_Bismillahir rahmanirraheem_
Qarar waqar sani sabulu ce ta _duniya wandon roba_ ta cika gidan ta karade wane daki da saqo na gidan sbd qarar muryar radio din da aka Kai qarshe gaba daya,
Hankalinsa kwance yake yana Shan waqarsa Yana sakace haqoransa da tsinke
Daka gansa zakasan babu Abinda ya damesa.
Dukkanin mutanen gidan 'dai 'dai suka ringa fitowa rayukansu a 'bace da takaicinsa na kullum Wanda inda sabo sun Saba da dabi'arsa ta tayardasu kullum da sautin radionsa da muryarsa Bata qasa
Gashi bamai ikon mgn 'yar gaban goshinsa da shaqiyin dansa suce ba Wanda ya isa
Amma rshin arzikinsu babu kalar Wanda basa fafatawa dashi wanda kallo daya zakayi musu kasan su din abin mamaki ne,
Rayuwarsu abin kallo ce sbd sudin abin mamakine.
Yana ganin mutanen gidan sunfara fitowa ya sake dauke Kai sama Yana jiran yaji wani Mai shafaffun Mai akai ne zaiyi mgn ya sauke Masa masifar dake cinsa ta takaicin iyami daya kwana dashi na biya Masa bashin dabaiyi niyar biyaba yanzu da kudinda yaci burin canza radio dashi na AMATULLAH da USI.
Cikin bacci qarar radio din ke shigarta Yana damunta,
Juya kwanciyarta tayi tana toshe kunnuwanta da pillow Amma
Sam qarar Bata daina shiga kunnuwanta ba.
Tsoki tasaki ahankali tana cewa'
Kawuuuu.
Saidata sake rintsawa ta juya kwanciyarta tsawon minti goma Amma Sam baccin ya gagara sbd qarar radio din dole ta yaye lullubinta ta miqe zaune tana miqa tana cewa'
Allah yasa yanda natashi yau cikin qoshin lfy yasa yau ranar sa'atace,
Allah yasa yauma na hadu da irin hajiyar Dana hadu da ita jiya nayi mata kukan tausayi tabani kudinda zanyo......
Kasa qarasawa tayi tareda zaro ido sbd USI data tuno
Da sauri ta dauki hularta dake kan katifarta ta sanya akai tareda zura silifas cikin sauri tana fitowa kota kan kawun batabi ba sbd daga yanayin waqar dayake sha a radio din ta fahimci yau ba sauqi a qule yake Wanda zai saukewa haushin yake nema shiyasa ba Wanda yace Masa uffan gudun masifa.
Bokiti ta dauka ta nufi fanfon dake can kusada qofar shigowa cikin gidan
Tana zuwa ta tararda wani bokitin yakusa cika
Ta gefen ido ta kalli maman junior dake tsaye alamar natane take jiran yacika hancinta na asalin yorbawa sai cika yakeyi Yana fidda iska sbd ita kullum a shirye take da duk inda masifa zata fado ta hauyi.
Shahada tayi ta rintse ido cikin ranta tace'
Bayina bane Allah ne ya qaddaro bazanbi layin jiraba
Ta sunkucesa da gudu ta fada bayin gidan daidai salamatu zata fito bayin tsoron ganin mutum a fujajan yayo ciki yasa ta zame ta Fadi qofar bayin
Aikuwa itakam amah Bata tsaya wata wata ba ta rufo bayin tana cewa'
Haka Allah yaso anty salamatu bayina bane Allah ne ya qaddaro zaki Fadi,
Kema maman junior yi hkr Allah ne ya qaddara da ruwanki zanyi wanka bayina bane.
Cikin wani irin tsananin baqin ciki da takaici salamatu ke kallon kanta zaune cikin ruwan qazantar qofar bayin bayan tayo wanka.,
Wani irin tiririn masifa zuciyarta keyi ta miqe amatuqar zuciye daidai isowar maman junior itama jikinta harwani mazarin masifa yakeyi tana cewa'
Wlh yau gidan Nan saidai kowa alaji landlord yakore agidan Nan Amma sai anyi balain da ko kawu fatihu duk masifarsa bazai hanani yiwa yarinyar Nan dukan tashi Kisha ruwan gishiri ba.
