"Ina son duk abin da Angel ɗina ke so, Abbi idan tafiyar zai sanya tai farin ciki na amince ka tafi da ita, ni zan dinga zuwa" da sauri Abra ta ce "A'a ba sai ka zo ba" Murmushi kawai Abbi ya yi ganin tsakani da Allah Abra ke duka maganganun ta. "Adnan ta ya ya ɗan kwali zai ja hula? Abra akwai tarin ƙuruciya da kuma rashin sabo a tattare da ita, shi ya sa take cewa haka. Ka kula da ita a yanzu kai take buƙata zuwa next week zan zo tare da Farouk haɗi da duk bayanan binciken da mu kayi zan sanya Private investigator In sha Allah komai zai zo cikin sauƙi"
Jinjina kai Adnan ya yi kafin ya ce "Mun gode sosai Allah ya saka da alkairi, zan kula da Angel kulawa da ko a wajanka bata samu ba, nima a matsayina na Police zanyi ƙoƙarina wajan bincika asalin Real parent's ɗinta"
Ganin da gske Abbi tafiya zai ya barta yasa Abra ƙankame jikin Abbi tana rusa kuka wanda duk wanda yaji kukan da take dole ya tausaya mata. He couldn't feel yadda hawayenta suka jiƙa masa jiki. Shi kansa idanunsa sunyi jajir Na'ima ta gama cutarsa itace silar komai da duk wani abu ɗaya faru ta ya ya zai yafe mata? Har Abada.
Da ƙyar Adnan ya janye Abra daga jikin Abbi ya mayar da ita nasa jikin, tare da rungometa sosai yana faɗin. "Me ya sa ki ke gudana Angel? I'm your husband ni ki ke buƙata a yanzu, the you know how much I love you?" Girgiza kai kawai Abbi ya yi tare da juyawa ya fita zuciyarsa cike da so da tausayin Abra.
Cilli Adnan ya yi da Abra yana nunata da hannu ya ce "Idan kinso ki mutu babu ruwan Sp Adnan Aliyu Matawalle, ko kin faɗawa Uban riƙon naki ba zai taɓa sawa na sakeki ba, domin na fishi iko da ke useless.." goge hawayenta tayi tsaf tare da kallon Adnan cikin dauriya tace. "Ba zan taɓa mutuwa sbd kai ba Sp Adnan Aliyu Matawalle, abubuwan da kke min idan ka haifu kada ka fasa" tana faɗin haka ta juya da sauri ta nufi Bedroom ɗin ta. Mamakin martanin da tayi masa yasa Adnan kasa motsawa balle yayi tunanin ɗaukan mataki akanta me hakan ke nufi? ta daina shakkar sa ko yaya ne?.Ya daɗe tsaye a wajan kafin ya nufi bedroom ɗinsa zuciya cike da tunanin abin da zai mata.
Abra taci kuka ta ƙoshi harta dan gana haka ta raya daren tana kaiwa Allah kukanta akan ya shiga lamarinta ya kawo mata mafita cikin abin da ke damunta ya kuma bayyana mata iyayenta, daga ƙarshe ta roƙi Allah akan ya haɗata da Salmanun-faris cikin gaggawa.
Washegari tana kwance tayi wanka wata simple duguwar riga ce a jikinta iya qwiwa sai fararen ƙafarta da suke a waje. Tai lamo jikin bed rungome da pillow gaba ɗaya tunaninta ya tsaya komai nata ya tsaya tana nan kamar wata statue. A hankali ta ji an murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin nata, Ƙamshin Pur oud da taji ya sa ta tabbatar da shi ne ya shigo ƙara haɗe fuska tayi ba tare data amsa Sallamar sa ba.
Tsaye ya yi a kan yana harɗe hannayensa a ƙirji Looking at her daga shi sai trousers babu ko singlet dai murɗaɗɗen jikinsa da yake a buɗe. "Where's my breakfast?" Shiru not respond domin yi tayi kamar bata ji Abin da yake faɗa ba.
