zan iya dawo da hannun agogo baya ba kuma bazan iya biyaka abinda kayi missing na kulawar iyaye ba, amma daga yau zan nuna maka me ake kira da soyayyar iyaye. Ina nema wa mahaifina gafara a gurinka a bisa abinda ya aikata, kuma ka sani, bayayi hakan bane dan son ransa ko dan ya cutar damu ba, a'a yayi hakan ne saboda yana ganin shine zabin da yafi dacewa a lokacin" ya mike tsaye kamar zai fita kuma sai ya tsaya ba tare daya juyo ba yace "you are no longer the little love I know, you are a grown up man now, kayi tunani akan duk abinda na gaya maka, sai ka yanke hukuncin da kaga ya dace" ni dai da ido nake binsa har yakai bakin kofa sai ya juyo muka hada ido, ga mamaki na sai naga yayi min murmushi sannan ya fita. Na dawo da hankali na kan sultan wanda har yanzu idanuwansa a kasa suke, I can't imagine me yake ji a ransa a yanzu, maganar is hard to digest, I only know that he needs a hug right now dan haka abinda na bashi kenan, a shoulder to cry on, na hau kan gadon na rungume shi idona yana fitar da kwalla, da sauri shima ya rungume ni kamar zai balla ni, sai jin saukar hawayensa nayi a bayana, nima kukan nake yi sosai. Rayuwar sultan kadai ta isa ta zama darasi ga dukkan mai tunani, komai yayi farko yana da karshe kuma ance mahakurci mawadaci ne watarana. Na fara rarrashinsa ina bubbuga bayansa a hankali, nace "shhhh it's over, komai ya wuce, everything is going to be alright".
Da daddare aka sallame mu, direct gida muka tafi. Ga mamakin mu har muka tafi Takawa yana asibitin, amma yana daya dakin sai dai ya turo amir ya ga me Sultan yake yi ya koma ya gaya masa. A motar Amir muka tafi gida, da escort a gaba, sai motar mu sai motar Takawa sannan sauran motocin. Yau sai ga Takawa a gidan mu, shine har cikin bedroom din Sultan, sai daya jaddada min lallai in tabbatar yaci abinci sannan ya rage masa AC n dakin ya tafi. Sultan duk ya zama wani shiru shiru, kuma na fahimce shi, abubuwa ne da yawa suka faru kusan a lokaci daya, yana bukatar lokaci yayi adjusting ya san menene abinyi. Abinda nayi ni kuma a bari na shine na bar maganar ban yi masa ba, na barshi ya shirya da kansa yayi min maganar sai in bashi shawarar da nake ganin ta dace.
Washegari maman Ibrahim ta zo Abuja, a ranar kuma ya farka, he is very lucky babu wani serious internal or external injury daya samu, yana farkawa ni ya fara tambaya if am OK, aka gaya masa am fine, sai yace Amina ta kira mu nida Sultan ta bamu hakuri akan abinda ya faru, yasan laifinsa ne, shi yayi pushing Sultan har ya tura motar sa rami, shima kansa bai san menene ya saka shi ya bi mu a baya ba, Amina tana gayamin a waya a raina nace 'destiny ne, da ace bai bimu ba, abindaya faru bai faru ba, da Sultan bai yi rashin lafiya har sihirin da aka yiwa mahaifinsa ya karye ba' Amina ta tambaye ni ko zan zo in duba shi nace sai na tambayi sultan, Sultan kam yadda yake very emotional nasan bama zan fara mentioning sunan Ibrahim ba, dan haka ban ma tambayeshi ba. Washe gari Amina suka zo min ita da little Moon, sosai yarinyar ta kwanta min a raina, nace "what is your name" tace "Moon" nace "really? Nima sunana Moon" tayi dariya nace mata "can I call you namesake?" Tace "yes". Daga yadda Amina take yiwa yarinyar na kara tabbatarwa cewa Amina is in love with Ibrahim, naji dadin hakan kuma har raina, ina yi musu fatan Allah ya tabbatar musu da alkhairin dake cikin lamarin.
MAIMOON
By
Maman Maama
Episode Eighty Five : Ibrahim
Happy Birthday Oluwaseun Ibrahim Adeniran. May you forever be happy. Kar ka chinye cake din kai kadai dai.
Ibrahim
Last thing da ya gani kafin motar sa ta fadi shine fuskar Moon, and she looks so scared. Sanda motar sa ta fadi babban tsoron sa shine ba mutuwa ba, tsoronsa shine kar wani abu ya sami Moon because of him. A lokacin daya dawo hankalinsa abinda ya fara tunawa shine Moon, Allah dai yasa babu abinda ya same ta, dan haka kalmar daya fara furtawa itace "Maimunatu" muryar mamansa yaji a kusa dashi tana yi masa magana, sannan kuma yaji shigowar wani namiji yana tattaba shi, mutumin ya bude idonsa ya haska masa wata karamar fitila, daga nan kuma ya koma bacci. Sai daya farka for the second time sannan ya fahimci kwanansa uku a asibiti unconscious, ga maman sa da little moon sun zo daga ibadan, amma ita maman sa abinda aka gaya mata shine accident yayi, ba ta san dalilin accident din ba, dan haka ya san bata da labarin ko Moon taji ciwo ko bata ji ba. Doctor ya saka ya kira Amina, wacce tun da ta kai shi asibiti kullum sai ta je ta duba shi, haka ma Daddy, doctor ya gaya wa Amina cewa ya farfado kuma yana nemanta, ba'afi awa daya da wayar ba sai gata tazo. Sosai ta nuna murnar ta daganin ya dawo hayyacinsa, ta ringa yiwa doctor din tambayoyi akan lafiyar Ibrahim din har sai da ta fahimci babu wani muhimmin concern dangane da lafiyar tasa, shi kam Ibrahim kallonta kawai yake yi yana murmushi, sai da doctor ya fita sannan yace "har haka aka damu dani dama ni ban sani ba?" Tace "no, ba damuwa nayi da kai ba. Naso ace ka balla spinal cord yadda ba zaka sake bin mata da miji ba" yace "yes you are right. Nasan banyi dai dai ba, komai yayi min ni na jawo wa kaina, I was just scared he would hurt Moon" tace "matarsa ce fa? In ma menene zaiyi mata ina ruwanka? Kuma ma Sultan will never hurt Moon. Yanzu gashi sanadiyyar abinda ya faru sunyi rigima, har ya kwanta a asibiti ma. She is pregnant fa. You ought to get over her by now" yace "I am over her. Abinda ya faru nima ban san ya akayi ya faru ba and am sorry na jawo problem a tsakanin su. Is she OK?" Tayi ajjiyar zuciya ta zauna a kujera tace "yes she is fine" yace "please can you go to her ki bata hakuri on my behalf? Ki basu hakuri ita da mijinta" ta bata fuska alamar bata son zuwa, ya marairaice murya, "please kinga bani da lafiya fa. Take little Moom with you in suka ganta sai sufi hakura". Har ran Amina bata so zuwa ba, ita a ganinta menene kuma na zuwa wani bada hakuri? Ai kamar kokarin tayar da magana ne kuma, aikin gama ya riga ya gama, daga Ibrahim har Sultan kowa jikinsa ya gaya masa shikenan magana ta wuce sai dai fatan a kiyayi gaba kuma. Amma sai ta yarda zata je din to put his mind at ease. Ta dauki little Moon suka tafi tare. Moon ta tare su sosai kuma taji dadin ganin takwararta amma kamar yadda Amina tayi tsammani sam ba ta ga alamar soyayyar Ibrahim a tare da Moon ba, sai care da mutunta juna, tace mata zata zo ta duba Ibrahim amma ita kan ta Aminan ta san fada kawai Moon tayi ba zuwan za tayi ba. Ga zasu taho Moon ta hada kaya da yawa ta bawa takwararta suka dawo asibiti gurin Ibrahim.
