Iya karfinta ta rike faruq, amman inaga faruq ya mance waye agaban shi, dan hankadata yake da iyakan karfin shi"
Da taimakon bashir suka samu suka tsaida shi, banda kerma babu abinda jikin shi keyi"
Dan haka anty ta saka kuka, ganin inda anty ke hawaye hankalin shi ya dawo jikinshi, cikin sanyin jiki ya zame daga rukon da bashir ya mishi ya tsuguna agabanta "
Idonshi ya bude akanta tsorata tayi ganin inda idon yayi kamar jini ya kwanta, har yanzun yana gabanta saidai bakinshi ya kasa cewa komai"
Zuwa can ya fara sauke ajiyan zuciya"
Itama anty cigaba tayi da kukanta bata da nigar saurarawa"
Bashi na gefensu ya rungume hannuwan shi"
Zuwa can faruq ya bude baki hankali yace, Anty dan Allah kidaina kukan nan, karya jawo miki wata matsalan"
Kamar jira anty take cikin kuka tace, au daman kasan kuka ka iya jawowa mutun matsala?, Yaro?, daman kasan kuka illah ce ajikin dan adam?, amman kake cutar da baiwar Allah shekara da shekaru ka kasa gane kukan ka iya jawo mata illah? Aiho Ashe babu dadi? toh bari kaji ciwon 'ya mace na 'ya mace ne, akullum ka kuntatawa naziya jinake kamar ni ka kintatawa, yanzun baka tunanin nan gaba ayiwa yarka,? danme zaka dinga azabtar da yariya?
Shiru falon yayi illah sheshshekar kukan anty dake tashi shiko faruq hawaye ne suka fara zobo mishi"
Anty ce taci gaba da cewa toh indai inada daraja a idonka ban amince kakai hannunka jikin naziya dasunan duka ba, idan kuma sontane bakayi toh ka sauwake mata, dan wulahkancin ya isa haka"
Har yanzun kansa na kasa ya kasa dagowa ya kalli anty zuwa can ya share zufan daya keto mishi sannan yace"
Toh yanzun anty kina nufin naziya ta daki banza kenan?, nihilah fah ta daka, wlh anty sotayi ma takashe min ita, saboda bakin kishinta na jaraba' bayan kafin na fita saida naroketa tayi hakuri da nihilah har zowa sanda zatai hankali, danme zata biye mata"
Cikin tuhuma Anty tace, yaro Anya kuwa giyar da kasha ada bata juyar maka da tunani ba, kodai har yanzun kana Shane?
Da saurinshi ya girgiza kai tare da fadin ni babu wani abun da nake sha anty"
Toh inason zan tambaye ka kuma ka gaya min abin da ke zuciyarka tsakanin ka da Allah, waishin ita naziya babu ko digon sontane azuciyar ka?
Gabanshi yaji ya fadi dan be taba zatan irin wannan tambayan daga gurin anty ba, tabbas bazai iya bude baki yace beson naziya ba dan iya zaman shi da ita ya fahimci mutun ce ita me sanyin hali, dan haka bazai iya tattace son naziya yake ko kuma shakuwa ce kawai tazama gurin daya, shidai yasan yanason nihilah"
Muryan anty ce ta katse mishi tunanin da cewa dakai fah nake mgn"
Zabura yayi da sauri sannan ya bude baki cikin rudewa yace"
Anty ni bansani ba ko Ina son ta"
Cike da haushi anty ta kalli shi dan zuwa yanzun ta fara gajiya da halin shi jitayi kaman ta gunduma mishi zagi amman saita daure"
Shiko bashir murmushi yayi azuciyar shi yace munafuki, nasan maganin ka"
Shiru sukayi zuwacan anty tace toh shikenan tunda kace baka sani ba, na baka sati 1 kaje kayi tunani idan har baka sonta ta zuwa nan da sati 1 ka kawomin takkadanta, Allah ya hada kowa da rabonsa"
Cikin sauri bashir yace yauwa anty inaga hakan ma yafi, murmushi yayi sannan yace anty idan hakan ya faru ina cikin manema"
Cikin sauri faruq ya dago ya kalli bashir sannan ya maida idonshi kasa"
Anty ma yi tayi kaman bataji me bashir yace ba"
****
Bashir ne ya fara fita dan bayason su hadu da faruq, saidai yana dafda shiga motarshi ya hango faruq abayan shi, dan haka ya hada harta gudu ya fice agidan"
Ya koma gida babu dadewa yaji sallaman faruq lokacin yana zaune shida umma fada takemai danme yabari faruq ya shigan mata daki, Sallaman shi yasa duk suka maida hankalin su gareshi"
Idonshi kerr akan bashir saida yamai kusan kallon minti 3 sannan ya nufeshi gadan gadan wani wawan mariya ya daukeshi dashi tare da fadin munafukin Allah yau Asirin ka ya tonu ashe ka dade kana ha'intata, mika hannun yayi ya shakemai wuya tun bashir naganin abin wasa harya fara tari"
Itama umma da zama tayi kawai tana kallon ikon Allah, amman jin bashir na kakari ta zabura ta isa garesu faruq ta fara ja harda kaimai duka"
Ganin da tayi besan tanayi ba ga bashir ido duk suyo waje yasa ta kurma ihu, aguje nihilah ta fito ganin faruq shake da bashir yasata kurma ihu,
Umma gani tayi ihun bazai mataba ba dan haka ta dake kirjin faruq dakarfin da harsai da ya kalleta itama cikin idon ta kalli shi sannan tace idan baka sakeshiba Allah ya isa ban yafe maka b.....
Tunkafin ta karasa ya sakeshi ajigace bashir ya fadi kasa yana haki, nihilah ce ta nufeshi dagudu tanamai fifita da dan kwalinta"
Umma ko har yanzun bata daina dukan kirjishiba tare ta tambaya shi abinda bashir yamai"
Cikin karaji yake fadin umma *ASIRINSA YA TONU*, yana matsayin kanina wadda na yadda dashi nakesashi adukkan al'amurana amman yana ha'intata, yarasa wadda zai so sai naxiya sabo dashi maci amanane, wlh bashir saina kasheka"
Gaba dayansu shi suke kallo bama kamar nihilah data wangale baki, fifita takewa bashir amman hankalinta nagurin faruq hawaye harya fara tsiyayo mata"
Sai alukacin hankalin shi yakai kan nihilah wani haushi ne yasake kamashi cikin fada yace ke dan ubanki zoki wuce daki idan nakaraganin kinbi hanyar da bashir yabi ma saina jimiki ciwo, azafafe ya juya ya fita, yayin da umma tabishi da kallo"
Yana fita ta juyar da hankalinta ga bashir cikin fada tace bashir me ya kaika aikata irin wannan, ta yaya mace da mijinta zakace kana so kafa nemi tashin hankali"
Umma rabo dashi karyan iskanci yake, yaya za,ayi naso naziya daman gwadashi nake, dan na fahimci yana sonta amman yake wulakantata dan kawai yaga sonta yafi nashi yawa, yake wahalar da ita"
Ajiyan zuciya umma tayi sannan tace lallai bashir baka da hankali, waye ya gaya maka anawa namiji irin wannan wasan? Toh ai ko saurayi ne ya nemi buduwar suka rabu yaji wani ya aureta haushi yakeji, bare matar da take tare da mijinta harda haihuwa atsakanin su, gsky baka kyauta ba, yazun idan ba anci Sa,aba zumuntan ku ta samu tangarda kenan tunda kaga ya dauki zafi kuma banga laifinshi ba"
*****
Faruq gida ya wuce kangadon shi ya kwanta, babu abinda zuciyarshi take mishi banda tafarfasa mgnr bashir ke masa yawo akai Ashe daman bashir son naziya yake? Na sakan kance mishi, ashe neman dama yake, shedan ne yacigaba damai busa, acikin zuciyarshi yake cewa ko shiyasa bashir da naziya suke shiri sosai , yayin da nihilah kuma basa shiri da bashir dolene ya tsanta bincike har ya gano meye atsakanin naziya da bashir, dan alamu sun nuna akwai wata kullalliya"
Tunawa yayi ya baro nihilah gidan umma dan haka ya mike afusace dan bazai yadda bashir ya gama kallemai mata ba, dan yanajin nihila ne har cikin bargoshi, ko kallonta bashir yayi ya cuce shi, bare har ya jiyemai zazzakar muryanta"
Lokacin daya isa gidan babu kowa afalon dan haka ya isa dakin umma, shiga yayi tare da sallama"
Umma rungume da nihilah sai faman fifita take mata"
Afirgice ya karasa inaga ya mance waye agurin dumin kuwa hanun shi yamika ya rike nata" yana fadin nihilah jikin ne sannu ko Allah ya baki lfy"
Umma ya kallah sannan yace umma naZo tafiya da itane"
Zame nihila tayi daga jikinta sannan tace a,a kabari gobe iyayen ku zasu dawo dan namusu waya nagaya musu halinda kuke ciki sun kuma ce ajira su"
Shiru yayi zuwa can yace umma nifah bazan iya barin nihilah ta kwana gidan nan ba matsawar bashir na cikinsa"
Tsoro ne ya baiyana fuskan umma wato abin harya kai haka?, nunfasawa tayi sannan tace toh yanzun yaya kakeson ayi?
Umma tafiya zamuyi ko kuma nima nakwana anan"
Waigowa tayi ta kalleshi sannan tace Hmmm toh bissimillah, juyawa tayi tafice adakin"
Jawo nihilah yayi ya rungume zuwa can ya fara sunbatanta taren da tura hanunwan shi cikin rigarta"
Hannuwan shi ta tattaro duk ta fito dasu sannan tace, yaya ashe daman kanason naziya, kana kishinta kaman mahaukaci kazo ka shake bashir kaman zaka kash......
