"Wallahi Ammi dagaske nake, kin san dai ba zan yi masa k'arya ba, ki zo ki ga yanda suke yi da Yarinyar, zaki tabbatar Ɗa da Mahaifi ne."
Jiki a sanyaye Ammi ta ce. "Wannan maganar ba ta waya ba ce, bari na kira Alhaji, za mu zo yanzun nan insha Allahu, amma dan Allah kar ki tayar da hankalinki da yawa, kin san a yanayin da kike ciki ba'a buƙatar ki saka damuwa a cikin ranki."
"Toh Ammi sai kin zo" Ta faɗi haka cikin kuka, zuciyarta na yi mata wani irin suya saboda tsananin kishi. Khamal ya shayar da ita ruwan mamaki, ba ta taɓa zaton haka daga gare shi ba, she trusted him over, ashe ya ce zai nuna mata halinsu na sojoji.
Cillar da wayar ta yi ta fito daga ɗakin kamar mahaukaciya, ko nauyin cikin jikinta ba ta ji. Zaune ta tarar da Captain a parlour kan kujera two seater, Abra na jikinsa ta yi bacci abinta. Kallon Television yake yi hankalinsa kwance tamkar babu wani abu na ɓacin rai da yake damun shi. Hakan ya ƙara k'ular da Na'ima, ta tsani wannan maziyar tasa, abu ya faru ya mayar da kai mahaukaci shi kuma ya dinga pretending like everything is okay.
Kamar zautacciya ta fara cillar da pillows ɗin kujera cikin kuka tana faɗin. "Wallahi Khamal ba ka isa ka tozarta ni ba, sai na kashe ka na kashe yarinyar in yaso nima a kashe ni!" Khamal dake bin ta da wani irin kallo cikin tsawa ya ce mata. "Na'ima! Wallahi kika sake wani abun ya samu Yarona da ke cikinki garin haukanki sai na nuna miki ɓacin raina, wanda baki taɓa ganin irinsa ba."
"Ya mutu ma ina ruwana Ni, kuma ɓacin rai ka daɗe baka nuna mun shi ba, ƙarƙari dai ka ce ka sake ni in tafi in bar maka gidanka, to idan ka sake nin sai me? Na ce sai me?" Tai maganar tana zazzare idanunta da sukai jawur, saboda azabar kishi da kuma kukan da tai.
A firgice Abra ta farka daga baccin saboda hargagin Na'ima, fashewa ta yi kuka tare da ƙanƙame Captain tana kiran sunan "Abbi".
Cikin tsana Na'ima ta wurga mata wani kallo tana huci kamar zata ci babu, ji take tamkar ta fizgo Abra daga jikin Khamal. Tsaki Captain ya yi ya miƙe tare da Abra a jikinsa ya shige bedroom ɗinsa yana rarrashin ta. Ganin haka yasa Na'ima fashewa da kuka tare da zama daɓas akan kujera, ganin yadda ya maida ita mahaukaciya.
"Khamal why? Me yasa zaka mun haka? Ban cancanci haka daga gare ka ba, kar ka saka mun tukwicin k'aunar da nake yi maka da cin amana."
Ta faɗi haka cikin sheshshek'a.
Ƙarfe biyar da mintuna su Ammi suka ƙaraso gidan, har lokacin Na'ima tana zaune a inda take, ta ci kuka ta gode Allah, sai wani irin haki take yi saboda tsabar ɗorawa kai masifa, ga nauyin ciki.
Tana jin ana knocking ta miƙe da sauri ta buɗe ƙofar, zatonta ya zama gaskiya su Ammi ne tare da Baffa.
Granny ce a gaba, baki buɗe take kallon Na'ima bayan sun shigo, tafa hannuwa ta shiga yi ta ce. "Na shiga uku ni Mari, wannan fita hayyacin naki da kika yi Na'ima na mene ne? Ko waya aka yi miki aka ce tsohuwa ko tsoho wani ya mutu?"
