*35&36*
.......Da sauri ummu taja da baya tare da k'ank'ame jikinta gabanta na wani irin bugawa"gefen zuciyarta kuma wata iriyar kunyarsa ce na ganinta da yayi haka......big man kuwa jikinsa na jingine da bango"hannunsa guda cikin Aljihun wondonsa"gudan hannunsa kuma yana shafa kansa dashi"yayinda lip nasa na k'asa yaturashi cikin bakinsa yana tauna tamkar zai hudashi"kallon k'asan ido yake binta dashi tun daga fararen k'afafuwanta datayima jan lalle na biki har zuwa samqn fuskarta"saidai yafahimci tana jin tsoro ko kunyar ya dinga ganinta irin haka....kusan second 5 bbu wanda yayi mgn cikinsu"shi dama yadawo ne daga masjeed kuma yajisa normal sai Abinda ba'a rasaba shine daya shigo yaga be gantaba"dalilin da yazo nan dan yafad'a mata ta koma dafa masa irin shayin d'azun"yasamu tana waya kuma duk Abinda take fad'a yanaji"saidai miskilin yama kasa mgn"ummu kuwa da sauri ta shige bath room banko k'ofar ta murza key"Abdallah kuwa takalmin k'afarsa cover shoes yacire yaje ya haye samqn bed d'in ta ya kwanta yana kallon sillin d'in d'akin"hankalinsa kwance tamkar yana cikin d'akinsa...tsawon mintina 15 ummu ta fito dg cikin bath room d'in"saidai ta yafo wani towel d'in samqn kafad'arta da nufin idan ta fito ta tsane ruwan jikinta dashi"saidai turus tayi dataga mutum kwance kan bed d'in ta"tamkar ta koma cikin bath room d'in haka taji"dan ita Azatonta yama jima da fita"d'aure fuska tayi tana kauda kanta tace"kaji sauk'i da Alama shine zaka fara da jan mgn ko?"kallonta yayi yaga tayi tsaye"yatsareta da ido be furta komai ba"dakai fa nake yaya Abdallah"ni katashi kaje d'akinka zan shirya"kawai saidai ka dinga shigowa bbu ko neman izini fisabilillahi"na gyara maka bed d'inka ka tafi can mana....ta k'are maganar tana nufar gefen mirror"Abdallah yatashi zaune yana fad'in ank'i atafi d'in"dama me gida da gidansa Ana masa shamaki da wani wajen?"juyowa tayi ta kallesa dariya na sub'uce mata"har fararen jerarrun hakoranta suka bayyana"shidai Abdallah yana kallonta bbu yabo bbu fallasa saman fuskarsa"saida ta gama dariyarta sannan tace"malam kadena kallonah dan Allah"kai yanzun bakaji nauyin furta me gida ba?"ka manta Auren dakayi ne?"gaba d'aya saima ya rasa me zai mata na kare kansa"ita kuwa bata koma mgn ba tana jiran yafita tafara shiryawa"sakkowa yayi dg samqn bed d'in yafara tunkaro Inda take"Atsorace taja baya tana fad'in toni mena maka fisabilillahi?"dan Allah kajira mana"banza yamata yana cigaba da nufar Inda take"da sauri tayi k'ok'arin nufar k'ofa yasha gabanta yana tab'e baki yace"matsalata dake gaddama"sannan baki iya k'watar kanki wajena"sannan ga tsoro ga jan fad'a ko?"nidai dan Allah kaje zan shirya"okay fita Anguwar yafi miki lafiya ta mahinmanci?"to Amma bakaji sauk'i ba?"ta tambayesa tana ja da baya"bbu laifi da sauk'i"kona koma dafa maka shayin?"kansa ya gyad'a mata"dama na dafa kamar nasan zaka buk'ata"kaje kasha sai kayi lunch pls"menene kika girkamun"tana nufar gaban mirror tace"faten dankali ne sbd kana mura nayi maka"saidai na sakq bushashshen kifi naga kuma bakacika son kifi ba"wai kinfi k'arfin ki juyo kimun mgn shine zaki juyamun baya?"wlh zanzo na fisge towel d'in naga yanda zakiyi....dan girman Allah kayi hak'uri nidai kaje ka zauna ka huta"bazan jeba har Abincin bazan ciba"Azatonsa zata rarrashesa sai yaji tace"shikenan Ai"bece komaiba yasaka takalminsa yafita dg cikin d'akin yabuga k'ofar da k'arfi"ummu ta tab'e baki taci gaba da shirinta"wajen k'arfe 3 