*Alhamdulilah jiki yau sauqi nagode sosai da addu'oinku gami da fatan alkairi*
Kai tsaye gida akayi da gawar ba wanda bai share hawaye ba cikinsu musanman ma wadanda suka ga yaron ayau da jiya se abin yake ta dawo musu sabo.
Ba abinda mahfuz yake se sharar hawaye haushi da tsanar kansa duk sunbi sun masa yawa shi ne sana diyar zuwan yaron duniya yaso ace yaron ya girma ya masa gata sedai gashi yama tafi besan waye mahaifinsa ba, ya kuma share hawaye lokacin da ya tuna ganinsa da yaron na qarshe.
A wasa yake masa magana my boy yau agurina zaka kwana ko ya maqe qeya a'a ni yau gurin dady na zani to ai nine dady naka yasa dariya kai uncle dina ne dady na biyu dadyn aunty farida(Nasir) da dady me sunana, bemasan sun iso gidanba seda Abbakar ya ta6ashi yai saurin futowa daga motar.
Gawar ce riqe hannun Abbakar ji yake kamar yaron zai farka yasa masa kuka kamar ko yaushe yace se ya bashi alawa kwallah ta tawo masa wadda ya kasa tareta, mahfuz yai saurin Amsar gawar shi kuma ya goge hawayensa.
Nasir kam ya kasa komi qafafunsa ma gabaki daya sunyi sanyi inbanda soyayyar uwa daban take to da nace ba wanda yafi nasir san yaron koda yake ko ummun batakaishi shaquwa da Abbakar dinba, shi har yanzu baima yadda wai yaron ya mutu ba jira yake kawai yaji sunce masa ya farfado.
Se kace ba dazu da safe ne da yazo gidanba yaga yaron yanata wasansa har dazai tafi yake masa wasa dady yau zamu unguwa da baba yace zai sayon kayan dadi cikin tsamin murya ta yara yake magana wadda seka zauna dashi zaka fuskanceshi.
To nima aragen kayan dadi yai dan jim sedai inzaka siyon wasu se insamma ka yai dariya ya lakuce hancin yaron kaji me wayo to naqi wayon naka shima yaron yasa dariya gani yake kamar alokacin abin ke faruwa bema san sanda shi kansa ya saki murmushi ba.
A bangaren Baba mahmud aka ajiye gawar dan anan za'a masa komi ba tare da wani 6ata lokaci ba aka dora ruwa baba mahmud ya kawo likkafani dan akwai da yawa adakinsa.
Ita kuwa ummu baiwar Allah tun lokacin da tasaka Abbakar amota takejin wani iri har dago mata hannun na baibai da yake mata ta kasa mantawa ji take kamar taje daukoshi in ya qara girma ayi kaciyar har motar ta fice bata denajin ba dadi ba duda yaron yasaba mata haka anman yau se takejin daban kodan za'a mai kaciya ne ta fada aranta gami da komawa bangarenta.
Tun dawowarta gidan bata shiga ko ina sai taje ta gaishesu shi kenan se karatunta kawai tasa agaba se kuma in yaronta yanan ta kunna musu kallo ko yaita mata hirarsa ta yara.
Tunani kala kala ya dabaibaye mata zuciya hakan yasa ta miqe ta shige daki danyin walaha kamar yadda ta saba.
Bayan ta idar ne ta dan kwanta danta huta batamasan sanda bacci yai gaba da ita ba.
Se wajen sha biyu ta farka adan firgigit ta farka tai saurin yin falo dan tasan yanzu Abbakar andawo dashi tasan yanacan yanata zuba shagwabar tasa daman qaqa balle an masa kaciya ita kam yau gurin Hajiya zai kwan dan bazai hanata bacci ba abinda take ta ayyanawa arai kenan.
Ganin falonta wayam yasata yin murmushi tasan yana gun hajiya kodai ta mahfuz ko kuma ta bilkisu wato matar baba mahmud.
Gyalenta ta dauka tai waje kai tsaye bangaren su mahfuz tai duda batasan zuwa sosai sedai takan danne dansu yadda dagaske ta haqura komi ya wuce din
Ba kowa anan ta danji wani abu aranta anman da ta tuna yadda kowa keji da Abbakar tasan kowa yana gurinsa hakan yasa ta juya zuwa 6angarenta.
Alawar da yafi so da madarar da ta hada masa tun safe kan inya dawo ta bashi ta dauka, dan tasan indai taje yaganta ko kasuwa ce gabansa se yasa kuka seta lallashe shi ta bashi alawar zai shiru.
Tunda taci karo da ummi qanwar Abbakar jikinta ta bata wani abu ta share tunaninta ko ran ummin ne a6ace kawai.
Tana shiga an kammala hadashi yaro yai tsawo kamar badan shekara uku zuwa hudu ba yai kyau fuskar nan ta kara haske kwance yake san6al kan tabarma kamar kai masa magana ya amsa.
Da sallamarta gami da fara'a ta shiga falon sedai yadda taga mutan ciki yasata tsayawa soro tai turus tana binsu da kallo.
Kowa ita ya zubama ido bawanda yai zaton ganinta ayanzu ta tsaya kawai tana binsu da kallo ta kasa gaba ta kasa baya ciki zatai ko waje.
Me makon taga yaronta yana mata kuka yana auke shi saidai ta ganshi kwance cikin siffar wanda ya mutu ina ita yaronta be mutu ba da sake abinda take fade cikin ranta kenan kama ce kawai Abbakar dina da ransa wallahi.
Jitai ana jan hannunta tai saurin kallon ko waye Nasir ne ta gani har gaban gawar ya kaita ya durkusar ta gami da saurin barin gurin dan baisan mai zaice mata ba.
Waye wannan take fade cikin daga murya kai kace bata sanshi ba ku fadin kuma karku cemin wannan yarona ne danni yarona da ransa.
Abbakar yazo ya riqeta ki nutsu ummu kar soyyar yaronnan tasa ki kasa fahintar gaskiya gabaki daya ta kasa kukan ma ta miqe gami da yin waje baba mahmud yace da hajiya subi bayanta.
Kai tsaye 6angarenta tayi ta dauko zaninta na atamfa guda biyu ta dawo inda gawar take abu kawai take kamar tababbiya.
Lulluba masa tayi ajikinsa gami da kinkimarsa daqyar tasashi cikin makarar yaran da aka kawo dan kaishi, ta kamo hannun baba mahmud babu ku yi saurin kaishi inda take mazauninmu na gaskiya gaggauta kaishi shine mun masa gata ta koma kansa gami da kuma bude fuskarsa ta shafata se alokacin kwalla ta kawo mata.
Tai saurin shanyeta gami da fadin Allah ya jiqanka yarona Allah yasa kaidin me cetonmu ne se munzo muma munan tafe ta miqe har taikai bakin qofa ta dawo ta dauke alawar da madarar da ta kawo masa da kayansa da aka cire masa tai waje.
Kowa ya cika da tausayinta kwallar su duk ta qaru.
Tsam ta rungume kayan inta tuna basu tai niyar saka masa ba yasa kuka sesu dan tare dashi ake za6o masa kayan sawa.
Tana shiga daki ta rufo qofa gami da tsayawa jikin taga tana kallo aka fito dashi akai waje dashi ba abinda ke bakinta se Allah ya jiqanka yaro na yayinda idaninta keta hango mata shi dazunnan da yake mata bai- bai zasu fita a mota yanzu gashi za'a fitar dashi a motarsa ta qarshe babu damar ya mata bai baidin.......
[1/17, 8:42 PM] Fadimafayau: *Abbakar*
*Na*
*F.A.Ya'u*
*Wattpad FadimaFayau*
*190-200*
Tananan tsaye bakin qofa cike da tunani fal ciki bama tajin bugun da tun d'azu ummi mariqiyar Abbakar keyi.
Ita kuma ganin tayi bugun shiru yasa ta juyawa dan yin bangaren su Bilkisu kamar ance ta kalli jikin taga takai kallonta nan, antin tata tagani tsaye tai saurin komawa ta tabota tai firgigit takai duba inda taji an ta6atan.
Ummi ta gani tsaye riqe da sweet campo tana mata murmushi tai saurin zuwa ta bud'e mata qofar yarinyar tai ciki tana kwalawa Abbakar kira tana waqa ina kake ne dan kaciya da warin tusa nazo da alawata bani baka se kayi tusa me wari naji.
