“Oh Amarsu irin wannan zurfin tunani haka?”.
Aunty Zakiyyar Gwaggo da bamma san lokacin data shigo ba ta faɗa cikin katseni ta hanyar taɓani na kawo nannauyan numfashi. “Har kin fara tunanin rabuwa da gidan ne raguwa? Sai bakin tsiya kuma”. Ta sake faɗa cike da tsokana. Murmushi na sakar mata ina duƙar da kaina. Na ce, “Kai aunty yaushe kika shigo bamma sani ba”.
“A taya zaki sani kin lula duniyar tunani. Yaya jikin naki dai to?”.
“Alhamdullah Aunty, dama babu inda ke min ciwo, allurar da suka min ce kawai ta sakani wannan dogon barcin”.
“ALLAH sarki to Alhamdullah ai haka akeso. ALLAH kuma ya kiyaye gaba. Ya tona asirin duk wanda keda hannu a kan hakan. Damma dai Alhamdullah addu'a tayi tasiri ƙwarai da gaske. Kuma da alama duk ma wanda suka kamakin ba mugaye bane. Dan masu amsar kuɗin nan sunfi haɗari. Amma waɗan nan da alama suna da tasu manufar ne a kanki gaskiya. Na kuma fi ƙyautata zaton akan auren nan ne kamar yanda kowa ke zargi, musamman akan wannan maman taku da Baby. Kowa yafi dangantasu da al'amarin nan wlhy, dan zuciyarsu babu ƙyau komai zasu iya aikatawa tunda sun gagara ɓoye hassadarsu”.
“In sha ALLAHU Aunty bazasu ci nasara ba kuma. Tunda gashi ma ALLAH ya kuɓutar dani cikin sauƙi, dan tabbas addu'ar ce tai tasiri a kansu suka sakeni batare da sun shirya ba, amma kuma ni bana danganta al'amarin da su Mum da dalalin auren nan kamar yanda kowa ke kallo, dan in dan auren ne ai kinga babu yanda za'ai su sakeni haka da sauƙi da sai lokacin bikin ya wuce ko”.
“Tabbas hakanne kam Samraah kema kinzo da batun dubawa. Amma dai ai zaki iya ganesu? Dan naga angon nan naki da gaske ya shirya ɗaukar mataki, a yanzu haka suna ƙofar gida da ƴan sanda da Musaddiq da Yaya Imam.”
Idanu na zuba mata kawai, sai kuma na nisa a hankali na ce, “Aunty bazan iya gane su ba. Saboda abinci kawai suke kawo min sau uku a rana. Kuma komai nasu a rufe hatta da hannayensu ma. Kuma basa mun magana sai dai su ajiye kawai su juya su fita. Ko'a ranar dana samu damar kiran Yaya Musaddiq ma kwato nayi, sai kuma suka kamani bayan sun amshe wayar suka shaƙamin abu suka ɗaukeni da ga gidan sai farkawa nai na ganni a wani sabon waje. Hakama yanzu sai da suka min allura sannan suka kawo ni ƙofar gidan nan.”
Aunty Zakiyya na shirin yin magana dai-dai nan Yaya Musaddiq yay sallama. A tare muka amsa masa. Batare da ya shigo ba yace nazo. Miƙewa nai na ɗauki hujjab ɗina na saka sannan na fita. A falon baƙi na samesu shi da d.c.o da Mansoor sai Gwaggo Gudidi da Abba. Daga can gefe Baby ce ta masifar zubama Mansoor ido kamar zata cinyesa. Shiko sai wani cin magani yake tamkar an aiko masa saƙon mutuwa. Sai da muka haɗa ido ya ɗan sauke numfashi tare da sakar min murmushi. Murtani na mayar masa nima ina duƙar da kaina ƙasa. Gaisar da d.c.o nayi cikin girmamawa, shima ya amsa min da kulawa tare da tambayata ya jikina. Kaina a ƙasan na ce, “Alhamdullah bana jin ciwon komai Sir”.
“Masha ALLAH, Alhamdullah haka muke son ji ai dama. Samraah wannan zuwan naki ne. Muna fatan zamu samu haɗin kai domin son sanin komai daya faru dake tun daga fitarki a gida a waccan ranar har zuwa yau da ALLAH ya maido mana ke bisa ƙarfin ikonsa”.
Babu musu na jinjina masa kaina tare da faɗin, “In sha ALLAHU ranka ya daɗe zan faɗi abinda na sani”.
