Bakin na sake turawa. Sannan na ce, “To kayi haƙuri”.
Murmushi Mansoor yay yana kaiwa zaune. “Ai dole ma na haƙura dan bana iya dogon fushi da ke. Ga yaya Musaddiq nan ma shaida ne”.
Murmushi Yaya Musaddiq ya sake saki, ni kuma na ɗan harari Mansoor ɗin. Shima murmushin yay a lokacin, tare da ɗan taɓe bakinsa ya ɗauke kansa gefe. Sai kuma ya sake juyowa gareni. “Mi MD yace dake?”.
Mask ɗin na cire ina kumbura fuska kamar MD ɗinne har yanzu a gabana. Labarin komai na basu, shi kuma ya faɗama Yaya Musaddiq komai tun daga farko. Sosai naga farin cikin abinda nai ɗin a fuskar Yaya Musaddiq, har takai ya kasa haƙuri ya dafa kaina da faɗin, “ALLAH yay miki albarka Kandalata. Abinda kikayi shine dai-dai, dan nima anan banga wani dalilin da za'a baki ƙyauta harta mota ba ki amsa. Ki cigaba da haka, dan gaskiya itace RUHIN dukan MUSULMI na ƙwarai. Sannan ita mace tana bine ta kowacce hanya domin kare mutuncinta da kimarta a al'adance da kuma addinance.”
“Nagode Yaya”.
Na faɗa cikin zumuɗi da jin daɗi. Dan kalamansa sun ƙaramin ƙwarin gwiwa ƙwarai da gaske. Ganin Mansoor bai tanka ba na ɗan juyo na kallesa. Murmushi ya sakar min, nima sai na mayar masa da murtani. Kaina tsaye na ce, “Amma kaima zaka maida musu?”.
“In sha ALLAHU”.
Ya bani amsa cikin tabbatarwa. Nan ma nayi farin ciki, daga haka na mance da dukkan damuwata muka koma hira mai daɗi. Harga ALLAH ina matuƙar son waɗan nan mazajen biyu, dan sunada matuƙar muhimmanci a rayuwata. Sun kuma taka rawa mai ƙarfin gaske da in har zan nuna kaina sai na haɗa da koda inuwarsu ce. Ko kaɗan bamuyi maganar videon nan a wajen ba saboda tsaro, sai da muka koma motar Mansoor sannan muka ƙarasa. Yaya ya bada shawarar mu binciki ɗan sanda mai gaskiya da zamu iya damƙama video ɗin kawai batare da sunanmu ba, kokuma mu haƙura a gogeshi mubar zancen, ko bajima ko ba daɗe idan har halin mutumin nan ne hakkin rai bazai barsa ba. Amma maganar yin fito-na-fito da shi bama ta taso ba a garemu.
Harga ALLAH maganar Yaya Musaddiq bata mun daɗi ba, taya kawai dan mutum nada kuɗi a dinga nuna tsoronsa haka bayan akwai hujja mai ƙarfi a tare da mu. Amma sai na danne yanayina nace mu sakesa a media kawai, dan a wannan zamanin banga wani ɗan sandan da suke hasashen samu ba. Su duka basu goya da bayana ba. Shima Mansoor yana bayan shawarar Yaya Musaddiq ɗin ne. Dole nima nabi ra'ayinsu, duk da tun farko dama ni na fara kawo shawarar kaiwa ƴan sandan, banbancin shawarar tasu da tawa ƙalilance. Bayan mun kammala tattaunawar munbar Yaya anan ni kuma Mansoor ya wuce kaini gida. Muna tafiya muna hirarmu mai daɗi, duk da yaso mu tsaya muci abinci naƙi yarda da hakan. Koda mukaje gidan ma sai da muka ɗan ƙara taɓa hira, duk da dai hirar tamu ma dai akan bikinmu ne, dan iyayensa zasu sake zuwa a satin sama domin saka rana. Ya kuma tabbatar min da bawani lokaci mai tsayi za'a saka ba. Dan shi ya gama kammala komai amarya kawai yake jira. Naji kunyar furucin nashi sosai, dan haka na ɓalle murfin motar na fita abina. Ina jiyo sautin dariyarsa ban kulashi ba, sai da zan shige gida gaba ɗaya ne na juyo. Ido ɗaya ya kashe min, aiko nai wuff na afka ciki..