Na'ima ba ta bi ta kanta ba ta yiwa su Ammi sannu da zuwa cikin dauriya.
Kama hannunta Ammi ta yi cikin lallami ta ce. "Na'ima ba ki ji abun da na faɗa miki ba ne na cewa ki kwantar da hankalinki? Kin ga yanda kika koma kuwa?"
Sake fashewa tai da kukan tace "To Ammi ya zan yi? Ba ki ji yanda zuciyata take mun wani irin zafi da suya ba ne."
Baffa ya yiwa kansa mazauni ya ce. "Ina shi Khamal ɗin yake?"
"Yana ɗakinsa tare da Yarinyar." Na'ima ta faɗa cikin ɗacin rai.
"A'a, wacce yarinyar kuma? Me kuke zance akai ne? Me yake faruwa ne?"
Granny ta tambayi haka tana bin su da kallo.
Ganin babu mai shirin ba ta amsa cikin fusata ta ce. "Yau na ga jaraba, ya ina tambayar ku, kun mun shiru kun mayar da ni wata gantalalliya? Ni dama tun da na ga Buba ya dawo gida hankali a tashe na san da wata a ƙasa, na tambayi me ya faru kuma saboda ba'a ɗauke ni da muhimmanci ba an ce mun ba komai, duba jikin Khamalu kawai za'a zo yi, na zo kuma na ji ana wani zance na daban da ban gane masa ba."
Cikin girmamawa Ammi ta ce. "Hajiya ki zauna zaki ji komai yanzu."
"Wanne irin in zauna kuma kamar wata ruɓaɓɓiya? Ƴarki ce ni da zaki ba ni wannan umarni haka?"
Ammi ba ta kuma magana ba ta nemi guri ta zauna, Na'ima da take jin kamar ta tsinkawa Granny mari saboda takaici ta nufi ɗakin Captain ta fara yin knocking da ƙarfi.
Lokacin yana kwance idanunsa a lumshe, raba Abra ya yi daga jikinsa a hankali wadda ya samu ta koma bacci da ƙyar sannan ya miƙe a fusace ya je ya buɗe ƙofar. Ganin haka yasa Na'ima ta juya ba tare da ta yi masa magana ba, kamar ya share ta ya koma sai dai ya daure ya bi bayanta.
Cikin mamaki yake duban su Ammi ganin su zaune a parlour ba tare da ya san da zuwan su ba. kallon Na'ima ya yi cikin ɓacin rai, akan wannan 'Yar maganar shine ta ɗaɗɗako iyayensa suka zo? Siririn tsaki ya ja a hankali ya ce. "Sannun ku da zuwa."
"Granny ta ce. "Yawwa, ya jikin naka ɗan albarka? Na ga jiki ya yi kyau Masha Allah."
"Da sauƙi Alhamdulillah." Ya ba ta amsa ba yabo ba fallasa.
Baffa ya ce. "Nemi guri ka zauna mu yi magana." Bai yi musu ba ya zauna a saman carpet.
"Wacce yarinya ka kawo gidanka Khamal?" Baffa ya jefa masa wannan tambayar.
A nutse ya fara magana cikin ladabi. "Baffa a wannan operation ɗin da muka fita na tsinci wata yarinya k'arama daban ba'a cikin yaran da aka yi kidnapping ɗinsu ba...." Bayanin komai ya yiwa Baffa har yadda suka yi da Na'ima bayan an kawo Abra.
Cikin zuzuta Granny ta ce. "Huhuhu, yau na ga ƙarfin hali, Na'ima ashe dama ke ba matar rufin asiri ba ce ba mu sani ba? Na ɗauka ko dabba Khamalu ya kawo gidan nan baza ki ce uffan ba sai dai ki karɓe ta hannu bibbiyu. To gidan naki ne ko nasa? ban da jaraba irin taki mutumin ba shi da lafiya amma ki saka shi a gaba da fitina, kina fama da narkeken ciki haihuwa ko yau ko gobe maimakon a gan ki da carbi a hannu kina lazimi akan Allah ya sauke ki lafiya, amma ke ta neman bala'i kike? Tirrr da wannan abu."
