Ta shiga ɗaki ta nemi guri ta zauna, tayi shiru tana tunanin yadda zata samu Anwar ya kuɓuta, babu zato taji an murɗa ƙofar ɗakin nata.
Mahaifinta ne ya shigo yana rarraba ido, gadan gadan yayo kanta yana faɗin "gidan ubanwa kika je?"
Miƙewa tayi a gigice ta shiga ja da baya tana faɗin "babu inda naje Daddy"
"ƙarya kike munafuka, harni zan saka doka ki sa ƙafa kiyi fatali da ita? Uwarki ta ɗaure miki gindin kiyi rashin mutunci ko? Ni da Daula waye ya haifeki?"
"Daddy niba gurinsa na je ba, Ai an ɗauke shi daga Asibiti"
Sekuma yayi sak, "Ubanwa waye ya gaya miki?"
"wallahi Daddy a gari naji"
"to gidan ubanwa kikaje? Zaki gayamin ko sena yanka ki a gidan nan?"
Girgiza kai take, takasa magana ya cakumo wuyanta yana zazzare ido, kakari ta dinga yi tana kuka tace "Wallahi Daddy ba inda naje, kawai gajiya nayi da zaman gidan na fita, dan Allah kayi haƙuri"
"se naci ubanki yadda idan na sake saka doka ba zaki takamin ba"
Cikin kuka Nurat tace "Wayyo Allah Mummy, ki temakeni karya kasheni"
Maimakon ya saketa sake shaƙeta yayi, yana kuma zaro mata ido kamar tsohon maye.
Kakarin Nurat ne yasa mahaifiyar ta, ta sallame salar da take, a guje ta rugo ɗakin Nurat, ta tarar ya shaƙe Nurat kamar ya kama sa'ansa ko kuma wani shahararren Ɓarawo.
"Kayi haukane, ka cikamin 'yata ita kaɗai ce dani, kana gani duk yaranmu mutuwa suke, ita kaɗai Allah ya barmin ka ƙyalemin' yata"
Juyowa yayi a fusace ya mangare mahaifiyar Nurat yace "itama ɗin gara in aikata inda waɗancn suka tafi, muddin zata dinga takemin doka, tasan a duniya bani da maƙiyi sama da Daula, danme zata dinga zuwa inda yake, akan me?"
Yai maganar tare da wurgi da Nurat, wadda tuni ta fara fita a hayyacinta, dan daya jefar da ita ko motsi ba tayi, se kokawa take da numfashi.
Da sauri Maman Nurat ta nufi kan Nurat, yayin da Alhaji Musa ya cigaba da banbami, ta ɗago Nurat sedai bata numfashi.
Cikin kuka tace "wallahi idan ka kashe min 'ya se nayi shari'a da kai, Kai kanka kawai ka sani, buƙata in ba ta kaba baka damu da kowa ba"
A fusace yace "Maza karki fasa yin shari'a dani, idan na kashe ta na kashe banza, duk son da nakewa mutum muddin ze bujiremin to zega ba dai dai ba tabbas"
Banza tayi masa, Taje ta buɗe fridge ta ɗakko ruwa me sanyi ta shiga shafawa Nurat, a hankali ta dinga sauke Numfashi, tana buɗe ido ta fashe da kuka tace "Mummy anya Daddy ne ya haife ni? Kalli yadda yayi yunƙurin kasheni me nayi masa haka?"
"kema da halinki Nurat, kin fiye taurin kai, na hana ki wannan abun da kike amma kin kasa ganewa, gashi ze kashe ki a banza"
Shiru Nurat tayi, tabbas tunda mahaifinta yake yunƙurin kashe ta akan taje inda Daula yake, to tabbas wani mummunan abu yake aikatawa, kuma na abunda baze iya aikatawa akan kowa ba.
Lumshe idon ta tayi tana jin yadda ƙirjinta yayi nauyi, wani irin baƙinciki ya mamaye zuciyarta.
Shikuwa Alhaji Musa yana komawa ɗaki ya shiga sintiri, kamar yadda ya zame masa jiki a 'yan kwanakin nan, ba shi da nutsuwa sam, musamman da' aka ce su Widad sun gudu daga inda aka sace su, gashi sunsa a nemo su a ko'ina suke amma abu ya gagara.
Gashi yanzu wata maganar rainin hankali da ta taso, wai an sace Daula akan gadon Asibiti, 'Anya ba wani rainin hankalim su Alhaji Haruna suke shiryawa ba?'
