Tsoho yace Eh Mu'ammar, dole sai da amincewarta zata cigaba da zama dakai, idan ko ta ce bataso banda na wani zabin da ya wuce na rabaku, ka fahinta? Zufa Amar ya fara ko ta ina, yasan babu yadda Islah xatace tana son zama dashi, ya san ta tsaneshi, idan tace ba tason shi ya zai rayu ba ita? Tsoho yace ku tashi ku tafi na sallameku, Mu'ammar ya miqe kamar wanda kwai ya fashewa a ciki, Suraj sai da ya dan ji tausayinshi, Amar ya shige daki ya fada gado ya fashe da kuka wiwww kamar wani mace, Suraj ya shigo dakin ya dafa shi yace Mu'ammar m still mad at u for What u did to my sister, but d choice is'nt mine to make, idan ta amince zata cigaba da zama dakai to falillahi Hamd, idan Kuma ba ta amince ba ina so ka rungumi kaddara,i want d best for my sis, Gobe InshaAllah zan fara processing visa in an ci saa zan samu na tafi kwanan nan don dawowa da ita, shawarar da zan baka shine ka dage da Addua. Mu'ammar yayi murmushi yace Nagode suraj, i knw i've wronged u all, DanAllah ku yafe min, Suraj yace ni na yafe maka, Yace Nagode. Suraj yace bari naje naga babynah, Mu'ammar yace dadin abun ma ina da nawa babyn, suraj yace a samu dai a shirya, Mu'ammar yace kar kadamu lokaci ne.
Kaduna
Ya jawad dan Allah ka shirya ka tafi aiki, yau 2 weeks kenan rabon da kaje aiki, jawad da ya shagala yana kallon fadila tana mai magana cikin yanayi na shagwaba, kamar kar ta daina, ganin yayi shiru ya kura mata ido, ta turo bakih tare da shagwabe wa, shine ka min banzan ina ma magana ko? Da sauri ya girgiza kai yace noo baby, i rather stay at home with u, dan go to work, on the contrary people want me dead, so gwara nayi zamana na kula da mata kar su sa kiyi takaba, coz u'll never get a hot guy like me when i die ya fada tare da kashe mata ido, fadila ta fashe da wani kukan da ita kanta tasan na shagwaba ne tana turo bakih, duk ya tariyo ta jikinsa yana yi shiru baby, tell me wht u want, a shagwabance tace Yaya ka koma bakin aikinka, yace ohh baby, baki ga so suke su hallakani ba takan aikin banza, su kudih ya dama, ni retire ma zanyi, ki kyalesu kawai, ina da kudin da zan kula dake har karshen rayuwar mu, i've gathered enough, ta fara bubbuga kafa tace nidai ka koma aiki, ya ce fine zan koma, but on one condition, tace anything yace ki kalleni cikin ido kice kina sona, ta turo bakih tana kallonshi, ya daga kafada yace toh kar kuma ki dameni da zuwa aiki, ba aiki, da sauri tace Ina sonka, I love you Yajawad, ya Rarrafo gunta yace sbd naje aiki kike fada min haka? Ta girgiza kai tace aa, saboda ina sonka, i love u with all my heart, Jawad ya sake ihun murna ya daga fadila sama yana juyi da ita, ita kuwa sai daria take tayi.
Abuja
Ta shiga kwankwasa mai kofah, Yazayd don Allah ka bude kofa, kayi breakfast, nd u are late for work, Yazayd donAllah ka fito, m worried about u, yana jinta yayi shiru, ya sha giya ya kai kwalba 50 daga jiya zuwa yau, amma bacci yaqi zuwa mai, yanda ya ga dare haka ya ga rana, Maysah kuwa da qyar ta samu bacci ya dauketa a dareb jiya, Yazayd don darajar Allah da manzon sa ka bude, tsaki ya buga, yace ke xabin tsoho kina shiga rayuwata, ki tafi i dont need u, tace naji just open up, ya rarrafo ya bude dakin, Maysah tayi saurin fadawa, duk warin giya ya cika dakin, amma hakan be hanata rungumeshi ba, tana kuka, shima kukan yakeyi, ta ja hannun shi ta wurga shi toilet ta dauko towel ta mika mishi, tace Kayi wanka, ya samu kanshi da bin umarninta, kafin ya fito ta gyara dakin, ta share ta kunna turaren wuta, ta kunna AC, ta ciro mai kayan da zai sa, yana fitowa ya je ya sa wani Jallabiya, tace Yazayd ga kayanka fa a kan gado, ba office zaka ba? Yayi dan tsaki yace ba inda zanje, ya ciro giyarsa ta karshe ya fasa sai sha, tayi tsalle ta fincike, tace shikenan mutum gani yake giya ce maganin matsalolinsa? Kallonta yakeyi yace ke zabin tsoho bani? Tace ba zan bada ba, ko tsoro vata ji ba ta shiga toilet ta tutular da giyan a sink, ya kalleta cikin takaici, ta qaraso gurinsa ta dafa shi sassauta murya tace Ya zayd what happened to u? U look miserable, da karfi ya tureta, what happened to me? I am HIV + dats wat happend to me, What are u even doing here? I tot i told u to leave? Yazayd bazan barka haka ba, nace zan zauna da kai a haka, ya kalleta da sauri, yace ke wai bakin sa meye HIV ba ko? Tace wlh ba sani, cutar da ke karya garkuwar jiki, Yazayd its not d end of d world, u can get treated, please muje Asibiti a rubuta maka magani, idan yaso sai kayi taking preacution nd u'll be alive and healthy, ya kalleta ya watsar yace i dont need any treatments, m dying anyways, tace Yazayd yace kee fita ki kyaleni, da karfi Yace ki fitaaaa, da gudu ta bar dakin sakamakon kukan da ya ci karfinta, ya bi bayanta da kallo, a hankali yace tausayinki nake zabin tsoho, i cannot ruin yourlife, you are still young and innocent, ba zan yarda rayuwarki ta kare kamar yadda tawa zata kare, na so zama dake har karshen rayuwata, don na nuna miki So da Kauna, na nuna ma tsoho Zabin shi Alheri ne, na nuna ma Kowa Cewa Kece Cikon Farincikinah, amma dole zan rabu dake, sabida ina sonki, Ina sonki Ruma, ya sake fashewa da kuka ya fada kan gado yana yi...
3 days Later
Cambridge England
Mamaki ya cikata ganin Ya Suraj a doorstep dinsu, da azama ta rungumeshi Yasuraj, nayi kewanka da yawa shima ya rungumeta, Islahulkhair kinganki haka kika koma? Tayi daria tace Yaya shigo mana ta ja hannu suka shiga, yace Islah ki shirya gove zamu wuce Naija, ta dago kai ta kalleshi, why? Yace Tsoho requests for ur presence, mijinki ya dawo!ta tabe bakih, yace bakiyi mamaki ba, tace yes coz nasan ya na nan, ta kwashe komai ta gaya mai ya jinjina kai, yace toh tsoho yace ba zai shiga hakkin ki va, zabi zai baki, so u choose wisely, tayi murmushi tace i know what i want.
Bayan kwana 2
Maiduguri
Islah durkushe gaban tsoho yace yauwa Islahulkhair, na aika a kira su, ayi komai gaban kowa, kar ace na danne hakkin wani, bazan matsa miki ba, abunda kikeso shi zaayi, idan ba kyason zama da Ammar zan sashi ya sakeki nan take yanke, zaki cigaba da karatunki har na zabi miki wani mijin da na ga ya dace dake, don ba zan yarda da zaman ki haka kurum ba, dole ki sake aure, amma kamar yadda kika sani, ba sauran Samari a gidan nan duk sunyi aure, dole Me aure zan zaba miki a cikin dangi, toh ki Zaba abunda kikeso bayan kinyi tunani, kar ki bari fushi ko daukar fansa ya kaiki ya baroki, Gaban Islah ya fadi, a ranta tace zama da kishiya? Ganin yan cikin gida sun fara shigowa ya sa Tsoho yin shiru.
********
Mu'ammar na so ya hada ido da Islah amma ta dauke kai, ta qi Kallonsa, so yake ya mata fuskar tausayi ko zata ji tausaynsa, cikin kwanan nan ya kasa bacci fargaba ne fal ranshi, ya zaiyi idan ya rasa Islah? Jin Tsoho yace toh Islah, Wani hukunci kika yanke game da Mu'ammar, kin amince zaki zauna dashi a matsayin miji ki koma dakin ki? Ko kin amince a raba aurenku wato ya sakeki? Wannan ba zabina bane, zabin kine, muna sauraronki. Islah ta hau tunani, Amincewarta na nufin ta bar karatunta na Cambridge, karatun da ta ci buri da shi, Baba hassan ya katse mata tunani yace khairi ke muke jira, ta dago kanta a hankali ta fara kallon iyayenta, da kawunninta da gwaggoninta da yayyunta ta kalli tsoho, sannan ta sauko da idanuwanta kan Mu'ammar, a lokacin Mu'ammar idonshi kulle yake, yana karanta duk adduar da ta zo mai bakih. Ta kura mai ido sosai duk abubuwan da ya mata suka shiga dawo mata, tace Tsoho Ina so na koma dakina, ina so na cigaba da zama da mijina, Ina so na samu Aljannata ta sanadiyar YaMuammar, na haqura da karatun, duk dakin a ka dau Alhamdulilah, Mu'ammar da ya daskare zaune, ya kasa tantance me kunnuwansa suka jiye mai, kamar a mafarki ya ke ji, a hankali ya bude idanuwansa fes a kan Islah, ya tabbatar ba mafarki yakeyi ba, Aiko ya takura ya saki Ihuu, yace Waiyoo dadi kasheni. Duk dakin a ka sa Daria har hajia babba sai da ta dara..
_Bibilicious Biebee_
58...Gidan Gandu
Gidan Gandu by Biebee Isa
Mu’ammar be ji kunya kowa ba ya matso kusa da Islah ya riqe hannunta, yace i promise u, ba zakiyi Nadama ba, Ba zakiyi da na sanin zama dani ba, ya kafe ta Idanuwanshi, Islah ma ta kafeshi da nata idanuwan, daman ta dade da yafe mai, so take ta ja ajinta a matsayinta na mace shisa ta dan wahalar dashi kadan, kuma da alamu ta kamu da sonsa sbd yanda ta kafeshi da idanuwanta, da Alamun sun manta inda suke, duk parlorn aka kafesu ds idanuwa, Uncle Abbakar yace kai ku tashi ku bamu guri kun wani tsura ma juna ido, ina basu san tanayi ba, Manyan parlorn sukayi murmushi, Baba hassan yace Mu’ammar kuna iya tafia, nan ma shiru, sai da Hajia babba ta daga murya tace yan soyayyan burauba, to Tsuntsun Soyayyah ma yaci ubanshi. Islah ta miqe a kunyace tafita da sauri, da gudu Mu’ammar ya rufa mata baya duk yan dakin suka hau daria suna yaran Zamani sai abarsu.
Hanyar Sassan Umma hajja tayi, tana sane yana biye da ita, ta share sai da ya sha gabanta tayl daure fuska, shi ko baki har kunne, ya riqo hannunta yace Thanks Angel, sunan da ya kirata dashi ya mata dadi da har bata san lokacin da murmushi ya subuce mata ba, ya matso daf da ita ya shafa fuskarta, tare da kai bakinshi kan nata, taso ta dan kara jan ajinta, amma sai ta share don Mu’ammar din ya fara bata tsausayi. Tsoho ya yanke shawaran Mu’ammar ya dauki matarsa ya tafi da ita gidansa na Zaria gobe, Baba Gambo yace tsoho ya maganar karatun ta? Tsoho yace toh wani karatu kuma bayan yarinya ta yarda zata zauna da mijinta, sai dai ya sama mata ABU zaria. Allah ya basu zaman Lafia Amin.
