Juyi Asmau tayi wanda yasa ta bude ido. Cikin na Col. Ishaq suka sauka da yake ta kallonta. A kwance take shi kuwa ya dora habarsa akan hannunsa daya ya zuba mata ido tana ta bacci. Ba karamar kunya taji ba tayi kasa cikin lallausan bargon da suka rufa dashi. Yana murmushi ya bude mata fuska tare da cewa
"Na tasheki da kallo ko, duk laifinki ne da kika sa nake jin dama tun ranar da muka fara haduwa aka daura mana aure."
Bai san irin yadda take jin kunyarsa ba. Ta rufe ido tana noke kai. Jin kanta take a takure kamar tayi tsuntsuwa ta gudu. Dama ya tabbatar da wuya yaji tayi magana. Duk da burinsa kunyarta ta ragu idan suna tare amma ya lura kamar karuwa tayi. Matsowa yayi daidai kunnenta yace "zaki iya tashi muyi sallah?"
A hankali ta gyada masa kai sannan tace cikin wata karamar murya "asuba tayi?"
Mamaki tayi domin gani take kamar yanzu ta rufe idonta ta fara bacci. Kamar yasan me take tunani yace "kina mamaki ne? Bayan kin cinye daren da kuka da ....."
Da sauri ta rufe masa baki kafin ya fadi abinda yayi niyya. Ai kuwa ya ciji tafin hannunta a hankali ta cire shi daga bakinsa ta saki kara tana kwabe fuska zata yi masa kuka. Dariya ya fara da yaga da gaske kukan zata yi harda guntun hawaye ya kama hannun yana hurawa.
"Yi hakuri my darling Asmau, matar soja bata kuka. Matar Jikamshi kuma ba raguwa bace"
Kyale shi tayi yana rarrashinta ta daidaici kafadarsa sai saukar cizo yaji. Ta soma dariya da taga ya shige shi sosai ai kuwa suka fara kokawa yana cewa sai ya rama. Ga tsoron kada ya rama din da gaske ga dariya tana cinta. Tun yana zai rama har ya koma yana kallon yadda take dariya da hawaye a idonta. Ji tayi ya rungumeta a hankali
"Allah Yayi miki albarka Matar Jikamshi. Yadda kike faranta min nima Allah Ya bani ikon yi miki haka."
Nutsuwa tayi ta dena dariyar tana cewa amin ga adduarsu sai ga kiran assalatu. Col. Ishaq yayi saurin tashi
"Kinga zaki sa mu makara ko? Na tashi da niyar nayi shirin zuwa masallaci sai na tasheki ne"
"Ka tashi dai kana cin zalina daga zuwana gidanka"
"Haka ma kika ce? Ji yadda kika cije ni fa. Ki zauna cikin shiri idan na dawo zan rama."
Sai da ya fito daga bandaki ya saka doguwar riga zai tafi masallacin dake bayan layinsu yazo inda take kwance don bazata tashi yana dakin ba yace "ki kular min da kanki sai na dawo" ya kusa bakin kofa yaji tace
"Allah Ya tsare min kai Ya dawo da kai lafiya"
Yaji dadin adduar sosai har bazai iya kwantatawa ba "nagode Matar Jikamshi amma hakan bazai hanani ramawa ba idan na dawo." Daga haka ya fita itama ta tashi ta kimtsa tazo ta fara nafila. Bayan ta idar da sallolinta zama tayi tana ta mika godiyarta ga Allah. Hakika ta sami babban rabo da Allah Ya nufeta da yin aure duk da abubuwan da suka faru a rayuwar ta. Mata irinta nawa ne suke cikin tashin hankali da muguwar kyama. Kuma wasu da gaske sun tuba amma hakan bai sa mutane raga musu ba. Ta san dai komai bazai taba gogewa kamar bai faru ba amma duk da haka auren da tayi yafiye mata komai. Ta auri irin mijin da kowace mace zata so kasancewa dashi. A take ta yanke shawarar neman izininsa na yin azumi duk ranakun litinin da alhamis domin neman karin kusanci da Allah da kuma tuba.
*****
A nan ya dawo ya sameta tana kuka da addua. Ya zauna a gefenta suka karasa tare sannan ya kuma bata baki akan ta cigaba da hakuri da rayuwa. Daga hira ya dawo da maganar rama cizo. Ta soma bashi hakuri yace bai san zance ba. Daga baya yace "nuna min inda bakya so a jikinki sai na rama a nan"
"Gaskiya ina son ko'ina"
Dariyar mugunta yake mata don yaga tsoro take ji. "To bari na saukaka miki. Rinka nuna min inda kika fi so, duk inda kika bari karshe shine ba kya so din. Sai ki bar min nayi yadda na ga dama".
Asmau ta hau tunani gashi ya kureta akan gado. Duk inda tasan ana jin zafin cizo ta fara lissafawa a cikin zuciyarta. Yace ita yake jira tace "to bakina nafi so"
Col. Ishaq ya dan bata rai "ni kuma nan ne bana so sosai a jikinki. Kinga sai na rama a nan ba sai munyi nisa ba"
Daga nan bai bari ta motsa ba bare ta gudu....
*****
Shi ya fara tashi wurin goma ya kalleta. Bacci take sosai kamar wata 'yar yarinya. Allah Sarki Asmau, duk wata matsalarta ta wuce a wurinsa. Yadda ta iya jajircewa akan aurensa duk da matsalarsa yasa yake jin sonta sosai a ransa. Zaiyi nasa kokarin sosai wurin kyautata mata. Duk wani gata da miji zaiyiwa mace shima zai kokarta. Baya son ko kadan suyi nadamar auren juna. Yadda take tunanin yayi mata alfarma shima hakan yake ji. A hankali ya fita daga dakin don kada motsinsa ya tasheta. Yasan ba karamar gajiya ta tara ba tun kafin a fara bikin. Ga ta biki ga rashin bacin kirki a nasa gidan.
Kitchen ya shiga wanda ya cika store din da kayan abinci tun kafin a kawo gara. Sauran kananan abubuwa da mace ke bukata na kitchen ya bawa Safiyya kanwarsa kudi yace ta tabbatar idan an gama jere ta sayo su ta ajiye. Ai kuwa ta siyo su kwai, kayan miya da 'yan tarkacen da ba'a rasa ba duk ta ajiye a inda ya kamata tun jiya. Su Shemau ta tarar suna karasa aiki lokacin da ta kawo kayan. Ya duba ya sami abubuwan da yake bukata ya fito dasu. Addua yake kada Asmau ta tashi sai ya gama komai. Ya dade da koyon girki a wajen Hajiyarsu. Ko ta koreshi daga kitchen sai ya dawo yace tayata zaiyi. Ita tana haka saboda namiji ne kuma dan fari shi kuwa ko a jikinsa. Har babansu yace ta rabu dashi. Ga amfanin koyon girkin yazo. Da Asmau idonta biyu kila tayi masa dariya ko kuma ta hana shi. Wata hira da suka taba yi ta fada masa abinda tafi son ci da safe ya tuna. A lokacin dama tunaninsa yayi mata shi ranar farkon aurensu.
Tana can tana baccin gajiya ya da fa masu indomie da attaruhu, albasa da caras yadda tace tana so. Ya dafa kwai ya yanka a gefe da cucumber sannan ya hada musu tea a cups ya zuba a tray.
Shi kadai yake murmushi har yaje dakin. Tana nan inda ya barta. Ajiye tray din yayi ya zauna kusa da ita ya janyota jikinsa. Ta bude ido kenan zata yi magana ta kula da agogo. Shadaya harda rabi. Ta zaro ido tana kokarin tashi."Subhanallah haka nayi ta bacci, ka dade da tashi ko? Ko breakfast ban hada maka ba. Bansan wane irin bacci nayi ba yau"
Duk ta damu ko kadan ba haka taso ba. Amare da take jin labari sun riga mazansu tashi sun hada musu abinci ita gashi rana ta fito tana bacci. Zaunar da ita ya sake yi "duk kin wani tada hankali kamar wadda tayi laifi. Bacci kuma ai dole kiyi, ko kin manta baki sami damar yi ba jiya"
Asmau ta ji kunya, duk inda zai dauko maganar da zata kunyatata ya iya. Ta sake yunkurin tashi sai ta ga tray din abincin har tiriri yake, sai lokacin ta farga da kamshin dake tashi taji cikinta na kukan yunwa. Idonta ne ya ciko da kwalla da ta ga yadda ya tsara komai kamar ba hirarsu ne sati daya kafin biki. Fadawa tayi jikinsa "Jikamshina nagode" tana jin wani sabon sonsa a ranta.
Wannan farincikin yake son gani daga gareta kuma ya samu. "Kije kiyi brush kada yayi sanyi. Idan kuma godiyar zaki yi zan baki goyon baya. Kinsan ana son yawan godiya" yana magana yana daga mata gira ta tashi da sauri tana dariya ta shige toilet.
Kafin ta fito wayarsa ta soma kara ya dauka ganin maigadinsa ne.
"Sir baki ne suka zo har mota biyu. Na bude musu?"
Col. Ishaq yaji kamar ya fita ya kori ko su waye. Shi fa yana mamakin wannan dabiar ta hausanmu. Ayi komai na hidimar biki da mace wai amma gari na wayewa sai su zo ganin amarya. Ko ganin gulma kamar yadda yake kiran ziyarar. Ai dai a bari ko azahar ayi. Amma yanzu ko shabiyu batayi ba ace an zo gidan sababbin aure ai ba'a so zaman lafiya ba. Bare a lokaci irin wannan da ya gama tsara yadda zai kasance idan sunci abinci da amaryarsa.
"Ina fata ba a gabansu ka kirani ba"
"Eh Sir, ina daga ciki ne"
Rai a bace yace "to ka fita kace wayata a kashe take kuma nayi umarni kada ka bude sai da izinina"
Ya ajiye wayar da yaji Asmau zata fito. Akan gadon suka ci duk kunyarta ta ajiye a gefe suna bawa juna a baki. Yadda ya kyautata mata itama haka take kokarin yi masa. Shaf ya manta da batun baki sai da Asmau ta fita kitchen zata mayar da kwanukan Hajiya ta kira shi. Ko gaisuwarsa bata amsa ba ta fara fada akan lallai yasa a bude gate ga baki nan 'yan uwansu ne da wasu daga gidansu Asmau duk sun hadu a bakin gate maigadi yaki budewa. Ba'a son ransa ba yace to tare da bata hakuri. Da Asmau ta dawo tace masa zata je tayi wanka.
"Nazo muyi tare?"
Ta fito da manyan idanunta "rufa min asiri"
"Nine sirrin naki Matar Jikamshi. Bakya bukatar rufe min komai. Kije kiyi amma idan kika dade zaki ganni"
Ta fita shi kuma yayi waje daga shi sai dogon wando da jallabiya. Bazai fada mata da baki ba yasan rudewa zatayi ta fara komaina gurguje. Abinda baya so kenan shiyasa ya kyaleta ma tayi wankan. Bayan ya bawa maigadi umarnin ya bude musu ya bude kofar falon ya koma ciki.
'Yan uwansu ne na Jikamshi masu komawa a ranar sai na Asmau 'yan Wushishi. Sake fitowa yayi da bayan sun shigo an fara hayaniya ana ta gaisawa. Wasu suna ina amarya take. Ai suna ganinsa har 'yan uwan nasa kunya sosai ta kamasu domin kana ganinsa zaka san bai dade da tashi ba. Yayi murmushin keta ganin duk sun daburce da ganinsa a haka suka gaisa, manyan cikinsu ma sunji kunya. A ransa yace gobe ma ku sake zuwa kallon kwakwaf. Basarwa yayi yace "tana shiryawa ne bari na kirowata"
Kafin ya karasa shigewa korido din ya soma jin suna kuskus ana cewa dama ba yanzu suka zo ba sai anjima. Dakin Asmau ya shiga tana kokarin zuge zip din riga. Tana ganinsa ta juya kada ya ga bayan ya shigo ya rungumeta ya zuge mata zip din yace "sarkin kunya kin gama shiryawa, muna da baki a falo"
A rude tace "baki kuma, yaushe suka zo. Ban duba kitchen din ba ko akwai wani abu mai sanyi da zamu bawa baki" tunanin yadda zatayi ta soma.
Dama ransa ya baci da zuwan bakin ganinta yanzu ya sa ya dan manta. Gashi yanzu duk an ruda masa mata. Ita ma bata gamawa sanin kan gidan ba an zo mata mutane sunfi goma.
"Shiyasa tun dazu da suka zo nace kada a bude gate din"
"Sun dade da zuwa? Meyasa kace kada a bude yanzu sai ace laifina ne"
A zatonsa zata ji dadin yadda yayi bai san mu mata mun saba da irin wannan bakin na bayan kai amarya ba. Idan ba'ayi sa'a ba ma kawayenta ke zuwa jin ya aka kwana. Amarya mai bakin aku tayi ta bayani dalla dalla. Gani yayi duk ta damu da bakin da bata san ko su waye ba yace "nayi miki gwaninta shine kike bata rai. To kije wurinsu ina daki idan kun gama"
Asmau taji wani iri. Maganarsa kadai ta sanar da ita ransa ya baci. Ya juya zai fita ta riko hannunsa "kayi hakuri Jikamshina"
Ya danyi murmushi "babu komai akwai lemo a fridge kuma ina jin da cake sai ki basu"
Fita yayi ya barta ta rasa yadda zatayi. Gashi yayi fushi sannan ga bakin da idan bata je ba zasu tafi da ita a baki. Haka ta yafa mayafi ta fita wurinsu. Su a takure ango ya basu kunya ita kuma ta kasa sakin jiki saboda kunyar an shanyasu a waje ga Jikamshinta yana fushi. Basu dade ba suka tafi ko irin leken gidan amarya basuyi ba tunda ansan yana gidan.
Suna tafiya ta koma dakinta ta canja kays zuwa wasu riga da siket da suka fiddo da jikinta sosai. Tasha turare da kwalliya ta tafi bawa angonta hakuri.
Zaune ta same shi akan wata doguwar kujera ta dakin ya gama shiryawa yana waya da alama Mami ce. Tunda Asmau ta shigo ya ganta da kwalliya da kamshin da take zubawa ya nemi fushinsa ya rasa. Hannu ya mika mata alamun ta karaso. Tana ji ya sallami Mami ya dubeta "apology accepted"
Tace tana jindadi "tun kafin na bada hakurin"
"Ganinki ya kori fushin amma ki sani bazan yarda da bakin nan ba. Sati biyu kawai aka bani a wurin aiki. Bazanyi sharing dinsu da bakin nan ba. Anjima zamu hada kaya gobe in sha Allah zamu je Yankari Game Reserve"
Ta sunkuyar da kai ta kara bashi hakuri sannan tace "ko naje na fara hada kayan yanzu?"
Ya ja hancinta "yanzu kuma ai lok[truncated by WhatsApp]
ABINDA AKE GUDU🙆🏽56
Batul Mamman💖
Bai san irin yadda take jin kunyarsa ba. Ta rufe ido tana noke kai. Jin kanta take a takure kamar tayi tsuntsuwa ta gudu. Dama ya tabbatar da wuya yaji tayi magana. Duk da burinsa kunyarta ta ragu idan suna tare amma ya lura kamar karuwa tayi. Matsowa yayi daidai kunnenta yace "zaki iya tashi muyi sallah?"
