hindatu a lokacin tashiga Toilet yakai sau 5,ganin har qarfe 3 angon bai shigo ba yasa tadan kishingida, tashi kawai tai taga 10:30 na safiya,cikin mamaki ta miqe saidai kuma wata shegiyar yunwa yasa cikinta ya fara bada wata qara,daqyar ta iya shiga toilet ta watsa ruwa tareda dauro alwala,wata baqar jallabiya ta zura da hijab tai sallah sannan ta fara tunanin abinda zataci, miqewa tai ta bude qofa a hankalin,tsaf taga falon babu komai hakan yasa ta fito ta fara laluben kitchen, can ta hango qaton kitchen din nata wanda yasha kaya,zan iya cewa babu abunda ba'a zuba ba, da sauri ta qarasa ciki ta dauko qwai tana qoqarin fasawa taji wayarta na qara,tsaki taja ta ajiye tai dakinta da saurinta, cwt indo taga ya fito a screen din yasa tai saurin dauka ta kafa a kunnenta, sautin nishin Aysha kawai takeji yana fita da qarfi da kuma sauri2, a rude ta fara hello aysha! Aysha lafiya kuwa? Aysh!!! Help me hindatu zan mutuuu Aysha ta fada cikin wata wahalalliyar murya, a tsorace Hindu tace labour ne yazo miki aysha! Ina ya adam! Ganinan zuwa ta fada tareda katse wayar, purse din datazo dashi jiya tai saurin dauka tareda ware mayafin abayar jikinta tai saurin ficewa daga gidan
Kamar zata tashi sama haka take tafiya tsabar sauri, batasha wata wahala ba tasamu mota, ko canjinta bata tsaya karba ba tafada gidan Ayshan tana qwala mata kira, a daki ta sameta tsugunne ta hada gumi sosae,da sauri ta qarasa tana qoqarin dagota taga jini, ya salaam,Aysha haihuwar ce Ashe, gashi ba kowa a gidan nikuma ban iya driving ba, idea ce ta fado mata ta fito qofar gidan,samarin dake zaune a qofar wani gida ta tambaya ko akwai wanda ya iya mota wani yace ya iya,roqonshi tai ya taimaka ya driving dinsu akai Aysha asibiti,ba musu ya taho dan babu laifi Adam yana musu dan hasafi,daqyar ta iya ruqo Aysha tasata a bayan motar sannan ta kwashi abunda tasan za'a buqata, tun a bakin qofa take qwalawa doctors d nurses din kira,aiko babu bata lokaci
[21/04, 22:47] Hassan India: Miss collapse
👠 SATAR FITA💃🏽
(123)
,aiko babu bata lokaci suka karbeta,sai a lokacin tai tunanin kiran mutane,Adam ta fara kira ta fada masa asibitin dasuke sannan ta kira ummy da umma harda su khadija da ruqayya,cikin en mintuna suka qaraso asibitin kusan tare.
Da sauri suka fara tambayar hindatun ya Ayshan take, tana labour room kawai take iya cewa dan gaba1a rude take, bata taba ganin mace na naquda ba sai yau, Ashe haka haihuwa take? Gaskiya wanda baiyiwa iyayensa biyayya ya tabe, gaba1 zaman arziqi ta kasa kusan 3 hours harta nemi yunwar datake ji tarasa saboda sautin ihu da salatin Aysha ba qaramar tayar mata da hankali yake ba, sai qarfe 2:40 suka farajin sautin kukan baby,Aysha ta sauka kenan, da azamarsu suka miqe lokacin doctor ya fito,da murmushi ya taresu tare da fadin Alhamdulillah,is a baby boy, zokuga washe baki gurin hindatu kamar itace angon qarnin, da saurinta tai hanyar dakin zata shiga doctor din yai saurin katseta yace sorry madam,ana gyarasu ne ita da babyn, ki basu 30 mins.
Dawowa tai ta tsaya tanaji doctor na fadin a kawo mata abinci d tea mai zafi,umma ce takira gida tasa sabuwar mai aikinta t hado musu, 30mins ma bata qarasa b aka turo Aysha zuwa dakin Hutu, hindatu ce gaba wajen shiga,itace ta fara daukan babyn, wow! Ya rukky yaron nan kamarmu 1 amma yayi hasken mamanshi, gaskia ka hadu hindatu ta fada tana kissing dinshi, da babanshi dai, ta ina kukai kama khadija ta fada tana qoqarin karbar yaron ummy tace to abunda yayi hindatu ai shiyayi Adam,da duka su biyu yaran suke kama,dana ganshi saina tuna yaya jibril, Allah yajiqan shi kowa ya fada a sanyaye, atiqa mai aikin umma tashigo dauke da qaton basket,aroma din girkin ne ya tunawa hindatu yunwar datake ji, farfesun hanta ne da macaroni sae tea and bread d chips, zauna kici Aysha,umma tafada tareda miqawa Aysha tea din,a hankali ta karba ta fara sha hindatu ta sauko daga gefen gadon ta fara zuba abincin, a gaggauce takeci tana hadawa d tea din,qoqarinta tai saurin
[21/04, 22:47] Hassan India: Miss collapse
👠 SATAR FITA💃🏽
(124)
A gaggauce takeci tana hadawa d tea din,qoqarinta tai saurin qarasawa ta karbi babyn dake hannun Adam, sukuwa su ummy mamaki ne ya kamasu yanda take tura abincin har saida khadija tace hindatu wai ba tareda sa'ad kuka kawota asibitin ba? Bamu ganshi b...
Sauke lomar data dauko tayi tareda hade rai,har ga ALLAH ta manta zancen wani miji balle aure, to ita a inama ta ganshi, rabonta datasa shi a idonta tun ranar budar kai dan ko jiya muryarsa kadai taji. Ana tambayarki umma ta fada fuskarta a gimtse. Turo baki tai a qule zatai magana ya turo qofa da sallamarsa. Ba qaramun bugawa qirjin hindatu yayi ba,Sam batayi tsammamin zuwansa ba,da sauri tai qasa da kanta lokaci 1 gumi ya fara keto mata,shima b qaramin mamakin ganinta yayi ba,to yaushe ma ta fito bai saniba,lallai yarinyar nan.
Dakewa yayi ya qarasa suka gaisa da ummy da umma dakuma ragowar sisters din nashi sannan ya qarasa kusa da Adam, gaisawa sukai yana masa congratulations sannan suka gaisa da Aysha, karbar babyn yayi yana kallo with full adoration,yanason yara sosai a rayuwarsa, musamman daya dauki wannan yaron sai yakejin dama ace dansa ne na cikinsa. Ummy ce ta katse masa tunani ta hanyar cewa, aida harna fara cigiyarka danaga hindatu ita kadai,nayi zaton ba tare kukazo ba danaga har yanzu baka shigo ba.
Qiris yarage jinin hindatu yahau tsabar tsurewa ganin irin kallon da sa'ad yake watsa mata,a tunaninta zai tona mata asiri amma saiya dake yace tare muke ummi,kawai nadan fita ne wata sabga.
Ohh,to madallah ai saiku tafi yanzu tunda gashi ta sauka lfy nasan yanzu za'a bada sallama.
Da sauri hindatu tace aa ummy yayi tafiyar ni sai anjima tunda ba tare mukazo ba.
Ba tare kukazo ba kuma? Umma ta tambaya cikeda zargi. Sai a lokacin hindatu ta ankare da abunda tace, ta rasa abunda zatace gashi kowa kallonta yakeyi. Dakewa tayi ta qaqalo murmushin yaqe tace kai ummah!bawai nufina haka ba,sonake nace ya tafi nizan taho anjima amma tunda ummy tace
[21/04, 22:48] Hassan India: Miss collapse
👠 SATAR FITA💃🏽
(125)
sonake nace ya tafi nizan taho anjima amma tunda ummy tace mutafi to sai an jima,tai saurin miqewa ta fice babu ko waiwaye saboda kar a sake watso mata wata tambayar.
A qofar dakin ta tsaya zuciyarta na bugawa da sauri2,gaba1 ta tsorata tana tunanin irin hukuncin da sa'ad zai mata taji an bude qofar. A razane ta juyo sukai kicibus da khadija, kallon2 suka shiga yiwa juna, khadija ce tafara janye idonta ta tabe baki tareda cewa hindatu daga kaiki dakin miji harkin fara gwada mishi halin naki? Wani hali kuma? Ta tambaya tareda tsuke fuska. SATAR FITA mana, ko an fada miki idan kinyi qarya baxan ganeba,wlh hindatu kiji tsoron Allah,aure ba kamar yan matanci bane. A tsiwace ta kalli khadija tareda watsa mata wani kallon banza ta daura dacewa kinga madam ina ruwanki,inace dai yayi muku bayanin komai dan haka ba ruwanki,ni bana shiga harkokin da suke tsakaninki da mijinki dan haka kema banida buqatar kina shiga harkokina da nawa mijin ta qarashe tareda kallon gefe. Ga mamakinta sai ganin sa'ad tayi tsaye a daya gefen shi a lallai waya yake amsawa amma hankalinsa gaba1 yana kansu, Sosai yake mamakin rashin kunya irin ta hindatu,ganin ta gane yana gurin yasashi barin gurin yayi hanyar fita daga asibitin khadija tabisu da kallon mamaki.