A ranar su Amira suka diro Maiduguri, chan dare kuma sai ga Jawad da Fadila, dangi sai murnar zuwansu sukeyi, Tsoho kuwa yafi murnan ganin jikokinsa, Barin fadila da ta ji sauki sosai,
Yanmatan su biyar, Hanifa Amira, Bilkisu, Fadila da Islah suka kulle kansu cikin dakin hajia Ama, ni banta ba ganinsu karkashin inuwa daya haka ba suna labarin arziki, sun burgeni matuqa da suka hada kansu, ba zaka taba cewa akwai wani sabanin da ya taba shiga tsakanin da ya daga cikinsu ba, Labari sukeyi suna kashewa suna dariya, ko wacce na bada labarin yadda mijinta ke ji da ita, Fadila tace Allah sarki Maysah, shes d only one missed here, bari na latsota ta hau IMO muyi VideoCall, Hanifa tayi daria tace sai kinsa taji haushi, Bilkisu tace kina so ta sa Yazayd kawota cikin daren nan, fadila tayi daria tace wayarta kashe take, Islah tace Allah ya so ta kam, yau da sai kun sa Yazayd tafian dare, duk suka yi daria. Nan Amira take basu labarin honeymoon dinsu na Paris suna ta kyalkyala daria. A gurin yan mazan ma haka suka su 4 suna labari, just like old times, dama sun kasance masu son junansu, sabanin da suka samu ne kwanakin baya ya sa suka bar kula juna, amma yanzu sun fahimci juna sun roqi juna gafara. Jawad ya kalli Suraj yace Wallahi gwanda da tsoho yayi hadin nan duk nafi ku jin dadi, Suraj yace wlh duk na fi ku dacen mata, Samir yace wlh i dont knw wat wud life be like idan ba Lilsismeerana a ciki ba, Mu’ammar yace bari na takaice muku zance Islahulkhairi ne heartbeat dina, duk suka fashe da daria, Zayyad yace wai Ya labarin Dr Zailani? Shiru ya boye, ko Maysah ce ta boyeshi, Jawad yace bari na latso mana shi mu mai tsiya, yace kashh wayar kashe take, Allah ya so ka Bros duk sukayi daria.
Abuja
Zayd ya rame yayi baqih ya jeme, ya fita hayyancinshi, kwananshi 4 kulle cikin daki, kullum Maysah Sai ta kwankwasa tana mai magiyar ya bude amma ko tankata beyi, sai ta jingina jikin kofar tayi ta kuka, yana jin kukan nan amma sai ya share, dama tuni tayi watsi da skuk dinta, Yau Tuesday zayd ya tashi da farar Safiyya ya tashi da wani irin fever, nishi sama sama kamar zai mutu, hankalin shi yayi matuqar tashi, sanyi yake ji sosai, nishin shi sama sama, Symptoms din kanjamau duk sunyi developing, Maysah ta fito taji yana wani irin tarih hankalinta ya tashi, Ta hau bubbuga kofar kamar zata balla kofar, yazayd ka bude kayi wa Allah ka bude min, ya so bude mata kofar amma bazai iya ba, baida karfin zuwa bude mata, hankalinta ya tashi, da sauni ta wawuri wayarta ta kunna, ta shiga neman layin Yaya Jawad. A lokacin yana tare da babynsa cikin mota, tana zuba mai shagwaba, yace Allah idan ina kiranki kina kin zuwa sai na kwasheki mun koma kaduna yau dinnan, tace Sorry baby, kawai sai mummy ta ga na fita da daddare? Ya murguda baki kamar yanda takeyi yace ba mijinki ya kiraki ba? tace sorry kaki babynah, da mun koma gida kaga daga ni sai kai koh? Da sauri yace to mu tafi gidan mana, tace haba ko 1 week bamuyi ba fa, kafin yayi magana wayarsa yayi kara, ko da ya duba Maysah ya gani, yayi murmushi yace ga matar yaya, ya dauka hello Sis Inlaw, cikin kuka tace YaJawad, yace Maysah me ya sameki? Tace yazayd ne, he’s bin sick, ya kulle kanshi for days, nd yanzu yana nishi sama sama, i can feel his heart beat yanzu haka, i’m afraid he’s dying, YaJawad ka taimaka, Cikin rudu jawad yace ina Maiduguri, but yanzu zan taho as fast as i can, gani nan zuwa, ki kwantar da hankalinki, he’s going to be alryt kinji, ya kashe wayan ya kalli fadila da ta tsura mai ido, yace baby ki koma cikin gida, kice musu na tafi Abuja, tace baby m coming with u, yace noo,tace pls, yace i dont have tym to argue uo staying here nd dats final, ki bari inje kinji? ta turo bakih tace Allah ya kiyaye hanya be safe, yayi murmushi dats my babe, ya bata kiss ta fita a motan tana daga mai hannu, shi kuma ya ja motar ya bar gidan kamar zai tashi sama, Jawad Allah ya tsare hanya.
Abuja
6:45 Jawad ya iso Abuja, sai da yaje ya dauko wanda xasu balla kofan don sunyi waya da Maysah ta shaida mai har ynz be fito ba, ta ma daina jin motsin shi, suna shiga gidan su ka shiga balla kofar, basu sha wahala ba kofar ya balle, rige rigen shiga dakin sukayi, Chan Maysah ta hango shi chan kasan gado duk ya fita hayyacinshi, da alamun rai a jikinsa amma bai motsi, da sauri Jawad yaje ya ciccibi Zayd ya rungume, ya na hawaye don ya tsorata da yanda yaga Zaid, what happened to u brother? Maysah tace i will brief u, buf we hve to take him to a hospital, Jawad ya dago shi, yayi waje dashi, maysah ta rufa mai baya, bayan mota ya sa shi, Ya ciro kudin da be san yawansu ba ya ba masu balle kofa, Maysah ta shiga motar Jawad ya ja motar su ka bar gidan, A hanya Maysah ke ba Jawas labarin abunda ya faru, ran jawad ya baci hankalinshi ya tashi yace wlh dana ga Badiyyar nan, ba abunda zai hanani kasheta. Maysah tace Yajawad ga wani asibiti nan, da alamu private ne,da sauri ya sa trafficator ya shiga asibitin, nan da nan aka karbi Zaid akayi Emergency dashi suka shiga bashi taimakon gaggawa, har sai da zaid ya farfado ya dan dawo hayacinshi, Zaid ya bude idonsa ya ga Maysah da Jawad a tsaye, ya fashe da kuka, Jawad yayi saurin rungumeshi, Zaid yace m dying bro, jawad yace no u are not, Zaid yace ni HIV+, Jawad ya girgiza kai yace i cant believe it, i refuse to believe it, Ya kalli Maysah yace anyi mishi test? ta girgiza kai ta na hawaye, to wa yace yana dashi? Zaid cikin wahala yace kar ka bata lokacinka danuwa na, ina dashi, Jawad ya buga tsaki ya juya yace da Nurse ta kira mai Dr, tace sorry sir, Dr sai 8 yake ganin patients, we can do anythng before he comes, what do u want? cikin daga murya Jawad yace get me The Doctor, nurse jiki na rawa ta fita. Bata jima ba sai gata ta dawo da Dr. jawad ya miqe ya bashi hannu, yace Dr pls help my bro, Dr ya kalli patient din ya zaro ido Dr James yace Dr Zailani? What happened to him? I’ve bin trying to reach him for days, briefly Jawad ya mai bayani, da sauri Dr james ya fita sai gashi ya dawo da wata nurse ture da wani wheelchair yace a daura Zaid suka fita, su jawad suka bisu a baya, wani restricted dakih suka shiga, Dr James ya diba jinin zaid da kanshi ya shiga testing jinin, sannan ya tura Jawad cikin wani Engine da zai tantance duk wani ciwo da cuta da ke jikinshi. Ya kalle su yace dis will take some minutes, Jawad ya rintse ido Maysah ta shiga zuba adduoin da ya zo bakinta, bayan kamar mintuna sha biyar machine din yayi kara, alamun ya gama bincikensa, har printout ya fito, Dr james ya dauki takardan ya ce Dis one is cleared, Everything is fine her, but i can see a minor ulcer, hakan ya faru ne na rashin cin abincinshi nd advisively yadaina shan giya coz zai iya jamishi wani ciwon, ba abunda suke son ji ba kenan, Jawad yace Dr HIV test zaka mai, we careless abt wadannan, Dr James yace just a minute, chan dan qaramin machine din yayi kara, hakan ya sa su duka maida hankalinsu gurin Dr james, Dr James yayi wani murmushi yace Dr Zailani, Congratulations, you are HIV negative,inshort u dont have any blood disease in you. You are all Okay.
_Bibilicious Biebee_
5⃣9⃣ 🏡Gidan Gandu🏠💕Biebee Isa💕 Zaid ya tashi da karfinsa, yace Dr, m HIV free? Dr James yace Yes, you are free frm anytype of Disease. Ihun murna Zaid ya sake, Maysah hawayen farinciki take, Ta na ma Allah Godia, Jawad ma farinciki ya bayyana a fuskarshi, Dr James yace Dr Zailani, m suprised y u dint bother to test ursef, jus bcoz uo wife is + it doesnt mean dat uo are positive too, ya kamata ace kasan hakan, Zaid yace Dr, the moment u told me abt her, i forgot everything, komai dauke ya min akai, kawai ni na sadakas ina da HIV, amma Alhamdulilah, Dr yace dama nasan babu, but to be more sure after 3months za a kara wani test din don tabbatar wa. Yace Ok, dr james ya rubuta mai maganin zazzabi, yace kuma ya kiyaye cin abinci, Ok Dr, can we go now? I have to admit u, no pls, i cant stay here anymore, Dr yayi daria yace ohh, ynx ka gane kan ka har kankamba ake ma Asibiti nah, yayi daria, yace toh ai na ji sauki ba abunda kr min ciwo, kaga gwara mu tafi, Dr james yace toh An sallameku. M expecting to see u at work tomorrow, Zaid ya marairaice yace m sick sir, kuma da na warke i zan zauna a gida kawai don na kula da my Amazing wife ko Zabin tsoho?, Maysah ta kai kanta kasa don kunya, duk sukayi daria, Zaid da kanshi ya kai kanshi kasa gurin da Jawad ya ajiye motarsa, don wani karfi yazo mai, dama fargaba ce ta maida shi haka. Suna isa gidan Jawad ya zube a parlo, Maysah ta yi hanyan kicin tace bari ta hada abinci, Zaid ya shige toilet don ramuwar wankan da baiyi ba na kwana 4...