A hankali ta gyada masa kai sannan tace cikin wata karamar murya "asuba tayi?"
Mamaki tayi domin gani take kamar yanzu ta rufe idonta ta fara bacci. Kamar yasan me take tunani yace "kina mamaki ne? Bayan kin cinye daren da kuka da ....."
Da sauri ta rufe masa baki kafin ya fadi abinda yayi niyya. Ai kuwa ya ciji tafin hannunta a hankali ta cire shi daga bakinsa ta saki kara tana kwabe fuska zata yi masa kuka. Dariya ya fara da yaga da gaske kukan zata yi harda guntun hawaye ya kama hannun yana hurawa.
"Yi hakuri my darling Asmau, matar soja bata kuka. Matar Jikamshi kuma ba raguwa bace"
Kyale shi tayi yana rarrashinta ta daidaici kafadarsa sai saukar cizo yaji. Ta soma dariya da taga ya shige shi sosai ai kuwa suka fara kokawa yana cewa sai ya rama. Ga tsoron kada ya rama din da gaske ga dariya tana cinta. Tun yana zai rama har ya koma yana kallon yadda take dariya da hawaye a idonta. Ji tayi ya rungumeta a hankali
"Allah Yayi miki albarka Matar Jikamshi. Yadda kike faranta min nima Allah Ya bani ikon yi miki haka."
Nutsuwa tayi ta dena dariyar tana cewa amin ga adduarsu sai ga kiran assalatu. Col. Ishaq yayi saurin tashi
"Kinga zaki sa mu makara ko? Na tashi da niyar nayi shirin zuwa masallaci sai na tasheki ne"
"Ka tashi dai kana cin zalina daga zuwana gidanka"
"Haka ma kika ce? Ji yadda kika cije ni fa. Ki zauna cikin shiri idan na dawo zan rama."
Sai da ya fito daga bandaki ya saka doguwar riga zai tafi masallacin dake bayan layinsu yazo inda take kwance don bazata tashi yana dakin ba yace "ki kular min da kanki sai na dawo" ya kusa bakin kofa yaji tace
"Allah Ya tsare min kai Ya dawo da kai lafiya"
Yaji dadin adduar sosai har bazai iya kwantatawa ba "nagode Matar Jikamshi amma hakan bazai hanani ramawa ba idan na dawo." Daga haka ya fita itama ta tashi ta kimtsa tazo ta fara nafila. Bayan ta idar da sallolinta zama tayi tana ta mika godiyarta ga Allah. Hakika ta sami babban rabo da Allah Ya nufeta da yin aure duk da abubuwan da suka faru a rayuwar ta. Mata irinta nawa ne suke cikin tashin hankali da muguwar kyama. Kuma wasu da gaske sun tuba amma hakan bai sa mutane raga musu ba. Ta san dai komai bazai taba gogewa kamar bai faru ba amma duk da haka auren da tayi yafiye mata komai. Ta auri irin mijin da kowace mace zata so kasancewa dashi. A take ta yanke shawarar neman izininsa na yin azumi duk ranakun litinin da alhamis domin neman karin kusanci da Allah da kuma tuba.
*****
A nan ya dawo ya sameta tana kuka da addua. Ya zauna a gefenta suka karasa tare sannan ya kuma bata baki akan ta cigaba da hakuri da rayuwa. Daga hira ya dawo da maganar rama cizo. Ta soma bashi hakuri yace bai san zance ba. Daga baya yace "nuna min inda bakya so a jikinki sai na rama a nan"
"Gaskiya ina son ko'ina"
Dariyar mugunta yake mata don yaga tsoro take ji. "To bari na saukaka miki. Rinka nuna min inda kika fi so, duk inda kika bari karshe shine ba kya so din. Sai ki bar min nayi yadda na ga dama".
Asmau ta hau tunani gashi ya kureta akan gado. Duk inda tasan ana jin zafin cizo ta fara lissafawa a cikin zuciyarta. Yace ita yake jira tace "to bakina nafi so"
Col. Ishaq ya dan bata rai "ni kuma nan ne bana so sosai a jikinki. Kinga sai na rama a nan ba sai munyi nisa ba"
Daga nan bai bari ta motsa ba bare ta gudu....
*****
Shi ya fara tashi wurin goma ya kalleta. Bacci take sosai kamar wata 'yar yarinya. Allah Sarki Asmau, duk wata matsalarta ta wuce a wurinsa. Yadda ta iya jajircewa akan aurensa duk da matsalarsa yasa yake jin sonta sosai a ransa. Zaiyi nasa kokarin sosai wurin kyautata mata. Duk wani gata da miji zaiyiwa mace shima zai kokarta. Baya son ko kadan suyi nadamar auren juna. Yadda take tunanin yayi mata alfarma shima hakan yake ji. A hankali ya fita daga dakin don kada motsinsa ya tasheta. Yasan ba karamar gajiya ta tara ba tun kafin a fara bikin. Ga ta biki ga rashin bacin kirki a nasa gidan.
Kitchen ya shiga wanda ya cika store din da kayan abinci tun kafin a kawo gara. Sauran kananan abubuwa da mace ke bukata na kitchen ya bawa Safiyya kanwarsa kudi yace ta tabbatar idan an gama jere ta sayo su ta ajiye. Ai kuwa ta siyo su kwai, kayan miya da 'yan tarkacen da ba'a rasa ba duk ta ajiye a inda ya kamata tun jiya. Su Shemau ta tarar suna karasa aiki lokacin da ta kawo kayan. Ya duba ya sami abubuwan da yake bukata ya fito dasu. Addua yake kada Asmau ta tashi sai ya gama komai. Ya dade da koyon girki a wajen Hajiyarsu. Ko ta koreshi daga kitchen sai ya dawo yace tayata zaiyi. Ita tana haka saboda namiji ne kuma dan fari shi kuwa ko a jikinsa. Har babansu yace ta rabu dashi. Ga amfanin koyon girkin yazo. Da Asmau idonta biyu kila tayi masa dariya ko kuma ta hana shi. Wata hira da suka taba yi ta fada masa abinda tafi son ci da safe ya tuna. A lokacin dama tunaninsa yayi mata shi ranar farkon aurensu.
Tana can tana baccin gajiya ya da fa masu indomie da attaruhu, albasa da caras yadda tace tana so. Ya dafa kwai ya yanka a gefe da cucumber sannan ya hada musu tea a cups ya zuba a tray.
Shi kadai yake murmushi har yaje dakin. Tana nan inda ya barta. Ajiye tray din yayi ya zauna kusa da ita ya janyota jikinsa. Ta bude ido kenan zata yi magana ta kula da agogo. Shadaya harda rabi. Ta zaro ido tana kokarin tashi."Subhanallah haka nayi ta bacci, ka dade da tashi ko? Ko breakfast ban hada maka ba. Bansan wane irin bacci nayi ba yau"
Duk ta damu ko kadan ba haka taso ba. Amare da take jin labari sun riga mazansu tashi sun hada musu abinci ita gashi rana ta fito tana bacci. Zaunar da ita ya sake yi "duk kin wani tada hankali kamar wadda tayi laifi. Bacci kuma ai dole kiyi, ko kin manta baki sami damar yi ba jiya"
Asmau ta ji kunya, duk inda zai dauko maganar da zata kunyatata ya iya. Ta sake yunkurin tashi sai ta ga tray din abincin har tiriri yake, sai lokacin ta farga da kamshin dake tashi taji cikinta na kukan yunwa. Idonta ne ya ciko da kwalla da ta ga yadda ya tsara komai kamar ba hirarsu ne sati daya kafin biki. Fadawa tayi jikinsa "Jikamshina nagode" tana jin wani sabon sonsa a ranta.
Wannan farincikin yake son gani daga gareta kuma ya samu. "Kije kiyi brush kada yayi sanyi. Idan kuma godiyar zaki yi zan baki goyon baya. Kinsan ana son yawan godiya" yana magana yana daga mata gira ta tashi da sauri tana dariya ta shige toilet.
Kafin ta fito wayarsa ta soma kara ya dauka ganin maigadinsa ne.
"Sir baki ne suka zo har mota biyu. Na bude musu?"
Col. Ishaq yaji kamar ya fita ya kori ko su waye. Shi fa yana mamakin wannan dabiar ta hausanmu. Ayi komai na hidimar biki da mace wai amma gari na wayewa sai su zo ganin amarya. Ko ganin gulma kamar yadda yake kiran ziyarar. Ai dai a bari ko azahar ayi. Amma yanzu ko shabiyu batayi ba ace an zo gidan sababbin aure ai ba'a so zaman lafiya ba. Bare a lokaci irin wannan da ya gama tsara yadda zai kasance idan sunci abinci da amaryarsa.
"Ina fata ba a gabansu ka kirani ba"
"Eh Sir, ina daga ciki ne"
Rai a bace yace "to ka fita kace wayata a kashe take kuma nayi umarni kada ka bude sai da izinina"
Ya ajiye wayar da yaji Asmau zata fito. Akan gadon suka ci duk kunyarta ta ajiye a gefe suna bawa juna a baki. Yadda ya kyautata mata itama haka take kokarin yi masa. Shaf ya manta da batun baki sai da Asmau ta fita kitchen zata mayar da kwanukan Hajiya ta kira shi. Ko gaisuwarsa bata amsa ba ta fara fada akan lallai yasa a bude gate ga baki nan 'yan uwansu ne da wasu daga gidansu Asmau duk sun hadu a bakin gate maigadi yaki budewa. Ba'a son ransa ba yace to tare da bata hakuri. Da Asmau ta dawo tace masa zata je tayi wanka.
"Nazo muyi tare?"
Ta fito da manyan idanunta "rufa min asiri"
"Nine sirrin naki Matar Jikamshi. Bakya bukatar rufe min komai. Kije kiyi amma idan kika dade zaki ganni"
Ta fita shi kuma yayi waje daga shi sai dogon wando da jallabiya. Bazai fada mata da baki ba yasan rudewa zatayi ta fara komaina gurguje. Abinda baya so kenan shiyasa ya kyaleta ma tayi wankan. Bayan ya bawa maigadi umarnin ya bude musu ya bude kofar falon ya koma ciki.
'Yan uwansu ne na Jikamshi masu komawa a ranar sai na Asmau 'yan Wushishi. Sake fitowa yayi da bayan sun shigo an fara hayaniya ana ta gaisawa. Wasu suna ina amarya take. Ai suna ganinsa har 'yan uwan nasa kunya sosai ta kamasu domin kana ganinsa zaka san bai dade da tashi ba. Yayi murmushin keta ganin duk sun daburce da ganinsa a haka suka gaisa, manyan cikinsu ma sunji kunya. A ransa yace gobe ma ku sake zuwa kallon kwakwaf. Basarwa yayi yace "tana shiryawa ne bari na kirowata"
Kafin ya karasa shigewa korido din ya soma jin suna kuskus ana cewa dama ba yanzu suka zo ba sai anjima. Dakin Asmau ya shiga tana kokarin zuge zip din riga. Tana ganinsa ta juya kada ya ga bayan ya shigo ya rungumeta ya zuge mata zip din yace "sarkin kunya kin gama shiryawa, muna da baki a falo"
A rude tace "baki kuma, yaushe suka zo. Ban duba kitchen din ba ko akwai waniz , , zaki abu mai sanyi da zamu bawa baki" tunanin yadda zatayi ta soma.
Dama ransa ya baci da zuwan bakin ganinta yanzu ya sa ya dan manta. Gashi yanzu duk an ruda masa mata. Ita ma bata gamawa sanin kan gidan ba an zo mata mutane sunfi goma.
"Shiyasa tun dazu da suka zo nace kada a bude gate din"
"Sun dade da zuwa? Meyasa kace kada a bude yanzu sai ace laifina ne"
A zatonsa zata ji dadin yadda yayi bai san mu mata mun saba da irin wannan bakin na bayan kai amarya ba. Idan ba'ayi sa'a ba ma kawayenta ke zuwa jin ya aka kwana. Amarya mai bakin aku tayi ta bayani dalla dalla. Gani yayi duk ta damu da bakin da bata san ko su waye ba yace "nayi miki gwaninta shine kike bata rai. To kije wurinsu ina daki idan kun gama"
Asmau taji wani iri. Maganarsa kadai ta sanar da ita ransa ya baci. Ya juya zai fita ta riko hannunsa "kayi hakuri Jikamshina"
Ya danyi murmushi "babu komai akwai lemo a fridge kuma ina jin da cake sai ki basu"
Fita yayi ya barta ta rasa yadda zatayi. Gashi yayi fushi sannan ga bakin da idan bata je ba zasu tafi da ita a baki. Haka ta yafa mayafi ta fita wurinsu. Su a takure ango ya basu kunya ita kuma ta kasa sakin jiki saboda kunyar an shanyasu a waje ga Jikamshinta yana fushi. Basu dade ba suka tafi ko irin leken gidan amarya basuyi ba tunda ansan yana gidan.
Suna tafiya ta koma dakinta ta canja kays zuwa wasu riga da siket da suka fiddo da jikinta sosai. Tasha turare da kwalliya ta tafi bawa angonta hakuri.
Zaune ta same shi akan wata doguwar kujera ta dakin ya gama shiryawa yana waya da alama Mami ce. Tunda Asmau ta shigo ya ganta da kwalliya da kamshin da take zubawa ya nemi fushinsa ya rasa. Hannu ya mika mata alamun ta karaso. Tana ji ya sallami Mami ya dubeta "apology accepted"
Tace tana jindadi "tun kafin na bada hakurin"
"Ganinki ya kori fushin amma ki sani bazan yarda da bakin nan ba. Sati biyu kawai aka bani a wurin aiki. Bazanyi sharing dinsu da bakin nan ba. Anjima zamu hada kaya gobe in sha Allah zamu je Yankari Game Reserve"
Ta sunkuyar da kai ta kara bashi hakuri sannan tace "ko naje na fara hada kayan yanzu?"
Ya ja hancinta "yanzu kuma ai lokacina ne ranki ya dade"
ABINDA AKE GUDU🙆🏽57
Batul Mamman💖
Washegari garau ta tashi kamar ba ita ba. Sai a lokacin hankalin Col. Ishaq ya kwanta ya lallai wani satin ta huta har ta kara samun lafiya.
Sun cigaba da harkokinsu cikin kwanciyar hankali ya karbo mata form din Jamb suka cike tare sai jiran lokacin jarabawa. Bayan sati daya Walida ta kirata ta sanar da ita zata kawo mata ziyara da neman shawara. Dadi ya kama Asmau ta shiga dakin Jikamshinta ta fada masa ta same shi ya mike akan gado yana baccin gajiya ko uniform dinsa bai iya cirewa ba. Daga taje ta zuba masa abinci kafin yayi wanka sai bacci. Asmau ta tsaya tana kallonsa cike da tausayi. Babu abinda baya wadata su dashi ita da Amatullah. Ji tayi a ranta inama zata haifa masa da ko 'ya mai kama dashi. Yana da tsayi da girma kana ganinsa kaga soja. Bata gajiya da kallon mijinta abin alfaharinta, komai nasa yayi mata. Fuskarsa kullum bata rabo da yi mata murmushi, idan kaga ya hade rai to yana wurin aiki ne. Amma duk da haka mutanen dake karkashinsa suna yabonsa da kirki da iya jan mutane a jiki. Col. Ishaq mutum ne mai jama'a, a irin zamansu da kyautatawarsa gareta haihuwa ce kadai tasan zata yi ta faranta masa rai sosai. Hawaye taji ya zubo mata tayi saurin sharewa kada ya gani hankalinsa ya tashi.
