"Aiki mukeyi,kuma kukanku zai iya bada matsala,ayi haquri da qaddarar Allah,mijinta yana bakin qoqarinsa qwarai da gaske,kuma ko yanzu ma an fara ganin nasara,son ba ko yaushe suka sakata surutan da bige bige ba".
A nan suka zauna cikin matsanancin halin kuka da jimami,shi kansa gidan gaba daya ya sauya yayi wani iri,dama raihanatu tana bakin qoqarin tsaftaceshi da kula dashi,ita kanta tana zaune rakube daga gefe,tausayin iyalin duka ya kamata ganin tashin hankalin da suka shiga da cutar bogin da aka laqabawa matar da bataji ba bata gani ba.
"Ko zan iya ganinta?" Maama ta fada cikin zallar alhini da tashin hankali. Kallon juna adam da malam usama sukayi,sai ya maida dubansa ga maaman
"Bako yaushe ake shiga gurinta ba,saboda hakan yana sakata yunqurin guduwa,da kuma surutai marasa kan gado,amma yanzu barin na fara shiga nayi mata wasu addu'o'i,yadda ba zata cutar da ku ba koda kun shiga din" ya fadi hakanne saboda allurar da aka danqara mata sunason ta fara aiki,jikinta ya saki gaba daya,yadda ko magana ba zata iya dasu ba barw ta fadi wani abun da zata shanshano ainihin batun.
Lokacin da ya shiga dakin ya isketa allurar ta fara mata aiki,ya hadiyi wani yawu muqut yana qare mata kallo,kullum yaga yarinyar sai ransa ya biya,tana da wani mugun kyau da kyakkyawar suffa,Allah Allah yake wataran ya samu dama kamar hakan nan sanda bata da sauran qarfi shima yadan dandanata,ya rage qishirwar dake ransa,baisan ma wanne irin rashin rabo bane ya sanya adam din yake mata wannan izayar,shikam inda shine ya mallaki zuqeqiyar mace irin wannan,baisan wanne asarar bace zata sakashi yayi sakacin da zai rasata ba,ai shi kam zai iya cewa ma Allah ya sallameshi a duniya dai.
Kamar masu cutar rashin kuzari haka suka shigo dakin,su hudu ciki harda afifa da maama,gaba daya dakin a hautsine yake da fasassun abubuwa,wanda duka setup ne. Wani irin kuka afifa ta saki,ta kuma durfafi sãahar a gigice ganin yadda gaba daya ta koma zararriya sak,dakatar da ita malam usama ke shirin yi yana fadin
"Subhanallahi,karki qarasa gareta,na samu nayi musu addu'o'in kashe jiki,karki zaburar dasu" saidai kafin ma ya qarasa bayaninsa tuni ta isa. Rungume sãahar din tayi cikin jikinta,dumin afifan yana ratsata ta sauke wata iriyar qaqqarfar ajiyar zuciya,ta lumshe idanunta da suka kasa sauka daga fuskar maama dinta,tanason koda motsa labbanta ne ta fadi kalmar da maama zata fahimci diyarta lafiya lau take amma ta kasa furta komai.
Irin kukan da suka wuni sunayi zai baiwa dukkan me imani tausayi,don ko raihanatu haka ta dinga boyewa a kitchen tana tayasu kukan, tare da jin qaqqarfar tsanar momee da shi kansa adam din,duk da kasancewarsu jininta. Abinci kuwa ba wanda ya iya sakawa cikinsa dukkansu,har zuwa dare suna zaune a gidan,daren da ya riski sãahar batasan ma me akeyi ba,tana can wata duniya ta daban da adam da likitocinsa suka kaita.
Da qyar Dr mamman ya lallabasu maama da afifa suka wuce gida,da nufin gobe sa dawo. Hankalin adam ya tashi sosai jin su yaa Saifullahi suna can neman asibiti me kyau da zasu dauketa su kaita,hakan ya tabbatar masa asirinsa yana gab da tonuwa,sannan kuma yana gab da tafka asarar da gwara mutuwar sãahar a wajensa akan yayi wannan asarar ta dukiyar daya narka zuwa dollar,ga passport dinsa na yaransa dana matarsa duka a hade. Kwana maama tayi tana kuka,tana ganin abun kamar almara, innocent sãahar dinta,wadda duka duka shekarunta tsakanin ashirin ne zuwa ashirin da daya,idan tayi wuta sa biyu amma wannan mummunar qaddarar ta afka mata.
A daren gaba daya afifa bata samu bacci ba itama,duk inda ta juya fuskar sãahar take gani,kamar yadda adam baiyi bacci ba shima,yanata juya yadda zai matsa sãahar din ta sallameshi salin alin,tun bata ritsa dashi ba.
Wannan tunanin ya sanya washegari ya yayyaba mata maganganun da suka qona mata rai yasa kuma akayi mata allurar maaye da kyau waiko zata magantu,wannan yasa ta zabure,ta dinga fashe fashe tare da surutai a dakin saboda qarfin allurar,hakan kuma sai yayi dai dai da zuwansu afifa. Abun ya yiwa adam dadi ganin tashin hankulan dake kan fuskarsu tare da sake yarda da cewa eh lallai sãahar din ta haukace,wani irin mawuyacin yini sukayi a gidan, qwayar shinkafa babu wanda ya kaiwa cikinsa sai zallar ruwa. Sãahar na kwance daga bakin qofar dakin inda allurar ta bugar da ita daga qarshe tana jin muryoyinsu jifa jifa,wannan yasa ta yita motsa bakinta tana magana dasu,amma babu me jinta kasancewar sautin baya fita,taji muyar maama dinta na addu'ar Allah ya yaye mata ya bata lafiya yafi sau shurin masaki, furucin dake qonawa gami da soya mata zuciya,ya tabbata dai da gaske adam yaci galaba a kanta,ya kumma manna mata haukan dai,sannan ya sauya mata suna zuwa MAHAUKACIYA, sunzo sun taddata tana attitude na mahaukata tuburan.
*_W A S H E G A R I_*
*_waiwaye_*
"Ina sonki.....kuma banajin zan daina sonki,saidai kin shiga hurumin daba naki ba,kin shigar gonar daba taki ba,kin tsallake iyakarki,kuma a yanzu nafi buqatar wadan nan abubuwan fiye dake,ki daukominsu ki damqamin,ke kuma na barki kici gaba da rayuwarki cikin salama" kai take girgizawa tana hawaye,wani irin mamakinsa tana jin kamar zai kasheta, kowacce rana da zata bullo zuwa faduwarta cikin shakka da kokwanto take,anya wannan din ADAM NE?,anya adam dinta ne?,anya musanyensa akayi mata ba?,ko kuma wata rundunar mugayen shaidanun aljanu ta shige jikinsa ne ta samu mafaka?,don abinda yakeyi a yanzun da ainihin wannan suffar tasa ta yanzu.......bata taba ganinta a tattare da adam dinta ba,koda kuwa cikin mafarkan bacci bare a kai ga rayuwa ta zahiri,adam din da ko quda baya qaunar ya sauka a kanta?,adam din dake kuka da idanunsa idan bata da lafiya?,adam din da yake kasa bacci saboda ta shiga damuwa?,adam din da yake kasa sukuni idan tana da buqata har sai ya adar mata?,dole ta shiga shakka.....amma kuma kullum yana qara tabbatar mata da cewa shi dinne fa,bawai kama ko musaye bane,to me yake faruwa?.
"Bazan taba baka ba.....burinka bazai taba cika ba,saidai na rasa rayuwata,kayi duk abinda kaga dama" ta fada tana jin bacin rai yana taso mata,tare da wani irin qwarin gwiwar tunkarar duk nau'in kalar azaba tuggu da makircin daya shirya mata.
Wani murmushi ya kuma saki yana dubanta,da wani irin kallo na qasa qasa mai cike da tarin mugunta
"Ke kike jawa kanki koma meye,tunda ke muguwa ce ba zaki iya sallamamin abinda kikafi qarfinsa ba tako ina,to nima bazan sassauta miki ba har sai sanda kika gasu,kikaji cewa zaki iya sallamawa" daga haka ya miqe,ya fara fidda kayan jikinsa yana zubarwa a wajen.
Idanu ta bude da kyau cikin tsananin tashin hankali tana dubansa,kada dai ace haqqinsa na aure yake shirin karba kamar yadda ya saba?,zallar rashin imanin da yake gwada mata bai sanya ya daga mata qafa ba,yakance
"Har yanzu fa a sunan matata kike,ban saki igiyar ba,wannan abun dake faruwa wani issue ne na daban daya shafi interest dina da kuma naki". A duk lokaci irin wannan idan ya rabeta tana jin inama zata bude idanu taganta kwance cikin ramin qabarinta?,banda addininmu ya haramta kisan kai,naka ko na Wani,tabbas da tuni ta tsufa da kai kanta kiyama.
Da gaske so yake ya kusanceta alhalin yasan cewa cikin jinin al'ada take,rashin imanin nasa qara gaba yake,dole tace rundunar shaidanun aljanu ne suka shigeshi,don lamarinsa yafi qarfin shaidani guda daya.
Kansa tsaye ya nufota gadan gadan,kamar ba adam din nan da abaya a lokutta irin wanann yake sanyata taji babu ya ita cikin 'ya'ya mata ba,ya sanyata taji duk duniya babu macen da tayi sa'ar abokin rayuwa irinta ba,a yanzu ya koma mata wani tsohon annamimin ifritu mashayin jinin bil'adama da ko motsinsa bataso ji bare ya rabeta,bashi da maraba da qaton shaidani a idanuwanta.
Ringing din wayarsa ya dakatar dashi daga sake tunkarota,sai ya koma cikin aljihun wandonsa da ya yasar yana lalubar wayar. Cikin hanzari ya karata a kunnensa,sai kuma yace
"Ok,yanzu yanzu?,tom" ya latse wayar da sauri ya maidata,sannan ya soma mayar da kayan jikin nasa tana daga zaune tana kallonsa.
Ga mamakinta sai taga yana bi yana balle button na rigarsa yana watsarwa,ya kama gaban rigar da qarfin tsiya ya ciccisge,sannan ya tsugunna ya jawo plate din tangaran din dake ajjiye gefe wanda ya kawo mata abincin da bata budawa bare ta taba,ya dagashi har abincin ya tamfatsa shi da qasa ya tarwatse,ya dauki wani yanki daga ciki ya yanki jikinsa ya kuma shashshafe maiqon a jikinsa.
Sake miqewa yayi ya fara fatali da kayan dake saman madubi da duk wani abu na glass dake dakin yana cewa da matuqar daukaka murya
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,ki tsaya......ki tsaya don Allah,ya salam,karki jiwa kanki ciwo, Hasbunallahu wa ni'imal wakeel,ya hayyu ya qayyumu ya baki lafiya" yana fada hawaye na sauka a idanunsa,yana kuma ci gaba da tarwatsa dakin tare da sake hargitsashi,bayan tsaiwa da tayi tayi masa gyara na nutsuwa,waiko hakan zai sanya wani daga cikin ahalin nata su ankara da cewa akwai hankali tattare da ita.
Sanqamewa tayi a zaune,tunaninta ya dinke cifff kan meye manufar adam na aikata haka?,saidai koma meye tasan halinsa,ungulu ne baya jewar banza,ba shakka akwai abinda yake shirin sake qullawa. Kafin takai ga lalubo abinda ke shirin faruwa sai ta tsinci muryoyin mutanen da a kullum take addu'ar isowarsu gareta,qila akwai wani haske da zai risketa,ya kuma zama silar fitarta daga duhu zuwa haske.
Da mugun qarfi ta yunqura zata dira daga gadon,yayi caraf ya tsallako ya damqeta ya cukuikuyeta da kyau yana sake yamutsa rigata da yamutsatsen gashinta.
Ya mata mugun riqon da bazata iya qwacewa ba,saboda banbancin qarfi da kuma qarancin garkuwa jiki dake tare da ita,don haka ta bude baki da zummar kiran daya daga ciki
"Koda kin kirasun ma sun shigo sunanki bazai canza ba a idanunsu,sunanki mahaukaciya har yau har gobe,sai ranar da kika fanshi kanki,ni kuma zan wankeki a idon duniya" daga haka yaci gaba da qaraji da ambaton sunan Allah yana mata kyakkyawan riqo,ita kuma taci gaba da yunqurin qwacewa hawaye na gudu bisa fuskarta, kokawa ta barke a tsakaninsu duk da cewa ba wata nasara a hakan sai azabar riqon da yayi mata da takesha,dai dai sanda aka turo qofar da sauri aka shigo,ya saki wani lafiyayyen murmushi daga can qasan zuciyarsa,burinsa ya cika,plan dinsa ya tafi a dai dai,dama abinda yakeso kenan,shigen abinda ya faru jiya,yau ma sun sake samunta a mahaukaciyarta.
Page 52
*H U G U M A*
*_TABARMAR ƘASHI_*💔
Page 52
Afifa ce wadda ta kasa jurewa ci gaba da jin muryar sãahar din cikin wannan birkitaccen yanayin,da sassarfa ta nufo sãahar dake riqe a hannun adam da yayi wata irin wajiga,yayi hajaran majaran
"Karki ce zaki tabata, qoqari nake a yanzun ma kada ta yiwa kanta illa,don ko kanta bata ganewa bare wani"
"Komai girman haukan da bestie takeyi jikina ya bani ba zata taba illatani ba,saketa" afifa ta fada da wani irin zafin zuciya. Tashi zuciyar shima tazo wuya,amma dole ya sakar mata sãahar din saboda su maama dake a tsaye daga bakin qofa,can qasan ransa kuwa yana sake cika maqil da afifa din,baya qaunar mu'amalarta sam sam da sãahar,saboda ita din sãahar ba mai damuwa ko maida hankali akan abubuwa bace,tana da mugun kawaici da kuma sanyi akan abubuwa,duk da zazzafa ce ta fannin miskulanci da kima qin daukan raini wulaqanci ko qanqanci daga gurin kowa.
Talau haka tayi a jikin afifa,maama ta taimaka mata suka kwantar da ita saman gadon,tanata buda baki da zummar yi musu magana,saidai kalma ko daya ta kasa fita daga bakinta,don allurar da aka shimfida mata ta fara aiki a jikinta.
Shurun dakin ya dauka saboda bacci daya kwashe sãahar,afifa ta dauke dubanta daga fuskar sãahar tana jan majina saboda kukan da tasha,ta maida dubanta ga adam dake tsaye jikin qofa,gaba daya fuskarsa babu komai kwance a samanta face zallar tashin hankali
"Zan samu qur'ani?" Ta tambayi adam din,sai ya daga kai da sauri
"Eh,akwai,amma karki ce zakiyi karatu ne,an samu ta samu bacci ba kuma wani matsalan ya biyo baya" kai ta girgiza tana kafeshi da ido
"Ba inda karanta qur'ani yake zama matsala,saidai waraka,ka daukomin" ta fada tana miqewa zuwa toilet din sãahar din don ta daura alwala.
Tayi alwalar tana fitowa ta taka wani abu,sai ta tsaya taja baya da sauri tana furta
"Subhanallah" ganin kwalba ce,ta sunkuya ta dauketa ta cillata a dust bin din,ta shimfida abun salla kusa da maama wadda ke zaune tun dazun,riqe da hannun sãahar,ta zuba mata ido tana mata wani irin kallon qurilla,cike da zallar tausayinta,time to time tana tofa mata addu'o'in da taketa karantawa.
Sanda ta idar da sallar saita dauki qur'anin da adam ya kawo ya ajjiye ya fita,ta zauna dai dai saman kan sãahar din ta bude ta fara karantawa. Sai data shafe awanni uku cur sannan ta miqe ta sauka daga gadon,ta ajjiye qur'anin,ta sake juyawa da nufin komawa bandakin don tayi fitsari.
Kamar gilmawar walqiya hasken kwalbar data yar dazu ya gifta mata,saita tsaya ta koma da baya,ta tsaya gaban sharar tana duban kwalbar wadda takewa kallon sani.
Duqawa tayi ta sanya hannu ta cirota kusa da syringe din dake nuna dashi aka zuqe ruwan aka zubawa duk wanda aka sakawan ma,ta soma bin rubutun jiki tana son tantance allurar data sani din ce?. Wani irin dimuwa firgici da kuma tashin hankali ne suka shigeta farat daya,ta waro idanunta kamar zasu fado qasa,saita juya da sauri fa koma saman gadon. Gaba daya jikinta rawa yakeyi,zuciyarta na ayyana mata abubuwa kala daban daban,babban burinta a yanzu sãahar din ta farka,akwai abubuwa da alama masu tarin yawa,akwai wasu abubuwa a lullube a kima binne babu ko shakkaMaimakon karatun da taso yi,saita kasa aiwatar da komai,ta koma ta zauna saman gadon tana riqe da hannun sãahar gam kamar wadda zata bacewa ganinta,kwanyarta nason hakaito mata abinda yake faruwa da sãahar amma gaba daya tunaninta yaqi aminta da hakan. Ta jima a cikin wannan yanayin kafin taji an budo qofa. Maama ce tare da Dr mamman,dukkansu suka tsuguna a gaban gadon sãahar din,kowanne fuskarsa a narke zuciyarsu cike da rauni.