A hankali Widad ta buɗe ido daga baccin da yayi awon gaba da ita, taga Yusuf ya jingina da jikin bango ya lumshe idanunsa, hannunsa ɗaya yana wasa da gashin kanta, a hankali tayi miƙa tare da hamma, da sauri ya buɗe ido yana jera mata sannu.
Ba tace komai ba se jinjina masa kai da take.
Miƙewa tayi zaune, se kuma yaga ta yamutsa fuska.
Kallon ta yayi da sauri yace "lafiya dai?"
Ɗan tura baki tayi tace "am not confortable at all, ji nake kaman am stain"
Yusuf yace "kiyi haƙuri insha Allah, zan san yadda zanyi a samo miki wancan da kike amfani da shi"
Widad tace "baza a samu wanda nake amfani da shi ba, sedai a siyomin kowanne ne, bana son wannan abun da nake using dashi yanzu, is so much irritating"
Yusuf yace "Shikenan, Insha Allah zan san abunyi"
"Sannan kuma..." se kuma tayi shiru
"sannan kuma me?" Yusuf ya tambaya
"Nasan baza'a samu shaving cream ko powder ba, a siyomin shaver please"
Cike da son ya kunnata Yusuf yace "shaver kuma, me zakiyi da shaver?"
"Abunda kake yi da ita" ta bashi amsa cike da tsiwa
Yayi murmushi yace "Aini gemuna nake askewa da ita"
Ta kalle shi ta ɗan tsuke baki tace "Nima nawa gemun zan aske"
Aikuwa Yusuf ya kwashe da dariya, sosai yadda tayi magana da abunda ta faɗa ɗin ya bashi dariya, kallonsa take yi yadda dariyar tayi masa kyau.
"wallahi idan ka ƙware ba ruwana"
Tai maganar tana shirin Miƙewa, ya kalleta yace "Ina zaki?"
"tsakar gida nake son fita"
"Amma kin manta halin da kike ciki ne?"
"To zama zan tayi ina kallonka, ni na gaji da kwanciyar ma, zan kula sosai"
Yusuf yace "Aini bana gajiya da kallon kyakkyawar fuskar nan taki, muyi zamanmu a ɗaki nima na iya hirar se in miki, kuma baki ci Abinci ba, ko kin manta?"
'ƙyale Abincin nan, ni idan ina period bana son Abinci sosai "
Yusuf yace " dama can haka kike, ina lura dake tarkace kawai kike ci ba Abinci ba, so nake ki ƙara Ƙiba ki daure kici ko kaɗan ne mana"
"Ni gaskiya, ba irin wannan nake so ba"
"wanne kike so" ya faɗa cike da kulawa.
Ɗan tsura masa ido tayi, sannan tace
"Bari dai inci kaɗan"
Ya ɗakko kwanon dambun ya ajiye mata, tasa cokali ta fara ci, dambun tsaki ne amma yaji gyaɗa da zogale yayi daɗi Sosai.
Widad tace "tunda nazo ƙauyen nan, ban taɓa cin Abinci me daɗin wannan ba"
Yusuf yayi murmushi yace "harda bredin jiya?"
Widad tace "hmm dan dai kar kaji haushi ne, amma gaskiya bredin nan ya daɗe a ajiye, se marmashewa yake ba daɗi"
Yusuf yace "dagaske ba kya son inji haushi?"
Ɗan kallonsa tayi tace "No i mean banyi niyyar magana ba lokacin shine kawai, ka ɗakko spoon muci Abinci mana"
Yusuf ya girgiza kai yace "A'a kici kawai, idan kin rage se inci"
Widad tace "meyasa? Ai ze ishemu"
Yusuf yace "bana son in samiki yawuna a jiki, naga bakya son hakan"
Ɗan tura baki tayi, cikin ƙunƙuni tace "na nawa kuma, ƙarewa ma ai Yawun naka ka samun a bakina jiya"
Yusuf yace "ai bazan manta wannan moment ɗinba, nayi kissing ɗin gimbiyata the most memorable moment in my life"
Widad tace "tabbas kam, ka kafa tarihi, kayi abunda wani mahaluki be taɓa gangancin gwadawa ba, kayi min abunda ban taɓa zaton wani zemin in ƙyaleshi ba, hmm ban san meyasa kake min abubuwa son ranka ba, ƙyaleka kawai nake"
"Are you sure babu wanda ya taɓa kissing ɗinki seni?"
