.
Bata rufe baki ba Inno da ta shigo amsar sheda tayo nan da gudu kamar ta lashe kafafun su ta shiga gaishe su, "Ayo Hajja Barka dai" Hajiya tayi dariya dan dama sun saba da Inno akwai iya roko, Inno ta kalle Rahma dake a tsaye kamar ace As ta zura a guje, "Ke Wagga diya baki wuce gida ba?" "Yanzu zani Inna," Hajiyar ta ce "yawwa Inno wannan fa?" Tana nuna Rahma, Inno ta zungure baki, "Ke gata nan arniya ce ko Salla bata iya saida Dawuda ya koya mata, muma bamusan dangin ta ba, Dawuda yace cikin gona tai ya ganta kamar matatta, toh shine taji dadin zama taki fadin dangin ta." Inno ta k'are maganar tana afka ma Rahma harara, Cikin kulawa Hajiyar ta kalle ta, "am Inno kuje zuwa anjima kafin na wuce zan biyo ta gidan," Cikin jin dadi inno takara sadda kan ta,"toh Hajiya godiya muke Allah yakara arziki," "Ameen ameen"inji d'ayar Matar Inno taja hannun Rahma suka fice wajen, Acan gefe suka tarar da Dawuda yana jiran su, nan ya kwashi kayan su,suka kama hanya, "Inna me kuka yi aciki hala? Naga Ku dad'e," "Au Wagga yarinta suka tambayar asalin ta," Nan take Fuskar shi ta nuna alamun damuwa shi Kansan baisan dalilin faruwar hakan ba, Haka dai har suka Isa gida yayin da Inno gayamasa cewa su Hajiya Bilkisu zasu biyo ta nan, Ba Dawuda kadai ba ko Rahman haka kawai taji rayuwar ta ba dad'i, Bayan la'asar su Hajiya Bilkisu tare da kawar ta Hajiya Samee sai masu taya ta aiki Maza, a kofar gidan Inno sukayi Sallama, gidan ya sha share sai kyalli yakeyi, cikin dauki da Murna Inno ta tare su, Nan suka zauna akan tabarma shi kuwa Dawuda da ya kasa ya tsare yana tsaye a katangar Gidan,
.
Hajiya Bilkisu cikin kulawa tace,"Am Inno kikace wannan babu abinda take tunawa ko?" "Awo hwa Ranki shi dad'e haka tacce," Hajiya Bilkisu ta kalle Dawuda tace,"taji ciwo ne akai lokacin?" Dawuda ya amsa da "awo taji ciwo sosai sai da tayi kwana shida bata tashi ba," Hajiya Bilkisu ta girgiza kai tare da cewa,"da ta farka me ta fara ambata? Ko kun kaita asibiti?" Dawuda yace,"saida tayi kwana biyu bata magana daga bisani ta tambaye mu waye mu? A Ina take? " Hajiya Bilkisu ta ce, "in ba damuwa Dawuda da ita Ruken Ina so Ku biyo ni yanzu, in yaso sai idan kunga likita Ku dawo," Dawuda jin cewa dashi za'a tafi hakan yayi masa dadi duk da yana fargabar samun lafiyar Ruke, Haka suka dunguma suka bi Hajiya Bilkisu acikin tawagar ta. Hajiya Bilkisu it's kanta haka kawai taji tana son taimaka wa Ruke, bata san dalilin da yasa Yarinyar ta kwanta mata ba, Nan suka Sauka Birnin Gusau acikin Dare Sosai. **** Je kiga tashin hankali karara akan fuskar Fajir, so yake yasan irin Matakin da zai.dauka amma abin ya gagara hakan yasa ya dinga furta "innalillahi wa inna alaihir raji un," Da kyar ya samu Salama a ransa, bai tsaya ko Ina ba sai Fadar Sarki, nan take ya zube a gaban Father yana wani irin kuka mai tsuma zuciya, Da kyar aka lallab'a shi ya shiga shaida wa Sarki abinda kunnen sa suka jiyo Masa. Abinda ya faru kuwa shine, Daidai lokacin da zai fita da yake har yayi niyar yin bacci aka kira shi a waya cewa anga wata batattar yarinya yazo yagani ko itace dan kuwa ita duk ta kone a fuska abu mai wuya ne agano kamannin ta, Cikin sauri ya shirya Sashen Salma ya nufa dan ya shaida mata fitar, a hankali ya dinga jiyo kukan ta yayin da take magana cikin tsoro, "Aunty dan Allah ki koma wajen sa wallahi Ina tsoron a ganeta, so nake gaba d'aya tabar kasar nan taje can k'asar matalauta, ko kuma akashe ta ga baki d'aya," Shiru tayi na lokaci kafin tace,"hmmm Wallahi Aunty muddin Fajir ya tabbata ni nake zubar da ciki da gangan ko mame zai iya yi, kee bakiga da nace a Maltina nasha ba yanda yatashi halaka Rahma a gidan nan, ai wallahi bokan nan nake maganin sa na aiki," Shiru tayi kuma ta fara dan kuka,"kai Aunty ko kudin banda rufin ido da boka ke masa kina zaton zai dinga bani? Ke nifa ina ganin ban dake da Bokan ki ko kallo na Fajir bazaiyi ba," Can ta k'ara zaro ido tace,"a,a Aunty Dan Allah ki tausaya min ko.." Shiru tayi da sauri jin karar faduwar wani abu a kofar dakin, da sauri ta kashe wayar kana ta bude k'ofar, Ganin Fajir a durkushe yasa ta jin wani irin fitsari mai zafi a wandon ta, Cikin gigita ta bude baki,"am.. eh ..ba. bacci ba kayi bane?"
