Bayan ya samu kanshi na uzzira mishi ya yi wanka ya shirya amma dole na zura mishi ido ya yi salla saboda an riga anyi a masallaci. Ni kuwa ko wakan banyi ba burina dai ya fita. Kafin ya kammala na ɗauki jakarsa na rataya a kafaɗa. Yace "Yau a haka zan tafi bazan saka turare ba?" Nace E yau a haka zaka tafi, domin dama ai danni ake sakawa ko?" Yace haka ne amma ayi haƙuri a ɗan yarfamin ko ba yawa." Na ɗauki wanda hannu na yakai na feshe shi,sannan na ce mu tafi.
A falo Hajiya ce kaɗai take yin salla a gurin salarta,na shiga waige waige ina faɗin to ina ummana ta shiga kuma! Na kalleshi, cikin kukan shagaɓa nace kaga ka gani ko? Gashinan ta tafi ina ta cewa ka yi sauri amma ka ƙi gashi kuma ta tafi ko ɗakina fa bata shiga ba... Da leɓen shi ya nuna min bayana. Cikin sauri na waiwaya sai naga Umma ta fito daga ɗakin Hajiya tana faɗin Baby kukan me kuma ki ke yi haka kamar wata ƙaramar yarinya? Na saki dariya ga hawaye nace na zaci fa ko har kin tafi ne. Tace "Shi ne ki ke yin me?" Shamaki ya ce "Shi ne ta ke kuka dan shagwaɓa." Umma tace Shagaɓar gaske kuwa banda shiririta ina ke ina kukan na tafi tunda ba tare zamu tafi ba.Ta zauna agurin zamanta na aje jakar nace Umma bari in saka miki abincin ko? Tace "Kaɗan zaki sa min don banajin yunwa. Na sa mata kaɗan na loda mata nama, da da hali saina kwashe mata naman ta kaiwa su Jafar, amma gudun zargi ko maganar Hajiya dale dai na haƙura. Hajiya ta idar Shamaki dama ita ya ke jira, domin in ta fara salla sai mutum ya jira dan wani lokacin na kan tambayi kai na ko dai Hajiya sai an amshi sallar sannan take idarwa. Yace "Hajiya na gama shirin zan fita kasuwa. Ta dafa kanshi kamar yadda ta saba. Tace Allah ya yi maka albarka ya bada sa'a ya tsare gabanka da bayan ka."
Yace Ameen ya kalli Umma yace Umma a gaida su Jamila da Abba. Tace zan faɗa musu Allah ya bada sa'a da rabo mai amfani. Yace Ameen Umma na gode.
Na bishi da jaka ina jin takaicin banga ya ba Ummana komai ba har yana wani zai jira su gaisa, a zuciya ta nace sai na roƙe shi yau koda zai hana ni.
Sai da mukaje falon da nake tsayawa, na haɗe girar sama da ƙasa, ya sa hannu ya ɗago fuskanta yace "Me kuma aka ce ya faru Baby?" Nace ce ina son in bawa Ummana wani abu na tsaraba koda kuɗi ne ta saya wa ƙanne na ,amma na kasance bana maganin ko sisi. Cikin shagwaɓa na yi maganar. Ya kwaikwayi muryata yace, "Na ba Hajiya saƙo zata ba Umma shike nan?" Kai masa ɗan dukan wasa nayi ina faɗin na gode. Ya saki fuska ta ya amshi jakar na ɗaga hannu nayi masa bye bye.
Na dawo Umma ta aje abincin tana shan ruwa,na kalli naman kamar ma bata ci ba, nace Umma to ya baƙi ci naman ba kuma? Tace na ci Baby Allah ya amfana. Hajiya tace "Nima dai naga kamar bata ci ba, nan dai kamar gidan ki ne bakya yi fulako ba." Umma tace Alhamdulillahi ai na ci. Hajiya tace "To ko kuma dai a juye ta kaiwa yara dan kinga karnuka za'a baiwa?" Umma tace "Haba dai bazan ɗaukii abinci ba ga shi can a gidan, zuwa zanyi ma in tafi,ƙarfe biyu Abbansu y ace in dawo. Gashi naga ɗaya da rabi ta gota. Hajiya tace "To kuma baki shiga ɗakin nata ba, ga mamakina sai naga Hajiya ta miƙe tana faɗin "Muje in raka ki, nima ban taɓa shiga ɗanikinsu ba, me zakaje ka yi a ɗakin yaro." Umma tace gaskiya dai, bare ko yaushe suna dabdala a nan gurin ki. Tace haka kuwa.
