By
Maman Maama
Episode Eighty eight :Khairat
Ta sake ni ta kama hannuna muka karasa kan kujera, ta zaunar dani sannan ta zauna a kusa dani still tana rike da hannuna, tana min murmushi from ear to ear, na dan sunkuyar da kaina saboda kallon da take min, ta saka hannu ta dago habata, tace "masha Allah, you my dear are very beautiful" naji kunyarta na sunkuyar da kaina. Ta dora hannunta akan cikina tana dariya excitedly, tace "wata nawa?" Ni dai duk kunya ta ishe ni, na kasa bata amsa, tace tana karkata kai "please kar ki yi min haka mana, talk to me, ki dauke ni kamar kawar ki kinji?" Na gyada mata kai, ta sake dora hannunta akan cikina tace "wata nawa?" Ina murmushi nace "almost four" ga mamaki na kawai sai naji babyn yayi motsi, itama taji a hannunta, ai kuwa murna kamar me, tace "shima yasan yazo gida, welcome home my little love" ni dai sai taya ta dariyar ta nake yi, sai da ta gama murnarta sannan tace "how is he?" Na san wa take nufi da he din, to amma na kasa sanin ta ina zan fara bawa uwa labarin danta wanda rabonta dashi shekara talatin? Jin bance komai ba yasa tace "ya kamannin sa suke yanzu" na dago kai na kalle ta nace "you just need to look in the mirror, he looks just like you" ta fadada murmushinta tace "but he has his father's built and temper" nace "yes, he do" ta sake juyo wa tana kallona tace "har yanzu yana da hot temper kenan? Sanda yana baby in yana son abu na hana shi sai yayi ta buga kansa a jikin bango, in na bashi abin ma daga baya sai ya karba ya jefar wai yayi zuciya" nayi murmushi, ta sake cewa "tell me menene yafi so duk duniya" na san me yafi so duk duniya amma am not going to tell her that, dan haka nace "food" ta bude baki da mamaki tace "har yanzu bai daina son abinci ba? Sultan har cikin dare yake tashi yaci abinci, sanda ina feeding dinsa sai da na hada masa da madara saboda tsabar cin sa, da ya fara yawo kuma babban abincin da yake so shine nama, daga nan sai fresh milk" nace mata "har yanzu ma, yana son nama sosai" tace "is he still making troubles? He was a trouble maker as a baby, yana da kiriniya sosai dan sanda ya fara crowling duk abinda nake so sai dai in dora a sama, a saman ma in ya samu abin takawa sai ya dauko, yayi ta faduwa yana jin ciwo amma sai ya koma" ina jinta ina ta murmushi a raina ina hango baby sultan yana ta kiriniya da wannan thick gashin kan nasa, tace "please tell me all about him, nuna min pictures dinsa in gani" na dauko waya ta na zare sim card din dan kada sultan ya kira, na kunna na nemo mata wani hoton sultan wanda yake looking very good and decent, na mika mata, tana karba tasa hannu ta rufe bakinta tace "Ya Allah, he is so grown up and handsome" sai kuma hawaye ya fara zuba a idonta "my son, my darling baby" daga hoton dana nuna mata maimakon ta dawo min da waya ta sai ta fara scrolling tana kallon pictures din mu, mostly na sultan ne da ni, sai few na yan gidan mu, in tazo kan wanda bata gane ba sai ta nuna min ta tambaye ni in bata amsa, har yanzu hawaye bai daina zuba a idonta ba, kuka take kuma tana dariya duk ita kadai, ni dai ji nake kamar in karbe waya ta saboda da akwai hotunan da bai kamata ta gani ba, amma ita babu ruwanta, kalli take yi kawai tana dariya, ta dago kai ta kalleni tace "he really loves you, I can already see it in his eyes" na gyda mata kai nace "yes, he does" sai can kuma ta ajiye wayar tace "oh dear, ko ruwa ban baki kin sha ba" nayi dariya kawai bance komai ba, hannuna ta kama ta jani har dakin da na fahimci cewa bedroom dinta ne, ni dai kawai kallonta nake yi, she is really beautiful and amazing, in ka ganta daga nesa ba zaka taba tsammanin babba bace ba, sai in kun zauna da ita ka kalle ta sosai sannan zaka ga shekarunta a fuskarta, jikinta kam babu alamar girma a tare dashi.
Anan dakin nayi sallah, ina idarwa sai ga Hafsat tazo kirana in fito muci abinci, sai a lokacin na kalli Hafsat sosai, nace "yanzu Hafsat dama ciki ne dake baki gaya min ba" ta murguda min baki, nace "yanzu khairat din watanta nawa har zaki ji mata sibling" tace "ke watanki nawa aka haifi faruk? Ni wata na nawa aka haife ki? Me ya ragu a jikin mu? Ko wani mugun ciwo babu wanda yake dashi a cikin mu, itama khairat babu abinda zai same ta" na bita muka tafi ina tambayar ta "wai duk wannan gidan ita kadai take zaune?" Tace "sai ma'aikata, sai kuma 'yan'uwa duk wanda yake so zai iya zuwa ya zauna" ni dai har yanzu kallon gidan nake yi, Hafsat ta dan dakeni tace "kar ki bamu kunya mana, ke tsiya ta dake kyauyanci" muna zuwa dining naga an cika shi da kayan abinci, nan take kwadayi na ya tashi, ina zama Ummee ta taso ta fara serving dina, komai sai da ta zuba min tace dan ni ta dafa dan haka komai sai naci, yi take kamar zata bani a baki, ni kuwa na saki jiki nayi ta zurin abinci, sai kuma naji ina missing sultan, ina ma dai yana gurin nan da sai dai a dauke shi saboda yawan abincin da zai ci. Muna gama ci Hafsat tace min ta kai min akwatina dakin da take, nan take Ummee ta bata rai tace zayed yaje ya dauko ya dawo dashi dakinta, tace yau a gado daya zamu kwana babu mai raba ta dani. Bayan mun tattare gurin muka tashi muka zagaya gidan, ita take tayi mana bayanin ko ina na gidan. Kafin mu gama na gaji sosai, dama ga gajiyar hanya, muna shiga mukayi sallama da Hafsat muka tafi dakin ummee, ina zuwa tace min inyi wanka inyi sallah sai in kwanta, ai kuwa hakan nayi dan Sallar da kyar nayi ta dan idona har rufe wa yake yi saboda bacci, amma ina kwanciya sai na tuna sultan, na tabbatar yau ba zai yi bacci ba, bana nan kuma na kashe wayata ballan tana ko murya ta yaji. Nima sosai naji ina missing dinsa, kamar in dauki wayata in kira shi kuma sai na daure zuciya ta, na runtse idona ina addu'ar bacci yazo amma ina, Sultan kawai nake so. Ranar ba karamin yaki nayi ba kafin in samu bacci ya dauke ni. Ban farka ba sai kusan assuba, na tashi zaune naga ummee a kusa dani tana bacci, abinda ya fara fado min a raina shine sultan, ko zai iya tashi sallar asuba yau? Dan nasan ba bacci zai yi ba kar yazo kuma yayi missing masallaci. Na tashi nayo alwala nazo na dauki alqurnin dana gani a gurin sallah na fara karantawa a hankali dan kar in tashi ummee, har sai da naji anyi assalatu sannan na tashe ta ni kuma na tayar da sallah. Da safe duk jikina babu dadi, na dauki waya ta da niyyar kiran sultan yafi a kirga ina ajiyewa, daga karshe dai na bawa Hafsat sim card dina nace to nace ta bani kar ta bani, tana dariya tace "ai kuwa ba zan baki ba ko zakiyi kukan jini". Tare muka shiga kitchen da Ummee, she is an amazing cook, muna aiki muna hira, nan na bata labarin cewa kafin inyi aure ban iya girki ba, sai daga baya na koya, ai kuwa tayi min alkawarin sai ta mayar dani kwararriya a girki. A kitchen din muka zuba abincin a kwano daya muka ci, ban san me yasa ba kawai naji na saki jikina da ita, ji nake yi kamar dama can nasan ta all my life.
Bayan nayi sallar azahar, ina zaune a dakin ummee ina tunanin ko me sultan yake yi yanzu? Sai ga ummee ta shigo, ta samu guri ta zauna a bakin gado, na dan juyo na kalleta tayi min murmushi. Tace " maimunatu so nake ki bani labarin sultan, tell me all about him, I want to know everything bana son ki boye min komai" na gyara zama na ina tunanin ta ina zan fara ne, she is his mother, she deserves to know everything. Nan na fara daga labarin da Takawa ya bamu na abinda ya faru bayan an dauke ta daga gidan, na gaya mata abinda sarki abdallah yayi, tun anan ta fara sharar hawaye, na dora da bata labarin rayuwar da sultan yayi tare da mahaifinsa, ban boye mata komai ba har zamansa a gidan kangararru da rayuwarsa a America, na gaya mata past drinking habit din sultan amma na tabbatar mata cewa yanzu ya daina, amma ban gaya mata dalilin fara shan giyar tasa na, na gaya mata haduwata dashi da yadda Daddy ya dauko shi ya dawo dashi gidan mu, amma ban gaya mata kiyayyar da Mommy tayi masa faga farko ba, na bata labarin auren mu da kuma sanadin karyewar asirin Takawa zuwa halin da muke ciki a yanzu, na dora da cewa "Sultan is emotionally not stable, shi yasa yaki zuwa, har yanzu kullum yana tunanin cewa mutane basa sonsa, da kyar ya yadda cewa Takawa yana sonsa da gaske, kema kuma yana tunanin ba sonsa kike ba saboda yana ganin kinyi abundaning dinsa tsahon shekaru baki taba neman sa ba, he is just scared to get his heart broken" bata cemin komai va saboda kukan da take yi, ta tashi ta fita daga dakin. She needed to be alone and I understand. Har bayan la'asar ban kuma ganin ta ba. Zayed yazo ya dauke mu ni da Hafsat muka tafi yawo, ya nuna min birnin Riyadh, garin ya hadu fiye da tunani na, lallai larabawa karshe ne gurin dukiya, ga tsari ga doka. Da magrib muka je gidan su Zayed na gaishe su, sun karbe ni sosai a matsayin kanwar Hafsat, Zayed yace mu bar Khairat ta gaya musu da kanta when she is good and ready. Muna komawa gidan Ummee muka same ta ita kadai a zaune a palon ta, akan kujerar dana sameta jiya, idonta akan kofa, na lura ta dan rame kadan akan jiya. Muna shigowa tayi mana murmushi, tace tana kallona "na dauka kin gudu" na karasa da sauri nace mata "I will never" .
Da daddare sai ka wayar sultan a wayar Hafsat, ta nuna min screen din, na daga kafada, ta dauka da sallama, daga ganin yadda Hafsat take yamutsa fuska nasan masifa yake mata, sai da ta barshi ya gama sannan tace "kana magana da Hafsat ne ba da maimuna ba" sun jima suna ta rigima daga alama cewa yake ta bani wayar ita kuma taki, da ta gaji ta kashe wayar tana kallona "he is really pissed off, yana neman ya kashe min dodon kunne" and my heart went out to sultan, yana can nasan ya hargitsa gidan mu gaba daya, poor Amir shi zaifi kowa dandanar zafin sultan. I hate hurting sultan amma shi zuma ne sai da wuta, he will never come to his mother in ba haka nayi masa ba. Duk hirar da muke yi Ummee tana jin mu amma tayi shiru, she seems deeply in thoughts. Sai bayan munyi sallama da Hafsat naje nayi shirin kwanciya na kwanta ina ta tunanin sultan sai gata ta shigo, ta zauna a bakin gado tana kallona tace "yana son yasan abinda ya hanani zuwa wajansa ko? Yana son yasan ko ina sonsa ko bana son sa? To ga labari zan baki ki gaya masa" na tashi zaune na jingina da jikin frame din gadon ina sauraron ta. Tace "bayan an dauko ni daga Nigeria, ban taho da komai ba, babu miji babu da, bani da ko hoton sa, daga ni sai kayan bacci a jikina sai abaya da hijab, babu wanda zai gane halinda na shiga a lokacin sai uwar da aka raba da mijinta da kuma dan karamin danta, suna farkon duniya ita tana karshe. Nayi kuka kamar raina zai fita, gaba daya family aka taru a kaina telling me cewa na basu mamaki, na zubar musu da mutuncin su a cikin jama'ar, saboda ba karamin abun kunya bane ace 'yarka budurwa ta gudu da saurayi, kowa abinda zai fada daban. Gashi an samu matsala da familyn wanda aka yi niyyar hadamu aure da shi. Aka sake sakani a daki aka rufe. Babu abinda yayi keeping dina alive a lokacin shine maganar sadiq da yace he will come for me, so I waited, not patiently but I waited. Kwana daya sadiq bai zo ba kwana na biyu shiru, a kwana na ukun ina dakina ina aikin dana saba wato kuka sai ga ummina tazo tayi kirana, ina zuwa palo na samu babana da uncle dina a zazzaune, na gaishe su sai suka miko min takarda suka ce daga Nigeria, da sauri na da bude ina so inji labarin Sadiq da Sultan amma me zan gani, wasika ce daga Sadiq cewa ya sake ni, bai yi stating dalili ba kawai dai ya sakeni, in his own handwriting, after all what we went through together, after irin rabuwar da mukayi da kuma irin alkawarin da yayi min cewa he will come for me, amma abinda na samu daga gare shi shine saki. I list everything, the trust of my family, my dignity, my husband and my son. I was totally broken. Na shirya akan lallai sai naje Nigeria na tambayi sadiq dalilin da yasa yayi min abinda yayi min, kuma in karbo dana, amma family na suna ganin yin hakan bashi da amfani, ya wulakanta ni ya yaudare ni ya rabani da iyayena, sannan kuma ya sake ni, to me zanje inyi masa kuma, sunce matsoraci ne shi, nusari wanda ba zai iya fighting for his family ba. Na nuna musu ni ba ta sadiq nake yi ba ta Sultan nake yi, amma still suka hana ni xuwa, abinda ummi na tace min shine inna je ma ba bani shi zasuyi ba, kuma nasan gaskiya ta fada ba zasu bani shiba, ta gaya min cewa inna dauko shi ba taho dashi gurina what kind of life zan bashi a matsayin dan mace babu uba? Duk abinda mutane suke fada akaina cewa yawon banza na tafi sai su tabbatar kenan in suka ganni da 'da babu uba, tace duk tsahon shekaru sultan shi zai neme ni da kansa. Duk na nuna musu kamar na yarda amma suna sakin jiki dani na gudu, unlucky for me wani friend din babana ya ganni a airport ya kira waya ya fada, aka zo aka sake mayar dani gida, nan take magana ta fara fita a cikin mutane, cewa khairat 'yar faisal abdallah ta fara yawon banza, ance na gudu da saurayi shekara uku sannan aka samo ni, fada da nasiha babu irin wadda ba'a yi min ba amma ni hankali na yana Nigeria, na gwada guduwa yafi a kirga, daga baya family na suka hadu suka yanke shawara, aka yi bannin dina daga fita daga kasar saudiyya gaba daya, ko baje airport da zarar anyi thumb printing dina shikenan ba za'a barni in shiga jirgi ba. Tun daga lokacin har yau ban taba taka kafata outside Saudi Arabia ba. I tried everything i can to get to sultan, I wrote him letters but they all turned back. My family made sure sunyi cutting duk wata hanya da zanyi contacting Nigeria. Su a ganinsu gurin sadiq nake son komawa, inna yi musu maganar sultan sai suce min zai neme ni da kansa. Da addu'ar da nasiha na fara hakura da zuwa Nigeria, amma ko dai da rana daya ban taba dauke hankali na daga kan sultan ba. Na yadda da abinda ummi na take gaya min cewa sultan zai neme ni da kansa, saboda nasan da ya fara hankali zai fara neman ina mahaifiyarsa take, kuma nasan Sadiq zai gaya masa labari na kuma nasan zai neme ni. I waited years in and years out amma shiru. Babu irin abinda ba'a yi min ba akan inyi aure amma naki, ba wai sadiq nake jira ba, bana son sultan yazo ya tarar na sake wani family din, kar yayi tunanin na manta dashi ko bana sonsa, I stayed alone for him, very lonely. Ina kallon 'yan'uwana maza da mata kowa yana yin aure yana barin gida amma ni naki inyi aure. Ina ta lissafa shekarun sultan, lokacin da na san cewa he is old enough ace ya mallaki hankalinsa ya fara nema na, a lokacin na kara saka ran zuwanshi, ban taba tsammanin cewa dana bai ma san wacece ni ba, ban taba tsammanin Sadiq ya manta dani ba. Da shekaru suka ja sai na fara tsoron ko wani abun ya same shi shi yasa bai neme ni ba har yanzu" kuka yaci karfinta tayi shiru, sai data tsagaita da kukan sannan taci gaba "I was so lonely and depressed, sai babana ya bani jari yace in fara business, it will keep me busy as I waited for my son, nan na fara kasuwanci, from small scale ina dan siyan kayayyaki ina siyarwa, Allah ya saka min albarka a ciki, nan take arzikina ya fara habaka, within few years na fara aikawa kasashen waje ana saro min kaya ina siyarwa, har na zama dealer nake supplying manyan shagunan garin nan da kaya. Amma dai dai da rana daya ban taba cire ran sultan zai zo ba, tunda na gina gidan nan na dawo duk sanda mota ta tsaya a bakin gate sai gaba na ya fadi ina saka ran shine yazo, amma shiru. Na kebe kaina daga cikin mutane ne saboda bana son maganganun da akeyi a kaina. Nasan Zayed yayi aure amma bansan wa ya aura ba, lokacin da yazo nan shida sister dinki naga cewa she is African kawai sai naji ina sonta, I told her about sultan. You have no idea how I felt sanda kika ce min ke matarsa ce" ta goge hawayenta ta juyo tana kallona "How long do you think zaiyi taking kafin yazo?" Nace "one week, at most, two weeks, shima saboda sai ya nemi visa ne" . Tayi murmushi tace "then we will wait for him, together".
