Da sauri Yusuf ya koma gurin partyn ba tare da fargabar komai ba ya shiga kutsawa yana neman Widad, amma babu ita babu alamar ta a gurin, can ya hango Nurat tana ƙoƙarin fita, seda ya bari ta fito daga gurin party, sannan yabi bayan ta a guje ya sha gaban ta, seda ta tsorata da ganin sa ta ɗan tsaya ta kalle shi tace "Are you ok?"
"Ina Widad?" ya jefo mata tambayar
"ban sani ba na barta akan stage tana rawa" tai maganar cikin wata irin gurɓatacciyar hausa.
Subhanallah shine abunda Yusuf ya furta, yai gaba yana sake duba gurin.
ba zato ba tsammani ya shammaci Nur ya fizgota ya shiga cikin duhuwar flowers da ita, yasa hannu ya shaƙeta, ya kalle ta a hasale kamar wani mahaukacin zaki yace
"Ko ki gayamin gaskiya ko kuma zan fita dake daga gurin nan, zan riƙe ki a matsayin garkuwa harse Naga Widad, idan kuwa rayuwar Widad ta salwanta taki ma ta salwanta, ki gayamin ina take?"
Yai maganar cikin ɗaga murya tare da shaƙe Nurat.
"Dan Allah, please don't kill me I will tell you, please secure my life"
"Your life will be secured if you tell me the truth" ya faɗa yana zare mata ido
Cikin kokawa da numfashi tace "Ok zan gaya maka, Dad ne yasa aka busa mata wani abu, yanzu tana harabar gurin nan a ɓoye, wasu zasu zo su ɗauke ta, idan baka hanzarta ba komai ze iya faruwa"
"Meyasa Mahaifinki yake ƙoƙarin sace ta?"
Cikin kuka tace "I sure to the Almighty ban sani ba, trust me"
Tasa Nurat yayi a gaba ta nuna masa ƙarƙashin bishiyar da aka ajiye Widad, tana kwance helplessly a ƙasa, unconscious kaman babu rai a jikin ta, ga jakar ta a gefen ta.
Ya waiga ba kowa a gurin, Yasa hannu ya sunkuce ta ya tafi da ita motar su da sauri, ya buɗe bayan motar ya kwantar da ita, yaja motar da gudun tsiya ya bar gurin.
Da gudu Nurat ta koma cikin gidan su tana haki, da yake hall ɗin party a cikin gidansu yake, ɗakin ta ta tafi kai tsaye ta shige banɗaki tana sauke numfashi, ta wanke fuskarta, ta buɗe fridge ta sha ruwa me sanyin gaske, sannan ɗakko wayarta ta kira layin mahaifinta.
Seda ta kusa tsinkewa sannan ya ɗaga yace
"Yaya i hope everything is going according to how it's planned?"
Cikin rawar baki tace "No Daddy something is going wrong"
Cikin sauri yace "meya faru?"
Cikin Rawar Murya Nurat tace "Daddy basu ƙaraso da wuri ba, nayi abunda kace Amma..
" Amma me? Ki gayamin menene? "
" Daddy ita da wani tazo, nayi abunda kace, but someone intimidate me, yace in ban faɗi inda take ba ze kashe ni"
"Waye shi?" ya faɗa a fusace
"Ban sani ba Daddy, Amma tare suka zo"
"Wace irin wawuya ce ke haka? Kinsan lokacin dana ɗauka ina wannan shirin? Idan wasu suka rigani mallakar Abun nan mun kaɗe"
"Daddy ba laifi na bane, laifin wanda ka turo su ɗauke ta nefa"
"Shut up, kin ɓata min shiri kina gayamin maganar banza"
"Am Sorry Dad is not my fault, but....
" Common Keep quiet " ya faɗa a Hasale, tare da katse wayar yana tsaki, tabbas ba dan wawancin nan 'yar cikin sa ce ta aikata masa ba da ba abunda ze hana yasa a Kashe ta.