Wayarta ta saita a kansa ta kashe flash light ta fara daukarsa a hoto. Sai da ta gaji don kanta ta juya zata fita taji ya tade mata kafa ta fado a kansa. Da farko ta tsorata sai kuma ta fasa bayan taji yadda ya riketa a jikinsa. Ta dube shi idanunsa har lokacin da alamar bacci ya sake kwantar da kansa ya rufe ido. Tace
"Tun yaushe ka tashi?"
Bai bude idon ba yace "tun da kika shigo kina kare min kallo mana. Ko nayi miki kyau ne"
Tayi murmushi tana shafa sajensa "kullum ma kyau kake min Jikamshina. Musamman idan kasa kayan nan kamar kada ka fita"
Yaji dadin abinda ta fada. Kamar yadda mata ke son a yabe su haka maza suke so suma matansu su yaba musu. Wayarta ya karba ya daukesu selfie suna yiwa juna murmushi. Bayan ya dauka yace "Matar Jikamshi kinyi kuka ko"
Asmau tayi saurin kai hannunta wurin idonta zata goge sauran hawayen da tayi lokacin da take tsaye yana bacci.
"Abu ne ya shigar min ido fa"
"Uhmm uhm Matar Jikamshi kada mu fara yiwa juna karya. Na kuma san halinki da saurin kuka. Fada min me kika saka a ranki."
A nutse yake kallonta ta sake shige masa tana jin wani hawayen na kokarin zuba.
"Kawai ina tunanin abinda zanyi maka ne na faranta maka rai sosai. Kayi min komai a rayuwa har bana jin akwai matar da tayi dacen abokin rayuwa kamar ni. Har kunyarka nakan ji a raina in ga kamar bana yi maka abin da ya dace"
"Babu abinda nake so daga gareki da baki bani ba. Kin bani Asmau da duk abinda Asmau ta mallaka. Adduata kullum Allah Ya bamu zaman lafiya mai dorewa."
Ta amsa da amin hawayen da take boyewa suka gangaro. Ba su suka fito ba sai da Amatullah ta dawo daga islamiyya lokacin an kusa kiran magariba.
*****
Bayan ya tafi aiki da safe sannan Amatullah ta tafi makaranta ta gama gyaran gida ta dora abinci. Walida na son alala shiyasa da tayiwa Jikamshi nashi abincin ta gyara wake tayi musu alala mai cike da dafaffen kwai da ta yanka kanana da kayan hadi. Kafin ta iso ta gama komai da zatayi har da juice din kwakwa da ayaba.
Sai da tayi wanka Walida ta iso suka zauna hira. A hirar ne suna cin abinci Walida take neman shawararta akan abokin Col. Ishaq wanda shina soja ne kuma likita a nan asibitin barrack dinsu. Sunansa Hussaini, yana da mace daya da yara hudu. Asmau dadi ya kamata tace "ashe dai da gaske yake, Walida ki amince ni dai a dan haduwarmu a fuskanci mutumin kirki ne kuma mai addini. Yazo gidannan tare da Jikamshina yayi min tambayoyi a kanki. Dama shiru nayi sai kinji daga bakinsa."
Walida tace "wato ko kunyata ba kya ji kike cewa Jikamshinki"
"Don ma kada kice abin yayi yawa ne na tsaya a nan. Kinsan yadda nake ji dashi kuwa. Hmmm Jikamshi mijin Matar Jikamshi" tana magana tana kashewa Walida ido don tsokana. Ai kuwa ta kai mata dundu ta kauce suka saka dariya.
Walida tace "to ya batun matarsa? Kinsan yadda muke da Anti bana son harkar kishiya. Ko shekara batayi ba a gidanmu Abba ya saki Mama. Auren shekara tara ya iya yi mata saki uku lokaci guda."
Asmau tana tausayin Walida ta wannan fannin. Bata tashi tasan soyayyar mahaifiya ba kamar yadda suka sani ita da nata 'yan uwan. Tsakaninta da babarta sai anyi hutu. Shima babanta baya bari ta dade "Walida ba duka aka zama daya ba. Munje gidansa suma sun zo mana nan. Ni dai ina ganin kamar tana da kirki gaskiya duk da idan aka ce kishiya yanzu sai tunaninmu ya sauya. Ki dage da adduar neman zabin Allah. Idan mijinki ne sai kiga mun sha biki cikin kwanciyar hankali. Kada ki bari tsoron abinda baki da masaniya akansa ya sakaki ki amincewa da shi. Baki san inda alkhairinki yake ba"
"In sha Allah zan dage da yin istikhara. Allah Yasa yankewar zaman nawa a gida tazo. Nima nayi auren nan na huta da gorin Anti"
"Ke ba'a cewa haka, aure ai saboda Allah ake yinsa ba gorin kowa ba. Da baki samu da wuri ba ai ba laifinki bane. Auren wuri ko rashinsa jarabawace wallahi"
Murmushin yake kawai Walida tayi tace "Kada ki manta na girmeki da fin shekara. Ni fa ina jin kamshin shekara talatin. Gorin dangi anyi anyi har na saba dashi"
"Masu shekaru arbain suce me Walida? Nayi tunanin yanzu ke mai iya bawa wasu shawara ce idan kika duba rayuwarmu. Kowane bawa mace ko namiji akwai hanyar da Allah ke gwada imaninsa. Fatanmu kada Allah Yasa mu kasa hakuri har mu fadawa shirka."
Sun cigaba da hirarsu Asmau ta soma jin zuciyarta na tashi. Da gudu ta tashi ta tafi toilet din cikin falon ta rinka kwara amai kamar kayan cikinta zasu fita. Walida duk ta gama tsorata ta dafe mata baya tana sannu. Hirar da basu karasa ba kenan sai da ta sani nutsuwa Walida tace "ke kuma aka ake yi sai dai idona ya gane min. Meye nufinki da, wato sai ya fito na gani kamar kowa." Ta kalli saitin cikin Asmau "dan albarka ko yar albarka Mama Walida na gaisuwa. Wannan aman nasan so kake nasan da zamanka. Ranka ya dade dan soja"
Asmau tayi murmushi mai ciwo. Ina ma dai gaske ne, "Walida ba ciki bane wallahi, kwanakin nan wake baya zama a cikina. Rannan ma daga cin kosai sai amai"
"Ban gane ba ciki bane, gashi kince wake na saka ki amai. Kin gwada ne kinga babu?"
"Babu amfanin gwajin nasan babu"
Walida bata gaskata ta ba tace "kina tsarin iyali ne, me ya kaiki daga aure ki fara da bin tsarin nan na sai an gama amarci"
Asmau tace "kema kinsan bazan soma ba"
"To mene ne, Asmau kinsan dai zaki iya fada min. Ni na iya karanta miki nawa sirrin amma ke..."
Ganin bata ji dadi ba Asmau ta fada mata komai game da Col. Ishaq
"Wannan sirrinmu ne daga mu sai iyaye muka sani."
Sosai Walida taji tausayin Asmau. Su kuma kullum sai sun hadu da wani nau'i na jarabawa.
"Naji yar uwa kuma ba fahimta. Amma haihuwa ta Allah ce. Shi ya tabbatar bazai taba haihuwa bane? Ki gwada yin test a gida idan babu shikenan. Sai da kika fara aman ma na kula kinyi haske kin kara jiki. Da na zata duk na amarcin ne"
"Walida ina son haihuwa da Jikamshina amma shekarun da yayi a auren fari sun ishemu shaida. Kada ki saka min rai da abinda yayi min nisa"
Walida ta tashi ta dauki mayafi da purse dinta daga cikin jaka "kinga bari naje can wurin titi naga kamar akwai pharmacy. Zan siyo miki PT strip ki gwada. Idan babu komai ba sai ya sani ba"
Bata saurari wani batu daga Asmau ba ta fita. Wurin mintuna ashirin sai gata ta dawo tayi uban gumi. Tasha yawo domin inda ta zata pharmacy ne ba shi bane sai da aka kwatanta mata wani. Asmau ta dage bazata yi gwajin ba Walida ta ji haushi sosai. "Ko albarkacin tafiyar da nayi ai kya yi min kara ki gwada."
Da kyar da nuna bacin rai Asmau ta karbi tsinken gwajin guda biyu ta shiga bandaki. Bata fi minti uku ba Walida taji ta kwalla kara. A razane ta tashi tayi hanyar bandakin suka yi karo da Asmau da ta fito. Walida na cewa me ta faru ta rungumeta sosai sai kuma kuka da dariya a hade.
"Kin gani Walida *ciki* *cikin haihuwa* gareni. Wayyo Allah Jikamshina Allah Yana sane da bayinSa"
Wayarta ta tafi daukowa suna ta dariya ita da Walida. Har ta nemo sunansa zata kira Walida ta karbe wayar.
"Mutumin da ya kwashi shekaru yana neman haihuwa zaki fadawa kina da ciki a waya? Haba kawalli, ai yau ranarsa ce. Tashi zakiyi mu shiga kitchen ki hada masa special abinci mu sake gyara gidan nan. Idan da hali tambaye shi muje gidan kunshi naga naki ya kusa ficewa. Ana yi miki zanyi miki kitson barebari kanana"
Asmau tayi dariya tana shafa ciki. Wai cikin Jikamshinta ne a tare da ita. "Nayi girki sai dai na kara masa wani abin ko farfesu haka. Bari na tambayi kunshin"
Sai da tayi da gaske ta iya boyewa bata fada masa a waya ba. Bai hanata zuwa ba yace su je da Mal Sabo amma idan akwai layi sosai ta dawo gida baya son dawowa dinnan ya tarar bata nan. Cikin sauri sauri suka sake kimtsa gidan suka tafi.
Ana gama saka mata lallen Walida ta kama kanta tayi mata kitso. Shuku ne wani sabon style mai kyau da yake gashin nada cika sosai yayi mata kyau fuskarta ta kara fitowa. Sai da aka dauko Amatullah daga makaranta aka zo daukarsu. Har gida suka kai Walida Asmau tana ta yi mata godiya.
Suna zuwa gida tayiwa Amatullah wanka ta saka mata wasu kayan sannan ta barta a daki saboda zata kunna turaren wuta kada ya dameta. Tana gamawa taje ta bata lokaci wurin wanka da shiriyawa.
Karfe tara a gida tayiwa Col. Ishaq. Asmau da Amatullah suka taro shi tun daga bakin kofa. Binta yayi da kallo ya kasa dauke idonsa. Kullum tana masa kwalliya amm yau kam ba don Amatullah na wurin ba bai san me zaiyi ba. Tana rike da hannunsa suka tafi daki zata taimaka masa yayi wanka yace "Kamar na cinyeki Matar Jikamshi. Kinyi kyau da yawa"
Tayi murmushi "nagode amma ko zaka cinyeni ka bari ka fara cin abinci"
Kusan tura shi bandaki tayi don yaki tafiya sai tsokanarta yake. Da ya gama ya dawo falo inda ta zuba musu abinci a plate daya har Amatullah wanda hakan tsarinsa ne cin abincin dare tare. Suna ci yana kallon yadda take ta murmushi da fara'a ya ajiye cokalinsa yace "ki taimakeni ki fada min abinda yake ranki ya saka min ke cikin irin wannan farincikin."
"Sai mun gama cin abinci"
Ya kwabe fuska "bazan iya cigaba da cin abincin nan ba duk dadinsa. So nake kawai ki fada min. Tun dazu kin sa kwakwalwata ta tafi dogon bincike ta kasa samun amsa"
"Ka bari mu gama please"
Shi kam hakurinsa ya kare. Tun dazu yana kallo ko abincin kirki bata ci ba sai murmushi. Ya dan tabata ta kallo fuskarsa. A hankali yadda ita kadai zata ji yace "ko ki fada min yanzu ko mu kwashi kunya a gaban 'yarmu"
Asmau ta gane me yake nufi duk da tana tunanin bazai iya ba amma Jikamshinta bashi da tabbas. Tashi tayi ta tafi daki ya bi bayanta da sauri. Kafin ta rufe kofar taji ya rungumota suna kallon juna
"Rada min idan baki so dakin ya sani bazan fadawa Safina kinyi yada ba"
Tayi dariya sannan ta kai bakinta saitin kunnensa "Allah Yayi mana kyautar da har abada bazamu taba dena gode maSa ba, Jikamshina..."
Kasa fada tayi sai ta kama hannunsa ta dora akan cikinta "Akwai kyautar Allah a cikin nan"
Ya ware ido sosai yana jiran karin bayani "go on"
Rungume shi tayi saboda kunyarsa take ji sosai a wannan lokacin cikin kankanuwar murya tace *Alhamdulillah, I am pregnant*"
Karfin adduar da yake a lokacin ta hana zuciyarsa bugawa. A hankali ya zame jikinsa daga nata cikin matukar kadawar zuciya ya kalleta. Murmushi take har lokacin hakan ya tabbatar masa ba karya take ba. Ta kula da kaduwarsa tace "nima ban gaskata ba sai da nayi PT dazu. Kaga ikon Allah ko Jikamshina"
Bai iya cewa komai ba sai juya wa da yayi a sanyaye ya shiga toilet. Asmau tabi bayansa taji ya rufe da mukulli. Dama tasan wannan labarin ba karamin farinciki zai saka shi ba. Abu daya ne yazo kanta ko alwala zaiyi suyi nafila. Cikin sauri ta tafi nata dakin ta dauro alwala ta sako hijab ta dawo. Ko da ta shiga dakin toilet dinsa a bude yake amma baya nan.
Falo taje da abin sallah biyu a hannu nan ma bata same shi ba. Tana lekawa ta taga ta hango yana fitar da motarsa daga gidan. Ta koma ta zauna da murmushi, wato ya tafi fadawa Hajiya. Gara da bai nemi ta raka shi ba ai da taji kunya.
Shiru shiru har shadaya ta wuce bai dawo ba. Tana ta kiran wayarsa baya dauka sai daga baya ta ga wayar a daki.
Hankalinta ya soma tashi amma bata son kiran Bilkisu ko Hajiya ayi zaton ta kasa hakuri daga miji ya fita.
******
Tuki yake bashi da wurin zuwa. Zuciyarsa ce take zafi har gumi yana karyo masa. Me yasa Asmau zata yi masa haka, yana da tabbacin tana son shi da zuciya daya. Amma waye ya fada mata lallai sai ta haihu zai cigaba da sonta. Ya dade da karbar kaddararsa me yasa ta aure shi idan bazata iya hakurin zama dashi ba. Waye ya bata wannan muguwar shawarar. Waye yayi sanadin rushewar farincinkin da yake bakin kokarinsa wurin ganin ya tabbata a rayuwar aurensu. Gefen titi yayi parking saboda baya ganin gabansa sosai. Zazzafan hawaye ne ya cika masa ido har yake ganin duhu. Ajiye girmansa yayi da mukaminsa yayi kuka, kuka na bakinciki da bacin rai. Kukan rasa mafita ga halin da abar sonsa ta saka shi a ciki. Sai da ya gaji da zaman ya rinka karanto addu'o'in neman sauki sannan ya koma gida.