Suna shiga dakin suka tarar Ibrahim ya tashi zaune suna magana da mama, Amina ta durkusa ta gaishe da mama wacce ta amsa mata da fara'arta, daga nan mama ta fita ta basu guri suyi magana. Ba tare daya kalli Amina ba yace da little Moon "sweetheart menene wannan a leda kika samo haka?" Ta karaso gurinsa tana washe baki tace "namesake dina ce ta bani" ya karba yana dubawa "wow duk wannan naki ne ke kadai, bata baki komai ki kawo min ba?" Tace "ba abinda ta bani in kawo maka" yace "kuma bata ce tana gaishe ni ba?" Tace "eh bata fada ba" ya dauki yarinyar ya dora a cinyarsa, yana shafa kanta "sweetheart yau kinga namesake dinki ko? How do you find her?" Tace "she is beautiful and nice" yace "yes sweetheart she is the nicest person I have ever known". Amina ta ajiye ledar hannunta ta juya zata fita, sai a lokacin ya tuna tana gurin, yace "wait" bata juyo ba yace "Maimunatu Please" chak ta tsaya kafin ta karasa kofar, ta juyo a hankali tana kallonsa, a nutse ta fara magana "I am not Maimunatu, I am Amina" ya tsaya kawai yana kallonta dan shi bai ma san ya kirata da Maimunatu ba sai data fada. Ta kalli little moon akan cinyarsa tace "Moon je ki nuna wa Mama kayan da kika samo" da sauri yarinyar ta dauki ledar ta fita da gudu. Bayan ta rufe kofa sukayi shiru suna kallon juna, yace "am sorry, I didn't meant to hurt you, ban san ya akayi bakina ya kauce ba" tace "cut it. Dalilin da yasa ka tura mu gidan Moon kenan wato, because deep down you you still love her, duk abinda kake fada min cewa you are over her duk ba haka bane ba, kace baka san dalilin da yasa kabi su a baya ba amma ni nasan ka bi su ne saboda har yau baka hakura da ita ba. To bara in gaya maka wani abu, she is more than over you. Tun kafin tayi aure ta daina sonka ballantana yanzu. She is happily married. She is not coming back to you. The sooner you get this into your head the better for you. Am not maimunatu am Amina, duk da mun hada jini da ita hakan ba yana nufin feelings din mu da halayen mu daya ne ba. Duk da munyi kama da ita ba hakan yana nufin zan iya rikidewa in zama ita ba. I am my own person. I can't be a substitute for someone. You lost something a rayuwar ka, ka koma baya kayi tracing may be You will find it. I dan kuma baka samu abinda kayi loosing ba then I pity your soul" ta juya ta fita.
Ibrahim ya dafe kansa tare da cewa "ya salam" ya koma da baya ya kwanta akan gadon. "What is wrong with me dear God" duk abinda Amina ta fada gaskiya ne, sai da ta fada kuma sannan ya kara tabbatar da cewa gaskiya ne. He enjoys being with her only because in yana tare da ita sometimes yana jin kamar yana tare da maimunatu ne, amma kuma yasan ba maimunatun bace ba. Amma kuma mai take nugi da he lost something, tana nufin yayi loosing maimunatu? But ai that's obvious, to menene yayi loosing?. Gaba daya ji yayi ya kasa sukuni, duniyar duka tayi masa kunci, me yasa shi rayuwarsa take a haka ne? Sam ya kasa samun farinciki tun ranar da ya juya bayansa ya tafi yabar maimunatu a gidansu tana kuka, ba zai iya tuna ranar da yayi farin ciki ba, genuine farin ciki, ba kuma zai iya tuna ranar da wani yayi farin ciki domin sa ba. Hatta mahaifiyarsa kawai yasan hakuri take yi dashi amma bajin dadinsa take yi ba. What did he miss? Moon is over him ya sani amma shi why can't he get over har?
Satin sa daya aka sallame shi daga asibitin, cikin satin nan ya kara zama miserable, dan har 'yar karamar Moon ma tsoron sa take ji dan daga tayi wani abu kadan zai daka mata tsawa, daga asibitin mama cewa tayi ba zasu je gidan sa ba, yaje yaci kansa shi kadai, ta dauki jikarta su kayi tafiyarsu tasha suka hau mota suka koma ibadan. Shi kadai ya koma gidan sa inda yake zaune shi kadai, ya kira number din Amina yafi cikin charbi amma bata dauka ba, yasan in yaje gurinta ma ba fitowa zatayi ba kuma shi din ma yana tinanin mai zai ce mata in yaje din? Ranar daya koma gurin aikinsa sai da ya kori mutum biyar daga aiki, ya bawa wadansu query, gaba daya kowa ma haushi yake bashi, shi kanshi haushi yake bawa kansa. Rannan ya dawo daga office kawai yaki komawa gida, to in ya koma gidan ma me zaiyi a can? ya kama driving yana zagaya gari a hankali fresh air tana kada shi, ya fara tuno kalaman Amina, she said he lost something a rayuwarsa, she advice him to trace back his life yayi finding menene yayi missing. To in zaiyi tracing back ta ina zai fara? Kafin ya koma gida ya yanke shawarar he is taking the next plight to ibadan, tunda anan ne rayuwar sa ta fara, in ma yana da matsala anan ne zai samu solution.
Da sassafe jirgin su ya sauka a ibadan, ya dauki taxi ta kai shi unguwarsu. Ya sauka ya tsaya yana karewa gurin kallo, babu abinda ya chanja, ya kalli masallacin da a da babansa yake limanci, ya tuna da lokacin da suke zuwa masallacin tare da babansa, what has happened? Ya shiga gidan su da sallama, jakarsa rike a hannunsa, mamansa da take wanke kwanuka ta tsaya tana kallonshi da mamaki. Shi kuma gidan yake karewa kallo, babu abinda ya chanza sai tsufa da gidan ya kara yi da lalacewa. Ya tuna da uwar dukiyar da yake tarawa yake ajiye wa a banza, for what? Ya ajiye jakar hannunsa anan tsakar gidan ya nufi dakin da baba ya zauna kafin rasuwarsa, ya tura kofar ya shiga yana feeling kamar zai ganshi akan tsohuwar kujerar sa da alqurani a gabansa, alqurani? Ya shiga dakin sosai yana kallon tarin littattafan addini a jejjere kamar yadda suke kullum. Cikin littattafan nan babu wanda bai haddace from page to page ba. Ji yayi kansa yana juyawa, when was the last time daya bude alqurani ya karanta? When was the last time daya zauna yayi cikakken azkar? When was the last time daya yi istikara ya nemi zabin Allah a cikin rayuwarsa? How did he expect things to go right a rayuwarsa? Ya juya ya kalli mahaifiyarsa da take tsaye still tana kallonsa, ya sani cewa jin dadin rayuwar mutum duniya da lahira yana jingina a jikin how much yake kyautatawa iyayensa, amma shi baya kyautatawa tasa uwar, duba gidan da take ciki duba gidan da shi yake ciki a abuja. Amma ai da ba haka yake ba, da sanda bashi da komai amma dan albashinsa biyu yake rabawa ya kawo mata rabi, lokacin ma tana da miji ba yanzu ba da bata da kowa sai shi. Ya tuna da baban sa da yadda yayi making sacrifices dan yaga ya zama wani abu a duniya, duk kuwa da cewa bashi ya haife shi ba, a karshe ya dauki 'yarsa ya bashi aure, amma me yayi? Sai ya wulakantata, yaki yin biyayya ga iyayensa, ya take maganar su ya nuna musu basu isa dashi ba, har efi ta bar duniya bata ji dadin aurensa ba, ta yaya zaiyi tsammanin rayuwarsa zata tafi masa a dai dai? Ya dauki alqurani guda daya ya bude ya fara buda pages din yana jin wani feeling mai dadi a ransa, how did this happened? When? When did he lose himself? Sai yanzu ya gane maganar Amina, ba wani abu yayi loosing ba sai kansa, he lost himself the moment da yayi deciding yana son yayi kudi dan ya auri Moon, tun daga ranar he became slave to the idea of becoming rich for Moon. Duk da karyar da Amira tayi masa cewa Moon tayi aure amma ya kasa cire hop din cewa zata dawo gurinsa, kuma yana son sanda zata dawo ta tarar cewa he is richer than yadda tayi tsammani. Duk tsahon shekarun nan komai yayi dan ita yake yi ba dan kansa ba. Hatta kaya in ya saka sai yayi tunanin in ta ganshi yanzu what will she think? In tunaninsa ya gaya masa ba zata so kayan ba sai ya cire ya saka wadansu. He became so obsessed in preparing for her to come back to him that he lost himself along the way. Ya ajiye alquranin hannunsa. He found himself now. Everything is going to be alright now.
