Nace to Zubaina ku nake jira ku shiga ku aje ku zo muje. Suka fara murna ga amarya ga amarya. Da sauri suka fito. Zuhra ta ce, "Wannan ƙamshi Yaya Baby har kin koma kalar bota ɗin." Nace kun fiye surutu. Muka kama hanya Jamila ta ce "Su Mariyan can lungun dama ƙawayanki ne?" Nace wai ta gidan gurasa? Tace "Su." Nace ina ni ina waɗannan marasa kamun kai? Tace "To sau uku suna zuwa nemanki, kuma na gansu gun party sunsha rawa." Na kwashe da dariya, nace yanzu Fati mai awara ta barnan, wai zasu zo mu kwana kin san su dawa? Tace 'a' a, su da Maimunar gidan Alhaji. Gaba ɗaya muka sa dariya. Zuhra tace "Ki kore su ne, saboda abokan ango suke yin wannan shishshigin ko suma wani zai ce yana so." Amina ta ce "Haka ne Yaya Baby. Na ce ba kora su zo. Kuma ba lallai akan tunanin su cewa Yaya shi ɗan Ali Baita ne tunda har zuwa yanzu banji daga bakinsa ba. Jamila tace "Haba yaya Baby karmu ruɗa kan ki mana, wace sauran hujja ki ke jira? Jiya ganin shi da 'yan uwansa ya isa hujja, ƙila ya dai ɓoye miki ne ko yana son ya miki bazata ne, kuma salon ya birge, Abba cewa ya yi shi tun a katin gayyata ya so ya fahimci haka." Da sauri nace wake da katin a cikin ku? To ni ban ma tsaya na kula da katin ba. Amina tace "Mu shiga gida in ɗauko miki." Tabarma muka baza a tsakar gida muna zama sai ga su Fati, nan suma suka saje da mu ana labari. Nace Amina ina katin? Tace "Shi nake dubawa na Abbanmu ne Allah ya sa bai fita da shi ba." Can kuwa sai gashi ta samo. Na kunna fitilar wayata ina karantawa. Tabbas iyalan marigayi A Baita. Shi kuma a sunansa sai aka sa Aliyu A.Baita, sam ban gane komai ba sai yanzu. Na miƙa mata kati tare da faɗin biri ya yi kama da mutum. Na Dulmiya cikin tunani, nifa zuciyata da son Aliyu Shamaki mai tsare kaya ko sai da kaya shagon mai gidansa a Zeena plaza kanti kwari ta kamu. Bawai Aliyu Ali Baita ba. Na ɗauki wayata na soma rubuta saƙo zuwa ga Yaya. Kalmar da na soma rubutawa itace...Yaya akwai babbar matsa. Ina buƙatar sanin wasu abubuwa game da kai.
Ina tura saƙon na tashi naje nayi alwala na shiga ɗakin Umman Amina nayi salla, ina idarwa Jamila tana shigo wa, ta zauna kusa da ni. "Yaya baby wai lafiya naga duk kin canza tunda ki ka karanta katin nan?" Na ce Jamila in har ta tabbata Yaya shine ɗan Ali Baita to bazan aure shi ba. Ta rufe min baki da tafin hannunta. "Menene haka ki ke faɗa, maimakon ki yi murna ki ce Alhamdulillah Allah ya miki gata sai kuma ki ɗebo wata rigima? Na ce Jamila masu kuɗin nan suna da wulaƙanci, in zargin nan ya tabbata Hajiyar da muka je gurinta ita ce mahaifiyar sa. Ta yaya zan iya zama da wannan Hamshaƙiyar. Me yasa har zuwa yau bai faɗa min gaskiyar shi ba, dubi yadda 'yan matannan suka cika gidan nan saboda kawai zan auri ɗan Ali Baita, ki tuna yadda za su yi dariya a lokacin da ya sako ni. Gara yanzu aji ni nace na fasa. Jamila tace "Duk wannan hasashen ki ne, waya faɗa miki zai sake ki?" Nace ya saki mata uku ni ce 'yar gwal? Tace "Shawara ta ɗaya ki kira shi ku yi magana." Nace na tura masa saƙo. Ta amshi wayata da sauri ta shiga ta karanta abinda na rubuta. Ta kalle ni. "Wayyo Allah Yaya Baby, ya zaki masa irin wannan saƙon." Nace To me zance masa. Sautin kiran wayata ya katse mu, ta miƙo min "Gashi yana kira." Na ɗaga tare da sallama. Yace "Babyna kin ci abincin kuwa?" Nace ba zan iya cin abinci a halin da nake ciki ba. Yace "Subhanallah me yafaru?" Nace baka ga saƙon na ba kenan? Yace Gaskiya babu wani saƙo da ya shigo cikin wayata. Ki faɗa min menene?" Amma kafin nan ƙifara cin abinci. Nace ba'a gama miya ba tukunna. Yace "To ki jira ni." Ya kashe wayar. Na kalli Jamila, na san ya gani kawai zai ce min bai gani bane. Jamila ta ce "Ki bari ya zo ɗin karki yanke hukuncin da ba haka bane."
