*23&24*
........washe gari misalin k'arfe 12:00 pm dubban jama'a suka shaida gagarumin d'aurin Auren *Abdallah mohd jibo & ummulkhairy rufa'i* Akan sadaki naira dubu d'ari biyar"d'aurin Auren da Aka d'aura Ababban masallacin Anguwar tudun wada"wanda bbu masaka tsinke sbd taruwar jama'a"Ango na gefen Amininsa yaci wankan shadda sky blue da Akayima Aiki da blue d'in zare! Hmm big man saima yafi kyau Akayanmu na hausawa"y'an jarida nata k'ok'arin yimasa tambayoyi yabasar"marok'a nata wasashi da masa kirari"saidai kawai yaji kamal yace"yabaka kyautar mashin ,yabaka kyautar dubu kaza"kusan Akan mutum 5 yana yin haka"can Abdallah ya ballah masa harara yana fad'in malam duk wanda kakoma yima kyauta da sunan injini kaine zaka biyasa wlh"dariya kamal yadin gayi"yayinda daddy bakinsa yak'i rufuwa sbd farin cikin d'aura Auren Abdallah"manyan mutane nata yimasa Allah yasa Alkhairi"Anyi pics shida Abokansa dasu daddy sannan suka nufi wajen reception"Acikin gidan daddy kuma umma balki ta shirya taron yini"wanda Aranta bak'in cikin Auren takeyi"Amma sbd tayi suna wajen daddy da danginsa saita nuna son Auren takeyi tanata hidima"daddy kuwa yabata manyan kud'ad'e sbd Aci Asha kowa yaji dad'i"saida ta wafci Abinda ta gadama sannan tayi Amfani da sauran kud'in...part d'in Amarya Aljannar duniya"dg bayan gidan Aka gina musu b'angaren su kuma harda get"fad'in tsaruwarsa b'ata bakine"dan yafi cikin gidan kyau da tsari da komai"daka shigo main parlour"gefen upstairs dining area ne"daga gefe kuma kitchen ne"sai gefen dama d'akunan bacci biyu ne kowane da toilet Aciki"parlourn ma Akwai toilet"sai up stairs Anan parlourn Abdallah da bed room d'insa yake"komai na cikin gidan coffee brown ne"gaba d'aya komai dg waje aka kawosa"d'aki guda ne kawai Aka shiryawa ummu dg gidansu"sai kayan kitchen"dama kuma Abdallah be kaiga zuba kayan kitchen d'in ba"saida Akayi jere shekaran jiya yagani"hakan yasa yafasa"gudan d'akin kuma kayan dubai ne had'add'u masu masifar tsada"Abin saidai wanda yagani"Ana gama reception Abdallah ya sallami friends nasa"turawan kuwa sai gobe zasu tafi"silalewa yayi kamal be koma sanin Inda yakeba.... sa'ada kuwa tana gidan Ammi itada leemart sbd Ammin itama taro takeyi"
Ab'angaren Amarya ummu kuwa tun wajen 11 am me make up datazo har nan gida ta tsantsara mata kwalliya ta musammun"bayan ta gama mata"ta shirya cikin shadda giznah light pink"An mata Aiki da blue d'in zare"sosai ta fito Amaryarta"uwar Amarya ma ta shirya cikin sabon leshi"gidan cike yake da bak'i y'an me duguri da kuma dangin mahaifin ummu"sai k'awayen ummu"tun wajen k'arfe 12 k'irjinta ke bugawa har su babah suka shigo da me photo"Aka kama bud'a hakan ya tabbatar ma da ummu cewa ta zama matar Abdallah"sosai gabanta ke fad'uwa tana jin kamar tayi kuka"haka dai ta daure Akayi musu photo da mutane"goggo luba ta dai tursasa kanta tayi wanka ta shirya Amma bata shiga photo ba"kuma bata shiga cikin sabgar komi"mama kuwa bata damu ba"dan tamafi buk'atar hakan"saidai komai da aka dafa na biki An d'iba An bata"dan mama bata jiran baba"kusan dubu d'ari biyar danginta suka had'a mata"babah kuwa da k'yar yabada dubu d'ari biyu sbd bedashi"sune Aka had'a da kud'in sadaki dana neman Aure Aketa hidimar komai"sai wajen k'arfe 3 ummu ta canza kaya zuwa leshi"kuma Alokacin kowa yasaka Anko"Amma banda goggo luba da zuri'arta"burunta Afara zancen kai Amarya sbd tabi taga gidan dan Akwai y'an binne binne da boka yabata tayi Agidan Amarya"wai Auren bazai jimaba za'a sakota kamar yadda Aka sako Asiya"hidima tayi domin komai Anyishi waja waja"sbd naira dubu d'ari biyar kamal yabama lawisa su sayi komai na buk'ata da zasu bama mutanansu"wanda Asali million guda yabada ummu tace"sunyi yawa dubu d'ari biyar yayi"wanda hakan ya tabbatar ma kamal batada son Abin duniya"Inda watace Amsa zatayi ko tace Ak'ara tunda tasan Abdallah nada kud'i.....