Mama ta karaso bakin kofar tana kallonsa tace da yarabanci "Seun lafiya kake kuwa? Yaushe kazo gari? Me kake yi a dakin nan?" Ya mike tsaye ya karasa gabanta ya zube a kan guiwoyinsa, yace "Mama dan Allah ki gafarta min. Nayi kuskure a baya, rayuwata gaba daya bata tafiya dai dai. Dan Allah mama ki yafe min kiyi min addu'ah ko Allah zai dube ni ya shiga rayuwata" Tace "my son, ni ban rike ka da komai ba, kullum addu'ah nake maka Allah ya dawo da kai kan hanya. Kuma Alhamdulillah tunda har kazo ka nemi gafara ta to na tabbatar ka fahimci kuskurenka. Allah yayi maka jagora"
MAIMOON
By
Maman Maama
Episode Eighty Six : The Phone Call
Bayan sati daya da dawowar mu daga asibiti, Sultan ya fara saukowa daga emotional height din da ya hau, ya fara accepting Takawa a hankali. A nasa bangaraen kuwa, Takawa kullum sai yazo part din mu, tun ina jin nauyinsa ina baya baya dashi har na saba na fara yi masa surutu in yazo, dan haka duk sanda yazo nice abokiyar hirar sa Sultan bin mu kawai yake yi da kallo, daga baya sai Takawa ya mayar da zuwa gurin mu da daddare al'ada, kullum anan yake cin abincin dare a palon sultan, sai tanzu nake kara jin dadin koyon girkin da nayi, duk da dai har yanzu asma'u tana nan amma hannu bibbiyu yafi sauri. Kullum Takawa bashi da labarin bawa Sultan sai na khairat, Sultan kam sai yayi shiru ya rabu dashi baya tanka masa. Nayi nayi da Sultan ya gaya masa cewa mun sami labarin ta amma yaki. Shi har yanzu fushi yake yi da ita, yace in ta ki neman mijinta saboda taji haushin ya sake ta to shi kuma fa? Ina laifinsa a ciki.
Wata ranar friday da daddare, Takawa yazo kamar yadda ya saba, ni kuma ina ta faman hidimar jera musu abinci akam carpet, sai ga Amir nan ma yazo, ya gaishe da Takawa, suka gaisa da Sultan ni kuma na gaishe shi. Sultan yana ta tsokanar sa suna dariya kamar yadda ya saba, sai Takawa yace "Sultan baka da kunya, Amir fa uba ne a gurinka" Sultan ya bata fuska yace "Uba kuma?" Takawa yace "eh. Mahaifina ne yayi adopting dinsa, dan haka legally kani na ne, hakan ya saka ya zama uba a gurinka" dani da Amir mukayi ta dariya, Amir har da rike ciki, Sultan ya bata fuska yace "wallahi ba'a isa ba" Takawa yace "daga yau baba Amir zaka ke ce masa. Amir duk ranar da bai ce maka baba ba kazo ka gaya min" Amir harda yiwa sultan gwalo, sannan yayi mana sallama ya fita, ina tayi masa mitar yaki tsayawa yaci abinci. Yana fiya na dauko yankakken apple na kawo gaban Takawa ya dauka ya fara ci yana min godiya, idonsa akan sultan yace "me Amir yake ciki ne?" Sultan yace "as far as I know bashi da problem. Amir is the must cheerful man I have ever known, kullum cikin farin ciki yake, sam bai dauki duniya da zafi ba ko kuma wai ya saka wa kansa damuwa akan neman asalinsa. Matsalar da yake fuskanta daya ce, akan neman auren da yake yi, iyayen yarinyar da yake nema sun hana shi aurenta, wannan shi yasa kwanan baya naga ya tayar da hankalinsa amma yanzu ya fara dawowa normal duk da dai har yanzu ba wai rabuwa yayi da yarinyar ba" Takawa yace "wacece yarinyar?" Sultan ya gaya masa sunan mahaifinta wanda yake malami ne a maiguduri, Takawa yace "ka gaya wa Amir, ya gayawa yarinyar ta gaya wa iyayenta, ni zanje har maiduguri in nema masa auren ta, nine waliyinsa" nan take sultan ya washe baki yana dariya, sai ince wannan shine karo na farko da naga sultan yayi wa mahaifinsa dariya, nima kaina sai da naji dadi, Amir deserves more than that, saboda duk wahalar da sultan ya sha a rayuwa tare suka shata, shima ya kamata ace ya samu farin ciki. Amma kuma can kasan zuciyata ina tausayawa kawata Amira, Amir din ma data dan samu gashi ya gudu ya barta zaiyi aurensa, amma kuma banji haushin Amir ba tunda bai taba furtawa yace yana son ta ba ballantana ace ya yaudare ta. Amma duk da haka sai dana yiwa Sultan maganar bayan Takawa ya tafi, kamar bai jini ba daga farko sai kuma yace "why do you care about her ne wai? Ina ruwanki da ita? She is not loyal" nace "she was not loyal. Amma hakan ba wai yana nufin bata yi learning lessons din ta ba. Everyone deserves a chance at redemption" ya sake dauke kai, na saka hannu na juyo fuskarsa gurina nace "pleeeassse" ya kara bata fuska "to wai ke me kike so ayi mata ne? Shi Amir ga wacce yake so, so kike ince masa Amir ka fasa auren wacce kake so ka auri wacce Moon take so?" Nace "ba haka nake nufi ba honey, kasan yadda Amir suke da Amira, na tabbatar ba za'a rasa sonta a cikin zuciyarsa ba kawai dai wancan son ne ya danne wannan. Kuma shi na miji ai mijin mace hudu ne ko?" Yana kallona kuma sai ya fara murmushi yace "ki sani, in dai akayi auren nan sai na gayawa Aisha ke kika ce ayi mata kishiya tun kafin a aure ta" nayi dariya nace "a'a kar ka hada ni da kawata, in dai har akayi auren to dama an rubuta cewa matar sa ce, bani na saka ba, shi aure ai rai ne dashi, ba'a creating dinsa ba kuma a destroying dinsa, sai dai a zama sila".