A fili Yace
"dole in toshe duk wata kafa da zesa su Alhaji Haruna su san nayi yunƙurin sace Yarinyar nan ni kaɗai, kuma dole in gano wane yaron ne suka je gurin tare"
Yusuf kam gudu yake bana wasa ba, ya dinga kauce wa dukkanin hanyoyin da zesa ya haɗu da cunkoson ababen hawa, ko kuma jam'ian tsaro, be sassauta da gudu ba seda yaga ya shigo layin su Widad, a hankali ya ƙara sa tuƙin yana zuwa ƙofar gate ɗin ya saki wani irin horn me gigitarwa, duk a ƙoƙarin sa na ganin ya kai Widad gida lafiya.
A gigice Isa ya buɗe ƙofar dake jikin tangamemen Gate ɗin ya leƙo ya fara masifa "haba Yusufa, wannan wani irin horn ne kaman me shirin sanar da tashin duniya"
Cikin harzuƙa Yusuf yace "Open the Gate"
Dukda Isa ba turanci yake ji ba amma ya gane Yusuf na magana ne akan ya buɗe masa ƙofa, Cikin Sauri Isa ya buɗe masa Gate Yusuf ya shiga da motar yayi parking, ya sakko da sauri daga cikin Motar ya buɗe inda ya Kwantar da Widad, har yanzu bata hayyacin ta, Yasa hannu ya ɗakko ta tareda Jakar ta ya nufi Cikin gidan da ita, Isa ya biyo bayan sa da Sauri yana ƙasa da murya cike da gulma yake Faɗin
"Yusufa meyasami Uwar ɗakin naka kuma? Kodai Shaye2 tayi ne? Naganta kamar a buge"
Cikin tsawa Yusuf yace "Idan ka ƙara taku ɗaya daga inda kake zan ɓata maka rai"
Gaba ɗaya Isa mamaki ya kama shi yadda Yusuf ɗin ke wani magana cikin Izza da isa.
Babu kowa a babban Falon dan haka Kai tsaye part ɗin ta ya nufa da ita, Ya kwantar da ita akan gadon ta.
Yasa hannu a aljihunsa, ya ɗau wayarsa ya kira Abbas, bugu ɗaya ya ɗauka yace
"Kai ya haka? Zaka kirani a wannan daren?"
"Kai akwai matsala fa"
"Matsalar meke nan?"
"Widad na kai gurin birthday akayi barazanar za'a kasheni idan ban bar gurin ba, ina komawa na neme ta na rasa, da ƙyar na ganta, yanzu haka na dawo da ita gida Amma bata san inda kanta yake ba, I thinks they Use sedative substance on her, nayi niyyar in tsaya da ita a Asibiti Amma naga hakan hatsari ne babba"
Abbas ya numfasa yace "Gaskiya kam zata farfaɗo Insha Allah, gobe in Allah ya kaimu ka shigo Office kawai za muyi magana"
"Shikenan Allah ya kaimu" suka yi Sallama, ya maida Wayar Aljihunsa ya kalli Widad da take ta bacci bata san meke faruwa ba se sauke numfashi take, Yusuf ya ɗauki bargon dake gefen ta ya rufe ta dashi saboda yanayin Sanyi, wayarta ce keta ringing a Jakarta ya buɗe Jakar ya ɗakko wayar ya kashe ta gaba ɗaya, Sannan ya kama hanyar fita.
Yusuf ya fito ya nufi hanyar fita, yaci karo da Ramlah a babban falo, share ta yayi ze wuce.
"Daga ina kuke a daren nan? Me kake a ɗakin Widad a wannan lokacin?" muryar Matar gidan ce, dake tsaye a ƙafar bene.
Yusuf ya juyo ya kalle ta sannan yace "Na kaita unguwa ne"
"Me kake a ɗakin ta a wannan lokacin? Bata da lafiya ne, na kaita ɗakin ta ne"
"Ka kaita ɗakin ta kai a wa?" Ramla ta tambaye shi.