Zamansa ya gayara sosai yana fuskantata. Kafin ya furta, “Yauwa Ina jinki”. Bayani na fara masa tiryan-tiryan tun daga shirin fitata. Kiran dana samu daga MD har zuwa fita cikin layi da tare napep. Jefamin handkerchief da wanda na samu a napep ɗin yayi bayan ya kira sunana tabbacin ya sanni ko yana son tabbatar da ni ɗin ce, har zuwa buɗe ido na ganni a wani waje daban. Yanda na rayu a gidan farko har zuwa kiran wayar Yaya Musaddiq da nayi da wayar ɗaya daga cikin mutanen da kuma canja min gida da sukayi. Sai dai na samu kaina da kasa faɗar wanda ya saka akai kidnapping ɗin nawa kamar yanda ya nuna min kansa da buƙatar na bashi abinda ke a hannuna da yayi, hakama dalilin ɗaukar tawa duk ban faɗa ba. Maidoni gida da sukayi da kuma kiran da yayma Nurse a asibiti ta bani. Kawai dai na sanar musu kamar yanda na sanarma Aunty Zakiyya ne. Sosai falon yay tsitt suna saurarena. Yayinda d.c.o ya kafeni da idanu ko ƙyaftawa bayayi. Jinai duk na tsargu, amma na dake abina kun dai san mutuniyar taku ai. Dan kansa ya gaji ya janye idanunsa a kaina. Cikin sauke numfashi ya furta, “Kin tabbata iya abinda ta faru kenan Samraah? Dan bana son ki ɓoye mana komai, kar kiji tsoron barazana ma idan sun miki babu abinda zai faru”.
“Iyakarsa kenan yallaɓai. In har na ba mance wani abu to bashi da muhimmanci ne”.
Kansa ya jinjina cikin nuna gamsuwa, kafin ya kalla yaronsa dake rubuta duk abinda nake faɗa, sai kuma ya maida idonsa kansu Yaya Musaddiq. “Inaga fa dole ne mu sake gayyatar MD ɗin nan nasu, dan komai idan aka tattara ya ta'allaka ne akansa. Amma bawai ina tabbatar da shi ɗin ne ba. Dan ita shiri'a saɓanin hankali. Kuma tunda har ta dawo gida cikin ƙoshin lafiya Alhmdllh, koma minene zai zo mana da sauƙi. Yanzu dai inaga sai a kiyaye gaskiya. Fita anyhow dole ta jingine ta. Mukuma duk inda ta saka ƙafa idan ma har ta fitan zata kasance a ƙarƙashin kulawarmu ne.”
“In sha ALLAHU babu damuwa ranka ya daɗe. Dan ko batun zuwa aiki ma dama zata ɗan dakata, in ma zata cigaban ne sai bayan bikinta idan mijinta ya amince sai taje ɗin”.
“Wannan ma dabara ce kam mai ƙyau sosai. Amma taron bikin nan fa dole ayisa da kulawa. Koda yake zamu haɗata da jami'ar mu mace domin ta kasance da ita ama duk inda take like handbag ɗinsu na mata. Hakan zai sauƙaƙa mana aikin mu insha ALLAHU.”
Kowa a falon yaji daɗin zancen nasa kuwa. Dan har fuskokinsu sun gagara ɓoyewa. Ni dai kaina a ƙasa kawai abubuwa da yawa nata min kai kawo a zuciya. D.c.o ya ɗan ƙara tattaunawa da su Yaya Musaddiq kafin suyi mana sallama su wuce. Tare da jaddada min duk sanda suka buƙaci gani na zan iya ganinsu a gidan, ko kuma su aiko a ɗaukan zuwa office ɗinsu. Da to kawai na amsa musu ni dai. Gwaggo Gudidi sai jera musu godiya take. Mansoor da Yaya Musaddiq kuma suka tafi musu rakkiya waje. Muma miƙewa mukai muka koma cikin gidan. Dan Aunty Zakiyya ta tabbatar min da yau babu fashi zata fara min gyaran jiki. Ban musa ba, dan nima ina son zuwa fadar masoyina fes tamkar wata ɗan daren sha biyar.........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_
........Tun daga shigowar ƴan sanda har fitarsu a gidan Mum ta sani, amma batako leƙo ba. Sun tafi ma babu jimawa sai ga Mamanta da ƙanwarta dake aure a Bauchi. Acewarta tazo ne bikin Samraah domin yima Mom Kara. Bata bari sun zauna a falo ba ta shige dasu bedroom ɗinta. Da kanta kuma ta fito ta haɗa musu abinci takai musu. Ko kunya babu yanda ƙanwarta ta cire mayafi ta fara lodar abinci haka itama Maman tayi. Kai bakace a gidan suruki take ba. Bayani ta sake ma ƙanwar tata akan duk yanda aka samo Samraah, dan ita Mamansu tasan komai. Ƴar uwar tata kai ta jinjina. Sai kuma tai ɗan jimm alamar tunani, kafin ta sake ɗagowa tana kallonsu bayan ta gama ƙulla abinda take ganin zai fanshi yarinyar nan tsakaninta da ALLAH. Dan magana ta gaskiya ita su Samraah sun jima suna bata tausayi, sai dai bazata iya fitowa ta faɗa ba dan tana shakkar Yayar tata da Mamansu saboda masifaffu ne na bugawa a jarida. Amma tana ji a ranta a wannan gaɓar bazata bari a cutama marainiyar ALLAH ba. Sai dai dole tai komai cikin siyasa. “Niko inada shawara”. Ta faɗa kanta tsaye.duk sake maida hankali sukai a kanta. Cike da zumuɗi Mum tace, “Miye shawarar Ikili, dan ALLAH faɗi muji”.