Bayan sallar magrib motocin d'aukar Amarya suka iso k'ofar gidan su lawisa sbd Acan da marece Akaje da ummu Aka shiryata cikin lifaya green"sai k'amshi takeyi"taci uban kuka kamar ranta zai fita"goggo murja da umman lawisa da yayar babanta sune rik'e da ita suka sakata cikin motar da Aka nuna itace Amarya zata shiga"bayan ta shiga suma suka shiga suka sakata tsakkiya"yayinda lawisa ta zauna gefen me zaman banza"kamal ya shigo driver sit ya gaida manyan yaja motar yana jin yanda ummu ke shashshekar kuka.... Aransa kuma yana tunanin ina big man yashige wayoyinsa duk Akashe? kuma ba'asan ina yajeba"da wannan tunanin suka iso katafaren gidan Alh mohd jibo"gaban ummu ya tsananta fad'uwa"duk Addu'ar data zo mata Abaki yi takeyi"sai bayan mutane sun fara shiga ciki sannan Aka fito da ita"saida Aka tabbatar tayi Addu'o in daya kamata sannan ta shiga da k'afar dama cikin gidan"kai tsaye babban parlourn gidan suka nufa"Anan ne masu marabar Amarya suka taru"duk dangin Ammi da dangin daddy ne"umma balki nabin dangin Ammi da kallon banza"sa'ada ma na zaune gefe tanata murnan zuwan ummu gidan"bayan y'an gaishe gaishe Aka bud'e taro da addu'a"kafin Abada Amanar ummu"umma balki ta tab'e baki sbd bata d'auka ba"su umma na lura da ita"yayinda dangin Ammi dana daddy sukace sun d'auka Ai y'arsu ce"dg haka Aka nufi sashen ummu da ita"wanda Anan cikin gidan daddy duk mutane nata k'auyanci"saida sukaga sashen ummu sannan sukayi k'auyanci me dalili"duk hange hangen goggo luba na taduba Inda zatayi binne binne bata ganiba"ko ina shafe da tiles"haraban gidan kuma bbu dama ko ina ga haske ga jama'a"haka dai ta hak'ura tana shan Alwashin zata canza shiri"dan bazata sab'uba ummu ta Auri me kud'i y'ay'an ta na tulke Agida harda bazawara....kowa son barka yakeyi da ganin wannan gida"masu k'auyanci nayi har zuwa isha'i sannan kowa ya watse"kamal dama yasanarwa lawisa karsu tafi itada sa'ada sai big man yadawo tukum"saita kirashi yamaida ita gida"bed sheet lawisa ta shimfid'a samqn bed d'in"sannan suka gyara parlourn itada sa'ada"kafin suyi sallar isha'i"dan ita ummu bata sallah har yanzun"tana zaune gefen gadon tayitagumi"tana tunanin wane irin kalar rashin mutunci mutumin nan zai mata yau??"ko kuwa k'ilan bazai kulataba?.... ringing d'in wayar lawisa yakatse mata tunani"taji gabanta yafad'i sadda lawisa ke d'aga wayar tana cewa gata nan"da kallo kawai tabita batayi mgn ba lawisa na murmushi tace"Amarya ga Angonki nan yadawo zan wuce gida"kai haba lausy?"to zaman me zanyi?"goben zakizo pls?"in sha Allah! to shikenan nagode sosai k'awata Allah yabar zumunci"karki damu bbu godiya tsakaninmu"baby taso muje yanzun yayanki zaizo"wai kina nufin itama tafiyar zatayi??"lawisa batayi mgn ba takama hannun sa'ada suka fita dg cikin bed room d'in dukda kuwa ummu na tsaidasu....Amain parlour suka sami uban gayyar tsaye da kamal da Alama mgn sukeyi yana yiwa kamal musu"sbd su duka fuskokinsu bbu walwala"yaci wankan sabbin k'ananun kaya"yayi kyau har yagaji"lawisa Aranta tace me Ak'idar turawa kana Anguncinma bazaka saka kayan Al'adar ba hausheba....lawisa kije gani nan zuwa"cewar kamal"dato ta Amsa ko kallon gefen da big man ke tsaye bata yiba"sbd itama bata son wannan d'aga kan dayakeyi shiyasa sai yazama