Ummu kasa ce mata komi tai tashige cikin daki ganin ta dube ko ina baya nan yasata fitowa anti ina aka kaimin baby na dan haka take kiransa kalli har tsarabar kaciya nayo nasa shine za'a kaishi wani gurin ni wallahi adawon da yarona ni da kaina zan iya kula dashi tun ganin gawar danta se yanzu taji kuka ya tawo mata na sosai.
Sosai ta fashe da kuka ganin kayan da ke riqe hannun ummi alawa ce, sai fan milk guda biyu da mangwaro irin katon nan duda tasan sunada su a fridge hakan besata siyo masa ba.
Saurin watsar da kayan hannunta ummi tai tayo gurin antin nata tana tambayarta me yasata kuka hakan ya qara sawa ta rushe da sabon kukan
Seda tai me isarta sannan tai shiru inda ita ummi ganin taqiyin shiru yasa ta tuni fashewa da nata kukan, ganin haka yasa ummu daurewa tai shiru.
Miqewa tayi taje ta zuboma ummi Abinci ta miqa mata ta kalleta da zimmar yin magana ta juyar dakai karki cemin komi kici abinci kawai tun jiya rabonki da abinci ina kallonki baki ci abinci ba kika tafi.
Seda ta gama ci sannan ummu tace kije ki kwa6e kayan in yaso sekije can bangaren baba mahmud ki zauna insan zama ni kadai bata kawo komi ranta ba ta miqe tai daki duda tanasan jin dalilin kukan antin tata sedai batasan ta kuma sata kukan.
Acan 6angaren baba mshmud ummi ta shiga tasha jinin jikinta ganin duk mutan gidan anan babu kuma alamar wai suna farin ciki ne.
Fadila ce yar gidan Baba kabiru ta mstso dab da ita ta dafata tace ummi ya haquri kumi ta kalleta soroso haquri kuma ta fada eh mana haqurin danmu wato Abbakar ta miqe wane Abbakar kuma.
Zee ta matso babyn ki mana da yake duk sun san haka take ce masa tai saurin barin falon rasa inda ma zata tayi kasa shiga inda ummu take tai tai bayan gidan tahau rusa kuka.
Iya shaquwa ta shaqu da yaron ashe bazai girma ta ga aurensa ba kamar yadda kullin take buri tun yana zanin goye ta saba dashi da masa komi har ya bude ido yai wayo yake kiranta da umma ashe dazu ganin qarshe tamai da zata tafi makaranta ta makara sun fito tana riqe dashi tai masa wanka ummu ta fito tana fada banace inkin makara ki dinga tafiyarki ba banishi nan ta amshe shi maza jeki ki shirya.
Ta fito ta biya ta dakin ummu yana zaune kan cinyar mumyn tasa suna za6ar kayan dazaisa tace anti ni natafi to Allah bada sa'a kije ki amshi kudinki gurin kawu to tace gami da lakace masa hanci baby se na dawo yasa dariya tai waje.
Jitai an dafa ta tai saurin goge hawayenta gami da juyowa Yah Abbakar ta gani ya komar da ita yazaunar shima ya zauna.
Haba ummi ki dena kuka duk me rai mamaci ne addu'a zaki masa ki kuma dena kukan kinga in momy dinsa taga kin tada hankalinki ita nata kuma tashi zaiti ki daure ko ita take kukan kiyi ta rarrashinta kinji ko to tace gami da kuma share sabon hawayen da yazo mata da sharje majinar a hijabinta irin na me kuka.
Yaita mata nasiha seda yaga tai shiru ya miqe yanzu kije can kisa taci abinci nasan tun safennan bata ci komi ba to tace ta miqe tai cikin gida.
Duk qawayenta sun zo mata gaisuwa har wasu cikin mazan ajinsu Ahmad har mum dinsa seda tazo dan ita har Abbakar din tasani.
Su Aisha ma kullin suna tafe kullin kuma basa gajiyawa da yima ummu nasiha duda tana qoqari sosai wajen boye damuwarta.
*Bayan wata hudu da rasuwar Baby Abbakar.*
Sannu a hankali ummu ta fawwalawa Allah ta riqi karatunta da diyar ruqonta duda wani sa'in takan tuna da yaronta sedai addu'a kawai take masa.
Yan abu daya ke damunta shi ne san mijinta wanda ala dole ake san rabasu gabaki daya baba mahmud ya hanashi zuwa gidan nasu.
In makaranta zata ya daukar mata driver shi ke kaita ya tsaya ko zatakai yanma ya dawo da ita gashi wannan semester din Abbakar din baya daukansu ko zuwa yai department dinsu sedai su kalli juna daga nesa dan bata isa tai masa magana ba dan in driver din yaganta kamar a idon Baban nata ne.
Zaune take gaban gaban iyayen nata baba mahmud ya fara da gyaran murya kamin ya kira sunanta, ta daga ido ta kalleshi yace ba komai yasa muka kiraki ba se dan mu gabatar miki da lawyer din da zai kareki a kotu dan munyi munyi da yaroncan ya sake ki ya qi.
Tai saurin daqowa ta kuma kallonsu wannan shine lawyer din wanda aka nuna yasaki murmushi gami da fadin sunana Barrister Bashir salman ni zan kula da shari'ar taku ta kuma kallonsa tama kasa magana gabaki daya ta rasa abin fade.
Ki tashi kije gobe ne zaman kotun zai fara in ana buqatar wani abu daga gareki zan kiraki to Baba tace dan bata cewa kawun ma ta miqe tai waje.
Tana fita kukan da ta kwace ya tawo mata tai saurin barin bangaren tana shiga falonta ta rushe da kuka...
[1/18, 10:14 PM] Fadimafayau: *Abbakar*
*Na*
*F.A.Ya'u*
*Wattpad FadimaFayau*
*200-210*
Jitai an dafa ta cikin sauri ta dago dan ganin waye ummi ta gani anti mene kike kuka dan Allah ki rage damuwa kinji tasa hannu ta goge mata hawayen da ya 6ata mata fuska.
Anti dan Allah ki fadan meke damunki ko addu'a ce na tayaki ba komi ummi kawai na tuna da baya ne.
Ummi tace anti kan Yaya Abbakar ne ko ummu tai saurin kallonta da mama ki ummi ta qara da cewa insha Allah bazasu rabaku ba anti.
Ummu cike take fal da mamaki wato tana ma ummi kallon yarinya, bata qara shiga mamaku ga seda taji ummin na fadin anman anti kince musu kina sansa ta kalleta sororo alamar me kike nufi.
Anti kema se kinyi wani abu ni inaji ajiki na bawai sunasan rabaku ba ne suna son ji daga gare ki ne sunasan suji kince karsu rabaku da bakinki.
Ummu tace to inba san rabamu suke ba me yasa gobe zasu fara zaman court narasa me yasa suke san rabamu na rasa me ya musu.
Ummi tace anti kiyi haquri ki daure kije kice musu kinasansa ina cewa sukai zasu rabaku dan suna zaton auren dole ya miki dan baki da gata yanzu inya sakeki se wanda kike so zasu baki indai haka ne kenan ko shi din kika ce kinaso zasu baki.
Mamaki fal ran ummu me yasa dani banyi tunanin haka ba da ita kallon yarinya qarama takema ummi ashe duk tana sane da abinda ke faruwa agidan nace "ummu kenan daman yawancin iyaye kan ma yaransu kallon yara qanana irin basu san komi bacin da wasu yaran sunfi wani babban fahinta da iya zance"
Ruqo hannunta ummi tai anti ki daure kije ki fada musu har bakin falon baba mahfud ummin ta rakota seda taga tashiga sannan ta juya zuwa gurinsu.
Da baba Bashir ummu taci karo yace ummulkairi ba yanzu kika bar nan bane tai saurin cewa eh Daman magana nakesan muyi to to yace ai se mu koma cikin tabi bayansa.
Sauran da suma suka miqe da zummar fita suka dawo suka zauna ganin ya zauna itama ta zauna yace tace zata fadi magana ne.
Baba mahmud yace munajinki ummulkairi tai ta maza gami da nemo duk nutsuwarta kamin tace daman roqarku zanyi dan Allah karku rabamu da shi wallahi inasansa.
Gabaki daya suka kalli juna gami da sakin murmushi kamin Baba mahmud ya dora kika ce kinasansa tai shiro da kinsan haka kikai shiru ai da bata kai ga haka ba ma.
Yanzu kije maganar shiga kotu anbarta zan nemeshi dan shirya yadda tarewar zata kasance jitai kamar tasa ihu dan murna ta miqe tana sun sun dakai yayin da fuskarta ke dauke da murmushin farin ciki.
