Bude Motan yayi ya fito, ganin bai cemata komai ba yasa itama ta bude ta bisa a baya,daki ya Kama musu sannan aka gaya masa nombar dakin, binsa tadinga yi har dakin ya tura kofa suka shiga.
Zama tayi a gefen gado tana bin dakin da kallo,fita yayi sai gashi yadawo da leda a hunnunsa ya zauna kusa da ita.
"Ya sufyan ba rakaka kace zanyi ba,mekuma mukazoyi hotel?".
Murmushi ya mata " bagashi kin rakoni ba,abinda kuma kikazoyi shine kinzo wurin mijinki, haba sofy kwata kwata kin biyewa Momy ta kwacemin ke, takaiga har fitama inzakiyi sai dai kifita bansaniba, gaskiya ni nagaji da wannan horo, nagaji safiyya".
Kallo ta bishi da shi dan ya bata tausayi,itafa ba laifinta bane hasali ma ita tama fishi damuwa kan rashinsa kusa da ita ,katse mata shirun yayi "ga ice-cream nan dauko mana musha".
Mikewa tayi jiki ba karfi dan bacci takeji kuma tasan da kyar zai barta tayi, tare suka sha ice cream din sai hira yake mata kaman bashi ya daure fuska dazun ba hmm namiji kenan tunda yana bukatar wani Abu yanzu ba.
Hamma ta farayi"ya sufyan bacci nakeji",
Shagwabe mata fuska yayi"bacci kuma sofy". Dariya yabata kawai ta mike ta wanke bakinta sannan tazo ta haye gado. Sai dai yayi shafa'i sannan ya kashe musu wuta ya kwanta,janyo ta yayi lokacin bacci ya fara dibarta, tana jinshi ta hau mutsuu mutsu, rada mata yayi a kunne "plsss...."
Ranar sai uku da rabi ya barta, aiko baccin gajiya yayi gaba da ita. Da kyar ya sungumeta zuwa toilet ya mata wanka sannan suka kwanta. Sunso su makara sallahr asuba dan sai da aka idar da sallahr a duk masallatai sannan ya farka, a gurguje ya tasheta sukayi alwala ya jasu sallah. A nan kan daddumar bacci ya kara dauketa, kallonta yayi yana murmushi "kyau ne da ita ciki da wajenta".
Daukanta yayi ya kwantar da ita sannan ya zauna ya cigaba da azkar dinsa na safe, yana gamawa ya bita suka cigaba da baccin da basu suka farka ba sai sha biyu.
Shiya fita ya siyo musu abinda zasu ci, lokacin tafito daga wanka daure da towel, ganin yadda tayi da fuska alamun rigima ya sashi karasawa gareta "lafiya sofyna".
Cikin shagwaba tace "kaga ni yanzu Ina kayan dazansa".
Murmushi yayi hade da Jan kumatunta "shine abin rigima to ni nafison kizauna da towel kinfi kyau".
"Nida zan wuce yanzu".
"To naji kibari muci abinci muyi sallah sai muje insiyan miki ko".
Da haka ya lallasheta sukaci abincin tana rike ta towel din dan karami ne kar ya fadi, sai kallo yake binta dashi, sunayin sallahr azahar ya dinga lallabata har sai da ta kara barinsa ya Kasan ce da ita "kai ya sufyan baya gajiya".
Sai yamma ya fita ya siyo mata riguna dogaye kala biyar masu kyau, bayan ta yi wanka ne tace masa to ya maidata gida, ya ce ta bari sai dare tukun, bayan sunyi sallah isha'i sai wani lallakfemata yakeyi da salon soyayyarshi yana mata didin baki dan ta mance, haka ta kara kwana wurinsa suka sha soyayyarsu.
Kwana biyun datayi wurinsa ita kanta tasan ta gurzu,shikuwa ba abinda ya damesa har wata 'Yar kiba yayi ta kwanciyar hankali.
Sai yamma ya maidata gidan aunty Amina,safiyya sai tambayar aunty take ko Momy ta kira ta tambayeta "ta kira mana jiya nace kina gun mijin ki".
Hanjin cikinta ne suka kada "nashiga aljanna, dan Allah aunty ki gayamin gaskiya".
Aunty tayi dariya "kedai kikasani, kigama hada kayanki muje na kaiki, wasa nake miki, kedai ba daga zuwa min kwana biyu kin gudu gun ya sufyan ba".
"Uhm wallahi Anty bazaki ganebane, nayi nayi ya dawo dani yaki"
"To wai momy ta barku kukoma gida mana, ko yana wani abun anan ne?"
"Uhm uhm, wai saita sa rana"
Gidan umma suka soma zuwa sannan suka shiga gun Momy,tunda ta dawo kuma aka koma gidan jiya, satinta uku gidan Momy tayi fresh tayi kyau abinda, ko'ina a jikinta ya cicciko hips tun balle hips dinta da kirji, dama kuma ga gyra tana sha, shiyasa ko kallonta nayi sai ka kara.
Safina ce yau tazo gidan , can anjima saiga aunty Amina tazo, safiyya sai murna take ansamu Abinda akeso, Suna falo sai hira sukeyi.
Safina ta kalli safiyya wacce take sanye da Riga purple doguwa fitted ce rigar,"lallai yarinya kina hutawa gun Momy, kinga yadda kikayi kuwa".
Safiyya tawani juya mata ido "ya San ranki, ba dole nayi kiba ba ,ba Inda nake zuwa".
Sufyan ne ya shigo folo., idonsa akanta ya zauna suka gaishe shi, kallon tuhuma yake mata cewan ta boye kanta. Juyawa tayi ga momy data karaso falon da plate din abinci a hannunta "yawwa auta ga ganyen nan dakikace kinaso".
Dariya tayi da Sauri ta janyo kwanan gabanta,safina ta kalli Momy "wai Momy yaushe kika daina son mu ne dan Allah, yanzu sofy ce kadai a falon?".
Aunty Amina tayi dariya "to ke safina bakiga ita safiyyar lalura gareta ba, ai dole muyi hakuri har saita sauke".
Dukkan su su ukun suka juyo da kallonsu ga safiyya wacce ta Kasa hadiye ganyen data tura a baki.
"Nifa dama ince, wannan kiba datayi da haske Ashe Ashe da magana, Ashe an kunso".
Momy tabi safiyya da kallo baki bude wacce jitayi kamar ta Ruga da gudu dan wannan abu "kar kicemin yanzu auta ciki gareta ban saniba Aminatu a gidannan".
Aunty tayi dariya Kasa Kasa ganin sufyan na Neman zillewa ya fice "haba Momy, kalleta fa , nasan ko nayi rantsuwa bazanyi kaffara ba, safiyya Nada ciki".
Momy ta soma tattafa hannuwa "ooh ni mairo, Ashe yaron nan Baka da kunya, yaushe kuma hakan ta faru ban saniba..shikenan yaran nan sun maidani sotuwa...
[3/9, 9:06 AM] YAYA HAYAT: ```MACE KADARA CE MAI TSADA```
```©UMMU SABREENA da AUNTY AYSHA...```
```Febuary 2017```
```<<55>>```
Sannu ya dinga mata tana tallabe a jikinsa, ya dauko tissue ya goge mata baki sannnan ya gyara mata kwanciya Inda tayi male male a Kasa "sofy mutafi asibitin ko".
