Thursday, July 23, 2020
JARABABBEN KISHI Page 21 to 30
Share this
JARABABBEN KISHI Page 16 to 20
Share this
JARABABBEN KISHI Page 11 to 15
Share this
JARABABBEN KISHI Page 1 to 10
Share this
Monday, July 1, 2019
JARABABBEN KISHI part 4 (The end)
Kan Abeeda ta dawo tace "sai dai wannan tsohuwar ta fita tabar muku dakin, amma badai gidan ubana ba kinji".
I itama miyau ta watsa mata a saitin bakin Abeeda. Sannan ta fice ta shige motarta sai da tasa motar tayi gunji kannan ta figeta, don saura kadan ta take Abban su Saheeb din Nace hmm
Juyowa yayi yace "tabbas wancan Suhayr ce Lafya take gudu kaman zata tashi sama?" Tabe baki yayi yace "Allah ya tsare."
Tsakiyar tanka sheshen falonta ta tsaya tana huci, Tace "tabbas hakurina ya kare, Bazan iya jurewa irin abubuwan da Saheeb yakemun ba harya je ya aura kawata koda yake ba komai Allah yana sama yana kallo ban gaza ba, wajen yiwa mijina biyayya ba wajen sauke duk wasu hakko ki waje daya na gaza
Wajen Rashin boye garwashin kishina, JARAB EL GHIRA Akaro na farko da suhayr tafara karaya kenan Saheeb daya ya farfado ya nemi Abeeda ya rasa, bai zarce koh ina ba sai gida koh a mutu koh ayi rai koda Suhayr zata yanka tsokanshi ne sai yaje ya fayyace mata komai. Abinchi takeci takeba Noor abaki yana mata kwaranci,
"Abba! Abba!!" Kallonsa tayi tace "Abba baya sonmu karka sake kiran sunan Abba kaji."
Hancinsa ta lakuta. "Saheeb yana tsaye yace "abbanka yana sonka sosai, karka sake kayi amfani da kalmar umma She's rong" dagowa Suhayr tayi da mamaki tace "what!?
Me kazo yi a cikin gidan nan? Kafin in rufe idona in bude Ka fit......." bata karasa ba ya rufe mata baki," "Am going no whr suhayr you can do your worse but today you have to learn me your ears
Bantaba zatan zaki iya aikata munmunan aikin da kika aikata yau ba". Hmm wata dariyar mugunta tayi tace "koh ???". Saheeb yace "ki tuna Allah subhanahu wata'ala ya fadi acikin littafinsa mai tsarki, yace auri bibbiyu, uku-uku hurhudu Sannan yace in baza muyi adalciba muyi daya,
Toh kinga ina da kwakkwaran hujja ta kara aure". "Dakata Saheeb" cire hannu tayi daga cikin abinchin ta kira mai mata raino tace dauki Noor kuje dakin wasa.
Kusada Saheeb tazo tace "dole kasamu bakin yimun wa'azi tunda yanzu kasamu masu gidan rana, I don't blame you saheeb I never new that you are Savege till today, da baka da komai ai ka hakura da aure sabo da jaraba dake cinka,
H'm na mamajo Saheeb in kaso kayi Hudu I don't care amma abun da nake so kasani, In har ka cuceni dai-dai da kwayar zarra ban saniba toh Allah kadai zai isar mun ba mutum ba,
Sannan in dai anan gidan zakasa Abeeda toh bazan taba yarda ba, Sannan inaso mu zauna Ayau muyi lissafi kabani uwar kudi kadauki riba, Saika ciyar damu dashi." Tirkash saurin juyowa yayi ya kalleta tace " kwarai yau za ayita ta kare tunda har ka iya kara aure,
Nasan katsaya da kafan ka kuma gidan nan da kake gani na barshi nima Sai dai ka kama mana haya mu biyu". Zare Ido yayi cikin rudani, na shiga uku me yasa Suhayr zata yanke mun irin wannan hukuncin?
"Pls Suhayr kiyi hakuri kiyafe mun," Tace "Ai ni baka mun ba amma kayiwa kanka, Inace kudi gareka? ka sani yanzu basai anyi nisaba, Zauna muyi lissafi gobe muje ka turamun a account dina".
