Abun da ya fara basa mamaki shine tsarin garin, ashe haka Niger ɗin take? Duk zatonsa ya ɗauka Agadez a Niger wani yanki ne na sahara wanda babu wayayyu acikinsa, zatonsa ba haka garin yake ba. sai yaga yankin sahara ne amman wayayyu ga kuɗi, ga mulki ga gine-gine kamar ba ƙasar Hausa ba.
Bai gama shan mamaki ba sai lokacin da aka tarbesa dan zuwa gidan can Attahiru Algabid ɗin, yasha kallo cikin mota ahanya.
Bai gama mamaki ba sai da aka zo gida yaga tsararren gida mai kyau na kece raini. Ya jinjina kansa ashe haka buzaye sukeda kuɗi? Ya ɗauka dai rufin asirine Algabid gareshi bai zaci haka yake da kuɗi ba, amman yasan fa business ɗin shinkafa akwai kawo kuɗi ya yarda da hakan akan kansa.
Wata irin tarbar Yusuf ya samu ta musamman agida Attahiru Algabid, tun daga masaukinsa da kalar abincinka da aka tarbesa yasan lallai yazo gidan karamci da sanin ya kamata.
Bayan gaishe-gaishe, aka barsa ya huta kasancewar dare ne.
Wanka ya yi da ruwa masu ɗumi ya fara shan tea wanda aka haɗa masa na musamman, ya yi sallolin da ake binsa kafin yaci abinci.
Adaren Algabid bai barsa ya kwantaba sabida daren auren ne, haka suka ɗauke shi a mota suna yawo ana nuna masa wuraren tarihi, duk inda suka je sai Yusuf ya yi hoto.
Washegari, aka tashi da shirye-shiryen ɗaurin aure, Yusuf yanata kallon al'adunsu na aure wani ya yi video wani ya yi murmushi ya girgiza kansa.
Ana dab da ɗaurin aure Yusuf yaji cikinsa ya ɗan murɗa yasan ba mamaki canjin abinci ne da ruwa, yama Algabid bayani zai ɗan shiga ciki ya fito kafin ƴan ɗari aure su ƙaraso.
Lokacin da Yusuf ya shigo ɓangaren da aka sauke shi dan shiga toilet, yana shirin buɗe ƙofar mace na fitowa aciki, karo sukayi ta saki ihu tana ja baya, da harshen buzanci tana faɗin.
"Kayi haƙuri wlh matsuwa nayi da fitsari shine Ghaliya tace nazo nan ɓangaren ba kowa."
Ta faɗa tana runtse idanunta, ta duƙe a ƙofar toilet.
Yusuf tunda uwarsa ta haifeshi bai taɓa tunanin zaiga yarinya kyakkyawa wadda kallon farko zaiji ta kwanta masa har cikin ransa, kallo ɗaya yaji ya kamu da ƙaunarta ba sai Sa'adah.
A tsarinsa da farko baya son mai kyau sabida kar ta dinga ja masa aji, anasa tunanin zasuyi Manage da kyawunsa ba wai sai matarsa tanada kyau ba, tunda shi yanada idan ta kasance mai tarbiyya da kyawun hali ya wadatar.
Da manyan lumsassun fararen idanunsa yake binta da kallo, yana sakin murmushi, ba ƙaramin kyau shigar jikinta ta masa ba.
Ya ɗan ɗuko nesa da ita cikin taushin murya da nutsuwarsa ya furta.
"Bansan me kika ce ba, maimaita da Hausa Please, kinji kyakkyawar buzawa."
Dara-daran idanunta wanda suke farare ta ɗago ta kalleshi sai ta yi saurin sadda kanta ƙasa, tana wasa da yatsun hannunta wanda suka sha zanen jan lalle, ahankali ta shiga maimaita masa abinda tace da Hausan.
Anutse yace.
"Ok ba komai me sunanki?"
Bata kalleshi ba tace.
