Muka kalli juna ni da Sultan sannan muka kalleta, she was blushing, Sultan ya mike tsaye bacin rai a rubuce a fuskarsa yace "wait, what? Aure? Who did you marry? Kawai dan ki zo Nigeria sai kiyi aure?" Duk kallonsa muke yi daga ni har Ummee, ya fara zagaye palon yana magana "koma waye i will have nothing to do with him. Tunda kin aure shi ya kawo ki Nigeria shikenan mission accomplished, ya sake ki kawai ki dawo gidana ki zauna, in ma ba kya son zama a gidana sai in sai miki wani gidan ki zauna, but I don't want to see any man near you" ni kam dariya kamar zata kwace min ganin yadda ya hakikance yake fada, lallai kishi kumallon maza, lol, tabbas da ace Ummee tayi aure da anyi drama da sultan. Ummee tace "sultan you shouldn't judge people before you get to know them, give him a chance, yana da kirki sosai, you will like him" da sauri yace "I won't. Kuma ma nasan tunda da gaggawa akayi auren yanzu haka baki gama sanin halinsa ba, he may even be a 419 guy for all we know, ko kuma ma arm robber, Nigerians are not like Arabs, ba'a saurin trusting mutane anan Ummee" she was calm duk wannan fadan da yake yi, tace "Sultan I know him tun kafin musan zamu haife ka, zan iya cewa I knew him more than anyone a wancan lokacin, kuma har yanzu ma he hasn't change a bit" ya tsaya da zagayen da yake yana kallonta, sai a lokacin dariya ta kwace min, ya juyo yana kallona fuska a daure yace "menene abin dariya kuma?" Na tsaya da dariyar da nake nace "sultan, Ummee is trying to tell you cewa sun mayar da auren su ita da Takawa" ya dan jima yana kallona inayi masa murmushi, sai kuma ya juya ya kalli Ummee, ta gyada masa kai, a hankali kuma kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki sai ya dawo ya zauna a kusa da ita, ta saka hannu tana shafa gashin kansa, tace "you look so much kike your father when you are angry" yace "amma Ummee me ya faru? Ji nake fada kuke yi da Takawa" ta danyi dariya tace "dama can kullum fada muke yi dashi, he is so stubborn and hot headed like you" ya kwantar da kansa a kafadar ta yace "I love you, Ummee" na mike a hankali na koma cikin gida, ina jin dadin auren Takawa da Ummee a raina amma deeply kuma ina alhinin rashin Baffa.
Washe gari da wuri Takawa yazo, da jiniya da hakimai da dogarai da komai yazo, Allah bai yi zasu gaisa da baffa ba. Kofar gidan baffa kuwa ya cika taf da mutane sunxo ganin sarkin abuja. Ya jima a gurin su Daddy sannan ya aiko aka kira ni, muka tafi tare da mata da yawa muka gaishe shi yayi mana gaisuwa sannan muka dawo cikin gida. Bayan azahar aka aiko su Ummee su fito zasu tafi, Ummee dama ta shirya amma muka nemi Huda muka rasa, gashi kuma ta bar handbag dinta da wayarta a ciki ballantana a kira ta, ni da Amina muka fita daki by daki muna nemanta amma shiru, gashi ana ta jiransu a waje, na zagaya bayan dakin hajja inda take 'yan shuke shuken ta kawai sai na hango hijab din huda a bayan katanga, na kara sauri sai na hango tare suke da wani namiji, gaba na ya fadi, na shiga ni maimunatu, kar dai munir ne ya ja 'yar mutane bayan gida zai lalata musu yarinya inzo inji kunya, ga mamaki na ina zuwa sai na ga Faruk, na tsaya ina kallonsu duk basu san ma nazo gurin ba, faruk ya karkace a jikin jini yana ta zuba mata tsari ita kuma ta sunkuyar da kai kasa tana ta murmushi, nayi gyaran murya, suka juyo a tare suna kallona, da sauri ta ja hijab dinta ta rufe fuskarta shi kuma ya juya baya yana shafa keya, nace "ki zo ana jiranki zaku tafi" sumi sumi tazo ta wuce ni, bance masa komai ba na juya zan tafi, ya biyo ni da sauri, "ammm...... dama wai bata san kayan lambu ba shine nake nuna mata" ba tare dana kalleshi ba nace "to" a raina nace 'maida karuwa 'yar iska' wai dan karamin faruk din nan nr har ya girma shima zai fara tsara 'yammata, sai kuma na tuno cewa yanzu fa service yake yi, dan haka ya girma kenan. Duniya kenan.
Muka fita rakasu sultan yana ta bacin ran Takawa yace tare zasu koma, ni kuma sai anyi sadakar bakwai sai mu taho tare da su Mommy. Na san dan dai babu yadda zaiyi ne, gashi ko wata sallamar kirki bamu yi ba. Motar Takawa suka shiga, shi yana gaba kusa da driver, Takawa da Ummee suna baya a tare. Sai kawai na samu kaina da murmushin jin dadi. Suka shiga motocinsu suka tafi mu kuma muka koma gida. Ranar da Baffa yayi kwana biyar da rasuwa Amira tazo yi mana gaisuwa, ita da Mama da wata aunt din ta. Sun jima sosai sannan sukayi shirin tafiya, mun taho rakasu ni da Hafsat da Amina muna dan tafiya a hankali muka bar su mama suka yi gaba, ina ta studying Amira, she looks happy. Nace "how are you?" Tace "actually am great. Yanzu na fahimci family is everything, babu abinda yafi dadi irin ka ganka a cikin 'yan'uwanka, yanzu a kano duk inda na kalla hagu da dama duk 'yan'uwana ne, kuma rashin zama a cikin su tun farko shi ya saka nake ganin kamar basa sona ashe abin ba haka yake ba" nace "ya angon naki kuma yazo?" Nan take naga wani murmushi ya shi kadai ya isa amsar sauran tambayoyin nawa, tace "yazo, bai jima ba ya koma, da yake karatunsa yazo karshe ne abubuwa sundan shige masa gaba" nace "and" tace "he is OK. A bit different though, mamansa shuwa ce, kuma kamar duk ita yayo, so technically za'a iya ce masa shuwa. He is really nice, a doctor, kuma naji dadin yadda ya karbe ni" na tsaya ina kallonta wani tunani yana zuwa min raina, nace "wait, ya sunan sa?" Tana kallona da mamaki tace "Mahdi" sai kuma ta rufe baki tace "oh my God, kin san shi ashe, Oxford yake yi kuma medicine" nace excitedly "Mahdi was my best friend a Oxford. Congratulations Amira. Mahdi is the best husband that you can ever wish for" nan muka rabu da alkawarin next time idan muka hadu zan bata labarin rayuwar makarantar mu da mahdi. Bayan sun tafi na zauna ina tunanin hukuncin ubangiji. Tayi ba dai dai ba a rayuwa amma kuma tayi nadama, mun yafe mata mu da ta bata wa, Allah ma sai ya yafe mata, sannan kuma tazo ta farantawa mahaifiyarta rai ta hanyar bata zabin mijin da zata aura, sai ubangiji yayi mata zabin alkairi ya bata Mahdi, wanda ni a ganina yafi Amir din da da na dauka zasuyi aure, ya kuma fi Abbas din da naso hada ta dashi. Allah kenan.
Ranar sadakar bakwai Ibrahim yazo yi mana gaisuwa, dama Amina tace min yazo dashi akayi jana'iza. Muka fita gaba daya dasu Hafsat yayi mana gaisuwa, sam babu wani special treatment daya bani, idonsa suna kan Aminan sa. A ranar muka taho gaba daya har Daddy, Amina kadai muka bari acan saboda 'yan shirye shirye da zata yi saboda bikin su yanzu saura sati uku. Su inna sun so a daga bukukuwan amma mazan gidan suka ce babu wani abu, sai dai an yanke shawarar Abuja za'a tafi ayi bikin gaba daya a can. Muna zuwa Abuja gida muka wuce, Sultan yayi ta nacin in taho gida amma naki, saboda ba karamin gajiya nayi ba kuma nasan ina komawa gida sai ya karamin wata gajiyar. Da kyar na samu na lallabashi ya hakura ya barni na kwana a gida. Tunda muka sauka a gida daga ni har Hafsat muka baje cikkuna a gado muka yi ta bacci. Washegari bayan sultan ya taso daga office ya biyo muka tafi. Naga duk ya chanja a kwana biyar din da ban ganshi ba, he looks so calm and happy, loneliness din da nake gani kullum a idonsa is now totally gone, a raina nace lallai duk duniya babu abinda yafi iyaye dadi, komai girman mutum, komai arzikinsa, komai yawan matansa da 'ya'yansa, soyayyar iyaye daban ce, ballantana ga sultan wanda da bai san taba, dan haka yanzu kara'i ake masa. Ina shiga motar ya matso ya jawo fuskata ya fara kissing dina, na barshi yayi dan kansa ya hakura, yace "damn it baby girl, I missed you" nace "ina kayi missing dina bayan nasan kana can Ummee tana goya ka da zani" yayi dariya yace "da ace zan tsaya da sai ta goya nin ai" na taya shi dariyar nace "how is she?" Yace "tana can tana shan amarci" na dungure masa kai nace "Ummeen kake gaya wa tana amarci ko?" Yace "in munje zaki gane wa idonki ai".
Muna shiga naga gidan gaba ki daya ya chanza min, gaba daya an chanza masa traditional setting din sa an mayar da shi modern. Part din Takawa in ka shiga ba zaka dauka a Nigeria kake ba saboda haduwarsa, anan kuma ummee take, basu wani raba dakuna ba. Komai wayewar ka in ka shiga gurin sai kayi kallo. Da sauri Ummee tazo ta rungume ni tana min sannu da zuwa, ta sunkuya kusa da cikina tace " Hello dear, welcome back home" daki daki sai da ta shiga dani ta nuna min, master bedroom ne naki shiga, ina suruka ina ganin makwancin surukai?, lol. Part din Hajiya yana nan yadda yake, tana nan kuma har yanzu a ciki, amma kuma a kusa da gurin anyi wa su saratu sababbin dakuna suma, an kawata musu gurin gwanin ban sha'awa. Sultan yana ta tabani wai in tashi mu tafi amma Ummee tana ta zuba min hira, tana tsara min yadda aka tsara bikin Amir wanda za'ayi next week. Ban tambayeta labarin yadda aka mayar da auren su da Takawa ba ita ma kuma bata gayamin ba. Muna ta hira har akayi sallar magrib, sultan ya fita masallaci mu kuma mukayi anan, tare suka dawo da Takawa, ni dai yana shigowa kaina a kasa na gaishe shi, ya amsa min sosai harda tambayata ya karin hakuri, na dago kaina na amsa masa "Alhamdulillah" and he smiled, this is the second time dana taba ganin murmushinsa. He looks different shima, he looks happy, har wani haske naga yayi da wani annurin fuska irin na angwaye. Tare muka ci abincin dare, ni dai duk a takure naji ni. Su kam hirar su suke yi sosai, Ummee sai dariya take yi, she looks so happy, basu da wani problem in the world, komai yayi farko yana da karshe, duk wata wahala da mutum yake sha a rayuwa mai wucewa ce, musamman idan kana kan gaskiyar ka, musamman idan baka zalinci kowa ba, to ka tabbatar cewa ubangiji yana sane da kai, kuma He has a special plan for you. Allah yasa mu dace.
Muna zuwa gidan mu a palon farko na tarar da baba gaji da 'yammatanta, bakunan su har kunne suna murnar dawowa ta, gidan kal kal kamar banyi tafiya ba, ko'ina sai kamshi yake yi. Na zauna duk suka zo suka gaishe ni kuma duk na ambaci sunayensu, suka dauko kayayyaki na suka kai min dakina, zasu kawo min abinci nace musu na koshi. Anan palon na baje dani da cikina muna hutawa, sai da na gama hutawa sannan na tashi na tafi part dina. Ina tura kofar corridor naka duk fitulun gurin a kashe, amma kuma ga haske nan yana fitowa daga kofar da take facing dina, kofar dakin da sultan ya gina a matsayin our baby's room, ni dai a sani na dakin a rufe yake tunda aka kawo ni ba'a taba koda bude shi ba saboda babu komai a cikinsa. Na karasa na tura kofar naji ta a bude, ina shiga naji kida a hankali yana tashi, irin wakokin nan na lullaby. Ido na bude ina kallon dakin, exactly irin dakin da na taba gani a cikin system din Ummee a Riyadh. A zahiri ma sai naga yafi kyau akan hoton. Kadan ne ya rage ban saki kara ba saboda mamaki, hannuna yana rawa na dauko wayata na kira sultan, "sultan baby's room din nan yayi kyau sosai" yace "what baby's room?" Nace "gashi kuwa, an gama an saka komai" da sauri yace "wait a minute, gani nan zuwa" bai fi minti biyu ba sai gashi ya shigo, ina nan tsaye har yanzu a inda nake ina kallon dakin, komai na dakin blue ne, sai shades din ne wani mai duhu wani mai haske, an saka komai tun daga labulaye da capet, baby crib da drawers, da sofa guda daya da breastfeeding pillows a kanta, ga playpen da toys da yawa a ciki, baby swing, baby carrier, trolley, walker, feeders da starilizer, hatta tissues babu abinda babu a dakin, na karasa na bude closet din dakin, nan ma wani mamakin nasha, kayan baby ne fal a ciki, wadansu anyi hanging wadansu an jera su a lockers, kuma abin burgewar shine yadda akayi arranging kayan according to size, from newborn, sai 1-3 months, sai 3-6 months, 6-9 months, haka har 5 years. Diapers da wipes kuwa ina jin sai mun shekara bamu nema ba. Na juya na rungume sultan nace "oh sultan, it is beautiful" yace "I have no idea yaushe aka hada dakin nan" na dan cika shi ina kallonsa nace "nasan waye, Ummee ce" ji nayi kawai babu abinda nake so irin inga na haihu na fara kula da baby na, har wata kwallar dadi naji tana bin idona, ya ilahi, bansan ta inda zan fara gode wa Allah ba. Na saka hannu ina shafa lallausan bargon da aka shimfida akan crib din, a lokacin ne ido na ya hango pictures din da aka rataye a both sides din gadon, daga hannu dama hoton wani baby ne, na dauka ina kalla, sultan ne yana baby, with his red lips, ya tabe baki irin yadda babies suke yi in zasu yi kuka, dariya na kama yi, yazo ya karba shima yana dariya, na lakuce masa hanci nace "daga gani dama kai rigimamme ne kana baby" ya dauko picture din barin hagu shima yana kalla, ni ce nima ina baby, nayi murmushi dimples dina duk biyun sun lotsa, ya saka hannu yana shafa fuskata a hoton, nace "see? In dai babyn nan yayi rigima to kai ya dauko" ya ajiye hoton ya juyo yana kallona yace "idan kuma yayi surutu fa? Da shagwaba, da son jiki?" Nace "oho, wannan kuma bansan wa yayo ba" ya jawo ni jikinsa ya rungume ni ta baya yana dan juyi damu yace "kin san lissafi nake yi yau in kin huta gobe zamu fara shiga kasuwa siyayya?" Nace "ai mu yanzu 'yan gata ne, komai yi mana ake yi" ya yi murmushi yace "yeah, you are right. Ni fargaba ta daya, kada a haifi babyn nan su dauke mana shi su hana mu" nayi dariya nace "shikenan sai mu bar musu shi mu haifi wani". Hmmm kawai yace min. Na dauko waya ta nayi dialing number din Ummee, sultan ya gani yace "ke cikin daren nan zaki kira mata tana dakin mijinta" na harare shi, tana dauka nace "oh Ummee, it is beautiful" tayo dariya tace "har kun gani kenan, do you like it?" Sultan ya zuro kansa yace "we love it Ummee and we love you" ina jiyo dariyar Takawa a background, a raina nace 'dama yana dariya?' Ummee tace "we Love you too sweethearts. Yanzu saura abu daya ya rage" nace "Ummee komai komai ya kammala babu abinda yayi saura kuma" tace "akwai. Addu'ah. Addu'ah ita zamu saka yanzu a gaba muyi tayi ba dare babu rana. Allah ya sauke ki lafiya ya kawo mana new little love lafiya" sultan yace "what? Ummee sunana ne fa?" Tace "daga ranar da aka haife shi za'ayi maka retire, amma before then, you are still our little love, so enjoy it while it last" mukayi dariya a tare, tacigaba da cewa "maimunatu daga yanzu ki dage da cin dabino sosai, sannan kike cin abinci sosai kuma mai kyau wanda zai kara miki karfi da lafiya. Sannan abu na karshe ki tabbatar kullum wayarki tana kusa dake kuma ki tabbatar akwai kudi a ciki kuma akwai chaji. Hospital bag din ku tana gurina, na hada miki kayanki dana baby wanda zaku bukata a asibiti. Allah ya sauke ki lafiya." Sultan yace "Ameen" nima na fada amma a raina, ya karbi wayar ya kashe. Ranar a dakina muka kwana, sultan sai da ya karbi dukkan bashin daya ke bina, nima kuma haka, dan nima ina son mijina. Na kwanta a jikinsa ina shakar kamshin sa da nayi missing kwana biyu, ya taba cikina da yake ta mutsu mutsu yace "kai fa na lura kiriniya ce da kai, to ka sani, wannan wasan bana yara bane ba, ga playpen dinka can Ummee ta sayo maka da toys dinka, sune abokan wasan ka ba mu ba, idan Mommy da Daddy suna yin wani abu yara basa zuwa gurin" nayi dariya ina shafa kansa nace "idan bai yi kiriniya ba ai sai Allah ya tambaye shi" ya dan bata rai yace "yarinyar nan naga alama kinga gurin kwana na shi yasa kika raina ni, zanyi maganin ki ne, dan kinka yanzu ina dan daga miki kafa ko? I will be back to my normal self and sai kin raina kanki" kafin muyi bacci na tambayi sultan "wai Ummee ta dade a garin nan ne har ta shirya dakin can?" Yace "watanta daya da sati daya a Nigeria yanzu" sannan ya bani labarin abinda ya faru bayan tafiyar mu daga Riyadh.