Saheeb bashida bakin magana Sai zufa yakeyi. Anyi lissafi ancire kudi naira miliyan biyu, Kudin da aka bashi jari, Saheeb yayi matukar mamaki ganin riba zunzurutun, riba har tafi uwar kudi yawa
Baiyi mamaki ba saboda yasan cewa, ya San yadda yake tafiyar da kasuwancin shi, Murna ya dinga yi itako Suhayr bataso ba. "Toh ina saurare zuwa jibi Don bazan zauna a cikin gidan nan ba, A cikin gidanka nake so in zauna bana ubana ba,
Sabi da ko wacce mace da gidan miji take takama ba gidan uba ba." "Toh" yace tunda yaga ta sauko, tashi yayi yace "zani gidan umma da sauri tace "wace umma look man you are not going any whr we are sleeping together Harsai ranan daka sama mana gida mu biyu mu koma,
Ina so koh shago bazaka budeba," Saheeb yana masifar son Suhayr shi yasa komi tayi yakanji haushi amma, sonta baya koh girgidi a cikin ziciyarsa. gidan su Saheeb koh amarya tana chan tayi tsuru tsuru, sai hawaye ke zuba a idanunta.
Kowa ya ganta sai ta mika mai buhun tausayi, hhh lol 😩 gaba daya halittarta Suhayr ta canza, Hatta hakoranta na gaba babu guda daya "Nikwa me zan yi banda dariya, an maidata tsohuwar karfi da yaji"
Umman Saheeb ce ke lallashi, yan'uwan Abeeda duk sun zo. Umma ta dinga basu hakuri, Abeeda tace "yanzu wani mataki hjy ta dauka akan Suhayr?".
"Wani mataki ta dauka kuwa suda sukeda sojaji da mopol da yan sanda? Ai sune gwamnati", cewar auntyn Zaria kanwar hjy saude ce aure ya kaita Zaria shi yasa ake ce mata auntyn Zaria. "ke kinsan cewa matarsa yar iskace kika shige mai?"
Abeeda tace "Aunty koda Suhayr zata kasheni ne naji nagani, zama da Saheeb ba fashi," wage baki aunty Zaria tayi tace "Allah ya baku zaman lafya kuzo mutafi, ba wanda yace kala, Sai kanwar babanta "inya samu gidan a kawo miki kayan dakin."
"Toh" Abeeda tace jiki ba kwari gashi ba Saheeb ba labarinsa. Musty ne yashigo yana waka, mai rabon shan wahala koh a karkashin gado yake saiya iskeshi, kowa binsa yayi da kallo daga karshe ya fashe da dariya yace " ke kadan kika gani wahala yanzu kika fara sha, yanzu kika tsoma kafa indai Suhayr ce, kin kade,
Ji yadda ta canza miki halitta wata rana kar yaki zatayi ta watsaki waje....." "Kai dakata" cewar ummansu "bansan shashanci"
Dariya yayi ya fice aguje. Saheeb ya damu kwarai Rashin ganin Abeedah haka itama. Neman gida yakeyi shida Suhayr suke zuwa koh ina, Anyi nasara ansamu gida a wajajen, kofar famfo.
Flat ne kato mai falo biyu, akowani falo akwai dakuna biyu sai kitchen a ciki Suhayr tace "gida yayi kyau, yanzu zan dawo gidan mijina in sakata in wala," kallon ta kawai Saheeb keyi. Yakasa cewa uffan, can yace "Yanzu hankalinki ya kwanta koh?"
Juyowa tayi da sauri tace, "Ina ka taba ganin mai kishiya hankalinta a kwance? Ai har abada tana cikin tashin hankali har sai taga tarabu da kishiyar nan lafya, ko kuma kishiyar ta mutu" Kasa cewa uffan yayi yace "muje insamo miki mai kwashe kaya"
"Toh" tace acikin zuciyanta tace " hmmm na dauka zakayi magana ne Saheeb dana fede ma bindi har wutsiya" Sun tare a gida daya Saheeb ya tarasu don yayi musu fada,
Sannan uwar gda ta fadi kwana nawa ta yanke? zaa dinga raba kwana. "dan Allah Ku hada kanku Suhayr banason tashin hankali, nayi aurene don samun natsuwa da kwanciyan hankali, badon indinga raba fadaba,......