Motar samfurin corolla S maroon colour ya bude ya shiga tareda murza mata key,ganin hakan yasata qarasawa,bayan ta bude ta shiga sai faman hade rai takeyi duk kuwa da dukan 3-3 da qirjinta yakeyi, A.C ya kunna,sanyin A.c ya maye motar ga qamshi dake tashi maimakon taga sunyi gaba kawai sai gani tayi ya kifa kansa akan sitiyarin motar,tsaki taja qasa2 tana gyara zamanta,wasa2 har kusan 1:40 mins suna gurin, gashi tayi qoqarin bude qofar tajita a garqame wato yasa lock kenan baqin ciki ya cikata,ta cika tayi fam kamar ta fashe,to me wannan mutumin yake nufi dani? Ta tambayi kanta tana qara gyara zamanta, ganin ba sarki sai Allah yasata bude baki tace wai yaushe zamu tafine? Nifa na gaji
[21/04, 22:48] Hassan India: Miss collapse
👠 SATAR FITA💃🏽
(126)
Nifa na gaji gaskiya. Dagowa yayi ba tareda ya juyo ba yace ashe kin shigo? Kut! Rainin wayo ma kenan nufinsa baima San na shigo b. Shiru kawai tayi ta kasa magana tsabar takaici,kusan 5 mins b wanda yayi magana can yace amma kinsan dai niba drivern ki bane koh?
Harara ta watsa masa ta cikin mirror sannan ta bude qofar tajita a bude,yanxu ya bude kenan tafada a zuciyarta, gaban motar ta dawo fuskarta a hade tana karkata qafa yaja motar.
Ko parking bai qarasa ba tabude motar da sauri tayi cikin gidan kamar zata tashi sama, dakinta ta fada ta rage kayan jikinta tayi wanka sannan tafito ta fada kitchen,yunwa sosai takeji dan dazu kasaci tayi.ga mamakinta kawai sai ganin sa'ad tayi cikin kitchen din,sanye yake d wando 3 qauter baqin sai singlet itama din baqace,hankali kwance yake girkinsa baima san tana gurin ba,macaroni ce yadafa sae qamshi takeyi ya dauki plate ya diba sannan ya juyo, tanan tayi kasaqe tana kallonsa,shikam kallo daya yayi mata ya kauda kansa, a falon nata yayiwa kansa mazauni saboda ma'aikata gidan sun cigaba da aikinsu a nasa bangaren,hindatu kam tana ganin ya fice tayi saurin fadawa kitchen din ta bude tukunyar,yawunta har tsinkewa yakeyi tayi saurin gyara zamanta akan stool din dake kitchen din tafara tura abincin, tsabar dadi batasan sanda ta tashi da macaronin ba, sannan tafito hannunta riqe da robar ruwan faro tanasha, a falon ta taddashi zaune yanacin nasa abincin har yanxu ko rabi baici ba,a zuciyarta tace iyayin kawai,gaban T.v ta qarasa ta harhada komae ta kunna star times, tashar st. Novella takai tana gyara zamanta fuskarta dauke da fara'a, the lying heart suke haskawa tana bala'in son actor din film din saboda haduwarsa, murmushI kawai take dokawa duk sanda aka haskoshi,haka kurum sa'ad yaji ransa yana baci ya tashi ya kashe TV din gaba1, rai a bace take kallonsa harya dawo ya zauna, a fusace tace wannan wani irin wulaqanci ne! Ina cikin kallo kawai xakazo ka kashemun!
[21/04, 22:48] Hassan India: Miss collapse
👠 SATAR FITA💃🏽
(127)
Baiko kulata ba yacigaba dacin abincinsa,itama a zuciye ta tashi taje ta kunna TV ta dawo, remote din ya dauke da sauri ya canza tasha zuwa zcinema, wani film suke haskawa waishi police, dukda shi b masoyin kallo bane amma haka kawai yaji yana sha'awar kallon film din, hakan ba qaramin sosa mata rai yayi ba ta miqe tayi dakinta a fusace.
Ba ita ta fitoba sai qarfe 9:30 shima yunwa ce takoro ta, cikin sa'a taga ya dafa shinkafa da miya, dadi ya kamata ta zauna ta lodi abincinta sannan ta kira Aysha,hira sosae sukeyi d AYSHA tana tambayarta labarin baby.
Hindatu dason yara, kema nan d 9 months ki daure ki sullubo mana baby,
Uhmm bakida hankali Aysha,yanzu idan kikaji ance na haihu nan d 9 months baza kiji tsoro ba?
Tsoro kuma? Tsoron me keda kikeda miji? Zata sake magana hindatu ta yanke wayar.
Zaman sa'ad da hindatu dai gashinan gashinan zamuce,dan sam basayin shiri,kullum hindatu a cikin bala'i take dukda kuwa ba kulata yake ba,a haka akai sunan Aysha yaro yaci sunan kakansa jibril amma dady sukece masa.
2wks kenan da auren. Ita kadai take masifar zaman gidan ya gundireta gashi umma ranar sunan Aysha tasha fada a gun umma saboda taje sunan batare da tambayar mijinta ba.
Sallama taji ta amsa a daqile,tunaninta yan uwansu Aysha ne dasuketa sintiri tunda aka kawota,tsalle ta doka ta rungume daya daga cikin yan matan tana cewa Fatima magaji! Yaushe rabon duniya? Harara wacca ta kira fatiman ta watsa mata kafin tazauna akan kujerar tace abunda yafi hakan m ai fada zakiyi tunda har kikai aure baki fadamin b.
Magaji ba haka bane wlhy, kinsan auren nawa a gaugace akayi kuma bawai nice nayi gayyatar ba Aysha ce,amma kiyi haquri. Ba komai hindatu,dama card din bikina na kawo miki dis Friday kamu,ta fada tana zaro cards din,dan Allah hindatu kizo. Haba Fateemah harsai kin roqa,insha Allah zanzo,bari nadan kawo miki abun tabawa,ta miqe Fatima tai saurin riqota tareda miqewa tace barshi amarya, wlh a hanya muke
[21/04, 22:48] Hassan India: Miss collapse
👠 SATAR FITA💃🏽
(128))
Wlh a hanya muke da angon,mun gode.
To bari nazo mu gaisa da angon,tafada tana gyara zaman mayafin data dauko, fitowa hindatu tai suka gaisa da angon sosae suka tafi, fuskarta dauke da fara'a ta juya tashiga gidan. Tura gate din tayi taku 1,2 taji an fincikota an hadeta da bango, a gigice ta bude baki zatai ihu sukai ido hudu da sa'ad, iya zamanta dashi bata taba ganin bacin rai irin wannan a tare dashi b.
Wani dan iskan ne wancan! Ya fada a tsawace,a tsorace hindatu tace saurayin friend dina ne...fateem..mah..katin bikinta suka kawomin. Sassauta riqon yayi amma har lokacin ranshi a bace yake yace shine dan kin rainamun wayo zaki fita a haka? Kamar b matar aureba, bakida hankali ne! Shuru tai jikinta na rawa. Tsaki yaja d qarfi ya juya zai tafi tace to xancen zuwa bikin nawa fa!
Wani mugun kallo y zuba mata yace b inda zakije.
Wlh ba abunda zai hanani zuwa ta fada qasa2.
Washegari ta kira Aysha tana mata zancen bikin.
B inda zanje hindatu,jego nakeyi fa kema kinsan bazanje ba, kema yaushe kikayi auren dazaki fara gantali.
D qarfi taja tsaki tace kinga Aysha b shawara n tambayeki b balle nasiha,tunda kince bazaki je b kisha zamanki nikam wlh sai naje.
Allah y kyauta toh,Aysha ta fada hindatu tace Ameen.
Sosai hindatu ta tsara kwalliyarta,b wanda zai kalleta yace mata matar aure, qarfe 5 tafice daga gidan ranta fess ta qarasa gidan, kasancewar gidan babba ne yasa aka ware musu daki daban n qawayen amarya,hira sukeyi sosae d shewa wajen qarfe 6 saiga maman amarya tashigo,drawer dake dakin tafara binkitawa a rikice,tass ta zubo da kayan amma bataga komai b, a rikice ta juyo da dubanta kansu tace ina akwatin sarqar dana ajiye a cikin drawer nan?
Sarqa kuma? Suka tambaya a tsorace suna miqewa,kunga banson rainin wayo, wlh saikun fito da kayan mutane. Kafin kace me mutane sun taru. Hankalin en matan a tashe suka fara raba ido s rantse2, kunga malamai wannan bazai kai muku ba, zaifi muku Ku fito da kayan
[21/04, 22:49] Hassan India: Miss collapse
👠 SATAR FITA💃🏽
(129)
Hankalin en matan a tashe suka fara raba ido s rantse2, kunga malamai wannan bazai kai muku ba, zaifi muku Ku fito da kayan mutane kokuma mu kira police. Wata mata tafada.
Ganin dai sunqi fito s sarqar yasa matar fita sae gata d motar yan sanda, su 6 ne en sanda suka wulla a bayan motar suka tafi dasu.
Ko kadan babu alamun fara'a a tattare da inspector din, Tambayoyi ya shiga jero musu akan sarqar da suka sata amma fir kowacce tace batasan zancen ba hakan ya batawa dan sandan rai yace a watsasu a bayan kanta.
