"Waye ya kashe Mahaifiyar Widad? Me yasa aka kasheta!!? Meyasa ake bibiya da barazana ga dukkanin wanda yake da kusanci da ita!!!? Meye dalilin rushewar binciken wanda suka kashe mahaifiyar Widad? Meye Alaƙar kisan Mahaifiyar Widad da wanda Widad tasa aka ɗaure!!!? Meye alaƙar ciwon Widad da ƙwayar dake cikin tea ɗin da'aka kawo mata?
Wannan sune jerin tambayoyin da suka shiga kaiwa suna komowa a cikin ƙwaƙwalwar Yusuf.
Ta ɗago ta kalli Yusuf tace "let's keep this aside, Yusuf ka taɓayin budurwa? Ko kana da budurwa a halin yanzu?"
Jin tambayar Yusuf yayi wani banbarakwai, ta tuna masa da abu mafi ciwo a rayuwar sa da baze manta ba har ya koma ga Allah, ya kalle ta ya ɓoye damuwar sa yayi murmushi yace "Budurwa kuma? Wacece zata so talakan mutum kamata? Ni bani da wata budurwa ni kaɗai ne, ai nayi ƙarami inyi budurwa"
Murmushi tayi tace "ka fiye abun dariya, a haka kamar baka magana, Amma ka iya sa mutum dariya, yanzu babba da kai kace kayi ƙarami da budurwa?"
"Eh mana ko dan kin gani ƙato? Yarone ni ƙarami"
Ta sake yi masa wani murmushin tace "hmm Shikenan, kodai Widad kake so?"
Zare ido yayi kamar idon ze faɗo yace "Ni, rufamin Asiri, inani ina 'ya' yan manya, ai iyakacin talaka daku yayi muku aiki ku biyashi"
"Amma meyasa kake nuna damuwar ka a kanta haka? Dukda tarin wulaƙanci da rashin mutunci da take maka a wasu lokutan?"
"Saboda batamin wulaƙanci se idan na saɓawa umarnin ta, kuma mahaifinta yana matuƙar mutuntani, kuma kinga nine a ƙarƙashin
ta, dole inyi haƙuri da duk abunda zata yi min"
Amal ta numfasa tace "hakane, Amma ina shiga matuƙar baƙin ciki a duk lokacin da naga tana cin zarafin ka, shiyasa nake ganin meze hana ka ajiye mata aikin ta, in samo maka wani aikin ka huta da wulaƙanci?"
Yusuf yayi Murmushi yace "Inajin daɗin wannan aikin a hakan, bana so kiyi wani abu da ze ɓata ran mahaifiyar ki, Amma ina godiya da karamcinki a kowane lokaci, tunda kin gama, muje in sauke ki a gida nima in tafi, kafin Madam ta farga tare muka fita dake" yai maganar cike da ƙoƙarin basar da maganganun Amal
Amal ta jinjina kai ta miƙe, suka bar gurin.
***************************
"Bayanai sun sameni cewar, Akwai yuwuwar Bala ya tona mana Asiri, yayi iƙrarin cewa tunda aka kaishi prison babu wani ƙoƙari da muke dan fitar dashi, munawa kabmu ƙoƙarine kawai, dan haka na yanke shawarar in kiraka muyi wata magana, fatan zaka buɗe kunnenka ka saurereni"
"To Yallaɓai, ina saurarenka"
"Hashim, Abunda nake so da kai shine, So nake a zuba magani a Abincin daza'a bawa Bala, wanda ze sashi rashin lafiya, daga nan se a kaishi Asibitin doctor Mukhtar, a can nake so a ƙarasamin shi, a kauda shi daga duniyar gaba ɗaya dan baze ɓata mana shiri ba"
Hashim Yace "Amma Yallaɓai aikin nan fa yana da hatsari sosai, kasada ne me girma, idan aka gano da hannuna a ciki zan rasa aikina, kuma za'a kamani"
A hasle mutumin yace "Kowace irin kasada ce gara ayita matuƙar Sunana baze fito ba, bazan zuba ido suna na ya ɓaci a banza ba ba tare da na cimma burina ba, Amfanin Bala ya ƙare dan haka a kauda shi bashi da sauran amfani a gareni, kana da damar yin hakan, kana da dama a hannunka dan haka kayi yadda nace, tun kafin raina ya ɓaci"
Hashim yace "Amma Yallaɓai......
