Tun daga lokacin har dare yayi basu sake haduwa ba, abincin ranan data dafa ko dinning hall din bai ma je ba bare ya gani, ta d'auki abinci ta sa a cikin freezer ta cinye salad din.
Washe gari da safe tak'i hada breakfast dashi, saboda ko ganinsa ba ta sake yi ba tun jiya da rana, a zaton ta ma ya koma Kaduna ne.
A hanya suka yi crossing, zata shiga bedroom shi kuma zai fita, ta gefenta ya rab'a zai wuce tace mishi "ina kwana", ya dakata ya kalle ta a fusace, yace "daga yau na hanaki yi min magana, kina ji na?"
Shiru tayi kanta a sunkuye, ta ja hijab dinta ta gyara sannan ta wuce shi. Da yamma Inteesar ta dawo gidanta domin taya ta kwanan har zuwa ranan Friday idan Abdul ya dawo, sosai Jaleelah tayi jarumta ta b'oye duk wani damuwarta, ga wani tsirfa data d'auka na kullum zama da hijabi kamar mai takaba, ko hirar da suke yi da dariya ya isa ya rage mata damuwa. Ranan Thursday da safe Inteesar ta koma gidan Umma ta d'auko wasu kayanta sannan ta dawo gidan Jaleelah.
Rokonta tayi akan ta rufa mata asiri zata je birthday party din kawarta don ta san Umma ba zata barta ba, amma kamin nan sai ta ziyarci gidajen kawayenta. Jaleelah tace mata ba komai ta tafi amma idan aka kira sallar magrib bata dawo ba sai ta tona. Before 9am ta gama shirinta ta fice. Tana fita itama Jaleelah ta shirya ta fita zuwa asibiti for her prenatal check up.
Bayan ta ga likita ta kamo hanyar gida, instead of ta wuce gida kai tsaye sai ta wuce gidan Sajida, saboda ita d'aya zata yi ta zama idan ta koma. Bata ta shi barin gidan ba sai bayan sallar la'asar.
Ba k'aramin faduwa gabanta yayi ba lokacin da ta fito daga keke napep ta hango motar Abdul a pake a gefen gidan. Kirjinta na dukan uku uku ta isa bakin gate din, kamar ta karisa kusa da motar saboda ta ga alamar yana ciki amma ta fasa saboda kashedin daya yi mata. Da sauri ta bude gate din ta shige amma ta bar mishi kofar a bude, sai a sannan ya d'ago da kanshi daga duk'e yana shafa wayarsa, shi bai ma ga sanda ta iso ba ganinta kawai yayi a jikin gate tana shiga shima ya fito daga motar ya bi bayanta.
Tana jin footsteps dinsa tayi gaggawar bud'e entrance door ta shige, a inner sitting room ta zauna bata kai ga cire hijab dinta ba ya shigo. Ta d'ukar da kanta don ba zata iya gaishe shi ba, hucinsa ya gama yi sannan yace mata "daga ina kike?"
Ta dafe goshinta tace "asibiti"
Cikin fad'a yace mata "da izinin wa? Ko zaman kanki kike yi"
Tayi shiru bata bashi amsa ba, yace "look, this is what I can't tolerate kina ji na? Ba zaki mayar dani d'an iska ba sai yadda kika so zaki dinga yi, baki da hankali ne ko ilimi ne baki dashi? why do you choose to behave worst than an ignorant can??"
Hawaye ne ya zubo daga idanuwanta, ta share su sannanta mik'e tace mishi "I'm sorry", ta wuce shi ta shige bedroom. Akan sofa ta hurga jakarta da hijabinta ta haye gado ta fara kuka baji ba gani, sai da tayi mai isarta sannan ta tashi ta shiga bathroom don wanke fuskarta, daga haka kawai tayi wanka ta fito, duk a tunaninta Abdul ya tafi, short fluffy dress ta d'auko ta sa wanda iyakarsa gwiwa.
A bakin window ta tsaya tana kallon waje, iska maraice mai sanyi yana ta hura ta. Banda aikin hawaye babu abinda take yi, idan ta tuna rashin mutunci kala d'aya da yayi mata in a low tone of her voice much of a murmur sai tace "not even for the sake of our unborn child"
Sai kuma sabon kuka ya zo mata, tafi danganta rashin mutuncin da yake mata da tsanar da yake ma cikin da take d'auke da shi.
K'arar bud'o k'ofar da akayi ne yasa tayi gaggawar share hawayen fuskarta, duk a tunaninta Inteesar ce, murmushi ta kirkiro sannan ta juyo, tana juyawa suka ido hud'u da Abdul wanda ya shigo d'aukan wasu muhimman takardu wa'inda sune musabbabin zuwansa gidan. Wani irin kunyarshi taji, ko don it's been a long while bata sa irin kayan a gabanshi bane. Da sauri ta karisa wurin sofa ta d'auki hijab dinta ta sanya sannan ta fita. Shi kuwa sai binta da idanu yake yi yana ganin kamar gizo idanunsa ke yi masa. Wardrobe ya bud'e ya d'auko papers din, sai da ya gama kare musu kallo sannan yayi placing dinsu bisa chase drawer sannan ya zauna a gefen gado yana nazari.
Zuwa can kuma ya tashi ya fita, a sitting room ya tarar da ita tayi zugum, daga nesa yace mata "ke zo nan"
Sannan ya juya ya koma cikin bedroom din. Tsoro ne ya kamata, don ta tsani masifar da yake mata. Tana d'ar d'ar ta shiga bedroom din, a tsaye ta ganshi yana jiranta. Daga jikin kofar ta tsaya tace "gani"
Yace "a nan ne zaki tsaya min, my friend move closer"
Kusa da shi ta tsaya tsakaninsu bai yi taku biyu ba, ta sake cewa "gani"
Jawo ta kusa da shi yayi sannan ya cire mata hijab saboda ya gogewa zuciyarshi kokwanto, surar jikinta ya k'are kallo yaga tabbas ba gizo idanunsa ke masa ba "was I blind?", ya tambayi kanshi, hannunsa ya d'aura a kan cikin, cikin sanyayyar murya yace "what is this?"
A ranta ta nanata tambayar "what is this?"
Sai ta fara hawaye, a hankali ta fara kuka, ta juya zata d'auki hijab dinta ta sa ya rik'e mata hannu, ta d'ago da fuskarta dake wanke da hawaye, yace "I'm asking you"
Shiru tayi masa saboda takaici bata iya magana ba, a gefen gado ta xauna shima ya zauna a gefenta, yana zama ta mik'e zata fita ya je ya tsaya a gabanta, yace "this is one of the things I dislike, na tsani shariya, I'm talking to you"
Bata daina hawayen ba tace "you are calling a part of you that I hold in my womb "this"?"
Fuskarsa na mai d'auke da puzzled expression yace "ban gane ba... Which pregnancy? After you killed the one I knew about?"
Da confidence d'inta tace "ni ban kashe shi ba"
Yace "then tell me how? Don wannan katoton cikin naki yafi four months! kuma da bakinki kika ce min zakiyi abortion even at the expense of your life, kuma.. The next thing I heard shine kina bleeding an kaiki asibiti, and I'm sure ko baki yi ba you attempted"
Kuka take yi sosai, tace "ni babu abinda nayi, kuma koma nayi ai kamata yayi kayi farinciki, since you hate it!"
A zabure ya kalleta yana mai mamaki, yace "what? Jaleelah... Babyn nawa? Nine na fad'a miki haka?"
Ta share hawayen dake fuskarta tace "ai ba sai ka fad'a ba, since I became pregnant you dumped me, baka kulani, kullum masifa, inna yi abu ka zage ni kaji haushi na, you don't bother to know what I'm going through, I know you probably hate me and the unborn"
Habarta ya taro yana kallon fuskarta, yace "me yasa zan tsaneki..."
Ta katse shi "na sani mana", yace "I just hate what you've done... Kin kira ni kin gama min rashin kunya sannan kika ce zaki yi abortion, wallahi don magrib yayi ne time din da ranan zan zo, the next day I left my work place before closing time saboda ke and I came you weren't home, Munawwar ne ya kira ya fada min you were bleeding, and I know you had messed up!!"
Tace "naje yin alwala ne na fad'i a toilet, amma I didn't do anything silly, I was just upset shiyasa na fad'a maka haka amma I didn't mean it"
Ajiyar zuciya yayi yace "abinda bakin ki ya ja miki kenan, next time you are upset you should know what to say", tace "I'm sorry", hugging dinta yayi sannan yayi mata rad'a a kunninta, itama tayi masa sannan ya sake yi mata, nok'e kafada tayi ta b'ata fuska tana girgiza kai alamar a'a, yayi dariya yace "to it's okay", dariya tayi sannan tayi hugging dinsa.
Sai bayan sallar magrib sannan Inteesar ta dawo, lokacin Abdul yana masallaci bai dawo ba, hankalinta ya so ya tashi data ga motarsa. A kitchen ta tarar da Jaleelah tana soya dankali, tayi sallama Jaleelah ta amsa mata, sannan tace "wato ke sai yanxu ko? Ai zaki sani"
Tace "yaushe ya Abdul ya dawo?"
Tace "nima na dawo daga asibiti ne na ganshi"
Tace "Allah ya sa da yaje gida bai tambayi Umma ina nake ba tace ina nan"
Jaleelah tace "koma bai tambaya ba sai na tona tunda ni bance ki kai dare ba"
Kiris ya rage ta durkusa har kasa ta bata hakuri, Jaleelah kam ta daure fuska amma tana so tayi dariya, ana cikin haka Abdul ya dawo muryoyin da yajiyo yasa shi ya wuce kitchen ya tarar da Inteesar nata rokon Jaleelah, yace "lafiya dai?"
Da sauri Jaleelah tace "a'a kawai wai rancen 5k take so ni kuma bazan iya bata ba Ameer, ta fiye taurin bashi"
Yace "ke me zaki yi da shi?" Yana dubanta, Jaleelah ta sake yin magana kamin Inteesar "anko ne wai zata yi na kawarta"
Abdul yace "to zo muje autan Umma"
Ido suka had'a da Jaleelah suka yi murmushi sannan Inteesar tabi bayanshi.
Har 10pm yana Kano, ba don Inteesar tana nan ba da kwana zai yi ya gwada Jaleelah how much he missed her and her cries. Sai 10:40pm sannan ya tafi Jaleelah tayi mishi rakiya har bakin motarsa. Jan ta ya dinga yi da surutu, feeling so remorsed. Data gaji tace "dan Allah ka tafi kaji?"
Yace "eh naji, dama ba yau kika fara kora na ba"
Tace "ba haka nake nufi ba, nufi na dare na k'ara yi"
Yace "ka ji yarinya wai ni zata ma boko"
Tayi dariya tace "wai yarinya, ai na wuce nan"
Shima yayi dariya yace "to shikenan, amma ina missing kukanki, kinga gobe dole sai kinyi shi, ina nan dawowa"
Hannunta ta d'aura bisa lips d'inta tana murmushi tace "to naji, yanzu dai kayi hakuri ta tafi it's almost 11pm, nasan matarka tana can tana expecting dinka"
Yace "yea, gobe ma tare zamu zo"
Tace "Allah ya kawo ku lafiya, dan Allah nabi Inteesar idan zata tafi sai idan ka zo mu dawo tare?"
Ido ya ware yace "salon ko d'an headache ne ya kama ki Umma ta hanaki biyo ni?"
Tace "a'a ba zata hana ba, kaji?"
Yace "to... Ki kula min da kanki da babynmu ko?"
Tayi nodding kanta yayinda ya shiga cikin motar, sai da ya zauna ta rufe mishi kofa yace "awww! Kinga I forget to kiss the princess and tell her bye, and also tell her Daddy loves her"
B'ata fuska tayi tace "so nawa zaka dinga kissing dinta, wannan hala so kake yi ana haifo ta tayi kissing midwife din"
Yayi dariya yace "to je ki bude min gate zan fita"
Ba don ta so ba ta kama hanya zata je ta bud'e masa ya fito da sauri ya riga ta isa ya bude sannan ya fitar da motar ya dawo ya rufe, har lokacin bata shiga ciki ba tana tsaye tana kallonshi, bayan ya rufe gate ya tsaya a gabanta, yace "to ni zan wuce, sai Allah ya kaimu gobe"
Tace "to Mr Airfoce, Allah ya kai min kai lafiya ya dawo min da kai lafiya, ya kare ka daga sharrin karfe da sharrin ko wani abin k'i"
Yana murmushi ya amsa mata da amin sannan ya tallafo fuskarta yayi kissing dinta a forehead kamin ya fita tayi locking gate din.
Tana komawa ciki ta wuce bedroom wurin Inteesar, a gefenta ta zauna tace "malama ina kudina?"
Inteesar ta tashi zaune tana dariya tace "kudina dai"
Tace "dalla ke fa yar rainin wayau ce, bani 3k ki rike 2k ko na hadaki da Umma"
Na yadda ta iya haka nan ta bata. Ko ba komai ta samu tsuntsu daga sama gasasshe.
Sai past 12am Abdul ya isa gida. D'akin Raheemah ya lek'a ya ganta a kwance tana sharar barci ya rufo kofar ya wuce nasa d'akin, Shower yayi taking sannan ya kwanta bacci yana ji kamar ya janyo goben nan in a second. Addu'o'i yayi sannan bacci yayi awon gaba da shi.
Washe gari da safe bayan ya gama shirinsa ya fita parlour. A kan seater ya tarar da Raheemah a kwance, da kyar ta iya ce masa "morning"
Ya amsa mata da "morning. Hope breakfast is ready"
Cikin kasalliyar murya tace "amm I thought ba zaka dawo bane yau shiyasa, ban yi ba"
Yace "and I thought I came and woke you up for fajr prayer"
Da mamaki take kallonshi, don saboda tsabar nauyin bacci bata ma san ya shigo ya tashe ta kuma har ta tashin sannan ta koma ta kwanta.
Tace "dama I want to talk to you"
Yana daga tsaye yace "fad'i maganarki"
Tace "I need a housemaid.. Saboda gaskiya aiki yana min yawa"
Shiru yayi yana kallonta, tace "kaji? Kaga gashi yanzu zaka fita baka yi breakfast ba, if to say akwai house help din nan kaga da yanzu tayi preparing mana"
A kaikaice ya kalleta, yace "to ki dinga kwanciya kawai mana. And ki shirya anjima zamu tafi Kano in Allah ya yarda"
Ya sa kai ya wuce ta.
4:30pm suka isa Kano. A gidan Umma suka yi masauki. Yadda Inteesar ke jin haushin ta yasa ko sannu da zuwa bata iya ce mata ba yayinda suka shigo main parlour suka tarar da ita da Umma, duk da this is her first time of been to their house. A k'asa Abdul ya nemi wuri ya zauna ita kuma Raheemah ta zauna daga gefen Inteesar dake kwance akan kujera. Umma kam sai washe baki take yi unlike Inteesar da ta had'a fuska kamar hadari. Cikin ladabi Abdul ya gaishe da Umma, Raheemah ma ba yabo ba fallasa ta gaishe ta. Inteesar tace "ya Abdul sannu da zuwa. Ina wuni?"
Yace "lafiya k'alau, ita sister in law din taki baki iya mata sannu da zuwa ba?"
Kwabe fuska tayi tace "aww.. Sannu"
Tana fadin haka ta tashi ta shige d'akin Umma don sanar ma Jaleelah isowar kishiyarta. Wani mugun kallo Raheemah ta bi ta dashi wanda ya faru a kan idon Umma, murmushi tayi ta kwala Inteesar din kira ta fito, tayi mata umurni da ta kawo ma Raheemah ruwa da lemo sannan ta kawo mata abinci.
Sai da Umma taga b'acin rai a kwayoyin idanuwanta, ba yadda ta iya hakanan ta je ta kawo, sai da ta ajiye mata su duka a gabanta sannan tace "ai da ma kin barshi, don a k'oshe nake"
Abdul yayi mamakin jin haka, don daya dawo babu abinda ta dafa sai indomie din data ci da hantsi, bayan shi bata sake cin komai ba sannan kuma tace a koshe take. Ko shima daya dawo tace masa bata samu damar yin girki ba daga sallar juma'a ya wuce Sahal Restaurant yaci abinci sannan ya dawo.
Inteesar bata yi wata wata ba ta kwashe abincin ta mayar kitchen sannan ta sake komawa d'akin Umma. A bedroom ta tarar da Jaleelah tana folding kayan Umma da aka wanke mata d'azu da safe kamin a goge, tace "Jaleelah ga tunkiyarki nan fa"
Tace "tunkiya kuma Inteesar? Umma ce ta siya min ko wane?"
Yarfe hannu tayi tace "tunkiyar da Yaya AbdulHakam ya kwaso nake miki magana"
Tace "oh'hooo wannan matar?"
Tace "eh ita"
Suna cikin magana Umma ta kwalawa Jaleelah kira ta amsa, suka had'a ido da Inteesar tace "kije ki ganta"
Ta wuce ta gabanta na dukan uku uku ta fito falon. Murmushi mai had'e da yak'e ta kirkiro yayinda tayi arba dasu, Umma tace "dama abokiyar zamanki ce suka iso shine nace ki fito ku gaisa"
Tana murmushin ta karisa ciki ta zauna a gefen Umma, ita da Abdul suna kasa ita kuma Raheemah da Umma suna sama. Umma ta tashi ta shige d'aki ta barsu su gaisa.
Jaleelah ta dubi Abdul tana wani irin special murmushi, tace "Ameer yaushe kuka iso?"