Girgiza kai tayi "haba sofy tayaya bakida lafiya kuma kice kar muje asibiti, ko na dauke ki ne mu tafi"
Da kyar ta bude bakin ta "dan Allah ya sufyan ka barni yanzu bacci nakeson yi ,inna tashi sai muje".
Janta yayi ta kwanta a jikinsa yadinga shafa mata baya har bacci ya dauketa "to yanzu haka zata zauna ba komai a cikinta".
Yana nan zaune shiru sai baccinta take jikinta duk yayi laushi amma dai ba zafi. Kwantar da ita yayi sannan ya fita ya kulle gidan, yacewa Amira taje ta kwanta.
Komawa yayi dakin yayi wanka sannan ya jata zuwa jikinsa suka kwanta, karfe daya ta farka da wata uwar yunwa, mikewa tayi ta nufi toilet tayi brush sannan ta janyo furan da bata shanye ba jiya ta soma sha.
Motsinta ne ya Tayar da shi da Sauri ya sauko ya zauna kusa da ita "sofy maimakon kitashe ni ,keda baki da lafiya".
Murmushi tayi ta shigaba da zakalkalar furanta "ba kya tsoro ya saki amai".
"To ai ni shi nakeso sha". Haka ya jirata ta shanye furan tas, anci sa'a bai dawo ba. Haka ta koma ta cigaba da baccinta a jikinsa
Wanshekare da safe Amira ita ta hada musu breakfast ta gyara gidan sannan ta jera su a dining. Shiya taimaka mata tayi wanka sannan yaje dakinta ya kwaso mata kayayyanki da zata bukata.
Gaisawa sukayi da Amira dake shirya musu dining "ya jikin anty "
"Da sauki Amira, ina tsammanin zamu je asibiti da ita yanzu".
Amira tayi rau da fuska "Allah sarki Anty, bari na shiga na gaisheta ko ta tashi
"Eh ta farka, tafin mata da breakfast din daki".
Amira ta shiga dakin da sallama, safiyya ta amsa mata tana murmushi, zuwa tayi ta kanga kanta jikin sofy "aunty yaya yace baki da lafiya, meke damunki".
Safiyya ta lakace mata hanci "bakiji tsoron kwana ke daya ba".
"Uhm uhm. Nace meke damunki".
"Amai nefa kawai Amira, amma ai naji sauki".
Bude flask din abincin Amira ta somayi "fankasau ne tayi da miyar alayyaho sai kunu data dama na dawa".
Safiyya na gani miyanta ya tsinke "Amira yanzu duk ke kikayi wannan da safe".
Amira tayi dariya "Anty ai ba wuya nasan zakiso ne, bari na zuba miki".
"Hadamin da ya sufyan nasan shima zaici".
Hada musu tayi tare,sannan ta kwashe kayan ta fita dasu, tare sukaci da ya sufyan sannan suka nufi asibitin iyali dake unguwan rimi.
Dayake safwan yayi aiki a wurin , cikin kulawa suka duba safiyya "cikin dake jikinta shi yake sata kome taci ya dawo,amma zata dena dazar cikin yayi kwari, in cikin yakai wata hudu zata na zuwa awo, yanzu zamu bata magungunan kara garkuwa jiki ga mai ciki".
Godiya sufyan ya musu sannan suka fito, yahuza suya suka biya ya saimata nama da fura,sannan a hanya ya siyan mata agwaluma suka nufi gida.
Haka sufyan ya dinga jinyarta shida Amira har cikin ya shiga watanni biyar, inka ganta zaka dauka haihuwa zatayi sabida yadda cikin yake da girma.
Tunda kuma tasamu sauki sufyan ya cigaba na gurzarta, dama ya cemata yana daga mata kafa ne sabida baby na wahalar da ita, aiko yanzu tana gane kuranta a hannunsa.
"Amira dinga matsawa a hankali kinji".
Amira tayi murmushi "aunty wallahi na kosa ki haihu, ai ingaya miki wurina yaran zasuna kwana".ta cigaba da matsa mata kafa
Safiyya tayi dariya "narasa keda uban baby waya fi wani zumudi ba, nidai kawai Allah ya saukeni lafiya".
Wayartace tayi kara ta dauka ,Momy ce ke kiranta "assalamu alaikum Momy ina wuni".
"Lafiya lau auta ya jiki jikin".
Murmushi tayi a kunya ce "lafiya lau momy".
"Yawwa kina lafiya dai ko, karfa kidinga biye mishi yana baki kayan sanyi kinasha, sabida abinda ke cikin".
"To insha'allahu Momy".
"Yawwa 'Yar albarka ina Amira".
"Gatanan kusa dani mikawa Amira wayar tayi suka gaisa da Momy sannan sukayi sallama.
Suna zaune sai suka ji ana buga gate, Amira ce ta fita tana tambayan wanene. Bude wa tayi Don ance ana Neman safiyya ne kuma kaman ta dauki muryan.
Bude gate din tayi aka shigo da mota, wucewa ciki tayi domin ta Sanar da sofy. Kafin safiyya ta fito har anfara sallama a kofar falon.
Izini safiyya ta bayar a shigo bayan ta dauko hijjabi tasa. Shigo wa yayi cikin murmushi yayin da Amira ta mike cikin mamaki baki bude...
[3/9, 9:06 AM] YAYA HAYAT: ```MACE KADARA CE MAI TSADA```
```©UMMU SABREENA da AUNTY AYSHA...```
```Febuary 2017```
```<<56>>```
Safiyya ce ta iya boye mamakinta "a ah Faisal zauna mana, karaso ciki".
Da Sauri Amira ta bar falon gudun kar kukan daya taho mata ya kwace a gabansu. Girgiza kai safiyya tayi ta bita da kallo , shi ya katse mata shirun "Brr. Ina wuni ya kwana dayawa".
Murmushi ta masa "lafiya lau Faisal yasu hajiya".
"Alhamdulillahi Suna gaisheku, Ashe dai zan iya gane gidan".
Safiyya tayi dariya "halan kwatance aka maka?".
"Eh tambaya nadinga yi ,ina ne gidan brr sufyan, shine aka nunamin".
"Bari na kawo maka ruwa"safiyya ta fadi tana kokarin tashi.
Tsayar da ita yayi "a ah Brr kibarshi keda bakijin dadi".
Murmushi ta masa" ai kuma kaga ba'a bar bako haka ba" zuwa tayi kitchen ta dauko masa faro da exotic da cups, ta kawo masa.
"Abdul yakoma Lagos din kenan" safiyya tafadi tana kokarin zama.
"Eh yana Lagos, shina tambaya yabani nombarki yace ai kullum ya kira wayar akashe".
eh dayake na sake layine".
Shiru ya danyi kafin yace "Brr wannan kaman Amira Nagani a falonki dazu".
Murmushi safiyya tayi "eh itace,ta girma ko".
Murmushi yayi"wallahi brr ba Inda ban shiga nemansu ba a garin ban Don na basu hakuri akan laifin Dana musu, to alokacin akace mana lawyer daya tsaya musu a kotu ya daukesu, to da aka sakeni sai nayiwa abdul magana cewan zan je basu hakuri sai yacemin ai ance sun bar garin, a nan ne ma yake cemin ai mijin kine lawyer din, munyi mamaki sosai dan bamu taba sani ba. Kwatsam kuma akace ai kun bar Kasan, kuma gashi bamusan wani state kike ba balle muyi tunanin su Amira na can.