"Ni ba a kowa ba, ni a ɗan uwan ta musulmi, kuma ma'aikacinta"
"Kai shashasha rufemin baki" Hajiya Halima ta katse shi cikin tsawa.
"Naga kanka yana rawa, to bari in tuna maka kai ba kowa bane face matsiyacin talaka, ka dena jin kanka kamar wani me iko dan kaga mai gidan nan yana wani baka girma na musamman kai ɗin ba kowa bane ba"
Amal da take jiyo hayaniya ta fito daga ɗakin ta, tana zuwa ta tarar da mahaifiyar ta ta saka Yusuf a gaba tana zagin sa
"Haba Mummy, me Yusuf yayi miki kike masa wannan cin mutunci haka?"
Ramla tace "An zage shi ɗin, meye alaƙar ki dashi? Ɗan uban waye shi da ze dinga wani jin kansa, dan yaga ya samu gindin zama, saboda tsabar cin fuska akan wannan banzan waccan mara mutuncin ta dizgani"
Yusuf ya ɗan murmusa yace
"Nasani niba kowa bane, talaka ne ni gaba da baya, dan haka ku kwantar da hankalin ku,kuma ni bana sawa kaina ni wani ne" yana gama faɗin haka ya juya ya fice.
Amal tace "Mummy koma menene laifin Widad ne, ni banga abunda Yusuf yayi ba"
Hajiya Halima cikin tsawa tace "dalla rufemin baki banza, naga zaƙewar ki kema tana yawa akan yaron nan, ki shiga hankalin ki tunda wuri, ni sam yaron nan be minba, ya fiye kalar munafukai"
Ramla tai caraf tace "wallahi kuwa Mummy, ni kaina ban yadda dashi ba, Ina jiran sakamakon binciken da kika sa ayi a kansa ne"
Amal tace "Mummy koma menene Yusuf bare ne aiki ne ya kawo shi gidan nan, bekamata a saka shi a wannan sabgar ba"
"Amal kenan ke har yanzu yarinya ce, baki san inda rayuwa tasa gaba ba, kashedina dake shine, tun wuri ki fita daga sabgar yaron nan, dan muddin na gano wani abu saɓanin abunda nayi zato a tattare dashi ba abunda ze hana insa ayi masa abunda ya dace da shi"
"Amma mum....
"Ke rufemin baki, shashasha kawai"
Mummy tayi maganar tare da juyawa zuwa ɓangaren ta, Ramla ma tabi bayan ta suka bar Amal a falon tsaye.
Yusuf na fitowa, Nura ya biyo shi yace
"A'a kaga ɗan gatan 'yar masu gida, gaskiya Yusuf ka ciri tuta, naga' yar masu gida tana yi da kai, ƙiri Ƙiri ta koreni kuka tafi unguwa, naga duk inda zaka tare kuke tafiya"
Kafin Yusuf ya bashi amsa, Isa mai gadi ma ya nufosu yana cewa
"Nikam Malam Yusuf baka gayamin meyasami Uwar ɗakin ka ba, nifa abun ya bani mamaki, iya sanina dai bata shaye2, sedai taɓun hankali amma meyafaru da ita haka?"
Kallon su yayi ɗaya bayan ɗaya yana karantar tsantsar munafunci da son jin gulma a fuskokin su, sharesu yayi bece musu komai ba yai gaba abunsa ya fice ya bar gidan.
Yusuf na fita, Nura yace
"Ji shi se kace ɗan uban wani, muna masa magana amma yayi mana banza, da Alhaji ne uban sa bansan wulaƙancin da ze ba"
Isa yace "Bar mara mutunci, ji yadda muna masa magana ya share mu, Anya Nura mutumin nan ba Asiri yayi wa me gidan nan ba?"