Yace "bamu jima ba ai"
Bata bar murmushin ba ta dubi Raheemah ta ta kicincine fuska tace "sannu ko", a d'akile ta amsa mata da yawwa. Kusa da Abdul Jaleelah ta matsa, tace "kunyi surprising dina, ai da ka sani ka kira ni da na zo na tarbe ku daga compound"
Murmushi yayi mata yace "see you, kina so kiba princess dina wahala ko?"
Tace "eh kuma haka ne, jiya da daddare ta gaji"
Yace "eh mana, kije ki kawo min abinci mana Ameerah"
Tace "ah to ita amaryar fa?"
Ta fad'a tana nuna Raheemah, yace "oh ita ta koshi"
Tace "to.. Kai baka ci abinci daga gida bane?"
Yace "bana son yawan tambaya, bata dafa ba kije ki kawo min wanda kuka dafa", da gangar ya fada ma Jaleelah cewa Raheemah bata dafa abinci ba saboda taji haushi ta canja hali.
Ta tashi ta wuce Raheemah ta bita da idanu, cikin yayi mata kyau ya zauna dabasbas a jikinta, duk da ya k'ara girma akan lokacin data ganta a wurin dinner. Ta dawo d'auke da babban tray mai d'auke da food flasks da jug da cups da kwalin exotic. Tun kamin ta kariso yayi sauri ya tashi ya amshe ta suna dariya, yace "kada a wahalar min da princess d'ina"
Tare suka zauna, Abdul kam yana sane yake yin haka saboda Raheemah ta sake hali, banda chatting bata da wata Sana'a, wata rana sai ta had'a sallar azahar, la'asar, magriba, da isha shima sai ta zo wanka da daddare sannan take yi, saboda ba ko wane rana bane take samun yin wanka da rana ba ko da safe bare kuma a zo maganar wankan safe da na rana ko na wartsake gajiya, wata rana ma idan tsamin jikinta bai dameta ba bata yin wankan tunda ba tare suke kwana ba sai idan za ayi sunna, ta fiye yin wanka a ranan da take so taje turaka.
Abdul ya bud'e babban flask yaga tuwon shinkafa, ya bud'e karamin yaga rayeyyen miyan agushi daya sha nama, ya d'auki plate zai sa tayi saurin amshewa, tace "princess tana so Queen dinta ta dinga serving King"
Ta amshi plate din tayi serving dinsa, ba kasafai yake samun daman cin irin wannan abincin ba sai ya zo Kano.
Da kanta ta zuba masa ruwa ya wanke hannu cikin bowl sannan yayi basmala ya fara cin abincin. He was eating with relish, sai murmushi yake zubawa haka ma Jaleelah. D'akin ya d'au shiru, sai sannan Jaleelah tace "oh! Kaga ba mu gaisa da amarya ba, ina yini?"
Raheemah ta d'an yi yar murmushi mai d'auke da tarin ma'anoni, tace "lafiya"
Amsa gaisuwar data tsana, ta gaishe ka kace mata lafiya, hakan yasa tayi banza da ita ta mayar da dubanta ga Abdul wanda yake ta cin tuwon kamar an kwato shi daga yunwa duk da yaje restaurant yaci.
Bayan ya kammala Jaleelah ta kawo ruwa tana zuba mishi ya wanke hannu a cikin bowl. Yayi wa Allah godiya sannan yace "my Jawhara wa yayi abincin nan?"
Tace "ni nayi miya Umma kuma tayi tuwo"
Yace "auta fa?"
Tace "ita tayi gyaran gida ne"
Yace "good.. Gaskiya yayi dadi sosai, you tried, Allah yayi miki albarka", abinda bai tab'a fad'awa Raheemah ba, murmushin jin dadi tayi tace "ameen, nagode my Jawhar"
Sannan ta hada plate da su flaks din ta kwashe su ta kai kitchen ta dawo ta zauna. Yace "yauwa, Alhamdulillah"
Sannan ya dubi Raheemah yace "Hajiya ki d'an sauko kasa ko?", dama yaji haushin zamanta a saman, mahaifiyarshi tana sama itama tana sama, tace "anything?", yace "not at all, magana zamu yi", dama already a k'ule take, tace "shine sai na sauko? Just say it, I'm more confortable like this"
Cije lebenshi yayi, yace "right... So today I officially and formally introduce you to each other... Jaleelah ga amarya Raheemah nan, Raheemah ga Jaleelah nan uwar gida na"
Shiru tayi tana kallonshi ita kuwa Jaleelah sai murmushi saboda bata yi tunanin Abdul zai yi treating dinta yadda yayi ba a gaban Raheemah, saboda yadda ta san yana masifar son ta.
Ya cigaba "shi aure bautar ubangiji ne, kuma shi ya halasta ma bawansa auren mace fiye da d'aya duk da ba wajibci bane, amma it's a divine right da Allah ya azurta ko wani musulmi da shi. Ina fata zaku girmama junanku ku kuma mutunta junanku, duk da kishi halas ne ina fata zaku yi tsabtataccen kishi ba mara ma'ana ba, and also, kishinku ya zama akan kyautatawa ba wai cutarwa ba. Finally, each of you holds a special position in my heart".
[4/20, 7:45 PM] Leenah💋: ⚜Mijin Jaleelah⚜
53
By Linah Shams✍🏼
Raheemah bata iya cewa komai ba saboda hakanan taji ranta na k'una, sai Jaleelah ce tace "to Allah ya bamu zaman lafiya", ya amsa mata da ameen. Duk yadda ya so da ya ga sunyi hira su uku Raheemah tak'i bada had'in kai, ya lura ma gaf take data fara fad'a mishi bak'ak'en maganganu, hakan yasa yayi tunanin kawai ya d'auke ta ya kaita gidan iyayenta kamin a fara kiran sallah. Dukansu suka tashi suka nufi d'akin Umma, Raheemah tayi mata sallama sannan suka fita dukansu zuwa compound har da Jaleelah. Saboda haushin da Raheemah ta ji ko jerawa da su bata yi ba ta wuce da sauri ta shiga mota. Abdul kam yana ganin ta shiga yaja ya tsaya a gaban Jaleelah, yace "wai nufinki bazan yi kissing princess ba yau?"
Tace "a'a kaga dai a gaban matarka ne ni babu ruwana", yace "and so? Baby na fa kawai zanyi kissing"
Tace "a'a kaga may be ma fushi tayi ko jerawa damu ta k'i yi", yace "you don't have anything to do with her, she isn't your concern, I'm your concern"
Turo mishi baki tayi amma kamin tayi magana ya tsugunna yayi kissing cikin, da sauri ta ja da baya tana fad'in "laaaa"
Yace "ke kika sani dai, kiyi sauri ki shirya ina dawowa zamu wuce", tace "to kayiwa matarka sai da safe ko"
Yace "to" sannan ya wuce ita kuma ta koma ciki. A mota Raheemah kuka ne kawai bata yi ba, amma tak'i yi masa magana har suka isa gidansu, tare suka shiga ta umurci mai gadi da ya kai shi guest room kamar wani bak'o ita kuma tayi shigewarta cikin gida. Har aka fara kiran sallah bata fito ba bare tayi mishi iso ya gaisa da Mom saboda mahaifinta baya k'asar shi kuma. Haka nan ya tashi ya wuce masallaci don samun jam'i. Sai lokacin ne ta aiko kanuwarta Kuhaylah ta je ta kira shi su gaisa da Mom ta ga bashi, ta koma ta fad'a mata, abin sai ya k'ara shak'ar da ita.
Bayan an idar da sallah ya sake dawowa gidan ya zauna a guest room din, yayi ta zaman jira bata fito ba har sai da ya daga waya ya kira ta sannan ta sake aika Kuhaylah ta shigo da shi. Kamar yadda ta zauna a sama da zata gaishe da mahaifiyarshi haka shima ya zauna a saman. Cikin girmamawa ya gaishe ta. Bayan gaisuwa da ban gajiya babu abinda ya sake cewa, d'akin yayi tsit, zaman minti goma yayi sannan ya tashi yayi wa Mom sallama, yana ta jira ya ga Raheemah ta mik'e yi masa rakiya amma ta cigaba da zamanta har ya shiga mota yana expecting fitowarta, yaga bata fito ba hakanan ya wuce. Bayan fitarsa ne Mom tace mata "ke ba zaki yi ma mijinki rakiya bane kiji ko akwai abinda yake so?"
Ta zunb'uro mata baki tace "babu inda zani, ai bai so na masa rakiyan ba"
Mom tace "anya yarinyar nan ba namiji aka so a Haifa ba? Anya ma hakanmu zai cin ma ruwa?"
Tace "Mom mene nayi kuma?"
Ta tab'e baki tace "ke kika sani, hala ni haka kika ga ina ma ubanki"
Tace "Mom wlhy baki San me yayi min bane da da kanki zaki Goya min baya"
Tace "me yayi miki?"
"Gidansu fa muka je muka tarar da matarshi a can, Mom wai a gabana ne yake rawar k'afa wannan shegiyar zata yi serving dinsa, wai har yana fad'a mata ban dafa mishi abinci bane, kuma yayi kissing cikinta a gaba na fa Mom"
Mom tace "ai kaga d'an iska, amma ke meya hanaki yi masa girki? Ko sharri yayi miki?"
Tace "a'a kawai gajiya nayi banyi ba"
Mom taji kamar ta kwashe ta da mari, tace "to shi kuma cikin uwarki ta hanaki d'auka?"
Ware idanu tayi tace "Mom ciki kuma? Allah ya kiyaye, da wuri haka?"
Tace "to Allah ya baki sa'a baby, kiyi yadda kike so kinji? Tunda ke ba a isa a fada miki ki ji ba, sakarya kawai"
Tace "to Mom kwana nawa ne da auren?"
Tace "idan kika sake min magana zan ci miki mutunci"
Ji tayi kamar tayi tsaki ta tashi fuu ta nufi upstairs tana mata kunk'unai, Mom tace "ba laifin ki bane, laifin ubanki ne yarinya".
Abdul na isa gida yace ma Jaleelah ta zo su wuce, ko sallar isha bata yi ba haka ya sata ta fito, suka yiwa Umma sallama suka tafi. Hakanan taji tana jin wani matsanancin farinciki ba tare da ta san dalili ba.
Da kanshi ya d'auke ta tun daga compound dinsu har zuwa bedroom. A kan gado ya ajiye ta yayi kneeling a gabanta, ya sumbanci cikinta sannan yace "hi princess, Daddy loves you, you'll soon hear your first Adhaan insha Allah"
Jaleelah tayi murmushi tana jin dad'i, tace "I'm jealous fa Ameer"
Yace "uhm? Really? To ki bari muyi sallan isha you'll receive your fair share"
Dariya tayi ta mik'e, ya cire mata hijab da kanshi yace "ki yi sauri ki fito idan kin shiga yin alwalan nima nayi, sai muyi jam'i".
••°••
Through out the weekend suna Tare, komai tare suke yi... The weekend was romantic. Tunda yaje ya ajiye Raheemah bai sake nemanta ba, banda masallaci babu inda yake xuwa kullum yana manne da Jaleelah. Duk da tana da juna biyu bata denying dinsa, shi kuma akan ta sam bai iya nuna hakuri ba bare ma he missed her for the longest time ever.
Ranan Sunday bai fita d'aukan Raheemah ba su wuce gida sai past 5pm. Ji yake yi kamar ya tafi da Jaleelah ko ya cigaba da zama da ita which wasn't possible.
Raheemah ta fita shekaru, amma ta fita hankali da iya magana, sai dai wani lokaci dole ka gane yarinta a cikin maganarta. Babu abinda zata nuna mata sai kyawun diri dana fuska duk da ita ma tana da nata dai dai gorgodo.
Ranan saboda gajiya iyakarta balcony, bata iya rakasa ba har parking lot saboda tasan idan ta bishi suka je can ma sabon tsayuwa ne kuma kanta ciwo yake mata amma bata bari ya sani ba. Ban kwana irin ta masoya suka yi sannan ya tafi. Sai da yaje gidan Umma yayi mata sallama sannan ya wuce gidansu Raheemah, sai da ya kira ta a hanya ya shaida mata zuwanshi kamin ya karisa. Wannan time din da kanshi ya shiga har parlourn Mom suka gaisa, sannan ya mike da niyyar fita waje ya jira ta kamin ta gama shiryawa. Yana kokarin tashi Mom tace "d'an dakata ko AbdulHakam"
Ya koma ya zauna tareda baza kunnuwansa, tace "ba wata magana ce mai tsawo zamu yi ba, magana ce akan baby, tace min wai aiki na mata yawa shine nace ko zaka sama mata yar aiki ne?"
Yace "aikin mene take yi?"
Mom tace "wane irin aiki bayan aikin gida da ka sani, ko akwai wani aiki ne da take yi bayan wannan?"
Yace "toh... Ita ce tace miki tana son yar aikin?"
Mom tace "eh"
Yace "to. Kin ga Mama gaskiya idan na d'aukan mata mai aiki dole ne sai na d'auka wa mata ta, ita da ma cikinta ya girma"
Mom ta katse shi "bawan Allah maganar yar aiki muke yi ba maganar matarka ba"
Sosai yake ganin girman matar, yace "eh na sani, I'm trying to be more clear ne, saboda gaskiya I can't afford to pay for it"
Ba wai don ba shi da kudin bane ya fadi haka sai don bai ga dalilin da zaisa ya d'auki mata yar aiki ba daga ita sai shi a gidan, Mom tace "don wannan ba wata matsala bace, gobe ko jibi in Allah ya kai mu yar aikinta na nan tafe"
Yace "to Allah ya kaimu" sannan ya tashi ya koma waje yana zaman jiran fitowarta su wuce.
Ta fito falon sagale da shoulder bag d'inta a kafada sai kuma mayafinta data rike a hannu, Mom tace "tafiyan kenan baby?"
Tana daga tsaye tace "eh Mom, sai munyi waya"
Tace "to dama bari na fad'a miki, ki je ki gyara zaman auren ki da mijinki, kin ganni nan, ni ba kanwar lasa bace, ina Neman taimako dai dai gwargwado na neman tsarin rayuwata da wasu abubuwan, amma fa baki ki isa naje gidan boka neman miki taimako ba, banje akan ubanki ba don haka baki isa inje miki gidan boka akan mijinki ba, 'yar aiki dai zan turo miki da ita, amma kije ki koyi zama da miji, ko dan kissan nan ma baki iya ba. Kije Allah ya kiyaye hanya"
Ta tab'e baki ta amsa mata da "amin" tayi tafiyarta.
Sai gab da sallar magrib sannan Inteesar ta koma gidan Jaleelah. Sosai take jin dadin zamanta a gidan saboda yadda take sakewa, wasu abubuwan ta san idan a gidan Umma ne ba barinta zata yi ba. Musanman yanzu da ta yi new catch, Mo'az. Kullum cikin waya suke ba dare ba rana, abinda Umma ba zata tab'a lamunta ba kenan. Kuma takan kai 12am tana amsa waya har sai Jaleelah ta taka mata burki. Gashi watarana ita take zab'an abinda zata ci.
Bayan sallar isha Mommy ta kira Jaleelah don jin lafiyarta, saboda sai bayan da aka sallameta daga asibiti sannan Umma ta kira ta ta fad'a mata. Hira suka yi sosai na d'a da uwa. Kullum idan Mommy ta kirata ko ta kira sai ta yi mata 'yan nasihohi akan ta bi mijinta ta dinga hakuri musanman ma yanzu da yayi sabon aure, sannan ta k'ara ja mata kunni akan furta kalmar saki, and marriage isn't a bed of roses, it's just a picture of fantasies from mere observation.
Sosai take natsuwa idan Mommy na mata fad'an, kullum tana alfahari da ita saboda yadda taga ta k'ara hankali.
Washe garin ranan Monday da safe, Jaleelah tayi kewar Abdul, d'an kwana biyun da suka yi tare yasa har kewarshi take yi, saboda tare suke yin komai idan ya dawo daga masallaci. Shi yafi yin ayyukan ma ita dai sai dai ta dinga binshi a baya yana cewa ta mik'a mishi ko ta mayar, hatta breakfast shi yake had'a musu saboda wai baya so Princess ta sha wahala.
Ta d'auki wayarta ta kira shi don tasan a irin wannan lokacin yake dressing ta san wayar tana kusa dashi, tana dialing aka yi picking, sai abun ya bata mamaki, "this is unlike him"
Ta kara wayar a kunnenta tace "hello"
Raheemah data yi picking daga d'ayan side din tace "lafiya kike kiran miji na da sassafe?"
Jaleelah tace "ina kwana?"
Tace "ke kika santa, daga yau kada ki k'ara kira min miji da sassafe, kina ji na?"
Tace "kiyi hakuri ki dan bashi wayar"
Tace "ke wai ke mayyar ina ne? Bayan kin shiga tsakani na dashi kin aureshi yanzu kuma kin zo kin hanani sakat?"
Jaleelah tace "miji fa namu ne duka, magana nake so nayi dashi, ki bashi wayar idan yana kusa"
Tace "ke har kin isa? Banda kaddara kin isa Abdul ya aure ki? Auren taimako auren kaddara!"
Tayi 'yar dariya tace "Raheemah kenan, baki ga auren kaddara ba a wurin dinner dinki? Baki ga yadda ake so ba? Hmm.. Kin fa so ki bani dariya, har kina da guts din da zaki budi baki ki min gori akan Abdul? To ki tambayeshi kiji matsayina a wurin shi, I'm more than just a wife to him, I'm his love, his best friend and his companion.. Unlike you, you're just his wretched wife! And remember, ragowa na kike aure, duk yadda kika so da rayuwa ba zaki tab'a canja hakan ba, I'm his first wife, the first woman to sleep in his arms, his first sexmate.. Ki tambaye shi kiji, I'm the woman that makes him cry in the night and makes him sing and smile in the morning, I'm the woman that crowned him a king without any palace.. I hold in my womb his Prince or Princess And insha Allah I'll be the first woman to provide him with a human that will call him papa"
Tana tafe tana zagaye bedroom din take fada mata haka, Inteesar na kitchen tana had'a musu breakfast saboda Umma ta d'aukewa Jaleelah aikin komai Inteesar ke yi, sai dai idan ta tausaya mata.