Kallonta salamatu tayi a harziqe tana cewa'
Saiki sameta cikin bayin tunda akanki aka Fara sauke masifa duniya
Kinzo kina qaramin haushi
Idan ke duka zaki mata wlh ni yau saina dauko motar Yan Banga a gidan Nan kowa yaci ubansa tunda Nagano kowane shege a gidan Nan ya rainani tunda anga Ina zaman kaina.
Kota kanta maman junior batabi ba tahau dukan qofar bayin tana fadin'
Yau wlh zakisan halina dabaki saniba tun kafin kizo duniya nasan rashin arziki bazakizo ki rainawa kowa hankaliba kullum komai kikayi kina Kiran sunan qaddara ne daga Allah wlh yau Ina roqan Allah yahadaki da qaddarar Nan da kike kirawa mutane bayan nagama Miki dukan tuwon qasa.
Alhaji mande dake jiyo yanda ake buga qofar bayin gidansa da qarfi ba arziki ya zubo babbar riga yafito ya zagayo gidan tun a soron gidan yake jiyo qarar radion kawu fatihu yaja tsokin takaici ko sallama baiyiba ya fado gidan Yana cewa'
Uban waye zamansa ya qare a gidan Nan yau yake gyangyademin qofar bayi??
Maman junior najin haka tayo gurinsa tana masifa tana zayyane Masa Abinda yafaru bakinta ta kumfar masifar customers dinta nata jiranta ruwan dafa musu doyane tazo diba.
Tanajinsu cikin bayin Amma ko ajikinta tayo wankan da sauri ta fito basuma ankaraba ta fada dakinta tahau shiri
cikin sauri ta shirya cikin doguwar riga baqa mara Fadi sosai ta sanya hijab iya wuyanta ash ta dauki Jakarta qarama ta rataya a wuya ta fice.
Gaban kawu tazo tana ciro qaramar wayarta jaka tace'
Kawu sannu da tashi.
Yi yayi kamar baijitaba Yana gyara zaman radionsa data ishi kowa gidan.
Qofar dakinsu ta kalla inda iyami ke zaune tana sakawa Koko sugar tace'
Iyami Ina kwana??
Lafiya kalau.''tace itama fuska a tsuke.
Murmushi tayi Wanda yasa kumatunta lotsawa haqoranta suka bayyana
Sbd tagano fadansune dai Wanda basa rabuwa dashi itada kawun Kuma ta tabbatarda akan kudi ne..
Dariya tayi tana juyawa tace'
Allah kasa muyi kudi kawu da iyami su daina fada.
Harta fito gidan alhaji mande da maman junior Basu daina fadaba sbd fadan tsakaninsu yakoma.
Titi ta nufa da sauri tana adduar samun kudinda zata bailing usi.
Tana isowa titin tasamu adaidaita ta tare ta fada cikin sauri tace'
Blue fox zaka kaini.
Tafiyar mintuna gomace takaisu gurin cikin sauri ta biyasa ta nufi harabar gurin dake tsareda security masu baqaqen uniform ta shiga
tana kallon wasu motoci biyu dasuka dauki hankalinta sbd tsananin kyawunsu da sheqin dasukeyi Dan har kanka kake gani ta jikinsu
ta kalli sama tace'
Ya Allah kasa muyi kudinda zamu mallaki irinsu nida usi mu Hana su kawu fada.
Ciki ta qarasa da sauri tana adduar Allah yasa yau tasamu sa'ar wani a cikin restaurant din.
Tana shiga ta nufi dakinsu na staffs din gurin inda suke sauya Kaya zuwa uniform din aikinsu.
Kayanta ta sauya izuwa uniform din aikin waitress dogon wando baqi da riga riga ash saita bar qaramin ash hijab dinta na iya wuya.
So takeyi ta tafi da wuri yau sbd gabaki daya hankalinta nakan usi.
Ta tabbatarda yanacan cikin wahala da damuwa duk da dai alqawarinsu ne bazasu taba saka kansu cikin damuwaba duk halinda zasu shiga sbd damuwa ciwo ce a ganinsu idan kasone zaka sakawa kanka damuwa a almarin duniya.
Amah!!!
Naam"ta karba tana juyowa daga jera drinks datakeyi a fridge.
Manager dinsune sanye cikin black Suit da medical glass a fuskarsa cikin tsuke fuska yace"
Ki hada black coffee dinda ake karbarwa _MD ZABEERA_ kullum ana kaimasa yau yazo da kansa zaisha anan,
And ki tabbatarda kinyisa yanda koyaushe ake hadawa kar asamu matsala amah.