A falo na samu duka mutanen gidan tsaye carko-carko har Abbas yau yana gida. Ga kayana a barbaje an musu filla-filla. “Yauwa ga ɓarau-ɓarau ɗin nan ta dawo”. Furucin Bibaa ya dawo da hankalina kansu. Kafin nai wata magana kawai naji saukar mari. Duk da azabarsa ta matuƙar ratsani banyi ko gezau ba. Sai wanda ya marenin na zubama ido kawai, ba kuma kowa bane face Abbas. Nunani yay da ɗan yatsa tamkar zai tsokale min ido ya ce, “K dan uwarki kawo sarƙar Mom da kika sata, shegiya ɓarauniya mai kama da aljanun daren salla”.
Cikin dakiya irin tawa na ce, “Karka sake zagar min uwa. Sata kuma kanku ya kamata ku bincika, tunda kune ke shiga ɗakin Mom ɗin ai. Ni ba ɓarauniya bace, kuma in sha ALLAHU babu wani tsananin rayuwa da zaisa na aikata ta”.
Daga haka na duƙa domin tattare kayana. Amma sai ji nai an shaƙoni ta baya. Har hijjab ɗina na matsemin maƙoshi. Da sauri nasa hannu naja hijjab ɗin sama. Sannan na miƙe. Baby ce mai riƙon nawa yanzu, itama hannu ta ɗaga zata maran, sai dai kafin ta sauke min ni na sauke mata nawa yatsun biyar akan farar fuskarta. Saurin janye nata hannun tai tare da sakina ta haɗa duka hannuwanta biyu ta riƙe kuncinta. “Karki soma fara wannan wasar dani a gidan nan, shima daya maran ɗin ba ƙyalesa nai ba balle ke shashasha”.
“Toni bari na marekin sai ki haɗa ki rama” Mom ta faɗa tana wani zaburowa kaina. Banyi ko motsi ba harta ƙaraso ta maran ɗin a haggu da dama. Sannan ta shaƙoni. Kakari na fara, amma ko gezau bata da alamar sakina. Sai ma faɗi take, “Dan ubanki ina sarƙata? Ina kikaje kika saida ta? Dan nasan fitar da kukai ke da annamimin mai saki yin komai a gidan nan abinda kuka je saidawa kenan. Kuma wlhy bazan yarda ba, sarƙata ko kuɗinta”.
Zuwa yanzu kwata-kwata bana iya numfashi da ƙyau, hakan yasa Abba da tun ɗazun baice komai ba ya ƙaraso da sassarfa yana ƙoƙarin cire hannun Mom ɗin daga wuyana. “Kinga Jalilah saketa Please. Sakarta ta faɗa inda take kada ki kasheta mana”. Sam bata da alamar sakin nawa kuwa. Dan haka ya tureta da ƙarfinsa har sai da tai taga-taga zata faɗi, ni ma dai zubewa nai a wajen ina sauke wahalallen numfashi a gwagwgwame. Ga tari dake neman sarƙeni. Da sauri auta yazo gabana ya duƙa yana miƙamin ruwa. Banyi musu ba na amsa, dan ina buƙatarsa. Sauri-sauri na fara sha, sai ji nai an kaɓe ruwan ya zube jikina gaba ɗaya. Yayinda Auta ya fasa wani kukan azaba. Da sauri na tashi zaune, dan bata ruwan da aka zubarmin nake ba ta shi nake. Yaron na sona sosai a gidan, kawai dai dan baida yawan magana ne sai idan shi yaso, dan miskili ne na bugawa a jarida. Ba komai akai masa ba, Baby ce data figesa daga kusa dani kawai yake ma ihun kuka, Bibaa kuma na huci alamar itace ta kaɓar da ruwan da ya bani......
