Gaba ɗaya sansanin sojojin cike yake, da manya da ƙana nan sojoji. (Part of Nigerian Armed forces headquarters Abuja, Motto (s) victory is from God Alone!".
Gaba ɗaya sojojin dake cikin Headquarter ɗin, basu damu da ruwan dake sauka kamar da bakin ƙwarya ba, wasu na tsaye, wasu na zaune wasu kuma suna abinda ya shafe su, wasu kuma suna in da babu ruwan suna shan Cigarettes (sigari).
Tun yana tafiya da sauri har ya fara daidaita tafiyarsa ,wanda daman hakan al'adar sa ce, duk inda ya gilma cikin Headquarter ɗin hannu ake sara masa zuwa sama, alama dai shi ɗin Babban mutum ne, matsayi mai girma gareshi a cikin sojojin.
Wani office ya nufa cike da nutsuwa, yana zuwa aka bashi hanya ya shige, yana shiga office ɗin ya ƙame!.. tare da ɗaga hannunsa sama alamar girmamawa da masu ɗamara kewa junansu. Sojan da yake zaune sanye da kaaki, yayi Murmushi cikin sakin fuska yace
"Have a seat.." yai Maganar yana nuna masa kujera.
Kamar ba zai zauna ba, se kuma ya zauna saman Kujera. General Ibrahim A.M ya kalli matashin saurayin dake gabansa kafin yace "Munyi magana da Chief of Army staff, akan Operation da za'a fita, aiki ne mai wahala kuma bama son, Kidnappers ɗin su samu information na aikin nan, dan opretion ne me hatsarin gaske, yana da kyau ku kula, bamu da tabbaci kowa zai dawo da rai acikin ku, dan kun san komai dai"
Matashin dai kansa yake a ƙasa, yana sauraren General babu alamar zai magana, ya tattara dukkan nutsuwarsa yana sauraren shugaban nasa.
General Ibrahim ya buɗe wani file yana dubawa kafin ya kalli saurayin yace
"Hope you are ready for it, and kayi sallama da iyalanka?" .
Sai a lokacin Matashin saurayin ya ɗaga idanunsa wanda sukai ja sosai ya kalli General Ibrahim, kallon da yake masa yasa General Ibrahim faɗin "Oh, I forgot you just came back from Zamfara yesterday"
Matashin dai bai ce komai ba, da Idanu kawai yake bin General.
General Ibrahim yace "Zaka iya tafiya, jirgi na jiranku a airport, and airforce zasu rigaku zuwa ku kula da kyau akan dukkanin bayanan da zasu baku, da kuma umarnin da zaku samu daga garemu"
Matashin saurayin ya miƙe tsaye yace "ok sir" tare da sake sara masa, sannan ya juya, yana tafiya a hankali har ya fice daga cikin office ɗin General Ibrahim.
Cikin nutsuwa General Ibrahim ya ɗauki Wayarsa tare da danna wasu lambobi, babu jimawa aka ɗauki wayar daya kira, ƙasa ya yi da Murya yace
"Akwai kyakykyawan labari" daga cikin wayar wata shaƙaƙƙiyar murya ta bayyana akace "Mene labarin?"
General Ibrahim ya ce "Chief of Army staff, ya bada umarni ga Sojojin da suke Headquarter na nan Abuja zuwa Naija state, kai tsaye kuma cikin Dajin Zugurma in da kuke tsare da yaran nan, kuma a wannan karon sun samu cikakken ikon yin harbi, umarni ne daga NAC. _Nigerian Army council_"
Mutumin da General Ibrahim ya kira ya yi dariya kafin ya ce. "Ganganci haihuwa da damuna, a tunaninsu zasu Iya ƙwace ƴan matan da mukai kidnapping ne? Bayan gwamnati ta hanamu abinda muka buƙata?"
General Ibrahim yace "Na kira dai dan in sanar maka da zuwan su, a Kowane lokaci sojojin sama zasu tsinkayi dajin, nine zan tsara komai na Operation ɗin tare da jami'anmu na nan Naija state, zan sanar maka da duk wani arrangement na yaƙin, kaga kuna da damar da zaku samu galaba a kansu, dan haka se ku shirya zuwansu"
Mutumin ya yi dariya yace "Daman ance da ɗan gari akanci gari, mune mutanan banza, kai kuma maci amanar ƙasa"
General Ibrahim ya yi Murmushi yace "To Rayuwar sai da haka, in ba haka ba a banza za ka gama aiki Kai retire amma na abinci ya gagareka, ko a kashe ka a banza gurin kare ƙasar da ta gaza biyawa masu bata tsaro buƙatunsu, dan haka zan tura maka account number, ka bani share ɗina saboda na samu labarin wasu daga iyayen yaran sun baku kuɗi akan ku sakar musu yaransu"
Mutumin yace "Zanci kaza kazanka, a gidan uwar wa zanga pos ko Networkina cikin tsakiyar jeji?"
