Bayan sallar isha'i ta fito wanka, ta sha fa mai tana ta faman kiran wayar Nuren ya ƙi dagawa, duk ta bi ta damu ko abinci ma ta ƙi ci, Umma tayi-tayi Samima ta zo taci abinci amma ta ki har Umma ta gaji ta kyaleta, kayan bacci ta canza ta kwanta, dan gobe da safe sammako zasu yi, su tafi shago su karasa ƙimtsawa, da misali karfe goma ta kasa bacci tana so Nuren ya ɗaga waya ta ba shi hakuri amma ya ƙi, bata yi tsammani ba ta ji radaɗin da take ji idan zata koma macijiya, da sauri ta yi cillir da wayarta dake hannunta ta miƙe zaune, ihu Samima ta fara yi, Baba da Umma su na zaune a parlour suka ji ihunta suka taso da gudu suka shigo, su na shigowa Samima ta ce.
"Umma Baba, dan Allah ku fita, kar wani abu ya same ku" ƙin fita suka yi, yayinda Umma ta kamo Samima, tsananin zafin azaba Samima ta fara ji, ta kalli fatar jikinta ta ga ya fara sabulewa, da sauri ta miƙe ta fice daga dakin, tana fitowa ta makale a jikin labule tana huci bakinta na fitar da hayaƙi, a kiɗime su Baba da Umma suka fito, su na fitowa, Samima ta koma daki da gudu ta dannawa dakin key, da sauri su Umma suka hau bugawa ta tsaya tana kwallara kara, da sauri Baba ya kira Nuren ya sanar da shi abun da ke faruwa, Allah yaso Nuren din bai koma gida ba yana gidan su Suhail, da gudu ya ta so ya kamo hanyar unguwarsu Samima, kafin ka ce me sai ga shi, haka ya shigo kamar mahaukaci ya ce.
"Bata bude dakin ba?" Baba ya ce.
"Ta ƙi budewa"
"Samima ki buɗe dakin nan!!" Nuren ya faɗa yana dukan kofar dakin, a lokacin rabinta har ta koma maciji, saman jikinta ne bai gama rufuwa ba, da karfi ta ce.
"Na ce kubar wajan nan!! Bazan buɗe ba!!" ta hau kuka, ta kwanta a dan gadonta ta naɗe jelar macijin ta rufe da bargonta tana kuka mai ciwo, Nuren ya ce.
"Baba, Umma ku matsa" su na matsawa ya hau buge kofar yana shirin ballawa, ya kallesu ya ce.
"Plss idan na bude karku shigo, ku yarda dani kawai ku koma gefe" Baba ya gya ɗa kai suka koma gefe su na addua, da kyar Nuren ya balle kofar ta bude ya shige dakin ya ce.
"Samima!!!?" tana ganinsa ta miƙe da gurnani ta zama macijiyar gaba daya ta yi kansa zata kai masa sara, da sauri ya rungumeta jikinsa na b'ari, idonsa rufe gam, rungumeta da ya yi ta kasa wani karabus illa rausaya kai da ta fara yi,a hankali ya ɗago ya haye gadon ya kamo fuskarta a macijin yana karanto adduar da Malam Abba ya ba shi ya din ga yi, a tana macijin sai ga hawaye a idonta, ba karamin shahada Nuren ya yi ba, a hankalin samanta ta fara dawowa mutum, daga kugunta zuwa samanta ta koma mutum amma daga kugunta zuwa ƙasanta jelar maciji ne, kuka ta saka mai sauti a hankali ya rungumeta, da haka suka kwanta a gadon ya ja bargo ya rufe mata jelar macijin, shi ma ya kwanta ya rungumota a jikinsa, suka yi shuru, Baba jin shuru ya saka shi cewa da karfi.
"Nuren kana lafiya!!?" Nuren ya amsa da "eh Baba lafiya, ba komai yanzu,kuna iya zuwa ku kwanta nima zan kwana a nan" Baba ya amsa da "to" a haka Samima da Nuren suka kwanta yana rungume da ita rabi mutum rabi macijiya, da ikon Allah kuwa wani bacci mai dadi ne ya kwashesu a hakan.
@@@@@@@
Da burin Asabe idan ta mai da Samima macijiya, ta sari iyayenta ta kashesu, tasan dole ne itama ta mutu, Nuren kuma mai sauki ne in dai Samima ta mutu dole ya dawo wajansu.
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
Gajeran labari, mai cike da sabon salo, mun zo karshe fa. Saura shafi daya da yardan Allah, ku biyo ni dan jin yadda zata kaya 🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️
ARADUN ALLAH NA SHA TYPING.... HARDA NA JIYA NA HADA MUKU. 🤢🤢🤢
UMMU AHLAN TA KU CE👍🏻
[02/09 à 08:47] 🌹🌹Flower 🌹 🌹: *SAMIMA* 🐉🐍
( _macijiya ce_)
Na
*ZAHRA ABDUL*
(MOMYN AHLAN)
Gajeran labari.