"Sadakin aikinka naira million biyu ne, idan ba zaka iya ba zan saka a gefe in saka wani yayi min, Amma kasani kaima bazan barka a doron ƙasa ba tunda kasan sirrina, tashi ka fita na gama magana da kai "
**********************
Widad ta koma normal kamar ba ita ba, dan haka Daddy ya fara shirin komawa saboda Ayyukan da yake dasu, sedai sun fafata da Widad sosai dan ya sake yi mata batun Aure, ita kuma ta ƙara tabbatar masa tana nan akan bakarta ba gudu ba ja da baya, hakan yasa suka ɗan samu saɓani, ya tafi ba tare da tayi masa rakiya ba.
Yusuf yaje ya tsananta bincike akan gano waye mahaifin Nurat, wadda suka je gurin birthday ɗinta shi da Widad, ya samu bayanin wasu abubuwan ne daga gurin Amal, wadda ta riga ta gama narkewa a ƙaunar Yusuf.
Mahaifin Nurat babban ɗan siyasa ne, sukan haɗu da mahaifin Widad a gurin kasuwanci, amma bayanai sun nuna akwai tsohuwar Alaƙa dake tsakaninsu wadda daga baya tayi rauni, 'yarsa da Widad sun haɗu a gurin karatu ne a ƙasar waje, ita kaɗaice ƙawar Widad a Nigeria, se
'ya'yan Alhaji Bulama, shima ba wata alaƙace ta kusa tsakanin su ba, dan bata yarda a raɓeta, ba kowa ke iya jure halinta ba.
Tsangwama ta yau daban ta gobe daban, haka Hajiya Halima, Ramla da ma'aikatan gidan suke nunawa Yusuf, shi kuma ko a jikin sa, aikin da yaje yi shi kawai yake.
Isa mai gadi yayi yayi yasan daga ina Yusuf yake zuwa, Amma fafur Yusuf yaƙi gayamasa, daga baya ma se ya janye jikin sa, bayan gaisawa babu abunda ke shiga tsakankanin su.
Wasa2 aka shiga wata na uku, Amma Widad bata biya Yusuf haƙƙinsa ba, shi kuma koda wasa be taɓa magana ba.
Yusuf yana zaune a harabar gidan yana danna wayar sa, daga sama yaji ance "Ssss" ɗaga kai yayi ya hango Widad ta saman bene, tayi masa alama da hannun ta yaje.
Yusuf ya miƙe ya shiga, tana zaune a falo tana cin gugguru, tana ci tana bawa magenta, Su Hajiya Halima na falon ita da su Ramla gaba ɗaya.
Yana shigowa Amal ta kalle shi tana kashe masa ido, seda yakusa faɗuwa dan gani yake gaba ɗaya sunga abunda Amal tayi, Widad dake kaɗa ƙafa tana kallon Abunda Amal tayi, bata tanka ba ta cigaba da watsa popcorn ɗinta.
Gefen kujerar da Widad ke zaune yaje ya zauna a ƙasan carfet yace
"Gani ranki ya daɗe"
Ta kalle shi ta yamutse tace
"Kai nifa bana son all such kind of names, Malam sunana Widad, ka dinga kirana da sunana"
Murmushi yayi mata tare da ɗan girgiza kai yace "Bazan iya ba, nafi jin daɗin ince Madam, ko ranki ya daɗe"
"to bana so, niba basarakiya bace, ka kira ni da sunana kawai"
"Aike kinfi basarakiya ma gimbiyar Daddynta"
Wani ɗan guntun Murmushi tayi, wanda ita kaɗai tasan ma'anar sa.
Wani uban tsaki Amal tayi wanda bata san ya fito ba, ta miƙe a fusace da nufin ta bar falon saboda haushi.
"Amal!" Widad ta kira sunan ta. cak ta tsaya ba tare da ta waigo ba.
"Me nayi miki ne?" Widad ta jefa mata tambayar
Fuska a cunkushe Amal tace "bakomai"
Murmushi Widad tayi wanda ya ƙara fito da kyawunta, tana girgiza santala santalan ƙafafuwanta, sannan tace
"Kin san Widad bata Soyayya, balle ince zan so abunda kike so, shi kansa Son ban yadda dashi ba balle inyi shi, koda zanyi so bazan so maƙasƙancin Mutum kamar direba na ba, balle inyi wani abu da zesa kiji haushi saboda shi, ki kwantar da hankalinki ba abunda zanyi da wannan abun, rainin hankalinsa da ƙwarin gwiwarsa gurin karyamin dokoki ne ke burgeni wasu lokutan, ban taɓa ma'aikacin da yake rainamin hankali da son yimin katsaladan a cikin lamaurana yadda yakeso kamarsa ba, wani abu dana fuskanta shine, ze iya jure duk wani hali da AƘIDATA, hmm ki huta beb ba wani abun damuwa a cikin abunda nake" ta ƙarasa maganar tare da wani murmushi na rainin hankali.