Washegari weekend, Sultan yana gida tun safe yana zuba mulki, duk yabi ya addabeni kamar zanyi masa kuka, dama kwana biyun nan kamar wanda ake kara tunzurashi a kaina, ni kuma yanzu ga kasala da take damuna da bacci, ko da yaushe a gajiye nake jina duk da ba wani aikin kirki nake yi ba, dan gyaran part din sultan ma mostly yanzu shi yake yin kayansa indai har yana gida sai dai in baya nan. Da kyar na samu na kwaci kaina daga gurinsa nace zan je kitchen muyi girki da asma'u, ina fitowa ko kallon hanyar kitchen din banyi ba na tafi part dina na shiga na rufe kofa harda saka key, duk da nasan cewa a banza nake yi in dai har sultan ne sai ya shigo sai dai in baiyi niyya ba. In kwanciya a gado ko minti daya banyi ba nayi bacci. Ina cikin baccin naji ana min tafiyar tsutsa a kafa ta, na janye kafar aka sake biyo ni, na tashi zaune da kyar nake bude idona dan bacci, na ga sultan a zaune a tsakiyar gadon yana kallona, yace "girkin kenan ko?" Kamar zanyi kuka nace "bacci nake ji Sultan dan Allah ka rabu dani" shima ya kwaikwayi muryata, "weekend ne fa yau. Weekdays ina damunki ne? Wanda ba'ayi da rana ranar aiki shi nake fanshewa da weekend" bai ankara ba kawai saiji yayi na fashe masa da kuka, ya saki baki yana kallona, na fara cewa "wayyo Mommy ki zo ki taimake ni Sultan zai kashe ni" dariya ya fara yi yana kallona ina ta kuka na, sai daya bari nayi mai isa ta sannan yace "kinsan da Mommy zata ganki yanzu me zatace?" Na girgiza kaina ina share hawayena, yace "cewa zatayi 'ke kika ce kina so, da baki ce kina so ba da ba'a baki shi ba'" na watsa masa harara nace "na fasa sonka ai yanzu, bacci nake so" na yunkura zan sauka daga kan gadon ya jawo ni ya dawo dani ya kwantar, yayi min rumfa da jikinsa yace "ba wani abu zanyi miki ba fa kike ta wannan gudun, wani cikin zanyi miki, kinga sai ki haifa min twins" na fara dariya nace "kai wa yace maka haka ake yin twins din?" Ya saka hannu cikin riga ta yace "haka ake yi mana, in aka yi ciki sai a sake yin wani sai a haifi guda biyu" na lumshe ido ina jin abinda hannunsa yake min nace "gaskiya sultan bacci kake yi a biology classes dinka na secondary school" na bude ido ina kallonsa yana min murmushin mugunta ganin yadda jikina ya fara saki, Sultan ya riga ya gane lagona, duk wani guje guje na da waye, he just need to put his hands on me shikenan magana ta kare. Sai da ya tabbatar he got me right where he wants me sannan ya fara raba jikinsa da nawa a hankali still da murmushi akan fuskarsa, naga cewa da gaske tashi yake son yi ai kuwa na saka hannu biyu na jawo shi na dawo dashi na hade bakinmu, ina jinsa yana dariya a cikin kirjinsa, a raina nace 'wallahi sai na rama, kayi da 'yar halak'.
Anan daki na yayi wanka, sai naga ya saka kaya kamar mai shirin fita, nace "fita zaka yi ne?" Yace "ba nisa zanyi ba, cikin gida zanje gurin Takawa" naji dadi sosai nace "naji dadi sosai da zaka je gurinsa, shima kuma zaiji dadi" ya zauna a bakin gado yana kallona ina goge ruwa a kaina, na gane magana yake so muyi dan haka na karaso na zauna kusa dashi, yace "ina so muyi magana dashi ne akan Abbas. Ya dage lallai sai ya kore shi daga gidan nan. Ni kuma ina ganin rashin kyautawar hakan, shi Abbas ba laifinsa bane ba, bashi ya zabi yadda haihuwarsa zata kasance ba, ba kuma shi ya zabi yadda za'a raine shi ba, bai kamata ace zai yi paying for his parents crime ba" na saka hannu ina kara kwantar da kwantaccen gashin kansa nace "me kake so ayi yanzu?" Yace "so nake yi Takawa ya kira shi su zauna ya gaya masa gaskiyar lamari da kansa cikin sigar lallami da lumana, ya kuma barshi ya cigaba da zama a gidan nan ya kuma cigaba da zuwa fada, babu wanda zai san abinda ya faru sai mu kadai. Kinga in akayi haka sunan family din da suke ta fighting for zai zama ba'a bata shi ba, kowa zai samu abinda yake so. Masu kirari suna yiwa sarki kirari da uban masu uba uban marasa uba, to gwara ya fara zama uban marasa uban akan Abbas" tunda ya fara maganar kallonsa kawai nake yi, a raina nace 'masha Allah' sai daya gama sannan nace "hakan shine dai dai mijina, am very proud of you. Cikar imanin mutum shine ya so wa dan'uwansa abinfa yake so wa kansa, kasan zafin rashin iyaye shi yasa kake kula iyakacin karfinka kaga babu wanda ya dandana wannan zafin, ko da kuwa mutumin da ya aikata maka sharri ne, cikar mutum shine ya rama mugunta da alkhairi. Allah ba zai taba barinka ta tabe ba sultan" nayi masa kiss a gefen bakinsa, yace "wow" ya juyo sosai ya nuna min bakin ya kashe min ido, na makale kafada ina dariya. Nace "ni kuma ga tawa shawarar; idan kun gama settling wannan maganar, ina ganin ka mayar da Abbas makaranta, yadda zai samu future mai kyau nan gaba, ya koma makaranta ko first degree ya samu ya kammala, in ma ba zai yi aiki ba ya ajiye takardun. Kuma komawarsa makaranta zata saka ya dauke hankalinsa daga kan sarauta yasan cewa yana da opportunities a rayuwa beyond his imagination" sultan ya daga kafada yace "OK, I can see what I can do. Amma in yace baya so kinsan bazan dauke shi aka in kaishi ba"
Washegari suka zauna akan maganar. Abbas did not take maganar lightly kuma ni na fahimce shi, maganar da ciwo. Da kyar Sultan ya shawo kansa dan cewa yayi sai yaga bayan Hajiya, Hajiya kam tayi kuka da idonta, ranar Abbas a gidan mu ya kwana part din baki maza. Bayan sultan ya dawo daga gurinsa ya same ni zaune da hijab ga key din mota a hannuna, ya tsaya rike da labule yana kallona, na langwabar da kai gefe, yace "yau kuma me babyn take so?" Nace "Namiji ne fa ba mace ba. Vanilla flavoured ice cream yake so. Sannan da sponge cake ya sha cream da yawa. Sai kuma tsire mai kuli kuli" dariya yayi sosai ya karaso ya karbi key din ya miko min hannunsa yace "you got it". Muna tafiya a mota muna shan ice cream din mu wayar sultan tayi kara, ya dauka, daga gaisuwar da yake nasan Takawa ne, yaje ya tarar bama nan, budar bakin sultan sai cewa yayi "mun tafi shan ice cream, baby ne yake rigima yace shi ice cream zai sha" na bude baki ina kallonsa, duk inda kake tunanin rashin kunyar sultan ta wuce nan, yace "what? He deserves to know da wuri saboda ya fara siyan pampers".