Ibrahim yace "Haka ne, ka shirya min kuɗina zan san yadda zan in karɓa, dan Ina da buƙatarsu" yana faɗin hakan ya kashe Wayarsa, yana jin akan kuɗi babu abinda ba zai ba.
Tabbas da ɗan gari ake cin gari.
Matashin na fitowa daga cikin office ɗin General ya nufi wani waje domin ɗakko jakarsa, tsaye ya yi ganin wata budurwa sanye da kayan sojoji ta nufu inda yake, hakan yasa ya ƙara haɗe ransa sosai. Budurwar mai suna Salima tace
"Haba Captain at least yau kayi min Murmushi, saboda kai nabar Maiduguri nazo Abuja" Wanda aka kira da Captain ɗin, ya kalli Salima se kuma ya ɗauke kansa, Salima ta haɗe rai tace
"Ban san me nayi maka ba, sama da shekaru biyar nake bibiyar ka, tun kafin kayi Aure" Captain ya gyara tsaiwa cikin tsare gira, murya a kaushashe yace "Bana harka da mutunan banza, ba zan mu'amala da karuwa kazar kowa ba" Yawo mai ɗaci Salima ta haɗiye tace "Yanzu har akwai mutumin kirki a cikin sojoji? Gashi nan kullum tara mata kuke, kuma mu matan dan mun nemi maza sai ya zama iftila'i, nifa a yau kace kana so na, zan zama iya taka kai ɗaya ban damu da matan da zakai harka dasu ba, indai zaka biya min tawa buƙatar"
tsaki Captain yaja tare da ratsa wa ta gefenta ya shige.. duk inda ya gilma sai yaga mace da namiji manne da juna tare da sheƙe a yarsu, ko kunya babu..
Sanarwa aka fara yi, wanda ya Sanya Captain ɗaukan jakarsa, ya nufi filin wajan, Salima taso hadda ita za'ai posting zuwa Naija state.
Farar safiya ce, A ranar Asabar wanda yayi daidai ga 25 ga watan Mayu, shekara ta dubu biyu da goma sha ɗaya. Jirgin Sojoji ne (Helicopter). Yake shawagi a saman dajin Zugurma na jihar Naija state. Sosai jirgin yake zaga dajin ta sama, sautinsa ya cika ko ina a dajin, ya dinga bada wata irin amsa kuwwa.
Ƙarfe 12 daidai, jirgin su Captain na sojoji ya sauka a filin tashi da saukar jirage na Niger state, cikin ƙanƙanin lokaci suka kammala duk wani shiri da za suyi, suka nufi cikin dajin.
Tafe suke a cikin manyan motocin yaƙi, ciki har da egwa yayin da wasu suke tafe a ƙasa, suna tafe suna 'yan iface ifacensu na sojoji, kafin samu umarnin cewar su tsaya su yada zango a wani guri, kasancewar sunyi tafiya me nisa, ba tare da jin wani ƙwaƙwaran motsi a dajin ba.
Daga cikin ɗaya daga cikin motocin, Wani matashi ne zaune, a kujerar mazaunin direba, Zame abin kansa yayi a hankali, yana fitowa daga cikin motar, Idanunsa akan wani matashi wanda yake gyara zaman bindigar sa, cikin rashin ko in kula na sojoji ya nemi waje ya zauna. Musulman cikin su na ƙoƙarin yin alwala suyi salla, wasu suna cin Abinci yayin da wasu suka keɓe suna shan sigari.
Captain Denial ya buɗe jajayen idanunsa akan wani soja yace "Ka gama naka aikin, tun da ka kawo mu cikin wannan jejin" ya faɗa cikin harshen turanci. ya shafa kansa yace
"War is not mine"
Captain Denial ya yi Murmushi yace "You go see" ma'ana zaka gani!.