,
Wayar sa kawai ya dauka wadda ta fadi sanadiyar zafafan maganganun da ya jiyo daga dakin Wanda bai taba zato ko tsammanin jiyo su ba, koda wani zaizo ya fad'a masa wadannan laifuka da sunan Salma ta aikata su bazai taba yarda ba karshe ko karar sa zai kai yayi fursuna, Amma yau gashi da bakin ta ta fad'a yaso matuk'a yaji ba daidai bane abinda yake jiyo wa amma Ina! Kaddara ta riga fata. Cikin makanta dan kuwa bai ma san inda yake sa k'afar sa ba ya bar part en,ya zaiyi da Hakk'in Rahma? Ya zaiyi da Hakk'in Daddy dake kwance a asibiti rai a hannun Rabba?. A haka har ya isa Fada. Mai Martaba cikin tsananin fushi nan take ya aika dogara da a kamo Salma a zo da ita a gaban shi. Abin da Salma bata sani ba kuwa, Aunty yaudarar ta suke, a lokacin da aka gano Rahma ta bata cikin jin dadi ta Kira Aunty a tsammanin ta boka Aunty tasa yayi aiki, Aunty da bata san zancen ba amma nan take tace ai sarkar ta ma tasaida ta bawa boka yayi aiki yanzu sai Salma ta biya, Cikin zargi Aunty ta Kira Boka taso tayi masa wayau ta bugi cikin sa akan yayi musu aiki ne, da yake ya fita ilmi nesa ba kusa ba nan take yace, ai duk abin tagani shine yasan buk'atar su kuma ya biya saura su biya shi, wanda da zata tambaye shi baisan amsar ba amma da yake mai ilmi ne nan ya bugi cikin ta har ya gano matsalar Salma ce nan ya zuka musu karya da kurciya yayi kuma bazata dawo ba. Nan suka yi yar jejeniya ta kudin sa, yayin da Aunty ta linkasu biyo ta karba a wajen Salma, Tabbas kafin aure Salma da Fajir saida bokan yayi aiki dan da fari da familyn sa suka nuna batayi musu ba matuk'a yaso ya rabu da ita amma yakasa babu tilastawa aka barshi ya aure ta. Sarki kuwa ana zuwa da Salma dake hauka tuburan tana neman ayi mata hakuri ya kalle Fajir tare da cewa "yanzu ba sai anjima ba kabata takardar ta,na raba auren!" Fajir ko dar baiji ba, ya nemo takarda da Biro ya rubuta saki biyu, Kuka Salma keyi tana neman Afuwa,"wayyo Fajir kayi min rai kaceceni ka yafeni , dan Allah kada ka sake ni" Ko kallon ta baiyi ba yayi umurni da akaita fursuna har sai Rahma ta dawo idan kuma akaci karo da Gawar Rahma toh itama tasan nata hukuncin kenan, Daddy da yaji labari ne bayan kwana biyu da faruwar hakan shi yasa aka fitar da Salma a fursunar yayin da yake cewa taje duniya zatayi mata hankali, Aikuwa Salma da gudu tabar kasar nan, bayan ta koma ta kwashe kayan ta a gidan Fajir ita kanta a yanzu ta yafe Fajir dan barin kasar zai fiye mata Dadi kafin Sarki yasan an sakota. Nan fa aka shiga du'ai ta ko'ina duk da kullun sai an sauke kur'ani yanzu kuwa sai ukku ake saukar, Daddy yagama fita hayyacinsa yayi zaman Asibiti har ya barwa Allah ya tattaro yayo gida, idan yakasance babu abinda yake iya yiwa kansa ko bayan gida sai an kashi, daga kwance sai kwance kullun shine rike da photon Rahma yana Kuka, haka zai yini yana karatun qur' an. Fajir kuwa kamar zautacce, dole shima ya tattaro ya koma dakin kakar sa da zama d'an bashida magana sai ace Rahma tazo, ji yake sam numfashin sa bazai fita daidai ba muddin ba Rahma, a yanzu dukan su sunfi sha'war ganin gawar ta akan rashin jin labarin ta, abun yai ma Masarauta illa.
.
Goge fuskar ta tayi tare da amsar ruwan da take bata kana ta fara bashi labarin iya abinda ta gano, *"Rahma"* "Don't worry dear next time tunanin ki zai zurfafa," Inji Mr Naiz Haka suka koma gida tare da Hajiya Bilkisu yayinda take murnar ankusa cin nasara, Kwana shida kenan yau zuwa na ukku zasuyi, a iya yanzu tagano waye duka familyn ta hadi da abubuwa gaba d'aya na rayuwar ta da suka gudana, Mutum biyu ne babu photon su acikin kwakwalwar ta,yau ne karo na karshe da za'a dora ta akan na'ura dan haka Rahma da Bilkisu duka hankalin su a tashe suna fatan nasara. "Fadi! Waye???? Zo zo zo yeah deeeeppppp!" Dr Naiz ya fad'a tare da rolling din hannu sa a idon Rahma wanda take jirkita idanun ta a duk inda ya jirkita hannun sa,nan take kuma ta rufe idanun ta. "Daddyyyyyyy! Dad! Dad!!!!!!,"
.
