"Idan muka koma bangaren kyau, tofah saidai ace masha Allah dogaye ne masu fadin qirji da fuskar su a kewaye Wanda yyi daidai da dara-daran idanun su masu matukar kyau tamkar masu jin bacci, hancin su kuwa dogo ne yyinda kasan sa akwai kewayeyyen pink lips. Sumar Kansu kuwa akwance take har wani sheki take habawa taji gyara. Omar shine babba yyinda farooq shine karami ma'ana hasan da hussaini.
Idan akace 'yan mata ba'a mgn toh tanan zaka iya banbantasu domin farooq akwai son 'yan mata yana chilling life dinsa, yyinda omar baima da lkcin ko wacce kucaka. Dariya bata damesu ba, dukda farooq yana kula 'yan mata bawai ko wacce jik and jak yake kulawa ba aa sai me class sanna su suke biyoshi bawai shike binsu ba.
"Yau kwana daya kenan da dawowar su daga india bayan kammala karatun su da sukayi, inda omar ya kanci harkar likitanci fannin operation, yyinda farooq ya dauki fannin duba matsalar data shafi mata (Gynecologist).
"Sai wajajen 11 suka shigo side din iyayen nasu, dake jiransu danyin breakfast. "Bayan sun gaisa daddy ya kallesu cike da murmushi. Mummy ma haka ganin twins dinta sun gama kr2. "Bayan sun kammala cin abincin daddy yyi gyaran murya kowa yyi shiru yana sauraren abinda zai ce....
Nuceey luv😘
[8/13, 4:18 PM] Nuceey luv😘: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓
6-10
"Daddy yace toh Alhamdulillah tunda Allah ya kawo mu wannan lkcn da muka dade muna jira. "Abu na farko shine na Gina muku hospital naku me suna *OMAR* *FAROOQ* *SPECIALIST* *HOSPITAL* a tare twins din sukayi murmushi hakan ya tabbatar wa iyayen nasu sunji dadi kenan. "Daddy yace bayan nan kowa na Gina masa gida nan ma murmushin sukayi, "abu na karshe shine kowa inaso ya fito da Matar da zai aura, Amman Ku sani a tsarina banason Ku kwaso 'ya'yan talakawa hop kun gane....mummy tayi saurin kallon daddy bude baki tayi tace haba alhji talaka da me kudi duka mutum daya yyi su ai, kuma...daddy ya daga mata hannu enough plss, mummy na ganin haka taja bakin ta tayi shiru dan batason ja in ja da alhji gaban yaransu dan a ganin ta be dace ka dinga CeCe kuce a gaban yara ba.
"Daddy ya kalli twins yace hop kun gane, gaba1 suka gyada Kansu. "Ana suka tashi dan komawa side dinsu. "A hanya farooq yyi 'Yar dariya hakan yasa omar ya kalle shi yace lpy? "Farooq yace wai daddy ke zancen aure, omar yaja tsaki yace ai ko beyi ba kaikam kana bukatar aure, "farooq ya zaro ido yace haba bro. Nayi karami dayawa. "Omar ya tabe baki yace shi yasa kuma kke chilling da enmata koh, farooq ya Sosa qeya batare d yace komai ba, nan kowa ya shige dakinsa.
"Omar kwance kan gado yana tunanin abinda daddy yace shidai mgnr gsky be shirya aure yanxu ba, hasalima mata basa gaban sa shi a nasa tunanin bega abin burgewa a aure ba, dukda yanada enmatan dake nuna so gare hakan be tabajin a zuciyar sa mace ta birge shi ba, wasu ma zaton su ko farooq ne Amman d sunga ba fuska zasu gane omar ne, ajiyar zuciya ya saki yyinda ya tuno cewa daddy yace bayason su auri 'yan talaka wato kwarya tabi kwarya, murmushin yake yayi toh shi ko zaiyi aure ya rasa wacce zaiso sai masu warin kodaddan kaya?,god forbid masu kudin ma sai a slow, shi yasa Sam baya son dawowa naija sbd wannan mgnr auren yasan dole sai sunyi musu. Da wannan tunanin bacci ya sace shi.
Nuceey luv😘
[8/13, 11:18 PM] Nuceey luv😘: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓
11_15
"Da yamma duk sunci kwalliyar su, anan falo suka tarad da mummy tana kallon News. "Gud evening mummy, a tare suka furta, mummy da murmushi ta kallesu tace aa my twins har kun fito. "Eh mummy suka bata amsa bayan sun zauna. "Mummy tace gud. "Sannan ta kallesu tace twins, gaba1 sukace na'am. Mummy tace bawai nace kuyi watsi da mgnr mahaifin Ku bane, Amman inaso Ku fahimci Abu daya ita rayuwa da mai kudi da talaka duk Allah ne ya halicce su, shin meye ribarku idan kun kyamaci talaka? Nidai burina Ku samo mata na gari masu cikar kamala da sanin ya kamata. "Gaba1 shiru sukayi suna sauraron ta saidai kash yanda ya shiga haka ya fita a kunnen su, a fili kuwa nuna mata sukayi ah ba komai mummy zamu kiyaye insha Allah. "Sosai mummy taji dadi ta kuma sa musu albarka.
"Kasancewar yau Monday da wuri suka shira, sosai sukayi kyau tamkar a sace su, bayan sun gama breakfast, suka dunguma zuwa mota don tafiya hospital cox yau ake bikin bude shi, dan haka anyi gayyata sosai dan taya twins din daddy murna.
"Sosai aka taru bayan addu'o'i da akayi tare da fatan dorewa har abada, da kuma Allah ya sanya Alkhairi cikin harkar, nan daddy yace xa'a fara diban ma'aikata ranar laraba domin tantance kwararrun likitici. "Bangaren mata kuwa abin ba'ace komai sosai kowacce mace me aji taci burin kasancewa mata daya daga cikin su.