Hartakai bakin qofa Baba mahmud yace ummulkairi tai saurin kintsa kanta dan niyarta tana fita tasa tsalle ta juyo inda wata matsala zaki iya samun ko wanne cikinmu kinji to tace tai waje.
Alhamdulillah take ta fade gami da dansa gudu tai bangarenta tana shiga ta rungume ummi tana murna.
Seda ta nutsu ta fara tunanin ko ta ya zata ma Abbakar albishir tunda yanzu bata da waya tun kwanan Babyn ta arba'in da rasuwa aka kwace wayar duk dan karsuyi waya da abin sonta.
Ummi kije gidansu Takwararki kice tazo inji ni ta tawo da wayarta to anti tace ta miqe tai waje.
Afalo ta taddasu sunata fira ta gaida hajiya dasu Abbakar dinma kamin tace anti takwara daman mum(da yake wani zubin haka take cewa ummun) ce tace kizo kuma ki tawo da wayarki in kina wani abun kiban wayarki kawai in kai mata.
Ta6 wa ni rufan asiri muje inkai da kaina haka kawai a bunciken waya suka saka dariya gabaki daya ta ware mayafin abatar dake daure kanta ta yafa dan daman ashirye take sukai waje.
Abbakar ne ya biyo su yace yar mu zonan ta qarasa na'am yaya ya dan hade rai wato ita mum ni yaya to da ita dani waye ma yafi kama da wanda ya haife ki tasa dariya ita mana yadan hade rai alamar serious magana zaiyi itama ta nutsu.
Me mamar taki zatai da waya tadan kalleshi ko bajiki ni bane tace ai kai zata kira yai saurin cewa ni kuma eh yaya to me zata fadan a'a yaya kadai bari ta kirakan tukunna.
Pls ki fadan bazan ma nuna kin fadan ba yo daman cewa zatai anfasa zaman kotun yanzu su Baba sun yadda da aurenku da gaske kike eh mana yai dariya kije tukwicinki nanan tafe ya ja ya tsaya gami da tsurama wayarsa idanu jiran kiran ummu.
Ummi na shiga falon ummu ta amshe wayarta gami da yin daki ummi tace haba anti kofa gaisawa bamuyi ba bakuna ki fadan me zakiyi da waya ba ta juyo kindai san cikin samarinki ba wanda yakai matsayin in snatching dinsa ko tasa dariya waya sani ko kin hango wani ne da an raba auren ki maqale masa tsaki taja gami da fadin wushe nan yarinya ummi ta qara da inji dan fillo ba.
Tana shiga daki ta hau kiran Abbakar dan ko number dinsa bata tsaya nema ba takanta ta saka dan ta haddace number dinsa.
Bugu daya ya daga duda yasan komi abinka da namijin duniya se mazewa yai a'a ummi lafiya kika kirani bacun kinsan ina gida shiru tai can yace wai bazakiyi magana bane.
Daurewa tai tace Barka da safiya barka dai ya fada cikin sanyin murya dan tuni jin muryarta ya rage masa kuzari a'a ummulkairi kece lafiya dai ko tai shiru kamin tace daman kirawo ka nai mu gaisa yadanyi shiru aransa yace nikam zanso ganin randa yarinyar nan zata sake dani da yawa" nace araina kamar yau ne".
Daman kan zaman kotunnan ne yai saurin cewa gobe ko tace eh karkiji komi ki dena damuwa kinji insha Allah baza'a rabamu ba tai murmushi yai yace kinji dadi ko nace bazamu rabu ba ko tai dariya eh mana.
Kan yace wani abu ta kuma magana daman fada ma zanyi anfasa zaman kotun yanzu su baba sun yadda da aurenmu bata jura cewarsa ba ta kashe wayar gami da yowa waje.
Ummi ta miqama wayarta tace gashi nan nagode tasa dariya anti irin wannan dadewa ana duben waya tai dariya se gashi duk ba number ko hoton wanda ya burgeni ciki kai anti har yayan nawa tasa dariya to shi saurayinki ne ummi tace dadina dake anti kwai iya baqa.
Kiransa ne ya kuma shigowa wayar ummi ta miqo mata wayar anti yaya a'a bazan daga ba pls anti wallahi bazan daga ba kice masa na shiga toilet .
Ummi ta daga wayar yaya tace bazata kar6a ba kuma wai tace ince tana toilet yai dariya to inta fito kice nace to tace kai yaya cewa fa nai ta fadan bawai tana ciki da gaske ba ya kuma yin dariya hoo ummi sarkin hada husuma to batai lefi ba inkin wasa kece ma zakiyi tasa qara ni kuma eh ke ya kashe wayar.
Ta kalli ummu cike da barkwanci tace eyye angama da yaya na tasa dariya to ance miki nidin wasa ce.
Shi kuwa yana kashe wayar yai cikin falo besan sanda farin ciki yasashi sakin qara ba irinta farin ciki hajiya tace kai kuma mene haka nan ya fada mata komi da ya faru itama tai murna sosai.
Tun wayarsu da ummu yake faman baza idanu dan ganin kiransu Baban ummu anman shiru yai sati guda kenan duda an aiko musu an janye batun zaman kotun anman ba'a musu bayanin komi ba duk ranshi babu dadi shi ya qagu yaganta a gidansa.
Zaune yake a office dinsa yana duba takardun da yama dalibai test kira ya shigo wayarsa kamar karya daga yana dubawa yaga Baba mahmud ne yai saurin karawa a kunne gami da sallama cikin girmamawa ya gaidashi kafin baba mahmud din yace yau kazo gida inasan ganinka bai jira yace to bama ya kashe wayar.
Murna ce ta cika masa rai agonsa ya duba yaga yanxu warfe biyu ne yanma batai ba yace ya ninke takardun da yake dubawa yai inda yake da koyarwa yau.
Biyar dedai agidansu mahfuz din ta masa kai tsaye gurin baba mahmud yai dan rabonsa da mahfuz tun mutuwar ko ya kirashi baya dagawa se yaga dama duda bayasan haka sedai babu yadda ya iya.
Cikin mutunci sika gaisa kafin baba mahmud ya dora da bakomi yasa na kiraka ba sedan in sanar da kai ko kuma mu tatttauna kan batun auranku da ummu.
Abbakar yadan muskuta cike da farin ciki Baba mahmud ya dora inasan in fada ma ada bawai qiyayya yasa muka tilasta seka saketa ba bakuma qi bane yasa muka takura se anje kotu ba duda daman ba xuwan zamuyi ha sedan munasan samun tabbaci daga gareta na tana sanka dan bamasan za6a mata wanda bata so.
Yanzu zamuso muji a ina kake ganin zata zauna seka fada mana dan kai mata kayan daki kuma inasan in fada maka mu agaskiya bamu yadda da kunyi aure ba Abbakar yai saurin kallonsa eh bamu yadda ba gaskiya.
Hakan yasa muka yanke nanda wata guda zamu daura muku sabon aure sannan doke ka kuma bata sadaki danmu bamusan ka bata ba kuma inasan kasani yarinyarmu kamar ko wacce mace take dan haka dole ka kawo lefe kamar yadda ake a al'adance dan bama san barin wani sarari da za'a mata gori a rayuwarta duda abaya mun riga munyi sake.
Dan haka kaje ka turo wakilanka kamar yadda kowa yake inyaso semuyi magana dashi.
Wakilan Abbakar sunzo anyi maganar komi wata daya kacal aka saka dan gudanar da bikin nasu.
Amarya ummu se gyara takesha kowa da irin tasa gudun mawar sedai Baba mahmud ya hana Hajiyar Mahfuz kawo komi indai naci ne kosha ko shafawa da sunan abaima ummu dan gyaran amar sabida yace ba'a sake da maqiyi.
Taji ba dadi sedai tasan ita taja ma kanta ummu duk batasan sunyi haka ba duda haka Hajiyar batai fushi ba komi da ita ake.
Ummu tai kyau tai wani fresh gashi daman sunyi hutun mid semester tai wata yar qiba.
Yau take juma'a yau kuma aka saka dan daurin auren nasu a masallacin old campus na BUK za'a daura bayan sallar juma'a.
Zaune take cikin qawayenta su Aisha sunata tsokanarta wayar Aisha tai qara ganin sunan da ke yawo kan screen din wayar yasata miqawa ummu.
Abinda ya ziyarci kunnenta ne yasata sakin ajiyar zuciya wani farin ciki ya ziyarce ta ba komi bane face lasifiqa da taji ana fadin Alhamdulillah an daura auren ummulkairi Yasir Mahmud da Abbakar Fahad kan sadaki dubu Hansin.