Shigowar 'yan gidan gurasa ya sa raina ƙara ɓaci. Jamila tana ta lallashina da ƙoƙarin nuna min cewa ƙila ya ɓoye min ne saboda wani dalili nashi. Ta tilasta min zuwa gurin da 'yan matan suke muka gaggaisa ana ta hirar gurin Party tare da kallon hotunanmu. Duk kowacce tambaya take wai ina muka haɗu da shi. Nace shi ya kawo kanshi har lungunmu, inda ya ganni. Maimuna tace gashi daga gani yana mugun sonki, ko ina a hoton yana kallonki. Wayata dake hannun Jamila tana tura min hotunanmu a wayar Mariya ta soma ringin. Jamila tace ga ango yana kira, na amsa duk suka bi ni da ido, na ɗaga da sallama. Yace ina ƙofar gida. Nace sai ka ƙaro gaba gida na ƙarshe a lungun can zamu kwana. Yace "To ki fito ki tare ni." Nace to. yace "Kada ki kashe wayar fa." Nace to. Na saka takalmi ina ce musu bari in dawo, sai naji kusan duk sun amsa da to amarya. Ina fita yana ƙarasowa ya aje ledar hannunsa, ya zauna a bakin dakalin. Na ƙarasa na zauna, na gaida shi cikin girmamawa kamar yadda na saba. Ya amsa sanan yace "Faɗa min wane saƙo kika Turi min?" Na sunkuyar da kai cewa na yi akwai matsala. Na ɗago na dube shi, Yaya ka faɗa min waye kai?" Yace "Me kike son sani?" Kai ɗan Ali Baita ne? Na jeho masa tambaya. "Me yasa kika tambaye ni?" Na juya masa baya, ka bani amsa kawai In shine me zai faru?" Ya sake jeho min tambaya. Ban yi soyayya da ɗan Alhaji Baita ba, da Aliyu na yi soyayya talaka mai tsaron kantin Zeena plaza.
🖊️🖊️🖊️
*HAMSHAƘIYAR UWA🧕🏻*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*
_PAID BOOK_
_Kuɗin karatu ₦600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a turo shaidar biya ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_
*DOKA*
_Ban amince wani ya ɗora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_
*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*
*Page 18*
Kuma shi zan aura inyi rayuwa da shi cikin yanayin akwai ko babu. "Ya matso daf da ni. Yanzu ma dashi zaki rayu Baby ni yaron Alhaji Baita ne amma ba ɗan daya haifaba, ɗan jire kanti ne." Na juya muna fuskantar juna.ka tabbata? Yace "Na tabbata kuma zan tabbatar miki da zarar an gama bikin nan." Na sauke ajiyar zuciya tare da faɗin to duk kashe kuɗin nan da ake yi fa? Kuma a katin gayyata ka ɗora sunan Ali Baita. Ya ƙara ƙasa da murya. "Ba zan iya hana su kyautata min ba Baby, saboda mun zama ɗaya da su mutanen kirki ne hatta katin su suka buga sai ganin shi na yi. Kuma don Allah kar ki damu kanki kar ki saurari kowa abinda na faɗa miki kawai zakiji, ko mutane sun yi wata magana duk hasashe ne. abinda ni na faɗa miki shine kawai zaki y arda da shi kinji ko?" Na sunkuyar da kai nace To. Ya sauke ajiyar zuciya, "Yawwa amaryata, amma fa kin ɗaga min hankali da ace ni ɗan cikin Baita ne yanzu shike nan gobe sai a fasa aurenmu?" Na turo baki tare da faɗin e mana, haƙura zanyi. Ya yi ' yar dariya maimakon kiyi murna kin samu mai kuɗi." Nace taɓ aini bana ra'ayin auren mai kuɗi gara ma in muna tare kayi kuɗin, ance suna da wulaƙanci ga sakin mace ayi ta mata gori, arziki, kaga kaina ka rabu da matanka har kashi uku kaga kuwa dole in yi ta kaina. Haka iyayen ta ba a basu daraja dan suna talakawa. To da in aure ka ka sake ni Yaya gara ba muyi auren ba. Ya ɗan yi shiru. Can yace "Baby da aure da saki iri daya ne da mutuwa, nasan kina damuwa ne saboda na saki mata har uku, kar ki damu da wannan ke dai ki yi aure