Numfashi Ikilima ta sauke tare da ajiye cokalin hannunta ta sake fuskantarsu. “Ban sani ba shawarar ko zata gamsar daku, amma dai a yanayin da nake gani kamar guri ya ƙure mana a yanzu zata iya zama mafita. Mizai hana mubar yarinyar nan tai aurenta kawai. Bayan bikin mu duƙufa samowa Baby mijin aure na garari da yafi shi wannan yaron. Bayan itama ansha nata bikin mun nunama musu koda goma ta lalace tafi biyar albarka, sannan mu fara shiri akan komai ma da muke ganin ya dace akan auren nata. Dalilina na kawo wannan shawarar shine idan fa muka hana auren nan kamar mun gogama gidan nan wani baƙin fenti ne. Kun san dai halin mutane ai, hakan kuma na nufin kammu muka cutar tunda namu yaran ne dai basuyi aure ba a bayanta, dan ita wani zai iya jin tausayinta yazo ya aureta, sannan mu za'aita zagi da zargin mun hana ko muna mata baƙin ciki. Amma idan muka bari akayi hankali kwance babu mai aibanta mu balle idan mutanen kirki sun zo neman auren su Bibaa wani shege ya sokemu. Kunga mun samu nasara biyu kenan, mun kuɓutar da yaranmu, sannan mun sama musu abinda muke fata. Yo har miye wani Mansoor yake ma komi ALLAH na tuba. Shi da dukiyar ba tasa bace ta babansa ce. Mu ɗan gaske zamu samo mai dukiyar kansa da kansa. Dama ba akwai mutumin nan daya haukace akan baby na anguwarmu ba amma tanata masa wulaƙanci ita bazata zauna da kishiya ba. To wlhy yanzu yazo nan Kano yayi wani mahaukacin gida a hotoro g.r.a ina gaya muku kuma aure yake son yi ruwa a jallo ya saka matar anan, su kuma waɗan can zasu cigaba da zamansu can Bauchin saboda ya musu tayi sunce su bazasu iya barin mahaifarsu da ƴan uwansu ba. Amma yaya kuka gani?”.
Cike da zumuɗi Maman ta ce, “Ni dai wannan shawara tamun wlhy Ikilima, amma ke Jalilah yaya kika gani?”.
Shiru Mun tai kamar bazatace komai ba, sai kuma ta sauke numfashi mai nauyi da faɗin, “Nima shawarar ta ɗan mun, sai dai ina tsoron tsutsun Baby wlhy, Dan nasan yanda ta tsani kishiya...”
“Yo biye mata zamuyi, tuni zamu shiga mu fita a dasa mata sonshi a zuciya sanda ma zata soshin fawa tai shawara. Mufa muka haifeta ba itace ta haifemu ba. Kishiyoyi kuwa ai dasu da babu duk ɗaya ne tunda ba'a waje guda zasu zauna ba”.