Duk sun sauka daga motar, se wani soja wanda tun da aka sauka cikin dajin bai ɗago kansa ba, balle yayi magana. Daniel ya kalleshi kafin yace
"Captain Khamal" wanda aka kira da Captain Khamal ɗin, ya ɗago kansa a hankali, Baƙi ne shi sosai, irin baƙin nan mai kyau da kuma ɗaukan Idanu, ( _He's dark-skinned yet handsome_ ).
Kana ganinsa kasan bashi da son wasa, zuciyarsa a tsaye take! Tsayyen mutum akan ra'ayinsa, fuskarsa nan tasa a ɗaure take koda yaushe. (But Friendly to his family).
"Akwai matsala ne?" Captain ya Girgiza kansa, yana ƙoƙarin sanya rigarsa ta uniform ɗin soja.
Ɗaya sojan ya nisa yace "Wannan yaƙi ne mai hatsari sosai, idan a kai nasara zaka iya samun matsayi mai girma, saboda kana ƙoƙari sosai akan harkar tsaro ka san aiki sosai, akwai yiwuwar ka samu ƙarin matsayi me girma, amma naga kamar baka farin ciki?"
Captain Khamal ya ware manyan idanunsa akan Jamil, cikin rashin damuwa yace
"Ihu zan tayi ke nan? Saboda na fito
yaƙi, za'a ƙaran girma? Ko mene?"
Jamil ya ɗaga kafaɗa tare da watsa hannunsa yace "Kada ka gayan ba daɗi Malam, ƙilan masifa ka haɗawa kanka, rabonka da Matarka watanni wajan biyar kenan, dole ka rasa walwala ga matan nan birjik kawai ka rage zafi, gaba ɗaya duniyar nawa take daga kano sai Abuja fa, amma ka takure kanka kamar wani gunki" Taɓe baki Captain Khamal ya yi yana gyara zaman bindigar sa, ganin yayi masa banza yasa Jamil faɗin "I advise you, as you best friend, not as coulliqe".
Captain yaja tsaki yace
"Ko kaɗan, mahaukacin banza ba abunda kake tunani bane"
Jamil ya ware idanunsa yana ƙoƙarin hana kansa dariya, ganin yadda Khamal ya hayyayaƙo masa, amma ya san tastuniyar gizo ba ta wuce ƙoƙi yace "Nine mahaukacin? Wallahi akwai wata yarinya tana zuwa gidana kullum, kawai zan bar baka ita, in mun koma Abuja" tsaki Khamal yaja yana yin waje yana faɗin "Dana aikata zina, gwara na mutu" yana faɗin hakan ya fita daga cikin motar. Jamil yabi bayansa da kallo yana Mamakin ƙarfin imani da haƙuri irin na Khamal, da yawan sojoji suna da hanyar ragewa kansu damuwa, amma banda Khamal da ya kasance me tsantseni.
Captain babban matsayi ne a cikin sojoji. A rank in the military and maritime service, and the highest-ranking company officer. A Captain gets three vertically aligned silver stars on the shoulders. This is the highest rank among the tactical troop organization. Idan ka shige matakin Captain ka fara hawa babban matsayi a Nigerian Army council (NAC).
Captain Khamal yabi cikin dajin da kallo yana mamakin girman da yake dashi, ta ina zasu fara lalubar waɗan nan ƴan matan? Zasu koma gida duka da ransu ko yaya ne? Yana tsaye hannunsa zube cikin Aljihu gaba ɗaya jikinsa kayan yaƙi ne, Daga baya yaji an dafa shi da sauri ya juya yana zare Bindiga, Captain Denial yayi Murmushi yana busa hayaƙin sigari yace
"Kai da kake a daji ai ba kai babu tsoro" Khamal dai ya taɓe baki yana jin warin Tabar na juya masa ciki, Denial ya ɗauki photo daga cikin aljihun Wandonsa ya miƙewa Captain Khamal photon yace "Ka ajjiye a wajanka" A hankali Captain yake bin photon da kallo ganin photon mace da kuma ƙaramar yarinya ɗauke a hannunta, cikin rashin fahimta yace. "me zan dashi?" Denial yace "Koda zan mutu a nan, ka bawa matata domin jikina yana bani ba kowa zai bar dajin nan da ransa ba a cikin mu, za'ai artabu duba da information ɗin da muka samu akan 'yan bindigar"
Khamal kallon Denial kawai yake, ba tare da yace komai ba ya saka photon cikin aljihun Wandonsa.