ta fito"tayi kyau cikin Ankon Atamfa lemon green me zanen bak'i da fari"siket d'in me tsaga dg baya yaka mata sosai"ta yafa mayafi samqn kafad'arta bak'i"hand bag da takalmi masu tsini duk bak'ak'e tasaka"tasha make up gwanin kyau tanata k'amshi"Abdallah na zaune samqn kujera yanata cin magani"bbu yanda ya iya yaci Abincin da shayin"ummu ta k'araso tana cafe key d'in motarta ta zauna gefensa yakoma had'e rai"ita dariya ma yabata dan yanzun ta saba da halayensa"sannu da hutawa y'allabai"harara ya banko mata yak'i mgn"nidai pls zanje na zuba mai a mota kuma banida...sai kuma tayi shiru"tab'e baki yayi cikin cool voice yace"maganar bata dameki ba shiyasa bazaki fad'a ba"yak'are maganar yana binta da kallon k'asan ido....batayi mgn ba ta mik'e tsaye da nufin kawai ta tafi samqn nafef"Abdallah yayi saurin finciko hannunta tajuyo kamar zata fad'i"ya zaunar da ita gab dashi"murya bbu Alamar wasa yace"fad'amun menene ?"nidai dan Allah kabarni natafi bbu komai fa"koma matsowa gab da ita yayi har jikinsu na gugar juna"still yana rik'e da hannun ta"yadubi idanuwanta tayi saurin yin k'asa da kanta tana son k'wace hannun ta daya rik'e"bazan cikakiba saikin fad'amun ko kuwa ki fasa zuwa Anguwar"dama zance maka ne banida kud'in zuba mai shine fa"kuma ATM d'ina yayi espire"hmm! tunda nake dake kin tab'a cemun kinason na siya miki Abu kaza?"kokin tab'a cemun kina son na baki kud'i?"duk bakya cewa sbd kina ganin kinfi k'arfin Amsar Abin hannun mak'iyinki ko?"shiru tayi tanata kiciniyar k'wace hannunta"yatab'e baki yace"kitashi kije d'akina cikin lokar gado ki d'akko ko nawa kike so?"nidai takalmin nan sun cika tsini kaje ka kamun man....sai kuma tayi shiru data tuna waye big man ta isama ta Aikesa?"idan barakije da kankiba ki bari"murmushi ummu tayi Aranta tace wlh sai kaje ta hanya me sauk'i"Afili kuwa kukan shagwab'a tasaka ta kwantar da kanta gefen kafad'arsa murya can k'asa tace"zanfa iya fad'uwa kan stairs d'in can pls yaya Abdallah kaje kaji?.....da farko haushin yadda tayi masa yaji Aransa"Amma kuma ajikinsa sai yaji kamarma karta dena mgn"yana wannan tunanin yaji ta janye kanta tana fad'in ka cikamun hannuna"bakyaso naje na d'akko miki?"inaso mana"beyi mgn ba saidai gaba d'aya yajishi wani iri"tashi tsaye yayi cikin nutsuwa ya nufi samqn"be jimaba ya sakko da kud'i masu yawa Ahannunsa"Amamakin ummu sai taga rafar y'an d'ari biyar guda hud'u ya Aza mata samqn cinyarta" yana fad'in gashi nan saiki k'yaleni da wata rigima"kallon kud'in tayi ta kuma kallesa yana k'ok'arin zama gefenta"Ahankali tace"yaya Abdallah duk kana nufin da wannan kud'in zan zuba man?"kanki akeji idan zaki d'auka kije to idan bakyaso ke kika sani"nifa wlh ko 5k kabani nagode sunyi yawa zan d'auki dubu 50 nagode Allah yak'ara bud'i"haka nan yaji ya tsintsi kansa dajin dad'in Addu'ar tata"saidai beyi mgn ba ya fisge hand bag nata yabud'e yasaka kud'in ciki"ido cikin ido ya kalleta yana fad'in idan Abdallah yayi kyauta ba'a mayar masa"ki tashi da sadeeq zaku fita azuba miki man"shiya dawo ke ki wuce yana bakin get"tsabar mamakin big man kasa mgn ummu tayi ta mik'e tsaye ta tafi ,shi kuma yabi bayanta da kallo harta b'acewa ganinsa.... Agefen motarta ta sami sadeeq tsaye yana jiranta"kamar yadda yasaba ya gaisheta da ladabi ta Amsa tana bud'e motar suka shiga.....duk Abinda yaka mata Ayi saida sadeeq yaga Anyi sannan yabar ummu ta wucewarta Anguwa"wanda duk wani motsinta da bugun zuciyarta Abdallah take tunani.......