**************
"Tafe take cike da nutsuwa hijab dinta har kasa yyinda take rungume da qur'ani a hannun ta, "Assalamu Alaykum, sallama tayi cikin wani madaidaicin gida, Wanda yake ginin kasa ne da Alama gidan ya dade dan har katan gar taso ta rushe, qara maimaita sallama tayi nan taji shiru anan ta qara sauri bayan tana kokarin cire hijab dinta, ta nufi d'an dakin su dake kwaya d'aya JAL a cikin gidan. "Bude labulen tayi, ganin Umman ta tayi kwance tana nishi kadan2 da sauri ta afka dakin nan ta shiga kiranta ummaaa, umma, meya sameki? Wacce aka kira da umma tace da kyar ba komai Imaan zanji sauki insha Allah, buh umma meke damun ki? "Umma tace cikina ke ciwo inaga ramar da naci jiya take son 6atamin ciki karki damu zanji sauki insha Allah... Ta karasa mgnr tana nishi. "Imaan badan ta yadda ba ta kyaleta kurum dan ta lura a 'yan kwanakin nan umma batajin dadi dauriyace kurum irin tata. "Mikewa imaan tayi ta canja kayan jikin ta sannan ta fita dan dafawa umma ganyen darbejiya kamar yanda ta bukata dan tasha.
*******
"Kwararrun ma'aikata maza da mata aka diba a wannan hospital din bayan tantance su da akayi, aka tatse, aka yashe, kafin aka bar me rabo acewar _Omar_ da _farooq_ basa son malalatan doctors Wanda basu San kan aikin su ba, shiyasa dayawa Wanda suka shiga musamman matan suke jinsu on top. " bayan gama tantancewa suka sa date akan Monday zasu fara aiki a hospital din bayan sanar wa d sukayi.
Nuceey luv😘
[1/29, 5:48 PM] +234 813 725 2431: [8/14, 3:22 PM] Nuceey luv😘: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓
16_20
"Masha Allah Monday nayi kowa ya fada bakin aiki, sosai ma'aikatan suke da kwazo kuma marasa lpy sunzo Wanda suke Neman sauki, "Wanda suke buqatar operation kuwa sai hamdala suke domin Dr Omar yasan aikinsa yyi komai successfully, yyinda Dr farooq shima yasan nasa aikin dan sosai mata masu matsaloli suka halarci ganin kwararran likita. "Aiki ya kankama ba iya Kano ba hatta makotan jahohi da dama sun samu lbrin asibitin *OMAR* *FAROOQ* *SPECIALIST* *HOSPITAL* Me tarin kwararrun ma'aikata.
*****
"Wanke wanke take tana 'yan wakokin ta, ji tayi nishin umma ya tsanan ta, da dauri ta ajiye komai ta fada dakin, ummaa, ta kira sunan ta sau uku Amman da kyar umma ta iya amsa mata, "ba shiri ta bankada kasan tabar mar dake dakin su nan ta tarad da 500 a kasan wajen, ita kadai CE kawai arzikin su a duk fadin gidan, "cike da tausayin Kansu ta kalli umma, tace umma tashi mu tafi asibiti, umma ta girgiza kai dan tasan koda sunje basuda kudin magani. "Imaan ta canja kayan jikin ta zuwa Riga da skirt da dogon hijab dinda na islamiyya. "Nan ta daukowa umma nata hijab din, umma ba yanda ta iya dan ita kanta tanajin jiki ta rasa meke damun cikin ta. "Dakyar ta mike sannan ta tashi da kyar, "imaan ta sakala hannun ta a kafadar umma, vayan sun fito tayi dabarar rufe dakin na su, sannan suka fito waje. "Mai napep ne yaxo wucewa nan imaan tayi saurin tare shi. "Me napep yace INA zaku? "Imaan tace general hospital, me napep yace kudin Ku 600, "zaro ido imaan tayi tace dan Allah malam ka sassauta mana, me napep yace toh kawo Dari biyar. "Imaan tace haba dan Allah ka tausaya mana mahaifiyata bata da lpy wai baka ga halin da take ciki bane? "Me napep yace malama iya ragewa na miki, nima ya kamata ki tausaya min a wannan zamanin na 'Yar buhariyya kinsan komai yyi tsada dala ta tashi. "Imaan ranta bace tace komai da an tabo mutane dala ya tashi wani Sam be San me ake nufi da dalar ba Amman sbd Dora lefi da rashin rungumar kaddara a kowanne hali da muka tsinci kanmu sai Ku dorawa shugaba alhalin shi ba _kunfayaqun_ bane. "Ah lalle toh idan wa'azi zakimin kinga tafiya ta Sana'a na fito nema ba wa'azi ba.
"Imaan ta kalli umma duk ta canja kamanni da gani tanajin jiki, da sauri ta tsaida me napep din dake shirin tafiya, tace dan Allah babu wani hospital nan kusa? "Me napep yace shigo muje akwai sbd da aka bude satin daya wuce, "da sauri imaan tace nawa ne kudin daga nan? Me napep yace 250, "imaan tace toh muje, haka da kyar umma ta shiga napep din sannan imaan itama ta shiga.
"Basu wani dade ba sai gasu a wannan hospital din, gaban imaan ne ya bada rass yanda ta ga tsaruwar hospital din shiya tabbatar mata da private ne, to yanxu INA zata samu kudin magani? "Kallon me napep tayi tace wannan ai private ne malam babu wani me saukin kudin? Me napep yace ke yarinyar nan kin cika mita wallahi ni Ku fita inada abun yi. "Imaan ta kalli umma, umma ta daga mata kai alamar su fita, haka suka fito bayan ta biyashi kudin sa. "Sannu a hankali suka shiga cikin asibitin imaan ta rikice da kallon tsaruwar wajen kamar ba hospital ba, ta rasa INA zasu bi dan ganin doctor, "wata matace tazo wucewa da Alama ta rako marar lapiya ne., am baiwar Allah imaan ta tsaida ta. "Matar tace na'am lpy? Imaan tace dan Allah INA xanbi dan ganin doctor? Matar tayi mata kwatance sannan ta tafi. "Basu yi wani tafiya me nisa ba suka isa wajen nan suka zauna, nan imaan ta tambayi wata INA ake yankar kati. "Nuna mata wajen akayi nan taji ance ta kawo 200, ba yanda ta iya haka ta biya.