"Ni zance maka Asiri yayi masa hadda 'yar sa ma, kana gani ɗazu ta hana Ramla binsu saboda shi, da muka dawo daga filin jirgi se cewa tayi ni in sauka in hau motar haya in tafi gida, shi kuma ya kaita unguwa"
Isa ya jinjina kai yace "Kana gani duk jin kai da izzar ta, duk Aƙidar ta ta rashin yadda da mutane Amma duk inda zata tare dashi suke tafiya, dudu yaushe yazo gidan nan? Ko wata ɗaya be cika ba ya samu wannan gindin zaman, mu kuwa shekara nawa muna aiki a gidan nan? Ba abunda yake haɗamu da ita se cin mutunci da wulaƙanci "
Nura yace "to ai magana ce a buɗe, Allah kaɗai yasan abunda suke yi"
Isa yace "kuma fa hakane zancen ka Nura, taɓ aikuwa zamu ƙara saka ido sosai, zamuyi maganin wannan gani-ganin da yake mana"
Haka suka zauna suka cigaba da gulma, suna muzanta Yusuf da miyagun kalamai.
Yusuf kam kansa ya kulle Sosai, daya koma gida ma kasa bacci yayi, yana ta nazari akan abubuwa da dama yana son gano bakin zaren amma ya rasa ta ina ze fara, gaba ɗaya Al'amuran a cukurkuɗe suke, me zesa Baban Nurat yunƙurin sace Widad? Waye mahaifin Nurat? Dole Akwai dalilin da yasa Widad take da wannan AƘIDA na ƙyamar talaka da nesanta kanta da mutane, yanayin Abubuwan da take yi wasu lokutan yasa Yusuf ya fara gazgata cewar tana da taɓin ƙwaƙwalwa, tunani ya haɗu ya cunkushe massarafar gangar jikinsa wato ƙwaƙwalwarsa, ba shiri ya tsagaita tunanin ya kwanta da ƙudurin dole yaje Office da safe, akwai buƙatar yaga Abbas.
A hankali ta motsa daga nannauyan Baccin da take, ji tayi kanta kamar an ɗora mata wani nannauyan dutse, gaba ɗaya gaɓoɓinta sun mata nauyi, a hankali ta buɗe idon ta ta ƙarewa ɗakin nata kallo, ta mayar da idanunta ta lumshe na wasu daƙiƙu sannan ta sake buɗe su, a hankali taja jikin ta ta miƙe zaune, kallon jikin ta tayi tare da ƙoƙarin son tuna abunda ya faru, sosai take takura ƙwaƙwalwarta don ta tuna mata abunda ya faru, Amma fafur ta kasa tuna komai, dafe kanta tayi wanda taji yana sara mata, ta miƙe jiri na kwasar ta ta tafi banɗaki.
Da sassafe ko karyawa Yusuf beyi ba ya fito ze fita. Umma dake kitchen tana ƙoƙarin haɗa Abinci ta leƙo tace
"Yusuf me zan gani haka? Ba zaka tsaya ka karya bane?"
Yusuf yace "Umma sauri nake ne, bana son in makara akwai aikin da nake son yi"
"Yusuf nifa gaskiya wannan aikin da kake a gidan masu kuɗin nan ba sonsa nake ba, nasan halin masu kuɗi da rashin mutunci da wulaƙanta talaka, nidai gaskiya su canza maka wannan aikin su baka wani, danni gaskiya bana son kaje inda za'a wulaƙanta min kai"
Kallon Umman sa yayi, ya ɗanyi murmushi ya tako gaban ta ya riƙe hannayen ta yace
"Kyakkyawar Uwa, Uwa da babu irin ta, ina Alfahari dake Umma na, yadda kike kula dani Allah ya kulamin dake ko bayan raina, ki kwantar da hankalin ki, basa wulaƙanta ni, kuma yanayin aiki ne yazo a haka, dana Kamm zan koma Office, idan kuma kince ba kyason aikin se in haƙura gaba ɗaya"
Badan ranta yaso ba tace "Yusuf ba aikin ne bana so ba, ni wannan aikin da suka baka ne bana so, yaushe rabon da muci Abinci tare, in ka fita tun safe se dare, Amma shikenan dai, Allah yayi maka Albarka, Allah ya sadaka da Alkhairi a duk inda kake"
"Ameen Umma na, bari in sauri sena dawo"
"Allah ya kiyaye hanya"
Ya amsa da "Ameen" ya fice.