Episode Ninety Six : The New Bride
Riyadh; bayan tafiyar su Moon;
A hankali Ummee ta juya ta koma cikin gida, tana shiga palon kawai taji gaba ki daya ta tsani gidan kuma, ta tsuguna anan bakin kofar tana jin hawaye yana fitowa daga idanunta. Ta jima a haka sannan taji karar wayarta kamar daga sama, da bata yi niyyar tashi ta dauka ba dan she is in no mood for chitchat, sai kuma tayi tunanin ko moon ce zata gaya mata wani abu, dan haka ta tashi da sauri ta karasa gurin yawar ta dauka, number din Nigeria ta gani, bata san number din ba amma jikinta ya bata ko waye, ta ajiye wayar bata dauka ba a ranta tana cewa 'duk laifin ka ne ai, muna zaman mu ka jawo gashi nan sun tafi sun barni ni kadai' ta zauna akan kujera tana lissafin abinda zata yi kuma, sai ta sake jin karar wayarta, wannan number din ce dai, Sadiq ne, tun da suka rabu ranar nan da daddare a abuja shekaru talatin da suka wuce bata kuma jin koda muryarsa ba sai dazu. Da taso shi kamar rai, son da ya saka har ta guji iyayenta ta aikata abinda bata taba tunanin zaya iya aikatawa ba, amma ta aikata saboda shi. A lokacin daya aiko mata da takardar saki kuma ji ta yi a ranta kamar duk duniya babu wanda ta tsana kamarsa, amma duk da haka duk tsahon shekarun nan, babu wani namijin data taba kalla da sunan namiji, ga larabawan nan, kyawawa na ajin karshe, amma duk kallon mata take musu a idonta, bata jin da akwai wanda zata iya sakawa a matsayin data sakashi a da. Sai kuma ga Maimunatu tazo mata da labarin cewa duk abinda ya faru baya cikin hankalinsa, sakin da yayi mata ma bai ma san ya sake tan ba, asali ma, bai ma san da ita ba all these years. Ga kuma labarin wahalar da sultan yasha a hannunsa. Sai ya zama ta kasa tantance taka mai mai me take ji a dangane dashi. Shin haushinsa take ji, ko tsanarsa tayi ko tausayinsa take ji. Wani kiran ya sake shigowa, ta daga wayar a hankali ta amsa, ta saka a kunnenta amma kuma sai ta kasa magana, to me zata ce masa? Shima daga daya barin maganar ya kasa, sun jima a haka suna sauraren numfashin juna, shekara talatin ba kwana talatin bane ba. Ya lumshe idonsa yana picturing dinta a ransa, sannan murya cikin makogwaronsa yace "how are you, Khairat?" Taji kiran sunan ta da yayi har cikin ranta, da akwai wani tone da yake kiran sunan ta dashi wanda shi kadai ne yake kiranta da hakan, all those thirty years melted in her heart. Ta dan gyara muryarta kadan dan kar ya fahimci yana da wani effect a kanta yace "They are gone, sultan and Moon, bansan inda suka tafi ba" yace "Sultan is a big boy, He will take care of them. Am asking how are you" ta goge hawayen idonta tace "am fine. Am a strong woman now. I have been taking care of myself for thirty years, I can take care of my self now, I don't need you" bai damu da abinda tace ba yace "then why are you crying?" Tayi shiru dan bata dauka zai gane kuka take ba, ya sake cewa "why are you crying, Khairat?" Nan take kukan ya taho mata gaba daya, tayi tayin kayanta bai hana ta ba, har da sheshsheka, sai da ta gama kayanta ta goge hawayenta sannan ya sake yin magana, muryarsa tayi masa nauyi sosai, yace "do you want me to come?" tace "I want my son. I want Sultan. I am tired of living alone. Sultan yayi fushi sun tafi sun barni ni kadai. Ban san inda suka tafi ba" kamar baiji abinda ta fada ba ya sake maimaita tambayar da yayi mata "do you want me to come?" A hankali tace "yes, yes I want you to come" yace "then I will come, I will come for you like I promised. Am sorry I kept you waiting" tace "Sultan ban san inda suka tafi ba" ya dan jima yana tunani sannan yace "zan saka a duba su anan airport din, duk inda zasu je dai nasan jirgi zasu hau, in kuma basu hau jirgi ba to suna cikin kasar nan. Daga nan zamu san inda suka tafi sai mu neme su a can" ta gyada kai kamar yana kallonta, yace "shikenan hankalinki zai kwanta ko Ummeen Little Love?" Bata ce komai ba, yace "I will come to Riyadh jibi insha Allah" ji tayi zuciyar ta ta fara bugawa da karfi, ta kashe wayar tana kallon screen din wayar, jibi? Two days kenan? Anya kuwa zata iya ganin sa? Ya yake yanzu? Ta tuna cewa yanzu shi sarki ne, yayi aure bayan rabuwarsu har ya haifi yara biyu, how much has he changed? Is he still the Sadiq she knows ko kuma ya koma total stranger?
A cikin kwana biyun da tayi tana jiran zuwansa har sai da ta rame saboda tunani, wani lokacin sai zuciyarta ta gaya mata ta kirashi kawai tace masa kar yazo yayi zaman sa, tunda in yazo ma mai zai yi mata? Babu wani abu a tsakanin su yanzu, ta tabbatar babu sonsa yanzu a zuciyarta, bata jin haushinsa dai irin da amma bata sonsa, duk sanda tayi wannan tunanin kuma sai ta tsaya ta tambayi kanta, anya kuwa? Amma kuma tana da tabbacin cewa shi babu wani abu a ransa a game da ita, zai zo ne dai akan maganar dan su, amma koma menene a tsakanin su is now over. Ya gaya mata yayi tracing su sultan, dan haka yanzu bata da fargaba a kan su, tasan they are safe. Ranar da zai zo ta gyara masa guest room, amma kuma sai ta tsaya tana tunanin bai kamata ta sauke shi a gidan ta ba tunda ita kadai ce a gidan, sai kuma tayi tunanin mai yasa take wannan tunanin a kansa bayan babu komai a tsakanin su. Bai gaya mata karfe nawa zai baro Nigeria ba dan haka bata san karfe nawa zai sauka ba, ita kuma bata tambayeshi ba, so she get ready, sits down on the sofa and waited, with her hands between her thighs. Akayi asahar ta tashi tayi sallah ta dawo ta zauna, akayi la'asar ma haka, magrib tazo itama ta wuce, sai da taji ana kiran sallar isha sannan hawayen da take ta rikewa ya fara gangarowa daga idonta, he is not coming, he is never coming. Ta mike a hankali ta koma bedroom dinta. Tana idar da sallah taji karar wayarta, sai da taji kirjinta ya buga, ta mike ta dauki wayar tana saka ran ganin 'sultan's dad' kamar yadda tayi saving number dinsa, amma sai taga number din mahaifiyarta. Ta zauna a bakin gado ta dauka da sallama. Tace mata "ki zo yanzu ki same mu a gidan babanki Umar" daga nan ta kashe wayar. Ta ajiye wayar ta rike kanta da hannu biyu, ya salam, me ya faru kuma? Kar dai ace sun gano cewa sun shirya da Sadiq zai zo gidanta, tasan halin uncle Umar sosai, abu na farko da zai fara yi shine zai karbe gidanta yace ta koma gidansa da zama. Amma kuma sanda ta kai masa sultan ai bai nuna wani abu ba, nuna wa yayi kamar komai ya wuce. Bata da zabi, duk da shekarunta amma bata kinyin abu in iyayenta sun gaya mata. Dan haka ta tashi ta tafi. Babu kowa a kofar gidan dan haka ta shige cikin gidan direct, tana gaisawa da matan gidan suka gaya mata ta shiga palon uncle din nata ana jiranta, ta gyara lullubin ta ta shiga da sallama. Gabanta ne ya fadi ganin mutane da dan yawa a palon, ba tare data tsaya kallon waye da waye ba ta shiga, ta zauna daga nesa akan carpet ta fara gaishe su. Sai a lokacin ta lura da akwai bakin fuska a dakin, ta tsaya da gaisuwar da take yi tana kallon su, duk da sun dan juya bayansu daga inda take zaune amma ta gane shi ta yana yin zamansa, ya harde kafafuwansa ya zauna a kansu, tun sanda ta san shi haka yake zama duk sanda zai zauna a kasa ba'a kan kujera ba haka yake zama, kuma taga sultan ma haka yake zama, Sadiq ne, he is here. Bata gaishe su ba daga shi har abokin rakiyar tasa , ta karasa gaishe da iyayenta ta zauna kanta a kasa tana jiran taji ta ina za'a fara yi mata ruwan bala'i.
Abokin tafiyar Takawa ne ya bude taron da addu'ah, ya nemi zabin ubangiji akan duk maganganun da za'ayi a gurin sannan kuma ya nemi tsarin ubangiji daga shaidan da mukarrabansa. Yana gamawa Takawa ya fara magana cikin larabci da jefi jefin turanci, yace "sunana Sadiq Abdallah. Ni bakar fata ne mutumin kasar Nigeria. Ni tsohon mijin 'yarku ne Khairat kuma ni ubane a gurin tilon danta, Abubakar. Nazo ne gabanku yau ina neman afuwar ku akan abinda na aikata na rashin kyautawa a gare ku shekaru talatin da uku da suka wuce, sannan ina neman alfarmar a mayar mana da auren mu ni da matata idan kun amince" ya juya ya kalle ta cikin ido, yace "idan itama ta amince" shiru dakin yayi na tsahon lokaci. Khairat kam gaba daya kanta ya toshe , what is he doing? An jima bayan ya gama uncle Umar ya fara magana wacce take cikin larabci mai chakude da turanci "assalamu alaikum. Babu abinda zan iya cewa yau sai Alhamdulillah. A lokacin da Sadiq yazo neman auren khairat a gurina yazo ya nema, amma a lokacin na shafa wa idona toka ba tare da na bashi dama ba nace bazan bashi ba, saboda ina ganin zai zama abin kunya mu aurar da 'yar mu ga wanda ba balarabe ba, ban duba cewa a cikin abubuwan da ubangiji yace a duba kafin a bayar da aure babu kabila ko kalar fata ba, na tauye hakkin sji Sadiq din sannan kuma na tauye hakkin ita khairat din, dan haka zan iya cewa duk abinda ya faru nine sila, saboda na tsallake tsarin addini nabi son raina, wannan shine ya jawo 'yar mu ta bijirewa umarnin mu tabi saurayi ta gudu daga kasar a wancan lokacin, tun a lokacin nasan cewa laifi nane amma pride ya hanani inyi admitting, sai muka tattara laifin duk muka dorawa shi yaron da yazo ya dauke mana yarinya, muka sha alwashin sai munga bayansa. Abin kunyar da nake gudu kar ace mun aura wa 'yar mu wanda ba balarabe ba sai ya zamanto gwara shima akan abin kunyar da muka fuskanta, cewa 'yar mu ta gudu ana gobe daurin aurenta ta shiga duniya. Wannan yasa muka kara kaimi gurin nemansu dan muga mun goge mugun suna a gurin mutane, kuma amma bamu same suba sai bayan shekara uku, sai a lokacin muka fahimci shima yaron dan babban gida ne, jinin sarauta ne, amma duk da haka maimakon mu zauna ayi maslaha sai muka dauki damarar sai mun nuna masa kuskurensa, muka je har gidan aurenta a gaban surukanta da mijinta muka dauko ta, muka raba ta da mijinta muka kuma rabata da dan jaririn danta. Amma Allah shine shaidar mu, bamu taba tsammanin raba sun da mukayi zai tabbata ba, mun raba su ne saboda mu hukuntasu a bisa abinda suka aikata, tunda har 'da ya shiga tsakanin munyi niyyar zamu hakura mu barsu. Amma sai yazo ya same mu ya bamu hakuri kuma ya nemi aurenta properly yadda kowa zai tabbatar cewa aurar da 'yar mu mukayi ba wai duniya ta shiga ba. Munce zamu hukunta shi idan yazo, amma mun san duk wanda yake da courage din shiga gidan mutane ya dauki 'yarsu ya gudu da ita to tabbas yana da courage din fuskantar hukunci a kanta. Amma kuma sai muka tarar da sabanin hakan, maimakon yazo din kamar yadda muka saka rai sai ya aiko mana da takardar sakin ta. Wannan shine abinda yafi komai kona mana rai, mu ana babban cin mutunci shine a auri 'yarka sannan kuma a sake ta. Ga kuma tashin hankalin da yarinyar ta shiga a dalilin sakin da akayi mata, da raba ta da danta da akayi. Tayi ta kokarin komawa amma muka hana ta saboda mu a gurin mu zubar da darajarta ne ace ta koma gurinsa duk kuwa da sakin ta da yayi, pride din mu ya saka muke ganin cewa shi ya kamata ya neme ta ba ita ba. Shi ya kamata yazo ya bata hakuri, ya bamu hakuri gaba daya. To Alhamdulillah yanzu gashi yazo, kuma ya bamu hakurin, kuma mun hakura, sauran magana kuma ta rage tsakanin sa da ita, in ta amince shi kenan ko a gobe sai a mayar musu da auren su".