Mamakin Hajiya ya hana ni magana ina biye da su ina tunanin. Hajiya dai ƙila dan kar mu tattauna wata maganar da Ummane ta yi wannan katan katan ɗin ta ƙi bamu fili ko kuwa kulawa ce da mutuntawa ta yi wa Umma.? Bani da amsa dan haka naci gaba da binsu.
Ta nuna wa Umma ko ina tun daga banɗaki har saura ɗakunan Umma dai tana ta addu'a da fatan alkhairi
Sannan suka zauna a kan kujera,na zauna a gaban su kamar mai nema gafara,Umma ta fara magana. "To Hajiya masan dai kuna ta haƙuri da ƙuruciya,yaran yanzu sai anyi haƙuri, a daure ana tsawata mata in tayi ba daidai ba a sata a hanya na hukunci kuma a yi mata ba sai an sanar da mu ba,. Allah ya sa mutu ka raba tsakanin su." Hajiya ta amsa da Ameen, ai ita Rabi'atu bata da matsala yarinya ce mai biyayya laifin ta da nii ɗaya ne. Na zaro ido cikin faɗuwar gaba domin inji laifin nawa. Taci gaba da fadin Duk yadda yarinyar nan zata so mijinta ba za ta yi ya ni Uwar da na haife shi ba Haka ne?" Umma tace "Ko alamar ƙafar ki bata kama ba." Hajiya tace madalla, to wai yarinyar nan nace ta shirya za'a kaita gidan wani malami wanda zai bata taimako Allah cikin ikon sa sai yadda ta yi da mijinta, kina kallo gata dai a cikin irin wannan gida amma bata maganin kwabo ɗaya,ko kina da shi?" Na girgiza kai tare da faɗin bani da shi. Tace yanzu dubi ke ba surukarsa bace, da fatar baki yace miki ki gaida gida,zancan gaskiya hakan ya kyautu?" Umma dai bata yi magana ba. Hajiya ta ci gaba da faɗin. Nasan har maƙota da wasu a dangi sai sun yi da ku,suce 'yar ku tana aure a gidan Alhaji Baita amma har yanzu kuna nan jiya i yau. Koma ace laifita ne ta yi aure gidan daula ta mance da ku, wasu ma cewa za suyi ana baku kun ƙi nunawa ne dan kar ku sammusu, maganar haka take?" Umma tace haka ne. Hajiya ta nuna ni da yatsa tace, "To kinganta nan fir taƙi zuwa gidan malamin har da ɗauke min ƙafa ina hankalce da ita,in ba mijin ta ne a gurina ba ta daina zuwa tunda ta san ba yadda za a yi in yi mata maganar a gaban sa. Ita bazata gurin Malami ba,ba kyau ba sai an mallake shi ba. Jifa sokonci. Kuma ita hakan zai wa amfani,nima kuma ta ɓangare na wani abin in zai min gaddama sai in bi ta hannunta kin san dai ɗan yau."
Mamakin Hajiya ya sa na kasa daina kallon ta, ko dai so take Shamaki ya fara yi mata sujjada. Mutumin da kara in ta aje ba zai taɓa tsallaka shi ba.
Muryar Umma ta katseni, tayi gyaran murya sannan ta ce, Wato Hajiya ni ma dai a nawa ganin sam bai kyautu Baby ta kai sunan mijinta gidan malami ba koda baya iya sauke hakkin da Allah ya ɗora masa nata na aure. Balle duk maganar nan ana yinta ne game da wata kyautatawa wadda in bai yi ba Allah ba zai kamashi da wani laifi ba. Babu shakka ban goyi bayan wannan abin ba. Kuma wai ma Hajiya dan mutane za su ce ko maƙota za su yi damu, Allah na tuba zaka hana bawa ya ɗauki zunubi ne, kace dole sai ya yi aikin lada? Kinga kuwa bamu isa mu hana a yi munafircinmu ba, kuma ko da me kuka bamu Hajiya wannan ba zai hana mai magana ya yi magar shiba. Dan haka don Allah Hajiya kar a nuna mata wannan hanyar, kinsan yaran zamani wataran sai ta tafi da kanta neman wata buƙatar da zata ɓatawa kowa rai. Munriga mun ɗora ta a hanyar sallar dare,in wata damuwa ce ta faɗawa Allah,kuma ta ke yi wa mijinta addu'a Allah ya tsare shi. Ta dubi Hajiya wadda ta zuba mata ido tace, ki yi hakuri in na faɗi ba dai dai ba. Amma shawara ta ƙarshe ku barshi ya ji da masu jiran shi na waje,kinsan 'yan kasuwa ba'a raba su da magauta, a gida sai a tsananta addu'a bare ta ku Hajiya, bakin Mahaifiya ya sha gaban bakin duk wani malami." Hajiya ta sauke ajiyar zuciya ta ce "To ai shikenan tunda kin goye mata baya, na kyale ku ,yanzu ita ko dan kishiyoyin da suka fita ko wasu da zasu shigo bakya bata ƙwarin gwiwa ta amshi taimako ba?"