Yusuf ya kalli Widad, yaji haushin maganganun ta, ya ƙudurce wani abu a ransa.
Ta kalli Yusuf cike da kashedi tace "Kaikuma tara ka kawai nake, ina sane da duk abunda kake yi, ina gargaɗinka akan contract ɗin daka sawa hannu, Ni kaɗai na ɗaukeka aiki, ni kaɗai zakayiwa Aiki, idan har zakayi soyayya or what ever Rubbish you call it, kayishi bayan ka bar gidan nan, hope I made my self clear "
Yusuf ya jinjina kai, a fusace Mummy tace "Aikuwa se naci uban Amal akan yaron nan, ka kiyayi 'yata ba kai ba ita, banda tsiyar ɗan talaka ina kai ina Amal, ƙwarya tabi ƙwarya mana, wallahi duk lokacin da ka kuma shiga sabgarta sena saɓa maka"
"Cewa akayi ana sonsa bashi yace yana so ba, ko ba kya gani ne? Kina zaƙewa gurin ci masa mutunci wasu lokutan, na lura Daddy yana matuƙar ji dashi saboda biyayyarsa, yana girmama shi sosai, ko dan haka at least dole a ɗagamasa ƙafa saboda yana matsayi me girma a gurin megida, dan haka a dinga ɗaga masa ƙafa a dena son shiga hurumin dabe dace ba"
Ta kalli Yusuf tace "Aiken ka zanyi, kaje ɗakina, ka ɗauki key a drower mudubi, ka buɗe wardrobe ɗina ta ƙarshe, ka ɗakko ATM ɗina kazo"
Ba Hajiya Halima ba har Ramla da Yusuf seda suka kalle ta da sauri.
Ta basar ta maida hankali kan talabijin, kamar ba ita tayi magana ba, jiki a sanyaye Yusuf ya miƙe ya nufi ɗakin ta, gaban sa se faɗuwa yake, inda ta kwatanta masa yaje ya ɗau key ɗin ya buɗe wardrobe ɗin da tace.
Ramla ta kalli Widad tace "Amma Widad kamar be kamata kitura ƙato kamar wannan ɗakinki ba"
Widad bata kalle ta ba tace
"gayamin abunda ya kamata Uwata"
Ramla taja bakin ta ta tsuke, dan tasan idan taja maganar se ranta ya ɓaci.
"Subhanallah" shine abunda Yusuf ya furta, dan bayan sutura dake cikin wardrobe ɗin Widad, hadda bandir bandir na kuɗi na Nigeria dana ƙasashen ƙetare.
A gagguce ya ɗau abunda ze ɗauka ya fita ya kai mata, maimakon ta karɓa se ce masa tayi "Kaje na baka hutu na sati ɗaya dan ba inda zanje a kwanan nan, ina so kaje da ATM card ɗin nan, ka cire kuɗi, ka siyomin latest trending phone me kyau guda biyu"
Yusuf yace "Yanzu zan siyo in kawo miki?"
Ƙura masa ido tayi ba tace komai ba, kallon gargaɗi take masa akan bata son rainin hankali, dan haja Yusuf ya girgiza kai ze fita, Widad tace "Ji mana" ya tsaya tare da waigowa ya kalle ta
"Yanzu idan na tambaye ka kasan inda rai yake, wace amsa zaka bani?"
Ɓoye mamakin tambayar da tayi masa yayi yace "Allah Mahalicci shikaɗai yasan wannan Amsar"
Ta jinjina kai tace "Good you can go"
Hajiya Halima a gigice tace
"Widad baki da hankali ne? Ya zaki bawa baƙo wanda baki san daga inda yake ba ki ɗau ATM wanda Account ɗin cike yake da kuɗi, Yallaɓai ma yana zuba dukiyar sa a ciki, kodan baki san zafin dukiyar ba sama taka aka tara aka baki, yanzu idan ya gudu yaƙi dawowa fa?"