Tunda aka fara maganganun, khairat kanta yana kasa, tana wasa da 'yan yatsunta, ji take tamkar mafarki take yi amma kuma gashi kamar gaske. Bata dawo daga tunanin taba taji ana ta fita daga palon, zata tashi auntyn ta tace "ki zauna kuyi magana tukunna, zuwa gobe sai ku fadi shawarar da kuka yanke" ta koma ta zauna zuciyarta tana bugawa, tayi sauri tayi wa kanta fada "why are you behaving like a teenager? Ke da za'a haifawa jika very soon?" Nan take ta maida hankalinta guri guda ta juyo tana fuskantar Sadiq da abokin tafiyarsa, sai yanzu ta kalli abokin Sadiq din sosai, he looks familiar, and he also looks like maimumatu and Hafsat, shi ya fara gaisheta, ta sunkuyar da kanta kasa ta gaishe shi itama, ya amsa, sai kuma suka yi shiru, ya mike tsaye yace da Takawa zai jira a waje, har yakai bakin kofa tace "You are Maimumatu's Father, right?" Ya juyo yana murmushi yace mata "that's right" tayi dariya tace "Ina Fatima? Ya baku taho tare ba?" Yana murmushi yace "zata zo itama, maybe daukan amarya zata zo, tunda ni nazo daurin aure" sai kuma taji kunya ta sunkuyar da kanta, shi kuma ya fita. Sun jima bayan ya fita babu wanda ya ce komai, sannan Takawa yace "so..., Fatima zata zo daukan amaryar a gaya mata ta shirya ko kuma ba zata zo ba a gaya mata tayi zamanta?" Ta dago suka hada ido, he looks just as she imagined he would, older, stronger and very confident, but then he is still the Sadiq she knows, the Sadiq she fall in love with, her husband, the father of her son, it feels like not a single day has passed. It feels like kamar dazu ne aka tashe su daga bacci aka ce su je ana kiransu a palon Takawa marigayi.
Sati daya chif bayan nan aka mayar da auren Sadiq Abdallah da Khairat Faisal Abdallah. Daurin auren ya samu halartar kafatanin 'yan'uwa da abokan arziki daga barin khairat, a bangaren Sadiq kuwa jirgi guda aka chika da manyan mutane daga Nigeria suka je suka halarci daurin auren. Abin ya kayatar sosai. A take mujallu da jaridu na duniya suka yi ta watsa labarin auren saboda ana ganin wani karin kulla zumunci ne a tsakanin kasashen musulmai. Wannan tamkar wani ci gaba ne ga musulunci da musulmai baki daya. Ana gama daurin aure ango ya dauki amaryarsa suka tafi umra dan nuna godiyar su ga ubangiji akan dawo musu da rayuwarsu da yayi, da kuma neman taimakonsa akan dukkan abubuwan da zasu saka a gaba. Sai da sukayi sati biyu sannan suka dawo Riyadh, daga nan kuma amarya ta fara shirye shiryen biyo angonta Nigeria amma shi kam ango yace ba zai jira wannan fi'ilin sai amarya ta tare ba dan haka shi kawai sai ya tare a gidan amaryar. Ajjiyar da aka yi masa ta three full decades ya zage yake ta karba. It is like nothing has changed, jin su suke kamar sanda suna America farkon auren su. Duk abinda suke kuma hankalinsu yana kan sultan, suna keeping tabs on him. Sai da aka kammala gyaran gidan da Takawa ya saka ayi masa sannan amarya ta tare. Kamar yadda Daddy yayi alkawari, Mommy ya bawa private jet dinsa suka taho tare da Nani da wadansu zababbun mata daga fada suka dauko amarya daga Riyadh zuwa Nigeria. Wannan shi ya kara dankon zumunci tsakanin Ummee da Mommy.
Episode Ninety Seven : The Real Prince
Bikin Amir aka fara. Babu abinda Ummee da Takawa basu yi masa ba. Duk wani gata da 'da yake nema a gurin iyayensa Amir ya samu a lokacin bikinsa, sanda za'a tafi dauko amarya Ummee hana ni zuwa tayi, tace maiduguri yayi nisa bazan je ba, amma sanda aka kawo amaryar direct fada aka kawo ta gurin Ummee, ni kuma ina zaune a hannun daman Ummee. Sai a lokacin naga abinda Amir yake yiwa naci, ba wai kyau ne da yarinyar na kuzo mu gani ba, a'a, nutsatstsiya ce sosai, kana ganin ta kasan she is well brought up, har cikin raina ina kyautata zaton cewa Amir yayi dacen mace ta gari insha Allah. Washegarin da aka kawo Aisha, ni da Sultan muka shirya musu dinner. Takanas na kira saratu da fa'iza suka taya ni organizing dinner din, a cikin fada muka karbi hall akayi, sultan ya zuba kudi sosai, kuma abin ya kayatar sosai. Bayan an tashi daga dinner Amir ya sake kawo min Aisha har gida muka sake gaisawa. Haka kawai naji ta kwanta min a rai.
Saratu da Fa'iza kam by now sun fahimci cewa auren iyayensu ya rabu amma bana jin sun san dalilin rabuwar auren. Ba laifi sun dangana, dan suna yiwa Ummee biyayya dai dai gwargwado, Ummee kuma kullum tana jan su a jikinta, dan komai zatayi sai ta hada da daya daga cikin su. Abbas har yanzu basu shirya da Hajiya ba, dan har yanzu anan gurina yake komai nasa. Yaji shawarata kuwa, dan ya koma makaranta, shi da kansa yaje ya nemarwa kansa admission, saboda sunan Takawa da yake amfani dashi bai sha wahala ba gurin neman admission aka bashi, tunda ya fara zuwa makaranta ya tattara harkar sarautar ya ajiye a gefe ya rungumi karatunsa. Dama ashe ba wai so yake ba tunda ba'a jininsa take ba, kawai dai dan ana matsa masa ne shi yasa yake yi. Ya nuna min rashin jin dadinsa game da kafsa masa da Amira tayi, ni kuma nayi masa alkawarin zan samo masa mata wacce tafi Amira komai.
Na sami wani private hospital mai kyau, likitan su kwararre ne a harkar gynecology, nayi booking anan zan haihu. Sun yi min aune aunen duk daya kamata suyi min kuma sun gayamin zanke zuwa duk sati ana dubani, tunda yanzu edd na saura sati uku ya cika. Likitan yayi noticing high bp na, kuma mun zauna munyi magana dashi akan irin kalubalen da zan iya fuskanta. Na riga na sani, tun sanda na samu ciki, amma so far Alhamdulillah, dan lafiya lau nake bani da wani problem in banda bp din da take high. Rannan muna palona ni da sultan, ina zaune akan kujera shi kuma yana kwance akan kujerar ya dora kansa akan cinyata muna kallo, na saka hannuna absently ina shafa gashinsa, ina jin cikarsa da laushinsa, nace "wannan gashin dai ya kamata a rage shi, in ba haka ba zan fara yi maka kitso" ya danyi dariya yace "bismillah" na fara tsagawa da hannuna ina kitsawa, yace "ouch, da zafi fa" nace "kar ka bada ni mana, ka tsaya inyi maka mai kyau" ya biye min kuwa ya tsaya, nayi ta jagwalgwala masa gashin, nayi masa kitso guda biyar, ya tashi zaume yana shafa kan ni kuma ina tayi masa dariya, shine har da zuwa bedroom ya kalla a madubi, ya dawo ya tsaya yana kallona yace "da ace ni macene da maza sai sun bi layi sannan zan zaba" nayi dariya ina kallonsa nace "Allah yasan nufin jaki shi yasa bai bashi kaho ba" ya koma daki sai gashi da comb ya dawo ya kwanta ya dora kansa a cinyata yace "tsefe min" na karbi comb din ina tsefe masa ina tajewa. Yana kwance yayi shiru kamar mai bacci amma ba baccin yake ba. Na fara magana "I fell in love with you the second time I saw you" ya gyara kwanciyarsa yayi rigingine yana kallona yace "a dinner din Hafsat?" Na girgiza kaina nace "A Hilton" ya dan bata rai alamar tunani yace "that's the first time" na girgiza kaina nace "no, it is the second. The first time dana fara ganin ka a TV ne. Kuna fada da wani akan titi 'yan jarida suna dauka, daga baya aka kirawo police suka zo suka kama ku, they handcuffed you and you were smiling, it was as if you were enjoying yourself" ya danyi murmushi yace "I was" na cigaba "wannan shine dalilin da yasa sanda muka hadu a Hilton, duk da cewa naji wani abu a zuciyata game da kai amma sai na baka wrong information, saboda a lokacin na riga na saka a zuciyata cewa you are a bad person. But my love for you is too strong. A hankali na fara gane ainahin ko kai wanene and the love I have for you grow stronger" duk maganar da nake idona yana cikin nasa hannuna kuma yana kan fuskarsa ina shafawa. Na cigaba "a lokacin burina akan ka gida biyu ne, na farko shine in aure ka, kuma Alhamdulillah, wannan burin nawa ya cika" wani tattausan murmushi yayi min, ya daga gira yace "and how does it feel?" Nace "what?" Yace "how does marrying me feel?" Na mayar masa da murmushinsa nima nace "great, really great, better than I imagined it would" yace "good. Then what is your second wish?" Na danyi shiru ina tunanin ta yadda zan gaya masa ba tare da yayi wa abin wata fassara ta daban ba, nace "burina na biyu shine ina so mutane su sanka kamar yadda na sanka" ya dan bata fuska yace "bangane me kike nufi ba?" Nace "Mu mutane muna da wata halayya, abinda duk muka fara gani ko ji a dangane da wani shine abinda muke rikewa a ran mu, har sai wani abin ya faru da zai chanza mana ra'ayin mu. Ka tuna ranar da na ganka a hanya ka tare hanya da motar ka ka hana mutane wucewa?" Ya danyi murmushi yace "Of cause I remember" nace "a lokacin mutanen da suke gurin gaba dayansu babu wanda yake fadin abin alkhairi a tare da kai, wani a gurin bai ma taba ganin ka ba, dan haka abinda yaji an fada a gurin shine abinda shima zai tafi yana fada a gaba. Wannan misali daya kenan, na tabbatar akwai examples da yawa na irin wadannan abubuwan da suka faru tsakanin ka da mutane. Yanzu da ace zaka yi baddakama ka fita cikin mutanen gari kayi musu tambaya a game da kai nasan da zaka sha mamakin amsoshin da zasu baka. Na san ka chanza, wadanda suke tare da kai ma duk sun sani, amma sauran mutanen gari fa? Ta yaya zasu sani?" Yace "I don't care about mutanen gari. I never care about what people say akaina" nace "but I do. It has always been my dream to clear your name. To make people know you and love you" yace "what are you going to do then? Are you going to change their minds?" Nace "No, but I will do something that will create something that will make them change their minds" ya dan dauke kansa daga kallona yana kallon side, na saka hannu na juyo fuskarsa gurina nace "please sweetheart" yace "Maimunatu bana son kije kiyi abinda zaki shiga trouble a kaina. We are happy the way we are." Na langwabar da kai nace "nayi maka alkawarim abinda nake son yi babu trouble a cikin sa, ina cikin gidan nan zan yi ba tare dana fita ko gate ba. Please just say yes" kamar ba zaiyi magana ba sai kuma yace "OK. Amma duk abinda zakiyi sai na sani tukunna" na sunkuya nayi kissing dinsa a goshi nace "Thank you".
Na riga na gama tsara duk abinda nake so inyi, dan haka washe gari tun da nayi sallar assuba ban jira sultan ya dawo daga masjid ba, na fita na tafi dakina. Na dauko laptop dina na dube project din da nayi akan sultan. Na zauna na fara editing, nayi summarizing ya zama page daya kawai, sannan na kara abubuwan da nayi learning recently akan sultan. Sai da na gama kuma sannan nazo na fassara da hausa. Sai ya zama kamar ace front and back ne, front din turanci back din hausa. Sai dana gama sannan kuma nazo na zauna na sake redrawing zanen sultan dana taba yi, exactly irin wancan sai dai a wannan ma na kara abubuwan da na kara a wancan. Ina cikin zanen sultan ya shigo, ya zagayo bayana ya tsaya yana kallon zanen yace "hmmm, wannan shine plan dinki?" Nace "yes" ya kalli zanen yace "ni fa nace miki shape din kaina ba kamar mangwaro bane ba. So kike ki rage min kasuwa dan kar wata ta shigo ko?" Kalmar watan daya fada naji ta daki kirjina, kawai sai na hango shi a idona tare da wata, na ajiye pencil din hannuna na rufe computer ta na mike tsaye, ina jinsa yana yi min dariyar ganin yadda na bata raina amma ko kallonsa banyi ba saboda wani haushinsa da nake ji. Ya rike hannuna yana kokarin juyo dani in kalle shi amma naki, ya rabu dani ya rungume ni ta baya ya saka kansa a wuya na yace "fushi kika yi Love?" Bance masa komai ba, yace "wasa fa nake miki" nace "I know, but it still hurts" yace "rikon da kika yi wa zuciyata Moon bana jin da akwai wacce take da karfin karbarta a hannunki. My heart was made to love you, only you. I was born to love only you. Ban taba son wata ba kafin ke kuma bazan taba son wata ba bayan ke. Only you" ya juyo dani yace "to yimin murmushi mana in gani" na sunkuyar da kaina ina son in dan kara tsahon fushin nawa, chakulkuli ya far yi min, nan take na fara dariya har kamar zan fadi, yayi saurin rike ni ya hada da jikinsa shima yana dariyar. Muka juya muna kallon zane na, yace "to taya zaki raba wa mutane? Binsu za kike yi gida gida kina basu?" Nace "Nope, am going to use a helicopter" bude baki kawai yayi yana kallona.
Amir na kira a waya na gaya masa duk abinda nake so, wajan azahar yazo muka sake yin maganar dashi, na cire pages din dana keso na bashi a flash, na dauko kudin dana san zai bukata na bashi amma yaki karba ya tafi. Da daddare sultan yana gurin Takawa ni kuma ina zaune ina cin abincin da Ummee ta aiko min dashi sai ga wayar Mommy, na dauka na gaishe ta tace "Moon mai ya faru ne?" Nasan maganar da take nufi amma nace "Mommy akan me fa?" Tace "The whole of Abuja is on fire akan sultan. Yanzu friends dina sunfi uku da suka kira ni suna tambayata" a raina nace 'sako na ya isa kenan' a fili kuma nace "me ya faru ne Mommy" tace "dazu da yamma helicopter yayi ta yawo a gari yana watso takardu, unguwa unguwa, takardun zanen project dinki" sai kuma tayi shiru, jin bance komai ba tace "Moon, did you do it?" Nace "yes Mommy" tace "why?" Nace "Mommy just ke da abokan aikin ki a office ku shirya, you will have alot of cases this week".
Hakan kuwa akayi, kusan duk garin Abuja lungu da sako, unguwannin masu kudi da kuma unguwannin talakawa babu wanda bai samu sako na ba. Nan take 'yan jarida suka samu abinyi, sultan kin zuwa yayi office a satin, Takawa kuma yace a rufe gate din palace kar abar wani dan jarida ya shigo. Kamar yadda nayi tsammani, talakawan duk da sultan yake taimakawa, wadanda nasan labarinsu da wadanda ban sani ba, haka suka ringa fitowa suna gaskata maganganuna na cikin takarda ta, wadansu ma shi kansa sultan ya manta dasu, haka aka ringa dauko dukkan files dinsa na gurin police ana resolving cases din. A haka har zancen orphanages dinsa ya fito shima, 'yan jarida kam sun samu abin yi, nan suka dukufa bincike har suka tonawa dan majalissar da yace shine yayi orphanage din asiri. A satin, kusan duk jaridar daka dauka hoton sultan ne a front page dinta, anyi masa title 'Our Prince' wadansu kuma su rubuta 'Our Lion'. Sultan kam har yanzu bai ce komai ba, in ma na kunna TV ana maganar sai ya chanza channel. Ni kam babu abinda nake yi sai godiya ga ubangiji da yasa plan dina ya zama successful. Sultan's name is now clear a cikin mutane. Babu wanda in sultan ya wuce zai zage shi, ko an samu mai zagin ma, to kuwa tabbas za'a samu masu kare mishi. 'Ya'yana ba zasu tashi ana musu gorin babansu was a criminal ba. Wannan kenan.