"Sa'adatu ana kirana da Sa'adah."
Ta ƙarashe maganan ta miƙe ta fice aguje.
Yusuf yabi bayanta da kallo yana murmushi, sai kuma ya yi saurin bin bayanta yaga inda zata shiga, sai yaja ya tsaya, ya juya ya shiga toilet din aransa Yana jin ya yi mata idan har za'a basa.
Duk yadda Yusuf ya yi tunanin auren buzaye abin ya wuce saninsa da tunaninsa shi dai kam ya sha kallo, wuni gudu Sa'adah tana maƙale acikin ransa, amman kuma bai sake ganin ko walƙiyarta ba.
Can ɓangaren Sa'adah yanayi ne mai girma ta tsinci kanta acikinsa tun haɗuwarta da Yusuf, batada kuzari, ko idanunta ta rufe ta buɗe fuskar Yusuf take gani, hakan ya saka tabar gidan bikin ta gudu gidansu, duk kuwa yadda suke abota da Ghaliya amarya.
Sa'adatu Mas'ud Siddi buzaye ne gaba da baya haifaffun Agadez mahaifinsu yanada kuɗi sosai kuma wayayye ne su biyar ne ya'yansa.
Saliha wadda suke kira Salha ita ce babba sai Mubarak Sharif Nusaiba Sa'adatu, ita ce ƙarama wanda shekara ɗaya ne tsakaninsu da Nusaiba aka haifeta suka taso kamar ƴan biyu.
Sa'adah sun samu tarbiyya wajan iyayansu, sunyi karatu na boko da addini, cikin ikon ALLAH Dukansu kowa ya sauke Qur'ani mai girma.
Salha tanada aure da yaranta Mubarak ma yanada aure Nusaiba tanada aure Sharif da Sa'adah ne kawai basuda aure, alokacin da suka haɗu daYusuf.
Sa'adah ta kasance kyakkyawar buzuwa mai diri sosai tanada kirki batada hayaniya haka batada rikici abu kaɗan yake furgitata ya fitar da ita daga hayyacinta, tanada tsoro sosai dan ko kyankyaso tsoronsa take matuƙa. Sa'adah Shagwaɓaɓɓiyace sosai kasancewarta autah, Aisha Annah mahaifiyarsu MACACE mai kirki da kyauta da son mutane batada ƙyamar baƙar fata irin na wasu buzayen kowa nata ne, ba wanda baya shedarsu a unguwarsu.
Sidi Agali ɗan ƙanwar Annah ne kyakkyawan sauriya buzu na asali ya taso da ƙaunar Sa'adah ya rayu da sonta, baida buri sai na ya mallaketa a duniya, ita kuma ba son aure take masa ba son ɗan uwa na jini take masa.
Sa'adatu tanada masoya dayawa sai dai har yau bata tsayar da mijin aure ba tana dai kulasu kaɗan².
Sa'adah bata jima da kammala école normale ba, wato ta fito malamar makaranta, kenan Amman bata fara koyarwaba saboda ana cikin hutun makaranta sai an dawo zata fara zuwa.
Yusuf da dare bayan taro ya watse ya samu Algabid ya masa tambaya akan Sa'adah ya fadi sunanta da kwatancenta.
Algabid ya ganeta yace.
"Wannan ai ta kwana gidan sauƙi ɗiyar Mas'ud Abokina ce, kuma ƙawar ghaliya, gidansu yaransa masu tarbiyya ne kuma ita ɗaya ta rage ba aure sai yayanta yana karatu itama kwananan ta kammala karatun ta agaba zata fara koyarwa. Idan da gaske kake muje kayi magana da mahaifinta kafin kabar garin sabida kar kaje kayi ƙwabron baki ayi ciki da kai."
Yusuf baiyi ƙasa aguiwa ba, ya amince suka tafi gidansu Sa'adah.