"Kalma ta farko kin faɗi abunda ya dace a kaina, kin faɗa daidai ba kuskure, bani da hankali ni mahaukaciya ce kamar yadda kuka saba faɗa, dukiya kuma ta ubana ce, idan na salwantar da ita ba abunda zece tunda nima akwai tawa a ciki, ki dena tada jijiyar wuya akan dukiyar daba taki ba, idan tunanin ki abunda zaki samu bayan me ita ya mutu, sena tabattar da na ƙarar da komai kafin ya mutu koni na mutu, shine hanyar da zan baƙantawa masu harin dukiyar nan rai, and Mark you idan wani abu ya samu dukiya ta a yanzu to ba shakka kece, saboda babu wanda yasan da ATM ɗina a hannun sa seke da iyalanki"
Widad ta miƙe ta barmusu falon suna kallon kallo.
***********************
"Mummy, me yasa Daddy yayi yunƙurin sawa a sace Widad ne? Am so much Confused fa, tunda akayi abun nan ta bar gidan nan bata ƙara kirana a waya ba"
Mahaifiyar Nurat tayi ajiyar zuciya tace "Nurat nima ban sani ba gaskiya, ni banda yanzu da kika gayamin ma ban san abunda yake shiryawa ba, yanzu ina magana ze iya ɗaukar mummunan mataki a kaina, kin san halin sa"
"Amma Mummy abun ya ɗauremin kai, kinji yadda ya dingamin masifa dan na bari an ɗauke ta, kuma fa wani ne yayi barazanar ze saceni nima in har ban gaya masa inda take ba"
"Mhmm Nurat, kija bakinki kiyi shiru da wannan maganar, dan muddin kika bari wani yaji maganar nan mun kaɗe a gurin mahaifinki"
"Insha Allah Mum ba wanda zan gayawa"
*************************
Tunda Yusuf ya tafi da ATM ɗin nan Hajiya Halima ke cikin zullumi, dan ba ƙaramar dukiya ce danƙare a account ɗin nan ba, tunani take yadda zata gano inda Yusuf yake, tasa a ƙwato mata ATM card ɗin nan.
Ramla ta aika ta kira mata Isa me gadi, ba tare da ɓata lokaci ba ya biyo Ramla jikin sa na tsuma zuwa falon Matar gidan.
"Kai wani irin sokon gara ne haka? Har yanzu ace ka kasa gano inda wannan talakan banzan yake?"
"Wallahi ranki ya daɗe ya dena zama a cikin mu ma, wani girman kai yake ji da shi, yanzu shi kaɗai yake al'amuransa ko inda muke ya dena zuwa, iyakacinmu da shi gaisawa"
Dogon tsaki Hajiya Halima taja tace "dallacan sakarai ni rufemin baki, tashi ka bar nan sakarai kawai, ni na tsaya bi ta kanka, zan nemi wanda zasu yi min aikin".
Isa ya tashi jiki a sanyaye ya bar falon,
Mummy ta kalli Ramla tace "Ramla meye abunyi ne? Me ya kamata muyi?"
"wallahi Mummy kaina ya kulle, na rasa abunyi, yarinyar nan ta tabbata mahaukaciya, Mummy idan dukiyar nan ta salwanta ya zamuyi?"
Hajiya Halima tayi ajiyar zuciya tace "bana tunanin yaron nan ze gudu da ATM ɗin nan, Widad tana da wayo ze iya yuwuwa tarko tayi masa, Amma tunda harta yadda dashi haka, dole mu janyo shi cikin mu"
"Hakane Mummy zeyi mana Amfani, idan har ya kasance a ɓangaren mu, Ammafa kamar zeyi taurin kai gayen"
'idan yaƙi yin yadda muke so, then we should exact power over him, you know what I mean "
Ramla ta jinjina kai tare da yin murmushi tace
"Am proud of you Momma "
*****************************
Kwance yake akan makeken gado a wani tangamemen ɗaki me ɗauke da kayan alatu, ya mimmiƙe ƙafafuwan sa hannun sa riƙe da waya yana kallon hotuna. Gefen sa wani matashin ne zaune a gefen gado yana tattaɓa System.
Hotunan Widad ne akan screen ɗin wayar kala kala yana kallo yana murmushi, kowanne se ya tsaya yayi zooming ɗinsa ya ƙare mata kallo, yanayi yana shafa sajensa tare da tattausan murmushi, ga dukkan alamu yana jin daɗin kallon hotunan nata. A hankali ya furta
"Can't wait to see you darling"
Matashin da ke gefen sa ne ya waigo ya kalle shi yace
"Nifa ka isheni, se kace akanka aka fara Soyayya, kullum se kayi zancen yarinyar nan seka kalli hotunan ta, kuma ban taɓa jin ko waya kayi da ita ba"
Shafa sumar kansa yayi tare da yin murmushi yace "bazaka gane bane Fahad, yarinyar ce 'yar daru se hankali, dukda ƙanwa tace amma halinta daban yake, ina tunanin yadda zata karɓi soyayya ta idan na bayyana mata"
"saboda me kake wannan tunanin?"