Episode Eighty Nine : Khairat 2
Na taso na dawo kusa da ita na zauna nace "yes Ummee, we will. Nayi miki alkawarin Sultan zai zo gidan nan, kuma in yazo zaki yi mamakin sa, dan duk wannan zuciyar da wannan fushin na dan lokaci ne, haka yake, akwai saurin hawa kuma akwai saurin sauka, I assure you yana ganinki shikenan komai zai wuce, he is just not sure of yadda zaki karbe shi ne, duk wannan girman jikin da wannan kwarjinin a ido ne kawai, in side him he is the kindest man I have ever known, yana da tsananin tausayi da kuma kokarin kyautatawa mutane, ko da kuwa wadanda suka zalince shine bai damu ba, he said kyautatawa mutane makes him feel good shi yasa yake yi, ballantana ke da kika haife shi, kallo daya zaiyi miki and it will all be over, he will take you in his arms and cry on your shoulders, he will love you fiye da yadda kike tsammani, zai zamar miki 'da daya tamkar da dubu, he will feel Lucky to have you as his mother" sosai Maganganu na sun kwantar mata da hankali dan har murmushi na gani akan lips dinta, ta kama hannayena duka biyun tace "Maimunatu bansan me zance miki ba daga ke har iyayenki, you are really an angel a rayuwar dana, bani da bakin da zan gode miki sai dai in dawwama har karshen rayuwata ina yi miki addu'ar" na dora hannunta daya akan cikina tace "ubangiji Allah ya jagoranci rayuwarki, da duk kanin zuri'ar ki, ya baku kyakykyawar rayuwa fil duniya wal ahkhira, Allah ya daga garajarki da duk kanin ahlinki, Allah ya kade duk wani sharri dake cikin rayuwar ku ya tabbatar da alkhairi a duk al'amuranki, Allah yayi miki sakayya a bisa duk abinda kika yi a rayuwar sultan. Allah ya albarkaci zuri'arki yasa su zamo sanyin idaniya a gare mu baki daya. Allah kuma ya kara soyayya a tsakanin ki keda mijinki, ya dauwamar da zaman lafiya a tsakaninku, ya sa ku kasance tare har karshen yaruwar ku" duk abinda take fada ina cewa amin, kuma ina jin dadi har raina, sai da ta gama yi min addu'ar sannan ta jawo ni jikinta ta rungume tace "Nagode Maimunatu".
Kwana biyu bayan nan, ni gani nake yi ma kamar nafi sultan damuwa, komai nake yi hankali na yana kansa, da kaina nace Hafsat ta bani sim card dina amma taki, kullum sultan yana cikin kiran wayar Hafsat, tun yana yi mata masifa har ya koma bata hakuri yana lallashinta, ita kuma tace sai ta rama fadan da yayi mata, innaji suna waya sai in ji kamar in kwace wayar amma nasan muna yin magana da sultan zai kalallame ni yace in dawo Nigeria, I don't think I can resist him in inajin muryarsa. Little khairat ce ta zama babbar kawara, tana ta rarrafenta ko'ina har ta fara tsayawa, in tana gurina babu abinda yake kaita gurin Hafsat sai in zata ci abinci. Ummee kuwa sosai muka kara sabawa da ita. Kamar yadda tayi min alkawari haka ta zage wajan koyamin girki, irin abincin larabawa iri iri haka take koyamin, babu abinda take so irin in zauna inyi ta bata labarin sultan, wannan kullum shine abin hirar mu. Hotunan sa kuwa na waya ta ta gansu yafi a kirga. A wayar Hafsat na hada ta da Mommy suka gaisa, nan take suka kulla kawance. Mommy ta gaya min ta yaba da ita tun kafin ma ta ganta.
Ranar dana kwana biyar a Riyadh, muna dinner da daddare sai ga kiran sultan a wayar Hafsat. Ta nuna min screen din sannan ta daga. Sun danyi magana sannan tace min "yace in ba zaki karbi wayar ba in saka shi a speaker zai yi miki magana, na kalli Ummee naga alamun anticipation a fuskar ta, she has never heard her son's voice tun da suka rabu, na gyada wa Hafsat kai, ta saka wayar a speaker ta ajiye a kusa dani, naji muryarsa "Moon please listen to me, why are you punishing me for the crime I didn't commit? Ni laifin me nayi wai? Kina so zuciyata ta buga in mutu ko?" Na danyi murmushi, dadin baki yake so yayi min, ya cigaba da magana, "Love please, nasan kinaji na, kuma nasan me kike so, I promise you zanzo amma kinsan it will take time, dan Allah na wahala haka, kar kice ba zaki yi min magana ba sai nazo, I can't take it kin sani" Ummee ta taso ta dauki wayar da fitar daga hands free ta miko min, na karba na ajiye khairat da take bacci a kan cinya ta, na mike na fita veranda, ina jiyo Hafsat tana gyaran muryar tsokana amma ban kula taba, na saka wayar a kunne na nace "My Love" kamar ba zaiyi magana ba amma ina jiyo numfashinsa a hankali, sannan yace "why are you doing this?" Nace "I just want you to come and see your mother, shikenan" yace "you should have talk to me ai, ki gaya min ga abinda kike so, you know I can do anything for you love" nace "nayi maka maganar ai kaki yadda, babu yadda zanyi da kai ne" ya dan yi shiru sannan yace "you have no idea how damn good it feels to hear your voice" Nace "me too" yace "ba wani nan, da kin damu dani ai da baki kashe wayarki ba, you always say kina sona but nasan ko rabin wanda nake miki ba kya yimin" nace "kai ma kasan ba haka bane ba. Kawai dai we show our love ne in different ways ni da kai. Zuwa na garin nan da kashe wayata da nayi are all ways of showing you how much I love you. Sometimes you have to sacrifice something to get something better" yace "zaki yi min dadin baki ko?" Nayi dariya, nace "tun da nazo garin nan bana samun bacci me dadi saboda babu kai, ba karamin dauriya nayi ba these five days" yace "uhmmm, na ji ki dai amma ban yarda ba, kina can kina sharar baccin ki kin barni da rungumar pillow da mafarkai ko?" Nace "sorry" yayi ajjiyar zuciya yace "so, how is she?" Nace "come and see for yourself" yace "hmmm baza ki fada min ba kenan ko?" Nace "eh din. In kana son kasan ya take kazo da kanka ka ganta" yace "I will come ai, na gaya miki zanzo. Ina baby na kuma? Haka kawai kin raba ta da daddyn ta" nace "na gaya maka namiji ne fa ba mace ba, he is fine. Can you believe Ummee tana taba cikina ya fara motsi" yace "what? You mean she touched your tummy?" Nace "yes, she does, she is really nice Sultan" muka ci gaba da hira, sam ban san time yana ta tafiya ba, haka muke dama duk sanda muke tare da sultan ko a fili ko a waya ji muke yi kamar time ya tsaya. Sanda ba koma ciki na tarar har kowa ya kwanta, dan haka nima na shirya na kwanta, da safe Hafsat tazo ta cillo min sim card dina tace "bani wayata" na mika mata nima na kunna tawa.
Kwana na goma cif a Riyadh Sultan yazo, tun sanda yayo waya cewa zaizo gaba daya ummee ta tayar da hankalinta, ana gobe zuwansa kuwa sam bata yi bacci ba, daga baya ta tashi ta fara salloli tana rokon Allah for courage. Ni kam tausayinta nake ji har raina, ban san ya take ji a ranta ba. Twelve na rana jirgin su sultan zai sauka, abinciccikan da muka shirya masa nasan duk cinsa sai ya gaji ya bari, Hafsat tana dariya tace "Moon gwara ki tanadi maganin gudawa a kusa". Muna gama shirya komai na tafi daki nayi wanka, ina fitowa Ummee ta shigo ta kawo min wata doguwar riga pink mai ratsin blue a sides dinta, sai stones a gaban rigar, da viel shima blue. Tayi kyau sosai rigar. Na karba nayi mata godiya. Kwalliya na zauna na tsara sosai, na saka rigar naga tayi min bala'in kyau, na fito palo na bar ummee itama tana shiryawa itama. Lokacin dauko shi yana yi zayed yazo, nace su tafi kawai shi da Hafsat ni na jirashi a gida, Hafsat ta kalle ni tace "you are wicked" nayi dariya kawai. Nasan halin sultan, ba karamin aikinsa bane yana ganina a airport ya ce komawa zamuyi, ko kuma in babu jirgi yace mu kwana a hotel da safe mu koma, nayi wa ummee alkawarin zan kawo mata sultan har gida and am going to keep that promise. Su Hafsat suna tafiya sai ga Ummee ta fito, ta saka riga irin tawa sai dai tata blue ce da ratsin pink, tayi nadin veil mai kyau, ta zo ta zauna a kusa dani tayi irin zaman da tayi ranar da zanzo, at the edge of the seat da hannayenta a tsakanin cinyoyinta, muna nan zaune babu wanda yayi magana har muka ji karar bude gate, daganan muka ji tsayuwar mota da sound din bude mota da rufewa, naji ummee ta kama hannuna ta rike kam, na kasa kallon fuskarta, a hankali muka ji an bude sliding door din palon, idona na kafa a gurin, na ganshi ya shigo, bakin wando ne geans a jikinsa mai kauri, da farar shirt yayi stocking ya daura bakin belt, gashin kansa a tsatstsaye kamar wanda ya tashi daga bacci, nasan abinda yasa yayi wannan shigar, so yake ya nuna wa ummensa what he used to be. Idanuwansa a kanmu muma namu a kansa, ya saki jakar hannunsa ta fadi a kasa, ummee ta saki hannuna ta mike tsaye tana jujjuya hannunta, ya kalle ta for some seconds sannan ya dawo da idonsa kaina. Na mike tsaye nima, da sauri ya karaso inda muke, ban ankara ba kawai sai ji nayi ya jawo ni jikinsa ya rungume, na fara kokarin ture shi amma yaki ya sake ni, ya saka fuskar sa a wuyana, a hankali nace "sultan ummee fa tana kallon mu" yace "i know" Nace "go to her" ga mamaki na sai cewa yayi "kunyar ta nake ji" dariya na fara yi kasa kasa, ummee ta zagayo ta bayansa tana kallona tace "me yake cewa?" Ina dariya nace "wai kunyarki yake ji" ta danyi murmushi kwalla ta fara taruwa a idonta, ta dora hannunta a hargitsatstsen gashinsa tana shafawa tace a hankali "my little love" ai kuwa ya sake chusa kansa a wuyana yace "am not little" ta sake cewa "me yace?" Nace "wai he is not little" tayi dariya hawayenta suna karasa saukowa tace "to shikenan, ka koma big love yanzu" har yanzu ya kasa dago fuskarsa ya kalle ta, ni kam dariya kawai nake yi, ban taba ganin sultan yana jin kunyar wani ba sai yau, yace a hankali "yanzu sai tace zata fara pampering dina kuma" tace "ai har na hada maka bottle, yanzu zanje inyi warming in baka" ta dora kanta a bayansa hawayenta yana zuba a jikin rigarsa, ni kam dariya kamar cikina zai yi ciwo, lokaci daya kuma sai ya sake ni ya juya ya rungume ta, take ta saki kukanta gaba daya, na dan ja da baya ina kallon su ina jin dadi a raina, a hankali na sulale na bar musu palon.