Asmau na zaune a falo a haka bacci ya dauketa. Zuciyarsa ta sake karaya da ya ganta rungume da abin sallah tana bacci ga Amatullah a kusa da ita. Dukawa yayi ya dauketa ya kaita nata dakin ya dawo ya tsaya yana kallon Asmau. Sai da ya daure zuciyarsa ya iya tabata ta bude ido a hankali. Magana taso yi ta kula da ja da kankacewar idanunsa.
"Tashi kije ki kwanta"
Bai bari tayi magana ba ya shige ya barta a wurin fuskarsa a daure cikin tsananin bacin rai. Yau da gobe tafi karfin wasa. Asmau ta fuskanci rayuwa irin wadda bata fatan wata mace ta gani. Yanayin da taga Jikamshinta ya sha bamban da abinda tayi tsammani. Wannan kadai ya bata amsar shirunsa da fitarsa daga gidan. _ZARGI_ irin wanda Allah Kadai Ya isa Ya wawarewa bawa. Sai dai abin mamaki gane hakan bai sata kuka ba. Ashe kuka wuri yake samu, ashe kuka rahma ne. Hannu tasa ta dafe kirjinta da taji yayi kamar an daure shi tamau ta kashe fitila da tv ta tafi daki.
Duhu ta gani alamun ya kwanta sai ta koma nata dakin ta sako kayan bacci ta dawo. Tana kwanciya ashe a kansa ne saboda ya raba gadon ba kamar yadda ya saba ba. Yau a tsakiya ya kwanta. Ji tayi yana kokarin matsawa tayi saurin tashi tana bashi hakuri amma bai amsa mata ba. Bata yi fushin ta bar masa dakinsa ba ta koma gefen gadon ta kwanta.
Sai karfe takwas saura mintuna ta tashi a makare. Wayam ta ga baya dakin. Ta fita da sauri motarsa bata cikin gidan. Jikinta yayi sanyi ta koma tayi sallah da ya saba tashinta idan zashi masallaci. Ta shiga dakin Amatullah ta tarar bata nan ga kayan baccinta a kan gado. Dan murmushi tayi ko babu komai bai dena kyautatawa 'yarta ba.
Haka Asmau ta yini ranar da kuncin zuciya. Duk bayan lokaci sai ta duba wayarta ko ya kira ko text amma babu ko daya. Haka ta ke zaunawa ta tsara masa kalamai masu ratsa zuciya ta tura masa. Idan ya gani a take yake gogewa. Sai yanzu yake nadamar auren Asmau yana mai nanatawa kansa tambaya daya *cikin jikinta na waye?*.
*****
Sati guda suka yi baya mata magana kuma baya shiga sabgarta. Ita kuma tayi alkawarin bazata takura shiba har Allah Ya sauketa lafiya. Daurewa take tana nunawa kamar babu abinda ya faru ta cigaba da yin abubuwan kyautata masa ko da bazai kula ba. Walida ta kirata taji yaya murnarsa da ta fada masa tana da ciki ta shirga mata karya don ta rufawa mijinta da kanta asiri.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽58
Batul Mamman💖
A daddafe take iya yin komai. Cikin da alama mai laulayi ne domin bata son warin komai ga yawan tashin zuciya. Rashin wadataccen abinci yasa ko aman yazo sai dai tayi wahalar banza babu komai a cikinta. Cikin dan lokaci ta fada. Babu wanda ta iya fadawa damuwarta sai Allah. Kullum sallah take da karatu tana mai tsananta addua da neman mafita. Idan ta damu da yawa ta kira Umma suyi hira taji sauki a ranta.
A nasa bangaren Col. Ishaq ba karamin jigata yayi ba da rashin Asmau. Sonta yana nan a ransa amma yana kyamar halin da ta jefa su a jiki. Har yau ya rasa matakin da zai dauka bayan fita harkarta da yayi. Gidan yayi musu zafi duk su biyun. Gado daya suke kwana ya juya mata baya. Haka zata yi bacci tana kallon bayansa tana hawaye.
Ranar asabar lokacin sun dauki sati uku a wannan yanayin tana fitowa daga kitchen shi kuma zai shiga daukan cup ya hada tea. Kallon kallo suke yiwa juna ta matsa ta bashi hanya. Yana shiga ya bugo kofar da kafarsa ashe hannunta na wurin kofar ta matse. Ciwo taji har tafin kafarta tayi kara cikin zafin nama ya bude kofar. Hannun ta rike sosai tana fitar da hawaye ta kasa tsayuwa wuri daya don azaba. Mantawa yayi da fushinsa da komai ya kama yatsun nata biyu da yaga ta rike ya shigar da ita kitchen ya sakar mata ruwa. Idonta a rufe tana kuka a hankali. Ciwon bai dameta ba kamar yadda Jikamshinta ya canja mata.
Har zuciyarsa yake jin kukan tana bashi tausayi sosai. Ya soma hura mata yatsun amma yana gani har sun fara kumbura. Fuskarta yake kallo itama yau bata kawar da nata idon ba ta zuba masa ido. Yadda ta rame shima haka ya rame. Yana rike da hannun ya kai yatsun nata bakinsa ya saka a ciki. Kallonsa kawai take tana kara sonsa duk da halin da suke ciki a lokacin. Kusan minti uku yatsunta na bakinsa sannan ya cire yace "kinji sauki ko nasa miki kankara"
Yaushe rabon da yayi mata magana. Ita da jin muryarsa sai dai idan waya yake. Girgiza kai tayi ta janye hannunta ta tafi. Wani iri yaji, yunwar ma ta fita a kansa sai rudani na rashin sanin yadda zaiyi da Asmau. Dakinta ya bita ya sameta zaune a kasa a kuryar gado tana kuka a hankali. Bai ce mata komai ba ya bude inda take ajiye mayafai ya dauko mata wani kato mai kauri. Tayar da ita yayi tsaya ya yafa mata sannan ya riko hannunta suka fito falo ya dauki mukullin motarsa.
Cigaba yayi da jan hannunta har gaban mota. Ya bude mata ta shiga ta zauna sannan ya cewa Mal Sabo idan ya dauko Amatullah ya kaita gidan Ismail. Sai ta kula ya mikawa Mal Sabon wata karamar jaka wadda take tunanin kayan Amatullah ne a ciki.
Da ya zauna ya tayar da motar Ismail din ya kira ya fada masa za'a kawo Safina kila ta kwana. Shi kuwa sai murna yace dama yana gida.
*****
Barrack dinsu suka je bangaren asibiti. Ita dai binsa take a baya har suka shiga ciki. Wani office ya shiga ya barta a reception. Ba dadewa ya fito yace ta shigo.
Hussaini ne a ciki sanye da kayan sojoji amma ya dora coat din likitoci.
"Ranki ya dade sai ki zauna a waje kuma? Sir kasan fa ita ce mai hadani da Walida ya kamata ka tayani kamfen"
Duk su biyun ya kula babu wanda dan guntun wasansa ya bawa dariya. Shima sai ya ci serious ya koma mazauninsa. Yasan yau abokin nasa a matsayin shugabansa ya shigo.
Col. Ishaq ya kamo hannunta da ya matse wanda yatsun sun kumbura faratan kuma sunyi jawur alamar taruwar jini daya har ya fashe ta saman farcen "Doctor a duba mata hannun nan bana so ya zama babban ciwo"
Hussaini ya kallo hannun sai ya dauki waya ya kira nurse aka zo suka tafi da Asmau yace ayi mata dressing. Bayan sun fita yace "ai yadda na ganku ne har naji tsoro ko anyi fadan masoya ashe amarya ciwo taji"
"Kaga ba batun wasa ina so duk wani test da akeyi a gano ciki kayi mata please"
Hussaini ya mike da sauri "Sir ciki??? Iko sai Allah, bashi da abokin tarayya. Lallai Allah maji rokon bayi."
Col Ishaq yayi masa wani irin kallo "me kake nufi ne? Kafi kowa sanin matsalata yanzu na fada maka zancen ciki kuma kana murna"
"Wannan ai abin farinciki ne da murna. Bari na fada musu ayi test din Allah Yasa akwai. Kai da kaina zanyi mata ma"
Ran Col. Ishaq ya soma baci yace "Hussaini bana son wasa. Kada ka manta banda dangina bani da wani amini sama da kai. Kai kadai na fadawa komai game da Asmau kafin na aureta. Sauran a gari suka ji idan har sun sani. After all these years aure kasa da shekara ko wata shida bamuyi ba tace min tana da ciki" muryarsa tayi rauni sosai dauriya ce kawai yake.
Zama Hussaini yayi a kujerar da take kallon ta Col. Ishaq hankakinsa a tashe.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Kada kace min zarginta kake yi. Col. Ishaq Jikamshi waye ya fada maka bazaka taba haihuwa ba? Na tabbatar ba ni bane"
Maganar ta fara daure masa kai yace "ku likitoci kun iya boyewa mutane zahirin abu sai kuyi ta rufa rufa don kada ku tsorata patient. Ka gwadani ka kuma hadani da likitocin da lalurata ta shafe su. Kowanne sai ya cemin lokaci ne baiyi ba. wane magani ne ban sha ba. Sai gashi Badar ta haihu daga yin aure. Wannan ya tabbatar min ni nake da matsalar. Nine bana haihuwa "
Hussaini ya jima yana kallon abokinsa kafin yayi magana "idan ni ko wasu a nan zamu boye maka idan bazaka taba haihuwa ba, asibitocin da kaje a kasashen waje kasan bazasu yi maka karya ba. Babu wanda ya kai bature baro baro. Sai ya fada maka nan da lokaci kaza zaka mutu. Duk wani sakamakonka kana bani copy na ajiye. Babu inda akace bazaka taba haihuwa ba. Dukkansu suna cewa ko dai akwai matsala a mahaifar Badariyya ko kuma wani dalili dai ya hana cikin samuwa amma ba rashin lafiya gareku ba."
Col. Ishaq ji yayi ya fara jin zafi. Me Hussaini yake nufi. Wai zai iya haihuwa???.
Hussaini ya cigaba "idan wasu zasu boye maka ni bazan bari kayi ta kashe kudi kamar baka san zafin nema ba akan haihuwa alhalin nasan bazaka samu ba. Garin yaya ka yankewa kanka wannan shawarar har kake zargin matarka. Allah Sarki shiyasa naga ta kasa magana da kuka shigo. Bani da masaniya game da Asmau bayan abinda ka fada min amma bana jin zata aikata wannan mummunan aikin gareka. Kada ka manta taga rayuwa a dalilin kuskuren farko. Wallahi ni ka kara tsoratani akan zina. Idan har zaka zargeta duk son da kake mata lallai har a nade duniya fentin zina bazai taba barin Asmau ba. Ya Allah Ka nesantamu daga wannan bala'i "
Jikin Col. Ishaq ya gama sanyi kam yanzu. A lokacin da Asmau tayi masa albishir da samun karuwa a lokacin tarihin rayuwarta ta baya ya dawo masa har yake tunanin ko a garuruwan da ta zauna ta cigaba da mugun aiki. Tashi yayi da sauri Hussaini ya dakatar dashi "ka jira nayi mata gwaji a tabbatar"
Zama yayi amma jinsa yake a kan kaya. So yake ya ga Matar Jikamshi a jikin Jikamshinta. Wani irin sonta yake ji na daban yana ratsa shi. Gabadaya yaji ya tsani kansa da zuciyarsa da ta raya masa wannan mummunan zargi..
Tana zaune an saka mata bandeji a yatsun Hussaini ya shigo dakin da suke. Nurse ya bawa umarni ta debi jininta nan da nan ya karba ya tafi lab dinsu. Da kansa yayi gwajin har sau biyu ya tabbatar babu karya Asmau tana da ciki. Dawowa yayi yayi mata tambayoyi wanda tana amsawa tana hawaye. Yaji tausayinta sosai sannan suka koma office dinsa.
Ko da suka shiga kunya ce ta kama Col. Ishaq ya kasa yi mata magana. Hussaini yana murmushi yace "congrats Sir, uwargida tana da ciki wata na uku kenan. Zan bata appointment idan tazo sai a bata maganunguna ayi scanning domin ganin lafiyar baby. Allah Ya inganta Ya raba lafiya."
Col. Ishaq kamar yayi me don murna. Yana cewa Amin ita kuwa Asmau ta fita daga office din saboda kukan da yazo mata. A bakin mota ya sameta bayan Hussaini ya nanata masa lallai yayi kokarin shawo kanta saboda yayi mata laifi.
Sun shiga mota sun zauna bata ko kalli inda yake ba. Shiru suka yi yaja motar sai gidan Hajiya. Ta goge idonta sannan tabi bayansa suka shiga ciki. Hajiyan na daki tana kashingide ya shiga da sallama.
Ta tashi zaune tana amsawa. Asmau ta tsaya a bakin kofa kawai sai ji tayi ya kama hannunta ya ja har gaban gadon Hajiya. Kunya kuwa daga ita har Hajiyan. Zama yayi a kusa da ita a kasa sai ta fashe da kuka Hajiya tace "lafiyarku kuwa, me kayi mata"
Baya son kukan Asmau haka kuma baya son bacin ranta wanda shine ya haddasa mata. Kansa a sunkuye yace "Hajiya daga asibiti muke yanzu, tana da ciki wata biyu"
*Alhamdulillah....* Hajiya ta fada sai kawai ta rungumo Asmau jikinta. Abin mamaki kuka ta saka Asmau na tayata.
"Waye yace babu Allah? Allah sarkin dukkan mai sarauta. Ubangijin Annabi Adamu tsira da AmincinKa ya kara tabbata ga Annabi Muhammadu SAW. Ban taba fitar da rai da zaka ga jininka ba Ishaq. Allah Ya amsa min, Allah nagode. Sai dai bawa yaga jinkiri wanda komai daren dadewa zamu kwashi ladan hakurinmu a duniya ko a lahira. Allah Yayi miki albarka Ya raba lafiya"
Duk duniya babu matan da yake so sama da Hajiyarsa da matarsa. Yau Hajiya harda kiran sunansa don murna. Gasu a gabansa suna kuka. Hajiya ta dago kan Asmau tana kallo "ba abin kuka bane Asmau. Ki godewa Allah"
Col. Ishaq yace "Hajiya nayi mata laifi. Ko kallonta na kasa yi shiyasa na kawota wurinki"
Ai kuwa yasha harara a wurin Haj Lubabatu.
"Asmau me yayi miki? A wannan yanayin har
zaka bata mata rai"
Muryarta har ta dashe da kuka tace "ba laifinsa bane Hajiya. Laifina ne, kuskurena ne, da ban biyewa zuciyata da shaidan ba hakan bazata faru ba"
"Don Allah kuyi min bayani. Me kayi mata nace?"
Asmau ce ta kuma yin magana don ya kasa dago kansa "bakin fentin da nayiwa kaina bazai taba wankuwa ba ko me zanyi a duniya. Allah ne kadai shaida akan tuban bayinSa. Ban taba yi muku karya ba wallahi sau daya tsautsayi ya fada min. Da banyi cikin shege ba...."
Toshe mata baki yayi da hannu ya hanata karasa magana a gaban Hajiyarsa yana kokarin rungumeta. Hawaye ne da baisan daga ina ba suke zarya a kumatunsa.