dole take gaidashi"sa'ada ta kallesa tace"sweet heart saida safe ka kulamun da Anty nah zanzo da safen na gaidaku ko?"kansa kawai ya gyad'a mata suka fita suda lawisa"kamal yatab'e baki yana nuna ledar dake k'asa kan carpet yace"gashi nan idan kaga dama ka d'auka kabata"idan bazaka bataba kayi yadda kakeso"na rasa wace irin tsana kakeyiwa yarinyar nan??"yanzun yadace kaje wajen preety Ayau?"kaga kamal ! ta yaya zaka tasani gaba kanamun surutai wai?"kasan dai ba'a tursasani?"sbd haka ni bbu Abinda zan kai mata"idan kadamu taci shiga da kanka kabata mana"preety kuma itace taje Inda nake tasameni"yanzun haka na yanke shawaran ko shekara guda ne mukayi zan saketa na Auri preety"kamal ya girgiza kansa yana fad'in nifa Aganina ko watannima zaka iya yi saika saketa"dg haka yabud'e k'ofar ya fita be koma cewa komai ba"big man yatab'e baki ya d'auki ledar yana dubawa"kazace gashashshiya da fresh milk da ruwa faro masu sanyi"murmushin mugunta yasaki yana rik'e da ledar yafita"masu gadi yaje yabama kafin yadawo yarufe gidan"kai tsaye part nasa yanufa"kusan mintinansa 50 Aciki kafin ya sakko down stairs d'in yasha sabon wanka da milk d'in jallabiya Ajikinsa yanata zabga k'amshi"yau har wani fari ya k'ara"sai yayi tamkar black America"yanata yatsina fuska yana wannan shan k'amshi yanufi bed room d'in ummu da nan ne yake zaton tana ciki....ummu kuwa ganin har hour guda tacika be shigo ba"sai hankalinta yad'an kwanta tayi zaton bazai shigo ba"dama da wankan ta"doguwar rigar bacci ta tashi ta d'akko cikin kayanta na gida"bayan tasaka ta kashe wutar d'akin tayi addu'a ta kwanta"saidai tabar dum night kunne dake samqn bed side drower"wayarta Ahannunta tanata danne danne"gashi bbu key jikin k'ofar data rufe"tana wannan tunanin big man yaturo k'ofar da k'arfi yashigo batare daya rufe ba"dogayen tsuka yadinga ja yana kunnah hasken d'akin batare da yayi sallama ba....da hanzari ta tashi zaune hantar cikinta na kad'awa"ta jawo mayafi dake gefenta ta rufe jikinta dashi"k'afarsa guda me takalmi slifas ya Aza gefen gaban gadon yayi bala'in had'e rai yana binta da wani irin mugun kallo"sai yaji tamkar sannan ne ta maresa.....wani irin mugun shakkarsa da tsoronsa taji wanda bata tab'a jiba"Amma sai tayi jarumta ta dake bata nuna ba"K! sakko k'asa ki duk'a zanyi mgn"banganeba?"ta fad'a cikin tsiwa"tsaki yaja yanufo gefen bed d'in"da sauri ta sauka"dukda haka saida ya finciko hannunta guda ya turata samqn bed d'in da k'arfi"ta fad'a kanta yabugi gaban gadon"tasaki k'arar Azaba"cikin daka tsawa yace"bazaki sakko k'asan ba?"batayi mgn ba tana dafe da kanta ta sakko k'asan ta duk'a gabansa"hawaye masu zafi suka wanke mata fuskarta"k'amshin turarukan jikinta yadaki hancinsa"ya yatsina fuska yakoma nesa da ita sosai"ya d'auki kusan mintina 3 kafin cikin dakakkiyar muryarsa yace"inaso ki bude kunnuwanki kiji dokokina da sharud'd'ana"dan Atsarina bana maimaita mgn"kin d'auka bazan shigoba shine har kin kashe haske kinbi lafiyar gado kega Amarya ko??"sai kuma yayi shiru yakama wani irin murmushi yana kallonta"saida yayi me isarsa yaci gaba da cewa"inaso kisani ba hutu kikazo yiba Agida"sannan na yadda munyi wannan AUREN ne dake harda dalilin son na sai taki na koya miki yadda mace ke girmama