Episode Ninety : His Mother's Son
Bedroom din Ummee na shiga na turo kofa, na zauna a bakin gado ina ta murmushi ni kadai like an idiot, reaction din sultan ya bani mamaki kuma ya kara tabbatar min da cewa there is no one like mother. Na san dama zai sauko amma banyi tsammanin saukowar shi da sauri haka ba. Wai kunyar ta yake ji, sultan ne wai da kunya, abin ma abin dariya. Na gaji da zama na jawo pillow na kashingida ina jin farin ciki sosai a raina, burina ya kusa cika, nayi wa kaina alkawarin I will totally change sultan's life around kuma so far babu abinda zance sai Alhamdulillah. Wannan duk ba yi na bane yin Allah ne. Ina nan kwance har akayi sallar azahar na tashi na naje nayi sallah, ina idarwa na koma nayi kwanciya ta, na dauki waya na kira Hafsat tace min sun fita da zayed da khairat, ina nan a kwance sai ga Ummee ta shigo, ta tsaya a bakin kofa tana kallona sannan tace "waye zaiyi serving mijinki abinci da kika zo kika kwanta?" Na dan tashi ina dariya, ta daga gira tace "he has been asking for you, yaki cin abincin ma, wai shi kunya ta yake ji" na tashi na gyara veil dina muka fita tare. A dining na same shi ya tisa abinci a gaba ya zuba uban tagumi, na dan yi gyaran murya, ya juyo da sauri, ina kallonsa har da ajjiyar zuciya ya taso ya taho, na fara waige waigen ummee amma naga bata gurin, na karasa nima gurinsa na shige cikin kirjinsa ya rufe ni da hannayensa, a tare muka sauke ajjiyar zuciya, sosai nayi missing mijina, na lumshe idona ina shakar kamshinsa da yake kwantar min da hankali a koda yaushe, nace "I missed you, mijina" ya danyi dariya yace "ba zan yi magana ba ni, a aikace zaki ga kalmar missing din" na dan ture shi nace "nan dai gidan ummee ne ba gidan mu ba, dan haka mind your steps" na fara tafiya dining ya biyo ni, yace "ai itama tasan ba zata hanani matata ba, in kuwa ta gwada to akwai rigima" na jawo masa kujera ya zauna, na sunkuya dai dai fuskarsa nace "albishirinka?" Yace "goro" nace "a dakin ummee nake kwana a kan gadonta tare da ita" ya yamutsa fuska yace "da kenan, likacin bana nan, yanzu nazo dole a bani matata" nace "to idan tazo sai ka gaya mata" yace "kunyarta nake ji. Shine dazu kika gudu kika barni tare da ita ko?" Na fara bude masa dishes din gurin nace ya zabi wanne zanyi serving dinsa first, amma ga mamaki na sai naga sam bai wani rude akan abincin ba kamar yadda nayi tunani, ni kawai yake kallo, nace "food always come first, hausawa suna cewa ci shi yake gaba da sallah ma" ya daha gira yace "not to me" sallamar ummee mukaji, ina kallon sultan ya wani sunkuyar da kansa kasa, kamar zanyi dariya na maze na fara zuba masa abinci, ummee ta karaso ta zauna tana kallonsa yadda yake juya cokali a cikin abincin, ta kalleni tace "in bashi yake so ba ki zuba masa wani mana" ya dago kai yana kallona yace 'it is OK, am just tired ne, shi yasa" tace "try to eat something then, sai kaje kayi wanka ka kwanta ka huta" yana kallona nayi sauri na dauke kaina na tafi na fara serving ummee, nima na zuba abinci na na fara ci, ummee gaba daya hankalinta a kansa yake, nima ina kallonsa ta gefen idona, a hankali ya fara cin abincin kuma, sai kuma ya fara ci da dan sauri, muka hada ido da ummee mukayi murmushi, yace "this food is really good" nace "ummee ce ta yi shi, for you, ita ta girka all this food, for you" yana shafa kai ya dan kalleta yace "thank you" tace "bani kadai nayi ba ai, tare da maimunatu mukayi" ai kuwa sultan ya zage yaci abincin sosai, kusan komai sai da na zuba masa yaci, yana ci kuma yana santi, ummee sai tsokanar sa take yi yana zuba mata zance, kunyar ta fara tafiya. Muna gamawa ummee tace "an kai maka kayanka dakinka, maimunatu sai ki raka shi yayi wanka ya huta ko?" Na dan bata rai irin ni bana so din nan, ya mike ya fara tafiya, har yakai bakin kofa ya juyo yana kallona yace, "ban san gurin ba fa, sai anzo an nuna min" ummee ta harare ni tayi min alamar go da hannunta, ni dai duk kunya ta ishe ni, na bishi a baya. Muna fita nayi gaba, nasan gurin dama ummee ta nuna min sanda ta zagaya dani gidan, katon palo ne da three bedrooms, komai na gurin red and cream ne, hatta electronics din gurin. Muna shiga ya rufo kofa yana kallona, nace "welcome to gidan ka da baka san dashi ba" kallo daya yayi wa dakin yace "wato da ba zaki zo ba ko?" Na saka hannu ina shafa sajen sa, ya lumshe ido yana kara kwantar da fuskarsa a hannuna, nace "Ummee tana gurin kuma sai kawai in yi saurin tahowa? Kai ma kanka kake cewa kana jin kunyarta ballantana ni?" Ya dora hannunsa akan cikina, sai kuma ya danyi murmushi yace "ya naji kamar ya kara girma ne wai? How is she?" Nace "He is fine, yayi missing Daddy dinsa". Bedroom daya na kai shi na hada masa ruwan wanka, shi lallai wai sai dai muyi tare ni kuma bana son in bata kalliyata ummee ta gane. Amma ina sam bai fahimci wannan yaren ba, da nayi masa taurin kai ma dauka na yayi har ni har kayan jikina ya saka a tub, ba kwalliya ba har kaya na ma na bata kenan. Ba zan iya lissafa tsahon lokacin da muka bata a bandakin ba, dan anan aka nuna min duk missing din da ake ta fada min kuma na fahimci lallai anyi missing din nawa. Sai daya karar min da duk energy na dan kasa fitowa nayi daga toilet din sai shi ya fito dani ya dora akan gado, ya kunna room heater ya saka jallabiyya ya fita, naji dadin dumin da dakin yayi na fara bacci, cikin baccin naji dawowarsa, na dan bude ido na ganshi da tray a hannunsa, ya ajiye yana cewa " kinsan dai babu kyau baccin la'asar kuma kike yi ko?" Na dan tashi ina kara jan bargo jikina, ya kama bargon zai cire na saka kara yayi dariya yace "as if U don't know what is there" nace "oho dai, ba zan bude ba" to amma dai zaki sha madarar nan ko? Tunda kince na karar miki da karfin ki to gashi nan na biya ki" ya zubo madarar ya miko min, shima ya zuba ya zauna a bakin gado yana sha. Anan yake bani labarin da kyar Takawa ya barshi ya taho, yana so yazo din kuma baya son rabuwa dashi. Muka zauna kowa yana bawa dan uwansa labarin abinda ya faru bayan rabuwa, amma sam ban bashi labarin da ummee ta bani ba, a ganina wannan ba hurumi na bane ba, nafi son ta bashi labarin da kanta yadda hakan zai kara karfafa alakar su. Sai da mukayi sallar magrib sannan muka fara shirin fita, ga kayana har underwears a jike a toilet, na rasa inda zan saka kaina, sultan ya saka kaya yabani jallabiyar sa yace in saka, na saka na dauki mayafin doguwar riga ta na saka, muna fita dakin da aka sauki Hafsat na tafi da sauri dan bana son Ummee ta ganni, Allah ya taimake ni dakin a bude yake na shiga na samu kayan ta na saka sannan na tafi palon ummee, sultan na gani a bakin kofa wai kunya yake ji ya shiga shi kadai, ni kuma nace kunya nake ji mu shiga tare, muna ta muhawara sai gata ta bude kofar tana kallon mu, duk muka sunkuyar da kai kamar wasu munafukai, tace min "shine kika gudu kika barni da girki ni kadai ko?" Na dan sosa kaina nace "I tot abincin dazu zai isa har dare" tace "sai kije kiyi arranging table din" ta matsa ta bamu guri muka shigo, tana kallon sultan tace "welcome little love" da alamar tsokana a muryarta, ai kuwa sultan harda rufe fuska, ni kam dariya nake masa, ni banga abin kunya a uwa ba, tana shiga daki ya biyo ni dining room "wai baki lura cewa she looks too young ba?" Nace "eh na gani mana, amma ai dama jikinsu da namu ba daya bane ba, plus bata hayaiyafa ba, haihuwa kuma tana daga cikin abubuwan da suke saka mata tsufa" yace "ni kunyar ta nake ji wallahi" nace "wai menene abin kunyar a ciki?" Yace "yanzu fa kinsan tayi min tsarki ina baby, nayi mata a mai a jiki" nace "amai kadai? Kayi mata kashi kayi mata fitsari duk a jikinta" da sauri yace "no, banyi ba" nace "in tazo a tambaye ta?" Yace "a'a a bar maganar kawai" nace "she gave birth to you sultan, she nurse you, she fed you, and she loves you more than anything in this world". Kafin mu fara dinner na kira Hafsat tace min ba zasu dawo yau ba, a gidan su zayed zasu kwana saboda suna shirye shiryen komawa England. Muna gama dinner nace da ummee bara in je daki, ina shiga daki nayi kwanciyata sabida dama sultan ya tara min gajiya. Sai wajan ten na tashi nayi sallar isha, na dan bude kofa na leka falo, still sunanan, sultan na gani durkushe a gaban ummee ya dora kansa akan cinyarta, bana ganin fuskarta amma ina jin muryarta tana masa magana da alamar tayi kuka, na mayar da kofar na rufe na koma na cigaba da baccina. Cikin baccin naji tana tashi na, na farka da kyar ina kallonta, tace "tashi ki tafi dakin mijinki, da safe kya dauki kayanki" zance nata a'a tace "I insist" dole na tashi na dan dauki abubuwan da zan bukata, itace ma mai tuna min da wani abin, ni dai duk kunya ta ishe ni, na dau kayana na fita. Ina shiga part din sultan na tarar har ya kwanta, motsina ne ya tashe shi, ya na kallona nace "ta koro ni" har da dan rawarsa yace "uwa dadi" na dan fara kuka shagwaba, ya bude min bargo kusa dashi yace "shigo in rarrashe ki" na ajiye jakar hannuna na shige jikinsa, har da kara cusa kaina na zagaye shi da hannayena, a cikin kunnena yace "ana so ana kaiwa kasuwa ko?". Yau nayi baccin da banyi ba a cikin kwana goman da nayi a Riyadh, washe gari ma sai daki aka kawo mana breakfast.
Kwanan sultan biyu a Riyadh su Hafsat suka koma England, naji babu dadi saboda na saba da ganin ta kwana biyu, har airport muka rakasu suka tafi. Sultan yanzu ya saki jikinsa sosai da ummeensa, dan har hira da dariya zan gansu suna yi tare. A ranar ne kuma Ummee tayi deciding zata nuna mu a gurin 'yan'uwanta. A ranar da daddare ummee ta dauke mu ta kai mu gidan su, gurin mahaifiyarta, mahaifinta kam ya rasu last two years. 'Yar dattijuwar tana ganin mu ta gane sultan, sai kuka, ta rungume shi tana ta godiya ga Allah, bata iya turanci ba dan haka da larabci take magana, sai dai abinda bamu gane ba ummee tayi mana bayani, tace " ashe da akwai rabon zan ganka Abubakar? Kakanka har yabar duniya yana nadamar rabaka da mahaifiyar ka da suka yi, muna neman afuwar ka ka yafe mana," mun jima a gurin ta sannan muka tafi, sai da tasaka muka yi mata alkawarin ba zamu bar garin ba sai mun dawo gurinta. Daga nan gidan uncle din Ummee muka tafi, wanda yanzu shine kamar head of the family n su, ni dai gaba na yana ta faduwa ina tunanin yadda zamu kare dashi tunda har dashi aka je aka dauko ummee, ga mamaki na sai na ga sun karbe mu sosai, ya jawo sultan jikinsa yace "Abubakar din mu ya dawo gida" matan gidan ma sosai suka karbe mu, duk sun san da maganar sultan, 'ya'yan gidan ne dai sai kallonsa suke suna cewa dama khairat tana da 'da? Yayi mana nasiha sosai akan cewa ba laifin khairat bane ba, laifin sune su iyayenta, su suka rabata da mijinta da 'dan ta saboda pride dinsu, ya nuna wa sultan kuma cewa nan gidan su ne, kowa anan dan'uwansa ne babu banbanci, da zamu tafi yace "ina sadiq din kuma? Shi yaushe zaizo?" Duk kannin mu bamu da amsar wannan tambayar. Muna mota zamu koma gida na yiwa ummee tambayar da ta dade a raina nace "ummee ni kuwa ina don inji me yasa likacin aurenki kika samu matsala amma lokacin auren zayed shi bai samu matsala ba" tace "da akwai dalilai. Na farko ni mace ce zayed kuma namiji ne, a gurin zaben miji maza sunfi samun freedom akan mata, saboda mu mata muna da weakness, nan da nan za'a yaudare mu shi yasa iyaye suka fi saka idonsu akan spouse din mata akan maza. Dalili na biyu shi zayed kusan rabin rayiwarsa a England yayi ta, dan haka sanda ya tashi aure in banda wadanda suka je nema mishi auren babu wanda zai ce yasan matar sa, bayan anyi auren ma a England din suka zauna bai kawo ta nan ba har sai da ta haihu, zayed is older and stronger than I was, dan haka babu wanda zai kalli matarsa yace wani abu a kanta, dalili na uku kuma the most important shine, tsakanin aure na dana zayed shekara talatin, three full decades, abubuwa da yawa sun chanza, duk yawancin masu akida ta tribalism a family din mu babu su yanzu sai kalilan, suma kuma sunyi sanyi sosai" na fahimci bayanan ta, na kara tambayar ta daya abinda yake zuciya ta, nace "to yanzu ummee idan Takawa ya dawo kina ganin ba zai samu matsala ba kenan?" Tayi shiru kamar bata jini ba, sai naji babu dadi a raina, I shouldn't have asked that, sometimes surutu na yana sakawa in wuce limit dina, nace "am sorry ummee I shouldn't have asked that" tace "Sadiq ba zai zo ba ai, da ace zai zo da tare zasu zo da sultan, tunda kika ga basu zo tare ba to ba zai zo ba". Ban kuma tambayar ta komai ba, sultan ma kuma tunda muka fara maganar baice komai ba. Washegari muka cigaba da zagayawa gida jen 'yan'uwan ummee, kuma Alhamdulillah muna samun karbuwa a gurin su, duk da few of them ne suka san da zaman sultan a duniya. Rannan mukayi waya da Mommy, tace min " Ibrahim fa yazo neman auren Amina a gurin Daddy" da murna ta nace "laaa, amma shine Amina ko ta kirani ta gaya min?" Mommy tace "ai Amina ta tayar da rigima, tace ita yanzu bata son shi" nace "me ya faru?" Tace "wa ya sani ne, taki gaya min komai, shi yasa na kira ki ko zaki tambayar mana ita, kinga yaron nan sai faman zirga zirga yake amma ko fita gurinsa taki yadda tayi ballantana suyi magana, kuma naga daddyn ku sosai yana son hada wannan auren" nace "insha Allah Mommy zanyi mata magana, ko menene ma zamu sani". Ina kiran Amina ce min tayi "babu wani abu da zaki gaya min in chanza mind dina fa" nace "kin san ma maganar da zanyi miki kenan?" Tace "ai kowa maganar da yake min kenan, tunda ni ce mai auren nasa kuma nace na fasa banayi ba shi kenan ba sai a kyale ni" nace "OK munji mun kyale ki kin fasa auren sa, to amma ko zamu iya sanin dalili?" Kamar ba zata yi magana ba sai kuma tace "he doesn't love me. Duk abinda yake fada a baki ne kawai amma vai kai zuci ba" nace "ya zaki ce haka Amina? Wani abin yayi miki daya nuna miki cewa baya sonki?" Ta fara kuka tace "har yanzu Moon ke yake so, yana kulani ne kawai saboda muna kama dake, bana son in aureshi muyi ta samun matsala akan hakan" nan ta bani labarin abinda ya faru tsakanin su kwanan baya, nace "amma Amina tunda kika ga ya dawo ai ina ganin ya kamata ki saurare shi, ballantana kuma da maganar aure ya dawo, meaning he is serious this time around. Bansan menene a zuciyar Ibrahim ba amma nasan yayi nadamar abinda yayi wa matarsa ta farko, kuma yayi mata hakan ne saboda baya sonta, bana jin zai kuma making the same mistake a kanki, idan da baya sonki da gaske da ba zai ce zai aure ki ba" na jima ina bata shawarwari, da gaske Amina tana son Ibrahim dan haka na san zata sauko ne ta sake bashi second chance.
Bayan munyi waya da Amina sai nayi deciding inkira Amira in ji ita ma ya take ciki, na kira ta ta dauka da murnarta, tace "Moon naje gidanki aka ce ba kya kasar ma, ina kuka tafi haka babu ko sallama?" Nace "munje saudi gurin ummeen sultan" tace "dama 'yar can ce?" Nace maka kawai "eh" munjima muna hira sannan tace "kanin ki yazo gurina rannan" da sauri nace "and?" Tace "I don't know Moon, sam banji wani abu a raina akansa ba. Amir ma yazo yana gayamin maganar aurensa, he said if am interested in him, bayan auren nasa we will talk. Moon nayi addu'ah nayi istikhara amma banji komai a raina game da Abbas ba, I tot I had something for amir amma tunda yayi min maganar aurensa naji na hakura" nace "yanzu me zakiyi Amira?" Tace "Moon alhakinku ne yake ta bina har yanzu, shi dama alhaki ai kuikuyo ne, me shi yake bi, happiness dinku dana katse muku shi ya saka zanyi spending the rest of my life in sadness" nace "ba haka bane Amira, shi ubangiji ai mai gafara ne, yana yafiya kuma yana son bayinsa masu nadama da neman gafara, sai dai laifin da kika yi ba ubangiji kika yiwa ba, mu kika yiwa, dan haka ubangiji ba zai yafe miki ba har sai mu mun yafe miki. Ni na yafe miki ba tun yau ba, amma abin tambayar shine, kin nemi gafarar Ibrahim? Shi kika fi cutarwa, shine yafi kowa shan wahala kuma har yanzu bai huta ba, shawara ta gareki shine, ki je ki nemi Ibrahim ki roke shi gafara, na tabbatar zai yafe miki, in kuma ya yafe miki, na tabbatar zaki ga chanji sosai a rayuwar ki, saboda hakkin wani baya taba barin mutum yaci gaba a rayuwa".