Indomie ce ta dafa musu, haduwa sukayi kan table duka, zuba ma Zaid ba tare da ta kalleshi ba, tundazun yake son karantar ta, fir taqi yarda su hada ido, Fira sukeyi Jawad na basu labarin dawowan Mu'ammar, Xaid yace muma dai gobe za muje Maiduguri, Maysah ta dago kanta suka hada ido aikuwa idon zaid akanta, da sauri ta kawar da kanta tana murmushi. Wayar Jawad tayi qara, yace ohh god, ya dauka, yace hello baby, m so sorry, fadila tace shine kaki nemana koh? Jawad ya shiga bata haquri, yana wani narkewa yana shagwaba, yana fada mata how much he missed her, baki bude Zaid da Maysah suke kallonshi, ji yanda yake magana kamar mace, Jawad ya kalli zaid da matarshi ya murguda musu bakih, yace baby bari naje daki, wannan yayan naki da matarsa sun sa min ido, Zaid ya kaimai dukkan wasa, yace kato da kai kana shagwaba, jawad ya sa handsfree yace baby kinji bros nace min kato koh? Fadila tace ravu dashi baby,ai kasan ka fi jariri zama baby koh? Zaid ya bishi da gudu shi kuma ya shige dakih yana daria. Maysah ma darian ta ke, Zaid ya tako har gabanta ya na mata wani irin kallo, da sauri ta tashi ta fara hada kwanonin da suka bata, Zayd ya riqe hannunta ya juyo shi gareta, ya hada idanuwansu, Zabin Tsoho kin qi kallo na, kin ki nuna min farincikin da kike ciki na rashin samun cutar nan. Yace i am so sorry for pushing you away, i dint mean to hurt u, but i want u to understand that its for ur own good. Maysah tayi murmushi tace na fahimceka va sai ka min bayannin komai ba, Zaid yace dole na fahimtar dake, don kar kiyo tunanin wani abun daban. Yanzu gobe zamuje na kaiki gurin tsohonki koh? ta gyada kai, tace nagode, Zaid ya hadeta da jikinshi ya rungumeta tsam, a hankali ya rada mata a kunne yace thank u for everything, i pushed u away but u stayed, kinsan matsala na amma kika yi kasadar zama dani, u were willing to damn d consequences nd take d risk, i cannot afford to loose u, Zabin tsoho i cannot live without u, U are a Blessing to my life, I love you Rumaysah, Maysah da hawaye ya gama wanke mata fuska, ta qara rungumeshi tsam, farinciki take tayi, tana gode ma Allah.. A rannan ta ga soyayyah a wurin Zaid har ta na ta mamakin dana Zaid yana magana?
Maiduguri
Motarsu na tsayuwa fadila tazo ta rungume Jawad shi kuna ya dagata sama, baby i missed u, Zaid yace ku dai kuka sani, da sauri Fadila tazo tana dari Yazayd ina wuni ya amsa yace sai ynz aka ganni? Tayi daria ta rungume Maysah, tace sannu da zuwa Maysanmu tace yauwa Eleerhnmu,Baby zo ki cire mun wani abu a ido da sauri fadila tayi kan Jawad tana sannu muga idon, Zaid ya kalli Maysah ya girgiza kai yace Wadannan koh? Tayi daria, Handbag dinta zata dauka Zaid yayi saurin dauka, ya rataya shi a hannunshi, Sannan ya juya gun fadila tace ke da mijinki ku kwaso mana kaya idan kuna gama love din, ya kama hannun maysah ya riqe, tace Yazayd ka bani handbag dina, ya kashe mata ido yace come nd get it, tayi murmushi, sukayi hanyar Sasshen tsoho hannunsi riqe da juna. Sukayi Sallama. Tsoho ya tashi ya hade su biyu ya rungume yana hawayen farinciki, Zaid yace tsoho naji jikinka da zafih, lafia? Tsoho yace kai tafi chan, kalaw nake zaka ja min wani zafin jiki. Zaid dai ya share, suka zube kasa suna kwasar gaisuwa...
******
Su duka 12 su na zaune gaban Tsoho, Kallo daya zaka ma Tsoho kasan cewa yana cikin farinciki, murna, da Annashuwa. Tsoho yace Alhamdulilah naji dadi, kun bani mamaki, ina mai Alfahari daku, Ina mai farin cikin ku nawa ne, Da farko zaku ga kamar tsana ce ya sani hadin auren ku da waenda kuka ki jini, ko ku ka tsana, toh ba haka bane, Na yi hadin nan ne don sama muku dauwamamen farinciki tsakaninku, Matayenku sune gatan ku, sune abun Alfaharinku, sune Rufin Asirinku, ya nuna Mu'ammar yace matar da ka tsana kamar me itace ta zama me ceton ranka don jinin jikinta ta baka to Islahulkhair itace GATANKA, kai kuma Surajo Bilkisu ta tsare maka kanta da rayuwar aurenta duk da tsanar da take maka amma hakan be sa ta kauce hanya ba, ka ga kuwa itace abun ALFAHARINKA, kai Zayyad na san kai ba ka zafafa abun ba tun farko, ka yi haquri ka riqe matarka da mutunci, baka ta ba kawo kararta ba, ka shanye duk wasu bakin cikin da ta ke dasa maka, ni ina alfahari da kai, sbd duk cikin zuriyata babu mai sauqin hali kamarka, ta dalilin haka yasa Allah ya jarrabeta da sonka, gashi kuwa yanzu son ka kamar ya haukatar da ita, ya kalli Hanifa duk sukayi daria, Tsoho yace Hanifa Zayyad ne NISF HAYAT dinki, ya kalli Amira yace mutane da yawa sun dauke ki mara lafia, sbd hallaiyarki ta neman magana, fada, da rashin ta ido, ni nasan ba haka kike ba, nasan Jikata mai hankali ce, nasan ke me ta ido ce, na san ke me son a zauna lafia ce, Shi ya sa na baki Samir, Don nasan shi yafi kowa sonki a da har ma a yanzu, shi zai kula dake, Samir shine HABIBI na gaskia. Ya kalli Jawad yace Bayan aurenku sai na fara tunani anya banyi gangancin hada abokan fada aure ba? Mata da zafin kai take, miji da zafin kai yake, tuni na ke kasa kunne naji an kirani ance daya ya halbe daya, nan ma akayi daria, amma sai labari ya sha bambam, wai ashe kawar fada ce ta amsar ma abokin fada bullet, kuma a lokacin ba sa shiri, sai ynz na gano cewa bawai shiri ne ba kwayi tun farko ba, kun kasa gane cewa son junanku kuke tun farkon haduwan ku da juna, amma kiyyaya ya hanaku gani, tabbas ku Abin KWATANCE ne ga Al'umma, ya kalli Zaid, yace Zaidu na tsoho, aurenka da badiyya rubutaccen alamari ne, ido na sama ka sabida na san ba a hayyacinka kake ba, aiki sihiiri ke dauwainiya da kai, amma sai na ce bari na bari duniya ta koya ma hankali, na barka ka aureta, ko da ba ka samu ciwon nan ba, amma ka ji jiki, don fargaba ya maida ka wani abun. Tun filazal na san cewa ba wacce ta dace da kai Sai Rumah, abu daya ya banbamta ta duk sa'ointa, Haquri, na san cewa ba wacce zatayi haquri da halayyen Zaid duk cikin saointa sai Ruma, duk da kai baka damu da ita ba don idon ka na kan Badiyya, ta zauna da kai, ta yi haquri da halin da ta tsinci kanta a cikin gidanka, ta ma matarka da sirikarka bauta, ta tsaya kusa dakai da kake tunanin lokacin rabuwarku tayi. Zaid, Rumaisa'u ce _GATANKA_ itace _SIRRINKA_ itace ABUN _ALFAHARINKA_, itace _RAYUWARKA_. Toh farinciki nah shine yanxu duk kun gane abun da nake son cimmawa a farko, kun ga hangen da nake muku? ku kasance masu rufama juna asiri, ku dauki juna daya ba bare a cikin ku, banda nuna wannan ba dan Sashen mu bane to ba ruwana dashi, duk daya kuke a guriba, dukkanku nawa ne, inasonku duka, ku kula da junanku, ku tsaya ma junanku a matsalolinku, a tare suka ce InshaAllah Zamu zama abunda zakuyi Alfahari damu, Suraj yace tsoho Allah ya ja da rai, ya nuna maka jikokin mu, Tsoho yace anya kuwa surajo? Na tsufa da yawa, Allah ma ya sa naga yaranku, suka ce zaka Gani InshaAllah, Jawad yace Tsoho Zabinka Alheri ne wlh,dama ka kara xaba min wata, ka ga sai na ga Alheri masu yawa ta kowani gaba, Fadila ta wurga mai harara, da sauri yace sorry Baby dama Misali nake badawa. Duk sukayi dariya yace mun gode da ziyarar da ku ka kawo mana, ina so ko wanne ya shirya ya koma gidansa da bakin aikinsa zuwa Ranar Jumaa, Allah ya muku Albarka, suka amsa da Amin, duk suka tashi, daya bayan daya suke rungume tsoho, yana sa musu Albarka.
_Bibilicious Biebee_
6⃣0⃣ 🏡Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕fita suka fara yi, Tsoho ya cire bakih ya kira Maysah, yace Ruma in ganki mana, tace to tsoho, Zaid ya tsaya shima, tsoho yace sai a barni da Ruma ko? Zaid ya shafa kai ya fita yasan maganarshi zaayi, Tsoho yace Ruma, ya maganar shaye shayen Zaid? Har ynz yanayi? Ta danyi shiru ta sadda kanta kasa, Tsoho yace na fahimci kina son boye sirrin mijinki, hakan na da kyau, amma ki fada min, Har yanzu Zaid na shan giya? A hankali Maysah tace, Eh tsoho yana sha, balle idan ransa ya baci, sai ya sha gwangwani ya Kai 20, tsoho ya gyada kai yace haka ne, ya ciro wani garin magani a aljihu, yace ki barbada mai a lemu, ko abinci, InshaAllah idan har ya sha, toh InshaAllahu ko kamshin Giya ba zai so ba, balle yayi marmarin sha. Maysah ta amsa cikin jin dadi, tace Nagode tsoho Allah ya qara girma, yace Amin Ruma nah, ya miqo mata jarida yace ansa ki karanta min, ta ansa tace i miss dis, ta shiga karanta mai Newspapern.
*******
Hajia Babba ta dura Ashar, tace wallahi ba za ta sabu ba, rabon da naje Hajj tun shekara biyu da suka wuce, yanzu kuma yace da Aishalle zai tafi, ba zai sabu ba, ta miqe kamar zata tashi sama ta nufi Sasshen Tsoho.
******
Zaid ya kalli Tsoho yace tsoho baka da lafia, gaya min, jikinka zafi, ka bari na duba ka, tsoho yace kai zaidu ka bar kira min ciwo, nace ma kalau nake koh? Tsaya ma ka gani, tsoho ya miqe ya na gudu a hankali, yace kagani koh? Zaid dai murmushi yayi ba wai don ya gamsu da abunda tsoho yace ba, sai kawai don kar ya matsa mishi da tambaya, ya ce toh nagani, tsaya muyi hoto, tsoho kuwa ya gyara zaman gilashin zaid ya kashe musu hotuna yana posting. Hajia Babba ta shigo ko sallama babu, tace Alhaji me nakeji haka a cikin gida? Wai Hajj zaku kai da Aishalle? Wannan wani irin rashin Adalci ne? Ta rufe ido sai masifa takeyi, Zaid yace kaka kiyi shiru mana, ki bari zan biya miki Hajj, tace kai dalla rufawa mutane baki, saura sati 2 su tashi wuri ya qure, Wannan rashin Adalcin har ina? Wallahi Alhaji kaji tsoron Allah kar ya tambayeka, hayagagan da ihun da hajia babba keyi ya janyo hankalin mutanen gidan, kan kace wani abu parlorn tsoho ya cika tam, yan cikin gida suka cika parlon, ganin idon mutane be sa Hajia Babba daina yayyafa ruwan rashin mutunci ba, Ran Tsoho ya baci, yace karime mina miki na rashin Adalci? Allah shaida ne ina bakin kokari nacewa na ba wa kowa haqqinsa cikin ku 3, bayan shekaru 2 na ke zuwa hajj, kuma ina daukar daya daga cikinku, ya kalli yan dakin yace ku shiga maganar nan, shekaru 6 da suka wuce da hajjo na tafi, bayan shekara 2 na tafi da karime, bayan shekara2 da wa ya kamata na tafi? Duka dakin aka amsa da Hajia Ama, Tsoho yace madallah, karime gaya min, me nayi na rashin Adalci? ta manta shaf da ita akaje last amma da yake masifa na cinta sai ta fara borin kunya, eh ai dama ka fi sonta, ba tun yau kake min haka ba,Allah dai na kallon ka, Tsoho ya miqe tsaye don zuciyarsa na mishi zafih, gashi be da isashen lafia, ba tu yau ba, daurewa kawai yakeyi don kar ya tada ma Iyalansa hankali, tib ya fadi kasa. Gabaki daya suka yo kanshi, hajia Babba ta sake ihu, zata yo kanshi, Zaid ya fizgota cikin zafin nama ya fitar da ita waje, ya dawo ya kullo kofa, baba hassan ya shiga neman layin Dr Munnir, da sauri Zaid ya shiga ba Tsoho taimakon gaggawa, masu kuka nayi, tsam ya dauki tsoho kamar jariri yayi cikin daki da shi ya shimfideshi kan Gado, ya shiga shafa mai ruwa a hankali, ya sauke gauron numfashi yace yana numfashi, duka dakin sukace Alhamdulilah, Hajia Babba kuka takeyi daga waje, Alhaji na tuba wlh, kar ka mutu da bakin cikina, wlh bazan kara tada maka hankali ba, xan zauna da Aishalle lafia, nayi Alqawari zan zauna da kowa lafia, ku bude man dan girman Allah, ku taimaka ku bude man, kar Alhaji ya mutu, Auren saurayi da budurwa mukayi, muna son junanmu, mutuwa ki fara daukeni, kar ki dauke Alhaji, karki dauken farinciki na, Ta dinga sambatu,duk da suna cikin tashin hankali, hakan be hanasu murmusa wa ba, ana haka sai ga Dr Munnir ya nufo sashen, ganin hajia babba a waje tana ihu ya sa gabanshi faduwa, badai tsoho Zailani ya mutu ba, ya qarasa gurinta yace hajia lafia? Hajia babba da majina ya gama mata facafaca da fuska ta share hawaye tace kulleni sukayi duk suna ciki, DonAllah su bude ka ceto min shi, ba zan iya rayuwa bashi ba, kuran ya mutu sai na bishi, de munnir ya shiga kwankwasawa, Zayyad yazo ya bude mai, wuf hajia babba ta shige tana ina Alhajin, Zayd yace karku bari ta shigo, su jawad suka tattare ta, ita ko kira take, Alhaji kar ka mutu wlh ka mutu sai na biyoka ka yafe min, Dr munnir ya kalle mutan dakin yace he needs fresh air, Baba Gambo yace duk ku fita, Ya tasa qeyarsu Hajia Ama yace Mama mu tafi, ya farfado, ku barshi ya huta pls, duk suka yi hanyar waje, Maysah na tafia tana waiwayen tsoho, Zaid ta ma Alamu da ido, tace take care of him.