Addu'a yayi mata kamar ko yaushe,sannan yace su shirya su wuce gida,duk da ya gama karantarta sam batason tafiya gidan
"A nan yau zan kwana" afifa ta fada kanta tsaye,saboda zuciya da gangar jikinta suna bata abubuwa da dama da takeson tabbatar dasu,akwai qaqqarfan zargin daya shiga zuciyarta
"Anya?,zaki iya?" Dr mamman girema ya fada yana kallon afifan,kafin ta bada amsa adam da yake shigowa yayi caraf da zancan cikin tashin hankalin daya bugi qirjinsa na jin cewa zata kwana da sãahar
"Gaskiya abba banajin zata iya,zan iya ci gaba da kwana da ita kafin randa zamu wuce asibitin,babu abinda ta rasa,zan kuma ci gaba da kulawa,ba zata rasa komai din ba in sha Allah har zuwa lokacin da Allah zai bata lafiya"
"Kana qoqari kam,mun shaida mun kuma yaba sosai,a qalla yau kaima ka kwanta kayi bacci sosai yadda ya kamata, saboda haka yau ni zan kwana da bestie in sha Allah,don na tabbatar koda nice irin hakan ta sameni,ba zata gujeni ba koda na kwana daya ne" ta fada tana sakin qwalla,don tanason karya zuciyar dr mamman ya qyaleta ta kwanan. Ta samu nasara kuwa,don dukkansu qas sukayi da kansu,yayin da maama ke share hawaye
"Gaskiya ne,kaima ya kamata ka huta koda iya yaune, ubangiji yayi maka albarka bisa qoqarinka"
"Ameem ya Allah abba" ga fada kansa a qasa yana murza yatsunsa,zuciyarsa na wani irin bugawa da zallar tashin hankali tare da tunanin mafita,don ba shakka zuwa nan da awa daya zuwa biyu sãahar din zata iya farkawa,farkawarta kuma dai dai yake da tonuwar asirinsa da tashin ballin dukkan wani rufaffen asirinsa.
Har motarsu dr mamman ta tashi yana tsaye kamar wanda aka kafa a wajen,daga qarshe dabara ta fado masa,ya fada motarsa kai tsaye yabi bayansu ya wuce gurin likitansa. Allurar da ake mata me sanya nannauyan bacci har fiye da wadda aka saba yi mata,da kuma wadda ke sanya birkicewar kwanya ya karbo,dukkansu yasa aka sauya musu gida,tunda yasan me afifan ta karanta,harkar kafiya ne,a yanzun tana cikin matasan likitoci masu qarancin shekaru da jahar kano ke dasu,yanason yayi wasa ds hankalinta,ta kuma yiwa 'yar uwar tata da take mutuwar so take aibatashi sabods ita allurar da zata sake mata illa tako ina.
Tana zaune tana karanta qur'anin ya tura qofar,ta daga kai a hankali ta qare masa nutsatsen kallo amma a fakaice,sai a yanzun ta lura da wasu abubuwa a tattare dashi,cikin son nuna kulawa ya qaraso ya ajjiye ledar hannunsa,sannan ya matsa gaban gadon ya shafi wuyan sãahar din dake baccin mutuwa,ganin bata motsa ba ya tabbatar akwai ssuran lokuta kafin allurar ta saketa
"Alhamdulillah,Allah ya qara lafiya" ya fadi da sigar dake nuna damuwa da kuma kulawa. Waiwayawa yayi ya kalli afifa
"Ina ganin kije kici abinci sai ki buda daya dakin ki kwanta ko?" Qaramin murmushi ta sake
"Banda abinka mr Adam,ai ba hutawa nazo yi ba,jinya nazo yi,yau kaine da baccin nan,kada ka damu" tsaki yaja cikin ransa yana tsinewa afifan,yassn tunda har ra dawo dole ne aikinsa a yanzu ya hadu da qalubale masu yawa,amma idan tasan wata ai batasan wata ba,zaiji da ita
"To yayi,yanzu ga alluranta nan,za'a yi mata su kafin ta farka,hakan yana taimakawa wajen farkawarta ba tare da buge buge ko surutai ba"
"Okay" ta furta tana ajjiye qur'anin,ta buda ledar tana fiddo ruwan alluran hade da syringe din.
Duban farko ta yiwa alluran tasan cewa ba ainihin mazubinsu suke ba,abu na biyu kenan daya qara qarfafa zarginta,ta fitar dasu kaf ta zuqe ruwan allurar a syringe,ta matso ta dora tsinin allurar saman hannun sãahar da batasan abinda akeyi ba.
Page 53
*H U G U M A*
*_TABARMAR ƘASHI_*💔
Page 53
Sai kuma ta daga kai ta kalli adam din dake tsaye qyam a kansu yana duban alluran
"Bani tissue mana" amsawa yayi da to cikin hanzarin da baiso ta aiwatar da wani abun da zai kawo kuskure wajen yin allurar,ya ciro tissu din ya bata,ta karba ta dora a bakin tsinin allurar,ta fara zirarawa ruwan zuwa cikin tissue din data linkata,sai data qarar da ita a ciki tas sannan ta zare allurar,tayi hanzari danne tissue din a qasan cinyarta gudun kada ya fahimci jiqewar da tayi.
Sanda yaga ta kammala wani dadi ne ya kamashi,ko yanzun hankalinsa ya samu ya kwanta,yaukam zaiyi bacci abinsa sosai,yasan har gobe zuwa wajejen azahar tana cikin bacci da tambele idan ma ta farka din kafin sannan,wala'alla ma ya gayyato wata cikin 'yammatansa idan kowa yayi bacci ta tayashi debe kewa,da wannan tabbacin gaibun daya samu ya fita a dakin abinsa hankali kwance.
Kwanciyar hankalin da afifan ta gani a fuskarsa sanda yake fita din ta sake dasa qaqqarfan zargi a ranta,sai ta bude alqur'anin cikin nutsuwa ta fara karantawa da madaidaicin sauti me cike da nutsuwa.
Kusan awa guda cur ta shafe a hakan,a hankali taji wani sassanyan hannu ya dafa hannunta dake saman qur'anin,kafin ta daga kai taji ta kira sunanta da wata iriyar siriryar galabaitacciyar murya
"Bestie,kema wai kin yarda ni din mahaukaciya ce?,na haukace?" Wasu irin birkitattun hawaye ne suka shiga silalowa afifa,banda ta sanya hannunta ta toshe bakinta da kuka mai qarfi zata barke dashi,hannunta na saman bakinta tana girgiza kai,sai kawai ta rungume sãahar din a jikinta tana sakin kukan data boye sautinsa
"Bazan taba yarda ba bestie,koda ma da gaske ne ina qaunarki a hakan" kuka dukkansu suka saki rurus,suka dinga rerashi babu wani me rarrashin wani,har tsahon wani lokaci kafin afifa da idanunta sukayi jazur ta magantu
"Bestie,wanne irin mummunan abune kika yiwa adam ya yanke hukuncin mai dake haka?" Ido ta lumshe ragowar hawayen dake maqale a idanunta masu zafi suka gangaro,tabba inda ace ruwan hawaye yana qarewa da tuni nata ya jima da qarewa
"Wannan damuwar da kika tafi kika barni a cikinta,wadda nayi alqawarin gaya miki ita,ashe itace zata zaftaro bisa kaina,tayi shirin kaini lahira koda ban shirya ba" a nutse ta rattabawa afifan komai. Wani mugun birkicewa afifan tayi,ta miqe zata sauka a gadon da zafi zafinta, fuskarta gaba daya ta sauya kamanni.
Da sauri sãahar ta cafko hannunta,don tasan halinta sarai komai ma zata iyayi
"Ina zaki?"
"Adam din zanje na samu ayita ta qare,tsinanne matsiyaci dan wuta" girgiza kai ta hauyi da sauri
"Tunkarar adam a irin wannan yanayin abune me hatsarin gaske,idan baka iya kama barawo ba sai shi barawon ya kamaka,sai kinbi ta takatsantsan da hikima sosai kafin ya zamana mai laifi red handed,baki tsoron kema yace dalilin kwanan da kikayi kin shafi aljanuna ko ciwon haukata?" Sanyaya jikinta yayi,lallai a yadda idanun adam suka rufe babu abinda bazai iya aikatawa ba,yadda ya matsu da jakar koma meye akace zaiyi zaiyi din,saita koma ta zauna tana ci gaba da kukanta,zuciyarta kuma ta zurafafa da tunanin daukan fansa.
Da qyar suka lallashi juna,ta kama sãahar da jikinta sam ba qwari ta rakata toilet,ta daura alwala tazo ta rama sallolin da ake binta,afifa na gefe tana kallonta tana kuka, sãahar din da bata wasa da sallah?,duk tsanani duk rintsi bata yarda lokacin sallah ya wuceta ba ba tare da ta yita akan lokacinta ba.
Abincin da raihanatu ta bayar adam ya shigo dashi tun dazu ta buda,ta saka sãahar din a gaba akan sai taci,da qyar tayi cokali biyar,saboda cikinta ya sake wani mugun tsukewa,baya iya daukan abincin sam me yawa,dama kuma tun asali na gwanar abincin bace.
Daga ita har sãahar ba wanda ya rintsa a daren,sãahar din nata bat labarin irin azabobin da adam ya gana mata,tayi kuka tayi kuka har ta bawa uku lada,a daren ta gama shirya yadda komai zai tafi,tsarin kuma ya yiwa sãahar din itama.
Washegari da adam din daya kwana da wata macen suna holewa kan gadon aurensa ya shigo ko a fuska bata nuna masa komai ba,saima zallar tsoron kwana da sãahar din data nuna masa ta dinga ji. Murmushin jin dadi da samun cikakkiyar nasara ya saki yana sauke dubansa ga sãahar daje kwance shame shame kamar dai yadda take a jiya,a yanzun sauran tsoronsa ya kau,abinda ya rage masa ya sake matsa qaimi kawai ta bashi jakarsa kafin yayyenta su iso su wuce da ita wani banzan asibiti. Afifa ce dama tsoronsa,yasan halinta tsafff, za'a iya fuskantar matsala ta sanadinta,amma a yadda yaga tayi firgai firgai ta kuma ce a jiyan batayi bacci ba,alamu sun nuna ba zata iya sake kwana ba(baizan qarfin aminci da soyayyar dake tsakaninsu ta ginu sosai bisa tubalin Allah da ma'aiki ba,ba abota irin ta wannan zamanin ba,iya fatar baki). Ilai kuwa yadda ya zata hakance ta afku,afifa ta hada kayanta tayi musu sallama bayan ta gama tsara komai ta fice a motarta.
Ba gida ta wuce ba,can cikin kasuwar qofar ruwa ta zarce,ta kuma sauka kai tsaye gurin mutumin da yafi kowa qwarewa wajen yanka muqullin da zai dace da kowacce qofa, cikin lokaci qanqani aka gama yanka mata saboda kudin data zuba ta biya,ta karba ta dawo gida,ta hada wasu kaya ta baiwa maama dake shirin tafiya gidan,tace ta ajiiye mata dakin sãahar din gobe zata koma ta sake kwana da ita
"Kada ta barnatar miki fa" hawaye ne suka ciko idanun afifan,mutum da hankalinsa amma ya sanya kowa yana mata kallon tabbabiya
"Ba zata taba ba in sha Allah" shuru maaman tayi tana juya kayan
"Na rasa abinda yasa har yanzu naqi ji a jikina sãahar ta samu tabin qwaqwalwa,jiya muna hanya da abbanku dana fada yace shaidan keson yimin wasa da imani na,na yarda da qaddara ne kyau ko akasinta"
"In sha Allah nan kusa bestie zata dawo cikinmu muci gaba da rayuwa kamar kowa" abinda afifa ta fada kawai kenan tana sharce hawayen fuskarta.
Fitar maama daga gidan ya baiwa afifa damar shiga dakinta ta dauke jakar ta canza mata muhalli,saboda gudun abinda zaije yazo,ta gama sarawa girman sharrin adam,tasan bazai taba rasa kawowa a ransa jakar na gidan ba,zai kuma ya tsara komai da zai sanya a aminta dashi a damqa masa ita.
Kuka sosai ta zauna tana yi sanda ta gama qarewa kayan dake cikin jakar kallo,burinta kawai taga ta watsawa passport din wuta da sauran takardun,to amma suna buqatar evidence,don haka tayi haquri ta tattarasu ta kaisu cikin motarta.
Kamar ko yaushe bayan kowa ya tafi yaja qofar ya kulleta,don ba kwana dakin yakeyi ba sai idan yana da buqata. Cikin sanda ta bude kayan da maama ta ajjiye cikin drower dinta,wanda tunda ta shigo dasu take ankare dasu tare da fatan kada hankalin adam yakai kai. Ta warware kayan a nutse ta ciro muqullin ta maidasu gurinsu,ta duba daya bangaren kayan nata ta ciro hijabi ta sakawa jikinta, sannan ta fara takawa cikin sanda da takatsantsan,qirjinta yana wani irin bugawa,bakinta dauke da tarin addu'ar samun nasarar ficewa daga gidan ba tare da kowa ya ganta ba,tana takawa iska na yawo da ita saboda jimawa da tayi rabon da tayi doguwar tafiya,ga ciwo da uban allurai rashin cin abinci da uban tashin hankalin da yasa ta zabge ta rame.
Cikin nasara ta bude qofar dakin da muqullin,ta budeta a hankali ta fara takowa ta falon,motsi taji me qarfi daga bayanta,abinda ya kada hantar cikinta kenan ta waiwaya da sauri har tana shirin kaiwa qasa saboda tsananin razana.
Page 54
*H U G U M A*
*_TABARMAR ƘASHI_*💔
54
Raihanatu ta gani a tsaye,itama jikinta rawa yakeyi,plate din data debo suna shirin watsewa a hannunta. Bud baki sãahar tayi zatayi magana raihanatu tayi saurin dora yatsanta saman labbanta alamun sãahar din tayi shuru,sai ta maida plates din saman dining,ta sauko da mugun hanzari cikin wani taku na sand'a,ta qaraso inda sãahar ke tsaye ta finciki hannunta da mugun sauri ta bude mata qofar parlor din suka fice.
Tsakanin baranda da farfajiyar gidan suka ja cak suka tsaya,dukkansu kowa yana maida numfashi,qirjinsu yana wani irin dagawa
"Mai gadi.....yana nan anty,bari na dauk....ke masa hankali" bata tsaya jin ta bakin sãahar din ba ta lallaba tabi ta cikin flowers din ta zagaya bayan dakin me gadin. Dutse ta samu me dan girma ta jefa ta saman roofing din ya bada sauti qwaalll,sautin da ya dan ja hankalinsa,sai yayi tsaki yaci gaba da abinda yakeyi. Sake daukan wasu dutsunan har biyu tayi ta sake jefawa,ya sauka kuwa a tare,sai ya fusata ya miqe don ya zagaya ya duba daga ina jifan yake,kafin ya qaraso tuni ta fita ta koma wajen sãahar,ta sake jan hannunta gudu gudu sauri sauri,ta bude mata qofar gate din tana magana cikin ruwan hawaye
"Jeki anty,Allah zai dafa miki,ubangiji yayi miki sakayya,duk da ban gama sanin kan komai ba amma zuciyata da gangar jikina sun gama gayamin me yake faruwa,ko yanzun yana dakinki da wata,ko iya wannan sakayyar Allah ne kadai zaiyita" tana gama fada ta maida qofar cikin matuqar takatsantsan ta rufeta ta koma cikin da sauri ba tare data bari me gadin ya ganta ba.
Bibbiyu ta dinga gani cikin qwayar idanunta,jiri sosai ya dinga dibanta ta fara hada hanya. Da hanzari afifa dake zaune tana jiranta tsahon sa'a guda ta buda murfin motar ta fito da mugun sauri,ta tarbeta a hanya ta riqeta qam ta sanyata cikin motar,dai dai lokacin da numfashinta ya fara sauyawa,alamu suka fara nuna tana neman suma ne,wanann ya saka afifa tayar da motar da mugun gudu suka bar layin.
A lokacin babu wanda ta gayawa abinda ke faruwa,saboda bataso a sani din,don taci alwashin saita wujijjiga rayuwar adam din. A yanzun da sãahar ta sume mata dole ta nemi taimakon wani. Kai tsaye anty farheen ta kira,ta gaya mata asibitin da take tace tazo yanzu don Allah
"Wa kikai wannan asibitin me nisa?,duk hospitals din da muke zuwa na kusa damu"
"Ba lokaci anty don Allah ki qaraso yanzu,its urgent"
"Ba laifi,gani nan" ta fadi maganar tana ajjiye wayar. Muhyiddeen baya nan already,don haka ta barwa masi aikinta duka yaran,ta tayar da driver suka fito daga gidan cikin motarta.
Ba qaramin razana tayi ba lokacin da afifa ta gama zayyane mata komai,kuka sosai ta saki ita kanta anty farheen tana tsinewa adam din
"Dole mu dauki mummunan matakin shari'a a kansa,tabbas baici bulus ba" kai afifa ta girgiza
"A'ah anty,mubi komai a sannu kamar yadda sãahar ta shawarta,ni kaina yanzun tsoro yake bani,kaidinsa ya wuce tunaninmu,duk yadda nakai ga tsanarsa da qin jininsa......ban taba kawowa zai iya aikata haka ba,so sai mun iya takunmu,tsaf zai iya wanke kansa a wajen iyayenmu maza da 'yan uwanmu,bari kiji plans dina" a nutse ta warwarewa farheen shirinta,shirin ya yiwa farheen din sosai,kuma itace hanya guda daya da zata iya sanyawa adam ya tona asirin kansa da kansa.
Anty farheen bata bar asibitin ba sai kusan qarfe daya saura na dare,tace gobe zata dawo asibitin secretly ta kawo musu breakfast,don so samu a gobe ta maida sãahar gidanta aci gaba da yi mata treatment a can,don batason rashin ganin gilmawar afifa ya sanya adam ko wani cikin 'yan gida ya fahimci akwai wani abu,basason hakan ya kasance,har sai zuwa sanda suka tsara faruwar hakan.
^^^^^^Sam adam bai waiwayi dakin sãahar ba tun bayan tafiyar afifa,duk da yasan afifan a yau ta tafi gida,sai ya tattare shi da karuwarsa suka qule dakinsa sukaci karensu babu babbaka. Kwata kwata bai doshi dakin ba sai bayan sallar asuba,ya miqe yana jiri saboda buguwar da yayi a daren jiya,da kuma masha'ar daya aikata son ransa.