"Ni sa'an mugun Ubanki ne da zan dinga magana kina jina? Ko kuma mugun halin uban naki kika fara wanda ban san da shi ba?" Sai a lokacin ta buɗe idanunta ta kallesa tare da mirginawa wanda ya sanya duguwar rigarta tattarewa zuwa can sama, har farin pant ɗinta ya bayyana cikin ƙasa da murya ta ce. "Daman ance ai kyan ɗan ƙwarai ya gaji iyayensa,babu laifi dan na ɗauki halin mahaifina" a fusace yayi kanta zai daka tayi saurin zillewa wanda ya sa gaba ɗaya rigar jikinta barin jikin tai naked! Cak Adnan ya tsaya domin it's the first time daya ganta naked haka nan cikin haske, notin kansa ya nemi kuncewa domin idan akwai abin da ke saurin raunata zuciyarsa bai shige buƙatarsa zuwa ga matarsa ba, Abin da yake kwaɗayi a kullum wanda yake sanyaya zuciyarsa.
Takawa ya shiga yi zuwa inda take sai da sukai dab da juna ya ce "Ubanki mugu ne Abra, Azzalumi,Macuci, Ma yaudari, mai baƙar zuciya kona bar shi Ubangiji ba zai bar shi ba. Domin Ubanki kura da fatar Akuya ne!"
"Ka sani Uba, Uba ne ba'a taɓa sauyawa tuwo suna, duk lalacewar shi, shi ne ya yi sanadiyar zuwana duniya. Ka saurara da aibata min shi duk da ban san abin da ya aikata a gare ka ba, zuciya nake gudu kada haƙurina ya gaza" Zuciyar Adnan na tafasa ya ce "Well-done Abra Khamal Khamis. Well-done barewa ba tayi gudu ɗanta ya kasa rarrafawa ba, yanzu ne wasan namu zai fara bada citta tunda har kin zamu zarafin mai da min da martani haka nake so muje zuwa shege ka fasa" banza tai masa da sauri ta juya zata shige bathroom. Bata san mene ya faru ba, sai jinta tayi kane kane a jikin Sp Adnan Aliyu Matawalle yayi mata wata iriyar ƙyakkyawar runguma wacce da iya zuciya ɗaya yayi mata ita, domin gangar jiki bata iya ɓoye ainahin abin da zuciya ke buƙata.
He started kissing her from her mouth to her neck. It was a kiss that he had never given her before, babu wutar ɗaukan fansa ko ta ƙiyayya. It is something that shows what the heart wants and needs. Now Abra needs it in his body. Nan take ya nuna mata buƙatar miji zuwa ga matarsa.
Abra ta rasa yaya zatai, a kullum faɗo mata yake kamar jaka ba tare da so ko tattali ba, yana sauke buƙatarsa shi ke nan. Daga baya kuma ya ci mata mutuncin da ko maƙiyinta ba lallai yayi mata ba. Tana karatun novel dan haka zai wani tunani ya faɗo jikin ranta. Taya shi abin da yake tayi sai da yazo gangara ta tsakanin buƙata ta hankaɗa shi gefe da gudu tai bathroom tana haki. Adnan ji yayi kamar zai mutu ko hannunsa ya kasa motsawa sbd ciwon da mararsa ke masa, zai zufa dake yanko masa idanunsa yayi jajur ya ƙorawa ƙofar bathroom ɗin idanun, zubar da aji ne yayi begin nata akan wani abu na jikinta.
Ta daɗe cikin bathroom ɗin kafin ta fito, ga mmakinta sai taga ɗakin nata yayi duhu sosai kafin ta motsa taji an cillata kan gado, duk yadda taso ƙwace kanta kasawa tayi sai da ya tara masa gajiya tare da jifatanta da maganganun masu ɗaci kafin ya fita yana faɗin. "Ba kyauta aka bani ke ba, kuɗi nasa na aureki kuma dole nazo maki aduk sanda nai niyya Ubanki ma yake abin da yaga dama balle ni da nake miji a gareki, mara galihu baiwata!" Ashe kuka ma cikin rahama yake domin kasa yinsa tayi a yanzu Zuciyarta tai mata nauyi sosai.
Misalin ƙarfe huɗu na yamma tana zaune a Parlour sanye take da duguwar riga mara nauyi sosai, gashin kanta duk a cukurkuɗe tai zururu a hankali taji an murɗa handle ɗin ƙofar parlourn an shigo, bata motsa ba domin ta san shi ne ba kuma ta mara ba dawowar shi. Idanu taji a jikinta alamar ana Kallonta haka kawai taji gabanta ya faɗi da sauri ta ɗaga kanta, Innalillahi wanda ta gani tsaye ya shammaceta bata taɓa zato ko tunanin ganinsa a wannan lokacin ba. Jikinta na rawa ta miƙe tsaye tana binsa da kallo cikin wata murya ta ce "Faris.." sai kuma ta kwasa da gudu tai kansa......