SHAFI NA TARA. ✍🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
Da asuba Baba ne ya buga musu kofa, a tare suka buɗe ido, rana ƙwal a idonsu, salati ya fara gami da adduar tashi daga bacci ya duba agogon dake ɗaure a hannunsa ya ga har takwas da minti ashrin, da sauri ya tashi,ita ma ta yaye bargon a hankali ta ga kafarta ya koma na mutum, gauron ajiyar zuciya ta sauke ya kalleta suka haɗa ido ya galla mata harara ya shige toilet dinta,dan ya yi alwala, sunkuyar da kai ta yi a ranta ta ce.
"Na shiga uku ni Samima!! Wallahi bai hakura ba,har yanzu yana fushi dani" sai ta fara hawaye, ko da ya fito bai kalleta ba, ya ce.
"Ki tashi kiyi alwala ki zo muyi sallah" jiki ba kwari ta miƙe ta shige toilet ta yi alwalan ta fito ta shinfiɗa musu sallaya ya ja su sallah, bayan sun idar ta gaishesa, ba tare da ya kalleta ba ya amsa ya tashi ya fice tana shirin yi masa magana, a hankali ta miƙe ta bi bayansa, a parlour ta iske shi zaune da Baba da Umma, durƙusawa itama ta yi ta gaida iyayenta, Umma ta kamota ta rungumeta tana tambayar babu inda yake mata ciwo ko, ta amsa da eh, miƙewa Nuren ya yi ya ce.
"Baba,Umma, zan wuce gida, idan akwai wani abun sai ku neme ni" Umma ta ce.
"To Nuren Allah ya yi albarka fa, mun gode sosai wallahi, amm kuma na ce ba, ya maganar show din su Samima? Kasan fa da da yanzu ba ɗaya bane,idan ka ga ba ka da bukata ba sai an yi ba" Umma ta fada tana kallon Nuren, Baba ya ce.
"Gaskiya hakane maganarki Zulaiha, ga shi ita Samima ba wai ta warke bane, kar su je show din kuma abun ya ta shi mu shiga uku" da gefen ido Nuren ya kalli Samima ya ga tana share hawaye, yasan yadda take kaunar wannan show din da za a yi, shi ma ba zai so ace bata je ta yi ba, tun da hukumar tacewa ta ba ta takarda inda aka zabeta ta uku, amma haushin abun da ta yi masa jiya ya saka shi cewa.
"Baba,Umma, karku damu zan duba na gani, idan ya kamata ta je show din ko bai kamata ba,idan ya kamata zan sanar muku, ko kuma na aiko Suhail ya ɗauketa ya kai ta shop dinta, amma idan na ga ba zai yu ba kawai zanje nayi cancel din sunanta" Baba da Umma suka amsa masa da "to ba damuwa" ya fice, da sauri Samima ta bi bayansa tana masa magana amma ya ƙi kulata,har ya shiga mota, ganin da gaske tafiyar zai yi dan har ya kunna motar, kawai ita ma ta faɗa motar, tana shiga ta saka masa kuka,rintse ido Nuren ya yi, jin yadda sautin kukan nata ya daki ƙirjinsa, ya ce.
"Ohhhh, Samima wai me kike so ne kam? Ki fita min anan, ina so na je gida ne Momy duk ta bi ta damu bata ganni ba, dan Allah fita" cikin kuka ta haɗa hannuwanta biyu.
"Dan Allah Yayana kayi hakuri, wallahi ba zan sake ba, na ji na yarda idan har baka so nayi wannan show din na hakura ka je ka yi cancel din sunana, amma dan Allah ka daina fushi dani, tun jiya na kasa samun sukuni a zuciyata, hakika Yayana duk macen da ta yi sa'ar samun ka a matsayin miji za a iya kiran wannan mace da suna *SA'ADATU,SA'AR MATA* domin kuwa ta yi zarra, wa hakane nake ganin kai na a matsayin macen da ta fi ko wace mace a duniya, dan ba kowa bane zai kasance tare dani a halin da nake ciki ba, abun da na aikata jiya bai kamata ace na aikata ba, mai sonka bai cancanci ka bata masa rau ba, a jiya na sake shiga karatun tanatsu dan Allah Yayana ka yafe min dan Allah da Manzon Allah S,A,W, da soyayyar da ka ke min" ta ci gaba da kuka, ɗan lumshe ido Nuren ya yi, ya ce.
"Shiii!! Ya isa haka Ƙanwata kuma Matata, ni fa ba fushi nake yi dake ba, kawai ina so ne ki gane kuskurenki,tun da kuma kin gane ai shi kenan, yanzu abun da nake so dake ki koma cikin gida ki shirya Suhail zai zo ya dauke ki ku tafi shago,nima yanzu gida zanje Momy ta ganni sannan na shirya na tafi office zan zo na same ku da yamma idan na ta so daga office zan yi kokari na ga na kasance da ke uhum?" ta gya ɗa masa kai tana murmushi ya ce.
"To share hawayenki, bana son ganin kukan ki ko kaɗan" share hawayen ta yi tana shirin fita a motar ya sake cewa.
"Ammm ba ki ji ba, na ce ba?" juyowa ta yi suka hada ido, ya kashe mata ido daya gami da cewa.
"INA SONKI!!" DAM!!!DAMM!! Gabanta ya buga, nan take kunya ya lullub'eta ta fice a motar da gudu ta shiga gida, har tana buge Umma dake shanya, Umma ta ce.
"Na shiga tara, Samima karyani za ki yi ne? Ko bakya gani ne?