Hajiya da kanta ta sa hannu ta janye Asmau ranta yayi masifar baci. Ita rashin kunyar tasa ma yau bata gani ba. Cikin fushi tace "hala cewa kayi ba cikinka bane?"
Bazaiyi mata karya ba ya gyada kai. Kowa a gaban mahaifiyarsa yaro ne. Tsawa tayi masa sosai abinda ya bawa Asmau tsoro.
"Shekarunka da iliminka sun tashi a banza. Kuma ka bani kunya ashe son da kake ikirarin yi mata yana da iyaka. Idan bata yafe maka ba zargin nan kasan cewa zaka hadu da fushin.... "
Asmau ta kara fashewa da kuka ganin yadda mijinta abin sonta yake hawaye kamar karamin yaro ana yi masa fada bayan bashi da laifi "A'a Hajiya kiyi hakuri wallahi ba laifinsa bane. Laifina ne da na zubar da mutuncina a waje." Ta juya tana kallonsa shima ita yake kallo "ni nace ban yafe maka bane da ka kawo kanka kara, ko fushi banyi da kai ba. Don Allah ka dena kuka Jikamshina"
"Da gaske kin yafe min Matar Jikamshi?" Ya fada yana dago hannu zai share mata hawaye. Ta gyada kai tana murmushi.
Haj Lubabatu taji dadi sosai, wannan so da suke yiwa juna daga Allah ne. Gani tayi za'a fara rashin kunya a gabanta kamar sun manta tana wurin Col. Ishaq ya gama matsowa kusa da Asmau sai tayi gyaran murya ta sake hade rai.
"Dan bamu wuri zanyi mata magana"
Sai da ta maimaita ya tashi ya fita daga shi har Asmau suna kallon juna. Bayan ya fita Hajiya tace "Asmau kafin nace komai ina rokonki alfarma don Allah kada Haj Bara'atu taji zancen nan. Ko kadan bazata ji dadi ba. Sannan ina so ki kara hakuri da kaddara. Kamar yadda kika fada duk matar da ta taba aikata kuskure har wani namijin ya kusanceta to wallahi har abada lokaci zuwa lokaci akwai sanda zargi ko yaya zai darsu a zuciyar wadanda suke tare da ita. Zaki ga kinyi abin bajinta da burgewa amma karshe tuhumarki za'ayi. Kada ki rabe dayan biyun yaron nan yana sonki. Kiyi hakuri da halin da zakiyi ta tsintar kanki a ciki saboda abinda ya faru a baya"
Murmushi Asmau tayi "ko kadan banji haushinsa ba. Kukana nadama ce akan abinda nayi a baya. Na tabbatar ba don haka ba Allah kadai Yasan farincikin da zaiyi tun farko. Da wata yake aure wadda bata da tabo irin nawa zaiji dadi mara misaltuwa. Ni kuwa dole ne yaji tsoron ko ba nasa bane musamman da ya gama yarda bazai haihu ba"
Hajiya tace "shi kadai ya yankewa kansa wannan hukuncin babu ruwan likitoci. Badariyya ta haihu saboda rabonta na can shima gashi Allah Ya bashi nashi. Allah Yayi muku albarka." Ta kallo kofa "Sai ka shigo tunda ka koyi labe kaima"
Asmau ta kallo wurin kofa sai gashi Jikamshinta ya shigo. Ko tun yaushe yake wurin bata sani ba. Maganganunsu da Hajiya sun kara sashi jin bai kyautawa Asmau ba. Dole yayi kokari wurin mantar da ita kuncin da ya dasa mata.
Hajiya tace "sai ka tafi gida ita a nan zata kwana. Asmau me zan dafa miki?"
Asmau tace "Hajiya don Allah ki zauna bana jin yunwa"
"Dole kici abinci duk kin rame. Kai kuma me kake jira ka tafi mana."
Asmau na kallo ko motsi yaki yi. Hajiya ta fita daga dakin don take takensa rashin kunyar da ta rasa inda suka gado ta yake neman yi. Kitchen ta tafi tana tunanin me zata dafawa Asmau taci. Baiwar Allah duk ta rame. Shima kuma ya fada kamar bashi ba.
Yana dena jin takun Hajiya ya daga Asmau yana juyi da ita "I love you so much Matar Jikamshi. Ki yafe min kinji"
Zata yi dariya saboda yau zuciyarta a wanke take yace "kada kiyi dariya ko so kike Hajiya taji tace baki da kunya"
"Kai da ka daukeni a tsakar dakinta ai ka fini rashin kunyar"
Ya sauketa "bari nayi miki a hankali saboda baby na. Amma fa idan Hajiya bata bari mun tafi gidanmu ba to za'ayiwa babyn nan kani ko kanwa a gidanta"
Murmushi tayi na jindadi Jikamshinta ya dawo. Shi kuma ya janyota yana bin fuskarta da kiss ko ta ina.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽59
Batul Mamman💖
Jin taku kamar na Hajiya yasa Col. Ishaq ya sauke Asmau. Gani yake kamar a da can ba sonta yake ba saboda yadda yake jinta a ransa yanzu. Ita din ma shi take kallo cike da so. Bata da abinda zata saka masa dashi face addua da kuma tsantsar kulawa irin wadda ta dace da miji.
A haka suna wannan kallon kallon da murmushi a fuskokinsu Hajiya ta karaso dakin tace ya wuce gida ya daukowa Asmau kaya kamar na sati daya. Ramarta tayi yawa tana so ta zauna har ta mayar da jikinta. A take murmushin dake fuskar Col. Ishaq ya bace. Asmau ta gimtse dariya don da gaske ya bata rai. Hajiya ta saka shi a gaba suka fita tare. Bata kyale shi ba sai da taga ya shiga motarsa ya tayar.
Suna fita Asmau ta kwashe da dariya. Tsakaninta da Allah itama tana kewar mijinta. Amma yanayinsa ne yasa tayi dariya don tasan akwai rigima a gaba. Yana iya cewa me yasa da Hajiya tace zata kwana bata nuna bata so ba.
Har ya isa gida tunanin yadda zaiyi da Hajiyarsa yake. Ko don bata san yaushe rabonsa da su yiwa juna kallon kirki bane shi da Asmau. Yau da ta kasance ranar farinciki sosai garesu, sun shirya ga kuma babbar kyauta shine zata hanasu celebrating. Shawarar da yasan zata fishshe shi ya yanke sannan ya koma gidan.
*****
Tuwon masara Haj Lubabatu tayi da miyar kuka wadda taji naman rago da wake. Tana yi zuciyarta fes ciki da farinciki. Ba karamin tausayin Ishaq take ba gashi dama ance mahakurci mawadaci. Ta san irin yadda rashin haihuwa ya dame shi sosai. A dalilin hakan babu irin bacin ran da bai gani ba saboda yana da sa abu a rai. Ko yaya aka fadi maganar haihuwa mai kama da gori sai ka gani a fuskarsa.
Duk yadda Asmau taso taya Hajiya aiki hanata tayi tace ta koma daki ta kwanta. Yadda take ji da ita da cikin jikinta ai bazata yi sake wani abu ya faru ba duk da komai na Allah ne. Da Bilkisu ta dawo daga makaranta ne ma ta tayata har suka karasa. A falo suka zauna su ukun suna hira Bilkisu ce mai yin fiye da rabin zancen. Hajiya ta sa ta zubawa Asmau tuwo mai yawa tace kuma sai ta cinye. Zuwa lokacin hankalinta ya fara tafiya ga inda Jikamshinta ya tsaya gashi har anyi isha bai dawo ba kuma wayarta tana gida. Haka ta rinka cin tuwon a hankali sai taji sallamarsa. Wani sanyi taji ya ratsata amma ta basar ta cigaba da cin abinci tana kallon plate a dole bata so ta kalle shi kada Hajiya ta gani.
Wata jaka ce yar madaidaiciya ya shigo da ita mai dauke da kaya. Bilkisu ta gaishe shi sannan ta karbi jakar ta kai dakin Hajiya kamar yadda ta bata umarni. Hajiyan ma tashi tayi
"Bari naje nayi sallah duk kunyi kun barni. Ki tabbatar kin cinye tuwon nan kafin na dawo. Kai kuma sai da safe nasan kila kafin na idar ka tafi"
Col. Ishay yace "to Hajiya Allah Ya bamu alhairi" a ladabce
Tana tafiya ya dauke plate din gaban Asmau sannan yaja hannunta. Ta bude baki zata yi magana taji ina zai kaita ya marairaice fuska "please Matar Jikamshi magana zamuyi kafin Hajiya ta fito"
"A ina?" Ta tambayeshi tana waigen kofa. Bai bata amsa ba ya ja hannunta suka bi wani korido suka je wani daki. Dakin a share yake kamar ana kwana sai dai ko ba'a fada mata ba ta gane dakinsa ne na da kafin aurensu. Bakin gado ya zaunar da ita ya janyo kujera irin ta aiki a gaban wani tebur gabanta ya zauna shima
"Har abinci kike iya ci tun dazu baki ganni ba amma ko a jikinki"
"Allah Sarki Jikamshina kalli ka gani kadan naci saboda na rasa inda ka tsaya gashi babu waya a hannuna"
Murmushi yayi mata yana kara godewa Allah wai Asma'unsa ciki gareta.
"Yanzu dai ki bani abincin nan yunwa nake ji. Amma gaskiya bazan yarda ki rinka bawa baby na tuwo ba."
Ta dan sha kunu cikin wasa "sai na fadawa Hajiya kuma ka tashi ka tafi gida kada dare ya kara yi"
Wani kallo yayi mata mai nuni da zancenta wasa ne "babu inda zani, ke yanzu sai ki kwana a nan ba tare dani ba?"
Ta girgiza kai "da Hajiya tace kayan sati sai da zuciyata tayi tsalle.....amma na murna"
"Zakiyi bayani ne. Ni dai bani abinci naci."
Da hannun ta rinka bashi itama tana ci. Sunyi kusan minti shabiyar saboda cin tuwon ma wani sabon salo ake masa. Idan ta bashi sai ya lashe mata yatsu ko ya cijeta. Tayi ihunta a hankali tace zata rama sannan su cigaba. Bayan sun gama ta wanke hannu a bandakin dake cikin dakin shima yazo suna kuskure baki don brush dinta yana cikin jaka. Ya rike fuskarta da hannuwansa yana shirin kissing dinta suka ji kamar muryar Hajiya.
Nan da nan Asmau ta rude ta rasa yadda zatayi. Shima uban gayyar yau dai ya rasa abinyi don kuwa duk abin sa Hajiyarsa yana jin kunyarta. Idon Asmau harda hawaye da taji Hajiya tana tambayar Bilkisu ina ta shiga daga cikin korido din. Taku kadan zasu kara su iso dakin. Duka ta kaiwa Col. Ishaq a kirji
"Duk laifinka ne da ka jawo ni dakin nan. Yanzu da wane ido zan fita don Allah"
"Kinji ki da wani zance, ba fa daukoki nayi ba da kafarki kika taho ke dadi miji. Ai da sai ki fada min ba dadewa zatayi a dakin ba"
"Yanzu laifina kake gani, ba a gabanka tace mana sallah zata yi ba." Sosai ta gama rudewa.
Col. Ishaq ma dai ya rasa mafita don bai san yadda zaiyi ba idan Hajiya ta bude kofar dakin nan.
Ganin sunyi tsuru ga Bilkisu tana ta kiranta yasa ta saddakar kawai. Gara ta fita da tayi ta zama tana tsoron su bude ayi zaton wani abin ma suke yi. Bude baki tayi tace "Haji..."
Yayi maza ya toshe bakin da hannunsa yana magana a daidai kunnenta duk ya riketa saboda tana kokarin kwacewa "tona mana asiri zakiyi kuma"
Ta soma cizon hannunsa yana runtse ido yau ba na wasan da ta saba bane da gaske mai zafi take masa.
"Matar Jikamshi zan rama kuma kada ma kiyi tunanin zan hakura idan kika fara wannan hawayen karyan"
Tana ji ya saketa bayan takun su Hajiya ya bar wurin ya soma tsokanarta "kunyar karya ma kike yi, kin gama saita baki zakiyi kissing Jikamshinki shine daga jin muryar Hajiya kika wani rude bayan kinfi kowa sannin a gidanta kike"
Duk yadda suke dashi har yanzu wani abin idan yayi ko ya fada sai taji kunya. Ta rufe idonta tayi hanyar kofa batare da ta amsa masa maganarsa ta farko ba tace "sai da safe"
Ai kuwa ya rikota yana bata hakuri kada ta fita yanzu.
Bayan dan lokaci kadan ya fita wai zai duba mata idan Hajiya ta kwanta sai taje ta kwanta kawai itama. Jinsa kawai take amma da wane ido zata kalli Hajiyan da safe.
Shigarsa falon ke da wuya ta fito ya sunkuyar da kansa kasa. Yi tayi kamar bata gane me yake ba tace "kaje dakina ka dauko jakar Asmau ka kai mata ko akwai abinda take bukata. Kuma ka rufe gidan. Sai da safe" daga nan ta juya ta koma ciki. Yafi minti uku a tsaye sai da ta sake kiransa tana cewa zata rufe kofar dakinta idan bai zo ya dauka ba. Ya shiga kamar salihin gaske ya dauko ya fita. Hajiya tayi murmushi kawai. Yaran zamani sai addua. Basa kunyar idon manya idan suna son juna.
*****
Asmau na kai kawo a tsakar dakin ya shigo da jaka yana murmushi. Bai zata Hajiya zatayi saurin barinsa da Asmau ba amma dama niyarsa ya kwana a gidan don nasa kayan na mota. Idan ta ga yaki tafiya yasan zata barsu su koma nasu gidan.
"Bukatarki ta biya Hajiya tace ki kwana a nan."
Ta zaro ido "da gaske? Jikamshina ka gama dani. Daga yau bazan kara fita daga dakin nan ba. Ranar da zan tafi ma sai Hajiya bata nan zan fito"
Ya soma dariya "ke dai kinji dadi kawai. Bari naje na dauko nawa kayan dama da shiri nazo. Ki kunna mana heather sai muyi wanka duk zafi ya isheni."
Harara ta wurga masa ya fice yana mata dariya. Da ya dawo duk suka yi wanka ta haye wata doguwar kujera da yake kwanciya ya huta da. Yace ta dawo gadon ta noke kafada "da kunya fa, Hajiya na gidan nan na kwanta kusa da kai"
Tasowa yayi daga gadon ya dawo ya hau kujerar ya matseta a karshe don tayi musu kadan. Cikinta ya shafa yana lumshe idanu "duk yadda kike so haka za'ayi, iyaka dai gobe muce ba kwanan gado muka yi ba na kujera ne"
Hannu ta kai zata tureshi ya sureta gabadaya sai kan gadon yana fada mata irin yadda yayi kewarta.