Like · Reply · Report · 7 minutes ago
Phatee Lamin
*****
Dr Munnir zaune gaban tsoho, yace Alhaji donAllah ka daina fadar mana da gaba, u cant be cheating death anymore, ka tsufa, ba ko da yaushe zaka dinga dacewa idan ka fadi kasa ba, wata rana idan ka farfado lafia wata rana ba zaka farfado lafia ba, Wannan ba shine kadai hanyar da zaka samu Zaman Lafia a cikin Zuri'ar ka ba, tsoho yayi murmushi yace Dr kenan, ka yarda dani wannan shine lokaci na karshe da zanyi karyar mutuwa, nayi na farko na ci nasara, wannan ma na ci nasara, don na tabbatar maka da cewa wannan ne hanyar shiryiwar karime, na tabbatar maka Karime zata zauna da kowa lafia kamar yanda tayi Alqawari, tana sona fiye da komai, ganin zata rasani ya sata nadama, Amma InshaAllah ba zan sake yin haka ba, ko don na bar tada ma Zuriyata hankali ba, dis is d last, it will never repeaf itself again. Dr yace Alhamdulilah Allah ya sa hakan ne Sanadiyar hadin kansu tsoho yace Amin. Zaid da ya shigo dakin yanzu ya ji su tsaf, murmushi kawai yayi a ranshi yace wannan Tsoho da dubara yake, ga karfin Hali, Allah dai ya ja da rai, Amma komin banza ya tsoratar da hajia Babba, yayi daria. Su tsoho na ganin zaid sukayi shiru, ba su san ya ji su ba. Tsoho ya wayance da cewa Zaidu je ka kira min kowa, Zaid yace toh Tsoho mai dubara, Tsoho da Dr suka bi bayanshi da kallo, tsoho yace likita ko ya ji mu ne? Dr yace anya? Da kyar ne gaskia..
******
Hajia Babba kulle cikin dakinta taci kuka har idanuwanta sun kumbura, idon nan yayi luhu luhu abinka da farar mace, nadamar gaske ta shigeta, tunani takeyi tun da aka auro Aishalle da Hajjo ba wacce ta taba ko harararta, ita ke musu tijara da nuna isa, ita ta adabe su, ba su taba mata laifin komai, basu taba tankata ba ko da kuwa zata rufesu da duka, fiye da shekaru 50 suna fama da ita, to meyasa ba zata daina wannan halaiyarta ta zauna dasu lafia ba? Duk sun tsufa, ta son Alhaji na sonta, kuma yana sauke duk haqqoqinta da ke kansa, amma ta danne gaskia saboda kishi, Nadama ya shigeta ta fara istighfari da neman yafiyar ubangijinta.
******
Nasiha me ratsa jiki Tsoho ya shiga yi ma daukacin zuriarshi, na su ji tsoron Allah, su bi junansu, su hada kansu, su zama tsintsiya madaurinki daya. Hajia Babba ta doka sallama a nutse a kofar parlorn, duk hankalinsu ya koma kanta, ta shigo kanta a kasa kamar wata sabuwar Amarya, Gaban Hajia Ama da Umma Hajja ta tsaya ta durqusa gabansu, ta kamo hanayensu tace Aishalle, Hajjo, na dade ina baqanta muku rai, na dade ina chuzguna muku, na chusa ma jinina kiyayyar jininku, na rabasu, na saka tsana mai karfi tsakanknsu, na dade ina shiga rayuwarku, ku yafe min, ku gafarta mun, kuka sukeyi dukkansu, hajia Ama tace kiyi shiru yaya, na yafe miki, Allah ya yafe min, Umma hajja tace bakomai yaya dama ban taba riqe ki a raina ba, kar ki manta ke yar uwa tace, na yafe miki. Suka rungume juna su 3 suna kuka, duk parlorn aka hau kabbara, sunji dadin wannan abu, ba wanda ya kai tsoho farinciki, Hajia babba ta miqe ta koma gaban tsoho, tace Alhaji ka yafe min, nasan duk nice sillar shigar ka damuwa, nice kadai matsalarka, Alhaji ka yafe min, tsoho baki har kunne, yace Karimeta, ai ba ki min komai ba, na san duk abun da kikayi saboda ni ki kayi, kishi na kikeyi, amma kin wanke kanki, Allah ya yafe mana gaba ki daya, uwargida ran gida in baki ba gida, karime ta musbahu mutu ka raba, hajia babba ta rufe fuska wai ita kunya, aiko su jikoki suka hau tafi suna sowa don jin kirarin da tsoho ya ma hajia babba. Nan kowa ya shiga neman yafiyan wanda suka bata ma wa, duk aka yayyafe juna, Kowa murna yakeyi barin ma tsoho da ya fi kowa jin dadi, ko yanzu Allah ya dauki ransa be da fargaban komai, Burinsa ya cika, ya hada kan Zuriyarsa kaf, ya maidasu Tsintiysa madaurinki daya, sai fatan Allah ya basu dauwamamiyar farinciki, ya kara hada kansu, ya barsu tare cikin so da kauna. Allah ya bar Zailani Family.
zcf
_Bibilicious Biebee_
6⃣1⃣ 🏡Gidan Gandu🏠by💕Biebee Isa💕 A karshe Baba Hussaini ya rufe taro da addua aka watse, kowa sai murna da farinciki.
Yau juma'ah duk sunyi shirin komawa gidajensu, Hajia Babba ta shirya musu kayan miya, kamar daddawa, kuka, kubewa busasshe da sauransu, kowa da kullinshi, Amira tace ai su wlh ba sa so, ai ni da bigbro ba ma shiri da tuwo, so ba abunda zamuyi da daddawa hajia babba ta hararesu, tace ai ke ba a muku abun arziqi, da ke da mijinki kamar ragowan yunwa, Amira zatayi magana Samir yace yi shiru lilsismeera, ta ga na fi tsohon mijinta ne, Hajia babba tace kai yaro, Musbahu ya wuce ka, ka ga dan saurayi son kowa kin wanda ya rasa, duk suka sa daria, Zayd yace yauwa Ruma ya ma sunan abun nan da kike samun a tea? Me kamshin nan, tace oh kanumfari, yace yauwa shi hajia ki bamu inaso, Hajia babba tace gaskia bandashi, sai dai in kakar ka Aishalle na san tana harka da kayan yajin nan, Hajia Ama da ke zaune ta na kallonsu tace eh akwai Kanumfari guri na, bari na je na kullo muku, Zaid yace ba sai kin tashi ba, a ina kika ajiye muje mu dauko ni da Ruma, ta musu kwatance ya ja hannun matarsa suka fita., Fadila tana ta jin dadi don ta nason tuwo, Jawad yace ina zaaje da wadannan tarkacen? Fadila tace Baby kaduna mana, yace wallahi ba zaa sa min mota yayi ta warin daddawa ba, ta turo bakih tace hajia babba kina jinshi ko? Hajia tace kai dallah chan ka bar dadi, ina ma amfanin wannan cimar da ka ke ci, banda tsotseka ba abunda yake kara ma a jiki, ka dage da cin abincin gargajiya, irinsu tuwon masara ko kayi kumari, amma sai wani abu da sunan ko dadi babu, ya sunan abun ma? Ko guiza yake? Duk suka fashe da daria, yace haba hajia sai ki bamu kunya, pizza ake cewa, tace kai ni rabani da abincin mayu da aljannu, duk suka fashe da daria. Mu'ammar yace indai ta ni ne to gaskia ki bar kayan warinki, ba maso koh Khairi? Islah ta sunkunyar dakai tana daria, Hajia babba tace yan Ingilan burauba, kun ma kanku, Ta kalli su Zayyad da suraj tace Wai ku tsaya ma, idan kunsan ba kwaso ku aje min kayana kar ku je dashi chan ku ajiye min nayi asara. Suraj yace mu muna cin tuwo gidan mu gaskia amma ba sosai ba, sai muna marmari ko honeybunch? Bilkisu tace eh muna so hajia babba, Zayyad yace no ni ina cin tuwo, ban son shinkafar nan, Umma hajja tace ai ni burgeni kakeyi Zayyad ba ruwanka da zaben abinci, kai dan gargajiya ne, yace gaskia ni komai aka dafa ci kakeyi, hajia babba tace kaji dadinka. Nan suka dan taba fira, sukayi sallama kafin suka nufa Sashen Tsoho don yi mai Sallama.
Nasihar ce dai ya qara musu, a karshe ya sa musu Albarka, suka shirya tafia, Mu'ammar da suraj da jawad da Zaid suka dauki hanya daya. Samir ya dauki hanyar bauchi, Zayyad kuma aka kaisu Airport.
*****
Zaria
Tunda ya shigo gidan yake kwala mata kirah, a parlor suka yi kicibus, tace YaAmar lafiya wannan kira haka? Yace close ur eyes, ba ta mai gardama ba, ta rufe idonta, ya sa mata wasu takardu a hannu yace ta bude idonta, ta bude Tickets to Cambridge England ne, ta zaro ido tace yaya? Yace i told u, m ready to sacrifice everything, akwai time zaki koma skool, nd i will apply for masters, still kuma i will find a job, we'll start allover there, we will build our home, nd i will give u the joy and happiness u truly deserve. Dadi ya kashe Islah ba ta san lokavin da ta rungumeshi ba tare da manna mai kiss a baki, tace i love u yaAmar, yace i love u more swrhrt.