Rigima suka somayi tsakaninsu kowacce na fadin albarkacin bakinta, idanuwan hindatu sosai ta raina fata,dana sani har cikin ranta. Wata bukekiyar police ce ta leqa cell din tayi musu uzinin fitowa, kowacce jiki a sanyaye take fitowa akace su bada numbers din wadanda zasuyi bailing su, hankalin hindatu ya qara tashi sosai ganin kowa na bada number har akazo kanta,tai wiki wiki da idanuwa,to number wa zata bayar? Zata kira gida ne tace gata a police an kamata da laifin sata ta sanadiyyar SATAR FITA! lallai. Keh kina bata mana lokaci fa! Dan sandan ya fada yana muzurai. Dan Allah kuyi haquri wlh banida kowaaa... ta fada kamar zatayi kuka! Bakida kowa? Ban gane bakida kowa ba? Gyada kai hindatu tayi hawaye ya fara taruwa a idanuwanta, wata uwar tsawa dan sandan ya buga yace a maidata cell zuwa Monday sai a Shiga court, tanaji tana gani suka maidata ciki, a gabanta akaita zuwa ana bailing mata yarage ita kadai,tashin hankali.
Qarfe 8:45 ya qarasa gida,a gajiye ya fada toilet ya watsa ruwa ya fito,wata muguwar yunwa ce ta ciyoshi gashi yanda ya gajin nan baison fita ko kadan,part din hindatu ya zarce da qudurin samun abinda zaici,yayi mamaki qwarai da bai ganta gaban tv kaman yanda ya saba ba, haka kkitchen din ma dry babu alamun girki, tsaki yaja ya daura indomie, cikin yan mintuna ya fito da plate din a hannunsa,a falon ya zauna ya kunna TV yana tsammanin ganinta amma baiga alama ba harya cinye abinci
[21/04, 22:49] Hassan India: Miss collapse
👠 SATAR FITA💃🏽
(130)
harya cinye abincin,dakinta ya tura a hankali amma bai ganta ba hakama toilet,hankali tashe ya shiga caje gidan amma ba alamun hindatu abu kamar wasa,sae a lokacin ya tuna tace zata biki ya hanata, sosai ya jinjinawa rashin ji irin na hindatu tareda alqawarin daukan tsatstsauran mataki a kanta.
Yana nan zaune a falon har 11:30,hakan ya tayar masa da hankali ya fara tunanin anya kuwa lafiya,gashi kaf wayarsa babu numbern ta, tunanin kiran Adam ne ya fado masa ya danna masa kira,Adam dake shirin bacci ya dauki wayar da mamaki ya fara tambayar sa'ad ko lafiya.
Adam number yarinyar nan zaka turomin yanzu plz! Wata yarinya? Adam ya tambaya cikin mamaki yana miqewa daga gadon. Jiddatu take ko waccece,wannan er dai ta gidana.
Lafiya dai koh? Adam nifa yarinyar nan bata gida,na nemeta tun dazu na rasa.
Kamar ya bata gida?kasan qarfe nawa kuwa?fada kukai kokuma me?
Fadan lafiya? Nasan dai tacemun zata biki na hanata daga nan kuma bansan komai ba.
Amma har yanzu?anya kuwa lfy? To nima tunanin danake kenan, nayi tunanin tazo gidanka.
Ko kadan,kuma gashi sae kusan 11 na dawo daga gurin umma balle muce can taje.
Bari 12 tayi idan bata dawoba zaka jini sa'ad ya fada tareda sauke wayar.
Meya faru Adam? Aysha ta tambayeshi
Wai hindatu ce har yanzu bata dawo gida ba,ta fita bayan sa'ad ya hanata, wannan wata irin yarinya ce ya fada ranshi a bace.
Zata dawo husby,kadan qara haquri Aysha ta fada jiki a sanyaye sannan ta fice, tasan dai hindatu tace zataje kamun Fatima,amma ace har daren nan,da walaki. Juye2 Aysha take tayi har kusan 2 kuma taje ta tambayi Adam yace har yanzu bata dawo ba.
Dakinta ta dawo tq dauko wayarta tq kunna tareda lalubar number shamsiyya garba wata qawarsu, ringing 2 shamsiyyar ta dauka. Sama2 suka gaisa take tambayarta kun hadu da hindatu gurin kamun Fatima ne?
Muko muka hadu, ae nayi danasanin zuwa bikin Fatima.
Meya faru? aysha ta tambaya a tsorace.
[21/04, 22:49] Hassan India: Miss collapse
👠 SATAR FITA💃🏽
(131)
Labarin abunda ya faru shamsiyya ta bawa Aysha tareda da tabbatar mata dacewa a police din suka barta,wlh na tausayawa hindatu,ita datake da aure kuma sarai kinsan halin yan sanda yawancinsu basuda kirki.
Da sauri Aysha ta katse wayar,jiki na bari ta gayawa Adam abunda ya faru tareda roqarsa suje suyi bailing hindatu.
Lallai hindatu bazata shiryu ba,wato duk wadannan abubuwan da suka sameta amma baxa tayi hankali ba. Ba inda zamuje Aysha,zan kirawo mijinta nai masa bayani shida kansa zaije idan yaso ya dauki matakin daya dace da ita.
Husby karf....baiko saurareta ba ya dannawa sa'ad kira tareda masa bayani.
Cikin en mintuna ya qarasa station din, zuciyarsa kamar zaiyi aman huta yakeji,police din daya samu a gurin yayiwa bayanin shi mijin hindatu ne, wuqi2 sukai da idanuwansa saeda ya sake musu magana suka fiddo hindatu wadda ta sassauya kamanni tana takawa daqyar,kallo daya yayi mata ya kawar da kansa zuwaga police din dake masa bayanin case din,check ya zaro ya rubuta adadin kudin sarqar ya miqawa police din yace gashinan ya biya basai anje court din ba,ya finciki hannun hindatu sukai gaba, a gaban motar ya wulla ta shima ya shiga, a 180 suka qarasa gida ya kutsa kan motarsa yayi parking a parking space ya fito a zuciye yayi cikin gidan. Kusan 30 mins yayi baiga shigowar hindatun ba hakan yasashi fitowa hannunsa riqe da robar malt, tsugunne ya sameta ta hade kanta da gwiwa tana kuka,tsawa ya buga mata yana fadin bazaki miqe mu wuce ba! Ganin bata ko dago ba ya qara fusata shi ya finciko hannunta da qarfi, wata gigitacciyar qara tasaka har saida ya tsorata ya maida dubansa ga qafarta. Innanillahi wa inna ilayhi raji"uun...jinii....
[21/04, 22:50] Hassan India: Miss collapse
👠SATAR FITA💃🏽
(132)
Tsugunnawa tayi tana sheshsheqar kuka shikuma yayi sororo yana kallonta cikin kaduwa, meya sameki? Ya tambayeta cikin wata rikitacciyar murya!magana fa nake miki! Ya sake tambayarta cikin kakkausar murya, ganin batada niyyar amsawa yasashi duqawa ya dauketa gaba1, a tsorace ta kalleshi a tana qoqarin qwacewa ya riqeta qam tareda sake daure fuskarsa ya fara takawa a hankali,rumtse idanuwanta tayi da sauri ta cusa fuskarta cikin qirjinsa zuciyarta na dukan 3-3, tunda suka baro police station take cikin razani da firgicin abunda ya faru amma yanzu data tsinci kanta a qirjinsa sai takejin kamar an sauke mata kashi 70 cikin matsalolinta, jin datai ya sauketa akan gado ne yasata dawowa daga duniyar tunanin data tafi amma har lokacin ta kasa dagowa ta kalleshi.
Hannunsa yasa ya dago habarta fuskarsa a daure yace I'm asking you for the last time meya sameki?
Da sauri ta rumtse idanuwanta qirjinta na bugun 3-3 tace Babb..Babb..babu abunda ya sameni.... bata ankara ba kawai saiji tayi ya fara fincikar skirt din jikinta a gigice taja baya ganin zata gudu yasashi saurin damqe qafarta ya fincikota da qarfi ya fara rikiciniyar zare skirt din tayi saurin riqeshi tana sheshsheqar kuka tace dan Allah kayi haquri plz don't do dis plzxxx..
Hannunsa ya zare a hankali yace OK then,talk to me what happen to u?
Muryarta a sarqaqe tace police din nan ne ya nameni.... me! Ya nemeki? Kuma kikai me?
Wlh ban yadda ba,ka yadda dani ban bashi kaina ba nayi duk wani qoqari dazan iya wajen ganin na kare kaina daga sharrinsu amma.....kuka ne yaci qarfinta ta kasa qarasawa, nan danan idanuwan sa'ad suka kada sukai jawur qirjinsa yadau zafi sosae, kenan sunyi masa raping mata!
Amma sun gama dashi! Dukda dai bashida tabbacin hindatu virgin ce amma dai koma metayi ai kafin ya aureta ne yanzu kuma ta zama mallakinsa, basusan waye sa'ad ba! Sai yasa sunyi danasanin ranar da aka haifesu.
Ya dade baiji kukan daya narkar masa da zuciya ba
[21/04, 22:50] Hassan India: Miss collapse
👠SATAR FITA💃🏽
(133)
Ya dade baiji kukan daya narkar masa da zuciya ba kamar wanda hindatu keyi yanzu.
Hannu yasa yayi cupping face dinta idanuwanta sun kumbura sosae yace I'll avenge! Bazan taba bari wani yacimun mutuncin mata ba, they'll regret what dey did to u. They dare to rape my wife! Kamar zaice wani abu kuma saiya juya a fusace yabar dakin kamar zai tashi sama yayi hanyar waje ganin haka yasa hindatu miqewa da sauri ba tareda tayi la'akari da azabun datake ji a jikinta ba tabi bayansa a guje,lokacin data qarasa harya bude murfin mota zai shiga tayi saurin tareshi,numfashinta har sama yakeyi tace ya Sa'ad ina zakaje? Police din zan koma! Ya fada a tsawace, ba yanda kake tunani bane ya sa'ad basuyi raping dina ba! Juyowa yayi yana qare mata kallo ta cikin farin watan data haske garin, har a lokacin ta kasa hada idanuwanta dashi.