Hannun shi yasa da sauri ya bege mata baki cikin mazurai yace banason kina kiran sunan bashir da bakinki idan kika kara Allah ya isa, banason bashir na tsane shi, tunda na fahimci idon shi nakan gonata, nihilah ina da matukar kishi, da ace kece bashir yace yana so to da lallai zan kashe bashir, nihilah naziya fah matatace amman dan rashin kunya har yabude bakinshi yace zai aureta"
Yana mgnr ne yana shafa jikin nihilah zuwacan yace nihilah kisan abinda nakeso dake daga yau indai ina gabanki bason nasakejin kin kira sunan naziya, kisa kawai azuciyar ki ni faruq daki ne ke 1 kicire naziya azuciyar ki, idan kikai haka zan baki mamaki"
Ajiyan zuciyata sauke dan babu laifi tadanji dadin mgr shi"
Saida ya gama luguiguita ta sannan ya mike Bari naji na danyi wani bincike yanzun zan dawo"
****
Shika dai yake tafiyar shi cikin mota cikin minti 30 ya isa gidan, bayan ya faka motar shi ya tsaya yana tunanin yaushe rabon shi da gidan fatima tun nihilah na karama da take samishi kuka saiya kawota"
Yana kokarin sakkowa daga cikin motar mijin Fatima na fitowa daga cikin gidan"
Cikin sakin fuska ya karaso ya mikawa faruq hannun suka gaisa"
Bayan sungaisane yace ma furuq mushiga mana"
Faruq na murmushi yace, basaima nashiga ba, ta leko kawai mugaisa"
Beyi musuba dan surukuta yake da furuq sosai, dan shi befaye sakin fuskaba sabanin bashir dayake wankar"
Cikin sakin fuska nasir ya kalli fatima dake wanke2 yace toh saiki saki aikin yau babban yaya ya tunamu ya kawo mana ziyara"
Fara,a ta saki cikin sauri ta fara dauraye hannunta tana fadin"
Yaya bashir kenan Kuma fah munyi waya becemin zaizo ba"
Daidai lokacin da suka fito falo yace ba bashir bane faruq ne"
Baki fatima ta kama tare da馃槼 sannan tace badai yaya faruq ba, saidai bashir, shi wannan inbanda masifa me ya iya"
Hanyar fita tayi daidai lukacin da yake cewa kina nufin ni bansan faruq din bane?
Bakaramin mamaki tayiba ganin furuq jingine jikin motar shi, adan tsorace ta karasa tare da addu'an Allah sa karyai mata masifa kafin su rabu"
Ganin inda take dardar yasashi fadin ke dallah inzakizo kizo ni sauri nake"
鉂勷煉mn Yazeed鉂勷煉�
鉂勷煉︹潉馃挦鉂勷煉�
*ASIRINSA YA TONU*
鉂勷煉︹潉馃挦鉂勷煉�
鉂勨潉鉂勨潉馃挦
*By*
鉂勨潉鉂勷煉�
*Fadeela Lamido*
鉂勨潉馃挦
鉂勷煉�
鉂勨潉馃挦
*Page 94 to 96*
鉂勨潉馃挦
Ahankali ta karasa gaban shi, kamar bazaiyi mgn ba, zuwacan ya nisa sannan yace"
Kinajina wani dan aiki Zan baki, nasan nihilah najin maganar ki, inason ki same ta ki mata dan nasiha ta dan rage xafin kishin nan nata"
Cikin mamaki fatima take sauraranshi yanzun shi da kanshi bazai mata nasihar ba saiya nemin wani duk masifan ashe na banza ne, lallai maza halinsu saisu nihilan gudawa nawa take, yariyar daya kusa haifa ya nuku gari ya taho man....
Muryan shi taji yaci gaba da cewa, fatima bana juran Ganin nihilah cikin damuwa, ina tsintan kaina nima cikinta har na kasa sararrafa kaina, ganin inda fatima ta sunkuyar dakai ya sashi dakatawa yana leken fuskanta, cikin natsuwa yace ke fatima kinajina kuwa?
Cikin nutsuwa ta dago kai tare da fadin inajinka yaya"
Toh mgn ne zanyi dake me mahimmanci, inason ki taimaka min na gyara gidana, ni yanzun bani da wani gata.....
Cikin sauri ta kalleshi tare da mamaki akan fuskanta, adan tsurace tace yaya ya zakace haka?
Eh gaskiya na fada fatima bani da gata haka kuma bani da abukin shawara, ita anty kulum cikin kushe nihilah take saikace ba itace ta haifita ba, amman ta iya yabon 'yayan wasu, kullum cikin yabon naziya take, umma ko dama can basona take ba, ta wareni acikin
yayanta, yanzun ne ma take dan min mgn, shiko bashir munafukine akwai wani abu azuciyar shi"
Kurrr fatima tamai tana mamakin yadda ya saki baki yana irin wannan maganganun masu kama da sambatu"
Cikin tsawa yace kimajina kuwa kin wani tsareni da ido "
Sunkuyar dakai tayi sannan tace, yaya ai duk naji abin da kace , dazun ma munyi waya da umma take gayamin abin dake faruwa inasha Allahu gobe zanje gidan kuma zan same nihilah kamar yadda kace"
Yauwa yar kanwata dako kin kyauta min amman ba fada zaki mata ba, karki yadda kisata kuka, indai kinga zatai kuka kibarta kawai dan bamata da lfy"
Cafff fatima ta fada azuciyarta afili kuma tace karka damu yaya"
Da haka sukayi sallama ya tafi, koda fatima ta shiga gida gadon ta fada tare da fasa kuka dan gani take yayan nata kamar ba cikin hayyacin shi yake ba, yace awa matarshi nasiha kuma yace kar asata kuka, wannan wacce irin soyayya ce"
Faruq ko gidan umma ya nufa, yana dafda shiga unguwar alhaji ibrahim ya kirashi awaya, gefen hanya ya koma ya tsaida motar sannan dauka"
Sallama yayi amman alhaji ibrahim be amsa ba cikin bacin rai yace kana inane yanzun ?
Cikin sanyin jiki yace ina kan hanyar zuwa gidan umma"
Uban me zakayi agidan? anya kuwa lfy fiya kalau kake?
Baba nihilah fa tana gidan, kuma ni gaskiya ban yadda da bash.....
Kunci ubanku kaida Aishan yazun in banda kai mahaukaci ne tayaya aure zaiyuwu tsakanin bashir da naziya bayan kana raye ba mutuwa kayi ba, ko ka mance uwa daya uba daya kuke kaida bashir?
Cikin rawan baki yace baba ainasani cewa babu aure atsakinin su, amman tunda har ya iya furtamin haka zai iya ha intata yamin zamba cikin abinci"
Shiru alhaji ibrahim yayi har ya gama sauraran sa sannan yace"
Faruq meyasa san zuciya yakeson ya rufe maka ido, duk cikin yaran nan namuu kaine babba meyasa kakeson zama me kawo mana matsala, bashir wasa yakeyi kuma al'ada akwai wasa tsakanin kani da matar wansa"
Baba shifa cewa yayi idan na saki yana cikin manema"
Kai faruq dadi na dakai naci kaman kuturu, yanzun dai ka kama hanya ka wuce gidan ka kakwanta ban amince maka kwana gidana ba, dan mahaifiyar ka tacemin kace can zaka kwana toh ban yadda ba, tun wuri ka wuce gidan ka, idan mun dawo gobe zanyi kiran ka"
Juyawa faruq yayi badan ransa yaso ba, ranan yadda yaga rana haka yaga daredare, zuciyar shi cike da takaici"
Dan haka washegari bece zashi office ba dan
Yasan ko yaje bazai iya aikata komai ba"
Da misalin 2:30pm faruq kwance akan makeken gadon sa, babu abinda yake sai tubka da warwara, ya saka wannan ya kwance wancen yana cikin haka wayarshi tayi kara, kira ne na gaggawa daga daddy dan haka cikin sauri ya tashi ya tafi"
Cikin kankanin lokaci ya isa gidan alhaji ibrahin, yayi mamakin ganin mutanen dake ciki kusan dangi ne gaba daya aciki, saidai yan kadan da basa gurin"
Bashir ne ya bude taron da addu'a bayan yagama daddy yace"
Nasan dukkanin kunsan abinda ya taramu gurin nan, kaman yadda kowa yasani abubuwa da dama sun faru, amman abinda yafi firgitani fada tsakanin bashir da faruq, kwata2 banji dadi ba, cikin tohuma daddy yajuya ya kalli faruq sannan yace"
Faruq meyasa idonka yakeson rufewa, yazun duk yadda kuke dakai da bashir?, banda shirmenka .me zai kawo zargi, tun
Wuri ka gyara tunanin ka bana son shashanci"
Anty ce ta katse daddy da cewa wlh yaro sai kun tasan mai tsaye kwata2 ya cenja hali yazama wani irin fitinanne, banda haka bashir fa cikin wasa yayi mgnr, menene abin tada hankali harda su duka"
Hmmm ai abin yama wuce duka shakeshi fah yayi kaman zai kashe, wlh da babu kowa kusa Allah kadai yasan me zai faruq, cewar umma da take kokarin mikewa"
Alhaji Ibrahim ne yayi gyaran murya sannan yace duk bawannan ba, kai bashir zo ka bashi hakuri kuma tunda ya nuna beson wasa daga yau karka sake mai irin wasan"
Murtuke fuska bashir yayi sannan yace, baba ai basai na bashi hakuriba tunda na fada cewa wasa nake, kuma shi kanshi yasan wasa nake kawai yaso cimin mutunci ne"
A,a bashir kabashi hakuri nace ai durkusawa wada ba gajiyawa bane"
Toh shikenan baba ahankali ya mika hannun shi ya rike faruq sannan yace"
Allah yabaka hakuri faruq ni wasa nake maka, wlh babu komai azuciyata"
Faruq bece komai ba illah kyauda kanshi da yayi gefe"
Alhaji ibrahim yace toh na kashe wannan mgnr karna sake jinta"
Sai kuma mgn akan matan ka da akace sun samu saba bani......
Cikin sauri faruq yace baba dan Allah ina neman alfarma abar wannan mgnr zanyi hukunci dakaina"
Lala sam ban amince ba hukuncin ka na hauka alhaji ibrahim ne ke fadin haka lokacin da yake kallon cikin idon faruq din"
Kara kwantar dakai yayi yace, baba wlh da hankalina, nasan abin da nake yi, wannan karon inason nayi hukunci da kaina......