Daki daki take shiga tana kiran sa, Dayan d'akin ta shiga"daddyyyyyyy!" "Daddy's girl, I'm here," Mutumen ya fad'a yayinda take Fuskar bayan sa, wato ya bata baya, "Daddy let's go to my room," "No my dear I have a lot to do now" "Oh so? I'm leaving dis house," Da sauri ya juyo suka hada Ido dashi, da k'arfi jikin ta ya fara jijjiga cikin fargaba likita ya kashe na'urorin, Da kyar take fidda numfashi tana fad'in,"I'm sorry Dad dats waz not my intention, I'm sorry Aunt." "Calm down dear, now saura daya ki tuna and idan aka samu kuskure shine last stage dinda zai iya lalata brain dinki, so Ki zurfafa tinani," Sai bayan mintuna talatin ya maidata kwance tareda kara dora na'urorin. "Go ahead!" "Oh Yahh I'm sorry," Baice da ita komai ba sai fuskar shi da take a done k'asa. "Yahh kaini Room ena,! Yahhhh! My only husband! Yahh where are you,!" "Kin zamemin Bala,i kin zame ma kowa Masifa! Haka ake gata?? Toh wallahi Bari kiji yanda kika zubar min da ciki sai kin bar gidan nan, mai mugun hali, bana kaunar koda da kwayar zarra ne, an riga da an cuceni had'ani zama da ke!" Wad'an nan kalamai sune suka zo mata nan take a tariyomata duk abinda ya faru a rayuwar tun yarinta har izuwa accident din ta.
.
Dr Zaid yana hango hakan ya kashe komai ya barta akwance nan, saida ta share awa daya a kwance kana ta bude idon ta. "Daddy zo zan mutu a Motar nan, Yahh wuta fa kalli," Magana take cikin rashin hankali wata allura Dr yayi mata kana ta bude idon ta tana kallon su, Zare idanu ta shiga yi tana Mamakin a Ina take, daidai nan Hajiya Bilkisu ta shigo, "Sannu Ruke Alhamdulillahi komai daidai," Rahma ido ta bita dashi, Hajiya Bilkisu tace, "kizo muje gida a yanzu sai Ki fadamun komai," Ala hak'ikanin gaskiya sai ayau Rahma ta taba ganin wannan Matar abinda zuciyar ta bata toh taya zata ce suje gida? Rahma cikin rashin sani tace,"wacce ke?" Dammm! Nan take Rahma ta juyo ta kalleni tace wacce ce Ruke?
.
Hajiya Bilkisu ta kalle likita cikin tambayar ya haka? Dr yayi murmushi yace,"kada ki damu Hajiya Bilkisu ai anyi mai wuyar abinda ya faru da ita na watanni ba abu mai wuya bane ta tuna allurar da nayi mata a yanzu da wadda zan mata gobe da jibi shine zaisa duk komai ya dawo normal a wajen ta," Hajiya Bilkisu ta gamsu dan haka ta lallab'a Rahma suka tafi, Rahma kamar Mai tsoron Bilkisu ko abincin da kyar take sakewa taci, sam taki gayawa Bilkisu mai ya faru da yek tun farko Dr ya haneta dayi mata doguwar tambaya har sai ta warke garau. Bayan kwana ukku ne Rahma ta tuna komai, kuka kam ta Shashi tuno irin rayuwar da tayi a kauyen Dan kaiwa, ita Rahma yar Wellington itace tayi zama a kauye futuk, Babu abinda ya tsaya mata irin wai ana shirin auren ta da Dawuda, lallai dole tayi godiya ga Allah, kuma dole ta godewa Hajiya Bilkisu. Cikin tsananin Mamaki Bilkisu ta mike tsaye tana nuna Rahma da hannu bayan Rahma tagama Sanar da ita komai na rayuwar ta. Rahma kallon Mamaki tabi Hajiyar dashi wanda a yanzu take kiran ta da Mummy, Hajiya Bilkisu ta ce,"Rahma!!dama ke diyar D'an Sarki ce? Dama Father shine kakanki? Fajir kuwa Mijin ki da kike so baya son ki? Islam kuma kawar ki????" Rahma wad'an nan tambayoyin sun bala'in bata shock, da sauri ta amsa da "Eh Mum sune kinsan su ne? Kinsan masarauta Kano ne?" Mum takoma ta zauna tare da nuna alamun damuwa tattare a fuskar ta,"Allah sarkin Iko mai yadda yaso!" Abinda tace kenan kafin ta fara hawayen da suka Rahma jin fargaba sosai, Hajiya Bilkisu ta kalle ta cikin jimami tace,"Father shine Siriki na, Dan Sarki kuwa mutume nane kuma k'anen Miji na, Fajir shine D'ana na fari, Islamic ce 'Yata ta biyu,"" Rahma zaro ido tayi sosai tana mamaki lallai Rabbi shine Sarkin iko, "Mum dama kece mahaifiyar Fajir?"
.