Yace Baby kinji me naji tai dan dariya a'a my Habu yai dariya kema ko Habun nanfa Hajiya kawai ke fade tadan miqe to aini nace My a'a kinadai san muyi fada kenan tai dariya wato nayi lefi tun ba'aje ko ina ba to kuwa anya amaryar ce ni yai dariya kan yace wani abu ta kashe wayar.
Aiko tana kashewa su Hafsa na shigowa wato har an fara soyewar ko tace to da tsayawa kallonku zan.
Yau asabar ita ce yini shagali kawai ake sha gidan ya dinke ba masaka tsinke abu daya ke damun ummu rashin ganin ko mutun daya daga ummanta itakam agaskiya bata ga anfanin mutun ya aure wanda ba yar garinsu ba.
Goma dedai masu kai amarya suka kai ummu gidanta dake Nan waje jen state road gida ne na alfarma da ya kunshi duk wani abin more rayuwa da jin dadin dan adam.
Anan da yawa suka kwana yayin da wasu suka tafi.
Washe gari da rana masu gyara inda za'ai walima suka hallara kan yanma sun gama komi guri ya fito tas kai kace gurin yin biki ne na taskeba ba gida ba.
Itama ummu masu kwalliya sunzo sun shiryata sun mata kwalliya irin wadda ake yayi yanzu su Aisha ma duk anan suka kwana sune qirgin biki dasu ake ta hidima.
Wajen hudu gida ya fara daukan harama mutane sun fara hallara ango ma kamar amarya dinne yai kyau sosai komai irin na amarya yasa shima milk shadda yasa mai dinkin kofi da golding kamar dai Amar yar tasa.
Sunyi kyau sosai atare suka futi bayansu qawayenta ne se nasa suma biye dasu fadin kyan dasukai bata lokaci ne kaidai kana kallonsu kasan dansu akayi junansu.
Ba'abinda yaima ummu dadi se ganin innar Ummi tazo harda gwaggo da qawarta Ta Niger aikam tai murna sosai.
Aisha ce ta bude taro da addu'a gami dayin taqaitaccen yarihin amarya da turanci sannan mahfuz yai na ango Abbakar yai mamaki dan be ta6a zaton Mahfux zaizo gurinba balle har yamayi jawabi kowa zazzaune yake sai music me sanyi dake tashi awajen.
Kamar ance ummu ta dago ta hangi ummanta da qannenta sun fito a mota da sauri ta miqe tai gunsu cike da farin ciki bama tasan sa'adda kuka ya kufce mata ba dagyar suka lallasheta Fadya qanwarta ta gyara mata kwalliyarta suka tawo gurin tare.
Kana ganinsu kaga jini daya koda yake ummu tama fisu kyau kawai dai ita baqa ce nasan da ita tayo farin su kyau ba'a magana.
Ummanta itama tai bayani cikin harshen larabci gami da saka musu albarka.
Kowa yaci yasha ya gyatse kowa se saka musu albarka yake se isha kowa ya watse anman duk yadda ummanta tai kan su tafi can main house ummu taqi dole anan suka kwan.
Satinsu daya suka shirya se jordan bayan karamci da suka sha gurin dangin ummu mijinta da yan uwansa.
Rayuwar gidan ummu rayuwa gwanin sha'awa komi atsare suke yinsa shi yake kaita makaranta in ta tashi lokacin ya tashi su tawo tare in be tashi ba ta tawo ita kadai tun yan sch din na gulmarta har sun fara gajiya.
Wasu ma daga wata department din ko faculty dinma har zuwa ganin wace me sa'ar ce tai nasarar auren Mutun mafi farinjini da burge yan mata.
Wasu yan matan ma in sunzo da niyar kusheta se su raina kansu dan gani suke tafisu komi wasu ma sekaji sun koma fadin ai shine ma yai sa'a ba ita ba nace "Hmm students se abarmu"
Bayan shekara uku da auren ummu da Abbakar zaune take suna fira dan basu da wata damu inka dauke rashin haihuwar da suke fama dashi anman in ba haka ba kam rayuwarsu fal take da farin ciki.
Abotar Abbakar da mahfuz ta koma kamar da sedai gidan Abbakar din ne baya zuwa daqyar ya fara zuwa shi kome Abbakar zemsai bazai shiga ciki ba iyakarsa farfajiya.
Aure kam mahfux yaqiyi sunyi sunyi yaqi inma kai masa maganar aure yanzu zakuyi fada
Cikin sa ne ya motsa masa duda ya dade be motsa ba tun yana daurewa har yafara kasawa ta dube shi ganin yana yamutsa fuska tace my me ke damunka kan yafe wani abu cikin ya kuma murdawa tuni ya zubo daga kan kujetar tai saurin yin gurin sa ganin kamar baya nunfashi yasa qoqarin daga shi sedai banbancin halitta wato raunin mace yasa ta kasa.
Waje tai ta kira me gadi driver baya nan su biyu da ita dashi suka daukeshi sukai mota hijabi kawai ta dauka da key din mota tai waje me gadi ya ja mata falon dan yaga bata hayyacinta.
Hajiya ki jira Bala yazo seku tafi No buden qofa kawai ya bude gate din ta ja motar da gudu tai waje dan tuni ta koyi mota.
Kai kawo kawai take aqofar dakin da aka shigar dashi doctor ya fito gami da fadin madan abin ya zama worse ki kira namiji muna buqatar sa hannun wani namiji dan mu masa aiki qodarsa ce ta ta6u sosai kasantuwarta jaruma sosai yasata kasa fashewa da kuka.
Doctor pls ban aron wayarka yadan kalleta kamin yace ok biyo ni office tabi shi yana bata tahau kiran Yah nasir dan ta haddace number dinsa.
Yana dagawa tace yah ummu ce muna asibitin malan Yaya ne ba lafiya pls kazo da wuri ka biya ka fadawa hajiyarsa bata jira cewarsa ba ta katse wayar.
Hankali tashe ya kira ummi qanwar Abbakar ya fada mata ya kira mahfuz kan ya fada agida shi kuma yai asibitin seda yace ya tambayi inda suke ta fada masa.
Mahfuz dinma hankali tashe yai asibitin hajiya kam se kuka take har sukazo asibitin.
Duk suna tsai tsaye gefensa dan ansamu yadan farfado ido kawai yake binsu dashi har yakai kan ummu ya miqa mata hannu tai saurin zuwa cikin dashasshiyar murya irin ta mara lafiya yake magana.
Ummulkairi na yafe miki kema ki yafe min inaso ki sani ni Abbakar me sanki ne har abada sedai inaji a jikina ba'a yomu dan mu rayu tare har abada ba inaji ajiki na bazan tashi ba tai saurin rufe masa baki tana girgiza kai hawayen da tun dazu take qarfin halin boyesu suka kwaranyo kan fuskarta yasa hannu ya goge mata su.
Ya ce ummu ki dena kuka banasan ko bayan raina ki shiga damuwa pls kinji ko ta gyada kai gami da fadin bazaka mutu kaji yai murmushi kawai ummu mutuwa nakan kowa intazo ba yadda za'ai eh tace anman insha Allahu ba yanzu zaka mutu ba.
Ya ruqo hannunta yace inaso in roqeki alfarma dan Allah bayan bana raye karki auri ko wa inba mahfuz ba dan Allah alfarma zaki mun danni badan shi ba dan kuma Allah.
Ya miqo hannunsa gun hajiyarsa yace hajiya ki yafemin cikin kuka take fadin na yafe ma Abbakar anman bazaka mutu ba kaji sannu a hankali nunfashinsa ke qasa tuni tari ta turniqeshi Nasir yai waje ya kira doctor duk aka ce su fice.
Jiki a salu6e doctor ya fito ummu tabishi tana tambayarsa jikin Abbakar yai mata banza nasir ya bishi da sauri.
Kasantuwar yasan Nasir yasa shi tsayawa Baka fada mana komi ba kayi gaba yakamata ka fada mana jikin nasa doctor din ya dan share gumi da fadin am sorry we lost him abinda ummu taji kenan ta zube agurin kowa har doctor din akayo kanta.....
[1/20, 2:22 PM] Fadimafayau: *Abbakar*
*Na*
*F.A.Ya'u*
*Wattpad FadimaFayau*
*210-215*
Nurse doctor yasa ta kawo gado na marasa lafiya suka kama ummu suka dora kan gadon nurse ta hau turata zuwa office din doctor din.
