*45&46*
........ Abdallah na fita ummu taje tafara gyara d'akinsa"wanda tafi awa guda tana k'yalkyale ko ina na part d'in nasa"bayan ta idar ta d'auki wayar ta takira lawisa ta nufi kitchen tana wayar"sai dariya sukeyi itada Aminiyar tata tana sanar mata Abdallah yashigo hannu"ita kuma tana k'ara bata shawarwari"bayan sun idar da wayar ta aza fried rice with chicken"tana girkin sa'ada ta shigo"Atare suka gama lokacin Anata kiran sallar magrib"kasancewar ummu bata sallah saita shiga wanka"bayan ta fito ta shirya cikin k'ananun kaya riga da wondo farare k'al"ta fito suka zauna sukaci Abinci itada sa'ada"sai wajen isha'i sa'ada ta tafi cikin gida"ummu kuwa gaba d'aya hankalinta na wajen Abdallah"kallo takeyi Amma tunaninta da nutsuwarta basu wajen kallon"har takwas na dare ta gota Amma shiru"can ta d'auki wayar ta tana jin kamar ta kirashi taji lafiya?"Amma bataso yayi zaton tadamu dashi "tana wannan tunanin taji motsin yana saka key zai bud'e k'ofar"saida taji k'irjinta yabuga!"ta gyara zamanta tana maida hankalinta wajen TV"Ahankali ya shigo cikin parlourn yamaida k'ofar yarufe da key"cikin taushin muryanshi yyi sallama yana hango ummu zaune tana kallo"ya kalleta ya kalli TV d'in"yafahimci tanason kallon American firm"da wannan tunanin yazo ya zauna gefenta"kasancewar kan 3 seeter take zaune"beji dad'in yadda ta d'auke masa kantaba"saiya Ajiye lodijin hannunsa yana fad'in khairee ya gidan??"lafiya qlau sannu da zuwa"bazan Amsaba bayan nine nafara miki mgn"Amma yaya Abdallah shine kajima Aka barni ni kad'ai ko?"tak'are maganar kamar zatayi kuka"hak'uri zakiyi khairee"kinsan ban cika wuce 8 ban dawoba kuma nasanar miki tare da daddy zamu fita"ni kaina duk nagaji"Amma bazan koma yin dare hakaba kinjiko?"kanta ta gyad'a masa"ina Aminiyar taki?"ta tafi tun d'azun" kasa mana ido ko?"hmm! Ai naga sbd ita bbu Abinda bazaki iyaba khairee"hakane itama Awajenta"beyi mgn ba saiya zare takalmin k'afarsa ya gyara zamansa ya Aza kansa samqn cinyoyinta yana fad'in khairee yau harda tausa zakimun nagaji sosai"shiru tayi tak'i mgn"yakama hannunta guda ya sark'e da nashi yana fad'in wai fushin me kikeyi khairee?"bata kallesaba tashafa suman kansa me uban laushi Ahankali tace"katashi muje kaci Abinci mana"ke me maganar kin ci? naci nida baby"meyasa baku jirani ba?"dama tare mukecin Abinci? kaida sai 8 kake dinner kamar bature"ta k'are maganar tana murd'e masa kunne.....ninama fi wani baturen yarinya"yak'are maganar yana yana aza hannunsa samqn nata data murd'e masa kunne dashi tanata dariya"malama menayi zaki tasani gaba kina mun dariya da rabon na mayar miki da ita kuka yanzun nan"yafad'a yana tura yatsanta guda cikin bakinsa yaciza yadda baza taji zafi ba....ahhhhh ! da zafi ni baran yardaba saina rama"ta fad'a cikin shagwab'a tana duk'o kanta zata k'wace hannunta daya rik'e"hakan yabama nashanunta damar gugar goshin Abdallah da kansa"Adole yacika hannayen nata bbu shiri sbd yanayin daya tsintsi kansa Aciki"ita kuwa yana cika hannun ta gyara zamanta"shi kuma yatashi zaune yana bin k'irjinta da kallo"lura da Inda yake kallo yasaka taji kunya"batare data kallesaba tace"tashi muje kaci Abincin"to khairee ga tsarabar dana miki baki dubaba"nifa bana so"har cikin ransa yaji bbu dad'i"shima sai cewa yayi nima bazanci Abincin ba"shikenan Ai cikinka ne"dg haka ta mik'e tsaye yana fad'in ina zakije?"banza ta masa ta shige d'akinta ta murza key"har cikin ranta bataso Abinda ta