"Sannu a hankali har aka zo kan sunan umma, nan suka mike suka shiga office din doctor, tunda suka shigo yake rubuce2 saida ya gama ya dago kai yace meke damunta? Imaan tayi masa bayanin komai. "Dr yace sai anyi mata scanning kafin musam meke cikin ta.. Imaan tace a INA akeyi? Dr ya daga waya ya kira wata nurse bayan 4mins saiga ta. "Nurse din tace Dr islma'il wats going on? "Dr ya kalli su imaan yace tafi dasu ayi mata scanning, nurse tace ohk.
"Wani daki suka shiga nurse din tace zaku biya kudi, take cikin imaan ya bada kululu.. Karfin hali tayi tace nawa ne kudin? Nurse din tace 5000, imaan ta zaro ido sannan tace am toh dan Allah kiyi mata zanje na ranto kudin. Nurse ta kalli imaan kallon raini tace Amman bakida hankali ko, imaan tace kamar ya? Nurse din tace an taba aiki ba kudi ne? Imaan tace dan Allah nace ai, take nurse din tace oya tattare mamarki kubar hospital din nan tun kafin Dr Omar ya iso.
Nuceey luv😘
[8/14, 4:15 PM] Nuceey luv😘: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ*
21_25
"Imaan tace waye shi? Nurse din tace ke dallah ban sani ba, imaan tace dan Allah gayamin waye shi, nurse din ta mike a kan kujera tace tashi kubar dakin nan, haka ta koro su waje, daidai lkcn Dr Omar yazo wucewa, da sauri nurse din ta dan sunkuyi Alamar girma tace morning sir, Dr Omar batare d ya kalleta ba ya daga mata hannu kawai, Imaan na ganin haka tace oh da Alama wannan shine Dr Omar kamar yanda taji Matar ta fada da farko. "Da sauri ta sha gaban sa, ba nurse din ba hatta shi kansa Dr Omar din saida yyi mamakin abin da imaan tayi, imaan kanta tsaye tace dan Allah idan Kaine Dr Omar ka taimaka kace a dubamin lpyr umma tana cikin wani hali wallahi, "Dr Omar ransa a 6ace ya daga murya yace wacece ke? Waya baki right na ki shigemin gaba? Imaan take kwalla ta ciko mata dan yanda taga umma na juyi a kasa tace ka taimakamin Dan Allah, Dr Omar cikin zafin rai yace da xaki shigo hospital, kinga An rubuta *TAIMAKO* *SPECIALIST* *HOSPITAL* ❓. "Imaan ta girgiza kai dan ita ko sunan hospital din bata daga kai ta gani ba. "Anan Dr Omar yaja wani dogon tsaki sannan ya kwalla kiran cleaners dake hospital din, "da dauri suka fito dan kowa tsoron shi suke. " cike da izza yace Ku fitar min da wa'annan garbage ( datti) din. Atake sukace ohk sir. Imaan kuwa ranta yyi kololuwar baci, garbage? Ta maimata, ganin ya fara tafiya ta daga murya tace mungode da wulakanci, saidai ka sani dan Adam ko ya yake akwai tasa ranar. "Dr Omar yanajin ta Amman be waiwayo ba dan tsari da irin wannan masu warin kodaddan kayan 6ata lkci ne. "Cleaners din mata suka kama umma da nufin fitar da ita, Amman ga mamakin su suka jita sharab kaman kayan wanki hakan ya tabbatar musu da rai yyi halin sa. "Take kowa ya matsa, imaan ta kallesu tace umma ta suma Ku taimakamin mufitar d ita dan Allah, wata mata tace yarinyar saifa hakuri dan Allah ya amshi abarsa... What? Karya kuke wallahi umma nada rai tacemin very soon zata samu lpy, wayyo umma ki tashi ki qaryata mutanen nan. Haka imaan tayi ta surutai, kamar wata zararra, "bayan minti 20 aka kai umma gidan ta na gsky. "Imaan kuwa fita tayi tana hada hanya tana kuka kowa daya kalleta saita basa tausayi, saidai fah kowa ya wuce dan wannan zamanin tsoro gareshi mutane sun 6ata sunan wasu, ma'ana idan mutum yyi niyyar taimakon ka sai kaga Wanda aka taimaka ya kai Wanda ya jawo shi cikin inuwa zuwa rana. "Haka imaan tayi ta galallawar ta kan hanya, ga yunwa ga tashin hankali, A kasan wata bishiya ta dan rakube dukda akwai samari dake zama ta wajen hakan be hanata zama ba sbd gajiya da tayi.
"Da dare kowa na harkokin gaban sa, imaan tana kasan bishiyar nan, bata koma gida ba kasncewar 'yar 50 din data rage mata ta fadi, babu kuma Wanda zai taimaka mata ta koma gida, cikin ta ne yake juyawa sakamakon rashin abinci tun jiya d rana da taci, "a hankali take jin hirar wasu samari kala2 suna cewa ah baba da ganin ta ai zatayi mai, tun rana take kasan bishiyar nan, kaga mu afka mata kawai. Imaan najin haka ta mike ganin su tayi sun nufo ta. "A take tasa gudu dan ta lura basuda imani, ai suna gaanin tasa gudu suma suka Mara mata baya, sosai hankalin imaan ya tashi ganin ita suke be dgske.
"Tafiya yake yana driving hankali kwance, sai jin music yake, yana cikin tafiya yaji ya bugu Abu, ai da sauri ya fito a motar, "ganin mace yyi kwance da alama taxo tsallakawa ne, duba kanta yyi yaga jini Na zuba kamar an bude famfo, dan karamin tsaki yaja danshi bazai je hospital ba at dis tym around, kusan 12 fah kenan, daukar ta yyi yasa bayan mota da nufin tafiya da ita gida.