Watsa dambu tayi a bakinta, ta ja wasu seconds sannan tace "Idan an taɓayi kana tunanin zanji tsoron ka ne? Ban taɓa shan yawun Ƙato ba se a kanka, kuma bashi ka ɗauka, tunda kasa na haɗiye yawunka"
Murmushi Yusuf yayi yace "Yaushe ne ranar biyan bashin?"
Banza tayi masa taƙi ko kallon inda yake, can Yusuf yace "Amma meyasa kike zuwa Clubs da kuma Hotel?"
Jin tambayar tayi a bazata, take taji tana kokawa da dambun dake bakinta, gaba ɗaya Mood ɗinta ya canza a hankali tace
"ai tun a lokacin na gaya maka me nake zuwa yi, na gaya maka ni karuwa ce kamar yadda matan gurin suke"
Haɗe rai Yusuf yayi yace "Kamar yadda bakya son ƙarya, na tabbata kema bakya aikata ta se bisa kuskure, meyasa zaki gayamin haka? Ko kina son zuciya ta ta buga ne?".
"Tunda baka yarda ba shikenan, amma kasan dai bazan zauna ina rantse maka dan ka yarda dani bako?"
Ta ajiye spoon ɗin Abincin ta je ta sha ruwa, tayi waje abunta ta bar Yusuf a gurin a zaune.
Roƙon Allah ya shiga yi akan Allah yasa abunda Widad ta faɗa ƙaryane, dan ba ƙaramin kishi yaji ba, kuma yasan halin ta ko meye zata yi ƙoƙarin gaya maka gaskiya, ko ta maka daɗi ko akasin hakan'
Tana fitowa Gwaggo tace "Amarya kin ware kenan?"
Widad tace "eh Alhamdilillah"
"Masha Allah, haka nake son ji"
Hari tace "Wai meya same ki ne?"
Widad tace "Kaji Baba Harin nan, sekace kin damu dani, bayan ko gani kika yi zan mutu murna zaki yi, to ciwon yara nake bana tsofaffi ba dan haka base kinji ba"
Aikuwa a fusace Hari tace "karki ƙara cemin tsohuwa, ta ina nayi miki kama da tsohuwa? Da ƙuruciyata dudu shekarun nawa ba zasu gaza Ashirin da shida ba, amma kike kiramin tsufa"
Ai gaba ɗaya wanda ke tsakar gidan ba wanda be dariya ba, Widad tace "A'a kin manta a zanin goyo kike ma ƙarewar yarinta, harfa jikokine dake amma kice shekarar ki Ashirin da shida, shekarar ki biyar akamiki Aure kenan"
Hari tace "koma yane dai, niba tsohuwa bace ba ehee, dan jina nake garas kamar 'yar shekara goma sha shida"
Widad tayi dariya tace "dama zaki dinga gayune, za kiga yadda zaki koma yarinya sharaf, amma indai baki dena ƙazanta ba, to tabbas wataran za' a kalle ki ace shekararki sittin da 'yan kai"
Hari tayi kicin kicin da Fuska, dan Widad ta fara kaita bango, idan ta cigaba da biye mata to tabbas za suyi ba daɗi, dan haka tayiwa Widad banza.
Widad ta ƙarasa inda Hindu ke tsinke zogale ta zauna tace "Hindatu, ya ki keyi? bari in tayaki"
Hindu Ta gwadawa Widad yadda ake tsintar zogale, ta zauna suna yi tare.
Can Widad tace "Hindu, wai kuma idan kuna period bakwa amfani da pad ne? Se tsimma"
Hindu tace "meye kuma firiyios?"
Widad tace "A'a ba kije makaranta bane? Me yasa Common things idan na faɗa, seki ce baki sani ba?"