"Yi hakuri Ummana wallahi ban kula bane"
"Ahh ina kuwa za ki kula,kin shigo da gudu kamar an wurgo kwallo" Umma ta faɗa tana ɗaukar bokitinta, Samima ta ce.
"Umma Yayana ya ce na shirya Yaya Suhail zai zo ya dauke ni muje shago, ya amince zanyi show din" ta faɗa tana murmushi Umma ta ajiye bokitin hannunta ta dafa Samima ta ce.
"Samima har ga Allah bana son kiyi wannan show din, ciwonki baya tashi sai dare, tsorona ɗaya ki zo fitowa ciwonki ya tashi gaban jama'a karki manta akwai gidan tv da jaridu da redio a wajan, me kike tunani zai faru?" Samima ta dukar da kai cike da damuwa ta ce.
"To ke nan Umma ni a rayuwata babu abun da zan iya yi?"
"Ko kadan ba haka bane Samima,jarabawa ce, kuma Allah yana sane damu"
"To Umma ki min addua Allah yasa a fara lafiya a gama lafiya"
"Kullum ina miki Samima, sai dai na kara a kan wanda nake miki, yanzu ki wuce ki je ki shirya kar Suhail ya zo ya ta jiranki"
"To Ummana" Samima ta faɗa tana shigewa.
Nuren na zuwa gida sai da ya fara zuwa ya ga Momynsa kafin ya yi wanka ya tafi office, dan a office ya samu Abbansa, suka ci gaba da aikin dake gabansu, Samima kuwa tana gama shiryawa Suhail na zuwa ya dauketa suka wuce babban shop dinta, mutane har an fara cika, ko ina ga wulla maganar show din ake yi, sosai kayayyakin Samima suka yi kyau, ko da ta je sai da ta dinka wasu arnakun gown designer guda biyu wa kanta wanda zata yi fita dasu, kowa ya ga gown din sai ya yi magana a wajan, yayinda Suhail shi ma ya sake ɗinka wasu guda hudu ma wasu matan da za ayi fita dasu, sosai aka ƙa wa ta wajan fiye da tunani, aka jere kujeru na alfarma domin baƙi, tun da ta zo bata zauna ba, ta yi nan ta yi can, ta duba wannan ta duba wancan, wayarta dake hannunta ne ya ɗauki ruri tana dubawa ta ga Sauda ce, da sauri ta ɗaga tana cewa.
"Ƙawata ya aka yi? Fatan dai za ku zo din dai ko?" Sauda ta kwashe da dariya ta ce.
"Zuwa kai, idan kika ji zuwa ma ɗaya kenan, yanzu haka ma in gaya miki muna tare dasu Sarah da Sally, ke har da Hidayan Abbas, da anyi sallar magriba za mu zo, har dasu Momyn'mu, Yayan Sarah ma ya ce zai zo"
"Au har ya dawo daga lagos din ne?" cewar Samima dan Yayan Sarah yana aiki ne a lagos ne dan haka bai cika zama a adamawa ba ya fi zama a lagos.
"Eh ya dawo jiya, ya huta fa, amma wai a'a ya yi missing dinki zai zo ya ga show din ki" gaban Samima ya faɗi jin abun da Sauda ta faɗa, amma ta basar ta ce.
"To sai kun zo" daga haka suka yi sallama, ta ci gaba da ƙimtsawa, ya yinda wasu club su ma sun iso, wajan yamma team biyar sun bayyana inda jama'a har an fara cika, tsaye take a bakin gate din ta haɗe rai tana duba agogo tare da kallo kowace mota mai shigowa amma bata ga na shi ba, Suhail ne ya fito ya ganta ya ce.
"Ahh Samima,me kuma kike yi anan? Ke da ake nemanki a ciki, ba wuya fa sai ki ga lokaci ya tafi akwai wanda kike jira su zo ne?" kamar zata yi kuka ta ce.
"Eh Yaya Suhail, har yanzu Yayana bai zo ba, kuma fa shi ya ce min zai kasance tare dani da yamma amma na ji sa shuru, kai ina zaka je na ganka da makullin mota?"
"Zan je ɗauko su Umma da Baba ne, sai na biya na dauki ƙannena da Ummina na kawo su nan"
"To Yayana fa?" Suhail ya ce.
"Oho masa, ba shi ya ce zai zo ba, ki kwantar da hankalinki zai zo ai, yanzu ki koma ciki, ko kuma ki kira wayarsa"
"Yaya Suhail ina ta faman kiransa baya ɗagawa yanzu kuma wayar ma bata shiga" Suhail zai sake magana wata fashion ta fito da sauri gami da cewa.
"Mss Samima, rigar da Aisha zata saka fa ta ƙasa ya warware" ba shiri ta bi bayanta suka koma ciki Suhail kuma mota ya shiga ya ɗauki titi dan biyar ta kusa.
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
"Sha'awaaa!!!! Sha'awaaa!!!" da gudu Sha'awa ta fito daga banɗaki dama shigowarta kenan gidan, kuma kashi ne ya korota gida tana so ta gama ta fice, butar hannunta ta ajiye tana gyara zaman dankwalinta ta ce.