******
Washegari da kyar ta iya tashi ta shirya cikin wani riga da zani na atampa. Jikamshi yana makale da ita a dakin kamar zata gudu. Motsi kadan sai ya hau shafa mata ciki. Ita kuwa idonta na kan agogo tana tunanin fita daga dakin su gamu da Hajiya. Kai hatta Bilkisu ma kunyarta take ji. Ganin duk ta damu yasa yaje ya duba Hajiya tana daki ya fadawa pAsmau. Da sauri ta fita taje falo ta zauna dama bata so kowa yaga fitowarta daga dakinsa. Da Hajiya ta fito tana kallon Asmau ta kula da bala'in kunyar dake tattare da ita. Shima ya fito lokacin banda murmushi da kallo da yake bin Asmau dashi babu abinda yake. Sunyi breakfast Asmau duk a takure gaban surukar da ta gama ganin rashin kunyarsu. Hajiya tace "idan kun gama sai ku tafi gida saboda Safina ko. Zan sa a nemo miki mai tayaki aiki idan ba'a samu ba sai Bilkisu ta dawo nan wurinku saboda ta taimaka miki"
Suka yi shiru kawunansu a kasa. Zancen su tafi gidan ne yasa su jin kunya. Wato taga abin nasu ba mai karewa bane gara su koma gidansu. Zancen Bilkisu kuwa cewa yayi gara a samu mai aikin saboda baya son a bar Hajiya ita kadai. Bilkisun ce kawai a gabanta yanzu.
Suna sallar azahar suka fito Hajiya ta zuba mata abinci wai ya ishesu har dare kada tayi girki. Sai godiya take da yiwa wannan dattijuwa addua da fatan alkhairi. Yaushe zata manta da ranar da suka fara haduwa wanda tun lokacin Haj Lubabatu take kyautata mata gashi bata kyamaci aurenta da danta ba.
Tayi tunanin gida zasu wuce sai taga yayi hanyar Hotoro. Dadi kuwa ya kamata sai murna zata ga Umma. Lokacin da ya dena mata magana tana ta kewar mahaifiyarta amma ta kasa fada masa zata gida. Ya lura da murnarta har ya tsokaneta ko a nan ma zasu kwana ne su sake yiwa baby kani ko kanwa. Murmushi tayi, Jikamshi bashi da dama.
Umma da Hajjo sunyi murna da zuwansu sosai. Sai da Umma ta lura da ramarta to a gaban idon suruki sai ta kasa tambayarta me yake damunta. Tsoronta kada ya zamana gori ake mata tasa abin a rai. Don kuwa bayan sun dawo daga Yankari sunje Jikamshi inda wasu cikin 'yan uwansa mata suka fada mata magana son ransu. Sun ji amsa kuwa daidai dasu daga bakin Jikamshin Asmau. Ranar tasha kuka sosai da kansa ya kira Umma yace ta tayashi rarrashinta.
Ido irin na manya Hajjo tace "ya naga kina wani kyalli ne Asmau ga 'yar rama kinyi. Nasan dai kina tare da wannan sojan ba kewarmu kike ba"
Col. Ishaq da Umma suka yi murmushi ita kuma Asmau ta fada kan Hajjo tana dariya.
Tana fadawa ya tashi da sauri don ya manta Umman na wurin yace "wane irin ganganci ne haka don Allah kiyi hankali da jikinki"
Kunya ta kamata da su Umma suka soma kallonta. Hajjo tace "Ishaq ko dai abinda nake zargi ne? Naki fada ne dai ko ba hakan bane na tayar muku da hankali"
Asmau ta tashi ta fita daga dakin da gudu. Umma ma kunyar taji sai kace wata 'yar fari ta tashi ta bar dakin. Hajjo tace "Alhamdulillah kaga ikon Allah. Allah Ya kara hada kanku Ya kareku daga sharrin makiya da mahassada" idonta fal hawaye yana cewa amin tana addua.
A dakin Umma Asmau ji tayi Umman ta shigo ta rungumeta. Hawayen farinciki take itama "Alhamdulillah ala kulli hal. Kinga yadda Allah Ya dubi zukatanku da taimakon da kuka yi niyar yiwa juna Ya baku abinda zai kara inganta zamanku. Amma dama ba cewa akayi bazai taba haihuwa ba?"
Asmau tana nata hawayen ta labartawa Umma bayanin da yace likita yayi masa ba tare da ta fadi matsalar da suka fuskanta ba a dalilin cikin. Tasha addua a bakin Ummanta. Sannan tace duk abinda take so ta fada mata. Dole ne su taya Col. Ishaq tattalin abinda yafi so a rayuwarsa. A nan suka yi sallar laasar sannan suka wuce gida. Kulawa kam Asmau tana gani a wurin Jikamshinta sai godiyar Allah.
*****
Tana zaune a dakin da suke girki duk hayaki ya bude ta taji sallama. Mai sallamar yayi ta yi ta tashi rai a bace ga bakincikin itacen yaki kamawa ga takaicin lokacin girkin na kurewa yanzu fitsararriyar yarinyar nan zata zo ta sakata a gaba da rashin kunya. Fuska a daure ta bude karamin gate din tana kallon mutanen su biyu.
"Don jaraba kuyi ta sallama kamar kuna bin mutane bashi. Me kuke nema?"
Daya cikinsu yace "ina Gidado?"
Tana ta harare harare tace "kana magana da Zinaru ne uwar Gidado."
Dayan ya bata wata takarda "gashi daga Hajiya Zulaiha lallai ku tashi daga gidan nan da sati biyu ko a hadaku da hukuma"
Zinaru ta soma raba idanu. Abinda da ake gudu ya faru. Idan suka tashi ina zasu je. Yadda ta tsani rayuwar kauyensu ta dauko tilon danta ta gudo yanzu ana neman a mayar da ita duk tsahon shekarun nan. Sakin fuska tayi harda murmushi
"Ku dena ambaton Haj Zulaiha nasan bazata koremu ba. Wasu ne dai suke neman shiga tsakaninmu. Hala baku da labari Gidado mijinta ne har yau. Ai ba rabuwa suka yi ba. Sabani ne irin na masoya"
Wanda ya bata takardar yace "kinga ki bashi sakon nan. Lallai ne ya aiko mata da takardarta kuma ku bar gidan nan. Idan ba haka ba zaku ji sammaci daga kotu"
Zinaru na kallo suka tafi tace "shegu masu karawa wuta fetur."
Ciki ta koma ta tarar da Amarya tsaye a wurin girkin tana ta wani jijjiga jiki tana bata rai. Zinaru ta shigo ta dan rakube a gefen bango. Amarya tace "yanzu ko wutar baki hada ba bare ki dama min kunun. Idan cikin nan ya zube kwarankwatsa dubu sai na fadawa Baba ya karbe shagon da ya bawa Gidado. Ku haka kuke rayuwa ne shi malalaci ke kuma sai dai aci banza. Anjima kadan zani gida ni na gaji da wannan auren miji babu abinda ya iya sai bacci da shaye shaye"
Gaban Zinaru ya fadi. Yanzu dan shagon da Baban Amarya ya basu Gidado ke kasa gwanjo a kasuwa idan ya ga damar fita idan suka rasa shi ai tasu ta kare. Tun yaushe suka cinye jarin kayan miyarta shiyasa bata fita sai aikin Amarya da dan cikinta.
Tana dogon tunanin sai ga baban Amarya. Dama da wuya yayi kwana uku bai zo ba. Ita kadai ce 'yarsa yake ji da ita kamar rai. Zinaru tayi wuki wuki don bashi da mutumci ko kadan. Ko sallamarsa bata gama amsawa ba ya banko kai cikin gidan. Don abin kunya harda kai gwiwa kasa tana gaishe shi saboda ta girme shi ya amsa yana shan kamshi.
"Ina shi yaron nan yake? Yau kwana biyu bai bude shago ba. Idan baya so ne sai na bawa wani ko na bayar haya"
Amarya ta kwabe fuska "dama yaushe zai zo Baba. Bashi da aiki fa sai na shaye shaye tun jiya bai san inda kansa yake ba. Ga amai ya kwara a dakin"
Babanta ya dafe kirji "ince ko ba ke kike gyara wurin ba idan yayi amai"
Tayi kwalkwal da idanu "waye zai gyara idan banyi ba. Yanzu ma itace nake so ya siyo min wani saboda wannan yayi danshi yau da marmarin kunu na tashi. Amma yaki fitowa"
Zinaru sai bude baki take amma ta ma kasa magana don mamakin karyar da Amarya ke gillawa.
Ran Garbebe ya baci sosai. Yadda yake son yarsa shiyasa tana cewa Gidado take so ya amince. Yanzu ga ciki burinsa ta haihu ya sami jika. Ya dallawa Zinaru harara sannan ya fara kwalawa Gidado kira. Mutumin banza haka ya fito daga shi sai wani kodadden wando duk jirwaye.
Garbebe yace "na gaji da wannan rashin kirkin naku. Kaje ka kwashe gwanjonka daga shagona. Ke kuma Zinaru idan jikan ne baki so ki fada ba sai kunyi mata horon yunwa ba. Daga yau bazata kara aikin amai ba don ba baiwarku bace"
Gidado yace "uwar tawa kake fadawa magana haka?"
Zinaru ta kwabe shi cikin harshen fulatanci "kyaleni dasu ka koma daki. Takarda aka kawo daga wurin uwar yaranka nasan bazasu yarda ta kuma zama da kai ba. Amma na sami dillali zan biya shi ya taimaka mu sayar da gidannan ko babu takardu. Ita kuma wannan kazar matsiyatan ka bari mu karbi kudin gidan sai ka saketa itama su karata ita da uban nata. Har yanzu da kyaunka Gidado baza mu rasa 'yar masu kudin da zaka iya aura ba"
Shiru Gidado yayi da yaji zancen saki tsakaninsa da Zulaiha. Yara har shida tsakaninsu dole yaji yana sonta duk irin halinsa kuwa.
Garbebe ya ja hannun Amarya suka yi wajen kofar gidan yace "shegun nan basu san mu fulani bane hala"
Amarya tace "basa yin yaren a gidan shiyasa bana yi musu. Basu san na iya ba"
Garbebe ya tafa hannuwa "karen bana ke maganin zomon bana. Kyaleni dasu ki koma amma ki fara shiri gaskiya aurenku ya kare. Ya ma kika ce sunan baban matarsa ta fari?"
Amarya ta fada masa ya kwashi kafa sai gidan su Zulaiha.
*****
Qasim da Ma'u ke hira a bangaren da ake ajiye motoci tana cewa ya shigo ciki yaci abinci saboda ya kwaso hanya. Innarsu ce tace ta kirashi ma amma yaki amincewa wai gara ta kawo masa nan.
"Kai har ka fini kunya ma"
Qasim yace "haka kike gani ko, nan da wata uku ne zaki gane waye Qasim"
Ma'u tayi dariya "har kasa mana ranar ne?"
"Nan da sati biyu za'a kawo kudi da sa rana. ni dai nace wata biyu za'a saka daga nan sai ki fara shirin komawa Zamfara"
Tayi murmushi "Allah Ya tabbatar mana da alkhairi"
Hayaniya suka ji daga bakin gate karshe dai maigadi yazo ya fada mata wani ke neman Alhaji tace baya nan bari taje ta gani. Qasim ya daure fuska "ina zaune zaki je bakin gate ganin wanda ba'a sani ba. Muje tare dai just incase na gida ne."
Ma'u ta mike suka tafi. Mutumin dai basu sanshi ba amma sun fahimci labarin da ya kawo musu na cewa Zinaru zata sayar da gidan Zulaiha. Ma'u tace bari ta fada a cikin gida. Tare da Zulaihan suka fito. Tana ganinsa ta gane shi, lokacin da take tare da Gidado har dashi ake mata wulakanci kala kala wai shi mai 'ya. Yanzu kuwa russunawa yayi yana diban gaisuwa kafin ya sake mata bayanin abinda ya kawo shi. Zulaiha tayi masa godiya tace babu komai hukuma zata shiga zancen tana nuna Qasim. Garbebe ya dan tsaya yana jiran ihsani ladan kawo gulma yaga babu wanda yayi motsi cikinsu sai ya tafi kawai. Ko ba komai ya tarewa Zinaru hanyar samu.
Yana fita wata mota hadaddiya ta shigo gidan. Wani mutum ne a bayan motar dreba na jansa. Maigadi yana ta daga hannu saboda Alh Najib akwai kyauta. Kusa da inda Qasim, Ma'u da Zulaiha ke tsaye suna zancen hali irin na Gidado da Zinaru akayi parking motar ya fito. Da fara'asa ya mikawa Qasim hannu suka gaisa sannan ya gaisa da Ma'u da Zulaiha wadda ta kasa kallonsa ma.
Ciki ya shiga yace Alhaji na hanya zai jira shi ne. Bayan ya wuce Zulaiha ta tafi jikinta babu kwari. Ma'u tace "wannan Alhaji yaso aura mata fa taki yarda tun farko. Anti Zulaiha tayi masa wulakanci sosai gashi yanzu tana kunyarsa."
Qasim yace "rabon haihuwa yasa ta auri wancan. Kuma gara haka akan ta haifesu a titi. Tunda ba yau zan tafi ba sai ki fadawa Alhaji in shiga case din Gidadon nan"
"Ai kuwa zaiyi murna. Bari ya dawo anjima sai na fada masa".
*****
Cikin kwanaki biyu Zinaru da Gidado sun tattara komai nasu zasu bar gidan sannan yayi mata saki daya. Tayi ta rokon Zulaiha wai ko albarkacin yara ta yafe musu a mayar da auren. Ko kallon kirki basu samu ba daga gareta balle yan uwanta. Da kwanan titi gara na kauye a dole tayi shirin komaa garinsu wane kauye a cikin Taraba state. Bats sani ba mijinta da ta baro yana da rai ko ya mutu. Alhajin su Zulaiha yace lallai wasu daga cikin yayyenta maza su bi bayansu aga tushensu albarkacin yara.
Zinaru an sha kuka ga Amarya ma Garbebe ya karbar mata takardar saki. Su Humaira ko a jikinsu saboda irin mugun zaman da suka yi a hannun kakarsu da Babansu wanda bai san kowa ba sai kansa. Ganin idon Qasim ne ma yasa yabi Zinaru a son ransa ko a karkashin gada ya kwana indai zai sami ganyensa ya busa.
Alh Najib kuwa tunda yaji anyi saki ya sanar da Alhaji idan Zulaiha ta gama idda a fada mata har yanzu yana sonta. Yana da mata dai da yara hudu. Banda auren wuri shekarunta goma sha shida ta auri Gidado ko secondary bata gama ba.
*****
Sati biyu a tsakani aka taho nemawa Qasim auren Ma'u harda Col. Ishaq Jikamshi cikin tawagar su Alh Adamu. Wannan abu yayi dadi domin rashin auren Asmau bai sa sun kullaci juna ba. Daga zuwa kawo kudi Alhaji yace indai sun amince a kawo sadaki kawai a daura aure kada ayi ta wahalar da mutane. Haka kuwa akayi aka saka biki da tariya wata guda. Col. Ishaq ne ya kira Qasim da wannan albishir. Yayi murna sosai shikenan shima ya shiga sahun magidanta. Innarsa kuwa kamar tayi me don dadi. Allah Ya taumaketa danta yayi aure kuma ya auro yar mutumci irin wadda take so.
*****
Zuwa yanzu kowa yasan da cikin Asmau a cikin 'yan uwanta da nasa. Kulawa take samu ta kowane bangare kada Mami taji labari. Sosai take kaunarta yanzu.