Da yake inata bibiyar duk Inda zanji labarinku sai rannan naga mijin naki a mota ya wuce, shinefa nace to tabbas kun dawo Kaduna kuma dole na nemo Amira Don na roketa ta yafemin"
Safiyya da tunda yasoma magana take binsa da ido "kwata kwata ba Faisal din data sani bane before, dan kuwa tsaf ya canza ,yanayin maganarsa da natsuwarsa ba kaman Faisal din da ba, shigarshi ma danyen shadda ce a jikinsa blue da hula, ko fuskarsa ka kalla zaka gane ya zama mutumin kirki tunda ba wannan dan iskan askin".
Numfasawa tayi " to alhamdulillahi Faisal, gaskiya naji dadi da wannan zancen naka,dama dan Adam haka akesonshi koda yaushe mai yawan tuba a duk lokacin daya yiwa Allah laifi. A lokacin da abdul ya min maganar case dinku tun kafin kusameni da zancen na San Amira dan kuwa nike kula da ita a hospital nida mijina, na ansa case dinne dan tsoron kar akaiwa wani azzalumin lawyer ya zaluncesu bada niyyar Don na taimakawa zalunci ba, kuma ko bayan da aka sallameta to tana wurina, kuma gaskiya naji dadin zuwanka, kuma insha allahu zata yafe maka".
Cikin damuwa Faisal ya ce " to Brr dan Allah ki kirata in roketa".
Safiyya ta mike ta wuce dakin Amira, samunta tayi kwance a kan gado tayi shiru hawaye na bin kuncin ta, share mata su safiyya tayi " ya daga ganin mutum kin barni dashi a falo ni kadai, auhoo nagane nufinki.
Wato in ma masu sace mutane su saceni nida babynki ko".
Amira bata San sands tayi murmushi ba "kai aunty ba haka bane, ni banason ganin sa ne".
"Haba Amira kikason damai yazo, dan haka kitaso muje kiji mezaice, hakuri fa yazo ya baki".
Turbune fuska Amira tayi "nifa Anty ba Inda zanje, koma dai maiyamin ai shikenan ya wuce kuma yama kanshi, Allah ya yafemana gaba daya".
Ba yadda safiyya batayi da Amira ta fita ba taki, daga karshe ma kuka tasa mata, dan haka ta fita ta sami Faisal tace masa " Faisal naje nasamu tayi bacci amma zuwa gobe kadawo insha Allah komai zai dai dai ta".
"Brr kodai ta taki fitowa ne, dan Allah ki bata hakuri".
Kakalo murmushi safiyya tayi "kar kadamu zata yafema kadai dawo zuwa goben".
Mikewa Faisal yayi lokacin sufyan ya turo kofan ya shigo. Kallo ya bi Faisal dashi kafin ya karaso ciki, safiyya ta matso ta anshi briefcase din hannunsa tana mai mishi sannu da zuwa.
Faisal ya kariso yana gaidashi, mika mishi hannu sufyan yayi suka gaisa fuskarsa ba yabo ba fallasa. Wucewa yayi ciki yayinda safiyya ta raka Faisal sannan ta dawo.
Kai tsaye ruwa taje ta kawo masa da cup ta nufi wurinsa, zaune tasa meshi yana waya, tsugunnawa tayi ta cire masa safar kafarsa, sannan ta cire masa bakar suit din sama.
Rike hannunta yayi ya zaunar da ita akan cinyar shi yana sunsunata a haka har yagama wayar.
"Har kin raka bakon naki?".
Dariya tayi tana mai Jan kumatun sa "bakon Amira dai, kuma wollah taki fitowa wai yazonefa ya nemi gafaranta amma yarinyar nan taki".
Sufyan ya shafi dan cikin nata "ai naga yanzu ya natsu".
Lumshe ido jin abinda yake mata " nima daga ganinsa nagane ya yi hankali yanzu, saima ka saurari zancen shi zaka gane".
Kwantar da ita yayi a kan gadon ya fara kissing din bakinta,kwace bakin ta tayi ta rada masa a kunne "kabari kayi wanka mana".
Cigaba da shafa cikinta yayi "kibari nayi wasa da baby na tukun".
Ya sufyan kenan, kullum haka yake mata sai yace yana wasa da baby shine, da daddare sai dai inta mishi wayau tace cikinta ya fara ciwo sannan yake barinta.
Tare suka shiga sukayi wanka nanma saida suka sha soyayya a bayi sannan suka fito. Tana fitowa ta hau bacci yanata mata dariya.
Wanshekare da yamma Faisal ya dawo gidan. Da kyar da sidin goshi safiyya ta tilasta mata ta fita waje tasameshi.
Fuskarta a daure tana sanye da hijjabi light pink har Kasa, fuskar nan fayau da ita Sak Fulani. Tsayawa tayi nesa dashi shikuma yana daga jikin motarshi.
Karisowa yayi kusa da ita yadda zataji mai zaice, yana karasowa ta matsa, ya kara matsowa ta matsa, murmushi kawai yayi "nasan abinda kikeji a zuciyarki game dani, zuciyar ki tana gaya miki Cewar kina tsaye ne tare da azzalumi, na ansa laifi na Amira, amma dan girman Allah kiyi hakuri ki yafemin abinda na miki, wallahi yanzu na nagane kuskure na, jiya nazo Brr. Tace min kina bacci yauma gashi na dawo gabanki dan Allah ki yafemin".
Shiru ta masa sabida yadda zuciyarta ke tukuki, wannan fa shi ya lalata mata rayuwa ya kuma dasa mata bakin cikin da bazashi taba gogewa ba a ranta,.
Tsugunnawa yayi a gabanta idonsa jajir "gani gurfane gabanki Amira, kiyiwa darajar alqur'ani kimin afuwa nasan
na bata muku keda mahaifiyar ki amma ki yi hakuri ba danni ba".
Muryarta na rawa "shike nan Allah ya yafemana gaba daya". Da gudu ta shige ciki sabida kukan dayazo mata.
Barinshi tayi a wurin tsugunne ya bita da kallo yanajin abun dayasaba ji kullum akanta...
```MACE KADARA CE MAI TSADA```
```©UMMU SABREENA da AUNTY AYSHA...```
```Febuary 2017```
```<<57>>```
Koda ta Shiga falon ta taradda sofy kwance a Kasa tana bacci dan haka daki ta wuce ta cigaba da kukanta. Safiyya na farkawa ta mike ta nufi dakin Amira. Samunta tayi kwance shiru dafata safiyya tayi "ya wuce ne".
Gyada mata kai kawai tayi, safiyya ta sauke ajiyar zuciya "karkisa damuwa a zuciyarki Amira, ki zama mai yafiya a rayuwarki duk da ansan wannan abune mai girma amma kuma haka akeson mutum dan kuwa muma duk girman laifin da mukewa Allah shima haka muke rokonsa ya yafe mana".
"Taso muje mu daura girki danni dan wake nake son ci, mikewa sukayi suka shiga kitchen domin daura dan wake (Wanda nasan daga jin ance danwake ran Anty Sis ya biya lol).
Kwanaki biyu da suka wuce saiga Faisal ya kara dawowa ranar da yamma, safiyya ta tarbeshi. Lokacin Amira na kitchen tana wanke plates.
Bayan sun gaisa ne Faisal kece mata "Brr. Kinga nasa ke dawowa ko".