2 hrs ·
Episode Ninety One : His Mother's Son 2
Tace "to ni yanzu moon ta ina zan same shi?" Nace "How will I know ni da bana kasar ma" tace "Moon tsoronsa nakeji, tunda ya gane gaskiya bamu hadu ba, bansan wacce irin karba zai yi min ba" na danyi tunani a raina, tabbas Ibrahim yana jin haushin Amira sosai, dan haka ba lallai ne yasaurare ta ba in taje wajansa, Allah ma yasa karya faffalla mata mari. Sai kuma wata shawara ta fado min arai na, nace "abinda za'ayi Amira, kije gidan mu gurin Amina, ni zan kira ta in yi mata bayanin abinda nake so tayi, zata hada ki da Ibrahim kuyi magana, duk abinda ake ciki kuma sai muyi waya" ina gama yawa da amira na sake kiran Amina, ta dauka tace "what again?" Nace "ke dalla can ba maganar shi zanyi miki ba" sai nayi mata bayanin duk yadda mukayi da Amira, nace "yanzu taimako nake nema a gurinki, so nake ki hada su ta roke shi gafara, kema dan Allah sai ki tayata rokonshi" tace "kuma kika ce min ba maganarsa zakiyi min ba" nayi dariya nace "amma ai ba maganarsa dake nayi miki ba, maganar abinda ya faru tsakaninsa da amira nayi miki" ta danyi tsaki tace "ba lallai ne fa ya yafe matan ba, tunda har yanzu bai manta ki ba ba lallai ya yafewa wadda ta raba ku ba" nace "in kika hada su ne zaki tabbatar cewa ya manta dani yanzu, nayi miki alkawarin zaki sha mamaki, bazan miki alkawarin zai manta dani completely ba tunda nima ban manta dashi completely ba amma babu zancan soyayya, an wuce gurin, sai mutunta juna. Duk kanin mu, ni da ke, Ibrahim da Amira, duk mutane ne mu, muna making wrong decisions a rayuwar mu, muna sabawa Allah ma kansa ballantana mutum, amma in muka nemi gafarar Allah sai ya yafe mana, ya sake bamu chance saboda yana son mu chanza mu zama mutanen kirki, ti me yasa mu mutane ba zamu ke yafe wa junan mu ba? Me yasa zamu ke riko a ranmu bayan munsan cewa muma muna so in mun yiwa wani laifi ya yafe mana. Please Amina kiyi kokari kiga Ibrahim ya yafe wa Amira kema sai ki yafe masa ki sake bashi chance" ina kallon sultan ya shigo dakin da takardu a hannunsa ya tsaya yana kallona, Amina tace "shikenan, zanyi magana da Amirar in gani, I will see what I can do" muka ajiyar wayar. Sultan har yanzu yana tsaye yana kallona, am sure yaji ambaton sunan Ibrahim da nayi a waya, na tsaya ina jiran inga reaction dinsa, ya karaso inda nake yace "miss problem solver, kina nan amma kina solving problems din wadanda suke thousands miles away" naji dadi da ya fahimce ni, ya zauna a gefe na ya miko min takardun hannunsa yace "Ummee tayi miki maganar nan?" Na karbi takardun ina dubawa, da sauri na mike zaune sosai ina kara dubawa, na girgiza masa kai nace "bata yi min maganar ba, ta dai ce saboda kai ta fara kasuwancin ta, amma bata gaya min cewa sunan ka ne akan komai ba" dukkan takardun abinda Ummee ta mallaka ne, hatta takardun wannan gidan, da bank account dinta, da takardun dukkan contracts din data karba na shigo da kaya, duk sunan sultan ne a jiki. Na ajiye takardun ina kallonsa, yace "how do I tell her ni bana son kudinta?" Na girgiza kaina nace "mahaifiyar kace sultan, duk abinda ta baka ba faduwa tayi ba kuma kaima in ka karba ba faduwa kayi ba, karbar da zaka yi a ganina shine nuna godiyar ka gareta, inka mayar mata ka nuna mata baka so ba zata ji dadi ba, ka karba amma sai kace mata ka barta a matsayin care taker ta dukiyar taka, ta cigaba da kula da ita kamar yadda takeyi da" yace "to wannan uban cash din kuma da yake banki ya zanyi dashi?" Nace "kudi ne fa, you can do anything with it" ya jawo ni kan cinyarsa yace "ke a shawarar ki me kike ganin ya dace inyi dasu?" Na gyara kwanciyata a kan cinyarsa na danyi tunani kadan sannan nace "why not ka sake gina wata orphanage din, kuma ka bunkasa wacce kake da ita already, kace kana son gina musu makaranta da daukan malamai. Kaga idan kayi haka daga kai har ummee zaku samu lada har karshen rayuwar ku", yana murmushi yace "har ke da kika kawo shawarar" na mayar masa da murmushin nace "yes, har ni dana kawo shawarar". Washegari Ummee ta kaini gidan su zayed na wuni a can Umm zayed me kirki sosai gata wayayyiya, da sister dinsa zahra, na sake sosai dasu muna ta hira da zahra ina vata labarin England, wai tana son zuwa tayi karatu amma an hana ta a gida, muma cikin hira tace "amma kinfi sister dinki kirki, ita bata yiwa mutane magana" nayi dariya nace "ba haka bane ba, Hafsat tana da kirki sosai, kawai dai banbancin halayya ne a tsakanin mu, ni ina da surutu da saurin sabo da mutane ita kuma bata kula mutane sosai, amma in kika saba da ita zaki fahimci tana da kirki sosai. Abinda zakiyi ki lallaba a barki ki je England gurinsu ki dan kwana biyu, zakiyi mamakin kirkin Hafsat" sai magrib sultan yazo ya dauke ni muka koma gida. A hanya yake ce min "yaushe zamu koma Nigeria ne, Takawa yana ta waya wai ya kamata in taho haka nan" nima nayi missing gida sosai, amma nace masa "akwai rigima da ummee kenan" yace "sosai kuwa, dan yadda take ta plans dinta tunani take yi munzo garin nan kenan, ta manta ina aiki a can, besides Takawa ba zai taba barina in dawo nan da zama ba" a raina nace wasa kenan, dan nashi namiji guda daya kamar rai, his only heir, sultan yace "abinda za'ayi yanzu in munje gida, naga kunfi shiri da ita, ki tayar mata da maganar komawar mu Nigeria mu gani abinda zata ce, sai muyi mata bayanin ai ana ta nemana a office din mu sannan kema asibitin da kikayi booking zaki yi antenatal suna nemanki, mu ce mata amma zamu ke zuwa from time to time" na yarda da shawarar sultan dan haka muna dinner na fara maganar, dama sai da na gama jero adduoi sannan na fara magana, tunda na fara ta ajiye spoon din hannunta tana kallona, na duburburce na kasa karasawa, na kalli sultan amma sam yaki dago kansa ya kalleni, tace "yaushe kuka hada wannan plan din? A hanya ko kuma dazu a daki? You are not going anywhere. Me zakayi da aikin a can din? In aikin yi kake so sai ka nema anan ai. Ke kuma wanne antenatal zaki yi wanda ba zaki iya yi anan ba? You are a doctor, kinsan duk abinda kike ji kinsan kuma drugs din da zaki sha, ki rubuta masa sai ya siyo miki, sai menene kuma ake yi a antenatal din? Akwai kanin zayed shima doctor ne anan, ki shirya gobe sai muje ayi miki scanning" na kalli sultan na ga har yanzu baya kallona, nace a raina, wato zura ni kayi dama ka barni ni kadai ko? Ai kuwa muna komawa part din mu na fara sauke masa kwandon bala'i, "shine dazu kaki yin magana ko" yace "dama nasan ba zata yarda ba, I just want to confirm" nace "shine kayi using dina kayi confirmation din ko? I tot we are suppose to be a team" yace "we are a team. Yanzu ni bansan me zance wa Takawa ba idan ya sake kira, dazu daya kira cewa yayi da yasan zamu dade da kema ba zai barki ki taho ba ballantana har in biyo ki. Yanzu me zance masa?" Nace "oho, ni dai ba zaka sake yin using dina ba ehe, kawai dan ace ni ce marar kunya" ya jani muka zauna yana langwabar da kai, "hava love, ba using dinki nayi ba, kin san ina jin kunyar ummee ba zan iya yi mata musu ba shi yasa nayi shiru. Ina son komawa Nigeria amma kuma bana son inyi hurting ummee" na danyi tunani sai kuma nayi murmushi nace "then tell Takawa the truth, ka gaya masa ummee tace ba zamu dawo ba anan zamu cigaba da rayuwa har illa masha Allah" ya dan yi shiru sai kuma ya fara dariya, yace "that means war" nace "then let them have the war, mu sai mu zama 'yan kallo" ya manna min kiss yace "that's why I love you more every day".
Washe gari muka je scanning. Dani da Sultan da Ummee. Private clinic ne na Ahmad kanin zayed, kusan sa'an sultan ne dan haka muna zuwa suka kama hira, yana da fara'ar sosai da wasa kamar zayed. Tare muka shiga dakin scanning din gaba daya, ya fara min tambayoyi ina amsawa yana tsokana ta, ummee tayi masa bayanin cewa nima doctor ce, yace "shi kenan ma kinga abin yazo da sauki, duk bayanan da zan miki kin sani, sai dai kawai mu duba muga lafiyar babyn shikenan" nace "doctor we don't want to know the sex of the baby" da sauri sultan yace "when did we decide on that?" na harare shi, ummee tayi dariya, nace "kullum yana cewa mace ce ni kuma ina cewa namiji ne, so I tot mu barshi kawai in an haihu magani" sultan yace "no, ban yarda ba, dan kinsan ke zaki yi loosing shi yasa kika ce haka" Ahmad yace "ai ya danganta da kwanciyar babyn, idan babyn ya kwanta yadda zamuga sex din shi kenan in kuma ba haka ba sai mu bari daga baya mu sake dubawa" ni dai na bata rai, dan nasan in aka ga macece sultan in ya saka ni a gaba da tsokana har sai nayi kuka. Ummee taga na bata rai tace "abinda za'a yi, in kaga sex din kar ka fada musu, ni zaka fada wa, ni zanyi deciding me za'ayi dashi" sultan ya fara kunkunin ummee tafi sona a kansa. Doctor Ahmad har da juya screen din dan kar in gani, sam bai daga min riga ta ba, ta cikin rigar ya saka handle din ya kama jujjuya shi akan cikin yana yiwa ummee da sultan bayanin komai, sultan sai washe baki yake yi. Sun fi minti talatin suna kallo, sultan wai bai gaji da gani ba, sai da doctor yace "kai da za'a haifa maka a baka a hannunka ba sai kayi ta kalla ba?" Ya rubuta result ya bamu, ya rubuta wani ya bawa ummee. Alhamdulillah komai normal yake tafiya. Daga nan muka koma gida. Washegari doctor Ahmad ya kira sultan wai yana son muje gidan sa mu wuni a can, yana son ya hada ni da matar sa. Matarsa mai kirki sosai, Firdausi, zamuyi kusan sa'anni ni da ita, sai dai ita har tayi 'ya'ya biyu, Amra da Afra, su sultan suka fita suka barmu tare, tare muka hada lunch tana ta yaba methods of cooking dina, bata san cewa da zero nake ba daga baya na koya, muna gama shirya table su sultan suka dawo muka yi lunch tare, nace da doctor Ahmad, "da fatan dai baka gaya masa ba" yace "ai nayi wa ummee alkawari, duk wanda yake so ya sani sai dai ya tambaye ta" nan muka zauna hira akan banbancin al'adun mu da nasu, da yadda zamani yake chanza both al'adun mu da nasu. Ummee ce ta kira ni a waya tace mu dawo gida haka nan, na duba agogo naga 4:30, nayi mamaki cewa da tayi mu dawo da wuri bayan hira tana dadi, Ahmad yace bara su biyo mu kawai dama sun jima basu je gidan ummee sun gaishe ta ba. Muna yin packing na lura da motoci da yawa a gidan, ni dai ina mamaki na kalli sultan ya daga min kafada alamar shima bai sani ba, a palon farko muka ga al rataye balloons pink and blue, a kofar shiga palo na biyu an yi decoration an rubuta 'Welcome to the Gender Reveal Party' mamaki ne ya kamamu, dama Ummee party ta shirya mana? Muna shiga kuwa aka dau tafi da sowa, da 'yan'uwan sultan nan kusan duk wanda yake gari yazo, na kalli Ahmad naga yana mana dariya, wato dashi aka hada baki shi yasa ya gayyace mu gidan sa. Ni dai ba zan iya cewa ga abinda ya faru ba, they are all talking at the same time kuma mostly larabci suke yi, ni dai naga an jamu ni da sultan gefe, aka hada hannayen mu aka daure da pink and blue ribbons, sai kuma naga an turo wani table da katon cake akai, fari tas cake din kamar snow, aka kawo gabanmu aka ajiye, aka kawo mana 'yar karamar wuka fara aka saka mana a hannayen da aka daure, ina kallon zahra tana recording da wayarta, suka fara chanting 'cut the cake, cut the cake' sultan ya kalleni yace "are you ready?" Na juya na kalli ummee, ta gyada min kai, na kalli sultan nace "yes" nan aka dauki tafi da sowa, suna chanting "pink means girl, blue means boy" wato in muka yanka cikin cake din muka ga pink to girl ce, in kuma muka ga blue to boy ne, na kalli sultan naga sai zuba murmushi yake, dadi ya ishe shi, gani ga ummeensa ga 'yan uwansa duka kuma muna sonsa, ga kuma cikin jikina, dan haka bai damu ba ko mace ce ko namiji ba, nima sai naji ban damu ba, fatana Allah ya bani mai albarka. Muka dauki wukar a tare muka yanka cake din, tun kafin mu karasa yanka wa na ga blue, muna gama yankawa kuma aka dauki ihun "it is a boy" ni dai dariya kawai nake yi, na kalli sultan naga shima dariyar yake yi, ya kalle ni yace "Congratulations My Love, you won" yayi kissing dina a cheeks sannan yayi min a goshi, sai kuma ya rungume ni a jikinsa ya rada min "I Love You" a cikin kunne na, nima nace masa "I love you more".