Mlm saluhu ne yayi gyaran murya sannan yace"
Inaga kubarshi din, inaga zaifi, tunda yace yanason yayi hukunci dakanshi yana da kyau abarshi yayi din, dan shine yake zaune dasu yasan halin kowacce cikin su, kuma kunsan ance me daki shiyasan inda yake masa yoyo, duk wadda hunkuncin da zai yanke bemata dadi ba kunga gaba ta kiyaye"
Shiru falon yayi zuwa can anty tace nidai ban yadda ace wai yaro ne zaiyi hunci ba, dan Allah kar kubashi wannan daman, naziya wahala kawai take sha ahannun shi be bari hankalinta ya kwanta ba bare taji dadin zama dashi.....
Cikin sauri mlm yace hutu kuma? Aini banba faruq naziya aure dan ta huta ba, aure fa na turata wadda nake saran ta sanadinshi zata shiga *Aljannah* kuma akullum nasihata gareta tawa mijinta biyayya sannan tasa azuciyarta ibada take, ba zuwa ta mike kafafu tana jiran kyale kyalen duniya ba"
Gaba daya falon zancen mlm saluhu ya shigesu, kusan kowa idonshi cike yake da hawaye, anty da naziya ko tuni suka fara kuka"
Itama nihila dake dafda fatima ajikinta yayi sanyi sosai, shiko faruq sunkuyar da kanshi kasa yayi kaman mejin kunya"
Ahankali daddy yayi gyaran murya sannan ya kira sunan faruq ahankali yace"
Nasan kai ba jahila bane ilmin daidai gwargwado kana dashi, idan kaje yanke hukuncin kaji tsoron Allah kayi adalci, karkaga bamu agurin kace zakayi abinda kaga dama, kasani idan bama wajen Allah na kallon ka, kuma zaka tsaya agaban shi aranan da babu wani kalma da zaka iya kare kanka da ita"
Daddy narufe baki faruq ya fara musu godiya tare da kara tabbatar musu insha Allah zaiyi adalci,
Gaba daya mazan sukayi waje sanadin kiran sallan da sukaji"
Matan kowace haramar sallan sukayi"
Anty fatima da nihilah zaune adakin umma bayan sun idar da sallah, kallon nihilah tayi tace"
Nihilah wai meyasa bakison naziya ne, bayan tana da Kirki amman har yanzun naga jininku yaki haduwa duk da cewa ita bata nuna miki irin kiyayyan da kike nuna mata"
Shiru nihila tayi tana wasa da gefen hajjabinta"
Badake nake mgn ba Fatima ta fada bayan ta daure fuskanta"
Ahankali tace anty nidai da ace zata rabu da yaya to da zamu shirya amman ni gaskiya yanzun bansonta"
Kina nufin ya saki naziya ki zauna dashi ke daya?
Da saurinta tace eh"
Murmushi fatima tayi sannan tace nihilah kina ganin ke daya zaki iyamai maganin matsalan shi?
Cikin rashin fahimta tace anty aishi bashi da da wata matsala"
Baki fahimci niba ina nufin zaki iya daukan bukatan shi aduk lokacin daya gaiyaceki shinfidan shi?
Cikin sauri nihilah ta馃槼 sannan tace a,a anty shida yakejin shi kaman inji, wlh bana iyawa idan na gaji hakura yake"
Fatima taso yin dariya amman saita daure sannan tace to kinga amfanin mata 2 kenan, ranan da baya dakinki saiki dan huta na kwana 2 kinga kishiya abokiyar zamace ba ba abokiyar gaba ba"
Cikijin kunya tace anty nifah koni daya ce zan iya kulah dashi"
A,a nihilah yanzun fa kikace yanajinshi kaman injin"
Toh anty idan yaga ni kadai ce ai dole ya hakura"
Cikin murmushi anty tace toh ashe ba dai injin din bane, indai har zai iya hakura, ni abinda nake kuje muki yanzun amisali yaya faruq ya saki naziya bayan kwana biyu ya fahimci bazaki iya daukan dawainiyar saba yaje ya jajubo miki gogaggiyar yar duniya, kiyi yaya da ita?, barganin yana kyaunar ki, dole ya kulah da lfyn jikin shi, dan haka nake baki shawara kiyi hakuri ku zauna lfy"
Hawaye nihilah ta fara sharewa tace toh naji amman dan Allah kitayani addu,a Allah yayamin"
Sosai anty ta tausaya mata dan haka ta mika hannu ta jawota ajikinta tana rarrashin ta, suna cikin haka anty ta shigo taita mata nasiha sannan tace ta tashi taje falo faruq najiranta zasu tafi gida"
****
Tana isa falon ta hangoshi zaune ya daga kanshi sama, naziya nagefe ta takure, kai tsaye tanufeshi kanciyarshi ta zauna tare da shafa sajensa tadan huramai Iska afuskan shi"
Ajiyan zuciya ya sauke sannan ya kama kanta ya kwantar akirjin shi yana fadin kinfara ko?
Kukan shagwaba ta fara tare da fadin toh ni me nayi"
Nandanan faruq ya fara fita hayyacin sa adaburce yace ya isa haka tashi muje gida"
**
Suna isa gidan ko wacce ta wuce barayinta yayin da zuciyar naziya ke dukan uku uku, dan batasan wani irin hukunci faruq zai yanke mata ba, dan ta tabbatar hukuncin akanta zai kare dan ta kula har tsoron batawa nihilah rai yake"
Shiko faruq addu'a yaitayi acikin zuciyar shi Allah yasa yafi karfin zuciyar shi yayi adalci"
Sai kusan karfe goma ya baro gidan anty dan haka kai tsaye dakin nihilah yanufah,
Samunta yayi ta cure waje daya tana rike da cikinta"
Dasaurin shi ya karasa yana fadin jikin ne?
Cikin shagwaba tace nifa yunwa nakeji cikina kaman babu komai nake jinshi, aini agidan umma su 4 take bani abinci arana dan likitama cewa yayi inci abinci sosai"
Shiru yayi harta gama sannan yace, naziya batayi girki bane?
Toro baki tayi sannan tace toh ni kotayi ma inaruwa na da abincinta danni baci zanyi ba"
Tamke fuska yayi sosai sannan yace, jiba nihilah banason rigima kisan dai ba girmana bane yawon suyo abinci bazaiyu inada mata biyu indinga yawon suyo abinci ba, duk abinda kikeson ci kishiga kitchen ki girka, amman yanzun tunda baki da lfy ki fada abinda kikeso insa naziya ta girka miki, kuma sannan inason na gargadeki akan shiga dakin mutun babu sallama, tayaya zaki shiga dakin naziya bazaki mata sallama ba sa,arkice ita kodan kinga ina lalabaki ne yabaki daman da zaki mata rashin kunya"
Cikin matsanancin mamaki nihilah ke kallon shi cikin tunzura tace au goyon bayanta kake kenan nida ta zageni fah cemin tayi fah dabba"
Shima cikin zafi wadda batasan yanashi akantaba yace nikikewa tsawa? nihilah ina mgn kina mayar min, bayan kice baki da gaskiya duk sunan da ta kiraki dashi aike kijawowa kanki, daga yau kuma karki kara shiga part dinta batare da kin mata sallama ba, abinci kuma nata zaki rankaci bazan kara zuwa soyo abinci ba, sannan indai kinason farin cikina kiba naziya girmata dan Allah nihilah badan halina ba kibata girmanta kuzauna lfy kwatar da murya yakarayi sanna yaci gaba da cewa nihilah dan Allah kitaima keni nasan inasonki fiye da inda nakeson kaina, dan haka inason kibani goyon baya nayi dalci atsakanin ku, tare da kara sakani kan hanya idan kinga inashirin kyaucewa, nihilah ko kinason sanadin rashin adalcin danakeyi makomata ta zama wuta ne?
Cikin kuka ta girgiza kai dukda magan ganunshi na farko sun tsaya mata arai amman daga karshe ta tausawa zancen shi, dan haka ta daukan ma zuciyarta wani alkawari dan ganinta hakan ne kwanciyar hankalinta"
Shima hawayen yake sharewa amman yana fakan idonta karta gane halin da yake ciki, zuwa can ya dake yace nihilah kin min alkawarin kwantar da kanki ku zauna lfy na naziya?
Tana goge hayen ta daga kai alamar eh"
Murmushi yayi sannan yace nagode Aisha Allah ya miki albarka har naji sunki ya kara nukuwa azuciyata, dan mirgonota yayi jikin shi sannan yace bari naje na karbo miki abinci ko zakizo mujene muci tare"
Gargiza kai tayi dan haka ya mike tare da sun batan ta akumatu ya fice"
Yana fitowa ya daure fuska sannan ya nufi part din naziya"
Tunda ta kalli yanayin shi gabata ya fadin, dan haka ta mike da saurinta tana kokarin shiga toilet"
Cikin fada yace idan kika matsa anan gurin sai ranki ya baci, yau daga ni sai ke babu me ceton ki"
Ja tayi ta tsaya dan bata da bakin mgn illah rawa da jikinta ya fara"
Takowa yayi har ya iso gabanta batai aune ba saijin saukan Mari tayi akuncen ta, kafin ta ankara ya kara mata wani"
Agigice ta tsanyara kawara tare da fashewa da kuka dan saida taga gilmawan wasu wayoyi, sabo da radadin da taji"
Cikin fada yace wannan yazan na farko kuma na karshe da zaki dake nihilah duk abin nihilah tamiki kiyi hakuri harna dawo, bance ki hukuntata ba, dan aurenta nake kamar yadda nake auren ki, yarki ce ita dazaki rufeta da duka?"
Kuka kawai naziya keyi harya gama babatun shi ya fice"
Dakin nihilah ya koma dauke da kulolin abinci saidai yana shiga ya sameta kwance kamar me bacci, dan girgizata yayi ta bude ido yace oya sakko kici abinci"
Cikin yanayi irin na me bacci tace yaya likita yace idan nayi bacci adaina tashina kumani yanzun banjin yunwan ka ajiyemin ka tafi abin ka anjima zanci"
Tana mgrn tana lumshe ido kamar mejin baccin gaske dan haka ya kyaleta gadon ya haye ya jawota jikinshi wasa yasoyi da ita amman taki yadda duk nacinsa saida ya gwada akanta dan dai ta bashi hadin kai amman taki, dan haka abun yai matukar bashi mamaki domin ita mutunce meson wasanni amman yau daga yakai hannun jikinta saita goce, daga karshema kudunnewa tayi cikin bargo tabarshi agefe"
Ido ya zuba mata kamar me kallon TV acikin zuciyar shi yace me yariyar nan ke nufi ne? Zuwa can ya kula kamar baccinta yayi nisa dan haka ya mike ya fice"
Part din naziya sake komawa dan gaskiya mutun neshi mabukaci yaso ya rage dare gurin nihilah amman taki amincewa , dan haka dole ya aje fushinshi agefe yaje gurin naziya"
Toron kofar naziya taji anyi daker ta iya daga idonta da jini ya kwanta ta kalleshi, wani haushi ne ya rufeta jitake babu wadda ta tsana aduniya kaman shi, kumatun ta ta dafe wadda ya kunbura yayi suntun"
Shima tunda ya shigo yake kallonta saidai taki bari su hada ido, cikin gadara yace ke naziya kisame ni adakina kiyi sauri karki batamin lokaci........