Na'ima ta saka kuka ta ce. "To kuma a rasa mai riƙon yarinyar sai shi kaɗai? Cewa fa ya yi idan ba'a ga iyayenta ba a nan za ta cigaba da zama tare da mu."
Baffa yana duban ta ya ce. "Ki kwantar da hankalinki Na'ima, a yanayin da kike ciki ba'a son kina saka damuwa har haka a cikin ranki."
Ammi ta nisa ta ce. "Amma Khamal daga tsintar yarinya sai ka ce kana son ta zaka riƙe ta? Mene ma'anar yin hakan?"
"Wallahi first love ba da wata manufa nake son riƙe Yarinyar nan ba, tun kallon farko da yi mata na ji ina jin tausayinta sosai a cikin raina. Ni fa ban ga abun ɗaga hankali a wannan abun ba, me yarinyar za ta tsare mata in ta zauna a gidan? Ammi ke uwace ya rayuwar wannan yarinya za ta kasance idan ta faɗa hannun ɓata gari?"
Na'ima ta e "Ai dama dole ka ce haka tun da Ubangiji ya toni asirin ka, to wallahi sai dai ka zaɓa ko ni ko ita, amma ni dai ba zan zauna da ita a cikin gidan nan ba."
"Sai ki san inda dare ya yi miki, gida dai nawa ne kuma abun da na gama zan yi a cikinsa." Ya ba ta amsa cikin haɗe rai.
Tsawatar musu Baffa ya yi ya ce. "Ya isa haka! Ba zuwa muka yi mu saka ku a gaba kuna sa'insa ba."
Ya mayar da duban sa ga Na'ima ya ce. "Ki yi hak'uri ki bar yarinyar ta zauna a nan ɗin kafin Allah ya bayyana iyayenta, kar kuma ki saka a ranki na goyi bayan Khamal ne, a'a ko kaɗan, na san halin Khamal na san waye shi, ba'a shaidar ɗan mutum amma zan yabi Khamal akan ba ya aikata zina, tun daa da ba shi da mata bai yi ba balle yanzu da yake da ke. Taimako ne zai yi na riƙon yarinyar, domin idan ya bar ta ba'a san yanda rayuwarta zata kasance ba, duk da gwamnati za ta kula da ita tare da ba ta kariya amma nan ɗin sai ya fi safe."
Granny dake bin su da ido ta fashe da kuka ta ce. "Allah wadaran naka ya lalace, yanzu Na'ima saboda tsabar baki da ta ido mijinki kike dangantawa da zina? To ki je dan kanki, Allah kuma ya saka mana akan wannan k'azafi da kika yiwa jikana."
Ta share hawayen fuskarta tana mitsi_mitsi da ido ta ce. "Kin ci albarkacin cikin dake jikinki, amma wallahi da yau a bazawara zaki kwana a gidan Ubanki, domin kuwa ke ba matar mutunci ba ce, ja'ira da ido kamar an soya Aya."
Baffa ya ce. "A'a Hajiya a dai bi komai a sannu.."
Bai gama rufe baki ba ta hayayyaƙo masa da faɗin. "Na ƙi na bi a sannun, Sharrin zina fa ta yiwa jikana, ku kuma yana ɗanku kun zauna kuna yin abu wani lako_lako kun ƙi yin abu da jiki ki ɗauki mummunan mataki a kanta."