Kai tsaye headquarters su ta jam'ian tsaro na farin kaya ya tafi.
Kasancewar Yusuf mutumin kirki yasa tun daga gate masu gadi suke gaida shi, ya tsaya suka gama gaisawa sannan ya shige ciki.
Ofishin sa ya nufa kai tsaye, yana zuwa ya tarar da shi tsaf ana shiga a gyara masa dukda baya nan, Na'ura me ƙwaƙwalwarsa ya ɗakko ya kunna, ya ɗan jira kaɗan sannan ya fara daddanawa.
Gaba ɗaya ya nutsu sosai hankalinsa kacokan yana kan Computer, da gani kasan ƙoƙarin gano wani abu yake me mahimmanci.
Sallamar da'akayi a office ɗin ne yasa shi ɗagowa, Sakina ce sanye da suit na aiki kamar yadda ta saba, fuskar ta ɗauke da murmushi ta ƙaraso tana wani fari da ido, Sam Yusuf baya ƙaunar mace mara kamun kai, shiyasa sam Sakina bata burgeshi.
Kujera taja ta zauna, ta kalle shi tace "wata sabon gani, aiki ya ɓoye mana kai gaba ɗaya haka, ba'a jin ɗuriyar ka ko a waya, na kira ka harna gaji baka ɗagawa"
Yusuf "Aikine ya ɗanmin yawa shiyasa, Ya aikin?"
Cikin iyayi tace "Alhamdilillah, Fatan dai kana lafiya?"
Cike da basarwa yace "Lafiya ƙalau"
Ya cigaba da latsa computer sa.
"Kwana biyu da baka zuwa duk gurin nan ba daɗi, nayi farincikin zuwan ka sosai"
Bece mata komai ba ya ɗakko wayarsa ya ɗan daddana ya kanga a kunnen sa, ya ɗanyi shiru na wasu daƙiƙu sannan yace
"Ya Abbas ka shigo ne?"
Ya sake yin shiru sannan yace
"Ok nima na shigo yau akwai buƙatar in ganka, bari inzo office ɗin naka"
Yana gama wayar ya miƙe ya fice ya bar Sakina a gurin, ba tare da yace mata komai ba.
Wani ƙululun baƙin ciki ne ya tokarewa Sakina zuciya, tabi bayan sa da kallo tare da yin ƙwafa.
Yana fita ya nufi Office ɗin Abbas, yaje ya tarar da shi yana karin kumallo, ya zauna suka gaisa, Abbas ya zubawa Yusuf shayi ya miƙa masa sannan yace "Mutumin ya? Yau ka samu chance ɗin ɓullowa kenan? Meye labari ne?"
Yusuf yace "labari kam akwai shi Abbas, nifa gaba ɗaya a rikice nake wallahi, gaba ɗaya na rasa bakin zaren"
"Take it easy man, bi komai a sannu, me ake ciki?"
Nan Yusuf ya warware masa irin abubuwan da suka faru har zuwa ga yunƙurin sace Widad da'akayi jiya.
Shiru Abbas yayi yace "Lallai lamarin akwai rikitarwa, Mahaifin Nurat ze shiga cikin suspects ɗinmu, yanzu abunda za'ayi ka bani Adress ɗin gidan, zamu je muyi bincike, semun fara gano waye ma mahaifin Nurat ɗin"
Shikenan zan turomaka Complete Adress ɗin ta Email ɗinka. Suka zauna suka cigaba da tattaunawa.