Sosai yake gudu, dan yaga jinin d gske yake fita. Tafiyar 15mins ne ta kaishi tangamemen gidan nasu, "da gudu ya dauko ta a bayan mota sannan ya shiga da ita gidan, "mummy ya kira sunan ta, mummy dake shirin tashi dan komawa daki tayi bcci ta juyo ganin sa riqe da yarinyar mummy tace _subhanallahi_ me name gani farooq? Farooq yace wlhy mummy kade ta nayi a mota tazo tsallakawa, mummy tace toh me kke jira ji yanda jini me zuba oya yi sauri ka dauko _first_ _aid_ _box_ farooq ya kwantar da ita yace ohk. "Side dinsu ya wuce a gurguje yaxo sannan ya fara kokarin tsaida jinin, bayan ya gama sannan ya gwada jinin Yarinyar yaga group O positive, ya kalli mummy, mummy tace meya faru? Farooq yace tana bukatar jini ne, mummy tace toh sa mata naka. Farooq yace ba daya bane, coz nawa O negative ne, mummy tace toh yanxu ya za'ayi? "Farooq ya kalli Omar da tun shigowar shi yana kan wani kujera yasa system a gaba da alama akwai abinda yake, gefe guda coffee ne ya gefe Yana sha a hankali, "yace uhum ko bro zai bada nashi. "Mummy tace ban gane ba, bakuda bambanci ta kowanne waje taya jinin Ku baze zo daya ba?
Nuceey luv😘
[8/14, 4:56 PM] Nuceey luv😘: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓
26_30
"Farooq yace yes mummy we ar identical twins, buh it can't nevar be dsame, mummy mutane dayawa basa iya banbantamu Amman ke kina iyawa, kinga dole akwai hanyar da kike ganemu koh. "Mummy tayi murmushi tace yeah, yanzu dai a samu mafita. "Farooq yace ki dan fadawa bro ko zai bata, mummy ta kira sunan.Omar tace zo a Debi jinin ka a bawa wannan baiwar Allah'n. "Omar dukda yasan positive gareshi Amman ya hade girar sama data kasa yace ni mummy jini na negative ne, mummy ta saki baki tace tohhh yaushe ka faramin karya omar? Sunan da ya Dade beji mummy ta kirashi kai tsaye ba. Gashi Sam bayason bacin ranta, dan haka yace ma farooq zo ka diba, ya fada yana kumbura fuska, farooq kuwa dariya ce taso kwace masa ganin yanda bro dinsa ya wani bo ne face. "Yana sa allura jikin sa, omar yace auchhhh... "Farooq yyi murmushi a zuciyar sa yace ji mutumin d yake fede mutane Amman ji yanda yake wani noke jiki.. Omar ne ya katse shi da fadin kayi abinda ke gabanka ba tunani ba ka wani barmin allura cikin jiki tana zuke min jini. "Dariyar d farooq yake boye ta subuce, yace sorry bro nan ya cire allurar, Omar kuwa yahau jijjiga hannu ransa a bace.
"Mummy tace kaita dakina saika daura mata jinin tunda dare yyi ai ba'a barta a falo ba, farooq yace toh mummy, nan yace bari naje side dinmu na dawo 2mins pls, mummy tace no prob. "Kallon omar tayi daya ci gaba da latsa system kamar bashi ne dazu yake karar ciwo ba, daidai zai kai coffe bakinsa mummy tace kai son tashi ka dauki yarinyar muje daki kafin ya dawo, Atake omar ya fara tari dan coffee daya sha be wuce ba, mummy tace sannu, ganin tarin yake d gske ta bude fridge dake dakin ta dauko masa ruwa, karba yyi yasha, bayan ya lafa.. Mummy tace toh tashi ka... Bata karasa ba ya sake wani tarin wannan karan na karya ne danshi harga Allah beji zai iya daukar ta ba dukda tunda aka shigo d yarinyar be kalleta ba, wayasani koh kazama ce ya fada a ransa yana me ci gaba d tarin karya dukdan kar mummy ta matsa masa d zancen. "Mummy kam ta dauka tarin gaske ne sai sannu take masa, ahaka farooq ya qaraso da sauri sannan ya dauki yarinyar ya kaita dakin mummy, omar na ganin haka ya daina tarin. "Kan dan karamin gadon mummy ya ajiyeta sannan ya daura mata karin jinin.
"Mummy ta shigo, farooq ya dago bayan ya gama yace gata nan mummy gud nyt. Mummy tace ohk nyt.
"Dasafe around 11 duk sun hallara kan dining danyin breakfast, mummy ta kalli farooq bayan duk sun gaishe ta, tace yarinyar nan bata farfado ba fah har yanzu. "Farooq yace ba damuwa mummy nan da 5hrs zata tashi insha Allah. "Mummy tace Toh Allah yasa, farooq yace ameen, omar kam sai cin abincin sa yake cike da kwanciyar hankali,
"Farooq yace wai mummy yaushe daddy zai dawo? Mummy tace sai jibi. Farooq ya gyada kai yace toh Allah ya kaimu tace ameen.
Nuceey luv😘
[1/29, 5:48 PM] +234 813 725 2431: [8/16, 1:20 AM] Nuceey luv😘: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓
31_35
"Bayan 5hrs yarinyar ta fara motsi da hannun ta, can ta fara motsi da kafar ta, "daidai lkcin mummy ta shigo dakin, ganin tana motsi tayi saurin isa gaban ta sai hamdala take, fuskar ta tashafa tace sannu koh, a hankali yarinyar ta bude idanun ta, tass ta sauke su kan mummy, a razane tayi kokarin tashi, mummy ta tayata mikewa, yarinyar tsayawa tayi tana kallon dakin daya yi mugun haduwa, tunda take arayuwa bata taba shigar daki irin wannnan ba, shin kodai gidan yankan kai ne? Take zuciyar ta ta bada dammm, kallon ta tadawo kan mummy da itama kallon ta take, "muryar ta na rawa tace baiwar Allah dan Allah a INA nake? "Mummy tayi murmushi tace kwantar da hankalin ki, yanxu dai sakko daga gadon nan kiyi wanka tun jiya kike bacci, "zaro ido tayi balo-balo tace bcci tun jiya? Kallon Agogon dake manne a dakin tayi Wanda yyi mugun haduwa 4:05 ta gani, a rikece tace meya kawoni nan dan Allah... Bata karasa ba taji cikin ta ya murda kanta ya Sara ahhhh tace, mummy ta riko ta tace tashi ga bayi shiga kiyi wanka daga baya saimu yi mgn, ba musu ta mike, sannan ta fada toilet bayan mummy ta taimaka Mata.