Zama yayi a bakin gadon yana jiran fitowarta,amma sai yaji shuru,don haka ya miqe ya nufi bandakin yana zage zage
"Na kusa kawo qarshen matsalata,tsaf zan iya hallakaki muddin kikace zakici gaba da boyemin jakata,ke kiyi asarry rayuwarki ni nayi asarar dukiyata" wata muguwar razana yayi lokacin da yaga bandakin wayam,ya fidda idanunsa waje kamar yana shirin zurarosu qas,ya waiwaya da sauri yana tuna cewa lokacin da yazo shiga dakin baifa budeshi da maqulli ba,yana turashi yaga ya bude,a zabure ya fito yana kwarara ihu kamar hauka sabon kamu,yayo falo yana qwalawa rahinatu kira.
Tunda ta idar da sallar asuba take zaune tana zaman tsammanin jiran jin makamancin wannan kiran,sai da tayi addu'ar neman samun tallafin nutsuwa daga ubangiji ta shafa sannan ta fito,a sannan har ya gagara zaman jiranta ya bankado qofar dakin,kadan ya rage ta daki fuskarta
"Ina sãahar take?" Ya tambayeta cikin tsawa
"Tana dakinta yaya" ta amsa masa a nutse,kamar da gaske batasan komai ba,ido ya zaro waje
"Tana dakinta zanzo ina tambayarki inda take don ubanki?" Cikin nuna zallar mamaki tace
"Bata dakinta kuma yaaya?,to ina ta tafi?, innalillahi wa inna ilaihi raji'un" duk sai ta nuna rudewarta a fili
"Ni tunda ka shigo kacemin na wuce dakina,kada ka sake ganin gilmawata ai ban sake fitowa ba yaaya sai yanzu daka kirani" yadda yaga ta rude shine ya sake gigitashi ya kuma rudashi,ya saki qofar da sauri yana barin wajen hadi da kama gashin kanshi da hannunsa bibbiyu kamar wanda yasha cocaine ya bugu da kyau,haka ya dinga zirga zirga kafin ya afka dakinsa.
Tana nan tsaye taji hayaniyarsu shi da kilakin tasa,kafin zuwa wani lokaci taji yana jibgarta,ba jimawa sai gata ya jawota kiiiii zuwa falon gidan da wasu gantalallun kayan bacci da basu da maraba da tsirara
"Tsinanniya mitsiyaciya,ke kika jawomin,saida na gaya miki kada ki bani abun bugarwa,a situation din da nake ciki bani da buqatar sa amma saida kika bani,yanzu kina shirin jazamin masifar da tafi kowacce girma,fita ki barmin gida" haka ya korata ko kayan jikinta bai bari ta canza ba.
Dawowa yayi yaci gaba da yin safa da marwar cikin tashin hankali
"Ya akayi ta fita daga dakin dana kulleta?,ina ta tafi?" Tambayoyin daya dinga yiwa kansa daya gama cakewa kenan,sai ya juya a gurguje ya durfafi me gadi yana tuhumarsa,saidai ya tabbatar masa yau din banda afifa data fita a gaban idanunsu dukka ba wanda ya sake fita daga gidan.
Qaramin hauka ya dinga yi tuburan, raihanatu na maqale tana hawaye,gami da janjantawa kanta game da muhallin da rayuwa ta jefota,dangin uwa marasa saiti,marasa imani jahilai masu shegen son kansu da kwadayin abun duniya fiye da komai.
Sanda ya kirata yace itama ta fito tabar gidan yana auna mata zagi,hakan dadi yayi mata,don duka tsoro ya kamta,ganin gidan ba kowa sai ita dashi yanata kuma wani abu kamar me tabin hankali,don haka a gurguje ta zira slippers dinta bata ma tsaya daukan komai nata ba ta qara gaba.
*_BAYAN AWA UKU_*
Mutum takwas ne cikin falon,ciki harda afifa maama da dr mamman sai yaa muhyi da yaa Saifullahi,wanda ba wanda yasan da zuwansu a yau din,sai kuma gashi sunzo sun tarar da tashin hankalin rasa sãahar.
A falon saika rasa tantance waye yafi wani shiga tashin hankali?,maama Kuka kawai takeyi wiwiwi wanda yake taba ran afifa,yakeson kuma ya karyar mata da gwiwarta. Duk bayan mintuna saita saci kallon adam da yake shirin zaucewa,ya kasa zama ya kasa tsaiwa,sai kai kawo kawai da yakeyi yana kiran sunan Allah,ta sake sarewa,ta kuma sake jin tsoron kaidin mutum,lallai dan adam me buhun sharri ne,ba wanda bai tausayawa adam din ba a falon yanayin da suka ga ya shiga,ba tare da sanij cewa shine ummul aba'isin faruwar komai ba
Zaman da sukeyi a yanzu na zaman jiran tsammani ne,bayan sun bada report na batanta a kafafen yada labarai da kuma police station guri guri.
"kayi haquri adam,in sha Allah za'a ganta cikin aminci" abba ya fada cikin son qarfafawa adam din gwiwa,duk sa cewa shi dinma bawai yana da qwarin gwiwar bane
"Abba bansan ya akayi ta fita ba,ina ta tafi?, innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ya fada da madaukakiyar murya,kai afifa ta kawar ta tabe baki,tabbas bawai yana cikin tashin hankali bane saboda batan sãahar,yana cikin tashin hankali ne kawai saboda jakarsa.
Wuni sukayi ranar a haka,har zuwa dare,ba wani labari ko alamun samun sãahar.
Ta fannin afifa duk da tanason komawa gidan yaa muhyi su kwana da sãahar din wadda tuni anty farheen ta samo likita ya fara bata kulawa ta musamman,to amma zamanta tare da maama dake cikin tashin hankali yana da matuqar amfani,tunda tasan ko ba komai zata debe mata kewa ta kuma kwantar mata da hankali,don haka ta bita gida,amma tana tuntubar anty farheen akan duk yanayin da ake ciki,ta shaida mata tana samun sauqi da kuma kyakkyawar kulawa. Lokaci lokaci take satar jiki taje taga sãahar din. Sosai sãahar din ke murmurewa tana sake samun lafiya,saboda kulawa ta musamman da anty farheen din take bata,duk da cewa sãahar din bata da aiki sai koke koke,saboda matuqar dimuwa da kaduwa ta shigeshi akan abinda adam yayi mata,gaba daya so take ta zama depressed,amma dagewar anty farheen da jajircewarta yanata aiki a kanta,baji ba gani haka take bata kulawa da shawarwari
"Um um ummin abba,baki godewa Allah ba kenan?,baki godewa ni'imarsa ba?,ya kubuto dake daga sharrin da bakisan iya zurfinsa ba?,da yawan koke koke zaki sakawa ubangijinki?"
"Dole nayi kuka anty,ashe dama haka maza suke?,dama masoyi yana iya komawa maqiyi mafi ban tsoro me muni?,ashe su din basusan halacci ba?,basusan soyayya ta ainihi ba?,basusan tausayi imani da jin qai ba?,ashe adam zai iya yimin haka anty?,me yayi saura kuma a duniya?,tunda har adam zaiyi haka,wanne masoyi ne bazai iya cin amanar masoyi ba?" A lokacin dukka bayanin da zata yi mata bazaiyi amfani ko tasiri ba,don haka sai kawai taci gaba da lallashinta cikin hikima da kwantar da kai.
KOMAI NISAN JIFA
Bayan zamun tabbacin warwarewar sãahar,suka tabbatar ta dawo cikin hayyaci da nutsuwarta,da taimakin likitansu dake duba mafi akasadin matsalar data shafi familyn gaba daya. Ba abinda afifa ta boyewa Dr usman,ta kuma nemi taimakonsa ya zama jagora wajen zama MABUDIN tonuwar asirin adam,ba tare da jinkiri ba ya amince,don shi kansa al'amarin yayi masifar tsimashi tare da tayar masa da hankali matuqa da gaske.
Tun cikin satin ta tayar da maganar zuwa duba filaye da kadarorin sãahar,tace
"Ya zaid,ya kamata a duba,kasan mutane babu amana, qilan wasu suji labarin batanta suje suyi rub da ciki a kai" zaid din ya gamsu da zancanta,yace zai samu lokaci yaje ya dudduba din.
Lokuta lokuta sukanje gidan,basu barshi hakanan ba,kamar ko wanne lokaci,yau ma sun je gidan kusan su dukansu,banda zaid da yace zai fara wucewa duba filayen sãahar din,abinda yayi matuqar yiwa afifa dadi,ta dinga kallon adam da yaketa mazari irin na rashin gaskiya a tsakaninsu,tana jiran jin dawowar zaid.
Maama na tsaka da jajensa kan ya dade ya iso gidan,cikin wani irin yanayi daya tabbatarwa afifa boom din data dana ya soma tashi
"Lafiya?" Maama ta tambayeshi
"Akwai matsala maama,lokacin dana isa na fara da duba filayenta daka bakin titi,amma ga mamakina kusan fiye da rabinsu an tada gini a cikinsu harma anyi nisa,ko dana zauna na fara bibiyar lamarin,na nemi haduwa da ainihin masu filin,na samu ganin mutum uku a ciki,don suna gurin suna duba aikin da akeyi musu,kuma dukkansu sun shaida min siyan fili sukayi,kowanne kuma ya nunamin takardar shaidar mallakar filin original copy" wani irin sauti cikin adam din ya bayar,wanne irin sabuwar masifa ce kuma take shirin afko masa bayan yana tsakiyar wannan dumu dumu bai gama fita daga cikinta ba?,dakiya da qarfin hali ya aro,cikin nuna bacin rai gami da mamaki yace
"Kai,wanne irin rainin wayau ne wannan?,me yasa mutane masu da kirki basu da imani?,daga batan baiwar Allahn sai kawai su hau gine mata filaye?"
"Basu x laifi,kuma suna da gaskiya,don kowanne ya shaidamin a hannun mijinta ya samu damar mallakar filin,ya tabbatar musu kuma babu wata matsala" ai baisan sanda ya miqe ba,ya soma fada yana yarfa hannu,sam ya manta a gaban su waye yake
"A gidan ubanwa suka sanni?,ni zasu yiwa sharri saboda sunga Allah ya rufamin asiri?,muna zaman lafiya da soyayya da matata?,ko su waye wlh bazan qyalesu ba,tabbas saina kaisu qara kotu" relaxing ya zaid yayi yana qare masa kallo
"Ka kwantar ds hankalinka,ko nima bazan qyalesu ba sai nayi shari'a dasu,so shi yasa a gobe na yanke hadaku ku duka acire me gaskiya da mara gaskiya,tun kafin ta ritsa da wanda baida laifin komai" mummunar faduwa gabansa yayi,amma ya maze
'"hakan yayi,ko baka hadamu ba ni zan nemesu,na kuma nemi fansar batamin suna da sukeso suyi" sai yaci gaba da fada,ya kasa shuru hakanan ya kasa nutsuwa ya zauna guri guda.
Daren ranar bacci barawo duk qwarewarsa bai iya satarsa ba,ya dauki wayarsa ya kira momee ya zayyane mata komai
"Kada ka wani damu,kuje din,iyaka ka murje idonka kace baka sansu ba,zanma shigo gidan goben saboda ka samu supporting " akan hakan suka samu matsaya,saidai abinda basu sani ba,tuni afifa ta gama nata shirin na goben,don ko da suka tashi zuwa,tare da Dr suka taho,bisa shawarar adam din ya bada report na duka lalurar sãahar din ya duba da kyau. Tace hakan yana da kyau,idan da yiwuwar suyi attaching nasa cikin cigiyar neman sãahar da akeyi,qila wannan ya sauqaqe samunta da wuri.
Page 55
*H U G U M A*
*_TABARMAR ƘASHI_*💔
Page 55
A nutse ya zauna a falon gidan yana duba report din qarya da Dr din bogin da adam yayi hiring ya hada,ga duk qwararren likita yana kallon abun zai fahimci an tsarashi ne kawai,saboda babu gaba babu baya,bayanan babu wani cikakken abun kamawa.
Nannauyar ajiyar zuiciya ya sauke,wannan mutumin bayan qwarewa da yayi wajen hada plan,harda sa'a ma daya taka cikin al'amarinsa,ko kuma qaddarar da bahaushe yakewa take da bata wuce rana da lokacinta,saboda ya duba ya dubo,family irin na dr mamman girema,ba abu bane me sauqi kayi musu irin wannan abu lokaci guda hankalinsu bai kai kai ba,duk da akwai tasirin boko sosai a tattare dasu,amma suna da ilimin addini a tattare dasu. Daga qarshe ya rufe file din yana sauke ajiyar zuciya,lallai banda ma wannan......sun bashi amana qwarai,ta yadda tunaninsu bai taba kawo musu wai adam din zai aikata wani abu makamancin wannan ba.
A nutse likitan ya maida dubansa ga momee dinsa data iso tanata kumfar baki akan case din filayen,tana ta fada akan duk wanda ya murqushe dukiyar,ya kuma bi d'anta da sharri bazasu qyale ba. Duba daya yayi mata ya karanci 'yar bariki ce tsantsa,amma dattako da karamci irin na iyalan dr mamman girema yasa basu taba nuna mata komai ba face zallar karamci da mutuntawa.
Afifa dake dakin sãahar tana tattaro dukka kwalaben alluran da aka dinga juyewa gangar jikin 'yar uwartata,tana jiyo dukka kumfar bakin momee,tun ranar tasan cewa komai da hadin bakinta ake aikatashi,tsanar da take wa matar ta sake ninkuwa cikin ranta. Qoqarin dauke hankalinta tayi akan maganganun amma kuma ta kasa,bala'i biyu ne ya hade mata,na farko qarfin alluran da aka dinga dibgawa sãahar din,wanda tasan banda ikon Allah,babu abinda zai hana kwanyarta juyewa,na biyu kuma yadda momee din ke magana kamar mutuniyar arziqi,wannan yasa ta miqe a fusace,ta daga inda ta yiwa jakar ajiya ta musamman ta cirota ta kuma fito daga dakin da wani irin hanzari,tana huci kamar ta hadiyi kunama.
Yadda ta buda qofar da qarfi har tana dukan bango ya dawo da hankalin dukka mutumin dake falon kanta,yaa zaid yana shirin tambayarta lafiya?,saita miqa kwalaben ga likitan
"Dr,dubamin wadan nan kwalaben,allurar meye?" Hannu biyu yasa ya karba ya fara dubasu daya bayan daya. Wani gumi ne ya yanko masa shima,ya daga kansa ya zubawa adam idanu.
Tun baice komai ba ilahirin jikin adam din ya dauki rawa,ko kadan baisan da zaman kwalaben ba a dakin,yasan duk sanda akayi allurar indai ya tuna zai kwashesu ya fita dasu,to waye ya tarasu?,ba shakka sãahar dince,hakan yana nufin duk lokacin da akayi mata allura tana fakar idonsa ta dauki kwalbar kenan ta adana?,lallai ta shiryama zuwan wannan ranar
"Wanne dan wutar ne cikin likitoci yake iya zuqar wannan ruwan allurar ya zubesu ga jikin dan adam?" Abinda likitan ya fara tambayarsa kenan cikin matsanancin bacin rai.
Duk yadda yaso ya shirya qaryar da zata sanyashi ya bulle amma bakinsa yaqi bashi hadin kai,saboda rawa kawai labbansa sukeyi,da qyar ya fusgo kalmar
"Bansan a inda aka samosu ba,don wannan kwalaben ni ban taba ganinsu bama"ya tabbatar qarya yake,tunda ya riga yasan da komai,sai kawai ya maida dubansa ga ya zaid ya fara karanto masa aikin da allurar takeyi a jikin dan adam,da kuma girman illarta.
Kuka kawai maama ta fashe dashi tana kiran sunan Allah,yayin da adam ya jiqe jagab kamar an masa wanka da ruwa,jikinsa yana bashi yau ba ranar sa'ar sa bace,yau ranar tonin sililinsa ce,momee ce mai qarfin halin miqewa,cikin borin kunya ta fara maganganu
"Dama dai kawai kun shirya ci mana mutunci da wulaqantamu,saboda talakawa ne mu bamu da komai,banda haka ta yaya yaron da bashi a zaune bashi a tsaye game da al'amarin diyarku amma ku rasa sharrin da zaku jefeshi dashi sai wannan,idan banda shi da yasan girman halacci ma waye zai zauna da mahaukaciya....."
"Ke tsohuwa,ki iya kalamanki" afifa ta dakawa momee tsawa da muryar da ita kanta batasan tana da irinta ba
"Tunda har kuna da bakin kare kanku,ai waqa a bakin me ita tafi dadi" saita fidda waya tana kiran anty farheen
"Muna hanya afifa,muna gab da shigowa layin"
"Saikun qaraso" sai ga juya gasu dr mamman
"Abba,don Allah ku jira minti uku,ga raba gardamar nan isowa" jin kalmar afifa ta qarshe ta kada hanjin cikin momee,zatonta ya bata jami'an tsaro kawai suka kira musu kai tsaye,sai ta kama hannun adam tana cewa
"Tashi mu tafi,Allah zai saka mana da wannan qazamin qazafin da sukayi maka saboda kana auren diyarsu"
"Ina zaku?,ku koma ku zauna,ai bakwa tafi muna zarginku ba,gwara a warware gaskiya ko hajiya?" Cewa dr mamman girema.
Jikinta ne ya dauki rawa ta fara kame kame,saidai kafin ta dire kame kamen nata sallamar sãahar ta dauki hankalin kowa.