namiji"idan naga kin saitu sai kiyi ta kanki"dokata ta farko bana son k'azanta"me Aiki guda na d'auka tana miki share share da wanke wanke"shima dan kar Ace kamata gidana bbu me Aiki"dukda bana tsoron ta mutane Amma ta hakanma za'a gane manufar Auren mu"shiyasa na d'auki me Aiki"Amma part d'ina wajibi ki gyara sbd me Aiki nina samu"duk ranar da kikayi kuskuran k'in gyarawa wlh saikin gane bakida wayo"sai abu na biyu girki"bana wasa da cikina"saidai inada manyan dokoki ga Abinda zanci"fatana Allah yasa kinma iya girkin"ko kuwa brain d'in bbu komai sai raina mutane da musu tsiwa?"to bari kiji sai kin wanke hannu sannan kifara Azamun girkin da zanci"idan girki beyi dad'i ba zan tsareki ki cinye ki kuma biyani kud'ina sbd bazanyi Asara ba"idan kinsan baki iyaba garama zuwa safe kisanar mun"sai Abu na gaba ban Amince da kikamun gayyar friends naki Agidana ba zan iya musu korar kare nagansu"sai Abu na gaba duk wani danginah dazaizo nan gidan kika nuna musu bakya sona sai kin sani"sai zancen fita bbu Abinda yadameni da rayuwarki kije Inda kika gadama saidai bbu maganar zuwa wajen Aiki da kamal yamun zancen"dan Abin kunyane kamata Ace matata na Aiki A wannan local skul d'in"idan kin fita dg gidan nan zakiyi Aikinki"Amma banda nan"sai Abu na gaba yimun sannu da zuwa da kamun duk Abinda zan buk'ata yazama dole Agareki"bbu zancen ki gaisheni daga tsaye ko mikamun abu dg tsaye"ki tabbatar gobe da safe kinzo kin gaidani kin gyaramun d'aki nah be fore 7 am"sannan kin had'amun ruwan wanka"kin fitomun da kayan sawa"sannan kin fito da takalmin dazai shiga da kayan kin goge kin fito mun da duk Abinda zan buk'ata"muddin kika karyamun doka wlh kiyi kuka da kanki da Abinda zan miki dan beda kyau"kuma ta wannan dokokin ne zakisan mace k'asa take da namiji"zancen marinah dakikayi mutane da yawa sun fassarashi da Abinda sukaga dama"saidai irin wannan hukuncin dana yanke miki shine daidai dake bazan marekiba"saidai Inda naso zan iya datse miki hannun da kika mareni dashi bbu Abinda kuma zai faru"Amma sbd ki kafa tarihin kin mari mutum kamata yasaka na barki.....iya nan yayi shiru"ummu kuwa da tsantsar mamaki take saurarensa tama kasa mgn"Azuciyarta tace"lallai tawa tasameni ni ummu"na tabka babban kuskure dana yadda na Auri mutumin nan.....kinji ko bakiji ba??"yafad'a Atsawace"kanta Ak'asa tace naji"yaja tsaki yafita dg cikin d'akin kamar zai tashi sama batare daya rufe k'ofar ba"ta kife kanta Ak'asa tana rera wani irin kuka me cin rai"tana jin tausayin kanta"tafi mintina 30 tana kuka"kafin ta tashi ta shige toilet ta wanke fuskarta ta kama ruwa sannan ta fito"rufe k'ofar tayi takashe hasken d'akin sannan tayi bissimilah ta hau samqn bed d'in ta kwanta tanata sakin Ajiyar zuciya"tajima tana tunani da juye juye sai wajen k'arfe 12 bacci barawo yasaceta......washe gari misalin k'arfe 6:45 am"Abdallah ya shigo cikin parlourn dawowarsa kenan dg masallaci yajima Acan sai yanzun yadawo"upstairs d'in ya haye yashige parlourn sa"bega Alamar An gyaraba hakama bed room"yaduba time bakwai saura"kasancewar dama nemanta da fitinah yakeyi kawai saiya sakko down stairs d'in"yanata d'aure fuska ya murd'a handle d'in k'ofar d'akin yatsaya dg bakin k'ofar yana hangota"tana kwance samqn bed dg tsakkiya"ta