A cikin satin Takawa yaje maiduguri nemarwa Amir auren Aishan sa, ai kuwa iyayenta jiki na karkarwa suka ce sun bayar. Tare da sultan suka tafi. A bauchi suka sauka sannan suka hau motoci zuwa maidugurin, suka kuma dawowa bauchi igan sarki suka yi taro sannan suka dawo Abuja. Tun a hanya sultan yayi min waya wai ya gaji, shi ya dade rabon dayayi irin wannn gajiyar. Yana dawowa kuwa da kyar na samu yaci abinci duk kuwa da soyayyar sultan da abinci. Dakinsa ya wuce yana tafiya yana hada hanya saboda bacci. Ina kallonsa ina dariya a raina. Allah ya nuna min ranar da zan rama abinda sultan yake yi min a gidan nan, yau zai gane shayi ma ruwa ne, zai ji yadda nake ji idan ya hanani bacci. Dakina na tafi nima naje na tsalala wanka, na shafe jikina da turaruka da mayuka irin duk wanda sultan yake so, na dauko wata rigar bacci na da tun da nazo gidan ban taba saka taba saboda kallonta ma kadai in nayi kunya nake ji, na saka, na dauko jan jambaki da nasan yana ruda sultan na shafa a lips dina, na zura hijab a raina ina cewa sultan yau ka kade har ganyenka. Ina shiga dakin na ganshi ya bararraje akan gado daga shi sai three quarter wando, ya kure ACn dakin kamar ka shiga freezer, na taba jikin sa naji sanyi kalau, naje na rage ACn na dawo ina kallonsa, a hankali na hau kan gadon na fara shafa fuskarsa, "sultan? Sultan?" Amma sultan shiru kamar gawa, nayi masa chakulkuli a kafa irin yadda yake min amma bai san ina yi ba, a raina nace aikuwa sai ka tashi yau. Na shiga toilet na dauko cotton bud, nazo na fara sosa masa kunne a hankali, yayi juyi ya janyo pillow ya dora akan sa. Haushi kamar ya kashe ni amma naki hakura, na fara shafashi duk inda nasan yana so amma maimakon ya farka sai jikin sane yake farkawar. Naji tsoro na daina. Na koma kiran sunan sa da dan karfi, sai a lokacin yayi juyi ya dauke pillow daga kansa, na kara volume din kirana, ya dan bude idonsa da suka yi ja sosai saboda bacci ya kalleni kamar zaiyi kuka, nace "pay back time" ya kwabe fuska ya gane me nake nufi yace "dan Allah Moon ba yau ba. Ki bari wata rana kya ramar, you have no idea irin baccin da nakeji yau" nace "nima lokacin da kake tashina you had no idea irin baccin da nake ji" bai ce min komai ba ya juya baya ya ja bargo, na tsallaka ta samansa na yaye bargon ina dariya, hankali na ya kwanta, ko a haka na barshi nima na rama. Ya dago yana kallona ina dariya, a hankali naga baccin idonsa yana washewa lust yana replacing baccin, idonsa akan rigar dake jikina, nayi sauri na daina dariyar nace "shikenan ma babu wani abu na hakura kwanta kayi baccinka" ya dago yana kallon fuskata yanayinsa yana chanzawa, yana min rikitaccen kallo yace "no thank you, na fasa baccin kuma, I got something sweeter than bacci" da sauri na ja da baya, yau na kunto wa kaina ruwa kuma bani da lema, ai kam kafin in sauka ya kamo ni yana kare min kallo, na fara bashi hakuri "kaga ka gaji da yawa, dan Allah ka kwanta kayi baccinka kawai, kaga gobe zakaje office kar kazo ka makara" yayi dariya yace "a da kenan, yanxu na chanza shawara" ya kawo bakinsa dai dai kunnena yace "tunda har kika tambayeni bashin da kike bina, dole ki karba".
Nasha kama Sultan yana kallon picture din Ummee a waya ta, sai nazo kuma sai ya basar yayi kamar wani abin yake yi daban, shi a dole wai bai damu da ita ba. Ni kuma da naga haka sai ba saka hoton nata a screen saver dina, yana dauka ya gani ya juyo yana kallona da alamar tambaya, na daga masa kafada nace "for easy viewing" ya ajiye wayar yayi tafiyar sa irin baya son maganar nan. A bangaren Hafsat kuwa har suka gama zaman su a Riyadh Ummee bata fada mata wata maganar da zata dangantata da Nigeria ba ko kuma da Sultan. Rannan kawai sai ga Hafsat ta kirani tace zasu koma Riyadh Abban Zayed baya jin dadi zasu je su duba shi. Kuma tayi min alkawarin insha Allah wannan karon zata samo labari ko da kuwa a gurin Ummeen zayed ne. Kwana uku bayan nan muna zaune da Asmau tana yi min kitso sai ga wayar Hafsat na dauka ina addu'ar Allah yasa labari mai dadi ne, tace "Moon she talked to me" nace "how managed? Ya kika yi mata?" Tace "zama nayi ina ta bata labarin Nigeria da Abuja, na kuma bata labarin Mommyn mu da yadda take son mu bata son rabuwa damu ko kadan. Irin heart to heart talk din nan. Daganan kawai sai tace min ai itama tana da da, kuma tana sonsa fiye da komai a duniya, tana nan kuma tana jiran ranar da zai zo gurinta. All these years zaman jiran yazo gurinta take yi, all these dukiyar da take tarawa, shi take ajiyewa dan tasan komai daran dadewa zai zo gurinta" nayi shiru inajin hawaye yana taruwa a idona, tace "yanzu kina ganin in gaya mata nasan shi ko kuma me kike so in ce mata" na danyi tunani kadan sannan na tsarawa Hafsat duk abinda nake so ta gayawa Ummee. A ranar da daddare muna zaune a palon Sultan, ina kwance akan kujera ina game a wayarsa shi kuma kan study table dinsa yana zane, sai ga kiran Hafsat a waya ta, sai da na jera adduoi sannan na dauka, na daga murya yadda zan calling attention din sultan nayi mata sallama, tace min da fulatanci "na gaya mata duk yadda kika ce" ina jin haka na saka waya ta a hands free, Hafsat ta koma turanci "Maimunatu this is zayed aunt, she wants to talk to you about her son" ina kallon sultan ya ajiye pencil din hannunsa, nima sai da na hadiye yawu saboda bakina naji ya bushe, ina jin Hafsat tana bata wayar tana mata bayanin ga sister din tata, naji muryarta ta larabawa tace "As Salaam-o-Alaikum" na amsa mata murya ta na rawa, idona akan na sultan wanda ya juyo yana kallona, ta fara magana da turancin ta mai accent din larabawa "Am sorry to disturb you. What is your name?" Nace "Maimunatu" tace "Nice name you get, I always wanted to name my daughter that, but I didn't get a daughter I got a son. I talked to your sister about him she said she didn't know him, but she said you might. His name is Sultan, he is a Prince in Abuja. Very handsome and very strong. I only want to know how he is doing" sai da na tattaro dukkan jarumtata sannan na iya magana, still idanuna a cikin na sultan wadanda suka chanja kala, nace "I don't only know him, he is my husband, Ummee"