Sanye cikin wani lallausan yadi da aka yiwa dinkin doguwar riga,da gyale mahadinsa,fuskarta har yau bata cika ba a yadda take a baya,saidai sassanyan kyan nan da baya gushewa kwance saman fuskar tata. Akwai alamu na samun nutsuwa a tattare da ita,sabanin satittikan baya da dukka wata natsuwa tayi qaura daga rayuwarta,ake shirin haukatata,a maidata mahaukaciya zalla,idan ta yiwu ma yazo da qarar kwana,bataga abinda zai hanata ta baqunci lahira ba.
Cikin azama tare da son nunawa duniya shi din wankakke ne,kuma masoyi ga matarsa ya miqe cikin zallar mamaki ya nufeta yana qwala kiran sunanta. Rungumeta yayi nufin yi,saidai kafin yakai ga aikata hakan ya samu tsarabar wani lafiyayyen mari saman fuskarta,sannan ta tattara dukka qarfin data shigo dashi ta ingizashi baya ya fada saman momee dake zaune cikin kaduwa da tsurewa.
Zumbur ya miqe yana shafa wajen,sannan ya maida dubansa a kanta,sanda take tsaye ta kafeshi da fararen manyan idanunta dake dauke yau din da wani irin matsanancin fushi da bai taba ganin irinsa tattare da ita ba
"Baki warke bane sãahar?,subhanallahi"
"Kaine zaka shiga taka haukar yanzun nan,mayaudari maciyin amana,ina neman tsarin Allah daga kai" sai ta fashe da kuka ta soma sulalewa a gurin zata zauna,anty farheen ta riqeta da kyau tana bata baki. Tuni maama ta qaraso bayan ta tabbatar ba mafarki takeyi ba,ta rungume 'yarta tsam tana jero addu'o'in godiya ga Allah
"Ya kamata kowa ya samu waje ya zauna" yaa Saifullahi ya magantu cikin nutsuwarsa,domin ya karanci akwai babban al'amari dake shirin faruwa,komai ya fara bayyanar masa saman fuskar adam da babarsa,sannan ya akayi sãahar take a gidan muhyiddeen duk da tsahon lokacin da aka dauka ana nemanta ba tare da kowa ya sani ba?,ga adam da momee suna matsawa daga bakin qofa?,tamkar yaa zaid ya lura,sai ya matsa yayiwa kansa mazauni daga can hanyar qofar,suka zamana a tsakiya.
A nutse afifa ta qaraso tsakiyarsu ta dire jakar. Lokacin da idanun adam suka sauka a kan jakar sai ga fitsari ya balle masa yana daga zaunen,zazzafar gudawa ta soma qoqarin kufce masa amma ya matseta da kyau,gurbatacciyar ziciyarsa tana gaya masa akwai sauran dama adam,kada ka karaya,muddin baka amsa ba ba wanda ya isa ya tilastaka,koda kuwa a kotu ne.
A gaban kowa sãahar ta matso,ta daga jakar ta zazzage komai ya tarwatse a qasa,wani zazzafan kuka ya taso mata,amma ta danneshi. Daya bayan daya ta soma basu labarin yadda suka fara hadaka a rayuwarsu,yarjajeniyar rashin daukan ciki,canjin halayensa,kamashi da tayi a waya da zuba mata tablet da yayi na zubda ciki,bayyanar ha'incin da yake mata ba tare amma data kama sunan raihanatu ba,azabar daya dinga gana mata har zuwa sanda Allah yayi fitarta daga gidan da taimakon afifa da kuma raihanatu. Kamar wani mahaukacin zaki ya miqe ya soma zage zage,yaa zaid baisan sanda yasa qafa ya kwasheshi ba cikin matsanancin fushi,sai gashi kif a qasa
"Idan ka sake mana magana sai na cire maka harshe" kota ina jikin momee rawa yake,duk sauran qwarin gwiwar da take dasu sun kwaranye sunbi ruwa,don itama wasu abubuwan batasan dasu ba.
Jakar ta fara musu bayani,tana zazzage abubuwan ciki tana nunawa kowa,sai maama ta kasa daurewa,ta rufe fuskarta da hannunta kuka mara sauti yana qwace mata. Duka duka nawa sãahar din take da har zata fuskanci irin wannan cin zarafin cin fuska da zallar cin amana daga gurin da namiji?,ko ita data kawota duniya bata taba fuskantar wani abu da yayi kamanceceniya da wannan ba
"Duk abinda ta fada gaskiya ne,ni shaida ce" muryar raihanatu ta ratsa falon,sai suka waiwaya suna kallonta, idanunta cike fal da qwallar tausayin sãahar din,don itama wasu abubuwan sai yanzu takeji.
Mamaki ya cika momee qwarai,wato raihanatu zata zame mata 'yar kuka?,ta raini makashiyarta?
"Ki daina mamaki momee,ko kina tunanin bansan ba don Allah kike riqe dani ba?,bayan bautar da nake muku kina lissafin sake maidani machine din tatsar kudinki?, bayan kin cinye dukka abinda mahaifiyata ta mallaka,tun tana raye bata da bakin musa miki?" Maganar ta sake zuwarma momee a bazata,lokaci guda ta nemi sukurkuta mata runani,ya akayi yarinyar tasan wannan
"ni zaki butulcewa raihanatu?"
"Dalla malama ki rufewa mutane baki" yaa Saifullahi ya fada cikin muguwar tsawa,ransa baqiqqirin,tamkar zai kifawa momee din mari,hannu Dr mamman ya daga masa,saboda shi wani abuma ya tsaye masa a wuya ya kasa magana,idanunsa qirrr saman fuskar adam,yana tuna girma da nauyin karamcin da ya yiwa rayuwarsa,tarin alkhairai wanda ko sãahar da take matarsa ya hana ya gaya mata,yakance masa
"Nayi maka ne fisabilillahi saboda Allah,ko ummin abba banaso ta sani,kasan su mata,wani qaramin tunani garesu,qanqani abu zai hadaka dasu sai su goranta maka".
Sam basu farga ba,ashe tuni yaa zain yayi kiran mopol,kafin kace wani abu sai isowarsu akaji da sanyo kansu cikin gidan
"Waye yayi hakan a cikinku?" Dr mamman ya tambaya
"Kayi haquri abba,nine" ya zaid ya fada yana miqewa,yanason a hukunta masa adam da mahaifiyarsa hukunci Mafi tsanani da radadi,irin hukuncin da har su koma ga Allah ba zasu mance dashi ba.
"Amma ina zaune ba zaka fara neman shawarata ba zain?"
"Kayimin afuwa abba" yana gama fada ga fita,cikin second biyar suka cika falon.
"Wait please" ya Saifullahi ya fada,ya miqa hannu ya ciro paper,ya zaro pen daga aljihunsa ya dorawa adam da ake qoqarin cukuikuyewa
"Maza rubuta mata takardarta" kai ya girgiza cikin taurin zuciya da taurin kai
"Matata ce,kuma ina sonta har yanzu,don haka bazan saketa ba,saidai......." Bai qarasa fada ba ya Saifullahin ya daukeshi da wani kyakkyawan mari
"Mu zaka gayawa maganar banza da wofi?,wato saboda baka daku ba har kana da qwarin gwiwar yi mana musu ko?" Duk da marin amma sai ya sake girgiza kai
"Saidai ta mutu da igiyar aure na"
"Ba zata mutu ba kuwa,saboda mudin ba jahilai bane,kawai kotu akwai shari'a kuma" ya muhyiddeen da mamakin adam ke sake kasheshi ya fada. Saidai yana rufe bakinsa mopol din ya saukewa adam din wani irin zazzafar mahangurba da lokaci guda ta sauke masa jini ta hanci da labbansa,ta kuma tara masa wani lafiyayyen jini a gefen idanunsa. Ihu momee ta saki tana neman taimakon wai za'a kasheta ita da danta
"Saketa,ka saketa nace karsu kasheka baka da gata" koda momee din bata fada ba zai rubuta,shi kadai yasan kalar azabar da yaji,idanunsa a rurrufe ya rubuta mata saki daya. A fusace ya Saifullahin ya duba
"Don ubanka qarashe mata sauran biyun" dr mamman ne da nasa mamakin ya qarasa daskarar dashi ya daga masa hannu
"Rabu dashi" ya basu umarni a taqaice,daa yaso ya hana a tafi dasu,amma yadda suka nuna rashin nadama kwata kwata bisa fuskarsu yasa ya kasa hana mopol din tafiya dasu.
"So nake a azabtarmin dasu yadda ya kamata,a sassaba masa kamanni shida uwarsa,banason kowa yasan inda suke,kada kuma a daga musu qafa ko na kwana daya,zamuyi waya" yacewa da shugabansun
"Karka damu,sakamakon mummuna ai mummuna ne" shima ya fada cike da jin takaicin adam da uwarsa.
Ko minti biyar basu qara a gidan ba suka tattara nasu ya nasu suka fice a gidan,sãahar ce tabi raihanatu da kallo wadda ta hada nata kayan ta fara yin titi
"Abba bata da kowa a qasar nan,kuma ko yanzun bata da wajen zama,dama suke riqe da ita,na tabbatar kuma ba zasu ci gaba da riqonta ba" wannan yasa suka dauki raihanatun,abban kuma ya tabbatarwa sa sãahar zai kula da nauyinta da rayuwarta,zuwa gaba kadan kuma zasuje ghana a binciko danginta na qwarai,don susan irin riqon da momee tayi mata. Ajiyar zuciya sãahar ta sauke
"Allah yasa su iya wani abu,saboda momee ta cikasu da kyaututtuka,a yanzu kuwa lalacewa ta tattaru a cikin dangi,duk lalacewarka izgilancinka da rashin ganin girman mutane,taka mutane da mugunyar halinka kaida iyalinka,muddin kana ungo ungo,sai idanun 'yan uwa su rufe daga aibunka,a rasa wani tsayayyen da idan kayi ba daidai ba za'a tsaya a tsawatar maka a kuma hukuntaka dai dai da laifinka" kai abban ya jinjina,maganar sãahar tana kan hanya
"Wannan shine yake kawo lalacewar zumunci da tabarbarewarsa,dole sai an hadu za'a gyara,dole sai an hadu an hukunta me qarfi ko mara qarfi,ya zamana kowa baifi qarfin doka ba,Allah ya kyauta,yasa mufi qarfin zukatanmu"
_NOTE:wadannan matsalolin da suke babbar masifa ce suna nan suna ruruwa cikin al'umma,a yanzu dan qanwarki ko dan yayarki yana iya cin zarafinki,uwarsa ta goya masa baya,saboda suna yiwa dangin nan dan ihsanin da bai taka kara ya karya ba,su kansu masu fada aji a dangin sai kaga sun zama hoto,basu da wani amfani saboda ba kowa suke iya juyawa ba,sun wulaqantar da kansu saboda suna tsoron wasu sashe,idan sunyi ba dai dai ba basu isa su hukuntasu ba,ke kuma uwa wallahi wallahi kanki kikewa baqar dabara,kin nunawa 'ya'yanki kowa baida mutunci,babu me gaya musu suji,saboda kema a haka kika taso,kina ganin kinfi qarfin a baki shawara ko a tsawatarmiki,kin ruguza iyalinki da hannunki,bayan babu ranki haka zasuci wahala,saboda masuyi don ganin idanunkin guduwa zasuyi su barsu,kina qabari ke kuma kina amsar query akan tarbiyyar da kika yiwa yaranki,kina qabari ana nan duniya ana alawadai da halin yaranki,abinda kina raye babu me iya fada,kin mutu kin barwa dangi masifa,qila akwai mata a cikinsu,sai kiga yarinya ta kasa zaman gidan miji,ta kasa biyayyar aure saboda a tarbiyyar da uwarta tayi mata batasan biyayya ba saidai ita a bita,sai tsananin rabo yake zaunar dasu,to duka mu sani,dake uwa da kika zama shashasha sauna,wadda ke iya bari diyan cikinta su wulaqanta 'yan uwanta saboda yunwar ilimin addini da qarancinsa,dasu dangi da suke ganin barna su kasa tsaiwa a gyara saboda kowa yana tsoron fadin gaskiya,ta silar haka zumunci ya gurgunce,wallahi wallahi kowa sai ya tsaya yayi bayani gaban Allah,da wanda aka cuta da wansa yayi cutar,Allah ka bamu dacewa,ka bamu ikon tsaiwa akan gaskiya akan mutum ko wayeshi,komai girma da matsayinsa,ka rabamu da kwadayin abun hannun kowa,ka wadatamu da wadatar zuci daga gurinka👏🏽_
Page 56
*H U G U M A*
*_TABARMAR ƘASHI_*💔
Page 56
Cikin lokacin kowa qoqari yake ya faranta ran sãahar,tamkar rige rige akeyi,kowa yana bakin qoqarin ganin ya sanyata walwala,dukkansu sun fahimci depression ya fara kamata,ta soma wasu attitude da suke bayyana hakan. Anty farheen ita ta tashi tsayin daka a kanta,daga qarshe ta karbeta daga hannun maama,duk da maaman taso a barta da diyarta,to amma farheen din nada wani irin kirki da tausayi,dole ta haqura ta bar mata ita.
Zamanta hannun farheen yasa ta qaru da abubuwa masu tarin yawa,sannan ta taimaka mata wajen mantawa da wasu abubuwan,tare da fara dawowa cikin saitinta. A lokacin ya muhyiddeen ya samu wani aiki a Scotland,sai duka suka tattara har sãahar din suka wuce can. Koda sukaje din asibiti me kyau farheen tasa yaa muhyi ya duba musu suka fara zuwa ita da sãahar din,akwai sashen guiding and counselling masu kula da matsaloli irin wadan nan da hanyoyin kubutar da tunani daga wannan damuwar,abinka da qasashen da sukaci gaba,watanni kadan saiga sãahar din ta koma dariyarta da walwalarta,ta sake murjewa,gayu ya sake zama a jikinta fiye da kima saboda tasirin zamanta da anty farheen,idan ka ganta saita bala'in burgeki ke da kika diya mace ma,nan da nan anty farheen tayi amfani da wannan damar ta nema mata makaranta da kanta,ta dora karatun mastering degree dinta.
Cikin shekarun komai yazo ya wuce,saidai babu ta yadda za'a ji ciwo sannan a warke ba tare da ya barwa mutum tabo ba,koda a gangar jiki ne bare kuma a guri me matuqar muhimmanci da sammatsi irin ZUCIYA,zalincin adama gareta yasa ta hadu sa ciwon kai mai matuqar tsanani sanadin alluran da aka dingayi mata ba bisa qa'ida ba,wanda inda ace anci gaba da yinsu,tsaf kwanyarta zata juye cewar likita,wannan tabon shine abinda ya haifarwa da sãahar tsanar maza,tsana me tsanani,babu halitta da takewa bahagon kallo irinsu,ta tsani taji kalmar soyayya,kalmar AURE kuwa tana sanyata jin wani tashin hankali,kwatankwacin mutumin da yaqi ya tunkaro shi,duk wani abu da zai sanyata hulda da maza ta datseshi,wannan ne yasa tunda suka dawo Nigeria tayi zamanta wajen anty farheen dake ji da ita,take kuma sake maidata macen da idan aka kalla sai an sake juyawa an kalla cikin hikima. Batason kowa yayi mata zancan aiki,shi yasa taqi fidda results nata data samu,results me kyau da yayi bala'in burge yayyenta,duk da dama tunda can sunsan ita din bata da wasa ta fannin karatu,hakanan tana da kwanyar da dukka cikin gidan ita da yaa Saifullahi keda irinta,duk da sauran suma ba daga baya ba,wannan yasa kowanne yake riqe da wani babban matsayi,ya kuma tara dukiyar da a qananun shekarunsu idan aka gaya maka yawanta zakayi mamaki,dukka cikinsu babu rago,babu kuma koma baya.
A wancan lokacin sati guda dr mamman yace su zain su saki adam,su barshi da halinsa,yayi imanin bazai gama rayuwa a daron duniya ya wanye qalau ba tare da Allah ya hukuntashi ba,duk kuma yadda sukaso hukuntashi hukuncin Allah shine gaba da nasu. Hatta da afifa bata bayar da goyon baya ba,ita inda son samu ne,akai adam din muhallin da hatta hasken rana baya shiga gurin ayi masa daurin rai da rai.
Sun bar dr mamman aka cewa an sakeshi,amma basu barsu ba saida sukayi watanni uku cur suna karban hukunci a hannun sajoji,kafin sannan kuwa gaba dayansu ba wanda baiji a jikinsa ba,duk wani abu da sukasan ya mallaka ta silarsu sun karbeshi,ciki harda gidan da momee ke zaune,da wanda suka rayu shi da sãahar,sai a sannan suka gane cewa gidan ashe shima ya saidashi,ta yadda idan yabar qasar saidai sãahar taji ana batun ta tashi ga masu gida. Tuni suka sayar da gida,su kuma ainihin wadanda suka siya a wajensa dama baikai ga basu takardun ba,ya karba kudinne kawai,nufinsa sai ranar da zasu bar qasar ya danqa musu ya qara gaba,sukace ba zasu yarda ba,yaa zain yace su nema kudinsu a hannun dan damfarar da suka bawa. Sunsan tako ina family din dr mamman girema ba abun wasa bane,sunfi kuma qarfin wannan gidan bare suce cuwa cuwa sukayi,don haka suka karkata akalar tuhumarsu ga adam wanda a sannan ko gidan da zai kwanta a ciki ya huce tarin gajiyar da sojojin suka hada musu ya kuma yi jinyar raunukan jikinsa bashi dashi.
A sannan tuni abba ya samawa raihanatu karatu a maryam abacha American university dake garin maradi a jahar nijer,tana can ta dora karatunta daga inda ta tsaya,babban burinta kenan a rayuwa,wanda momee tasha gaya mata bazai taba cika ba,ba zata dinga adashin da batasan ranar kwasarsa ba.