Ta ƙasan ido Na'ima ta dinga wurga mata harara. Nasiha mai ratsa jiki Baffa ya yi musu akan su ƙara hak'uri da juna, sannan ya yiwa Na'ima faɗa akan zargin da ta yiwa Captain, ya nuna mata hakan ba daidai ba ne, musamman da already dama ta riga ta san halin Captain, bai kamata daga ta gan shi da yarinya ta ce ƴarsa ba ce. Sannan ya ba ta hak'uri akan riƙon Abra da ya ce su yi, dan ya gani baro baro a fuskarta ba ta ji daɗin hakan ba ko kaɗan. Shi kuma Baffa haka Ubangiji ya yi shi, mutum ne mai faɗar gaskiya komai ɗacinta, ko da ba za ta yi maka daɗi ba sai ya faɗa, sai dai ka ji haushin sa. Ammi ma ta ɗora da ta ƴar nasihar da ban baki a gare su gaba-d'aya. Na'ima kawai jin su take yi amma ba ta fahimtar me suke cewa, ita kawai gani take yi sun goyawa ɗansu baya ne.
"Sai masifa da wasu surutai ake yi, amma ko yarinyar da ake jarabar a kanta ba mu gani ba." Cewar Granny tana yatsina fuska cike da rikicin tsufa.
Captain da hankalinsa gaba-d'aya yana kan Abra, ya miƙe ba tare ya yi magana ba ya nufi ɗakinsa, Na'ima ta bi shi da kallo hawaye na zuba daga cikin idonta, wani irin haushinsa cunkushe a cikin zuciyarta.
Yana shiga ya tarar Abra ta tashi daga baccin, tana ta kuka tare da kiran sunansa. Rungume ta ya yi tsam a jikinsa ya shiga rarrashin ta. Ajiyar zuciya ta saki tana kallon fuskarsa cikin maganarta da ƙarfi ta ce. "Abbi"
"Na'am My daughter, I'm sorry na tafi na bar ki ke kaɗai ko?" Ya yi maganar yana shafa kanta. Duk da ba ta ji me ya ce sosai ba sai ta tura bakinta gaba. Kissing kuncinta ya yi cikin murmurshi sannan ya ɗauke ta suka fito parlour.
Kallon Abra kawai su Ammi suke cikin mamaki. Ammi ta ce. "Ikon Allah, wannan yarinya haka kamar Balarabiya?"
Wani salati Granny ta rafka tare da miƙewa tsaye tana gyara ɗaurin zaninta ta ce. "Huhuhu, mutanen duniya babu gaskiya da tsoron Allah, ban da tsabar sharri ina Khamalu zai haifi wannan kyakkyawar yarinyar mai zubi da turawa, yana ɗan baƙi da shi? A gaskiya wannan mata babu abun da za mu ce miki sai dai kawai Allah ya shiga tsakaninmu da ke, haka kawai kina daga kwance ki narkawa jikana sharri, bayan kuma kina zaune a cikin gidansa kin gama cin abincinsa kin yi ƙat dake, kin murmuro daga ramar da kika zo da ita." Ammi ta ce. "Hajiya wannan maganar fa an wuce ta, ɓacin rai ne ya saka Na'ima ta yi haka."
Baffa da ya kasa ɗauke idonsa daga kan Abra ya miƙa mata hannu, ba ta yi musu ba ta je gurinsa, ko dan ta ga suna kama da Abbinta ne. Baffa ya ce. "Allah Sarki, sannu yarinya, Allah ya bayyana iyayenki." Ammi ta amsa da Amin. Granny ta zo zata ɗauki Abra ta ƙi yarda da ita, da ta takura sai Yarinyar ta saka kuka ta koma gurin Abbinta ta lafe a jikinsa.
Riƙe haɓa Granny ta yi ta ce. "Yau na ga yarinya da jaraba, dan ma zan taimaka in ɗauke ki ba tare da na san daga inda kike ba shine zaki mun tijara, ban da ma zuciyar musulunci irin tawa mene haɗina dake? Aba jawur a koɗe kamar ƙosai" Ta taɓe baki tare da komawa ta zauna tana cigaba da mitocinta.
Baffa ya miƙe yana duban su Captain ya ce. "Mu za mu wuce, sai a daɗa hak'uri da juna, ɗa kuma na kowa ne, idan ka riƙe na wani kai baka san wa zai riƙe maka naka ba." Na'ima ta danne zuciyarta ta ce. "Insha Allahu Baffa, mun gode Allah ya ƙara girma."