Sosai suke bin cikawa dan gano abinda ke damunta jininta ne yadan hau se kuma dan qaramin ciki da suka gano tattare da ita na kimanin sati goma wata biyu da sati biyu sai kuma suman da tai tuni suka bata duk wani temako da ya kamata.
Sai da doctor din ya tabbatar ta fita daga danger ya fito ya fadawa Nasir komi kan matsalarta duk tausayin ummun ya kamashi.
Farida matarsa yace ta zauna gurin ummun ya bar gurin.
Duk wani cike cike da ya kamata na karbar tawarsu sunyi mota kawai suke jira dan daukan gawar.
Tun lokacin da doctor yace Abbakar ya mutu mahfuz ya kasa komi bare kuma Hajiyar mahfuz da itama suman ne kawai batai ba duk sun kasa komi Nasir ne kawai ke komi.
Koda Muktasir qanin Nasir yazo da hahis din da ya samo irin C-20 din nan Nasir yai dakin inda Abbakar ke kwance lullube juyawa yai zatonsa zaiga mahfuz sedai wayam adan fusace ya koma.
Wai mahfuz me kake nufi ka taso kasan ni kadai bazan iya daga gawa ba ko kuwa so kake muyi ta ajiyeta anan eyye.
Gatan da kawai zamu masa shine muyi maza muje mu kaishi makwancinsa da wuri shima sai ya fison haka.
A fusace mahfuz ya kalle shi wai yaya waya ce maka Abbakar dina ya mutu wallahi be mutu ba hajiya da ke faman kuka ta dafa mahfuz, pls kaje ku kaishi mutuwa dole ce ko be mutu yanzu ba dole zai mutun ne kayi haquri kaji, zaiyi magana Hajiya ta gurgiza masa kai alamar kar yace komi.
Miqewa yai jiki ba kwari kansa na wani irin sarawa yabi bayan Nasir shida Muktasir ganin Abbakar dinsa lullu6e cikin siffar gawa yasa shi rushewa da kuka.
Da qyar yai shiru ya kamashi zuwa gadon da zai fitar musu dashi Nasir da Muktasir suka hau tura gawar yayin da Mahfuz ya zube agurin yana ci gaba da kuka.
Ba abinda yake fadi se Nakarya alqawari ka yafemin bazan iya cika shi ba ba kowane alqawari bane sai akoyaushe Abbakar na roqonsa in ya rigashi mutuwa baya san kuka yafi san addu'a ada yana ganin kamar zai iya ashe kuka in aka maka ma mutuwa ta jiki bakai kake kawo shi ba shi yake kawo kansa.
Bari mu dan leqa ban garen Hajiya Batula da Salma tsohuwar matar Mahfuz.
Tun bayan rabuwar auren Salma da mahfuz da suka kakkarya asirin Hajiyar mahfuz suka quduri niyar kota halin qaqa ne sai sun tarwatsa rayuwar gidan su Mahfuz din.
Se kuma sunsa ala dole ko baya so ya dawo da Salma dansu fi jin dadin rama abinda ya musu kunji fa jahilci saki uku ne fa bawai guda daya ba.
Sune kullin cikin bin malamai komai nasu agun malamai yake warewa sedai ba Nasara abinda basu sani ba yanzu mahfuz ba mahfuz dun da dasuka sani bane dan ya canza ya maida ibada abokiyarsa kullun cikin nenan tsari Yake.
Cikin halin Salma Na bin maza babu wanda ya zauna dan wani sa'in yanzu inta kada kanta tabar gida seta fi wata tanacan guest house na samarinta ko dakinsu lala cewa ma kamar dada mata akai.
Hajiyar ta ko ajikinta dan kuwa Salmar ke mata komi dan tuni mahaifin su salman ya sallama ta gidansa ma ya koreta taqi tafiya kasan tuwarsa ba mesan riki ci ba ya gyaleta take zaman yayanta anman ba ruwansa da ita.
Cikin yawon malamanta ta hadu da wani boka har halin da su mahfuz ke ciki ya nuna mata ganinsu cikin farin ciki ya mugun daga mata hankali dan ita babu abinda yanzu ta tsana irin ta gansu cikin farin ciki.
Rai 6ace ta kalli Boka wallahi su ne ya za'ai atar watsa munsu acire duk wani farin ciki daga rayuwarsu.
Boka ya bushe da dariya wannan me sauqi ne daga garemu sedai fa anman zai iya zama me wuya agareku ta dube shi adan tsorace Boka ka fadi ko mene zamu iya indai burin mu zai cika ya bushe da dariya she giya ke ya fada.
Aikin bazai ta6a ci ba sai in har na kwanta da ke gaban yarin taki sau uku sannan itama haka kuma duk a lokaci daya ta miqe what boka agaban diya ta fa.
Ya bushe da dariya wadda ta har gizama Hajiya Batula tunana seda yai me isarsa kamin ya hade rai yai gum da bakinsa kafin wani kuka mai tsuma zuciya yahau tashi shima seda akayi sosai sannan kuma gurin yai tsit wata murya me ban tsoro tace zaki zauna ko kuwa.
Tai saurin komawa ta zauna dole ki bi umar ninmu seda muka fada miki abin zai miki wuya kika amince bama fadar buqata ta dan yalolo(aljanin da yake aiki dashi) face se an aiwatar bawai dan kun burgemu bane ko muna sha'awarku sedan kasancewar qazantar da zaki fitar alokacin inatama nata diyar taki wanda zata fitar shi zai zama abincin dan yalolo kuma mahadin aikinku.
Duk a tsora ce take sedai abinka da wanda zuciyarsa ta bushe ta daure tace to boka gobe zamu zo insha Allah daga baya aka daka mata tsawa ke gyara bakinki nan ba'a kira mana Allah kinsan da Allah din kika zo gurin mu.
Tashi ki fice kuzo da wurwuri dan gama aiki ta miqe tana qoqarin ijiye kudin jakarta boka yace maza kiyi sauri ki ajiye wannan najasar ki bamu guri zamu saka jim6ato ya fitar mana dasu.
Tana fita boka ya bushe da dariya gami da dauke kudin ya zura a aljihu.
Ko da ta koma gida ta fadawa salma yadda sukai da boka salman bataji komi ba ta amince dan ita tuni ta saba da irin hk gaban wasu da yawa ma balle gaban babarta.
Ni kinsan me ma umma se kin fada ni na fasa komawa gidan mahfuz kawai dai a cusa musu baqin cikin a tarwatsa su.
Ni na sami wanda ya fishi in munje gurin bokan se yamin aiki akansa mutumin yayi irin wanda nake so ne ga kudi ga dukiya ga harka matsala ta dashi kawai mutumin bani yake so ba jikina yake so kinga in munje se asamo min kansa.
In na samu kansa ai mu mun warke gidan nanma umma barinsa zakiyi in siya miki wani ki huta da gori suka tafa Hajiya suka tafa ita da diyar tata tace she giya ke hakan za'ai.
Washe gari suka rankaya gurin boka abinka da wanda zuciyar su ta bushe basu ji komi ba se rana suka baro gurin bokan.
Aran na kwana ukun ne boka ya basu maganin da zasuje su barbada a kogi dan tarwatsa gidan gobe kuma se su dawo su amshi sauran maganin sukai sukai ya basu duka yace sharadi ne dole ba'a badawa alokaci guda haka suka haqura suka baro gurin boka da zimmar gobe zasu dawo.
Se dare suka je kogin wudil dan daga gurin boka can wudil din suka nufa seda suka barbada maganin sannan suka kuma biyo hanyar kano.
Washe gari da wurwuri suka nufi gurin boka dan karbo sauran kayan aikin dan sun qagu magani ya tara aiki dan boka ya fada musu indai bai basu dayan ba magani bazai ci ba kuma bala'in kuma duniya su zai shafa shi yasa suketa sauri su amso sauran.
Abunda suka gani yai mugun daga musu hankali wato dai boka suka gani kwance cikin mata gugun mutuwa yanata ihu yana fadin na dena karku kashe ni atsorace sike can wata murya ta hau magana zaku bar nan ko kuma se fushin mu yahauku da gudu suka bar bukkar.
Suna fita bukkar ta hau ci da wuta boka yanata ihu yayin da su Salma tuni suka dauki qafa suka hau gudu basu suka tsaya ba se a titi suka tari mota se kano.
Akan hanyarsu ta dawowa sukai hadari inda yawanci minor injury ne aka samu sai salma data karye Umman tata kuma da farko kamar ba abinda yasameta sedai duk yadda taso motsa jikinta ta kasa.