Safiyya tayi murmushi " aikuwa Faisal, dafatan dai ba wata matsala"
Dan Sosa kai yayi "wallahi brr.problem ne kuma kenazo nayi kamun kafa dake, brr. Ku taimaka kubani Amira kar rayuwata ta shiga garari ,wallahi brr. Sai bayan da abin nan ya faru sonta ya dinga wahalar dani.kullum tunaninta ne a cikin raina kuma nasan Amira itace da-dai da rayuwa".
Karan fashewar tambulan din da sukaji ne yasa dukkansu juyawa, Amira ce ta tsaya baki bude tana kallon Faisal da alamu taji abunda yake fadi. Juyawa tayi da gudu ta bar falon.
Safiyya ta juyo da kallonta ga Faisal Wanda yakeji kaman ya bita ciki , sauki gauron numfashi tayi "to Faisal bazance maka bazan Baka Amira ba, Kasan Indai ta wurina ne bakada matsala, yanzu Kasan akwai mahaifiyarta da kuma shi maigida na, amma inya dawo zan Sanar masa".
Shiru taga yayi kaman Wanda ruwa ya cinye"karka damu Faisal insha Allahu komai zai zama normal".
Mikewa yayi ya mata sallama ya fita,safiyya bata bitaba sabida tasan yanzu kotaje bazataji duk Abinda zata gaya mata ba.
Couscous ta dafa jallop taji kayan Lambu na hanta, sai tayi kunun aya ta jera musu a dining. Wanka ta shiga dakinta tayi lokacin anata kiraye kirayen sallah magriba. Kampala tasa Riga da zani, cikin ya mata cas tayi haske sosai dan kuwa kirjinta da hips dinta sun cika sosai. Turarukan ta ta shafa lokacin dataji tsayuwar motar sufyan.
Fita tayi ta tarboshi ya manna mata kiss a goshi suka taho tare zuwa dakinsa. Wanka ta turasa yayi sannan ta fito masa da kayan sa farar jallabiya yasa.
Sallah isha'i tayi kafin ya fito ya shirya, mikewa tayi zata fita ya rikota "dear ina zakije".
Dariya tayi "zanje bikon Amira ne yau fushi take taki fitowa".
"Meyasa meta ne?".
"Kaidai bari nadawo sannan nagaya maka".
"To ga kankanan can na kawo miki sai ki hada fruits salad din dakikace".
Fita tayi ta nufi dakin Amira, ta sameta ta fito daga wanka kenan, safiyya ta daure fuska cikin wasa ta juya zata fita, da Sauri Amira ta sha gabanta " haba aunty kar kiyi fushi dani mana"
Juyawa safiyya tayi dayan bangaren, Amira ta koma wurin, safiyya ta kara juyawa Amira ta bita gun ta rike mata hannu zatayi kuka , "shine bazaki futo kici abinci ba ko, me aka miki zaki zauna a daki kiki fitowa?".
Amira tayi murmushi "to maman takwas kiyi dariya mana kin wani sha kunu".
Safiyya tayi dariya "au kema abinda yayan naki yake min fata haka zakice, to maza kifito kizo muci abinci, oya gama shirya wa bari na hada fruit salad dinnan".
Tare sukaci abinci su ukun a falo, safiyya dai fruit salad din tayi ta sha ta barsu da couscous din. "Kina gani ko Amira, yanzu da Momy zata gani sai tace nine bana tasata gaba taci abinci bancin nima fama nakeyi".
Amira tayi dariya yayinda safiyya ko kulashi batayi ba taciga da Jan fruit salad dinta sai mita yake mata.
Tana kwance a jikinsa bayan angama soyewa tana sauke ajiyar zuciya idonta a lumshe, shafa gashin kanta yayi" baki fadamin abinda kikace zaki gayamin dazun ba dear".
Kankameshi tayi tana murmushi "dama dazunne Faisal yazomin da wani zance nan ta gaya masa yadda sukayi da kuma abinda tace masa.
Shiru taga yayi amma hannunsa na kan cikinta, sajen dake kwance a fuskarsa ta shafa " haba dear yanaji kayi shiru".
"Eh to gaskiya yazo da babban zance, amma gwara da kikace masa zamu Sanar da mahaifiyarta tukun, kuma dai sofy kinsan bazan yiwa yarinya auren dole ba ko".
"Nasani dear,dama wai nace masa zan Sanar dakai, kuma ni wallahi murna nayi sabida dayawan wasu Matan basu samu abinda tasamu ba, namiji ya miki fyade kuma ya dawo ya aureki, amma ita gashi yadawo ya nemi gafaranta, kuma ai dama shiyafi cancanta daya aureta tunda shi ya fara..."
Shiru tayi bata karasa ba, sufyan ya shafi libs dinta yana murmushi "yaya da dakatawa, cigaba mana".
Shigar da kanta tayi kirjinsa tana shakar kamshin dake fita a jikinsa "nidai dear Allah ina goyon bayansa, kaima ka goyi bayan abin".
"To mum takwas yanzu ke abin ya ragewa dashi kanshi wajen ya shawo hankalinta ta so shi, dan dai bazan yarda ta auri Wanda bata soba",
Daga mishi gira tayi hade da lasar lebenta na Kasa "to ai shine rufin asirinta, kuma auren dole da kake Cewa ai muma shi aka mana amma munata kuka gashi yanzu ji nakayi bazan iya rayuwa batare da ya sufyan dina ba".
Kankameta yayi yana dariya, nan yafara bata Sumba ta ko'ina suka Lula...
```MACE KADARA CE MAI TSADA```
```©UMMU SABREENA da AUNTY AYSHA...```
```Febuary 2017```
```<<58>>```
Wanshekare safiyya na zaune tana yiwa Amira drying kanta safiyya ta fara mata zancen "Amira kenan, wato dai ke har yanzu yarinya ce".
Amira tayi murmushi "aunty nice yarinya, yanzu fa nakusa shiga 18yrs saura baifi 3mnths ba".
"Ahaf, ai haryanzu yarinya ce ke, bawai zan tilasta miki bane akan sai kinso Faisal,amma ke da kanki ki kalleshi yanzu yanda ya canza, ya gyara halayensa dukka".
Amira ta turo baki "ni gaskiya Anty inkina min maganar shi zan tashi na bar falon, tayaya ma zan shiga zuri'ar gidan alhaji mugu".
Safiyya tayi dariya "aiko kin tashi saina biki dakin, yanzu ke Amira ba Allah bane ya soki da rahama, ace Wanda ya maki wannan aika aika yadawo yace zai aureki, haba kiyi tunani mana, alhaji kuma ina ruwanki dashi ai bashi kike aure ba, wallahi Amira Faisal na sonki tsakani da Allah".
"Uhmm nidai Anty dan Allah ki kyaleni ni ko ganin sa ma banason yi, kedai kawai kice kinzama uwar-dakin sa".
"Kinsan dai bazan kaiki Inda zaki wulakanta ba ko, dan haka na baki kwanaki kiyi tunani".
Mikewa Amira tayi ta shige kitchen dan duba girkin da ta Dora, wayar safiyya tayi kara, taduba taga safina ce, da Sauri ta dauka hadi da sallama.
"Mai ciki, wallahi banison sunan nan hhhh wai yaushe zaki kiramun ne".
Safiyya ta kyalkyale da dariya "babu shika shikan rashin mutuncin da baki iyaba cwt, ina yarinyata".
"Gatanan tanata wasa, ya jiki jikin, ya zama da kyar".
Murmushi safiyya tayi "wallahi gashi nan cwt, yanzu fa watan cikin biyar amma wallahi duk yabi ya takuramin wai a haka yayanki kicewa na haifi 'yan uku, ina zan iya".