Abuja
Time din da ya shigo gidan bata nan ta je skul, ya gaji sosai ya fada dakih, yana si Yayi baccin rana amma ya kasa, giyyarsa ya ciro cikin fridge ya bude zai sha kenan ta shigo da sallama, da sauri ya boye kar ta gani, DonAllah ya daura mai wani irin kunyarta, ba ya so ta ga yana shan giya, shiyasa tunda suka dawo daga Maiduguri yake sha a boye, ta ganshi ta ga me yakeyi. Amma ba ta nuna mai ta gani ba, sai a sannan ta tuno da maganin da tsoho ya bata. Ta qudiri a ranta yaum zatayi amfani da maganin, Allah dai ya as a dace. Yace Yaxayd ina wuni, duk ya bi ya daburce yace lafia lau, banji shigowarki ba, tace ina ta sallama ba amsa ai, ganin ya kasa sakewa da ita ya sa tace bari taje ta rage kayan jikinta, ta fita, tana fita ya kwankwade giyyarsa, daki ta shiga bayan ta cire hijav dinta, ta bude kayan ta, ta ciro ledan maganin da tsoho ya bata, ta shiga kichin ta shiga hada musu lunch, cikin jug din sobo ta juye maganin nan tas, ta kai dinning, zuwa tayi ta shiga kwankwasa mai, sama sama ya ke jinta don har ya fara bacci.Tace yazayd ga lunch na gama, ka fito kaci, cikin magagin bacci yace ki bari sai anjima, ta marairaice tace plss, yace ok lemme dressup, sai da ya fads toilet ya sakar ma kanshi shower kafin ya fito, kan table ya isketa, ta yi serving dinshi, white rice ne and sauce, ya ci kadan, ta zuba mai sobo ya sha sosai sbd yayi dadi, ba a fi 5 mins ba, ya ji zuciyarshi na tashi, Warin giya yake ji, Amai ya zo mai da gudu ya fads toilet ya dinga kwarara Amai ba tsayawa, Maysah sai sannu take mishi, sai da ya kusan minti 20 kafin aman ya tsaya, ya bata tausayi sosai, ta bashi roban ruwa ya sha ya kuskure bakinshi, ta riqoshi ta kaishi daki, ji yayi dakin na warin giya, yace ki kaini dakinki, haka ta miqar dashi ta kaishi dakinta, duk ya galabaita, Sai da yayi kwana 3 kafin Aman ya tsaya, duk ya rame ya qare, sai da wani colleague dinshi yazo Gida ya samai drip, randa Zaid ya warke ya shiga dakinshi ya fiffirto da dukka kwalayen giyan da na fridge yayi waje dasu ya cinna musu wuta, Maysah na kallonshi, dadi ya rufeta, nan take ta kira tsoho ta shaida mai abun da ya faru, shima yaji dadi, yace ai Zaid kuma da Giya har Abada, yanzu ko wani ya gani yana shan giya sai yayi Amai, don kyamar giyya yakeyi yanxu, Mijinki ya daina shan giya da Yardar Allah. Maysah tace Nagode Tsoho Allah ya bar mana kai. Murmushi tsoho Yayi ya kashe wayar..
(3months later)
Mrs Zaid hurry up, zaki sani latti fah, daga ciki tace just a minute Mr Zaid, yace ko na tafi? ta fito tana gyara zaman gyalenta tace ai na ma fito, Zayd ya matso yace u grw more beautiful every morning, murmushi tace ai ban kai ka ba, yace i love everything about u, murmushi tayi ta ce mu tafi kar Ka amsa query gurin Dr James, har zata shiga mota ya riqo hannunta, yace na sa miki ido wato ke ba ki san ido ba ko? Ta zaro ido tace yazayd me nayih? Oh baki san me kikayi ba ko? ta marairaice tace kayi haquri Yazayd, me nayi? Shima ya bi ya marairaice kamar yadda tayi, ya turo baki yace ban taba jin kin ce min i love u ba, waiyo Allah, kunya ta lulluba maysah, ya tsare ta da ido yace ehen ina jinki, ganin kunyanta ya motso ya saketa ya bude mata mota yace na lura akwai sauran kunyana a tare dake, a hankali zan cireshi, da sauri ta kawar da kai tare da yin murmushi.
Karfe 12 ya gama ganin patients a OPD, ya kalleta yace Mrs Zaid kin gaji ko? Ta girgiza kai tace Aa, ina kallon ka ne yanda kake duba patients cikin kwarewa, kaji dadinka Allah Girma, yayi murmushi, yace dadi na da Zabin tsoho akwai Adduoi kamar mutanen da, tayi daria, yace oya ta shi muje muga patients a ward, daga chan sai mu wuce gida, ta miqe ds sauri suka fita daga office hannun su riqe da juna, suna tafia suna birge mutane, wanda Suka sansi sai suce MrAndMrs Zaid, sai su daga musu hannu, a haka har suka isa Ward, Zaid ya shiga ganin patients dinshi, ita kuma tana basu kudi sadaka, ana ta musu godia, su ka fito, daidai wani daki sukaji wata murya na cewa Myzyd, myzyd, sai kuma sukaji wani irin qara daga dakin da gudu suka shiga dakin, Zaid ya kalli wacce ke kan gadon, da alamu rai yayi halinsa, ya tsura ma gawar ido yana so ya gane wacece amma ya kasa, fuskar ta chanza kamanni sosai Fusksrta duk yayi baqi fatarta ta fara kwayewa, kuraje duk sunyi fanchami a jikin, jikinta ba kyan gani, Zaid ya cire baki ya kira nurse, yace haka kuke barin patients? I dont think dis one is Alive now, nurse tace sorry sir, ta mutu, ai mutuwa hutu ne a gareta, patients din HIV+ ce, tunda mamarta ta kawota bata sake dawowa ba, kwanaki sai da mukayi cuffing hanayenta don cizgar gabanta takeyi ta na yagan fatar jikinta, Zaid ya girgiza kai waye likitan patient din? Tace ai Dr Maikudi ne, yazo ya dubata? Tace aa bezo ba, yace haba mana call him, dis patient needs RA, ya kamata a kaita Murtuary before ta koma wani abun, Rumah ki basu sadakan mu tafi, da alamu Zaid be gane ko wacece ba, Maysah da ta ganeta ta fashe da kuka sbd tsoron Duniya, dubeta da yar gayu, yar kwalisa mai iko da kasaita, dubi yanda Allah yayi da ita, tcae Yazayd baka gane ko wacece ba? Yace kinsan ta ne? Tace Badiyya ce, badiyya matarka ta da, wani uban tsaki Zayd ya buga ya ma badiyya wani mugun kallon tsana, yace die, Go to hell and burn to ashes, ya fizgo hannun Maysah yace mu tafi, haba Yazayd, lets help her, she needs us, Zaid yace me zan mata rai zan dawo mata dashi? Uwarta ta ajiyeta ta barta mu sai mu kwasa? Ka yafe mata pls, ta riga da ta mutu, ka yafe mata ko za ta samu wani saukin, yayi tsaki yace ke ya ka mata ki yafe mata sbd ke ta azabtar ni da taso azabtarwa Allah be ba ta iko ba, so sai ki yafe mata tace ni bata min komai ba, Allah bai barin irinsu, tace yazayd a dauketa a mata sallah, Da karfi zaid yace Rumaysah, shige mu tafi, sum sum Maysah ta wuce ta na kallon yadda gawar badiyya ya wulaqance lokaci guda a ranta tace Allah ya gafarta miki, ya ji kanki nidai na yafe miki. Zaid ko wurin be kara kallo ba, ya rufa mata baya, yace u reap wat u sow.
Maiduguri
Karfe 2 na dare, Zuciyarsa ta buga, da sauri ya bude idon sa saboda zafin da yaji, ya sa hannu ya dafe kirjinsa, rabon da yaji ko da ciwon yatsa ne an fi shekara 40, amma yau gashi zuciarsa har ta dara Zafih, tun bayan dawowarsa hajj yake jinsa wani iri, Musbahu Zailani yayi dan gajeran murmushi, a hankali yace wannan Ciwon Ajali ne.
_Bibilicious Biebee_
Like · Reply · Report · 1 hour ago
Gidan6⃣2⃣ Gandu
Gidan Gandu by Biebee Isa Har karfe 4 Tsoho ya zauna zaman jiran mutuwa, ba mutuwa ba alamun shi, har ya far ji ana kiran Assalatu mutuwa ba tazo ba. Ya miqe jiki a sanyayaye ya nufi masallaci, sukayi sallah, ba wanda zai kalleshi yace yana da damuwa, amma shi yasan me ya ke gani. Dawowa yayi ya zauna kan kujerarshi a parlor, yan GIDAN GANDU suka dinga shigowa gaisheshi kamar ko wacce asuba. Be nuna ma kowa wani abu ba don be son ya tads hankalinshi, kuma be yarda suyi dogon gaisuwa kamar da, da suka fahimci kamar be son magana da sun gaisheshi suke tafia, Hajia Babba ce ta shigo, ta zauna gefenshi, Alhaji barka da Asuba, yace karime ta musbahu, tayi murmushi yace zauna kiji, ta zauna, ya shiga mata fira yana bata labarai masu sanyaya zuciya, cikin dabara yace wai idan na mutu ya zakiyi? Tace chap Alhj ai bana son ma tunanin mutuwarka, na fiso na mutu kafin naga mutuwarka, don na san ina iya zaucewa, yace haba karime, sai kace ba musulma ba, ai kinsan Qaddara koh? Ashe ba so na kikeyi ba tunda mutuwata zata sa ki hauka, ya turo baki, tace Alhaji ni na san ba wanda ya kaini sonka, yace Ahap, ai in kina sona bazaki taba bari wasu suyi man kuka ba balle ki, Addua kadai ce mamaci ke buqata, tace wai tsaya Alhaji, wannan maganganun na meye ne? Yace in banda abinki karime waya san gawar fari? So ake ko da yaushe bawa ya zama cikin shiri, Hajia Ama da Umma Hajja sukayi Sallama, suka amsa musu, suka zo suka gaids Tsoho, suka gaisa da hajia Babba, Duk yanda Hajia Ama taso ta hada Ido da tsoho ta kasa, tsoho ya qi yarda su hada ido, haka kurum taji gabanta na faduwa, ta daure tace Alhaji lafia kake? Murmushi ya fara yace Kalaw nake Aishalle, tace Anya? Hajia Babba tace ke ma kya fada, yanzu ya ke min magana me kama da wasiyya, duk na rasa gane inda maganar tashi ta dosa, Umma Hajja tace Alhaji ko wani abun ke damunka? Ka fada DonAllah, kar kayi nauyin baki, yace ku saurara kuji, shi fa bawa so ake ya zama cikin shirin mutuwa a ko da yaushe, balle mu da mu ka kwana biyu, mun tsufa, ba a sa gawar fari ba, ko ba haka ba? Duk suka gyada kai, to ku kasance masu dangana, ku kasance masu, tsoron Allah, ku kasance masu tuna mutuwa, tsoho ya saba musu irin wannan nasihar, to sai suka share fargaban da ke ransu sai suka dauki wannan nasiha ce kamar wacce ya ke musu kullum. Kuma ina roqon Allah ya hada min Hajjo, Aishalle da karime a matsayin Mataye na na Aljanna, ko a Aljanna baku ba kishiyoyi, ku din kenan duk suka yi murmushi, sukace Amin Alhaji Allah ya hada mu duka a chan, yace Amin Matayena, sanyin idanuna. Ku tashi ku tafi ina so na dan koma bacci, duk jikinsu yayi sanyi, sun san cewa idan tsoho ya farka da Assalatu be koma wa wani baccin sai wani daren, Amma yau yace zai koma, basa son sa abun a ransu ne shiyasa suka fita jiki a sanyaye.