misalin k'arfe 8:5 pm ummu ta turo k'ofar parlourn ta shigo da sallama"kasancewar saida ta tsaya ta bama Aminu 150k yaje yasiyo kayan Abinci yakaima baba injita sannan ta tafo gida"shiyasa har isha'i tayi mata waje"Abdallah na zaune kan kujera yunwa yakeji sbd ko dinner bata aza ba"yana jin sallamarta yamata banza"ta k'araso cikin parlourn tana fad'in yaya Abdallah ya jikin ?"bansaniba"sai yanzun kikaga damar dawowa ko?"wlh nad'an...bana son ji! yakatse mata mgn Atsawace"batare daya kalletaba"dan Allah kayi hak'uri"baran yiba"zancen fita kuma kingama"batace komaiba ta wuce cikin d'akinta"magrib da isha'i kawai tayi ta fito parlourn da hijab har k'asa d'inkin jalbab ajikinta"big man na zaune yana danne danne Awaya"kitchen ta shiga ta fara tunanin meye zata girka masa?...."shayin d'azun ta dafa masa sannan ta Aza indomie da k'wai"bayan ta zuba indomie d'in ta fito rik'e da cup d'in shayin Ahannunta"fuskarta bbu walwala sbd bataji dad'in disgin daya mata ba"gabansa ta duk'a ta Ajiye cup d'in saman center table tana fad'in kafara shan shayin kafin indomie d'in ta ida"banasha ! ki d'auki kayanki"shima indomie d'in bana ci"kije kiyi Abinda kika gadama"shiru tayi batace komaiba ta d'auki cup d'in shayin taje kitchen ta zubar"indomie d'in ta juyota cikin tray ta nufi d'akin ta"zama tayi ta kira sa'ada ta waya"ta sanar mata tazo suci Abinci"bbu jumawa ta shigo d'akin sukaci tare"saidai cikin zuciyarta ta damu da fushin da Abdallah keyi da ita"tana tunanin sbd takai dare ne yake fushi"bayan sun gama sa'ada ta fita da tray d'in takai kitchen tayiwa Abdallah sallama ta fita"shi kuwa gaba d'aya yarasa meyasa yakejin zafin fitar datayi takai dare?"sai tsaki yake ja jefi jefi"dg bisani ya tashi yakoma part nasa"kayan wanka yasaka yashige bath room"yafi mintina 20 sannan yafito ya shirya cikin guntun boxer ya kwanta"saidai yarage iskan fanka ,yakashe AC"kuma Alhamdllh yasami sauk'in murar bisa kulawar da ummu ta bashi yau"saidai kuma yana rufe ido zuciyarsa ta dinga hasko masa ita sadda take d'aure da towel da kuma jiya da dare daya ganta da kayan bacci"tsaki yaketa jaa"kamar zai huda harshensa"sbd haushin tunata dayakeji"sai wajen 11 pm bacci ya kwasheshi"washe gari da safe yaje masjeed koda ummu taje gyara d'akin be nan"har vests da jallaboyinsa guda 3 ta wanke masa da taga yajika su da klin a bath room"tana jera Abin break fast yashigo da milk d'in jallabiya Ajikinsa"yana ganinta ya had'e rai"da sauri ta duk'a ta gaishesa"bana so ki rik'e Abinki"mgn ta kikeji ne?"yafad'a cikin shan k'amshi yarab'a gefenta ya wuce"ummu ranta yab'aci matuk'a"tasha Alwashin fita harkansa"Abdallah kuwa daya shigo yaga ta gyara d'akin yaji sanyi Azuciyarsa"lokacin daya shiga bath room yaga ta wanke masa jallabiyoyinsa sai yaji dama d'azun be disgata ba"da wannan tunanin yayi wanka"saidai yayi niyar idan ta masa mgn yayi break fast zaiyi"lokacin daya gama shiryawa ya sakko down stairs d'in"bbu kowa a parlourn"fita yayi ya rufe k'ofar da key.....
