Na bigi cikin Juma dan in samu labari. Nace Juma tunda naji ki shiru na san cewa ana zaune lafiya dama shiyasa nace kije dai a gani. Tace "Injiwa ya fada miki so biyu dai ina hada kaya Zan tafi sai tazo tana bani hakuri domin tasan in na tafi zataci gidansu gu Hajiya da shi uban dakina. shine ya sa take dan shakka ta, dan duk radda ya kaini karkiga yadda ya ja mata kunne a gabana, har sai da ta bani tausai."
Nace To ai haka yafi, kuma tunda tana sanshi ya na santa ai baza kiji suna husuma ba, tunda shi tashin hankali ko ba da kai ake yi ba kinsan bashi da dadi. Na fada tare da baza kunne inji me zata ce. Tace "To wani lokacin su yi tsiya wani lokacin kuma su yi dadi, amma fa akwai radda ya yi mata dukan tsiya,. Na zaro ido tare da maimaita fadin duka! Juma tace Nima dai nayi mamaki, domin ban taba gani ya daki mace ba duk matansa na baya." Nace kuma ke baki je ceto ba? Tace Ai bari nai sai da ya lallasa ta sannan naje ceto, ina fadin wannan ba dabi'ar ka bace uban dakina. Yafice yana fadin ki sake min bincike a waya. Ita kuma zan je in bata hakuri sai ta huce a kaina wai infice bata son gulma. Shine nace, a a kinga "yarnan bani ce na kar zomon ba kuma ratayar ma ni ba a bani ba. Na tafi ina dariya.
Nace duka dai Juma Shamaki ne da dukan mace? Tace "Af sai dai kar a kuma. Waya fa ta bincike masa, kin taba ganin mace mai binciken wayar miji ta zauna lafiya? A zuciyata Nace Ai ko bai dake ta ba da ya barta iya ciwon zuciyar abinda zata gani ya ishe ta. A fili nace ummm ai shike nan amma dai magana ta gaskiya wannan bai kai abin duka ba shima. Juma tace Ni kuwa har Allah ya kara nayi mata saboda rainin da ta yi min. "
Haka dai akayi salla ta wuce mahajjata suka shiga dawowa. Ni a sallar banje gida ba, amma su Jamila da wasu 'yan unguwarmu sun zo.
Ranar da zasu dawo munsha aiki, ni sai lokacin na yi gayun sallana, wato kitso da kunshi, sannan nayi dinki. Na yi kyau cikin leshi. Shamaki bai ji nauyin Hajiya da Azima ba ya rungume ni. Yace "Na yi kewar ki Baby. " Nima nace na yi kewar ka Babban bako. Sannan na rungume Hajiya.
Sunci sun sha sannan aka kama hirarraki. Azima tace Juma ta zo su tafi Juma tace sai dare zata zo. Hajiya ta ce min "Mijinki ya shiga ciki amma kina nan. Nace yau ai gidan Azima zai tafi domin ranar da zaku tafi ai yana nan. Hajiya tace "To ai da Azimar aka tafi suna tare ai. Na tashi na shiga dakin yana kwance kan gado yana chatin motsin taba kofata da sallamar tawa sai suka dan tsorata shi alamun rashin gaskiya suka bayyana a fuskarshi.
Ya aje wayar ya tashi zaune, Baby me yasa ki ka ki zuwa kinsan abinda ya shigo da ni. Nace ce ni tsoro ya hani zuwa na yi mafarki na dauki wayar ka ina bincike sai ka kamani shine kamin duka. Ya zaro ido, "Ai bazaki taba daukar min waya bama bare ta kaimu ga haka. "
Na ce Kenan zaka iya dukana in abin ace an daukar maka wayar? Yace Baby waya sirrin mai ita ce, kar ki fara bin al aurar wani, ko Allah baya son kana bin diddigin neman sanin sirrin wani bawansa da ke boye wanda shi bai bayyana ba." Nace haka ne. Ya kama hannu na, Baby ina son ki, ina son mu haihu da ke Baby, na yi ta rokon Allah ya baki ciki duk shekara." Na kwace hannuna ya zaka min wannan addu'ar in Allah ya amsa fa? Yace haka nake fata sai inyi murna, ya amsa addu'a ta." Nace ni kuma in tashan wahalar goyo da ciki? Yace zan taya ki, kuma ga su Mubina za su taya mu. Sai mu karo masu raino mu hada da Rahin. " Na kai mishi dukan wasa tare da fadin dubu nawa zan haifa ne har da lissafin 'yan raino babu adadi? Yace zo in baki amsa. Ranar sai da Shamaki ya shafe min duk wani kokwanto da ke zuciya ta, ta sake amincewa da shi, harma na yarda cewa ni daya ce a zuciyar sa.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, na dan ja baya da duba masa waya sai jifa jifa. Abinda na lura shine bazan iya raba Shamaki da neman mata ba. Kuma tunda yana boye min in tafi a haka.