Mekike nufi?
Lok..lokkacin daka shigo police din suna qoqarin raping dina munata rigima dasu,shine sukamin duka har suka jimun ciwo saida sukaji zuwanka sannan suka rabu dani ta fada tana wasa da yatsun hannunta.
Taya zan tabbatar da hakan?
Ka duba kagani ta fada tana kallon fuskarsa.
Ina zan duba?
Da sauri ta dago ta kalleshi,sai yanzu ta fahimci katobarar datayi ganin yana binta da wani irin kallo yasa tayi saurin juyawa da nufin guduwa amma taku 2 tayi ta tsugunne Auchhh ne kawai ya fito daga bakinta har sa'ad ya qaraso gurin ya dauketa ya daurata a kafadarsa,dariya ma kawai take bashi ganin tana mutsu2n qwacewa,har dakinsa ya kaita ya zaunar a bakin gado sannan ya shiga toilet, ruwan zafi ya hada mata yace tashiga, ba musu ta shiga toilet din tayi wankanta ta gasa jikinta sosai sannan tafito tana dingisa qafarta,shaf ta manta ba'a dakinta takeba har saida ta shigo tsakiyar falon ya turo qofa yashigo hannunsa riqe da wani guntun plate,da sauri ta juya masa baya, wani mitsitsin towel ta daura da kadan ya sauko cinyarta,bai kulata ba ya daura plate din akan gadon sannan ya koma ya
[21/04, 22:50] Hassan India: Miss collapse
👠SATAR FITA💃🏽
(134)
Da sauri ta kadan ya sauko cinyarta,bai kulata ba ya daura plate din akan gadon sannan ya koma ya janyota zuwa gadon,fuskarsa ba yabo ba fallasa yace inane gurin ciwon.
Zare ido tashiga yi kamar wata mara gaskiya, ehm I'm listening yace mata yana bude spirit din.
Ganin tayi shiru yasashi dagowa fuskarsa adan hade yace kina batamin time.
Kalar tausayi tayi tace ae abun fa a cikin jikina yake. And so?niba mijinki bane bude nagani mana. Cuno baki tayi a hankali tadan daga gefen towel din ta nuna masa, a hankali ya fara dauraye gurin da hydrogen,zafin sosae yake cinta shikuma zuciyarsa cikeda kishi dan alamun yatsu yagani a gurin, sai kuma ina? Tafin qafarta ta nuna masa da gwiwarta,a hankali ya shiga shafa mata harya gama ya miqe zai fita ita kuma ta kwanta a hankali taji wani arnan zafi. Auochh tace cikin azaba tana yarfe hannu yai saurin dawowa,lafiya dai ya tambaya yana kallonta ita kuma tana nuna masa bayanta, da sauri ya qarasa kan gadon yana qoqarin zare mata towel ta baya tai saurin riqewa tace ya sa'ad me zakayi? Ko qala baice mata ba ya janye towel din,da sauri ta kwanta akan cikinta shikuma yabi bayanta da kallo, ko kadan ba rama a bayanta dukda bawai qiba gareta ba,babu quraje ko wasu tabo,idanuwansa ya dora kan ciwon da sukaji mata a hankali a janyo hydrogen din da spirit, tsaf yayi mata plasta ya janyo wani pain relief yana shafa mata a hankali cikin wani irin yanayi,wani irin abu yakeji yana masa yawo a jijiyoyin jikinsa ganin nutsuwarsa tana neman kufce masa yasashi saurin miqewa yayi waje da kayan, hindatu kan tunda ya fara shafa mata relief bacci mai nauyi ya kwasheta shi baima saniba saida ya dawo ya ganta ta bararraje abunda jikinta ya rabu da towel din gaba1, godiya yayiwa Allah data kasance rufda ciki tayi dukda kuwa yasan babu kyau saidai nata lalura ne, gyara mata kwanciya yayi a hankali gudun karta farka ya fada toilet ya dauro alwala yayi sallah har saida akai asbah sannan
[21/04, 22:50] Hassan India: Miss collapse
👠SATAR FITA💃🏽
(135)
hankali gudun karta farka ya fada toilet ya dauro alwala yayi sallah har saida akai asbah sannan ya kwanta,bai farka ba sai kusan 9:30,hindatu na kwance har lokacin ya fada toilet yayi wanka yafito,a gaggauce ya shirya tsaf sannan yashiga kitchen, bai dade da fita ba hindatu ta farka, a hankali ta miqe ta fice tayi part dinta,wanka tayi tareda sallah sannan tafito, a falon sukayi kicibus da sa'ad hannunsa dauke da qaton basket, da mamaki ta kalleshi shima kallon yabita dashi, rigar data saka tai mata kyau sosae,doguwar rigace har qasa irin mai budewar nan amma ta kamata sosai tasama,shima din ya mata kyau dan baqin kayane a jikinsa,riga armless d wando 3 quater
Hanya tabashi ya wuce sannan ta shiga kitchen din,tsaf ta ganshi kamar ba abunda akayi, fitowa tayi ta shiga falon, anan ta sameshi zaune yana zuba kunun gyadar a cup, mamakinshi takeyi sosae,saad ya iya girki sosai wanda kadan za'a samu matan da suka iya irinshi yanzu,cikin plask din kuma wainar gero ce taji quli2 sai qamshi take zubawa,yawun hindatu ya tsinke sosai amma girman kai bazai bari tace zataci ba,ta gefen idonta take kallonsa yana juyowa saitai saurin kawar da kanta,yanzu kam ba iya abinci take kallo ba,har yanda yakecin abincin take kallo a yangance kamar baison ci, da kuma yanayin fuskarsa,skin dinsa nada bala'in kyau kamar ta Chinese har qyalli takeyi,quarter million din fuskarsa yayi lub-lub kana gani kasan yanashan gyara, dis guy is cute ko kadan batasan maganar datai ya fito fili ba saida ya juyo yace me kikace?
Diri2 ta farayi ganin ya kafeta da idanuwa yasa tace ina kwana. Yanda ta fada a tsorace yaso bashi dariya amma ya gimtse yace an tashi lfy?
Lpy lau tace tareda miqewa a kunyance zata gudu yayi saurin riqo hannunta. Subhanallahh! Tace a zuciyarta saboda wani irin shocking daya shigar mata jiki a lokaci 1,shi wannan meyasa yake hakane ta tambayi kanta ba tareda ta kalleshi ba,come and hv ur breakfast yace tareda qara
[21/04, 22:51] Hassan India: Miss collapse
👠SATAR FITA💃🏽
(136)
kanta ba tareda ta kalleshi ba,come and hv ur breakfast yace tareda qara janyota da kyau, a sabule ta zauna gefensa,tarasa dalilin dayasa yau takejin wata kunyar sa'ad,kodan basu taba wani zaman arziqi bane sai tsakanin daren jiya da safiyar yau oho, a hankali ta tsiyaya kunun a cikin cup ta fara sha shikuma ya miqe,hamdala tayiwa Allah dan tanada yaqinin bazata iya sha ba a yanda ya tattare ta, aeko da sauri da sauri ta dinga turawa harda su qwarewa,kafin kace me wannan ta cinye,a gaggauce ta tarrare kayan takai kitchen ta wankesu fes takuma gyara gurin, tana qoqarin zama ya shigo hannunsa riqe da tray din jiya, gaskiya yau dakaina zanyi tafada a ranta lokacin daya zauna a kujerar gefenta yana hada kan kayan, dagowa yayi ya kalleta yaga shi take kallo,murmushi yayi a hankali ya qarasa kusa da ita ya riqo lallausar qafarta,wani irin yanayi tashi lokacin dayake matsa qafar a hankali har wani lumshe ido takeyi ta manta da zafin su spirit, daga nan zuwa gwiwarta,ba musu tajuya baya kamar yanda ya umarceta ya sauke zip dinta zuwa qugunta ya sake mata plastern bayanta, yana qoqarin daga gefen rigarta ne tayi saurin riqe hannunsa tayi qasa ta kanta muryarta can ciki tace zanyi dakaina, zare hannunsa yayi yana murmushi yace ai baki iya ba,ki bari nai miki. Ya sa'ad plz zanyi dakaina kabari,ganin zata bata masa lokaci yasashi saurin janyota qasa zuwa kan lallausan rug din dake falon,kafin tayi wani yunquri ya dage rigar yafara yana sake mata bandage din,lokaci 1 suka nemi nutsuwarsu suka rasa,bama yashi sa'ad din,hannunsa had rawa yakeyi daqyar ya iya qarasa saka mata bandage din yafara wasa da hannunsa a saman cikinta zuwa cibiyarta, sosai hakan ya rikita hindatu shikuma ya gama rudewa gaba1 ya dora bakinsa kan cikinta yana binta dawasu mahaukatan kisses, ganin hakan yasa hindatu fara qoqarin qwatar kanta amma takasa, a tsorace take kiran ya sa'ad plz kabari, kadaina amma baima san tanayi ba ya Dora goshinsa
[21/04, 22:51] Hassan India: Miss collapse
👠SATAR FITA💃🏽
(137)
ni mijinki ne let me exercise my right plz ya qarashe tareda daura lips dinsa akan nata,da sauri hindatu ta lumshe idonta zuciyarta na bugawa da sauri da sauri,turo qofar da akayi ne ya tsaidashi, wai masu gidan nan basa amsa sallama ne! Adam ya fada da dan qarfinsa alamun motsin dayaji shiya kai idonsu kansu, d sauri ya juya tare da fadin sorry ya fice.