kimanin kwana 2 kenan ummu na wasar b'uya da Abdallah"tun ranar data gaishesa be Amsa ba ta dena girki dashi"gyaran d'akin ma ta dena yi masa"idan tasan yana gidan bata zama parlourn"idan kuwa suna tare da sa'ada ya shigo ko kallo be ishetaba"ita kanta sa'ada tana mamakinsu wata ran"dg ita sai sa'ada da mai Aikinta take musu girki"Abdallah kuwa ba k'aramin b'aci ransa yayiba da Abinda take masa"musammun yasaba itake gyara masa d'aki dan beson k'azanta"data dena saidai yanzun shine ke Ajiye Abinda yakeyi ya gyara Abinsa"saidai yasha Alwashin shima fita harkanta"Aganinsa sai me idan ta fita harkansa?"idan yaga dama saiya saketa su rabu da juna ba wata tsiya bace awajensa??"dama mutum ne shi dabai cika yawon mgn ba"kuma beda fara'a"sai yanzun Abin yamasa yawa"yanzun ko sa'ada be fira da ita sai y'ar mgn d'aya biyu shikenan....Ayau kuma laraba ya shirya tafiya k'asar malesia sbd dama duk k'arshen shekara yana zuwa can k'asar Abinciki lafiyarsa"tun wajen k'arfe 10 na safe yagama shiryawarsa be mayi break fast ba"ya bari saiya shiga jirgi tukum yayi can"sakkowa yayi downstairs da troley nasa yana jiran sadeeq yazo yafita dashi yakai masa mota"ya shirya cikin suit farare k'al ga sabon Aski da gyaran fuskan da aka masa jiya"sai yayi kamar irin black America d'in nan"masha Allah ! yayi kyau bana wasa ba"duk macen dataga big man indai bbu igiya ukku kanta dole ta kyasa...lolx"bayan ya ajiye troley d'in bakin k'ofa" ya nufi gefen kujera ya zauna yana tunanin yasanarwa wannan matsiwaciyar tafiyar tasa ko kuwa??"yana wannan tunanin ummu ta fito dg cikin d'akin ta Azatonta bema gidan"tana sanye da wondo pencil bak'i da riga bak'a me dogon hannu"kanta bbu d'an kwali"kayan sunyi bala'in fito mata da suran jikinta"kuma sun haska faran fatar jikinta"tana hango Abdallah zuciyarta ta buga ta juya zata koma"cikin kakkausar muryanshi da bbu wasa Acikin ta yace" *khairee* zonan! k'in juyowa tayi bata kuma tafi ba"shi kuma yana kallonta.....motsin turo k'ofar da sadeeq yayi yasaka ta juyo da sauri"saidai bataso sadeeq ya ganta da irin wannan shigar ba"gaisheta yayi yaja troley d'in yafita"ita kuwa idanuwanta cike da k'wallah ta nufi wajen Abdallah dake zaune yayi bala'in had'e rai"k'asa take k'ok'arin d'ukawa tamkar Ammasa tilas yace"zoki ki zauna a nan"yanuna mata kusa dashi"ni bazan zoba yaya Abdallah?"kaida bbu ruwanka dani"kema ba shareni kikayi ba?"zakizo ki zauna muyi mgn ko kuwa sai ranki yab'aci?"Ai duk wani guje guje da kikeyi sbd ki b'oyemun duk ina lura dake"batayi mgn ba tazo gefensa ta zauna"ya d'auki kusan second 10 kafin yace"malesia zanje yau"jirgin k'arfe 12 zan hau"5days zanyi nadawo"ki kula da baby da gidan"iya Abinda yafad'a kenan"yana zaro kud'i dg cikin wata leda dake hannunsa rafar y'an 1k guda 2 yamik'a mata yana fad'in gashi ki rik'e idan kunada buk'atar wani abu"k'in Amsar kud'in tayi"saima hararar kud'in da hannunsa tayi"duk yana lura da ita"ganin tana b'ata masa lokaci yasaka afusace yace"gashinan inkin gadama ki d'auka"da rabon kafin natafi sai nasaki kuka"yafad'a yana jan tsaki"ummu kuwa bata koma mgn ba"shi kuma ya ajiye mata kud'in samqn center table"Ahaka sa'ada ta shigo parlourn"dama tasan da tafiyar"kallonsu tayi tace"black and white"yaya kayi shigar fararen kaya ita kuma Anty ummu bak'ak'e"Abdallah beyi mgn ba yana danna waya"ummu kuwa mik'ewa tsaye tayi ta nufi d'akinta"da gayya ta dinga