masaba kawai dai tanayin hakan ne dan yasan mata suna suka tara"time ta duba 8:35 pm"hakan yasa ta hau online sai wajen 9 pm tayi shirin kwanciya bacci"saidai data rufe Idonta hangota kwance asaman jikin Abdallah takeyi"gaba d'aya sai taji tafison su kwanta tare..... Abdallah kuwa ransa yayi bala'in sosuwa da Abinda ummu ta masa"yana jin zai fita harkatanta kawai"dama ice cream ne da gashashshen naman rago me ruwa ruwa yasiyo mata da shawarma"zama yayi yaci Abinda zai iya ci yagoge bakinsa yaje ya kwashe Abincin data girka da Abinda yarage yafita yabayarwa masu gadi"sannan yadawo yarufe k'ofar ya Haye upstairs"tunda yatura k'ofar parlourn k'amshin turaruka wuta masu k'amshi suka daki hancinsa"ya lumshe idanuwansa yanufi bed room d'in"nanma k'amshin ne"yabi ko ina da kallo ta masa k'al"kayan jikinsa yacire yana kallon saman bed d'in"Atake yatuna baccinsu na d'azun da ummu"saidai har yanzun zafin Abinda ta masa yana sukar zuciyarsa"farin towel ya d'aura iya k'ugunsa yashiga bath room"da jallabiyoyinsa kala ukku da boxers kala 3 data wanke ya had'a ido"har cikin zuciyarsa yaji dad'i"komai ummu zata masa na kyautatawa yana jin dad'i bayadai nunawa"ko yadda take kulawa da sa'ada da Ammi ba k'aramin faranta ransa hakan keyiba Amma miskilin be tab'a nuna mata yaji dad'i ba"da ruwan d'umi yayi wankan sbd gajiya"bayan yafito ya shirya ya kwanta"saidai gaba d'aya tunanin moments nasu nayau ke yawo Acikin k'wanyarsa"gaba d'aya sai yaji yafi buk'atar da su kwanta tare da ita suyi baccinsu kamar d'azun"Abin mamaki kuma yaji mararsa ta d'aure yana jin wani irin feeling"lumshe idanuwansa yayi yana manna pillows saman k'irjinsa yana tuna ranar dayaga Albarkatun k'irjin ummu"da kuma yanda d'azun ta goga masa su gefen goshinsa da kansa....ji yayi tsikar jikinsa ta tashi"ya bud'e lumsassun idanuwansa yana girgiza kansa yana fad'in why??"can yaja tsaki yana mamakin wai yau shine dajin sha'awa?"bayan shidai yasan mafarki kawai yakeyi, shima bakoda yaushe ba"Amma yadai zauna yaji wai yana jin sha'awar y'a mace be tab'a jiba"yasha ganin turawa da pant da bra Amma bejin komai sai gashi kan ummu yafara ji.....daya gaji da juyi samqn bed d'in saiya tashi yasaka jallabiya ya sakko k'asan"saidai yana murd'a handle d'in k'ofar d'akinta yajita rufe"jikinsa Asanyaye ya koma saman yana tunanin sbd shi yasaka ta rufe k'ofar"ya fahimci har yanzun ummu bata sonsa ko kad'an"Awannan daren dg ummu har Abdallah duk cikin rashin walwala dajin dad'i sukayishi"washe gari daya fita sallah be jimaba yadawo ya kwanta a main parlour kan 3 seeter bacci me nauyi yayi Awon gaba da shi......misalin k'arfe 8:43 am"ummu ta fito parlourn cikin shirinta na doguwar rigar Atamfa bak'a me zanen jaa da fari "ta yane kanta da k'aramin veil ja"Abdallah dake kwance har yanzun a parlourn yana bacci ta kallah"Aranta tana mamakin meyasa bazaije d'akinsa ya kwantaba?"tun d'azun dataketa zarya dg sashensa zuwa kitchen da d'akin baccinta duk yana bacci"kodai bashida lafiya ne?"ta tambayi kanta tana k'ok'arin zama kan kujera sbd ko break fast bata yiba"tana zama wayarsa dake cikin Aljihu tafara ringing"motsin ringing d'in wayar yasaka Abdallah dake kwance bud'e idanuwansa"ummu dai kanta Ak'asa tana satar kallon gefen dayake"tashi zaune yayi yana Addu'ar tashi dg bacci yana tsaki daya kalli fuskar wayar"ummu kuwa Mik'ewa tsaye tayi da nufin taje tayi break fast"dan tayi Alk'awarin saiya mata mgn sannan zata kulashi.....tana