Nigeria
Ibrahim;
Satinsa biyu a Ibadan ya dawo abuja, a zaman da yayi a ibadan ya kuma kulla dangantakarsa da ubangiji kuma ya kara kulla wa da mama da sauran 'yan uwansa, dan takanas ya fita yawon zumunci, kusan duk 'yan uwansa da suke ibadan, barim mama da baba da kuma babansa mahaifi babu gurin wadanda baije ba, kuma duk inda yaje sai ya kai musu goma ta arziki. Yana dawowa Abuja kuwa ya karawa employees dinsa albashi, wadanda ya kora ya kira su suka dawo bakin aikin su. Shi kansa yaji chanji a jikinsa, dan yanzu fresh yake jin kansa, zuciyarsa da take a kuntace a da yanzu tas yake jinta. Ya nemi masu aikin construction suka zo sukayi masa renovating gidansa aka kara dakuna, aka fitar wa da mama part dinta, da nashi part din shi da Amina, daga baya kuma akayi dan karamin BQ saboda kannensa maza. Har furnitures sai da ya zuba da komai sannan ya koma ibadan, nan fa mama ta saka rigima ita ba zata koma gidan sa ba, sai da ya hada da gaya wa 'yan'uwanta da yasan tana jin maganar su sannan ta yarda ta biyo shi, ita da maimunatu da kannen Ibrahim maza su biyo, matan dama duk sunyi aure suna gidajen mazajen su, mazan kuma an gama secondary school amma babu halin shiga jami'a, 'yar collage din ma ta gagare su. Ai kuwa suna ganin gidan da zasu zauna yanzu sai murna, wahala ta kare dadi yazo kuma, suna zuwa ya nema musu admission a university of Abuja, Allah ya so lokacin sabon dauka ne kuma yana da hanya tunda yana da kudi, dan haka basu samu matsala ba suka samu, maimunatu kuma ya nema mata makaranta me kyau sosai ya saka ta, yayi hiring 'yan aiki saboda kula da gida, baya son mama ta ringa aiki da kanta, amma duk da haka tace a bar mata girki zata ke yi musu da kanta tunda bata saba da zaman banza ba. Ya saka mata DSTV a dakinta saboda in babu kowa ta ringa debe mata kewa. Maimunatu kuwa a part dinsa ya ware mata daki, ya cika mata shi da dukiya duk abinda yasan little girl zata bukata sai da ya saka mata, amma ita duk wannan bai dame ta ba, ita babban burinta shine ta ganshi tare da ita, dan sam kin zama tayi a dakinta sai nashi dakin ta dawo, tare suke kwana ta makalkale shi kamar zai gudu, har ransa yake jin tausayinta, bata san mahaifiyarta ba shi kuma mahaifin nata yayi watsi da ita yana chasing dead dreams dinsa, rannan yana shiryata zai kaita makaranta tace "Daddy please don't take us back to ibadan" ya durkusa a gabanta yana shafa gefen fuskarta yace "I promise you I won't". Dadin gidan yake ji sosai yanzu, amma da har baya so ya dawo gida saboda zaman kadaicin da yake ciki, yanzu kuwa kullum cikin nishadi yake da dariya, bashi da wani sauran problem sai Amina. Sam Amina taki kulashi, tun ranar nan har yau taki daukan wayarsa, yaje gidan yafi sau a kirga amma taku fitowa, direct take cewa a gaya masa ba zata zo ba, yayi messages din ban hakurin har kalamansa sun kare, kullum yana ganinta online a WhatsApp amma maganar duniyar nan in yayi mata ba zata bashi amsa ba, kuma tana karantawa yana gani. Gashi kuma wani irin sabon sonta ne yake kara shigar sa, ita kuma kamar da gayya kullum sai ta chanza DP dinta, sai yayi saving yayi ta kallo, sam yanzu ya daina kanin fuskar moon a fuskarta, har mamaki yake yi ya akayi da yake ganin suna kama, they are totally different, kowacce is special in her own way. Daga baya ya yanke shawarar zai biyo mata ta sama, dan haka yaje gidan ya binciki ranar da zai samu Daddy, ranar kuwa yaje ya aika akayi masa sallama dashi, Daddy ya gane shi dan haka yayi masa iso har palon bakinsa yana tambayarsa ya saukin jiki, Ibrahim kan har ya manta ma da yayi wata jinya, shi yanzu jinyar zuciyarsa ce a gabansa. Nan ya yiwa Daddy bayanin abinda yake tafe dashi, Daddy yayi murna sosai amma kuma sai ya tambashi ko Aminan ce tace masa yazo? Nan fa Ibrahim ya fara shafa kai, daddy yace kar ya damu zai yi magana da Aminar yaji menene amsarta, duk abinda ake ciki zai saka walid ya kira shi a waya ya gaya masa. Ibrahim ya riga yasan amsar da Amina zata bayar dan haka sanda walid ya kira shi ya gaya masa abinda tace bai yi mamaki ba, amma Daddy yace a gaya masa ya cigaba da nemanta, inta chanza ra'ayi shikenan, in bata chanza ba kuma sai dai yayi hakuri dan ba za'a yi mata dole ba. Nan Ibrahim ya kara kaimi gurin rarrashi da ba da hakuri amma shiru kamar an shuka dusa, kuma har a zuciyarsa bai taba tunanin ya hakura ba saboda yana ji a ransa cewa itace matarsa. Ranar wata Friday kawai yana zaune a office sai yaga message, har sai da ya mitstsika idonsa dan yana ganin kamar yaudarar sa idon yake yi, Amina, ya bude ya fara karantawa "if you can, come over tomorrow, someone wants to meet you" da sauri yayi reply, "of cause I can, And I really hope that someone is you". Saturday yana yin sallar la'asar ya cewa mama zai dan fita ya dawo, sai gidan su Amina, suka gaisa da baba habu dan yanzu sun fara sabawa dashi, ya shiga yayi packing ya kira ta a waya, bata dauka ba har ta katse, sai kuma gata ta fito, ta kira wani yaron gidan tayi masa magana sannan ta koma ciki, yaron yazo yayi masa iso zuwa palon su yaya Walid, ya shiga ya zauna yana karewa haduwar gurin kallo, sam yanzu dukiyar gidan bata tsorata shi saboda yasan karamcin jama'ar gidan. Yaji motsi a bakin kofa, yayi sauti ya juya, Amina ce a tsaye da dogon hijab a jikinta tayi sallama ta karaso ciki, murna kamar ta kashe Ibrahim, gani yake kamar bai taba ganin macen da hijab yayi wa kyau irin amina ba. Ya mike yana amsa sallamar ta, sai kuma yaji wata sallamar daban, ya kalli bakin kofar, nan take annurin fuskarsa ya kau, ko a mafarki baya fatan ganin wannan fuskar, me take yi anan, ta karaso palon kamar wadda kwai ya fashewa a ciki, ya kalli Amina da sauri yace "what is she doing here?" Amina ta yamutsa fuska tace "dama ita ce mai son ganin naka bani ba" Amira ta karaso ta durkusa a gaban Ibrahim, da sauri ya matsa yace "tashi daga kusa dani kar kisa inyi amai" Amina taji wani takaici ya kama ta, ta rike kugu zata zazzaga masa masifa kuma sai ta dakata tana so taga yadda zasu kare kafin ta yanke hukunci, Amira ta fara magana muryarta na rawa "Ibrahim dan Allah ka yafe min. Nasan na munanawa rayuwarka, wallahi sharrin shaidan ne da son zuciya suka kaini ga aikata haka, dan Allah ka yafemin, ni yanzu yafiyar ka ita kadai nake bukata, ka yafemin ko na samu Allah ya yafemin ko rayuwata zata yi kyau" ya kalle ta ya dauke kai, sai kuma ya kalli Amina, ba dan abinda Amirar tayi ba da bai hadu da Amina har yayi mata wannan son da yake yi mata yanzu ba, ya tuna da little Maimunatun sa, ba dan abinda Amira tayi ba da ba'a haife ta ba, ya kuma tunawa da cikin dake jikin Moon, dan Sultan, shima badan Amira ta raba shi da Moon ba da ba za'a haifeshi ba. Babu wanda ya isa ya raya ko ya kashe sai Allah, kamar yadda babu wanda ya isa ya wuce kaddarar sa. Ya kalli Amira yaga yadda take kuka daga dukkan alamu va karamar nadama tayi ba, ya dauke kansa yace "na yafe miki, Allah ya yafe mana baki daya" ba Amira kadai ba, hatta Amina sai da tayi mamakin saurin yafiyar da yayi wa Amira, ya kuma kallon Amirar da take durkushe har yanzu a gabansa yace "tashi ki tafi, na yafe miki nace" da sauri ta mike tana kallon Amina sai kuma ta fita, ya dawo da kansa kallon Amina yace "I now have the most precious jewel in the world, why will I be unhappy?" Murmushi taji ya subuce mata, sai kuma ta sake bata rai, ya karaso kusa da ita yace "ko nima sai na durkusa a kasan ne?" Ta juya kamar zata fita sai ta tsaya ta juyo tace masa "ka dawo ku sake magana da Daddy, wannan karon da izini na". Dadi kamar ya kashe Ibrahim, sai kuma wani tsoron Allah ya kama shi. Haka fa Allah yake kallon mu idan munyi masa laifi mun roke shi gafara, sai ta duba yaga cewa mu din masu gafara ne ga 'yan'uwan mu? Kafin ya yafe masa ko akasin haka. Wannan ma wani darasin ne.
Episode Ninety Two and Three : Maldives 1 and 2
Riyadh;
Three weeks after the gender reveal party. Sosai Takawa ya putting pressure a kan sultan, sultan ya kara saka ni nayi wa Ummee magana amma wannan karon ko kallon kirki ban samu daga gareta ba. Sai ma ce min tayi in gaya wa wanda ya turo ni yazo ya same ta da kansa. Sam yanzu sultan bashi da cikakkiyar nutsuwa, yana son komawa gurin babansa kuma baya son ya bata wa ummeen sa rai. Ina yin iyakacin kokarina gurin kwantar masa da hankali amma nasan sultan is a busy person, zaman banza da rashin aikin yi shi yake irritating dinsa, duk da ya samu Ahmad sun kulla abokantaka, kullum zai zo ya dauke shi su fita amma hakan is not enough for sultan. Yanzu har ya kai matakin in Takawa ya kira sultan sai yaki dauka, he is out of excuses. Rannan ina shiryawa zan shiga gurin Ummee sultan kuma yana kwance akan kujera ya rufe idonsa, nasan ba bacci yake ji ba, sai da na gama shiryawa sannan na durkusa a kusa dashi na hura masa iska a fuskarsa, ya dan bude ido yana kallona, nace "zan shiga gurin Ummee" ya mayar da idonsa ya rufe yace "zan shigo an jima" na tashi na tafi jikina babu dadi, bana son ganin sultan cikin damuwa sam, sai inji duk nima na shiga damuwar. I must do something about this. Ban sha wahalar hada sultan da ummeensa dan in cigaba da ganinsa cikin damuwa ba, amma kuma menene abinyi? A harkar da ta shafi iyaye dole mutum yayi taka tsan tsan. A bedroom na sami Ummee tana zaune a kan gado da system a gabanta, na shiga da sallama, ta amsa min idonta akan screen din system din, sannan tayi min alama da hannunta na inzo in zauna kusa da ita, ina zama ta juyo min da screen din system din, fuskarta dauke da murmushi tace "what do you think of this?" Na kalli abin da take nuna min, model ne na dakin baby, with complete furniture, crib, drawers, night stand da komai, dakin yayi kyau sosai, amma kuma sultan ya gama tsara mana baby room din mu tun sanda yake zana plan din gidan mu a Abuja. Na kasa bawa Ummee answer, ta cigaba da magana "ina tunanin bedroom din tsakiya ba part dinku za'a mayar baby's room, sultan sai yayi mana dan renovating dinsa kadan, yayi closet a ciki, sai mu fara order kayan baby kuma, furnitures first, sai electronics sannan sai mu dawo kan clothings" tayi ajjiyar zuciya, "we have alot to do, list ya kamata mu rubuta..." Sallamar sultan ce ta katse mata maganar ta, muka amsa masa a tare, yana kallon mu yace "yau hirar ta daki ce kenan" ta dan bubbuga kan gadon kusa da ita tace "come Abubakar, sit with us" ya karaso ya zauna yana satar kallona, tace "we were just talking about the baby, baby room muke so mu fara shiryawa, muna bukatar taimakon ka gurin renovating dakin babyn" ya dan dafe kansa kamar mai ciwon kai yace "Ummee babyn nan fa yana da atleast wata uku kafin yazo, besides already yana da room dinsa a Nigeria" take naga murmushin fuskarta ya kau, tace "Nigeria? I tot I made myself clear cewa babu zancan komawa Nigeria ko?" Sultan ya bata rai, he has reached his limit. Ya saka hannu ya dauko wayar sa yana dialing, kawai sai gani nayi ya ajiye ta akan table din gaban gadon, tana kara sai kuma mugaji an dauka, muryar Takawa, yace cikin fada "Sultan wato ina ta kiranka shine kaki dauka ko? Wannan wanne irin aikin vanza kake aikatawa haka? Kawai ka dauki iyalinka ka tafi dasu can wata uwa duniya ku zauna a can? Zaman me kuke yi har yanzu? Aikin da ka bari wa zai yi maka?" Sultan yayi gyaran murya yace "barka da yamma" Takawa yace "bazan amsa ba, me ya hanaka dawowa har yanzu?" Sultan yana kallon Ummee yace "bani na hana kaina tahowa ba, Ummee ce tace bazan dawo Nigeria ba a Riyadh zan cigaba da zama, na saka ka a speaker phone yanzu tana jin abinda kake cewa, sai kuyi magana a tsakanin ku" na kalli fuskar Ummee naga wani missed emotions, sama sama take numfashi, ta kasa magana, sultan ma ita yake kallo ita kuma wayar take kallo. An jima a haka sannan Takawa yace "Khairat, kin san dai bai kamata kice zaki hana yaron nan dawowa gidan su ba ko?" Ta hadiye yawu ta kara bata fuska tace "why not? Nan ma ai gidan su ne, kamar yadda yake da iko da gidanka haka yake da iko da nawa. Kamar yadda kake da iko dashi haka nima nake da iko dashi, in fact na ma fika iko dashi, nace ba zai dawo ba and that is final" yace "you can't do that. Aikin sa kuma fa?" Tace "wani zan samar masa anan" yace "'yan uwansa kuma fa da suke ta nemansa anan me kike so in ce musu? Mutanen gari fa da suka dogara dashi me kike so in ce musu? He is a Prince for God's sake khairat, he has a role here, ko anan ma zaki samar masa matsayin Prince din ne?" Tace "bazan mayar dashi Prince anan ba amma zan bashi rayiwa fiye da wacce zaka bashi a matsayin Prince din, zancan me zaka gayawa mutane kuma oho, that's your problem not mine, abinda na sani shine dana yazo gurina kuma babu abinda zai kuma rabani dashi sai mutuwa" ya kwantar da murya Yace "khairat wannan maganar tsakani na dake ce, ki bar sultan ya taho tare da iyalinsa, kin san dai halin da moon take ciki, she needs her family besides her, in yazo sai mu taho tare dani dashi mu zauna muyi maganar sosai" ta danyi dariya tace "am not a kid ballantana kayi min wayo, Maimunatu will remain here ita da abinda yake cikinta, idan family dinta suna son ganinta da kansu zasu taho nan su ganta, ai dama aure babu inda baya kai mutum, aure ne ya kawo ta Riyadh, kuma babu wata care da zaku bata a can wadda bazan bata a nan ba" yace "amma dai kinsan nima ina da right akan su ko? Yanzu abinda za'ayi tunda sunyi wata biyu a gurinki, ki turo su suyi wata biyi ana sannan sai su take dawowa, kinga shikenan kowa will spend sometimes with him babu wanda zaice an cuce shi" tace "wata biyu? Cuta? You must be joking, sai da yayi shekara talatin ban ganshi a idona ba, how can you tell me wata biyu? In so kake a raba sai ka bari in yayi shekara talatin anan sannan ya koma gurinka" da sauri yace "shekara talatin? Do you think zan kara shekara talatin a duniya? Me yasa kike nema ki zamo mai son kanki ne?" Tace "son kai? Ai sai dai inyi maka wannan tambayar, tunda har ka iya bugo waya kace masa ya koma gurinka, saying you will let him come back again, bayan you don't keep your words, you will keep me waiting and waiting till eternity" ya danyi shiru da alama maganar ta shige shi sannan yace yace "am sure sultan ya gaya miki duk abinda ya faru bayan rabuwar mu, so am sure kinsan ba wai a sona na barki zaman jira tsahon shekaru ba" tace "that's your problem" yace "yes, it is my problem amma let me ask you something, ke menene ya hanaki zuwa kiga dan naki har tsahon shekaru talatin, ki kina son kice daure miki kafa akayi duk tsahon shekarun nan, baki damu dashi ba tunda har baki neme shi ba" nan da nan hawaye ya taru a idon Ummee, ni dai ina zaune sai in kalli ummee in kalli wayar, sultan ya mike tsaye yace "wait, all of you, ya ishe ku haka. All of you are forgetting something, am not your little love anymore. Am not a toy da zaku ke playing around with har kuna lissafin zaku ke passing dina around for one one month or one one week. Wannan duk maganar da kuke is between the two of your, dani da iyalina ba zamu kasance in the middle of it ba, ba zamu zama ball ba balle wannan ya buga ya bawa wannan ya buga. We will go away. Duk ranar da kuka yi settling kanku just give us a call sai mu dawo, amma ku tabbatar a cikin settlement din babu zancan muje gurin wannan sannan mu sake komawa gurin wannan, we are not toys, we are our own people" ya mika min hannu na kama ya daga ni tsaye, babu wanda yayi magana a cikin su sai Ummee data fara ruwan hawaye, yace "daddy wannan waya tace kuke fada a cikin ta, kana iya kiran wayarta sai ku cigaba a fadan acan" Takawa yace "sultan listen to me, kar ka dauki yarinyar mutane da ciki kana yawo da ita gari gari, zanzo Riyadh din, we will talk thi gs out" sultan yace "in kun gama talking things out din just give us a call" ya kashe wayar yana kallon Ummee, ita din ma shi take kallo, ba tare daya ce mata komai ba ya ja hannuna da sauri muka fita. Muna shiga part din mu ya zarce bedroom ya fara fito da kayan mu yana zubawa a kan gado, sannan ya jawo akwatina yana jerawa a ciki, hada wa kawai yake yi da nawa da nasa baya ware wa. Ni dai kawai ina tsaye ina kallon sa, nace "are we really going?" Yace "yes, and don't try to talk me out of it" nace "i won't. Amma ina zamuje?" Bai kalle ni ba yace "am not stupid, so kike in gaya miki ki gaya mata ko? But know one thing, ba America zamu je ba saboda can ne inda Takawa zai fara neman mu. In sun gama fadan zamu dawo. Zamu bar wayoyin mu a bude yadda zamuke magana dasu" nace "idan haihuwa ta kama ni a can kuma fa, mu kadai ya zamuyi?" Yace "a haka suka haife ni su kadai. And believe me, ba zasu kai har lokacin haihuwarki basu shirya ba, duk kansu kowa yana so ya zauna a waiting room ranar da zaki haihu" nayi murmushi dan nasan irin lissafin da Ummee take yi kullum, wani lokaci har tunani nake yi anya kuwa zata ke bani babyn ina dauka?.