Dagowa sa'ad yayi yana gyara rigar jikinsa itama hindatu tai saurin miqewa da sauri ta shige daki. Kusan 5 mins sa'ad ya kwashe a zaune kafin ya iya miqewa jikinsa a mace ya fito, a compound din gidan sa'ad ya tadda Adam tsaye jikin bango yana danna waya. Yana ganin sa'ad ya taho ya fara sakin wani murmushi shikuma sa'ad ya hade rai shi a lallai bayason Adam yai masa maganar, tare suka jera ciki Adam na wata dariya qasa2 suka zauna a falon. Sa'ad ka canza halinka,wato dayake ka samu matarka jiya shine mukaji shiru koh!bama k damu da yadda muka kwana ba tsabar shaqiyanci.
Hannu sa'ad ya dora kan lips dinsa yana kallon dakin da hindatu ta shiga murya qasa2 yace dallah kayi shiru mlm,meye hakan?
Dariya Adam ya sakeyi yace ohh! Yaushe kuma k fara tsoro,naga dai idan anyi magana sai kace ba haka b yau kuma sabodd.. da sauri sa'ad ya tareshi tareda miqewa yace malam fita Dan Allah kaga abunda kakeson gani saura kuma kaje k yadani.
Ohh! Basai ka koreni ba zan tafi saboda nasan yanx..... da sauri sa'ad ya turashi waje tareda turo qofar da sauri. Yanajin sautin dariyar sa'ad harya tafi sannan ya kwanta saman kujera ya miqe qafarsa tareda lumshe idanuwansa a hankali yana tunano abubuwan da suka faru yanxu.
Akan gado hindatu ta kifa jikinta na mugun rawa,ba qarya taji dadin abunda ya faru tsakaninta da sa'ad dan har yanxu jikinta bai daina amsawa ba,ta rumtse idanuwanta sosai tareda qanqame pillown dake gefen gadon. Tayi kusan 30 mins a hakan sannan ta miqe zaune,sai kuma yanxu take godewa Allah da wani abu bai shiga tsakaninta da sa'ad ba,ba mamaki abunda
[21/04, 22:51] Hassan India: Miss collapse
👠SATAR FITA💃🏽
(138)
ba mamaki abunda yake nema a gurinta kenan shiyasa ya sauko haka,mutumin da murmushi ma wahala yake masa shine zai sake da ita har haka? Nooooo ta fada a fili sannan ta tashi ta fada toilet, sai kusan 4 hindatu ta fito daga dakin shima yunwa ce ta korota, bata sameshi a falon ba kuma bata nemi tasan inda yakeba ta fada kitchen, da sauri2 take hada abunda zataci,cocoanut rice ne da coslow gidan ya kaure da qamshi harta gama girkin sannan ta fara aikin hada coslow,wuqa ce a hannunta tana yanka cabbage taji an rungumota ta baya har saida ta kusan yankewa,a tsorace ta fara qoqarin qwacewa,da sauri sa'ad ya dora bakinshi a gefen kunnenta murya can qasa yace shiii nine...kasa motsi tayi da wuqar a hannunta d cabbage din, shikuma ya cigaba da magana a hankali yana cewa ai nayi tunanin bazaki fito ba har na gama jirana na fita sai kuma daga baya na fahimci kunyar Adam kikeji nasan hakan ne kawai ya hanaki fitowa.lumshe ido hindatu tai muryarsa na ratsa duk wani sassa na jikinta, hannunsa ya dora a hankali kan nata ya riqe wuqar da dan ragowar cabbage din ya fara yankawa a hankali har saida suka gama sannan ya juyo da ita a hankali yace to how was it,kiyi rating qoqarina na dazu naji ko nayi qoqari ko kuma saina qara qoqari, ya fada yana qara janyota jikinsa yana dago habarta, I knw u enjoy it more ko ba hakaba en mata yanda ya kakkafeta da ido yasata jin wata muguwar kunya ta kamata,da sauri ta fada qirjinsa ta cusa fuskarta a kunyace,hannunsa ya kewaya ya rumgumeta gaba1 ya dora kansa a kan gashinta yana shaqar qamshinta a hankali, sun kwashi kusan 10 mins a gurin sannan ta zare kanta da sauri tana qoqarin wucewa yayi saurin riqe hannunta yace baki amsamin ba fa. Ya sa'ad plxx! Ta fada tana qoqarin qwace hannunta ya riqe hannun gaba1 yana er dariya yace nifa ba yayanki bane ki daina wani cemin yaya. To ka sakeni mana kajii... naqi din,ni bazan sakeki baa.. ya kwaikwayi muryarta.
Cuno baki yayi a shagwabe tana
[21/04, 22:52] Hassan India: Miss collapse
👠SATAR FITA💃🏽
(139)
kwaikwayi muryarta.
Cuno baki yayi a shagwabe tana bubbuga qafarta,hakan ba qamanin burgeta yayi ya kafeta da fararen idanuwansa har saida ta gaji t hure masa ido. Firgigit ya dawo daga duniyar tunani ya danyi murmushi yace ohk zan sakeki amma dai sai kinyi promising zakimun abu 1
I promise ta fada tana dan gyara tsayuwarta yayi dariya yace good, 1 good French kiss nakeso na 5 mins. Waro Ido tayi a tsorace tace nifa ban iya ba gaskiya. Uhmm to saiki koya ai yanxu yanzu. Murmushin mugunta tayi tace to naji zanyi but saika rufe idonka.
Toh ba matsala yace yana gyara tsayuwarsa, a hankali tasa hannuwanta ta tallabo fuskarsa tana kallon fuskarsa mai bala'in kyau, duqowa yayi yana jiran yaji ta fara kissing dinsa kawai saijin bugun qofa yayi da sautin dariyarta. Da sauri yabi bayanta yana cewa wato guduwa kikayi koh? Ko amsashi batai ba tashige daki tana dariya.
Lokaci yana tafiya rayuwa tana canza salo, zamantakewar hindatu da sa'ad kullum qara dadi takeyi basuda wata sauran damuwa musamman a gurin sa'ad hindatun ce ma duk sanda yayi mata maganar haqqinsa saita canza fuska ita a lallai bata yarda ba. Aiki takeyi sosai a gidan tahau stool tana goge yana amma hankalinta na gun sa'ad,tayi zurfi cikin tunanin yanayin aikinsa wanda ako da yaushe yana iya fita ko ya daure safe,rana, dare bashida takamaimai lokaci har zuwa Sunday kuma duk lokacin data nemi sanin wani aiki irin aiki ne sai yace businesses idan ta nuna rashin yardarta sai yayi qoqarin canza maganar,abun yana dan damunta dukda qoqarin datake wajen mantawa da batun,tayi zurfi cikin tunanin nata kawai saiji tayi ta zame zata fadi qasa da sauri sa'ad ya tareta dan shima shigowarsa kenan. Ajiyar zuciya ta sauke tareda zame kanta daga jikinsa tace yaushe kashigo? Ban jima ba, waya saki irin wannan aikin? Cuno baki tayi tana karkade jikinta tace ba dole nayi aiki ba,ka fita tun safe gidan ba kowa saini qwal kamar mayya kuma idan nace ka barni naje
[21/04, 22:52] Hassan India: Miss collapse
👠SATAR FITA💃🏽
(140)
Ka fita tun safe gidan ba kowa saini qwal kamar mayya kuma idan nace ka barni naje wani gurin sai kaqi.
Dan murmushi yayi yace to aike din bakison ganin kowa, kowacce mace da haka ta fara zuwa wani lokacin sai kiga ta tara iyali amma banda ke, na rasa me kike tsoro ko bakyaso ki ganki da dan babynki kaman aysha.
Gaba tayi da sauri dan batason jin zancen tace kayi sauri kai wanka ga abincinka nan yana jiranka.
Kallo yabita dashi harta qulewa ganinsa,shifa a gaskiya haqurinsa ya fara qarewa kan hindatu ya fahimci dan yana lallabata shiyasa take wulaqantashi son ranta,ya zama dole yayiwa tufkar hanci.
Kwanakin da suka biyo baya sa'ad baya samun yin zaman gida kullum sai yace aiki ya masa yawa idanma ya fita ya dawo to da daddare saiya sake fita wataran sai safiya ma hindatu take jin shigowarsa har saida ta gaji tayi masa magana amsar kuwa daya bata batai mata dadi ba dan cewa yayi idan ya xauna babu abunda take masa saidai ta tayar masa da hankali gara ya fita. Cikin daga murya hindatu tace kenan nufinka gurin wasu matan kake zuwa harka kwana!
Idan ma hakan nayi ai laifinki ne kina matsayin matana kin hanani haqqina. A fusace ta tashi tabar masa falon ranar hindatu taci kuka dan bata taba tsammanin tana son mijinta ba sai yanzu ga wani bala'in kishi daya lullubeta.