Tunda suka sauka cikin jejin basa jin motsin komai sai na kukan mugwayen dabbobi, A hankali Khamal ke tafiya yana zuwa wajan wata Bishiya ya yi saurin ɗauke kansa, saboda ganin Denial da yayi tsaye da wata Sojan mace suna murje jikin juna, ko tsoran a kawo musu hari basa yi.
Ya bar gurin yana jin ɓacin rai akan abunda ya gani, ya koma in da sauran sojojin suke, Jamil ne yace "Captain yanzu idan ka samu nasara shi kenan ka daina fita yaƙi?"
Captain ya ɗaga kafaɗa alamar bai sani ba, waje suka nema suka zauna, suna kallon yadda ake ta haɗa kayan yaƙi da alama abokan harin nasu basu farga dasu a dajin ba, ko kuma suma duk cikin irin na su shirin ne ba wanda ya sani sai Allah.
Jamil ya ɗauki Wayarsa zai vedio call da watsastsiyyar budurwarsa amma babu network gaba ɗaya cikin dajin, sai kawai ya ɗauki pen da paper ya fara Rubutu, yana tsaka da Rubutun suka fara jiyo ƙarar bindigogi ta ko'ina.
Garin sauri Jamil ya danƙawa Captain paper hannunsa. Kafin kace wani abu dajin ya ƙaraɗe da ƙarar Bindigu.
Cikin azama suma zaratan sojojin suka fara maida martani, tare da fara sakin harsashi cikin ƙwarewa da dakiya irin ta aiki, kan kace kwabo amsa kuwwar sautin bindigogin ya karaɗe dajin gaba ɗaya.
Sun kwashi dogon lokaci suna bata kashi, babu Sallah ga Musulmin cikin su babu abinci, hankalin duka sojojin a tashe ganin an fara kashe su ana neman aci galaba a kansu, ba tare sun kai ga in da 'yan mata suke ba.
An raunata da dama daga cikin sojojin, bayan komai ya lafa nan likitocin cikinsu suka fara aikin ba su taimakon gaggawa.
Cikin dare kowa ya ɓoye a inda yake, wayar Khamal ya fara haske da mamaki yake kallon wayar ganin screen ɗin wayar ya nuna sunan _My wife_ har zai katse sai ya tuna rabon da yayi waya da matarsa wata biyu kenan ciff. Bashi da tabbacin zai bar nan a raye, a nutse ya ɗaga kiran yana faɗin "Hey Beb..." Daga can Garin Kano matar Khamal mai suna Na'ima tace
"Hankali na, yaƙi kwanciya Dear" shiru yayi mata saboda motsin da yaji a daf da in da yake, A hankali Na'ima tace "Nayi kewarka tare da Babynka dake cikina, gaba ɗaya hankalina a tashe yake, ga bana samunka a waya, bana son wani abu ya sameka" idanunsa ya lumshe cikin ƙasa da murya yace "I miss you, ki kula, ina aiki ne yanzu" yana faɗin haka ya kashe wayar baki ɗaya.
A hankali ya fara tafiya a ƙasa, yana jan cikinsa a ƙasa zuwa inda yake hango mutum a kwance, mamaki ya kama shi ganin wata matashiyar yarinya kwance cikin jini se numfarfashi take, duk an yage suturar jikimta, da alamar fyaɗe akai mata, ba mutum ɗaya bama, saboda yanayin da take yafi ƙarfin ace mutum ɗaya ne yai mata.
Yarinyar ta kama hannun Khamal ta riƙe sosai muryarta na rawa, ganin ta kasa magana gashi se rirriƙeshi take yasa Khamal ya ɗora kunnansa a bakinta, A hankali yarinyar tace
"Ya...Ya... Yaaya" sai kuma tai shiru numfashinta na fisga da ƙarfi, tana ƙanƙame hannun Khamal tace "Basu da imani, basu da tausayi, kada ka barsu Yaya, kada ka barsu Yayaaa in ba kuyi sauri ba sauran ma haka za suyi musu, fyaɗe suke mana" ta ƙarasa maganar tana shaƙuwa.