鉂勷煉mn Yazeed鉂勷煉�
鉂勷煉︹潉馃挦鉂勷煉�
*ASIRINSA YA TONU*
鉂勷煉︹潉馃挦鉂勷煉�
鉂勨潉鉂勨潉馃挦
*By*
鉂勨潉鉂勷煉�
*Fadeela Lamido*
鉂勨潉馃挦
鉂勷煉�
鉂勨潉馃挦
*Page 97 to 98*
鉂勨潉馃挦
Bejira me zata ce ba yayi gaba abinsa"
Itako naziya mamaki abin ya bata lallai mutumin nan da karfin hali yake, ya gama dukana kuma yacemin wani wai na sameshi adaki, tsaki taja sannan ta mike ta isa gaban madubi, gani tayi gaba daya ta canza kamanni gaba daya fuskanta ya kunbura gawani jini daya kwanta gefen idonta guda 1, hawaye ne suka zobo mata tasa hannunta ta share wani irin zuciya ne ya bijiro mata dan haka ta mike afusace"
Kitchen ta nufa ta dauko zandareriyar wukanta, sannan ta maida hannuwanta baya ta nufi dakin faruq"
Ahankali ta tura kofar daidai lokacin da faruq din ya fito wanka yana daure da towel akugun sa, hannun sa daya dauke da turare yana fesawa asako da lungu na jikin shi"
Wani Mayataccen kallo yabita dashi rigar bacci ce me dan karan kyau ajikinta iya daidaita gwuiwa, sai yanzun ya kula da kunburin fuskanta, saidai yadda yaga tamaida hannuwanta baya ya dauke masa hankali dan betaba ganinta tayi haka din ba"
Idanunta ta kafeshi dashi tana kallon shi dan haka ya shiga kallon jikin shi ko zaiga me take kallo, iya dubanshi bega komai ba dan haka ya maida hankalin shi wajenta"
Ahankali ta fara tahowa gabanshi dan haka ya kafeta da ido, tana zuwa dafdashi ta tsaya cikin ido takaleshi sannan tace malam *ka sake ni*"
Bangane na sake ki ba daman na rikeki ne?
Cike da kwarin guiwa tace ina nufin ka sauwake min auren ka, bana yi"
Hmmm toni inayi, idan kuma sakin ahannunki yake sai nagani"
Zabura tayi sannan ta fito da wukar dake hannuta ta mika mishi tare da fadin amshi ka karasani na huta da bakin cikin auren ka, wlh ina me tabbatar maka idan baka kasheni ba ni zan kasheka, dan bana sonka na tsaneka, ka sakeni inhuta da zaman takaici da bakin cikin gidan ka, tana mgnr ne kaman zararriya tare da kara nufarshi da wukan"
Sosai hankalin faruq ya tashi daganin halin da take ciki tabas ya fahimci bata cikin hayyacinta kuma ayadda yaga yanayin ta babu abinda bazata aikata ba"
Mike mishi wukar take tare da kara matsawa kusa dashi"
Daker ya bude baki yace toh duk me ya kawo haka?
Bana sonkane kawai ka sakeni ko kuma ka kashi ne ka huta dan na taren maka rawar gaban hantsi, karashi mgnr tayi tana mika mishi wukan, dan haka ya mika hannu ya karba"
Kura ma wukar ido yayi sannan ya dago ya kalleta sosai sannan yace"
Naxiya yanzun dan namiki fada shine kikayi fushi haka? , naziya kina da hankali kuwa?, wuka fa kika bani, ni kikecewa na kashe ki?
Bata da niyar mgn saima rufe ido tayi tana huci kaman kububuwa"
Shima shiru yayi yana kallonta zuwa can yace naziya bude idonki ki zauna muyi mgn"
Bata bude idon ba kuma bata zauna ba tsaye take kawai kaman gunki"
Hankalin faruq kara tashi yayi dan haka idon shi sukayi jawur kallonta ya sakeyi sannan yace toh shikena tunda hukuncin dana miki be miki dadi ba Allah yabaki hakuri, wannan irin zuciya haka! Kefa daman baki iya fushi ba, dan Allah ki bude idonki indai nine natuba kiyafeni, hannun sa ya mika ya tabata da niyar jawota jikinshi zafi yaji rau ajikinta, hakan ya tabbatar mishi zazzabi ne ajikin dan haka ya dauketa cak yasata agado yana cigaba da fadin mutun bashi da lfy amman ya iya neman jafa'i"
Ciccijewa take tare da kokarin kwacewa ganin haka ya sakkan mata karfin shi gabadaya yana cigaba da fadin nace kiyi hakuri ko?, ni banason irin wannan fushin naki, Allah ya baki hakuri, haba naziyata, dan Allah ki huce haka nan ya isa"
Wani dan sanyi taji azuciyarta ganin inda faruq ya marairaice mata dan haka ta fara sauke ajiyan zuciya"
Ganin ta fara saukowa yasahi mikewa, inda yake aje magani ya nufa, zuwa can ya dawo hannun shi dauke da magani da ruwa gaban gadon ya zauna sannan yace sakko kisha magani"
Kin tashi tayi, yayi magana harya gaji dan haka ya dauko cukali ya dama, bata ankara ba saijinshi tayi yana dura mata, ruwa ya bata ta kora sannan ta koma ta kwanta hawaye na tsiyayo mata ta gefen ido"
Ahankali ya hau gadon cikin dibara ya daurata akan kirjin shi, cikin masifa takaimai duka akirjin tare da kukarin sauke kanta"
Dasauri ya rike hannuwan ta sannan ya kara mannata da jikin shi yana fadin, haba naziya zaki kashe ni ne?, ki kwanta kiyi bacci kinga jikin ki yayi zafi sosai"
Kwanciya tayi tai lamo dan ji take kaman an mata duka, ta dade kwance jikin shi amman bacci yaki zuwa mata"
Duk halin da take ciki faruq najinta dan shima yau idon shi kwata2 babu bacci, dan yadda naziya tamishi yau ya nunamai tana cikin mummunan hali, beji dadin halin dayaga tashiga ciki ba, jin yadda hawayenta ke sauka akirjin shi yasashi wani tunani anya kuwa naziya ba aljanu gareta ba?, yin wannan tunanin yasashi ya Fara karanto addu'oi yana tofa mata, cikin kankanin lokaci bacci me nauyi ya kwasheta"
Washegari
Tunda faruq ya tafi sallah ta wuce dakin ta, alhamdulillahi jikinta yayi sauki sosai dan fuskanta harta sabe, tsintan kanta tayi cikin farin ciki sosai dan yau har gari ya waye faruq beyi baccin kirki ba, daga ta motsa zatajishi yace sannu jikin ne? Zaki sha ruwa ne ko wani abu kike so?, tunda take da faruq bata taba samun irin wannan kulawa daga gareshi ba, koda ta kwanta agadonta bacci gagaranta yayi data rufe ido daren jiya take tunuwa"
Da misalin karfen 8:00am faruq ya shigo dakin, jallabiya ce fara sol ajikinshi, bakin gadon ya zauna sannan ya tura hannun shi cikin rigarta yana duba zazzabinta, tare da fadin yajiki?
Daker ta bude baki tace da sauke"
Murmushi yayi kadan sannan yace toh Allah ya kara sauki, waya taga ya kara akunnen shi zuwa can taci yana cewa"
Anty ataimaka mana da breakfast wlh matan gidan duk basu da lfy"
Bataji me akace ba zuwa can taji ya sake cewa wlh anty ba nihilah bace batama san nakira ba, yauwa anty mungode "
Kashe wayar yayi sannan ya kalli naziya ahankali yace"
Naziya naga jiya kinyi fushi sosai ina fatan zuwa yanzun kin huce? , karashe mgnr yayi tare da kafe ta da ido"
Mata da miji sai Allah ganin inda ya marairaice yayi matukar bata tausayi dan haka ta mika hannunta ta roko nashi, tare da kurawa hannun nashi ido, shiko fuskanta ya zuba ma ido yana murmushi, ganin bata da niyar mgn yasashi fadin bakice komai ba?
Tana wasa da hannun take fadin ya wuce Amman ni gaskiya bazan jurewa halin nihilah ba indai ta karamin rashin kunya bazan yadda ba"
Hmmm bazama ta kara ba dan itama jiya na mata fada, kuma ta fahimta, amman abu daya zan kara jajjada miki ban abince da duka ba, dan karfin ku ba daya bane kuma kinga ciki gareta yanzun da wani abu ya samu cikin kice me?, dan Allah ki dinga kokarin kina rage fushin ki"
Jitayi gaba daya jikinta yayi sanyi daman nihilah ciki gareta?, cikin sayin jiki tace toh kayi hakuri ni bansan tana da cikiba da bazan kulataba"
Dan murmushi yayi sannan yace bakomai naziya itama haryanzun bata san dashi ba, kuma naji dadi da kika fahimta Allah ya mike albarka, kuma kyauda idon sa'idawa akanmu馃槣
Ameen ta fada tana tura kanta cikin kirjinshi"
*Hmmm lallai naziya hausawa sunyi gaskiya dasuke cewa tsakanin mata da miji sai Allah*
Shima murmushi yayi tare da kissing dinta, afilin yace Allah ya hada min kanku"
mikewa yayi tare da fadin naziya bari na dubo jikin nihila"
****
Afalo ya samu nihilah ta daura kafanta daya kan daya, yana kallonta ya gane tayi kuka ta sanadin idonta daya kunbura, zama yayi dafda jikinta tare da jawo kafadan ta ta fada jikinshi, batai musuba saima Kara shigewa jikinshi datayi leken fuskanta yake yana fadin kinganni sai yanzun ko? Kiyi hakuri dan Allah naziya ce bata da lfy mun kwana bamuyi bacci ba, dan haka bayan nayi sallah na dan kwanta"
Hmmm bakomai"
Yadda tabashi amsa ne yamai wani irin dan haka ya kara cewa, ko baki yadda bane?