"Sanda ta shiga toilet din kallon kauyanci takeyi, tayi kusan 5mins tana tsaye ta rasa inda zata taba, fitowa tayi, mummy da mamaki tace harkin gam...., bakin tane ya katse ganin ko alamar wankan batayi ba, "yarinyar tace a hankali bansan ya zanyi ba. Mummy ta mike ohk, follow me, nan tabi bayan ta, cike da nutsuwa mummy ta nuna mata komai sannan ta fito. Nan itama tayi komai kamar yanda mummy tace.
"Fitowar ta, ta iske mummy bata dakin, nan tayi gaban mirror, anan ta shafa mai me kamshi kansancwar ta 'Yar son kamshi hakan be mata wahalar gane wasu abun ba. "Bayan ta gama ta juyo dan maimaita kayan ta. "Harta cira zata saka mummy ta shigo rike da tray na abinci, "da sauri mummy tace aa ga kaya nan na fiddo miki dasu dauki ki saka, wata doguwar riga CE me kyau gaban kirjin anyi mata kwalliyar duwatsu masu hasken kyau. "A kunyace ta dauki rigar ta saka tana mamakin wannan Matar daga haduwa bata santa ba tahau yi mata hidima.
"Bayan ta gama mummy ta miko mata tea me kauri, girgiza kai tayi tace ta koshi. "Mummy tace ki saki jikin ki bazan cutar dake ba, jin haka ta karbi tea din, daman cikin ta sai murdawa yake ga kanta sai zafi yake mata tamkar zai tsage. "Bayan ta kammala mummy ta miko mata plate na dankali da kwai, nan ma saida taci kusan rabin plate sannan ta aje, bayan gama mummy ta bata magani tasha.
"Saida ta huta na 5mins, sannan mummy tace ya sunan ki? Yarinyar tace *FATIMA* Amman amfi kirana da _IMAAN_, mummy tace wow wat a nice name, ta fada tana murmushi, Imaan itama murmushi tayi dukda ta qagu taji dalilin ta na zuwa gidan nan, "gane hakan yasa mummy ta fara bata lbrin abinda ya sameta da yanda aka kawota gidan, sai alkcin imaan ta tuna ashefa wa'annan samarin da suka bita da gudu shi yyi sanadin ta na tsallaka titi har abun yazo da tsautsayi. "Mummy tace so ki fadamin inane gidanku sannan meye dalilin ki na fitowa daga gida A wannan tsohon Daren????
Nuceey luv😘
[8/16, 10:27 AM] Nuceey luv😘: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓
36_40
"Imaan tace, sunana Fatima abubakar, INA zaune a nan kano unguwar rijiyar lemo, mahaifina malam abubakar da umma ta Sadiya sunyi auren so da kauna asalin su 'yan Maiduguri ne wannan tashe tashen bom din yasa sukayi hijira suka dawo garin Kano da zama, inda mahaifina ya sai dan madaidaicin gida da sauran kudin dake gareshi, daga nan ya fara sana'ar saida kaji, da wannnan muke cikin rufin asiri, tun INA shekara 5 a duniya Allah yyi masa rasuwa, sosai ummata ta shiga wani hali na tashin hankali kasancewar ba kowa suke dashi a garin kano ba, haka dai ta fara sana'ar wankau makota su kawo mata ta wanke a haka take ci damu, nayi makaranta ta INA js3 yanxu haka kasancewar halin yau dukda ta gwamnati CE dole za'a bukaci wasu kudi a wajen mu dan zana takar dar j.s.c.e. "tun lkcin muke ta fafutuka Allah be bamu ikon hada kudin ba, bangaren islamiyya kam Alhamdulillah na kammala sauka ta, sai hadda da wasu littafai da nake yanxu... "Labarina na karshe shine mafi muni da rashin dadin ji, nan taja numfashi tare da matse hawayen da suka cika mata ido tun dazu. "Sannan tace, jiya INA wanke wanke..... Tass ta zayyane wa mummy abinda ya faru da ita jiya, da rashin mahaifiyar ta da tayi.
"Allah sarki mummy tace cike da tausayin imaan, tace gsky na tausaya miki sosai dukda mummy ta fahimci a hospital na yaranta abun ya faru, saidai taja bakinta tayi shiru. "Ta kalleta tace Imaan, imaan tace na'am. Mummy tace kin amince na maye miki gurbin Wanda kika rasa? Imaan ta zaro ido waje dan Abin mamaki ya bata tace ni kuma?, mummy tace eh, Imaan tayi kasa d kanta tana wasa d 'yan yatsun ta. "Mummy tayi murmushi tace tun lkcn Dana ganki sai naji hankali na ya kwanta d ke, tunda nake yarana biyu, gashi inason 'ya mace a rayuwa wa. Koda ace akwai iyayen ki a Raye daman zan nemi alfarmarsu su bani ke, Amman cikin ikon Allah saiga yarinya tazo har gida na. "Imaan tayi murmushi kawai. "Mummy tace daga yau mummy zaki dinga kirana ba baiwar Allah ba.. Ta karasa fada tana murmushi. "Imaan itama murmushin tayi kasan zuciyar ta cike da farinciki dan koda ta koma gida bata fa kowa, gashi batasan ma inane hanyar Maiduguri ba. "Kallon mummy tayi da murmushi tace banda bakin da zan gode miki mummy saidai nace Allah ya saka da Alkhairi. "Mummy tace ameen. Tashi kiyi sallolin da ake binki, imaan tace toh.
"Bayan ta idar ta koma jikin mirror nan ta sake fesa turare da simple make up, sannan ta fito waje kamar yanda mummy tace mata. "A falo ta tarad da mummy zaune tana kallo. Itama zama tayi a kasa. Mummy tace haba imaan tashi daga nan ki dawo nan. "Imaan ta mike ta koma inda mummy ta nuna mata kusa da ita. Ahaka suna hira jefi-jefi, can sukaji An bude kofar falon tare da sallama.