Satin biki ya kama. Gidan mu ya chika kamar yadda aka saba in za'ayi biki. Ballantana wannan da yake bukukuwa ba biki ba. Hatta zainab din ya walid an dauko ta an dawo da ita abuja, anan za'ayi bikin baki daya. Hafsat ta dawo gidana, tace can yayi hayaniya da yawa, dan haka daga nan muke shiryawa mu fita tare. Sultan ma tunda bikin yazo kullum suna tare da su Ya walid, amma kuma hankalinsa gaba daya yana kaina, dan badan ummee ta saka baki ma ba da ba lallai ne ya barni zuwa bikin bama gaba daya. Yanzu ma kuma babu kwana, sai dai inje in wuni da daddare in dawo gida. A tare muka hada amaren mu da angwayen mu muka kama su rana daya duk a gida. Akayi mothers eve ranar thursday, ranar friday kuma za'ayi wuni, Saturday a yi daurin aure, da yamma akai amare sannan da daddare ayi dinner. An kai dinner din dare ne saboda ana son Fadila amaryar ya Habeeb ta samu damar halarta itama. Tun a ranar Thursday da daddare na lura kafafuwana sun fara kumbura, nasan wannan normal ne ga mai tsohon ciki musamman kuma ga hidimar biki da muke yi, dan haka da daddare na kwanta da wuri na dora kafata akan pillows, sam ban nunawa sultan ba saboda ba karamin aikinsa bane yace bazanje ranar wuni ba, ranar wuni muka shirya da sassafe muka fita, aka wuni ana shan shagali, sai dare sannan muka dawo gida. Muna zuwa gida Hafsat ce tayi min maganar yadda kafa ta ta kumbura suntum, tace "Moon you should stay home tomorrow, ki huta, daurin aure ne sai kai amare, dinner da daddare za'ayi kafin nan kin huta" nasan gaskiya take gaya min, I already have high bp, wannan kumburin nawa is not normal edema, it may be pre-eclampsia, amma sai nayi tunanin ai in naje goben ba wani abun zanyi ba, zama kawai zamuyi, in za'aje kai amare da dauko amarya zan iya zama na inki zuwa, sai da daddare in je dinner. Na riga sultan kwanciya dan haka na rufe jikina bai ga kumburin ba, kuma da sassafe ya fita, zasu fara zuwa bauchi daurin auren yaya Habeeb sannan a dawo abuja a daura na ya Walid da na Amina. Banbi shawarar Hafsat ba saboda ina ganin babu yadda za'ayi in zauna a gida bayan ana can ana shagali a gidan mu. Sultan yana tafiya nabi Hafsat muka tafi gida. Komai lafiya lau yake tafiya har aka yi daurin aururruka aka gama, aka zo hidimar kai amare. Dama already wadanda zasu dauko Fadila sun riga sun tafi, sai aka tafi kai zainab tunda ita ta gida ce ba sai an jira anzo an dauke ta ba. Basu dade da tafiya ba sai ga masu daukan Amina sun zo, nan fa kallo ya koma sama, duk aka fito compound ana kallonsu dan wani sabon bikin suka bude, sun yi shigar su irin ta yarabawa sunyi kyau sosai, sun taho da kaya sukace a bawa Amina ta saka, ina daga kwance naga kallo zai barni dan haka na mike nima na fita, wata 'yar matashiyar budurwa ce tazo ta tsaya gaban Amina ta karanta wata doguwar takarda mai dauke da dogon jawabi akan irin soyayyar da Ibrahim yake yi mata da alkawarin da yayi na zai rike ta amana, inta amince to ta bisu su tafi, in kuma bata amince ba to ta zauna a gida. Daga haka ta mika wa Amina hannu, Amina ta saka hannunta a cikin na yarinyar, nan take guri ya kaure da murna. Hayaniyar gurin ce tasa naji kaina yayi wani mugun sarawa, na rike kan da sauri, ganin babu wanda ya lura dani ya saka na lallaba na koma daki, ina duba hannayena naga sun kumbura suma, na kwanta akan gado na lumshe ido na ina jin ciwon kaina yana karuwa ga kide kiden da akeyi tamkar a cikin kaina suke kadawa. Na lalubi wayata na kira Hafsat amma wayar tana ta ringing bata dauka ba. Na koma na kwanta. Cikin hikimar ubangiji aka daina kidan, ina jin karar motoci alamar an tafi kai amina itama. Take naji gidan tsit dan kusan babu kowa a manya, babu kuma wanda yasan ina dakin, kowa zai dauka na tafi kai daya daga cikin amaren. Na danji kan ya rage ciwon, na tashi na nemi jakata na sha magungunana sannan na koma na kwanta. Take bacci mai nauyi ya dauke ni. Muryar Mommy ce ta tasheni, tana tabani tace "Moon dama kina gida? Ya akayi kika zauna ke kadai? Da wani abun ya faru fa?" Ni dai bance mata komai ba, tunda wani abun bai faru ba ai shikenan. Har yanzu akwai ciwon kan, na tashi zaune ina rike kaina Mommy tana ta jera min sannu, na kalli agogo naga har anyi magrib, dan haka na shiga toilet nayo alwala, ina dawowa dakin na kalli fuskata a madubi naji gaba na ya fadi, gabaki daya fuskar ta kumbura, na kalli hannayena naga har kyalli suke. I really need to go to the hospital right now amma bana son in tayar wa da mutane hankali ana cikin biki. Na tayar da sallah, nayi magrib da isha gabaki daya, ina kallon mutane sai shirin tafiya dinner sukeyi amma ni kam nasan wannan dinner din babu ni a cikin ta. Na koma nayi kwanciyata. Mommy ta shigo ta samu guri ta zauna tana kallona. Nace "Mommy baki fara shirin tafiya ba?" Tace "Moon ina zanje baki da lafiya? In naje ma ba zanji dadin dinner din ba, dan hankali na biyu zai rabu" sai naji babu dadi a raina, dan nasan kawayen Mommy da yawa zasu je gurin kuma za'ayi ta nemanta, nace "Mommy kiyi tafiyar ki kawai, ai ba wani abin ne yake min ciwo ba, kawai dai ina bukatar in huta ne shi yasa ba zanje ba" ta jawo pillow tana murmushi tace "nima ina bukatar hutun ai" nayi murmushi, dan nasan babu abinda zan gaya wa Mommy wanda zai saka ta tafi gurin dinner din nan ta barni a gida, God bless our mothers. Hafsat ma ta shigo tayi tayi Mommy ta tafi ita ta zauna amma Mommy taki yarda. Ni dai daga nan na koma bacci. Karar waya ta ne ya tashe ni, na duba naga 'my Sultan' na dauka ina jin ciwon kaina yana karuwa, yace "Moon baki fa lafiya me yasa baki kirani ba?" Ji nake kamar a cikin kaina yake maganar, nace "ai muna tare da Mommy, babu wani abu, kayi zamanka in an tashi sai kazo mu tafi gida" yace "you dey craze? Ya zanyi in zauna anan babu ke? Am coming right away" daga nan ya kashe wayar. Mommy tana zaune tace "zuwa zaiyi?" Nace mata "eh, dama ki shirya, in yazo kawai sai mu tafi gida ke kuma sai ki tafi gurin taron" ta gyada kai tace "bara yazo din tukunna sai in shirya. Ina baba gajin ki? Anan gurinki take kwana ko?" Nace "eh, anan take kwana. Ummee ma ta karo min wata baba Sa'a". Muna tare da Mommy sultan ya aiko a gayamin yazo, Mommy tace ace masa ya shigo dakin, ita kuma ta fita ta tafi nata dakin. Ina kwance ya shigo, ya tsaya a bakin kofa, na tabbatar ya lura da yadda jikina ya kumbura, yace "menene yake miki ciwo yanzu?" Nace "ciwon kai ne, sai jiri da nake ji inna tashi" ya karaso ya zauna a bakin gadon ya taba wuyana yace "your temperature is also high. BP din ne ko?" Na gyada masa kai. Yace "dama abinda nayi ta lissafi kenan. Wannan hayaniyar da zirga zirga is not good for you" na kirkiro murmushi nace "an gama ai. Babu dadi idan aka ce banzo ba, Amina babu abinda bata yi min a bikina ba. Ga su ya Walid suma ba zasu ji dadi ba" ya bata rai yace "da baki zo ba duk zasu fahimta, ai sunsan condition dinki" bance komai ba na rufe idona, dan maganar ma karamin ciwon kan take yi. Mommy tayi knocking ya tashi ya bude mata, ta shigo tana kallonsa tace "zaku tafi ne ko anan zaku zauna?" Yace "gwara mu tafi can din dai tunda yafi shiru zata fi hutawa sosai" tace "hakane, dan ana dawowa daga gurin dinner wanda bashi da high bp ma sai nashi ya tashi" ta jiyo tana kallona na dan yi mata murmushi nace "bye Mommy" tace "bye-bye, sai munyi waya" sai da muka ji tashin motar ta sannan sultan ya kama ni na mike tsaye muka fita, a hankali muke tafiya saboda jiri da nake ji, daga karshe ma dai dauka na yayi ya sakani a mota, ya zagaya ya shiga ya kunna motar yana kallona, na kirkiri murmushi nayi masa shima ya mayar min, amma nasan nashi murmushin bai kai zuci ba. Ya kama hannuna daya ya rike a hannunsa daya, yayi intertwining fingers din mu ya dora akan gear sannan ya tura hannayen mu a tare muka saka gear muka fara tafiya a hankali, hankalinsa rabi akan titi rabi akaina, hannunsa daya akan stirring wheel daya a cikin nawa. Na kwantar da kaina a jikin kujera ina jin dadin kamshi da sanyin motar, amma maimakon inji bp dina yana sauka sai naji yana kara hawa, na kalli sultan na tina da ranar dana fara ganinsa, a hankali naga ya fara zama dishi dishi, this is my worst fear tun sanda na samu ciki, preeclampsia, a raina nace 'ko yanzu na tafi, at least nayi wani abu a rayuwata".
Episode Ninety Eight: My Baby
Pre-eclampsia rare ciwo ne na masu tsohon ciki. Shine ciwon da yake saka mata convulsions (jijjiga) during labor. Alamominsa sune matsanancin hawan jini, kumburi, jiri, matsanancin ciwon kai, sensitivity to light, blurred visions etc. Matan da suke at risk of samun ciwon sune wadanda already suke da hawan jini kafin su samu ciki, wadanda mahaifiyar su ko sister din su ta taba yi, yara kanana da suka samu ciki da wuri ko kuma manya wadanda shekarun su suka ja sosai. In kina da ciki kuma kika ga kina da wadan nan alamomin dana lissafa a sama to kada ki yarda ki fara labor, it is very deadly, za'a iya rasaki ko babyn ko duk ku biyun, ko kuma ki samu wani mugun ciwon, wani lokacin har hauka ake haduwa dashi. In baiyi tsanani ba kuma cikin ki bai tsufa sosai ba, ana iya control dinsa, in yayi tsanani best solution shine ki tafi asibiti ayi miki aiki a cire babyn. Shikenan.