Dariya safina tayi "ai sai ki daure ki haifo mana, hmm guda dayan ma ya aka ciki cwt balle uku, yau ban ga kin zo schl ba shine nace ko jikin ne".
"Kafafuna ne suka rike tun safe shiyasa".
"Ina Amira take?"
"Gatacan a kitchen"
"To agaisheta sannan a gaida baby da babansa".
"To zasuji, sai nazo ganin takwarata".
Yanzu ta kai ga kullum Faisal na gidan safiyya sabida ya shawo kan Amira, amma yarinyar nan taki, in ma yazo ya ya ganta a waje to haka zata shige ciki ta barshi nan, wani lokaci har sai safiyya inta leko ne take ganinsa. Tayi fama da ita har ta gaji dan da ta fara mata maganarshi sai ta hau kuka wai ita ba aure zatayi yanzu ba karatu zata fara.
Sati daya kenan shima kanshi duk yayi wani iri kaman ba Faisal dan gayu ba, Ranar dai da daddare ya taso alhaji suka taho gidan, lokacin sufyan na nan, Suna falo dukkansu yana matsawa safiyya kafanta daya rike ita kuma tana cin popcorn.
Sallama akayi sufyan ya mike ya fita, gaisawa sukayi da alhaji cikin sakin fuska kaman ba shi ba, sufyan ya bude musu dayan falon suka shiga.
"Da farko dai ina mai Baku hakuri akan abinda yafaru, kuma dai ni na daukeshi matsayin kaddara, nayi matukar farin ciki da Faisal yazomin da wannan zance sai yacemin wai kuma yana fuskantar problem daga gun ita yarinyar"
"Nace masa dole ya fuskanci matsala tunda dai ga abinda ya faru, to shine Nazo da kaina dan Allah a taimaka mana, wallahi yaron nan ko abin cin kirki baya ci haka hajiya ke fama dashi wurin aiki dama ya dena zuwa kullum yana daki kamar maraya".
Sufyan ya danyi murmushi "eh to alhaji nima dama mai dakina tagayamin abinda ke faruwa, to sai na ce mata sai abinda yarinya tace da mahaifiyarta, amma dai nima insha'allahu zan yi iya bakin kokarina sannan zanje nasamu mahaifiyarta ".
Alhaji yama sufyan godiya sannan suka tafi. Koda ya koma lokacin Amira tana daki sai yake gayawa safiyya suwaye sukazo.
"Yanzu alhaji da Kansa yazo nan".
Sufyan ya kalleta yana dariya "sai ma kingashi sima yazama nagari".
Dariya sukayi dukkansu yace ta kira masa Amira.
"Yanzu alhaji da Faisal suka bar gidan nan akan maganarki, inaso inji daga bakin ki dan naji auntyn ki tace tanata fama dake kinki".
Amira kanta a Kasa" yaya ni fa karatu zan fara kaga, ni yanzu gaskiya ba aure zanyi ba, kuma ni ni bana....".
Safiyya ta dariya tana girgiza kai, sufyan yace " ai Amira aure bai hana karatu baga auntyn ki nayi ba yanzu, na tabbata bazakiyi Dana sani akan Faisal ba sabida nasa anmin bincike akan shekaran jiya kuma an tabbatar min yanzu yadaina halayensa na banza dayakeyi kuma kullum sallahr jam'i yanzu bata wuceshi, ki yi tunani mana Amira".
Hawaye tafarayi "yaya kaima yanzu kabiyewa Anty ta daina sona kun koma kan Faisal, yarinya dani za'amin aure".
Mai safiyya zatayi banda dariya,sufyan ya kalli Amira yana murmushi "kyale antynki kinji Amira, ni ina bayan ki amma kuma wannan shi ne son dazamu nuna miki , in yarinya tasamu mai sonta na gari to ayimata aurenta sai ta cigaba da karatun acan. Kuma na tabbata Faisal zai barki ki cigaba.
Yanzu dai tashi ki tafi kiyi shawara,zan nemeki.safiyya dai sai dariya take sufyan na binta da kallo " da yanzu zance miki ina bukatar ki sai kice min cikinki na ciwo amma ji dariyar dakikeyi sofy".
Wanshekare sufyan ya nufi gombe wurin inna da zancen Amira.
Koda tagama sauraren zancen sufyan shiru
Yaga tayi tana binsa da ido.
"Inna baki ce komai ba, ni dai nasan tabbas yaron da mahaifinsa sunyi hankali kuma nayi bincike a Kansu sosai, insha allahu alherine za'a kulla".
Ajiyar zuciya ta sauke tana mai murmushi " sufyanu ni me zance bayan 'ya a wurin Ku take, nidai lubabatu nabaku daman zabawa Amira mijin daya dace da ita ko bayan raina Amira takuce kaida mai dakinka, komai nata na gunku, Allah ya saka muku da alheri".
Sufyan ya fadada murmushin sa dan bai zaci inna luba zatace haka ba, nan yayita mata godiya sannan ya nufi gaida umma a fada da sarki. Momy kaya iri iri ta jido masa wai ya kawowa safiyya na Karin lafiya ne ga mai ciki.
A nan kuma Kaduna ranar saiga hajiya kulu (mahaifiyar Faisal) ita zo gidan sofy. Sun tarbeta hannu biyu biyu itada Amira suka cika gabanta da kayan tarban baki.
"Lalle Amira ta girma, ooh girman 'dan mutum ba wuya".
Amira tayi murmushi ta sadda kanta Kasa. Mikewa tayi tabar musu falon .
"Ai naga kaman kingane ni ko antyn Amira?"
Safiyya tayi dariya "naganeki hajiya sabida kamanku daya da Faisal ai".
Dariya sukayi dukkansu "dama nace mishi ya kawonj domin nima na kara rokon Ku, wallahi ba Faisal din da kuka sani da bane yanzu, kinga dai ni mahaifiyar shi ce bazan masa karya ba, kwata kwata yanzu abincin azziki baiza zauna yaci ba, shidai Amira, dan Allah a yimana hakuri, laifi dai yariga yayi adubemu da icon rahama abashi yarinyar nan, Ranan mafa saida jininsa ya hau ya dinga ganin jiri mukayi dashi asibiti",
Amira dake cikin dakin safiyya tana jinsu ta sulale a Kasa tana kuka a hankali "ita yazatayi da rayuwarta da wannan Faisal din, yabi ya daureta ta kowani bangare".
Safiyya ta numfasa "to hajiya wallahi muma muna bakin kokarin mu wajen ganin ta saurareshi ,kuma insha allahu zata sauko ,domin yarinyace mai hakuri ,da ikon Allah komai zai wuce Don shima mijin nawa yau ya tafi wajen mahaifiyar ta ne da zancen".
Godiya hajiya tayitawa safiyya, sannan ta bukaci a kira mata Amira, fitowa tayi ta zauna a Kasa gefenta, murmushi hajiya ta mata sannan ta mika mata wata Yar karamar jaka cike da kaya.
Amira tayi mata godiya sannan hajiya ta fita.
Bayan fitan tane safiyya ke cewa Amira dan Allah tayi hakuri ta yarda da auren nan insha allahu bazatayi Dana sani ba",
Amira jikinta a sanyaye tace "aunty wai inna yarda da auren Faisal mai zakiji".