Hindu tace "bari Amarya wallahi muna son karatun nan, amma ba yadda muka iya ne, kinga inda muke zuwa makarantar furamarai can wani ƙauye ne, kusan ƙauyuka biyar duk ita muke zuwa, to guri ba kusa ba nisa kafin kaje duk anyi wani abu baka nan, lokacin damuna kuwa bama samun zuwa, sannan akayi ruwan Sama me ƙarfi ya kwashe kwanon da'aka rufa azuzuwa, ai kuwa akace mu dena zuwa se an gyara, dan haka tun aji huɗu furamarai nidai na dena zuwa har yanzu "
Widad tayi shiru, ita ko a tatsuniya bata taɓa jin wannan al'amarin ba, ace a Nigeria akwai 'yan ƙasa wanda basa samun ilimi, ina wakilansu? Meye amfanin shugabannin da suka zaɓa suka wakilta dan suyi musu aiki? Ace ƙauyuka huɗu su dogara da primary ɗaya, kuma shima se sun sha baƙar wahala kafin suje, dole abun ya fita daga ransu'
Widad tace "gaskiya banji daɗi ba Hindu, ai Ilimi shine mutum, tabbas da'a bakin wani naji cewa zanyi ƙarya ne labarine kawai"
Hindu tace "aikuwa gashi a zahiri kinji, shiyasa duk muka haƙura wasu suka kama talla har zuwa lokacin da mace zata samu miji tayi Aure, dama idan kana karatun wasu kallon ɗan iska suke maka, muka koma zuwa ta Allo ta Allonma gata nan dai nidai na samu nayi izu biyar na haddace itama munyi yawa, babu wata kulawa yadda yakamata, dan anan wajejenmu makarantar Allo ɗaya ce"
Widad ta jinjina kai tace" to sauran litattaafai fa, kamar Ahlari, fiqhu hadisan manzon Allah salallahu alaihi wassalam, suma ana koya muku? "
Hindu tace" Taɓɗijan, Al'qur'ani kawai ake koya mana a makarantar Allo, kuma shima mun dena zuwa, se Baffanmu ne dai da yana koya mana Alhadisin Auwwalu, shima yace mana Babansa ne ya koya masa, kuma ma yanzu duk mun manta tunda shekarun da yawa "
Widad kawai tayi tagumi tana sauraren Hindu, tana jin kwamacalar da ko a Film bata taɓa ganin irinta ba, yanzu dama da irin wannan mutanen suna rayuwa a haka, amma ake samun mutanen da suke wawashe dukiyar al'umma, a 'ya' yan sanatoci akwai wanda tasan ana biya musu ku&in makaranta na secondary naira milyan uku, duk term miliyan ɗaya, iya 'yan tsirarin' ya'yansa, amma ga dubunnai zaune a gida babu arabi babu boko, irin wannan ne idan suka faɗa harkar ta'addanci basa imani sam.
Hindu ta kalli Widad tace "ya naga kinyi shiru ne?"
Widad tace "Mhmm bakomai"
Hindu tace "Yawwa, dan Allah meye Firiyas ɗin da kika ce?"
Widad tace "Period nace, ina nufin jinin Al'ada"
Hindu tace "Auho ai ban gane ba, seki cemin baƙon wata, ai mu da tsumma mukeyi, mu yayyanka tsumma semu dinga amfani dashi, duk wanda muka cire se mu wanke mu ninke"
Widad ta kalleta da sauri tace "ku wanke me?"
"tsimmar mana, idan ɗan kamfan mutum ɗaya ma haka ze haɗa duk ya wanke, ya ɗan jira ya bushe seya sake mayarwa"
Dafe kai Widad tayi, tayi shiru ta shiga duniyar tunani, ta tuna yadda take fantamawa a cikin kuɗi, babu abunda ta nema ta rasa a rayuwar ta, Kama daga Abinci, sutura abun hawa gurin kwana, har wasu kuɗi ne da ita na musamman wanda take kula da dabbobinta kawai, tayi kyautar mota, tayi kyautar gida ta bada kuɗi kamar aikin banza, ashe akwai bayin Allahn da sun fidda rai da samun wani jin daɗi.
Hindu tace "Amarya, Allah yasa ba wani abun na miki ba, naga kin ɓata rai?"
Widad tace "bakomai Hindu, mu cigaba da aikin kawai"
Widad bata iya tsinkar zogalen ba, dan haka wani yanayi wani kuma harda kararen jiki take zubawa, Hindu bata damu idan Widad ta zuba a haka se tabi tana gyarawa.
Hanne ce ta taho a fusace tasa hannu ta ɗauke robar da suke tara zogalen tace "Aikin banza, ke Hindu kin san ba abunda ta iya kawai kin ɗauki abu kin bata kinsa se ɓatawa mutane take, tana mayar mana da aiki baya kin zauna se surutan shirme ki keyi, da yanzu an wanke an ɗora amma duk ta ɓata mana"
Hindu tace "Haba Hanne, to ba a hankali zata iya ba, kuma ai tayani take tana yi ina gyarawa, meye a ciki dan munyi tare"
Tsaki Hanne Tayi, tai gaba da robar zogalen, Widad ko ɗaga kai ba tayi ba balle ta kalli Hanne, tayi shiru ba tace komai ba.