Raheemah taji zafin kalamanta, ta bud'e baki zata yi magana kenan Abdul ya shigo bedroom dinta saboda bai ga wayarsa ba, tana ganinshi ta fashe da kuka, da sauri ya karisa kusa da ita, yace "baby lafiya? Wani abu ne ya faru?"
Tana hawaye ta mik'a masa wayarsa a dole ta fara iya kissa, rungume shi tayi tana kuka harda shessheka, sai da ya tabbatar ta d'an yi kukan sannan yace "meya faru Raheemah?"
Tace "yarinyar nan ce ta kira ni ta zazzage ni"
Yana rarrashinta yace "I'm sorry for that, ki bar kuka haka I'll talk to her"
Tace "honey wannan yarinyar fa, sa'ar Kuhaylah"
Yace "it doesn't matter, ki yi hakuri zanyi mata magana, how about my breakfast?"
Tace "tea and bread", sai da ya nanata "tea and bread?"
Tace "yea"
Yace "okay", ya amshi wayarshi ya fita. Daga nan ya shiga d'akinsa ya gama shiryawa yayi tafiyarsa ba tareda yabi takan breakfast dinta ba.
Yana isa office Jaleelah ta sake kiranshi, usual norm dinsa ya bi sannan ya kira ta, da girmamawa ta gaishe shi, ya tambayeta lafiyarta dana princess dinsu tace masa duk lafiya k'alau suke, sannan ya tambayeta "Ameerah me ya had'a ki da Raheemah har kika yi mata rashin kunya? Kin San na fada miki bana son rashin kunyar nan ko?"
Sunkuyar da kai tayi kamar yana wurin, tace "kayi hakuri bazan sake ba kaji?"
Yace "naji, ki dinga kiyayarta, ko ba komai she's older than you, respect her pls"
Tace "to Ameer insha Allah, dama na kira ne nayi maka ban gajiya, naji lafiyarka, sannan nayi maka godiya once again"
Yace "alhamdulillah my love, ki dena cewa kin gode min, idan godiyar ne ai ni zanyi miki, most of all shine muyi wa Allah godiya, Alhamdulillah"
Itama tace "alhamdulillah, fi amanillahi dear"
Ya amsa mata da "okay Ameerah, sai munyi magana".
Da yamma bayan ya koma gida sai da Raheemah ta sake tuna mishi rashin kunyar da Jaleelah tayi mata saboda ta haddasa musu samun sab'ani, ta zauna tana fad'a mishi tsakanin k'arya da gaskiya, tace "baby kamar ni? Kamar ni ace yarinyar nan zata kira ni karuwa? Wai har tana cewa ban isa na haihu a gidanka ba saboda na gama zubar da k'wayayen haihuwa na wurin abortion a k'asar turai, wai ni din banza mara tarbiyya, wai jinin nupawa zuri'ar maita.. Yarinyar nan ta caja min kwakwalwa sosai baby har sai da ta haddasa min ciwon kai, shiyasa ko girki na kasa yi"
Sai da ya jinjina kai yana mamakin irin zagin da Jaleelah tayi wa Raheemah don yaji haushi, ko ba komai Raheemah na gaba da ita, sai da ya sake kiranta da ya fita compound ya k'ara nuna mata kuskurenta da kuma bacin ranshi, ita dai bata ce mishi komai ba tana ta ba shi hakuri. Saboda yadda yayi fushi da ita sai da yayi five days baya kiranta kuma ko ta kirashi baya picking, yana so yaji muryarta amma ya tabbata idan ba haka yayi ba yasan ba zata girmama mishi mata ba, baya so abubuwa su fara zuwa suna dawowa tun ba a kai ko ina ba. Raheemah ta dinga jin dadi saboda kullum sai ta duba call history dinsa amma bata ganin na "My Ameerah" sai dai jerin missed calls dinta, tun ranar da incident din ya faru bai sake waya da ita ba. Ko da weekend yayi bai je Kano ba.
Sosai abun ya dami Jaleelah, sai dai duk sallah sai tayi mishi addua. Ba ta kuma kuskura ta fad'awa Inteesar komai ba kamin taje ta fadawa Umma ta kirashi ta mishi fada, don ko kad'an bata jin dadi idan Umman tana yi masa fad'a musanman ma idan akanta ne. Friday nayi Inteesar ta tafi gida bata dawo ba sai ranan Sunday da yamma a tunaninta Abdul ya zo. Duk tsoronta hakanan ta hakura ta dinga kwana ita d'aya har Inteesar ta dawo.
[4/21, 8:19 PM] +234 806 358 6044: ⚜Mijin Jaleelah⚜
54
By Linah Shams✍🏼
Raheemah taji dadin faruwar hakan, sai dai duk da makircinta ya hana shi tafiya amma bata iya ririta shi ba. Don idan yana gida it's either tana d'akinta tana chatting ko bacci, to tana sitting room tana kallo, idan taji yunwa ta kwalawa mai aikinta kira ta zo ta kawo mata abinci. Tun da yarinyar ta zo gidan Abdul bai tab'a cin abin da ta dafa ba, kuma yayi mata iyaka da shiga mishi bedroom, saboda Raheemah tana aikenta ta gyara mishi d'aki shi kuma baya so. Hakan yasa yaji yana kewar Jaleelah sosai. Next weekend in Allah ya yarda sai ya koma ya sake ganinta.
Da daren ranan sunday Umma tana ta expecting zuwan d'an alhajinta, tana tunanin may be tafiyar dare zai yi amma bata ganshi ba har k'arfe tara ta kusa. Ta kuma kira wayarshi sau biyu bai samu daman picking ba. Hakan yasa ta kira Jaleelah don jin inda yake saboda tana so ta sanar mishi sak'on rasuwa da akayi musu ko zai samu daman zuwa ta'aziyya. Bayan Jaleelah ta gaishe ta sai ta tambaye ta "hala d'an Alhaji baya gida ne ko? Ko ya wuce ne?"
Sai da ta d'an yi nazari tace "bai riga ya iso nan gidan ba to ina ga"
Umma tace "to tun yaushe ya fita? Ina ta kiranshi bai d'auka ba kuma har yanzu bai kira ba"
Tace "ai bai zo ba wannan karshen makon"
Tace "ai nayi tunanin ya zo, meya sa bai zo ba? Ko aiki ne ya masa yawa", tace "eh haka yace min"
Tace "to shikenan zan sake kiranshi, sai da safe"
Ta amsa mata da "to Umma".
Ranan Monday bayan Abdul ya tafi wurin aiki Raheemah ta kira Jaleelah, ta d'auki number dinta daga wayar Abdul. Lokacin Jaleelah na kwance a gado tana jiran Inteesar ta kawo mata breakfast, duk a tunaninta idan ta d'aga wayar zata ga call din Abdul ne amma sai taga new number. Tayi picking tare da yin sallama, sai dai ba a amsa mata ba, kawai jin dariya tayi, Raheemah tace "matar AbdulHakam ce ko?"
Tace "eh, wace ce?"
Tace "sarauniyar AbdulHakam ce"
A take ta gane ko da wa take magana, 'yar dariya tayi tace "lallai kin sha hypo, sarauniyar AbdulHakam ai ita ce Umma, and this is what makes him my prince, he's a son of a queen"
Raheemah tace "I don't bloody care! Dama kawai ina so na tambaye ki ne, how market?"
Tayi murmushi tace "Alhamdulillah, kullum cikin cinta muke yi"
Tace "to idan kin isa next weekend ki sa shi yaje inda kike"
Ajiyar zuciya Jaleelah tayi, tace "baiwar Allah ba shekarun bane fa, ya kamata ki san akwai wayau da dubara, sannan aiki da hankali"
Tace "yadda nake cikin farinciki na hana shi zuwa gareki yau bazan iya fada miki maganar da zata sa ki kuka ba saboda zafin zai yi miki yawa"
Ta d'age giranta na dama tace "oh really? to shikenan, ni kuma nayi miki alkawari yau sai AbdulHakam ya zo Kano, watch out"
Ta yanke call din ba tare da ta jira cewarta ba. Lokacin Inteesar ta shigo kawo mata breakfast, akan gado ta ajiye mata tace "uwan biyu ga wannan", tayi yar murmushi tace "to an gode"
Ta zauna a gefenta tace "ki gode ma Allah daya dauraki a kaina ina son ki, da wannan shegiyar kishiyar taki ce wlhy da sai dai ta mutu da yunwa, amma bazan dafa abinci purposely saboda ita ba"
Jaleelah tace "oho dai, matar yayanki ce"
Tace "to ina ruwa na"
Tace "ke dai ci abinci ki zo muyi hira".
Da yamma Abdul na zaune a bedroom dinsa yana kallon kayan babyn da ya tara, sai duk wanda ya siya na mace sai ya siya na namiji saboda Allah zai iya yin ikonshi a zo a haifi prince. Kayan sun yi masa matukar kyau, sai kuma wasu da ya siyo unisex. Yana zaune yana dudduba kayan call din Jaleelah ya shigo wayarshi, da sauri ya tashi ya kwashe kayan ya bude wardrobe ya mayar da su sannan yayi locking, lokacin call dinta ya yanke sannan ya kira.
Mata kenan.
Voice dinta tamkar wacce take kuka tace "Ameer"
Hankali a tashe yace "meya same ki? Meya faru?"
Shesshekan kuka ta cigaba da yi, hankalinsa ya k'ara tashi, yace "Jaleelah kiyi min magana mana, me ya faru?"
Tace "bana jin dadi, I'm dying... Ameer zan mutu"
A razane yace "what?? Ciwon me kike yi? Inteesar fa?"
Tace "ni dai kawai ka zo may be I'm going to die, I want to see you...."
Har in'ina yake yi, yace "to insha Allah gani nan zuwa" Daka ganshi kaga wanda hankalinshi ya tashi, keys dinsa kawai ya d'auka ya fita yayi locking bedroom dinsa saboda gudun kar Raheemah ta aika yar aikinta tayi mishi gyaran d'aki ko wankin toilet. A hanyar fitarsa daga inner sitting room zuwa main parlour suka yi crossing, ita zata shiga shi kuma zai fita, yace "sai na dawo"
Ya wuce ta, tace "ina zaka?"
Yana tafiya yace mata "Kano", yayi ficewarsa daga gidan. Yana tafe yana tunani, "yanzu idan ta mutu ya zai ji? Yabi son zuciyarshi ko da weekend din nan yaki xuwa mata.
Tana ajiye wayar ta tuntsire da dariya, Inteesar na daga gefenta tace "so it's true after God fear women, kalli yadda kika tayarwa yayana da hankali, babu kyau k'aryan ciwo fa"
Tace "bafa cewa nayi banida lafiya ba, cewa nayi bana jin dadi, to dama dadin nake ji? Yaje ya tattare mata kiri kiri ya ki zuwa min wannan weekend din"
Tace "ba kin ce ma Umma aiki ne yayi masa yawa ba?"
Tace "ba wani aiki, na rufa mishi asiri ne kawai amma ko waya bama yi, matarsa ce ta hanashi zuwa, d'azun da safe ta kira ni take fada min wai ban isa ya zo inda nake ba, shine ni kuma nace nayi mata alkawari yau sai ya zo Kano"
Inteesar ta fashe da dariya, tace "wato ku yan duniya ko? Amma fa babe kinyi maganinta, kin burgeni"
Jaleelah tace "yanzu dai dan Allah ki kira Umma kice mata bana jin dadi zaki ga itama ta zo kar asirina ya tonu", ta karishe maganar tana dariya. Inteesar ta d'aga waya ta kira Umma ta shaida mata, tun da ta san lalurarta nan da nan ta fara shiri zata je dubiya. Nan Jaleelah ta kwanta tayi laushi kamar mara lafiyar gaske. Abdul na hanya ta sake kiranshi, voice dinta so weak, yace "Ameerah kar ki damu I'm on my way", tace "to Jawhar, na ma ji sauki"
Yace "Allah ya k'ara sauk'i, sai na zo".
••°••
Ran Raheemah a b'ace ta wuce sitting room, nan ta tarar da yar aikinta Ablah a zaune akan kujera tana kallo, sai ta nemi ta sauke fushinta akan yarinyar, tace mata "dan ubanki akan kujera ne zaki zauna? Idan na sake ganinki a nan sai na zane ki, kin gama min wanke wanken ne?"
Jiki na rawa ta sauka daga kan kujeran tace "eh"
Tace "to gyaran d'akin fa? Ko uwarki kike so na jira daga gyad'i gyad'i ta zo ta gyara min"
Bata iya bata amsa ba ta wuce bedroom dinta domin gyara mata. Bayan ta gama ta koma d'akin da aka bata ta kwanta ta ci kukanta ta gode ma Allah. Kusan kullum sai Raheemah ta zage ta kuma abu kad'an zata yi mata ta fara yi mata barazanar zane ta.
Saboda matsuwar da Abdul yayi na yaga Jaleelah a bakin gate yayi parking bai ko tsaya shigo da motar ba yayi shigewarsa cikin gidan, ko sallama ma ya kasa yi ya shiga bedroom din, nan ya tarar da Umma da Inteesar, Jaleelah kuma na kwance akan cinyarta idanuwanta a rufe, ajiyar zuciya yayi daya ga alamar ta samu sauki kenan, daga gefe ya d'an risuna ya gaishe da Umma. Ya dubi Inteesar yace "je ki kawo min cup na ruwa"
Ta tashi ta fita shi kuma ya zauna kan sofa. Sannan yace "Umma ya jikin nata? Ko zan kaita asibiti ne?"
Umma tace "gata nan da sauk'i dai, ko nima na so mu tafi asibitin amma tak'i yarda"
Yace "to ai Umma ba biye mata zaki yi ba, da kun tafi"
Duk a kunnin Jaleelah suke hiran. Inteesar ta shigo dauke da d'an k'aramin tray ta d'aura bottle d'in ruwa da cup a ciki ta ajiye mishi akan table din dake gabanshi sannan ta sake fita.
Umma ta dube shi tace "kar ka damu ta ji sauk'i duk laulayi ne, wai ina labarin siyan kayan haihuwa?"
Yace "akwai wa'inda na sissiya amma zan baki kudi ki k'aro mata sai sauran abubuwan buk'ata"
Tace "to", yace "dubu d'ari zai yi?", tace "me zai hana?"
Yace "to gobe idan Allah ya kaimu zan turawa Izz kudin ta account dinshi sai yaje ya cire miki"
Umma tace "to, Allah dai ya sauke ta lafiya"
Ya amsa mata da "amin".
Ana gab da fara kiran sallah Umma ta tashe ta, don har baccin gaske ya fara d'aukarta. Tace ta tashi ta zauna magrib tayi. Tana yamutsa fuska ta zauna sannan ta murza idanuwanta, AbdulHakam ta gani zaune a kan kujera yana kallonta, sai tayi nara nara da fuska kamar zata yi kuka, Umma tace "ko zaki ci abinci ne?"
Ta girgiza kai alamar a'a, tace "d'an Alhaji ko dai zan tafi da ita gida ne?"
Ba gabanshi kadai ya fad'i ba harda na Jaleelah, yace "ai Umma a nan ma Allah zai bata lafiya"
Take ta gane nufinshi, tace "to shikenan"
Har wata yar murmushi Jaleelah tayi da Umma bata gani ba. Bayan Abdul ya tafi masallaci ita ma ta tafi gida tareda tabbatar musu dawowar ta gobe cikin amincewar ubangiji.
Tana fita Jaleelah ta tashi ta zauna, Inteesar ta karisa kusa da ita tana dariya ta zauna, tace "Jaleelah baki da dama"
Itama dariyar tayi, tace "ke barni kawai, mata gaba d'aya tabi ta raina ni, Allah kad'ai yasan me ta gaya mishi 'yar banzan"
Inteesar ta tuntsire da dariya, tace "ai na so ace Ya Abdul yace dole sai kun je asibiti"
Tace "To muguwa bai ce ba. Kin ga bari na lallab'a naje nayi sallah kamin ya dawo tunda ke ba yi zaki yi ba", ta sauka daga kan gado ta shige toilet.
Abdul abin nema ya samu, dama yana hangen weekend gashi kuma yanzu Allah ya sa yaje before then. Inteesar dole ta koma d'ayan bedroom d'in ta bar musu nan. B'arjewa yayi abinsa da ya ga ta samu sauk'i a irin tasa fahimtar. 11pm ya fito daga wanka bayan Jaleelah ta fito, yayi changing zuwa nightie, kallon time yayi yaga gara kawai ya karisa darensa a nan gobe sai yayi fitar asuba.
Duk time d'in da zai koma sai yaji kamar ya tafi da ita, har da na sanin barin Raheemah ta zauna a Kaduna yayi. Saboda bata kula da buk'atunshi sai k'aramar yarinya ce take kula da shi.
Da asuban bayan ya dawo sai da suka sha sabon love kamin ya fara shirin tafiya. Komai ita tayi masa just as before, abinda Raheemah bata tab'a yi masa ba kenan, ta dai yarda suyi wanka tare idan ta suka fito kowa yayi abinda ya dame shi.