Yazanyin ince ban yadda ba yaya Allah ya bata lfy tunda yau baka da aiki ma kana iya komawa ka kwanta"
Hmmm nihilah kenan kodan irin kewannan tawa bazakiyi ba, har wani korata kike?
Murmushi tayi sannan tace nayi kewanka mana gashi ma nakwanta ajikin ka"
Ban yadda ba idan har kinason na yadda kinyi missing dina kitashi mushiga daga ciki"
Cikin sauri ta make kafada tare da fadin a,a nabarwa anty na"
Cike da mamaki ya kalleta Dan gsky tabashi mamaki, suna cikin haka naziya ta kirashi awaya take shai damai idi drive ya kawo sako daga gidan anty"
Cikin sauri ya mike yana fadin oya nihilah tashi muje muyi breakfast"
Batai musu ba ta mike tare da tura hannunta cikin nashi, ahaka suka iso falon, nihilah ce ta fara gaishe da naziya batare da ta kalleta ba"
Cikin sakin fuska naziya ta amsa karo na farko da nihilah ta fara gaishi ta kenan tun bayan aurenta da faruq"
Akasa suka zauna bayan sun kammala faruq ya kallesu ko wanne ya takure alaman rashin sabo, dan murmushi yayi sannan yace"
Yanaga duk kun takure ne , ku sake jikinku ku dan taba hira mana, ko na tashi na baku waje ne?
Kauda kai nihilah tayi can gefe sannan tace, nifa yaya bacci nakeji daki zani na kwanta"
Daure fuska yayi kadan sannan ya kyauda idonshi can gefe almar yayi fushi"
Murmushi nihilah tayi dan ta gane manufarshi, ahankali ta kali naziya tace , anty ina takwarata ?
Cikin sakin fuska tace tana daki bacci take"
Yake nihilah tayi sannan ta sake cewa badai tun baccin jiya ba"
A,a ta tashi harna mata wanka, komawa tayi"
Farin ciki ne ya baiyana akan fuskan faruq acikin zuciyar shi yace alhamdulillah nihilah anfara hankali, afili kuwa kallon nihilah yayi sannan yace"
Ke ta gada ai gurin bacci, juyawa yayi ya kalli naziya yace jiya fah bataci abincin dare ba tayi bacci wai har tana cemin likita yace adaina tashinta idan tana bacci"
Murmushi naziya tayi sannan tace toh ai lalura ce, matsalan dai rashin cin abincin ki dinga daurewa kina ci, tunda baki daya bace"
Bani daya bace? toh ni da uban waye? abinda nihilah ta fada azuciyar ta kenan cikin sauri ta mike tayi daki"
Gaba daya binta sukayi da kallo, harta shige daki"
Mikewa yayi sannan yacewa naziya ina zuwa"
Yana shiga ya same ta tayi rufda ciki tana kuka, tseye yayi akanta yana kallon Ikon Allah zuwa can ya zauna sannan ya dagota jikin shi ya kura mata ido sannan yace"
Menene ya faru ?
Cikin kukan tace ai kanajinta tana cemin wai bani daya bace, me take nufi?, tana nufin ni mahau kaciya ce ?
Murmushi yayi sannan yace nihilah rima ce ke damunki, kina nufin yanzun baki fahimci abinda take nufi ba?
Banza tayi dashi tana cigaba da kukanta, dan haka faruq yaciga da cewa nihilah naziya na nufin ki dinga kula kinacin abinci saboda karki wahalar da abinda ke cikin Ki, ma'ana dan dazaki haifan mana nan da wata 7"
Cikin sauri ta kalleshi sannan tace to ni nace mata ina da ciki ne, ko ko ita tamin cikin dazata......
Cikin murmushi ya dakatar da ita ta hanyar fadin, a'a ba ita tayiba, nine na nayi"
Tashi tayi ta zauna sannan tace kana nufin dgsk ne ina da ciki shine baka gaya min ba amman ita ka gayamata?
Itama daliline yasa na gaya mata, badan haka ba saidai kawai kiga cikin na girma ajikin Ki tunda ke baki da wayo"
Shiru tayi bata sake cewa komai ba har aka dau tsayon wani lokaci dan haka faruq ya mike yace"
Bari naje nayi wanka na leka gidan anty, kuma yau ki shirya min tarba ta musanman, dan ina lissafe kwana na 2 adakin naziya dan haka yau anan nake"
Wani irin kallo tamai sannan tace yaya nifah na bar mata, dan haka basai ka dawo dakina ba, kayi zaman ka acen, ni babu abin da nake bukata idan kuma ina da bukata zanyi mgn"
Shiru yayi yana kallonta cikin baccin rai yace au tanan kuma kika bullo har ina murna kin fara hankali, to bari kiji wlh karki soma hanani kanki, dan bazan iya jurewa ba, wlh tun wuri ki canja tunani idan ba haka ba kuwa zan hadaki da daddy"
Turo baki tayi sannan tace toni me nayi ma, dan nace nabar mata ai ba dole bane ko?
Girgiza kai yayi kawai ya fita, adakin"
***
Da daddare banyan faruq ya kammala duk wani abu dazaiyi ya nufi dakin nihilah saidai yana tura kofar yajita kule, jikinshi asanya ye ya fara buga wa har ya gaji beji motsin kowa ba dan haka ya juya dakin shi cikin tsananin fushi"
Juyi yaitayi agado, besan me nihila take nufi da wannan hukuncin nata ba, koma dai menene, hukuncin yayi tsauri da yawa kusan kwana 3 kenan rabon da ya kwana kusa da ita, sannan gana hudu 4 zai tabbata, daman haka masu mata 2 sukeji wannan ta gara ka tacan wannan ta gara ka nan, Allah ka kawo min agaji"
Misalin karfe biyu yamike ya nufi dakin naziya"
Tana baccinta me dadi taji ana buga kofar, ahankali tace waye"
Cikin kausashiyar murya yace nine zoki budemin kofah"
Ahankali ta bede kofar sannan ta sauke idonta akanshi"
Fitina ce karara a idonshi dan shi abinshi baya boyuwa, ganishi haka saida gabanta ya fadi dan tasan duk ranan dayazo mata ahaka tanajin jiki, ahankali tace fly?
Hannunta ya Kama tare da fadin zo muje ki dan taimaka min"
Runtse idon tayi sannan tace, ka manta yau adakin nihilah kake?
Ina sane zo muje nihilah fushi take ta rufe kofarta tuntuni"
Toh ka bata hakuri mana, amman ai bekamata ka dauki kwanan wata kabaiwa wata ba"
Naxiya ai lalura ce, kuma nata bugawa taki budewa ne"
Bata rai tayi sannan tace toh nidai gsky kayi haku wlh bazan iya ba"
Cikin sauri ya saki hannunta tare da fadin shikenan ku taro ku kashe ni, gabayan ku da lura baku damu da damuwata ba azafafe ya juya ya shige dakin shi"
*Idan na samu dama zan kara page 1 an jima*馃槏
鉂勷煉mn Yazeed鉂勷煉�
鉂勷煉︹潉馃挦鉂勷煉�
*ASIRINSA YA TONU*
鉂勷煉︹潉馃挦鉂勷煉�
鉂勨潉鉂勨潉馃挦
*By*
鉂勨潉鉂勷煉�
*Fadeela Lamido*
鉂勨潉馃挦
鉂勷煉�
鉂勨潉馃挦
*Page 99 to 100*
鉂勨潉馃挦
Koda safiya ta waye bebi dakan ko wacce cikin su ba, shiryawa yayj ya fice"
Naziya na kallon fitan shi, hankalinta ya tashi dan tasan fushi yayi dasu, tunani ta fara tunanin ko taje ta samu nihilah ne tamata fada ta daina rufewa mijinta kofah"
Wani shashi na zuciyarta yace ke ki kiyayi bakin ki, haka ta wuni ita kadai agidan dan ko keyar nihilah bata gani ba"
Faruq KO sai misalin 10:30pm ya dawo gidan kanshi tsaye ya shige dakin shi, wanka yayi sannan ya dawo falon ya zauna"
Tun dawowanshi naziya taji shigowan shi dan haka yanzun ma dataji motsin shi ta kasa hakuri, tana kukarin fitowa tajishi yana kwankwasa kofar nihilah tare da kiran sunan ta, nihilah nihila kiyi hakuri ki bude min, haka ya kwashe kusan minti 30, dan haka ya dawo falon ya zauna tare da daura tagumi"
Daidai lokacin naziya ta fito, daf dashi ta zauna sannan tace sannu da hutawa"
Kin amasawa yayi ya kauda idon shi gefe"
Shiru tayi zuwa can ta mike ta doshi dakin nihilah"
Ahankali ta fara kiran sunanta tare da fadin kanwata lfy kuwa yau baki fito ba?
Daga can cikin dakin naziya tace lfyta lau"
OK toh zoki budemin kofar man"
Nihila bata ce komai ba saidai taji ana kokarin bude kofar"
Ido 4 sukayi da nihila nan danan naziya ta saki murmushi sannan ta saka kanta cikin dakin naziya karo na farko data fara shiga dakin ahankali ta ruko hannunta bakin gadon ta zaunar da ita itama ta zauna sannan ta kalli nihilah tace nihilah zan baki shawara, amman kafin nabaki shawaran inason kicireni atsayin kishiya da kika ajeni, ki daukine tamkar yar uwanki da kuka fito ciki daya nihilah bani da niyar cutar dake, kamar yadda kike tunani, kuma zanci gaba da miki kallon kanwata koda baki son haka, badan komai ba saidan darajan mahaifiyar ki, domin bazan mance alherin da tamin arayuwa ba"
Nihilah meyasa kike rufewa mijiki kofa? Kinason gamawa da nuniya lfy kuwa?, nihilah miji fa yafi karfin wasa ace tunjiya yana buga miki kofa kiki budewa?