LITTAFIN DARE DA DUHU, na kuɗi ne biya 300 ta wannan acct ɗin 0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank. Idan katin waya ne zaka biya 500 kai Mgn ta wannan number. 09047871750/08081012143
[10/20, 7:45 PM] Abk: Da sauri Salman ya shiga girgiza mata kai, alamar kada ta ƙaraso wajansa domin ya san abin da zai faru idan ta zo. Ita ta haramta a garesa kamar yadda ya haramta a gareta. Da sauri ya yi baya ganin yadda ta yo kansa gadan-gadan, hawaye na bin fuskarta ga wani irin kuka da take tamkar wacce akai wa mutuwa.
Juyawa ya yi da sauri ba tare daya shirya ba da nufin barin parlourn yama fita daga cikin gidan baki ɗaya. Ƙyakkyawar rungomar da Abra tayi masa ta baya ita tayi sanadiyar ɗaukewar wutar kan Salman, cak ya tsaya zuciyarsa na bugawa da ƙarfin gaske, shi kansa ya san ya azabtu da rashin Yayar tasa, amma ba shi da iko da ita a yanzu mummunar ƙaddara tai musu shamaki da juna.
Gaba ɗaya ya kasa motsawa sbd yadda Abra ta ƙankamesa ta baya hannunta ɗaya a ƙirjinsa ɗaya kuma ta riƙe ƙugunsa dashi, wani irin kuka take wanda yake ratsa zuciyar Salman, saurare ɗaya yayiwa kukan yasan cewa bawai Iya na farin cikin ganinsa bane, akwai abin da yake faruwa a ƙasa.
Idanunsa da sukai jaa ya buɗe a hankali cikin nutsuwa ya saka hannunsa tare da zame hannayenta dake rungome da jikinsa da ƙyar. Juyawa yai ya fuskance ta ƙanta a ƙasa yana kallon yadda take kuka kamar zata haɗiyi zuciya. Tun daga sama har ƙasa yabi jikinta da kallo babu abin da ya bashi tsoro sai ramar da yaga tayi ba haka ya tafi yabar Angel ɗinsa ba.
Inda take ya matsa tare da sanya hannunsa duk biyun ya tallafo haɓarta fuskarta ta samu gurbi a cikin hannunsa, kasa magana ya yi sai binta da idanu kawai da yake, Eyeballs to Eyeballs suke kallo juna, Abra na shassheƙa ta ce.
"Faris"
Kasa amsata ya yi yana son tantance muryar data kirasa da ita, hannunsa ya zame kaɗan yana mai dashi cikin Aljihu a nutse ya ɗaga kansa sama ya fara bin parlourn da kallo kamar daga sama taji ya ce.
"Kin rame, kamar ba Angel tawa mai son girman nan ba" kwaɓe fuska tayi tare da matsawa kusa dashi ta shiga dukan ƙirjinsa tana sakin kuka tare da faɗin.
"Why did you go and leave me? Kai ne wanda nake gani naji daɗi, kai ne walwalata, farin cikina, me ne yasa zaka barni a lokacin da nake buƙatar ka? Why Why Why Faris" ta faɗa tana sakin raunataccen kuka while tana ƙara dukan ƙirjinsa da dukkan ƙarfin ta. Jajayen idanunsa ya lumshe yana jin yadda take dukansa kamar wanda yayi mata babban laifin nan, baya ita ce wacce ta bashi lasisi da damar tafiya ya barta,ita ta zaɓi waninsa ta kasa fahimtar feelings ɗinsa a gareta, ta gagara gane cewa so da ƙaunar da yake mata ba iya na ƴan uwa bane, so ne irin na masoya wanda zai kai matakin Mata da Miji.
Jin kukanta yake har ƙasan zuciyarsa, zafin da zuciyarsa ke masa a yanzu ya tabbatar yafi wanda zuciyar take mata, ji yake kamar ana ɗiga masa ruwan dalma a zuciyarsa. Ganin yadda take kukan har numfashinta ya fara sama alamar zata sume masa, cikin rashin abin yi da mafita yabi umarni da kuma ragamar zuciyarsa ya jawota jikinsa tare da yi mata masauƙi a jikinsa ya rufe ta ruf da hannayensa. Kamar tana jira tai holding nasa back sai kuka take tana ƙankamesa tare da faɗin.