"Kaiiii Balki mi ye haka? Wannan kira sai ka ce ana gobara, ni ai har kin ban tsoro wallahi mi ye to!!?" ta fada cike da tsiwa, Balki ta ce.
"Iskanci, ni kike yiwa haka? Dan na zo miki da labari,kika san me ya kawo ni?"
"Kai kina da matsala wallahi Balki, to fadi me ya kawo ki, ko kuma ki zo mu fice danni kin san wallahi idan na zauna a gida na minti uku ji nake kamar ana hura min wuta, zo muje daga waje na san da cewa ba a gida nake ba, dan kafata kaikaiyi take min" ta ja hannun Balki, Asabe ta fito tana cewa.
"Ahh Shaleleta yaushe kika shigo?" Sha'awa ko tsayawa ba ta yi ba tana cewa.
"Inna ban jima da shigowa ba,kuma kashi ne ya koroni na gama, dan haka na fita" Asabe ta rike baki.
"Ohh Allah ni Asabe, kwata-kwata yarinya kafarki sai kace wacce taci kafar kare, zaman gida ya gagareki?" tunanin da Asabe bata taba yi ba kenan sai yau, a waje kuma Balki ta ce.
"Keee Sha'awa wallahi wani labari na ji yanzun nan daga cikin gari wai
akwai wani show din da za ayi na....ammm, kai oho ni dai na manta sunansa da turanci dan kin san nima ban iya ba, amma dai na ji ana cewa na fitattun kaya ne, ke a inda ma nake jin labari har da ɗan gidan ALHAJI IBRAHIM wato NURAIN wanda kike son din nan,kuma
Kamar har da Samima a wajan, kuma wallahi taro ne na manyan mutane in gaya miki, har da yan gidan tv da jaridu" waro ido Sha'awanatu ta yi ta ce.
"Jakar uba!! Nuren zai je kuma shine har da Samima? Wallahi nima babu abun da zai hanani zuwa"
Balki ta ce.
"Ai na sani shi yasa jikina na rawa na zo na gaya miki, da dare ne kuma kin ga kuma yanzu yamma ta yi, da anyi magriba ko isha'i sai mu wuce dan Zee Zee,Rakkys dasu Safiya duk za mu je"
"Ai Balki kinyi farin kai da kika zo kika gaya min, yanzu kawai je ki idan na shirya zan zo na same ku" Balki ta amsa da to ta kama gabanta, Sha'awa kuma ta koma cikin gida tana haɗe rai, da sauri Asabe ta tarota tana cewa.
"Lafiya kuwa Shaleleta? Kin fita kina fara'a amma yanzu kin dawo kina haɗe rai?"
"To Inna ba wai wannan shegiyar mai kama da aljanar nan bace Samima, wai yau akwai fitattun kaya da za ayi, Nuren zai je da sauran manyan mutane shi ne har da Samima a wajan,kuma Inna, ina ya kamata ace ni ce a wajan ko?" wuff Asabe ta ce.
"Kwal Uba!! Samiman banza Samiman wofi, ai ke ya kamata ki kasance a wajan Shaleleta, gaya min yaushe ne za ayi abun?" Sha'awa ta turo dogon bakinta tana fadin.
"Balki ta ce min da dare ne" wani murmushin mugunta Asabe ta yi ta ce.
"Shirya ki tafi abun ki rai kwance,zan yi maganin ƴar banza, kina da uwa mai sonki da kaunarki mai share miki hawaye, shirya maza ki tafi shaleleta,a kanki babu abun da ba zan iya yi ba" cikin murna Sha'awa ta miƙe jikinta na rawa, Asabe ta kai mata ruwan wanka kewaye, ta je ta wawwatsa ta fito ta shirya shap-shap ta fito tana ɗagawa Asabe hannu tana murmushi, Asabe ta ce.
"Su Samima manya, lallai yau za ayi taro da macijiya" ta cije baki cike da mugunta ta juya ta koma daki.
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
Sai shidda Nuren ya samu damar karasowa wajan, sai sauri yake ta zubawa a lokacin kuma har su Umma,Baba iyayen Suhail da Ƙannensa mata biyu, dasu Momy da Ƙanwar Momy duk sun zo, Suhail ne kuma ya je ya dauko su dukkansu, Samima kuwa har ta fara hawayen rashin ganin Nuren, ta sha kwalliya kamar ba ita ba, tana tsaye a cikin jama'a da wani maroon gown ta naɗe veil dinsa a kanta sai ka ce balarabiya, da ɗan
saurinsa ya karaso cikin wajan yana wulla idonsa ta inda zai hangota, ai kuwa nan ya yi tozali da ita cikin mutane tana magana, amma kamar wacce take kuka, ya gama matowa a kallonta ya ji an dafasa ya juyo da sauri ya ga Suhail ne, dan ajiyar zuciya ya sauke Suhail ya ce.
"Haba Nuren ina ka tsaya ne tun dazu fa, hankalin Samima ya tashi har kuka sai da ta yi" murmushi Nuren ya yi ya ce.
"Allah sarki My Baby, fitina ce da son yi min asarar hawayenta amma ai tasan dole ne na zo"
"To mun ji, muje ko?" cewar Suhail, suka karasa wajan Samima dake magana da mutane Suhail ya kira sunanta, tana juyowa ta sauke idonta a kyakkyawar fuskarsa yana mata tsadaddan murmushi, wani kyau ta ga ya yi mata, kamar yadda shi ma a nasa bangaren hakan ne ta kasance, turo baki ta yi tana matse ido, Suhail ya ce.