"saboda tace shi kansa son bata yadda dashi ba"
Ƙyalƙyalewa da dariya Fahad yayi yace "Wallahi Anwar kana ruwa, se kace ita kaɗaice mace kaje ka nemi wata mana, dama da ganin ta zatayi izza, nifa rabona da ita tun tana yarinya ƙarama sosai"
Anwar yace "hmm tabbas da zaka ga Widad a yanzu ba zaka taɓa cewa in haƙura da ita ba, Ina matuƙar sonta, na ƙagu in koma gida, wallahi yadda na ƙagu in ganta be kai yadda nake son ganin su Amal da Ramla ba, gashi seka rigani komawa da sati biyu"
Fahad yace "lallai ka tsunduma da yawa, nima ina son in koma inga Ramla, dukda ni muna waya da chatting da ita"
"Aishi yasa nake ta Addu'a, Allah ya bani Widad a matsayin mata"
Fahad yace "Hmm Allah dai ya baka me sonka"
***********************
Gaba ɗaya hankalin Hajiya Halima yaƙi kwanciya, gashi duk wanda ze kaiwa Alhaji Nasir ƙarar Widad to lallai zasu ɓata, ranar kwana na bakwai da tafiyar Yusuf, Hajiya Halima se sintiri take tsakanin part ɗinta da babban falo, Widad kam ko a jikin ta shagalin ta kawai take.
Yusuf ne yayi Sallama a falon, Hajiya Halima na zaune a falon tun safe ta kasa sukuni seda Yusuf yazo.
Abunda ya ɗaurewa Yusuf kai be wuce yadda yau ta sakar masa fuska ta amsa masa gaisuwar cikin mutunci ba.
Zeyi magana kenan yaji ƙamshin turaren Widad, wanda ya alamta masa ta fito falon, waiwayawa yayi ita ɗin ce kuwa cikin shigarta ta ƙananan kaya kamar yadda ta saba, bakin ta ɗauke da chew gum tana taunawa tare da lumshe ido, a hankali tana taku me ɗaukar hankali ta tako ta ƙarasa shigowa falon, ta samu guri ta zauna ba tare da tace komai ba.
Yusuf ya tako zuwa gaban kujerar da take zaune ya durƙusa a gabanta ze fara magana, katse shi tayi ta hanyar yi masa alama da hannun ta na ya zauna akan kujerar dake kusa da wadda take kai.
Seda ya ɗaga ido ya kalli Hajiya Halima sannan ya tashi ya zauna yace
"Ranki ya daɗe ga saƙon"
Ya miƙa mata ledar wayoyin da receipt ɗinsu da kuma ATM card ɗin. Tasa hannu ta karɓa, ta buɗe ta ciro wayoyin manya masu kyau, ta jujjuya su a hannunta sannan ta kalli Yusuf tace "can i have your phone?"
Kallon ta yayi, tare da yin sororo
"are you deaf?" ta tambaye shi tana tsare shi da ido.
Ciro wayarsa yayi daga aljihu ya miƙa mata, Android phone ce, dukda ba wata me tsada bace Amma hoton sane da Ummansa akan wallpaper ɗin wayar, seda tayi nazarin hoton na wasu seconds sannan ta buɗe wayar Yusuf ta cire sim cards ɗinsa da memory ta haɗa da sabuwar waya guda ɗaya, da tsohuwar wayarsa ta bashi sannan tace
"i want see you tomorrow by 9:am Insha Allah, you will get your salary alert today, you can leave"
"amma ranki ya daɗe, wannan wayar ai tayi min girma, kuma..."
Ai ko kallon inda yake bata sake yiba ta miƙe ta nufi part ɗin ta.
Gaba ɗaya hankalin Hajiya Halima akan Yusuf yake, Yusuf ya fita daga falon, ganin bashi da wani aikin da zeyi ya sashi ya ƙudure tafiya gida, yana ta ƙara jinjina kyautar wayar da Widad ta bashi.