"Amira wallahi kin biyani kuma zanfi kowa murna cewan amirata tamin biyayya"
"To Anty Indai zai faranta miki rai shikenan na amince" ta fadi tana hawaye
Safiyya ta goge mata hawayen tana murmushi suka rungume juna...
```MACE KADARA CE MAI TSADA```
```©UMMU SABREENA da AUNTY AYSHA...```
```Febuary 2017```
```<<59>>```
_wannan nakune mutanen *the three* wato 'ya'yan Anty Sis, tundaga kan, lubiee, lubna,benazir, jeedah ,miemie bee, queen miemie, Yar ficika dai dai sauransu, Allah ya barmu tare cikin aminci,ILYSM_
Safiyya a ranar ta kira Faisal tayi masa albishir, aiko duk ya rikice mata a waya. Wanshekare ko gama breakfast basuyiba daya ke Saturday ne lokacin ma sufyan bai fita ba sai gashi yazo gidan.
Safiyya sai dariya take masa,sufyan ne yafita ya sameshi a waje sukayi maganan Cewar gobe ya turo da magabatan sa a ayi magana kawai. Faisal yayi masa godiya sannan safiyya ta tura masa Amira.
Ansan lokaci biki nan da wata uku, dan haka sai shirye shirye duk gidajen biyu sukeyi. Yayinda inna tazo ta dauki Amira ta suka tafi can kafancan wato garinsu sukayi sati biyu sannan suka Sanar da kowa maganar biki.
Gyara kuwa iri iri safiyya kewa Amira, Momy ma ta aiko musu dashi, jikin nan sumul inka ganta tayi kyau. An kawo kayen lefan ranar su safina duk sunzo domin ita yanzu sofy zama da kyar ne tashi da kyar. Kowa ya kalleta sai yace "sannu kinji, Allah ya raba lafiya". Shima kanshi sufyan din tausayi take basa shiyasa ya hanata yin komai a gidan yace a turo mata da kuyanga daya daga gidan sarki.
Biki saura kwana biyu akayi sisters eve Wanda safiyya ta shirya, amarya ansha kyau sai hotuna ke tashi, itadai safiyya tana daga zaune sai dai kallo domin lokacin cikinta watanni takwas kenan da kwanaki.
A na gobe biki akayi kamu a alhaji sani dauda multipurpose hall dake nan unguwan rimi, ango ya iso da jama'arsa ansha rawa sannan an zubar da kudi.
Wanshekare ranar juma'a misalin karfe daya da rabi aka daura auren a masallaci, gidan safiyya a cike ta ko'ina, Momy tazo itada umma ranar. Su Anty Amina dama an Dade da zuwa itada cwt.
Duk Inda safiyya zatabi kyaji Momy na fadin "yi ahankali kinji auta, sannu fa sannu".
Safiyya sabida tsabar gajiya duk tayi jaa kafafunta su kunbura. Daukan waya tayi ta kira sufyan , shagwaba ta fara masa wai yazo batajin dadi, da Sauri ya shigo ta bayan dakinsa.
Lokacin tana falo Suna magana da inna, tasowa tayi ta nufi dakinsa, da Sauri taje ta rungumesa yana shafa bayanta "sofy meke damunki ne".
Janta yayi suka zauna akan gado tana kwance jikinsa, shagwabe fuska tayi "kawai wallahi bacci nakeji kafafuna duk sun rike".
Kallonta yayi yadda tayi kyau cikin wani material Fari da baki, sai kamshi takeyi, zame dankwalin kanta yayi ya shaki kamshin dake fita a kanta "banace kar ki wahalar da kanki ba tunda bakida lafiya k
sofy".
Kara shigewa jikinsa tayi "to dear zan bar baki ne nazauna a daki ,ai Kasan dai dole na fito".
Wayarsa ce tayi ringing ya dauka, yayin da bacci yayi awon gaba da ita a jikinsa duk ta cukwikwiyeshi da malunmalun dinsa.
Da yake wasu souvenirs din adakinsa suke dan haka safina tashigo dakin, dariya ta hau yi " Momy na can na cigiyarta Ashe tana nan makale da miji".
Ya sufyan yamata nuni da hannu datayi a hankali kar ta tashi, dariya tayi ta dauki abinda zata dauka ta fita. Haka ya zauna tanata bacci yana mammatsa mata jiki har karfe hudu sannan ta farka.
Murmushi ta masa yace "tashi kiyi wanka ko kyaji dadin jikin ki".
Shi ya taimaka mata tayi wanka ta sauya wasu kayan sannan ya kira safina a waya cewan ta kawo mata abinci. Saida ta cika ciki sannan ya wuce masallaci ita kuma ta koma gun baki.
Da daddare akazo aka wuce da amarya gidan hajiya kulu domin a can zata kwana gobe sai a wuce da ita gidan mijinta dake unguwan sunusi.
Wanshekare da Momy zasu wuce ta kira sufyan "dama kan maganar dawo da yarinyar nan gida haihuwa ne, Kasan wata na Tara kenan cikin nan nata kuma dai nafari ne, dan haka ko zamu tafi da ita ne yau".
Sufyan ya tsugunnar da kai Kasa "Momy da kin barta anan bayan ta sauka sai ta koma, Allah duk wata kulawa ina bata agida".
Momy ta bude baki "to sannu gwanin iya kula, ko bakaga Amina da safina da suka cikin ya tsufa Suma dawowa dasu gida mukayi ba, wannan Abu wajibi a gunmu kuma dole ta dawo gida in cikinta ya tsufa, domin duk kulawar dazaka bata bata kai tamu ba, zan iya maka uziri yau sabida tanada baki ,amma yanzu kawai kagaya min ranar dazaka kawomin ita".
Kanshi a Kasa yace "nan da sati mai zuwa insha allahu zan kawota".
"Yawwa ko kaifa sufyanu, kana ganin yarinya kaman ciki zai fasata Don girma, Allah dai ya sauketa lafiya".
"Amin amin"
Satin na zagayowa sufyan ya dauketa sai gombe, Momy sai nan nan take da ita dan kuwa bata komai a gidan nan, har ruwan wanka sai dai Momy ta Tara mata a roba ta kaimata komai take bukata. Kawai matsalanta daya kafafunta da suke kumbura kuma dama sufyan ke matsa mata su yanzu kuma bata iya Cewa Momy ta matsa mata.
Kullum Suna makale a waya yana gaya mata yadda yayi missing dinta,dama duk weekend a gidan Momy yakeyi.
Kayan jarirai iri iri ba Wanda basu Siya ba, in yazo shi ke kaita asibiti, lokacin da aka mata scanning tace kar a gaya mata mace ne ko namiji nurses din sai dariya suke mata wai maman twins ce ita.
Ranar da yamma sungama suna waya da sufyan yake cemata "sofy bakyajin dadi muryarki duk ta canza".
Murmushi tayi dan kuwa jun kugun ta take kaman ba'a jikinta yakeba "lafiya ta kalau dear banajin komai".
Haka ta daure sunata hira har ta kashe wayar , kiran Amira ne ya shigo ta dauka "aunty har yanzu shiru".
"Uhm amira amarya, kona haihu ai nasan bazai barki kizo gombe ba sabida amarci.
Amira ta shagwabe mata fuska kaman tana gabanta "haba aunty ai wallahi ko akafa sai Nazo , shima kullum sai yayi zancen haihu warki".
nan dai tadinga cijewa har sukagama wayar da Amira, Momy ce ta leko ta ganta kwance alamun tana bacci, kashe mata wuta tayi sannan tayiwa jakadiya magana Cewar sofy fa na ciki dan kuwa ita ke kwana da ita.