Mum bata amsa ba sai system da ta jawo ta shiga nuna ma Rahma picx da yawa na Fajir ne yana karami, wani yana a hannun Daddyn Rahma wani kuwa yana a hannun mahaifonshi mai rasuwa, Rahma kuka ta shiga yi yayin da Ita kanta Bilqisu shi takeyi. Rungume juna sukayi suna kukan farin ciki, a hankali Rahma ta jaye jikin ta ta kalle Mum tace,"Mum meyasa baki waiwayesu ba tun bayan tafiyar ki?" Bilkisu tayi Murmushin karfin hali tace,"kamar yadda kikaji anan suna kirana da Bilkisu, toh wannan bashi bane asalin suna na ba,Sumayya ne sunan yayinda Bilkisu yakasance sunan Yaya ta, a halin yanzu duk wani matsayi da kika ganni Ina akan matsayinta ne, lokacin da Miji na Jafar ya rasu nayi haramar baro Nigeria zuwa inda Yaya ta wadda ita ta raine ni, lokacin muka samu sabani da'yan gidan ku yayinda nayi haramar tafiya da 'ya'ya na nan take Father ya shaida mun babu inda zani da su, amma ni mai iya zama ce idan ma auren zanyi su zasuyi min, nikuwa a lokacin babu abinda nake so kamar na bar gidan, dan haka cikin dare na hada kan 'ya'ya na na gudu, saidai ko Ina ban kai ba Fadawan Sarki suka zagaye ni, ala dole na bar Yayan nawa, Zamana a wajen Yaya ta ya canja rayuwa ta wanda kafin ta rasu saida tasa nayi mata alk'awarin Auren mijin ta wanda yakasance tsoho kutuf suna zaune a China, haka kuwa akayi bayan rasuwar ta na aure Mijin ta yayinda suna na ya tashi daga Sumayya zuwa Bilkisu, duk bayan shekaru ukku Ina zuwa naga 'ya'ya na, a tafiyar farko da nayi na samu labarin rasuwar Aisha, a halin yanzu dai rabo na da can Tun Islam tana 13yrs ban k'ara waiwayar su ba, yanzu kuma Mijina ya rasu." Ta karashe maganar cikin kuka, Rahma kukan takeyi, Shakuwa mai k'arfi ta shiga tsakanin Rahma da sirikar ta, Shirin komawa suke Nigeria ainun duk da Sumayya bata sanar ba cewa anga jikanyar Saraki! Saura sati d'aya su koma ne Mum ta fahimci kamar Rahma tana cikin wata fargaba, yau ma zaune take a falo tana kallo amma sam Hankalin ta baya kan TV, Sumayya da tafi to da niyar fita kasuwa ta zauna a gefen Rahma, hakan yasa ta juyo ta kalleta, "Rahma, meyake damunki? Kamar kada musaka ranar tafiya naga duk kin firgice menene?"
.
Rahma da hawaye suka sirnano mata ta dora kanta akan jikin Mum tace,"Mum Yahh Fajir baya so na, bana son na koma naganshi hakan zai sani ciwon zuciya, Mum nima bansan ya ake nake jin Fajir har acan kasan zuciya ta ba, a iya yanzu so nake na cire shi a rayuwa ta, zan aure Dawud koma menene zan iya yimasa," Mum'da taji kalaman basuyi mata dadi ba ta dan fara bubbuga bayan Rahma,"Rahma kada ki damu, Kibari muje din idan Fajir yana akan bakar sa ni da kaina zan nema miki Saki a wajen Father, amma da sharadi!" Rahma ta dago kanta tace "Sharadin meye Mum?" Hannun ta taja sukayi daki, Da sauri naje in shiga Mum ta banko kofar wanda yasa aka bugemin goshi na! D'aga tafiyar sukayi har na tsawon wata biyu! GIDA NIGERIA. A saman Matattakalar benen jirgin ta tsaya tare da zare madubin dake idon ta tayi, wani irin Farin ciki taji ya mamaye ta, A hankali ta fara sauko wa dauke da jakar hannun ta, sanye take da doguwar riga kirar 'yan Spain rolling tayi da veil dark. Tana saukowa ta jirayi Mum dake bayan ta, cikin farin ciki da Jin dad'i suka karasa wajen da aka ajiye motoci domin tarbon mutane, Kawar Hajiya Bilkisu suka hango a gefe cikin farin ciki ta karaso wajen su, "Welcome back My Hajiya" Abinda tace kenen yayin da suka rungume juna tare da Mum, Cikin Mamaki ta kalli Rahma, "Ah ah Su Ruke! Masha Allah, Allah bangane Ruke bace," Rahma kuwa dariya tayi tace,"Aunty Barka," Basu bata lokaci ba suka wuce gidan Hajiya Zulai dake nan Abuja, Anan suka shiga gaisawa bayan sun huta ne Mum take bawa kawarta Zainab labarin ko wacece Ruke!, Cikin Mamaki Zainab ta kalle Mum tace,"dama itace? Ance jikanyar Saraki Kano ta bata, amma fa ga labari cewa akayi aikin kishiyar tane, shiyasa da naga Ruke akace accident tayi wlh sam Allah bai kawo min wannan tunani ba," Mum tace,"hakane kuma kinga fa itace Matar Fajir," Zainab ta