“Yo Mama ko waje guna ne Baby bata da matsala. Dan matansa wlhy a hakan ma kowa rayuwarsa yake babu wadda ta damu da wata tunda kowa da gidanta kuma kowacce kuɗi take juyawa na hauka. Yi kishin ma fa dama matan malam shehune sukafi zaman yin na haukannan aita damben tsiya da hayaniya. Amma mata masu aji da kuɗin nan zakiga kishin ma na ƴan boko akeyi, itama kuma dai tanada iliminta babu abinda za'a nuna mata. Kuma tana shiga zai bata maƙudan kuɗi ta fara kasuwanci kamar sauran dan haka yake yi”
“Hakane wlhy Ikilima. Ni kubar komai a hannuna kawai zanyi maganinta, yanzun kam hidimar biki duk mu ware aitayinta damu. Ai kwantan mage zamu musu a yayin kama ɓera, tuni sai suzo hannunmu batare da sun farga ba”....
(😂ALLAH ya rabamu da son zuciya to).
💦🌟💦🌟💦🌟💦
Zaune yake a office yana ƴan ayyukansa sakatariyarsa ta shigo ta sanar masa d.c.o yazo yana son ganinsa. Karo na farko da MD yaji ransa ya fara ɓaci da bibbinin da d.c.o ɗin ke masa. Idan yace da yana da dalili yanzu kam shi baiga dalilin ba. Samraah dai ce ta kuma dawo sai me kuma, shi ma yaje dubata tare da staffs nasu har asibiti. To minene kuma na zuwa masa office yau. Rashin amsa ya sashi jan sirrin tsaki, tare da bama sakatariya umarnin ta barsa ya shigo.
Fitarta bai fi da mintuna uku ba ko sai ga d.c.o ɗin ya shigo, sun gaisa cike da girmama juna. Kafin MD ya ce, “Yallaɓai akwai wata matsala ne?”.
“No babu matsalar komai MD. Waccan dai matsalar ce akan staff ɗinku Samraah Abdul-wahab Gwarzo. Dan kasan koda ta bayyana ya kamata mu cigaba da bibiyar case ɗin domin gano da kama wanda sukai kidnapping ɗinta kodan musan dalilinsu”.
“Hakan nada ƙyau yallaɓai. Domin muma zamu so ace an kama sun. Sai dai muna ƙarama ALLAH godiya da kuɓutar tata cikin ƙoshin lafiya. Yanzu mike tafe da kai?”.
“Uhm kamar dai yanda aka saba zamu sake gayyatarka office ɗin mu idan babu damuwa. Kana kuma da damar muje ka samemu a can, ko mu tafi tare”.
Murmushi MD yayi mai ƙayatarwa. Sai kuma cikin rashin damuwa ya ce, “Babu matsala muje ɗin kawai, dan bawani aiki nake da shi ba sosai yanzun. Zuwa anjima kuma aikin zai iya shamin kai, kaga kuma bai ƙyautu ace ban amsa gayyatar ba”
“To Masha ALLAH, hakane kam mun gode sosai”.
Murmushi kawai MD ya sake masa yana miƙewa. A jere suka fice suna ƴar hirarsu tamkar wasu abokai. Dan haka sauran staffs basu fahimci komai ba face tunanin akan dai case ɗin Samraah ɗin ne. Kuma babu wani damuwa a cikin ganin MD da ƴan sandan dake bincike akan case ɗin tunda ba yau ne mafari ba. Suma kansu dai duk sai da suka sha tambayoyi a kwanakin baya....
💢🌟💢🌟💢🌟💢
Kwanaki na biyu kenan da dawowa gida. Kwanaki biyu kuma kacal ya rage ɗaurin aurena. Dan zuwa yau har baƙin kusa sun fara isowa musamman dangi na jiki sosai. Ga Aunty Zakiyya ta duƙufa min gyaran jiki da ɗuramin abubuwa. Niko dana faki idonta sai na zubar dan bana sha sosai. Abinda zai baku mamaki duk da haramin biki da gida ya fara ɗauka ga masu gidan babu wani alamar motsi irin na biki a tattare da su. Dan hatta da abinci da aka girkama baƙin dake a gidan yau Yaya Musaddiq ne ya kawosa. Suko su Gwaggo suka girka batare da sun bi takan Mum daketa faman ɗacin rai ba. Shi dai Abba saboda su Gwaggo Gudidi yana ɗan nuna alamar damuwa da shirye-shirye. Sai dai fa bana aljihu ba na gayyatar mutanensa kawai, sai kuma takurama Yaya Musaddiq da yake ta bayan fage akan kuɗin kayan ɗakina da wanda za'ai hidimar abincin biki. Shiko Yaya Musaddiq nata masa zame-zame. Sai a yau ya fito fili ya shaida masa karya damu shi ya riga da ya kammala komai. Dan hatta da kayan kitchen ɗina ma a tanade suke tuni. Hakama kayan gado kafintan ya jima da kammalasu duk da Mansoor yace kar ayi shi baibi ta nasa ba. Wannan zance ya ƙona zuciyar Abba matuƙa. Amma ya gagara magana kodan mutane dake cike a gidan, yasan fitowar zancen babban abin kunya ne a garesa musamman a wajen danginsu dana ɓangaren mahaifinmu.