*Dama hausawa sukance ALHAKI KWAIKWIYO NE,ME SHI YAKE BI*
_DUK INDA ZA'A JE AZO KA TABBATAR KAI AKA CUTA,KARKA ZAMA KAINE WANDA KAYI WANANN CUTAR,A RABUWAR AURE 'YAN UWANA MATA,KARKI YADDA IDAN TA KAMA A RABUN YA ZAMANA KECE ME MATSALA KO KECE AZZALUMAR, WALLAHI KIKA BARI HAKA TA FARU KUMA KIKA FITO SAIKIN RAINA KANKI,MUDDIN KE AKA ZALUNTA,KARKIYI KAICO,KADA KUMA KIYI BAQINCIKI,DOMIN ALLAH BAYA KI GYANGADI BARE BACCI_
*_wannan kenan_*
*_Dawowa labari_*
Juyawa ta sakeyi a karo na babu adadi bayan gama dukka wannan bitar da qwaqwalwarta tayi,gefan da afifa ke kwance ta kalla,kusan wasu matsalolin tare suka fuskancesu ita da afifan,amma sau tari sai taji inama itace afifan?,inama bata taba sanin wani adam ba bare ya shiga rayuwarta ya cutar da ita haka ba?. Tsaki taja qasa qasa bayan fargar da ita da zuicyarta tayi,saita miqe ta sauko daga gadon a hankali ta nufi toilet,cikin ranta tana sake jin yaqini da qwarin gwiwar cewa,ya zame mata tabbas tayi wani abu,har yanzu batajin cewa tayi warkewar da zata doshi wani aikin ko kuma aure,dole tayi hobbasar da zata sake nesantata daga dukkan wata mu'alama da zata sake hadata da azzalumar halittar maza,marasa tausayi da jin qai,marasa amana kuma,dole ta yiwa kanta wannan aikin.
Daren gaba daya ta raya,da tarin addu'o'in ta da buqatunta jingim wajen Allah,ko kafin ta kammala ma wata irin nutsuwa ta maye gurbin bacin rai da fargabar dake motsa zuciyarta,albarkacin wannan kuma a nan saman abun sallar daddadan bacci ya saceta.
Afifa ta rigata tashi sallar asuba,batayi mamakin ganinta a kwance a nan ba,saboda ba kowanne dare ne take iya kwanciya ta shareshi dukka tana bacci ba,saita qarasa cikin tausayawa da qauna ta tabata tana kiran sunanta. Idanunta ta bude tana kallon afifa
"Ya shehiya sãahar,a tashi ayi sallar asuba,Allah ya amsa addu'ar nan,ina fatan kin sakani a ciki,Allah ya kawo masoyi na gari" qaramin murmushi tayi duk da cewa daga bacci ta tashi,hakan kuma ya sake qarawa fuskarta kyau,sai da tayi brush ta daura alwala ta fito sannan ta amsa mata
"Allah ya kakkawo,saidai ita afifa akwai wanda take jira" bata tsaya jin amsarta ta tayar da sallah ta barta da baki a bude tana cewa dariya nason kamata
"Kajimin yarinya zatamin sharri?".
Dukka wani azkar data saba yi sai data yishi,haka kawai taji idanunta babu wani sauran bacci,duk da cewa ba wani baccin kirki ta samu ba adaren jiyan,don haka ta shafa addu'o'inta ta nade abun sallar,ta dauki wayarta ta koma saman gadon su,tana kallon afifa da idanunta ke rufe,da alama bacci ne sosai a kanta, saita ja duvet itama tana shirin rufa,dai dai lokacin da tex din ahmad ke shigowa wayarta.
Ko bata buda ba tasan saqon barka da safiya ne,taja qaramin tsaki,tana tunanin sai yaushe zai gaji da naci yace ya haqura da ita?,ba amsa,don haka ta share saqon bayan ta buda wayar.
Watsapp tahau zata buda wani qaramin document na addu'o'i da anty farheen ta turo mata,yana da dan nauyi,don haka da tayi clicking akai,sai ta fita da zummar rage jira kafin ya kammala buduwa.
Haka kawai ta samu kanta da buda jerin list na mutanen da sukayi status a safiyar ranar,duk da cewa kuwa ba dabi'arta bane hakan. Sunan mr sadeeqa yana sama sama,auntie din su nurain 'ya'yan yaa Saifullahi. Sam ta mance da matar a rayuwarta,duk da cewa tana da kirki qwarai,tun kafin tayi aure lokacin da takanje gidan yaa Saifullahi din,wani lokaci ita ke kaisu school da safe,a nan suka dan saba da ita saboda matuqar kirkinta,sai kuma dabi'arsu tason yara tazo daya,wannan ya sanya suka dan saba suke gaisawa,har sukayi exchanging numbers.
Batasan ya akayi ba hannunta ya taba status din mrs sadeeqa,take ya bude,hotone na wata baby girl,duk da cewa hoton ya danyi blurry kadan,amma hakan bazai hanaka iya gane kyan yarinyar ba,tayi rubutu a qasan hoton kamar haka
_she has being suffering and battling epilepsy,she is looking for a good nanny,praying for an easy recovery my class cute angel_😥😥.
Epilepsy qwaqwalwarta tayi mata tariyar maganarsu ta jiya da sukeyi da afifa kenan kafin ta fita,take tausayin yarinyar taji ya taba zuciyarta duk da bata iya ganin fuskarta sosai,fingers dinta guda biyu ta saka tayi zooming hoton,still dai it was blurry,hakanan kawai tayi replying status din da cewa
_"is that serious?,she's looking for a Nanny"_ sai data tura saqon kuma sai tayi shuru,ita kadai tana tunanin meye amfanin tambayar data tura. Da sauri ta koma ta jerin charts dinta da zummar gogewa,amma sai ta tarar mrs sadeeqa din tuni ta gani,har ma tana typing wani abu,hakan yasa ta haqura ta koma duba document dinta da take budewa,amma kuma hankalinta nakan inbox din mrs sadeeqa.
Har zata buda taga shigowar saqo daga mrs sadeeqa din. Sake fita tayi ta duba
"Yeah,she's my student,ina tausayinta sosai,akwai wata ne daga bangarenki?" Tausayin data darsu a zuciyarta taji ya sake motsawa,a taqaice ta tafa mata
"No,but zan bincika,i will back to you idan na samu Allah ya bata lafiya"
"Ameen,thanks for your concern". Kashe data din tayi,ya dudduba addu'o'in sosai,zuwa lokacin garin ya fara haske,sai ta kashe wayar gaba daya ta sake gyara kwanciyarta ta kwanta tana rufe idanunta da fatan samuwar baccin.
Bacci tayi sosai,har na kusan awanni hudu,wanda qarshen baccin yazo mata da mafarkin da ya sanyata farkawa. Miqewa tayi ta zauna sosai tana duban gefan afifa,bata a gurin,tabi dakin da kallo,da alama ma harta gyara dakin,gadon da take kwance a kai ne kawai bata gyara ba. Hannunta ta sanya ta tattare gashinta daya zame daga band din data matseshi dashi saboda santsinsa,ta daureshi gudi daya tana sauke qaramar ajiyar zuciya,tunaninta na komawa baya kan mafarkin da shine silar farkawarta a yanzu,zuciyarta cike fal da mamaki,to meye hadinta da yarinyar da bata taba ganinta ba sai dazu a status din mrs sadeeqa da har zata yi mafarkinta?,ko a dazun ma bata gama tantance fuskarta ba,kamar yadda a mafarkin ma bata gama ganin fuskarta sosai ba.
"La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin" ta fada a hankali,sannan ta zamo ta sauka daga gadon,har yanzu zuciyarta bata daina mamakin yanayin data ga yarinyar a mafarki ba. Kuka takeyi sosai tana riqo hannunta,yayin da ita kuma take qoqarin zame hannun nata ta tafi ta barta,daga bayan yarinyar kuma wata matace take biye da ita da sharbebiyar wuqa tana son caka mata. Da wannan tunanin ta isa toilet din,ta ciri brush ta matsa toothpaste ta fara wanke bakinta,har yanzu tana nacin son gano abinda mafarkin ke nufi amma ko daya tunaninta bai iya hasaso komai ba,to shin me ma zata hasaso din?,bayan batasan wace yarinyar ba,daga qarshe sai ta tattara tunanin ta watsar,ta barwa ranta cewa tsabar son yara da take dashi a jininta ne,da kuma yadda zuciyarta ke da rauni akan dukka abinda ya shafi yaro.
Wanka tayi gaba daya sannan ta dawo dakin tana shiryawa,afifa ta shigo da dan tray data shiryo breakfast dinta a kai,hannunta daya riqe da waya tana amsawa. Idanunta akan fuskar sãahar din harta qaraso,sai ta miqa mata wayar muryarta can qasa tace
"Please" hadi da karyar da kai gefe daya alamun roqo. Kafeta tayi da idanu tana son nuna mata bata kyauta mata ba da zata sanyata yin abinda batayi niyya ba,sai kuma daga bisani ta miqa hannu ta karba wayar,don afifa ce tafi qarfin komai a wajenta,ta kara wayar a kunnenta tana qoqarin tsane jikinta da qaramin towel.
Page 57
*H U G U M A*
*_TABARMAR ƘASHI_*💔
Page 57
Kamar yadda tayi tsammani mahmud ne,ajiyar zuciya mai nauyi ya fara saukewa
"Kiyi haquri,duk yadda naso nayi miki yadda kikaso,zuciyata ta gaza bani hadin kai,na mugun jarrabtata da sonki har bansan iyaka ba" bakinta ta tabe,tana jin kamar ta saki wayar ta tarwatse,da wadan nan kalaman nasa gwara ya sakar mata ihu a kunnenta yafi mata sauqi,amma hakanan ta daure ta amsa a taqaice
"Is okay,bana dan jin dadi ne,that's why na kashe wayar"
"Ya salam" ya fada cikin nuna kulawa
"Me ya sameki?"
"Noo,lite headache ne,amma i feel better"
"To alhamdulillah,kibar wayar a kashe ki samu ki huta sosai,idan inason jinki zan kira ta line din afifa,bata wayar zamuyi magana" batace komai ba ta zare wayar ta miqa mata tana harararta,tana danne dariya ta karba,batasan me ya gaya mata ba,taga ta miqe ta fita,ta bita da kallo tana tabe baki taci gaba da shiryawa.
Tana cikin saka kaya afifan ta dawo,ta koma ta zauna tana ci gaba da cin abincinta,saita fasa daurin dankwalin da tayi niyya,dama can dankwali asara ne cikin dinkunanta,ta qaraso gaban afifan bayan ta jawo stool ta zauna ta sanya hannu suka fara ci tare. Har suka danyi nisa babu me cewa da dan uwansa wani abu,afifa ta karanci yau mutanen ne a kusa,ita kuma bakinta magana ce fal,don haka ta koma ta zauna sosai tana kallon sãahar
"Na baki shawara?" Dubanta sau daya tayi sannan tace
"Bani mana,is ether na dauka ko na bar miki kayarki"
"Alright,ammm......magana ta gaskiya na jima banga soyayya me zafi irin wadda mahmud yakeyi miki ba....."
"Tam, contract din kuma da kika karba kenan da safen nan,ko azahar batayi ba?" Dole ba tare data shirya ba dariya ta qwace mata sosai
"Allah ya isa bestie,wait......wai me kika mayar dani?"
"Me dalili,naga alama sana'ar da kikeso ki koma kenan" wannan karon ma saida wata dariyar mai sauti ta kufce mata har tana shirin qwarewa,a nutse sãahar din ta tsiyaya ruwa ta miqa mata
"Maza karba kisha kada ki wuce gana ya rasa campaign officer dinsa" tana dariyar tana sha,har taji dai dai ta ajjiye,tayi gyaran murya kadan tana dubanta da idanunta da suka tara hawaye
"Seriously nake miki magana,amma naga kinason ki maida abun wani joke,don Allah bestie ki manta da komai,ya kamata kiyi moving forward mana,kina tunanin zamanki a haka adam bazaiyi tunanin shi kike jira ba?,har yanzu soyayyarsa ta hanaki kallon kowa bare ki aureshi?"
"Soyayya?" Ta furta kalmar kamar ranar ta fara jinta,kai afifa ta jinjina
"Yes" wani qaramin murmushi me ciwo sãahar din ta saki,sai kawai ta miqe
"Banda bayan soyayya dake tsakanin namiji da mace,kawai nau'ikan soyayya kala kala, kamar wadda ke tsakanin 'yan uwa da iyaye,da nace Allah ya tsinewa soyayya albarka" ido afifa ta zaro,ta kuma hangame baki yana kallon sãahar,wadda tayi furucinta hankalinta kwance,saima ta gyada kai ta juya tana nufar qofa
"Naga alama tunda kika samu annual leave din nan rashin aikin yi ya sameki,shi yasa kika amsa contract daga wajen gana,to wallahi ke dashi ba wanda zaya matsamin" tana kaiwa qarshe ne dai dai sanda take fita a dakin gaba daya.
Gurin ummee tayi tafiyarta,wunin ranar gaba daya taqi tsaiwa sauraron bayanan mahmud. Saidai wani abun mamaki,duk bayan wasu mintuna sai yarinyar da ko sunanta bata sani ba ta fado a ranta,hakanan maganar da sukayi da mrs sadeeqa,wunin ranar har yamma,batayin minti arba'in cikakke bata fado mata a rai ba.
Ta idar da sallar la'asar tana yiwa ummee din gyaran wardrobe dinta kiran yaa Saifullahi ya shigo wayarta,cikin girmamawa ta daga kiran ta kara a kunnenta,ta gaidashi a aladabce,saboda shine babba duka gidan,kuma hatta da yaa muhyi yana bashi girma,duk da cewa shike binsa,akwai girmama na gaba sosai a tsakaninsu
"Kina gidan inna ummee dinne?,akwai baqo da zayazo ya sameki,abba yace a shaida miki" gabanta ne ya fadi,rudewa kuma ta sameta lokaci guda,har ta kama sunansa ba tare data shirya ba
"Mahmud?"
"Eh fa,da wani abu?" Ya tambaya kai tsaye da seniority din nan nasa
"A'ah,daman.....dama munje therapy saloon ne"
"Alright,zai kiraki yanzun saiki gaya masa" daga haka ya yanke wayarsa abinsa.
Wayar ta jefar gefe kamar zata saki kuka,da qyar ta tsara qaryar gashi kuma da alama haqanta bai cimma ruwa ba. Bata gama wannan tunanin ba kiran mahmud din ya shigo,kamar ta dora hannu aka tayi kuka haka ta daga kiran.
Akwai wani irin farinciki sosai cikin muryarsa
"Can I get the address?,saina sameku a can?"
"no,mu hadu a gida kawai after one hour" kamar zai zuba ruwa a qasa yasha haka yaji,cikin madaukakin farinciki yace
"Thank you,thank you so much" bata tsaya jin qarashen godiyar tasa ba ta yanke kiran tana gunaguni,ta ajjiye wayar gefe tana dafe kanta.
Ko kwalli bata sanyawa idanunta ba haka ta fito,afifa tayi tayi amma tayi biris da ita,daga baya ma cewa tayi
"Idan kika matsamin Allah sai na fasa fita"
"Allah ya baki haquri masifaffiya" sai taja bakinta tayi shuru,tasan kadan daga aikinta.
Tun kafin ta isa afifa tasa an cika shi da kayan motsa baki kala kala,tahowarta ya sanyashi miqewa,bai zauna ba har sai data zauna sannan ya zauna yana mata barka da fitowa,ta danne zuciyarta ta gaidashi,abinda ya masa dadi sosai. Duk yadda yasan zai sha kanta sai da yayi,tana zaune tana saurarensa har ya gama,sannan ta motsa labbanta
"Inda zakayi haquri da hakan yafi,saboda tuni na rufe babin soyayya daga rayuwata" kai ya girgiza
"Banajin zan iya,banajin zan iya daina sonki,kiyimin alfarma ki amincemin ki aureni,zan iya zama dake a hakan koda ke baki sona" tsam ta miqe,saboda ta fuskanci mahmud din yayi nisa,kuma bayajin kira sam. Ta bude bakinta da niyyar magana ya zaid ya iso wajen.
Yanayin yadda taga suna gaisawa da shi cike da sanayya mutunci da girmama juna ya daga hankalinta,sanda suka gama gaisawan da tambaye tambayen juna sai zaid din ya kalleta
"Ki riqeshi da kyau,mutumin kirki ne sosai" maganar tayi mugun tabata,har kuma mahmud yayi mata sallama ya wuce bata sake fahimtar abinda yake fada ba. Haka taci gaba da kasancewa har zuwa dare,tabbas!,ba shakka komai zai iya faruwa,muddin mahmud yaci gaba da samun irin wannan soyayyar daga wajen 'yan gidansu,idan tace komai,tana nufin komai din,ciki harda tausata ta karba aurensa ba tare data shirya ba!.
Wannan sautin da ya tsarga daga cikin kwanyarta shi ya sakata miqewa zumbur ta zauna saman gadonsu,afifa dake gaban system tana wani aiki ta waiwayo tana dubanta,saita maida kai tana ci gaba da aikinta ganin ta dauko wayarta itama ta bude. Tun bayan tafiyar mahmud ta fahimci tana cikin damuwa,ta riga da tasan damuwarta na meye,so shi yasa ma bata tambayeta akan komai ba.