Dan haka na duka fadawa Allah.
Kwanci tashi har shekara ta gabato, saura sati uku in cika shekara, na zama cikin tunani da yawan addu'a Allah ya zaba min abinda yafi alkhari, sannan na sanar da Umma dan ta tayani da addu'a kuma dan kar suga na dawo gida kwatsam. Shi kanshi Shamaki ya fahimci cewa ina cikin damuwa 'yar kibar da na fara duk na jeme, hakan ya jefa shi cikin damuwa wanda har sai da ya tsarani don jin ba a si. Na fada masa. Yace "Baby Allah ya jarabce ni da son ki, na tabbata in har na kuskura na sake ki Hajiya ce zatafi kowa yin da ta sani, wanda hakan shine zai kawo taje da kanta ta nemo ki. Ya numfasa sannan yace ina son kimin alkwari, ko da Hajiya ta sa na sake ki, karki kula kowa na san zata kawo kanta in taga zan mutu."
Na girgiza kai tare da fadin Aiko sai dai ka mutu, domin ni bazan taba dawo makaba matsawar ka sake ni, sai dai in sonka ya zama ajalina. Na daga yatsana dan manuni, na ce na rantse da girman Ubangijin daya busa min numfashi in har ka sake ni har.... Sai sai naji ya toshe min baki, yana fadin "Bazan sake ki ba Babyna. Karki rantse, ni mijinki ne na har abada, zan san ya zanyi in fahimtar da Hajiya cewa ke din mace ce mai wahalar samu. "
Haka dai muka yita gardama, wannan lamarin ya hana Shamaki sakat shima ya rage bacci ya shiga addu'a Allah ya sa Hajiya ta hakura.
Cikin kwankin Hajiya ta zama cikin yawan damuwa tare da ganawa da lauyoyin su har na fara tunani duk cikin aikin hada sakamako na ne.
Azima ciki yana ta girma har ya fito, amma daga Hajiya har Shamaki banga suna wani marari akan cikin ba.
Mubina ta wayi gari tana irin wannan suman wanda yara ke ayi a yananyin karshen damina. Aka kwatar ta a Asibiti ni ce a gurinta. Randa muka kwana biyu tana kwance ta tada kai da cinyata tana cin ayaba. Sai ga wata mata ta turo kofa ta shigo da sallama. Na amsa tare da yi mata sannu da zuwa, na nuna mata kujera, ta zauna muka gaisa. Tace baki sanni ba ko? " Kafin in amsa sai naji Mubina ta dago da sauri tace, Anty. Matar ta janyo kujerar ta matso gaban gadon tace Mubina ya jiki? " Take na gane mahaifiyar ta ce, Na daga ta na zaunar suna kallon juna. Ta kamata ta rungume tsam sai hawaye a idon Uwar, nace Allah sarki, ki yi hakuri ai jikin nata da sauki. Tace 'Yar uwa ya mai jikin nace da sauki. Tace kece matar Shamaki? " nace e. Tace "Kin shekara a gidan Shamaki? " Nace A a, saura kwanaki. Tace "Kin haihu? " Nace ban haihu ba. Tace ki godewa Allah domin da kin haihu sai kin fi fuskantar tashin hankali da damuwa.