MAIMOON
By
Maman Maama
Episode Eighty Seven : Riyadh
Sai da naji daukewar numfashinta ta cikin wayar, sai kuma ta fara maganar da sauri cikin rawar murya kamar mai shirin yin kuka "what? What did you just said? Sultan is your husband? Yana ina ? Yana kusa dake?" Nace "yana jin duk abinda kike fada ummee" ta sake cewa "what? Sultan? Kana jina? My son are you there?" Sultan ya taso da sauri ya taho inda nake zaune ya kwace yawar daga hannuna, ban ankara ba sai gani nayi ya buga ta da jikin bangon dakin, a take ta tarwatse a kasa, ya tsaya yana kallona yana numfashi sama sama tamkar wanda yayi gudu, sannan kuma ba tare daya sake cewa komai ba ya juya ya shiga kofar corridon da zata kaika bedroom dinsa, yana shiga ya bugo kofar da karfi har sai da dakin yayi motsi. Na mike tsaye ina kallon kofar, dama nasan sai munyi drama da sultan akan ummeen sa, amma na shirya damarar sai na daidaita su, so help me God. Na karasa inda pieces din wayata suke na durkusa na tsince, wannan wayar ta gama yawo sai dai kuma wata ba ita ba, na zare sim card dina da memory card na tattara sauran na zuba a wastebasket, na kashe kayan wutar dakin na rufe koina na bishi dakinsa, ina shiga na tarar dashi a kwance a kan gado ko kayan jikinsa bai cire ba, idonsa a rufe kuma nasan ba bacci yake ba, na shiga toilet nayi shirin kwanciya nazo na saka wata T-shirt dinsa babba wacce tazo min har chinya ta, har yanzu yana nan a yadda yake, na kashe fitilar dakin na hau gadon nayi addu'ah sannan na jawo pillow na can nesa dashi na kwanta na juya masa baya, ko minti biyu banyi da kwanciya ba na jishi ya mirgino ya dawo jikina, ya saka hannuwanshi ya zagayo ni ta baya, bance masa komai ba, mun jima a haka sannan naji yace "why did you call her bayan na gaya miki I want nothing to do with her?" Nace "bani na kirata ba ai, ita ta kirani" yace "amma ai ke kika saka har ta kira ki din, kina sane ai" nace "afuwan, ayi hakuri" yace "please don't call her again" nace "I don't even have her number ta yaya zan kirata? Besides, ka fasa min wayar ma" yace "I will get you another one tomorrow. Ko ta kuma kiranki kar ki dauka, am doing perfectly fine without her" na juyo ina kallonsa na bata rai duk da nasan duhu ne ba gani zaiyi ba, nace "why are you blaming her wai? Bayan kasan bata da laifi" yace "she left me, shine laifinta" nace "she didn't, a gaba na Takawa ya gaya maka a ka aka dauke ta aka fita da ita, what is her fault in that?" Yace "she should have come back for me, why didn't she look for me all these years?" Nace "bansani ba sultan, amma nasan dole tana da dalilin ta, uwa tafi gaban komai a duniyar nan. Ba zaka san dalilin da yasa bata dawo ta neme ka ba har sai ka bata chance, har sai kayi magana da ita, idan kunyi maganar kaji cewa hujjarta is not good enough nayi maka alkawarin ba zan sake yi maka maganar ta ba" na daure shi da jijiyoyin jikinsa, bashi da amsar da zai bani sai cewa yayi "maganar ta isa haka. Let's sleep".
Washegari na daura niyar fara abinda zan yiwa sultan, dan haka dana hada mana breakfast sai naci nawa a kitchen na kawo masa nasa coffee room dinsa, na tafiyata dakina, ina zaune a palo ya shigo, naji kamshin turarensa amma ban dago na kalleshi ba, yace "me yasa baki zo munci abinci tare ba?" Na bawa iska ajjiyarsa, ya karasa shigo wa dakin ya tsaya a gaba na, ya shirya alamar office zai fita, kallo daya nayi masa na dauke kaina, yace "magana fa nake miki Moon" na yamutsa fuska nace "naji ai, nafi son cin abincin ni kadai ne shi yasa" ya saka hannu ya juyo da fuskata yace "wai duk akan maganar wayar ne? Yanzu kafin inje office ma zan siya miki wata" bance masa komai ba kuma ban kalle shi ba. Ya dora lips dinsa akan nawa yana kissing, na kwace fuskata na mike na bar gurin ina juya masa bombom, ina shiga daki na bugo kofa ta da karfi irin yadda yayi min jiya.
Ranar Amir ne yazo daukar musu abinci, yana zuwa ya miko min waya yace "gashi inji oga kwata kwata, yace yayi miki charge, kuma dan Allah ki kirasa yanzu" na karba nace "to nagode" yace "ki kirashi fa, dan tun safe yana can ya kasa zana komai, yace rashin jin muryarki ne" na kirkiro murmushi nace "zan kira ai" Amir yana fita na jefar da wayar akan kujera nayi tafiya ta daki. Ranar sultan bai kai yadda ya saba kaiwa a office ba sai gashi ya dawo, ya tarar dani na tasa gyada mai gishiri a gaba ina ci, na daga kaina nayi masa sannu da zuwa na cigaba da abinda nake yi, yazo ya zauna a gaba na ya harde kafa yana leka fuska ta yana murmushi, saura kadan in mayar masa amma na daure na bata fuska, yayi ajjiyar zuciya yayi tagumi da hannu biyu yace "wa ya baki gyada?" Nace "ai kawa nayi aka siyo min" yace "amma kinsan duk abinda kike so ba tare muke zuwa mu siyo ba?" Nace "na hutashshe ka" yace "ina wayarki?" Nace "bana bukatar waya ni, tunda babu wanda zan kira da ita" Har ya tashi ya tafi kuma sai ya dawo ya sunkuya ya dauke ni chak ya tafi dani bedroom dinsa. Ban hana shi komai ba amma barinsa nayi yayi abinsa shi kadai, shi kadai yayi kidansa kuma yayi rawarsa, kamar zaiyi kuka yace "Love menene hakan ne kike yi wai. Please come back to your normal self, I don't like this new you" ba tare dana kalleshi ba nace "kai ka siya ai da kudinka" ya danyi shiru sannan yace "yanzu me kike so ayi?" Na juyo ina kallonsa nace "ka shirya mu tafi Riyadh" da sauri ya girgiza kai "no way, babu inda zamu je" na mike na dauki riga ta ina sakawa nace "ok, suit yourself" ina jin yana kirana nayi tafiyata ba tare dana waigo ba. Haka na cigaba da gasawa sultan gyada a hannu, he is beyond frustrated yanzu, ban hana shi taba ni ba amma shi kansa ba jin dadin abin yake yi ba, murmushi kuwa rabon da inyi masa tun kafin muyi waya da Ummee. Na kunna wayata na saka sim card dina saboda kar mutane suyi ta nema na, ban jima da kunna wa ba kuwa Hafsat ta kira