Sun samu tarba mai kyau daga Mas'ud mahaifin Sa'adah, yace yaje ya nemi yardata idan ta amince da aurensa zata bisa ƙasar su da yaje ƙasar zai iya ya turo da magabatansa babu laifi, tunda Algabid yasan mahaifiyarsa.
Ai kuwa Yusuf yaji daɗin karamcin Mas'ud cikin ikon ALLAH kwana biyu kacal, Yusuf da Sa'adah sun dai-daita tsakaninsu,ya bata tarihinsa itama ta basa nata tarihin, sun ƙulla alaƙar soyayya mai ƙarfi, wanda har Agali ya ciwa Yusuf mutunci ya masa korar kare akan bazai taɓa aurenta ba idan yana raye shine mijinta, sai da magana taje wajan manya Mas'ud baiji daɗi ba nan akaba Sa'adah zaɓi tace Yusuf take so shi kenan magana ta mutu, amman Agali bai fita harakarta ba.
Kwana huɗu Yusuf ya yi a Agadez saboda Sa'adah kafin ya wuce Nigeria.
Yana zuwa Mahmood ya hausa da faɗa sai da ƙyar ya saurareshi, ya masa bayanin abinda ya tsayar da shi, akan Sa'adah, da farko Mahmood ƙi ya yi yace duk matan da suke Nigeria sai yaje Niger ya kwaso mace, macan ma buzuwa, tazo tana mulkarsa.
Daƙyar da lallaɓawa ya masa bayanin tarbiyya yarinyar da Dattakun gidansu, duk da haka Mahmood bai yarda ba sai ya saka wani abokin kasuwancin mahaifinsu dattijone na kirki ya saka aka masa binciken gidansu Sa'adah, ya tabbatar da gidane na mutunci ne.
Bayan zuwansa da wata biyu lokacin soyayyarsu tayi wata irin nuna, lokacin ne su Mahmood Abdulkarim da Jamilu ƙanin mahaifinsu Yakubu suka shirya tafi Niger nemawa Yusuf auren Sa'adah.
Daman sun ajiye magana za'a kawo kuɗin aure da akwatuna tare, sabida nisa bazai yiyuba ace halo su koma kai kaya dan haka aka tafi da Hajarah da Rafi'atu ƙanwar Murja suma an sakasu cikin sabgar, hakan yayiwa Hamisu daɗi wanda shi sai ɗaurin aure za'aje da shi.
Tsaddaun akwatuna Yusuf ya yiwa Sa'adah shaƙe da kayan zamani wanda ba abinda bai saka mata ba, harda kayansu na buzaye da tafi so wanda shi yake tura mata kuɗi tana zaɓo duk irin kayan da take so sai da ta gama siyan irinsu kakaf kalar kayan da take so na Bugaje ta turo masa ya zuba cikin akwatin wanda ya kashe maƙuddan kuɗin da bai san nawa ya kashe ba.
Sosai baƙin suka samu tarba mai kyau wajan iyayan Sa'adah.
Kusan dai auren buzuwar mace da tsada, sadaki akan mahaifinta yace baya son kuɗi dayawa millon da rabi suka biya kaya kuma akwatuna 12 cif shaƙe da kaya dangi sun yaba suna mamaki ashe ba buzaye kawai sukewa mace kaya ba masu uban yawa?
An saka rana wata uku masu zuwa, za'a sha biki, wanda ƴan ɗaurin aure idan sun zo zasu tafi da amaryarsu.
Sun kuma amince da sharaɗin mahaifinta Yusuf zai samo mata aikin koyarwar acan Nigeria sai ta dinga koyawa yaran French tunda akwai malaman French a Nigeria, wanda shine burin Sa'adah ta fito malamar makaranta.
Rafi'atu sun sha tukuici ba kaɗan ba da karramawa, Wada har suka baro ƙasar Niger suna santin Agadez da yabon matar Yusuf da danginta.
Hajiya Murja sosai take murna babban ɗanta zaiyi aure ta yaba kyan Sa'adah sosai.