Umma ta yi 'yar dariya tare da faɗin mijin mace huɗu kuma a tauye shi da mace ɗaya Allah ya rufa masa asiri. Ai Hajiya duk namiji da burin aure ya ke mutuwa saidai in Allah bai ƙaddara mishi ba. Dan Allah ina neman alfarma Hajiya a bar zancan gidan Malamin nan, Abbasu in yaji ba ita ba har ni zai saɓa min ƙwarai.
Juma ta ƙwanƙwasa ƙofa da sallama . Hajiya tace ta shigo , ta miƙo wayar Umma
da ta aje a inda ta zauna a falo, tace "Ana ta kiran wayar ne." Umma ta amsa da sauri tana faɗin Abban su ne.Daidai lokacin kiran ya sake shigowa. Ta ɗaga tana faɗin yi haƙuri wayar tana can sitirum ne mu kuma gamu a cikin ɗani. Muna jiyo murya Abba kasancewar wayar Umma ta samu matsala ko yaushe murya a buɗe ta ke. Yace "Kenan shantakewa ki ka yi a gidan yarinyar ke da na baki ƙarfe biyu yanzu saura mintina ko baro gidan nakiyi ba." Tace yanzu zan taho muna 'yar hira ne da surukarta kaga gata ma ku gaisa.
Yace to bata, suka gaida shima dai ya bada haƙuri akan cewa su yi haƙuri da ni in har na yi ba daidai ba. Suka yi sallama yace da Umma ta gaishe ni, kuma ta taho domin gashi nan zai koma gidan yanzu.
To haka dai muka sake fitowa gaba ɗaya,domin Hajiya bata da niyyar bamu guri, muka dawo Falon Hajiya. Umma ta miƙo leda mai layi layi tace ga tafarnuwa da kayan ƙamahi Hajiya, tsarabar ce sai na rasa me zan kawo muku tunda Allah ya sa kuna da komai.
Hajiya tace "To muna godiya Allah ya saka da alkhari. Hajiya ta dube ni, "Shiga ciki kan gado ki ɗakko mata Envelope ta sayawa yara alawa a hanya. Ta dubi Juma da ke kwashe kayan abinci tace "Je ki faɗawa direba zai maida baƙuwa gida.
Har mota na raka Umma sai da naga motar ta bar harabar gidan sannan na dawo ciki. Hajiya ta kalle ni, ke ce "'yar fari ko?" Nace E. Hajiya. Tace. "Naga itama yarinya ce mahaifiyar ta ki. Nayi Murmushi tace "Gurinta ki ka samo wannan shegen baƙin wayon ko?" Nayi 'yar dariya nace bari in shiga ciki.
Na yi wanka na yi salla naji daɗin zuwan Ummana duk da Hajiya ta hana mu sakewa. To wai ita Hajiya domin kar in faɗawa Umma cewa Shamaki zai ƙara aure shine ko kuwa dai tana zaton zan faɗawa Umma cewa bata min yadda kamata ne?
Bani da amsa don haka sai na tashi na ce bari in kira Umma inji ko sun isa gida.
Na faɗa kan gado na, na ɗauki wayata na kira layin Umma, ta ɗaga tace "Yanzu fa na ke shirin kiran ki in faɗa Miki cewa
Dubu Hamsin ne a 'yar takarda nan da Hajiya ta bani."