Mutuwa ita kadai ke iya raba da da mahaifi sai kuwa gidan Alhaji Baita. Da ana kawo su hutu yanzu kuma an daina gaba daya. Jiya na yi wani mugun mafarki game da Mubina. Na kira Shamaki da farko bai fada min ba, sai na soma kuka ina fada masa cewar ina son ganin yarinyata, nayi wani mafarki a game da ita, in har na rasata zan bi ba a sin haka. Shine ya fada min wai kuna nan bata da lafiya. " Nace sai hakuri, domin bawa baya tserewa kaddarar sa. Ni kam tuni na yi imani cewa zan bar gidan na saka raina cewa ta ina cika shekara. Tace "Haka zai zo miki da dan sauki, ni dama ba wata soyayya muka yi da shi ba, amma ya iya kalamai ga iya wanka, sannan mutum yana ganin daula, kinsan dole ya rikice rana daya a diro a ce ka fice. " Nace Dama ba wata tambaya da aka ce Hajiya na yi duk karya ce? Tace zata tambaye ki game da wasu abubuwa musamman na rabon zakka da kujerun hajji, kamar ni dama da tace in raba uwa da ubana sune farko sai kannasu, san nan na sirka danginta biyu. To ko banza dai sun meta hazo. Sai kuma ta tambaye ki waye Shamaki. Ni cemata nayi danta ne mana. Saine tace in fice mata. Amma rabani da 'yarnan yafi komai ciwo a gurina. Nace dole zata nemeki bare "ya mace in ta samu gidan mijinta lokacin da zata ke zuwa ina za su sani. Tace "Amma kafin hakan ai an wahala da sauran lokaci. Nace kiyi ta mata addu'a muma ko bana gidan zan kasance mai musu addu'a domin ina so su yarannan dukansu. Tace Na gode ke ma Allah ta baki ko ba a nan ba, ya kula mana da su baki daya. " Nace Ameen muna ta hira tana bani wasu 'yan bayanai, kuma na yi mata alkawarin zan binciko dalilin da yasa aka daina daina kai yaran hutu. Da kyar ta iya tafiya sai da wanda ya kawota ya shigo ya lallasheta. Haka ta barmu cikin jimami.
.....
*HAMSHAƘIYAR UWA🧕🏻*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*
*💃🏻💃🏻💃🏻Masoya masu jiran littafin HAMSHAKIYAR UWA Complete Document,a yanzun haka ya kammala akwai document din HAMSHAKIYAR UWA Complete game bukata zai iya tura kudi kai tsaye ta wannan account number ₦600👇🏻*
*0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a turo shaidar biya ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn*
*Phone 08140004302*
Shamaki ya shigo dakin Asibitin da dare, ya same mu muna hira da Mubina tana bani labarin Antynta yace wacece Antinta. " Nace wai Maman ta, yace to mu hada kaya mutafi an sallame mu". Nace to. Mubina ashe tana rike da maganar sai cewa ta yi, Mommy ba kince zaki tunawa Daddy a kaini gidan Anty ba. " Shamaki yace "Wacece kuma Anty? Nace Mamanta, mana meyasa yanzu aka daina kai su hutu ne? Yace "Uwar Meema ta ja musu, tana fadawa yarinyar abubuwan da basu kamata ba, kuma tana yi mata tambayoyi yarinyar ta zo tana min tambaya a gaban Hajiya Wai Maman ta tace Hajiya tana yi musu wasa ko sai fada. Sannan wai in an basu kudi tana boyewa in za a kawo ta sai ta saka a kayanta ta kaiwa maman. Shine Hajiya tace baza a kara kai su ba." Nace gaskiya bata kyauta ba gashi ta sa an shiga hakkin saura, domin su baruwan su, amma ba zai yiwu a kai su sukadai ba. Dakatarwar dai shine abinda ya dace a yanzu ha na har abada ba. .
Muka isa gida Hajiya tana kwance a gurin da take salla, ban taba ganin ta kwanta a gurin ba, na isa na zauna kusa da its nace Hajiya lafiya kuwa naga kin kwanta. Ta tashi zaune fuskar ta ta fada. Nace bakya jin dadi ko? Tace bana jin dadi amma da sauki. Shamaki ya iso shima ya tsugunna, yace Hajiya tun jiya nace baki da lafiya kin ce a a. Ta yi dan murmushi zazzabi ne kuma na samu sauki, karfine kawai bani da shi. Muka yi mata sannu, ya zauna ni kuma na shiga ciki dan in watsa ruwa.