Aure yana sauran sati ɗaya Ikram lokacin cikinta ya shiga wata shidda da kwanaki ƙalilan, Adam da kansa ya kawota.
Yusuf ya gama gina gidan mai masifa kyau na zamani wanda ya ƙeru iya ƙeruwa, part biyu ya yi manya-manyan sabida ya saka aransa Momy Murja na nan tafe sai ta zauna dasu kowa na part ɗinsa.
Iyayan Sa'adah Ana biki sauran kwana biyar suka turo Salha da Munnira da Tanti Mimi gyaran ɗaki wanda a Kano Mubarak ya shiga gaba suka siya mata fitinannun kayan ɗakin da kitchen komai na ƙasar waje suka siya masha Allah sunyi rawar azo agani an kashe nera bikin autah.
Sosai suka tsara mata gidanta gadonta da kujerun carpets labulaye komai iri dayane, milk colour ne, kitchen ma an ƙawatata tunda aka ce musu kallon amarya na kitchen suka dage kuwa suka kashe kuɗi wajan ƙawata kitchen ɗinta.
Yusuf ma ya zuba kaya ana Bedroom ɗinsa da falonsa, amman shi komai maroon colour ya saka anasa ɓangaren.
Sai ɓangaren mahaifiyarsa Ash colour ya zuba mata.
Kullun cikin tsammanin zuwan Hajiya Murja su Yusuf suke, amman sai me shiru kakeji ba labarinta, ta shiga musu kame² har biki yazo, Ikram tasha kuka ta Kuma ɗauki alƙawarin koda bayan bikina sai tasan ƙaryar da ta ƙulla wadda hankalinta zai tashi sai tazo koda batada shirine.
Can Niger amaryar Sa'adah tasha gyara ba kaɗan ba irin nasu na buzaye tsayawa faɗin yadda ta koma ɓata lokaci ne, maganin mata nasu na gargajiya na gyaran amare aka mata, ta tsumi iya tsumuwa.
Ana gobe ɗaurin aure dangin Yusuf suka iso Agadez, washegari aka tashi da shagalin biki, ɗaurin auren safe akayi, dubban al'umma suka sheda ɗaurin aure tsakanin Sa'adatu Mas'ud Siddi da Yusuf Yakubu Yunus mai shinkafa akan sadaki mai daraja.
Inda Banbino ya cashe abun ba'a cewa komai, biki ya ƙaryata jama'a dayawa sunyi wa Yusuf kara zuwa ɗaurin auren duk da uban nisan da yake tsakanin Gombe da Agadez.
Sa'adah tanaji tana gani aka ɗauke zuwa wata uwa duniya dan bautar Allah, wato zaman aure.
Tasha nasiha da faɗa wajan mahaifiyarta haka mahaifinta sai dangi na kusa yayarta Salha da tanti Mimi sai ƙawar Sa'adah Adiyah, su uku ne sukayi rakiyar amarya zuwa ƙasar Nigeria Gombe.
Can Saudiya Haj Murja taci bikinta hankali kwance an tara ƴan duniya anyi shagali, ansha raye-raye kamar baza'a mutu ba kai idan kunga yadda aka Tarawa Murja jama'aaaa da kuɗi abun ba'a cewa komai, su Lubnah ƙirjin biki.
Washegarin da amarya tazo gidan mijinta su kuma ranan akasha biki nan Gombe, wanda anyi shagulgula ba laifi anyi dinner anyi walimar burgewa kowa na yabon kyawun matar Yusuf.
Su Aunty Salha kwanansu uku suka juya wanda Sa'adah ta dinga haukan kuka, daƙyar Yusuf da Ikram suka shayo kanta.
Randa baƙi suka koma Yusuf bai ɗagawa Sa'adah ƙafa ba, ya gwangwaje amarcinsa inda ya sameta cikakkiyar budurwa, wannan dare Sa'adah tace sun gina wata irin soyayya mai wuyar mantawa kamar yadda baza manta azabar da taci ahannunsa ba.