Kai tsaye ta kirayi layin mrs sadeeqa,bugu daya tal ta daga,da alama tana kusa da wayar,cikin mamakin ganin kiranta da kuma zumudi hadi da girmama suka fara gaisawa,tana tambayarta tsaffin dalibanta su fadeel
"Basu dawo qasar ba har yanzu....." Ta furta cikin son yankewar tambayoyin ta kuma isar da nata saqon
"Ma sha Allah" mrs sadeeqa ta fada
"Inason tambaya ne naji,your student,ta samu nanny din nan kuwa?" Kai ta girgiza
"Kai,gaskiya i don't think so"
"So if you don't mind nace akwai me buqatar aikin" murmushi ta saki
"Ma sha Allah,so far dai banajin akwai wadda tayi musu,duk da hajiyan tata tace akwai wadanda aka yiwa screening,amma basu cancanta ba" duk da batun screening wa nanny's din ya bawa sãahar mamaki,amma ba wannan bane yanzun a gabanta
"Alright,hakan yayi"
"Naji dadi,nasan ko wace za'a samu daha bangarenki she wil be the best among others in sha Allah,wace a ina take?,sai na yiwa hajjajun magana"
"Nice" ta fada da qwarin gwiwa. Ba mrs sadeeqa ba,hatta afifa dake aiki batasan sanda ta tashi ta zauna sosai tana duban sãahar da wani irin madaukakin mamaki ba,tare da tantamar abinda kunnuwanta suke son jiye mata
"Na'am madam,me kika ce?" Mrs sadeeqa ta tambayeta cike da kokwanton abinda taji daga bakinta
"Yes,nice,ni zanyi aikin" dan murmushi mrs sadeeqa ta saki
"Madam,ko baki kula sosai da wanne irin aiki bane ake magana,ba aikin company ko na banki ko lecturing bane......raino ne,na yarinya me lalura,duk da ba qarama bace sosai,amma dai raino ne" ido sãahar ta lumshe sannan ta budesu lokaci guda
"Ya salam ya Allah" ta furta a qasan zuciyarta,batason ta fara da samun matsala tun yanzu,saboda ba zata iya jurewa ba,zuciyarta ta karkata matuqa,ta kuma kwadaitu da buqatar aikin
"I Know,na fahimta,just......ina sha'awar yin aikin ne" shuru mrs sadeeqa tayi cikin kokwanto matuqa, kafin daga baya tace
"Zaki iya kuwa madam,wouldn't it be a disgrace?"
"Surely mrs sadeeqa,ko ba komai aikin lada ne" ta fadi hakan har zuciyarta
"Gaskiya ne,i will talk to hajiyan,zan miki magana,kin gama samu ma in sha Allah,you are not the kind of people to be ignored"
"Thank you ma'am" sãahar ta fada tana gintse kiran
"Thanks for what sãahar?,wanne mummunan tsari ne wannan?,a nanny?" Afifa ta furta kamar zatayi kuka,kalmar na sukar ranta.
A nutse abinta hankali kwance take kallon afifa din harta gama,saita sauka daga inda take zaune,ta dawo kusa da afifan ta zauna sosai tana fuskantar ta
"Wannan shine burina a yanzu, abinda kuma nakeso,bazan iya boye miki komai ba bestie,shi yasa nayi wayar ma a gabanki,jikina yana bani mahmud nason yin galaba akan su abba dasu ya Saifullahi,idan banyi wasa ba kuma komai yana iya faruwa,so I want to be far away from him for a while that's why na nemi wannan aikin,banason mahmud afifa,bazan iya aurenshi ba,zanyi nesa dashi,duk sanda na samu tabbaci da yaqinin iya zama da wani namijin.....koda shi mahmud dinne zan dawo a kurkusa,i won't be longer,support me please bestie"
"What a bad idea sãahar?,you mean....zaki koma 'yar aiki fa kenan?,wait.... idan na yarda ma su abba kina tunanin zasu yarda da ke?" Murmushi ta saki kadan
"A yanzun nafi sha'awar zama 'yar aikin bestie,ko banza babu ruwana da kowa da matsalarsa,zan zauna guri daya nayi rayuwata da yarinya qarama,zan cika burina na raino wanda adam ya dakushe min.......zan samu ladan yarinyar dake dauke da cutar epilepsy,ban sani ba,kota silar jinyar Allah ya yayemin tawa damuwar bestie,don Allah ki maaramin baya,kada ki watsamin qasa a ido" shuru afifa tayi tana jin yadda sãahar ta riqe hannunta da kyau,da alama tana buqatar yin hakan,kanta ya kulle sosai,ta yaya zata mara mata baya ta mayar da kanta nanny?,bayan da gantanta?,duk randa maganar ta bayyana me zatace da su abba da maama?. Sosai sãahar din ya tsareta da ido cikin laushi da salon rarrashi,sai ta rasa amsar da zata bata,daga bisani Allah ya kimsa mata,ta waiwayo ya dubeta tana sauke ajiyar zuciya
"Ni dake duka muje muyi istikhara,idan mun samu nutsuwa akan abun,zan maara miki baya"
"Kin tabbata da gaske kike?" Murmushi ta saki
"Da gaske nake,amma ki tanadi abinda zaki gayawa su abba,don ni bazan iya musu qarya ba" miqewa tayi daga tsugunon da tayi ta zauna sosai
"Kinfi kowa sanin ba dabi'ata bace,so nima ba qaryar zanyi masa ba".
Akan haka suka samu matsaya ita da afifa din,sannan kuma dukansu suka shiga istikhara din kamar yadda afifa ta shawarcesu. Cikin kwana ukun kuma baki dayansu ita da afifan,kowanne ya samu nutsuwa cikin ransa,rudanin dake ran afifa ya kau,haka dan kokwanton da ita sãahar din kanta takeyi game da aikin sai taji babu shi,taji har cikin ranta zata iya,fatanta daya kada abba yace ba zatayi ba.
*_TOFA😂,me yake shirin faruwa kuma?,GUDUN K'ADDARA sãahar ke shirin yi ko kuwa?,ku biyoni dai muje zuwa_*
Page 58
*H U G U M A*
*_TABARMAR ƘASHI_*💔
Page 58
Kwana biyu kacal Mrs sadeeqa tayi kiranta,ta gaya mata cewa hajiyan tayi accepting nata,saboda haka ta shirya kwana uku masu zuwa zasu zo da mota a dauketa ta kama aikinta.
Taji dadin hakan,amma kuma fargaba ta lullubeta na yadda zata tunkari abban,wuni tayi cikin rashin sukunin,afifa na kallonta taqi bata shawarar komai
"Na gama aikina ai,tunda har nace bazan gayawa abba manufar komai aka aikinki ba"
"Haba bestie"
"Da gaske nake" ta sake jaddada mata,sai daga bisani ta samu qwarin gwiwa,bayan wata idea ta fado mata,ta dauki wayarta da sauri ta fara kiran anty farheen.
"anty,zan sameki yau a gida?"
"Eh ba inda zani yau,akwai wani abu ne?"
"Saina iso kawai" tace da ita,saita ajjiye wayar ta fada toilet kawai ta fara wanka,so take ta gama da kowacce matsala a yau,tayi shirin tafiyarta hankali kwance.
Cikin lokaci qalilan ta shirya cikin wata doguwar rigar abaya qirar qasan oman mai sulbi da kuma tsarin zubin duwatsu masu daukan hankali,fuskarta ta sake wani fresh da wani irin haske me kyau,kalar abayan na charcoal color ya karbi farar fatarta sosai,sassanyan qamshinta na bin kowanne sashe na dakin har zuwa falon da batakai ga fitowa ba.
'Dan abinda take da buqata ta dauka a wata qawatacciyar qaramar jaka me jikin mage,dai dai lokacin da afifa ke kitchen tana duba girkin abbansu da basu aikin gidan suka dora ta dawo dakin,ta murza qofar ta shigo,idanunta akan sãahar
"Madam nanny" ta fada tana murmushi hadi da tabe baki, zagayyun fararen idanunta ta juya tana goya jakar a bayanta
"Yes,daga yau sunana kenan" qaramar dariya afifa tayi tana zama saman stool
"Kinsan Allah zaiyi wuya ma su karbeki as nanny,shin wai ke baki kallon kanki ne?,wace zata daukeki 'yar aiki muddin tana da aure?,wace wawiyar ce?....."
"Don Allah afifa tsaya,kiyimin fatan alkhairi mana,wannan duka fatan tsiyan na meye ne ha'an"
"Baqinciki nakeyi, bestie na zata zama 'yar aiki"
"Okay,that's fine,kici gaba da fada" saita fara zura dogayen qafafunta cikin wani lallausan plate din takalmi
"Ina zakine ma babu ko gayyata?" Ta jefeta da tambayar bayan ta dakata daga danna wayarta
"Gidan yaa muhyi"
"Jirani don Allah na shirya" ta fada tana miqewa da gudu bayan ta cillar da wayar tata ta shige toilet ba tare data tsaya jiran jin abinda sãahar din zata ce ba. Iska me zafi ta fitar,afifa dole saita bata mata lokaci,tanason ta gama komai da wuri ta iske abbanta a gida,ta kalli agogon dake daure a hannunta dan india dan kamfanin Daniel Wellington,saita maida dubanta ga qofar bandakin
"Ki sameni a wajen ummee,don't stay longer please" saita tsugunna ta dauki laptop dinta me tambarin apple ta fice daga dakin.
•••••••••"daga ina kuke halan da yamman nan?" Farheen ta fadi tana zama saman kujera,bayan ta fito musu da plate din snacks,me aikinta dauke da daya try din data shirya musu smoothie,don ita din gwanar girki ce kala kala,fridge dinta kawai idan ka bude zaka samu fresh snacks sosai,a nan din sãahar ta koyi girki masu yawan gaske
"Nanny sãahar ce ta tasomu,ni fa amma gayyar sodi nazo,don bata gayyaceni ba nace ta tsayani mu taho tare" afifa tayi maganar tana duban sãahar daketa ji da rigimar khalipha shi da aleena data qara wayo sosai
"Nanny kuma?" Farheen ta fada tana dan dariya,a zatonta fadan da suka dan saba tabawa ne da shaqiyanci ma juna ya motsa tsakaninta da sãahar din
"Eh mana anty,koda yake dai ance waqa a bakin me ita yafi dadi" ta qarshe zancan tana jawo cup din da smoothie din yake,ta gyaran zaman straw din jiki ta fara zuqa a hankali tana lumshe ido,zaqi da dadinsa yana ratsata
"Uhmmmm,ta yaya don Allah ya muhyi zai iya qara aure ana masa wannan delicious din" qaramar dariya farheen tayi,tasan afifa qwarai badai iya tsokana ba,amma hakan na mata dadi,don babu komai tsakaninta da dangin mijinta face tsantsar girmama juna da zaman lafiya hadi da qaunar juna
"Basu da tabbas fa,iya girki ko qwarewa a wani abun baya hanasu qara aure idan sunso,koda kuwa ke din hurul'eeni ce,saidai kawai dai ki iya din don ki amsa sunanki na mace,sannan saboda lafiyarki yaranki dashi kansa me gidan,yaranki mata kuma ki zame musu makaranta,sannan koda wata zatazo din ya zamana ba'a fiki da komai ba,kin wuce kiyi kwaikwayo saidai keda ita ku goga,kowa ya baje hajarsa" kai sosai afifa take gyadawa cikin gamsuwa,zaiyi wahala ka zauna da farheen baka qaru da ita ba ta kowanne fanni na rayuwa.
"Ke kuma yaushe kika zama nanny?" Ta maida tambayarta ga sãahar,daga kanta tayi,sai kuma ta zaunar da aleena sosai tsakanin qafafunta
"Shi mutum idan gulma tayi masa yawa sai addu'a,da kin barta ta qarshe miki labarin..... bestie naga alama bazaki rufan asiri ba" dariya sosai afifa keyi harda kwanciya cikin kujera,abun yana bata mamaki yadda sãahar lokaci daya ta daukaki batun aikin da zahiri tafi qarfinsa,ita kanta a gidansu 'yan aiki nawa ne?,so amma a yanzun ita bata jin komai akan aikin,tunda suka tsaya sukayi addu'a a tare.
"To nayi miki qarya ne,ba nanny din bace?"
"Ban sani ba.....am anty don Allah alfarma nazo nema" ta qarashe maganar tana maida hankalinta ga farheen
"Ina jinki,Allah yasa bata fi qarfina ba". Komai ta zayyanewa farheen shi,saboda babu 'yar boye boye a tsakaninsu,sannan ta qarashe da cewa
"Matsalata daya abba zaice zaiyi bincike akan inda zani aikin,abu daya nakeson kiyimin,zance masa kin sansu,sannan wata uku kacal zanyi na dawo" shuru farheen tayi tana jinjina kai,tana qaunar sãahar har cikin ranta tamkar qanwarta uwa daya uba daya,zata iyayi mata kowacce alfarma,to amma kuma akwai matuqar girmamawa da ganin mutuncin juna tsakaninta da surukanta,batason tayi musu qarya
"Zan iyayi miki kowacce alfarma,amma bazan iya shaidar abinda bani da tabbaci ba,inason ki bani address dinsu na gani,zan aika ayimin binciken ingancin halayyar mutanen gidan"
"Alright" ba wani jinkiri ta kira Mrs sadeeqa kai tsaye,ta kuma tura mata komai da komai.
Address din ta tura mata,ita kuma ta miqawa farheen wayar. A fili ta karanta address din
"Wannan layin ai kamar layin gidan qawata sauma,bari nayi confirming" khalifa ta tura ya dauko mata wayarta,saita tashi tabar gurin. Duk da hankalin sãahar nakan yaran,amma kuma fiye da rabin tunaninta yana kan farheen data fita a falon.
Ta kusa mintuna ashirin sannan ta fito,ta koma ta zauna a inda ta tashi
"Yanzu kuma ina da qwarin gwiwar bada shaida,layin gidan qawata ne,tasan gidan,sanann me gidan ma tacemin sananne ne sosai,mutumin kirki ne qwarai da ya samu yabo da shaidar al'umma,ko jiya shine wanda ya qaddamar da committee na tsaro na unguwar,kusan ko yaushe suna tare da me gidanta tsakanin sallar magrib da isha'i,duk da ba mazauni bane,yakanyi watanni ma baya gari,yarinyar ce tace bata santa sosai ba,tunda ba inda take fita,amma tace eh tabbas yana da diya guda daya. Ajiyar zuciya sãahar ta sake,sai ta sake jin nutsuwa tana ratsata,yanzun kam ta samu qwarin gwiwar tunkarar abba,muddin farheen tace ta san gidan,tana da yaqinin babu lallai abba ya zurafafa ko yace zai hanata,yana ganin kimarta sosai cikin surukansa.
Ana idar da magriba sãahar din ta miqe
"Zan wuce gida bestie ya za'a yi?"
"Kije kawai,drivern anty farheen sai ya saukeni"
"Ba wata damuwa?"
"Babu miss nanny" harara ta watsa mata,ta dauki qaramar hand bag dinta ta tsugunna tayi kissing aleena a cheeks dinta.
A kan hanya ita kadai tana driving tana tsara zantukan da zata tunkari abba dasu,wani lokacin takanji abban me sauqi ne akan maama,amma tasan muddin abban ya amince,maama din ma komai zaya zo da sauqin in sha Allah.
Mintuna talatin kacal suka kaita gida,saboda tana tuqin tana duba lokaci,tanason ta saita lokacinta dai dai da sanda zata riski abban yana hutawa.
Baaba habu ne mutum na farko daya fara yi mata barka da zuwa bayan ya dage mata gate din gidan ta wuce zuwa ciki,ya iso gaban motar sanda take fitowa
"Barka da zuwa farar d'iya" qaramin murmushi dake qawata fuskarta qwarai ta saki tana fitowa a motar
"Baba habu,baaba rabi ta koya maka ko?" Murmushin dake dauke da dattijanka yayi
"Sunan ya dace da me shine ai,kedai Allah yayi miki albarka keda sauran 'yan uwanki"
"Ameen ya Allah baba habu,Allah ya qara girma" kamar sauran lokuta,bata fiya wucewa ba tare data yi masa alkhairi ba,tun tasowarta yake cikin gidansu yake kuma musu aiki bisa gaskiya da amana,ko sau daya bata taba jin wani yayi kuka a kansa ba,hakanan baaba rabi,ba kasafai gidansu suke sauya me aiki ba,saboda suma masu aikin idan suka fara,basa barin gidan haka siddan saidai mutuwa ko kuma aure.
Hannu biyu yasa ya karba yana godiya,ba kasafai ta fiyason yawan godiyarsa ba,ko ya dinga sanya hannu bibbiyu idan zai karba abu daga wajenta ba,to amma koda zatayi maganar ma bazai canza ba,ya riga ya saba
"Ameen ameen,baba habu ayi min addu'a" ta fadi tana rufe jakarta
"Kullum cikin yi muku nake,amma a yanzun ma bazan fasa ba,Allah ya tabbatar miki da dukkan alkhairi a rayuwarki"
"Ameen ya hayyu ya qayyumu,na gode sosai" cikin wannan girmamawar da mutuntawar ta nufi entrance na gidan,bakinta dauke da
"La haula wala quwwata illa billahil aliyyul azeem" don taga motar abban nata,hakan kuma ya tabbatar mata yana gidan,koda ya fita to masallaci ne kawai.
Falon nasu ba kowa,ta danja qaramin tsaki,ta tsani wannan loneliness din na gidan sam,shi yasa bata cike sati guda a gidan,kwanaki taji maama tana batun zuwa nijer cikin 'yan uwa ta dauko yara biyu mata,batasan inda zancan ya kwana ba har yanzu.
Dakinta ta duba don sanar mata da isowarta amma bata risketa a can ba,saita zarce kitchen tana tafe tana yaba tsafta da kulawar da gidan nasu yake samu,wannan ya sanya ta taso da dabi'a ta masifar tsafta qwarai.
Sallamarta ya sanyata waiwayowa sanda take juye tea a flask
"Daga ina da daren nan?"