A kiɗime Khamal ya shiga girgiza yarinyar amma ina tuni rai yayi halinsa, wani irin numfashi ya fara fitarwa jikinsa ya ɗauki rawa, yana da tabbaci tana ɗaya daga cikin ƴan matan da aka sace, runste idanunsa yayi a hankali ya rufe mata Idanunta tare da jan zanin jikinta ya rufeta, har yanzu tana riƙe da hannunsa, wani irin baƙin ciki yana ratsa zuciyarsa, ace a ƙasarka amma ranka da mutuncinka ba a bakin komai yake ba, kai mutuwar wulaƙanci irin wannan saboda son zuciyar wasu tsirarun mutane.
Cikin dare Khamal ya dinga bincikar dajin, yana zagawa da map ɗin da ke hannunsa, da yake akwai hasken farin wata.
A haka Khamal ya gano suna daf da in da yaran suke, saboda hayaniyar da ya dinga jin tana tasowa nesa kaɗan da in da yake, dan haka cikin ƙwarewa irin ta aiki Khamal da jama'arsa suka ƙarasa in da suke, Nan da nan suma suka farga, suka fara musayar wuta, wasu daga ciki ga yara a hannunsa,wasu kuma jikinsu duk jini alamar ba'a jima dayi musu fyaɗe ba. Yaran suna a matuƙar galabaice.
A daren su Captain basu iya bacci ba, duk yawan bataliyar nan ta sojojin, an kashe da dama daga cikinsu, an illata wasu, a daren suka kama wasu daga cikin 'yan ta'addan yayin da wasu daga cikin su suka samu nasarar tserewa zuwa cikin dajin.
Sanyin safiyar yasa Captain Miƙewa yana tafiya a hankali, suka tattare 'yan matan guri guda, duk sun galabaita saboda wahala, wasunsu ba su da lafiya wasu babu suturar kirki a jikinsu, nan sojojin suka fara yiwa 'yan matan jagora dan fitar da su daga cikin sarƙaƙiyar dajin, yayin da wasu sojojin ke ta kwaso gawarwakin'yan uwansu da aka kashe.
"Khamal" aka kira sunansa, da sauri ya juya ganin Jamil kwance cikin jini, anyi masa harbi kusan guda uku, jikinsa na rawa yace "Jamil" Jamil ya girgiza kai yace "Khamal ina maka fatan tsira da ranka, kaje wajan matata kace ta yafe min, wlh ban san adadin ƴan matan da nayi mu'amala dasu ba, yanzu haka ina ɗauke da Hiv, ina da tabbacin matata ma tana dashi, bata san hawa ba bata san sauka ba, na ɗora mata mugun ciwo" Khamal ya Girgiza kansa yace
"Kayi salati" Khamal ya fara salati Jamil yana maimaita wa, a nan jikin Khamal Ubangiji ya ɗauki ran Jamil....
Kwanan su wajan uku, cikin dajin gaba ɗaya kuma sun kwashe ƴan matan an fita da su, a kwanaki ukun nan, kullum se sunyi musayar wuta da 'yan bindiga.
sojojin duk sun ƙare, se wanda ba'a rasa ba, da gudu Major yake tafiya ganin wata budurwa yashe a ƙasa, kafin ya Ƙarasa wajanta yaji ance
"Kaiiii" Aka daka masa tsawa da karfi, Juyawa yayi ya ware idanunsa ganin wani riƙe da bindiga zai harbeshi, Denial ya tare harbin hakan yasa aka harbi Denial a ƙirji...
Captain ya zaro bindiga ya fara Harbin ɗan ta'addan , sai daya kashe shi sannan ya nufi wajan Denial yace "Mene yasa haka Denial?" Denial ya girgiza kai yace "Kai na musamman ne, gwara na mutu kai ka rayu, bana faɗa maka ba? Daman nasan mutuwa zan, kada ka manta da abinda na baka, a cikin mu akwai maciya amanar ƙasa, amma kai da gaske kake naka aikin, Khamal na baka amanar iyali na.. zaka iya, nasan zaka iya ka kula dasu"
Yana faɗin hakan rai yayi halinsa, wani irin ihu Khamal ya saki mene yasa haka ke faruwa? Su sojoji a haka rayuwarsu zata ƙare ne? Sunyi shiri na gaske akan faɗan nan, amma kamar 'yan ta'addan sun san da zuwansuz duk sun samu nasarar kashe zaratan sojoji masu ƙoƙari, ciki har da makusantan abokansa, Miƙewa ya yi, gaba ɗaya jikinsa jini ne kayansa duk sun yage, ga yunwa, ƙishirwa.