Na rintse idona ina lissafa condition dina, a take na yanke shawara. Na bude idon na sauke su akan sultan, a hankali nayi magana "sultan stop the car" ya dan kalle ni yaga am serious sai yasa signa yayi packing a gefen titi. Ya juyo gaba daya yana kallona "Moon menene? What do you need? Jikin ne?" Na danyi masa murmushi kadan nace "asibiti zaka kaini ba gida ba" ya dan tsorata kadan "is the baby coming?" Na girgiza masa kai, "asibiti zamuje, za suyi min aiki su fitar da babyn" a take naga tashin hankali a rubuce a fuskarsa, na rike hannunsa sosai nace "don't do this sultan please, I need your support and strength. Please don't freak out" ya dan nutsu kadan yace "me yasa kika ce zasu yi miki aiki? Kince kuma ba labor kike ba" nan nayi masa bayanin duk situation dina da risks din da naje facing. Sosai naga hankalinsa ya tashi, ya daki stirring wheel da hannunsa yace "damn it, I hate that Ibrahim" na bata rai nace "Ibrahim bai dora min ciwo ba Allah ne ya dora min. Ba akaina aka fara ba ba kuma akaina za'a gama ba. Tunda na samu ciki lafiya lau nake, ko mugun laulayi banyi ba, wadansu matan daga ranar da suka samu ciki ba zasu samu lafiya ba har sai sun haihu. Wadansu matan talauci ya saka ko abinci mai kyau basa samu a lokacin da suke da ciki, wadansu matan basa samun medical care, wadansu matan zasi hadu da ciwo irin nawa amma basu san menene ba kuma su zo su fara labor a haka, a karshe su samu matsala koma su mutu gaba daya. Amma ni na samu komai, komai da nake bukata na samu, abinda nake bukata a yanzu shine support dinka, together we will get through this" ya dan nutsu ya dakata yana kallona, na mayar da idona na rufe inajin kaina tamkar zai rabe gida biyu, ga wani jiri da nake ji duk da cewa a zaune nake. Naji hannun sultan yana shafa fuskata, na dan bude idona ina kallonsa, na rike hannunsa da yake kan fuskata nace cikin sanyin murya "I need you to be strong" ya hadiye wani abu a makogwaronsa yace "yanzu me zamuyi" nace "asibiti zamuje. Amma please bana son ka kira kowa, Mommy da ummee in suka zo zasu kara min pressure ne. We can do this alone. Everything is going to be alright" da hannu daya ya dauko wayarsa yayi dialing, na fahimci doctor na yake kira, yana dauka ya fara masa bayanin abinda nace masa da kuma symptoms dina, banji mai doctor din yace masa ba yace "alright, we are on our way" ya kashe, hannun na yana cikin nasa ya kunna motar yayi reverse muka dau hanyar hospital, na koma na kwanta na rufe idona. Sama sama naji shigowar mu asibitin, naji sultan yana gayawa doctor a waya cewa gamu mun iso, hannunsa daya a rike da nawa dayan kuma ya saka yana shafa fuskata, na dan bude ido da niyyar in kalleshi amma hasken fitulun cikin asibitin ya saka na mayar da idona na rufe ba tare dana kalle shi din ba, naji zuwan doctor gurin mu, ya kunna fitilar wayarsa ya haska ni, na kara runtse idona saboda bana son hasken, yace da sultan "gwara da Allah yasa kuka taho yanzu baku zauna kunce sai safe ba, she is in critical condition and we will have to take the baby out now" sultan yace "yes, haka tace". Doctor din ya tafi sai ga wasu nurses sun kawo gadon daukan marasa lafiya, sultan ya chika hannuna ya zagayo ya dora ni akan gadon aka tura ni zuwa cikin asibitin. Ko sau daya sultan bai cika hannuna ba har aka kaini dakin da za'a shiryani. Doctor ya kawo wa sultan takardu yayi signing, har zai fita sultan ya tsayar dashi ya fara magana muryarsa kamar wanda zaiyi kuka yace "doctor please, nasan kasan aikinka ba wai koya maka zanyi ba, but please if anything should arise, in kana ganin Moon zata iya samun wata matsala, please doctor just forget about the baby and save my wife. Gwara in rasa shi akan ace wani abu ya same ta" doctor ya dawo ya tsaya a gaban sultan ya dora hannunsa akan kafadar sa, fuskarsa da murmushi yace "Our Prince, insha Allah nayi maka alkawarin zan kawo maka matarka da dan ka lafiya lau, babu abinda zai same su duk su biyun" sultan ya danyi murmushin yake yace "thank you doctor" doctor yace "amma nima ina bukatar wani taimako daga gareka, akwai maganar da zamuyi ka biyo ni office yanzu" sultan ya dan juyo ya kalleni yace da doctor din "bazamu iya maganar anan ba? Cos I don't want to leave her alone" doctor yace "OK, sai muyi anan din" suka zauna akan kujera doctor ya fara magana yace "kaga dai halin da take ciki yanzu, dan haka dole ba zamuyi mata anaesthesia ba, muna bukatar control over her bp, in muka yi mata allurar bacci ba zamu samu wannan control din ba, we need to keep her awake through the entire operation. Da akwai aikin da ake yi na ido biyu, zamu kashe lower part of her body yadda ba zata ji zafin komai ba har mu gama. Taimakon da nake nema a gurinka shine ina so ka shiga operation room din a tare damu ka zauna a kusa da ita kana yi mata magana mai dadi wacce zata kwantar mata da hankali" sultan yayi saurin girgiza kansa yace "I can't watch" doctor yace "you won't. Zamu saka labule a saman cikin ta mu raba ta biyu, her upper part tana gurinka zaku ke maganar ku, her lower part yana gurin mu muna aikin mu, baza kusan ma muna yi ba sai in mun gama muyi muku magana. Just don't let her sleep" sultan ya gyada kai yace "OK. I can do that" doctor ya mike tsaye yace "and we will need blood, just in case" da sauri sultan yace "you can take mine" doctor yayi murmushi yace "in yayi matching da nata ba. Zamu gwada mu gani in yayi dai dai sau mu dauka, in baiyi dai dai ba kuma sai ka samo mana wasu 'yan'uwanka ko nata a gwada a cikinsu ko za'a samu". In less than one hour da zuwan mu asibitin har an shirya ni suma doctors din sun shirya, duk abinda suke ina jinsu amma bana cewa komai saboda magana ma kara min ciwo take, idona kuma a rufe saboda bana son haske. Sai da aka tura gadona cikin theatre room sannan nayi nadamar cewa da nayi kar a kira kowa, ji nayi babu abinda nake son gani irin Mommy na da Daddy na, kuka naji yana taho min, nayi sauri na mayar dashi dan nasan ina fara kuka zan kara wa kaina ciwo kuma sultan zai kara rikicewa, so far dai yayi abin kirki sai dai ko dai dai da second daya bai matsa daga kusa dani ba. Muna shiga suka yi min wata allura a tsakiyar bayana mai dan karen ciwo, amma tana shiga naji kamar an yanke min daga cikina zuwa kafafuwana, kamar ba'a jikina suke ba, na juya ina kallon sultan wanda idonsa ya kada yayi jawur nace "ka kira daddy ka gaya masa. At least they will pray for me" ya dauko wayarsa, na lura hannunsa har rawa yake, bai iya kiran Daddy ba sai text ya tura masa. Aka sauko da labule aka raba jikina biyu. Sai ya zamana kamar ba'a daki daya muke da doctors din ba, jikina ya bani sun fara aikin amma banji komai ba. Na kalli sultan daya kankame hannuna kamar za'a kwace ni, nace "naji kamar cewa akayi kayi min hira" ya danyi murmushi nervously yace "labarin me kike in baki" nace "anything. Kamar the best day of your life" yace "da akwai ranaku da yawa da zan iya kira da best days of my life. Kuma duk days din da akwai ki a ciki. Because you are my life. Rana ta farko ita ranar dana fara ganinki. It was the day that my life begun. Daga nan sai days din da muka yi spending a America, I will never forget those days. Daga nan sai ranar daurin auren mu and then our first night, you took away not only my body but also my soul. Then, ranar da Takawa ya kira ni da his little love and asked for my forgiveness. Sai ranar dana fara ganin Ummee na. Sai kuma ranakun mu a Maldives" yayi murmushi yace "seriously ban so muka dawo ba" nayi murmushi nima, yace "rana ta karshe a yanzu ita ce yau, ranar da zamu ga result of our love. Zamu raine shi together, mu bashi tarbiya da soyayya da kulawa, we will give him all the things that I missed in my childhood. He is going to grow up to be better than me saboda he have the best mother in the whole world" I was so lost a maganganun sultan har na manta ma aiki ake min, sai kawai kukan baby muka ji, muka yi murmushi a tare, doctor ya dan daga labulen yace da sultan "a miko maka shi ka rike?" Sultan yayi saurim girgiza kai yace "babu hannun da zan rike shi dashi, I won't let go of her hand. Sai dai ku ku rike shi a wajanku" doctor ya saki baki yana kallon sultan, shi kuwa ko a jikinsa, nace "doctor kawo min shi ni in rike shi" doctor yace "ke kina ji da kanki ina ke ina rike baby? Ka rike ta da hannu daya sai ka dau babyn da dayan hannun, shi yasa Allah yayi maka hannu biyu saboda kayi two things at the same time. Kuma idan yaron nan ya girma sai na gaya masa" ya koma sai gashi ya dawo da baby a cikin towel, har yanzu kuka yake ta tsanyara wa, sai kuma naga sultan ya cika ni ya tashi ya karbe shi, fuskarsa cike da farin ciki, na fara lissafin yanzu fa dinke ni akeyi sai kuma nayi sauri na kawar da wannan tunanin daga raina, sultan ya zauna ya juyo min da fuskar babyn yace "look Moon, he is perfect. Dake yake kama" na kalli babyn, ba dani yake kama ba, hancinsa da bakin sa irin na sultan, idonsa da kuma kalar fatarsa irin nawa ne. Na saka hannu na shafa kansa nace "Allah yayi maka albarka".
Sai da aka gama dinke ni tas, suka gwada bp dina suka ga cewa is almost stable sannan sukace zan iya yin bacci yanzu, suka yi min allurar bacci. Tun kafin a gama zare allurar nayi bacci. Sanda na farka a wani dakin daban na ganni, babu ciwon kan kuma gani na ma ya fara dawowa dai dai, sai azaba da naji a gurin da aka bude cikina, na dora hannuna a gurin naji kamar inyi ihu saboda zafi, na hango sultan a zaune akan sallaya, daga alama sallah ya idar, babu kowa a dakin sai shi kadai. A hankali nace "Sultan" ya juyo da sauri ya taso yazo gurina "Moon? Wani abu yana miki ciwo? Me kike so?" Na nuna masa gurin aikina yace "bara in kira doctor" nace "Mommy tazo?" Yace "suna can sun hada kai ita da Ummee suna kuka a waje" na danyi murmushin yake, kafin ya bar gurin wani baccin ya sake dauke ni. Farka wa ta ta biyu Mommy ce a zaune a kusa dani, idanuwanta sun kumbura kamar zasu fado kasa, fuskarta tayi jawur. Na jima ina kallonta bata san ma na farka ba. A hankali nace "Mommy ki daina kuka, ba mutuwa zanyi ba, the worst part is over. Allurar bacci ce kawai take dibana" ai kuwa kamar cewa nayi Mommy yi kuka, nan da nan hawaye ya fara zuba, ta rike hannuna "Moon na shiga uku, ina can ina wurin dinner ke kina asibiti ana bude cikinki. Why didn't you tell me?" Nace "am sorry mother" na kalli agogon dakin naga 4:30, amma kuma ga rana ina kallo ta taga, this means har gari ya waye yamma tayi kenan. Na duba naga drip a hannuna, shi yasa banji yunwa ba. Akwai sauran ciwon kan kadan amma ina gani tas yanzu. Kumburin ma ya ragu. Nace "Mommy ina Daddy?" Tace "dazu ya tafi, ya zo sau biyu yana ganin ki, sun hana shigowa ne saboda kar a tashe ki. Shima wancan rigimammen an fita dashi yana ta tsala kuka, daga ganin sa acici ne. Bara inje in karbo shi sai a gwada feeding disa ko zai sha" har takai bakin kofa sai ta juyo tace "Allah yasa Khairat ta bani, dan ta hana kowa, duk wanda zai ganshi sai dai ya kalle shi a hannunta" nayi murmushi, dama nasan abinda zai faru kenan. Ai kuwa Ummee bata bawa Mommy ba, sai gata da kanta ta taho dashi, ta zauna tana yi min sannu, ina so in sake ganin fuskarsa amma ta kudundune shi a jikinta, tace "kafin ince komai, tell me, idea din waye a cikin ku kuka taho asibiti ba tare da kun gaya wa kowa ba?" Nayi shiru bance komai ba, tace "you almost give us a heart attack. Mun dauka kuna gidan biki, du kuma sun dauka kun dawo gida" nace "we are sorry Ummee" ta shafa kaina tana murmushi tace "ya jikin ki? Menene yake miki ciwo yanzu?" Nace "babu komai" tace "gurin aikin fa?" Nace "yana yi kadan. Nasan zasu zo anjima suyi min allura" sai a lokacin ta miko min babyn, sai kuma naji inajin kunyarta naki karba, Mommy ce tazo ta dan daga ni kadan tasaka min pillows a baya na sannan ta karbi babyn ta dora min a kan kirjina, na saka hannu na tare shi dan kar ya sauka kan ciwo na, ni duk kunyar Ummee nake ji ita kuma taki ta gane ballantana ta fita. Mommy ta fahimci kunya nake ji tace "Khairat ko zaki zo muje mu gano masu gwajin jinin can ko an dace an samu wanda yayi?" Ba tare data kalle taba tace "jeki kawai Fatima, gwara in zauna a gurinta kar mu barta ita kadai" Mommy tayi ajjiyar zuciya ta daga kafada ta fita. Na rasa yadda zanyi gashi shi kuma har ya fara kusur kusur yana tabe baki zaiyi kuka, Ummee tace "what are you waiting for? Feed him gashi nan zaiyi kuka. Tun da yazo duniya baici komai ba sai dan dabino da zam zam da babansa ya bashi" ya na iya da raina, dole na gyara riga na bashi, ai kuwa da sauri ya karba kamar yasan menene, ya nutsu sosai yana sha, na kura masa ido ina kallo, I can't believe wannan perfect halittar daga jikina ta fito, Allahu Akbar shine abinda kawai zan iya fada. Na bashi ring finger dina ya rike da hannunsa, sai kawai naga ya bude ido yana kallona, nayi masa murmushi sai kace yasan me nakeyi. Ummee ta zagayo ta bayana ta lakuce masa hanci tace "like father like son" Sultan ne ya shigo ya tsaya daga bakin kofa yana kallon mu, fuskarsa filled with feelings, Ummee tayi masa alamr ya shigi da hannunta, ya karaso ya ajiye ledar hannunsa yana kallona yace "ya jikin?" Na sunkuyar da kai nace "da sauki" ya matso kusa da gadon yana kallon babyn yace "an samu abinda ake so kenan, za'a bar kunnen mu ya huta" sai da ya gama sha dan kansa ya cika sannan na gyra rigata, Ummee ta karbe shi ta saka shi a kafada yayi gyatsa sannan ta bawa sultan shi tace "zauna in yi muku pictures" ba musu ya zauna a gefen gadon ya jawo ni jikinsa da hannu daya, daya hannun kuma ya rike babyn a jikin mu, Ummee tayi mana pictures da yawa. Ya dauko ledar daya shigo da ita ya fito da fruits, ya dauko ayaba ya bare ya miko min yace "doctor yace zaki iya cin fruits" na karba na fara ci sai muka ji anyi knocking kofa, Ummee ta saka min mayafi aka turo kofar, mutane suka fara shigowa kamar va zasu kare ba. Hafsat tana kan gaba, da sauri tazo ta dauki babyn daga kan cinyata tana cewa "shine ka hanamu karasa bikin mu ko?" Hatta amare da angwayen jiya duk sunzo, a raina nace 'jiya na hana first nights da yawa' Amina tazo tana yimin sannu, Zainab da Fadila, saratu da Faiza, Huda da Aishan Amir duk suka zagaye ni, mazan kuma suka tafi suna gaisawa da Sultan. Ina kallon Ibrahim ya mika wa Sultan hannu amma yaki karba, sai ya wayance da bare min ayaba. Ana ta hayaniya ana daukan hotu a ba baby, Ummee kuwa sai cewa take a daina jagwalgwala shi kar yayi ciwon jiki. Ni kam sai kallon su nake ina jin dadi a raina. Daddy yayi sallama ya shigo, ji nayi kamar in tashi inje in rungume shi, bai kula kowa ba har masu gaishe shi ya taho gurina bakinsa har kunne, ya sunkuyo yayi kissing dina a goshi yace "well done my daughter. Barakallahu fi ki" ya zauna a kujera yace ku kawo min wannan ragon mazan daya kasa jure taron biki" akayi dariya gaba daya.
Aka mika masa shi ya karba yayi masa addu'ah sannan yace "Sultan wannan ai kayi wa Moon yawo" Sultan ya karasa kusa dashi ya leka fuskar babyn yace "wannan idon ba nawa bane Daddy, kuma daga dukkan alama sai yafi ni haske" duk akayi dariya, ya Habeeb yace "Sultan in surukai suna magana aka akan dan mutum baya amsawa" Sultan yace "Daddy ai ba suruki na bane" a raina nace 'koma waye yayi magana amsa zaka bashi'.
Doctor ya bude kofa ya shigo. Yana kallona yace "Maman baby an tashi kenan, at last" nayi murmushi na gaishe shi, ya zo dudduba ni ya bani magungunan da zansha, yayi min allura a hannu, yace "zamu sake miki allurar bacci in an jima, saboda kamata yayi ace kinyi 24hours kina hutawa" sannan ya dauko takarda yana kallon mazan gurin yace "ga result din tests din da akayi muku na jini. Abbakar Sadiq Abdallah, jininka bai yi dai dai ba" su ya walid har da yiwa sultan dariya ganin yadda ya bata rai. Doctor yace "Lawan Muhammad Dikko kaima naka baiyi ba, Habeeb muhammad dikko naka kaima baiyi ba, Faruk Muhammad dikko kaima zero" akayi musu dariya suma gaba daya "Abbas sadiq abdallah kaima baiyi ba, Abdullahi Abdallah kaima zero, Adeniran Ibrahim, congratulations, kai kayi winning, naka yayi matching, mun gwada kuma munga it's free of all blood transmitted diseases, in ka shirya sai muje mu diba" gaba daya aka juya ana kallon Ibrahim, shi kuma ya kalli sultan, sultan kuma ya kalleni, ni kuma na sunkuyar da kaina.
Episode Ninety Nine : New Little Love
Sorry for the delay guys. Na ga sakon ku akan sunan baby, naji dadin yadda kukayi responding. Mutane sun zabi sunaye kamar haka : Muhammad, Abdullahi, Ibrahim, Abubakar, Lawan da sauransu. A lissafina wadanda suka ce Muhammad sunfi yawa dan haka zamu saka Muhammad din. Masu cewa Ibrahim, I salute your loyalty to Ibrahim amma bansan ta yadda zan yi convincing Sultan ya sakawa dansa sunan tsohon saurayin matarsa ba. Lol. Love you all.