"Stay with me, don't leave me again. I am happy when you are near me. Idan zaka tafi ka tafi dani kaji"
Shiru Salman ya yi mata, har lokacin yana riƙe da ita a jikinsa zuciyarsa kamar zata fito waje haka nan ya keji.
"Faris.." ta faɗa tana ɗaga kanta tare da kallon fuskarsa wacce tayi jaa sosai. "Kayi magana mana ɗan ƙanina" ta ƙare maganar tana Murmushi while hawaye na zubu mata ta rasa yadda zatai she can't believe wai Faris ne tsaye a gabanta. Hannunta ta miƙa taja dogun hancinsa tana faɗin "Say sometimes yaushe ka zo? Waya faɗa maka gidana" zameta yayi daga jikinsa ya tsaya kamar an dasa shi ya ce.
"Banji daɗin ganinki haka ba, Abra." Kanta ta sunkuyar ƙasa a karo na farko taji kamar ta faɗawa wani halin da take ciki musamman yanzu da take ganin Salman a gabanta. Amma idan ta tuna gargaɗin Adnan a gareta, sai ta ji tsoro da fargaba ya kamata, kuma tayi tuni ga Sirrin Aure tsakanin ma'aurata, sai taji duk jikinta yayi sanyi. Shiru ta yiwa Salman ba tare da ta ce komai ba.
"Is something bad happened to you? Look Angel kasa jurewa da ganinki a cikin mafarkina da nayi ne ya sanya na biyo jirgi na tawo ba tare da sanin makarantar da nake ba,kina so zuciyar Faris ɗinki ta buga ne?"
Girgiza masa kai tayi muryarta na rawa tace "Ka zauna na kawo maka ruwa, me zaka ci?" "Banzo dan naci abincin gidan mijinki ba, I'm here sbd sanin halin da kike ciki, da kuma dalilin da yasa kike addabata a cikin barcina" shiru tayi masa hawaye wani yana bin wani wata tsawa ya buga ya ce "Talk Abra, Talk" dugun numfashi taja tana ɗaga kai da sauri ya ƙaraso inda take tsaye ya kama hannunta zuwa kan kujera ya zaunar da ita.
Juyawa yayi da sauri kuma ya nufi wajan deep freezer yaje ya buɗe, ruwa mai sanyi ya ɗauka ya dawo inda take zaune, a lokacin har idanunta ya fara lumshe a gefenta ya zauna ya kama Fuskarta tare da bata ruwan, tana sha yana ɗan bubbuga bayanta tare da shafa kanta. Ajjiyar zuciya mai ƙarfi ta saki kanta ta ɗora saman cinyarsa ta ce.
"Zuciyata babu daɗi Faris, komai ya lalace duniya ta juya min baya nasan da kana kusa dani da hakan bai faru ba, bana da mafita bana da mataimaki, bana da ikon faɗin abin da yake raina, Ubangiji ne zai min maganin komai ka tayani da addu'a...," Kukan da yaci ƙarfinta ne yasa ta kasa ƙarasa abin da tai niyya. Shiru yayi mata har lokacin yana shafa kanta ganin ta fara dawowa hayyacinta ya sa ya ce.
"Kinci Abinci?" Kai ta girgiza masa ya ce "to ɗagani, kin wani haye min cinya" murmushi tayi tana faɗin.
"Wallahi bacci ma nake shirin yi, naji cinyar ta ƙara laushi"
"Ko?" Ta miƙe tsaye tana faɗin "Sure" sai a lokacin ta shiga kallonsa maroon ɗin voyel ne jikinsa mai manyan zane amma shara shara haka Voyel ɗin yake, hatta farar singlet ɗinsa ana gani ya ƙara fari tas dashi, ga ƙirjinsa daya buɗe fuskarsa ta fara cika da gemu da saje, sai jajayen laɓɓansa da suke haske. Zaka iya tunanin yayi shekaru ashirin da biyar ko da bakwai haka.
Marairaice mata fuska ya yi ya ce "Yaya" dry tai tana watsa hannunta ta ce "You have changed totally wallahi mai kake ci acan China?"