juya mazaunanta"abin mamaki Abdallah kuma idanuwansa na kanta harta shige cikin d'aki"saidai yaji haushin da bata yimasa fatan Alkhairi ba"saiya mik'e tsaye suka jera shida sa'ada ta masa rakkiya har bakin get"itama saida yamata warning ta kula da kanta"kuma ta dinga taya ummu kwana"sannan yabata dubu 50 yashige mota"tanata d'aga masa hannu har driver yaja motar suka fita..... sa'ada kuwa dukda tana yarinya sai taga ummu be kamata Ace mijinta zai tafi har wata k'asa batayi masa rakkiya ba"da wannan tunanin ta iso shashensu ummu d'in"tana shigowa tayi cin karo da kud'in da Abdallah yabama ummu"d'aukar kud'in tayi ta wuce bed room d'in ummu dasu Ahannunta"tana mamakin meyasa tabar kud'i nan bayan k'ofar rufe take ba'a rufe da key ba?.....✍️
wannan book d'in nakudine idan kina buk'atar siya serious normal grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK
Ki turo shaidar biyanki ta what's app number d'ina 08100084251
Idan kika karanta mun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba
❤🔥❤🔥 *AUREN YARJEJENIYA* ❤🔥❤🔥
*37&38*
........da sallama sa'ada ta shigo cikin d'akin tana fad'in Anty ga kud'inki da kika bari a parlour"kuma parlourn Abud'e bakisan wanda zai shigo ba ke kina cikin d'aki"ta k'are maganar tana aza kud'in samqn mirror"yayinda ummu dake kwance samqn bed ruf da ciki batayi mgn ba"Asalima tunda ta shigo d'akin kukan data rik'e d'azun takamayi"tana tunanin Ashe yauda ran kanta takeyi data fara zaton big man yafara sonta"sbd idan yadamu da ita ko yaya zaice ta kula da kanta"Amma wai ta kula da baby da gidan"be damu da ita da rayuwarta ba"sbd game son kud'i shine zai bata kud'i yatafi?"to ita bazata tab'a ko sisi ba"zata mayar masa da kudinsa idan yadawo....tana wannan tunanin sa'ada ta shigo"cikin dubara ta goge hawayenta Acikin pillow d'in ta d'ago kanta tana kallon sa'ada tace"nama manta na barsu can kai nane ke wani irin ciwo"subahanallahi! kinsha magani Anty? Eh nasha"yauwa Anty wlh inada wata matsala"tun jiya nake ta ciwon mara"yau da safe da zanyi fitsari naga jini A gabana"to saina tuna islamiya Ance mace tana yin jinin al'ada"kuma naga yanzun ban Ida cika 14yrs ba"kamar da d'azun nasanarwa yaya saidai na fasa"kuma Ammi na kirata da safen nan bata d'auka ba"tashi zaune ummu tayi tace"baby zoki zauna nan muyi mgn"bbu musu sa'ada tazo ta zauna gefen bed d'in...tiryan tiryan ummu tayi mata bayanin jinin al'ada"da nuna mata har y'ar 12 yrs ma zata iya farawa ba dole sai ka kai 15 yrs ko16yrs ba"dg k'arshe taje ta d'akko pad da pant d'inta ta nuna mata yanda zatayi idan zata saka pad"sosai sa'ada taji kunya"ummu tabata pad leda guda tace"kije ki Ajiye kina d'auka kina sakawa duk bayan awa 3"ki tabbar kin gyara jikinki kin shafa turaruka"sannan karki sanarwa kowa"Indan ya d'auke kimun mgn zan koya miki wankan"Ai na iya Anty sbd ana koya mana A islamiya"to fad'amun yadda Akeyi"cewar ummu"Akunyace tayiwa ummu bayani"gyaran data mata kad'an ne"ta kuma sanar mata Abubuwa guda ukku da idan tagani period d'in ya d'auke"sannan ta tsoratar da ita data nisanci kowane namiji daba muharraminta ba"sbd yanzun ta tashi dg sahun yarinya"duk bayanin daya kamata uwa ta gari tayiwa y'arta idan ta fahimci ta balaga to irin shine ummu tayiwa sa'ada"kuma Alhmdllh ta fahimci komai"ta kuma godema Allah daya bama yayanta mace ta k'warai meson danginsa"Amsar pad d'in tayi saidai ta kasa tafiya"kije mana