wannan tunanin taji Amon muryarsa yana fad'in khairee! juyowa tayi suka had'a ido"saurin sunkuyar da kanta k'asa tayi"tana mamakin meyasa idanuwansa sukayi jajir"ga damuwa data fahimci yanada ita...zonan! iya Abinda yafad'a kenan Atak'aice yana kallon dreesing d'in jikinta"batayi mgn ba ta nufi Inda yake zaune ta duk'a gefen k'afafuwansa tana fad'in ina kwana?"meyasa bakimun mgn ba saida na kiraki?"kin kuwa san hukuncin macen data kwana mijinta na fushi da ita??"da mamaki ummu ta d'ago kanta ta kallesa tasaki murmushi me k'ayatarwa tana fad'in yaya Abdallah kenan! kana bani mamaki wlh"shin manta irin AUREN da mukayi kakeyi ne kome?"yana k'ok'arin mgn wayarsa takoma ringing"yaja tsaki Akaro na biyu yana d'aukar wayar"ko sallamar junuid be Amsaba yace"pls junuid bansan takura kasani ?ko fitarma banyiba ina gidama"dg d'ayan b'angaren junuid yace" Ai dama gamu nan bakin get sbd munje office baka nan akace kana gida"gani nan fitowa"kodai mu shigo ne?"ummu dake sauraren komai tayi saurin cewa ni wlh barasu shigomun gida ba"kujira zan fito"iya Abinda yafad'a kenan yana kashe wayar"yanzun fitar zakayi ko wanka bakayi ba?" ya zanyi dasu tunda sunzo?"bansan miye dalilin zuwan nasu ba"tashi muje na rakaka to"sunafa bakin get"shiru tayi ta mik'e tsaye zata bar wajen"yayi saurin ruk'o hannunta ta fad'o ajikinsa"miye haka yaya Abdallah?"nika cikani dan Allah"shareta yayi ya zaunar da ita Atsakkiyar cinyoyinsa yana fad'in yau kuma irin wannan dressing d'in Akayi?"Eh mana"haba ki canza kin fimun kyau da English wears ko dogayen riguna haka"kasa mgn ummu tayi tana dai saurarensa"kinji?"uhmm! bana son nayi mgn kiyi shiru"meyasa jiya kika tafi kika barni khairee?"bakai bane kace bazakaci Abincin ba"toke meyasa kikak'i Amsar tsarabata?"hmm ! sbd nasan rabuwa zamuyi kamar yadda kake so"d'aure fuska yayi bece komaiba ya janyeta dg jikinsa suka mik'e tsaye" yana rik'e da hannun ta suka fita dg cikin parlourn"junuid da tj na tsaye dg bakin get"ba k'aramin mamaki sukayi ba da suka gansu sun fito tare"ummu kuwa sbd ta nuna musu yanzun Abdallah sai Abinda take muradi yakeyi ,kuma taji meye dalilin zuwansu yasaka ta biyosa" kan resting chairs suka zauna"ummu ta aza kanta Agefen kafad'arsa "hannunta guda sark'e cikin nasa"cikin shagwab'a tace"nifa ko break fast banyiba"yanzun idan mun koma sai muyi tare ko?"batayi mgn ba sbd ta hango su tj sun doso Inda suke"sallama suka musu ummu dai batako kallesuba"saidai Abdallah ne ya Amsa yana danna waya"big man idan babu damuwa ko zata d'an bamu waje ne muyi mgn,ko kuwa muje sai zuwa Anjima? ?"d'aure fuska Abdallah yayi yana fad'in koma miye ku fad'amun a gabanta mana"dan idan nakoma ciki kafin nafito wani Aiki ne"d'an murmushin takaici ummu tayi"dan wata iriyar tsanarsu takeji Aranta"sbd tasan ba mutanan Arzik'i bane su"sosa k'eya tj yayi suna zama yana jin duk yadda zaiyi saiya raba wannan shegiyar yarinyar me kama da Aljannu da Abdallah"junuid kuwa Ahankali yace"dama dan Allah wani hannun jarine zamu k'afa muna buk'atar million 4 shine mukeso dan Allah ka Ara mana"d'an murmushi big man yayi wanda iyakacinsa fatar bakinsa"dama yayi zaton kud'i suke so"kuma ransa yabashi k'arya sukeyi"k'ilan y'an matan su na bariki zasuje suyima sharholiya"kuma sunsan baya basu rance saidai yabasu kyauta....yana wannan tunanin ummu ta katsesa da cewa"gaskiya yaya Abdallah niban Amince kabasu Aron irin wa'annan kud'in har haka ba"shi hannun jari idan