******
Ya kalle su su sha takwas, tara maza tara mata, ya kalli yanuwanshi da ya riqa su biyu tun suna yara, ya juya ya kalli yaran Danuwansa Rabiu, su 5, yan ukku da yan biyu, sannan ya juya ya kalli yaransa. Sai ya saki murmushi, yace Alhamdulilah, duk suka zuba mai idanu, yace kunsan ba abun da ya kai Hadin kai dadi? Hadin kai wani abu ne idan da akwai shi a wuri, to ba abunda ya kaishi dadi, idan anaso a samu hadin kai to dole ku zama rufa ma juna Asiri, Dole ku zama masu yarda akan shawara daya, dole ku bi na gabanku, dole ku so junan ku, dole ku zama daya, dole ku zamo tsintsiya ma daurinki daya. Sai abu na karshe, dole ku tsaya akan junan ku ina nufin masu taimaka ma juna, idan kun hada wannan to kun samu hadin kan junanku. Jikinsu yayi sanyi, Aunty Abida ta fashe da kuka, tace Baba wani abu ya faru? Ko baka da lafia ne? Tambayar da sauran ke son yi kenan, yace bakomai Abida, Nasiha ce da na saba yi muku yau da kullum, Aunty Nuratu tace amma ta yau ta sha bambam, Baba ba ka lafia, ko a kira Dr Munnir? Yayi murmushi yace idan mutuwa ma zanyi Dr Munnir ya isa ya hana? Suka girgiza kai, ba wanda ya san gawar fari, ni dai ku hada min kanku, ko da ace wata ran bana nan, a duk inda nake Zan kasance mai Alfahari da ku, ku bi manyan ku, Mudassir da Labaran, sai yan 3, na baku Girma, na baku shugabbancin wannan Gida, Ku kasance Adalai, ku cire son kai, ku kasance masu son junanku. Baba Hassan da ya gane inda zancenshi ya dosa, ya rarrafo ya kama kafarshi yana kuka, yace Baba, kar ka tafi, ban mu taba kukan rashin mahaifi ba, kaine mahaifin mu, kai ne gatan mu, kaine katangar mu, kar ka tafi baba, idan ka tafi ya zamuyi,? Wa zai ciro mu daga baraka idan mun fada, Tsoho yayi daria sosai, yace kai hassan, wai kai yaro ne? Ka manta kuna da yara masu girman Zayd da Zayyad? Ku zaku kula da kanku, ni na gama nawa, ku ya rage kuyi naku, Hankali na na kwance ne saboda nasan kune manyan gidan nan, ba zaku taba bari Zuriyata ta gaiyara ba, zaku tashi tsaye kamar ina raye. Abunda nake so daga gareku shine Adduarku, da neman gamawa lafia, Aunt Sadiya na kuka tace ai wlh ka ma gama da dunia lafia, don ni na fi sa ka a cikin Shariffai, tsoho ya katseta, yace Aa Halimatuwa, kar kice haka, ba wanda ya san gaibu, ni dai Adduarku nake bukata, kuma bansan yan kuke kuken nan, ba zan ji dadi ku dinga min asarar hawayenku ba, bana son kukan ku, Baba Abbakar, ya fashe da kuka yace baba ka yafe mana, yace kul Abubakar, ba ku taba bata min rai ba, amma duk da haka na yafe muku Allah ya muku Albarka, ku tashi ku tafi, suka tashi jiki ba kwari. Sukayi Gaba, ya kira baba hassan, a hankali yace mai Be Strong Hassan, u are d Man here, kuma banason zaman makoki kaji? baba hassan ya kasa cewa komai sai daga kai da yakeyi kamar kandagare, ya fita da sauri.
Magana ta zagaye Gidan Gandu, duk iyaye sun kira yaransu da ke wajen gari sun sanar dasu, wurin 7am Aunty Abida ta sanar da Zaid, murmushi yayi yace tsoho na son cimma wani abu ne, tace bangane ba, wlh abunda yake bari is more like wasiyya, zaid Tsoho na fama da internal pain, but becoz he loves us dat much ya kasa sanar damu, Zaid m scared to loose him, i love him, gaban zaid ya fadi, yace Mom noone is loosing Anyone, gamu nan zuwa. Hankalinsa ya tashi, ya shiga tada Maysah a hankali yace tashi mu tafi tace ina? Maid, lafia? Yace tsoho ne, wai be lafia, wani tsalle tayi ta fada toilet, donyi wanka, Zaid ya kira Jawad, jawae a rude yake yace ai gashi nan sun dauki hanyar Maiduguri, tun dazu Samir ya kirashi ya gaya mai, Zaid yace nima ga mu nan tahowa. Be safe brother ka kwantar da hankalinka kayi driving kajih?
_Bibilicious Biebee_
47 mins · Public
More
Gidan6⃣3⃣ Gandu
Gidan Gandu by Biebee Isa Da Tsoho akayi Sallar Azahar, mamaki kowa yakeyi, har sun fara tunanin ko dama nasihar ce ya ke musu dazun da asuba, gashi har anyi azahar dashi, nan suka fidda shakkun mutuwa, kawai dai nasiha yake musu, jikoki duk sun hallara, na nesa da na kusa, banda Zayd da Maysah, harta Zayyad da hanifa da ke lagos sun iso. Dama Islah da Mu’ammar ba su dade da dawowa Naija ba sbd Islah tagama Exams Wannan kenan.
Tsoho kwance kan gado, yana kallon sama, jikokin nashi su 10 sukayi sallama, ya dan kallo su yana kokarin tashi, dama su yake jira, yace ga su gasu, duk suka bi suka zagaye shi, Ina Zaid Da Rumah? Jawad yace suna tafe don sun shigo maiduguri, sun kusa isowa gida, tsoho yace wani irin gudu Zaid keyi haka, Allah dai ya kiyaye, suka amsa da Amin, yace yauwa ku saurara kuji abunda zan fada muku, kunsan ance ba a son gawar fari ba ko? Toh bari na bar wasiyya incase na rigaku mutuwa, gabansu duka ya yanke ya fadi, yace, ina so d’a ko d’iyar Zayyad ya auri da ko diyar Mu’ammar, ina so d’a ko d’iyar Suraj ya auri da ko d’iyar Jawad, ina so d’a ko d’iyar Samir ya auri d’a ko d’iyar Zayd, wannan shine burina akan yaranku, idan anyi wannan hadin, sauran kuma na baya, na bar ma iyayenku, don bnsan iyakan zuriar da zaku haifa ba, iyayenku xasu zaba musu waenda suka dace dasu, kun gane wannan? Duk suka daga kai sama, yace yauwa, sai kuma magana ta biyu dangin turawa, bari muga idan akwai sauran turanci akaina, duk sukayi murmushi yace Afternoon tips, Love One Another, be there for one another, stand together side by side. Kunji? Suka daga kai, yace wato idan anyi mutuwa ba’a so ayi kuka, kuka kamar saukar garwashi ne a jikin mamaci, Addua kadai mamaci ke buqata, kun ga kamar ni nan idan dayanku ya mutu, kunsan me zanyi? Suka girgiza kai, yace zanyi murmushi ince Alhamdulilah, bazan yi kuka ba, ya kalli Islahulkhair ai ke ma bazakiyi kuka ba ko idan na mutu? Ta daga kai tace InshaAllah ba zanyi ba ya juya ya kalli fadila yayi murmushi sannan ya murguda baki yace ni bazanyi kuka idan kin mutu ba, kema ai ba zakiyi ba koh?tana kuka tana murguda baki tace bazanyi ba, yace hanifa fa? Itama kukan takeyi tace bazanyi ba, Bilkisu me gadon zinari fa? Tana kuka tana cewa eh tsoho bazan ma kuka ba, yayi murmushi ya kalli mazan da duk fuskokin su suka rikide sukayi ja, masu karyayen zuciya kamar Mu’ammar, Suraj, jawad da samir kuka sukeyi kamar mata, Zayyad kuwa fuskarsa ce tayi jaaa, Tsoho yace haba mazaje nah, be strong mana, m not dead already, just take care of ur wives, be there for them, value them, love nd cherish them, i will be there watching u all. I am proud of u all. Ina sonku duka
*****
Ko parking be samu yayi da kyau ba, suka fito shi da Maysah, A sittin suka kwasa a guje, ba shi ba ba maysan ba, sukayi sashen tsoho, mutanen tsakar gida suka mimiqe don yanda suka ga zaid da maysah na relay sun zata tsoho ya mutu. rige rigen shiga cikin dakin sukeyi Lokacin da Maysah da Zayd suka hada ido da tsoho a tare suka saukar da Ajiyar zuciya, tsoho yayi murmushi yace sannunku da zuwa likita bokon turai da matarsa. Ruma matso nan kinji? ta matsa kusa dashi jiki a sanyaye, Zaid ma ya matso kusa dashi, Abunda Tsoho ya gaya ma su Suraj shi ya sake maimaita ma su Maysah, hankalinsu ya tashi, yace Ruma ai ba za ki min kuka ba koh ta toshe bakinta hannhn bibbiyu don wani kuka mai karfi ya zo mata, ta shiga daga kai tana bazan ma kuka ba tsoho, yace promise? Ta gyada kai tace eh tsoho, Ta ja da baya tana kuka. Lokacin dakin ya cika makil, Tsoho yace ku zo muyi musabaha, Assalamu Alaikum ya miqa musu hannu daya bayan daya suka zo suna bashi hannu suna amsa sallamar da ya ke musu, maza da matansu, manya da yaransu, kuka akeyi, duk yawan su sai da tsoho Yayi musabaha dasu, yace MashaAllah, kar ku manta, ku riqe zumuncin, Allah ya raya ku ya muku Albarka, Allah ya sa ku gama da dunia Lafia, Assalam Alaikum warah–matullah muryar tsoho ya sarke. Baba hassan ya shiga karanta mai kalmatush shahada, duk dakin aka amsa, ko wa ya shiga maimaita kalamatush shahada, Cikin ikon Allah tsoho ya amsa, ya maimaita kalmar shahada, yana kaiwa karshe malaika ya ida zare ransa, Allahu Akbar inji baba hassan, yace Allah ya masa cikawa, Maysah ta yi saurin kallonshi tace aa baba kalla fa, idonshi biyu, duba kagani murmushi yake mana, tsoho yi musu magana kaji, baba Mudassir ya matsa gurin gadon, ya shafe idon tsoho, ya rufe shi da zannin gado, Innalillahi wa ina ilaihir rajiun, kullun nafsin zaikatul maut, Luuuu, Maysah ta fadi kasa summamiyah, luu fadika ta fadi, bilkisu ta bita, hajia Babba ta zube itama, karan faduwan mutane kawai kakeji, haka suka dinga zubewa, wasu fargaba wasu tsoro. Allahu Akbar mutuwar tsoho tayi kyau, Uncle umar kadai ya yi karfin halin kiran dr munnir yace yazo da nurses gida ba lafia, Zaid tsaye gaban gawan tsoho, ko gezau beyi ba, fuskar nan tayi jaa, jijiyoyin kanshi suka mimiqe kamar zasu fito, tsigar jikinsa Suka tashi, be ma san wainar da ake toya ba, hajia Ama na kusa da zayd, ta tsura wa gawar ido, ta rungume hannuwanta saman kirjinta, ta shilla duniar tunani, Dr Munnir ya zo da emergency, hankalinshi ya tashi ainun ganin gawar tsoho, shima kukan yasa, nan nurses dinshi suka fara farfado da waenda suka suma, su jawad ds sauransu duk suna cikin masa suma, Maysah na farfadowa ta sake zubewa kasa, Hajia Babba ma ta farfado ta taso cikin zafin nama tayi gadon, Oh daman mutuwa zakayi shine ka barmin wasiyya dazun?ko banyi kuka yanzu ba Dole zanyi kukan rashinka nan gaba, amma nasan nima ina nan tafe, na kusa bin ka bazan iya rayuwa bakai ba, tayi saurin share hawayen idonta tace kuyi sauri a suturceshi akai shi makwancinsa na gaskia, Allah ya jikanka, ta ba kowa mamaki, Baba Hassan ya kalli Hajia Babba yace Mama ku za ku mishi wanka. Cikin Rabin Awa an gama yi ma tsoho ko mai, nan suka dinga shiga one by one suna mai addua, A lokacin yanzu suman Maysah 3, aka hanata shiga inda gawar take amma fir taqi tace sai ta shiga ta mai Addua, Uncle umar yace a barta, ta shiga ta dade ta na mai Addua, tana fitowa ta kara zubewa kasa.