✨(☯෴☯)(☯☯)(☯෴☯)✨
Badan Maash yaso ba dole ya shirya suka fita da Baba prof.. zuwa Company, daga can suka tsaya sukaci abinci a wani haɗaɗɗen restaurant. Daga haka suka wuce airport domin masa rakkiya, dan ya rasa jirgin sha biyu sai ya sake bucking na yamma. A hanyarsu ta zuwa airport ɗin ne Baba prof.. ke tsegunta masa yama yarinyar da tai hira da shi ɗazun ƙyauta amma ta dawo masa da shi. Dan haka mamakin yarinyar ya kasa barinsa har yanzun.
Shiru Maash dake saurarensa yay tamkar bai ji ba. Sai dai a ransa faɗin yake (Ai bazata amsa ba. Ita dake harin miliyan ɗari biyar). “Wai baka jini bane?” Baba prof.. ya katse masa tunani. Cikin basarwar tasa da magana ciki-ciki ya ce, “Ban san mi zance bane Grandpa”.
“A komai ai dama kai baka da abin cewa. Ko akan hirar ya kamata ma ka tambayi dalilina nayin hakan, amma ka share abinka. Awwab wai yaushe ne zaka canja? Anya matar da zaka aura zata iya ɗaukar wannan baƙin halin naka kuwa?”.
“Ni nace zanyi aure ne?”.
Ya faɗa a wani yanayi mai kama da jin zafi. Murmushi kawai Baba prof.. yay yana girgiza kansa. Sai kuma ya ce, “Oh haka zakaita zama kenan?”.
Bai tanka masa ba sai ma ɗauke kansa da yay. Shima Baba prof.. ɗin sai bai sake magana ba har suka iso. Sama-sama sukai sallama, batare da yaga tafiyarsu ba ma yace Tijjani ya juya da shi gida.
Abinka da lafiyayyar mota, cikin ƙanƙanin lokaci suka iso gidan. Security ya buɗe musu gate cike da girmamawa. Tun kafin motar ta tsaya idanunsa suka sauka akan matashin saurayi da ke zaune a ɗan tudun da akai wajen flowers, Hayatu na daga gefensa zaune a kujerar roba dan bada shi suka fita ba. Sai dai tunda motar ta shigo ya miƙe tsaye. Suna gama dai-daita parking kuma ya iso da sauri kafin ma Guards dake tare da su ko Tijjanin ya fito ya buɗe masa shi ya buɗe masa.
“Sannunku da dawowa Sir”.
Hayatu ya faɗa yana rissinar da kai. Shima kan kawai ya jinjina masa yana kamo gefe da gefen jacket ɗinsa ya saka maɓallinta guda ɗaya jal dake a tsakkiya. Batare da ya sake kallon inda saurayin nan da yay galala yana kallonsa ba ya wuce hanyar falonsa cikin takun dake tabbatar da shi a sadaukinsa, kai daka gansa kaga tsayayyen namiji da iskar lokaci ke kaɗa masa. Wayoyinsa biyu da ya fita da su Hayatu ya kwaso a motar, sai wata ƴar ƙaramar bag mai ƙyau da Baba prof.. ya bashi, ba komai bane a ciki kuma sai turare mai azabar tsadar tsiya da ƙamshi. Saurayin nan ya kalla ya ce, “Ka jirani anan Sani ina zuwa”.
Cikin girmamawa saurayin ya amsa masa da “To Yaya a fito lafiya”. Zaune ya samesa bayansa jingine da kujera ya lumshe idanu alamar gajiya. A hankali ya ajiye masa wayoyin gefensa, bag ɗin kuma a saman Centre table. Sai kuma ya nufi freight ya ɗakko ruwa da glass cup. A gabansa ya zo ya ajiye, tare da tsiyayawa ya miƙa masa cike da girmamawa. “Sir ga ruwa”. Shiru kamar bazai motsa ba, sai kuma ya miƙa hannu ya amsa batare da ya ɗago ko ya buɗe idanu ba. Ɗan jimm Hayatu yayi, sai kuma ya sake daurewa ya ce, “Sir dama yaron da zai yi aikin nan ne yazo gashi can a compound, a shigo da shi ne ka gansa?”.