Before 6:15am Inteesar ta gama had'a musu breakfast saboda bata sallah bata tsaya yin komai ba. Then har Abdul ya shirya. Tare suka yi breakfast d'in su uku sannan da ya gama ya tashi ya fita Jaleelah ta mara masa baya. Bai tafi ba sai da yayi kissing princess d'insa. Suka rabu cikin farinciki da annashuwa. Sai da ya biya gidansu Umma ya gaishe su sannan ya wuce. Gudu yayi ba kad'an ba a hanya. To 8am ya isa gida. Bai shiga da motar bama ya barta a waje don ya makara, uniform kawai zai sa ya fito gidan.
A falo ya tarar da Ablah tana mopping, cikin girmamawa tace "ina kwana"
Ya wuce ta yana fad'in "lafiya lau 'yan mata".
Bayan yayi changing ya lek'a d'akin Raheemah yaga tana ta sharar baccinta yayi wucewarsa.
A zaman da Inteesar tayi a gidan Jaleelah yasa suka zama kamar best friends. Ko wace ta San sister dinta Jaleelah. Har ziyara suke kawo mata ko kuma idan hanya ta biyo da su su yada zango a gidanta. Haka ma Mo'az, kullum cikin jin labarin sis Jaleelah yake. Har zance yake zuwa gidan amma bai tab'a ganinta ba.
Lokacin da Abdul yake office kusan bayan duk 1hr sai ya kira Jaleelah. Wannan abu kuwa yayi mata sugar. Haka ma da ya koma gida yayi ta kiranta.
Da daren ranan aka saki admission list na BUK and fortunately Inteesar ta samu admission a first list. Sun yi farinciki sosai don a daren sai da ta koma taje ta fadawa Umma da Abba sannan ta dawo, sosai suka yi farinciki. This is the chance she's been waiting for, tana shiga university bada dadewa ba Mo'az zai turo manyanshi a nema mishi aurenta.
A gidan Abdul da Raheemah kuma Raheemah na nan a kwance bata da lafiya, tafi complaing kanta da cikinta. Abdul yayi iyakar iyawanshi wurin ganin sun tafi asibiti tace ba zata ba. Yaje chemist yayi complaining aka har had'o mishi magunguna shima tak'i sha. Around 12am da taji azaba yak'i na k'are da kanta ta rok'e shi ya kaita asibiti yace sai dai tayi hakuri zuwa wayewar gari. A daddafe ta kai safiyar, ko wanka ta Kasa yi a haka suka tafi asibitin.
Bayan yan tambayoyin da likita yayi mata ya tura su lab tayi test na fitsari a bata result din immediately. Bayan sunje sunyi suka sake komawa wurin Doctor d'in. Rubuce rubucenshi yayi a cikin file d'inta sannan ya d'ago ya kalli Abdul yana murmushi, mik'a mishi hannu yayi yana fad'in "congratulations Sir"
Abdul ya mik'a masa hannu suka yi handshake, yace "you'll soon be a father insha Allah"
Abdul yace "thank you". Ita kuwa sab'anin abinda Abdul yake ji take ji, zuciyarta tayi bak'i sid'ik, kwananta nawa ne da aure da har zata d'auki wani ciki, da ita d'aya taje asibitin da babu abinda zai hanata fitar da cikin.
Abdul kuwa sai murna yake yi kamar wani sabon ango. Yana masifar son babies. Fatanshi Allah ya sauke su lafiya dukansu. Ko kad'an Raheemah bata nuna farincikinta ba, fuskarta a had'e babu annuri har suka isa gida.
[4/23, 5:58 PM] Leenah💋: ⚜Mijin Jaleelah⚜
55
By Linah Shams✍🏼
*The Sun*💖
2 weeks later aka yi releasing admission list na ABU Zaria, fortunately again itama Jaleelah tayi securing admission inda zata karanci Economics. Lokacin she was 8months pregnant ita kuma Raheemah 2months pregnant.
Kullum Abdul cikin kula da su yake yi, sai yaji kamar ya had'a su gida d'aya saboda ya samu daman kula da ko waccensu dai dai misali musamman Jaleelah da cikinta ya tsufa kuma sai weekends yake zuwa inda take, sai dai suyi magana ta waya. Duk farincikin da yake yi da za a bud'e masa zuciyar Raheemah da sai ya sha mamaki, don bata k'i ace yau ta wayi gari cikin ya fita ba. Saboda ita tafi so ta mori amarcinta kamin ta fara haihuwa, yanzu kuwa mai akayi da maza?.
Wani weekend da ya zo Abdul ya d'auki Raheemah suka tafi Kano ita kuma Ablah Raheemah ta tura ta zuwa gidan wata k'awarta a layinsu ta dinga kwana kamin su dawo. Taji dadin tafiyar saboda bak'in kudirin dake ranta. A gidan iyayenshi suka sauka. Bayan ya shigar da motarsa gidan suna k'ok'arin fitowa Jaleelah da shigowarta gidan kenan ita da Inteesar ta k'wala mishi kira "Ameer!!" yayinda suka fito daga motar. Waigawa yayi yana kallonta yana murmushi, sai yau ya k'ara ganin yadda cikinta yayi girma da ya hango ta daga d'an nesa. Cikin d'an sauri sauri ta karisa kusa da shi ta rungume shi ba tare da ta ji ko wani d'ar a ranta ba. Shima wrapping dinta yayi da arms dinsa, bata ji kunyar Inteesar da Raheemah ba tayi kissing lips d'insa. Bet suka yi da Inteesar taga eh dagaske Jaleelar zata iya, ita da kanta taji kunya ta kama hanya ta wuce su, bata kai ga shiga cikin parlour ba taji Jaleelah ta kwala ihu mai k'arfi, da sauri ta waigo taga ko mene ne taga Raheema a tsaye a gefenta ita kuma Jaleelahr tana rik'e da kuncinta tana hawaye, tuni Abdul shima ya d'aga hannu ya wanke ta da mari, ya d'aga hannu zai k'ara mata Jaleelah tayi saurin rik'e mishi hannun, a fusace ya kalleta cikin fad'a yace mata "let go of my hand!", daburcewa tayi amma bata sake mishi hannun ba, tace "dan Allah uncle Abdu ka kyaleta mana"
Sai ga Umma ta zo, Jaleelah na ganinta ta sake mishi hannun. Umma ta dubi Raheemah dake zubda hawaye tana rik'e da kuncinta tace "d'an Alhaji lafiya? Meke faruwa haka?"
Bai ce ma Umma komai ba ya dubi Raheemah ya zabga tsaki sannan yace mata "bloody fool"
Yayi wucewarsa. Sosai taji zafin zagin gashi kuma ta d'auke shi a matsayin dizgi da wulakanci, shima bai kai ga shiga d'aki ba ta sake d'aga hannu ta kwashe Jaleelah da mari a gaban Umma, ihu ta sake kwalawa wanda yafi na farko alamun zafin marin yanzu yafi na baya, Abdul a fusace ya dawo shima ya d'auke ta da tagwayen mari. Ya shak'o ta Umma ta bige mishi hannu tana fad'in "dama baka da wayau? Da girmanka kake marin mace?"
Raheemah tace "mugu azzalumi, you are a monster!"
Umma tace "haba meke damunki Raheemah?"
Cikin hayagaga tace "ki barni na fad'a mishi mana, banza mayaudari kawai, akan wannan jakar ce har zaka iya mari na!"
Jaleelah kam wuce su tayi ta shige d'aki Inteesar ta bi bayanta, Umma tace "amma baku kyauta ma kanku ba musanman kai d'an Alhaji, don me zaka mari mace? Baka san kimarta bane?"
Yace "Umma Jaleelah fa ta mara ba tare da ta yi mata komai ba"
Raheemah tace "Allah ya isa na wlhy, if not that you're selfish meya sa zaka yi hugging dinta a gaba na while I'm also pregnant for you"
Rai a b'ace yace mata "if you think I do that for the sake of pregnancy then abort it! Wawuya kawai"
Ya wuce ta cikin fushi ya shige cikin gida. Umma tayi ta rarrashinta nan ma ta nemi ta huce a kanta, tayi ta yi da ita ta shiga ciki kamin ta wuce gida a samu a sasanta tace Allah ya kiyaye mata gidan ubanta yafi na nan komai don haka ba zata zauna ba tayi tafiyarta. Gidan aminyarta Rabab ta sauka, ta shiga tana kuka kamar ranta zai fita. Fitowar Rabab din kenan daga kitchen, ta ajiye plate din dake hannunta kan center table ta karisa wurin Raheemah suka karisa parlourn tare, a kan kujera suka zauna, Rabab tace "wai Raheemah lafiya? Meya same ki kike kuka haka?"
Ta juya mata gefen fuskarta tare da yakice mayafinta gefe, tace "me kika gani?"
Tace "subhanallahi! Wa yayi miki irin wannan d'anyen aikin"
Tace "wa idan ba AbdulHakam ba"
Rabab tace "haba wani irin AbdulHakam kuma babu dadin ji, shaye shaye ya fara yi ko kuma fitowarku kenan daga psychiatric?"
Tace "da don wannan ne bama zan yi kuka ba, saboda nasan da matsala, hankalinshi garau yayi min wannan cin zarafin"
Tace "amma, garin yaya?"
Share hawayen fuskarta tayi tace "Rabab wai a gabana ne zai rungume wannan tsinanniyar har su yi kiss? Put yourself in my shoes, me zaki yi musu?"
Tace "ai da sai ta gwammace kida da karatu"
Tace "to ni marinta kawai nayi yayi min wannan d'anyen aikin akan fata ta"
Rabab ta zabga ashariya, tace "to ke kuma sai ki kayi me? Baki haukace musu ba?"
Tace "sai da nayi mata marin da yafi na farko, shine ya sake zuwa ya mare ni"
Rabab ta sake zabga ashariya, tace "hehehe! Ni har ya isa ya d'aga hannu ya mareni ban illata mishi mata ba"
Raheemah tace "wlhy, wai saboda tana da ciki kuma nima ai yanzu ina da cikin, two months"
Rabab tayi dariya mai kama dana basawa, tace "shegiya nawan, shine har kika tsaya zasu wulakanta ki"
Tace "to ai the most annoying thing shine ce min yayi wai idan ina tunanin don ciki ne ya sa yake mata abubuwan da yake yi to in je in zubar da nawa"
Rabab ta dafe kirji, tace "ki nuna mishi maganin biri karen maguzawa, maganin shege mahaukaci, wallahi da nice ke sai na zubda shege, har ya isa? Ya isa? Guda nawa yake, meya ke takama ne dashi wai Raheemah da har yake miki haka?"
Tace "to yana tak'ama da ina son shi shiyasa. Amma ke da kika san komai, ai zuciyata kika karanta don cikin nan kamar na zubar, kuma wallahi sai ya bani takarda ta kamin watan nan ya k'are"
Hannu Rabab ta bata suka tafa, tace "shegiya nawan! Amma fa ki bi a hankali, ni bance kije ki nemi saki ba"
Ta tab'e fuska tace "naki ake ji baiwar Allah, amma ko da d'aya ne sai ya bani saboda ko zai san muhimmanci na a rayuwarshi, kuma bari kiji ta bakin Sufayya Ghali". Handbag dinta ta bude ta zaro android phone dinta, ta nemo number din Sufayya ta doka mata kira ta sa shi a loudspeaker. Bata b'ata lokaci ba tayi picking, "aloww"
Raheemah ta amsa da "hello ya kike?"
Tace "dai dai wlhy, matar soja ashe kina kiran jama'a, ai na aza ko sojan yace a ware mu ne"
Tsaki tayi tace "haba wane ne babanshi a Kano, ke Nigeria ma da har zai sa nayi dumping dinki" ta
Labarta mata duk abinda ya faru tayi sannan tace "ke ya kika gani, dani nace zubar da cikin zanyi". Sufayya dama ta tsani Abdul ba don komai ba sai don bak'in cikin rasa shi da tayi, tace "to da me kike jira, kije ki zubar da shi"
Tace "dama ni tun farko ba son cikin nake yi ba, saboda du du du kwana nawa ne da auren da zan yi ciki?"
Tace "my friend do away with that pregnancy!"
Raheemah tace "an gama Hajiya"
Tattaunawa suka yi da Rabab bayan sun gama da kanta ta mayar da ita gida a cikin motar ta kirar honda civic.
••°••
Abdul na shiga ciki d'akin Inteesar ya nufa directly, he desperately wanted to see his wife. Bai ma lura da Inteesar ba. Yana Shiga ya wuce straight wurin Jaleelah yayi hugging dinta yana patting dinta a baya, Inteesar fita tayi ta basu wuri sai ga Umma ta shigo. Sai sannan suka rabe, Umma ta karisa ta rik'e hannun Jaleelah, ita kam dadi shagwaba ta langabar da kanta kan shoulder din Umman, Umma ta dubi Abdul tace "kayi maza ka tafi gidan iyayen yarinyar nan ka basu hakuri, itama ka bata hakuri"
Da mamaki hade da ware idanu ya kalleta, yace "Umma kiyi hakuri, amma gaskiya...."
Ta dakatar dashi, "ba ra'ayinka na zo ji ba, umurni na zo baka"
Ta ja hannun Jaleelah suka fita. A fusace shima ya fita ya bar gidan, ranshi a b'ace yake tukin har ya isa gidansu, yayi parking a gefen hanya sannan ya fito ya tsaya a bakin gate din yayi knocking, mai gadi ya bude ya ga Abdul ne, murmushi ya fara yana yak'e fararen hakoransa, Abdul ya d'an Shanye b'acin ranshi suka gaisa, yace "Raheemah na ciki ko?"
Yace "a'a bata riga ta iso ba"
Yace "ba ta iso ba?"
Yace "eh ranka shi dad'e"
Abdul yace "to ba matsala"
Wurin motarsa ya koma ya hau bayan ya zauna. Tunani kawai yake yi, dama rashin mutuncin yarinyar nan har ya kai haka. Yafi k'arfin mintuna ashirin yana zaune a wurin sai zuwa can yaga mota na zuwa, shi bai ma kawo ita bace a ciki, Kansa a sunkuye yana operating wayarsa suka zo suka wuce ita da Rabab. Sai da yaji karan bude gate sannan ya d'aga kai ya kalli motar ya sake mayar da dubanshi ga wayarshi. No sooner sai ga mai gadin ya zo inda yake, yace "yallabai ga Aunty Babyn can ta dawo"
Yace "okay", tare da saukowa daga saman motan yabi bayan mai gadin suka shiga gidan. Fitowarta daga mota yayi daidai da shigowarsu, tana ganinshi ta fashe da matsanancin kuka tare da wucewa cikin gida da gudu. Rabab ta fito ta watsa mishi wani uban harara ta wuce shi, shi bama ta ita yake yi ba. Yadda Raheemah take kuka yasa gwiwarsa yayi sanyi, he made a woman cry. He made his wife cry.
Kasa shiga ciki yayi sai ya juya ya koma wurin mai gadin ya zauna. Sai bayan 20mins sannan ya rok'i mai gadin ya shiga ya kira mishi Raheemah. Ba musu ya tashi ya shiga ciki b'angaren Mom, daga d'an gefe ya tsaya yana ta sallama, Mom dake ta balbalin bala'i bata samu daman amsawa ba sai Rabab ce ta amsa, yace "dama mijin Aunty Baby yake son ganinta"
Mom bata iya cewa ma ya shigo ba jiki ba mayafi ta mik'e tace "muje in ganshi"
Abdul na ganin bullowarsu cikin compound din yayi saurin tashi tsaye. Tun daga hanya Mom take surutai har ta isa kusa dashi, tace "ashe dama haka kake? Ashe kai wulakantaccen mutum ne ban tab'a sani ba? Dama haka kake d'an k'aramin gida? Tarbiyyan gidanku kenan dukan macce? Kamar kana da wayau ashe baka shi. Assha, iliminka bai amfane ka da komai ba. Kuma wannan duka da kayi mata ba ita ka wulakanta ba, mu ka wulakanta. Yanzu bayan ka gama jibganta a gaban uwarka me ka zo yi a nan?"
Sosai ya danne b'acin ranshi, yace "Mama ki yi hakuri, insha Allah hakan ba zai sake faruwa ba"
Cikin d'aga murya tace "ai ban b'oye maka ba tun farko, ba za kai min yarinya cikin gidanka ka dinga wulakanta ta ba"
Kasa magana yayi, tace "munafikin banza kawai" sannan ta buga tsaki ta wuce. Duk a kan idanuwan mai gadin akayi komai, bayan ta wuce ya zo yana ta bashi hakuri. Nuna mishi yayi babu komai ya fita ya wuce gida ranshi na k'una. Ko da ya isa gida kasa fitowa daga motan yayi yana jin zafin kalaman Mom sannan ya fita ya shige ciki. A parlour'n Umma ya tarar da su dukansu, yana shiga ko amsa sallamarsa ba su yi ba Umma tace "d'an Alhaji babu inda kaje", a gefen Inteesar ya zauna, yace "naje"
Tace "k'arya kake yi, kawai ka raina ni, amma babu inda kaje"
Yace "haba Umma meyasa wai baki yarda dani? Wallahi naje. Naje mana"
B'acin rai ne k'arara a fuskarsa ga idanuwanta sun yi ja kamar ze yi kuka, Sai jikin Umma yayi sanyi, tace "to naga ka dawo da wuri ne"
Cijewa yayi yace "eh, mamanta tak'i hakura"
Umma tace "amma ya kamata ka koma anjima da daddare"
Yace "Umma kiyi hakuri bazan iya komawa ba, kar kiga yadda ta dinga muzanta ni, what for? Bata saurare ni ba bare taji me zance, bak'ak'en maganganu tayi ta sakar min tana aibanta ni, I can't! Bazan iya komawa ba"
Tace "d'an Alhaji hakuri zaka yi, dole ka koma anjima"
Yace "Umma ki gane, ko wane d'an halaq dole ne ya kare martabar gidansu, bazan iya komawa ba ta zagi gidan dana fito, ki bari sai zuciyarta tayi sanyi, idan sun neme ni falillahil hamdu idan kuma basu neme ni then shikenan sai ayi mai yihuwa"
Da sauri Umma tace "kar in sake jin haka na fad'a maka"
Shiru yayi bai sake cewa komai ba sai wayarsa ta fara ringing, nan ya fita ya bar d'akin zuwa compound. Jaleelah kam abin duniya duk ya bi ya dame ta, everything was happening because of her, ba zata yi farinciki ba matukar Raheemah da Abdul suka rabu saboda ita ce sila, akanta hakan ya faru.