Yaqe baki tayi da murmushin qarya tace'"
Bazaa samu matsalab inshallah manager.
Juyawa yayi ya fice Yana cewa' Allah yasa.
Kamar yanda tasan ana hadawa haka tafara hadawa cikin sauri sauri tana gama zubawa Yana sake shigowa yace"
Yawwa ki hada a tray ki Kai VIP 3 yagama Abinda zaiyi tafiya zaiyima.
Babu Abinda ta tsana kamar kai abinci a aikinnan nasu tafison abarta a hadawa suna dauka suna kaiwa sbd idan tana ganin masu kudi burinta sake hauhawa yakeyi.
Tsaki tasaki ta dauke baki ta dauka tana tafe tana qananun tsoki tana Harare harare.
VIP dinsu Yana can sama Saida tagama tsinewa manager ko kafin takai saman daukeda tray din.
Saida ta tsaya ta huta kafin ta nufi VIP 3 din tana isa security din dake gurin ya tura mata qofar gurin yana washe mata baki sbd mutuniyarsace ba ruwanta lafiyayyan takeaway take Masa idan zasu tashi shiyasa kowa gurin yake yinta Dan babu ruwanta bayarwa takeyi shiyasa lissafin nasu yanxu gurin kullum cikin rudarwa yake tunda aka dauketa aiki gurin.
Tana shiga ta tsaya cak tareda lumshe ido tasaki wata irin ajiyar zuciya afili tace'"
Hummmmm masu kudi turarensu ma qamshinsa na dabam ne,
Ya Allah ga amah da usi.
Bude ido tayi ahankali daidai wayarsa na daukar ringin batareda ya juyoba ya sanya dogon hannunsa da fatarsa ke sheqin hutu da haske ya dauki wayar tareda miqewa ya nufi window ya Dora wayar a kunne batareda yace komaiba.
Zare idanuwanta dake neman rufewa su suma tayi tana girgiza kanta ahankali tace'"
Ya Allah.
Table ta nufa ta ajiye tray din idanuwanta suka sauka kan wallet dinsa dake ajiye da kudi acike acikinta batasan lokacinda tayi saurin dire tray din ta dauki wallet din ta bude taba zaro ido tace"
Yau ranar sa'atace ya Allah nagode maka.
Kudin ta zaro gabaki daya tana musu kallon qurilla fuskarta cikeda farin ciki tace'
Kayi hakuri Dan balarabe Amma nafika buqatan kudin Nan.
Aje wallet din tayi ta juya da sauri cikin farin ciki tana damqe kudin ta fice tana sauri Dan karya gama waya ya juyo yaga ba kudinsa ya biyota yace kudinsa zai qwata itakuma bazata bayarba.
Ta glass din window dayake tsaye yake kallonta cikeda tsananin mamaki da qyamar halinta daya sanyashi kasa juyowa akaro na farko dayaga mace da irin wannan halin mafi Muni agaresa Wanda hakan yasahi kashe wayar wadda tunda ya daga baice komai sai sauraren zancen da ake Masa tacan Wanda kusan hakan dabi'arsa ce.
Shin yau itace ranar farko da qaddarar amatu zata fara??????
Ita soyayya guba ce a rayuwar wasu,
A yayinda wasu take qaddara ce a tasu rayuwar,
Wasu Kuma takan zamo tamkar guguwar batarda farin ciki,
Wasu Kuma farin ciki ce agaresu,
Nikuma a tawa rayuwar Ina kallon soyayya da ma'anoni da dama wanda bansan a ma'aunin jerin dazan kirata.
Soyayyarsa ce babban al'amarinda yasameni bayan zamantowata wadda batada kowa batada wani buri a rayuwa bayan naji dadin rayuwata batareda nasaka damuwar zamana mara kowaba a duniya,
Qaddarar rabonsace ta hadani da Dan uwa mafi kusanci da mahimmanci a rayuwarsa,
Dan uwansa ya ginu da soyayyata a yayinda tawa zuciyar ta ginu da soyayyarsa batareda laakari da ganin ya Dade da zamtowa na wata.
Mezai faru a yayinda tsaftatacciyar zuciyar AMATULLAH ta kamu da soyayyar Wanda tasa zuciyar takeyiwa soyayya kallon Abu Mai rauni a zukatan mutane????