Nan ma yaja wasu sakanni kafin yace, “Shigo da shi”. Da ga haka ya ɗan ɗago ya kurɓi ruwan, sai kuma ya sake maida hannunsa a goshinsa yana ɗan murzawa........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
......A tare Hayatu da saurayin sukai sallama. A saman lips ya amsa musu. Suna ƙarasowa saurayin ya zube a ƙasan lallausan carpet ɗin tsakkiyar kujerun, sai faman kalle-kalle yake kamar wanda ya buɗe ido da ga makanta. Sai da Hayatu ya ɗan zunguresa da ƙafa sannan ya dawo hayyacinsa ya ɗan nutsu. Ganin idon Maash a kansa ya sake nutsuwa tare da faɗin, “Ranka ya daɗe ina wuni”.
A hankali Maash ya ce, “Lafiya, miye sunan ka?”.
“Sani”. Ya bada amsa da sauri.
“Kayi karatu?”.
“Eh ranka ya daɗe, har matakin N.C.E na kai. Sannan na sauke Alkur'ani tare da littatafan addini masu yawa”.
Kai kawai Maash ya jinjina masa, dan shi hausan ma ba wai duka yake ganewa ba. Sai dai yaji dukkan bayanin saurayin. Hayatu ya kalla, dan haka yay saurin gyara tsaiwarsa da ɗan matsowa kusa da shi. Dan shi koda ido Maash ya kallesa yasan mi hakan ke nufi. Kai tsaye ya ce, “Na sanshi sosai Sir farin sani, dan ɗan uwana ne, da mahaifiyarsa da mahaifina uwarsu ɗaya ubansu ɗaya. Sai dai su anan Kano suke. Yasan ciki dabai na garin Kano, sannan ita kanta yarinyar ma ya santa a dalilin shirin da take gabatarwa na matasa, har hira ta taɓa yi dasu wata biyu da suka shige lokacin bai kammala makarantarsa ba”.
Nanma shirun yay ƙafarsa ɗaya akan ɗaya yana kallon saurayin kawai, sai da ya mula dan kansa sannan ya furta, “Ka tabbatar zai iya?”.
“In sha ALLAHU zai iya Sir. Kuma zai riƙe sirrin dan in ma ya tona kamar kansa ya tonama asiri ne. Mu bamu sanshi ba bamu da alaƙa da shi idan aka samu kuskure”.
“Fine.”
Ya faɗa a taƙaice yana miƙewa abinsa. Ƙofar bedroom ɗinsa ya nufa, sai da yana gab da shiga corridor ɗin ya ce, “Ka bashi key ɗin mota da 500k na mai. Sallamarsa sai ya gama aiki”. Daga haka yay shigewarsa. Waro idanu sosai Sani yayi, jikinsa na rawa ya ce, “Yaya dubu ɗari biyar fa. For mai ɗin mota kawai? Na shiga uku ni Sani ɗan inna”.
Dariya abin ya bama Hayatu, sai dai baiyi ba yay murmushi kawai da faɗin, “Kaga tashi muje waje sai kai murnar. Ka jirani bara na kai masa wannan”.
Ai kafin ma Hayatu ya rufe baki Sani ya kai ƙofa da sassarfa...
_😂Sani a taimakan dana data mana🤣😝._
💢💦💢💦💢💦💢
A rikice Yaya Musaddiq ya iso gida sakamakon kiran da nai masa ina kuka. Sai dai kafin ma nakai ƙarshen abinda zan gaya masa Baby ta kaɗar da wayar tawa gefe ta daki tayis. A take tai ƙarar fashewa. Koda na ɗagota screen ɗin yay rugu-rugu ta koma fari gaba ɗaya alamar ta samu matsala. To anan ne fa na kasa haƙuri, bamma san sanda nai kukan kura a kanta ba sai ganina sukai na haye ruwan cikinta ina jibga tamkar ALLAH ya aiko ni. Aiko Bibaa da Abbas suka shigar mata suma suka hau dukana. Auta kuwa ya hau ihu da kururuwar kuka. Abba zai rabamu Mom ta riƙesa da makircinta. Sarkin yawa yafi sarƙin ƙarfi, duk da nima na more akan Baby suma sun dakeni sosai harda jimin ciwo. Wannan faɗa bai rabu ba sai da Yaya Musaddiq ya shigo. A haukace ya faɗo falon batare da neman izini ba ya hankaɗe Abbas gefe tare da Bibaa. Sannan nima ya ɗagani akan Baby. Sake yo kaina Abbas yay Yaya ya shiga tsakkiyar mu yana daka masa tsawa. “Abbas!! Kai miyasa baka da wayo ne? Maimakon ka rabasu matsayinka na babba amma rashin hankali da kai ma akeyi?”.