"Tunanin ki ke ƙara min lafiya" idanunta a kansa ta kasa magana yana ɗago kai suka haɗa idanu ya zaro mata idanunsa ya ce "Ki je ki kawo Abinci Angel stop looking at me haka nan, kada ki fara ganin munina tun ina kyau a idanunki"
"Zoka ta yani" Waro idanu ya yi waje ya ce "Wa? Ni Salman Khamal Khamis? Jeki kawai Yaya ina jiran ki" "haba mana Faris yaushe rabon da muyi girki tare" girgiza kai kawai yayi ya ce. "Yaya gsky ba zan iya ba"
Turo baki tayi ta juya zuwa kitchen ɗin ajjiyar zuciya ya sauke sai a lokacin hawayen da suke maƙale a idanunsa suka silalo a hankali, da sauri ya sa hannunsa ya goge tare da Miƙewa yabi bayanta.
Duk abin da take da Idanu kawai yake binta, yana nan tsaye da ƙyar ta samu ya yanka mata albasa da carrot. Babu jimawa ta kammala haɗa fried rice with chicken kabab. A plate ɗaya ta zuba ta saka 2 spoons, ya rigata tafiya a zaune ta samesa kan kujera ta ce.
"Baka gaya min ya Mamina take ba da Abbi, Ammi, Granny i so much missing them wallahi" shi dai bai ce komai ba ta ce.
"Ga abinci" "kefa?" Girgiza kai tayi ta ce "bana ci" ƙuri yayi mata da ido kafin ya ɗauki spoon yana sakkowa ƙasa, A nutse yake bata abincin tana ci harta ƙoshi . Zamewa tayi ta ɗora kanta a cinyarsa idanunta a sama shi dai bai motsa sai girgiza ƙafarsa da yake, hakan yai wa Abra daɗi domin sai ya zamana kamar rarrashinta yake bai aune ba yaji saukar numfashinta bacci ya ɗauke ta.
Tunani Salman ya fara, game da sauyin Abra amma ya kasa gane gaskiyar al'amarin, sai ya alaƙanta hakan da sabuwar rayuwar data samu kanta ciki, da kuma tafiyar da ya yi barta wannan dalilin sune suka sauyata, ya san tana son mijinta tana kuma farin ciki da aurensa. Babu wanda ya san da batun zuwansa Nigeria, domin shi kansa bai yi tunanin cewa zai iya zuwa cikin gaggawa haka ba, Khairy ce ta bashi Information na gidan Abra, kuma yaci sa'a yana da aboki a Kaduna, yana zuwa kuma bai sha Wahala wajan maigadin gidan ba, har lokacin da ya nufi ƙofar parlourn bai yi tunanin zai sanya Abra acikin ƙwayar idanunsa ba, sai gashi yana buɗe ƙofar ta sadashi yayar tasa. Numfashi ya sauke yana kallon yadda take bacci ta ƙanƙame hannunsa a ƙirjinta, zuciyarta na ɗan bugawa a hankali. "Zaki dawo gareni, zaki zama mallakina Insha Allah yaya" kwanciya ya fara tunanin gyara mata.
Yana ƙoƙarin ɗaukanta zuwa saman kejera yaji ance "Well-done Salman Khamal Khamis Well-done masoyi na ƙwarai" ko ba a faɗawa Salman ba ya san Sp Adnan Aliyu Matawalle ne. Murmushi ya yi a hankali ya ɗauki Abra ya kwantar saman Kujera yana duba yadda baccin nata ya yi nisa, hannunsa ya zuba cikin Aljihu idanunsa akan Adnan ba tare da ya ce komai ba.
Adnan daman ba barin gidan ya yi ba, domin tun safe yana nan, kuma a lokacin daya fita yabar ƙofar a buɗe ne, sbd bai tunanin zai jima, sai gashi yana zuwa cikin Garden ɗin gidan nasa har bacci ya ɗaukesa a can, wannan dalilin ne ya bawa Salman damar ganin Abra cikin sauƙin.
Adnan ya ce "Daka fahimci ka zama loser a Soyayyar Abra sai ka tattara kayanka zuwa China, saboda kada ayi aurenta akan idanunka right?"
Salman ya juya ya kalli Abra ba tare daya kalli Adnan ba ya ce. "I love her, duk wani bugun numfashina da Soyayyarta yake fita, ban san adadin son da nake mata, idan da ace nine mijin Angel a yanzu ina da tabbaci da tafi haka, fari, ƙiba, kwanciyar hankali" janye idanunsa ya yi daga kanta ya kalli Adnan ya ce.