ni "Moon me ya faru ne ranar nan? Wayar ta dauke kuma munyi ta kira shiru bata shiga? Na gaya mata duk yadda mukayi da sultan, tace "ai kuwa ta tayar da hankalinta, ranar kusan kwana tayi tana kuka, har sai da nayi nadamar tayar da maganar nan. Yanzu menene abinyi?" Nace "kin san halin sultan, and he is probing harder than I thought, amma zan cigaba da ganin yadda zanyi dashi. Ki kwantar mata da hankali, ki san abinda zaki gaya mata". Ranar hankali na ya kara tashi akan maganar ummee, na yanke shawarar zan shigar da Takawa cikin maganar. Yana zuwa da daddare na riga sultan zuwa, naje na gaishe shi ya amsa da fara'arsa yana min godiyar kokarin da nake gurin yi musu hidimar abinci. Na dauko waya ta na buda hoton Ummee na ajiye masa a gabansa ina kallon fuskarsa, ga mamaki na sai naga banga changin komai ba, ya dagi kai yana kallona yace "Hafsat ce ta turo miki?" Mamaki ya kara kamani nace "eh" ya gyada kai yace "tun washegarin ranar dana dawo hayyacina na aika har can Riyadh din nace a binciko min labarinta, an kuma bani labarin komai, nasan dan wanta ne yake auren yayarki Hafsat, har number dinta an turo min, what I lack is the courage to call her" na kalleshi da mamakin wai kamar shi ne zai ce bashi da courage, yace "yes, after all we went through together sannan kuma na tura mata da takardar saki kuma na kwace mata danta tsahon shekaru talatin, I don't know me zance mata in na kirata ko kuma na je wajanta" na sunkuyar da kaina, yace "sultan yaga picture din?" Nace "eh ya gani" yace "me yace?" Nace "he didn't say anything yet" yace "kina ganin zaije?" Nace "maybe, amma ba yanzu ba" yace "yayi fushi ko?" Kai kawai na gyada masa, kafin ya sake cewa komai sultan ya shigo dakin, ya bimu da kallo yana kallon waya ta a gaban Takawa, bai ce komai ba na mike na bar gurin, ina kallon sultan yana harara ta a raina nace yau akwai daru kenan. Ai kuwa Takawa yana tafiya sai gashi har dakina, "zancan me kuke yi dazu kafin inzo?" Nace "zancen Ummee muke yi" cikin fushi yace "dama dashi kuka hada baki kenan" na girgiza kaina nace "bamu taba maganar dashi ba sai yau, yanzun ma kuma ni ce na fara yi masa maganar, ashe duk abinda nake son in fada masa ya sani, yana da address dinta da number wayarta da komai amma ya kasa kiranta saboda bai san me zai ce mata ba" ya zauna a kusa dani yace "me yace?" Na juyo ina kallonsa nace "ya tambayeni in ina ganin zaka iya zuwa gurinta" ya mike tsaye da sauri "no, I am not going to be dan aiken soyayyar su, if he want his wife he should go get her by himself" nace "then go as her son, ba wai dan aiken takawa ba" ya sake cewa "NO, ita me yasa ba zata zo Nigeria ba? In tana son gani na tasan a inda nake, abinda zatayi kawai shine ta je airport ta shiga jirgi ya kawo ta Nigeria. Tunda kika ga tsahon shekara talatin bata zo ba to bata son ganina, ba zanje ta wulakanta ni inzo in ji haushi ba, maybe tayi wadansu yayan and she don't need me in her life" yana maganar yana zagaye dakin, nace "bata yi wadansu yayan ba, in fact vata kuma yin wani auren ba tun barinta Nigeria" ya tsaya da zagayen da yake yi ya kalle ni yace "then why didn't she come for me?" Na mika masa wayata nace "call her and ask her, ni bansani ba" ya karbi wayar ya ajiye a gefe, at least wannan karon ba'a fasa min waya ba. Na mike tsaye na karasa gabansa, na saka hannu biyu na riko fuskarsa nace "Sultan she has been crying tun ranar da muka yi waya da ita, ta gane abinda ya faru, ta gane kai ka kashe wayar saboda ba kason magana da ita, ta gane cewa fushi kakeyi da ita. Sultan mahaifiyar kace fa, kar ka bari ubangiji yayi fushi da kai akanta Sultan, ko ma menene tayi ya kamata ka saurare ta" bai ce min komai ba ya sauke idonsa kasa, amma nasan I got his attention, na jayo hannunsa muka dawo muka zauna akan kujera, yace "ni yanzu inna kira ta to me zance mata? I miss you zance mata ko me?" Nace "I miss you din ma is in order" yace "no, it's not, ban san taba ballantana inyi missing dinta" nace "then let's go to her. In baka san me zaka ce mata a waya ba in muka je ka ganta ido da ido am sure zaka san me zaka ce mata" ya girgiza kansa stubbornly, ba tare da warning ba na hade bakin mu na fara kissing dinsa da zafi zafi, nan da nan kuwa ya dauki zafi, dama abinda yake ta nema ne ido rufe naki in bashi, yau sai gashi har gida, nan na fara sarrafa shi son raina, duk abinda nasan yana so shi nayi masa double, na ruda shi sosai na rikita masa tunanin sa, duk wani stubbornness dinsa sai da na cire masa shi ya dawo a tafin hannuna, a nan kan kujerar muka sauke hajar mu. Ana gamawa Sultan yace shi kari yake so, na bata rai na juya masa baya, ya jawo ni ya kwantar a kirjinsa yayi ajjiyar zuciya yace "why do you care about her? Baki santa ba, baki san halinta ba, for all we know maybe tana zuwa gidan nan ke ce mutum ta farko da zata ce bata so" nace "maybe, maybe not. Maybe tana zuwa gidan nan son da zata yi min sai yafi wanda zata yi maka, we will never find out idan bamu je ba" ya bata fuska kamar zai yi kuka yace "please Love I really don't want to go" nace "then let me go. In kai ba zaka iya zuwa ba ni ka barni inje, Hafsat da zayed suna can, at least in naje muka yi magana da ita zan samo maka duk amsar tambayoyin ka, daga nan sai ka yanke shawarar me zakayi next" yayi shiru yana tunani, ba dan hannunsa da yake shafa cikina ba zan iya cewa bacci yake yi saboda dadewar da yayi a haka. Can yayi magana "zaki je next week, zakiyi three days a can, a gurin su Hafsat zaki sauka saboda bana son a wulakanta min ke, in na fita gobe zan fara processing tafiyar taki" da sauri na mike zaune ina rawar murna, na manta ma babu kaya a jikina sai daga baya na tuna na koma na dunkule a jikinsa, yana dariya ya dago ni yace "amma da sharadi, daga yau duk abinda nake so shi za'a ke yimin, ko yaushe ne kuma ko a ina ne, in ba haka ba an fasa tafiyar" nace "yes sir, an gama" ya mike tsaye ya mikar dani yace "yanzu sai muje daki mu cigaba daga inda muka tsaya".