Cikin damuwa Hindu tace "dan Allah Amarya kiyi haƙuri, ni ban san meyasa take wannan abubuwan ba"
Widad tayi murmushi tace "Ni banyi fushi ba ai, bakomai"
Saleh ya ɗau waya ya kira Abbas, sedai har tayi ringing ta katse be ɗaga ba, tana katsewar ne Abbas ya biyo kiran, Saleh ya ɗaga tare da yin Sallama Abbas ya amsa, Saleh yace
"Malam Abbas, kayi gaba ko waiwaye baka yi, kana da labarin an sace amininka kuwa tare da 'yar gidan Daula?"
Abbas yace "ƙwarai kuwa na sani, dan nine ma na gayawa mahaifiyarsa"
Saleh yace "Wani tunani kayi akai kuwa?"
"wani tunani zanyi kuwa, maganinsa kenan ai, shegen shishshiginsa da rawar kai yaja masa, ni Allah ne ya dube ni, dani naso in maye gurbinsa da dani za'a ɗauke, Amma kuwa an karɓi files ɗin daga hannunsa?"
Shiru Saleh yayi sannan yace "basu karɓa ba tukuna, ni suke jira, har yanzu basu san cewar Yusuf ne jami'in tsaron ba, zancen da nake maka yanzu haka Yusuf sun tsere daga inda aka ɓoye su"
Abbas yace "haba dai, garin yaya akayi suka tsere? Kai Yusuf fa ba ƙaramin hatsabibi bane ba"
Saleh yace "babu wanda ya sani, kuma har suka gudu ba'a samu karɓar abun nan daga hannun yarinyar ba, yanzu maganar da nake maka, shi kansa Daulan an ɗauke shi a gadon Asibiti, babu wanda yasan inda yake"
"Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, garin yaya, yanzu shikenan munyi biyu babu, nifa ba wanda yake tuntuɓata yanzu tunda akamin transfer"
Saleh yace "karka damu, ina son ka saurareni da kyau, duk abunda ake ciki zan dinga sanar da kai, karka kusakura wani daga cikin su yayi yunƙurin haɗa kai da kai, dan yanzu gaba ɗaya kawunansu a rarrabe yake, duk wanda ya tuntuɓeka koya tambayeka wani abu game da wanda aka bawa binciken nan kace baka sani ba"
Abbas yace "to aini basu sanni ba, kai suka sani me zesa su nemeni?"
"Abbas mutane ne masu wayo matuƙa, yanzu haka a manyanka na gurin aiki wani ze iya bugun cikinka ya tambayeka wani abu, karka kuskura ka gaya wani, wani abu akan harkar nan, na gaya maka kansu ya rarrabu, wasu zasu iya zamewa suyi harkar nan babu mu, bayan wahalar da mukayi "
Abbas yace " bakomai na fahimce ka, Insha Allah babu wanda zeji wata magana daga bakina, dama kai ka jawoni cikin harkar "
Saleh yace " Good nagode "
Sukayi Sallama, Saleh ya jinjina kai yanzu ya sake jinjinawa Widad, lallai bata da laifi naƙin yadda da mutane, ƙir ƙiri Abbas na jikin Yusuf ne, amma saboda kuɗi yake masa zagon ƙasa, tabbas mutum abun tsoro ne, kuma da alama Abbas Soko ne, dan haka yi masa wayo ba wani abu bane me wahala.
Saleh yana son sake komawa gurinsu Widad, dan haka yana ta ɗanyi musu siyayya.
Alhaji Musa ne ya kira shi a waya yace 'lallai yana son ganinsa a guest house ɗinsa'
Haka Saleh ya bar abunda yake yi ya tafi gidan Alhaji Musa.
Yaje ya tarar dashi a lambun dake gidan, suka gaisa Alhaji Musa yace "Saleh ina cikin damuwa fa"
"wace irin damuwa kuma ranka ya daɗe?"