"Gidan ya muhyi" ta fadi tana zagayowa ta rungumeta ta baya
"Yau kuma?,sakeni to kada na qone"
"Da kin barta ai hajiya,auta ce fa" cewar lariya me aikinsu
"Wannan gansamar?" Ta fadi dai dai sanda sãahar din ta zagayo ta karbe qaramar rariya da cup din da take tace shayin taci gaba da aikin
"Amma na hanaki tafiyar dare irin haka ko?,abbanku ma kuma bayaso"
"Za'a kiyaye in sha Allah maama"
"To Allah yayi albarka"
"Ameen maama na". Tsaf ta gama hada mata komai sannan suka fito tare bayan taji abban yana masallaci,ita tayi dakinta ita kuma ta wuce sassan abban.
Kayan jikinta ta fidda,ta shiga wanka,ta wanke jikinta da kyau da ruwa me dumi sosai,sai data fara yin sallar isha'i sannan ta shirya cikin riga d wando masu laushi,rigar ta kawo mata har cinya me gajeran hannu,sai wandon shima daya saukar mata har qasa,ta kama gashinta ta hade da pink ribbom sannan ta shafe jikinta da lallausan turarenta. Wani kyau tayi sosai,kayan sun karbeta kamar bana barci ba,idan ka ganta a lokacin zata dauka duka duka shekarunta sha takwas ne zuwa sha tara. Remote din ac ta dauka ta rage qarfinta,ta ajjiye saman bedside table sannan ta dauki hijab dinta me hannu ta saka,ta zira slippers dinta ta fito daga dakin.
Tana takawa qirjinta yana dukan uku uku,addu'o'i fal bakinta,daga jiya zuwa yau ta wani mugun damuwa da aikin,damuwar da ita kanta takanji mamaki,batasan dalili ba,tafi danganta hakan da abubuwa biyu,neman mafaka da kuma tausayin yarinyar da ya sauka tun daga saman zuciyarta har ciki tun jiya.
Da sallama ta shiga parlor din abba,ya amsa mata yana dauke dubansa daga kan zain dake zaune a gabansa ya mayar kanta,ta qaraso cikin nutsuwa tana zama a gefansu. Abban ta fara gaidawa sannan ya zain,sai ta karbi maama dake qoqarin serving nasu abinci ta fara zuba musu,data kammala sai ta koma gefe ta lafe kawai,hankalinta yana rabuwa gida biyu, rabi a hirarsu,rabi kuma tana tauna yadda maganar zata fita a bakinta
"Yadai ummin abba?,akwai labari?" Dr mamman ya fada sanda ya gama tauna lomar abincin dake bakinsa,murmushi ta saki,tayi qas da kanta tana murza yatsunta
"Babu abba"
"Ban yarda ba,bari mu gama cin abincin tukunna" ba abun mamaki bane sam don ya fahimci damuwarta lokaci daya,shi din wani irin mutum ne daya samar da shaquwa da sabo sosai tsakaninsa da iyalinsa,akwai fahimtar juna da kuma sakin fuskar da bai haifar da raini ko rashin girmamawa ba a tsakaninsu ba.
Ba jimawa zain yayi musu sallama ya wuce,falon ya zama daga ita sai abban,don maama ma ta wuce bedroom dinsa tana sanya turaren wuta,wanda hakan din dabi'arta ce,duk da ko yaushe gidan ma gaba daya cikin turare yake,amma muddin abban yana gab da kwanciya sai ta kunna burner ta saka wani turaren,wanda yawanci yana riqe dakin har zuwa safiya,a gurinta sãahar ta koyi wannan,yana qarawa bacci dadi da armashi sosai.
"Ummi na,ma yake faruwa?,kada kiji nauyina,ki gayamin" sake takurewa tayi kadan tana jin fargaba,ta saci kallon abban,abinda ya alamta masa da gaske akwai magana me muhimmanci da takeson gaya masa
"Ehmmm,ina jinki ummi na"
"Abba....." Sai ta kasa ci gaba
"Ina jinki,fell free mana ummi"
"Abba don Allah wata alfarma nazo nema,wadda nake da tabbacin indai ka amince tafi dukkan wani aiki da zanyi kyau da samun lada me tarin yawa,abba.....inason ka saurareni,sannan kayimin alfarma"
"Ina jinki" ya fada yana tattara hankalinsa a kanta.
Page 59
*H U G U M A*
*_TABARMAR ƘASHI_*💔
Page 59
"na samu aiki abba.....amma ba irin aikin da kuke tunani zanyi ba,aiki ne na kula da mara lafiya"
"Kula da mara lafiya kuma?" Ya tambayeta cikin mamaki,kai ta jinjina
"Banda abinki ummi,ai ba sai kinyi da kanki ba,idan kikayi bayani,sai na biya a daukowa mara lafiyan me kula dashi har zuwa sanda Allah zai bashi lafiya" kai ta girgiza alamun a'ah
"Ba jinya bace ta kullum kullum da ake kwance ba,abba yarinya ce marainiya,wadda take fama da epilepsy,tana buqatar kulawa ta wasu watanni daga gurin tsayayyar nanny da zata iya kulawa da ita da kyau"
"Ikon Allah" kawai dr mamman ya fada,ya gyara zamansa yana kallon sãahar din,abinda ya bata damar dorawa
"Zanyi aikin nan abba idan lamuncemin,bawai don neman kudi ba,sabida babu abinda na rasa daga wajenku,zanyi ne kadai saboda kwadayin lada wajen Allah,wanda na tabbatar hatta ku zakuyi tarayya a cikinsa,don Allah abba ka lamuncemin,haka kawai na tsinci kaina cikin kwadayin wannan ladan" kai ya gyada,maganarta gaskiya ne,saidai abun ya masa banbarakwai,diyarsa da aikin nanny a wani gidan?.
"Duk maganarki haka take,to amma banda abun ummin abba,ko biya kikayi akayi kina da wannan ladar ai" zamanta ta gyara
"Abba suna da wadatar da zasu iya biyan kowanne mutum,amma kudi basa iya taba siyan nagarta da cancanta" kai ya jinjina cikin dogon nazari
"Abba bazan jima ba,tana samun lafiya shikenan" ta yanke masa tunaninsa ta hanyar fadin haka. Dole murmushi ya kubce masa saboda yadda tayi maganar cikin kwantar da murya tana langabe kai,da alama da gaske har cikin zuciyarta takeson tayi aikin.
"Shikenan,kiban address,zan sa fahad ya yimin bincike akan nagartar mutanen gidan,don bazan bawa wani cikin yayyenki bama"
"Kana iya tambayar anty farheen,ita ta fara bincikawa ma, neighbors na qawarta ne,kuma Alhmdlh basu da matsala,shi yasa aikin ya sake kwanta min a raina" fadin farheen din ya sake sanyawa hankalinsa ya dan kwanta
"Zan nemeki" ta miqe tayi masa sai da safe ta wuce sashensu.
Washegari da safe taga sauyin fuska daga wajen maama,sai tasha jinin jikinta,abban yana fita kuwa ta kirata,sababi ta fara tare da gaya mata itakam bataga dalilin wannan aikin ba,sosai ta kwantar da kai tana kwatanta mata amma maama tayi biris. Wuni guda ana abu daya har dare,shima abban ya gaza shawo kanta,sai da tayi kiran afifa. Itama afifan qin zuwa tayi da farko,ko da tazo dinma sai ta hadasu duka ta fatattakesu,daga bisani afifan tabi bayan maama,batasan ya suka qarke ba,tadai shigo tana harararta
"Burinki ya cika new nanny" murmushi me kyau ya subucewa fuskarta,yadda tayi maganar ya tabbatar mata da ta shawo mata kan maama,saita rungumeta tana cewa
"Allah ya barmin bestie na" murmushi itama ta saka
"Ba wani dadin baki fa,bawai ance kije ki manta da mahmud ba" baya taja tana hade rai,afifa ta bita da kallo tana jan qwafa,itadai batasan sai yaushe sãahar zata dauka daga kan wannan aqidar ba,tana addu'ar Allah ya kawo mutumin da zai sauya wannan tsattsauran ra'ayin nata.
*****Cikin takun nan nasa me cike da tsantsar qasaita da kuma wani irin aji suke nufar sassan hajiya qarama. Sanye yake da yadin baby cashmere me tsada dan qasar indai,wanda aka tsarawa wani irin dinki shi ba dinkin suit ba hakanan ba style na Pakistan ba,sosai dinkin ya qara masa kyau da kwarjini,ya kuma fidda qirar jikinsa qwarai dake dauke da siffar qarfi,duk inda ya gifta sai ya bada ajiyar sassanyan qamshin turarensa me masifar tsada daya sanya qamshin baya bajewa da wuri. Hnunsa riqe da siririn hannun fadeelan suke takawa zuwa sassan momy qarama,daga kan fuskarta har idanunta shabe shabe suke da hawaye,wanda rabi na shagwaba ne,rabi kuma tana ji har cikin zuciyarta yadda zatayi kewar mahaifin nata. Qasa qasa yake magana da ita tamkar wata babba
"Calm down my angel,ipad dinki na wajen momy qarama,nayi alqawarin kiranki kullum through video calls,i will do my very best na dawo da wuri,new nanny dinki na nan zuwa" kafada ta maqale tana zirara da hawaye
"Nikam banason wata nanny kuma,kai zanbi" murmushi ya saki saman miskilar fuskarnan tasa,sai ya sanya hannuwansa ya dagata ya azata zuwa kafadarsa yana ci gaba da takawa hadi da lallashinta cikin hikima. Duk duniya ita daya yake iya tsaiwa ya lallasa haka,banda a kanta,baisan koda hanyar yadda ake rarrashi ba.
Suna shiga falon momy qarama na fitowa daga kitchen,hannunta riqe da mug dake cike da tea
"Badai har ka fito ba?" Agogonsa ya duba yana amsata
"Am ready to go,banason na wuce haka kada nayi missing flight"
"Gaskiya ne" ta fada tana neman wajen zama,sai shima ya zauna saman daya daga cikin qawatattun kujerun dake falon
"Na sanya jibril yayi magana da mutanen can,za'a kawo food stuff,idan akwai abinda babu ki gaya musu kawai,zan saka elyas yayi transfer ta account dinki,naki ne keda fadeela,shikenan koda wani abu?" Qasaitaccen murmushi ta saki,a duniya idan akwai wadda ta shigo rayuwa a sa'a to tana cikin sahun farko na jerin wadan nan matan,tana jin dadi,kanta kuma yana sake fasuwa a duk sanda toufeeq ke treating nata haka
"Eh to,batun nanny din fadeela ne,yau in sha Allah zatazo,wannan karon ina saka ran an samu wadda zata iya kula mana da fadeelan in sha Allah,duk da naso ka ganta kafin ka wuce" miqewa tsaye yayi
"Ba damuwa,indai tayi miki fine,just ta kula da aikinta shine abun buqata,and then ta fadi nawa takeson salary dinta,every month ko qasa da haka,duk ba damuwa indai zata kula da qa'idoji da sharuda"
"Karka damu in sha Allah" tare suka sake fita da fadeelan,still tana maqale dashi. Kuka ta saka masa sosai security dinsa ya buda masa motar ya shiga,sai da yasa akayi kiean baaba ramatu,da wayau da dabara ta rabata da gurin tana kuka.
Har suka fita a gidan yana jin sautin kukanta cikin kwanyarsa,ya lumshe manyan idanunsa da suka sauya launi saboda wani bacin rai daya sokeshi,sannan ya budesu sosai yana jin wani ciwo cikin ransa,sam wannan ba itace kalar rayuwar daya tsarama kansa da kuma 'ya'yan da zaya haifa ba,wannan din wata bahaguwar rayuwa ce da qaddara ta tsago da ita cikin nasa shirin da tsarin ta kuma wargaza komai
"AMEESHA" sunan da bazai taba gogewa cikin tarihin rayuwarsa ba,koda ace ya fita daga zuciyarsa da dukkan wani abu daya danganceshi. Cikin hanzari ya watsar da tunanin,ta hanyar ciro wayarsa ya laluba wata number da yayi alqawarin kira ya kira din,ya fara amsa wayar cikin wani irin sanyi bayan ya maida bayansa yayi relaxing a jikin kujerar.
Koda ya gama wayar shuru yayi yana juya wayar a hannunsa,kamar wanda take sabuwa ga idanunsa ranar ya fara saninta,yau din gaba daya duk wanda ya kalleshi yasan yanayin komai ne cikin sanyi,yanayin da sam bashi a halittarshi.
Tsaiwar motocin ya janye hankalinsa,ya daga kan nasa yana duban driver dinsa
"What's happening?"
"I don't know sir,but.... lemme check" ya fada,sai driver din ya bude ya fita ya barshi shi da guard dinsa guda daya dake zaune a gaban motar.
Ko minti uku baiyi ba ya dawo da gaggawa
"An samu matsala sir,harith ne ya bige wani tsoho......"
"Ya salam" ya furta da sauri,ba tare da ya bari ya kammala bayaninsa ya bude qofar motar da kanshi ya sanya qafafunsa ya fito wajen,cikin sakanni guard dinnasa dukka suka fito suka take bayansa.
Har a sannan tsohon yana zaune a qasa yanata bala'i,harith din da wadanda suke mota daya suna tsaye a kansa. Tsawa daya ya daka musu cikin bacin rai dukkansu sukaja baya suna sunkuyar da kai,ya ratsa ya tsakaninsu ya isa gaban tsohon,ya duqa zai dagoshi suka matso da nufin karbarsa,ya daga musu hannu alamun dakatarwa,ya tsugunna gaban tsohon bayan ya tadashi sosai.
"Kayi haquri baaba,am very sorry,bada niyya bane na tabbatar,amma kayi mana afuwa gaba daya" dukka wani fushi da fada daga dattijon sai ya sauka,saidai idanunsa suna zube cikin na toufeeq din yana kallonsa,ya saki ajiyar zuciya
"Shikenan,ba komai"
"Ina fata baiji maka ciwo ba ko?" Ya sake fada yana kamashi ya miqar dashi ya tayar dashi tsaye yana kade masa jiki,cikin matuqar martaba da mutuntawa,duk da alamu da suka nuna babu wani sukunin rayuwa me yawa tattare da tsohon
"Ba komai yaro,banji ciwo na,buguwa ce kadan a hannu na"
"Dole a dubaka kada ya zame maka matsala baaba" cancel din mota daya yayi cikin jerin gwanon motocin,yace su miqashi asibiti a dubashi,sannan su kaishi ga iyalinsa, yayi kiran elyas da hannu,y qaraso cikin girmamawa,ya gaya masa abinda yake da buqatar a bawa tsohon
"Okay sir" ya fada a ladabce.
"Yaro!" Yaji muryar tsohon ta kirashi dai dai sanda yake shirin saka qafafunsa a motar,ya tsaya cak ya waiwaya yana dubansa
"Ban taba tsammanin mutum me arziqi har haka zai iya tsaiwa ya saurari talakan da bai mallaki komai kamata ba,na gode qwarai da karamcinka,a duk lokacin da kaji tasowar fushi daga zuciyarka,ka yawaita ambaton A'UZUBILLAHI MINASH SHAIDANIR RAJIM, HASBUNALLAHU LA ILAHA ILLA HUWA ALAIHI TAWAKKALTU WA HUWA RABBUL ARSHIL AZEEM" Shuru toufeeq yayi yana kallonsa har ya shige motar harith ya rufe,ya zagaya ya tayar da motar
"Sir..... it's getting late,we should leave" jikinsa a wani irin mace ya shiga motar yana maimaita kalmomin da dattijon ya gaya masa,daidai sanda jibril ya rufe qofar kira ya shigo wayarsa
"Maji" sunan daya bayyana kenan wanda furtasa ya hade masa da faduwar gaban da baisan dalilin saukarta ba.
Tattaro dukka nutsuwarsa yayi sanda motar ke dagawa ta dauki hanya sosai,cikin muryar da ita daya duk duniya yakewa magana da ita,duk da baisan hakan yana faruwa ba yayi mata sallama,sannan ya gaidata,ta amsa masa da wani irin kulawa
"Ina fadeela tah?" Ta tambayeshi a sanyaye. Wani nauyi yaji ya saukar masa,ya shirya yana hanyar barin qasar,tun da bai shaida mata ba sai a yanzu?,a yanzun ma da itace tayi kiranshi?,yaya zataji idan ya gaya mata hakan?
"Ko baka gida nayi kira da layin da zan sameta?" Ta jefa masa tambayar. Sosai nauyi ya sake kamashi,ya sani tana da wancan layin na baaba ramatu,to amma takan tsallake kowa tayi kiransa koda lokuttan da take da yaqinin baya tare da fadeelan,tun da jimawa ya fahimci tana hakanne don taji tasa muryar da lafiyarsa,tunda har yanzu hannayenta sun gaza iya koyar daukar wayar suyi kira a nata lambobin da layin domin suji lafiyarta,koda wasa.....koda sau daya......koda da gwaji. Wani al'amarine da yake damun qwaryar zuciyarsa qwarai cike da wata irin damuwa,amma ya gaza ta kowacce fuska.....ya gaza kawo gyara koda qanqani ne.......sau tari yanajin naqasu,gazawa da kuma kasawa,hadi da wata cikakkiyar tayawa me wawakeken girma daga rayuwarsa,amma baisan ta yadda zai gyara ba.....ta ina?,kuma a yaushe?,rashin matallafine ko kuwa?,duka shima bai sani ba.
"Allah ya kiyaye,ya tsare, ubangiji ya bayar da dukka sa'a da kariyarsa,fatan alkhairi" ta fada a taqaice ta kuma gimtse wayar.
Wani abune ya sauko ya daki zuciyarsa,take tayi wani irin rauni,yanajin wata irin kunyarta na mamayarsa, kunyar da dukka d'a na qwarai yakeji a lokacin da yayi wani abu na sabawa ga iyayensa,duk da a karan kansa yasha gayawa kansa shi din ba na gari bane......yanajin wani irin karyewa a tata muryar,kamar wadda kuka ke shirin subucewa,amma duk yadda yaso ya juya zuciyarsa ta bita don taji meye damuwarta ya kasa,sai ya soke hannayensa guri guda yana matsesu da wani irin qarfi,kamar yana shirin ballasu.