bautar Allah ,kuma Baby ni da ke alkawarin da zan miki duk juyi bazan sake ki ba, kema ina son ki yi min alƙawarin cewa duk wahala bazaki guje ni ba." Cikin sauri nace na yi maka. Yace to "Mun kashe wannan wutar gobe kamar haka kina gidana jiya Abba ya kira ni zancan kafi na kayan ɗakin ki. To jiyan ana fenti ne yau kuma mun tashi da perty , amma gobe bayan ɗaurin aure sai akai kayan ko?" Nayi murmushi Wannan maganar ku ce ta manya. Yace "Haka ne, to ga kaji nan a leda da madara da sauransu don Allah ki ci ki ƙoshi kinji?" Nace kai ka ci abinci? Yace "Hajiya a baki yau ta bani fura wai tun jiya banci komai ba kamar wani ɗan ƙaramin yaro ta ajiye Ni ta bani." Muka sa dariya. Nace kai ɗan gatan Hajiya ne. Yace "Ke 'yar gatana ce, zauna in baƙi a bakin kema." Nace'A'a. Yace "To shike nan ki koma ciki ki ci sosai don Allah Alhaji Shamsu ya kawo ni yana jirana dan ya koma gurin iyalinsa da wuri." Nace wai dama kana da Abokai? Yace "E mana duk zaki san su a hankali." Na ɗauki ledar na shiga ciki, shi kuma ya wace, na dawo ina leƙenshi ya tafi da sauri. Yanzu kam hankalina ya kwanta koda ƙarya ya yi min."
Jamila ta tare ni da faɗin "Me muka samu ne?" Nace Yaya da abinsa wai yasan banci abinci ba shine ya kawo min naman kaza. Nan fa suka ɗauki sowa da guɗa suna faɗin wannan ango yana ji da ke. Kaji uku ne nace Jamila ta cire ɗaya ta ɗauki madarar ta haɗa ta kai wa su Umma, na ɗauki nawa nace Amina ta raba musu. Muna gamawa sai ga mutane sun shigo da guɗa wai za ayi kamu, suka fesa min turare irin dai yadda ake yi a al'ada aka gama kowa ya watse sai mu 'yan kwana.
Cikin dare bacci ya ƙaurace min wai gobe zan zama matar aure, na ɗakko waya ta ina kallon hotunanmu da Shamaki, faɗin cewa na dace ma ƙauyanci ne, Allah ne kawai ya bani shi ba wayona ko wata dabarata ba a kyan fuska duk da yana namiji ya fi kuma ko da ina mace ban san a gaba ba, amma ni da kaina na san bani da wata ƙira mai ɗaukar hankalin maza ɗan gara ko daga sama. Wata zuciyar ta ce gobe kamar yanzu muna tare da shi. Gabana ya fadi ni ba ƙanƙanuwar yarinya bace na san meye aure duk da bansan shi a zahirance ba, dole inji fargaba ban sani ba ko ina da budurcin da ya tambaye ni ko babu.
Sai dai ina da tabbacin ban taɓa zina ba. Ni dai har kiran sallar farko idona biyu ina ta saƙe saƙe daga binasi bacci ya ɗauke ni. Da safe na yi wanka cikin shadda Maman Iman ta kirani ta ce ta turo direba zai kaini gidan kwalliya. Na sanar da Umma tace to muje da Jamila amma karmu jima kafin ɗaura aure mu dawo.
Yau ɗin ma dai kamar jiya, tsara min kwalliya tamkar wata 'yar tsana. Ta bani wasu kayan tace inyi canji cikin wani ƙaramin akwati sai wata leda mai ɗauke da sarƙoƙi a jikin ledar an rubuta DIJANGALA ENTERPRISE. Kenan acan suka sai min. Ta sa direba ya ɗakko mu. Layin mu cike da mutane da motoci ya tsaya nesa kaɗan da lungunmu dan ba gurin fakin, muka sauka mukayi masa godiya muka nufi lungunmu. Jamila ta ce "Yaya Baby kalli ƙofar gidan Abbansu Zuhra ki ga motoci kuwa.?" Nace kinsan ɗan kasuwa in yana da mu'amala da mutane za su zo masa. Tace "kin dai ƙi yarda." Nace wai bana faɗa miki yadda muka yi da shi ba a jiya, amma kina ta musu, ki barsu in an kaini sun ga gidansa sai su samuwa kan su lafiya. Mutane sai kallona suke masu min Allah ya sanya alkhairi suna yi har muka shiga gida. Ya cika ɗajim da mutane sai kallo ya dawo kaina.