Maimakon Abbas ya bada amsa sai Mom ce ta taso a fusace taba Yaya Musaddiq ɗin amsar. Daga ni har shi take haɗawa tana zagewa da kirani ɓarauniya, kai har iyayenmu ma haɗowa take. Yayinda ƴaƴanta ke faman huci kamar zasu daki Yayan shima. Duk da abinda ake Abba na falon ya gagara sake cewa komai.
Karon farko dana ga ɓacin ran Yaya a fili game da abinda ake mana a gidan. Dan muryarsa har zuga take wajen faɗin, “Mom ki daina danganta Samraah da sata dan bata taɓa yima wani aka gani ba. Fitarta ta yau kuwa kowa yasan inda taje tunda abune a bayyane. Ya kamata dai ki binciki sarƙarki a tsakanin ku da kuke gidan zaune.” daga haka yaja hannuna dan mu fice. Amma sai Mom ɗin da Abbas suka sha gabanmu. Abbas ne ke faɗin, “Kai har ka isa ka fiddata anan bata ajiye sarƙa ko kuɗin sarƙa ba. An kuma kirata ɓarauniyar ko akwai abinda zakayi ne?”.
Wani daƙilallen murmushi yaya Musaddiq ɗin ya saki a karo na farko. Sai dai baice komai ba ya sake jan hannuna zamu raɓasu mu wuce.
“Mussadiq!”.
Abba ya ambata a karo na farko. Cak ya dakata, sai dai bai juyoba bai kuma yi magana ba har sai da Abban ya sake magana. Still dai hannun nawa na riƙe a nashi muka dawo gaban Abban. Da hannu yay masa nuni daya zauna. Nan ɗin ma kamar bazai zaunaba ɗin sai kuma dai ya zauna. Hakan yasa nima na zauna a kusa da shi. Mom ya kalla ita da su Abbas suma yace suzo su zauna...
Kusan mintina uku falon yay tsit sai ƙwafa da Mom keyi a jajjere tana harararmu ni da Yaya Musaddiq. Sai da Abba ya tabbatar kowa zuciyarsa ta nutsu kafin ya fara magana. “Bana jin daɗin wannan rayuwar da akeyi a gidan nan sam. Mu ace kullum sai maƙwafta sun jiyomu muna ihu da hayaniya kamar wasu marasa abinyi ko wanda basu je ajin makaranta ba. Bakwa ganin hakan zubarma da kammu mutunci ne?....”
“Abban Abbas kaje ga maganarka kai tsaye nifa bana son wani kwana-kwana. Batun sarƙata ake anan ba wani mutunci ko yanda maƙwafta ke kallonmu ba. Su ya dama, sun kuma ga zasu iya ne. Dan haka ka musu magana su futomin da sarƙata in har ana son zaman lafiya a gidan nan. Inba haka ba wlhy police station zan kai su. Ai acan dole su fito da ita ya arziƙi ko tsiya.”
Daga haka ta miƙe fuuu tabar falon. Shima Abbas miƙewarsa yay ya fice. Baby ta taɓe baki itama ta miƙe ta fita. Bibaa dai bata tashi ba, amma itama sai harare-harare take. Gaba ɗaya yanayin Abba ya sake sauyawa, sai dai mun san babu abinda zai iya. Ilai kuwa hankalinsa ya maido kammu. Babu kunya babu tsoron ALLAH ya shiga faɗin, “Ke Samraah ki fito musu da sarƙarsu ko ki faɗi ina kika saida aje a amso kinji, wlhy wannan fitinar ta isheni. Ku barni da abinda ya daman mana”.