Saura sati biyu bikin Qasim tana ta shirin zuwa Jos yana kallonta kawai. Ciki wata hudu ga laulayin da take fama amma ta dage da roko har da addua akan ya barta taje ko don Zulaiha. Sun gama rigimarsu yana ta shan kunu Amatullah tace masa tayi masa tuni zai kaita siyan takalmin makaranta na gudu. Da kyar ya yarda suka tafi da Asmau. A hanya aka shirya dama basa dogon fushi da juna. Sun gama siyayyarsu suna fitowa daidai inda suka ajiye mota suka hadu da wasu maza su biyu cikin shiga ta kamala kayansu ma iri daya. Daya ne ya kura mata ido har Col. Ishaq ya lura zaiyi masa magana Asmau ta kallesu. Baki ta bude cike da tsantsar mamaki.
"Annur, Gaddafi?"
ABINDA AKE GUDU🙆🏽60
Batul Mamman💖
Annur ya soma murmushi haka ma Gaddafi sannan yace "Antinmu wallahi da farko ban tabbatar kece ba. Alhamdulillah, Allah Ya kaddara zamu sake haduwa"
Gaddafi yace "an kusa shekara bakwai fa idan ma ba'ayi ba"
Asmau sai murmushi take da ta sake haduwa da 'yan samarin da suka taimaka mata lokacin da take nakudar Amatullah. Bata jin zata taba manta kammaninsu duk da a wancan lokacin suna tare da kuruciya sosai bata tunanin zasu kai shekara sha takwas ma. Jikamshinta ta kalla zata yi masa bayaninsu yace "kina fadan sunansu na gane ko su waye" shima fuskarsa da fara'a. Duk wanda ya taba taimakon Matarsa yana ganinsa da kima da daraja. Sannan bashi da mantuwar sunaye indai a tarihin rayuwarta ne.
Hannu ya mika musu suka gaisa yace shine mijinta. Fuskokinsu sun nuna jindadin wannan labari sosai. Col. Ishaq yace "ku shiga kuyi siyayyarku sai muje ku ga gidanmu saboda a cigaba da zumunci."
"Ai kuma mun fasa zamu dawo wani lokacin." Annur ne yayi maganar yana kallon Amatullah da alamar tambaya amma dai yayi shiru. Tasu motar suka shiga suka bi bayansu Asmau.
Col. Ishaq na tuki ta riko hannunsa daya tana murmushi.
"Nagode da ka gayyato su gida. Bani da abinda zan saka musu dashi da irin taimakon da suka yi min amma yadda ka karrama su kadai yasa naji dadi sosai."
Yayi mata murmushi "Matar Jikamshi, kin hadu da mutane da dama a rayuwarki wanda banda tsohuwar nan ta Azare kowanne cikinsu ya taka wata muhimmiyar rawa wurin nesanta rayuwarki daga lalacewa. Duk wanda ya taimakeki ni ya taimakawa dole na kyautata musu nima"
Tsohuwar da ya fada ta gane da Uwargida yake tayi 'yar dariya "Uwargida fa ta shiryu Jikamshina"
"Wani suna naji ta kiraki dashi shine raina ya baci."
Bata rai yayi sosai Asmau ta rinka dariya. Itama ta tsani wannan sunan wai 'Yar Dabas. Tuna mata yake da zamanta a gidan da irin bakar wuyar da ta sha. Tana dariya yana kallon bakinta ya dan sassauta murya "I miss you"
"Gani a kusa da kai fa"
"Ba ke ba wadannan lips din nake nufi"
Ta danyi fari da ido yace "nagode Allah da Ya bani ke Matar Jikamshi. Komai naki ina so, har da wannan fari da idon"
Kamar wadda aka jeho sai jin muryar Amatullah sukayi a tsakaninsu tana daga bayan mota tace "Babana inyi maka fayi da ido nima na iya"
Shiru suka yi duk su biyun. Saboda tana ta aikin gwada sabon takalminta sun manta tana motar ma. Ta sake maimaita tambayar yace "Princess ba kyau ayi fari da ido"
Ta turo baki "Amma kacewa Ummi kana so tayi"
Tohhh yarinya zata kure babanta. Asmau kyalesu tayi don tasan halin Amatullah yanzu ta rinka jan zancen da wata sabuwar tambayar kenan.
Sake tunani yayi sannan yace mata "baki ji abinda na fada bane sosai, cewa nayi akwai abu a saman idonta ina so tayi fari da idon sai ya fadi"
Amatullah ta koma ta zauna tana cewa "auuu ashe banji ba. Amma dai na iya fayin inyi maka?"
Rike dariyarsa yayi yace mata ta bari su je gida yanzu tuki yake yi. Shi da Asmau suka hada ido suka yi murmushi. Dole ne su rinka kiyaye abinda suke yi a gaban Amatullah don wayo ne da ita. Sai kaga kamar bata kula da abu ba sai zance ya tashi ta maido dashi.
Kyakkyawar tarba suka yiwa su Gaddafi. A nan suke bata labarin yadda rayuwarsu ta canja bayan haduwa da ita da suka yi harda komawarsu asibiti nemanta. A yanzu basu dade da dawowa daga Jami'ar Madinah ba inda sukayi degree. Asmau taji dadi da ta kasance silar shiriya garesu. Sunyi hira sosai da Col. Ishaq aka nuna musu Amatullah a matsayin yarinyar da ta haifa. Da zasu tafi duk su biyun sunyi mata alkhairi na kudi wanda su Asmau suka nuna rashin amincewarsu. Gaddafi yace sun dauketa kamar 'yarsu ne don Allah kada a mayar da hannun kyauta baya.
Haka su rabu cikin mutunta juna har nambobinsu na waya Col. Ishaq ya karba.
A hanyarsu ta komawa shagon ne Annur ya cewa Gaddafi "gaskiya mijin Antinmu yana da kirki sosai. Kuma ko ba'a fada ba ba karamin so yake mata ba. Yarinyar nan Amatullah nake tausayi. Nan gaba zata ji babu dadi idan ta gane yadda aka haifeta. Aure wannan sai kaga yazo da matsala saboda bata da uba"
Gaddafi yana tuki yace "haka ne amma komai na Allah ne. Gashi cikin ikonsa mamanta ma tayi aure. Nifa saboda labarinta kasan na gama tsorata da harkar mata. Haka kawai shaidan ya gifta tsakaninmu na nazo na mutu na bar 'yar mutane da ciki. Idan ban tuba ba me zan fadawa Allah"
"Shiyasa hakan da muke zaune yafiye min komai, idan mun tashi aure sai mu nema ya zamana babu wannan doguwar soyayyar ayi komai idan anyi auren"
Dariya Gaddafi yayi "nifa na sami wata sai munje gida zan baka labari. Ban riga na fada mata ba sai munyi shawara da kai"
Annur yayi dariya "na dade da gano ku ai, jira nake naji yadda za'ayi abin ban sani ba. Ba Noor kake so ba?"
Mamaki ne ya bayyana a kan fuskar Gaddafi. Tabbas kanwar abokinsa yake so amma ko ita bata sani ba. Annur ya bashi goyon baya sosai yace ai yana kula da yadda baya iya boye son nata idan ya ganta.
"Kai kuma wa ka samo mana?"
"Kaji lokacin da Amatullah tace min Uncle Annuy? Daga lokacin na kudurtawa zuciyata ita zan jira. Yadda Col. Ishaq ya wankewa Antinmu bacin rai na rayuwa haka nake fatan nayi mata nan gaba"
Gaddafi yana tuki yana dariya "haba dai Annur kayi mata tsufa wallahi. Shekararka kusan ashirin da biyar fa. Ka bari ta sami yaro daidai ita"
Annur ya shafa kansa yana murmushi "idan na sami mata yanzu zanyi aure ko don kare mutuncina amma zancen yarinyar nan ka bari kawai, lokaci ne kawai zai nuna mana"
*****
Bikin Qasim ya matso sai da Hajiya ta shiga zancen Col. Ishaq ya yarda Asmau taje. Dama makaranta ma ya roketa alfarmar ta bari sai wata shekarar bayan ta haihu. A gidan Mami zasu sauka harda Bilkisu da Amatullah zasu tafi. Su Umma suma zasu je da Mama. Sunyi mota biyu lokacin Yassar yazo hutu daga NDA inda Col. Ishaq ya sama masa yana yin short service. Shine zai tuka motarsu Asmau shi kuma dreban gidan Mama Yalwa ya tuka su ita da Umma da Shemau.
Ranar da zasu tafi Asmau kamar bazata fito daga gida ba. Jikamshi ya makale mata sai mita yake zata tafi ta barshi. Ga dokoki ya kafa na kula da ciki. Ba don sai an kawo amarya Qasim ya shirya dinner a cikin Kano ba ai da binsu zaiyi ma. Sun rabu ana kewar juna suka je suka shiga mota.
Yassar ta kula baya magana sosai a motar har tana tsokanarsa ko sababbin sojoji basa magana ne. Bai ce komai ba sai Bilkisu da ta sha kunu a gaban mota tace "Anti Asmau ko zaki tambayar min su Umma na koma motarsu"
"Wani abin ne ya faru kike son canja wurin zama?"
Shiru tayi sai kuma ta soma hawaye. Nan da nan hankalin Asmau yayi mugun tashi. Shi kuwa Yassar hannunsa rawa ya soma yi ya sami gefen hanya yayi parking din motar. Asmau tana ta tambayar me akayi mata sai ji tayi Yassar yace "Bilkisu"
Ta dago kai idanunta sun kumbura sunyi jawur.
"Idan ba cewa zakayi kana sona ba ka rabu dani. Allah zai bani wani"
Asmau ta hangame baki cike da mamaki. Rashin kunya a gaban masoyi ta yarda gadon gidansu Jikamshi ne. Anya Bilkisu bata manta tana bayan motar ba. Allah Yasa ma Amatullah tayi bacci.
Yassar yace "kema kinsan ina sonki don Allah ki share hawayen kinga a hanya muke"
Ta murguda masa baki "a haka ne kana sona tunda ka tafi ba waya ba text sai na gaji na nemeka. Kuma kaki fadawa kowa balle a fara shirin bikinmu sai iya zuwa bikin wasu"
Asmau ta shiga tafa hannu a hankali tace "Bilkisu kwantar da hankalinki naji komai muna dawowa in sha Allah magana zata je gaba kinji ko. Kinsan Yassar din ne akwai tsoron mata"
Dora hannu Bilkisu tayi a kanta tare da jan mayafi ta rufe fuska. Wallahi ta manta da Asmau a motar. Haushi Yassar dinta ya bata tun bikin su Asmau da ta samu yace yana sonta bai kara waiwayenta ba.
A nasa bangaren shima wata matsananciyar kunya yaji. Ko Bilkisun ba don baya sonta yake kin nemanta ba. Shi bai san me zai rinka fada mata ba a waya ko text. Shiru suka yi su biyun Yassar ya tayar da mota Asmau tana ta dariya. Abu yayi dadi zumunci zai kara kulluwa tsakaninsu. Tsabar murna a lokacin ta turawa Jikamshi text tana fada masa. Shi dinma ya nuna farincikinsa sosai yace sai sun dawo. Bilkisu dai har aka isa Jos bebiyar dole ta zama.
Ansha biki Zulaiha ta sake bawa Asmau labarin yadda suka kare dasu Zinaru dama ta sanar da ita a waya. Asmau tace ina ma tana wurin ta ga idanun Zinaru mai son kudin tsiya. Daga nan suka koma hirar cikin Asmau da kuma Alh Najib da yake jiran Zulaiha ta gama iddah. Ita dai tace bata da ra'ayin aure tasha wahala a wancan ga yara har shida waye zai dauketa tare dasu. Shawara Asmau ta bata kada ta bari dama ta kubuce mata wurin yiwa babanta biyayya.
Ranar Asabar da sassafe suka dauko amarya suka taho Kano da ita. Washegari akayi dinner sannan aka wuce da ita Shanono inda zatayi sati sannan su tafi Zamfara da angonta.
Ranar da suka dawo Col. Ishaq kamar ya cinye Asmau. Kwanaki uku kawai ji yake kamar ya dade sosai basa tare. Itama tayi kewarsa domin kuwa duk kulawar da take samu bata kai tasa ba.
*****
Cikinta na da wata shida ya fara siyayyar kayan baby. Wani lokacin yaje da ita wani lokacin kuwa sai dai taga ya shigo da kaya. Tun daga gadon yara (cot), kayan sawa da duk wani abin amfani ya tanada. Ita har gajiya tayi da cewa ya barsu haka. Mutum mai shekarunsa zaiyi haihuwar fari sai dai a zuba ido.
Wata rana ya dawo daga aiki a gajiye yake fada mata ta hada kaya jibi zasu tafi Port Harcout an tura shi aiki na wata daya. Amatullah sun fara hutu sai a kaita gidan Umma kafin su dawo. Asmau ta zauna ta hada musu kaya washegari suka kai Amatullah gidan Umma sannan suka je yiwa Hajiya sallama.
Tunda ya fara bayanin abinda ya kawo su Hajiya ta dakatar dashi.
"Babu inda zaka je min da ita da wannan cikin. Wa kuke dashi a can da zaka kaita cikin arna ka ajiye. Idan haihuwa tazo yaya zaku yi?"
Yace "Hajiya akwai musulmai kuma da sauran lokacin haihuwar har maje mu dawo"
"Kasan Allah babu inda zata je. Ko dai ka fasa tafiyar ko kuma ita ta zauna a nan ko can hotoro. Wannan karon ba kyaleka zanyi ba irin yadda ka tabayi min har na bari kuka koma gida"
Asmau kanta na kasa Col. Ishaq yaki shiru don ba karamar cuta bace gareshi tafiyar wata daya babu matarsa. Hajiya ta dage harda kiran Umma. Itama Umman tace abinda ta gani kenan da suka kai mata Amatullah sai dai batayi magana ba. Hajiya tace ta gama magana shawara na garesu. Jiki babu kwari suka tafi gida.
Asmau tayi ta bashi baki akan yayi hakuri ya dena nuna bacin rai amma ya kasa.
"Matar Jikamshi wata daya ba sati bane. Ta yaya zanyi kwanakin nan ni kadai bayan na riga na saba da yin komai tare dake"
Idonta na shirin zubo da hawaye tace "kayi hakuri kaima kasan abinda ta fada domin amfaninmu ne. Bazaka iya fasa tafiyar ba? Wallahi bana son kayi min nisa"
Kuka ta soma yi ya rungumeta "bani da yadda zanyi ne. Umarni ne daga sama"
A ranar ko kadan basuyi bacci ba sai aikin rarrashin juna. Tayi ta masa kuka har muryarta ta dashe. Bayan ya dawo daga sallar asuba ya hada mata kaya a wani akwatin. Ko abincin kirki sun kasa ci haka suka fita ya kaita gidan Umma ya wuce office. Daga nan dreba ya kaisu airport su hudu suka tafi. Harda Hussaini wanda idan sun dawo za'ayi bikinsa da Walida.
Sai da ya kusa sati sannan ta warware ta dena zaman daki. Umma tayi dariya kawai. Safe, rana da dare aiki yana yi masa sauki sai waya. Kafin su kwanta kullum sai anyi video call yana kallonta da cikinta da kuma princess dinsa.