Da safe da suka hadu sosae sa'ad ya fahimci tayi kuka saboda yanda fuskarta ta kumbura amma bai nuna damuwarsa ba saima wata shariya daya mata ya fice. Kusan 3 days kenan gidan duk ya gundiri hindatu ta kalli agogo qarfe 9:15 na dare amma ba labarin sa'ad itama bata tsammaci ganinsa ba,kamar an tsikareta ta miqe ta fara zagaya gidan har zuwa garden din da aka killace a gidan, a hankali take tafiya a ciki gurin banin sha'awa da daddare yanda akasa wasu kalolin fitulu tanata tafiya har saida takai qololuwar gurin sai kuma taji kamar sautin magana,da mugun mamaki ta kalli inda take jiyo amon, alamun daki ne ita bata taba lura ba,da saurinta
[21/04, 22:52] Hassan India: Miss collapse
👠SATAR FITA💃🏽
(141)
,da saurinta ta qarasa har zata bude wata zuciyar ta kwabeta,dan duqawa tayi ta zura idanuwanta ta qofar makulli tana leqawa,kusan sumewa tayi a tsaye ganin abunda bata taba tsammani ba.
Sa'ad ne zaune cikin dakin dayake tareda wasu mutane mata da maza kusan su 6 kowanne sanye sa baqaqen kaya sunayin wani yare wanda ita kanta bata fahimta ba, gani tai wani daga cikin dakin ya miqe ya tura wata qofa sai ganinshi tai dauke dawani mutum baqi an daure masa hannaye da qafa tareda toshe masa baki, batajin abunda sa'ad din yake cewa amma da alama ya fusata ne da abunda mutumin yace masa, gani tai ya zura hannunsa a aljihu a fusace ga mamakinta sai gani tayi ya zaro bindiga,a gigice hindatu tayi baya bata saniba saiji tayi ta taka jela ashe karnuka ne a gurin a gigice tasaka ihu ganin karnukan sunyo kanta da wani mugun haushi.
A razane gaba1 suka miqe sa'ad ya musu alama dasu nutsu,da sauri ya fito,a tsaye ya samu hindatu,yanayinta kawai ya isa ya tabbatar masa a gigice yake saboda irin haushin da karnukan suke y daka musu tsawa suka tsaya,hannunsa yasa ya finciko hindatu da qarfi suka fito har zuwa dakinta, ranshi a bace yace meya kanki can gurin da tsohon daren nan!
Cikin qarfin hali tace dole ka tambayeni mana sa'ad! Ashe haka kake!wlh k cuceni k cutar da zuciyana dakasa na fara sonka! Ka cutar da iyayenmu dasuka yadda dakai!ka cutar da kanka sa'ad! Me Allah ya rageka dashi dahar zaka dinga wannan mummunar dabi'ar! Fashi!sata!yankan kai bansan wacce ce takamaimai sana'arka ba! Bazan yafe maka ba sa'ad kuma baxan iya zama dakai ba! Wlh saina bar maka gidanka yanxu yanxun nan tafada tareda yin hanyar wardrobe dinta ta fara jefo kayanta tana hadesu akan gado,da sauri sa'ad ya qarasa ya riqe kafadunta yana girgizawa hindatu come back to ur senses! Meye haka kike fada!at least ki saurari abinda zance mana.
Ba abunda zan saurara daga bakinka! Qarya kawai zaka shiryamin! Wannan shine businesses din naka tana fada tana dukans
[21/04, 22:53] Hassan India: Miss collapse
👠SATAR FITA💃🏽
(142)
businesses din naka tana fada tana dukansa a qirji da dukkanin hannayenta har saida muryata ta dishe sa'ad ya rungumeta gaba1 ya lalubi bakinta ya fara kai mata wasu mugun kisses,for d 1 tym daya fara kissing dinta,qoqarin kwacewa takeyi amma ta kasa har saida suka zube akan gadon,nan fa ya canza salo ya fara aikawa duk wani sassa na jikinta sakwanni, hindatu kam iya qarfinta take qoqarin tureshi amma ta kasa dolenta ta saddaqar tana jiran taji ya shigeta. A sanyaye sa'ad ya janye jikinsa daga hindatu,he can't believe hindatu virgin ce bayan duk rashin jinta na baya, a daddafe ya iya barin dakin ya shige nasa dakin tareda warewa kansa ruwa,koda ya fito ma kaya kawai ya iya zurawa ya kwanta jin cikinsa na masa ciwo.
Bangaren hindatu kam saida taci kukanta sannan ta fada toilet tana zabgawa Allah godiya da sa'ad baici nasara a kanta ba. Daqyar bacci ya iya kwasarta, lokacin data tashi tayi mamakin ganin rana harta qwalle wai qarfe 12, da sauri ta miqe ta sake fesa wanka, qudirinta ta gudu gida ta sanarda kowa abunda yake faruwa, mayafinta kawai ta yafa ta zura takalma ta fito da saurinta tana tura gate taji an budeta. Ayshaa! Ta fada a mamakance,itama Ayshan kallonta take tace ah hindatu ina zakije haka?
Murmushin yaqe tayi ta karbi junior tace da almajiri nake nema fa,amma shikenan ma muje sukayi ciki gaba1.
Yini cur Aysha tayi a gidan dan sai dare Adam zaizo daukanta,rayuwarsu abun sha'awa basuda wani tension ba kamar irin tata rayuwar ba,taso ace cikin lokacin nan sun sami nutsuwa ita da sa'ad amma bayan abunda idonta ya ganar mata gaba1 yanxu tsoron sa'ad din takeji,tanason yiwa Aysha zancen amma kuma batason tonawa mijinta asiri tafison ko zasu rabu ya kasance asirinsa bai tonu ba, shigowar Adam ne ya katse musu hirar da sukeyi suka gaisa da hindatu,sai anan yake tambayarta sa'ad,gabanta yayi mugun faduwa dan ita kwata2 basu hadu da sa'ad ba,kasada kawai tayi tace yana dakinsa Adam yayi gaba yana cewa shi
[21/04, 22:53] Hassan India: Miss collapse
👠SATAR FITA💃🏽
(143)
Kasada kawai tayi tace yana dakinsa Adam yayi gaba yana cewa shi wannan mijin naki bansan sanda zai daina zurfin ciki ba,zaiyi tafiya bazai fadamin ba sai yau.
Tafiya ya sa'ad zaiyi?ina zaije Aysha ta jero mata tambayoyin a lokaci 1,murmushin yaqe hindatu tayi tace eh wlh Aysha tafiya zaiyi.
Hindatu...Aysha taja sunanta cikin taushin murya tace kamar akwai abunda yake damunki meya faru?
Ba abunda ya faru Aysha kawai dai nafara missing din ya sa'ad ne tun kafin yatafi.
Hindatu kenan, kinsan bazan tursasa miki ki fadamin matsalarki ba,kuma nasan duk duniya bakida wanda zaki fadawa matsalarki bayan ni, duk sanda kika shirya fadamin ina nan ina jiranki. Aysha ba yanda kike tunani bane ki bar zancen bari na duba abincin ina zuwa tayi saurin miqewa ta shige kitchen saboda kukan dayaci karfinta.
Tura dakin Adam yayi ganin baiga sa'ad a falon ba,can qarshen gadon ya hango sa'ad cikin bargo yanata rawar sanyi,da sauri Adam ya qarasa ya yaye bargon yana fadin subhanallah! Sa'ad bakada lafiya ne?
Hannunsa dake kan cikin ya dauke cikin mamaki yace sa'ad har yanzu ciwon cikin? Gyada masa kai yayi a wahalce tareda nuna masa drawern daya ajiye magungunan,a gaggauce Adam ya miqo masa maganin da ruwa yasha sannan ya samo ruwa yana danna mishi jikinshi da ruwan,saida zazzabin yadan sauko sannan Adam ya kalleshi cikin tausayawa yace sa'ad nifa ban gane maka ba, ciwon cikin har yanzu da aurenka kodai har yanzu kai da hindatu baku sasanta kanku bane? Lumshe ido sa'ad yayi a wahalce yace Adam nayi iyakar qoqarina gurin karkato da hankalin hindatu,hankalina ya fara kwanciya ganin mun sake da junanmu har na fara nuna mata ina buqatar haqqina amma yanzu komai ya rushe Adam! Komai ya rushee ya fada hawaye nabin gefen idonsa, sa'ad ban ganeba k fahimtar dani. Cikin sanyin murya sa'ad yakewa Adam bayani har zuwa abunda hindatu tace wato saita rabu dashi.
Tsaki Adam yaja cikin takaici yace to saime sa'ad!aikinka ne wannan kasan ko gida
[21/04, 22:53] Hassan India: Miss collapse
👠SATAR FITA💃🏽
(144)
Tsaki Adam yaja cikin takaici yace to saime sa'ad!aikinka ne wannan kasan ko gida hindatu ta tafi saboda wannan maganar dole ta dawo,sa'ad nasan hindatu tanada zurfin ciki bazata bari kowa yaji labarin nan ba,kuma zancen haqqinka dayake kanta sa'ad ganin damarka ne k qyaleta,sa'ad ya kamata ace tsakaninka da hindatu an wuce wannan gurin, tafiya zakayi can wata uwa duniya,ina jiye maka sharrin shaidan sa'ad daa da yanxu ba daya bane ya kamata kasan yanda zakayi kafin kayi tafiyar nan.
Adam hindatu bazata saurareni ba,tariga tayimun mummunar fassara. Saika tilastata sa'ad ka karbi haqqinka ta dole aiba haram bane,kaiba yaro bane kuma itama hindatu ba qaramar yarinya bace da zaku tsaya kuna batawa kanku lokaci.
Adam bazan iya tursasa hindatu ba!she's too young idan nace zan mata dole wlh ciwo zanji mata kasani kaima tunda kai likita ne.