Jikin nihilah yayi sanyi magan ganun naziya sun kashe mata jiki, gefe daya kuma mamaki take daman kishiya nawa kishiyarta nasiha ta kula da mijinta kodai da gsk naziya yar uwa ta daukeni ba kishiya ba, ahankali ta farajin wani farin ciki na shigarta"
Muryan naziya taji tana cewa dan Allah nihilah karki kara rufemai kofa, karkisa shi ya shiga cikin wani hali"
Ahankali nihilah tace anty nifa cewa nayi yaje gurin ki ni.....
Dakatar da ita naziya tayi ta hanya cewa waye ya gaya miki ana haka"
Daidai lokacin sukaji muryan faruq da basu san shigowan shi ba yana fadin yauwa gaya mata"
Dariya naziya tayi sannan ta mike ta kamo hannunshi tana murmushi ta hada dana nihilah sannan tace toh saida safen ku, kanwata kifah taimaka mai, harta kai kofa faruq yace naziya"
Ahankali ta juyo, mikewa yayi tare da fadin bari nazo nayi miki godiya"
Cikin sauri ta fara tafiya tana fadin na yafe cikin sauri ta saki kofar"
Babu laifi nihilah tasashi cikin farin ciki wanan daren, saidai yana sauka ajikinta ta fara amai, amai ne sosai me galabaitar da mutum"
Tas ya gyara gurin sannan ya dauketa cak ya mata wanka, tun daga ranan nihilah ta koma tsoron faruq, bataki su zauna suyi hira daga nesa ba amman batason ya matso kusa da ita, bere ya fara mika hannun shi jikinta, yanzun ta fara kakarin amai"
Dan haka duk ranan da ya koma dakin naziya take shan dan karan wahala, domin nihila idan tayi kokari tabashi sau daya, acikin kwanaki 2 da zaiyi adakinta"
Ahaka har suka kwashe tsayon wata 6 cikin nihilah yayi girma sosai daker take tafiya, zuwa wannan lokacin sunyi sabo da naziya sosai"
Mutane da dama na mamakin shakuwar su, dan babu wadda ya zata nihilah zatabar bakin kishinta akan faruq kamar haka"
Shi kanshi faruq din mamaki abin yake mashi musamman idan suna kuskus waisu adole basa so suji me suke cewa"
Ana cikin haka naxiya ta sake samun ciki, lokacin watan nihilah 9 da haihuwa yayin da cikin nihilah yake da 8, hankalin naziya yaso ya tashi amman tunda ta gayawa faruq yace babu komai ta kwantar da hankalinta"
Anty da kanta tazo ta karbi nihilah tare da kayanta, sadiq ko daman yana gidan umma"
Naziya da nihila ne zaune afalon naziya suna hira, yayin da suka baje gyada suna ci"
Daidai lokacin faruq da bashir suka shigo, bayan sun gaisa da bashir ya sake hannun shi ya debi gyadan yana fadin ina kuka samu gyada?
Inna hajiya ce ta kawo mana cewar naziya da take kokarin mikewa"
Saitin kunnen nihilah taje ta mata rada akune tana dariya yayin da nihilah ta kalli faruq adan firgice"
Menene faruq ya fada ganin inda suke kallon shi yayin da naziya ke dariyan mugunta ita kuma nihilah ta firgice"
Kara kulewa faruq yayi sannan yace wai menen haka ne?
Bashir ma kallon su yayi baki sake zuwa can yace alallai wai haka suke ma?
Kumawa naziya tayi mazauninta tare da fadin a'a mgnr muce"
Mikewa nihilah tayi tana kokarin shiga part dinta faruq ya ce ke inazuwa ana hira kuma?
Tsayawa tayi cak sannan ta marairai ce tace yaya wani irin masifamfen bacci nakeji"
Bashir da naziya ne suka kwashe da dariya, yayin da faruq yace"
Hmmm daman abinda kuke shiryawa kenan?
Cikin murmushi bashir yace gaskiya gidan nan akwai muna funci, kasannan menene ?, ka kawo musu ta uku"
Yake faruq yayi sannan yace barni da su, nasan maganin su, kallon nihilah yayi yace zo kiyi hiran ki, niyau ba anan gidan zan kwana ba, kafata kafan bashir"
Bashir ne ya kwashe da dariya tare da fadin wannan dai nihilan naga ranar da zata girma, o Ikon Allah yanzun a idan nihilah ta haihu yaran ka uku kenan, lallai girma ba wuya gakuma naxiya ma ana laulayi"
Murmushi faruq yayi sannan yace bari kawai bashir, ai idan na tuna haka bakaramin farin ciki nakeji ba, dan inason yara dayawa nifah idan za,a dinga haihuwa duk shekara agidan nan bazai tameni ba"
Hmmm toh ku kunji saiku bada himma, cewar faruq"
Naziyace ta tabe baki sannan tace nikam bandani awannan tsarin nashi dan daga wannan bazan sake haihuwa ba, saidai nawa nihilah addu,an ta gama fly"
Shiru faruq yayi yama rasa wanne irin amsa zai bata, hira sukaci gaba tsakanin bashir da naziya shiko faruq mgnr naziya ce ke mishi yawo akai"
Damisali 11:00 bashir yabar gidan, mikewa naziya tayi da nufin shiga daki faruq ya kirata"
Cikin tuhuma yace me kike nufi da mgrki ta dazun?
Wacce mgn Keenan?
Inajiki fa kina cewa daga wannan bazaki sake haihuwa ba, kin barwa nihilah wacce irin mgn ce wannan?
Ayya Allah ya baka hakuri ni bammasan sanda na fada ba, kuma ai duk abinda Allah ya nufa babu me canza shi ku inason nakara idan Allah be nufaba bazan karan ba"
OK wa'azi ma kike min?
A,a ba wa'azi bane tuna tarwa ne"
Nihilah dake gefe ne ta kalli faruq tace wlh yaya nima indai anty ta tsaida haihuwa nima tsayarwa zanyi"
Fada faru ya fara ta inda yake shiga batan yake fitaba daga karshe ma wucewa dakinshi yayi yabarso jugum"
Kan kujera naziya ta koma ta zauna cikin damuwa tace nihilah tashi ki bishi kibashi hakuri"
A'a nikam bazani ba ai kece kika bata mai rai ke yakamata kibashi hakuri"
Nihilah kin manta yau kwanan kine?
Cikin ido nihila ta kalleta sannan tace ba mantawa nayi ba, inasane, amman wlh na barmiki shi har na haihu inyaso kema idan cikin ki ya tsufa lokacin na haihu saina karbe Ki"
Hmm nihilah ni zakiyiwa wayo, kika sani ba kona tafi nabar mikishi"
Cikin mamaki nihila tace kitafi zuwa ina? ai duk inda zaki kafata kafar ki ni ai idan kika barni da ya faruq kin barni da aiki ne, inyi yaya dashi"
Dan murmushi naxiya tayi sannan tace nihilah to yanzun idan na mutu fah ?
Innalillahi wa inna ilaihir raju'un nihila ta fada tana dafa kirji tace anty harkin fadan min da gaba, dan Allah karki kara irin wannan mgnr"
Dariya naziya tayi sannan tace gsky nihilah ke matsuraciya ce.....
Mn yazeed
鉂勷煉︹潉馃挦鉂勷煉�
*ASIRINSA YA TONU*
鉂勷煉︹潉馃挦鉂勷煉�
鉂勨潉鉂勨潉馃挦
*By*
鉂勨潉鉂勷煉�
*Fadeela Lamido*
鉂勨潉馃挦
鉂勷煉�
鉂勨潉馃挦
*Page 101*
鉂勨潉馃挦
*Kafin nakarkare saina mika sakon jinnata ga waddan group's dake kasa*
馃憞馃徎
*Fadeela Lamido Novels*
*Taskar Billy Galadanchi*
*Asirinsa Ya Tonu Fans*
*Asirinsa Ya Tonu Fans 2*
*First class women's*
*Mata Adon Gari*
*Melody novel group*
*Hamagee,s novel*
*Home of novels*
*Mijina sirrina group*
*Mukaru da juna*
馃憤馃徎馃憤馃徎馃憤馃徎馃憤馃徎馃憤馃徎馃憤馃徎馃槝
*Gaisuwa da fatan alheri geruku gareku fasihan marubuta, mu*
馃憞馃徎
_*Zeenaseer*_
_*Bilkisu galadanchi*_
_*Faty Afreen*_
*_Feedo_*
*_Cwtjiddah_*
_*Aisha Aliyu garkuwa*_
*_Deeje waxiri_*
*_Mmn Farida_*
*_Miss xoxo_*
*_Bebendeen_*
*_Yar mutun Wudil_*
*_Hamagee_*
*_Mum nauwal_*
馃槝馃槝馃槝馃槝
*Bari nayi amfani da wannan daman najinjinawa wannan sharariya marubuciya wato*
馃憞馃徎
*馃憫Safiya Abdullahi Hukuma*
馃弳馃弳馃弳馃弳 I love u so much馃槝
Koda nihilah ta shiga gurin faruq zama kawai tayi ta rafka uban ta gumi, tun yana kallonta ta gefen idon shi har ya gaji ya mike ya isa gareta"
Cikin yanayi me nuna kulawa yace"
Meya faru kika rafka uban tagumi haka, saika ce kin rasani?
Jikinta asanyaye tace anty naziya ce ta bani tsoro"
Murmushi yayi kadan sannan yace, kinga tuntuni nake cemiki ki rage tsoro kinga gashi yanzun naziya ta fahimce Ke matsoraciya ce tasamu abin tsokana tana kwasan dariya, me tace miki?
Kanta asa tace cewa tayi wai yanzun idan ta mutu yaya zanyi?
Shiru yayi yana nazari zuwa can yace toh meye abin tsoro banda abinki"
Da sauri ta kalleshi sannan tace yaya mutuwa fa tace? ni gaskiya naji tsoro kuma mgnr tasani atunani yaya dan Allah yanzun idan ta mutu ya zanyi?