****
Kwanci tashi saura kwana biyu ya dawo gida. Ita da Sabira suka je ta tayata gyaran gidan domin tayi nauyi sosai. Harda kitso da kunshi Jikamshi zai dawo. Ranar da zai dawo kuwa karfe tara na safe ta gama shiri zata tafi gida. Umma ta rinka ja mata rai tana dariya a ranta yadda Asmau take ta kallon agogo. Sai goma da rabi ta fito ta ajiyeta a gida ta wuce office. Amatullah tana gidan Nasiba tana karasa hutunta.
Karfe daya taji motarsa ta bude kofa da sauri. Col. Ishaq ya tsaya yana kallonta. Ciki yayi girma sosai. Ita ma shi take kallo har wani jiki ya danyi ta fasa rungumeshi taja da baya. Rufe kofa yayi yana binta "haba Matar Jikamshi kada kiyi min rowar kanki. A tausayawa bawan Allah"
"Shine kayi kiba duk da baka gani na ko"
Ya janyota yana murmushi "yau 'yan rigimar suna kusa ne? Bayan wata daya not even a kiss sai korafi zan samu. Bari na koma tunda bakiyi murnar dawowata ba"
Kin sakinsa tayi ta rungumeshi sosai tana kuka "bazaka kara tafiya irin wannan ka barni ba. Kullum da kyar nake bacci"
Yayi kissing dinta yana kallon fuskarta "na sani my sweet Asmau. In sha Allah next time kafata kafarki."
Daki suka je zai shiga wanka yaga tana dan runtse ido ya tambayeta ko meye tace kafarta ce ta dan rike. Ranar sallah kawai ke fitar dashi daga gida. Kowa yana kokarin nunawa dayan irin yadda yayi kewarsa. Makale suke da juna kamar ranar aka kawo masa ita. A haka kuma tana ta dan jin ciwo daga mararta zuwa baya amma tana cijewa don tasan akwai wurin sati uku kafin lokacin haihuwarta.
Cikin dare suna bacci taji ciwon ba mai daukewa bane ta tashi ta fita a hankali. Ita kadai take ta kai kawo a falo ciwo yana ta gaba gaba har taji tafiya tana neman gagararta. Da jan kafa ta dawo dakin ta zauna a bakin gado. Sai da ta zauna ta fara cewa "Jikamshina" ta kira sau uku yana baccinsa. Wani ciwo taji sosai bata san lokacin da tace
"ISHAQ" da karfi ba.
Tashi yayi ya rasa daga ina take kiransa. Ciwo yayi ciwo ta sake cewa Ishaq, fitila ya kunna ya ganta a bakin gado sai gumi take. Ya rude sosai yace me kike yi a nan.
Tambayar ma haushi ta bata ta cije dai tace "nakuda nake"
Rigarsa ya nema ya saka ya fara neman mukullin mota. Ciwo na cinta tace "Jikamshina bazan iya tashi ba. Haihuwar ta matso. Ka dauko sabuwar reza a waccan drawer din"
Ya zaro idanu a tsorace "inyi me da reza?"
Tana wash wash tace "yanke cibiya"
A take jikinsa ya fara rawa.
"Kiyi hakuri na kaiki asibiti don Allah kada ki haihu a gabana wallahi bazan iya gani ba suma zanyi. Ko ta awaki bana son gani" yadda yake maganar kasan a tsorace yake sosai.
Durkushe yake a gabanta ta daure ta rike masa hannu "Jikamshina kafin muje asibiti ko wani yazo zan iya haihuwa. Ka daure ka duba min ko baka son baby din"
Jikinsa a sanyaye yace "ina so"
Wani nishin ciwon ta gama sannan tace ya dauko rezar. Yaje ya dauko ya dawo gabanta ya zauna tare da mike kafafu. Yana zama yaga ruwa yana fito mata ya dago kai a razane.
"Ruwan jikinki zai kare don Allah ki bari na kira ko Hussaini ne"
Jin bata amsa ba ya dan dago "Asmau kina jina"
Idonta a rufe ta gyada kai "faya ce ta fashe kada ka damu"
Yana kallon yadda take famam cije lebe tausayinta ya kama shi. Babu inda baya rawa a jikinsa idonsa a rufe yake ya fito da reza sai kyalli take amma bai san me ma zaiyi da ita ba. Sai da tace ya bude idonsa ya rinka gani ta kusa haihuwa.
Budewar yayi ya juya gefe tare da rike mata kafa yana ta faman cewa "push Matar Jikamshi, push, yauwa gashi nan kin kusa ko? Push, push nasan zaki iya"
Ji tayi kamar ta haure shi da kafarta don takaici. Wai push ga uban ciwo gashi ya kasa yi mata abin kirki. Sake cewa push yayi ta ce cikin bacin rai
"Idan ka sake cewa push wallahi zan haureka"
"Au toh, bansan ba'a fada ba. Naji haka akeyi a tv. Yanzu me kike so?"
Gumin fuskarta ya goge mata sannan tace "addua zaka rinka yi min kuma *ka bude ido ka kalli yadda baby zai fito* kada a sami matsala"
Ya rinka gyada kai tana magana. Ita ke fama da ciwon kuma ita ke fada masa yadda zaiyi. Daga lokacin addua ya rinka karanto mata itama tana yi. Can yaji ta fara nishi ya sake cewa push ai kuwa ta kai masa hauri da kafa. Ji tayi ta tsani kalmar gabadaya. Yana kallo kan baby ya fara fitowa sai ji tayi ya fara kiran sallah. A yanayin da take ciki babu halin dariya. Da yaga abin na gaske ne yace "na shiga uku in hade miki kafarki kada kiji ciwo."
"Kashemu zakayi ne? Ka tara hannu kada ya fado a kasa" Ta fada da kyar.
Yace "toh, ita rezar ina zan yanka miki?"
Tunani tayi kada yayi mata karin da bata shirya masa ba tace "ajiyeta a gefe tukunna" wai tana wannan yanayin yake damunta haka.
Ya ajiye ya mika hannu ya cigaba da kiran sallah tana nishi har Allah Ya taimaketa baby ya fito tare da mahaifa sai kukansa taji. Da jinin da komai Col. Ishaq ya rungume dansa yana hawayen farinciki. Asmau nuna masa yadda zai yanke cibiya sannan ta mayar da kai ta dan kwanta tana mayar da numfashi.
Da dan rungume a jikinsa ya zagayo ya rungumeta sunyi kace kace dasu.
"Allah Yayi miki albarka Asmau. Allah Ya sakawa iyayenmu da alkhairi"
Baby din ya bata yana ta canyara kuka ya dauki wayarsa lokacin biyar da rabi ya kira Hajiyarsa. Cikin bacci ta farka ganin mai wayar ta tashi a gigice. Tana dauka ta jiyo kukan jariri. Col. Ishaq yace "Hajiya mun haihu"
Bakinta ya kasa rufuwa don murna tace "kun haihu ko ta haihu"
Yana ta murmushi yana kallon Asmau da dansu yace "wallahi tare muka yi komai muna gida. Saura wankan ne ban iya ba"
Hajiya ko tambayar me aka haifa bata yi ba ta tashi cikin sauri ta tafi dakin Bilkisu ta tayar da ita tace ta kira mata Dahiru shine gidansa yafi kusa da nata yazo ya kaita gidansu Asmau. Da yazo suna hanya tana addua Allah Yasa haihuwar babu matsala.
Ai kuwa sun sha kallo don da dansa a kafada yazo ya bude musu kofa lokacin an fara kiran asuba. Hajiya tayi saurin karbar baby din tace maza yaje yayi wanka. Ko da ta shiga kitchen ya dora ruwa a manyan tukwane biyu akan gas cooker.
Wurin da Asmau ta haihu ya gyara shi tas ya dauke kafet din ya fito dashi waje. Hajiya ta yaba masa duk da bata fada ba. Asmau ta gani tana dauko robar wankan baby. Tana jin muryar Hajiya kunya ta kamata. Hajiya tace Bilkisu ta juyo mata ruwan tayi wanka ita kuma zata yiwa baby. Anjima kuma da kanta zata yiwa maijego.
Kafin takwas na safe Asmau maijego da jaririnta sunyi fes. Col. Ishaq kuwa baki har kunne. Tare da Hajiya suka je asibiti aka yi mata allurai aka basu magani suka dawo gida. Lokacin su Umma suka zo gida ya cika da yan uwa.
Col. Ishaq shima jegon yake don kuwa daki ya shige yana baccin gajiya saboda irin aikin karbar haihuwa da yayi.
Shi da 'yan uwansa sun nunawa Asmau gata sosai. Amatullah an dawo gida sai murna tayi kani. Kayan barka lodi guda su Mami suka kai gidansu Asmau.
Ranar suna aka shirya walima gagaruma aka ci aka sha yaro yaci suna Abdallah. Su Zulaiha, Rashida, Zubaida, Walida da Ma'u matar Qasim sun sha hidima.
Daren ranar Asmau tayi wanka ta fito ta sami su Ainau suna ta hade mata kayan barkan da ta samu. Hawaye ne ya ciko mata Shemau tace " zaki fara ko."
"Amatullah nake tunani, lokacin da na haifeta babu mai kaunarta. Ita nata uban ma bai san da ita ba har ya koma ga Allah. Ko pant bata dashi sai da Allah Ya hadamu da Zulaiha ta bata kayan Ali. Bazan taba mantawa da bambancin dan zina da dan aure ba. Allah Ya yafe mana" sai kuka yaci karfinta. Su Shemau sunji tausayinsa suka rinka bata baki.
Washegari Col. Ishaw yace tazo ta ga wani abu a waje. Mota ce mai kyau ya siya mata. Bata san lokacin da ta rungumeshi a wurin ba don murna.
*****
Duk abinda miji zaiyiwa mata Col. Ishaq yana wadata Asmau dashi. Ta bangaren yara kuwa duk yadda yake matukar son Abdallah hakan bai hana shi cigaba da nuna tsantsar kulawa ga Amatullah ba. Asmau bata taba ganin wani abu daga gare shi da zai sa taji ya ware Amatullah saboda ba tasa bace ko kuma yanayin haihuwarta. Shiyasa a kullum bata gajiya wurin saka shi a adduarta.
Abdallah na da wata uku Yassar ya dawo daga short service dinsa ya dage shi fa aure yake so. Ga ginin da Umma take yi masa da saura amma haka ya hada har da nasa 'yan kudin kafin aiki ya kankama. Bilkisu ta kunno shi sosai akan maganar aure kuma ya zama irinta. Dama zama dasu Jikamshi sai an koyi hali. Iyaye dai sunyi murna kuma an saka rana.
Bikin Walida ma ya tashi su Asmau sunyi rawar gani. Sai da aka gama ta fara shirin makaranta an gama komai. Jikamshi ya cika alkawari bai hanata ba. Yarinya ta samu suke tafiya tare tana rike mata Abdallah idan zata shiga aji. Yana da wata tara amma da girmansa ga kamaninsa da babansa kamar yayi kaki. A haka ne wata rana ta tashi da safe da amai ko makaranta ta kasa zuwa. Gwajin farko ta gane ciki ne. Murna a wurin Col. Ishaq kamar cikin farko. Yayi ta tattalin matarsa. Dole ta yaye Abdallah ga karatu. A haka tayi ta fama har ta haifi 'yarta mace wannan karon a asibiti. Yarinya taci sunan Hajiya wato Lubabatu amma suna kiranta Amaturrahman.
*Bayan shekara uku*
Asmau ce tsaye a kofar dakin yaranta suna bacci. Amatullah da Amaturrahman akan gado suna rungume da juna. Shakuwarsu har ta baci. Saboda Amatullah bata iya fadin sunan kanwarta sosai itama idan an tambayeta sunanta sai tace Amatuyyahman. Duk yadda mutum yaso gyarawa sai tace ba haka Yaya take fada ba. Abdallah yana kwance a kan nasa gadon ga kayan wasa sun baza.
Hannuwan Jikamshinta taji ya rungumeta ta baya tare da dora kansa a kafadarta. A daidai kunnenta yake magana
"Tunanin me kike yi Matar Jikamshi?"
Kwantowa ta sake yi a jikinsa tace "ina godiya ga Allah akan ni'imarSa gareni."
Hannunta yaja suka tafi dakinsa ya tura kofar da kafa. Yana juyowa yaga tana hawaye.
"Allah nagode Maka baki da aiki sai kuka. Ni kaina daga haduwarmu zuwa yanzu sau nawa kina sani kukan nan. Yau kuma me ya faru?"
"Ina tsoron ranar da yaran nan zasu tsaneni. Gara gara ma su Abdallah amma Amatullah sai taji ina ma bani bace mahaifiyarta. Me zan fada musu a lokacin da suka kara wayo mutane suka sanar da su mamansu ta taba ciki a waje? Ya zanyi da Amatullah idan ta tuhumeni da gurbata mata asali? Idan suka kyamaceni yaya zanyi da rayuwata?"
Kuka take yi da gaske. Kwantar da ita Jikamshi yayi ya kwanta kusa da ita kanta yana kan kirjinsa.
"Daga ranar da kika ji rasuwar Abubakar da batun cikinki kin taba tunanin zaki kara samun nutsuwa a rayuwarki?"
"A'a"
"To a yanzu Allah Ya kyautata miki rayuwa ko kuwa?"
"Ya kyautata min"
"Ina so ki sani cewa tunanin gaban da baki gani ba babu alkhairi a ciki. *Abinda ake gudu* ya riga ya faru. Adduarmu shine Allah Ya kara karemu daga sharrin shaidan da mukarrabansa. Yara kuma da kike tunani bazasu taba guje miki ba da izinin Allah. Ke dai kiyi iya yinki wurin basu tarbiya da nuna musu so irin na uwa, sauran kuma mu barwa Allah. A karshe Matar Jikamshi, Asma'un Ishaq ina mai kara shaida miki idan duniya zata gujeki in sha Allah bazan taba rabuwa dake ba. Kece Ishaq, Ishaq kuma Asmau. I love you with all my being"
Kara rungumeshi tayi sosai tana hawayen farinciki "I love you too Jikamshina. Allah Ya barmu tare"
Suka ce Amin a tare.
*****************
*ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH*
Ina godiya ga Allah da Ya bani ikon gama wannan labari. Ina fata Allah Yasa mu amfana da abinda yake cikinsa wanda yake daidai. Kuskuren dake ciki Allah Ya yafe min Ya kawar da hankulanmu daga aiki dashi. Allah Ya karemu daga abinda ake gudu.
Godiya mai tarin yawa gareku masoya wannan labari. Hakika kun cancanci yabo domin kun bani kwarin gwiwa sosai. Bazan kama suna ba domin kuwa kuna da yawa kada nayi abinda ake gudu na manta da wasu. Allah Ya saka muku da alkhairi.
*Gaisuwa gareku* matan
1.Batul Mamman novel grp
2. Yan uwa na Fikrah writers association.
3. Taskira
4. Rufaida Omar fans
5. Maryam Ameen novels
6. Tafeesu novels
7. RAZ novella
8. Zauren Biebee Isah
9. Feenat Jaafar novels
10. Mss MJay novels
11. Hausa novels only
12. Hausa novels xallah
13. Zauren karatu
14. Fairytopia novels
15. Rash kardam novels
16. Queen Meemi fans
18. Fati Ali novels
19. N,N $ Z novels
Da wadanda ban saka ba duk ina godiya da mika sakon gaisuwa.