Tanajin Momy kawai shiru tayi dan yadda kwankwason ta ke juyawa abunka da haihuwar Fari batason ya ciwon nakudan yakeba.
Jin datayi ruwa na bin kafafunta ne yasa ta yin wata Yar kara...
```MACE KADARA CE MAI TSADA```
```©UMMU SABREENA da AUNTY AYSHA.. ```
```Febuary 2017```
```<<60>>```
*SADAUKARWA*
Mun sadaukar da wannan littafi ga *mata masu tsada*
Aunty sis
Lubabatu mai tafsir
Lubna sufyan
Nty Maijiddah Musa
Sanah s matazu
Brr. Jameela danja
Zuhra ajiya
Humaira bashir melody
*TUKWAICI NE GAREKU*
pharm. Mami Sadiya
Fatima (amiraty)
Maman haneep
Feena Ja'afar
Biebie isa
Miemie bee
Queen miemie
Aysha chuchu
Jeedah aliyu
Benazir Omar
*GODIYA MAI YAWA*
muqaru da juna grp
Taskar lubiee maitafsir
Dandalin meesha luv
Hawwa Hausa novel
Miemie bee novels
The three
*YABAN GWANI...*
*AUNTY SIS*
Uwa ma bada mama, baya Goya marayu, addu'oin ki garemu shike bamu kwarin gwiwa da kuma goyon baya
*GORO NE...*
halimaty
Faridaty
Zakiyyaty
*KUNA RANMU...*
duk masoyanmu kuma masoya littafin *mace kadara ce mai tsada*ubangiji Allah ya saka muku da alkhairi ga duk kaunarku garemu, hakika masoyinka masoyinka ne, kusani Cewar kullum kuna cikin ran *Ummu sabreena da aunty aysha*. MUNA GODIYA DA KUMA FATAN ALKHAIRI GAREKU A DUK INDA KUKE....
Da Sauri jakadiya ta shigo dakin tana fadin "subhanallahi, sannu bari na taso Momy".,
Fita tayi da Sauri ta isa side din daddy tana knocking, da Sauri Momy ta fito jin cewan safiyya ba lafiya.
Da daddy ne ya fito da mota momy da jakadiya
Suka kama safiyya wacce bakin ta ya mutu dan ciwo.
Asibitin su safwan aka wuce da ita, Momy tasa waya ta kirashi Cewar ya zo asibiti gashi nan sun kawo safiyya batajin dadi.
Suna zuwa aka wuce da ita labour room ,ganin yadda taketa wahala yasanya Momy hawaye, cikin Sauri safwan ya iso bai tsaya sun gaisa dasu momy ba ya shige dakin da aka kaita.
Daddy ya matso ya zaunar da Momy kusa dashi sabida yadda takasa tsaye takasa zaune, kallon agogo suka kalla lokacin karfe goma da rabi na dare. Shiru suka zauna har karfe sha daya da rabi, jikin Momy da jakadiya duk ya gama sanyi ganin ba Wanda ya fito daga dakin da aka shigar da sofy.
Safwan ne ya fito da sauri Momy ta isa garesa "safwan ina autar takene?".
Murmushi yamata ganin yadda ta damu "Momy 'yan biyu ne, munyi munyi takasa haihuwa, dan haka zamu shigar da ita dakin theater ne".
Momy ta fara kuka, daddy ya kalli safwan "OK Allah ya sauke ta lafiya, Allah yasa ayi a sa'a. Kayi signing kawai".
Cikin kuka momy ta kallesu "a kira mijinta a gaya masa".
Daddy ya jata suka zauna "bai kamata a kirasa cikin Daren nan ba, kiyita mata addu'a kinga keta gado, da twins zata fara".
Hawayen idonta ta goge ta danyi murmushi "Allah ya rabasu lafiya".
Gangaro da ita akayi suka wuce da ita, minti biyu da shigarsu sai ga wata nurse ta fito da Sauri ta nufo Momy "ina kayan dakukazo dashi?".
Momy ta miko mata basket din kayan ,pad da pant kawai ta dauka ta koma ciki da Sauri.
Sai gashi an kara gangaro da ita, safwan na rike da baby daya itama nurse na rike da baby daya.
Momy ta karaso da Sauri tana binsu har aka shigar da ita resting room. Momy ta riko hannunta tana murmushi "auta! Auta!! Sannu kinji".
Safwan ne ya shigo shida dady kowanne da guda daya a hannunsa. Safwan ya mikawa Momy na hannunsa ta amsa tana hamdala "wai har anyi aikinne".
"A ah muna shiga kuma cikin ikon Allah saiga haihuwan gadan gadan".
Daddy ya yiwa safiyya sannu "gashi an haihu baban yara baiji ba".
Momy tayi dariya "wai na hannunka mace ce ko namiji ,ni nan dai namiji ne".
Safwan yayi dariya "ai duk mazane , Momy saikin zaba Wanda yamiki".
Dariya sukayi dukkansu yayinda safiyya baccin wuya yayi gaba da ita.
Safwan shi ya kira sufyan ya mishi albishir. Yayi yayi yagaya masa mace ne ko namiji safwan ya kiya, yace "inkazo zakaga ko mace ce ko namiji".
Flight ya biyo zuwa gombe, lokacin 'yan Uwa sai zuwa suke dan ance sai ta kwana za'a sallameta.
Ta tashi kenan Momy ta hada mata tea tana sha, anty Amina na rike ba daya sai ga sufyan ya shigo, yana sanye da suit Baka da wando, yayi kyau da ka Ganshi zaka gane angon karni ne.
Kusa da ita ya zauna yana mai gaida momy, kallonta yayi hade da kashe mata ido daya , shagwabe masa fuska tayi.
Daukan babyn dake gefenta yayi ya zuba masa ido, Anty Amina ta mika masa dayan "ga dayan nan ya sufyan".
Bude ido yayi sosai bakin sa a bude dan farin ciki "au guda biyu ne, masha Allah, sannu sofy".
Aunty Amina tayi dariya itada momy, duk ya daukesu ya makalkale yama rasa maizaice, safina ce ta shigo tana fadin "maman twins".
Dariya sukayi ta karaso ta dauki daya tana fadin "wai gaskiya an gaisheki cwt, wannan luba K
Luban yara".
Nan Momy ke sheda musu ai da aiki za'a mata cikin ikon Allah kuma ta haihu da kanta.
Sufyan bai samu ya gana da sofy ba sabida mutane, wanshekare kuwa aka sallamota gida. Ranar Amira ta iso sai murna take kaman zata shigar da yaran ciki.
Sai da daddare ne jama'a suka lafa sufyan ya taddata a daki tana feeding daya.
Zuwa yayi ya zauna ya dauki dayan "wannan dani yake kama".
Murmushi tayi ,"wanene babba ne a cikinsu , ya tambayeta bayan ta miko masa dayan , momy tace wannan ne babba ta nuna Wanda yafi hasken.
Jingina jikinta tayi a jikinsa ya yimata kiss a goshi "Allah ya miki albarka sofy, Allah ya barmu tare har karshen rayuwar mu, Allah yasa ke matatace har a aljanna".
Murmushi tayi "amin my dear".
Kallonta yayi "dama ranar dazaki haihu inajin yadda kike magana na gane, sannu lallai kin sha aiki sofy na".
Murmushi ta mishi tana kallon baban Wanda ya ke kama sosai da sufyan domin har hasken sa yadauko karamin kuma shi bai kai babban haske ba.