Satin da Zan cika shekara Shamaki ya sanar da ni cewa zai tafi China daga can zashi Dubai. Kuma gaba daya tafiyar sati biyu zai yi. Nace to in ka tafi gashi saura kwana shida in cika shekara to kuma in banci jarabawa ba, yaya za ayi baka nan? Yace "Yadda za ayi ke nan ta yi hakuri domin haka na kirkiri wannan tafiyar sai dai na yi mamaki da ya kasance bata hana ni ba, kila hakan yana nufin cewa bazata raba mu ba. " Nace kar ka saki jiki akan haka kuma sai ka tafi tace ka turo sakin ta waya. Yace "Wai ke baza ki taba fadi alkhari ba saboda Allah?" Nace to ai bana son in yaudari kai na ne, saboda ko zan tafi dai dama na dangana. Ya rungume ni insha Allahu muna tare har abada, sai naji dumin hawaye a kafatata. Nace dago dasauri, kuka kuma Shamaki? Na fada cikin mamaki. Yace Tunda shekara ta gabato sai ina samun kaina cikin yawan kuka da damuwa, wanda nasan cewa tsoron rabuwa da ke ne. Na sa hannu a fuskar shi ina shafo hawayen nima sai naji nawa sun soma sauka.
Ya tafi ya barni cikin jimami. Ranar da ya tafi da dare wayar cikin gida ta bugs misalin Karfe biyu na tashi na fita. Nasan cewa munyi sallama da Hajiya na kuma shafa mata man zafi.
Na fito
ba kowa a falon Hajiya na nufi dakinta, Tana zaune a tsakiyar gado, na shiga da sauri ina fadin Hajiya lafiya? Tace lafiya kalau zauna. " Na zauna jikina sai kyarma ya ke yi. duk na firgita. Ta kalle ni sosai tace "Me ya ke baki tsoro? " Nace Ba komai na yi tsammanin baki da lafiya ne. Tace lafiya ta kalau kwantar da hankali. Ta kara matsowa, kin kuwa san dalilin da yasa na bar mijinki ya yi tafiya? " Gabana ya yanke ya yi wata muguwar faduwa, nace a a. Tace "Saboda in har yana nan bazai taba barina in yi hukuncin da ya dace ba, saboda son da ku ke yi wa juna wanda ni kadai na san dalilin son. Ina fata kina aje da lissafin kayan azumi wanda ki ka raba, shine zaki gabatar min da lissafin."
Na tashi cikin fargaba naje na dakko takardar na dawo. Nace gata nan. Tace to kowanne zaki fada min dalilin da yasa ki ka bashi abinda ki ka bashi. " Na kalle ta cikin rashin fahimta, naji zuciya ta ta fara zuwa wuya, tana fadin wai gidan nan na Aljanna ne da nake ta fuskantar damuwa da wasu ka idoji? Wata zuciyar ta bani amsa da cewa ba gidan Aljanna bane amma na neman Aljanna ne. Dan haka sai lallashi zuciyata sannan nace ban gane abinda ku ke nufi ba Hajiya.
Tace misali ai kin ba kanina kayan abinci da kudi ko?" Nace E, Tace to fada min dalilin da yasa ki ka bashi. " Nace To gaskiyar magana ni dai na yi la'akari da kusanci, domin musulunci ya nuna mana muhimmanci fara taimako daga kusa kafin kaje nesa. Tace "su Juma fa? " Nace ai na fada muku kwanaki, suma kusancin ne sannan suna yi mana hidima duk da muna biyansu kyautatawa yana da dadi.
Sannan taimako ne. Na numfasa, don Allah Hajiya kar ku tambaye ni dalilin da yasa na baiwa sauran domin ban san su ba. Tace 'To ya akayi kika basu? " Nace nabi layin sunayen ne har zuwa adadin kudin daga nan na fara da wadan da ba kudi, su kuma daya zan iya fada miki wani abu akan su ba, saboda suma layin na bi, sai guda daya wadda itama ta fada min ne da kanta.