Mutuwar tsoho ya cika gari da ma kasar gabaki daya, yan unguwa suka cika gida, har shehun borno ya hallarta, Manyan mutanen kasa sun zo, kowa fadan halaiyar marigayin yakeyi, A Lallai sunyi rashin tsoho, mutum mai girma da karama, mutumi ne gatan talakawa, shine gineginen Masallatai da Islamiyoyi, kowa ya dauko matsalarshi kan tsoho suke saukewa don ya magance musu, duk fadin Girman Gandu haka aka cika gida Dam da mutane don sallahtar Gawan tsoho, aka gama sallah aka daukeshi aka kaishi gidan shi na gaskia, mutanen da suka suma a makabartar da yawa suke, sai dai kaji tim, kafin a ceto wannan wannan ya sake faduwa. Sun ga tashin hankali ba kadan ba. Mutane Suka fara watsewa, aka bar yaransa da jikokinshi kadai a maqabartan, suka dinga zuba mai Addua, da kyar aka raba su Zaid da kabarin tsoho. Suka koma gida. Hankalin a tashe, ko wannaensu na sonyi kuka, amma da sun tuna maganganun tsoho sai su shanyen kuka, amma hawaye basu daina xuba a idanuwansu ba, don wadannan hawayen ba za su iya tsaida su ba. Allah ya ji kan Musbahu Zailani, Allah ka sa Aljanna ce makomar shi, Allah ka ba zuriyarshi haqurin jure rashin shi Amin .
_Bibilicious Biebee_
46 mins · Public
More
6⃣4⃣ 🏡Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕 Ba su yarda sunyi zaman makoki ba, don yana daga cikin wasiyyun tsoho da anzo an musu gaisuwa suke saurin sallama bakin, Baba Labaran ya shaida ma yan unguwa cewa zasu cigaba da ga inda tsoho ya tsaya, duk me neman tallafi kar ya ji shamaki yazo ya sanar dasu.
*****
Baza'a a iya bayyana tashin hankalin da yan Gidan Gandu suka shiga ba, duk yanda ake tunani abun ya wuce nan, bayan kwana biyu baba Mudassir ya umurci kowa ya koma bakin aikinsa, su koma garuruwansu, haka ko wannensu ya kwashi matarsa ya tafi, su hajia Babba kuma sai ince Allah ya sa a fita Takaba lafiya. Allah ya baku ikon jure Rashin Tsoho.
6months later
Maiduguri
Su Hajia Babba, Hajia Ama, da Umma Hajja sun fita takaba, sun hada kawunnansu, Komai na tafia daidai a gidan, Zaman lafia sukeyi.
Bauchi
Football suke yi a dan karamin field din gidan, ko da Amira ta harba kwallon nan, be tsaya ko ina ba sai kan cikin Samir, da sauri ya fadi hannunsa riqe da cikinsa, yana fadin Wash Allah, ai tuni ta ruga gurinsa inda ya kwanta, oh no bigbrosamir, m sorry, shi kuma ya fara ihun karya, ta na duqowa yayi saurin dagowa ya rungume ta, yace thats all folk's, na rama jiya haka kika sa na rude da kikace na bugeki da kwallo, tace haba bigbrosamir ba haka akeyi ba fa, kai u seem serious, dis is cheating, ba zan yarda ba, yace sorry ma, a min haquri, ta maqe kafada tace nidai sai ka goyani,n yace done, ya duqa yace oya hau, ta danne bayanshi ya tashi yana guda da ita, ita kuma sai palla daria takeyi.ta manna mai kiss tace ina son bigbrosamir dina, yace inason lilsismeerahnah...
Kano
Billy nah, m home, Queen? Where are u? tana jin shi, ta boye bayan labule, ya ajiye brief case din shi ya shiga duka dakunnan bata nan, har toilet ya leqa be ganta ba, ya shiga kichin ba alamunta, hankalinshi ya soma tashi, Toh ina ta shige?while tasan bana so na dawo ban ganta ba, Bilkisu ta toshe bakinta sbd daria na son kubce mata. Hango kafafunta yayi ta labule, yayi murmushi ya miqe, ganin ya nufota ne ya sa ta fito tana kyalkyala daria. Ta yi hugging dinshi tace sorry my king, ya ja hancinta yace kina so ki wahalar dani ko Queen? Tace na tuba, ya maqe kafada kamar wani yaro, yace naqi din sai kin min kiss, tace oya kulle ido, ya rufe ido, ta daddage ta gantsara mai cizo ya saki kara da gudu tayi dakih tana daria, yace lallai yarinya kin kai kanki, yau sai na rama duk cizunan da kika min. Daga ciki tace haba king sorry mana u know i love u ryt? Yace i love you more shiyasa xan rama ya biga ciki tare da kullo kofar😏
Cambridge England
Tana dawowa daga skul ta shiga kitchen, tasan Haniebunch is on his way home, noodles ta shiga dafawa, yana shigowa yaji alamun akwai mutum a kichin, a hankali ya lallaba ya shiga kichin din, ta dage sai juya abincin takeyi ba tasan da shigowan shi ba sai ji tayi an rungumeta ta baya, dan guntun ihu ta sake don ta tsorata, a hankali ya rada mata shhh, honeybunch, its me, murmushi ta sake, tace welcome honey i've missed u, i missed u more, ya juyo da ita ya sake rungumeta, yace i love u so much, i love u too, yayi hada bakinshi da nata ya fara kissing, abincin ya fara kwari alamun konewa, ina samm basu san yanayi ba, Islah ta fara jin kaurin yayi yawa da sauri ta dan bubbuga mishi baya, yayaya saketa, suna leqa tukunya sai suka fashe da daria, don noodles din ya qone qurmus, ta shagwabe fuska yaya u see ur life ko? Yace aa kice dai u see iur lives ko? Tace ni me nayi? Yace toh ni ma menayi? I was jus kissing my wife, Islah tace frm now on, ba ruwanka da shiga kichin especially idan ina ciki, yace wlh baki isa ba, duk inda kike nima kafana na nan, nd guess what, i've been hired at d IATA Training center, i will b part of d trainees, nd i will be paid thousands of pounds, Islahulkhair ta rungumeshi tare da sakin ihu, tace This calls for a celebration, yace je ki shirya, kizo muje mu dauki Zaineema Da Asad(sunyi aure) then we'll have our lunch. Tace okay honeybunch i love u, me more.
Gombe
Kwance take kan cinyarshi suna kallo, yace hanie nah, da Gombe da lagos ina kika fi jin dadin xaman? tace kai ma ka san nan ya fi dadi, gashi muna kusa da su Amira, nan ina ganin mutane, chan ko ba na ganin kowa, ai Wallahi na fi kowa jin dadin wannan trsnsfer din da aka maka, atleast i dont have to worry about that fatiti, Zayyad yayi daria harda riqe ciki, Hanifa kin ciki rigima, kinsan Atutu is my best frnd, ba komai tsakani na da ita, Plan mukayi ni da ita shisa tazo nan gida, ba wacce nake so sai ke Hanifa, an halicce ki ne don ni kadai, don ki zama matata, ina miki so mai yawa, i love u so much, theres noone in my heart just you nd u alone, hanifa ta rungume Zayyad, tace Yayanah, ina sonka nima sosai, i cannot live without u, sonka a jinin jikina yake, i dont knw wat my life wud be like if uo not in it, tace yaya tell dat ur besty if i see her leg in my house again, m going to cut dem all of, coz u are mine nd mine alon, Zayyad yayi daria, yace karki damu da Fatiti, coz she's married, kar ma ki damu da ko wacce mace kar ki manta no kishiya in ur Family's policy, tayi daria, yace one more thing kin kusa fara GSU, an samo admission din, tayi saurin rungumeshi tana i love u wallahi, thanks yayana, ina farincikin sanar dakai dat m two months pregnant, wani ihu Zayyad yayi ya tashi ya godema Allah, ya rungume matarsa kamar zaa kwace mishi ita yana fadin Thanks so much sweety, Atlast we gonna have a Musbah junior, tayi saurin rufe fuskanta tana daria.
Kaduna
Zaune take a kan carpet tana kallon indian Series, Jawad ya zo ya tsaya a kanta yana murguda mata baki, yo ita ina ma ta sani tana chan ta na kallo, Ya zo ya tsaya yace Ni wallahi sai nayi disconnecting dukka Wires din TV dinnan, idan ana kallo mantawa akeyi na dani, bama a da lokacina, ta miqe da sauri oyoyo baby, yace dont baby me sai ynx ki ka ganni? tace sorry mana, zo kaji, ya maqe kafada kamar wani karamin yaro, yace kuma idan nayi mafarki sai na gaya ma Tsoho abun da kike min, da sauri ta narke tace haba baby, kayi haquri ba zan sake ba, in short bazan kara kallon ba ma, kayi haquri kajih, yace to nayi a min kiss sannan a min wanka, sai a shafa min mai sai a zo a lallabani inci abinci kuma sai a lallabani nayi bacci, m a baby dats wat i do always, tayi daria tace yes u ar a baby, dole zan maka komai, don kasan i love u so much, ya ce amma kinsan cewa nawa son yafi naki yawa, da sauri ta girgiza kai wallahi nawa yafi, yace nawa yafi, ta bata rai kamar zatayi kuka tace wallahi nawa yafi, Ai Allah na kallona, ya zauna ya fara zuba mata shagwaba, hardasu a kasa tirjetirje kamar wani yaro yace ni bazan yarda ba, ni kice nawa yafi naki yawa, idan ba haka ba i will go for a hungerstrike, nd i wont bath again, tace lalala babban magana, naji naka yafi yawa, shikenan? Ya rungumeta yana daria yace yauwa baby, shisa nakesonki, kin san son da nake miki yayi yawa da yawa, ta mai gwalo tace amma nawa yafi yawa, ta zura a guje ya bi bayanta, suka dinga zagaya parlorn suna daria karshe ya samu nassaran chapkota, suka zube kan sofa, i love u baby, i love too baby.