Da dare bayan sun koma gida ta kasa sukuni, sai tunani take yi akan abin da ya faru earlier. Duk lokacinda ta zauna tunani kawai take yi "what if auren Raheemah da Abdul ya k'are?" Har sai da Abdul din ya fuskanci haka. Tana kwance akan gado amma hankalinta gaba d'aya baya jikinta, kissing cikinta yayi sannan yayi kissing cheek dinta, sai sannan ta dawo hayyacinta, murmushi ta kiriro da suka hada ido, shima ya sakar mata da murmushi, yace "hajiya tunani"
Tashi zaune tayi ta janye kafafuwanta ya zauna, ya dafa ta which is more of a hugging, yace "queen din princess dina. Me kike tunani?"
tace "ba komai, I wasn't thinking"
Yace "a'a kar muyi haka dake Ameerah, I've been observing you, meya same ki?"
Tausayinshi taji, ta d'ago da kanta tana kallonshi, tace "do you think I'm really a blessing in your life?"
Confusedly yace "as in how?"
Ta mayar da kanta kan shoulder dinshi, tace "can't you see everything is going upside down? Just because of me"
Yace "then who tell you upside down is always wrong And... That downside up is the correct situation?"
Ajiyar zuciya tayi tace "dan Allah kaje ka bawa iyayen matarka hakuri, I can't help seeing you guys part, at first I became a barrier between you two, ka zo ka aure ni instead of ka aure ta, you've gone through hard time with your parents kamin ka aure ta, just because you are married to me. Yanzu ka aureta kuma akaina kun samu matsala. Pls kaje ka basu hak'uri Ameer, ko da ya kai point din rabuwa I will give up on you, zan hakura saboda she's your first love"
Abdul ya d'ago da kanta ya kalli fuskarta, yace "I can never give up on you. Dama you can give up me? Upon all the love and the stuggles we had together"
Imagining rabuwarsu tayi sai fara hawaye. Hugging dinsa tayi so tight bata ma yi considering big tummy dinta ba, tace "I love you Ameer... Pls kar ka rabu da ni. You're the love of my life"
Wrapping dinta yayi da arms dinsa, yace "insha Allah only death can do us apart".
⚜Mijin Jaleelah⚜
56
By Linah Shams✍🏼
*we're almost done lovies*🙏🏼💖
Har weekend d'in ya k'are Abdul bai sake waiwayar inda Raheemah take ba don gudun kar ya sake fuskantar wulak'anci kwatankwacin wanda ya fuskanta a baya. Haka itama Raheemah, bata tab'a nemanshi ba tun ranar da suka rabu, tasan yanzu yana nan yana missing d'inta.
Ranan Monday da daddare ta zauna ta kitse duk wani rashin mutunci da take da shirin yi ba tareda ta nemi shawaran kowa ba, dama shi mara mutunci daban yake, duk ta gama saka da warwaranta ba tareda tayi tunanin abinda zai kai ya komo ba. Tana so hakanta ya cimma ruwa kamin mahaifinta ya dawo daga tafiyar da yayi zuwa k'asar Uganda.
Da safiyar ranan Tuesday, ta tashi da wuri tayi wanka tayi shigarta na doguwar riga da d'an k'aramin veil data yane kanta dashi. Handbag dinta ta d'auka ta zura k'afafuwanta cikin wedges shoe ta fito. D'akin Mom ta nufa, a hanya ta had'u da Kuhaylah da Hambali, suka gaisheta ta wuce su ta na amsawa. Murd'a hannun k'ofar tayi ta shiga da sallama, amma irin sallamar da baya jiran amsawa, a gefen gado ta tarar da Mom na zaune, tace "Mom ina kwana"
Ta amsa mata da "ina zaki da sassafe haka?"
langabe mata tayi tace "Mom wlhy jiya na kwana da fever ne"
Tace "to yanzu yaya? Kin ji sauk'i?"
Tace "a'a ina so naje naga doctor ne"
Mom tace "to ki zauna a gida mana a kira Doctor Ayan ya zo ya duba ki", tace "a'a Mom ki bari kawai naje Sahara Hospital, na riga nayi booking doctor tun last night"
Tace "to in raka ki ne ko zaku je da Kuhaylah?"
Da sauri tace "a'a Mom no need. I'll go by my self, zan iya"
Kud'i mai yawa Mom ta irgo ta mik'a mata, tace "Allah ya k'ara sauk'i"
Ta amsa mata da "amin" sannan ta fice daga d'akin. Already dama driver ya gama wanke motocin gidan saboda a nan yake kwana.
Sai da ta zabi mota daidai hawarta sannan ta kwalawa Lukman din kira ya zo suka fita. Sahara Hospital suka nufa kai tsaye. Bayan zaman da tayi na kusan 20mins a reception ta samu ganin Doctor. Bata b'ata lokaci ba wurin fad'a mishi k'udurinta na ganin ta fitar da cikin jikinta, ko da likitan ya tambayeta dalili ce mishi tayi ba huruminshi bane. Sai da suka yi tsadar kudin aikinta sannan yace mata ta dawo ranar Alhamis don yin aikin. Tayi mishi godiya sannan ta tafi.
Raheemah ta kasance yar so a wurin iyayenta, musamman mahaifinta da ko hawayenta baya son gani saboda sai da suka shekara bakwai da aure sannan aka haifeta, lokacin ma sun fidda rai da samun haihuwa. Itace first born a gidansu, ta taso cikin dukiya, shagwaba da k'auna. Ba mai hanata kuma ba Wanda ya isa ya sata. Mom bata fara dana sanin nunawa Raheemah so ba sai da ta fara girma, abinda take so kadai take yi ga rainin tsiya, kan mahaifinta kadai take gani da gashi don ko mahaifiyarta tana ganin damarta. Shi kuwa Dad kullum cikin k'aunar diyarsa yake, ko kadan baya ganin laifinta. Sai daga baya sannan aka haifi kanninta biyu, Kuhaylah da Hambali.
Bayan ta koma gida ta shaidawa Mom cewa ta samu ganin doctor amma yace ta dawo ranan Thursday da yamma. Tun washe garin ranar ta fara k'aryan bleeding da ciwon ciki, amma bata yarda ta nunawa Mom yayi tsanani ba. Da Mom d'in tayi insisting su tafi asibiti sai tace ta kira Doctor ya bata safety measures kuma taji sauki. Ranan Thursday nayi tun da azahar ta shirya ta bar gidan zuwa asibiti. Ko gezau bata ji ba a zuciyarta, gaba d'aya idanuwanta sun rufe akan rashin gaskiya. Babban k'arin bak'in cikinta shine Abdul d'in ma yak'i nemanta har ranan, kwana shida kenan, tasan yana can yana ririta wannan shegiyar yarinyar.
Sai bayan sallar la'asar sannan likitan ya zo as promised. Ba tare da wani jinkiri ba suka shiga yin abinda ya kamata. Akayi abortion successfully amma sai ta kwana biyu a asibiti. Hankalinta a kwance ta daga waya ta kira Mom, bayan tayi picking tace "Mom kin jini shiru ko ki kira"
Tace "dama jiranki nake ta yi ki dawo inji idan ke mahaukaciya ce, ki bar gidan iyayenki tun rana har dare baki dawo ba kuma baki iya kiran waya ba"
Tace "Mom but kin san fa banida lafiya kuma asibiti na tafi"
Tace "rufe min baki! Yanzu kina gidan ubanki ne?", k'asa k'asa tayi da murya tace "Mom anyi admitting dina ne, cikin ya fita"
Sai da gaban Mom ya kusa fad'i, tace "Subhanallahi.. Ai ba yadda banyi dake ba ki koma wurin likita kika ce a'a ai ya baki safety measures, yanzu gashi nan ai cikin ya fita"
Kamar salihar gaske tace "Mom haka Allah ya k'addara"
Tace "to, ya jikin naki? Ba wani matsala"
Tace "eh amma sai saturday zan dawo"
Tace "to gani nan zuwa"
Ta amsa mata da "to". Ta katse wayar tana dariyar jin dadi. Ita kuwa Mom sai jimami take yi kamar irin har an haifi cikin abinda aka haifa ya girma sun saba. Sai kiran dangi take yi tana shaida musu Raheemah tayi b'ari.
Ruwan zafi kawai ta dafa ta juye a flask ta d'auki kayan tea ta zuba a basket sannan ta kwaso ma Raheemar kayan canjawa ta wuce asibitin. A nan ta kwana sai washe gari Kuhaylah taje ta amshe ta ita kuma ta koma gida.
B'angaren Abdul da Jaleelah abun ba a cewa komai, duk da cewa da tunanin Raheemah yake kwana yake tashi, baya so wani abu ya sami aurensu kamar yadda Jaleelah take fata. Hakan yasa yake tunanin sake zuwa gidansu wannan weekend d'in, yasan by now iyayenta sun d'an huce duk da basu saurare shi ba. Sai akayi babban rashin sa'a ayyuka suka yi masa yawa sai ranan Sunday ya samu kanshi, ba don ya gaji ba da sai yaje yaga Jaleelah yayi kissing unseen princess dinshi.
Ranan Monday da yamma bayan ya dawo daga wurin aikinsa yana zaune a balcony shi kad'ai ya d'aga waya ya kira Jaleelah. Sun sha hira sosai sannan ya kira Raheemah. Lokacin tana kwance a d'akinta ita d'aya tana cin potato chips sai mango juice dake ajiye cikin tray a gefenta. Sai da ta gama yatsine yatsine sannan ta d'auki wayar tayi mata rik'on wulakanci. Tana tauna chips d'in tace "hello"
Ya amsa mata da "ya kike?"
Tab'e baki tayi cikin muryar raini tace "lafiya", yace "ya gida?", shima tace "lafiya"
Yace "ranan sunday na kira wayarki ban same ki ba"
Tace mishi "ko?"
Sai ya tsargu da yadda take yi mishi magana, yace "ban gane ko ba, I mean I called but I couldn't get you"
Tace "excuse me malam, yi a hankali"
Ajiyar zuciya yayi yace "understand mana. I did'nt call for something of this nature, ina so muyi magana ne"
Sai taji dad'i a ranta, tasan yanzu ne take da daman da zata gasa mishi aya a hannu, tace "fad'i maganarka"
Yace "ki bawa Mom hakuri saboda ko da na zo d'aukan ki ba zata hana ba"
Shewa tayi tace "ai duk wanda kaji an bashi hakuri to an cuce shi ne, ka auna zancenka a mizani ka auna da kalamai na"
Yace "I admit it nayi laifi, shikenan?", duk dai don a tsira da mutunci yace mata haka. Tace "a'a wallahi, ba shikenan ba, da saura"
Yace "to ina ji"
Taja numfashi sannan tace "a'a it's nothing much ai, takarda ta zaka zo min da ita idan zaka zo kaga babu abinda ma zai sa Mom tayi maka sababi saboda baka auren 'yarta anymore"
Wani iri yaji maganganun nata, yace "Raheemah divorce isn't the best solution"
Cikin tsawa tace "then let it be the worst solution!"
Cikin kakkausar murya yace "it may be, but I can't divorce you"
Tsaki tayi sannan ta yanke wayar tana yar dariya. Lamban Rabab ta nemo ta kwad'a mata kira. Bugu d'aya biyu uku tayi picking, ba ta jira sun gaisa ba tace "Rababatu aiki na ci"
Tace "bani in sha"
Tayi gyaran murya tace "kin san nace miki zanyi abortion ko?", tace "eh eh haka kika ce min"
Tace "to nayi, kuma fortunately babu abinda ya same ni"
Ta fashe da dariya irin na yan duniya, tace "amma fa baki da kirki matar nan, na ma yi tunanin ko har kun daidaita da shi sojan naki ne"
Tace "barshi sai yayi hankali zamu shirya, yana nan na fara gasa shi, saura kuma takardan saki na"
Ta waro idanuwa waje tace "Raheemah a hankali dai, kar ki kai ga haka", tace "ke Dalla.. Har kece zaki bani instructions na bi, ai sai na gara ashi son rai"
Tace "to Allah ya baki sa'a"
Tace mata "amin" ta yanke wayar.
Sosai Abdul ya damu da matakin da Raheemah ta d'auka, duk da he tolerate her he still loves her. Ya shiga damuwa ba k'ank'ani ba, kuma yasan Jaleelah ba zata ji dadin samun wannan labarin ba.
Saboda haka ne ma ya kosa weekend yayi yaje ya sami Mom yayi mata bayani ya kuma bata hakuri ko zata fuskance shi, yasan Dad baya nan da shi zai yiwa magana ko kuma ya tura Baban Tarauni idan abin ya ci tura.
Friday nayi ya tattara inashi inashi ya wuce Kano. Gidan Jaleelah ya fara sauka this time around, haihuwa ko yau ko gobe. Tayi farincikin ganinshi sosai don bata yi expecting ganinshi ba at this moment saboda ta san sai yaje gidansu Umma. Duk yadda yake murmushi sai da ta gane yana cikin damuwa, kamar yadda bai fad'a mata ba haka itama bata tambaye shi ba. Tana zaune kwatsam taji tana son ganin Mommy bayan cikinta ya motsa mata. Sai ta fara tunani idan ta zo ta mutu a wurin haihuwa fa, it's been a longer while bata ga mahaifiyarta ba. Nan da nan ta kawo ma kanta mutuwa saboda cikinta yayi mata girma da yawa. Yana cikin cin abinci ta matsa kusa da shi ta zauna damuwa bayyane a fuskarta, yace "Maman Princess dina"
Tace "Ameer..."
Yana cin abincin yace "mene ne? Kin zo kiyi feeding dina ne?"
Ta b'ata fuska tace "a'a", yace "to mene ne? Baki da lafiya ne?", tace "a'a"
Ya juya ya kalle ta, idanuwanta kamar zata yi kuka, yace "mene ne?"
Tace "ka kai ni wurin Mommy"
Ana wata ga wata. Yace "me ya same ta? Wani abun ne Ameerah? Please explain to me"
Tace "ni kawai ka kaini wurin Mommy"
Yace "amma Ameerah kin san cikin ki ya tsufa, ki bari idan kika haihu sai ki koma"
Kuka ta fara yi mishi babu ji babu gani, tun yana lallashinta har ranshi ya fara b'aci, da ranan Allah kawai tace mishi Kaduna zata. Number'n Mom ya lalubo ya kira, cikin girma da arziki suka gaisa, ita bata ma kawo da Mommy yake waya ba tana gefe tana rera kuka, yace "dama Jaleelah ce gata nan tana ta kuka wai zata zo wurinki"
Mommy tace "kuka kuma? Bata da lafiya ne?"
Yace "wlhy Mommy lafiyarta k'alau, ban san me ya same ta ba"
Tace "to bata wayar"
Ya mik'a mata wayar ta kara a kunnenta, tana sharan hawaye ta gaishe da ita sannan Mommy tace "me ya faru Jaleelah?"
Tace "Mommy ni kawai zan dawo wurinki, idan ba zai kai ni ba ni ki zo ki d'auke ni dan Allah, dan Allah Mommy", hawaye na sake zubowa daga idanuwanta, shi dai Abdul sai binta da idanu yake yi, Mommy tace "wani abu akayi miki?", tace "a'a... Ni dai ki zo ki dauke ni"
Mommy tace "idan akwai wani abu ne ki fada min, remember, I'm your Mother". Tace "Mommy ni ina ganin mutuwa kawai zanyi, kuma na dade ban ganki ba, idan na mutu fa"
Sai ta rushe da kuka. Jikin Mommy yayi sanyi tace "ba zaki mutu ba kinji Jaleelah. Allah zai kawo miki komai da sauki kuma nima zan yi miki addu'a kinji?"
Cikinta ta kalla runtumeme sai kuma sabon hawaye, tace "Mommy Allah mutuwa zanyi", tace "Jaleelah dukkan mai rai mamaci ne, idan kika ga kin mutu kwananki ne ya kare, kinji? In Allah ya yarda zaki haihu lafiya"
Shiru tayi tana shesshekan kuka, Mommy tace "kina ji na?"
Tace "eh ina ji Mommy", tace "zan kira Mamanku muyi magana amma ki daina kuka kinji babyn Mommy?"
Sai tayi murmushi tace "to Mommy amma dan Allah zan zo"
Tace "ki bari sai Allah ya sauke ki lafiya"
Tace "to Mommy sai anjima"
Ta mikawa Abdul wayar suka yi sallama. Sai da ya katse wayar sannan ya kura mata idanu na kusan 1min, cikinta kawai yake kallo. For sure yayi girma da yawa, may be sai dai ko ayi mata CS. Sai ta bashi tausayi, kusa da ita ya matsa ya share mata fuska, yace "dan Allah ki daina kuka kinji baby na?"