"Kai har kanada bakin cemun, kayi aure don kwanciyan hankali? daman duk zaman da mukayi daman zaman azaba kakeyi?"
Saheeb yace "Ah ah Suhayr kinyi misunderstanding dinane ba haka nake nufiba".... " ai bakai ba kwanciyan hankali, tunda ka iya kara aure, kwanciyan hankali sai dai kaji a makota, Kwana kuma kuya shafa kuna iya yankewa", dan Nikam sai---------------------------
------------------------------
----------- ---------------
----
[7/23, 12:18 PM] 🅰 " 🅰 " D, 🅱⭕Y: DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚
[7/23, 12:19 PM] 🅰 " 🅰 " D, 🅱⭕Y: _______JARABABEN*KISHI______
_______________________________
------ Littafi --- Na daya ------
----- 🔛-----
**★** PART (13) **★**
Post
By :----Man Bash ----
.
.
Fuuu ta tashi kitchen ta shiga tafara dafa abinci itada hauwa mai aikinta. Tuni kamshi ya bude koh ina gashi Saheeb yunwa yakeji, Tashi yayi ya fita duk akan idon Suhayr, Abu ya ruko a Leda guda daya..
Tace hmm " wato naka kaida amarya ko toh kayi kadan, kofar taje ta bude tace "Memuka samu ne Ango mijin amarya"? Bata tsaya ba ta amsa ledan taga kaza daya da lemuka, dagowa tayi tace "Ashe adalcin da kake ikirarin zakayi kenan........."
"Na dauki wannan ka koma ka siyo muku wanda zakuci nima inada bakin cin kaza." bata tsaya ta kalli fuskanshi ba, ta wuce kara fita zaiyi Abeeda tace karka damu Mijina na hakuri , Tabbas indai haka zaa cigaba da zama tabbas ba Adalci koh sauraran Abeeda baiyi ba ya fita yaje ya siyo mata wasu, Ya wuce dakinta dashi,
Wani irin darene Wanda gaba daya sunkasa tantace irinsa, babu wanda ke dokin wani cikin su, kowa bakinciki yakeyi, to Ni me zance sai dai fatan azauna ayita hakuri kawai . Suhayr sallar dare takeyi kullun har kwanan Abeeda din suka kare,
Tana Neman tsari Allah ya kareta daga sharrin kishiya. Ya shirya tsaf zashi shago, ya fito yace "Suhayr zan fita," Tace "Allah ya tsare ya kiyayeka yabaka sa a." wani irin dadi yaji wanda baitaba jiba, tuni ya rungumeta yayi mata"hot kiss "Zan aiko harisu anjima zai kawo muku kayan abinchi." "Toh" tace
Ah "nima zani school, kabari kawai inzan dawo zan biyo in kwashi kayan," komai cikin gidan Saheeb yana tafiya dai-dai amma fah baida wani sakewa, Saboda Suhayr ta tsaya kaida fata cewa bata yarda da cuta ba,
Wata Safiyar juma'a ne Abeeda na kwance tajiyo Suhayr ta kure waka, ROMANTIC na korede bello da tiwa savage Itakuma a rayuwa ta tsani jin wani sauti dazai dame jinta. Tashi tayi koh Sallama
Sai kawai ta fada falon Suhayr direct wajen home theatre ta wuce ta zare socket din. Suhayr abun yabata mamaki, baki bude Suhayr tace "ke wace irin karyace marar sanin ciwon kai?
Banshiga harkanki ba kishiga nawa? Meye matsalanki da wakana, You must be very stupid Abeeda, you heard me ryt?". Abeeda tace "Kin wani cika mana gida da sauti ki tuna nan gidan mijinane Suhayr ba gdan ubanki ba". Ta nuna Suhayr da yatsa.
Tuni Suhayr ta karya dan yatsan tace, "kinyi kuskuren sako ubana cikin wannan maganan". wayarta ta dauko ta kira Saheeb yana dagawa tace "Saheeb yanzu zanyi kulikulin "Saude" da matarka." Saheeb yayi saurin cewa "Suhayr meya faru???".