Wayar Yusuf ce ta fara ringing ya ɗakko ya duba, lambar Isa megadi ce a akan allon wayar tasa, ya ɗaga ya kara a kunnen sa, suka gaisa Isa yace masa "Ana neman ka"
"Shikenan gani nan zuwa"
Yusuf ya kalli Abbas yace "Abbas bari in canza kaya, waccan rigimammiyar tana nemana yau nasan zan sha tijara, dan titsiyeni za tayi tace sena gayamata meyafaru"
Dariya Abbas yayi yace "Ina jinjina maka Yusuf, yadda kake iya aiki da wannan Yarinyar mara alƙibla"
"to ya zanyi tunda kun takura kunce se nayi, dole in kwantar da kai inyi haƙuri da halin ta, Amma kasan wani abu Abbas?"
"A'a seka faɗa"
"Ni yanzu gaba ɗaya tausayi take bani, gaba ɗaya rayuwar ta ba irin yadda kowa ke gudanar da rayuwar sa take yi ba, duk yadda zan kwatanta naka ba zaka gane ba, ina kyauta ta zaton akwai wani pain a zuciyar ta, da yake ƙara assasa condition ɗin da take ciki "
"Hmm Yusuf kenan ba wani pain, kawai iskanci ne na yaran masu kuɗi, ta taka wanda take so tayi rashin mutunci saboda tana da masu gidan rana"
Yusuf yace "Haba Abbas, su talakawan me suka yi take musu haka? Wai waya gaya maka talakawa kawai take wa haka? Hmm ni nasan abunda nake gani kawai, ba iya Wulaƙanta mutane ba, Akwai wani ɓoyayyen abu da yake damun ta, ina jin tausayinta sosai"
Abbas ya ƙyalƙyale da dariya yace "Kai mutumina, ko dai ka koma ruwa ne?"
"Na koma ruwa kamar Yaya?"
"To naji kace kana tausayinta, na sani ko babbar magana zaka janyo mana"
Shiru Yusuf ya ɗanyi jiki a sanyaye ya kalli Abbas yace
"Abbas ai na rufe wannan babin har Abada, sedai wani ikon na Allah, just recently ka manta abunda ya faru dani ne? Ina ni ina Widad, as i told you before i give up gaskiya babu yarinyar da zan ƙara cewa ina so, zanyi haƙuri da ƙaddara ta, in zauna Yadda Allah ya ajiye ni, ni yanzu bari in tafi kar in ƙarawa kaina laifi, dukda yanzu ma nasan laifi na riga nayi shi, zan sha tijara a gurin Widad" yai maganar tare da miƙewa ya fice.
Abbas yayi shiru yabi bayan Yusuf da kallo, he's very gentle and innocent, abubuwa da yawa marasa daɗi sun faru da Yusuf, gashi shi kullum zuciyar sa a wanke take, baya nufin cutar da kowa.
A fili Abbas yace "Anya kuwa nayi adalci idan aka haɗa kai dani, aka cutar da Yusuf, Kai Amma kuma Alherin da zan samu a wannan sabgar ya isa in ajiye wannan wahalallen aikin in more rayuwa ta"
Yusuf ya canza kaya ya tafi gidan su Widad, ya tsaya suka gaisa da ma'aikatan gidan sannan ya nufi cikin gidan, babu wanda yake da wannan damar ta shiga cikin gidan kai tsaye, ko ba Aiken sa akayi ba se Yusuf, shi Yusuf be san da wannan dokar ba ma sam, kai tsaye ya shiga Babban falon da yake shine mahaɗar iyalan gidan.
Ya shiga da sallama a bakin sa, ya tarar da Amal a zaune tana kallon zee world, tana ganin sa tayi murmushi tace
"Sannu da zuwa, yau ka makara fa"
Murmushi yayi yace "Allah ya bada haƙuri, Madam ta tashi ne?"