"Loser? Haka kace ko baka da labarin sbd ina gab da rabaku aka tura ni China karatu? Baka da labarin Soyayyar da Angel ke min kwatankwacin ta bata yi maka? Ban san ina tunanin Sp Adnan Aliyu Matawalle ya tafi ba, daya kasa gane cewa ba soyayyya ƴan uwa Abra ke min soyayya ce irin ta Miji da mata"
Tafa hannu Adnan ya shiga yi kafin ya ce "Kace duk a sbd farin cikin Abra aka haɗa baki dakai wajan muna furtarta, kuka kasa faɗa mata cewa Major Khamal Khamis ba shi ne ya haifeta ba?" Dry Faris ya yi irinta Abbi sak kafin ya riƙe ƙirjinsa sosai ya ce.
"Masoyi na Gaskiya shi ne zai gujewa ɓacin ran wacce yake so, Abra matsalar ta shafa amma naji inama nine wanda aka tsinta ba ita ba, a kuma ranar dana san ba a ciki ɗaya muka fito ba, na gane cewa ina tsanin so da ƙaunar Abra, ina mata son da ko rabinsa baka yi mata, ban taɓa zama loser akan abu ba, haka ba zan fara akan soyayyar Abra ba, ka sanya a ranka tamkar ajjiya haka take a wajanka Tabbas zan dawo na amsheta a hannunka a lokacin da babu abin da ka isa ka aikata".
"The you love me Faris?"
Suka ji saukar Muryar Abra a kunnuwansu. Runste idanunsa ya yi ya kasa juyawa ya kalleta. "Mene ya sa Faris? Ashe kasan gaskiya wacece ni ka kasa faɗa min? Kana tunanin rashin faɗa min zai sanya nai farin ciki? Ina yarda da junan da mukai? Ina kariyar da kace zaka bani tana ina?" Shiru kawai ya yi mata da sauri ta ƙarasa gabansa ta ce.
"Magana nake Faris" idanunsa da sukai jajur ya buɗe tare da zuba mata su. Ya ce "kibar wannan maganar yaya"
"Me ya sa zan bari Faris? Ka faɗa min gsky Say something Salman Khamal Khamis say it" ta faɗa tana jijjiga shi idanunsa a kanta ya riƙe hannayenta ya ce.
"Sbd ina Sonki, Ina Sonki Angel, na buɗe idanu dake, na rayuwa dake, mun tashi tare da Soyayyar juna, ina jinki a Zuciyata ina kishin ki tun ban san wacece ke ba, na ɓoye miki gskyar Al'amarin sbd farin cikinki ki, ina son ki dauwama cikin farin ciki. A duk sanda kika gane cewa Abbi ba shine wanda ya haifeki ba kina iya zama wata Abrar ba wacce na sani ba, a lokacin kuma na fahimci tsanar da Mami ke maki haka ne sanadi, daga nan kuma soyayyar da nake maki ta fara juyewa zuwa so na aure. Na kasa fahimtar dake how much I loves you, how much I care for you... Kullum cikin tunanin ni ƙaninki kike, kallon yaro kike min Angel so I have no choice wanda ya sa dole naja bakina nai shiru ina kishin mutumin da kika aura".
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" shi ne abin da Abra ta faɗa, is that the reason da ya sa Faris yayi kissing nata a lokacin da zai bar ƙasar? Ta kasa fahimta. Kuka ne ya kwace mata ta ce "Me yasa ka tafi ka barni?"
"Bani da laifi, Mami ta shirya komai sbd na faɗa mata sonki nake ƙaunarki nake, gaba ɗaya plan ɗinta ne, babu wanda ya san da zuwana ƙasar nan a family Khairy ce ta bani Information inda kike zaune da komai. Bani da farin ciki Yaya ban ga alamar kina farin ciki da wanda kike aure ba?"
Abra ta kasa cewa komai domin bata san da wacce kalma zatai amfani da ita wajan faɗawa Salman cewa bata jin daɗin auren ba, kuma bata da ikon faɗa masa komai, ajjiyar zuciya ta sauke "tayaya zan farin ciki Faris? Baka tare dani rashin ka shine sanadin shigata cikin wannan halin"
Adnan dake tsaye ya dakawa Salman tsayawa ya ce "out of my house loser!" Girgiza kai Abra tai ta ce "No Salman kada ka tafi akwai abin da nake son faɗa maka"
Kauuuu!! Adnan ya ɗauke ta da mari, haushi, baƙin ciki, kishi suka taso masa lokaci guda kafin ya ce "Kina matsayin matata kike magana da wani banza ɗan iska under age? You're
0 comments:
Post a Comment