Cikin rannaunar murya tace "amma Ameer baka gani zan mutu?"
Yace "haba Jaleelah, ki daina fad'in haka mana, ba zaki mutu ba kinji?"
Tace "to... I'm just thinking... Amm.. Idan ma na mutu ai ba komai, Raheemah will take care of you for me"
Ya furzar da iska daga bakinshi, yana so ya mantar da ita batun mutuwar nan da take fad'a, yace "she isn't willing to be back.. She wants a divorce"
Kamar ita akace za a saka hankalinta ya tashi, tace "pls no.. This is silly"
Yace "yea nima ai ba zan sake ta ba.. Ya Princess? Bata ji daga Abbanta ba last weekend ko?"
Murmushi tayi dukansu suna kallon cikin, yace "zo muje in duba lafiyarta"
Tana dariya yaja hannunta suka tashi suka wuce.
Sai to six sannan suka bar gidan zuwa gidan Umma. Abdul sai ririta yake yi saboda ta daina tunanin mutuwa. Ko me ya gani a hanya sai ya tambayeta ko tana so. Haka har suka kai wurin wani shopping complex tace ya tsaya ya siya mata maltina da fresh milk. Tare suka fito daga motan zasu shiga. A hanyar shiga suka ci karo da Raheemah sai suka ja da baya don bata hanya, fuskarta sanye da sun glasses. Wani irin kallon ta bi su da shi, sannan ta tab'e baki zata wuce, Abdul yace "excuse me"
Taja ta tsaya, yace "ina zaki?"
Ta cire glasses din idanuwanta tace "shiyasa nace maka ka bani takardata saboda gudun irin haka"
Cikin sanyin murya Jaleelah tace "don Allah Yaya Raheemah kiyi hakuri, divorce isn't the appropriate solution"
Tace "dalla rufa min baki shegiya munafuka, annamimiya kawai yar tasha gantalalliya fitsararriya mara k..."
Abdul yaji tana karanto zagi kamar wani karatu ya katse ta, yace "ya isa haka Raheemah, je ki gida"
Hararshi tayi tace "baka isa ba yanzu, a da ne kake da wannan matsayin", ta mayar da glasses dinta ta karisa wurin motarta ta bud'e ta shige ta bar wurin. Jaleelah ta d'aga kai ta kalli Abdul, assuring smile ta bashi shima ya mayar mata da murmushin suka shige cikin shopping complex din.
⚜Mijin Jaleelah⚜
57
By Linah Shams✍🏼
Umma na ajiye wayar ko second biyar ba ayi ba sai ta jiyo sallamar Abdul da Jaleelah, dukansu suka amsa ita da Inteesar. Inteesar da Jaleelah sai washe baki suke yi. Kusa da Inteesar Jaleelah ta zauna, bata kai ga gaishe da Umma ba Inteesar tace "dama yanzun nan nake tunanin kiranki"
Tace "da akwai hot gulma ne?"
Tace "a'a ba wani gulma yau, may be sai zuwa Monday, dama zan fada miki ne ASUU sun tafi strike"
Zaro idanu tayi tareda mokade baki, tace "saboda bak'in ciki?"
Inteesar tace "kema dai kya gani"
Tace "hala basu san wannan year din zan shiga uni bane suka tafi strike, amma ba komai zan sa a nemo min number'n ko wane chancellor muyi magana"
Umma ta katse su "yanzu naga dalilin daya sa yarinyar can har rawar k'afa take yi idan zata gidanki, ashe shiririta kuke yi"
Sai sannan Jaleelah ta tuna bata ma gaishe ta ba, tace"Umma ina wuni", tace "da ku ka gama shirmen, to lafiya k'alau"
Dariya suka yi dukansu, Umman tace "ai dariya ma na baku? Gulmar taku itama ta kusa karewa, na baku nan da litinin mai zuwa"
Inteesar tace "mene ne Umma?", tace "eh zan tarkatota ta dawo gida"
Inteesar tace "to Umma ai duk d'aya ne", tace "don k'aniyarki ba d'aya bane, a d'aki na zata zauna"
Sinnar da kanta tayi tana dariya sannan ta d'ago da kanta ta gaishe da Abdul, cikin fara'a ya amsa mata sannan suka tashi ita da Jaleelah suka fita zuwa backyard.
Umma ta dubi Abdul, tace "d'an Alhaji wai nikam ina labarin Raheemah?"
Yace "tana nan Umma"
Tace "to ka sake komawa gidan nasu ne?"
Yace "a'a, amma da yau na so komawa, duk da bana tunanin hakan mai yihuwa ne", tace "wace irin magana kenan?"
Yace "to Umma yanzu muka had'u da ita a hanya mun tsaya siyan maltina, kin gansu nan a cikin leda", ya fad'a yana nuna mata ledar da Jaleelah ta ajiye a k'asa, ya cigaba "a can wurin siyan muka had'u da ita, Umma ta bud'e baki ta gaishe ni ma tafi karfin haka, nine na tsayar da ita nake tambayarta inda zata, wallahi kar ki so kiga yadda ta dinga fad'a min magana, Jaleelah ma data bata hakuri sai da ta zage ta"
Umma tace "da cewan me?"
Yace "wai saki take nema"
Tace "saki kuma? Ya kamata manya su shiga maganarku"
Yace "nima abinda nake tunani kenan"
Tace "kamin ka koma kaje ka samu Babanku Bak'o kayi mishi bayanin komai, ko da Babanku Iliyasu sai su had'u suje su sami mahaifin nata suyi magana"
Yace "to idan Allah ya kaimu gobe da safe sai in tafi"
Tace "Allah ya kaimu, yanzu dai lek'a bayan nan ka kira min Jaleelah, yanzu muka gama waya da mamanta, akwai abubuwan da zan bata dama tun da dadewa"
Yace "to", ya mik'e ya zagaya ya kira ta. Tare suka shigo da ita tana biye dashi a baya, ta zauna a k'asa kusada Umman tace "gani", tace "yanzu muka gama waya da Maman Afdal"
Tace "Mommy?"
Tace "eh, tace min wai sai kuka kike yi sai kin koma Kaduna"
Taji kunya sai ta sunkuyar da kanta, Umma tace "idan kin fi son can sai in sa D'an Alhaji ya mayar dake, idan zai koma sai Ku koma tare"
Tasan dai duk iya kyautatawa Umma tana mata, idan tace ta fi son komawa Kaduna tamkar ta nuna gajiyawar Umma ne, amma da tana da hali can zata koma, cikin sanyin murya tace "a'a zan zauna a nan, amma ina so ne naje naga Mamana ne, kar ya zo...."
Sai ta kasa karisa maganar ta kakare, Umma ta zuba mata idanu hakama Abdul, sai mood dinta ya sauya at once. Umma tace "kar ya zo mene?"
Hakanan ta daure tace "kar ya zo na mutu ban ganta ba"
Umma tace "ki sa a ranki in Allah ya yarda zaki haihu lafiya"
Cikin muryar tausayi tace "Umma ni dai ina ganin mutuwa zanyi", tace "a'a in Allah ya yarda zaki sauka lafiya kinji?"
Ta gyada kai alamar eh, Umma tace "yauwa".
Amma a ranta bata bar damuwa ba.
°°•°°
Washe gari da safe, around 9am Abdul ya tafi gidan Baban Tarauni. A zauren gidansa ya tarar dashi, bayan sun gaisa a nan sai suka shiga ciki inda ya gaishe da iyalinshi sannan suka shiga d'akinsa.
Abdul yace "dama Baba wata yar matsala ce ta taso shine nace bari na zo na same ka muyi magana"
Yace "to ina jinka D'an Alhaji"
Abdul yace "to.. Baba dama maganar yarinyar nan ne, amaryan da nayi"
"Uhm bani sunanta"
"Raheemah"
"Shakka babu, ina jinka"
"Sab'ani muka d'an samu shine ta koma gidansu wai sai na bata takardanta"
Baban Tarauni yayi salati, yace "tun yaushe kenan?"
Yace "kusan sati d'aya kenan"
Yace "to ya kamata ace da yamma munje mun sami iyayenta"
Yace "to Baba, nasan yanzu ma k'ila mahaifinta ya dawo daga tafiyarsa"
Baban Tarauni yace "to ka shirya muje ayi magana, idan na ka basu hakuri ne sai ka basu, idan na kashedi ne ma duk suyi maka, idan kuma d'iyarsu ce bata da gaskiya to sai nabi maka hakkinka d'ana"
Yace "to Baba. Nagode"
°°•°°
Abdul bai bar gidan Baban Tarauni ba har sai da akayi sallar la'asar, tare suka bar gidan zuwa gidansu Raheemah.
Babban sa'a suka ci da suka isa gidan, Dad na zaune a balcony din part dinsa bisa sun lounger yana dudduba recent news papers. Ko da suka karisa wurin sallama suka yi masa, yana mai cire gilashin fuskarsa ya amsa musu tareda ajiye jaridar dake hannuwanshi. Ya tashi ya shiga dasu cikin part dinsa, yana mai fara'a suka gaisa cikin girma da arziki. Abdul dai na daga kan rug a zaune. Baban Tarauni yace "dama magana ne tafe da mu, game da 'yar wurinka Raheemah"
Abba yace "eh ina ji"
Baban Tarauni ya numfasa, yace "to, mun dai zo bada hakuri ne, saboda yarinyar gaba ki d'aya ta bijire nasan duk yadda akayi ba k'aramin b'ata mata rai yayi ba tunda naga haka"
Dad yace "ina zuwa"
Dama already Raheemah ta same shi ta fad'a mishi tsakanin k'arya da gaskiya kuma ya hau ya zauna. Wayarsa ya d'aga ya kira Raheemah yace ta same shi a parlournshi yana jiranta. Ko good ten minutes ba ayi ba sai gata ta shigo da sallamarta zik'au zik'au jikinta ko mayafi babu.
A gefen Dad ta zauna, da k'yar ta iya gaishe da Baban Tarauni tana cin d'aci. A kaikaice ya amsa mata tareda girgiza Kansa, Allah ya taimaketa bai yi mata dogon sharhi ba don shi mutum ne da baya gani ya k'yale. Cikin shagwaba shagwaba tace "Dad gani"
Yace "ai na ganki yar Daddy, bakinki ne suka zo shine nace ki zo ayi magana a gabansu"
Sitting position dinsa ya gyara, yace "my dear son in law"
Abdul ya d'ago da kanshi tareda fad'in "na'am Baba"
Yace "this is a free world, kana ji na? Bazan iya amfani da aure a matsayin weapon din da zan kuntata ma 'yata ba, ban yi mata dole akan aurenta ba don haka bazan mata dole ta cigaba da zama ba. So for now, she's the one who have a say not me, itace take da hakkin yi maka magana ba ni ba..."
Ya mayar da dubanshi ga Raheemah dake zaune a gefenshi tayi lamo cikin seater, yace "har Daddy"
Ta amsa da "na'am Daddy"
Yace "spit it out, kina son cigaba da zama da mijinki ko kuwa?"
Ta d'an turo baki irin na shagwaba tace "Dad kawai na bani takardata"
Gaban Abdul sai da ya fad'i, ya k'ura mata idanu yana kallonta. Baban Tarauni yace "amma 'yar nan bana tunanin saki shine sulhu"
Banza tayi mishi irin ga d'an iska yana magana.
Dad da kanshi ya tashi yaje ya samo pen da paper ya dawo ya zauna. Yace wa Raheemah "kin tabbata sakin yafi miki?"
Ta girgiza kai alamar eh, a ranta tana jin dadin ganin tashin hankalin Abdul.
Dad ya dubi Abdul yace "son in law amsa nan"
Ya fad'a yana mik'a masa pen da paper'n. Abdul ya kalli Raheemah dake zaune tana karkad'e k'afa yace "Raheemah divorce isn't the solution... Think about our unburn child"
Ware idanu tayi ta kalleshi, tace "you don't have anything of such nature with me, cikina ya fita"
Kanshi yaji ya d'aure masa, "so women are devils"
Saboda tashin hankali da mamaki bai iya ce mata komai ba, ya kuma kasa amsan paper'n daga hannun Dad, cikin saurin baki Dad yace "my friend amsa ka rubuta mata"
Abdul ya d'aga kai ya kalli Baban Tarauni da rinannun idanuwansa. Baban Tarauni yace "rubuta mata saki d'aya ka tashi mu tafi"
Zai yi magana ya katse shi "rubuta nace"
Jiki a sanyaye Abdul ya rubuta mata saki d'aya ya mik'ama Dad, ko karantawa bai yi ba yayi handing takardan wa Raheemah, ta amsa ta fice daga parlour'n, suma su Baban Tarauni suka yi masa sallama sannan suka fita.
D'akinta ta wuce kai tsaye bata ko shiga d'akin Mom ba. A drawer ta saka takardan sannan ta koma kan gado ta cigaba da sha'anin rayuwarta, it's high time ma ace ta nemi aikin yi ta rage zafi duk da ba abinda ta nema ta rasa a rayuwarta.
Shi kuwa Abdul tun yana takaici har sai da yaji zafin rasa babynshi da yayi. A take wani bakin ciki ya taso ya tokare mishi makogoro. Baban Tarauni kuwa ya tsine mata yafi so one five kamin su isa gidanshi, gashi da baiwar mita. 30mins drive ne zuwa gidanshi amma tunda suka fito gidan yake abu d'aya har suka isa gidanshi. Abdul yayi masa godiya sannan ya ja motarsa zuwa gida rai a jagule.
Gidan Umma ya wuce kai tsaye, Inteesar kadai ya tarar a parlour, ko sallama ma bai iyayi ba saboda k'unar rai, yace "ke Umma fa?"
Tace "bata nan, ta shiga makwabta amma ta kusa dawowa tunda ta d'an jima da fita"
Yace "ita kuma Jaleelah fa?"
Tace "tana bacci"
Cikin fad'a yace mata "je ki tashe ta, ana gab da kiran sallar magrib ne take bacci"
Babu shiri ta tashi ta shiga d'akin ta tashe ta. Ita kuwa saboda kasala ko fitowa bata iya yi ba tayi zamanta a cikin d'akin. Bayan ta wartsake ta shiga toilet ta kama ruwa sannan ta d'auro alwala ta gabatar da sallar magrib a zaune kamar yadda take yi, saboda cikinta yayi girma da yawa.
A nan ta cigaba da zama har akayi sallar isha'i itama ta gabatar da nata tayi addu'o'inta sannan ta yunkura ta fito daga d'akin zuwa main parlour, shima saboda ta jiyo muryar Umma ne da Abdul. Da kyar take tafiya saboda kafafuwanta da suka rike mata da bayanta dake yi mata ciwo. Ta zauna a kan kujera tare da yin basmala, Umma ta dube ta tace "sannu"
Murmushi ta sakar mata ba tareda ta iya amsa sannun ba. Abdul ya dubeta yace "tashi mu wuce"
Tace "ka bar ni a nan kawai"
Kadan ne kawai na daga b'acin ranshi ya sauka, cikin zafi da d'aga murya yace "ina wasa dake ne? Tashi ki wuce"
Jikinta har rawa yake yi ta mik'e, Umma tace "haba D'an Alhaji, wani irin abu ne haka?"
Yace "to Umma ya take so nayi mata? Ta tashi mu tafi tana fad'a min a nan zata zauna"
Umma sai mamakin fad'arshi take yi, it's unlike him, he wasn't his normal self shiyasa ma bata ja da nisa ba tacewa Jaleelah ta tashi su tafi ranan Monday da yamma ko da rana zata zo ta d'auketa su dawo gida. Hakanan ta bishi suka tafi gidan ba don ta so ba.
"Women are devils!! This was how my first wife attempted to ruin me. Itama ta so ace ta cire cikinta.. Don ma Allah ya sa mai tsawancin kwana ne da tuni ta kashe shi"
Irin abubuwan da ya dinga sakawa a ranshi kenan har suka isa gida. Tun da ta shiga motar tayi fuskarta tausayi, daga ita har shi babu wanda yace ko uffan har suka isa gida.
Bai ko saurareta ba haka ya wuce ta bayan ya fito daga motar ya shige cikin gidan. Tafi minti biyar tana zaune a cikin motar sannan daga baya ta tashi ta fita tana tafiya da k'yar da k'yar ta shige ciki itama.
Bedroom ta wuce kai tsaye don gudun kar ta tsaya hutun jaki da kaya. Taga baya nan a ciki. Tayi ta zama tana barbaza idanuwa taga ta inda zai b'ullo amma babu shi babu alamanshi har tayi kusan 30mins da shiga d'akin. Hakan yasa tayi deciding ta tashi taje ta lalubo shi da kanta saboda tana jin tsoron kwana ita d'aya a d'akin. Bedroom din dake facing nata ta bud'e ta shiga da sallamarta, nan ta tarar dashi a zaune ya tallafo kanshi da hannayenshi biyu, sanye yake da trouser da white singlet, tana tafiya da zummar karisawa kusa da shi ya d'ago da rinannun idanusanshi suka yi four eyes. Wani mugun kallo yayi mata sannan ya daka mata tsawa "what the hell are you looking for here!?"
Rudewa tayi ta kasa magana, shima daya ga haka cikin fad'a yace mata "get out"
Kamar tana jira ya fad'i haka tayi gaggawar ficewa daga d'akin ta koma usual bedroom din da suke kwana.
Tun kamin ta karisa kan gadon ta fashe da kuka har ta isa ta kwanta. Kukanta taci ma ishi na fin two hours har sai da bacci ya sace ta.