Abuja
Ta shiga dakinsa hade da sallama, taji shiru ba amsa, Sweetie, where ar u? yana toilet yace here,get me d towel pls, tace me na ce maka kan shiga toilet ba towel? Kince na dinga shiga da shi, ayi haquri mallama a kawo mun, ta girgiza kai, ta dauko towel din ta yi knockimg tace gashi, yace oh no, na sa sabulu a fuska na, pls ki shigo ki kawo min, tace Yazayd isnt going to change, hop uo not planning something, yace no my love, i cross my heart, tana shiga ya danna ma kofa key, tsaye ta ganshi a bayanta yana daria, ta shagwabe fuska tace Yazayd plsss, wallahi yanzu nayi wanka, bakaga har kwaliyya na maka ba? Yace nagani kinyi kyau whch is y xan kara miki wanka, na miki kwalliya sai a ga na wanda yafi kyau, zatace wani abu yace malama kinsan dai bakyau magana cikin toilet ko so hush, ya matso daf da ita ya zame mata kaya, ya tura ta cikin bath, shima ya shiga, sai da suja ma juna wanka, kafin Zayd ya nado maysah a cikin towel ya kawota har gado, idonta a lumshe kamar me jin bacci, ya shafeta da mai, ya bude sif dinta ya ciro mata 3quater da wata er qaramar top, shima 3quater din ya dauko ya sa da riga bodyhug, ya dagata ya samata ya zaunar da ita, yyi tagumi hannu bibbiyu yana kallonta,ta hure mai ido tace kallon fa? Yace Zabinaaa, tayi fari da ido, yace yau kuma zabinka ne ba zabin tsoho ba? Yace ai ko da yaushe ke zabina ce, u are my choice, let me tell u a secret, i fell for u d very first time i set my eyes on u, sai dai bansan ko so bane don ban taba yi ba sai a kanki, Ashe tsoho ya rigani hango hakan, nd bansan me zanyi ba idan be hadani da ke ba, kece Zabina, kinji?tace Nagode, what kingode? Ke matar likita, wannan kunyan naki na shiga rayuwata, yanzu fa kika gama min wanka, y isit so dificcult to look me in d eye nd tell me u love me? Zan fayi addua Allah ya sa babyn ki mace ce ba namiji ba, inga ta inda za a ma Tsoho takwara, da sauri tace wallahi ba Amin ba, InshaAllah namiji ne, kai koma mace ce shes welcome, Don wallahi sai an ma tsoho takwara ko namiji ko mace, zaid yace how? Tace Musbahatu za'a sa mata, Zaid ya riqe cikinsa yana daria, wato sai dai anyi mai takwaran ko? Tace Gbam! Yace ban manta ba, look me in d eye nd tell me u love me, ta hada idanuwanta da nashi, ina sonka, i love u, ina kaunarka, ina maka son da ban san irinshi ba, ba kalaman da zasu bayyana kalar son da nake maka, sonka a jinina yake, i love u so much Dr Zaid, i want to spend d rest of my life with u, I cannot live without u, Allah ya bar mu tare, dadi kamar ya kashe zaid yace Amin Maman Musbahatu ko Musbah, tayi daria ta sa hannunta biyu ta rufe fuskarta tana daria. Ya zame hannunta ya bata wani hot kiss, cikin wata kasalalliyar murya yace, I am going to change the way u look at me, i'll put desire in ur eyes, u are mine since day one, even if we are from different worlds u belong only to me, u're created to be with me alone, i will choose u in a hundred life time, in a hundred worlds, in any version of reality, I will find u and I will choose you, because u are mine, nd u belong to me. I love you so much Rumaysa'u ta share hawayen farincikin da ya gangaro mata ta rungumeshi tace i love u too yazayd, i love u more.
_Bibilicious Biebee_
6⃣5⃣ 🏡Gidan Gandu🏠 by💕Biebee Isa💕
Hausawa nacewa Idan Zaka so mutum ka so shi saisa saisa, Idan zaka k'i shi to ka k'ishi saisa saisa, kar ka yawaita so, kuma kar ka yawai ta k'i, don wata rana So na rikidewa ya koma K'i, haka ma K'i na rikidewa ya koma so, Idan zaka so mutum, to ka so shi dan Allah, idan kuma zaka k'i mutum ka qi shi donAllah. Ni na yarda da wannan batu, na yarda da wannan zance, idan akayi laakari da Yadda Masoyan nan 12 suka kasance Maqiyan juna a farko, kamar masu ganin hanjin juna, suka tsauwala k'iyayyar juna, farat daya, dalili daya ya chanza Akalar Kiyayyar nan, ya koma soyyayah, yanzu sun kasance kamar tif da taya, har suna ikirirarin basa iya rayuwa ba juna ba. So tsaftataciyya suke ginawa a rayukansu, Tabbas Tsoho ba ya Raye, amma suna jinshi a kusa dasu, He lives in them, saboda duk abunda zasuyi su kan yi tuni da abun da ya umurce su a baya, sai su ga kamar a lokacin ne yake basu umurnin yin Abun. Burin Tsoho ya cika, kansu hade, Su Baba Mudassir da Baba labaran tsaye suke kan gidan, duk abunda suka san tsoho zaiyi shi sukeyi, wanda suka san bazaeiyi ba ba sayi, ko da a ka zo raban Gado, hankali kwance a ka gudanar da rabon, kowa ya samu kasonshi, Dama kafin ya rasu ya danqa ma waenda basu da gadonshi filaye da gonaki, Wasu daga cikin 'yayan tsoho sun gina Massalatai, islamiyoyi, rijiyoyi a kauyuka da sunan Musbahu Bn Zailani. Matanshi sun hada kansu, ba zaka taba cewa akwai wani abunda ya taba shiga tsakanin su ba, sun zama Tsintsiya madaurinki daya. Kullum Adduarsu Allah ya kara hada kansu, ya kai ma tsoho ladar abubuwan da sukayi domin shi..
5 years laterlater
Architect Suraj Umar da matarsa Bilkisu na da yaro daya Musbah(Hanif) mai kimani shekara 5
Engr Samir Gambo da Matarsa Amira na da yara biyu mata, yan biyu ne, Hassana(Sadeeqa) da Hussaina (Sajeeda) shekarunsu 3
Dr Zaid Mudassir da Matarsa Sister Rumaysa na da yara biyu maza suma yan biyun ne, Musbah(Afeef)da Rabi'u(Areef) shekarunsu 5
Aero. Engr Mu'ammar Labaran da matar sa Islahulkhair na da diya daya mai suna Aishatu(Yesmin)tana da shekaru 3.
Pet. Engr Jawad Mudassir da matarsa Fadila na da diya daya mai suna Karima(mimi).
Pharm. Zayyad Hussain da matarsa Hanifa na da yaro daya me suna Musbahu(Ayman)shekaranshi 6.
Sun hadu duka a GIDAN GANDU kasancewar duk suna hutu, Yau Tsoho ya cika shekaru 6 da rasuwa. Amma ba abunda ya chanza nadaga Gidan.
*****
Ayman, Afeef, Areef, Hanif Suka shigo parlorn Tsoho a guje suka fada kan Hajia Babba, suna cewa great grandma, munje Kabarin Tsoho, yanzu Grand Pa Abbakar ya kaimu, mun mushi addua, kuma mun gaya mai kuna gaisheshi kuma kunce kuna sonshi. Hajia babba tace Yauwa yan yarorina, kun kyauta, Grtgrandma Ama, kamar naji tsoho yace in gaisheki, duk akayi daria, Aunty nuratu tace u guys are hallucinating, d dead cant talk, Areef yace but Grams nur, i was told that Tsoho lives in us, Right Dad? Zaid ya yi murmushi yace Right son, Ayman yace so u see grams even if his long gone, we feel his presence around, Aunty Abida tace lallai wadanna yaran, u are soo brave, wayan ku yayi yawa. Sukace we have to be brave Grams, afterall we are our fathers sons, akayi daria duka, Ayman yace Grams Zainab, Dad yace min if i grow up, m going to get married to Yesmin, Wowww inji yan dakin, Hanif yace nd mimi will be my wife, Arif yace mummy told me i will be sajida's husband, Aunty Sadiya ta kalli Afeef tace kai baka magana? Wace zata zama matarka? Shiru kawai yayi yana kallonsu, Hajia Babba tayi karaf tace shine hassan ko? Maysah tadaga kai eh, tace ahap, ai idan be dauko halin ubanshi ba sai an chnza mai suna, miskili ne, da ya gado Zaidu sai ya zarceshi, duk akayi daria. Arif yace twin bro zai aura twin sis din sadeeqa, sajeeda,. Mu'ammar yace ku zonan, duk suka taso suka zauna kusa da shi, yace i can see my boy's are smart huh? Ina fatan yanda kuke da baki haka, haka kuke a school and islamia, suka daga kai yes Abba, yace i want u to study hard for now, i want you to grow into handsome prince-s charming nd make alotta money like Ur Daddy Samir, only then i'll get u married to ur betrothed, kungane? School first, ina so kuyi kokari sosai a makaranta, i want u to be amongst d best 3 in ur classes, duk wanda yayi more dan 3rd position, bashi ba hawan private jet dina, nd no vacation a Dubai kuna jina? Suka daga kai yes Abba, mun gane, yace good boys. Aunty Zainab tace mungode 'ya'yann mu, na fahimci cewa kuna gina soyayyar Zabin da tsoho ya ma yaranku a zuciyoyinsu, gwara tun Yanzu su tashi da son junansu, kar sai lokacin suce ba su san zancen ba, kamar yadda wasu sukayi a da, su fadila da Hanifa Suka fashe da daria,Aunty da mu ake kenan? Tace kun tsargu ne? Surah yace mun cika ma tsoho buririkanshi bayan ya rasu, wannan kadai ya rage, yace shima da lokaci yayi InshaAllahu za mu cika mai Burinsa na karshe, Allah dai ya kaimu rai da lafia, duk aka amsa da Amin.
Jawad ya kalli yan matan yace Hello Angels, Mimi, Sajeeda, Sadeeqa da Yesmin suka amsa da yes Daddy, wanna have some Ice cream? Da murna sukace yes Daddy, Okay, before i buy u icecream, ya'll shud get up and say ur Regular Prayers after Salat, loudly. Yaran su 7 suka miqe suka tsaya gaban parlorn yanda kowa na kallonsu, suka hada baki wurin cewa, Oh Allah Grant us Jannah, Oh Allah forgive our Sins, Oh Allah bless our Parents, Oh Allah, Let Tsoho's Soul Rest in Peace, Oh Allah reunite us With our Grt grandpa in Jannah. Amin, kowa ya amsa da Amin, Yaran sun burge kakkaninsu, sunji dadin Adduan da jikokinsu ke ma Mahiafinsu, duk suka hau kabbara suna jinjina ma iyayensu, Hajia Babba ta yabe baki tace wai su wadannan tattaba kunnen namu, ba sa hausa ne, Ko me sai da turanci? Me sukecewa ne, najk harda kiran tsoho,? Zayyad yayi murmushi. Ya fassara mata abin da sukace, Hajia Babba ta shiga tafa hannayenta tana cewa Sankyu Sankyu, Yauwa Yaran Albarka, Allah dai ya Raya ku duka, duk suka Amsa da Amin....
Long Live GIDAN GANDUN MARIGAYI TSOHO , Long live Zailani Family.
TAMMAT BI HAMDULILAHI.
Alhamdulilah, A nan na kawo karshen K'ageggen labari mai suna Gidan Gandu, kar wani ya ga kamar wani abu a ciki yayi kama da abunda ya faru a familynsu, toh wannan labari na Gidan Gandu k'irk'irarene, be faru ba, Nayi shi ne domin Isar da Sako a cikin Alumma, kuma ina fatan sakon ya isar. Abunda nayi kuskure ko ba daidai ba a gafarta min, danAdam Ajizi ne.
Thank u Nuratu Adamu Maiyadi for coming up with the name "🏡Gidan Gandu🏠"
Thanks Yalex, The Only Male i
know that Read this Novel.
Thanks Indon Biebee.
Thank u All Members of FEEDOH &BIEBEE'S ✍🏻FANS
WORLD OF HAUSA NOVELS📚
BEAUTIFUL LADIES💅🏻
GORGEOUS ANGELS👻
AFSHAHAR NOVELS📜
DANDALIN LUBIE MAITAFSIR
FANS👻
Gareku Masoyana, ku sani nayi 🏡Gidan Gandu🏠 domin kune, idan baku ba 🏡Gidan Gandu🏠, Nagode da Soyayyar da kuka nuna min, Da wa'yanda na sani da wa'yanda bansani ba, da masu kirana, da masu min messages, both sms nd whatsapp, da wanda basu samu damar samu na ba, ina miqa Godiata gareku. Thanks a bunch 💕Biebee Isa💕 loves you, wherever u are, you'll never be far, i'm keeping you near inside of my Heart. I love you all.
Nagode! Nagode!! Nagode!!! #Grateful #1love
Urs Truly Zainab Isa A.K.A Hell 💕Biebee Isa 💕IG:@nerb_esa
_Bibilicious Biebee_