Shiru dakin babu wanda yayi magana. Ummee ce ta fara katse shirun tace "me ake jira ne wai? Ka bishi mana kuje ya dauka asaka mata" babu wanda yayi magana still. Doctor ya fahimci akwai tension a gurin sai yace "bara inje office, Ibrahim in zaka bayar din ka same ni a office amma da sauri saboda ina son in saka mata sai inyi mata allura tayi bacci, kafin ta tashi an gama saka mata" ya juya har zai fita Daddy yace "doctor bara inzo ka dauki nawa, blood group din mu daya da ita, ban san ana bukatar jini ba da tuni na bayar. Ita da Hafsat group din mu daya su kuma boys din suka dauko Mommyn su" doctor yace "that's OK" ya fita. Ummee ta mike tsaye, "NO daddyn Moon, da shekarunka zaka bada jini bayan ga matashi yayi matching?" Ta kalli Ibrahim "ko kaine bakason ka bayar?" Still idonsa akan sultan yace "it would be my honor to give my blood to her. But I think it is better a dauki na daddyn kawai" Ummee ta sake cewa "why? Ji nake kai mijin sister dinta ne? Doctor yace blood din is clean, so why?" A hankali sultan yace "I don't want his blood in her" Ummee ta juyo tace "me kace?" ya maimaita da dan karfi "I don't want his blood in her" na rintse idona ina gode Allah daya kasance babu bare a gurin duk 'yan'uwa ne, ya Walid yace "Sultan, it is just blood. Babu abinda ake transferring a cikin jini in ba ciwo ba, kuma doctors sunce the blood is clean, don't make a case out of it please" sultan ya mike tsaye idonsa akan Ibrahim yace "it is not just blood, it is HIS blood, and that's what makes it different. I am her husband and I said ba za'a saka mata jininsa ba. I would rather buy it from a total stranger than take HIS. I don't even know what the FUCK he is doing here" idanuna a rufe naji karar mari, na saka hannu na na rufe fuskata, ba sai na kalla ba nasan wa aka mara kuma nasan wa yayi marin. Ummee ce ta mari sultan. Shi aka mara amma ni naji zafin. Ummee ta fara fada muryarta har rawa take yi, na tabbata da zan iya kallon idonta da zan ga hawaye a ciki, tace "Sultan a gaba na? A gaban Daddy? I know you are spoilt but didn't knew you are this spoilt. Mijin kanwar matarka, yazo har asibiti ya dubata kuma yayi offering zai bata jininsa a saka mata amma ka zage shi? Wanne irin mutum ne kai?" Daddy yayi magana "Khairat, Ibrahim is Moon's ex boyfriend, wannna shi yasa sultan yake reacting this way" Ummee tace "dan yana tsohon saurayinta hakan bai kamata ace ya saka yayi treating dinsa this way ba. Karewar aure ji nake 'da ta haifa masa ma yanzu. Shi kuma sister dinta ya aura. Menene kuma saura a ciki? Yanzu shi baiji kunyar ganin idonka ba? Baiji kunyar Amina ba? Ko da baya so ai da akwai hanyar da zai bi yace baya so ba sai yaci mana mutunci ba. Wannan ai mu ya wulakanta ba Ibrahim ba. Ina lura da Ibrahim din tunda ya shigo bai kalli inda Maimunatu take ba har ina tunanin me yasa haka ashe shi wulakanci yake gudu" fada Ummee take kamar zata ari baki. Sai da tayi shiru Ibrahim yace "am sorry. Ban zo da nufin creating trouble ba, na kawo Amina, muna tare da su Habeeb aka kira su gurin daukan jini, at first nace banda ni doctor din yana min wasa yace ina rowar jini ne, I didn't know it will match, I didn't want to create a scene shi yasa na bari aka dauka" Daddy yace masa "it is OK Ibrahim duk mun fahimta. It was just a misunderstanding. A bar maganar haka ta wuce" Ummee tace "ya kusa wucewa dai" ta kalli sultan tace "tashi ka bashi hakuri, kuma ka raka shi da kanka gurin doctor a dau jinin sannan ka kawo a saka mata, that's your punishment for been arrogant" da sauri Ibrahim yace "No ma'am, that's not necessary. Na fahimci sultan sosai kuma banji haushin sa ba. Idan nine nasan I might do something worse than what he did. Bana son a kuma samun wata matsala akaina." Ummee tace "ba akan ka bane Ibrahim, akan sa ne, ina son yasan cewa idan yayi ba dai dai ba dole ayi punishing dinsa. So nake inga in an saka mata jinin ya zaiyi" ta juya tana kallon sultan tace "tashi ka bashi hakuri nace" Sultan ya mike kamar mai ciwon cinya, ya tsara a gaban Ibrahim kamar ba zaiyi magana ba, amma nasan sultan baya taba yiwa Ummee musu duk da kuma nasan zuciyarsa yanzu kamar zata fashe yake jinta, ya dan jima a tsaye sannan yace "am sorry. And thanks for offering your blood" ya mika wa Ibrahim hannu, Ibrahim yayi murmushi yayi shaking hannun sultan yace "it is OK. You are welcome" daga nan suka juya suka fita tare. Suna fita Mommy tana shigowa, ta kalle mu daya bayan daya tace "what did I missed? Me ya faru?" Daddy yace "tsegumi. Kin riga kinyi missing ya wuce ki" daga haka ya mika mata babyn da yake hannunsa ya fita.
Ba'a jima ba suma su mommy suka fita suka bar mana dakin. Sunfi awa biyu a gurina, har akayi magrib, ana ta hira ana daukan pictures da baby, suna ta tsokanar Hafsat wai baby na yafi little khairat kyau saboda sultan yafi zayed kyau. Ita kuma ta dage sai kumfar baki take ita a dole zayed yafi sultan kyau. Sultan ya shigo ya zauna shima ya shiga cikin muhawarar, suka yi ta bugawa da Hafsat kowa yaki hakura, sultan yace zayed bama a class dinsa yake ba, yana class din kasansa, ita ma kuma tana class din kasana, dan haka ita da zayed ba zasu taba haihuwar 'ya'ya irin namu ba. Hafsat ta lakuce wa babyn hanci tace "akan wannan hancin ne dai ake wannan maganar, ita ma kuma khairat tana dashi wanda yafi wannan tsaho ma" sultan yace "kar ki bari ummee ta ganki kina lakuce masa hanci. Kuma ba maganar tsahon hanci ake yiba, maganar kyan hanci ake. Baki san in hanci yayi tsaho da yawa baya kyau ba?" Ina daga kwance nace "sultan don't forget about the lips" Hafsat ta juyo kaina "wannan bakin mai kama da danyen nama har wani kyau ne dashi? Daga ganin bakin irin na ubansa ne rashin kunya zai ringa yiwa yayun matarsa" Sultan yace "ke waye mara kunyar? Ko yayanki walid na girme shi ballantana ke" tace "amma dai baka girmi mijina ba" walid yace "ni din wata nawa ka bani?" Yace "na dai girme ka koma wata nawa ne, ko kwana daya na baka na girme ka" Habeeb yace "amma dai mun girmi matarka, dan haka dole ka bamu girma" Sultan yayi dariya yace "waye yace maka kun girme ta? Ai ni da ita soul din mu daya, gangar jiki ce kawai da ban, so technically she was born the day I was born, jikin ne dai sai daga baya aka haife shi. There is a strong chemical bond between us spiritually" Fadila tace "what kind of chemical bond? Covalent ko electrovalent ko hydrogen bond?" Ya dan bata fuska yana kallonta sannan ya juyo ya kalleni yace "which one is the strongest?" Duk akayi dariya, Aisha tace "ku da kuke da soul daya ai kamata yayi ace duk abinda ta sani kai ma ka sani ba sai ka tambaye ta ba" ya juya gurinta yana kallonta sai kuma yayi tagumi yace "kai Amir, yaushe ka koya wa matarka rashin kunya? Ka gaya mata idan manya suna magana yara basa saka baki shiru suke yi" nan kuma suka koma yi shida Amir. Suna ta sakani dariya gashi dinki na yana min ciwo idan nayi. Sultan sai famfa su yake, duk wanda ya fadi magana sai ya samu amsar da zai bashi. Hafsat ita kuma sai hawa take, har yanzu ta kasa gane halin sultan, a karshe tace wallahi sai an sake wannan hirar in zayed yazo. In kaga sultan a lokacin ba zaka taba cewa wani abu ya bata masa rai dazu ba, hirar sa kawai yake yana dariyarsa. Haka Sultan yake, akwai saurin hawa akwai kuma saurin sauka. Amaren mu ma duk sun ware suna ta hirar su, ina kwance ina dan saka musu baki kadan. Doctor ya shigo da ledar jini a hannunsa, yace su tafi za'ayi min allurar bacci in huta, nan suka fara fita kowa shida matarsa gwanin sha'awa, Amina ma ta kira nata a waya ashe ba nisa yayi ba dan haka yace ta fito gashinan a waje. Faruk yana shafa kai yace da sultan zai kai Huda gida suma suka fita, ya rage daga ni sai sultan da doctor, da baby kuma a kan gadonsa yana bacci. Doctor ya rataye jinin ya kamo hannuna zai saka min, na kalli sultan da ke tsaye kusa da doctor nace "doctor da ka bar jinin nan kawai" ya dakata yana kallona yace "why? Mun gwada red blood count dinki is low. Me yasa ba kyaso" na kalli sultan nace "Sultan ne baya so" sultan ya bude ido da baki yana kallona yace "ke? yaushe na fada miki haka? Sharri zaki yi min a gaban likita ko?" Doctor ya tsaya yana kallon mu yace "what is it doing to be? A saka ko kar a saka?" A tare muka yi magana da sultan, ni nace kar a saka shi kuma yace a saka, doctor ya tsaya yana kallon mu yace "ko in baku guri kuyi magana?" Sultan yace "No doctor, ka saka mata kawai" na gyara kwanciya ina kallon doctor ya gama arranging komai, yayi connecting tube din da cannula din hannuna sannan ya bude jinin, na bi jinin da kallo yana tahowa har naji ya fara shiga jikina. Na kwanta na lumshe idona, ina jin doctor din yayi min allura suka gama maganganun su da sultan sannan ya fita. Sultan ya dawo ya zauna a bakin gadon yana shafa kitsona yace "hey, har kinyi bacci?" Na dan bude ido bacci yana dauka na nayi masa murmushi, ya sunkuyo dai dai kunnena yace "it is not his blood". Abinda naji kenan bacci ya dauke ni.
Sanda na farka kamar tsakiyar dare ne. Na kalli inda baby yake naga bayanan. Na fara dube-dube sai na Sultan a zaune kawai ya rike babyn a hannunsa yana kallo fuskarsa dauke da murmushi. Na jima ina kallonsu amma bai ma san na farka ba. Sai da nayi gyaran murya sannan yayi sauri ya juyo. Sai kuma ya kalli babyn yace "hey Al'ameen, let's go greet Mom" ya taso ya dora min shi a chinya sannan ya taimakamin na tashi zaune. Na dauki babyn na fara feeding dinsa, yana kallon mu ya jawo kujera ya zauna yace "Maimunatu, meet Muhammad Al'ameen. Yaci sunan Daddy, Muhammad, zamu kirashi da Al'ameen saboda gaskiya, rikon amana da jajircewa irin na masu sunan sa. Ina fatan Allah yasa yayi gadon not only their name but har halayyarsu" nace "Ameen. Nagode" yace "don't mention. Daddy yayi min komai a rayuwa, yayi min abinda babu wani wanda ya taba yi min kuma babu wanda zai kuma yi min nan gaba. Babban abinda yayi min shine ya bani ke. He gave me a life. Because you are my life." Nace "Sultan, kafin inyi bacci, naji kamar kace it is not his blood, whose blood is it?" Yace "daddy's. Muna fita zamu je gurin daukan jinin yace ba zai bayar ba. He said idan shine yasan ba zai so jinin tsohon saurayin matarsa a jikin ta ba. So, he wish for me what he wish for himself. I owe him that. Bazan manta ba" naji dadi a raina da hakan ta kasance. God is really amazing.
Washe gari na fara tafiya, aka saka ni exercise na yi ta zagayawa a asibitin. Bayan na dawo daki Takawa yazo. Ummee dama tun sassafe tazo. Takawa ya dauki Al'ameen yayi masa addu'ah. Yana gama wa sultan ya mika hannu zai karbe shi, Takawa yace "au rowar sa zakayi min sultan? Daga dauka har zaka wani miko hannu a baka ko" sultan ya bata fuska "tun safe fa ban dauke shi ba, Ummee tunda tazo ta hana ni shi" Takawa yace "kwantar da hankalin ka, in aka sallameku kuka koma gida har sai ka gaji da daukan sa" Ummee tace "chafdi, ai bin su zanyi gidan nasu" Sultan har da bubbuga kafa a kasa kamar me shagwaba, Takawa yana yi masa dariya har da kyakyatawa. Hajiya ma tazo har asibiti ta duba ni, duk tayi sanyi babu wannan mulkin da dagawar. 'Yan'uwa da abokan arziki kuwa da basu samu zuwa ba sai waya suke min ana min barka, dan har kashe waya ta nake yi in dai ina son in samu bacci. Kwanan mu hudu a asibitin aka sallame mu. Tare muka tafi da daada tunda tana Abuja bata koma Niger ba. Muna koma wa gida ma bamu samu hutu ba, dan kullum gidan a cike yake da mutane. Ummee ta kasa ta tsare, daga baya ma hana daukan Al'ameen tayi sai dai duk wanda yazo ya kalle shi a hannunta ya tafi. Daddy yaji dadin saka sunan sa da aka yi sosai, Takawa kuma yace sunan yayi. Ana jibi suna Amina tazo zamuyi plans na taron sunan. Muna babban palo tare da sultan daya saka ni a gaba sai na cinye uban abincin da Ummee ta zuba min kafin ta tafi gida. Amina ta shigo da sallama, tun kafin ta zauna sultan yace "yana ganki ke kadai?" Tace "gashi can yana juya mota zai tafi" Sultan yace "ba zai shigo mu gaisa ba zai tafi?" Ya tashi ya fita sai gashi ya dawi shi kadai, yace "ya tafi, in ya dawo zai same ni" ni dai kawai kallon sultan nake ina mamaki. Amina tace "ina babyn kuma?" Sultan yayi ajjiyar zuciya yace "ummee ta tafi dashi" nayi dariya nace "kwantar da hankalin ki, in dai wannan acicin ne yanzu zaki ga an dawo dashi. Ai kuwa ba'ayi awa daya ba sai ga Fa'iza ta dawo dashi, tun suna daga waje muka jiyo kukan sa mukayi dariya, tana shigowa ta miko min shi tace "da kyar Ummee ta bani shi, wai ban iya daukan babies ba, wai sai dai ta kawo shi da kanta, Takawa ya hana shine ta bani shi da kyar" na karbe shi ina yi mata sannu na fara feeding dinsa. Su Hafsat ma duk ranar suka zo muka gama plans din suna.
Ranar suna yaro yaci sunan Daddy kamar yadda akayi masa huduba, za'a ke kiran sa da Al'ameen. Raguna guda biyu Daddy ya aiko dasu na suna, Takawa ma ya kawo biyu. Taf palace ya cika da mutane, both daga part dina da kuma part din sultan. Da sassafe jirgin su Zayed ya sauka, yace akwai aiki a gabansa amma ba za'a barshi a baya ba gurin taron sunan nan, besides shima yayi missing family dinsa, yace wannan karon a England Hafsat zata haihu sai dai duk mai son ganin babyn ya bi su can. Kamar daga sama sai ga Amira sun zo tare da Mahdi, ya gama final exams dinsa ya zo gida, an saka bikin su wata uku masu zuwa. Muka rungume juna da Amira, ta dauki Al'ameen tayi kissing dinsa, na sa aka raka Mahdi gurin su Sultan bayan mun gaisa shima ya dau baby. Kayan barka kam su Hafsat sai karba suke suna ajjiyewa, mun sha kaya sosai dani da baby. 'Yan uwan ummi sunzo sosai daga Riyadh. Wadansu mutanen da suka zo ma ni ban san su ba sai anyi min bayani. Masoya ta ko ina bulluwa suke dan taya mu murnar samun little love din mu. Sultan shima nasa taron daban yake yi a part dinsa, abokan sa sunzo sosai daga parts da yawa na Nigeria. Gang bang sunzo suma, amma kamar yadda sultan ya taba gaya min, they are no longer a gang, kowa daban yazo, kowa ya girma ya samu rayuwarsa, babu sauran ganging kuma. Amira ma tazo tare da mamanta, ta gaya mana an saka bikinta nan da wata uku, kafin nan mahadi ya karasa final exams dinsa ya dawo. Sai dare sannan aka fara raguwa. Bamu muka samu zama ba sai wajan karfe goman dare. Nan kuma aka zauna hira a palo. Ibrahim yazo daukan Amina tare da little Moon, Sultan da kansa ya fita ya shigo dashi, suka shigo suna dariya kamar abokai, sultan ya dauki little moon ya dora akan cinyarsa yana tsokanarta yana ce mata matarsa, ita kuma bata san ma me yaki nufi ba. Amira ta gaishe da Ibrahim kuma ya amsa mata da sakakkiyar fuska sosai, suka gaisa da Mahdi a matsayin mijin da zata aura. Aka zauna aka cigaba da hira. Kadan kadan nake saka baki a hirar. Gaba daya hankali na ya tafi akan lissafin rayuwa, na kalli duk mutanen da suke zagaye dani, they are my friends and family, they are my life. And most importantly, they are happy.