Tace "Wa kenan? Nace Wata tsohuwa makauniya. Ta zuba min ido da alamun mamaki a tare da ita, a hankali ta ce "Kinje Fage kenan? "
Gabana ya yanke ya fadi, ba shakka bazan yi wata karya ba, ko da banci jarabawa ba na san dai bazan zargi kai na da kar ya ba. Nace naje Fage Hajiya gurin tsohuwar nan.
Hajiya ta yi shiru tana kallon gefe daya, kamar tana tunanin wani abu. Can ta numfasa sannan tace, "Ban tsammaci cewa kema irin wannan hanyar zaki bi ba, amma dai zan yanke hukunci ne kawai daga abinda kika fada. Ta sakko daga kan gadon ta yi dan tattaki a hankali, ta kai kan wata kujera dake manne a jikin gadon ta zauna, sannan ta ce.
"Jikina ya yi sanyi domin na gama yanke shawara cewa ke ce matar gidan nan, amma sai gashi kuma kin kama hanyar neman jin sirrin da da kin yi hakuri da na fada miki shi daga bakina kuma sahihin labari. Amma zan yi miki uzrin na sauraronki sannan in auna, zan kuma baki makin ki cikin adalci.
Kafin inji abinda ya kai ki gidan tsohuwa da kuma abinda ki ka jiyo da sauran abubuwan da suka biyo baya ina son ki taya ni kallon wannan. "
Ta kunna TV da Remote din hannun ta. Cikin sauri na maida kai na ga kallon TV.
Ba kamar fimba da za a nuna can da can ko sunaye, Hotona ne ya bayyana. Gani lokacin da ake shigo da ni, babu magana hoton ne kawai, ga lokacin da za a kaini daki na, sai kuma ga ni ina neman dakin Shamaki, Sai kuma aga Juma ta nufi dakina da kayan abinci. Sai kuma lafon Shamaki, duk ga shinan lokatan da muka zauna ko muka ci abinci ko wasu dai 'yan wasanni ba masu yawa ba. Haka kuma ga lokacin da Azima ta shigo falon kuma ga lokacin da ta shiga dakin Shamaki. Zuciya ta dauki zafin takaici kamar a lokacin abin yake faruwa. Har na tambayi kai na ina ina a wannan lokacini.
Sannan ga lokacin data fito.
Haka dai muka yi ta kallo, akwai gurare da na yi ta fargabar kar a gani gurin duba wayar Shamaki amma sai da wani guri daya ya fito da na dauka a falon. Sai anan Hajiya ta yi magana idanunta suna kan TV din, tace 'Wannan ba wayar Shamaki bace? " Nima ba tare da na dauke kai ba, nace ita ce. Me kika yi a ciki? Nace duba masa sakwanni na yi. Sai lokacin ta waigo ta kalleni, kina zarginsa ne a lokacin? " Nace kwarai kuwa. Tace me yasa ki ke zargin sa? " Nace akwai wani guri da aka wuce, inda zan shiga dakin na dawo baya har nayi karo da fulawa ya zo yana kirana ban dawo ba, shine dalilin da yasa na binciki wayar sa.
Ta tsada TV din,
Me ya faru a lokacin? " Nace samu yana waya da wata mace wadda ta turo masa hotuna na sassan jikinta, yana yabawa da hotunan, yana fadin wasu kalamai da suke nuna jin dadin kasancewar su da ita. Na juyo da sauri domin bana son ya ganni bare yaji kunya tunda ya san na yarda da shi kuma in wani ya fada min cewa Mijina yana neman mata bazan yarda ba. Kuma sai Allah ya kaddara na ji da kunne na. Garin in gudu karya ganni sai fulawa ta fado shine ya biyoni. Hajiya ta sauke ajiyar zuciya. Tace "sai me ya faru daga nan? " Nace kawai naje nayi kuka ne a daki ban fada masa abinda ya faru ba har zuwa yau? "Me yasa baki fada masa ba? "Hajiya ta katse ni da tambaya. Kila ya musa, domin ban kamashi ido da ido ba, ko ya fusata ya dauki matakin da bai dace ba a cikin borin kunya. Na san cewa ta hanyar tattaunawa ne kadai ake iya warfare matsala.
Shine na fara bincikar wayar sa domin in samu tabbbain abinda naji. Anan na gano yadda suka shirya da wata yarinya zasu hadu a wani Hotal a ranar wata lahadi. Hajiya tace "To na fahimci cewa lahadin da ki ka yi karyar ciwo ce domin kar ya fita." Na jima ina tunanin dalilin wannan karyar. Na.