Yayiwa su Nura Sallama ya fice ba tare da ya gaya musu abunda Widad ta bashi ba, yana cikin tafiya kafin ya kai ƙarshen layin aka sha gaban sa da mota, tsayawa yayi cak yaga waye wannan.
Ramla ce ta fito daga motar tana masa wani irin kallo, ta kalle shi a yatsine tace "Nasan zakayi mamakin ganina anan, saboda bakamata mace kamarni ta tsaya tana ɓata yawunta akan talaka mutum maƙasƙanci kamar ka ba, sedai ita kasuwar buƙata idan ta taso tamkar guguwa take bata da shamaki, magana nake so muyi da kai me mahimmanci, wadda zata amfaneka, idan ba zaka damu ba ina so ka shiga mota muyi magana"
"talakan mutum maƙasƙanci a gurin ki, amma wataƙila me matsayi a gurin Allah be cancanci ya shiga motar mace me girman kai da tinƙaho ko ince tagumi da haɓar wani ba, bana buƙatar dukkan wani abun Amfani da ze taso daga gare ki komai mahimmancin sa kuwa, a gurin Allah nake nema dan haka ki bar abunki koma menene kuma komai amfaninsa"
"karkayiwa kanka gaggawa, ƙarshe kazo kana cizon yatsa, da da nasanin fatali da abunda ya tunkaro ka kayi masa shinge da riskarka saboda girman kai na banza, talakan mutum me dakakkiya zuciya irinka, zuciyarsa cike take buƙatar samun damarmaki, dama irin wadda kowa ke lalube a duhu ko a sarari, katsam se gashi ka sameta a sarari, Amma ka kasa ƙafa kai fatali da ita, me yasa kayi hakan? "
"lokaci abune me mahimmanci a gurina, ina bashi mahimmanci fiye da yadda kike tunani, zefi kyau ki taƙaita wannan dogon surutan naki marasa amfani, a cikin taƙaitattun kalmomi kimin bayani gwari gwari kamar yadda Uwargida Widad keyi, hakan zefi min sauƙi, kuma ze adana lokacin mu".
Wani kallon banza ta watsa masa sannan tace "ko Uwargida ko ubangida wannan kai ta shafa, ni daban ita daban, dama ta sameka amma ka watsar da ita a yadda kake gaka matashi har matashi, kai dai ba muni ba kuma ba nakasa ba, a wannan shekarun naka da ƙirar da Allah yayi maka kamata yayi ace kana wani ɗan ƙwalisa meji da kansa, katsam sega shi ka ƙare a direba, direban ma maƙasƙanci, kana tuƙa ƙaramar Yarinya tana cin zarafinka yadda taso, bata ganin gjrmanka da aikin da kake mata, da kasan maƙudan kuɗaɗen dake cikin Account ɗin nan da tabbas baka dawo gidan nan ba, dan da kai da talauci har gaban Abada, ba kaiba har 'ya'yan ka da jikokin ka ba zasuyi talauci ba, sedai kash garin yin gwaninta kayiwa kanka mugunta"
Yusuf yace "har yanzu jira nake ki faɗi abunda kike tafe dashi, na gaji da sauraren wannan salon maganar taki me tafiyar kura, kiyi gaba kiyi baya kamar kema baki yadda da kanki ba"
"Babu batun rashin yadda da kai sedai ina so muyi tarayya gurin temakon juna ne, ina son ka gayamin password ɗin Widad ne na banki, nayi maka Alƙawarin samun wani gwagwaɓan sakamako indai kayi abunda nace, hakan ze zama madadin wannan shiritar da kayi nayin wasarere da damar daka samu, kuma ze baka damar samun 'yantuwa daga wannan aikin dakake ƙarƙashin wannan Yarinyar me Baƙar Aƙida"
Wani irin kallo Yusuf yayi mata sannan yace
"dukda kasancewa ta talaka maƙasƙanci kamar yadda kuke kirana, Yusuf yafi ƙarfin karɓar abunda zaku bashi saboda wannan baƙin aikin da kuke so inyi, ku tara dukiya da guminku seku yi barazana da ita ko tinƙaho, Bana danasanin aiki na ƙarƙashin Widad, duk inda tayi faɗa ko tsiwa to tabbas an mata ba daidai bane, shiyasa komai tayi take birgeni, kasancewata meyi mata aiki be sa naji cewar ni maƙasƙanci bane, kasancewata me aiki a ƙarƙashinta na sani ƙara samun ilimin rayuwa, dan haka kece maƙ
0 comments:
Post a Comment