Asibiti aka wuce dasu aka dora salma yayinda umman aka gano ta samu matsalar spinal Cord, hankalinsu sosai ya tashi haka bayan sati biyu suka koma gida.
Tun salma na jinyarta harta dena ta maida hankalinta ga karuwancinta yaranta da bataso ta fifita Salma kansu su suke mata komi.
Watansu uku da yin wannan hadari jikin Hajiya Batul ya qi sauqi itama salma haka suna zuwa aka tabbatar musu sun kamu da HIV hajiya Batul hankalunta ya tashi gashi ko motsi bata iyayi kanta ne kawai ke iya motsawa ajikinta se mgn da take iyayi yanzu kuma ga wani bala'in wai HIV.
Jikin salma yaqi sauqi gashi duk abokanan shashan cin nata sun guje ta kullin inta zauna se kuka basu da aiki se fada ita da hajiyar tata.
Yauma kamar kullin salma kuka take tana fadin Allah ya isa tsakani na dake umma duk ke kika cuce ni dan ni duk cikin wanda muke harka babu me qanjamau kin cuce ni kin kaini na dauko alaqaqai.
Ita ma umman cikin fada take fadin na cuceki ko kika cucen da baki takuran ba kin nuna dole mu dau fansa ai da banje ba kullin cikin haka suke suyita yima junansu Allah ya isa.
[1/22, 10:22 PM] Fadimafayau: *Abbakar*
*Na*
*F.A.Ya'u*
*Wattpad Fadimafayau*
*210-220*
*Alhamdulillah haqiqa ina mai godema Allah da ya bani ikon rubuta wannan littafi nawa ya kuma bani ikon ganin qarshensa.*
*Fatan kuskuren da ke ciki za'amin afuwa ajizanci ne na dan adam*
*Kazalika ina godema duk wani ko wata da ya karanta wannan kittafi a ko ina yake ko take nagode sosai.*
*Taku ta musanmance*
*@Aeshakabir kinfi kowa san jarumi Abbakar a wattpad nagode sosai da Vote da comments Allah bar qauna.*
*@Amina-yarzazzau kema nagode sosai da vote da comments.*
*@Uomyasmin nagode sosai da Vote da comment.*
*@rehanerh kema godiya nake da Vote da comment.*
*Ban mance da kuba masoyan littafin Abbakar na WhatsApp*
*Safiyya kabir(Safiscos) godiya me tarin yawa.*
*Fatima Ahmad(Takwara) ina godiya fa.*
*Ummu Najees(cleavers writers grp) nagode.*
*Maimunatu Ibrahim(cleavers writers)
Godiya sosai.*
*Taslim Abbakar ina godiya*
*Nafisat Abbakar godiya nake*
*Zahra Bashir ina godiya sosai*
*Zakiyya Aminu Ibrahim*
*Kuna da yawa ina godiya gabaki daya ko kinga sunanki ko baki gani ba kisa aranki u mean alot to me nagode sosai.*
Cigaban labari
Kai tsaye mota sukai da gawar Muktasir da driver suka kama ma Nasir suka saka shi ciki me mota ya tsinki ganye ya maqalama mota alamar sun dauko gawa ne.
Mahfuz ne yai ta maza ya miqe yai waje gurin hajiyar Abbakar yai da take ta faman kuka umma tashi muje a hada shi agabanmu dan muyi sallamar qarshe.
Ta dube shi ido jawur cikin da shasshiyar murya take magana pls mahfuz karfa ka fadan da gaske ya mutu din ya dafa ta nima ban yadda ba gani nake kamar mafarki ne sedai yanzu na yadda tunda sun tafi dashi ki taso muje kar akaishi.
Miqewa tai tabishi abaya motarsa da yazo da ita suka shiga ya jasu sai gida.
Ita kuwa ummu Allurar da aka mata ta fara sakinta firgigit ta farka cikin kuka gami da qoqarin miqewa Farida tai saurin riqota tana girgiza mata kai alamar ta koma cikin zafin nama ta tura farida gami da tsinke drip din dake jikinta.
A sukwane ta miqe tai waje sedai kasan tuwar allurar bata gama sakinta ba jikinta kuma ba qwari yasa tuni jiri ya debeta ta fadi gurin da gudu Farida tai gunta cikin kuka ganin kamar bata numfashi yasata fita aguje daga dakin tai inda nurses ke.
Suna isa da gawar ana kiran la'asar hakan yasa da suka shigarta gidansu Abbakar dan can suka kaita ko wannensu ya daura alwala sukai masallaci.
Bayan an idar ne Nasir ke fadawa liman nan da nan ya sanar a lasifiqa hakan yasa tuni wanda suka halarci sallah din suka gar zaya dan ayi jana iza tare dasu.
Kafin wani lokaci tuni lokon ya cika danqam ba wanda baiji mutuwarba dan Abbakar mutun ne me kirki ba ruwansa bashi kuma da abokin rikici.
Tuni yaya Babba ta iso seda su nasir suka qaraso suka fito da gawar zuwa inda za'a mata wanta dan har an dora komi likkafani ma Baba mahmud ya kawo.
Kawunsa wato yayan babansa da kuma qanin habansa sune zasu masa wanka ruwa kawai suke jira.
An kammala hada gawar kwance yake cikin shigar da sedai amaka kuma in anyi babu me cire ma wato sanye yake cikin likkafani jira kawai gawarsa take akaita masaukinta na har abada.
Hajiyarsa aka fara kira tai masa addu'a ba abinda take fade se Allah ya jiqanka kuka kawai take ashe shine zai rigata tafiya abinda kawai tunani kenan tana tuno rana irin wannan da aka ce tazo tai sallama da mahaifinsa.
Alokacin gani take kamar zai dawo sedai gashi shekara ashirin da shida da rasuwarsa be dawoba kenan shima Habunta tafiya zaiyi ta har abada tuni ta fashe da kuka tabar dakin.
Kowa yai sallama da shi masu daukan gawa suka dauka sukai waje ummi.
Ummi qanwarsa ta dawo daga makaranta taga mutane jingim qofar gidansu anata alwla hankalinta ya tashi to wa ya mutu bacin lafiya tabar gidan daqyar ta qarasa zuwa ciki.
Tana shiga taga anyo waje da makara kasa tambayar mene tai kawai ta fashe da kuka me tsuma zuciya.
Daruruwan jama'a suka sallaci Abbakar daruruwa suka bi gawar dan mata rakiya zuwa makwancinta na gaskiya.
Kasan tuwar maqabartar da nisa yasa a motar gawa za'a kaishi ta masallaci wadda daman shi ya siya matsayin sadaqatujjariya.
Mahfuz tare sukaje suka sayo motar ganin Abbakar kwance cikin motar matsayin gawa yasa shi kuka sedai hawaye kawai kebin fuskarsa yayin da yake tuna yarintarsu da samar takarsu har yazuwa shigowar ummu rayuwarsu.
Yasani Abbakar amini ne bashi da kamarsa sansa yake so na tsakani da Allah wanda shi yasan baya masa irinsa takuma san duniya bazai samu wanda ke masa irin sa ba cikin abokansa yasan ko yan uwansa basa masa shi haqiqa nayi rashi ya fada.
A hankula ya bude lullubin da aka masa fuskar nan shar kamar yace Aminin ya Amsa.
Tuni an haqa kabari dan haka suna isa suka hau kiciniyar binne shi.
Ita kuwa farida tana kiran nurses suka qaraso daya cikinsu ta fita dan kira Doctor yayin da sauran suka maida ummu gado se faman fada suke ma farida dan mene zata barta ta miqe ita dai tai shiru dan tasan halin nurses da bala'i.
Koda doctor yazo ya dubata gami da yima Farida kashedin karta kuma barinta ta miqe dan za'a iya rasa cikin jikinta to kawai farida tace dan gabaki daya yaudin bata iya komi tun lokacin da doctor din yace Abbakar ya rasu.
Ummi na shiga gida aka fada mata ai Abbakar ya rasu nan tai waje ita dole adawo mata da yayanta dan be mutu ba dazunnan fa sukai waya bata da kudi ya mata transfer kuma ace mata ya mutu ina qarya ne dagyar aka kamota aka dawo da ita gida tana kuka.
Lokacin da suke shigar da gawar ne cikin kabari mahfuz yai saurin dakatar da fara zuba qasa wallahi da ransa yake fade Nasir ya ruqeshi haba mahfuz me kake haka ne yafa mutu.