Ce yawwa haka ne, sai kuma ciwon duba wayar ya kamani wanda kullum na duba sai na ci karo da sabon bakin ciki wanda sai dai in shiga daki insha kuka na. Hajiya ta dube ni, ta girgiza kai, sannan tace "Wane matakin ki ka dau ka". Nace fatan shiriya nake ta yi masa a gurin Allah, kuma dai har zuwa lokacin da ya yi wa Azima ciki ina cike da tashin hankali game da zaman mu. Zubur Hajiya ta mike tsaye, ta tsura min ido, "Da wane lokacin ya yi wa Azima ciki.? "A raina nace kaji wani raining wayo. Sai nace. Ban san da wane lokaci bane amma doke zai zama a cikin lokutan da take zuwa dakin shi ne ko suke fita, bana zaton cewa ko su zasu iya sanin lokacin. Hajiya tace "Ke nan kinsan tana zuwa to kina matar shi ke kina ina? Nace Hajiya bansan tsawon lokacin da suka dauka suna yin abin su ba. Kilama kafin in zo ne, haka kuma ai suna fita Hotel kamar dai yadda ki ka datse yin hakan ta hanyar daura musu auren gaggawa. Hajiya ta zauna a bakin gado, sannan ta kure ni da kallo. "Wane kokari ki ke yi zuwa yanzu domin ganin ya bar duk wadannan dabi u.? " Na ce zuwa yanzu ya san na san komai, ban yi rigima da shi akan haka ba, kuma na fahimci Allah ne kawai zai rabashi da haka, saboda haka shi nake fadawa, ina saran zai shirya shi lokaci daya. Sannan ina kokari fita hakkin shi yadda ba zai zama cikin bukata ba sai dai wani abu na sharrin shaidan.
Hajiya ta kada kai cikin gamsuwa. Sannan tace, bazaki nemo wani taimako ba ga masana domin hana shi aikata duk irin wannan biye biyen? " Nace Hajiya Allah shine mafi girman mai bada taimako nasan zai yi haka, sannan bazan tauye shiba in yana da bukatar sake aure fa tunda na karanta a wani group cewa maganin hana maza su nemi mata wani sihiri ne sai dai su tsaya ga ke kadai in sunje gurin wata baza su iya yin komai da ira ba. Hajiya ta ce je ki hau gadonki ki kwanta zamu dora gobe,. Saura kwana uku jara bawarki. Kin yi kokari sauran tun a text suka fadi,. Na kalle ta, ba wannan ce Jarabawar ba? Tayi murmushi Ai kin san kafin Jarabawa ana yi Text ko? Ban iya amsawa ba har sai da na kai kofar fita na waiwayo nace sai da safe. A daki ina kwance in tunani in har wannan text ne to ya jarabawar zata kasance?
*💃🏻💃🏻💃🏻Masoya masu jiran littafin HAMSHAKIYAR UWA Complete Document,a yanzun haka ya kammala akwai document din HAMSHAKIYAR UWA Complete game bukata zai iya tura kudi kai tsaye ta wannan account number ₦600👇🏻*
*0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a turo shaidar biya ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn*
*Phone 08140004302*
.....
Da safe bayan na yi salla na koma bacci saboda zaman cikin dare da muka yi da Hajiya Bacci mai nauyi ne ya sani na makara. Kwankwasa kofar da Juma ke yi shine ya farkar da ni, ashe wayar cikin gida ta jima tana ruri amma ban ji ba saboda bacci.
Na tashi da sauri na bude kofar Juma ce nace lafiya Juma na ganki da sassafe? Tace ni da matter gidan muka taho, Hajiya ta kira mu. " Nace har na zaci ko haihuwar ce. " ta ce a a, lafiya baki fito ba? Nace lafiya lau. Tace Hajiya tana neman ki, na shiga ban daki na yi fitsari sannan na fita. Hajiya bata falo na shiga dakin ta. Tana zaune akan kujera ta nuna min wani akwatin ga kayan ta a kusa da akwatin tace, " Shiry
0 comments:
Post a Comment