ZABEERA royal family wani ahaline daya ginu ya taso cikin tsanani da tsaurin ra'ayoyi akan 'yaya da jikokinsu tareda matayensu,
Ahaline da basusan bare ba haka 'yayansu suntaso cikin tsanani matsi na al'adar gidan Wanda yasa dukkaninsu sukeda tsananin tsoron manyansu da bin umarninsu,
Shikuma ko acikin duniyarsu ta doka da odar family din shi na dabam ne,
Ya taso cikin kuncin zuciya ya rayu acikinta,
Baisan walwalaba,
Baisan annushuwaba,
Baisan zama cikin Yan uwa yayi fara'a ba,
Abu daya rayuwarsa ta Saba dashi shine kadaici da rayauwar kadaici Wanda shine ya zabarwa kansa hakan..
Qaddara ta jeho AMATULLAH arayuwar ahalin ZABEERA wadda itakuma Tata rayuwar take cikeda da farin ciki da walwala tareda nishadi.
Shin itace zata canza rayuwar ahalin kokuwa sune zasu canza rayuwarta,
Rabo ne yakawota kokuwa qaddara????
Shin itace zata zama haske da walwalar farin cikin ZABEERA family??
Ta Yaya ZABEERA zasu karbeta a ayayinda suka gama gano wacece asalin ita da halayenta da asalin burinta Wanda shine yayi silar haduwarta da ZABEERA family.
Karku Bari labarin _min qalb_ yawuceku
Wannan karon salone na dabam.
#MIN QALB❤️
Mamuhgee
ZAFAFA BIAYAR
SIRADIN RAYUWA
safiyya huguma
MIN QALB
mamuhgee
YANKAN BAYA
billyn Abdul
KIBIYAR AJALI
Miss xoxo
ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA
hafsat rano
Pay @09033181070
Or 09032345899
[01/06, 8:50 AM] __*MAMUHGEE*__♥️🌹: _*MIN QALB*_
_Mamuhgee_
2
Bazai iya ganiba
sunaji suna gani qaton saurayin yake kokarin keta rayuwarta dabata gama sanin ciwon kantaba,
Ita kukan datakeyi dannewar dayayi Mata akan duwatsu suna cin jikinta
Shikuma Usman kukan zabar dayasha yake tunowa itace zaayiwa amatu Wanda sanadin hakan sunzama 6arayi dole da qarfi da yaji.
Qoqrin bude qafafuwanta qaton keyi
Usman yayi wani yunkuri tareda kama hannun Wanda ke maqure dashi ya sakar Masa mugun cizo Mai qarfi da haqoransa dasuka gama bushewa da dau'da.
A gigice yasakesa Yana yarfe hannu sbd azabar cizon.
Wani qaton dustsi Usman din yadauka baiyi wata wata ba ya buga akan qaton dake kan amatu
Take ya sulale gefe kansa na tartsin jini sosai ko ihu daya beyiba ya zube agurin Yana wani irin Shure Shure.
Suna ganin hakan wani irin tsoro yashigesu da gudu ya kamo hannun amatu Yana cewa'"
Zo mu gudu amatu.
A firgice dayan ya riqesu Yana cewa'"
Kun kasheshi....a kidime yake fadar hakan cikin tsananin tsoron ganin abokinsa na Shure shuren mutuwa.
Qoqarin jansu yakeyi Yana cewa'"
Wlh police zan kaiku Kun kashesa,
Bazaki guduba ku barni cikin masifa akamani.
Jansu yakeyi da qarfi cikin firgici da tashin hankali suna kuka sosai suna rokonsa ya sakesu Amma Shima a rude yake kansa zai wanke kota halin Yaya.
Irin kukan dasukeyi Basu taba yinsaba arayuwarsu sbd jin wani ya mutu sbd su Kuma Suma kashesu dayan sukaji yanacewa zaayi.
Sosai suke kuka suna rokonsa ya sakesu Amma ko jinsu bayayi Dan Shima kusan kukan yakeyi na tsoro da firgici.
Wata qatuwar gora daga bayansu aka kwadawa qaton a tsakiyar Kai
Ya tsaya cak tareda sakin hannuwansu Yana qoqarin juyawa yaga ko waye ya yanke jiki yafadi jini nafita a qeyar kansa.
Jikinsu na rawa cikin tsananin tsoro da firgici suka juyo suna qanqame hannuwan junansu tareda ja baya suna kallon qaton dashima yake Shure Shure.