Amal ta kwaɓe baki tace "waya san mata, ka zauna mana ka tsaya a tsaye"
"karki damu nidai ace mata nazo"
"Ni ban zanjeba seka zauna"
Yusuf ya zauna a ƙasan carfet, Amal ta ɓata fuska tace "ya zaka zauna a ƙasa kuma, haba Yusuf dan Allah ka zauna"
Haka Amal ta uzzura masa seda ya zauna akan kujera, ta miƙe tsaye tace
"bari in kawo maka ruwa, kafin ta fito bana so inje ta Wulaƙanta ni, idan ta ga dama zata fito da kanta" tana gama faɗin haka ta miƙe ta shiga wani ɓangaren.
Yusuf na nan zaune, ya ɗakko wayarsa yana ɗan daddanawa, sega Nura direba ya shigo da wata babbar jaka a hannun sa, da alama Aiken sa akayi yana ganin Yusuf a zaune akan kujera yayi turus yana kallon Yusuf.
Yusuf ya ɗaga kai ya dube shi yace
"ya dai Nura? Naga ka tsaya kana kallo na kamar baka sanni ba"
Kafin Nura yayi magana, sega Ramla da mahaifiyar ta sun fito, idon Ramla ya sauka akan Yusuf dake zaune akan kujera, buɗe baki tayi tace
"iyeee samun guri, ɗan kuturu da gaɗa cikin Rama, wato isarka da ƙasaitar taka harta kai ka dinga zama akan kujera sannu fa"
Rai a ɓace Mummy tace
"Kai ubanwa ya baka izinin shigowa falon nan harka zauna akan kujera, gidan ubanka ne kona uwarka da zaka shigo min falo ka zauna akan kujera, kai na fuskanci kanka na rawa fa"
Amal ce ta fito da ruwa da cup a hannun ta, ta ƙaraso falon tace
"Haba Mummy dan Allah kiyi haƙuri, wallahi ni nace ya zauna"
Yusuf kam shiru yayi bece komai ba, zama akaan kujera kawai yaja masa zagi da cin mutunci.
"dalla rufe min baki, se nayi maganin yaron nan, saboda jin kansa yake kamar ɗan uban wani, matsiyacin banza ɗan talaka, dama haka kuke baku iya samun guri ba, kana wani sumi sumi da kai mara mutunci, dama gaba ɗaya siffofifinka na munafukai ne bari Alhajin ya dawo, sena sa anyi maganin ka, bazaka tashi ba kana jina ina magana "
Gaba ɗaya ran Yusuf ya gama ɓaci, kujera kawai wannan akanta ake masa wannan cin zarafin.
A hankali ya yunƙura ze tashi rai a ɓace, cikin tsawa da rashin mutunci Ramla tace
"ba magana ake maka ba ba zaka tashi ba, banza kawai ɗan talakawa, an kusa korarka kowama ya huta, dalla tashi sakarai"
"baze tashi ba, Kujerar ba wani ya kawo ta ya ajiye ba se mamallakin gidan, dan haka babu wanda yake da ikon cin zarafi ko korara wanda ni yakewa aiki a gidan nan, baku kuka ɗauke shi aiki ba, Kuma duk wanda yake tunanin ze kori wanda na ɗauka aiki sedai ya bar gidan nan tunda mutum ba gidan nasa uban bane"
Widad ce tsaye sanye da gajeren wando, da vest a jikin ta gashin kanta a kwance a kafaɗarta kamar yadda ta saba shigar ta, cike da isa da nuna tsantsar iko tayi maganar.
Ramla ta harzuƙa za tayiwa Widad rashin mutunci Amma Mummy ta hana ta.
Widad tace "ki ƙyaleta ta faɗi abunda take so mana, keda ita kun sani banbancin ku da masu gadi da direbobin nan kaɗan ne ai, dan haka ku tsaya iya matsayin ku, kar wanda ya ƙara shiga hurumi na da wanda yakemin aiki, wannan ya zama kashe dina da gargaɗi na na ƙarshe a gareku, babu ruwan ku da ma'aikata na, wall
0 comments:
Post a Comment