rufe jikinta da blanket sbd sanyin AC dana Asuba"murmushin mugunta yasaki yakoma parlourn sa"yabud'e k'aramin fridge ya d'akko ruwa masu masifar sanyi"tun kafin ya iso d'akin ya b'alle murfin Ahankali ya shigo cikin d'akin yanufi gefen bed d'in ya janye blanket d'in kad'an"Adaidai saitin wuyanta yafara zuba mata ruwan sanyin......A razane ummu ta farka tana kurma ihu"ita Azatonta wani abu ne"saidai kawai taga mutum duk'e gabanta fuskarsa Asake yana Ida juye mata ruwan"ta murgina gefe da sauri tana rawar sanyi"sauk'inta rigar bama mai fidda tsiraici bace saidai ta lafe Ajikinta...ta fashe da wani irin kukan tausayin kanta.... kad'an kika gani ,kuma kuka bakima faraba yarinya matuk'ar kina bujuremun"kinzo kinata sharar bacci bakije kinyi Aikin dana sakaki bako?"to wlh daga yau ki tabbatar kafin nadawo masallaci kin gama gyara part nawa"idan nazo na koma bacci na farka kizo ki tabbar dana shirya sanan ki koma gyara d'akin"zancen break fast nasan Ammi zata Aiko dashi"bance ki Amshi duk Abinda yafito dg hannun matar daddy ba"sai Abu na k'arshe kimayi gaggawar Aza girki zuwa 12 kin gama sbd friends nawa da sukazo daga k'asashen waje yau zasu tafi k'asarsu da k'arfe 2pm"so nan zasuzo ku gaisa"ki tabbatar kin musu snacks da dambun kaji"sannan kiyi musu friend rice sbd itace nake ganin zasu iya ci"banida matsala Agidana tun kafin zuwanki komai na buk'ata Akwai"fita zanyi muddin nadawo nasamu part d'ina ba yanda nakeso ba kema kinsan sauran.....iya abinda yafad'a kenan yanufi k'ofa"inaso kasani d'an Adam ba Abin wulakantawa bane"kuma bbu wanda baya yin kuskure Arayuwarsa"zalinci da cutarwa da tsoratarwar dakamun sbd ka fini k'arfi kaje kaida Allah"duk Abinda kace nayi zanyi muddin be taka shari'a ba"Amma bazan tab'a Aikata Abinda nasan ba dole bane koda zaka kasheni....yatsina fuska yayi batare daya juyo ya kalle taba yace "okay yanzun sauri nakeyi idan nadawo zanyi lokacinki"k'aramar marar kunya kawai"dg haka yasakai yafice"ita kuma ta share hawayenta ta sauka dg samqn bed d'in"sabon towel ta d'akko ta tsane ruwan ta shanyashi samqn k'ofar bayin"kafin ta gyara samqn bed d'in"sannan ta shige toilet tayi brush ta kama ruwa"saima sannan taduba taga jinin yakusa d'aukewa"dama 7days takeyi"fitowa tayi tasaka hijab iya gwiwa sannan ta fito main parlour"key d'in dake jikin k'ofar ta murza tana k'arema parlourn kallo tana mamakin irin dukiyar da aka kashe masa"saidai hakan be burge taba zaman lafiya da kwanciyar hankali yafi zama cikin daula ko wace irice indai bbu kwanciyar hankali"da wannan tunanin ta haye upstairs d'in"tun dg bed room d'in har parlourn bbu Abinda yayi na Azo Agani na datti kawai y'an kaude kaude ne zatayi"Amma yaketa kumfar bakin Azo Agyara"batare data damu da kayan more rayuwar dake shashen ba taci gaba da Aikinta cikin hanzari"saida ta gama da parlourn sannan ta dawo bed room d'in"tana gyara samqn bed ta lura da wasu Abubuwa cikin takarda da kwalba samqn bed side drower"saida ta gama gyara samqn bed d'in sannan tazo ta fara dubawa......zaro ido tayi tana fad'in innalillahi wa inna ilaihir raju'un! shaye shaye mutum nan yakeyi ne ko kuwa ina yasamu kayen shaye shaye ni ummu?? ta fad'a da mamaki"kafin taja tsaki ta nufi bath room ta zubar tayi ploshing