za'a zuba mutane da yawa ke had'awa Ayi aga me za'a samu riba?"wannan wane irin jarine daza'a zuba har 4 millions Acikin sa??"kinga bewar Allah ina ruwanki Anan?"ke mukazo mukace ki bamu ne?"balle k.....you are very stupid! Abdallah ya katse junuid Afusace yana binsa da wani irin shegen kallo yace"ita matar tawa kake gayama mgn haka junuid?"ina ruwanka da ita?"yafad'a Aharzuk'e yana kama ummu suka mik'e tsaye"ta saka kuka"ya rungumeta Ajikinsa yana fad'in menene kike kuka?nidai bana son tarayyarka dasu.....tabbas big man ruwa baya tsami banza"wannan matar taka Asiri ne ta maka"cewar tj cikin wani yanayi suna mik'ewa tsaye"Abdallah beyi mgn yafara danna waya"hakan yatabbatar musu da cewa security zai kira amusu koran kare"da hanzari sukayi gaba"ummu ta b'oye dariyarta ranta fari k'ar"Abdallah kuwa tsaki yaja yana kama hannunta suka wuce ciki"Atare sukayi break fast"sannan ta rakashi yaje yayi wanka"yauma manyan kaya tasaka rigimar saiya saka...dg ita harshi idan suna tare suna zuba soyayya da bama juna kulawa zaka d'auka sun manta irin AUREN da sukayi ne"Aranar sai k'arfe 12 na rana Abdallah yafita....
Da yamma ummu na zaune kan kujera tana sanye da mini siket red da bak'ar t shirt me dogon hannu"ta d'aure gashinta da red d'in bant"tanata tunanin ina sa'ada taje koda safe bata shigo tayi break fast ba"kuma takira wayarta yafi sau 5 bata d'auka ba"tana cikin wannan damuwar Abdallah yashigo parlourn"sadeeq na biye dashi da ledoji Ahannunsa daya ruk'o masa"ummu ta Amsa sallamar su tana fad'in sannu da dawowa"yauwa my khairee"sadeeq ya Ajiye lodijin yana gaisheta yafita"Abdallah dake kallonta sai yaji dama be shigo da sadeeq ba yagantaba"sbd sosai ta masa kyau....yaya Abdallah dan Allah zanje cikin gida na duba baby nagani ko lafiya?"kaga yau Alhamis bbu islamiya kuma koda safe bata zoba na kirata shiru"ta k'are maganar kamar zatayi kuka tana mik'ewa tsaye"Abdallah dai yana tsaye yana kallon ta"yana tuna shimafa duk yau baiga baby ba"Ahankali yace"zo muje ki rakani nayi fitsari sai muje na rakaki ki dubata ko?"gaban ummu yafad'i tana tunanin shifa besan miye wani abu kunya ba"Amma Afili kuka tasaka masa itadai yabari taje ta duba yanzun"shikenan ya isa" jeki ki sako hijab d'inki"da gudu ta nufi d'akinta ta sako hijab har k'asa red me hannu"tana fitowa suka had'a ido da Abdallah dake tsaye ya jingina bayansa Ajikin bango "yazura hannunsa guda cikin Aljihun wondon shaddar dake jikinsa sky blue"ganin zata fita da gudu yasakasa saurin fad'in miye haka khairee?"so kikeyi ki fad'i ne?"kije Ahankali mana"dato ta Amsa ta fita"shi kuma saiya shige bed room d'in ta"Acikin toilet nata yayi buk'atar sa da hanzari yafito yarufe k'ofar parlourn ya nufi cikin gidan"sbd ransa yabashi umma balki zata iya yiwa ummu Abinda ta gadama marar dad'i...ummu kuwa da sallama ta shigo main parlour d'in"umma balki na zaune itada wata k'awarta suna mgn k'asa k'asa"sai mai Aiki dake jera dinner saman dining table"Amamakin ummu taga umma balki na jifarta da mugun kallo basu Amsa sallamar tata ba"sai mai Aikin ta Amsa mata"d'ukawa k'asa tayi tana fad'in umma ina wuninku??"daba'a wuniba da kin gammu tsohuwar munafukar Allah"ubanme yakawoki nan??"ummu batace komaiba ta mik'e tsaye ta nufi k'ofar d'akin sa'ada"ke wai dan ubanki bakiji ina miki mgn ba?"ubanme kike nema ne?"cewar umma balki afusace"sosai ran ummu yab'aci da irin zagin datake yi mata"tajuyo da nufin tayi mgn suka had'a ido da