Daga ranan bai sake taɓata ba sai dai da ta cika sati agidanta wanda suna shirye-shiryen tarbar zuwan Momy Murja mafarin ƙaddarata take shirin zuwa ƙasar Nigeria.
*DAWOWAR LABARI*
Hajiya Murja kusan suman wucin gadi tayi, lokacin da taji tattausan jikin surukarta manne da jikinta ba.
Tunda take aduniya bata taɓa jin jiki mai taushi da daɗin runguma ba da sanya nutsuwa ba, irin jikin Sa'adah. A take taji jikinta ya ɗauki vibration, wata irin fitinanniyar sha'awar yarinyan da sonta alokaci ɗaya suka mata dirar mikiya, ta yi saurin sanyan hannayenta ta rungume Sa'adah gam-gam tana sauke nannauyar ajiyar zuciya, wanda take mahaukacin bugawa.
Jin Sa'adah na mutsu² tana son janyewa, cikin dubara take goga ƙirjinta dana Sa'adah, taji wani irin hatsabibin taushin ƙirjinta na ratsa nata ƙirjin, take gashin jikinta ya fara mimmiƙewa, ta yi saurin sakin Sa'adah tana kamo hannunta, cikin sakin fuska tana danne abun da yake ɗawainiya da ita, tace.
"Baby Sa'ah! Na samuku lfy? Ashe dai balarabiya Yusuf ya auro mana koh?"
Ta faɗa tana nufar kujera da Sa'adah.
Wacce kunyar surukar tata take sosai, kanta aƙasa bata iya cewa komai ba.
Mahmood dasu Yusuf suke musu dariya.
Aydah kamo hannun Ikram suna bin bayansu tace.
"Goggo mu bakya tattalinmu sai Aunt Sa'adah koh?"
Murja tayi dariya tan
Zaunar da Sa'adah, ta zauna kusanta tana sakin hannunta, ta maida hankalinta wajansu ikram.
Tana kallon Ikram Tace.
"Bani wannan ledojin, wai Aydah ce ta girma haka? Ashe banga komai a hoto ba, haba! Aydah Ni na isa naƙi tattalinku babbar jika, amman Don Allah ku daina cewa goggon nan."
Ikram ta zumɓuro baki gaba tana ɗaukan ledojin tace.
"Kai Momy ai Ni daman bakya sona hummm ga shi yanzu ta ɗiyarki Sa'adah kike."
Sa'adah ta yi murmushi tana ma ya Ikram gwalo.
Yusuf ya zauna kusan mahaifiyarsu yana jin nutsuwa ta saukar masa.
Ledojin ta duba tana cewa.
"Fadilah ga tsarabarku keda Halimah da yaranku."
Fadilah da Halimah suka haɗa baki wajan godiya har yaran.
Mahmood yace.
"Momy Ni ban dani kenan?"
Dariya Murja ta yi tace.
"Ni na isa agaba zan warema kai da ƙanninka."
Yusuf yace.
"Ni fah?"
Ikram Tace.
"Agaba zaki bamu koh Momy?"
Ta faɗa tana kwanciya jikin mahaifiyarta.
Momy ta shafi cikin Ikram Tace.
"Allah sauke min ke lafiya.
Mahmood ai kun kyauta har dakai aka haɗa baki aka saka nazo a haukace? Amman zuwan fa ya yi naji daɗin hakan ALLAH ya muku Albarka, gani cikin iyalina. Mahmood muje akaini naga Auntie Mairamu fatan tana lafiya? Daga can na wuce gidan yaya Hamisu kasan fushi suke dani ba zuwa zasuyi wajenaba."
Mahmood yace.
"Toh kici abinci sai mutafi, ai Momy gaskiya baki kyautaba ne kuma in Sha Allah bazaki komaba kinzo Kenan."