Na ja dogon numfashi nace amma angode Allah ya saka da khairan. Gashi bamu samu minti hira ba. Tace "To wace hirar ma zamuyi ko kina da wata matsala ne?" Nace "To ba dai wata ƙatuwar matsala bace amma dai an saka mishi ranar aure da wata yarinya 'yar uwarshi, tana nan a gidan ko da kika zo tana ciki bata fita ne hatta makaranta ta daina zuwa. Umma tace "Tofa! Amma kin san abinda nake so da ke?" Na ce A a,Tace ki kama kanki ba ruwanki da auran sa. Sannan hanyar da da maganar gidan malami da Hajiya ke yi duk yadda aka yi so take ta gwada ki, ko dai wani abu mai kama da haka. Nima baki ga ta latsa min basira ba, kar nake kallon ta. Wata uwa ce zata ce a kai ɗanta gidan malami ki kiyaye sosai wata kitimirmira take haɗawa. Kuma ki ke nazari ko magana zaki furta domin na lura cewa 'yar shan loga ce, ga ta da alaye. Sannan karki taɓa damuwa da abinsu. Baki gani ba,naman nan ina son inci shi amma ina jin tsoro kar in bar miki abin faɗa dan haka na kauda kai daga gare shi na haɗiye kwaɗa yi na.
Nayi dariya nace zan kiyaye Umma, tunda ga kuɗi nan kin samu sai ki siyo muku mama ku dafa.
Tace wannan kuɗin zan ciri jari a ciki in ba Abbanku dubu goma shima. In sai wa Jamila tukwane, ba zan bari in maimaita kuskuren da nayi a baya ba a bikin ki. Nace haka ne Allah ya rufa asiri. Tace "Ameen dan Allah kar ki saka maganar aurannan ya dame ki, ke dai kiyi ƙoƙari ki iya allonki. Nace Insha Allahu.
Muka ɗanyi shiru can tace ina ganin fa kamar kin ƙara ramewa, anya babu wata matsala bayan wannan?" Nace babu, ai nayi zazzaɓi ne kwanaki harna kwanta a asibiti amma nayi ƙiba, sosai. Tace Allah ya ƙara lafiya, yanzu dai ki kwantar da hankalinki. Nace to Umma.
Bayan mun yi sallama na yi shiru ina tunani, yaushe kuwa zanyi wata ƙiba a gidan nan tunda nayi kuskuren duba wayar mijina.
Kuma gashi abin ya zame min masifa ko na ce bazan duba ba sai na duba. Gashi dole in haɗiye duk abinda na gani a cikinta tunda bani da damar fadawa wani domin in samu salama. Duk da cewa ina bukatar shawara amma bansan wa ya kamata in nema shawara ba, wanda asirina zai rufu. Zan ci gaba da miƙawa Allah kuka na shine mafi girman wanda zai bani mafita.
Azumi ya gabato bai fi sauran kwana tara ba, Shamaki baya samun zama yawanci sai na jima da bacci ya ke shigowa. Suna ta fama da lissafi za su cire Zakka. Za su tafi Umara,ita Hajiya acan zata yi Idi shine zai dawo kafin lokacin salla, amma sai an fara azumi da sati biyu zasu tafi.
Sun fara rabon zakka ina zaune ina jin su ana lissafin, masallatai da za'a kai miliyoyin kuɗi. Sai kuma wasu marasa ƙarfi, sai dangin su da za a baiwa dubu ɗari ɗari a Envelope da kayan abinci. Yayinsa kowa ta zo ta kawo list na mutanen da take son a taimaka. Ni kuwa matar gida ko oho,ina zaune bana maganin ahu, ko kitso da ƙunshi ko wanke kai saidai direban ya kai ni in turawa Hajiya account ta turo musu kuɗin.
Ɗinki kuwa da yace in bada kayan cikin lefena duka a ɗinka da na faɗa mata zan kai ɗinki Unguwar mu sai tace a a,ta sa Maman Iman ta kawo tela har gida ya gwadani ya kwashi kaya, sai dai ɗinki na gani bani da wata hanya da kwabo zai shigo min duk wani abu da nake buƙata za a kawo min.
To irin wannan uƙuba ta rashin kuɗi dan ma dai dama can ban saba riƙewa ba bare in damu sosai.