baby"cewar ummu"kiyi hak'uri da Abinda zan fad'a Anty"meyasa bakiyima yaya rakkiya bakin get ba dazai tafi?"na rasa meyasa wani lokacin saina ganku kamar ba masoya ba"kuma nasan laifin yaya ne Anty"hmm! sa'ada kenan"dani da yayanki ki kallemu ki barmu kawai"shekarunki basukai na in sanar miki wani da abu daya shafemu ba"kawai kimana Addu'a kinjiko?"sannan karki sake koda wasa kiyiwa Ammi zancen mu"dato sa'ada ta Amsa ta fita dg cikin d'akin......tunda big man yatafi sai sa'ada da sadeeq da leemart suka zama y'an gidan ummu"gefe guda kuma ummu na waya da lawisa tana bata shawarwarin yadda zata janye hankalin Abdallah"yanzun haka ummun so takeyi yadawo ta lallab'a shi taje ta gaido Ammi sbd bata tab'a zuwa gidan Ammi ba tunda ta Auresa"sa'ada kuwa Anata period bata b'oyema Ammi komai ba dangane da Abinda ummu ta koya mata"Aranar Ammi ta kira ummu tana mata godiya da yanda ta kula da sa'ada da tarbiyanta...shi kansa Abdallah d'in saida ta kirashi ta masa warning Akan yak'ara rik'e ummu da daraja sbd irin ummu ake kira mace ta gari"takuma sanar masa yanda ummu ke kula da tarbiyyar sa'ada"sbd ko yaya ta tambayeta abu zatace Anty ta koya mata kaza da kaza"dato kawai ya Amsa mata Aranar...
Ayau talata misalin k'arfe 11 na safe"Abdallah ne zaune Awani wajen cin Abinci"ya wanku cikin k'ananun kaya"yayi shiru yana danna waya be tab'a duk Abinda Aka Ajiyesa masa ba"yau kwanansa ukku kenan da zuwa malesia"kuma Ayau yagama duk Abinda yakawoshi k'asar"a lissafinsa yau kwananshi biyar rabonsa dayaci girkin ummu"dan tunda yazo nan saidai yasha tea sai snacks da lemo"daya fara cin Abinci zaiji babu dad'i"sai zuciyarsa ta dinga bujuro masa da son cin girkinta"ba k'aramin haushin kansa yakejiba idan yaji hakan"tun yana basarwa yana tursasa kansa harya dena"shigar kayan datayi Aranar dazai tafi malesia yakasa barin zuciyarsa"yanzun haka break fast ne yazo yayi Amma yakasa, yayi shiru"yana tuna maganganun da Ammi ta kirashi jiya da yamma tana masa game da ummu"harda gargad'in idan yayi gigin data sub'uce masa bazai tab'a samun kamar taba"shi kansa shaidane akan yadda ummu ta damu da baby da yadda take koyar da ita tarbiyya me kyau"abu kad'an yaji tace"yaya Anty ummu tacemun kaza bbu kyau ko be kamata ba"sannan yanzun ya fahimci shak'uwar da sukayi da sa'ada yasaka sa'adan rage shak'uwa dashi... Ajiyar zuciya yasaki kawai sai yatsintsi kansa da jin fad'uwar gaba"kawai sai yaji Ayau zai koma gida Nigeria"dan ransa yabashi kamar bbu lafiya"gashi dama yau wajen k'arfe 8 am yakira sa'ada bata d'auka ba"daddy da Ammi kawai yasamu ta waya sai kamal"dukda yana fushi da ummu yaji bbu dad'i dabata kirashi taji yana lafiya ba....wata zuciyar tace kaine yaka mata ka kirata kaji suna lafiya"Amatsayinka na wanda ya Ajiyeta"yaja tsaki yana tuna irin Auren da sukayi"Abincin dabai ciba kenan"yabar wajen yatari taxsi yatafi masaukinsa yafara tattara inasa inasa yafara shiri"sai bayan sallar Azahar wajen k'arfe 2 yahau jirgi"sai wajen k'arfe 5 na yamma suka iso Nigeria"kasancewar tun yana cikin jirgi yakira kamal yazo ya d'aukesa"Abin ban haushi shine kamal d'in yatafo da leemart"saida big man yazo yabud'e gefen me zaman banza yaganta"doguwar tsuka yaja ya maida k'ofar ya rufe da k'arfi yana bin kamal dake tsaye da wani irin mugun kallo yace"mlm bani troley d'ina"akanme zakazo da yarinyar nan?"shopping zamuje ka k
0 comments:
Post a Comment