Tare muka zauna muka shirya kayan mu. Basics kawai muka dauka yace ma sayi kayan sawa sosai a can, dan haka kananan jakankuna kawai muka dauka guda biyu, lokacin an kusa sallar magrib, muna fitowa daga part dinmu na nuna masa part din Ummee ya makale kafada "I don't want to see her crying" na tafi ni kadai, na tura kofar na shiga, tana zaune akan kujerar data zauna ranar da na fara zuwa gidan, idonta akan kofa, ta saka hannayenta a tsakanin cinyoyinta. Na tsaya a bakin kofa ina jin tausayinta har raina, Takawa zai iya tafiya neman sultan amma ita she is tied to saudiyya, dan haka dole sai dai azo gurinta ita ba zata iya zuwa wani gurin ba. Ta mike tsaye tana jujjuya hannunta tace "bai gaya miki ina zaku je ba ko?" Nace "yes" tace "yana ina?" Na nuna mata waje, na karasa kusa da ita na rike hannunta nace "I will call you daga duk inda muka je" tace "magrib tayi yanzu, kice masa ya bari sai da safe sai ku tafi" nayi shiru dan nasan ba zai yarda ba, sultan is soo headstrong in ya saka kansa abu babu mai hana shi, ta dora hannun ta akan cikina taji yadda dan cikin yake motsi sai ta danyi murmushi tace "be safe, ki kula dashi kamar yadda kika saba" nace "insha Allah" na juya na fita ina goge hawayen fuskata. Ina fita na tarar sultan har ya dauko daya daga cikin motocin gidan ya shiga yana jirana, na shiga ina cigaba da kuka na, yace "cry cry baby, dake da ita bansan wanda yafi wani ruwan hawaye ba" sai kuma naga ya juya yana kallon kofar shiga gidan, nima na kalli gurin, Ummee ce a tsaye, tayi folding hannayenta a kirjinta, mayafinta ya sauko kan kafadarta, iskar da ake yi a gurin tana ta yawo da gashinta, she looks so lonely and depressed. Sultan yayi sauri ya dauke kansa ya ja motar da gudu muka bar gurin, ni kuma har muka fita gate idona yana kanta.
Muna fita naga ya dauko wayarsa yana kiran Ahmad, tambayarsa yake hotel me kyau inda zamu iya kwana, Ahmad yana tambayarsa lafiya amma bai gaya masa komai ba, daga karshe dai gidan Ahmad din muka fara tafiya muka dauko shi sannan ya rakamu hotel din, yana ta mitar me yasa to ba zamu kwana a gidan saba amma sultan yaki yarda, kuma sai da ya saka shi yayi masa alkawarin ba zai ce da kowa komai ba, ya gaya masa zamu dawo wata rana amma ba yanzu ba. Wani lafiyayyen hotel ya kaimu, sultan ya biya kudin kwana daya, ya tambayesu in da akwai motar da take zuwa airport da safe suka ce masa eh, kawai sai ya bawa Ahmad key din motar da muka taho da ita yace ya ajiye motar a gurinsa, Ahmad ya tambaye ni ina zamu je na ce masa nima ban sani ba. Dan karamin daki ne single room mai hade da toilet, amma kuma ya hadu sosai. Sultan yayi mana order abinci sannan ya dawo ya zauna a kusa dani yace "Moon, do you think what am doing is right?" Bance masa komai ba saboda bansan abinda zance masa ba, yace "I don't know what to do shi yasa nayi haka, ina son komawa Nigeria dan acan rayuwata take ba nan ba, amma kuma bana son inyi hurting Ummee, ba zata iya bina ba saboda shi is tied to saudiyya, I don't know what to do, we will just let them figure out me zasuyi sannan sai mu dawo" na ce "ina zamuje?" Ya danyi murmushi yace "do you promise not to tell any one?" Nace "can I at least tell Mommy?" Yace "yes, only Mommy" nace "OK" yace "am taking you to the Maldives. Dama nayi miki alkawari tun tuni amma ban samu na cika miki ba" yana murmushi yace "we are going to have our honeymoon" nayi dariya na nuna masa cikina, yayi kissing cikin yace "he is welcome to join us". Ranar sultan bai kwanta da wuri ba, yana ta making phone calls, ya saya mana ticket, ya kama mana hotel a can Maldives din, sai daya tabbatar komai is settled sannan ya kwanta.
Washegari daga nan Riyadh muka shiga wani dan karamin jirgi zuwa Maldives. Tun a jirgi nasan lallai da gaske sultan honeymoon din yake so, nima na biye masa. Kusan duk wadanda suke cikin jirgin couples ne, tunda shi Maldives guri ne da ake zuwa mostly fir vacations and honeymoons. Maldives kasa ce amma ba kamar sauran kasashe ba, tana consisting thousands of islands a indian ocean, saboda yawan islands din wadansu islands din ma babu mutane a ciki. Capital dinsu shine Malee, wanda shine babban island din da yafi kowanne girma, kuma anan ne mutanen kasar suke zaune, sauran islands din duk an barwa tourist, wadansu islands din ma saboda kankantarsu hotel daya ne kawai a gurin, wadansu ma babu hotel din sai dai ayi 'yar bukka ayi decorating gurin mutane suna zuwa su wuni ko su kwana. A Velana international airport muka sauka, which is an island on it's own, daga nan kuma kowa sai ya fadi inda zaije sai yayi hiring speedboat a kaishi. Malee sultan ya fara cewa zamuje, nan mukayi ta zagaya garin muna kallon haduwarsa, muka shiga mall dinsu mukayi siyayyar kayan da zamu bukata a hotel din da zamu sauka. Ni kam maternity gowns nayi ta siya, sexy maternity gowns, sultan kam kananan kaya yayi ta diba, ya siya min wadansu nima amma ni nasan cikina ba zai barni ni saka ba, na dai samu wadanda nasan zasu saku na dauka, bama bukatar abinci ko toiletries duk hotel din mu zasuyi providing. Daga na muka tafi port din su muka hau motor speedboat dinsu zuwa Island din Soneva Jani, wanda shine hotel din da sultan ya zabar mana. Tun a cikin boat din sultan ya fara karbar amarcinsa, dan sanda muka zo hotel din ma bamu sani ba sai da me boat din yazo yayi mana knocking yace munzo. Muna sauko wa na saki baki ina kallon gurin, ni in ana cewa hotel abinda yake zuwa kaina shine dogon gini da manyan glass Windows da balconies, sam ba haka gurin yake ba, cabins ne separate from each other, gaba dayansu a cikin ocean suke, sai hanyar da tayi linking from one cabin to another. Daga gefe kuma beach ne, the sand is as white and as soft as snow sai tall trees a zagaye da beach din. Ruwan ocean din is so clear yadda har kana ganin kifaye suna swimming a ciki, ga hasken rana yana reflecting on the ocean, iska mai dadi tana kadawa. This is totally a paradise on earth. Allah kasa muna da rabo a cikin aljannar ka. In za'a samu guri mai kyau irin haka a duniya ya kake tunanin aljanna take?. Sultan ya kama hannuna yace "welcome to me dream. Tun ranar dana ganki na fara sonki, kuma tun sanda na fara sonki nake mafarkin kawo ki gurin nan" nace "ka taba zuwa ne dama?" Ya girgiza kai yace "just pictures nake gani ina saving" nace "it is really good, kamar mafarki, kamar ba gaske ba" A bakin beach din muka tsaya hand in hand muna kallon sunset, it looks so good, gani zakayi kamar sun din lumewa take yi cikin ocean, sai kuma ta bada rainbow color a cikin ocean din. Sai da rana ta gama faduwa sannan muka shiga reception cabin din, muka ciccike wadansu takardu, aka tambaye mu how long zamu zauna sultan yace "indefinitely" gaba daya sai da mukayi dariya a gurin, desk agent din ya kalli cikina yace "so, are you guys on honeymoon?" Sultan yace "yes, the baby decided he want to enjoy the honeymoon as well" muka sake yin dariya. Mutanen gurin are very friendly. Cabin din mu single room ne amma katon gaske, in kana so zaka iya raba dakin biyu da labule, da round bed karamin na dakin sultan a abuja, sai kujeru manya masu kama da gado, da kuma kananan kujeru guda biyu, da duk kab electronics din da aka san mutum zai nema da akwai a dakin. Kowanne cabin da akwai dan karamin swimming pool din da aka jawo masa ruwa direct daga ocean, yadda har kifaye suna iya biyo ruwan su shigo cikin swimming pool din. Setting din dakin looks so romantic yadda bai kamata ma mutum yaje shi kadai ba. Room service yana gama ajiye mana kayan mu, yayi setting komai na dakin sannan ya bamu keys ya juya ya fita, yana fita na juya ina kallon sultan nace "let's stay here, forever" yace "am glad you like it" ya daga ni ni da cikina ya ajiye akan gado, na dan ture shi nace "ba muyi sallar magrib ba fa" yace "dama ai sai munyi wanka za muyi sallar, gwara mu jefi tsuntsu biyu da dutse daya". Ya saka dan yatsansa yana zagaye lips dina da suke dauke da murmushi, sannan a hankali ya dora red lips dinsa akan pink lips dina, ya dan bude bakinsa kadan yadda nawa ya bude tare da nasa, a hankali ya fara hura min iskar bakinsa cikin nawa, na san abinda yake so dan haka na tura masa harshena kadan cikin bakinsa, ya karba kuwa harda ajjiyar zuciya ya fara yi masa shan alawa ni kuma ina taya shi ta hanyar zagaya harshen nawa a kusufa kusufa ta bakinsa, na saka hannayena cikin gashin kansa ina sosa masa, ya kara narkewa a jikina, na karbe harshe na ya biyo ni da nasa, na karba nima ina mayar masa da martani, in zaka tambayemu sunayenmu a lokacin ba lallai ne mu iya tunawa ba, na ji karar fitar zip din riga ta tare da balle hook din bra ta amma bansan sanda suka bar jikina ba sai jin hannunsa nayi on my naked skin, da rawar hannu na fara kokarin balle bottoms din rigarsa amma hakan ya gagara saboda jikina gaba daya ya zama numb, ganin na kasa ya saka ya dakatar da yawon da yake yi da hannunsa a jikina ya kama wuyan rigar tasa ya ja da karfi, a take duk bottoms din suka tarwatse akan gadon, ya zare rigar a jefar da ita. A tare muka yi team work muka balle belt dinsa, daga dogon wandon har gajeran a tare suka fita suma aka jefar dasu, duk abinda muke yi bakunan mu suna hade da juna, gani muke da mun rabu daya zai iya disappearing ya bar daya. Ya koma ya kwanta akan bayansa, ya jawo ni na dawo samansa. Muka cigaba daga inda muka tsaya.
Ana gama round one, Sultan ya fara shirye shiryen komawa filin daga na rike fuskarsa da hannayena duk biyun ina kallon idonsa nace "sultan sallah fa" yayi ajjiyar zuciya ya dora kansa akan kirjina yana sauke numfashi, sai kuma ya dago kai da sauri yana kallon agogo, nima na bishi muka kalla tare 8:30pm, muka kalli juna, sultan yace "akwai shaidan a gurin nan" da sauri ya mike ya tafi ya hada mana ruwan wanka, cewa nayi ya fara yi, dan wankan tare ma wani abin zai kuma jawowa. Dole muka hada magrib da isha mukayi a tare. Na dauko waya ta na saita alarm for all the five daily prayers, dan in kana gurin nan ba sani zakayi ba. Ranar sultan cewa yayi a waje zamu kwana, ya shimfida mana blanket mai laushi a kan floor din waje, ya saka mana pillow duga daya sannan ya sake daukar mana bargon lulluba. A gurin akayi serving din mu dinner, muna gamawa suka zo suka kwashe kayan. Dadin iskar gurin kadai ya isa ya saka mutum bacci ballantana ga gajiyar da muka kwaso, da assuba sanyi ne ya tashe mu duk kuwa da makalkale juna da mukayi muka kudunduna, dole muka koma daki mukayi sallah sannan muka koma bacci, duk da dai ba baccin muka koma ba dan sultan cewa yayi shi a dictionary dinsa babu baccin safe.
Da safe na kira Mommy na gaya mata inda muke nace amma kar ta gayawa kowa, she was concerned, tace "to ke yanzu ga yanayin da kike ciki kuma in wani abin ta faru fa? Ba gwara ke ya kawo ki gida ba shi ya zauna?" A raina nace 'Mommy kenan, me raba mu ni da sultan ai sai dai mutuwa kuma, mutuwar ma in san samu ne ta dauke mu tare' na kwantar mata hankali da nuna mata cewa ai suna da asibiti ne kyau anan din, sannan zanke zuwa lokaci zuwa lokaci ana duba lafiya ta data babyn, kuma nasan me nakeyi dan haka da naji wani chanjin da ban yarda dashi ba zan tafi asibiti. Muna gama waya da Mommy na kira Ummee itama, tana jin muryata ta sauke ajjiyar zuciya, "maimumatu I have been waiting, jiya banyi bacci ba, jow are you" na tabbatar mata cewa lafiya lau muke daga ni har sultan, kuma zamu ke kiranta akai akai muna gaisheta. Na bata sultan suka dan gaisa kadan sannan ya kashe.
Rayuwa mai dadi muke shimfidawa a Maldives, kullum zamu dauki hayar speedboat mu fita yawo, island by island, duk inda mukaje zamu dauki pictures da camera din da sultan ya sayo mana, in kuwa muka dawo cabin din mu to abu daya ne zamuyi tayi, sallah ce kawai da cin abinci suke raba mu da junanmu, har mamakin mu nake yi, sam bama gajiya da junan mu, yanzu za'ayi yanxu kuma za'aji kamar anyi sati ba'ayi ba. Cikina kam tunda na shiga third trimester sai kara uban girma yake yi da nauyi. Sam girman sa amma baya hanani sakewa da sultan, shima kuma hakan banga yana wani takura masa ba, da kamar game muka maida abin, in mun gwada wani abin yaki yi sai mu koma wani, it makes it more fun. Sultan seems a bit gentler dai yanzu, amma dai he is usually rough. Bani da wani complication, dan duk wata doka da ka'ida ina bi, exercise kam wannan inda ace yana yawa da har yawa zai yi min.