Kai Yaya Musaddiq ya girgiza kawai, yayinda ni kuma nakema Abban wani kallon takaici da baƙin ciki. Zanyi magana Yaya Musaddiq ya dakatar dani da faɗin, “Amma Abba bai kamata dan an nema wani abu an rasa ace Samraah ce ta ɗauka ba tunda ba ita kaɗai bace a gidan. Sannan ba kuma taɓa kamata akai da halin ba balle a kafa hujja da ita ɗin ce ba. Idan Samraah ta ɗauka sarƙa mizatai da shi. Karfa a manta tana aikinta, sannan ma kowa shaidane Mom bata taɓa barin tsakanin ni ko Samraah da Hafizzullah mu shigar mata ɗaki tun muna ƙanana. Amma tunda har kaima ka yarda da ita ɗince ta ɗauka ita Mom ɗin ta faɗin kuɗin sarƙar tata in sha ALLAHU za'a biyata. Amma kuma da ga yau zamu cigaba da gayama ALLAH kuma zamusa a tayamu kafin wani a cikinmu yabar duniya ALLAH ya tona asirin wanda ya ɗauki sarƙar”.
“Amin ya rabbi, ba addu'a a Nigeria ba ku tafi gaban ka'aba kuyi mara mutunci. Ai dama na daɗe da sanin kaima ƙwallen shege ne nata ne kawai ya fita ita fitsararriyar. Sarƙata kuma naira dubu ɗari huɗu na sayeta sai a biyan kuma bana son ya wuce yau ɗin nan. In ba hakaba wlhy kaiwa police station babu fashi”.
Murmushi kawai Yaya yayi, batare da yace komai ba ya miƙe. Kallona yay ya ce, “Tashi ki tattara kayanki ki maida ɗaki zanje na dawo”. Daga haka ya fice ni kuma na miƙe na shiga tattara kayan. Baka jin komai a gidan sai banbami da masifar Mom da zagin da take loda mana. Amma Abba kamar an ajiye gunki domin ado ko uhum bai sake cewa ba. Ni dai na tattare komai na nufi ɗaki, dan tuni na daina hawaye sai zuciyata dake wani irin suya da ƙuna tare da sake jin tsanar gidan da kowama na cikinsa. Yanda zuciyata ke mun zafi da raɗaɗi ji nake kamar nai kiran Mansoor nace masa gobe iyayensa suzo a tsaida bikinmu sati ɗaya kawai. Ni ko babu wani biki a ɗaura auren kawai na tare. Amma dai na dake dan bazan iya hakan ba, hasalima ni ban taɓa nunama Mansoor munada wata matsala a gidanmu ba, saboda hakan sirrinane bakuma zan iya tona sirrin cikina ga saurayi ba watarana yay min gori da hakan ko ya dinga kallon ƴan uwana a wulaƙance koda munyi aure. Koma dai mi suke mana su ɗin jininmu ne dai bamu da wanda ya fisu. Shiko wataran zai iya canjawa koma ya ɓata ɓat a rayuwata duk da bana fatan hakan kodan tsananin ƙauna da soyayyarsa da nake ji a cikin zuciya da ruhi na.........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒇𝒐𝒖𝒓_
......Sallamar Yaya Musaddiq da naji a falo bayan sallar isha'i ta sani miƙewa daga kwancen da nake zazzaɓi ya rufe ni. Nasan kuma ba komai ya jamin hakan ba sai caskalen da mukayi dan da gaske naci duka a wajensu. Daga inda nake na zubama Yaya Musaddiq daya dire baƙar leda a gaban Abba idanu na dake cika da ƙwalla. Yayinda kunnena ke sauraren abinda yake faɗa.
“Abba ga kuɗin sarƙar nan a bata. Naira dubu ɗari huɗu ne kamar yanda ta faɗa”. Daga haka ya miƙe ya nufi hanyar fita. Cikin sauri na take masa baya batare da nabi takan shewar da Mom keyi ba kuɗin daya ajiye ɗin a hannunta dan bata bar Abba ko taɓaw
0 comments:
Post a Comment