Ina kwance sai ga Juma wai inzo inji Hajiya. Na same ta a hakimce kamar kullum da carbi tana ja, ta bini da kallo har na fara tunanin ko nayi wani abu ba daidai ba. Na tsugunna nace Hajiya gani. Ta nuna gefen ta da yatsanta, "Ki ƙirga min wannan Envelope ɗin guda nawa ne." Na ce To. Na ƙirga guda ashirin ne. Tace "Dubu ɗari ɗari ne a ciki ina son ki rabawa mutum irishin ma su buƙata ciki harda su Juma, sannan yanzu zan saka Juma ta je ta rakaki can baya inda kayan abincin zakka su ke, na azumi , ki raba su ga masu buƙata. Na zaro idanu ina faɗin Hajiya bazan iya ba." Ta ɗago ta dube ni cikin gimtsewar fuska,tace kina auren Shamaki amma baki san yadda ake raba taimako ba? Na kalli Juma wadda ta min alamar inyi shiru da ido. Na maida dubana ga Hajiya wadda ta kuma tattara hankalinta ga carbin da take ja. Na miƙe na ce Juma muje ki nuna min.....
....
Muka fita can wata haraba ta bayan gidan ina ta tunani yadda zan bigi cikin Juma.
Nace wai kuwa Baba Juma a ina ake rabon kuma suwa da wa ake baiwa.? Tace "To kowace mace dai da yadda ta ke rabon ta wata ta yi a cikin gida wata kuma a waje amma can da dai a cikin gida ake yi kuma ba a taruwa, yanzu dai naki sai yadda ki ka yi da shi."
Nace kina nufin duk sauran matan sun yi irin wannan rabo? Juma ta ja baya ta riƙe ƙugu sannan Tace "Babu wadda ba ta yi irin wannan rabon ba." Nace ni damuwar ban san su wa zan baiwa ba. Kuma yaushe zan bayar? Tace "wannan duk yadda ki ka yi Hajiya bata da matsala da haka, in kina so ma zaki iya bari sai sun tafi Ummara sai ki yi yadda ki ke so." Na kalli Baba Juma tabbas tana min wani irin kallo mai kama da shurin jeki ki mutu.
Muka ƙarasa wani ƙaton store narke da shinkafa 'yar gwamnatin ga taliya da makaroni Suger Indomie da sauran kayan abinci na azumi.
Na kalla nace taɓɗi gaskiya in wannan aikin yana cikin jarabawar Hajiya ba shakka dole a faɗi.
Muka dawo ni dai ranar haka na yini ina nazari
Na ɗauki waya na kira mijina Shamaki ya ɗaga cikin sauri yace "Menene yi magana meeting zan shiga yanzu." Nace to dan Allah ina son magana da kai in ka fito. "Ki kira ni ƙarfe Shidda na yamma." Bai jira amsa ta ba ya kashe wayar.
Na ce kai nima fa ina da uwa,duk Duniya ita ce take min son da ba wanda ya ke min makamancin shi, dan haka ita ce zata bani mafita kamar yadda ya ke tutuyar ta shi uwar tana sama mishi mafita.
Na ɗaga waya na kira Umma, Muka gaisa nace Umma dama wani yanayi na samu kaina ina buƙatar wanda zai tsaya min har komai ya yi kyau "To kuwa wake gare ki bayan mu Baby?" Ta katse ni. "Menene faɗa min. Na kwashe komai na sanar wa Umma sannan na tsaya sauraron ta. Tace abu na farko yanzun ki je ki samu Hajiya ki ce abaki list na mutanen da za su amfana da wannan zakkar in ta baki sai mu sake yin magana."
Na zo bayan la'asar na samu Hajiya tana kallo na zauna na gaishe ta,sannan nace Hajiya dama list za a bani na waɗanda aka saba baiwa wannan taimakon. Hajiya ta ɗago ta dune ni kamar zata yi magana sai kuma ta kauda kai, sannan ta ɗaga wani fayal ta ciro wata doguwar takarda mai ɗauke da sunaye a jere tace "Gashi." Na amsa,nannan na nace yawwa Hajiya dama su waɗannan kuɗin na cikin... Ta ɗaga min hannu duk yadda ki ke buƙata haka zaki yi abida ya sa na baki list ɗinnan saboda kin tambaya ne,da baki tambaya ba bazan baki ba."
Na ce To na gane. Na koma ɗaki ina me alfahari da uwata na zauna na duba list mutum ɗari harda uku. Na kalli kuɗin aka durowar gefen gado na, nace gashi kuɗin na mutum ishirin ne.
Naira miliyan biyu ne ta riga ta raba kuɗin bare ince a rage su yadda kowa zai samu. Na sake duba takardar sosai ko a kwai sunayen da zanga anyi musu alama amma bangani ba,na kuma kiran Umma na faɗa mata ga halin da ake ciki.