"ki kimtsa turo baki da shagwabarki idan mun kai ki gidansa kya yi masa daga baya, yanzu kun ga magriba ta gabato ku taho" ya yi gaba abun sa, ta dan kallesa ta gefen ido shi ma ita yake kallo, bayan sun shiga change room, ya dan fake idon mutane ya matso kusa da ita, ya ce.
"Sorry Baby, ki min uzuri, ki saki ranki, irin wannan kyau da kika yi haka? Kar fa idon maza ya yi yawa a kanki dan zan iya soke fitarki" bata san lokacin da ta saki murmushi ba ta juyo ta ce.
"Kai Yayana, ban da zolaya fa, ai kai ne zance kar yan mata su maka caaa a kai, domin sai dauke ido kake yi"suka saka dariya a tare, ya ce.
" ina zuwa" ya fice wajan su Momy ya je dan ya bar ta su gama kimtsawa, bayan Sallar magriba team 1 suka fara fitowa, inda jama'a ke musu tafi ana daukar hoto, su Samima kuma su na can ciki ana ta faman make'up, duk da ita ba wani make'up ta yi ba, sosai yan team 1 club suka baje basirarsu su ma, basu da gamawa ba sai takwas, team 2 ne zasu fara gabatar da nasu kafin team 3 shi ne nasu Samima, sai misalin karfe tara saura kafin su Sha'awanatu da kawayenta su shidda suka iso, da kyar aka bar su ma suka shiga, su na zuwa suka samu kujera suka zauna su na ganin show, sai can wajan misalin sha ɗaya saura kafin team 3 suka fara fitowa, su ne su Samima, a hankali ta ɗan leko inda jama'a suke zaune tana lekarsu ta labule, caraff suka haɗa ido da Nuren ya sakar mata murmushi tare da daga mata babbar yatsarsa alamun karfafa mata guiwa, itama murmushin ta yi masa inda aka basu damar fara fitowa, ita ce wacce zasu fita wajan karshe dan haka ta koma ciki masu fita su na kan fita, wayarta ce ta yi kara ta duba ta ga Sauda ce, da sauri ta daga wayar ta sa a kunne Sauda ta ce.
"Woww Ƙawata, wallahi fashion dress dinku sunyi kyau, wallahi duk sun fi na team 1to2 kyau, gaskiya kawata na jinjina miki Allah ya ba ki basira, Anty Badi ta ce wacce ta fito ta uku ta yi mata kyau tana so" dariyar farin ciki Samima ta yi ta ce.
"Na gode Sauda, ashe kun iso, na ɗauka ai ba ku ma zo ba tukunna"
"Waaa!! Tab ai in gaya miki tun magriba muka zo, nasan ba zamu samu ganinki ba sai an gama" Samima ta ce.
"Eh haka ne kuma wallahi"
"To shi kenan Ƙawata sai mun ganki ko?" Samima ta yi murmushi gami da cewa "ok sai kun ganni" daga haka Sauda ta ajiye waya suka ci gaba da kallon masu fitowa, Sha'awanatu zaune sai wulla ido take yi inda zata hango Nuren amma bata gan shi ba, ga dai manya mutane jiga-jigai masu ji da naira gami da izza duk sun bayyana a wajan, Samima na tsaye gabanta sai faduwa yake yi, wata mai suna Ummiee fashion ta ce.
"Mss Samima, ki shirya mana ki canza kaya kin kusan fita fa" jiki a sanyaye ta amsa da kai ta wuce ta canza kaya zuwa dress din da ta dinka dazu, wani fininanniyar kyau Samima ta yi, ta ɗauki veil ta yi rolling din kanta da shi, Ma sha Allah ake ta faman faɗi ta koma gefe ta tsaya gabanta na dukan uku-uku, sake lekowa ta yi suka haɗa ido da Ummanta, Umma ta ga duk ta canza da ido ta yi mata alaman da menene? Amma ta girgiza kai, Umma ta yi mata murmushi, da kyar itama ta mai da wa Umma murmushin sannan ta koma layi dan ita ce a karshe a wa inda zasu fita, kamar da mintuna biyar haka, suka fara fita, tana fitowa duk da ita ce a karshe amma take ido ya koma kanta, inda maza da mata suka mato a kallonta, wasu na yaba dress din da ke jikinta, wasu kuma kyawunta kawai suke kallo, jiri Samima ta fara ji na ɗibarta, take kanta ya yi wani mummunar sarawa, jikinta ya dauki zafi radauu, ga wani radaɗi mai zafin gaske, ɗago idonta ta yi wanda suka yi jajur lokaci guda, ta ware ta kalli dimbin al'umma da suke wajan ga ana video ana daukar hoto, idonta ta sauke a kan Nuren wanda shi ma ya kura mata ido yana son gano halin da take ciki, duk da kishi duk ya tirniƙesa ganin yadda ake kalle masa mata, haka ta ɗaure ta ci gaba da tafiya, tana zuwa gaban mutane ta ji kafafunta ya fara harɗewa, ihu take son yi dan tasan ta shiga uku ta mutu kawai dan macijiya zata koma hawaye ne suka ballo mata, juyawa ta zo yi amma ta gagara, a hankali ta dukar da kanta kasa ta ɗan daga gown dinta ta ga kafafunta ya fara sabulewa, kallon Nuren ta yi hankali tashe ta hau girgiza kai alamun a'a, tana kallon jama'ar dake wannan waje, magana aka yi mata akan ta juya ta tafi amma ta kasa tafiya, nan fa ido ya tsaya a kanta caaa, da sauri Nuren ya miƙe har yana ɗan buge wanda suke gabansa duk da shi ma a kujerar gaba yake, Umma tuni ta hau goge hawaye tana adduar Allah ya fidda diyarta, wuff Nuren ya zo gabanta yana murmushi yana ɗagawa mutanen wajan hannun yana yaƙe, a kunnenta ya raɗa mata "taho" girgiza masa kai ta yi tana kallon kafarta, murmushin yaƙe Nuren ya ci gaba da yi, kawai yasa hannu ya ɗauketa cak ya juya da ita, yayinda mutane dayawa aka saki baki ana kallonsu, wasu kuma suka shiga alhinin miye dalilin da yasa yaron Alhaji Ibrahim mai Agogo daukar Samima? Kowa da abun da yake tunani a ransa, wasu kuma abun ya burgesu inda suka ga dacewar Nuren da Samima, Yayan Sarah mai su na Sharif cikin haushi ya ce.