nasu"tasaka takardan da kwalban cikin dustbin"bayan ta gama ta d'akko borner da turarukan wutar datazo dasu gidan ta turare masa bed room da parlourn sa"sannan taje ta k'ara gyara main parlour shima ta turare"sai wajen 8:30 tashiga wanka"bayan ta fito ta shirya cikin sabuwar gownt ta Atamfa super"batayi make up ba"powder kawai da kwalli ta shafa"Amma ba k'aramin kyau tayi ba"tana taje dogon gashinta taji knocking"fitowa tayi bant d'in na hannunta saita yafo d'an kwalin samqn kanta"taku d'aya idan tayi sai mazaunanta sun juya sbd d'inkin yakama mata jiki sosai"waye ne?"nice Anty"d'an murmushi tayi ta b'udema sa'ada k'ofar"ta shigo rik'e da basket Ahannunta ta rungume ummu tana fad'in oyoyo Anty nah"murmushi ummu tayi tace"baby kin tashi lafiya?"lafiya qlau"ta fad'a tana cikata"Ahankali tace"kinyi kyau sai k'amshi kikeyi kamar yaya"yanama ina?"yafita tun d'azun"to gashi inji umma balki"dukda dai nasan yaya becin Abinda yafito dg hannunta"haka nima bana ci"yanzun nike shiga kitchen na girka Abinda nakeso me d'an sauri"sbd yanzun yasallami kukunsa dake mana girki nadashi"karki damu dg yanzun saiki dinga cin Abinci Anan ko?"shi kuma wannan kije kibama masu gadi"Amma idan sun cinye su kawo kayan nan"idan na wanke sai Amaida mata"to Anty bara naje nakai musu Anjima wajen k'arfe 10 am zan dawo ko Akwai Aikin dazan tayaki"dato kawai ummu ta Amsa"sa'ada ta juya tafita"ita kuma ta rufe k'ofar ta zauna parlourn....sa'ada na bakin get motar Abdallah ta shigo cikin gidan"yana dg zaune a back sit ya hangota wajen masu gadi tsaye da basket zata basu"bayan ya fito dg cikin motar yasanarwa driver yakirata"tsaye yayi harta iso gefensa tana murmushi tace"sweet heart Anty ummu ta shirya tayi kyau sosai"da gaske?"Allah kuwa"miye kikeyi Acan?"dama umma balki tabani Abin break fast wai nakai muku"shine Anty tace"nakaiwa masu gadi"tab'e baki yayi yace"hakan shine daidai"dg yanzun takoma baki wani aybu ki kamana kice na hana karki sake ki karb'a"dato ta Amsa"yabud'e boot d'in motar ya d'akko basket d'in da Ammi ta shiryo musu break fast Aciki"sa'ada ta d'auka tana fad'in bara nakai maka yaya"dato ya Amsa bayan ya rufe boot d'in motar suka nufi part d'in ummu.....
wannan book d'in nakudine idan kina buk'atar siya serious normal grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK
Ki turo shaidar biyanki ta what's app number d'ina 08100084251
Idan kika karanta mun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba
❤🔥❤🔥 *AUREN YARJEJENIYA* ❤🔥❤🔥
*25&26*
........ sa'ada nata masa surutu har suka iso part d'in"yasaka key yabud'e k'ofar suka shigo cikin parlourn"ummu na zaune kan kujera harta d'aura d'an kwalin"tana waya da mama"tunda taji motsin za'a shigo tafara k'ok'arin yima mama sallama"batare data kallesuba ta k'ak'aro fara'ar dole ta Amsa sallamar sa'ada"big man ya zauna Agefenta"saida ta d'an matsa"sa'ada ta Ajiye basket d'in samqn center table tana fad'in Anty gashi nan inji Ammi"to mungude sosai baby"Amma ina zakije?"ta fad'a sbd ganin sa'ada d'in ta juya"zanje na shirya ne"to break fast d'infa?"saina dawo Anty"kinsan yaya yakoyamun k'in k'ari da wuri"ta fad'a tana k'ok'arin fita"sai sannan ummu tasaci kallonsa ya banko mata harara"ta tab'e baki tana k
0 comments:
Post a Comment