One episode more, and we are done Insha Allah.
Episode Hundred : Not The End.
One Year Later
Daddy yayi retire daga ambassadorship, yace lokaci yayi kuma da ya kamata ya dawo Nigeria ya zauna cikin 'yan'uwa da abokan arzikin sa, tunda dai yasan ya tara da yawa, ya kafa kansa ya kafa 'ya'yansa, ko da ace bai tara dukiya ba 'ya'yansa kadai sun isa su rike shi zuwa karshen rayuwarsa. Yaya Walid yana aiki a kamfanin hakar man fetur na SHELL a matsayin engineer, sosai yake samun kudi kuma da yake shi mai nutsuwa ne sosai da tattali, nan da nan ya fara shiga layin wadanda za'a kira da masu kudi. Yaya Habeeb yana aikin banki, duk da cewa shi mai yawan kashe kudi ne amma dai dai gwargwado yana samun cigaba shima. Ni kam da ni da Hafsat medical doctors ne, duk da dai har yanzu babu wanda ya fara aiki a cikin mu amma mazajen mu sun ishe mu duk bukatun mu. Faruk ya gama service dinsa ya koma masters, tun kafin ya tafi yace a nema masa auren Huda amma Daddy yace sai ya gama karatu ya samu aikin yi sannan za'a yi masa aure, an dai shigar da maganar manya sun sani. Daddy yana dawowa Nigeria ya aika 'yalleman aka daukk inna da Hajja ya dawo dasu Abuja su zauna tare dashi, tunda 'yalleman din kusan babu kowa sai uncle rufa'i, shi kuma ba mazauni bane sosai. Tunda labarin retirement din Daddy ya bazu a Nigeria, nan da nan aka fara aiko masa da offer din aiki, government, ministries, companies amma duk yaki karba yace hutawa yake so yayi. Amma bai dade a gida ba kuma sai yaji zaman gidan ya ishe shi, tunda babu kowa a gidan sai su inna da 'yan aiki, Mommy har yanzu tana aikin ta, dan haka rana daya Daddy yace ya karbi offer din da university of Abuja ta aiko masa akan ya zama next VC idan tenure din wanda yake kai ta kare. Dama shi Daddy harkar siyasa ce baya so, amma yana ganin as a VC zai taimakawa kasarsa without getting involved in politics. Bikin su Ya walid yana da wata goma Zainab da Fadila, wadanda yanzu sun zama kawaye sosai, suka haihu kusan a tare, Zainab ce ta fara haihuwar baby girl aka saka mata Mommy, ranar sunan ta Fadila ta haifi Daddy, dan haka yaran suka tashi kamar tagwaye, small Mommy da small Daddy.
Hafsat ta juye ta sake dauka. Lol. Ta haifi danta namiji watanni biyu bayan haihuwar Al'ameen. Mukaje England muka sha suna, yaro yaci sunan baban Zayed. AbdulMalik, muna kiransa da Ayaan. Watannin Ayaan biyar a duniya Hafsat ta kira ni tace min wani cikin ne da ita, nace "kai Hafsat, wannan ke ai har kinfi Mommy ma" tace "ai dama haka ake yi, idan ka koyi abu a gurin mutum sai kazo ka fishi iyawa kuma" mukayi dariya, tunda dai duk ita da yaranta lafiya lau suke to babu wata matsala.
Anyi bikin Amira da Mahdi, mun je kano munsha hidima. Duk da dai Sultan ya hana ni kwana yace Al'ameen yayi kankanta da shiga biki, ni kuwa nasan bata Al'ameen yake ba, ta kansa yake, dan Sultan yana nan yadda kuka san shi babu abinda ya ragu sai ma ince karuwa yayi. Mahdi ya samu aiki a asibitin malam Aminu kano. Last wayar da mukayi da Amira itama ta gayamin ta kamu. Suna zamansu lafiya lau from all indications.
Ibrahim da Jewel dinsa Amina kam soyayya sai abinda ya kara gaba. Dan ko ziyara mutum yaje gidan su sai ya fahimci suna kaunar junan su. Maman Ibrahim ma ta dauki son duniya ta dora akan Amina dan tana ganin itace sanadiyyar dai daituwar dan ta. Ita kuma Amina ta rike little Moon tamkar ita ta haife ta, in baka sani bama ba zaka ce ba ita ta haife ta din ba. Kullum kaga Ibrahim zaka ganshi cikin farin ciki, alamar cewa hankalinsa a kwance yake. Sosai suke zumunci shi da sultan, dan wani lokacin ma har yazo gidan mu ya tafi bana sani, sai daga baya sannan sultan ya gaya min. Sai dai kuma har yau, duk ranar da muka hadu da Ibrahim muka gaisa sai naga kishi a idon sultan, sai dai baya nuna wa har wasu su gane. I guess some things will never change.
An samu karuwa a gidan Amir shima. An samu namiji wanda a take Amir ya saka masa sunan Sultan. Abubakar Sadiq Abdallah. Kuma ake kiransa da Sultan. Sultan yaji dadi sosai amma sai ya bata fuska yace "ko kara ma babu, sultan zaku ce masa kamar wani sa'an ku? Ina lefin ma ku ringa ce masa Yaya?" A raina nace 'ho, sultan akwai son girma'. Har yanzu amir bai samu iyayensa ba, kuma dama bawai tayar da hankalinsa yayi yana neman su ba, yace "if it is meant to be, then it will be" gwara ya zauna ya gina rayuwarsa tare da mutanen da yake dasu, wadanda ya tabbatar suna kaunarsa akan yaje ya bata lokacin sa gurin neman wadanda ba lallai ne suna son sa ba.
Munir tun rasuwar Baffa ba karamin girgiza shi mutuwar tayi ba, kasancewar tunda akayi masa takunkumi a 'yalleman suke tare da Baffa suna kara shakuwa, mutuwar Baffa sai ta nunawa Munir cewa itafa duniya ba matabbata bace ba, kana cikin shagalinka za'a iya zuwa a zare ranka ba tare da ka tuba ba. Wannan ya saka shi ya kara nutsuwa, ya rungumi matarsa ya kuma rungimi aikinsa. Kowa a dangi yaji dadin chanjin munir, wannan ya saka Hajja tace to tunda dama neme-nemen mata ne ya lalata shi, to gwara a kara masa wata matar dan ya kara nutsuwa. Ai kuwa a take uncle rufa'i ya bashi Rufaida kanwar Amina. Munir baki har kunne saboda murna dan dama ya taba cewa yana sonta ta wulakanta shi saboda halinsa, amma tunda yanzu ya shiryu itama ba'a wani sha wahalar shawo kanta ba tace ta yarda.
Ummee da Takawa ana nan ana bude sabon page na rayuwa, dan idan ina gurin Ummee Takawa ya shigo tashi nake yi in fita, saboda kunya yake sakani ina ji shi kuma babu ruwansa, daga dukkan alamu rashin kunyar sultan ta gado ce. Sultan da Takawa are very much alike, saboda idan suna wani abin tamkar mutum daya ne da kamanni biyu. Ummee ta sayar da business dinta kaf na Riyadh, dukkan kudin ta zubasu a account din sultan. A take Takawa ya sake bata wani jarin ta fara sabon business a Nigeria, nan da nan aka hada mata connection da 'yan kasuwa take shigo musu da kaya daga kasashen waje. Sultan yace "amma Ummee wannan karon ba sunana kika saka ba ko?" Tace "sunan little love na saka" yace "Ummee I don't need money kin sani, in dai ta nine kiyi hutawarki" ta harare shi tace "dama kaine little love din?" Sultan ya tsaya saroro yana kallonta yace "OK. Kun fi kusa ke da shi". Hajiya tun tana saka ran Takawa zai mayar da ita har ta fara kosawa. Shi kam har manta wa ma yake yi da ita a duniya, dan in dai ba zuwa tayi gaishe shi ba baya ma tunawa da ita, duk sanda tazo gaishe shi kuwa sai ya hade rai sosai sannan yake amsa mata, dan baya son ma taga fuska ballantana ta kawomasa wata magana. Da Hajiya taga babu fuska sai ta fara bin manyan su tane rokon a roka mata shi ya mayar da ita. Yaya ta kira su gaba daya suka zauna a gabanta, tana yiwa Takawa maganar ce mata yayi shi ba zai iya mayar da Hajiya ba, tace "saboda me? Saboda kai baka yafiya? Baka son kaima Allah ya yafe maka?" Yace "ai na yafe mata, da ban yafe mata ba da tuni na koreta daga gidana ita da shegen danta. Ba zan mayar da ita ba saboda ina gudun sabawa Allah. Allah yace duk wanda yake da hali to ya auri mata biyu zuwa hudu in har yasan zai iyayin adalci a tsakanin su. Ni nasan bazan iya adalci a tsakanin khairat da wata mace ba, ba Zuwaira kadai ba, dan haka bazan iya mayar da ita ba. Zaman da muka yi da ita a da ma da ace ina da iko dana goge shi daga kwakwalwata na taina tunawa" jin haka yasa Hajiya tace ita kam ba zata iya zama babu miji ba, dan haka tunda ba zai mayar da ita ba to zata fita ta sami wani mijin tayi aurenta, Takawa yace Allah ya raka taki gona, amma kar ta saka ran tafiya da ko daya daga cikin 'ya'yansa, sai dai in nata dan zata dauka to bismillah. Haka kuwa akayi, Hajiya ta sayi gida da kudinta a wajen palace ta koma can da zama, amma kuma mijin aure yaki samuwa, matsalar shine da wahala sarki ya saki mace wani kuma ya aura. Ummee ta sami Takawa da lallami tace tunda shi yace ba zai mayar da Hajiya ba to dan Allah ya samo mata mijin aure da kansa, saboda gudun kar azo a kuma yin wani abin kunyar, tunda har ta fada da bakinta cewa ba zaya iya zama babu miji ba, albarkacin 'ya'yanta, tunda komai tayi dole za'a ce uwar 'ya'yansa ce tayi. Babu jimawa Takawa ya samo mata miji, wani tsohon abokinsa da suka yi secondary school tare, mazaunin garin kauran namoda ta jihar zamfara. Hajiya akayi sabon aure aka tare da ango. Su saratu suka fara nuna rashin jin dadin su akan sabon auren da mahaifiyarsu tayi, Takawa yana ganin haka yace suma duk su fito da mazaje yayi musu aure, dama kowacce ashe da nata saurayin suna tsoron fada ne kar ace sunyi laifi, dan haka babu jimawa muka sha shagalin bikinsu muka kaisu dakunan su. Daya Kaduna daya kuma anan Abuja. Abbas kam ko daga kai bai yi ba akan sabon auren Hajiya, karatun sa kawai ya saka a gaba yana gina sabuwar rayuwarsa.
Kamar yadda mukayi shawara da sultan a Riyadh haka akayi. Sultan ya gina sabuwar obrphanage, amma wannan karon a Kano ya gina ta, yace next time kuma a Lagos zaiyi tunda sune manyan buranen Nigeria. Ya kashe kudi sosai wajen ginin da furnishings. Sannan yazo ya dauki ma'aikata. Sai da komai ya kammala sannan ya damka ta a hannun abokin sa Mahmud, nan take aka bada cigiyar yara wadanda aka yar a titi da kuma marayu da suke basu da galihu, daga 'yan kwana daya zuwa shekaru goma sha biyar, babu jimawa orphanage din ta cika taf, sultan yace shi baya son publicity, ba ya son ma asan cewa shi ya gina, dan haka ya bar ta a hannun Mahmud sai dai duk wata zasu yo masa bill din abinda suke bukata sai ya tura musu. Lokaci zuwa lokaci kuma muna zuwa mu gano halin da yaran suke ciki, kuma sosai muna jin dadin abinda muke gani dan mahmud ya rike amana sosai. Ranar da muka fara zuwa sai da nayi kukan tausayin yaran nan, wadansu jarirai wadansu 'yan kananan yara kuma wai duk marayu ne, amma kuma Alhamdulillah, gaskiya suna samun kulawa sosai dan sultan yana sakar musu kudi, abincin da suke ci ko wadansu yaran da suke zaune a gaban iyayensu ba zasu samu kamarsa ba. Sai dai soyayyar iyaye ce dole sunyi missing din ta. A duk wata sultan yana gama ware mana abinda zamu bukata na watan to next shine orphans dinsa, sai ya ware musu sannan komai ya biyo baya. Kullum kuwa arzikin sultan karuwa yake yi, kowanne wata abinda yake samu yafi na watan daya gabata.