Muna yawan yawa gida, and things seems to be happening a Nigeria, abu na farko anyi bikin munir, suddenly abin ya faru, yaje 'yalleman da daddare ya fita aikin nasa, ya samu 'yar mutane a loko yana mammatsewa sai baban ta ya gansu, a take kuwa yaje ya gayawa baffa wanda ya kira uncle Rufa'i yace a daura musu aure, ga kewaye nan a gidan ta tare anan, sannan shima munir din ya baro Lagos tunda dama ba wata uwar yake yi acan ba sai kashe kudin mahaifinsa, ya dawo nan 'yalleman a nema masa ko teaching ne ya fara yi. Haka kuwa akayi, aka daura wa munir aure aka tattaro shi aka dawo dashi 'yalleman aka nemar masa aikin koyarwa. Ana bani labarin ina dariya, ita kanta Aminar da take bani labarin dariya take yi, tace "yanzu in kika ganshi sai kinji tausayinsa, baffa ya saka shi a gaba, dama baffa ga tsufa da rikici, kuma gashi dama babu kowa a gabansa, dan haka tare suke komai da munir. Abu na biyu da ya faru shine neman auren Amina da akaje yi 'yalleman, farko uncle Rufa'i yaki yarda, amma da yaga Daddy ne akan maganar sai yayi shiru, ansha dai rigima da Baffa dan cewa yayi shi bazai bawa bayarabe jikarsa ba, Daddy ne da uncle Ali suka dage, suka saka baffa a gaba da nasihohi ta lallami suna nuna masa irin tarbiyyar yaron, bashi da wani nakasu da addini zai ce kar a bashi aure, kuma suka nuna masa irin wannan intertribal marriages din shine zai kawo solution a rigin gimun kabilanci. Yanzu dai baffa ya yarda, an saka bikin Amina nan da wata biyu. Na lissafa naga kusan lokacin EDD na kenan. Sai shugabannin gwauraye na Abuja, yaya walid da yaya Habeeb, Daddy yace duk ya gaji da ganinsu suna zamar masa a gida, yace kowa a cikinsu ya fito da matar aure a hada dana Amina. Yaya Habeeb kam kamar danshi, dan sabofa yawan 'yammatansa sai da yayi ta ruwan ido kafin ya fitar da guda daya, wata Fadila 'yar Bauchi. A inda aka samu matsala shine gurin yaya walid, shi ko hanyar zuwa zance bai sani ba, ga 'yammatan kuma binsa suke yi kamar zasu kwanta masa, ga kuma kyan ga kudin, dan nesa ba kusa ba yaya Walid yafi yaya Habeeb kyau da iya daukar wanka, sai dai babu budurwa, da Daddy ya gaji da magana da kansa yayi wa Hajja waya yace ta samowa Walid mata a cikin 'yan'uwa, ai kuwa kamar an bawa kura ajjiyar nama, Hajja taji dadi sosai tana ganin Daddy ya huce mata haushin mu ni da Hafsat, kuma sai ta bawa kowa mamaki itama, mamar data zaba masa itace Zainab, 'yar autar uncle Ali. Yarinya ce karama dan wannan shekarar ta gama sec sch. Kyakykyawar bafulatana sosai ga hankali da tarbiyya irin ta uncle Aliyu, babu wasa. Uncle Aliyu bai ce komai ba sai ya tattara ta ya kaiwa hajja ita yace ita zata yi mata shirin auren, anan gurinta za'azo a dauke ta. Yaya walid kam farko cewa yayi bai yarda ba, wai shi tayi masa kankanta, sai da Daddy ya nuna masa bacin ransa sosai sannan ya hakura. Ni kam ina wata duniyar amma babu wanda ya kaini murna, dan dama can ina son yarinyar nan saboda nutsuwarta, sai dai ba tausaya mata an hada ta da shugaban bachelors na Abuja. Sultan kuwa da yaji labarin cewa yayi dai dai kenan, gwara da aka bashi karamar, dan yadda yake da shiru shirun nan in aka samo mai budadden ido aka bashi rakumi da akala zata mayar dashi. Jin labarin su Amina yasa na kira kawata Amira dan inji ya take ciki ita kuma, ta dauka da murnarta tace "maman baby shiru kin buya, wayarki ma bata shiga" nace "wallahi kuwa Amira, abubuwan ne sai a hankali" tace "dama nayi ta nemanki ne in gaya miki nagode da shawarar da kika bani, Ibrahim ya yafe min kuma sosai naji dadin yafiyarsa" nace "to me kike ciki yanzu?" Tace "ina kano yanzu. Bayan mun rabu da Ibrahim kawai sai naga cewa na bata wa mama rai itama da yawa, ta sha wahala sosai a kaina, dan haka na yanke shawarar zan huce mata haushin abinda nayi mata ta hanyar bar mata zabin mijin da zan aura, taji dadi kuma sosai, shine ta dauko ni muka dawo kano ta kawo ni gurin kanin baba, yanzu har ta saka gidan mu na abuja ma a kasuwa zata sayar ta sayi wani anan kano tayi zamanta, tace itama in ta samu miji aure zatayi" Nace "to zancen naki auren fa?" Tayi dariya tace "kinsan yadda tsarin yake ai, idan mace taki fitar da miji tayi aure sai a nemo dan uwanta shima wanda yaki aure sai a hada su. Yanzu dai wani cousin dina ne shima wai yaki yin aure, yana kasar waje karatu, shi akae cewa za'a hada mu, amma sai yazo munga juna tukunna" nayi mata fatan alkhairi muka yi sallama. Mommy tayi min waya tace "to bikin ma ba zaki zo ba sai surukan naki sun shirya?" Nace "ai bikin da saura Mommy, it won't take that long". Na kira Ummee ina son inyi tsegumi inji ya suke ciki, har muka gama hirar mu bata cemin komai ba, sai zancen kayan babies din da take yin order take min, har zamuyi sallama nace " Ummee is there any chance na zamu dawo gida nan kusa?" Ta yi shiru sannan tace "wato ku kuna son kuji status din mu amma mu ba zaku gaya mana naku ba ko? Tunda ba zaku gaya mana a ina kuke ba shikenan kowa ya rike labarinsa" but from her voice naji kamar things are going the right way. A bangaren sultan kuwa tunda muka zo Maldives ya kira Amir wanda shima duk shirye shiryen bikinsa sun sako shi a gaba, ga babban abokin ya gudu ya barshi, yace yake turo masa aiki yana yi daga nan, dama kuma aiyukan sun taro sosai, dan haka ya turo wa sultan da yawa. Haka sultan yake zama in his spare times yayi ta zane, ni kuma a lokacin nake samu inyi bacci, wani zanen in naga sultan yayi har mamaki nake yi, gaskiya zane baiwa ne ba kowa Allah ya bawa ba, dan in sultan yana zana gida ko mistake din measurement baya yi, wannan ya saka kullum contracts ne suke shigo masa ba sassautawa. Sultan is spending and making money at the same time.
Watan mu biyu a Maldives, ya zamanto cikina yana da wata takwas kenan. Ranar nan na kwanta ina ta bacci akan kujera, sultan kuma yana ta aikin zane a system dinsa, na farka naga 12:09 na dare, na shiga toilet nayo shirin kwanciya sai kuma naji ina son mijina, nace "wai wannan aikin ba zai kare bane ba?" Ya danyi tsaki yace "nima na gaji fa, the thing is complicated kuma wai gobe suke bukata zasu fara gini, dole yau zan kammala in tura musu. Nace "why not ka tura musu gobe su fara aiki jibi? Menene banbancin gobe da jibi?" Yace "I just want to finish it today, shikenan na huta, gobe sai fara wani" nace "OK" amma a raina nace "kayi aikin mu gani" na cire kayana na saka wata rigar baccina iya rabin cinya, babu komai a ciki, na zagayo ta gabansa na zauna a kujerar da take facing dinsa, ya dan dago kansa ya kalleni, ya danyi murmushi kadan ya cigaba da aikinsa, na dauko alawar tsinke na fara sha ina kallonsa, yana ta satar kallona ta saman system din gabansa, can yace "damn it, how do you want me to concentrate and finish this work on time while you are sitting there and looking like this?" Na cigaba da shan alawa ta nace "I don't want you to concentrate on that work, I have another work for you here" ya dan maida hankalinsa kan system din gabansa, na dauki kafa daya na dora akan daya, na jingina baya na da jikin kunerar, kallo daya yayi min sai yayi slamming system din ya rufe ta yace "fuck the work then, I will finish it tomorrow" ina dariya har ya karaso inda nake, nace "yanzu kayi magana" ya biyo ni kan kujerar yace "your wish is my command, master". Da safe muna baya wajan swimming pool, ina zaune na saka kafafuwana cikin ruwan shi kuma yana ta swimming dinsa sai wayar sa tayi kara, na dauka sai naga number din Zayed, ya karaso da sauri ya goge hannun sa ya karba ya saka a kunne, sum danyi magana sai naga ya kalle ni da sauri fuskarsa da damuwa, sai kuma ya kirkiri murmushi, amma nasan murmushin karya ne, da sauri ya karasa fitowa daga cikin ruwan ya shiga daki, bai damu da ruwan da yake diga daga jikinsa ba, daga gani bayaso inji abinda suke cewa ne, gaba na ne yayi muguwar faduwa har saida dan cikina ya motsa. Da sauri na tashi na bishi a baya. Ina shiga dakin yana kashe wayar, ya tsaya yana kallona, nima kallon nasa nake yi. Ya ajiye wayar yace "we are going to Nigeria" jiri naji ya debe ni, da sauri yazo ya rike ni ya kwantar a jikinsa, na bude bakina da kyar nace "waye ya mutu?" Ya dauke kansa daga kaina yace "kawai dan nace zamuje Nigeria sai kice wani ne ya mutu?" Na rike rigarsa nace "Hafsat ce ko? Zayed ne ya kiraka, Hafsat ce ta mutu ko?" Yace "in Hafsat ce ta mutu ta yaya zayed zai kira ni?" Sai na fashe da kuka nace "wayyo Mommy, wayyo Daddy, Na shiga uku" da sauri ya rike fuskata yace "ba Mommy da Daddy bane ba" nima na rike tasa fuskar nace "Faruk? Allah sarki faruk jiya mukayi waya dashi" ya dan bata rai yace "Moon, get yourself together, saboda an san abinda zakiyi kenan akace kar a gaya miki, you know your condition, gashi kina da high bp, kukan da zaki yi ba zai dawo da wanda ya mutu ba, sai dai kisa kanki dani da babyn mu cikin matsala. Ba Faruk bane ya mutu, ba Hafsat ba ba Mommy ba ba Daddy ba" a hankali nace "waye" ya jawo ni jikinsa ya rungume, na tsaya da kukana ina sauraron inji waye ya mutu.
Episode Ninety Four : RIP
Ya rike fuskata a hannunsa yana kallon cikin idona yace "kinsan dai da rayuwa da mutuwa duk na Allah ne ko? Kinsan babu wanda ya isa ya raya wani idan har Allah ya rubuta cewa kwanansa ya kare ko? Kuma kinsan babu wanda ya isa ya kashe wani in har kwanansa bai kare ba ko? Iyaye, 'yan uwa, miji ko mata, 'ya'ya dukka Allah ne yake bamu su kuma shi yake karbar su a lokacin da yaga ya dace. Duk lokacin da muka rasa wani abinda ya kamata muyi shine mu gode wa Allah daya bamu su tun farko, har muka rayu dasu muka ji dadinsu suma suka ji namu, dan daga mu harsu na Allah ne. Idan mutum ya riga ya mutu babban abinda yake bukata daga gare mu shine addu'ah, mu nema masa rahamar ubangiji tare damu baki daya, mu kuma yi fatan Allah ya sada mu dashi a aljannah inda zamuyi rayuwa ta har abada ba tare da tsofa ko mutuwa ba. Maimunatu Allah yayi wa Baffa rasuwa jiya da daddare, yau da safe akayi jana'izarsa aka kaishi gidansa na gaskiya." Wani sabon kuka ne ya taso min, yayi sauri ya hade bakinsa da nawa, sai da yaji na tsayar da kukan sannan ya sake ni, na ture shi da sauri na fara kokarin mike wa, ina jin kaina yana juyawa, wayyo Allah baffana, wai baffa ya tafi ya barmu shikenan ba zamu sake ganin sa ba? Na runtse idona ina hango kyakykyawar fuskarsa ta fulani mai cike da kwarjini da fara'a, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, sultan naji ya sake rike ni yana kokarin zaunar dani "Moon zaki fadi fa, menene hakan wai? Shi yasa tunda aka kaishi asibiti aka ce kar a gaya miki saboda an san halinki" na juyo da sauri ina kallonsa bibbiyu, nace "asibiti? Au dama bashi da lafiya amma baka gaya min ba? Daya mutum ma har sai da aka binne shi sannan za'a gaya min" ya sake kokarin rike ni na ture shi, yace "to inda an gaya mikin ma menene zaki yi masa? Za ki cire masa ciwon ne ko kuma zaki hana shi mutuwa?" Da karfi nace "I could have been there for him, I could have hold his hands and say goodbye to him" yace "and what difference will that make?" Nace cikin fada "It would have make me feel better". Na rufe fuskata da hannayena na fara kuka a hankali mai shiga zuciya. Duniya kenan, ina nan ina enjoying rayuwata ashe Baffa yana can yana sallama da duniyar gabaki daya. Sultan ya zo ya durkusa a gaba na, har yanzu swimsuit din jikinsa a jike take yace " ya salam, moon da kinsan yadda nake jin kukanki a raina da kin daina, da ina da dama da ba zaki taba kuka a rayuwar ki ba, amma ba zan iya dawo miki da baffa ba, dan Allah ki tausaya min ki daina kukan nan haka" ni haushi ma naji yana bani, daga shi har sauran 'yan gidan mu duk haushi suke bani, tunda duk muna waya dasu kuma duk sun san baffa yana asibiti amma babu wanda ya gaya min. Ya dora hannunsa akan cinya ta na ture hannun na juya baya na na cigaba da kuka na. Ina jin shi ya mike ya shiga toilet, naji alamar shower sai kuma ya fito ya shirya, har lokacin ina zaune ina kuka na, yazo ya zauna kusa dani, na matsa. Yace "am sorry Love, nasan bashi da lafiya amma kinka yanayin da kike ciki, ga problem din bp dinki, wannan yasa aka ce kar wanda ya gaya miki, babu wanda yasan mutuwa zaiyi saboda babu wanda yasan gawar fari sai Allah. Am sorry" yayi kokarin juyo dani in kalle shi amma naki yarda, ya rabu dani yace "zan je airport yanzu in gani ko da akwai plight zuwa Nigeria yau ko gobe. Please dan Allah promise me you will stop crying" ya zagayo ta side din da fuska ta take, ya saka hannu ya bude fuskata dana rufe da hannuna, fuskarsa tayi abin tausayi, ya goge min hawayen fuskata, yace "kinji abinda na gaya miki? Ina so inje in samo mana plight tickets amma bana son in barki kina kuka kuma, please ki daina sai in tafi. In baki daina ba kinga ba zanje in sama mana plight ba ballantana mu tafi Nigeria" na goge fuskata ina kallonsa nace "na daina to" yace "promise" nace "I promise" sai da yaga na tsaida hawayena sannan ya fita, yana fita na hau kan gado na kwanta na cigaba da kuka na.