⚜️⚜️⚜️ Kebantacce falo ne wanda ke dauke da wasu qasaitattun kujeru da suka zama cikamakin cikar adon falon,bashi da wani girma,amma yana da tsari me matuqar kyau tare da jan hankalin me kallo.
Saman daya daga cikin kujerun falon sãahar ce zaune,cikin kamilalliyar shigarta ta jilbab,wanda yake hade da doguwar rigarsa me dogon hannu,gefe da gefe na dan qaramin hijabin madin rigar a tsage yake,an masa wani irin ado daga bakin tsagar,farar kyakkyawar fuskarta ta fita sosai ta tsakiyar fuskar hijabin da wani irin kwantaccen kyau me daukan hankali.
Tun farko shigowarta gidan take nazarinsa daya bayan daya,ta kowacce fuska gidan ya amsa sunansa,ya kuma sake bayyana mata tarin dukiya tare da arziqin da masu gidan suka mallaka. Ta taso cikin gata soyayya kulawa tsakiyar nasu arziqin da dukiyar,tun daga kan mahaifinta zuwa yayyenta,hakanan dangi na mahaifi da mahaifiya,amma a yau daya,cikin mintunan da basu gaza goma ba kanta yana shirin kwancewa ta zama 'yar qauye cikin gidan.
Ba iya wannan ba,ta lura akwai tarin doka da bin tsari daga dukkan ma'aikatan gidan,kula gami da takatsantsan da tsoron kaucewa qa'ida,tun daga mai gadi,zuwa wadda ta rakota qofar sassan hajiyar gidan,kawo wadda ta kawota wannan falon da take zaune a yanzun tana jiran isowar matar,don ta ganta ta kuma karbeta gami da sake mata bayanin aikinta cikin gidan.
Wayarta na hannunta a lokacin tana shaidawa afifa ta iso,afifan da tace sam ita ba zata iya rakota ta ganta a bigiren 'yar aiki ba,saidai duk da haka batayi fushi ba,tana maqale a online tana bibiyar dukka motsin bestie din tata.
Qarar takalmin da ya fara ratso falon yaja hankalinta,saita kashe data dinta,ta kuma ajjiye wayar tsakanin qafafunta,ta daga kai tana aje dubanta daga guraben da sautin tafiyar yake fitowa.
Guri guda idanunsu suka hadu nata dana hajiya qaramar. Daidaita kallonta ya sakeyi kan fuskar sãahar duk da bata kai ga qarasowa gurin ba,wani abu yana sauka a zuciyarta,tanason ta karanceta irin karatun kallon farko,tanata qoqarin daidaita zuciyarta da taji kamar ta tsaya guri daya,ta gaza wanzar mata da kowanne feeling akan sãahar din,ba kamar yadda takanji ba akan sauran dukka nannys din fadeela na baya da sukabar gidan.
Page 60
*H U G U M A*
*_TABARMAR ƘASHI_*💔
Page 60
Cikin takunta na qasaita da nuna isa ta qaraso,ta dauke filon dake saman kujerar dake fuskantar sãahar din ta zauna,tana maida filon saman cinyarta,bayan ta dora qafarta daya saman daya
"Sãahar ko?" Hajiya qaraman ta jefeta da tambayar sunanta kai tsaye,kai ta gyada mata cikin tabbatarwa gami da furta
"Eh nice,barka da yamma"
"Barka kadai" ta amsa mata tana qare mata kallo a fakaice,zuciyarta cike fal da mamaki irin sassanyan kyan da yarinyar ke dashi,babu alama ko digo dake nuna wahala ko buqata daga jikinta,asalima ko ita din sãahar din fatarta tafi tata nuna jin dadi da hutu,to amma ta wani bangaren tasan zata samu nutsuwa,zata samu sauqi itama,ilimi zallah ya nuna kansa tattare da sãahar din.
Gyara zamanta tayi tana sauke qafafun nata,har yanzu idanunta akan fuskar sãahar din,kyanta yana sake bata mamaki
"Nasan mrs sadeeqa ta gaya miki komai,so amma koda zata gaya mikin ba komai zata iyayi miki bayani ba kamar yadda ni zanyi miki.....da farko kina iya kirana da hajiya ko hajiya qarama ko mommy qarama,kusan nice shugabar gidan nan,kowa da kika gani ya kwana ya tashi cikin gidan nan qarqashin ikona yake,hatta dashi me gidan kansa da abinda ya mallaka ya kuma haifa......aikinki guda daya ne tal cikin gidan nan,kula da jikata tamkar ke kika haifeta,munason ta samu kulawa fiye da yadda zaki bawa kanki kulawa,saboda yanayin ciwonta,bamason kiyi nesa da ita,saidai idan tayi bacci ne, kuma koda kin koma naki dakin zakici gaba da dubata ne gudun faruwar wani abun,wankanta da tsaftarta yana wuyanki,abinda zataci kuma wannan ba dolenki bane" sai Tayi shuru tana maida numfashi. A nutse sãahar ta daga kai tana dubanta tare da nazarin kalamanta,wanda suke cakude da sautin izza a cikinsu
"Fadeela.....ita daya muke da ita,itace sanyin idaniyarmu,farincikinta shine namu, sabawa daya daga cikin ayyukankin nan suna iya zama silar rasa aikinki" ci gaba kawai sãahar tayi da nazarin mommy qarama tana kuma kallonta
"Kin fahimta?" A nutse kuma a hankali ta gyada mata kai
"Da kyau,gidan nan yana da tsari,bawai zama bane kamar na sauran gidaje da kika sani,abu na gaba kowa aikinsa ya sanya a gaba,ba ruwan wani da shiga sabgar wani,ban yarda da zama tsakanin ma'aikata ana hira ba,kowa yayi abinda ya kawoshi ya wuce mazauninsa" shuru ta sakeyi tana kallon yadda sãahar ta kame,ta kuma bata hankali tare da manyan fararen idanunta tana kallonta
"Magana ta qarshe" ta furta tana zama serious sosai
"Nasan kinsan kalar ciwon da yake damun shelelenmu,right?" Kai ta jinjina tana ci gaba da sauraronta
"Yauwa,akwai magunguna da takesha,so gaskiya banason yawan qwayoyin da yake yawan bata,saboda haka duk lokacin da ya dace tasha magani zan shaida miki,kota waya,ko na tako har zuwa sashen da kaina,ban yarda ba ko sau daya ki dauki magani ki bata ba tare da sanina ba" wanann maganar ita ta zowa sãahar din a hagunce,sai ta gyara zamanta itama,ta kuma dora qafarta daya saman daya ba tare da tasan tayi hakan bama
"Amma why not ki yiwa likitan magana,idan zai yiwu da kansa zai fada,zai kuma rage mata,idan wasu kuma za'a yi exchanging dasu duka zai fadi"
"Look!" Hajiya qarama ta fada tana fidda idanunta waje
"Ina cewa ko minti biyar banyi ba da gaya miki rule's na gidan nan,who are you da zaki shiga lamarin da bai shafeki ba daga zuwanki?,na gaya miki hakanne don na taimakeki,bijirewa hakan zai iya shiga list na dalilan rasa aikinki" mamaki ne ya kama sãahar,tadan yamutsa fuska kadan tana juya maganar a ranta,kaf cikin maganar bataga inda tayi wani lafazi da bai dace ba
"Ke ba kowa bace face nanny da zatayi aiki a biyata" zuciyarta da kwanyarta suka tuna mata matsayinta cikin gidan,sai ta zame qafafunta data dora saman na juna a hankali lokacin da taga hajiya qaraman na kallon yadda ta hade qafafun
"Am sorry,zan kiyaye in sha Allah"
"Kin samawa kanki lafiya" ta furta tana sake tsuke fuskarta,saida can qasan ranta tana cike da mamakin yarinyar,kwata kwata batayi kama da masu aiki ba,koda kuwa makaho ne ya shafa zaiji hakan,duk da sun nema well educated amma kuma wannan kamar ajinta ya d'ara wajen.
Waya ta dauka tayi kira na qasa da second goma sha biyar,cikin minti daya tak matar ta iso,daya daga cikin masu aikin gidan,wanda basai ka tambayi hakan ba,saboda uniform da take sanye dashi,ta rusuna cikin girmamawa
"Sabuwar nanny din uktie,a kaita sassansu,ki damqata a hannun baaba ramatu"
"An gama ranki ya dade" ta fada cikin rusunawa,luggage din sãahar din ta dauka tayi gaba,don dukka nanny din data kasance ta fadeela ce a gidan,tana samun wani respect da kyautatawa darajar fadeelan,wannan haka tsarin gidan yake.
Har takai qofa momy qarama na rakata da kallo,batasan me yasa yarinyar ke jan hankalinta har haka ba,yadda take takunta a nutse daya na bin daya kadai yana nuna mata kamar akwai wata extra qasaita a jinin yarinyar
"Sãahar" ta kirayi sunanta da dan kaushi kadan,dakatawa tayi sannan ta waiwayo tana dubanta
"Mrs sadeeqa nada matuqar kirki,tana kuma da darajar da zata baki dukkan wata kima da martabawa a gidan nan,ba tare da ko na miki screening ba na dauki aikin kula da 'YAR SO na baki,ki kula da kyau,kada kuma ki gota iyaka" har yanzu kalaman matar basu daina bata mamaki ba,sai ta saki wan siririn murmushi ta jinjina kai kawai,sannan ta juya a nutsenta tana barin falon,tabi bayan ma'aikaciyar.
Kamar ko yaushe katafaren ni'imtaccen falon nasu a tsaftace yake sannan killace,iskar na'urar sanyaya daki tana busawa ta kowacce kusurwa na falon tana cakuda da qamshin fresheners.
Sau biyu me aikin tana sallama kafin qofar glass ta falo na biyu ta bude,baaba ramatu ta fito cikin kamalarta da carbi a hannu,da alama tana azkar din yammaci ne
"Qaraso mana,ke da baquwa ce?" Tayi tambayar idanunta akan sãahar dake tsaye a baya
"Nanny din fadeela ce hajiya tace a rakota" juyawa baaba ramatu tayi tana duban sãahar,sai kuma ta sakar mata murmushi
"Maraba,sannu da zuwa,Allah yasa tana jin hausarmu" tayi maganar cikin tantamar sãahar din tasan zo na kasheka da hausa. Murmushi ne ya subucewa sãahar din,karon farko tun shigowarta cikin gidan,yadda dattijuwar tayi magana cike da barkwanci yana burgeta
"Ina yini?" Ta fada a nutse don kore shakku daga zuciyar baaba ramatu,a mamakance riqe da baki t juyo ga sãahar
"Ma sha Allah,lafiya alhamdulillah,sannu da zuwa"
"Yauwa sannu" ta maidawa baaba ramatu
"Shigar mata da kayan nata ciki,dazu dazu aka kammala kintsa dakin muje ko 'yata?" tayi maganar da sakakkiyar murya tana yi mata jagora ga tsararren hallway din da zai sadaka da dakunan baccinsu.
Daya daga cikin qofofin dake kulle baaba ramatu ta tura ta shiga tana cewa sãahar
"Bismillah" sai tabi bayanta,bakinta dauke da addu'ar shiga sabon guri ko zama a baqon guri. Daki ne me yalwa wanda yake dauke da qawatattun kayan gado 'yan asalin qasar turkey,komai na dakin kwantacciyar kalar yellow green ne me kyau da daukan hankali,kalolin dake qarawa idanu qarfin gani,dakin nada wani irin tsari me burgewa,bai cika girma ba,hakanan bai cika qanqanta ba.
"To ga dakinki nan,idan kina da buqatar wani abun kina iya magana a kawo miki,aikinki kawai ki kula da fadeela" baaba ramatu ta fada cikin murmushi. Murmushin itama tayi
"Bana buqatar komai,amma ina ita babyn?,inaga ita ya kamata na fara gani ko?" Qaramin murmushi ya sake sauka a fuskar baaba ramatu,haka kawai kallon farko taji sãahar tayi mata,fadeelan bata tana nanny irinta ba,yawancinsu tun daga hanyar shigowarsu gidan zuwa hanyar isowarsu dakin suke rudewa da kalle kalle da kuma santin tarin dukiyar dake jibge a gidan,hakanan duka cikinsu babu wadda ta taba tambayar a kaita gurin wadda tazo gidan aiki dominta,har sai baaba ramatun ta buqaci hakan
"Tana dakinta,tun dazun taqi fitowa rigima takeji,tunda babanta yayi tafiya dazun ya barta take fushi da kowa harda ni dana daukota daga waje,ko abinci taqi ta karba" baaba ramatu ta fadi tana dan dariya.
Kai sãahar ta girgiza tana dan murmushi
"Ayyah,tana kewarsa ne tun yanzu,muje na gani ko zata yarda ta fito" gaba baaba ramatu tayi tana dan yi mata hirar fadeelan,yadda halayyarta da dabi'unta suke. Qofar dakin dake facing ta sãahar din baba ramatun ta tura ta bude, tsararren dakinta cikin kalolin white cream ya bayyana,wani irin daki da yafi kama da dakin hamshaqiyar mace me aure,dakin dake aka sanya masa dukkan wani abu na buqata jin dadi da kayan qawa,wanda hakan bai sanya ya cika tarkace da yawa ba,sai wani irin kyau da tsari na musamman daya bayar,ga tasirin tsafta sosai a tare dashi,ko ina qal qal yana fidda qamshi me dadin gaske.
"Fadeela" baaba ramatu ta ambaci sunanta sanda suke shiga dakin. Tana nade cikin duvet,ko motsi batayi ba
"Ki tashi ga sabuwar me kula dake tazo ganinki" kafadarta ta maqale,ta kuma bubbuga qafafunta
"Bana sonta" idanu baaba ramatu ta zaro waje tana kallon sãahar cikin rashin jin dadin kalaman fadeela,sãahar din da siririyar muryar fadeelan ta sanyata dariya tare da qarin dariyar zallar quruciyar data fuskanta tattare da ita
"Kul na qarajin kince bakiso wani,bakya sonta?"
"Eh ta koma,saboda nima daddy ya tafi...." Ta fadi tana yaye duvet din da sauri,sai kuma ta tsaya cak tana rarraba kallonta akan fuskar sãahar dake jifanta da murmushi. A hankali ta zame duvet din duka daga fuskar tata tana ci gaba da kallon sãahar.
Waiwaya sãahar din tayi ta kallo baaba ramatu
"Baaba a kawo abincin nata"
"To shikenan" ta fadi tana juyawa ta fice daga dakin,cikin ranta tana jin cewa sãahar din zata bada fiye da abinda ake zata.
Bata taka ba taci gaba da kallon fadeela tana murmushi,har sai da yarinyar ta miqe ta zauna sosai da kanta,sannan ta sauke hannuwanta ta taka zuwa bakin gadon ta zauna daga gefanta
"Kiyi haquri" sãahar ta fada tana kallonta,tana iya ganin sanda ta waiwayo da sauri tana kallonta,saita sake mata murmushi
"Ummmm"
"Ba abinda kika yimin fa amma kike cewa nayi haquri"
"A'ah,kince bakya sona,na dauka nayi miki wani abun" kai ta girgiza da sauri,saita shagwabe mata
"Abby ne ya tafi ya barni,bayan yace bazai sake tafiya ba dani ba" siraran hannuwan yarinyar ta kamo tana kallonsu,babu wata qiba sam,kamar bata cin wani abu da zai gina mata jiki,duk da daular da take ciki,saidai kyau da gogewar fata kawai
"Abbynki ba zaiyi qarya ba,lallai uzurin da sai yayi tafiyar ne kuma ba tare da ke ba ya kamashi,but na tabbatar bazai dade sosai ba" murmushi ya qwacewa fadeela
"Shima haka yacemin"
"So....you must trust him" kai fadeela ta jinjina tana murmushi
"Wait.....yanzun kinci abinci?" Kai ta girgiza fuskarta na sake narkewa,ido sãahar ta zaro
"Eehhhh,bakyason abby ya dawo yaga kin zama qatuwa?,baby fadeela ta zama 'yar lukuta?" Dariya fadeelan ta saki,yadda sãahar din ke bubba hannayenta tana mata sign na qiba
"Inaso auntie,inaso"
"Good,chubby fadeela"
"Yes anty,not slimy,a chubby,a daina tsokanata a school"
"Aha,oya gate up" tayi furucin tana miqa mata hannunta,sai tayi hanzarin dora nata hannun,cikin kulawa sãahar ta riqeta sosai ta sauko da ita tana karantar yadda walwala da farinciki ya maye gurbin bacin rai data dawo ta sameta a ciki,wani irin nau'in tausayinta ya sake saukar mata,saita ajjiyeta saman lallausan carfet din dake gaban gadonta,itama ta zauna akai,ta fara diban abincin tana bata a baki.
"Kin iya feeding mutum like my abby" murmushi sãahar tayi
"Really?" Kai ta gyada mata
"Okay,nayi alqawarin zaifi na Abby din naki gaba kadan. Wani dariya me cike da nishadi fadeelan ta saki, sãahar ta tsaya kawai tana kallonta,an gaya mata tana da wuyar sabo sosai,nannys dinta suna jimawa kafin ta fara sakin jikin dasu,duk da ba wani dogon zango sukeyi ba a gidan,amma sai gashi ita lokaci guda ta sake sosai da ita.
uhmmm,ga sabuwar nanny a sheqar da batasan ta waye ba, za'a dore kuwa?,to lokaci shi zai nuna mana,asha hutun weekend lafiya,fatan alkhairi a gareku gaba daya,masu comments ina gani na gode sosai,gurin amsa comment dinne baya dannuwa,but am really appreciating
*HUGUMA*
0 comments:
Post a Comment