bude baki tace,"chaiiiii kawata! Kada kice Fajir namu?" "Eh, itace 'yar Dan Sarki k'anen Miji na da nake gayamaki, auren zumunta ne," Nan dai tagayawa kawar ta komai, Hajiya Zainab har rawa tayi tana tsalle, Da safe aka taho da Dawuda zuwa Abuja dan kuwa Mum Ta shirya tafiyar zuwa Kano a yau dinnan. Tun abakin K'ofar Farko aka tare Motocin, Nan drivern su Hajiya ya fita ya fad'a musu cewa Maman Fajir ce tazo, ganin ta yasa suka shiga kwada mata kirari da yiwa Mai rasuwa fata takwarai. A fad'a kuwa, D'an Sarki ne zaune a k'asa, sai Fajir da Yah Abdullahi a gefe, shirin fita akeyi da D'an Sarki zuwa kasar waje akan ciwon sa da ya tsanan ta, Aman jini yake sosai a yanzu yakan iya tafiya ko zama amma fa da ka kalleshi sai kasan baya cikin hanyacin sa. Busa sukaji an dauka a k'ofa ta hudu wadda daga ita sai Fada, Mai Martaba ya kalli Fadawan sa yace, "wane bako ne ba sanar wa,?" Sukan su basu san wane bako bane saidai ihu da suke jiyowa, Wani bafade ne ya shigo a guje ya fadi gaban Sarki cikin tsananin murna, "Yahh Ranka shi Dad'e, Gimbiya ce da kanta ta dawo," Kafin su fahimci maganar sa Rahma ce ta shigo a guje tana dariya hade da Kuka, Tsayawa tayi cak tana kallon su duka, "Daddyyyyyyy! Fatherrrrrr!" Ta fada tare da fashewa da kuka, Dan Sarki ya taso da sauri yana tunanin ko ba ita bace? Hannuwanta ya kama yana lalaben ta, "Daddy it's me *Rahma Daddy's girl"* Fashewa yayi da kuka kana ya rungume ta, Father kuwa tasowa yayi yana fadar, "Mata? Mata ce?" Sakin Daddy tayi ta share hawaye, "Father?? Yanaga baka wani tsofa ba?" Ta fada tana dariya, Nan aka dauki kabbara da hamdala a fadar su kuwa makada kamar an sanar da su suka fara shaida ma Duniya Jikanyar Saraki ta dawo, Baku tambayeni Fajir ba?? Hhmm ai in gaya muku mutuwar tsaye yayi, tuni hawaye sun wanke fuskar shi, tasowa yayi yana kuka sosai tare da rungume Rahma, wadda har Ya Abdullahi saida ya rungume ta tsabar dad'i dan tuni ya ajiye komai gefe, dariya tayi kana ta dan ture shi, tana masa kallon ya haka?
.
Nan su Hajiya Sumayya suka shigo tare da Hajiya Zainab sai Dawuda, Rahma ta jawo Hannun Hajiya Sumayya ta zaunar da ita, dukan su a kasa suke yayin da Rahma take dale saman kafafun Mai Martaba, Nan Sumayya ta shaida su suka zo da ita, Masauki aka basu kan kace Kobo gidan ya cika, duka aka wuce a k'aramar fadar, Islam da kukan ta tashigo ta shiga rabon ido dan ganin Rahma, aikuwa da gudu suka rungume juna suna kukan Murna, Mama Safiya dake acikin gari tuni Labari ya je mata ai a hanzarce ta Iso gidan, haka ma Mama Sadiya anyi Sa'a tana kasar tazo duba jikin D'an Sarki, Ai fa bayan anci ansha abinci aka taro ana saurare Jim ya akayi Rahma ta had'u da Sumayya, Shi Fajir duk fushin da yake da Mahaifiyar sa, ganin ta tare da Rahma tuni yaji ya kau a zuciyar sa, Islam ido ta tsura mata yayin da Sumayya ta runs tana kuka da basu hakuri, Gyaran murya Sumayya tayi tare da Nuna Dawuda wanda kamar dutse ya zama, shikam da kansa yayiwa kansa Hisabi akan so, dam ya tabbatar ko giyar wake yasha bazai k'ara bude baki ba yace son Ruke yakeyi, Nan Hajiya Sumayya ta bada labarin zaman Rahma a dan kaiwa da irin rayuwar da tayi acan harda sunan da akayi mata sanadiyar ciwon Mantau, bayan ta shaida musu zuwan su da haduwar su da Rahma har fita da ita k'asar waje da aikin da akayi mata wanda yaci mak'udan kud'i, da duk wani abu da ya faru da rayuwar ta acikin wata tara, Nan aka dauki kabbara da Salati, Hajar da take diyar Mama Safiya tace, "su Ruke anyi Arziki!" Nan aka dauki dariya, Rahma ta gyara zaman ta ajikin kakan tace, "Am Daddy Ina so na baka hakuri da abinda ya faru a baya, ni bani da niyar yin kisa akan kowa, sharrin shedan ne kayafeni Dan Allah, ta karashe maganar tana kuka," Father yace,"haba Mata kuka nameye a yau dinnan? Baki ga kannen ki ba gasu can Aysha da Sabeer?" Ido ta dago nan ta hango Amaryar Daddy zaune tana murmushi dauke da Aysha yayin da Sabeer yake hannun Cousin Jabeer, Ido ta bude tace,"dama ta haihu ni akace min ta Mutu?"