Yana zaune a ƙasa yaji shawagen Helicopter, da alamar General ne ya ƙaraso,yasan ɗauki gaggawa aka kawo musu, kasa Miƙewa yayi har sai da wani soja yazo wajansa ya ɗaga sa, yana faɗin "Komai yazo ƙarshe Captain"
Sauran gawarwakin aka kwashe zuwa cikin wata babbar motar sojoji, raguwar 'yan ta'addan da sojojin suka kama suka ɗaure, suma aka zuba su cikin mota, suma sauran mutanen da suka tsitstsinto anyi garkuwa da su, a wata mota aka zuba su, Khamal ya miƙe ya na tafiya a hankali, kamar daga sama kunnansa ya fara jiyo masa kukan ƙaramin yaro, tsaye yayi, yai shiruu, jin kamar ba kuka bane yasa ya cigaba da tafiya. yana ƙoƙarin sanya ƙafarsa cikin mota, ya ƙara jiyo sautin kuka, a wannan karon kuma ya tabbatar gaskiya kunnansa ya jiyo masa, kuka ne da gaske, fasa hawa motar yai, sauran sojojin na kiransa amma be kula ba, a hankali yake tafiya jiki a sanyaye da ƙyar yake ɗaga ƙafarsa saboda wahala, ganin baiga kowa ba sai ya fara tunanin ko aljanu ne? Ko kuma kukan wata dabbar ce, wani kukan ya sake jiyowa da sauri ya juya zuwa inda yake jin kukan, ya ƙara nausawa cikin dajin, ware idanunsa yayi kan ƙaramar yarinyar dake zaune a ƙasa ta ƙanƙame jikinta waje guda, Idanunta rufe da alama gaba ɗaya a firgice take, Khamal ya ware idanunsa akan yarinyar gaba ɗaya ba zata shige shekara uku ba (3Years) fara ce sosai kamar buzuwa kamar kuma Balarabiya, tafi kama da ruwa biyu (Half-caste) domin gashinta wanda yafi ƙarfin kanta ya sauka har ƙasa kasancewar a zaune take, farar fatar jikinta tayi baƙi sosai, ga raunuka a jikinta..
Sosai Khamal ya girgiza da ganin ƙaramar yarinya a cikin jejin nan, sai ya fara tunanin ko dai Aljana ce?ko a cikin matan da akai kidnapping take, Samun kansa ya yi da cewa
"Ke" shiru tayi masa sai kukanta take tana ƙanƙame jikinta, cikin rashin sanin cewa yarinyar nada ƙarancin ji a kunnanta yasa Khamal ƙara cewa "Kee" nan ma tayi masa shiru.
"kada ka kuskura ka ɗauki yarinyar nan, ita ba kidnapping ɗinta mukai ba, ita tamu ce, rainonta za muyi, 'yar mu ce" Cewar wani mutum da ke tsaye, hannunsa riƙe da bindiga.
Captain Khamal ya kalli mutumin sai kuma ya kalli Yarinyar, kana yaja baya kaɗan yace "To me zan da ita tun da taku ce?" Ya faɗa yana Juyawa, mutumin ya sunkuya zai ɗauki yarinyar kenan yaji saukar bullet a bayansa, ihu ya saki yana faɗuwa ƙasa, cikin zafin zuciya Khamal ya fisgo Yarinyar yace "Keeee...." Sai a lokacin taji saukar muryarsa a kunnanta, fararen idanunta ta ɗaga, wanda yasa zuciyar Khamal bugawa, Yarinyar ta washe bakinta ta nufi wajan Captain Khamal tace
"Abbi..." Ta faɗi hakan tana ƙanƙame ƙafafuwan Khamal, “Abbi?” Khamal ya maimaita a zuciyarsa a fili kuma sunkuyawa yayi ya ɗauki yarinyar a kafaɗarsa, kai tsaye ya nufi in da motocin su suke da ita yana ƙoƙarin shiga cikin mota yaji saukar wani abu mai kama da kibiya ko mashi a gefen cikinsa, a hankali kuma yaji zafin saukar abu a jikinsa tsananin azaba yasa sam bai kawo cewa harbinsa akai ba, ƙafarsa ya ɗaga da ƙyar yana sauke Yarinyar muryarsa na rawa yace
"Shiga ciki" watsa hannunta tayi tace "Abbi" alamar bata gane zan can nasa ba, da
0 comments:
Post a Comment