To shknan sa'ad kar kayi abunda na fada maka saboda ciwon d zataji nadan lokaci,k cigaba d zama da naka ciwon har lokacin dakaso ya miqe yana cewa sai kazo sallama. Bayanshi sa'ad yabi har zuwa falon hindatu nan suka iskesu hindatu riqe da dady daya tashi daga bacci,kallo 1 hindatu tayi masa ta dauke idonta,gani tayi ya rame ba kamar jiya ba,tanaji suna gaisawa da Aysha tayi gaba ganin Adam ma yayi gaban, murmushin yaqe kawai takeyi har su Aysha suka fice, zuciyarta ta fara bugun 3-3,da sauri ta juya zatayi cikin gida wuta ta dauke, a tsorace tasa ihu tayi falonta a guje kawai saiji tayi tayi karo da mutum,da sauri ta qanqameshi tana fadin dan Allah karku kasheni wlh zanbar muku gidanku..dan Allah kuyi haquri ku taimaka min. Girgizata sa'ad ya shigayi ganin ta rude yana cewa nine hindatu ba abunda zai sameki! Ki kwantar da hankalinki plz. Ganin tayi daidaituwa yasashi hade bakinta danasa ya fara zuba mata wani French kiss,itama batayi qoqarin qwacewa ba saima kankameshi datayi,kusan 20 mins suka kwasa har saida hindatu ta bude idonta,lokaci 1 abunda ya faru daren jiya ya dawo mata
[21/04, 22:54] Hassan India: Miss collapse
👠SATAR FITA💃🏽
(145)
Lokaci 1 abunda ya faru daren jiya ya dawo mata,aiko da qarfi ta hankada sa'ad tareda cewa nooo ta fada dakinta d gudu ta saka key.
Daqyar sa'ad ya iya miqewa ya fice, washegari da sassafe yabar gidan, ta window hindatu taga fitarsa itama da sauri tamiqe da niyyar fita tana bude qofar falon kuwa tayi kwalli dawasu tiqa tiqan karnuka kowanne harshensa a waje yana yawo,suna ganinta suka fara haushi aeko da gudu takoma ciki,sai 10 sa'ad ya dawo gidan hakama washegari duk sanda ya dawo kuwa zai tadda dakin hindatu kulle da key,kwana 3 kenan hakan yana faruwa,yau kam tun 8 yadawo,wanka yayi yaci abinci yana tunanin gobe kamar wannan lokacin yayi nisa da Nigeria kuma zaiyi kusan 3 months bai dawo ba,maganar Adam ce kawai take masa yawo a kunnensa,zumbir ya miqe kamar an mintsileshi yayi part din hindatu,dakinta ya dosa da sauri ya fara bubbugawa daidai lokacin hindatu ta fito daga wanka. Sanin ba wanda zai buga mata qofa a wannan lokacin saishi yasata kallon qofar a kufule tace menene kuma? Cikin sanyin murya sa'ad yace hindatu ki taimaka ki budemin qofa zan mutu.. tabe baki hindatu tayi tace kaga ya sa'ad wlh bazan taba bude maka qofa ba,abunda kake nema a gurina bazaka taba samuba zaifi maka ka wuce k bani guri.
Lebe sa'ad ya cije cikin bacin rai yace hindatu wlh idan baki bude qofar nan ba zan ballata kuma idan n shigo ko kadan bazan tausaya miki ba. Murmushin mugunta tayi tace k dade baka ballaba ya sa'ad idan k bude duk yanda kaga dama kayi dani dan Allah.
Haka kikace? Eh haka nafada ta qarashe tana murguda baki kamar yana kallonta,ganin shurun kusan 10 mins yasa ta fara shafe jikinta da turare kamar yanda ta saba ta dauko wata rigar bacci mara nauyi ta fara zurawa kawai taji wani mugun qara, ihu tasaka a gigice rigar ta maqale mata a wuya. Ya sa'ad! Ta kira sunanshi a razane ganin yayo kanta,dagudu tayi hanyar toilet ba bata lokaci yasa qafa ya tadiye ta yayi saurin sakawa toilet din key. Tsoro+firgici ya ziya
[27/04, 17:04] 80k: Miss collapse
👠SATAR FITA💃🏽
(146)
Tsoro+firgici ya ziyarci hindatu ta fara jaa dabaya tana roqon sa'ad amma ina baisan tanayi ba,duka,zagi cizo ba irin wanda sa'ad baisha ba amma ko a jikinsa,ranar hindatu taji jiki gurin sa'ad dan sumanta 3 amma bai sarara mata ba saida aka fara kiran sallah asbah sannan ya rabu da ita ko motsin kirki bata iyawa,shikuwa ji yake kamar an cire masa qaya,kusan 1 hour sai gashi ya dawo sanye da baqaqen kaya kamar kullum bayansa rataye d wdata jibgegeyar jaka,gefen hindatu ya zauna yana kallonta,wani mugun sonta ke fizgarsa jiyake dama ya zauna yayi jinyar kayansa amma a nata bangaren runtse ido tayi tanajin tsanar sa'ad na ratsata, I love you hindatu yace cikin wata irin murya, Allah yasa qwallona ya shiga raga,take care of yourself yace tareda manna mata kiss peck a goshi ya fice,a hanya ya kira ummi yake fada mata hindatu batada lafiya idan babu damuwa taje ta ganta,ba bata lokaci kuwa ummi ta fito da saurinta duk tunaninta ko hindatu tanada ciki ne, tana parking motar tayi saurin fadawa ciki da sallamarta,jin baa amsa ba yasa tayi dakin hindatu,kwance ta sameta ta lullube da bargo har wuyanta tanata rawar sanyi da sauri ummi ta qarasa tana taba goshin hindatu cikin tausayawa, hindatu zazzabi kikeyi haka? Tun yaushe? Aida kunje asibiti ummy ta fada adan rude kafin ta shiga toilet ta samo ruwa da towel,hannu ummi tasa tana qoqarin janye bargon hindatu tayi saurin riqeta ta bude jajayen idanuwanta da suka kumbure murya na rawa tace ummi karki cire plx. Ya zakice haka hindatu,zazzabi ne a jikinki sosai,idan nadan shafa miki ruwan nan zai sauka,kafin hindatu tace wani abu ummy ta janye bargon, da sauri ummy ta mayar da bargo tana maimaita subhanallah, kallo tabi hindatu dashi yanda cikin wani irin yanayi tace hindatu dama duk tsawon wannan lokacin ba abunda ya taba shiga tsakaninku? Wani sabon kuka hindatu tasaka mai sauti,ummy kam har zuciyarta takejin kukan, kinga hindatu ya isa haka ki daina kuka bari na hada miki
[27/04, 17:04] 80k: Miss collapse
👠SATAR FITA💃🏽
(147)
na hada miki ruwa kiyi wanka tukunna,toilet ummy ta shiga ta hada ruwan zafi sannan ta fito da towel a hannunta ta ajiyewa hindatu ta fice daga dakin tayi kitchen, daqyar hindatu ta iya janyo towel din daga zaune ta dorashi ta fara qoqarin miqewa wani axababben radadi taji cikin jikinta ai batasan sanda ta qwala wata gigitacciyar qara ta zube a qasa, da sauri ummi ta qaraso ta kama kafadun hindatu tana cewa lafiyarki kuwa? Meya faru? Ummyy bazan iya miqewa ba!bazan iya tashiba ummy zan mutuu... ido ummy tabita dashi tace hindatu bleeding kikeyi kokowa kukayi ne?
Girgiza kai hindatu tayi cikin rawar murya tace ummy wlh saida na bash bashi haquri amma yaqi jina. Ajiyar zuciya ummy tayi kawai,ita ta taimakawa hindatu tayi wanka ta shirya sannan sukaje asibiti,a dole aka yiwa hindatu dinki,ba qaramin azaba taci ba,saida yamma aka sallamosu, gidan ummyn suka zarce bayan sunje sun kwashi yan kayan hindatu,ranar hindatu ko tafiya bata iya yi,washe gari da yamma aysha tazo, wai hindatu meya faru ne? Ummy tacemin bakida lafiya kuma taqi fadamun meyake damunki kema kuma kinyi shiru. Cikin sanyin murya hindatu tace Aysha sa'ad ya cuceni ya gama da rayuwa ta. Meya faru haka hindatu? Hannu tasa ta share hawayenta tace Aysha that beast raped me! Sa'ad ya cuceni ya rabani da martaba ta ta qarfi da yaji yayimin fyade! Bazan taba yafe masa ba Aysha ta qarashe maganar cikin kukah.
Ban ganeba hindatu,kina nufin dama duk soyayyar nan babu abunda ya taba shiga tsakaninku?
Aysha kinsani lokacin da mukai aure bamusan juna ba balle maganar so,Aysha da kyawawan halayen sa'ad ya fara ribatar zuciyana na fara sonshi, naji inason kasancewa tare dashi, tun a lokacin sa'ad yaso n amince dashi naqi yadda sai a lokacin dana yadda dashi dari bisa dari na qudurtawa kaina zan bashi amanar zuciyana da rayuwata,sai a lokacin na gano mummunan halin sa'ad dayake boyewa bayaso a gani, Aysha nayi danasanin zama matar sa'ad!nayi danasanin fara sonshi
[27/04, 17:04] 80k: Miss collapse
👠SATAR FITA💃🏽
(148)
Wani hali ne wannan hindatu!
Aysha ya sa'ad dan fashi ne!!! Da idona na ganshi da bindiga yana qoqarin kashe wani mutum shida wasu mutane a gidan aurena! A gidana aysha taya zan taba yadda n zauna d mugun mutum irin haka! Na tabbata watarana nima kasheni zaiyi,Aysha bazan koma gidan sa'ad b saidai y saken....hannu Aysha tasa ta kare bakin hindatu bata bari ta qarasa ba tace hindatu indai kika bari kika rasa ya sa'ad lallai kin tabbata asararriya kuma mara rabo. Nayi tunanin zaman da kukayi da yayana kinsan wasu abubuwa a tattare dashi ashe ba haka b,ya zamemin dole na fada miki waye mijinki.