Hura mata iska yayi a fuska bayan ya gama yi musu addu'a, ta lumshe idonta "wani Suna kikeso asamusu maman twins?".
"Ni duk Wanda Kasa musu yayi dadyn twins".
Murmushi yayi "to bari na musu khudba da sunan mai martaba da daddy, yayi".
"Yayi Allah ya musu albarka".
Daga mata gira yayi "kinga shekara mai zuwa sai ki haifo mai sunan umma da Momy".
Waro ido tayi "aniyarka ta bika, ai ban manta ba".
Dariya yadinga mata ita kuma ta mike Don ji Momy na kiranta tazo anyi baki 'yan barka.
Ranar Suna yaran sukaci Abubakar da uthman (hussain da hassan). Sunan da yayi armashi Don ba karamin kashe kudi akayi ba, mai martaba yabawa yaran dawakai, safiyya ansha kyau.
Faisal ma yazo shida hajiya, Amira taje ta shigo dasu, itama kana kallonta Kasan tana amarci sabida yadda ta cika.
Dama jiya safina tagama mata tsiyan wai ciki gareta. Anty Sis da mutanenta ansha ashobi, yaran dai sunyi goshi masha Allah.
Haka sofy ta zauna cikin kula wajen Momy itada twins, yayinda sufyan zai wuce aikin hajji shida aunty Amina da safwan. Amira ita kuma da Faisal zata tafi.
Bayan haihuwanta da kwanaki goma suka wuce. Kullum tana makale dashi a waya yayinda Momy ke tsumata da kayan gyra iri iri. Yaran bul bul sunashan hotuna gun mutane, itama kusan kullum sai ta ai ka masa da pics dinsu.
Ranar hasan arfa haka ta zauna gaban TV tanata kallo ,gani takeyi kaman zata ganshi. Haka sukayi babbar sallah cikin farin ciki yayinda sofy keta shirin komawa gida domin yanzu yaran watansu biyu kenan gwanin ban sha'awa.
Ana jibi zai dawo ta koma tare da kuyangarta daya mai suna maimuna bayan an gyare mata gidanta tsaf, ranar da zai dawo duk gidan ya dauki kamshin girki Dana turare.
Ta shirya tsaf itada twins, cikin red and black dukkansu. Ita sanye take da Riga da zani wash ready made masu kyau. Rigar mai laushi baka sai zani red anyi masa kwalliya da stones baki. Sai ta kashe dauri da dankwalin red shima , tasha Jan lalle da baki sai kamshinta take mai tadawa da sufyan hankali.
Khalil shi ya kawoshi gida, yana shigo wa ta rungumeshi batasan ma tare da ya Khalil sukeba. Bakinsa ta kama tafara mishi salonta na barka da zuwa. Dayake yafita tsayi sai ya kama kugunta ya dagata da kyau.
Khalil na ganin haka ya aje masa kayansu ya juya yana dariya. A kasa suka zube ganin abun nayi ne, daukanta yayi zuwa dakinsa suka gaisa da kyau, soyayya suka sha kaman zasu cinye juna tama manta da su hussain a falo.
Yana rungume da ita sai murmushi yake mata, murya can Kasan makoshi yace "sofy... I miss u, ina yarana".
Karamin yatsanta tasa tana zagaye dashi a kirjinsa "miss u too swthrt, yaranka Suna nan suma sunyi missing naka, kataso muje kayi wanka tukun sai akawo maka su".
Tare sukayi wanka sannan ta shiryasa, koda taje falo ta tarar maimuna ta kwashe su. Shiga wurinta tayi tana jiyo kukan hassan "ayyah my baby , maimuna shine baki kawo min su ba",
Dariya maimuna tayi "ai Anty inata kwankwasa kofan baki ji ba".
Murmushu safiyya tayi sannan ta kwashesu ta nufi dasu gun sufyan, yama rasa wanne zai dauka, kamar ya lashe su. Duk sunyi wayau sai bangala mishi dariya sukeyi.
Tare sukaci abinci sai anan ya tuna cewan fa tare da Khalil yake "sofy na mance fa tare da Khalil muka zo".
Safiyya ta zuba masa dambun naman plate tana dariya "aiko ya tafi,ni ban ma saniba".
Kashe mata ido yayi "ai ke dince kin rikitani dayawa".
Kada kwayan idonta tayi tare da lashe lebanta "nuna maka nayi kenan ba karamin missing dinka nayi ba".
Nan ya dinga amsa wayoyi anata mishi sannu dazuwa, cikin satin baya fita ko'ina sai soyayya dasuke sha, danma masu sannu da zuwa na musu cikas.
Safiyya ta shirya taje gidan Amira, ba karamin murna tayi ba, tarasa Inda zata sasu itada twins, itama ga 'dan cikin ta nan ya kunno kai. Sun sha hira dan a gidan ta wuni sai dare sufyan yazo ya kwashe su.
Twins Nada shekara daya sufyan ya shirya musu zuwa kauyen su papa, abinda yamusu dadi shine samun su papa sun musulunta dan kuwa bayan tafiyan sufyan wani yazo kauyen kuma musulmine dan haka gunsa suka anshi musulunci.
Sunyi matukar farin cikin ganinsu , sai daukan twins sukeyi musamman Camila, sufyan ya basu kudi sosai da sosai sannan ya ce zasu dinga ganawa ta waya domin sun kulla zumunci kenan.
Daga nan suka wuce Kasa mai tsarki sukayi ummara sannan suka dawo Nigeria. Gombe suka sauka gidan umma , daganan suka shiga gidan Momy.
Anty Amina tazo tanata fama da tsohon ciki , itama safina ranar sunzo nan suka zauna sunata hira, twins daga wannan ya rugo ya fada kan safiyya sai wannan ya zo ya cukwikwiyeta.
Momy ta dinga dariya ,"lalle kina fama auta da sojoji a gidanki".
Kwanansu biyu suka koma Kaduna, wanshekare itama Amira tazo da yarta safiyya suka musu sannu da zuwa. Ranar da daddare safiyya bayan ta kwantar da twins ta iso wurin sufyan daketa danne danne a system.
Bayanshi taje ta rungume ta manna masa kiss , lumshe ido yayi "sofy bazaki barni na karasa aikin nan ba ko zaki tsokanoni".
Mirginoshi tayi ya fado jikinta tana murmushi "to ni bacci nakeji fa".
Kwaikwayan muryanta yayi "to bari nazo kinsan ni bana jiran a kirani, Allah yasa yau nayi sa'a nasamun ma su twin sister".
Dukanshi tayi a kirji "badai a cikin nan nawaba, wollah ban mance ba".
Kashe mata ido yayi "OK. Ba matsala sai na karo yan mata 'yan shekaru 16 suzo suyita zazzagemin yara tunda ke kin kiya".
Tureshi tayi ta hade fuska, janyo ta yayi ya fara haukata ta da soyayyarshi, sai da komai ya lafa ya ke rada mata a kunne "kece ta farko a zuciyata safiyya, kuma insha allahu kece ta karshe, zuciyata taki ce na mallaka miki ita hade da gangar jikina duka, kece jinin jikina ke ce hasken idona kuma uwar 'ya'yana, ina sonki safiyya ta".
Kankameshi tayi itama ta rada masa a kunne " Kaine rayuwana ya sufyan, luv yhu too swthrt".
*************************
*ALHAMDULILLAH*