Wajan karfe daya ya dawo, inajin shigowarsa na rufe idona kamar bacci nake yi. Ya dan jima a tsaye yana kallona sannan ya hawo gadon ya dan taba jikina, yace "my God, kukan ki ka cigaba kenan ko? Bayan kinyi min alkawarin ba zakiyi ba" bance masa komai ba, naji ya sauka daga kan gadon, na bude idona ina kallonsa naga ya dauko first aid box din mu ya dauko min magunguna na, ya dauko bottle water ya bude ya hawo gadon ya mikar dani tsaye ya bani nasha. Na koma na kwanta ina kallonsa nace "so.., when are we going?" Ya dan shafa kansa yace "babu plight zuwa Nigeria yau da gobe, sai jibi idan Allah ya kaimu." ya miko min tickets guda biyu na karba ina kalla, that means sai Baffa ya kwana uku da mutuwa sannan zanje gida. Na lunshe idona ina jin jikina yana relaxing saboda maganin da nasha. Ina nan a kwance ina kallon sultan yana kokarin fara hada mana kayan mu, yayi waya restaurant ya fada musu abinda zasu kawo mana for lunch, da kyar na tashi nayi sallah na koma na kwanta. Bana kukan yanzu amma kuma raina gaba daya babu dadi, duk maganganun da muke yi da baffa ne suke dawo min rai na. Irin nasihohin da yake yawan yi mana akan gudun duniya, akan zumunci, akan biyayya ga iyaye da kuma miji. Da kyar sultan ya matsa min na danci abinci na koma na kwanta. Karfe biyar na yamma sultan ya gaji da zama shi kadai ya fita waje, sai kuma gashi ya dawo da sauri yazo ya daga ni tsaye ya fara kokarin cire min riga, na rike hannu sa, "sultan menene haka?" Bai ce min komai ba ya dauko wata rigar mai kauri da dogon hannu da collar ya saka min, ya saka min hula da safa ni dai duk ina kallonsa, nace "ina zamu je kuma" yace "kifi zaki je ki kamo mana ki gasa mana muci da daddare" na dan bata fuska nace "kifi kuma? Ni ban iya kama kifi ba" yayi murmushi yace "yau zaki koya, common, let's go" ya kama hannuna muka fita. A hankali naji na dan fara sakin raina, bawai na daina jin zafin mutuwar bane ba, na dai daina jin haushin sultan. Wani boat muka dauki haya muka shiga, daga ni sai shi, shi ya tuka ya kaimu tsakiyar ruwa sannan ya dauko wani dan kwando ya bude ya dauko wata kugiya ya daura zare a jikinta, sannan ya zagayo ya zauna a baya na, ya saka kafafuwansa a both sides dina, ya kama hannayena da nasa, ya saka fuskarsa a wuyana yace min a cikin kunnena "I am going to teach you how to catch a fish" cikin raunanniyar murya nace "sultan Baffa ne fa ya mutu, how can I just be busy catching fish bayan Baffa ya bar duniya?" Yace "mutuwar Baffa tana nuna mana abubuwa da yawa, daya daga cikinsu shine; there is an ending to life. Duk shekara, duk wata, duk sati, duk yini, duk awa, duk minutes, duk second din daya wuce ba zai dawo ba. What we need to do is to make the best of our time kafin namu lokacin muma yazo. We should live our life because it is a gift from God. Baffa yaji dadi, yayi rayuwa mai tsaho kuma mai kyau, ya tafi ya bar zuri'ah mai albarka. Wani tun kafin yayi aure ma yake mutuwa, wani tun yana yaro ma kafin yasan menene rayuwa yake mutuwa, wani ana haihuwarsa yake mutuwa, wani kuma tun a cikin mahaifiyar sa yake mutuwa, shi ko duniyar ma bai gani ba ballantana yaji dadinta. Wani kuma zai yi rayuwar mai tsahon har yakai kamar shekarun Baffa amma kuma sam babu abinda ya tsinana a cikin ta, babu abinda in ya tafi za'ace ga abinda ya bari na alkhairi sai dai na sharri. Amma baffa kuma fa? Ko mu daya bari ba mun isa mu taya shi gode wa Allah ba? Mu taya shi neman rahamar ubangiji ba?. Mutuwa is a circle of life, wani ya mutu sannan a haifi wani. Jiya da baffa ya mutu hundreds of babies were born all over the world, sannan hundreds of people sun mutu tare dashi" ya dora hannayen mu akan babyn mu da yake ta tsalle tsallensa babu abinda ya dame shi, yace "ranar da za mu haifi babyn mu, ranar hundreds of people zasu mutu. And what favor of our Lord do we deny?" Na lumshe idona ina ina jin dadin iskar gurin, ina jin dadin dumin jikin sultan, ina kuma jin dadin kalamansa, sannan inajin dadin motsin baby na a ciki na, what favor of my lord do I deny? Allah yayi min komai, ya bani komai, why should I be sad dan ya karbi abu guda daya daga cikin dubun daya bani? Na bude ido na ina kallon clear ocean din nace "I thought we are suppose to be fishing? Ya dan yi dariyar jin dadi yace "yes Love". Mun kama kifaye da yawa, dan sai da muka cika dan basket din da muka taho dashi, daga baya sai muka fara zaba, duk wanda muka ga mummuna ne sai mu mayar dashi cikin ruwa, gaba daya hankali naji ya kwanta, babu wani sauran bakin ciki a tare dani, nishadin mu kawai muke muna dariya, in mun kamo kifi yana ta tsalle mai in kankame sultan wai tsoro nake ji kar ya cije ni, in mun mayar dashi ruwa kuma sai muga sun fita a guje, nan ma muyi tayi musu dariya. Bamu ankara ba sai gani mukayi rana zata fadi, nan muka tsaya muna kallon rana tana setting on the ocean, rana tana gama faduwa kuma sai duhu ya fara saukowa, nan take naji tsoro ya kamani, na duba naga we are in the middle of nowhere, babu gida gaba babu gida baya, na zaro ido ina kallon sultan nace "sultan yanzu idan shark yazo ya cinye mu fa" yace "kin san kuwa akwai sharks a ruwan nan ba" da sauri na kankame shi "na shiga uku, shikenan a teku zamu mutu, ko gawar mu ma ba za'a gani ba, wayyo Daddy" dariya sultan yake min sosai sannan yace "am just joking, babu shark anan" ni dai ban yarda ba nace ya mayar damu hotel din mu. Hankali na vai kwanta ba sai da naji kafa ta ta taka kasa tukunna. Muna zuwa sultan ya dau basket din kifin ya kai restaurant din gurin yace su gyaro mana shi su kawo mana tare da kayan barbeque. Da daddare kifin mu muka gasa muka ci a matsayin abincin dare. Da daddare na tashi na gabatar da salloli na roka wa Baffa rahamar ubangiji.
Washegari ma Sultan bai barni na zauna ba ballantana inyi tunani ko kuka. Ya dauke ni muka tafi shopping. Kaya masu yawa ya saya mana ni da shi, bamu dawo dakin mu ba sai azahar, muna zuwa muka hada duk kayan mu da ba zamu bukata ba sultan ya dauka ya tafi shipping station din gurin ya bayar za'a kai mana har gida abuja. Tun da ya dawo yace min yau zai kai ni wani special guri muyi last dinner tunda gobe da safe zamu bar kasar. Muna sallar magrib muka shirya, ni kaina nasan munyi kyau, dama gashi na kara fari, in ka ganni ma ba zakace na taba shiga rana ba, ga kuma kibar ciki data kara min cika da budewa sosai, hips dina kamar wanda aka dauko aka dora min. Na saka riga da skirt bakake masu adon red, nayi rolling red veil wanda ya kara fito da hasken fata ta, kayan kuma tunda masu girma ne sai suka boye girman cikina. Sultan kuma suit ya saka ash, ya saka red shirt a ciki, ya taje kansa ya kwantar da gashinsa sai kyalli yake yi. Na zauna kawai ina kallonsa saboda kyan da yayi min. Golden brown skin dinsa tana reflecting duk fitilar data haska shi. Duk wanda ya kalle mu sai ya kara. Wani restaurant mukaje mai suna Ithaa, a karkashinin ruwa restaurant din yake, lifter zaka shiga tayi kasa da kai sannan sai kadan yi tafiya kadan a cikin wani glass corridor zuwa cikin restaurant din. Dan karami ne kuma shima duk da glass aka yi shi dan haka ji zaka yi kamar a tsakiyar ruwa kake, ni dai ji nayi kamar glass din zai fashe ruwa a shigo ya cinye mu. Gurin mutane 14 kawai yake dauka, amma fa abincinsu number one ne gurin dadi. Muna ci muna zuba soyayyar mu, dan gurin babu wanda ya damu da abinda wani yake yi. Bamu muka dawo dakin mu ba sai after ten. Muna zuwa muka kammala harhada sauran kayanmu mukayi sallah muka kwanta.
Washe gari da sassafe jirgin mu ya tashi, na leka ta window ina kallon islands din nace a hankali "Adiós Maldives, sai mun dawo" sultan yana kusa dani yace "we will come back for sure". Jirgin mu yana gama settling a sama na cire seatbelt dina na tashi na dawo kan cinyar sultan na kwanta, ban jima da kwanciya ba bacci ya dauke ni, sama sama naji sultan yana cewa plight attendant ta kawo mana bargo, ya dan kwantar da kujerar sa ya lullube mu da bargo. Gaba dayan mu bacci mukayi, dan sai da jirgi zai sauka a malam Aminu kano international airport sannan aka tashe mu. Muna fita reception muka tarar da Mahmud abokin sultan na kano wanda sultan ya kira ya gaya masa zamu zo yana jiran mu. Na kalli agogo naga 9:30am. Ikon Allah, banbancin lokuta a tsakanin garuruwa kadai ya ishi mutum abin mamaki. Mun baro Maldives 8:30, munyi tafiyar at least five hours amma kuma munzo Nigeria at 9:30am, to ina four hours din suka tafi?. Sai da muka tsaya muka danyi takeaway din abinci kuma sultan ya chanza kaya zuwa manyan kaya da hula sannan muka dauki hanyar 'yalleman. Sai a lokacin baji mutuwar tana sake dawomin a raina, muna zuwa kofar gidan naga cikar mutane a gurin, dan gabaki daya garin ma kusan a cike yake da mutane tunda yau ne sadakar uku. Kafin muyi packing na kira Amina nace tazo mu shiga tare saboda bana son shiga ni kadai. Ina shiga naga kowa ido shabe shabe da hawaye ai nan take na fara nawa nima, sai kuma kowa ya dora daga inda ya tsaya, naje na fada jikin Inna muna yi tare. Uncle Aliyu ne ya shigo da fadan sa, yace "dama tunda na jiyo sabon kuka nasan sarauniyar kuka ce tazo, menene haka maimunatu? Ana kokarin ayi masa adduoi ke kina kokarin ki tayar mana da sabon kuka ko?" Nan take na hadiye kuka na, na dau charbi ina ja amma ban san me nake cewa ba, hawaye ne kawai yake bin fuskata ina kallon irin jama'ar da Baffa ya bari, ga dakinsa nan kamar zai fito daga ciki. Sai yamma sannan jama'a suka dan ragu, sai a lokacin na samu naga Hafsat wacce itama nata cikin ya fito ba laifi, Daddy kuwa sai da daddare sannan na samu nayi masa gaisuwa. Washegari wajan 12:00 na safe duk kusan jikoki mata muna palon hajja a zazzaune sai ga aike wai inzo dakin inna nayi baki daga abuja sun zo min gaisuwa. A raina nace 'lallai Yaya da kokari, wannan tafiyar aita yi mata nisa da yawa, tunda munyi waya ba shikenan ba?' Na kama hannun Zainab amaryar yaya Walid muka tafi tare. Amma ga mamaki na ina shiga palon sai ganin Ummee nayi a zaune akan kujera tana kallona, na saka hannu na na mitstsike idona wai ko ba dai dai na gani ba amma still ita dince, da nani, da matar galadima da kuma Saratu da Huda. Na karasa gurinta da sauri na fada jikinta, ta rungume nu tana cewa "careful, kar kiji ciwo kuma" na fara kuka tana rarrashina, da hannu ta saka take goge min hawayena, duk mutanen gurin kallin mu suke da sakakken baki, nace "Ummee how comes you are in Nigeria? When did you come? Did Sultan know you are here?" Ta share min hawaye tace "I will tell you all about it later. Now let's pray for the dead" ta ringa jero adduoi muna amsawa. Na aika Zainab ta kira Hafsat, sai gasu tare da Amina, suka zo suka gaishe su. Haka mutane suka ringa shigowa suma gaishe da Ummee, wasu ma tsegumi ne yake kawo su. Hajja ta fara mita "idan nace sayar da yaran nan akayi sai ace min ba haka bane ba, in uta Hafsat ance balarabe ta aura to ita kuma maimuna fa? Ita data auri bahaushe menene hadin ta da larabawa?" Daga Mommy har Inna babu wanda ya tanka mata, ni dai ina nannade a jikin ummee ina lussafin ya akayi ta baro saudiyya ta taho Nigeria har tazo 'yalleman. Sai bayan sun ci abinci sun huta sannan na dauki waya ta na zagaya baya na kira sultan, yana dauka nace "kasan da zuwan Ummee kuwa?" Yace "wacce Ummee kike magana akai" nace "Ummee dai tamu, gata nan a dakin Inna" dariya yayi kadan yace "Moon rasuwa fa akayi, why are you making jokes" na koma na leka dakin ta taga na ganta akan sallaya tana addu'ah nace masa "wallahi va tsokanar ka nake ba Ummee ce suka zo da su Nani daga Abuja" ya kashe wayar, na koma dakin still ina kallonta, tayi min murmushi ta nuna min kusa ta ita alamar inzo in zauna. Da la'asar su Nani suka koma, amma banda Ummee da Huda, Ummee tace "sai gobe daddyn sultan zai zo sai mu tafi tare" ni dai kawai kallonta nake da mamaki. Sai bayan mun raka su mun dawo sannan nace mata "Ummee sultan fa bai san kinzo ba" tace "eh, bai sani ba" nace "dan Allah in kira shi ya ganki?" Ta dan dungure min kai tace "wai ke nan mai miji ko?" Na langwabe kai ina rokonta, tace "Ok, da daddare sai yazo mu gaisa, yana ina?" Nayi mata bayanin yana gidan nuraddeen, a can ya sauka.
Sai daga baya mutane suka gane Ummee surukata ce, sai kuma aka koma gulmar yadda muke da ita babu alamar sutukuta. Mommy sosai ta karbi Ummee suna ta hirar su, daga dukkan alama tasu tazo daya, ballantana nasan Mommy da son 'ya'yanta, soyayyar da taga Ummee tana nuna min ma kadai ya isa itama ta so ta. Da daddare bayan an watse sai few mutane, na kai Ummee palon waje, na kira sultan. Yana shigowa tsayawa yayi yana kallonta ya kasa magana, ta tashi ta rungume shi da sauri "my little love, how was the honeymoon?" Muka kalli juna ni da sultan, tace "do you guys enjoy Maldives?" Tayi dariya ganin yadda mukayi da fuskokin mu ta zauna muma muka zauna muka saka ta a tsakiya tace "kun dauka wai bamu san inda kuka tafi ba? Maldives kukaje, kuka sauka a hotel din soneva jani, cabin no 12" sultan ya bata rai "saka wa kikayi aka bi mu?" Tayi dariya tace "bani na saka ba, babanka ne, tun sanda kace masa zaku tafi ya aika wani a can Riyadh ya tsaya a airport yaga wanne plight kuka hau ya gaya masa, sannan ya kira Maldives din ma ya saka wani ya jira ku a airport yaga saukar ku kuma ya biku har hotel din da kuka sauka sannan ya gaya masa" sultan ya mike tsaye ya fara zagaye dakin "shikenan yanxu mutum bashi da private life kenan" ina dariya a raina ina cewa "sultan har yanzu America bata barka ba". Ya dawo ya zauna yana kallonta yace "to ya akayi kika taho Nigeria kuma keda akayi banning from leaving Saudi" Tace "They can't stop me from coming to Nigeria if am married to Nigerian".
Lol, we have new amarya in town.
0 comments:
Post a Comment