"Na fuskanci Nurat tana ƙoƙarin fara yin shisshigi ga al'amuran Daula, gashi yanzu ina ɗari ɗari da su Haruna, ina tsoron Ayi Amfani da ita a cutar da ita koni, yanzu babban abunda ya sake bani mamaki be wuce yadda Daula yayi ɓatan dabo ba, ko kusa ko alama an rasa inda yake, zargina yana ƙara tabatta akan ana min maƙarƙashiya, kodai su Alhaji Haruna suke cuta ta suke al'amuran su suka ɗai, kokuma akwai wani a gefe daya ke harin abunda muke hari, ko kuma yasan siriinmu yake son temakawa Daula"
Saleh yayi ajiyar zuciya yace "banƙi ta taka ba, Amma ko waye wannan tabbas na jikin ku ne, amma abun da mamaki ace an nemi Daula ko sama ko ƙasa an rasa sekace wata takadda"
"Shine abunda ya ɗauremin kai ai, ni yanzu gefe zan koma in nemawa kaina mafita, idan abun nan ya samu shikenan, in be samu ba shikenan, suma har yanzu da suka gudu babu wanda ya sake jin ɗuriyarsu, dan haka ni inaga tunda babu wanda yasan inda Daula yake, zan fito takarar Senate ne kawai "
Da sauri Saleh ya kalle shi yace " Amma ta yaya kake tunanin mutane zasu yarda su zaɓeka? Bayan Daula ya riga ya ɓata siyasarka a idon duniya? "
Alhaji Musa yace " shiyasa nima na ƙuduri aniyar kota wane hali, sena Wulaƙanta Daula a idon duniya, sannan malamai zan shiga a rufemin bakin jama'a, akwai yarana da suke aiki a wasu daga kamfanunukan Daula, zamu haɗa kai dasu mu karkatar da wasu kuɗaɗe inyi amfani da su, niba kuɗin Daula ne sjka dameni ba, yadda zan Wulaƙanta shi in ɗaiɗaita shine ya dameni, amma ko yanzu na rage raɗaɗin dake zuciyata, kuma zan cigaba da bibiyarsa se naga babu inda ya rage wanda ze jingina yaji daɗi, sannan in dawo kan su Alhaji Munir"
Yadda Alhaji Musa ke maganar babu alamun tausayi ko imani a tare da shi, har zuciyarsa yake faɗar wannan maganganun.
Saleh ya ɓoye duk mamakinsa, ya dinga ziga Alhaji Musa, Alhaji Musa ya kawo kuɗi ya bawa Saleh, Saleh a ransa yace "ka bada kuɗin da zanyiwa maƙiyan ka siyayya, kuma nima zancigaba da bibiyarku, ɗaya bayan ɗaya sena ɗau fansar cin amanata da kuka yi, da saɓa Yarjejeniyar da muka yi daku"
Widad gaba ɗaya hirar da suka yi da Hindu ta tsaye mata a zuciya, ta tuna yadda haka siddan se ɗan kasuwa yayiwa ɗan siyasa kyauta motar miliyoyi, ko biliyoyin nairori, Amma al'ummar su suna tagayyara, da yunwa da rashin kyakkyawan mahalli.
Yusuf yaga gaba ɗaya Widad tayi wani iri, seta zauna tayi shiru tana tunani, dukda shima zuciyarsa ba daɗi, Amma sam baya son ganinta a damuwa dan haka yace "Ran gimbiyata ya daɗe meke damunki ne?"
Jiki a sanyaye tace "Abubuwa da yawa"
Yusuf yace "Kamar me? Ko har yanzu fushin kike dani"?
Jiki a matukar sanyaye ta bashi labarin hirar da suka yi da Hindu, daga ƙarshe tace "tabbas ƙaddarar data sameni na zuwa ƙauyen nan, ishara ce Allah ya nunamin, na rayu cikin gata wanda nake ganin babu wani abu da zan iya nema in rasa a rayuwata, ranar da kace min akwai mutanen da Naira ɗari take gagararsu, gani nake kawai ka faɗane dan ka rainamin hankali saboda a lokacin, abun da ke cikin asusun bankina ya ninka ɗari sau ɗari, bani da wata damuwa ko matsala, Amma ace a rayuwa akwai tarin 'ya' ya mata da suke zaune ba ilimi? Akwai tarin mutanen da suke rayuwa da gurɓataccen ruwan sha? Akwai tarin yara manyan gobe da rayuwarsu ta lalace saboda rashin gurin samun ilimi, Yoseef yaran masu kuɗi na Almubazzaranci da dukiya, da yawanmu bamu san yadda aka tara kuɗin ba... Kasa ƙarasawa tayi gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, wani irin ɓacin rai ke taso mata, yadda ake ɓarnar kuɗi gurin bukukuwan birthday dana Aure, da makamantan su.
Yusuf ya taso daga inda yake, yazo ya samu guri ya zauna kusa da ita yace "Widad baki ga komai ba, a yanzu haka a cikin ni'ima muke, a gidan megari muke a zaune, kuma gidansa da rufin Asiri, ya kike tunanin gidajen sauran talakawa da suke garin nan?
0 comments:
Post a Comment