Ban gayyaci wasu ƙawaye ba dan banda su, amma a ranar da yamma sai ga su Ruƙayya ƴan Office dinmu da gayyar ƴan ajinmu na islamiyya. Naji daɗin ganinsu sosai, dan ko kusa banyi zato ba. A bakinsu na fara jin ƙananun maganganu akan rashin kawo kayan da zanyi amfani dasu na biki da Mansoor ya ce sai daga baya dan ba'a saka ɗinkakken kaya ko ɗaya a lefen ba, kuma kowa na saka ran yau ne za'a kawo ɗin saboda kamu da ake shirin yi gashi babu kayan dazan saka. Amma har yamma shiru kake ji. Gashi yanzu banda waya a hannuna ko ɗaya. Rabona da Mansoor kuma tun jiya da dare. Koda yake nice nace yau kar yazo, kai daga jiya ma bazan sake yarda mu haɗu ba sai a gidansa. Shiko ya yarda da hakan acewarsa zai gwada yaga ko zai iya. Nayi tunanin kiranshi amma zuciyata ya ƙwaɓeni game da hakan, dan haka bance da su komai ba na haɗiye zancen a raina har sai bayan sallar isha'i da nasan Yaya Musaddiq ya dawo gida sannan na lallaɓa ɗakinsa na samesa, a wajen kamu kuwa Aunty Zakiyya ta samo kayan dana saka kawai........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_
........Kai tsaye ɗakin Yaya Musaddiq na nufa. Bayan na gaishesa ya ɗan tsokaneni nai masa zancen da naji ana tsogumi ɗazun a kai. Murmushi yay min da faɗin, “Kandala ƙyale batun mutane da halinsu. Dan su basu iya komai ba daman sai gulma kawai. Yanzun nan babu jimawa muka rabu da Mansoor ɗin ma, dan munje can gidan nasa ne da kafintan da yay kayanki saboda zasu kaisu da sassafe gobe in sha ALLAHU. Ya kuma min batun kayan sai gobe in sha ALLAHU zasu kawo wata ƙanwar Mamynsu ce da zatazo da ga Dubai a yau da dare ake jira dan akwai wasu kaya a hannunta, amma shima yana cikin damuwar rashin kawo su shiyyasa ma ya kasa neman ko Hafizzullah a waya ya haɗaku dan kunyarki yake ji”.
Ajiyar zuciya na sauke a hankali. Dan nama san ƙanwar Mamyn tasu, yasha bani ita muyi waya. Murmushi yay min yana kai ma kaina rankwashi da faɗin, “Sam yanzu Kandala baki da kunya. Yanzu ni kike zuwa tambayar batun kayan aurenki ma”. Hannu na saka na rufe fuskata ina dariya. Shima dariyar yake yi. A dai-dai nan Hafizzullah ya shigo ɗakin da sallama. Dan tun washe garin da aka ganni yazo gida dama. Ledar hannunsa na warce ina faɗin, “Zaga gari mi kuma ka samo anan?”.
Ƙoƙarin warce ledar shima yake a hannuna yana hararata. Ban yarda masa ba har sai da na buɗe. Ganin awara yasa na taɓe baki ina miƙa masa. “Oh oh kwantar da hankalinka ashema naman talaka ce”.
“Oho dai, kema naga ci kike”.
“Ai ni in naci ba komai bane. Amma kamarka dai saurayi mai hurama ƴammata hanci abin kunya ne. ALLAH yau da ina da waya saina ɗauki hotonka nasa a status ƴan matanka sun gani”.
Dariya ya sanya da yimin gwalo, ya ce, “Ai sai ki samama kanki lafiya tunda baki da. Kuma sai na zuga Yaya Mansoor kar ya saya miki waya har sai kin shekara a gidansa”.
“ALLAH sarki jiki duk baƙin ciki su Hafizu. Aiko zakasha mamaki, kafin rana ita yau kasa a ranka na mallaki waya”. Na ƙare maganar ina kai masa
0 comments:
Post a Comment