Cikin sauri megadin makarantar ya matso gabansu tareda riqo hannuwansu yasaka musu kudi Yana waige waige Yace"
Kuyi gudu sosai kuje can qasan layin gaban kasuwar baya akwai makarantar almajirai ku shige cikinsu ku kwanta ku boye zanzo idan ankwana biyu
Kuyi sauri karku taba dawowa tanan
Kuyi sauri kuje..
Kallonsa sukeyi suna sake sakin sabon kuka sbd sunqara firgicewa da Abinda yake fada,
Yaturasu Yana cewa'"
Kuje kuje kuyi sauri karku dawo.
Gudu suka Fara suna waiwayensa sbd akaro na farko da wani ya taimakesu arayuwarsu.
Tun suna waiwayensa harsuka bace suna gudu cikin Daren gashi yace karsu hau titi subi kwana kwana.
Koda suka Kai makarantar almajiran dare yayi sosai gashi karnika sai haushi suke musu duk inda sukabi.
Suna kaiwa bakin makarantar suka tsaya suna rarraba idon Ina zasu boye sbd almajiran gasunan kwance birjik a fili kowa da matacciyar tabarmarsa wasu Kuma da kwalaye wasuma hakanan suke kwance a qasa ga cinnakai da qwari da komai Amma ba ruwansu kwance suke abinsu suna bacci.
Hanunta usman yakama suka qarasa can qarshe yacire matacciyar rigar jikinsa data gama yagewa ta mutu ya shimfida musu suka kwanta kowannensu jikinsa na rawa numfashinsu na fita da sauri sbd tsananin tsoron dasuke ciki.
Asubar fari dukkanin almajiran aka tadasu suyi sallah
Wanda wannan shine karo na farko dasuka tabayin sallah Shima Suma dai sunyi yanda sukaga kowa nayi gurin bin Abinda malam yayi.
Ana gama sallah kowa yadauko allonsa Yana bita.
Gari yafara haske sai sukaga almajiran na kallon amatu cikin mamaki suna kallon kanta Wanda gashinta ke butu butu da dau'da da qazanta Wanda yake son nuna ita mace ce.
Daga dama sukaji wani almajiri yace"
Kai wallahi idan malam yazo yaga mace dukanku zaiyi wayace mace tana zuwa Nan?hmm
Korarki ma malam zaiyi yanzu Yana fitowa.
Usman najin kora ya kama hannunta suka miqe anabinsu da kallo suka fice a sanyaye.
Harsunyi nisa kadan yatuno da maganar kawu megadi na cewa karsu koma yayi saurin juyawa da ita Yana kalle kallen inda zasu fake Kuma.
Ganin har yamma tayi suna gararin gurin zuwa yasa ya lalubo kudinda kawun yabasu yaje shagon dake kallon inda suke yasiyo Rezar nera ashirin yadawo yajata suka zagaya bayan wani gida Yana cewa'"
Amatu zo muyi aski irin nasu almajiran malam saimu koma cikinsu tunda bamuda wani gurin.
Haka ta zauna yahau yimata aski
Saida ya aske kan tas Wanda duk kusan Rabin kan ya yayyakenta sai jini ke fita kadan kadan Amma Sam Basu damuba Shima sama sama yayi nasa askin rabi yayi rabi beyiba suka dunkule Rezar sbd gaba suka koma makarantar dama kayan jikinsu duk riga da wandone dasuka gama yayyagewa suka sauya kamanni.
Dayake makarantar ba qa'ida sukebi ba take malam ya kaebesu yaga sabbin alamjirai aka Basu tsoffin allon karatu take suka shiga sahun almajirai batareda kowa yasan cewa amatun mace ceba Koda malam ya tambayi sunayensu sukace Usman da amadu.
Ahankali suka Saba da rayuwar almajiranci duk da akwai wuya Amma tafi musu rayuwarsu ta baya dansu yanzu ganin sukeyi sunyi gata.
Akai akai Usman kemata aski sbd kar gashinta yafito musamman sbd tanada saurin tsirowar gashin,
Sunsaba idan sungama ayyukan gidan malam akayi karatu aka gama su fita yawon bara sai yamma sudawo karatun yamma sannan sufita barar dare daga Nan Kuma dare nayi zuzo su kwanta.
Yanzu suna samun yin wanka a sati ko so dayane shiyasa suka Dan Fara canzawa.
Tun suna qirgen kwanakin zuwan kawu megadi harsuka daina suka koma qirgen kwanakin zuwansu har lissafi ya batar musu.