"Sarah wannan guy din fa wanene?"
Sarah ta ce.
"Cousin Brothern'ta ne" Sauda ta ce.
"Da wuya idan babu soyayya a tsakaninsu, dan komai idan Samima ta yi za ki ga yana kishi a kanta" tsaki Sharif ya yi, ya ɗan musu tsawa da cewa su rufa mi shi baki, lokacin da Nuren ya dauki Samima ya fice da ita zuwa wani daki ya ajiyeta ya fita dan ya dauko mata magani, ya gayawa Suhail da ya ci gaba da kula da komai ya tafi dai-dai yadda ya kamata a lallaba a gama, zai dauko hayaki a motarsa ya mata ne, Suhail ya amsa da to, ya koma wajan jama'a Nuren kuma ya yi waje, ashe Sha'awa tana biye dasu, tana ganin Nuren ya yi waje ta yi wajan Samima domin ta yi mata rashin mutunci, tana shiga ta samu Samima tana juyi a kasa, kugu Sha'awa ta riƙe tana yiwa Samima gatsali bata ma kula da jelar maciji da yake yawo a jikin Samima ba, tana ɗaga ido ta ga Samima ta koma macijiya, ihu Sha'awanatu ta saka tana neman guduwa nan take Samima ta bi kanta da sara, inda ta sareta a wuya, nan Sha'awa ta zube kasa, Samima ta sake sarenta a goshin sannan ta sake kai mata sara kafaɗa, tana shirin ta sake kai mata wani kenan Nuren ya buɗo kofa, salati ya saka gami da watsawa Samima ruwan wani magani sannan ya kunna mata hayaki, nan take ta zube ƙasa, dai-dai nan Umma ta shigo dakin ta ga mutum a kwance, salati Umma ta saka ta yi kan yarinyar, ta ɗagota nan ta ci karo da fuskar Sha'awa, salati Umma ta saka tana dafe kai ta ce.
"Innalillahi wa inna ilayhirrajiun!!! Sha'awanatuuu!!!! Sha'awanatuu!!!" Umma tana kiran sunanta tana jijjigata cikin tashin hankali Nuren ya ce.
"Umma Sha'awa!!?"
"Eh Nuren, Sha'awa ce wallahi Yarinyar Asabe, na shiga uku!! Sha'awanatu!!?"
Nan suka tsaya cirko-cirko, sai wajan awa ɗaya kafin Samima ta farfado ta yi arba da tashin hankali, Umma na zaune a gefe idonta suntum, ga Momy, Abba,Baba, Suhail,Nuren duk sun zuba hannu a kumatu, da sauri Samima ta yi kan Sha'awa tana ambata sunanta
Amma ko motsi Sha'awa bata yi, hummm!! kuka Samima ta sa ta ce.
"Dan Allah ku min magana, ko a kai Sha'awa asibiti, kar ta mutu dan Allah!! Wayyo Allah na!! Sha'awa!!?? Dan Allah Yayana mu kai ta asibiti mana" kuka sosai Samima ke yi, zuwa wani lokaci sai ga Baba Malam da shi da wasu mutane guda uku, su Momy da Umma, da Baba ne suka taimaka aka dauki Sha'awa aka fito da ita, an zo sakata a mota dai-dai kan idon Ƙawarta Balki da Murja, da gudu suka zo su na tambayar me ya sameta, Suhail ya ce.