Al'ameen yana da shekara daya a duniya muka nemi admission ni da Hafsat muka koma karatu, an sha rigima kafin su Ummee su yarda in tafi, twin house din na su Hafsat muka karba rent muka zauna a can. Kafin muje Zayed ya gama yi mana duk harkar registrations, dan haka ina zuwa karatu kawai muka fara. Bamu dade da fara karatu ba Hafsat ta haifi third child dinta, a girl, Aaysha. Daga nan kuma sai ta tsaya tace tayi uku sai ta huta kuma. Muna can Amina ta haihu itama, mun sami baby boy wanda yaci sunan marikin Ibrahim, Abdulshakur. Zaman mu tare dasu Hafsat ya kara dankon zumunci sosai tsakanin zayed da sultan, dan zayed zama yayi tamkar brother din sultan tunda dama sultan bashi da brother. Ni kuma da Hafsat zumuncin mu ya kara karuwa muka koma tamkar twins. Duk da cewa gidajen mu daban ne amma komai a tare muke yi, Al'ameen ya saba dasu khairat sosai. Bamu dade da komawa England ba Ummee ta matsa mana lallai sai da na yaye Al'ameen aka mayar dashi Nigeria gurinta. Nan fa Sultan shima ya damu da rashin Al'ameen saboda ba karamar shakuwa suka yi ba, shima Al'ameen a can kullum sai rigimar neman Dad dinsa da Mom dinsa, amma Ummee taki dawo mana dashi a haka har ya saba da ita sai dai muyi waya dashi ko kuma idan munje gaishe su. Shekarun mu biyu muna karatu muka kammala, kuma Alhamdulillah mun samu sakamako mai kyau. Ranar passing out dinmu family din mu sunzo sosai, dan har Takawa sai da yazo taya ni murna. A lokacin da cikina wata bakwai, wanda aka tabbatar min twins ne a ciki. Wannan ya saka sultan yace ba zamu koma Nigeria ba sai na haihu, lokacin haihuwata yana gabatowa ummee ta dauko al'ameen suka taho gurin mu, a haka har na haihu, wannan lokacin kuma Alhamdulillah da kaina na haihu ba'ayi min aiki ba, amma fa nasha wahala ba karama ba, na haifi mace da namiji wadanda a take sultan yayi musu huduba da sunan ummee da na Takawa. Muna kiransu da Bassam da Basma. Gaba dayansu babu wanda yayi min kara, dan kamar Ummee da sultan suka dauko sak. Sultan harda yi min gwalo yana tsokana ta. Bayan haihuwar twins muka tattaro muka dawo Nigeria. Tunda muka dawo naga sultan yana ta kumbiya kumbiya, nasan akwai abinda yake boye min amma na kasa gane menene. Wani lokacin idan yana waya ina shigowa zai katse, da yawan fita da yake yi yanzu har weekends in ya fita tun safe wani lokacin sai magrib zai dawo kuma ya dawo min a gajiye, in na tambayeshi ina yaje kuma sai yace min yana gurin Takawa ko kuma yace gurin Daddy yaje, ni kuwa nasan daga Takawa har Daddy babu wanda zai gajiyar da shi. Tun ina dannewa har na fara damuwa, rannan yana shigowa ya kwanta yana ta juyi nazo na zauna na saka masa kuka, tashi yayi ya zauna yayi tagumi yana kallona ina ta rera kuka na, yace "wannan shagwabar ta mecece kuma?" Nace "ba kai bane kake fita kullum kuma kaki ka gaya min inda kake zuwa" ya matso kusa dani ya jawo ni jikinsa yace "My Love, na gaya miki ba wani gurin nake zuwa ba fa, most of the times ina gurin Takawa" nace "ni dai ban yarda ba, yanzu haka ma zance kake zuwa" dariya yayi sosai yace "zance kuma Moon? Where on earth do you get this Idea?" Nace "to bayan kullum in kana waya ma in ka ganni sai ka kashe?" Ya sake dariya yace "Love how many times zan gaya miki babu wata a gaba na bayan ke?" Nace "you are acting otherwise. Tun da muka dawo Nigeria kake boye min wani abu, kuma nayi nayi da kai ka samo min aiki kaki yarda, ya za'ayi ace ban samu aiki ba, ina ka taba ganin doctor ya rasa aiki, na gaji da zaman gida, I want to do something, it has always been in my dream in ga na zama doctor ina taimakawa mutane" ya saka hannu yana share min hawayena yace "wannan shi yasa kike zubar min da precious hawayen ki? To tashi ki saka hijab dinki ki bar su Bassam a gurin nanny din su ki zo muje in kaiki inda nake zuwa kullum, in ma budurwarce zaki gani" na tashi da sauri ina jin excitement na saka hijab dina muka fita. Hanyar office dinsa naga mun dauka, a raina nace 'so yake ya wayance ya nuna min office yake zuwa kullum har weekends'. Amma kuma sai naga mun wuce office din kadan sai muka tsaya a next building after it. Ya fito ya zagayo ya bude min kofa nima na fito, muka jingina a jikin mota muna facing wani sabon gini wanda ko fenti ba'a yi masa ba, hawa biyu ne sama da kasa, kuma babba ne sosai. Sultan ya dora hannunsa a kafada ta yace "nan gurin nake zuwa kullum, bam sani ba ko anan budurwar tawa take?" Na dan ture shi nace "to amma ai kai ai architecture ne, menene hadin ka da field work kuma?" Yace "wannan ba aikin office bane ba, this is personal". Ya juyo dani ina facing dinsa yace " da banyi niyyar gaya miki ba har sai aikin ya kammala, amma tunda kin fara tunanin zance nake zuwa, gwara in gaya miki yanzu" ya cigaba "I am building a hospital for you. Shine wannan, tunda muka dawo nake aikinsa kuma almost na kusa gama wa. Takawa ya bayar da order za'a sayo miki duk machines din da ake bukata a asibiti. You will be the MD, sai ki dauki sauran ma'aikatan ki da kanki" na dan jima ina kallonsa kafin in fahimci da gaske yake bada wasa ba. Ai kuwa wani tsallen murna nayi na dafe jikinsa, shi kuma ya biye min ya ringa juyi dani a gurin in circles muna dariya, mutane har daga mota lekowa sukeyi suna kallon mu,, daga baya ya ajiye ni muka shige cikin building din da gudu kamar wasu yara. Da gudu muka rinka zagayawa room by room, sai na fahimci ma kamar gurin yafi girma daga ciki akan ta waje. I can't believe all this is mine. Muna gamawa na rungume sultan a jikina ina hawayen murna nace "bansan da wanne bakin zan gode maka ba. Na gode Allah ya kara maka budi, Allah ya raya mana zuri'ar mu" yace "Ameen my love, you deserve this and much more" daga nan ya saka babban dan yatsansa yana zagaya lips dina, ba sai na gaya muku abinda ya biyo baya ba. Lol.
Daddy na fara kira na gaya masa, yace min ai already ya sani, sultan ya gaya masa tun kafin ya fara aikin. Na kira Mahdi na gaya masa abinda ya faru, nace "I will appreciate it if you will help me in running the hospital" yace "it will be my pleasure" sannan yayi min murna sosai tare da fatan alkhairi.
Ranar har dare ina ta waya ina gaya wa mutane, kowa sai murna yake min da fatan alkhairi. Washegari da safe na shiga cikin gida nayi wa Takawa da Ummee godiya, Takawa yana ta yi min dariya wai sai washe baki nake yi, yace "haka zaki ke yiwa patients din naki?" Na sake washe bakin ina dariya. Ummee tace "yanzu menene plan dinki akan asibitin?" Nace "burina shine in rage kudin komai a asibitin, yadda mutane talakawa suma zasu ke samun best medical care a cikin kudi kalilan" Takawa ya gyada kai yace "Zakiyi mamakin kuwa yadda Allah zai saka miki albarka a cikin sa. In mutum ya fara business, ko wanne iri ne, idan ka saukaka kudin shine Allah yake saka maka albarka, idan kuma ka zafafa sai Allah ya barka da dabarar ka, wacce babu inda zata kaika. Sai kiga an fara business amma ko shekara ba za'ayi ba ra rushe saboda babu albarka a ciki" Allah yasa mu gane.
Watanni uku bayan nan aka gama komai, duk kayan da akayi order sun zo an sassaka, na shiga na duba komai sannan na sake rubuta wani list din na sauran kayan da nake bukata, Daddy ne ya karba yace shima yana son a saka shi a ladan, babu jimawa aka kawo kayan gaba daya. Yaya Walid ne ya shirya min opening party a cikin harabar asibitin, kusan duk 'yan'uwa sunzo, har Hafsat da Zayed sai da sula zo da 'ya'yansu guda uku kyawawa gasu kusan kansu daya, nan ma sultan ya saka ta a gaba da tsokanar wai duk saurin ta gashinan mun kamo ta, uku take dashi kuma muma uku muke dasu, ta harare shi tace "neman in kulaka kake yi muyi, ni kuma bani da lokacin ka, besides ni bana kula kannena". Itama yanzu ta samu aiki a hospital din da zayed yake aiki.
Sai wajan sha biyun dare muka tashi, saboda hira da taki karewa. Muna zuwa gida na yiwa yara na wanka har Al'ameen da yake tare dashi muka je partyn kuma dare yayi dan haka bamu mayar dashi gurin Ummee ba. Na shirya su tsaf suka yi bacci saboda gajiya suma da suka yi. Na zauna a bakin gado ina kallonsu, kusan kamannin su daya dukkansu, ni dai a idona gani nake duk duniya babu kyawawan yara irin nawa, sai kuma wani tunani ya fado min a raina. Sultan ya shigo da sallama, na juya nayi masa alamar yayi a hankali kar ya tashe su, ya karaso ya zauna a kusa shima yana kallonsu, yace " Hmmm, they are beautiful, aren't they?" Nace "They are perfect" na tashi tsaye ina mammatsa masa kafadar shi da wuyansa, ya sauke ajjiyar zuciya yana kwanto da kansa a cikina, nace "wai Sweetheart yaran nan wanne tribe ne su?" Ya dan bata fuska yana kallonsu yace "oho, waya sani ne, menene ma'anar tribe din ma gaba daya? Menene kuma amfanin sa?" Nace "babu, bashi da wani amfani sai gurin rarraba kawunan al'ummar musulmi. Mutane sun kasa gane wani abu, we are atronger if we stand together, amma in muka rarrabu anan zamuyi falling easily. Yanzu kamar yaran nan, suna da jinin hausawa, larabara, fulani da buzaye, to wanne tribe ne su? A hakikanin gaskiya basu da tribe amma da mutum ya kallesu yasan they are perfect, ni a ganina mixed din su ne ya kawo perfection din su. Basu kadai bama, duk yaron da aka haifa a auratayya tsakanin two different tribes in mun lura zamuga yafi both tribes din kyau, wannan shi yasa duk duniya halfcast sunfi kowa kyau. Anya kuwa wannan ba wata hanya bace da ubangiji yake nuna mana cewa in muka hade kan mu a guri daya sai munfi samun kyakykyawar rayuwa akan in muka rarrabu?" Sultan ya jawo ni muka fada kan gadon yayi juyi ya mayar dani kasansa yace "maimaita abinda kika ce akan halfcast" nayi murmushi ina shafa fuskarsa nace "kunfi kowa kyau a duniya. Kafi kowa kyau a duk mazan dana taba gani a duniya, ba larabawa ba ba turawa ba, ba Africans ba koma wanne kabila ne banga wanda ya kamo kafar ka akyau ba" yana murmushi yace "ban yarda da wannan theory din ba miss psychologist. Saboda nasan ban kaiki kyau ba" nace "believe me Sultan ka fini kyau, ni macece kai kuma namiji ne. The most amazing thing is your skin, I love it" na fada ina saka hannuna cikin rigarsa ina shafa muscles din da suke rudani tun farkon gani na dashi. Ya juya fuskarsa yana kallon yaran da suke bacci a gefen mu, ya daga ni sannan ya dauke ni yace "let's go to my room sai ki maimaita abinda kika ce kiga yadda zan yi dake" muka fita muna dariya gaba daya.
Washegari ya dawo daga office ya tarar dani a palo ina feeding Basma, Bassam yana tsaye akusa dani yana wasa da toy car dinsu, yana jin muryarsa ya yar da motar hannunsa ya tafi da 'yar koyon tafiyar da suka fara yi zai tare shi, ya fadi ya sake mike wa, Sultan ya karaso da sauri ya daga shi yana juyi dashi a tsakiyar palon, Basma ta sake ni itama ta sauka daga jikina ta tafi, ita ma ya dauke ta yana tsalle dasu suna ta dariya, nace "to ni kuma fa?" Ya juyo yana kallona yace "naki special ne" sannan ya ajiye su a kasa ya durkusa a gabansu yace "albishirin ku, yaye ku za'ayi" na bata fuska nace "ai basu isa yaye ba, ka bari ko fifteen months suyi mana" ya karaso gaba na ya ajiye min wasu takardu, na dauka ina dubawa, naga takardun visa ne da kuma plight ticket zuwa Maldives, na mike da sauri na makalkale shi ina murna, ya daga ni sama nima irin yadda ya yiwa twins ya ringa juyi dani, yaran suka saki baki suna kallon mu, ya sauke ni yace "I promised I will take you back, didn't I? Gwara mu tafi yanzu tun kafin ki fara aiki ki zama busy. Amma ki sani, yanzu ba ki da ciki dan haka kiyi shiri na sosai" na harare shi nace "wancan zuwan ma da nake da cikin me aka fasa" yace "to wannan will ve double. You better get ready" na rungume shi kamar zan shige jikinsa nace "I can't wait, Darling. I love you so much Sultan" ya zagaye ni da hannayensa yace "I love you too, MyMoon".
The End
But remember, every ending is just another beginning.
Alhamdulillah .
Na sadaukar da littafin Maimoon ga duk wanda ya karanta shi. Ina fatan duk wanda ya karanta yaji dadi ko kuma ya karu da wani abun to yayi min addu'ah, Allah ya bani dacewa a duniya da lahira.
Littafin Maimoon kyauta ne, duk wanda ya sayar min ta hanyar bugawa ko kuma a document ya sani Allah yana kallonsa kuma zai tambayeshi.
Da akwai lessons da na saka a littafin Maimoon, wanda nasan in dai har mutum yana biye to zai karu da one thing or another. Amma babban abinda nake so mutane su dauka shine to not judge a book by it's cover, things are not always what they seem, duk mutumin da ka hadu dashi a rayuwa to there is a story behind him, kowa da akwai labarin sa, kowa kuma da akwai dalilin da yasa yake yin abubuwan da aka ga yana yi. Akwai mutane da yawa a duniya kamar Sultan, suna nan a cikin unguwannin mu da lungunan mu, deep inside them mutanen kirki ne sosai amma yanayin rayuwa shi ya mayar dasu yadda suke, wadansu zaka gansu suna shaye shaye, wadansu sun zama 'yan daba, wadansu ma sata suke yi, amma da zamu zauna dasu mu tambayesu labarin rayuwarsu da sai mun zubar musu da hawaye, ba wai zabin sune ya saka suka zama haka ba, rayuwa ce ta mayar dasu hakan. Babban abinda zamuyi musu shine mu nuna musu soyayya, no matter how small, you have no idea how mu much a little love can change someone's life. Allah yasa mu dace.
Godiya mai yawa ga dukkanin masoya littafin Maimoon, ba zan taba mantawa da soyayyar ku gare ni ba. Ban taba tsammanin Maimoon zai samu karbuwa irin haka ba, musamman saboda kasancewarsa littafi na na farko, na fara da zero followers na gama da over ten thousand followers. Alhamdulillah. Ku sani duk ina sane daku, nasan sunayen most of you, kuma duk comments dinku ina karantawa kuma ina jin dadi.
Maman maama novels na WhatsApp na matan aure, you guys are always making my days, jazakumullahu bi khair. Maman Ahmad da jama'arta, Surayya ta hannun daman Sultan da Hannatu ta hannun daman Ibrahim, ina fatan kun gaisa kamar yadda sultan da Ibrahim suka gaisa. Nafisa Usman, R-sulym, ummu khulsum, Aishas (we have many), Fatimas, Ummis, Hadizas, Umaira, Saiham, Yagana, Nafeesa, dama sauran wadanda ban kira ba duk ina godiya.
Jinjina ga Umar Faruk (sadauki) wanda shi ya kirkira kuma ya tabbatar da kafuwar both WhatsApp and Facebook groups na maman maama novels, I will forever be greatful. Hayatuddeen, Aisha Tafida, Dr MB, Fadila, Haleema yuguda, Amina, Aysha, Rabiat, Abu Muhammad, da sauran wadanda ban kira sunan su ba, ina godiya for keeping the WhatsApp group lively. Ina jin dadin programs din ku na dare, kuma ina karuwa sosai, Allah ya bar zumunci.
Jinjina ta musamman ga constant Facebook followers of Moon, musamman
Abdul A A Rasheed wanda zan iya cewa shine first fan dina kuma ya cigaba da bin littafin maimoon har karshen sa. Ahmad, Salahuddeen Dama, Sadiya Usman Aliyu,
Yagana Babakura, Fadyla Ingawa , Ummi Ummusalma,Zeeta Aliyu , Aisha Aysha Muhammad Deejarh Muhammad , Bashir Muhammad Rahama , Maimuna, Nafisat Usman Tafida, Jamila Jibril , Nafisat Saleh , Muktar Ahmad, Hadiza UssainAdamu , Abdoulmaleeck Saleh, mata mutanenmu na amana, Ummu Kaltume Aminu , eve mohd, Abdulmajeed,
Zainab M Alhassan , Barkhe, It's B Y Ibrahim, da sauran wadanda karancin lokaci ba zai bar ni in fadi sunan su ba, ba wai dan ban san dasu bane. Allah ya bar zumunci, Ameen.
Maybe zan cigaba da rubutu, may be not, amma ko da zan cigaba din to ba nan kusa ba. Kamar yadda rana daya na tashi na fara rubuta Maimoon haka maybe wata rana zan iya tashi in fara rubuta wani.
Nagode
Alhamdulillah.
0 comments:
Post a Comment