Ko ayanxu dasuke cikin inuwar almajiranci abun dai 'dayane shine idan baka tsayawa kankaba Kaine a qasa ko yaushe,
Sunsha gwagwarmaya zamansu makarantar malam din,
Idan anyi sata su ake maqalawa,
Barna sune,
Laifi sune,
Hatta laifin cikin gidan malam su ake maqalawa shiyasa sunfi kowa azabtuwa sbd irin dukan da malam da ya manyan yaransa suke musu,
Shatin buloli ajikinsu yazama tamkar zanen fatarda aka haliccesu da itane,
Tun suna kuka a almari harsun qame sun daina sbd ganin rayuwar ahaka take koina na sama ya danne na qasan.
Duk hutunda akeyi sukam basa zuwa koina sbd basuda gurin zuwa shiyasa rashin tausayinsu yafi yawa sbd ansan ko an zalincesu basuda me tsaya musu.
Ahaka dai rayuwa taja tsananin rayuwa Yana qara musu yawa musamman yanxu da amatu take Fara nonuwa kullum cikin boye boye suke gashi yanxu abubuwan naqara tsanantar musu ne gashi amatu ko mgn batayi sosai da qarfi da yaji suke boyon mganarta kar agano mace ce.
Yanxu dasukayj wayo Usman shine me wahalar Abinda zasu ci duk da tare suke zuwa duk inda zasu gashi baqin jini tamkar a jininsu yake sbd duk inda sukaje tsanarsu da kyararsu akeyi shiyasa suka riqe aransu duniya kowa kansa kawai yasani basuda Abinda yafi musu junansu.
Wani hutu da akayi kamar daga sama saiga kawu megadi Wanda tuni suka Fara mantawa da kamanninsa,
Farin ciki da murnar dasukayi kamar shine danginsu da basuda musamman dasukaga yazo musu da gari kusan kwano buyi jikinsu har rawa yakeyi gurin yimasa godiya.
Amatu ya qurawa ido musamman kanta dake aske tas Yana qyalli ga wasu qananun quraje a jikinsu zuciyarsa na susa yaji dukkanin kuzarinsa ya karye sbd tabbas duk da baitaba haihuwaba ita 'ya mace ce bazaa jima ana boyeta ba amatsayin namiji.
Dazai tafi yasiya musu gwanjo kowannensu riga da wando masu Dan dama dama.
Tun daga lokacin yake Dan zuwa akai akai Yana dubasu sai rayuwar tadan Fara yimusu sauqi.
Awani zuwa da yayi
Baizo da niyar tafiya dasuba Amma atake tunaninsa ya sauya akan amatu sbd girma daya Fara zuwar Mata gadan gadan Yana tsoron amatsayinta na mace ta abalage acikin maza.
kallonsu yayi bayan sun zagayo bayan makarantar cikin karyewar zuciya Yana jinjina rabasun dazaiyi yace"
Usman kaga amatu tafara girma akwai hadari abarta cikinku anan..
Kallonsa sukayi atare cikin rashin fahimta.
Gyara tsayuwa yayi yace zantafi da ita zan kaita gurin me 'dakina idan yaso Kai saika riqa zuwa Mana hutu.
Atare suka girgiza Kai itada Usman din suna kallon juna idanuwansu na cikowa da hawaye.
Nasan zaa rina yafada cikin ransa Yana kallonsu zuciya a karye.
Kamo hanun Usman yayi yajasa gefe ya fahimtar dashi sosai ta yanda zai gane Abinda yake nufi
Harya gane Yakuma amince sbd har abada bazaiso Abinda zai samu amatu ba.
Daga haka suka hakura sunaji suna gani suka rabu da juna kawu yatafi da su kafin daga baya Usman yadawo makarantar malam.
Tunda amatu tadawo gidan kawu Bata taba haduwa da tsangwama ba saidai Kuma babuwa wani janta ajiki da iyami tayi.
Basuda qarfi sai rufin asiri da haka malam yasakata primary school dinda yake gadi wadda tuni aka maidata 'yar maigadi.
Usman shekara daya yayi batareda itaba ya tattara karatun yadawo gidan kawu Yana kwana a soro komai tsananin sanyi da zafi kuwa.
A haka kawu yasamar Masa aikin tsaron gidan wanka da bahaya a Tasha har Shima yashiga primary 2
Yana shiga primary 5
0 comments:
Post a Comment