Father yace "wayace maki haka?" Fajir yasan shine dan haka ya tsura mata Ido ita kuwa sai cewa tayi,"Nidai Father idan ban manta ba haka naji labari hakan yasa na k'ara rikicewa," Nan ta sauke ta karbi kannen ta tare da bawa Sadiya hakuri dukda har yanzu bata wani sakar ma Sadiyar fuska ba saidai kannenn ta da ta dauka tana wasa dasu, "Am Father!" Hakan yasa kowa ya maida hankalin sa akan ta, "Dama wannan shine Dawuda, kuma Auren mu ake shirin yi kafin muje Spain, so shiyasa aka daga auren amma yanzu tun da komai ya dawo lpy qlau sai ya turo iyayen nan aka ta saka rana," Ba Fajir ba duk ilahirin jama'ar dake wajen saida wannan zancen ya basu Mamaki, Ganin kowa ya kafe ta da Ido har shi Dawuda saida ya rikice da Jin zancen ta, Father yace"Mata wane irin zance kike haka?" Murmushi tayi tace"Eh Father Dawuda shine wanda nake so na aura,!" "Aure!!!?" Gaba d'aya kowa ya tambaya cikin tsananin Mamaki, Fajir kuwa ido a waje yake kallon ta, "Rahma bakida hankali ne? Aure kan aure zakiyi ko yaya?" Inji Jabeer dake zaune a kusan Fajir,wani kallo Rahma tayi masa"Aure kan aure?" Ta maimaita, Yah Abdullahi wato Abba yace,"Ina ce dai ai kinsan da aure akan Ki ko? Ko Fajir ba Mijin ki bane?" "Abba Fajir kuma? Father wai da gaske? Toh waye Fajir din?" Duk falon saida suka jiyo kukan cikin Fajir, addu'a Allah yasa wasa takeyi, "Kalle shi can shine Yayan ki Fajir kuma mijin ki," Girgiza kai Rahma tayi ta tashi daga jikin Father tayi wajen Daddy, "Daddy ni Dawuda nake so bansan wancan ba," "Baki san shi ba? Fajir Mijin ki yayan ki ?" Inji Mama Safiya, kuka Rahma ta fara Mum ta kalla wato Sumayya, "Mum Dan Allah kice su Bari, ni bansan wancan ba," Ta fada tana nuna Fajir, Sumayya tayi gyaran murya tace, "Ranka shi Dad'e a kyaleta akan bakar ta shi yafi domin kuwa likita ya tabbatar mun da haka cewa ba kowa bane zata tuna har sai ta samu natsuwa Sosai, saidai shi Fajir din yayi kokarin dinga nuna mata ko waye shi a wajen ta hakan zaisa ta tuno shi," Fajir ya mike a firgice,"nine ta manta? Nikadai? Saboda abinda nayi maki ne Rahma,? Dan Allah kada Ki hukunta ni da wannan hukunci mafi muni a rayuwa ta," Da sauri yazo ya kama hannayen ta yana Kuka, Sumayya tausayin Dan ta taji kuma tun shigowar su ta gano alamun son Rahma fal acikin kwayar idon shi, amma dole ne a hukunta shi, Rahma ta janye hannayen ta "Daddy kuce ya barni, ya daina taba ni," Kuka ta fara wanda yasa Jabeer yaja Fajir zuwa waje sai hauka yake ita kuwa fur ta nuna bata san shi ba. Ala Dole tilasta aka sa Fajir ya kyaleta har asan yadda za'a bullowa lamarin, A bangaren Maman Fada Rahma ta zauna, biki aka shiga yi sosai anyi walima har kashi hud'u, yayin da Dawuda yaci kyautar milayan ukku da gida da Mota, Mum kuwa Sam tace bazata karbi komai ba, hakan yasa Fajir ya dankaro mata Sarka ta gwal mai dan Karen tsada, Dawuda ya koma k'auyen su yana mai kukan rabuwa da masoyiya, Inno kam kamar ta shude akan jin dadi abinda Dawuda ya samo, ayanzu tayi danasani walakanci da tayi ma Rahma, dama ashe Ruke 'yar Saraki ce???
.
Ke kudaina ce mata Ruke fa Bayan dangi sun gama ganin Rahma D'an Sarki tafiya tasha kashi dan tuni ya warke, yanzu Fajir kadai aka Bari da sunu. Duk yabi ya gigice gashi Rahma ko kallon shi batayi, Sati d'aya da dawowar ta ya shigo Fada ya zube gaban Mai Martaba, Nan ya roke abashi Matar shi gaban kowa babu ko kunya, Daddy ma goya masa baya yayi acewar sa hakan zaisa ta tuna shi. Rahma kam da Daddy ya sanar mata a shirya ta Kuka ta dora da cewa Babu inda zata je wanda hakan duk shirin Mum Sumayya ne, Nan su Mama Safiya suka sa baki abarta har har wani Satin, Haka kuwa akayi yayinda Fajir ya shigo yayi musu tsaye dole sai an bashi Matar shi, saida Mama Sadiya ta kora shi, Gyara na musamman aka shiga yiwa Rahma, wani irin kara cikowa tayi kamar wadda ake hura wa, B..bs inta sun bala'in cikowa kamar yadda kugun ta yayi, Fajir