Dasauri ya tan kada Nasir gami da juyawa ga kawun Abbakar yana fadin kawu wallahi da ransa da karfi kawu ya girgizashi haba mahfuz wai yaushe zakasan kaddara ne karfa ka kafirta kanka mutuwar ce baka yadda da ita ba kome.
Cikin kuka yake magana wallahi kawu na yadda da mutuwa kawai dai Aminina ne be mutuba naga yai motsi ba motsi yaiba mahfuz gizo ne yake maka.
Wallahi kawu yayi motsi in kuma kun bunneshi to kuwa ku kuka kasheshi zan kuma dinga kallonku matsayin masu kisa dan kun kashemin dan uwa.
Kawu ne ya dubi Nasir kasantuwar yasan Nasir din karatun likitanci yai yana kuma koyar da masu karatun likitanci yasa ce masa Nasiru kuma duba manashi zaka fimu ganewa ko ya mutu din ko da ransa.
Nace yace Kawu wallahi ya mutu tun dazu muka tabbatar a asibiti nace ka dubamin ko so kake mu binneshi qarshe mu dawwama cikin kokonton ko da ransa muka binne shi eyye.
Sosai nasir ya doba shi baya numfashi babu alamar yanada rai zaiyi magana yaji shima kamar yana motsi abin ya bashi mamaki zuciyarsa fa babu alamun tana bugawa.
Hannun yasa dedai jijiyar kansa yai shiru gami da maida hankalinsa kanta tabbas tana bugawa alamar harbawar jini sedai kadan kadan take wato zai iya mutuwa ko yaushe in ba'ai wani abinba.
Da sauri ya juyo da ransa sedai yana cikin danger da sauri suka ciro shi daga kabarin gami da cire audigar da ke hancin sa da karkade kasar da aka fara zuba masa sukai asibiti.
Yadda yake cikin likkafani haka suka kaishi asibitin, batare da 6ata lokaci ba likitoci suka dunguma kansa oxygen aka saka masa dan te maka masa wajen yin nunfashi seda suka samu dagyar zuciyarsa ta fara bugawa yadda ya kamata suka dedaita numfashinsa sannan suka fito.
Mahfuz ka fadan meke damunsa ina ciwon qoda ne inji Nasir eh yaya qarya kake mahfuz alamun ciwonsa bana qoda bane.
Ciwon zuciya ne ya fada anman yana ciwon qodar wallahi nayi zaton ciwon zuciyarsa ya dade da warkewa tun yaushe yake ciwon zuciyar tun mutuwar babansu shi kenan Allah ya bashi lafiya amin yace.
Nasir ya kuma duban mahfuz yace kaje ka fadawa Hajiyarsa be mutu ba bazani ba yace Nasir yace bazaka fa kace eh inkaga nabar nan se ance min Aminin ya farfado.
Gyada kai kawai Nasir yai yai waje dan ya fuskanci mahfuz din yanzu baya hayyacinsa.
Gabaki daya hankalin kowa ya koma kan ganin farfadowar Abbakar sunma mance da baiwar Allah Ummu dake can kwance.
Se washe gari ummu ta farfado allurar ta saketa ta kuma dena jirin cikin kuka ta miqe tana fadin Anti Farida dan Allah karki cemin Yah Abbakar ya mutu ta dafa ta ummu nasanki da juriya ki zama jaruma pls mutuwa dole ce.
Ta miqe cikin kuka ba wata jaruma da zan zama ni inasan mijin kar abinne minshi wallahi zan zauna koda gawarsa ne wallahi.
Seda Hajiyar Abbakar tazo sannan ta tambayi ina Ummu se alokacin suka tuna da ita ba shiri sukai can bangaren da suka barta.
Tana ganinsu tahau kuka da sauri Nasir ya qarasa ya ruqo hannunta cikin kuka take tambayarsa mijinta yaja hannunta se inda Abbakar yake.
Kwanan Abbakar biyu a asibitun malan su mahfuz suka gama komi dan kaishi can qasar waje inda za'a kula dashi sosai duda suma nan din basu gajiya ba.
Da ummu aka tafi dan duk yadda sukai kan ta yi haquri ta zauna taqi.
Satinsu uku a india Abbakar ya farfado sedai baya iya komi se kallo da ido kawai.
Watansu biyu a india Abbakar yaji sauqi sosai jiki yai kyau komai yana iya yi da kansa sa6anin da dasaidai ummu tamai in bata kusa mahfuz.
Lokacin da yaji ummunsa nada ciki murna yai sosai harda dagata yana juyawa da ita tai saurin kwace kanta tana dariya tana fadin rufan asiri kaida baka da lpy da dai zan iya ai da na daga ka.
Shaquwarsu da abotarsu da mahfuz ta dawo kamar da koma fiye.
Daga india jordan suka wuce can gurin mahaifiyar ummu taji dadi sosai seda suka mata wata guda suka baro jordan zuwa Nigeria cike da kewa.
Lokacin da suka dawo Abbakar yai kyau yai qiba kaikace bai jinya ba cikin ummu ma ya dan fara fitowa.
Seda ta tabbatar ya ji sauqi sosai sannan ta kawo batun 6oye mata ciwon sa da yai wato be dauketa da mahin manci ba cikin kuka take magana jin kukanta yake har cikin ransa.
Ya jawota jikinsa yahau lallashinta dagyar tai shiru ummu ban boye miki ba nayi zaton na warke ai na fada miki ciwon qodar da nake.
Abin mata da miji yaita bata baki harta haqura kan alqawarin ya dena boye mata damuwarsa dan mahfuz ya fada mata yawan boye abu ransa da cunkushe damuwa ya jaza masa ciwon dan shima se ya takura yake fada masa meke damunsa.
Shi din mutunne da baya fadin abinda ke damunsa duk girman takaici yakan kunshe shi cikin ransa ne yaita in abu yai yawa ne yakan danyi kuka shima a boye.
Watansu biyar da dawowa ummi ta haifi yaranta yan biyu duk maza murna gurin uban gayya Abbakar bafa a magana.
Ranar suna yara suka ci sunan mahaifin ummu da na Abbakar suke kiransu da Walid da Amir.
Suna akai sosai bana wasa ba anyi gayya sosai.
Akullim inta kalli yan biyunta ta takalli tafkeken hotonsu dake jikin bangon dakin wanda sukai ita da Abbakar da babyn ta da ummi me rainonsa setaga kamar shine ahannunta banbancin kawai wannan biyu ne shi kuma daya ne.
Lokacin da rai arba'in har Niger sukaje ita da Abbakar da ummi dan ko bayan Rasuwar Baby Abbakar bata maida ita ba.
Sosai suka sami kar6uwa abinda ya baima ummu mamaki shine gani jarin fulawarta ya bunqasa ba wai yanzu iya magarya da zender ba state da dama na Niger kanzo siye buhu buhu.
Wajen miliyan biyar innar Ummi ta bata wanda tai tara tarawa cikin riba qin amsa tayi tace innar tasa ayi borehole da masallaci a unguwar dan lokacin data zauna agarin taga yadda suke matsalar ruwa tace sadaqatujjariya ga mahaifinta da kakarta da babansu mahfuz.
Sauran riba kuma tace in an samu araba biyu a ajiye mata daya daya inna ta dauka.
Qawarta Fiddo tayi aure har ya mutu bataji dadin gidan mijinba ummu ta tawo da ita dan ta cigaba da karatu a Nigeri.
Har can inda akama Abbakar masauki a niyame suka je sunyi murna sosai malan musa yace oh ashe zaka tuna damu bayan shekara biyar da tafuyarka Abbakar yai dariya na tafi cikin gaggawa bamuyi sallama ba zanso zumuncin mu ya dore sosai yai musu alkairi sukaita murna.
Ummu tuni ta gama degree dinta dan hartai masters lauya din da baban mahfuz yace dukiyarta nagunsa ma tuni ta nemo shi ta amshi komi nata gami da masa kyauta.
Kamfanin qere qere ta bude gami da tallafawa yara masu kwakwalwa duk yaron dake da fasaha ta qere qere ummu kan daukoshi musanman mara gata ta kaishi makaranta me kyau ta bashi aiki kamfaninta dan baje irin tasa fasahar in ka kammala jami'a inkaga zakai aiki da kamfaninta to in kuma bazakai ba takan tsaya maka dan samun inda kake so sedai bata ta6a tsayawa mutun dan barin nigeri da sunan aiki.
Tuni su Aisha sukai aure suma duk da yaransu zumuncinsu kuwa se abinda ya qaru.