Sai tace "Bari na gama da ita tukun sai in samu daman yimaka bayani" Yayi saurin cewa "Noo Suhayr pls don't do that." Karaf ta katse wayan Tace "yau zan nuna miki cewa nima gidan mijinane,
Bulala ta samu takama Abeeda tayi mata lilis da jiki tace " get out of my room" ta nuna mata hanyan fita. "Yau naji ikon Allah na hana akawoki da redio ne whey?
Zaki takurama rayuwana Yaunaji masifa Banda kaddara data Riga fata ke kin isa in tsaya dake?". Ta dinga sababi ita kadai Saheeb ne yabaro shago yazo kafin yazo tuni Suhayr ta gama da Abeeda,
Kiransu yayi gaba daya yace "Suhayr meye dalilin fadan nan?" "Saheeb nan dakinane koh ba dakina ba" yace "kwarai naki ne". Tace "inada ryt din yin yadda nakeso koh banda shi?" Saheeb yace "kina dashi" "Shine wannan kyankyason zata zo har dakina ta kashemu wakar da nakeji?"
Saheeb ya kalli Abeeda yace "Abeeda meyasa kikeson shiga sabgar daba takiba? Karki sake koda wasa don wallahi Suhayr bazata raga miki ba, Kowa ya zauna a matsayin sa". Ahaka rayuwa taci gaba da tafiya
*BAYAN SHEKARA BIYU*
Saheeb arziki ya bunkasa har kasar waje yake zuwa ya daina bada sako. Lokaci guda ya dankara katon gida flat hudu , Aiki ga mai yinka Ga sasan yara Gana mahaifinshi, Gana mai gadi. Suhayr kam ta kammala karatu, Aiki take a GtBank.
Abeeda tunda tayi aure narasa dalilin ta na tsayawa. Suhayr tuni ta kara haihuwa, yara biyu lokaci guda, da Sadiq da farouq, Itako Abeeda yarta daya mai sunan mahaifiyar Saheeb.
Kwatsam Saheeb ya kara Neman aure, Suhayr tace Sam bada itaba ba wata shawara dazata bashi, Nanfa Abeeda ta tsaya kaida fata. Itace ta shirya akwati, Suhayr tace "yau naga sabon salo tusa a loudspeaker Hmmm kishiya har wata abun zakwadi ce?
Anyi aure komai Normal suka koma sabon gidan su komai na daki saida Suhayr ta canza, Harta TV irin katonnan tasa, Suhayr yace zaiyi musu kaya itada Abeeda tace bataso abata kudinta.
Gida yayi albarka da yaya. duk shekara sai Abeeda ta haihu haka ma amaryar maryam, Ita koh Suhayr tace ta gama Allah shi raya mata ukun, Sai da saheeb yayi mata hudu ya rufe kofa, yayi farinciki yakuma godewa Allah daya barshi a Raye ya cika burinsa,
Kowa a cikin gdan yana bama suhayr girma, aunty kasa aunty sama. Har biyota sukeyi sasanta, dukda tana kishi amma daga baya taga Ashe abun ba haka yakeba, Inkayi dacen abokan zama tabbas kayi babban Sa'a
Ana girma ana hankali, kannin Saheeb duk sunyi aure, haka Suhayr ta tsaya kaida fata, Amrah wan Suhayr ta aura Sulaiman, Rayuwar gidan Saheeb abun shaawa, Shi kanshi girma yazo. Noor yana Nile university dake Abuja, yanbiyu suna Turkish international college,
Ammafa fada tsakanin Abeeda da maryam anayi saboda maryam bata iya gani ta kyale, Suhayr ce tazama alkali, Maryam batada kunya haka takewa umman saheeb Rashin kunya,
Suhayr tayi dariya tace "hmmm maryam kenan" ta dafata tace "Wata rana zaki bari nayi abunda yafi wannan Wallahi haka duk Rashin kunyanki nafiki, tunda kika ganni haka toh duniyace, ta horani, Naga ba sarki sai Allah abunda ake bazaa fasaba,"
Juyowan da maryam zatayi tace. "Bana bukatar wa'azinki, karki kuma shiga sabgan daba takiba". Suhayr ta mutu da manaki batasan lokacin data wanke maryam da mariba, tace "kinzo zamanin nayi sanyi kalau, da baki isa ki nunamun dan yatsaba,
Kaza kawai wacce bata gajiya da masifa Banda jaraba irinta maza me saheeb zaiyi dake? Yau nasan darajan iyaye bazan yarda kiciwa umma mutunciba, Never" ta tofa ma maryam miyau
Abeeda tace "Suhayr antuna da kenan", babban abunda zatama ta huce shine ta tofama miyau. Saheeb na tsaye yace "good Suhayr kinyi mun dai-dai". da Sauri ya rungumeta. Yace "duk cikin matana babu wacce rigimanta takaina Suhayr, tunda kikaga tayi sanyi toh wallahi tayi Wanda yafi wannan muni, kafin kizo."