Tace "To abinda za ki yi ƙoƙari ki gano shine waɗanda za a baiwa wannan dubu ɗari ɗarin domin tabbas na wasu ne daban kuma ana haɗa musu da kayan abinci sauran mutanan kuwa sai ki kira su tunda akwai suna da kuma lambar waya sannan ki tabbatar ba ki ba wani naki ko mu wannan kayan abinci da kuɗi ba."
Nace Haba Umma hauka ake, duk yadda za ayi dole in cire muku kuma,shirme kenan zan yi cewa fa aka yi duk yadda nayi daidai, banda ma tsoron Allah harni sai na ɗauki kashi ɗaya. Umma tace "Baki da hankali, ko ƙwayar gero kar ki sake ki aiko mana da shi. Ki bi list ɗin da ta baki, abinda za kiyi kawai shine ki ki fara da kiran lambar farko kiji waye a haka sai ki ware waɗan da zaki ba kuɗin, amma ki bari sai ranar lahadi tunda kince baya fita da wuri." Nace to zan yi haka amma zan kira su kafin ranar in sanar musu
Da safe da naje gaida Hajiya bayan na gaishe su har zan miƙe sai tace "Ranar yaushe za ki yi rabon zakka?" Na sunkuyar da kai nace ranar Lahadi. Tace "Nan da kwana hudu kenan me yasa ki ka kai shi har wannan kwanakin?"
Nace ina son in gano suwa za a ba wannan kuɗin ne. Ta ɗan yi jim sannan tace shike nan Allah ya taimaka. Shamaki ya matso kusa da kunne na "Jiya me ki ka sha ne na yi miki tashin duniyar nan amma ki ka kasa tashi?" Na rage murya nace na yi shaye shaye jiya irin su ruwa da lemo.muka sa dariya.
Nace na jira ka har kusan ɗaya baka shigo ba,bacci mai nauyi ne kawai. Yace "Dama maganar da kika ce za mu yi ce na so in tashe ki." Da gefen ido na kalli Hajiya kuma na gane hankalinta yana gurinmu. Nace ba fa wani abu bane,kawai ina so ne inji muryar ka, ko zanji sanyi a zuciya ta. Yace "Zafi ta yi a lokacin?" Nace ƙunar sonka ba. Ya ɗan kai min dukan wasa,yace Me wayo zaki faɗa min gaskiya bari in shigo. Na tashi na koma ciki.
Na ɗauki takardar ina ƙara kallon ta. A fili nace banda Hajiya ta so wahalar da ni, ai da sai tace kawai da sai ta faɗa min cewa kuɗinna wane da wane ne.
Na kira lambar farko Na miji ya ɗauka kuma da alama dattijo ne. Muka gaisa, nace daga gidan Alhaji Baita ne don Allah da wa nake magana? Sai aka ce "Da liman ne mai jan salla a masallacin gidan. Nace to ranar Lahadi za ka karɓi saƙo. Yace to Allah ya kai mu."
Bayan mun gama waya nace ina ruwa na Allah duk wanda yake sahun farko shi zan ba kuɗi kuma in haɗa masa da abinci.
Na kira na biyu shima na tambaya kamar yadda na yi na farko. Akace wacece baki gane da wa ki ke magana ba? Nace Matar Shamaki ce. Sai yace auto Babanku ne ƙanin Hajiya. Nace Baba ranar Lahadi za a bada saƙo, yace to "yar nan mu zamu zo mu karɓa? Nace Baba ya ake yi muku ne kawowa ake yi ko ku ke zuwa? Yace "To shekarun baya dai can kafin rabon ya koma hannun matan Shamaki direba ke kawo wa Bama sanin cewa za a bamu amma daga baya sai ace mu zo mu karɓa."
Cikin zumuɗi nace acan baya ɗin me ake baku ne Baba? Yace "A can baya dai dubu dari da buhun shinkafa da suga da gero. Nace to Baba bana ma ba sai ka zo ba, za a kawo maka kamar yadda ka lissafa. Yace to Allah ya yi albarka. Nace Ameen yace akwai wani ƙanenmu a ƙauye shi an daina bashi ma gaba ɗaya,kuma da har shi Hajiya ke bamu. Nace to za 'a bashi ya zo ranar lahadi ko shima kauyen ake kai masa da? Yace A'a gidan yake zuwa. Nace to.
Wato ashe dai lissafi
0 comments:
Post a Comment