Shi kuwa Abdul yadda yaga dare haka ya ga rana. Yayi bak'in cikin asaran babynsu da Raheemah ta ja wo. Kusan kudirinsu daya da Jaleelah sai dai ita tayi succeeding ita kuma Jaleelah bata yi succeeding ba. Saboda itama Jaleelahr ta so tayi aborting baby dinsu, amma bata sami nasara ba, da kuma sakin, shima don dai bata samu nasara bane.
1am Raheemah ta farka daga bacci, fitsarin da ya matse ta ya tashe ta. Bayan ta shiga toilet ta gabatar da uzurinta ta dawo bakin gado ta zauna, sai ta nemi baccin dake idanuwanta ta rasa. Take ta mik'ar da hannunta ya isa saitin drawer'n da ta saka takardar da Abdul ya rubuta mata ta ciro ta fara karanta. Shakka babu gashi nan saki d'aya ne ya rubuta da manyan bak'i, kamar lokacin taga takardar sai ta fara karantawa tiryan tiryan, a daren ta karanta takardan yafi cikin carbi.
Join our Facebook group *Sisters Nigeria*
Sisters only please🙏🙏
Lots of love💋💞
⚜Mijin Jaleelah⚜
58______59
By Linah Shams✍🏼
*I'm sorry for taking long. Sweet mother suddenly fell ill. So I was the one to take care of the home as the eldest daughter. It wasn't easy though to be a Mom. My salutations and sincere regards to all mothers, I see your struggles. But alhamdulillah, she's gotten better*
🙏🏼🙏🏼
Washe gari da safe da kyar Jaleelah ta iya tashi tayi sallah, saboda kanta dake mata ciwo da kuma body weakness daya saukan Mata, ga idanuwanta were red and swollen. Wayarta dake kan dressing mirror take ta so ta tashi ta dauko, amma ta tashin ma ya zama mata aiki da ta kira Inteesar ta zo ta had'a mata breakfast. Har 8am tayi bata iya tashi ba sai to 9, kuma har lokacin Abdul bai shigo inda take ba.
Da kyar take tafiya ta fito sitting room zuwa kitchen ko zata samu daman iya sarrafa wani abun ta ci, don ta fara jin yunwa. A nan taga Abdul a zaune yana shan tea, suka had'a ido ta kawar da kanta zata wuce shi ya kira sunanta, bata amsa ba ta waiga ta kalle shi, yace "come over", ba musu ta karisa inda yake ta tsaya mishi a ka, yace "sit mana, kin wani tsaya min a ka", ta zauna a gefenshi, mutuncinshi d'aya cikinta ya tsufa kuma tana ganin rasuwa zata yi idan ta zo haihuwa da sai ta tsulala mishi rashin mutunci, shima ai yasan halinta.
Kura mata idanu yayi, har sai da ta kare ta fara turo mishi baki, yace "mene ne haka kuma?"
Banza tayi mishi, ya shafa kumatunta yace "what happened to your eyes baby?"
A ranta tace "bawan Allahn nan ya raina ni"
Tace "kai ka sani kuka, you picked me up from my mother's place, ka kawo ni nan sannan ka wulakantani, meya sa baka barni a wurinta ba?"
Kwabe fuska yayi yace "to masu mama... Amma dagaske kuka kika yi da yawa haka? Your eyes are puffy"
Tace "you can see for your self, you made me cry last night, kasan ina jin tsoro you left me to sleep alone"
Light hug ya bata, yace "I'm so sorry love. I wasn't my self last night"
Tace "and... Meyasa ba ka zo ka dubani da safe ba, kasan larurata"
Cikin kunnenta yayi mata rad'a Yace "kunya naji, I know I had done you wrong"
Tace "but why?"
Ya numfasa sannan yace "I was upset, jiya naje gidansu Raheemah, and guess what? We got divorced!"
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'iun, but I thought I begged you not to dear", ta fad'a muryarta a raunane, yace "ya zanyi Jaleelah? Tace saki take so kuma babanta yace dole sai na bata takardanta tunda bata son zama dani"
Kwafa tayi tace "to Allah ya daidaita tsakaninku, ni yunwa nake ji"
Yace "to Ameerah, lemme go get something for you, Princess dina ma na san tana jin yunwa by now"
Daga haka ya tashi ya wuce zuwa kitchen domin samo mata abinda zata ci.
••°••
Bayan sun kammala breakfast a tsakiyar falo mai aikinsu ta zo ta kwashe abubuwan da sukayi amfani da su ta wuce kitchen. Kuhaylah da Hambali suka tashi suka wuce part din Daddy suna tafe suna hira. Mom ta dubi Raheemah tace "wai shi mijinki bashi da hankali ne? Ko jira yake yi sai mun neme shi"
Tace "ahh ai jiya ya zo"
Mom tace "ohkayyy.... Shine baki sanar dani ba, to ki kwashe kayanki ki koma can"
Tace "a'a Mom takardan saki na ya zo ya rubuta min"
Sai da Mom ta dafe kirji, tace "saki! Saki fa kika ce Baby"
Tace "eh Mom, to na gaji da zama da shi, shine kawai da ya zo bada hakuri na cewa Dad kawai takardata nake so"
Ran Mom idan yayi dubu ya b'aci, tace "Raheemah ashe ke dabba ce ban sani ba? Baki da hankali dama? Da kuruciyarki ne kika nemi saki a wurin mijinki? Duk yadda na mara miki baya kika auri yaron nan banyi miki gwaninta ba ashe? Amma ai laifin sakaran ubanki ne, sai ki dawo gida ki cigaba da zama mu dinga musayar wurin zama, idan na cire katare na a nan kema sai ki sa, idan kema kika cire na sa, ba haka kike so ba? Mara mutunci"
Tace "Mom I just want to teach him some lessons, nasan zamu shirya"
Takaici ma ya hana Mom ta zage ta sai ta tashi ta bar mata falon, ita kuwa hamshakiyar ko a jikinta.
Sai ranan sunday da yamma da Abdul zai koma Kaduna sannan ya sanar da Umma rabuwar aurenshi da Raheemah. Komai game da faruwan al'amarin ya labarta mata, ko kadan bata ji dadi ba amma tana fata su daidaita tsakaninsu kamin wani lokaci tunda saki d'aya aka yi.
Ranan tuesday da hantsi yana zaune a office dinsa lokacin he was less busy ya d'aga waya ya kira Raheemah, ko da taga call d'in farinciki ne ya dabaibaiye zuciyarta, tasan sulhu zai nema. Har da takwarkwasa a muryarta yayinda take yi mishi magana, yadda ya gaishe ta zaka aza babba ya gaisar, sannan yace "dama na kira ki ne nace it's high time you come and pack up your belongings"
Sai taji maganar wani gingingin, tace "amma idda na bai k'are ba"
Yace "eh na sani, kuma kema kin san ni ba jahili bane, a gidan dana sake ki a can zaki kammala iddanki"
Tace "oh this is absurd, kasan akwai sauran igiya biyu a tsakaninmu kuwa?"
Yace "I know morethan you do, amma idan kina so na sa almakashi na yanke su yanzu zan yi, it's as easy as that, ai mai wuyar shine kawai a fara"
Tace "Abdul this isn't what I mean, I mean I'm still your wife"
Yace "hajiya you are mistaken, I have only one wife, yaushe zaki zo ki kwashe kayanki"
Tace "Abdul look here, I'm still your wife", ta fad'a cikin muryar tausayi. Yace "I don't understand you again, me kike so ki fada min? That I'm a knuckledagger?"
Tace "God forbid. I mean I was just upset with you, amma ai komai ya riga ya wuce yanzu, please I'm sorry, I beg your pardon"
Yace "to shikenan, na hakura, zan mayar dake but under one condition"
Cikin saurin baki tace "baby say it"
Yace "ki dawo min da cikinki, cikin babyn mu, nasan zubarwa kika yi"
Shiru tayi for some seconds tana tunani, yace "something you can never do? To haka zalika nima, I can never take you back unless you'll come back with the pregnancy, kin gani yanzu kanki kika yiwa asara, bani ba, kamin kiyi cikinnan mata ta tayi, and insha Allah sai ta haifa min rayayyun babies not even a single baby"
Yayi disconnecting call d'in. Kuka ne kawai bata yi ba, Mom dake tsaye a kofar d'akinta ba tareda ta sani ba tace "ai kinyi asaran miji, dama kije ki dauko Ablah ko ki aika a dauko ta"
Ta juya tayi ficewarta.
The next day Raheemah ta shirya da sassafe ta wuce Kaduna. A office din AbdulHakam tayi branch, nan ta dinga bashi hakuri amma yaki yarda, ya farfada mata maganganu masu zafi fiye da zafin da yaji lokacin da ya samu labarin fitan cikinta. Hakan yasa ta zuciyya taje ta sami motar da zai kwashe mata kayanta. kawarta Shema'u, matar gidan da ta kai Ablah ita kadai ta tayata suka kwashe kayan d'akin tareda taimakon mai motan da karen motansa guda biyu suka kwashe kayanta kaf, duk wani abu da tasan mallakinta ne sai da ta d'auka, hatta tsintsiya bata bari ba. Kamin sallar la'asar sun gama kwashe komai, Shema'u kadai tayiwa sallama ta tafi.
Ko da Abdul ya dawo yaga haka farinciki yayi, a ranan bai kwana ba sai da ya tabbatar ya canjawa duk wani kofa da ke gidan key.
Da daddare Raheemah ta kasa sukuni, ta rasa Wanda zata tara ta fadawa damuwarta taji sanyi. Sai kawai ta wuce gidan Rabab. Har kuka sai da tayi yayinda take bata labari, Rabab dai baki tayi ta bata sannan ta nuna mata kuskurenta, daga baya ta nuna mata ya kamata ta tafi gida saboda mijinta yana ciki yana jiranta, sai taji wani kululu ya tsaya mata a wuya, ba yadda ta iya hakanan ta tashi ta wuce gida.
Mommy kuwa tun bayan da suka yi waya da Jaleelah duk ta bi ta damu, sai tana ganin kamar dagaske ne daughter dinta zata iya mutuwa. Hakan yasa ranan wednesday suka dunguma suka wuce Kano, Daddy da kanshi ya kaisu bayan ya dauki excuse daga wurin aikinshi. Ai kam sai da Umma ta kira Abba ya dawo daga kasuwa saboda yaga manyan baki. Mommy kuwa sai da tayi mamakin girman cikin Jaleelah.
A main parlour dukansu suka had'u a ka gama gaisawa daga bisani Abba da Daddy, da Afdal, da Murayyan suka koma part din Abba. Su kuma su Mommy suka zauna wurin Umma, Yaseen yaki bin Daddy. Ana haka sai ga Aunty Safiyya ta zo ita da Sajida, later on sai ga Mardiyya itama ta zo.
1pm nayi Aunty Safiyya ta roki Izz yaje ya kwaso musu yaransu daga schl ya sauke su gidansu Umma, sai gidan ya koma tamkar ana biki. Jaleelah ba karamin dadi taji ba data gansu, tana rakube a gefen Umma.
Suna tsaka da hirarrakinsu ta tashi zuwa bedroom din Umma don dauro alwala tayi sallah, tana shiga wayarta na fara ringing, ta san ba kowa bane face mijinta, da fara'a ta dauka suka gaisa, ya tambayeta "what's popping my love?"
Cikin murmushi tace "you are missing something here, kowa yana gida yau, harda yaya Khaleel, soon kuma mijin Aunty Mardiyya da Aunty Safiyya zasu zo, Izz yana gida, Abba ma haka, and most of all, Mommy, Daddy, Hadiyya, Murayyan, Yaseen, da Afdal duk suna nan"
Cike da mamaki yace "gaskiya I'm missing something great.. Yaushe su Mommy suka zo?"
Tace "sun dade fa sweetheart, I wish kana nan, kaga ga Umma ga Abba, ga Mommy ga Daddy, ga Yaya Khaleel ga Sajida, ga Aunty Safiyya da Nasir dinta, ga Aunty Mardiyya itama da Awwal dinta.. Kaga da sai ace ga Jaleelah ga Mijin Jaleelah"
Murmushi yayi yace "see your mouth.. Ga AbdulHakam dai da matar AbdulHakam"
Tace "it's still thesame, Ameer marana fa yana ciwo"
Yace "subhanallah, kin fadawa Umma?"
Tace "a'a"
Yace "please do tell her kin ji baby na? Pls"
Tace "to dear. Later".
15days later
Jaleelah ta tashi da labour pains. Tun tana ganin kamar zata iya daurewa har sai da ciwon ya fara cin karfinta. Taje ta sami Umma ta fada mata, then abin ya fara mata yawa. Umma bata yi k'asa a gwiwa ba suka zarce Sahara Hospital.
After two hours. It was a great fortune, ta haifi santaleliyar yarinyarta da kanta, after twenty five minutes ta sake sumbulo santalen baby, this time around it is a boy. Masha Allah
Sai dai fa ta jigata sosai ba kadan ba, hakan yasa aka shigar da ita ICU. Ba karamin farinciki Umma tayi ba, gaba d'aya ta kasa rufe bakinta yan asibitin sai barka suke yi mata. Nan ta Kira Inteesar ta shaida mata saboda tana so ta kawo musu ruwan zafi. Inteesar din ce ta kira Abdul take shaida mishi, bai boye farincikinshi ba, ranan ya d'auki two weeks leave daga office dinsu don a ranan ya wuce Kano.
Sai lokacin Jaleelah ta tabbatar danginsu Abdul suna da yawa, kwana uku suka yi a asibitin amma mutane sai bulbulowa suke yi from both sides. Ko baccin arziki ta kasa samu tunda ta haihu saboda yawan mutanez babies din ma basu zama wurinta.
Abdul kuwa ji yayi kamar ya kori mutanen saboda he wanted to be by her side. Farin cikinsa baya boyuwa, kullum cikin bayyana hakoransa yake, so it wasn't only a princess, akwai Prince shima Ashe ya boye ne.
Dangin Mommy da Daddy da yawa suka je barkan, haka ma ranan suna sun sami halarta. Aka sanyawa baby girl sunan Umma da Mommy, Zainaba, ana kiranta Farha sai namijin Al'amin.
Bayan anyi suna sisters din Mommy suka yi ta expecting dawowar Jaleelah amma Mommy tace ba zata dawo ba, a can zata zauna wurin Maman ta.
After a month ASUU suka janye strike, Jaleelah da Inteesar suka je suka yi registration da clearance. Bayan Jaleelah ta cika forty days tayi yawon arba'in a dangin mijinta for seven days, tare da Inteesar suke zuwa duk inda zata saboda ta taimake ta da daukan baby, sannan Umma ta mayar da ita Kaduna da kanta, dama already tayi repacking zuwa Kaduna.
Nan ma seven days tayi tana zagaye dangi, duk inda zata da Hadiyya suke tafiya, ita ta goya Farha Jaleelah kuma ta goya Al'amin. Bayan seven days din ta sake komawa Yarwa Close da zama for the second time. Sai da Mommy ta sama mata dattijuwa mai raino kamin ta koma, sai suka koma gidan tare da matar.
Duk sanda Abdul yake gida baya yarda yaran su zauna wurin ko Jaleelah bare mai rainonsu, sai ya dauke su ya kwantar dasu a kan gado, idan ya gaji da daukan d'aya sai ya ajiye d'ayan ya d'auki dan uwansa.
Sometimes sai dai Jaleelah ta zauna tayi ta kallonsa yana raino, sai da idan sun yi kuka yace ta dauke su.
Raheemah kam babu irin magiyar da bata yiwa Abdul ba akan yayi hakuri ya mayar da ita, ita ta yarda ma zata zauna a Kano ya dunga zuwa weekly, zai ma iya zuwa ko monthly ne if he so wish amma yace mata aurensu ya riga da ya zama tarihi, don ta taba tsammanin hakan daga gareta ba, da ko a mafarki yaga scene din da mahaifinta ya umurce shi da ya sakar mishi diyarsa da yana tashi sai yayi sadaka, sai gashi in reality hakan ta faru.
After 4months
Lokacin Farha da Al'amin sun d'an fara wayau. Jaleelah kuma tana zuwa schl dinta lami lafiya, Abdul ya kama mata single bedroom apartment off campus saboda d'an tazarar da suke da shi. Idan karatu yayi mata sauki sai ta koma gida.
She was performing excellently, Haka ma Inteesar, waccs yanzu a gidansu an san da Mo'az, farincikinta ya cika. In less than three months time za ayi bikin aurensu.
Tun Raheemah na neman Abdul har ta hakura ta cire rai da shi, Mom kam ko bi takanta bata yi, takan Kuhaylah kadai take yi wacce ake ta shirye shirye shiryen aurenta.
There was progress in everybody's life... 💡
⚜Mijin Jaleelah⚜
End.......
By Linah Shams✍🏼
*Today I'll miss you guys. I'll miss the post and the comments. However, I'm grateful to you, to write isn't as easy as that and to find time to read isn't also. ILYSM💖. Thanks for been loyal*
10years later.
Abuja, Nigeria.
11am
Abdul ne zaune da beautiful wives dinsa biyu, Jaleelah da Hafsat round a garden table a Zürich resort. Discussing suke tayi akan topic din "domestic violence", hankalinsu gaba suka mika ga hiran Wanda har mantar da su seven kids dinsu yayi. Kowannensu sai fad'in albarkacin bakinsa yake yi.
Tun daga nesa suka jiyo muryar Farha tana gudu tana fad'in "Mamma, Ummi", hakan ya katsar musu da hiran suka mayar da dubansu gareta tareda jiran isowarta, ta kariso tana haki, Abdul yace "Umma na lafiya?"
Numfashinta na hawa yana sauka tace "snake yayi biting Shukra"
A zabure Hafsat ta tashi, hankali a tashe tace "tana ina?"