"Baffa ba za ku jira a yi Sallah ba sai ku tafin, kuma ko ruwa fa ba ku sha ba." Cewar Captain.
Baffa ya ce. "Alhamdulillah, wucewa za mu yi, na ga sauran lokacin da ya rage a kira sallah zai kai mu gida insha Allahu."
Granny ta ce. "Dama ba'a yi niyyar ba mu ruwan ba, sai yanzu za'a wani ce mu zauna mu sha." Captain ya dube ta ya ce. "Kin taɓa zuwa gidan kafin yau an hana ki ruwan ne?"
Ɗaure fuska ta yi ta ce. "Ni dai ba zan biye ka mu yi tashin hankali ba tunda ba halina ba ne kowa ya shaida, ato." Sannan ta mayar da duban ta ga Baffa ta ce. "Sai dai in ce ku gaishe da gida, dan ni anan zan zauna in kula da wannan zabiyar yarinyar mai ƙwala ƙwalan idanuwa kamar na kakata haulatu, tunda ita wannan asararriyar ta yi nauyi ba iya kula da ita za ta yi ba, tana juyi da ƙyar tana mirgina uban ciki amma se jaraba, gobe idan Allah ya kai mu Shureim sai ya kawo mun kayan sakawata."
Baffa ya ce. "A'a tare za mu wuce da ke yanzu, Iman ta zo ta zauna a nan ɗin tunda sun kusa yin hutu a school." Bai jira cewarta ba ya yi gaba. Granny ta bi shi da wani irin kallo sannan ta miƙe ba tare da ta yi magana ba ta yi waje fuuu. Ɗan murmushi Captain ya yi ya bi bayansu.
Ammi ta miƙe tana duban Na'ima ta ce. "Ki yi hak'uri, na san zaki ga kamar ba'a kyauta miki ba, amma ba rashin kyautawa ba ne, hakan shine dai-dai. Ɗa na kowa ne, sanadiyyar riƙon yarinyar sai ki ga Ubangiji ya baki wani abun da baki taɓa zo ba a cikin rayuwarki, dan Allah ki riƙe yarinyar nan saboda da Allah, kar ki cutar da ita. Kema ba ki san me gaba zata haifar ba"
Na'ima ta share hawayen fuskarta cikin dakiya ta ce. "Insha Allahu Ammi, ɗazun ma ɓacin rai ya saka na yi hakan, ku yi hak'uri, insha Allahu komai ya wuce. Ammi ta ce. "Yawwa, Allah ya yi albarka, ya sauke ki lafiya." Ta amsa da Amin tare da miƙewa ta raka Ammi bakin ƙofa.
A haukace ta dawo cikin parlour ta shiga bedroom ɗinta ta kulle ta ɗauki wayarta ta kira lambar Yayarta, tana jin ta ɗaga ta fashe da kuka ta ce. "Na shiga uku Aunty, ina cikin damuwa, Khamal ya zo mun da wata masifa cikin gidana." A rud'e Aunty ta ce. "Subhanallahi! Mene ya faru?"
"Yarinya ya kawo mun cikin gidana wai za mu riƙe ta, a cewarsa wai a operation suka tsinto ta, ni kuma na san wallahi k'arya yake yi ƴarsa ce suka haifa da wata karuwar a waje."
"Ya aka yi kika san hakan? Ke da kullum cikin yabon Captain kike akan kamewarsa da rashin bin matan banza?"