Murja ta zaro idanunta tana kallon Sa'adah tace.
"Wai Baby Sa'ah da gaske bazan koma ba kuna son zama dani?"
Sa'adah ta kalli surukata cike da jin nauyi tace.
"Eh Momy don Allah ki zauna damu karki koma."
Hajiya Murja tana kallonta ta sauke numfashi tana kamo hannunta awayance take murzawa tace.
"Shi kenan Baby zan duba..."
Sa'adah ta sake damƙe hannunta tace.
"Please Momy don Allah karki koma muna sonki dayawa karkiyi nisa damu."
Momy ta rungumeta akaro na biyu tanajin wata irin fitinanniyar soyayyarta na huɗu kowace ƙofar mahuɗar gashin jikinta.
"Ok Baby naji zan zauna nima ina sonki."
Ta faɗa tana saurin sakin Sa'adah sabida tsaro, ta kalli Mahmood tace.
"Zan zauna rikici ya ƙare..."
Yusuf yace.
"Part ɗinki na shirya komai idan kin huta kwana biyu gidan babban yaya sai ki koma can."
Mahmood yace.
"Mun gode Momy ALLAH ya ƙara lafiya da girma."
Ta amsa da.
"Ameen."
Tana buga bayan ikram da ta rungumeta tana murna da zuba mata godiya.
Sa'adah tace.
"Momy mun shirya miki abinci acan da kayan marmari da maƙulashe.
Please babban yaya muje can dukkanmu daman baku taɓa zuwaba dasu Auntie's Fadilah don Allah muje can idan taci abincin sai ku wuce Tumfure gidan Umma koh?"
Ta faɗa kanta ƙasa.
Mahmood yace.
"Toh ƙanwata bazan ƙi miki alfarma ba muje ɗin, Fadilah ku shirya yaran."
Ya faɗa ya nufi ɓangarensa yana kiran Abdulkarim a waya.
Sa'adah cike da ladabi tace.
"Ngd babban yaya ALLAH ƙara girma."
Yana wucewa ya amsa da.
"Amin ya ALLAH.
Yusuf ya miƙe cikin nutsuwarsa murya mai taushi ahankali ya furta
"My Hayatie! Zo ki sameni a mota na baki saƙo kafin su Momy su shirya."
Ya faɗa yana zura hannayensa cikin aljihun wandonsa, ya nufi hanyar fita daga falon, cikin nutsuwarsa.
Cike da kunya ta ɗago ta saci kallon mutanen falon taga ba kowa sai Ikram da Momy.
A kunyace ta miƙe zatabi bayansa...✍🏽
Real ladingo Omu Farisatu😍
*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500
*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦500
2GB = ₦700. 1.5GB ₦1100
3GB = ₦1050. 2GB ₦1600
4GB = ₦1400. 3GB ₦2000
5GB = ₦1750. 4GB ₦2500
*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*_*SHEƊANIYAR*_
```{Suruka}```
_*Free Nobel🫱🏼🫲🏽*_
25/2/2023
_*SADAUKARWA Aunty Hajarah Hajeer Lawal,😘 And lovely Halimat Musa Waziri,Son So domin ALLAH😘*_
😍TUKUICI gareki Hajiya Fadilah Salisu Hamza❤️
بسم الله الرحمن الرحيم
*Chapter 11&12*
Sa'adah ta cira ƙafa dan tafiya tana faɗin.
"Ikram! Ina zuwa yanzu..."
Bata gama rufe baki ba, taji an riƙo hannunta, ta taja ta tsaya, tana waigowa.
Idanu suka haɗa da Murja tana miƙewa tsaye cikin kulawa tace.
Baby Sa'ah muje na baki tsarabarki ki wuce da ita, muje ki zaɓi duk abinda kikeso."
Ta faɗa tana jan hannunta bata saurareta ba.
Sa'adah kunya tasa ta bita, bata iya cewa komai ba.