sabon ginin sa dake Abuja yasa aka gyara Komai sabo akayi gidan Babba ne sosai ga shegen kyau kamar a turai,a yanzu can aka maida aikin sa duk da ajiye aikin yayi amma yanzu ya koma, Ranar da yazo Ranar Mum zata wuce Abuja tare da Islam suka zo, nan suka hadu har Rahma wadda saida ta kara wani kukan amarci, Suna sauka a birnin Abuja Rahma ta kekashe tace Mum zata biya tare da Islam, Kiri_kiri Fajir yace bazata ba, saida daga baya suje, nan Mum ta lallab'a ta suka Rabu a Filin jirgi. Rahma kam gidan yayi mata kyau dakin ta ta shiga tare da yin Hamdala gun Rabbi gata ga masoyin ta abin begen ta, wanda a yanzu yakasance abar kaunar sa, babu Salma babu son Salma a ranshi. Bacci tayi Sosai sai Magrib ta tashi, wanka tayo Bayan tayi Sallah ta shirya cikin Zilzila Turn sai short legging da saka, kwalliya tayi ba sosai ba ta feshe jikin ta da turarukan ta masu tsuma zuciya. A hankali ta fito tana tauna chewing gum tare da maida hankali akan wayar ta. "Ya ilahi" [9/25, 12:19 PM] Aunty Queen Mamu: *RAHMA* _(Daddy's girl)_ *40* *The end* Abinda Fajir ya fad'a kenan yayinda yake niyar kara kiranta a waya dan suci abinci, Shi kam Mamakin wannan girman da ta kara yake shi iya sanin sa ko nono baya ganowa ajikin ta but yanzu sai yake ganin kamar dasa mata su akayi,bata ko kalleshi ba duk da tasan ita yake kallo kujera taja tare da ajiye wayar ta gefe, "Ina wuni!" Firgititi ya janye idon sa akan ta, Bai iya amsawa ba sai abinci da ya fara zubawa, Daure wa kawai yake yana cin abinci amma tuni hankalin sa ya gushe, Rahma kuwa cin abinci ta take sosai tana kammala wa ta mike tsaye, "Am am Rahma!" Juyowa tayi ta kalle shi, "Ka kirani ne?" "Har kinci abincin? Kuma Ina zaki?" "Naci kuma bacci nake ji," Tana kaiwa Nan ta wucewar ta yayinda yayi mutuwar zaune, Da kyar ya iya Jan kafafu yabar wajen, d'akin ta ya nufa amma sai yaji a kulle, A daddafe yaga safiya ta waye masa, 8 nayi ya fito a zaton sa ko bacci takeyi, ya fara breakfast ya hango ta ta fito daga kitchen, a iya tunanin sa abinda take daure dashi bazai wuce gyale ba, dan har Pant enta Rosie yana hangowa, Tana zuwa ta zauna akan kujera kamshin ta ya buge hancin sa shi sam baisan rike da cup a hannun yake ba, Rahma kam indomiee take ci babu kama hannun yaro, da kyar yace, "Rahma babu gaisuwa?" Cikin wata irin kasalalliyar murya, "Bakaji bane sau ukku Ina gaida ka!" Kunya yaji ta kama sa, Tana gamawa ta barshi anan sankare, da kyar yaje aikin ya dawo, Yau kusan kwana hudu kenan saidai ta kashe shi ta hanya saka sexy dress, amma daga gaisuwa sai gaisuwa, daki ma idan ra shiga kullewa take, Yau kam fitowa tayi tsakar falon sam ta manta weekend ce, a zaton ta ya tafi aiki, a bakin k'ofa tayi tsaye tana tunanin me zataci na Rana, hannun ta taji an taba hakan yasa da sauri taja da baya, Ganin shine yasa ta danji gaban ta ya fad'i, A bango ta jingina yayinda ya matse ta abango hannayensa biyu ya dora akan bangon ginin yayi mata kwayenwa, "Rahma! Ki tausaya ki tuna Mijin ki kafin kisaka shi a wani hali," Amon muryar sa ya gigitata nan take jikin ta ya fara rawa, "Toh toh ai aini bansan ka ba!" "Baki sanni ba?" Bude baki tayi zatayi magana nan ya taki sa'ar ta yasaka bakin shi ana ta, Wani irin salon kissing ya shiga yi mata wanda taji numfashin ta na neman shud'ewa, Saida ta ya tsotseta Sosai kana ya sake ta tare da sakin wata irin ajiyar zuciya, Da gudu tabar falon ta nufi daki tana numfashi sama-sama, Jin take kamar taje ta rungume sa ya k'ara mata wani wani irin zazzafar kaunar shi take shigar ta, A hankali ta kwanta akan gado tana murmushin jin dadi, Shi kuwa gogan da kyar yaja kafa ya zauna akan kujera, Yau haka suka yini ko abincin dare bata fito cin sa ba, hakan yasa ya debi abinci ya konkosa kofar ta, "Waye?" Ta tambaya, "Mijin ki ne!" Kai tsaye ya fad'a, kin bude k'ofar tayi bai takura ta ba, ya koma dakin sa spare key ya dauko,
.