Shiru yayi zuwa can yace, yaya zamuyi dai zaki ce"
Shiru sukayi gaba daya kowanne jikin shi asanyaye zuwa can nihilah tace yaya nidai idan anty ta mutu kuka zantayi kuma bazanji dadin zama agidan nan ni daya ba, karashe mgnr tayi cikin hawaye"
Cikin sanyin jiki faruq yace jiba nihilah ki kwantar da hankalin ki dan naziya tayi zancen mutuwa bashi ke nuna ta kusan mutuwa ba, ai anason mutum akoda yaushe ya dinga tuna mutuwa, dan haka shi zaisa murage san abun duniya, idan har mutun na tunanin mutuwa na iya zuwa mai kowani lokaci, dole ne ya gyara aikin shi yaji tsoron haduwan shi da Allah, , dan haka wannan ba,a wani abu bane na dade da sanin cewa naziya mutuniyar kirki ce, dan haka nakeson mucigaba da kasancewa da ita, dan halinta yasa ta shiga raina, dan haka nakeson kicigaba da bani goyon baya dan na kwatan ta adalci atsakanin Ku"
Shiru yayi xuwa can ya sake cewa naziya nasan akwai masu zagina da yawa akan irin son da nake miki, bayan bani nasawa kainaba Allah ne ya dasa min sonki azuciyata kuma har yanzun bantajin ya rago ba saima karuwa daya ke, nihilah sonki shine jinina, bani nasawa kaina ba Allah ne ya dasa min, memakon mutane su tayani da addu'a adalci atsakanin ku amman sumin mummunan fahimta, dan haka zanfara musu addu'a Allah ya daura musu son wani bawa nashi dan suji irin abinda nakeji"
Cikin sauri nihila ta rufe mishi baki tare da fadin karka musu yaya kayi hakuri ni zanci gaba da maka addu'a , amman nima ka dingamin addu'a Allah ya rage min zafin kishin ka azuciyata"
Cikin ido ya kalleta sannan yace au nihilah daman har yanzun kishin nanan ne?, aini na dauka ya tafi tuni"
Kirjinshi ta kwanta sannan ta bude baki CIkin shagwaba tace daurewa kawai nakeyi yaya amman wani lokacin inajin kirjina namin zafi ko inji wani abu me nauyi ya tokaremin kirji, wlh yaya dan dai kawai anty ce amman da bazan barwa kowa kai ba, na yadda da ita 100 bisa 100 ahankali sonta yake shigata"
Dariya faruq yayi sosai sannan yace yau asirinki ya tonu, amman dan munafunci shine harkike cewa kinbar mata kwanan ki, sai kina nuna karman baki damu dani ba"
Dukanshi tayi akirji cikin kukan shagwaba tace toh ai kaine jikin ka baya gajiya kullum abu daya, nikuma nafison idan anyi so 1 saikuma abari sai bayan sati 1"
馃槼Babban mgn lallai nihilah baki da lfy zangayawa anty ta neman miki magani"
Haka sukaji kaba da rayuwa cikin farinci da kwanciyar hankali, duk bayan sati 2 faruq ke kaisu gidan umma daga can ya sauke su gidan anty sai dare ya dawo ya kwashesu dadi Anty takeji sosai ganin inda kansu ya hade sosai"
Cikin nihilah ya isa haihuwa komai angama shiryawa jiran haihuwa kawai ake"
Yau ta kama juma'a kuma yayi daidai da ranan da suke zuwa gida, dan haka tunkafin faruq ya fito sun gama shiryawa kowacce da handbag dinta ahannu"
Misalin karfe 7:30 faruq ya fito cikin shirin tafiya office turus ya tsaya yana kallonsu sannan yace"
Ina zuwa haka?
Cikin sakin fuska nihilah tace ka manta yau juma'a?
Eh a,a amman ya na gaya muku Anty taca karna kara kawo ku tunda cikin nihilah ya tsufa"
Naziyace tace toh ai can ma gida ne, mudai dan Allah ka kaimu akwai abin da zamuyi acandi"
Daure fuska yayi sannan ya fara tafiya yana dada taje kanshi da wani dan karamin kum dake hake hannun shi"
Cikin sauri nihilah ta rikeshi da da duk hannuwanta tana buga kafa take cewa dan Allah ka kaimu mana idan yaso daga wannan karka kara kamu"
Daf take dashi har cikinta na dungurin shi, cikin sauri yasa hannuwan shi yarike hannunta data kama kayanshi yana fadin haba nihilah zaki yamutsamin kaya"
Kara matsewa tayi tana fadin in sakeka ka gudu"
kallon naziya yayi data koma gefe tai zaman ta yace naziya zoki tajemin kai, sauri nake, ko kallon inda yake batai ba, saima juyar da kanta tayi gefe"
Toh fah ya fada azuciyar shi sannan ya juya ya kalli nihilah sannan yace nihilah sake ni, kinga yau juma'a kureran lokaci ne.....
Begama rufe baki ba ta sakeshi sanna ta nufi daki cikin sauri,
Bayanta yabi da kallo sannan yace azuciyar shi wa innan yaran idan bakaisu nayi ba yau zasu gana min azaba, domin abun 2 zai hadun min dame fushin munafukai dame fushin 'yan daba, gwamcewa yayi ya kaisu, dan haka ya juya ya kalli naziya yace kusameni amuta"
KO amatar kin kulasu yayi yanajin su suna hira har suna dan sakoshi ciki, amman yayi banza dasu dan haka suma sukasha jinin jikin su fushi yake dasu, dan haka jikinsu yayi sanyi sosai"
Suna sauka amotan ya juya abinshi batare daya ce musu komai ba, dan haka jikinsu babu kwari suka shiga gidan"
KO acikin gidan nihilah kasa sakin jiki tayi, ji take inama batazo ba, itako naziya tuni tacigaba da harkokinta"
Lura anty tayi nihilah kamar tana cikin damuwa dan haka ta kalleta tace nihilah yaudai nakula bakijin dadi jikin ko garin?
Sunkuyar dakai tayi sannan tace anty yaya ne yau ya tafi yana fushi damu"
Me kuka masa ?
Ahankali tafara fada mata duk abinda ya faru ba abinda ta rufe mata"
Naziya anty ta kwalawa kira sannan ta hadasu gaba daya taita musu nasiha"
Misalin karfe 12:00 nihila ta farajin maranta na mata cewo bata gayawa kowa ba ta wuce dakin inna hajiya ta kwanta ita daya dan ta baro inna hajiya afalo"
Murkususu taitayi zuwa can ta sakko kasa ta tsuguna, hawaye ne ya fara zubo Mata, gawani zufah dake keto mata"
Inna hajiya ta sayo kai ganin nihilah haka abin yayi matukar bata mamaki, dan haka ta bita da kallo"
Ganin murkususun na kara yawa yasata kiran anty babu bata lokaci anty shigu tana tambayan lfy nuni ta mata da nihilah cikin sauri ta karasa garen ta tana fadin me zan gani haka?
Gyarata anty tayi ta kwantar cikin tashin hankali anty tacewa inna hajiya inna nakuda take kuma inaga kan muje asibiti ta haihu"
Cikin sauri inna hajiya ta fita tana kwalawa naziya kira, aguje naziya ta taho tana tambayan lfy"?
Maza kije gida ki dauko kayan haihuwa nihilah nakuda take"
Tunkafin naziya tabar gidan azaba ya ishe nihilah banda hawaye babu abinda take, zuwa can ta fara sambatu cikin yanayin dake nuna mutum yana cikin azaba tace"
Anty nagode haka kikasha wuya kafin kika haifeni, nagode miki Allah yasaka miki da alheri, nikam bazan iya ba mutuwa zanyi idan yaya ya dawo kice mishi ya yafemin.....
Bakinta anty takaiwa duka tare da fadin nifa banason surutu, addu'a akeyi adaidai wannan lokacin ba surutu ba, ki roki Allah ya rabaki da abinda ke cikin, idan kina da wata bukata ma kina iya fadawa Allah, kuma acikin zuciyar ki zakiyi ba cikin hayagaga ba"
Shiru tayi bata sake cewa komai ba dan haka anty ta matsa saitin kunnenta tace ki roki Allah ya rage miki zafin kishin nan naki"
Dukda tana cikin wani hali amman taji dadi da anty ta tuna mata dan haka taji gaba da kaiwa Allah kukanta, befi minti 5 taji wani matsanancin azaba tare da kukan jariri"
Alhamdulillahi Anty da Inna hajiya suka fada atare sannan anty ta dauki jaririn ta nadeshi azani na mijine kato"
Lokacin da naziya ta dawo nihila hartayi wanka, hajiya b na gefe tana wanke jaririn"
Farin ciki ta shiga ba kadan ba, taita kiran faruq ta fadamai amman yaki daukan wayar"
Anty ko batace zata kirashi ba harkokinta taji gaba dayi"
Da musalin karfe 3:00 umma ta iso ganin jikanta ita da bashir suka iso"
Cikin farin ciki bashir ya dauki yaro bayan ya gama kare mishi kallo yace anty ni zanyiwa yaron nan huduba"
Cikin murmushi tace ai haka ne yafi dacewa bashir saidai dayake kasan Yaro, wata kilama yasa masa suna tunkan yazo nuniya, waigawa tayi takali naziya tace ko?
Sunkuyar dakai naziya tayi ta kasa cewa komai, saboda nauyin umma da takeji"
Tuni nihilah tayi bacci dan haka sukaji gaba da hiransu cikin farin ciki"
Suna cikin haka faruq ya shigo kamar anjehoshi saidai yana ganin umma ya saki kofar ya koma, bayan kofar sukabi da kallo, cikin sakin fuska umma tace shigo abinka, mu tafiya ma zamuyi"
Turo kofar yayi ya shigo kanshi akasa ya gaidasu ya wuce can gaban gadon da nihilah ke kwance naziya agefenta ya tsaya ya kure nihilah da ido"
Bashir ne ya miko mishi yaron ya rungume shi ajikinshi tare da subatan shi sannan ya fara tofamai addu'oi"
Muryan bashir yaji yana fadin danaso namai huduba amman anty tace abari ka dawo......