hafsat data fito dg cikin d'akin ta"ke banza kin isa uwata na miki mgn kimata banza! ta fad'a tana nufo Inda ummu take"cikin fushi ummu ta matso kamar zata wuce ta gefenta" ta d'auketa da wani gigitaccen mari tana fad'in ni kike kira da banza ban girmekiba??....ki k'ara mata wani marin nace khairee! cewar big man daya shigo cikin parlourn Agadarence"umma balki takama salati tana fad'in dama kaine katurota tazo ta gayamun mgn taci mutuncin y'ata?"hafsat kuwa kuka ta fashe dashi tana ja da baya sbd ganin Abdallah yana nufo Inda take cikin fushi"da sauri ummu ta fad'a jikinsa ta fashe da kuka itama"sbd tasan halinsa karyaje yayi Abinda daddy zaiyi fushi dashi"me Aikinsu dake tsaye da k'awar umma balki sai bada hak'uri sukeyi"Abdallah ya d'ago kansa ya kalli me Aikin sbd yana ganin girmanta yace"ina baby taje?"tana wajen hjy tun d'azun ta sanar mun dg boko zata wuce"Abdallah bece komaiba ya d'ago kan ummu yana share mata hawayenta da tafikan hannayensa"kafin yaja hannunta suka fita batare daya tanka umma balki dake b'ab'atun k'arya da sharri ba"suna fitowa ummu tace"yaya Abdallah ina jin tsoron kar matarcan ta had'aka da daddy fa? kamar bazaiyi mgn ba sai kuma ya girgiza mata kansa yana fad'in muje karki damu khairee"bata isa tayi Abinda Allah beyi ba"yafad'a yana rik'e da hannun ta suna tafiya"itadai bata koma mgn ba har suka iso sashen nasu"Abdallah yajata suka zauna kan kujera yana fad'in to kicire hijab d'in mana"batayi mgn ba ta cire kamar yadda ya buk'ata"shi kuwa wayarsa ya zaro yakira Ammi"tana d'auka yayi sallama yana fad'in Ammi baby na nan?"dg d'ayan b'angaren ta Amsa da Eh gata nan tanata Aikin nata wato shagwab'a"ga sadeeq yazo d'aukarta tak'i binsa"yarinyar nan bafa cikakken hankaline da itaba Ammi"ta tashi tazo nan bata sanar mana ba"duk khairee ta tashi hankalinta dataga bata gantaba duk yau"kuma ta kirata bata d'auka ba"wai dama bata sanar maka ba?"Allah ya kyauta ma Auta"Abdallah beyi mgn ba yakashe wayar"shine bazaka bani mu gaisa ba?"cewar ummu zata tashi"ya rik'e hannun ta guda yana fad'in Ai nasan kullum sai kunyi waya"kin daiji baby tana can zamu had'u da ita idan tadawo"dan Allah kayi hak'uri ka k'yaleta"ai dama goyon bayanta kikeyi ko?"yanzun tashi muje kayi lunch"bece komaiba yana rik'e da hannun ta suka wuce dining area...
Bayan kwana 2✍️
wannan book d'in nakudine idan kina buk'atar siya serious normal grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK
Ki turo shaidar biyanki ta what's app number d'ina 08100084251
Idan kika karanta mun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba
❤🔥❤🔥 *AUREN YARJEJENIYA* ❤🔥❤🔥
*47&48*
*Bayan kwana biyu*
kimanin kwana 2 kenan Abdallah na fama da matsalar ciwon mara da tsananin feeling d'in ummu"duk dare idan ya kwanta sai yaji inama Atare suke"office ko a gida bashida Aiki sai tunani"yayinda ummu keta baya dashi "shi kuma yana manne mata"sau dayawa tana masa Abubuwan dake sosa ransa"haka zaiyi fushinsa ya bama kansa hak'uri ya huce"ita kuwa ko Ajikinta da fushinsa"Ajiya friday sukaje shida ita gidan Ammi ta gaisheta"Amma bece su biya su gaida nata iyayen ba"tana zaton kodan sbd iyayenta na talakawa shiyasa be damu daya sansuba har yaje ya gaishesu ?"kimanin wata 5 kenan da Aurensu dashi Amma besan kowa nata ba"dukda ga yanayin yadda AUREN nasu yakasance Amma koma miye yaka mata Ace yasan wani nata"Ayinin ranar da wannan tunanin ummu ta wuni wanda Abin yamata ciwo sosai Aranta.....