"Mummy ta kalle sa da murmushi tace tofah yau Kaine ka dawo da wuri haka? Farooq yyi murmushi yace kinsan nabar patient a gida ya kamata na duba ta. Mummy tace hakane, imaan na jinsu saidai hankalin ta na kan film din da take kallo. "Nan farooq yace mummy INA take? Mummy tayi masa nuni da ita, oh abinda ya fada kenan danshi tunda ya shigo hankalin sa be kai gareta ba. "Matso yyi kusa da ita,.. Yaga hankalin ta na kan Kallo yadan buga kujeran yana kallon ta. "Da sauri ta jiyo gareshi. "Tana ganin sa ta hade girar sama data kasa dan har abada bazata manta fuskar nan ba, fuskar da tayi sanadin mutuwar umman ta. "Take ta maida kallon ta wajen Mummy, mummy tana ganin haka ta kauda kai, tasan za a rina, haka ta fada a zuciyar ta.
"Imaan zata sunkuyar da kanta kenan sai sukaji an sake bude kofa, daga kanta tayi, tasss ta sauke manyan idanun ta cikin nasa bala-balan idon, a razane ta maida kallon ta ga farooq Wanda shima ya hade rai kamar yanda omar yyi sbd yaga yyi mata mgn tayi banza dashi shine ransa ya fara baci. "Ido imaan ta zaro ganin fuskoki masu kama daya, Wanda duk kwakwarta ta kasa tantance waye omar daga cikin su. "A zuciyar ta tace *OMAR* *KO* *FAROOQ*??? Wanne ne a cikin su yyi mata rashin mutunci???
Nuceey luv😘
[1/29, 5:48 PM] +234 813 725 2431: [8/17, 5:34 PM] Nuceey luv😘: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓
41_45
"Omar kam mamakin ganin ta yyi, dan bazai manta yarinyar data sha gaban sa a hospital ba abinda yasan tabbas kowa shakkar sa yake shiyasa tayi matukar bata masa rai., wata xuciyar tace kodai itace yarinyar da ka bawa jini? Ai da sauri ya sake kallon ta lkcn imaan ta sunkuyar d kai. "Take ran omar ya sake baci shidai gsky idan wannan kazamar aka bawa jinin sa gsky an gama dashi. Mwtss Yaja tsaki qasa2 batare da kowa ya jisa ba. "bece uffan ba illa wucewa da yyi, "mummy na ganin hakan tayi kokarin kawar wa imaan tunanin da take, a hankali ta furta omar lpyr ka yau ko mgn babu? Jin hakan yasa imaan tayi saurin kallon mummy dan ganewa idon ta wanne direction mummy ke kallo. Anan ta tabbatar wa zuciyar ta Wanda y shigo yanxu shine omar. "Omar batare d ya kalli mummy ba yace yau a gajiye nake mummy, mummy tace oh toh sannu., "imaan tajuyo kallon ta ga farooq daidai lkcn shima ya dawo da kallon sa ga imaan din dan shi harya maida hankalin sa ga kallo. "Yanxun ma fuskar sa a daure ya sake maimaita mgnr dazu, cikin muryar ta me sanyi cike da nutsuwa tace masa da sauki. "Farooq yadan ware ido dan yanda take sarrafa bakin ta yyi matukar birge shi., besan lkcn daya dan saki fuskar sa ba. Shima a hankali yace toh INA ne yake miki ciwo yanxu? "Imaan ta sunkuyar da kanta ganin ya tsareta da ido, tace ba komai, yace kinsha mgni? Nan kuma kai ta gyda masa. Farooq ya mike yana fadin gud. Sannan ya tashi yyiwa mummy sallama ya shige side dinsu.
"Yana tafiya mummy ta kalli imaan tace sai kinyi hakuri da sabbin yayun ki, a hankali komai zai tafi normal, imaan kuwa ta kwakulo murmushi kawai dan bataso ta nunawa mummy irin tsantsar tsanar dake tattare a zuciyar ta da takeyiwa omar.
"Omar kuwa tana komawa daki bayan yyi wanka ya canja kayan sa zuwa na shan iska. "Ji yyi duk ransa a bace yake, dan haka ya mike da sauri ya nufi dakin farooq, q falon sa ya tarad dashi yana kallo. "Farooq yace lpy bro na ganka haka? Omar ya watso masa kallo bayan ya iso gareshi yace uban wa ya baka izini kasa wa wannnan kazamar jinin jiki na? "Farooq cike da rashin damuwa yace wannan kuma daga baya kenan ai da kasan bazaka bayar ba meyasa ka bata tun farko? Omar yace ba wannan na tambayeka ba ya katse shi zuciyar sa na zafi. "Farooq yace so ka tmbyi mummy, "omar yyi kwafa batare da yace komai ba yabar wajen. "Farooq kuwa tsaki kurum yaja.
" Da dare dukka sun hallara kan dining table, Amman banda imaan tana dakin mummy tayi zaman ta dan batason sake haduwa d wannan omar din. "Mummy najin shiru bata fito ba, dan haka ta mike ta koma dakin. "Mummy tace imaan taso mana muci abinci. Imaan tace na koshi mummy, mummy tace banason gardama oya taso. "Ba yanda imaan ta iya haka ta biyo bayan mummy. "Suna zuwa wajen taja mata kujera dan ta zauna. "Omar harya dauko spoon zai kai bakinsa yana ganin ta take yaji shu kansa abincin ya fita ransa dan wani irin kyama imaan din ke bashi Ahe spoon din yyi dukda wata irin yunwar da yakeji haka ya tashi yabar wajen. "Mummy na hankalce dashi saidai batace uffan ba. "Farooq kam tabe baki kurum yyi yaci gaba dacin abincin sa. "Imaan kuwa duk sai taji itama ranta ya sake baci. ganin irin kallon rainin da omar ya bita dashi saikace yaga kashi kafin yabar wajen. "Mummy CE ta katse ta d fadin zauna mana imaan, dolen ta, ta zauna sannan mummy ta turo mata plate gaban ta don ta Debi abinci.