Ƙawayen dolena suka shigo duk sun sha wanka, sai ga mai hoto da me ɗaukar bidiyo aka shiga ɗaukar hotuna. Can Jamila ta miƙo min wayata "Kina da saƙo daga ango." Na duba da sauri, "Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Na zama mijinki Baby." Na ɗago a sanyaye na kalli Jamila, idanuna suka cika da hawaye, ta ce "menene"? Sallamar Abba ce ta sa na maida kallona gareshi, yana faɗin "Alhamdulillahi an ɗaura Allah ya basu zaman haƙuri. Sai hawayen suka kwaranyo bazan iya fassara ko kukan menene ba. Jamila ta ce "Kingani zaki ɓata kwaliyarki ke da ki ke ta zumuɗin zaki auri Yaya meye na kuka?" Nan abokan wasa suka taso ni a gaba. Jamila ta dubi Abba zai fita ga mai hoto ana ta ɗauka. Tace Abba don Allah zo a mana hoto." Sai akace a kira Umma. A nan kam ban jure ba sai da na zubar da hawaye sosai hoton har su Jafar da Baba Habu ƙaramin mu ga cikin Ummanmu.
Jamila ta jani ɗakin Umma na canza kaya ta ɗan goge min inda hawaye ya min jirwaye a fuska. Muna fitowa sai tankani ake yi dan kyau. Atamfa ce mai adon zaiba, ta ɗauki ɗinki. Lokacin aka ce ga angwaye za su shigo su yi gaisuwa a yi hotuna. Nan naga munafircin mata. kowacce ta maido hankalinta ƙofar shigowa.
Yaya da Abokansa ƙamshin su ne ya fara shigowa kafin su shigo, ya yi kyau cikin shadda mai ruwan siminti tsananin kyan shaddar shine ya bayyana tsadar ta.
Ya murza hula saƙar Gabas wadda ta tafi da kayan. Yadda kowa ke kallon sa haka nima nake ƙare masa kallo, fara'a fuskarsa ita ta bayyana tsantsan farin cikin da yake ciki.Haƙorin Makkansa yana haskawa, ina son haƙorin sosai ya ƙara masa kyau.
Suka tsugunna suka gaida su Umma abokan wasanmu sai tsokanar sa suke yi. Jamila ta kamo hannuna tana faɗin "Kifito kin laɓe kuma kina leƙensa." Na fito ya bini da kallo. Abokan suka ce mai hoto ya matso. Haka dai aka yi ta ɗaukar hotuna Ango fara'a ta kasa yankewa. Murya ƙasa ƙasa yace "Baby ina son mu yi magana ga shi ko ina mutane." Nace to ya za ayi? Ko zamuje gidan Usman Amina tunda duk suna nan? Yace " Ina ne?" Nace inda ka same mu jiya. Ya ce "To." Har abokan muka taka da Jamila soron gidan muka shiga muka bar abokan da Jamila a waje tana yi musu tayin abinci suka ce walima zasu tafi yanzu. Muna shiga Yaya caraf ya kama hannuwana cikin ɗoki, duka biyun yana musu wani irrin kallo, tsigar jikina ta tashi yarr, zan kwace sai yace "Kiyi haƙuri Baby an ɗaura mana aure, tun a ,jiya ina son in shafa wannan fulawar amma bani da damar aikata haka, saboda nasan shara'a bata bani dama ba." Na jure yana shafawa da lallausan hannunsa sai kurum naji ya sunbaci bayan hannuna, ya kafe ni da ido, duk tsoro ya bayyana a fuskata cikin rawar murya nace, Yaya kar fa wani ya ganmu. Ya girgiza kai, muryar shi a sarƙe ya ce in ɗan rungume ki Babu?" Na kwace hannuwana da sauri, sannan nace suna jiran ka a waje fa. Ya matso naja baya da sauri nace Jamila. Ta shigo tana faɗin "Menene?" Ta kalleshi har lokacin ni yake kallo, batare da ya lalle ta ba ya yi mata alama da hannu wai taje. Ta yi yar dariya ta fita. Ya matso ina ja baya har naje bango daf dani ya tsaya ya saki ɗan murmushi. "In Jamila ta iya cetonki yanzu anjima ko gobe wa zaki kira?" Gabana ya yi mummunar faɗuwa, na ganni wata 'yar tsuntsuwa a gabanshi. Muryata na rawa nace ina son inje in sha ruwa ne Ya yi murmushi. Yasa yatsa ya lakuci janbakin leɓena, ya lasa akan harshen sa. Sannan ya kauce gefe tare da faɗin "To soyayyata, kunga ga hanya nan nasan dai yanzu sai. in an rako ni, ko da yake zamu yi waya aiko?" Da sauri na nufi ƙofa ina cewa e zamuyi waya. Sai na ji ya saki dariya tare da faɗin "Matsoraciya." Mukayi sallama da su suka tafi ina ta bin Yaya da kallo, ashe dai shima ɗin ba kyalle bane. Sannan ya ƙara jefa ni cikin tunani.