Ikram ta miƙe da ƙyar tana faɗin.
"Momy! Ai jiranta yake ki saketa zan amsa na fito mata da shi, zan zaɓa mata duk abinda ya dace."
Ta faɗa tana isowa wajansu.
Ganin yadda Ikram take kallon Murja ta marerece fuska, ya sakata sakin hannun Sa'adah sabida kar ɗiyarta taga ta fifita surukata akansu, dan tasan bazata taɓa zargin manufarta akan surukar ta ta ba.
Murmushin dole Momy Murja ta yi tana faɗin.
"Ok Baby kije zata fito miki da tsarabanki zan zaɓi miki da kaina."
Sa'adatu kansa ƙasa tace.
"Ngd Momy ALLAH ƙara girma da lafiya sai kun fito."
Ta faɗa tana gyara mayafin kanta, tare da rataya handbag ɗinta ta doshi hanyar falon dan fita.
Murja ta rakata da idanunta, tana kallon yadda jikinta yake motsawa abin gwanin burgewa, sai kace Sa'adah taje makarantar koyon tafiya.
Ji tayi wani shegen shauki na ɗaukanta, da wani irin fitinannan feeling na taso mata, ta lumshe idanunta tana faɗin.
"Ya Rabbi!"
Ikram ta rungume mahaifiyarta tana faɗin.
"Wai Momy lafiya kuwa? Ni fa ban ganeba? Kodai Aunty Sa'adah Bata miki bane kike wayancewa? Naga duk kin canza ba kamar lokacin da muka shigoba, kallon me kike mata haka? Wlh Momy Sa'adah tanada kirki sosai ga nutsuwa."
Murja ta janye Ikram daga jikinta tana kama hannunta suka nufi ɗaki tana faɗin.
"Maryamu! Ki rufamin asiri ALLAH ya rufamin, dan baki tashi ahannuna ba, da kin gane halina ai wlh da bana sonta ko kuma bata kwantamin ba acikin zuciyata, kinsan ALLAH ko kallonta bazan ba, ina mamaki yadda iyayanta suka amince suka aura mata Yusuf ne, larabawa kinsan basuda daɗi, ina son yarinyar sosai kamar yadda nake sonki da Yusuf. Zo zaɓa mata duk kalar abayoyin da zasu mata kyau, ga takalma nan da turaruka zaɓa mata ki zaɓawa kanki."
Ta faɗa tana nuna mata akwatunan, ta zube akan ƙatuwar katifar, kanta sama tana kallon silin ɗakin, baki ɗaya abinda takeji bazai kwatantu ba akan Sa'adah, wani irin numfashi take saukewa surar Sa'adah kawai take gani a cikin idanunta, tudun taushin albarkatun ƙirjinta takeji na ratsa dukkan jikinta.
Dariya Ikram ta dawo da ita daga duniyar tunanin da tafi, tai saurin ɗagowa tana kallon Ikram da ta yi zaune tana buɗe akwatin ta shiga zaro zafafan abayoyi tana faɗin.
"Momy! Wlh kinban dariya ba balarabiya bace buzuwa ce, ai haka suke zaka zaci larabawa ne. Toh Momy me su suke nema kuɗi ɗanki ALLAH ya hore masa, kyau ALLAH ya basa farin Allah ya basa, nutsuwa tarbiyya, cikar namiji mai kamun kai tamkar wani babban mutum mai manyan shekaru haka yaya Yusuf yake, wallahi bana cire shakkun a ko ina za'a ba yaya Yusuf auren kowace irin jansin MACACE.
Kai wannan abaya zatama Aunty Sa'adah kyau, ga wannan Green ɗin ma."
Momy ta miƙe tana faɗin.
"ALLAH ya albarkaci rayuwar ɗana Yusuf ya kuma kauda idanun maƙiya akansa."
Ikram Tace.
"Ameen Momy ki shirya k
0 comments:
Post a Comment