"Aunty ba ki ga yanda suke yi da yarinyar ba ne, shak'uwarsu ta fi ƙarfin a ce a cikin abun da bai 1 month suka yi kamar ta ba, kuma baki ga shegiyar Yarinyar ba, kyau kamar ita ta yi kanta, irin kyawun nan dai na ƴaƴan shegu, dan dama a gurin aikin nan nasu akwai mata masu bibiyarsa. Na kira iyayensa kuma domin su zo a yiwa tufkar hanci amma sun goyi bayan ɗansu, ni na yi kara ban kira nawa iyayen ba dan kar ace sun zo sun goyi da bayana, ashe su ma son kai za su yi. Wallahi Aunty ba ki ji yanda zuciyata take mun zafi ba, ni dai ba zan zauna da wannan yarinyar a gidan nan ba, ki bani mafita Please."
Aunty ta ce. "Shi Captain ɗin ya kuka yi da shi?, ki nuna masa bakya san riƙon yarinyar mana."
Cikin sheshshek'a Na'ima ta ce. "Aunty cewa fa ya yi sai dai in zaɓa ko in riƙe ta ko in bar masa gidansa, ya zaɓe ta a kaina, duk irin tarin soyayyar da Khamal yake mun amma yau ni yake faɗawa haka? ba dole in ji na tsani Yarinyar ba tunda a kanta ya faɗa mun haka."
Cikin mamaki Aunty ta ce. "Shi Captain ɗin ne ya faɗa miki haka?"
"Wallahi Aunty shine." Nan ta kwashe labarin duk abun da ya faru ta faɗawa Aunty. Cikin ɓacin rai Aunty ta ce. "Lallai ma Khamal, yanzu akan wata banza can shine zai nemi ya wulak'anta ki? Ya fifita ta a kanki? To amma idan ya san wata ai bai san wata ba, ki k'yale shi ki taushi zuciyarki, ki nuna masa kin amince zaki riƙe yarinyar, taa k'ark'ashin ƙasa za mu biyo masa, a gabansa ki dinga nuna duk duniya babu wanda ya kai ki k'aunar Yarinyar, a bayan idonsa kuma ki dinga cin ubanta son ranki kina gallaza mata, yanda komai ƙanƙantarta da kanta za ta nemi ta bar gidan, koma ta gudu da ƙafafuwanta."
"Ta yaya Aunty? Yarinya ce fa k'arama, ba tafi shekara uku ba, ni fa kawai damuwata yarinyar nan ta bar gidan nan a yau. Dan ba zan raini 'yar haram ba in ci kashinta in ci fitsarinta ba"
"Daɗina dake gajen hak'uri, ki yi yanda na ce miki kawai, da kissa da makirci zaki kori yarinyar daga gidan ba tare an yi tunanin ke kika aikata hakan ba, amma fa dole sai kin danne zuciyarki kin ajiye wannan masiffaffen kishin naki a gefe, in kuma ki kayi dalilin kashe Auren naki ai kin huta." Haka Aunty ta dinga tausar Na'ima da koya mata irin abubuwan makircin da za ta yi, har aka yi Sallar Magriba suna wayar, sai da ta ji shigowar Captain gidan sannan ta yi mata sallama ta share hawayen fuskarta ta tashi ta fito parlour.
A tsugunne ta tarar da shi yana cirewa Abra takalmin ƙafarta wadda ke shan choculate hankali kwance. Wani abu ne ya soki zuciyarta, wato masallacin ma da yarinyar ya tafi saboda tsantsar k'aunar da yake yi mata. Danne baƙin cikin da ya taso mata ta yi ta kakalo murmushi ta ce. "Sannu da zuwa My Man." Ko d'agowa bai yi ba balle ya ba ta amsa. Ƙarasawa ta yi ta tsugunna a gabansa cikin kissa ta ce. "Magana nake maka fa." Nan ma banza ya yi da ita. A hankali ta kamo hannunsa cikin marairaicewa ta ce. "Dan Allah ka yi hak'uri My Man, na tuba na gane gaskiya, wallahi ɗazun ma sharrin shaidan ne." Ta ƙarashe zancen idanunta cike da ƙwalla.
Ba tare da ya kalle ta ba ya ce. "Ya wuce." Yana ƙoƙarin janye hannunsa daga nata ta riƙe shi gam tare da sakar masa kuka. Numfashi ya sauke ya ce. "Mene haka kuma? Ba na ce na hak'ura ba?"