Nuceey luv😘
[8/17, 6:38 PM] Nuceey luv😘: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓
46_50
"Ahaka ta tura abincin bada dadewa ba farooq ya yabar wajen shima. "Haka itama tana gamawa ta tashi, kallo ta zauna ta fara yi.
*******
"Saida aka kai ruwa rana kafin daddy ya amince da zaman imaan a gidan dan a ganin sa tamkar an dauko wani datti ne an ra6a musu, kasancewar yau ya dowo., sosai mummy taji dadi na amincewar Daddy da yyi. Dan Haka ta fara tunanin kai imaan makaranta dan inganta rayuwar ta.
"Da safe bayan sun kammala a dining danyin breakfast, yauma sai daga baya imaan ta iso wajen. "Kanta a kasa ta shiga gaishe da daddy, daddy ya amsa mata ba yabo ba fallasa dan Har yanxu da dan sauran kin da yake mata. "Nan ta gaishe da mummy, mummy ta amsa mata ba yabo ba fallasa. "Kallon ta takoma ga twins duk hankalin su nakan abinci har omar kasancewar mummy ta bishi daki jiya ta nuna masa rashin dadin ta na kyamar imaan da yake nunawa a fili, nan ma muryar ta na rawa ta gaishe su. Kamar bazasu amsa ba can daga baya farooq ya amsa mata. Mummy tace xauna kici abinci, imaan ta zauna daidai kujerar da mummy ta nuna mata wacce take fuskantar omar. "Gurin yyi shiru kowa abinci yake aikawa cikin sa. "Imaan tayi nisa cikin tunani dan haka take zuciyar ta tabata shawarar tunda kowa hankalin sa nakan abinci bari ta dago da kanta dan tantance omar da farooq, dan idan suka hade rai bata gane waye omar, dan har muryar su iri daya CE. "A hankali ta dago kanta, daidai lkcn omar ya dago kansa dan ya gama cin abincin kenan, ai carab suka hada ido., atake omar ya watso mata kallo na cike da tsana. "Itama dukda ta tsorata hakan be hanata watsa masa hararaba. "Abinda ya bawa omar mamaki kenan, take ya boye mamakin ya sake hade gira. "Mikewa yyi zai bar wajen. "Mummy tace har ka gama? Yace eh mummy, "mummy tace da akwai zancen da nakeson maka. "Omar yace OK, sai mummy tace but jeka shirya sai kazo ka sameni, omar yace toh.
"Kowa ya gama sannan aka bar wajen. "Imaan CE ta tashi ta shiga tattare plate din dake wajen. "Saida ta gama mummy tace dauko hijab dinki. "Imaan tace toh. "Nan ta koma daki ta dauko sannan ta dawo falo. "Shima omar shirin tafiya office yyi sannan ya tarad d mummy a falo. "Bayan ya zauna. "Mummy tace yauwa son, so nake ka wuce da imaan wannan skul din danyi mata interview sannan kayi duk abinda suka bukata. "Gaban imaan ne ya bada rass itafa Sam batason kasancewa kan wannan marar imanin. "omar kam tsabar takaici kasa cewa komai yyi taya mummy zatace ya dauki wannnan dattin yasa a motar sa? "d Sauri yace am mummy inada emergency fah., mummy tace son kenan ai idan kanada emergency ranar koh breakfast bakayi ai, omar kamar zaiyi kuka yace toh mummy ga farooq nan sai ya kaita. Mummy ranta a bace tace idan bazakayi abinda nace ba ka fadamin basai kanamin kwana2 ba. "Omar ya sunkuyar da kansa zuciyar sa sai tafasa take shi tunda yarinyar nan tazo gidan nan mummy take masa fada kuma duk a dalilin ta abinda yafi komai tsana kenan ayi masa fada. "Dolen sa ya mike murya can ciki yace shikenan. Sannan ya kama hanyar fita.
"Mummy ta kalli imaan tace tashi ki bisa, itama ba musu ta mike, dan ta lura Sam mummy bataso ayi mata gardama.
"A mota ta samesa, "ya kifa kansa a sitiyari ransa na masa quna. "Imaan tayi kusan 5 sec kafin ta murda kofan baya da nufin shiga. "Omar najin alamun an bude ya dago kansa tare da watso mata wani mugun kallo. "A take imaan ta sunkuyar da kanta. "Wata irin tsuka yaja sannan yaja motar da qarfi Wanda yyi sanadiyar girgiza 'yanmatan hanjin imaan dan ta tsorata da lamarin sa a zuciyar ta tace kodai aljanu gareshi? Haka yake ta gudu kamar zai tashi sama. "Can kuma ya rage gudun daga baya kuma, ya tsaida motar. "Yana tsayawa yyi shiru bece komai ba. "Imaan ma shirun tayi tana kallon ikon Allah. "Can omar ya jiyo cikin tsawa yace jira kike na fitar dake ko me? "Imaan ta zaro ido yyinda take kokarin fita daga motar, a zuciyar tace toh taya zan San fita kkeso nayi bayan ni ba Allan musuru bace, "tana sauka Omar ya Watso mata wasu kudade masu yawa, batare daya yi mata bayanin komai ba ya fisgi motar sa ya barta a wajen. "Baki bude imaan ta saki ta bishi da kallo kamar wata wawiya tama rasa abin cewa dan takaici, a fili tace me kuma yake nufi da wannan kudaden???