Ta fito daga toilet ne tana zaune gaban madubi jikin ta take shafewa da mayuka da turarukan sirri, A hankali aka bude k'ofar wanda yasa ta juyo da k'arfi, "Yahhh....!" Baice da ita komai ba sai abinci da ya ajiye a gefe, "Ki cinye sa tas kafin in dawo," "Ka dawo kuma?" Ta fad'a tare da mik'ewa tsaye, Santala Santala cinyoyinta a fili rabin kirjinta ya fito daga yanayin yanda ta daura towel din, Matsowa yayi gab da ita, "Meyasa kike kullemin k'ofa?" "Toh aini bansan ka ba," Ta fada tana tunzura baki, cikin ta yayo wanda yasa ta ja da baya, Hannayen ta ya kamo, ya hada ta da kirjin sa, "Rahma! Bakisan yanda nake ji azuciya ta ba duk lokacin da kikace baki sanni ba, tabbas nasan na tauye Hakk'in ki a baya, na cuta maki, amma kiyi hakuri Ki yafeni sharrin shedan ne, dan Allah ki tuna dani kafin zuciya ta ta fashe tsabar son ki da yake wahalda ni" Jikin ta taji yayi sanyi sosai dama anzo gabar da take so, da kyar tace, "Yah sona kakeyi?" "So so so Rahma! So Wanda baya gushewa, Kauna ta jini da tsoka wadda ba'a iya cirewa, dan Allah ki tausaya min ki soni ko yaya ne" "Toh ai Yah Kaine da....," Batayi aune ba taji ya cafke harshen ta, nan take ya shiga nuna mata tsantsar k'auna, Batayi garaje ba ta shiga taimaka masa kan gado ya maida ta tare da cire towel en, na shanun ta suka bayyana masu daukar ido da rikitar wa, Rahma bedsheet taja tana rufe jikin ta shi kuwa gogan tuni yayi watsi da nashi tufafin, Inaaaaaa abu yayi dad'i, nan ya fara matsar su yana wani irin gurnani kamar mayunwacin Zaki, Rahma kuka ta fara dan abin ya fara fin karfin ta, Ganin tana jin zafi yasa ya fara shansu nan take ta fara nishi sosai, wasa ya shiga yi da ita wadda tatafi da hankalin ta batayi aune ba taji yana karanta addu'ar Saduwa, Nikam a lokacin bana hango komai dan sun kashe fitalar dakin, jin kunnuwa na suna jiyo abinda yafi karfin su yasa na fito a guje na rufa musu daki. ****** Hmmm wannan Ranar an sakata a kundin tarihin masoyan, Iya Kauna sun nunawa juna, haka suka kasance cikin so da kulawar juna, Fajir saida ya share wata baya zuwa Office saida asameshi a gida, sun darji amarci son ransu. Bidirin biride. Biki ake na nadin Sarauta gidan ya cika Sosai ana ta Hidima da baki kala-kala, Karfe ukku dai dai ne za'ayi Nadin tare da Daura Auren jikokin gidan su shida, Ukku Mata Ukku Maza, dag ciki harda Islam da Asmy sai Rabila, dama sune 'yan matan da suka rage sai kannen su, Maza kuwa Dan Baba Galadima ne sai Kanen Jodan ne guda biyu sai Jodan din, wanda ya fito daga prison wata biyu da suka wuce, Daddy ne yayi tsaye sai an fitar da shi, ya bala'in horuwa da natsu Sosai, hakan yasa aka nemo masa mata aka hada da kannen shi yau za'a aurar dasu. Rahma kam tsohon dakin ta ta shige ta rufe kofar akan irin azabar da bayan ta yake, Ganin karfe sha d'aya na Rana ne tasan Daddy yana can cikin mutane, Jin azabar sai karuwa take hakan yasa ta lalabo wayar ta ta kira Daddy, nan ta shaida masa bata lafiya a firgice yace gashi nan tafe, Fajir ganin Daddy ya amsa waya kuma yaga hankali sa a tashe yasa ya biyo shi dan Jin meke faruwa, Nan Daddy yasanar masa Rahma ce ba lafiya, Ai tsera akayi tsakanin Daddy da Fajir duk inda suka bi sai ance meya faru, Mama Sadiya ta biyo su baya suna isa falon ta suka dinga jiyo nishin ta, Da sauri suka karasa ciki, durkushe take ta rike gado da hannayenta biyu, duk irin yanda A.c da Fan suke aiki ita kuwa duk ta sharbe da gumi, "Subhnallah!" suka fada a tare, Mama Sadiya da ta Iso tace, "haba nifa tun dazu na fahimce cikin nan yana gab da fitowa, yanzu Ku dauke ta muje Asibiti kawai," Nan Fajir ya tallabota ita kuwa sai salati take, A kan gadon aka tura ta hannun ta daya rike da Fajir daya kuwa Daddy, "Daddy, La'ilah wayyo Allah Yah Ku rike ni inna lillahi, subhnallah, lahaula..!" Duk addu'ar da fito mata ita kayi, Daddy da Fajir sai yawo suke gaban dakin da aka hanasa shiga, A gogo na tafiya amma shiru kakeji har karfe biyu, Sarki ya Kira su yace su dawo tunda basuda abinda zasuyi mata, Daddy yana katse wayar sai ga likita ya fito ciki, yana dariya ya isa wajen su, Mama Sadiya da Aunty Sadiya da Mama Safiya duk suna wajen nan suma suka taso ganin likita, "Congrats princess ta haife Baby Boy" Nan suka dauki hamdala, Daddy da Fajir saida suka ga d'an sak kamannin Baban shi kana su wuce Nadin sarauta. Dadi biyu da biyu kowa ya gansu wannan masarautar kasan suna cikin tsantsar farin ciki, A yau dai aka nada Omar Muhammad a matsayin Sarki a masarautar, Murna biyu ake ga sabon Sarki ga kuma sabon magaji, Shagalin biki aka tayi har sati d'aya inda yaro yaci Sunan Jafar Yareemah.
.
_*MATACCIYA*_ *Yana nan zuwa maku inshaAllah*. *It's ur Aunt queen*