Nan ya tarsu yayi musu nasiha. gida yadawo normal kaman da, Inna-nallahi wa'inna ilaihir rajiun, Tabbas dukkan mai rai saiya dandana mutuwa, Allah yayiwa mahaifin Saheeb rasuwa, sanadiyan mashin daya
bigeshi
Banda yaxo da ajali, koh kujewa baiyiba. family din dan-koli sunyi babban rashi inda Saheeb yakasa zaune yakasa tsaye. kassss Allah Sarki to Nima dai ganin haka ne yasa naje dan Ayi zaman makokin dani ehe------------------------------
------------------------------
----------- ---------------
----
[7/23, 12:19 PM] 🅰 " 🅰 " D, 🅱⭕Y: DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚
[7/23, 12:32 PM] 🅰 " 🅰 " D, 🅱⭕Y: _______JARABABEN*KISHI______
_______________________________
------ Littafi --- Na daya ------
----- 🔛-----
**★** PART (14) **★**
Post
By :---- Abdul Dboy ----
.
.
Kuma shine takun karshe
----------------THE END---------------
Anyi bakwai kowa ya watse, Musty shine ke kan komai na dukiyar mahaifinsu, dayake basuda yan'uba
Bayan kwana biyu suhayr tadawo daga office karfe shidan yanma, sai ta jiyo hayaniya dayake da gajiya sallar kawai tayi ta fita, maryam tagani sai tada jijiyan wuya take, Tana cewa "don kin tsaya kaida fata a auroni shine me?
Sai naga niba cin amana nayiba keko, ananar kawarki kikaci kika aure mata miji Kece keda rabon shan kunya
baniba,"
Suhayr takasa koda motsi kallon Abeeda takeyi wacce take cikeda nadama, Muryar suhayr sukaji tana cewa "maryam banda shirme irin naki, dani da Abeeda mutu ka raba takaimin kaza,
Indai akan cin amana ne nayafe mata duniya da lahira, Sanadiyyan aureta nayi nadaman wasu abubuwa da dama, ciki harda. rage *JARAB EL GHIRA flames of jealousy da nayi na gane cewa kishi ba hauka bane,
Nagane cewa kishiya abokiyar zama ce, tabbas kaman yadda nayi dace daga baya da Abeeda tazo da zafin kai daga baya da taga ba riba fadan da kishiya, Maryam inaso kiba Abeeda Hkuri Sabi da munriga mun zama daya, tunda
muna da zuri'a".
Ana haka saiga zulaihat taho cikeda isa da takama, Tace "tabbas aunty suhayr
kinyi gaskiya, Munriga da munzama daya saidai fatan Allah yakara hada kan duk wasu kishiyoyi, dake fadin duniya, ya bamu hskurin zama da juna
sannan ya sassauta kishi a tsakanin mu".
Gaba daya suka rungume juna, daga nan kowacce tarike girmanta, Saheeb koh anzama Alhaji, Saida yakai su su duka Makkah harda mahaifiyarsa, da
mahaifiyar kowace matarsa, Saheeb yana cikin farin ciki, a cikin gdanshi burinshi ya cika,
kowacce kokarin faratamai rai takeyi.
To Nima ganin sun hada kan su yasa Na dauki Biro Na da yan' takardu na nayi gaba dan naga kamar babu wata fa'ida idan naci gaba da zama a cikin wadan nan iyalin ehe
Dan haka nake cewa ku SOOREE ehe ana mugun tare fah, Hhhh lol 😜 laifin dadi............?
*ALHAMDULILLAH................
.............. A NAN NAKAWO KARSHEN WANNAN 👉 LITTAFIN MAI SUNA WATO •JARABABEN*KISHI• HMM HAR KULLUN MAGANA TA DAYA CE WATO