Bekai ga rufe baki ba faruq ya mika mai yaron "
Cikin kankanin lokaci yamai haduba sannan ya dago yace sunan shi Ibrahim"
Allah yaraya gaba daya mutanen dake falon suka fada badan faruq daya fada azuciyar shi"
Hannunshi ya zuba cikin aljihunshi sannan yayi gaba yana fadin bashir zomuje anty na wuce sai gobe"
Muryan umma yaji tace Yaro, Karo na farko kenan daya tabajin anty ta kirashi aruwan shi dan haka cikin rawan jiki ya juyo yana kallota"
Ita ma cikin ido ta kalleshi sannan tace naji kace bashir yazo ku tafi matan naka fa?
Fuskanshi daure yace umma idan sungama abinda sukeyi zasu dawo ai"
Itama cikin daure fuka tace wannan ba mgn bace, su sukace baka akwai abinda suke"
Kanshi tsaye yace eh umma dama abinda suka shirya kenan, shiyasa suka matsamin saina kawosu, yanzun inda ta haihu ahanya ya zanyi dasu, wlh yanzu ba abinda suka iya inbada munafunce2"
Anty ce tace kai ne babban me laifin ai ko bance maka karka kara kawosu ba? Koko so kake kacemin sunfi karfin ka?
Kusan haka din ne anty dan kona hanasu hademin kai suke suyita fushi, ita nihilah dan tayi sati bataimin mgn ba bawani abu bane awajenta, ta iya gaba, itako naziya Yar dabace, wuka take daukowa......
Tunkafin ya karasa sukasa dariya hatta umma saida ta kauda fuskanta ta dara, anty karasa dariyarta tayi da fadin toh Allah ya shirye ku harkai dan kazama babban banza"
ummace ta tashi nihila ta sanya mata hijabi sannan ta roko hannunta sukayo waje"
Hargida umma ta rakasu sannan bashir ya maidata gida"
****
Naziya ce taita kula DA nihilah har akai suna"
Ranan sunan da daddare faruq ya matsawa naziya waishi yau zai koma dakin nihilah batace komai ba saima dariya dataitamai ganin inda yake wani irin abu kaman karamin yaro waishi adoleshi shagwaba yake mata takaishi wajen nihila, dukda tasan wasa yake mata amman abin dariya yake bata"
Lallashi take kaman tana lallashin yaro ahankali take shafa kanshi dariya nacinta tace to tashi muje"
Kafada ya make wai saidai ta dauke shi, mikewa tayi taita taitai ta daukeshi ta kasa saida yaji tana haki sannan ya jawota kangado ranjuna suka shiga farantawa bayan sun natsu hankalinsu ya dawo jikinsu, wanka suka fesa sannan suka nufi dakin nihilah"
Cikin fara'a nahilah tace au har yazun bakuyi bacci ba?
Naziya ce tace Hmmm wani bacci aini yau naga tabara wajen wannan yayan naki wai shi yau adole gurinki zai kwana"
Wasa yake miki nikam wlh kutashi ku koma sai nayi arba'in
Cikin daure fuska kaman bashine ya gama tabara ba yace ban yadda ba, bazan iya ba wlh nadaiyi na kwana 7 ya isa ha daga yau zamu cigaba da kwana 2 ....
Naziya batajira ya gama ba tace saida safen ku"
Tana fita nihilah tace yaya wlh har yanzun bani da tsarki ka tashi ka bita"
Ke wai me kika mai dani ne ? dole sai zakiba ni wani Abu zanso kasancewa ajikin Ki? , ni kwanciya kawai nakesonyi tare dake"
****
Bayan wata 4 Ibrahim yayi wayo sosai cikin naziya ko ya girma yayi wani irin tsini ajikinta duk ya kunbura"
Daga nihilah har faruq hankalin su atashe yake kullun addu'an su Allah ya sauki naziya lfy, gashi yau bikin bashir saura kwana uku zai auri yar autan hajiya mariya zainab"
Faruq da bashir keta shirye2 duk da cewa hankalin shi ba akwance yake ba, amman dolle ne ya shiga cikin bikin bashir
Ranan juma'a aka daura aurn bashir da zainab kowa ka kallah yana fara'a amman banda faruq da nihilah"
Ana tsaka da biki nihilah ta fito tana ta sauri"
Faruq na cikin abokansu ya hango wucewan ta"
Cikin sauri ya maki ya fara kirata ta, ko waigowa batayi bareta kallshe dan haka yashi cikin motar shi ya isa gareta "
Nihila yaya meye ya faru?
Cikin kuka tace yaya bazan iya zama ba, munbar anty itakadai agida gabana faduwa yake"
Shigo mutafi yace dan shima tun safe gabashi ke faduwa"
KO acikin mota nihilah banda kuka babu abinda take, dan haka suna isa tashige ciki"
Cikin jini suka sameta male male cikin mummunan tashin hankali faruq ya wawushita ya sayata amota suka nufi asibiti"
Emergency akashiga da ita nihilah duk ta fita haiyacinta kayanta duk jini hakama na faruq"
Suna tsaye agurin har karfe 8 nadare amman babu wadda ya fito daga cikin likitocin da suka shiga ciki, adaidai lokacin bashir ya fara kiran faruq awaya yana fadin wannan wani irin wulakanci ne, tun dazun muke jiranka usman yacemin kaje ka mayar da bir kitacciyar matarka gida, mujira2 kuma baka dawo ba"
Ganinan zuwa kawai faruq yace dan bazai iya wasa ba kaman yadda bashir yaso"
Juyawa yayi ya kalli nihilah sannan yace nihilah inazuwa bari naje na raka bashir gidanshi yanzun zan dawo banaso na lalata mishi wannan daren me mahimmaci arayuwan shi, yanzun idan yasan halin da muke ciki nan zaizo ya tare"
Gida ya koma ya canza kaya saidai daka kalleshi zaka gane abirkece yake"
Agidan bashir din ya samesu dan sungaji da jira koda ya shiga har sun gama suna kofarin fitowa wucesu yayi ya shiga cikin falon bashir na ganin shi ya daure fuska hakuri yaita bashi sannan ya mushi fatan alheri ya koma asibitin"
Saikusan 12:00 da dare likitan ya fito yana share zufa office dinshi ya nufa yayinda bashir ya bishi abaya"
Bayan sun zauna likitan yace Alhamdulillahi muyi nasaran Ciro abinda ke cikin saidai uwar ta jigata sosai, akwai yuwar zata iya rayuwa saboda hunkucin Allah babu inda baya kasancewa amman mawuyaci ne"
Innalillahi wa inna ilaihir raju'un shi faru ke maimaitawa hakuri likitan yaita bashi koda yaje ya samu nihila kasa daurewa yayi cikin kuka yake gaya Mata abinda likitan ya gaya mishi abin da be fahimta ba tunkafin ya karasa tayi suman tsaye kokarin faduwa take dan haka tareta, da taimakon ma aikatan asibitin suka sata agado sanan su ka fara bata taimakon farko"
Cikin Ikon Allah ta farfado mikewa tayi zubur tare da da fadin yaya inason naga anty naziya zangaya mata karta mutu ta barni na dade da gayamata bazan iya zamman gidan ba idan har batanan wlh yaya ka fadin mata kartai mana haka kace mata zakai fushi da ita indai ta mana haka"
hannu Yasa ya rufe mata baki cikin dakiya yace nihilah addu'a zakiyi ba surutu ba tashi muje kiyi alwala muyi sallah, sannan murokan mata sauki awajen allah"
Haka ko sallah suka kwana yi amasallacin dake cikin asabitin"
Washegeri kuwa daka kallesu zakaga duk sun rame sunyi zuro2 karfe 7:30am ya kira daddy ya gayamai halin da ake ciki, cikin kankanin lokaci asibintin ya cika makil"
Tsaye suke jigum2 kowa hankalin shi atashe likintan ne ya fito fuskanshi dauke da murmushi tunkafi ya karasu suka isa gareshi"
Alhamdulilah yace zaku iya shiga ta farka"
Aguje nihila tashiga kuka da dariya dauke akan fuskanta saidai tana isa gaban gadon ta samu faruq tsugune agaban naxiya tayi mamaki yadda akayi ya rugata zowa"
Kwakume suke da naziya, su anty suka shigo da katuwar jariyar naxiya ahannu su, faruq ne kadai ya amsheta amman nihilah kin amsata tayi tare da gallawa faruq harara dan me zai dauke ta"
Fuskanshi dauke da murmushi yace Allah ya huci zuciyar ki, amata uzuri ba laifinta bane ko mai mukadari ne daga Allah馃憜馃徎"
Satin naxiya 2 aka sallameta suna akayi nagani da fada duk cikin kulawan nihilah komai yake tafiya, yariyan taci sunan anty wato khadija"
*Bayan shera biyar*
Sadiq na hango cikin taran jama'a yana raira karatun al Qur'ani"
Tsaye nayi inakallon yadda yaron dan shekara 13 yake raira karatu haka"
Bayan yagama ya koma cikin dalubai yan uwasa, ya zauna sai alokacin na lura ashe sauka sadiq yayi, faruq na hango cikin fararan kaya gefenshi nihilah ne da naziya ne, sun sashi a tsakiya wasu kyawawan yara ne jikin nihila farare tas duk mata ne, ga dukkan alama yan buyu ne"
Jikin naxiya ma yaro ne karami saidai na nihilah sunfi wayo, lokacin da aka kira sadiq domin karban shahada bashir naga ya taso ya karba amtsayin shi na mahaifin sadiq din"
Yana amsa ya koma gurin da matar shi zainab ke zaune da yaransu biyu mace dana miji"
Bayan taron ya tashine na kula ashe kusan dangin gaba daya suna gurin, haduwa sukayi gaba daya sadiq atsakiya aka daukesu hoto"
Bayan sungama bashir yaja matarshi ya shige mota faruq ma hannun naziya ya kamo amman saita goce tana zaro ido tare da fadin baka ganin idon su daddy ne , kowa na kallon mu"
Tsaki yaja sannan ya matsa ya jawo nihilah jikinshi ba musu ta fada kirjinshi hannun su sarke da dana juna kuka nufi shiga mota"
Umma ce ta fara dauke kanta daga kallon su, anty ko binsu da kallo tayi sannan tace Ikon Allah wai yaro da nihilah bazasu firma bane?
Dariya kawai su daddy sukayi suna kokarin shiga tasu motar"
Nihilah ko kanta ta kara turawa cikin kirjin faruq tana fadin I love u so much yayana
*Alhamdulillah*