Zaman Fiddo gidan ummu yasa suka saba da mahfuz dan yanzu yana zuwa gidan harsuyi fira da ummu dan itama ta saki jiki bakamar daba da take kullin cikin daure masa fuska yanxu ta mance da komi ta kuma yafe masa.
Ansha bikin Fiddo da mahfuz sosai iyayen fiddo sukaji dadi yayin da take BUk tana karantar BSC nursing, lokacin yaran ummu shida haihuwa biyar maza uku mata uku.
Muktar qanin Abbakar ma ya dawo ya zama kwararren likita yazama shi ke kula da asibitin da mahaifinsu yabar musu gado.
Maryam qanwar Abbakar kuni ta jima da yin aure harda diyarta mace tana da wani tsohon cikin.
Ummi ma qanwar Abbakar tai aure ta auri muktasir qanin Mahfuz zumuncinsu kullin qaruwa yake.
Ummu diyar wato ummi yanxu ana level 3 yayin da tuni suka dedai ta kansu da Ahmad amin ummu jira kawai ake ta kammala asha biki.
Zaman auren ummu da Abbakar abune abin sha'awa ga kowa koyaushe cikin san junansu suke sedai kunsan ako yaushe aka ce aure dole ana samun matsaltsalu nanda can anman in ma'auratan suka iya zamantakewa ba mejin kansu.
*Bayan shekara Ashirin da biyar zuwa da bakwai..*
Duniya ba gurin zama bace tuni Hajiyar mahfuz ta jima da rasuwa, itama ta Abbakar din tsufa sosai kullin gidanta cike yake da jikoki harda tattaba kunne dansu Nur din yaya babba sun jima da haihuwa.
Yau jikinta yaqi dadi hakan yasa sukai asibiti da ita sedai kansuje ta rasu kowa yaji mutuwar nan sosai su Abbakar harda kuka.
Walid dan wajen ummu tuni suka dedai ta da Shukra yar gidan Aisha bayan wata biyu da rasuwar kakar tasu aka sha biki.
Shima Amir yar gidan mahfuz yakeso basu wani bata lokaci ba akai nasu auren.
Fatima kuwa tuni ta jima da mutuwa qawar ummu da Aisha wata sch mate dinsu a buk sedai ta bar diyarta daya wadda ummu ta dauketa take kula da ita duda kuwa dangin fatiman sunso su hanata da temakon Abbakar suka bata.
Itama Kairat din ta girma ansa ranarta lokaci kawai ake jira asha biki.
*Bayan shekara goma sha daya.*
Ummu ce zaune jikoki sun ke wayeta na yaranta dana gurin ummi da na gurin kairat sun cikata da hayani kowa da abinda ke fade daga wancan yace gwaggo kinga wane ko se wancan yace gwaggwo a ina kika ajiye min kazana.
Abbakar ya shigo duk an tsofe kannan ya furfure dan tuni yai ritaya yaransu ke musu komi duda kuwa ummu nada kamfaninta se abinda yai gaba shima.yanada nasa anman basa zuwa ko ina kamfanin ma kula musu ake dashi.
Ya dubeta sweetheart wai yaushe yaran nan zasu tafi ne ta dubesu kowa da abinda yake tai dari se nanda.sati uku what ya fada aikam iyayensu zan kira kowa yazo ya kwashe dansa haba ni nagaji abarnima in hutawa tsofa na da mata ta se ankawon jikoki tai dariya mu lokacin da muke kaima hajiya me tace yai dariya ita daban ai.
Na'im babban jikansu dan wajen ummi ya dubi kakan nin nasa yace kajifa wai Sweetheart har tsoffi sunsan love, Fadila yar wajen kairat tasa dariya bari kawai yah na'im ko kunya basa ji.
Eyye kingani ko yarannan samana ido kawai suke dole su tattafi Husain dan gurin walid yace ta6 ai ba inda zamuje Abbakar ya cilla masa lemar hannunsa kaji mara kunya to dole ku tafi Usman dan qarami da befi shekara hudu ba yazo ya fada kan Abbakar yana dariya.
Nana ma ta fada kansa Abbakar yace kai nidai na banu ummu yasa dariya.
An koma makaranta kowa ya koma gidansu anbar Abbakar daga shi sai ummunsa zaune suke yana shan fura kamar yadda al'adarsa take ya dan jawota jikinsa sweetheart ta ce na'am my D yaushe za'a kuma bada hutu nai missing din yaran nan tai dariya se bayan wata uku yai dan tsaki kamin yace.
Kai duniya ba komi bace ada mu biyu muke zaune muka haifi yaranmu sun tafi se jikoki suma tanzu sun tafi ta shafo gefen fuskarsa haka ne my D qarshe ma mutun shi daya zai dawwama akabari to Allah yasa mu cika da imani tace Amin ya kuma riqeta sosai ajikinsa sukai dan shiru na mintina kamin ummun tace my D yace na'am tace nagode.
Me akayi u support me alot yai dariya duty nane matsayin miji no need ki godemin tai dariya inasanka mijina shima yai dariya inasanki nima Allah yasa mu rayu a aljannah tare amin my D.
Alhamdullah nan nakawo qarshen littafin Abbakar.
*Abin lura*
_*Arayuwa muna buqatar yafiya gami da mantuwa kamar yadda ummulkairi ta mance da abinda mahfuz yai mata suka ci gaba da rqyuwarsu cikin jin dadi_
_*Mutun baya taba wuce rabonsa duk rintsi seka ci abinda Allah ya tsaga shine naka sannan zaka mutu inka nema baka samu ba to abinnan tabbas ba raboknka bane kamar yadda Abbakar har ansashi a kabari sedai kasantuwar rabonsa aduniya be qareba ya dawo ya ci gaba da rayuwa._
_*mutane da dama suna fadin me yasa bansama littafin suna Nasir ko ummulkairi ba sedai ni ina ganin Sunan Abbakar yafi dacewa da littafin Abbakar mutun ne me sadaukarwa kamar yadda yake ganin zai iya sadaukar da sosayyarsa ga aminsa._
_Abbakar mutun ne me iya tankwara zuciyarsa kamar yadda lokacin da zuciyarsa ta amince kan yin masha'a da ummu ya tankwarata yaqi yi duda alokacin tanada dama anman be hakanba se yazama mutumin kamsa kuma ni aguri hakan ya kamata mu zama masu danne san zuciyarmu in ba dedai bane._
_Abbakar mutunne me haquri da sanin ya.kamata duda kasantuwar rashin mutuncin mahfuz gareshi lokacin da mahfuz din ya shiga matsalar asiri shi ya shiga ya fita seda yaga yazama normal._
_Duda kasantuwar ummul kairi nada yaro bashi yai cikin ba bakuma da aure ta haifeshi ba anman hakan besa da sukai aure ya wulaqanta ta ba sannan kasantuwar yaron ba nasa ba baisa ya tsani yaronba yaso yaron tun kan yai nasa dan._
_Tabbas da zansa sunan wani ba Abbakar ba to kuwa na Nasir ne dan akoyaushe muna muqatar tausayi da san yan uwa muna buqatar muzamto jarumai alokacin da yazamto mana na baqin ciki._
_Nasir mutunne me san yan uwansa kulawa dasu ako wanne hali duda kasan tuwar farida yakeso da yaga auren ummu zak iya sauqaqa mata lamarinta ya akiye buqatar zuciyarsa dan ceto yar uwarsa._
_Nasir mutun ne da duk girman matsala yakan iya tattara nutsuwarsa guri guda kamin ya tunkareta kamar lokacin mutuwar baby Abbakar da shi kansa Habu din wanda kuna kowa anso yazamto mutun mai jarimtar nutsuwa a kowa ne hali._
_Miqama Allah lammuranmu akoyaushe shi yafi dan babu me maka abinda be ma ba zuwa gurin bokaye ba namu bane musanman mu mata komi kike buqata tashi cikin darw ki nema Allah na kowa ne zai baki duk girman buqata in kuwa kika riqi wani sa zaki qare cikin nadama kamar yadda Hajiya Batul tai._
_Kishi da yassada ba namu bane musanman kan yara inba haka ba zasu kaimu su baro kamar yadda suka kai Hajiyar mahfuz da shi kansa Mahfuz din danshi sharri dan aike ne in yaje ya dawo kan ka ke koma._
_Duk girman matsala in mukai haquri akwai sauqi kamar yadda ummu da tai haquri komi ya zamto labari_
*Godiya me tarin yawa ga duk wata ko wani da suka karanta fatan kukkuren da ke ciki za'a min afuwa ajizanci ne na dan adam.*
For comment or correction WhatsApp only pls
09028287218