Ayau yakama satday misalin k'arfe 6:11 pm"ummu na kitchen tsaye gaban gas cooker tana juyo Abinci Acikin warmer"bayan ta idar ta rufe"d'ago kan da zatayi hancinta yashak'o mata k'amshin turaren gwanin nata"saida taji k'irjinta yabuga"ta d'ago kanta da sauri suka had'a ido"yana tsaye da k'ananun kaya Ajikinsa"hannayensa na rungume ak'irjinsa yatsareta da mayun idanuwansa yana kallo kamar yaune yafara ganin ta"ummu kuwa suna had'a Ido dashi ta d'aure fuska sbd ganin irin kallon dayake binta dashi"shi kuwa d'an shafa kansa yayi yana d'age gira yace"madam yaya?"haba yaya Abdallah bbu ko sallama fisabilillahi ni har kabani tsoro ko?"ta k'are maganar cikin shagwab'a"dama can mecece ke inba matsoraciyar ba khairee?" bata kulashiba ta nufi wajen sink tana wanke hannunta"saidai kawai taji motsin takunsa Abayanta"ta juyo da sauri suka kusan cin karo da juna"tayi baya hanzari tana b'ata rai tace"kaje dan Allah kayi Alwalah ka tafi masjeed lokacin sallah yayi"ta k'are maganar tana yarfo masa ruwan hannunta Asaman kyakykyawar fuskarsa"yad'an saki guntun murmushi yana fad'in ke fin fara yin sallar ne?"girgiza kanta tayi tak'i mgn"hmm ! to jiya kika fara sallah nasan jinin ya d'auke"tsabar kunyar maganarsa kamar ta zura Aguje haka taji"yayinda shiko Ajikinsa"bata koma kulashiba tayi k'ok'arin tafiya ta gabansa ya ruk'o hannayenta tak'i kallonsa tana son k'wacewa"ya janyota jikinsa ya rungumeta yana fad'in meyasa kikemun haka khairee?"shiru tayi"ya zuro kansa gefen wuyanta ya fara sinsinar ta yana goga mata lallausan sajensa yana sakar mata hucin numfashinsa......sumar wucin gadi ummu tayi"gaba d'aya jikinta ya mutu murus"saidai tayi jarumtar son k'wacewa dg jikinsa"shi kuma ya matseta sosai"ita kanta yanayin da suke ciki yamata dad'i"kasancewar shekarunta sunkai label d'in da zata buk'aci namiji akusa da ita....ganin big man beda niyar cikata yasaka tayi lamo Ajikinsa"saida yasaki jikinsa sannan ta tureshi tayi wuf zata gudu"yakoma ruk'ota tana turjewa yajata jikin bango"ya ware mata hannayenta ya rik'esu da kyau"ita kuwa rufe Idonta tayi tana mamakin meyasa idanuwansa sukayi jajir??"binta yayi jikin bangon yana sinsinarta dg bisani ya had'e fuskarsa da tata yana son yayi kissing nata"tanata janyewa ga yarik'e hannayenta da gudan hannunsa"gudan hannun nasa kuma sai shafa mazaunanta yakeyi....dan Allah yaya Abdal....shiru tayi sbd nassarar cafkar bakinta da Abdallah yayi yana tsotsa tamkar zai cinyesa"sai juye juye takeyi yak'i barinta"har saida yayi nassarar kama harshenta yatsotse tas sannan yacikata"Aguje tabar cikin kitchen d'in"shi kuwa jingina bayansa Ajikin bango yayi ya rufe ido yana maida numfashi kamar wanda yayi wani Aiki"yayinda yadafe saitin zuciyarsa da gudan hannunsa" yafi mintina 10 Ahaka kafin dg bisani ya bud'e lumsassun idanuwansa yafita dg cikin kitchen d'in jikinsa bbu k'arfi ko kad'an"
0 comments:
Post a Comment