Washegari duk da farin ciki muka tashi, ni ina murnar na shawo kan sultan shi kuma yana murnar mun dawo rayuwar mu dai dai, dan haka ranar da kyar ya fita office. Bayan mun kammala duk abubuwan al'ada na gyaran gida muka shiga kitchen muna kokarin dora abincin yana, sai ga yarinya tazo tace min wai nayi bakuwa, na leka palon naga Amira na rike kugu nace " au dama ke ce bakuwar zaki wani zauna a palo? Ki tashi ki cire wannan mayafin ki taho kitchen" tana dariya ta ajiye mayafin ta ta taho, a kitchen din muka gaisa sosai sannan ta gaisa da Asma'u da sauran yarana, na lura tayi sanyi sosai kuma naji ina tausayinta har cikin raina. Sai da muka kusa kammala aikin sannan muka bar su Asma'u muka dawo palo muka zauna, muka fara hira, mostly hirar da yadda kawancen mu yake, da yadda tayi ta bani shawara akan sultan ni kuma na rufe idona naki dauka, wani gurin muyi dariya wani kuma muyi jimami, ina sane na sako mata zancen Ibrahim da labarin yanzu Amina yake nema, ina maganar ina kallon fuskarta inga yadda zata dauki maganar amma sai naga babu wani chanji a fuskarta sai ma alamar tana taya Amina murna. Muna nan zaune muka ji sallama, Amira tayi saurin daukan mayafinta ta yafa, a raina nace 'har yanzu ustazancin yana nan kenan' Abbas ne ya shigo cin abinci, da yake shima yanzu anan yake cin abinci tunda har yanzu bai huce da Hajiya ba. Ina sane nace Amira tayi serving dinsa, ta harare ni na langwabar da kai na nuna mata cikina, ta tashi ta bishi dining tana serving dinsa, ina jiyo maganganun su, dan Abbas akwai surutu kamar fa'iza, saratu ce mai shiru shiru dinsu. Bayan ta gama ta dawo gurina muka cigaba da hirar mu, sam ban bata labarin komai da yake wakana a rayuwar mu da sultan ba saboda ance once biting twice shy, bayan Abbas ya tafi muma muka je muka ci abinci tare sannan ta tafi gida. Bata jima da tafiya ba sai ga Abbas ya dawo, ina ganinsa nace a raina tarko na yayi kamu kenan, yazo ya zauna yana shafa kai yace "babbar yaya wacece dazu tazo gidan nan?" Na hade rai amma cikin wasa nace "ina ruwanka da ita?" Yace "please ki dan shigar dani mana" na wara hannuna nace "a nawa? Kasan ni bana aikin banza" yace "zanyi ta yi miki addu'ah kullum idan nayi sallah. Please" nace "ni ba zan shigar da kai ba, zan dai baka number dinta ka je ka shigar da kanka" yayi godiya ya karbi number din ya fita. Asma'u tana daga kitchen ta leko tace "dama nasan za'a rina, wai an saci zanin mahaukaciya" muka yi dariya tare.
Na kira Hafsat na gaya mata an bar ni zuwa, nace ta gaya wa Ummee cewa zanzo amma ni kadai, anan take gaya min cewa khairat ta hana ta komawa gidan su zayed tun da tasan dangantakata da ita, anan gidan yanzu take sai dai zayed yazo gurinta, tace min itama tana murnar zuwan nawa nan da sati daya. Satin da sauri yazo, tun kwana uku tafiya ta na fara hada kaya, sultan kam sai kumbura yake yi, kullum sai ya tsara min yadda tafiyar zata kasance, yace gurin Hafsat zan sauka, sau daya zanje gurin Ummee, in naga babu fuska kar in sake zuwa, ni dai to kawai nake ce masa amma ni na gama plan dina, ana gobe tafiyata naje gida na wuni gurin Mommy, Daddy dama baya nan lokacin, na gaya wa Mommy komai yadda ake ciki da kuma plan din da nayi, farko ta fahimta kuma ta yarda, sai kuma daga baya ta zama alarmed, "kin ga neman takawa dama suke yi suyi masa hukuncin sace musu 'yarsu da yayi, kar kije kuma su kama ki ke" nayi dariya nace "Mommy ba abinda zasu yi min, shekara talatin fa da yin abin, besides, gurin Hafsat zanje". Sai dare sultan yazo daukana, tun a mota yake cewa shi ya akayi ya bar ni wannan tafiyar ne, a ranar yadda muka ga dare haka muka ga rana, sultan yayi nadamar bari na yafi cikin charbi, sai kara jaddada min yake yi "three days kawai, babu kari, make sure wayarki a kunne take all the time, in kinga zasu daga miki kai ko su Hafsan ne ma ki rabu dasu kije ki kama hotel ki kwana da safe kiyi tahowar ki" ni dai sai to kawai nakr ce masa. Da safe saura kadan ya saka inyi missing plight kuma nasan yana sane, so yake in fasa tafiyar amma naki. Muna zuwa airport yace "ko dai ince na fasa barinki tafiyar nan ne?" Nace "nasan ma ba zaka fadi haka ba" yace "saboda me kika ce haka?" Nace "because you are a man of your words" ya girgiza kai kawai ya fito min da akwatina, har sai da aka fara cewa za'a rufe kofar jirgi sannan sultan ya sake ni na tafi. Ina shiga jirgin ina zama naji na fara missing dinsa, na dauko waya na kira shi nace "already missing you Darling" yace "then come down ki fasa tafiyar nan please" nace "no, na riga nayi niyyar, just pray for me" ya kashe wayar bai ce min komai ba.
Wajan asr jirgin mu ya sauka a birnin Riyadh. Ina fita reception na hango Hafsat da Zayed suna jirana, na karasa da sauri na rungume Hafsat da naga ta kara kiba da kyau, jin dadi sosai ya bayyana a tare da ita, Zayed ya karbi akwatina yana cewa "welcome to my home town sister In-law, kin zama in-law dina ta two sides" muka yi dariya a tare. Muna shiga mota yace "gidan khaloo (Aunty) zamu je ko?" Nace masa "eh" ni dai duk ina feeling nervous, ban san ya zata karbe ni ba, what if sultan is right? What if ta wulakanta ni?" A hanya Hafsat take ce min wai khairat har fenti ta saka aka sakewa gidan ta na tara ta, wai yau tun safe take kitchen tana girki, ta rasa me zata dafa min, jiya kuma sam bata yi bacci ba saboda anticipation. Wannan maganar ce ta dan kwantar min da hankali.
Tun daga gate din gidan nasan an ajiye dukiya a gidan nan. Ya hadu karshen haduwa, dan bazan iya tsayawa fassara haduwar sa ba. Ni dai kawai bin su Hafsat nake a baya da sakakken baki ina kallo, mun wuce palo sunfi uku sannan muka zo inda suka ce min shine palon ta, zayed ya bude kofar da sallama sai kuma yaja baya ya bani guri yayi min alama da in shiga, na hadiye yawu da kyar sannan na daga labule na shiga da sallama. Tana zaune akan kujerar da take facing din kofa, bakar abaya ce a jikinta da rolling irin na larabawa, gashin kanta ya fito ta kasan mayafinta ya sauka har gadon bayanta, ta saka hannayenta a tsakanin cinyoyinta, ta bude idanuwanta tana kallona, she looks more like sultan in reality than in the picture. Kallo daya nayi mata naga extreme of innocence a fuskarta. Ta mike tsaye tana jujjuya hannunta, idonta ya sauka akan dan karamin cikina, naga kwalla ta fara taruwa a idonta, ta kasa cewa komai, na karasa shiga palon a hankali, kafin inyi magana wayata tayi kara, ina dubawa naga sultan, na dauka da sallama, bai amsa ba yace "kin fasa yin kwana ukun, na duba naga gobe da akwai jirgin safe daga nan Riyadh zai dawo Nigeria, ki biyo shi ki dawo" nace masa "an gama" na katse kiran, na kashe wayar gaba daya na saka ta a jaka ta. A hankali tace "Sultan ne" Nace "eh shine" Tace "he is already regretting letting you come ko?" Nace "yes" take naga fuskarta ta chanja kalar tashin hankali, tace "fushi yake yi dani and I don't blame him, sai dai bansan me zanyi masa ya hakura ba. Cewa yayi ki koma Nigeria ko?" Nace "yes. But if he wants me, he will have to come and get me?" A hankali naga damuwar fuskarta tana washewa, farin ciki yana replacing, ta karaso gurina da sauri ta rungume ni tace "thank you my daughter".
Afuwan jiya kun jini shiru, abubuwa ne suka dan sha kaina amma lafiya lau nake Alhamdulillah, nagode da kulawarku sosai. I feel loved.
0 comments:
Post a Comment