🖊️🖊️🖊
️Maganganun shi sun jefa ni a fargaba, na shiga ɗimuwa sosai, harma na kasa cin komai, kuka na yini yi, mutane suna zaton kukan barin gida ne, duk da cewa akwai hakan amma dai fargaban karon battar da zamu yi da Yaya ya fi komai ɗaga min hankali.
Da taimakon su Jamila na yi ta canjin kayana. 'Yan kafin kayan ɗaki sun dawo duk sun ruɗe suna bada labarin gidana Gidan Hajiya Zeena ne. Sun gigice da ciye ciye da aka basu, wasu kuma suna murna sunga Hajiya Zeena. Nace to kenan dai Yaya ƙara rufe ni ya yi.
Jamila ta ce na faɗa miki, to ke menene na ki na ɗaga hankali mai maimakon murana Allah ya baki sai ki yi masa godiya. Shiru na yi domin bazata fahimce ni ba.
Da yamma motocin ɗaukar amarya suka iso motoci na gani a faɗa. Na ƙanƙame Umma ina kuka sai lokacin naji duk auren ya fita kaina. Tace "Meye hakan kuma, ki tafi Allah ya bada sa'a ya albarkaci zaman ku ina fata zaki ɗauki dukan shawarwarin da muka baki. Haka Umman su Zuhra ta ɓanɓare ni ina kallon Umma tana hawaye muka Fita gidan su Abban su Zuhra shida Annan mu suka min nasiha suna ta maimaita min in yi haƙuri, in zama mai yawan haƙuri har sai da na fara tunanin kalmar nan da ake ta nanata min akwai dalili. Muka fita nabi layinmu da kallo ta zuciyata ta sake karyewa sai naji tamkar na tafi kenan.
Ta ciki mayafi ina ganin harabar gidan na gane, kai tsaye suka shiga da ni falon Hajiya cike da mutane tana hakimce a kujerarta kamar yadda na zata, tana ta yi mana sannu da zuwa.
Aka kaini gabanta aka zaunar, aka ce ga 'yar ki Hajiya mun kawo miki. Tace "To Allah ya yi musu albarka ya sa mun ƙulla alkwairi ina fatan kun faɗa mata yadda zata zauna da mijinta lafiya. Yanzu ku kaita ɗakinta, nawa shi'anin sai gobe inda ita amarya zata girka mana abinci tare da taimakon masu aiki ta bamu ni da mutane na, ina fatan zaku zo domin ku ci girkin 'yar tawa. Sai kallon kallo ake yi. Umman Amina tace insha Allahu. Ta ce Maman Umar ta jagorance mu zuwa ɗakina.
Aljannar duniya, haka kowa ke faɗi, ni dai ina lulluɓe a zaune bakin gado ina jin yadda suke labarin kayan kyale kyale da na kallo kyan ɗakin ɗaki sun tafi da mutanen don haka sai waɗan da suka yi kafin abin ya zame masu sabo. Haka dai ina zaune bakin gado kai na a rufe kowa sai bani shawara yake yi ki kwantar da hankalin ki ki yi biyayya ki ci arziƙi iyayenki su ci. Da haka duk aka watse, nace don Allah a barnin su Jamila sa dawo zuwa dare. Aka bar su bayan kowa ya watse sai na cire mayafi daga fuskata na fito falo ina ƙarewa ɗakin kallo. Na ruɗe wai ni Rabi 'yar magini ni ce da wa
0 comments:
Post a Comment