"Maciji ne ya sareta, idan kun koma gida ku gayawa Gwaggo Asabe gobe da safe ta je gidan Baba Malam in da za ayi wa yarta magani" cikin tashin hankali su Balki suka kasa motsi, su Baba Malam suka wuce da Sha'awa, su kuma su Nuren suka koma ciki, sai wajan karfe biyu aka gama yayinda aka ba wa Samima award dan kuwa team dinta ne suka fi rinjayen jama'a, da kyar ta tsaya ta karbi award din idonta a kumbure, an dai samu an lallab'a jama'a aka watse, Suhail ya ba wa sauran ma'aikata umarnin su kimtsa komai su zasu wuce gida, mota Samima ta shiga ta hau rera sabon kuka, daga wajan show din basu zarce ko ina ba sai gidan Baba Malam a daren, ko da suka isa nan Baba Malam yake shaida musu da cewa Allah ya yiwa Sha'awanatu rayuwa, nan take Samima ta yanki jiki ta faɗi sumemmiya, wa innan bayin Allah yadda suka ga rana haka suka ga dare, da asuba su Balki suka je gidan Asabe suka shaida mata da cewa ai maciji ya sare Sha'awanatu tsakar dare, tana gidan Baba Malam ana yi mata magani, wani ihu Asabe ta saka gami da ficewa da gudu ba mayafi ba takalmi, a haukace ta gidan Baba Malam , tana isa ta shiga tana faɗin ina yarinyarta,ina Shalelerta, a wannan karon dabara ce ta fadowa Suhail ya ce.
"Amm Gwaggo Asabe ki kwantar da hankalinki ai haka dama Allah yake ikonsa, yanzu haka da kika ganmu muna ta faman alhinin abun da ya faru da Sha'awa ne, kuma ba kowani maciji bane ya sari Sha'awa illa Samima gata nan" nan Asabe ta yi kan Samima tana shirin kai mata shaƙa, Nuren ya fizgo matarsa ya sa ta a bayansa yana haɗe rai, Suhail ya ce.
"A'a Gwaggo Asabe, abun bana zuciya bane zo ki ga ƴarki, nan ya ja ta izuwa inda aka kwantar da Sha'awa an lullub'eta, Suhail ya yaye mayafin, ihu Asabe ta saka ta rungumo Sha'awa tana faɗin.
"Dama ke ta sara? Me ya kai ki wajanta da har ta sare ki Sha'awana!? Wayyo Shaleleta" Suhail ya ce.
"Gwaggo Asabe yanzu ba lokacin kuka bane ki bari kyayi daga baya, ki ceto rayuwar ƴarki idan kina so" da sauri Asabe ta miƙe tana cewa.
"Fada min me zan yi" murmushi Suhail ya yi a ransa ya ce "Asabe lokacinki ya yi da izinin Allah".
"Ammm, Baba Malam ya ce abu daya zai sa Sha'awa ta samu lafiya, shine ki faɗi inda kika binne maganin da kika mai da Samima ta zama macijiya, kina haƙowa Shalelerki zata farka, haka ne ko Baba Malam?" Baba Malam ya gya ɗa kai alamun eh, Suhail ya ce "to Gwaggo Asabe karki bata lokaci maza faɗa mana a ina kika binne?" cikin ficewar hankali Asabe ta ce.
"A can cikin kauyen jatau na binne" can wani kauyen dake ƙasa sosai da adamawa kauyen ma daji ne, Suhail ya ce.
"To maza kije ki haƙo ta" da gudu Asabe ta fice, su Umma,Momy,Baba,Abba,Nuren Samima,Baba Malam suka bita da kallo kafin su mai do da kallonsu kan Suhail, Nuren ya ce.
"Suhail, me ya sa zaka yi mata karya? Ai da ka fada mata Sha'awa ta rasu"
A masifance Suhail ya ce.
"Sai kuma aka gaya maka idan tasan cewa yarinyarta ta rasu zata faɗi inda ta binne asirin da ta yiwa Samima ne? Idan ka lura a yanzu dubun Asabe ya cika, dan kuwa yanzu zata girbi abun da ta shuka ne" Baba Malam ya ce.
"Tabbas hakane maganarka Suhail, yanzu abun da za ayi bari na aika a kira Malam Basiru ya zo ayi wa wannan yarinya sutura a kai ta makwancinta" haka kuwa aka yi kafin ɗan wani lokaci unguwa ta ɗauka Allah ya yi wa Sha'awanatu rasuwa sakamakon saran maciji, inda da yawan yan unguwa suke harin Samima, dan haka a ranar Samima bata iya fita ko nan da can ba, Asabe kuwa ba ita da dawowa ba sai washe gari, kafin ta dawo tsakar dare Samima ta hau ihu inda wani baƙin hayaki ke fita daga baƙinta tana zuba attishawa kamar zata shiɗe sosai Umma da Momy suka daddanneta, bayan ta gama ne aka yi mata hayaki ta hau bacci, ko da Baba Malam ya dubata a fili ya furta "Alhamdulillah" gami da cewa yanzu Samima ta dawo dai-dai, hawaye masu zafin gaske ne suka zubowa Umma, a kofar gidan Baba Malam ake karban gaisuwar Sha'awa, yayinda mahaifinta Malam Basiru kansa ya daure ya rasa mai ya faru da shi tsawon wasu shekaru, sosai ya rungume ƙaninsa Malam Nasiru mahaifin Samima su na kuka tare, kamar daga sama suka ga mata a kan su baki a gefe ga shin kanta kamar wacce wutar lantarki ta kama, sai aikin soshe-soshe take yi, ga wani uban warin dake tashi daga jikinta mai bugar da mutum, da karfi ta ce.