"Ai na san ba ka hak'uran ba, Please My Man ka san ba zan juri fushinka ba." Sakin fuskarsa ya yi ya ce. "Komai ya wuce ki bar kukan nan haka." Sannan ya saka hannu ya shafi cikinta cikin k'aunar Unborn ɗinsa." Ajiyar zuciya ta sauke ganin da gaske ya hak'uran. Hannu Abra ta kama ta ce. "Zo nan Daughter." Ƙin zuwa ta yi ta lafe a jikin Major tare da kwab'e fuska za ta yi kuka. Duk da haka ba ta yi zuciya ba ta shafa fuskarta ta ce. "Ya sunanki?"
"Abra."
Captain ya ba ta amsa idanunsa akan Abra.
"Wow nice name, Allah ya raya mana ke"
"Amin"
"Bari na je na yi Sallah." Na'ima ta faɗa tana miƙewa, dan dauriyarta ta kusa ƙarewa akan pretending ɗin da take yi, ji take tamkar ta janyo Abra ta shaƙe ta ta mutu saboda tsanarta dake ƙara cika mata zuciya.
Bai ce komai ba sai bin ta da ya yi da wani irin kallo, darajar cikin cikinta ta ci, da kuma nasihar da Ammi ta yi masa bayan sun fita, akan ya yi hak'uri ya mayar da komai ba komai ba tun da Na'iman ta yi nadamar abun da ta aikata, shi yasa kawai ya haƙura, amma da ya yi niyyar sai ya hukunta ta akan hauka da ƙazafin da ta yi masa.
LITTAFIN DARE DA DUHU, ₦300 NE KACAL, ZA KU TURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank.
KU TUNTUƁI WANNAN LAMBAR DAN TURA KATIN WAYA NA NAIRA 500 TA WANNAN 09047871750
DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU AKAN WANNAN LAMBAR 07063065780\09047871750
MUNGODE.
'Yan uwa da abokan arzkin wanda aka sacewa 'yan uwa hankalinsu yaƙi kwanciya, gani suke babu wani yunƙuri da gwamnati take yi, dan karɓo musu yaransu, musamman masu 'ya'ya mata a ciki.
Suka dinga kira ga gwamnati, akan Lallai a biya su wannan kuɗi, a karɓo musu yaransu.
Yayin da gefe guda, gwamanti na ta ƙoƙarin ganin yadda za'a karɓo yaran, ba tare da an illata wani ba, kuma ba tare da an biya wannan kuɗi ba, idan aka kwashi wannan zunzurutun kuɗi aka bawa 'yan ta'adda hakan ƙarara ze ƙara nuna gazawar gwamnati, wanda babu gwamnatin da zata so ace ta gaza.
Taro aka gabatar cikin dare, in da aka siyo manyan makaman yaƙi, da za'a rabawa Sojoji, cikin sirri aka kawo makaman aka saye su, a in da tsirarun da aka yadda da su a harkar tsaro ne kawai suka sani.
General Ibrahim ne tare da ƙaramin ministan tsaro, suka ɗai a wani ɗaki suna tattaunawa cikin harshen turanci.
Ƙaramin minista ya kalli General Ibrahim yace "ai mu wannan abu gaba ta kaimu, ka saka amintattun yaranka su fita da wasu daga cikin kayan da na gaya maka, aka kaisu wannan mararrabar, masu shi za su zi su karɓa, kuma akwai ƙishin ƙishin tun da gwamnatin tarayya ba zata karɓo su ba, Gwamnan jihar ze rage wani abu ya basu ya karɓosu, wanda muna da kaso me tsoka a ciki".
General Ibrahim yace "an gama ranka ya daɗe, duk yadda kace haka za'ai, sannan akwai wasu sojoji, da aka kora suke ta ragaita a gari, cikin sirri zan janyo su cikin h
0 comments:
Post a Comment