Nuceey luv😘
[1/29, 5:48 PM] +234 813 725 2431: ® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓
51_55
"Mamaki ne ya isheta, tayi kusan 10mins a tsaye ta Tara abin yi, "driving yake harya wuce sai ya ganta, hakan yasa yyi riverse, 'imaan na tsaye kamar soja sai ganin mota tayi ta tsaya gaban ta, da sauri ta matsa tare d kawar d kanta dan batasan ko waye ba. "Farooq yana daga ciki ya fito, imaan na dago kanta ta fahimci farooq ne kasancewar kayansu ya banbata bayan haka har motar su iri dayace. "Farooq ya matso kusa da ita sanna. Yace imaan me kike anan wajen? "Imaan kamar zatayi kuka, tace ya omar ne ya ajeni a nan kuma mummy tace ya kaini skul ayi duk abinda ya dace, "farooq y jijjiga kai yasan bro dinsa ba'a taboshi ba yana wulakanci bare kuma aka tabo shi. "Nan yace shiga mota muje. "Imaan tace toh. "Har zata shiga baya yace dawo gaba, haka tabi abinda yace. "Ga mamakin ta nan suka sake gangarawa inda omar y sauke ta, basuyi tafiyar 5mins suka isa makeken gate din Queen Amina secondary school, a sai yanzu ta fahimci dalilin kudin da ya omar ya bata wato taje tayi komai da kanta kenan?, yo ita idan mutum ya sani ba taya zaisan akwai skul ta wajen? "Ahaka suka karasa bayan sun shiga cikin skul din. "Nan farooq yyi mata komai yanda ya kamata har akayi mata interview yana wajen yana mamakin yanda imaan ke ja, komai aka tabo ta sani. For d first tym yaji tadan birgeshi Kadan dan yanason yaro me hazaka. "Bayan an gama PC skul din tace zuwa Monday ta fara zuwa skul. Farooq yyi mata godiya sannan suka fito. "Bayan sun fito imaan tace am ya farooq, farooq ya kalle ta batare d yace komai ba. "Kudin hannun ta d omar ya watsa mata take mika masa tace gashi, farooq ya yatsina fuska yace mezan dasu? Imaan tace kudin skul din kenan ai. "Farooq yace mtwss shige muje. "Imaan taja bakinta tayi shiru batare d tace komai ba, sannan suka bar makarantar. "Imaan na jiran ya maida ta gida sai gani tayi yabi wata hanyar, "imaan bata ida tunanin ta ba, taga ya shiga da ita hospital dinsu. "Har yyi parking imaan ta kalleshi zatayi magana farooq yasa yatsan sa a baki alamar tayi shiru, haka taja 'yan matan bakinta tayi shiru. Sanan ya fito, itama fitowar tayi, wata hanyar yabi dasu, dan haka itama ta fara binshi kamar jela, duk Wanda suka hadu saisun gaishe shi, ammn yi yake kamar besan d zaman su ba. "Ahaka su shiga can su fita can har suka kai office dinsa, imaan dai mamakin girma da lungu2 hospital din takeyi. "Bayan sun shiga ya nuna mata waje ta zauna. "Shikuma yasa rigar likitoci yafara gudanar d aikin sa. Imaan kam ta sunkuyar da kanta tana cike da kunya yanda mata ke fadar matsalolin su ga ya farooq, a yanda ta lura shi ko a kwalar rigar shi dan ko aikinsa yake batare d wata matsala ba. "Kusan azahar imaan na zaune harta fara gajiya, "ga yunwa data addabe ta, tana wannan zaman aka kawo mata abinci lkcn farooq ya fice dan yin salla. "Imaan tace waye ya turo ka? Yace oga. Sannan Wanda aka turo din ya fice. "Imaan kuwa yunwa takeji sosai dan haka ta fara aikawa cikinta abinci, har ta gama farooq be dawo ba, dan haka ta mike tayo alwala tayi salla. "A wajen yin addu'a ta bingire tana bacci. "Lkcn da farooq ya dawo tabe baki kurum yyi.
"Mummy na gida taga har azahar ba imaan babu labarin ta, dan haka tahau kiran omar Amman taji wayar a kashe, hankali tashe ta kira farooq tace dubamin omar ko lpy ya kashe wayar sa? Farooq yyi murmushi yasan imaan zata tambaya dan haka yace eh dazu munyi salla dashi a masallaci, saidai yacemin akwai emergency a gaban sa, maybe dan hakan ya kashe wayar sa. "Mummy ta sauke ajiyar hrt, har zata tambayr shi imaan sai kuma ta fasa. Nan suka katse wayar.
"Omar kuwa yana office hankali kwance yana gudanar da aikin sa, tun jiya wata number take damunsa, kuma duk layinsa dsme number ake kira, ana turo masa messages na kauna. Dalilin hakan yasa ya rufe gaba1 wayoyin sa dan bayason takura.
"Da yamma masu tafiya nayi, masu aikin dare na zuwa, omar ne ya fito a office bayan ya kammala abinda zaiyi, ya wuce inda motar sa take, anan ya shige yyi hanyar gida hankali kwance.
"Farooq kuwa sai magrib sannan yace imaan ta taso su tafi dan sosai hankalin imaan ya tashi duk taji zaman hospital din ya dameta, "lkcn da suka bar hospital din wata hanyar taga yabi da ita, da sauri ta kalleshi, "wannan karon ma hannu yasa mata alamar tayi shiru. "Wayar shice tayi kara bayan ya kara a kunne yace hello, oh yeah gani nan hanyar zuwa club din, ohk bye. "Imaan hankali tashe ta zaro manyan idanun ta batasan lkcn da ta furta club????? Da karfi ba, Wanda taso tsorata farooq, tsaki yaja yace yes, imaan tace dan Allah ka maidani wajen mummy, farooq yace cinyeki akace za'ayi? Imaan tayi shiru, farooq yace so karna sakejin bakin ki.. A zuciyar sa kuwa yasan dalilin sa nakin maida imaan gida da wuri, take yyi saurin kashe wayoyin sa ma gaba1.
"Omar kuwa bayan yyi parking a gida. Tsaye ya tarad d mummy a falo, yanayin sallama, mummy batare d ta amsa sa ba tace INA *imaan*??? darararammm take qirijin omar ya fara dukan Tara Tara danshi gaba1 ya manta da zancen wata imaan, shi sai yanxu ya tuna inda ya barta,a zuciyar sa yace so bata dawo gida ba kenan?, eh lalle yau mummy zatayi farfesun sa.... Bai ida zancen ba mummy ta katse shi da fadin bakaji me nace bane?
0 comments:
Post a Comment