"Ina shaleleta!!" sai a sannan ne aka ganeta, Baba Malam ya ce.
"Asabe!!? Ke ce!!?" murguɗa masa baki ta yi irin na zautattun mutanen nan, Suhail ya ce.
"Asabe sai dai hakuri, amma kin ga zaman mun nan zaman makokin ƴarki muke yi, dan ta cika tun a daren jiya, nayi miki haka ne dan ki haƙo asirin da kika yiwa Samima" ihu Asabe ta saka ta fara birgima a kasa tana faɗin mugayen aikin da ta aikata, yayinda wasu ke bin ta da mugun kallon Mamaki, Malam Basiru ya miƙe ya yi kan Asabe yana shirin rufeta da duka, Baba Malam ya hanasa ya ce.
"A'a ka rabu da ita ta ji da abun da ke damunta ma ya isheta" nan take Malam Basiru ya ce.
"Allah ya isa tsakanina dake Asabe kin cuceni!!! Kin cuceni!!! Na tsaneki!!! Na tsaneki!! Na sake ki saki ukuu Asabe!!" ihu Asabe ta saka ta miƙe ta zunduma da gudu tana fadin "wayyo ni wayyo ni Asaberuwa" ta wani bangare sautin aljanu ne ke tashi su na gaya mata ta gamu da bala'i, dauke ta suka yi cak suka mai da ta ramin da ta binne asirin da ta yiwa Samima suka jefata ciki,nan macizai suka rufu akan Asabe su na sarinta tana ihu, har ta mutu a yashe a jeji babu mai mata wanka bare sallah.
😭😭😭
Innalillahi wa inna ilayhirrajiun, Allah ka rabamu da son zuciya da hassada da kyashi da bakin ciki, Allah kasa muyi kyakkyawar karshe 😭😭😭 Allah ka yafe mana ka rabamu da bin hanyan b'ata wanda a karshe dana sani ne marar amfani, jin dadin duniya kalilance, duk yadda zaka yi ma wani dan uwanka mugunta na ɗan lokacine dan Ubangiji yana jiranka a madakata 😭😭
Allah ka yafe mana, Astaghfirullah wa'atubu ilayka ya Allah.
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 agurguje.
Bayan wata ɗaya komai ya dai-daita, a rayuwa komai mai wucewa ne, ba a sake ganin Asabe ko jin labarinta ba, yanzu kuma Samima ta wanku a idon yan unguwarsu , inda aka san da cewa ai matar Nuren ne dan haka sai shirye-shirye ake yi dan ta tare a gidan mijinta, bayan sati daya kuma ta tare a katafaren gidanta na alfarma, Nuren ya canzawa iyayen Samima gida, sosai Samima ke ganin gata a waja mijinta
Wani lokaci ma har tunani take yi anya ita ce kuwa? Bayan tarewar'su da wata shidda aka sha shagalin bikin Suhail rayuwa sai dai ace Alhamdulillah, Ma sha Allah.
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
*_BAYAN SHEKARA HUDU_*
wasu kyawawan yara ne su biyu suka fito da gudunsu su na dariya gami da zagaye garden din gidan wande daga gefe guda kayan wasansu ne, yaran ba zasu wuce shekaru uku ba, da ka gansu kasan cewa yan biyu ne kyautar Allah, Mom dinsu da Dad din su ne suka fito su na murmushi, ta wani kara kyau ta goge tayi ƙiba, kallonta ya yi ya ce.
"My sneak, na gode sosai da bani kyawawan yara da kika yi masu kama dake ina alfahari dake ina sonki My Sneak" da shike haka yake kiranta da shi, hannunsa ta kama suka zaune a kujera mai lilo, ta ce.
"Ni ce ya kamata nayi maka godiya mai sona, ka so ni a lokacin da jama'a suka gujeni wasu ma su na neman kasheni, ni ya fi cancanta da na gode maka, sabida a rayuwa ba zaka gane mai sonka tsakani da Allah ba har sai ka shi ga damuwa, kullum tunanina da mai zan saka maka alkhairin da ka min Yaya Nuren, ina matukar kaunarka Mijina" rungumeta Nuren ya yi ya ce.
"Ai kin gama biyana Hajiyata, ga kyawawan yarana twins, Khalil da Khalisat, ya faɗa yana kwalawa yaran kira wanda suke wasa abun sha'awa suka zo da gudu ya haɗe su ya rungumesu duka yana jin son su da kaunar su.
TAMMAT BI HAMDULILLAH.
Duka duka a nan na kawo karshen gajeran labarina mai suna *_SAMIMA MACIJIYA CE_* abun da na rubuta daidai Allah ya bamu ikon aiki da ita kuskurena kuma Allah ya yafe min.
*_A GASKIYA KUN SO LITTAFIN NAN FIYE DA TUNANINA, INA GAIDA MASOYANA WANDA NA SANI DA WANDA BAN SANI BA INA MUKU FATAN ALKHAIRI A DUK INDA KUKE, INA FATAN ZAKU BANI HADIN KAI A SABON GAJERAN LABARINA NA GABA MAI SUNA (DA NA SANI NA) NA GODE SOSAI SADUWAR ALKHAIRI_*.
UMMU AHLAN TAKU CE👍