Muryarta kamar zata fashe da kuka tace "tana can baya" tayi pointing hanyar da yatsar manuniyarta. Abdul da Jaleelah da suke tsaye suma suka bita a baya yayinda ta shiga gaba don kaisu inda incident din ya auku. Hafsat duk ta fisu shiga tashin hankali, itace kan gaba har suka isa wurin, amma babu shukra. Wata matashiyar mace ce tayi saurin isowa inda suke, tace "kune iyayenta?"
Da sauri Hafsat tace "eh pls tana ina ne?"
Murmushi ta sakar mata mai bada hope, tace "calm your mind, ko mai zai zo da sauki insha Allahu, Abban Yasmin yaje kaita asibiti"
A daburce tace "ina? Wane asibiti?"
Jaleelah uwar 'yan ma kasa cewa komai tayi, matar tace "bari na kira shi"
Nan ta ciro wayarta ta kira shi, bugu daya biyu ya dauka ta tambayeshi sunan asibitin, yace mata suna Royal Empire Clinic. Tana rufe baki Hafsat tace "Abba Farha pls to Ku zo mu tafi"
Abdul ya wuce sannan suka bishi a baya, itama matar ta bisu a baya. Amma Sai da Jaleelah ta koma ta kira yaransu guda biyar sannan ta je wurin motar. Already Hafsat ta shiga backseat ita da Farha da matar sai yaronta da baby Yasmin. Jaleelah ta shiga front seat. Al'Àmin, Amal, Abbati, Kalthoum, da Batool suka shige backseats.
Suna isa asibitin suka ci karo da mutumin a parking lot na asibitin, shima ya fito da niyyar komawa park din ne ya sanarwa iyayen yarinyar she's revived. Amma anyi admitting dinta a asibitin na twenty four hours for proper health check up.
Dukansu suka fito daga motar, matarsa tayi saurin karisawa inda yake "ga iyayenta"
Ya waiga domin ganinsu, kadan ya rage numfashinsa ya dauke saboda tsabaragin mamaki, instead of ya fad'a musu condition din yarinyarsu sai shiru kuma, Hafsat tace "Malam speak up mana, tana ina?"
Ko kallonta bai iya yi ba, Abdul kam kashe sa yayi da idanu zuciyarsa na tafasa ganin yadda ya kashe masa mata da idanu kuma itama kallonsa take yi. A hankali ya furta sunanta "Jaleelah???"
Matarsa was a little shocked, saboda sunan Yasmin kenan Jaleelah, itama ta kira sunanshi "Khaleefah?"
Cikin fushi Abdul yace "what the hell do you think you two are doing?"
Jaleelah ta daga kai ta kalle shi, yanayin bacin ran dake idanuwansa ya tabbatar mata da cewa yanzu wasn't the right time to speak, da Sauri ta saisaita kwakwalwarta tace "dan Allah lead us to"
Dukansu suka bi bayansa, amma banda kids da Abdul, wurin doctor suka fara zuwa yayi musu bayani sannan daga baya suka wuce d'akin da akayi admitting din Shukra. Alhamdulillah, ta samu proper medication. Hafsat ta rungumeta tana fad'in "babyn Ummi"
Tayi murmushi tace "Ummi na"
Tace "Shukran Ummi"
Ita kam Jaleelah bata iya cewa komai ba don ta tsargu da yadda Abdul yayi fushi, tace "Shukran Ummi kinji sauki?"
Ta gyada kai tareda fadin "eh Mamma"
Daga haka Jaleelah ta fice zuwa haraban hospital din zuwa wurin Abdul. Yana zaune a cikin mota ya had'a kai da steerwheel, cikin sassauta murya tace "Ameer"
D'agowa yayi da rinannun idanuwansa suka yi ido hudu, ya watsa mata wani irin mugun kallo, ta bud'e baki zata yi magana yace "don't dare!"
Haka nan ta b'ame bakinta tayi shiru sai ga Hafsat, bata ko kalleshi ba tace "Abban Farha ka zo ka duba Shukra, tace she wants to see you"
Kicikicin bude mota ta fara hakan yasa Jaleelah tayi gaggawar matsa masa. Tana kallonsu suka koma cikin asibitin ita kuma ta shige backseat wurin yara. Nan ta k'ara kallon yaron Khaleefah, sai yanzu ta ga kamanninshi da mahaifinshi, murmushi tayi, a ranta tana ayyanawa da yanzu itace mahaifiyarsa amma Allah bai nufa ba, tace "boy ya sunanka?"
Yaron mai kimanin shekaru shidda yace "Al-qasim"
Tace "masha Allah", sai ta zuba musu idanu tana kallon yadda suke surutu dukansu musanman first born din Hafsat, Batool.
Bayan kusan 20mins sai ga Abdul ya fito, Khaleefah da matarsa na biye dashi a baya, ko kallonsu bai yi ba ya shiga motar zai wuce, Jaleelah tace "a'a ga Al-qasim"
Sai ya dakata ya juya baya yana kallonsu, ko ba a fada masa ba ya San ko dan gidan waye, bai ce komai ba Jaleelah ta bude motar ta fita da shi, har gaban iyayenshi ta kai shi, sannan tace "mun gode sosai fa Alhaji Khaleefah"
Murmushi yayi bai iya ce mata komai ba, his heart was breaking, matarsa ce tace "a'a ba komai, idan ba zaki damu ba to ki bani phone number dinki, sai na kira na ji ya jikin Shukran". Jaleelah ta amsa wayarta ta sa mata numbern ta sannan suka yi sallama.
Hafsat ce zata kwana da Shukra a asibiti.
Bayan sun koma gida duka yaran suka taru a d'akinsu Farha, harda Al'amin. Ko bi takansu Jaleelah bata yi ba tabi bayan Abdul zuwa part dinsa, yana isa tsakiyar parlour itama ta shiga, yana waigowa ya ganta ransa ya k'ara b'aci, bata gai ka cewa wani abu ba cikin tsawa yace mata "get out of my sight"
Tace "please...."
Kamin ta fad'i next word yace "I don't want to see this your ugly face, out of my sight"
Ji tayi kamar ta fashe da kuka. Hakanan ta tafi part dinta ranta na k'una. Kai tsaye bedroom ta shige idanuwanta na zubar da kwalla.
Washe gari aka sallami Shukra daga hospital. A part d'in Hafsat ta sauka, ganin haka yasa sauran yaran suma suka koma can banda Farha da Al'amin, musanman Farha mai kawaziccin uwanta.
Tana ta monitoring moves din Jaleelah saboda mood dinta ya sauya, har sai da ta tambayeta, tace mata bata da lafiya ne, hakan ya kara hanata fita lokacinda Hafsat suka dawo daga asibiti.
The next day that happened to be Monday. Har office Khaleefah ya je ya sami Abdul, sosai ya bashi hakurin incidence din da ya faru. Sai da ya tabbatar ya hakura sannan ya tafi tareda yi masa sallama. Sai a sannan zuciyarsa ta dan yi sanyi don ko bi takanta ma baya yi tun ranar Saturday.
Ranan kam da ya koma gida ranan girkin Jaleelah ne. Bayan yayi wanka ya yi changing ya dauki wayarsa ya kira ta, yace mata ta a kawo mishi abinci. Suna gama wayar ta harhad'a komai ta sa Farha ta d'auka ta kai masa, da sallama ta Shiga parlourn sannan ta gaishe shi. Kan center table ta ajiye tray din sannan ta zauna a kasa kusa da kafafuwanshi, yace "Umma na, my beautiful princess"
Tace "na'am"
Yace "me kike so? Wani abu aka yi miki?"
Tace "a'a Mamma ce bata da lafiya kuma tak'i fadawa kowa"
Yace "Subhanallahi, since when?"
Tace "Saturday"
Yace "to zan kai ta asibiti, kin ji?", yasan how much she loves her Mom, murmushi tayi tace "to Abba, thank you"
Da gudu ta fita tana yi tana tsalle har ta isa part din Mamanta. A parlour ta tsaye bata kai ga karisawa cikin bedroom ba.
Bayan fitarta Abdul ya d'aga waya ya kira Jaleelah, bai jira tayi magana ba yace ta zo yana son ganinta kamin ta bashi response yayi disconnecting call d'in. Bakar after dress ta d'auka ta sa ta fita zuwa part dinsa. Still yana zaune a parlour amma ko taba abincin bai yi ba, daga nesa da shi ta tsaya tareda folding arms dinta, tace "gani"
Cije lebenshi yayi saboda haushi, yace "wai ke Jaleelah when will you grow up?"
Sunkuyar da kanta tayi ba tace masa komai ba, yayi shrug yace "you see... Kuma nayi miki magana still kin cigaba da tsayuwa a nan"
Ta d'ago da kanta ta kalle shi, tace "kar ka damu, say what you want to say hakan ma yayi"
Ya jingina bayan shi da jikin kujera yace "Me kike so ki mayar dani?"
A tak'aice ta d'an kalle shi, tace "I'll forever be loving your happiness and what you love, shiyasa I don't want to scare you off with my ugly face!"
Sai yanzu ya tuna ma ya fada mata haka, yar murmushi yayi yace "it isn't the right time to discuss that, you're a beautiful Queen, the mother of my beautiful princess, ki zo magana zan yi miki", bata sake cewa komai ba ta wuce ta zauna a kan one seater, ta kawar da kanta gefe, sai da yayi forcing dinta ta dawo ta zauna a gefenshi. Ya kira sunanta ta amsa mishi, yace "is it true baki da lafiya?"
Tace "a'a"
Yace "okay. D'azu saurayinki ya zo ya same ni"
A razane ta juya ta kalle shi, b'acin rai ne bayyane k'arara a cikin idanuwanta, tace "saurayi...... Ni?"
Had'e giran sama yayi da na k'asa yace "eh", kasa bashi amsa tayi sai ta fara hawaye, tace "me ya sa? Da aurenka a kaina ne kake fada min saurayi na? Which boyfriend do I have after you?"
Yace "the one you starred at before me"
B'akin ciki ne ya cika mata zuciya, tace "and what do you think I was doing?"
Yace "kin ga old bear"
Shiru tayi tana kallonshi na kusan 50secs, tace "are you running suspicious of me?"
Cikin saurin baki yace "what nonsense is that?"
Tace "forget the nonsensitive, ba a aure da zargi"
Gradually ranshi ya fara b'aci, ya juyo da fuskarta ta kalleshi, yace "me ke damunki? Nine zan zarge ki?"
Hannunsa dake gefen fuskarta ta rik'e, cikin zafi tace "to me sunan abinda kayi yanzu? Tell me.. You couldn't even listen to me. For a mere mistake, I was surprised seeing him and him been the person that came to the aid of our daughter!! Why? Why? Why please! Meya sa zanyi abinda da ban yi shi ba till now that I'm a mother of five? Tell me for God's own sake, me na nema a rayuwata na rasa da zanbi mijin wata, when you're the man I love and will love beyond eternity.. Why Ameer..."
Ta karishe maganar tana hawaye, yayi hugging dinta yana kara jin sonta a cikin ranshi, a hankali ya dinga rad'a mata I love you a cikin left ear dinta har sai da tayi shiru.
Washe gari da safe Jaleelah ce zata yi dropping din yara a school kamin ta wuce wurin aikinta, da Hafsat zata kaisu amma ita motar ta ba mai hakan yasa Abdul ma zai kai ta wurin aiki. Bayan tayi parking yaran suka fara fita kowa rik'e da foodflask dinsa, sai dai twins set d'aya a ke had'a musu. Farha da Al'Àmin basket dinsu d'aya, Amal da Abbati ma a had'e, sai auta Shukra nata da ban. Kalthoum da Batool suma na su separately.
Shukra na fita ta fara ihu tana fad'in "Al-qasim! Al-qasim Thabit!!"
Hakan yasa Khaleefah dake kokarin fito dashi daga mota ya waiga, yaga Shukra ce, da gudu ta karisa wurinsu, Khaleefah yayi raking fingers dinsa a kanta, yace "Shukra"
Tace "uncle ina kwana", yayi murmushi, yana k'ara assuring kanshi this is his most loved girlfriend's child, yace "kina lafiya? Ya Mommy?"
Tare da pointing motarsu tace "gata can ai ma"
Lokacin ya gama gyarawa Al-qasim tie dinsa, yace "okay, to kuyi sauri Ku shiga school, ayi karatu da yawa ko?"
Shukra tace "to", tareda rike hannun Al-qasim suka shige cikin school.
A hankali Khaleefah ya taka har zuwa wurin Jaleelah, cikin fara'a suka gaisa, yace "Anjayjay"
Murmushi tayi tace "don't be crazy, Ni'imah ta gama da ni"
Yayi dariya yace "the talkative and bold girl kenan"
Ta yi dariya tace "Khaleefah!!"
Shima dariyar yayi, sannan ya tsagaita, at once mood dinsa ya koma serious one, yace "I never thought zan kara ganinki a rayuwata"
Tace "to gashi ka ganni"
Yace "you're now a mother of...?"
Tace "five!. Two pairs of twins and a single daughter. Zainab and Al'Àmin, Muhammad Ja'afar and Aisha, then Ameenah, Shukra kenan"
Yace "masha Allah.. Allah ya raya mana su a kan sunna, I am sure kinga namesake dinki ba? Yasmina"
She's surprised, tace "Yasmin? Jaleelah sunanta?"
Yana murmushi ya gyada mata kai, sad smile tayi tace "thank you"
Shima irin smile din yayi, yace "I've lose you to someone for my selfish behaviour, now my kids are someone's"
D'an murmushi tayi, tace "we are never meant to be together, we would have been. Haka Allah ya so and I'm sure it's the best for us, always trust Allah's decision"
Yace "sure.. Bari na barki ki tafi wurin aikinki, bye"
"Okay bye"
Nan suka yi taking separate ways dinsu. Bayan rabuwarsu Khaleefah had to weep, saboda yayi muguwar hasara, although yayi imani da maganganun data fad'a masa, hakan yasa ranshi yayi sanyi.
Days went by, gidan Abdul komai zam zam. Hafsat da Jaleelah suna zaune k'alau, kishin su tsabtatacce suke yi. Lokacinda Farha da Al'Àmin suke da four years Abdul ya auri Hafsat, suna da yara biyu, Kalthoum da Batool.
Bayan wani lokaci suka saba da Jameelah sosai, matar Khaleefah. Har wuni tana zuwa musu haka suma Hafsat da Jaleelah. Sai suka zama kamar family friends, sometimes duka gidan suke bari su je gidanta haka itama, ko park zasu tare suke zuwa, ko shopping da wasu wurare. A haka har coincidence yasa suka had'u da Raheemah, ashe kawar Jameelah ce na sosai. Ranan da suka had'u a gidan sun sha hira kamar me tareda tuna baya. Raheemah tayi aure abunta, tana zaune a Lagos da mijinta amma idan ta sami Hutu tana zuwa arewa, but suna da gida a Abuja. She's blessed with one child, Hauwa suna kiranta Jeddah. Gaba d'aya ta canja, duk wani d'agawarta ya kau, duk da mai mata take aure she's happily making it. Saboda dadin hira dukansu sai past 9pm suka bar gidan Khaleefah.
Ranan kam da suka koma gida instead of suyi shirin bacci, part din Abdul suka koma, a can suka dasa sabon hira, sai da Jaleelah ta bashi labarin Raheemah sannan ta ji dadi. Bayan sun gama hiransu Hafsat ta koma part dinta ta bar Abdul da Jaleelah a nan bayan sun gama magana akan tafiyarsu Kano karshen month din nan idan yara sun sami hutun school.
Alhamdulillah, a nan ne Al'kalami na ya gama taka iya rawar ganinsa. Fatana Allah ya yafe min kurakuren dana aikata a ciki. Wannan labarin is nothing but fiction sai kuma part of it life experience ne. Don nishad'i kawai na yi novel din nan ba wai don na ilmantar ba (me na sani a duniyar? I'm just nineteen years of age so wa zan zauna ina ba ilimi a novel)
Knowledge isn't one easy thing to find. A novel sai dai ka sha labarin life experience da za kayi learning life lessons. Idan ilimi kike so yar uwa ba zaki same shi a novel ba, kije ki zauna a aji ki samo ilimi, I thought komai don a birge miji ake yinsa? To believe in my words mijinki da kanshi zai girmamaki, bama shi kadai ba hatta danginshi da naki da mutanen unguwa. Though ko wane ilimin da nashi amfamin cos as I heard kamar ma akwai mijin da baya son karatun novel.
My everyday commentators ina godiya. Your names are in large numbers I for mention you guys, thanks a lot.
Masu addu'a ma duka na gode, I'm grateful.
I wholeheartedly devote this novel to the four girls close to my heart.
Fatima Sani Muhammad
Salaha Mahmoud
Assafiya Muhammad Tom
Bilkisu Adamu Gambo
You mean the world to me babes.
And My Zahraty, Zahra Baba Alkali, then the loyal sister Ya Meena, love you die.
Asma'u Wasagu, my history will never forget you, you're such a marvellous princess.
Girls like Maimunatu Haruna Limanci are always on my mind. ILYSM💋💋
My salutations to the writers I admire the most
Zuwairat Nuhu
Khaleesat Haiydar
Benaziratu Omar
Rufaida Omar
Batool Mamman.
Thanks all
Allah ya had'a fuskokinmu da alkhairi.
Ramadan Mubaraq in advance.. Ayi azumi lafiya.
Allah ya yarda damu da ibadunmu.
Taku har Kullum, Aishatu Falalu (linah).
Reach me on my Facebook handle @Aisha Abubakar Imam
Ashnaah9@gmail.com