Mijinki babban dansandan ciki ne wanda akafi kira sea SSS, ya kasance daga cikin yansandan ciki mafiya qwazo guda 10 a fadin duniya,ya riqe manyan muqamai da awards masu yawa saboda qwazonsa da kuma irin ayyukan hatsari dayake yi, qasashe dayawa sunso daukan sa'ad yayi musu ayki amma ya nuna bayaso saboda matsi dayake samu daga gida a dole ya dawo Nigeria inda gwamnatin Nigeria ta girmamashi ta babban muqami. Lokacin dana fahimci zaman da kukeyi da ya sa'ad da fari nayi mamaki dan shi mutum ne mai tsauri da rashin son raini musamman game mata amma naga yana haqura da duk tsiwarki,tun a lokacin n tabbatar cewa sa'ad sonki yakeyi amma kinqi bada kai bori ya hau dukda na fahimci kema kina sonsa, hindatu yanzu sa'ad yayi nisa ya tafi America wani babban aiki da zasuyi mai matuqar hatsari,zai iya yiwuwa ya dawo da rai ko akasin haka, hindatu ki gyara zaman aurenki tun kafin lokaci ya qure miki kizo kina danasani,tana kaiwa nan tafice tabar hindatu zaune kamar ruwa ya cinyeta hawaye na shatata ta idanuwanta kamar an bude famfo
[30/04, 12:48] 80k: Miss collapse
👠SATAR FITA💃🏽
(149)
She can't believe it,ashe sa'ad babban mutum ne haka amma yake jure duk wata fitsararta har yake roqonta,saida taci kukanta ta qoshi ta bawa kanta haquri, ranar gaba1 sukuku tayi ta har saida ummi ta tambayeta abunda yake damunta tace ba komai amma deep down kewar mijinta da tausayin kanta takeyi, wasa2 har kusan 2 wks babu wayar sa'ad babu alamunta tun hindatu na jurewa harta gaji ta kira Aysha ta tambayeta ko sa'ad ya kira Adam, tun last week dai sukayi waya kafin su fara aikinsu,yanzu kuma sun fara aiki yace gurin babu service.
Amma Aysha ya sa'ad bai kirani ba ko sau 1.
Hindatu tana iya yiwuwa ya barki ki huta ne amma zan turo miki number dinsa,ki dinga gwadawa maybe ki samu t shiga.
Gwadawar duniya hindatu tayiwa number din amma bata shiga, a yanzu son mijinta ke lugwiwita duk wani lungu da saqo na jikinta ga kuma kewarsa da takeji, a falo ta tadda ummy tana kallo hankalinta kwance hindatu ta shigo,da fara'a ummy ta kalleta tace aah hindatu zauna mana, zama hindatu tayi fuskarta dauke da damuwa meyake faruwa ne? Dan shagwabe fuska tayi ta kwantar da kanta gefen kafadar ummy murya can qasa tace ummy inason naje na duba gida akwai abubuwan dazan dauko. To ba damuwa hindatu kinga yanzu dare yayi amma zuwa safiya zan hadaku d driver.
To ummy ta fada tana miqewa wayar ummy ta fara ringing, hindatu miqomin wayana a saman fridge mana, da sauri hindatu ta qarasa ta dauko wayar ta miqowa ummy, kamar zata tafi kuma saita tsaya, kara wayar ummy tayi a kunnenta tace salamu alaikum,daga can bangaren akace alaiki slaam ummynah. Gyara zama ummy tayi fuskarta dauke da mamaki tace sa'ad! Waro ido hindatu tayi ta toshe bakinta jikinta har rawa yakeyi,yafito ta ummy tayi da hannu tana cewa sa'ad ashe kun sami service din, murmushi yayi yace wlh ummy mundan samu service ne dan mintuna kafin muyi gaba so I thought of saying hiii,ka kyauta kuwa son ga hindatu ku gaisa ta miqawa hindatu wayar.
Miqewa hindatu tayi da sauri tayi
[30/04, 12:48] 80k: Miss collapse
👠SATAR FITA💃🏽
(150)
Miqewa hindatu tayi da sauri tayi dakinta da gudu ta kullo qofar, shiru daga duk bangaren murya a sarqaqe hindatu tace ya sa'addd!!! Har cikin brain dinsa saida yaji muryar hindatu,d sauri yayiwa kansa matsuguni a kujerar dake gefensa yama kasa mgn, hawaye ne y fara zubo mata wanda ita kanta batasan dalilinsu ba,gaba1 ta rikice tanajan numfashi tace ya sa`ad meyasa bk kirani ba,ko sau 1 kaji yanda nake da damuwata,kasan yanda nake missing dinka,duk wani sassa na jikina yana matuqar kewarka,kunnuwana suna qaunar jin sautin muryarka hakama idona yana kwadayin ganinka! Haba ya sa'ad wlh bazan iya jure wannan ba ka dawo matarka tana buqatarka a kusa dakai ta qarashe tana sheshsheqa.
Lumshe idonsa yayi ya kasa gaskata abunda kunnensa yakeji,hindatu ce take fada masa wannan mgnr, lallai Allah yafi qarfin komai ya tabbata wannan adduarsa ce.
Jin shirun yayi yawa yasa tayi saurin cewa hello ya sa'ad kana jina kuwa?
Murya qasa2 yace ina jinki hindatuu, naso ace kina kusa dani a wannan lokacin,yanzu jinake kaman I'm d luckiest person on earth,banyi tsammanin jin wadannan kalaman daga bakinki ba,anyways I love you alot Mrs sa'ad, take care of yourself, loads n lots of kisses,baiji abunda tace ba ya tsinke wayar,gaba1 muryar hindatu kasala take saka masa.
Tun daga ranar basu sakeyin waya ba yanzu sa'ad kusan 6 wks kenan da tafiyarsa,har wata er rama tayi tsabar kewar sa'ad datayi mata yawa, ita da ummy ne zaune a falon suna er hira sukaji sallama,duka su 2 suka daga suna kallon masu sallamar, a fili hindatu tace safeeyah musah! Murmushi safeeyan tayi ta qaraso falon ita da qanwarta suka gaisa da ummy sannan sukayi daya falon da hindatu tai musu jagora, a kujerun falon suka baje suna hirar yaushe gamo dan rabonsu kusan 4 yrs kenan shima anyi sa'a ne ita safeeyah tazo bikin wata qawarsu a kano dayake ita er katsina ce.
Katina safeeyan ta ciro guda 2 ta miqawa hindatu tana er dariya, kallon katin hindatu tayi kafin ta kar
[30/04, 12:48] 80k: Miss collapse
👠SATAR FITA💃🏽
(152)
ba. Hindatu kuma? Ummy ta tambayeshi da alamun mamaki tace ba kaine d kanka kace taje bikin qawarta a katsina ba,ko k manta ne? Nikuma ummy, wlh bance taje ba, I strictly warn her karta je amma furzar da iskar bakinsa yayi ya miqe a fusace ya fita, binsa da ido ummy tayi yanda ya miqe a fusace ya fita,lallai hindatu ta raina masa wayo, ransa a mugun bace ya shiga gida,toilet ya wuce ya watsa ruwa ya fito da saurinshi ya shiga mota da gudu ya figeta sai katsina zuciyarsa na matuqar tafarfasa, saida ya kusa shiga KT ma ya tuno baisan address din gidan datake ba dan haka y yanke shawarar kiran Aysha, ganin yanayin yanda yake masifa yasa Aysha jiki n rawa t fad a masa address din, katse wayar yayi yana qoqarin qara speed,dagowar dazaiyi kawai sai karo yayi d wani mai mota, buum! Motar tayi sama ta hantsila tareda kamawa da wuta.
Duk qoqarin da mutane sukayi wajen kashe wutar yaqi yiwuwa saima qara habaka d takeyi, dole aka kirawo fire service suka kashe wutar, babban asibitin dake katsina aka wuce dashi, tareda en sandan dasuka zo, I'm sorry sir he's dead cewar likitan daya fito, anan sukabar gawar cikin mutuary suka koma gurin motar, daqyar aka binciko wayar sa'ad datai kaca2 ta qone, sim din police din ya cira ya nemo number din Abba ya kira lokacin Abba da ummy n zaune a falo anata hira saboda zuwan bazata d baffa d umma sukai musu, shigowar number din sa'ad ce ta katse musu hirar Abba ya dauka yana yar dariya ya kara a kunnensa,jin murya daban yasashi gyara zama,gaisawa sukayi d police din yace sunana inspector jazuli ibrahim daga katsina, ya kuke d mai wayar nan? Da mamaki Abba yace ni babansa lpy kuwa?
Dan jimm dansandan yayi sannan yace kayi haquri alh. Mai wayar nan ya gamu d accident anan KT and unfortunately Allah y masa rasuwa
[30/04, 12:48] 80k: Miss collapse
👠SATAR FITA💃🏽
(151)
hindatu tana er dariya, kallon katin hindatu tayi kafin ta karba ta budeshi da mamaki tace Sophy aure zakiyi?murmushi safeeyah tayi tace abunda ya kawoni kano kenan, katinan ku keda indo dan Allah karkice bazaki zo ba nasan dai mijinki baya gari balle kice bazaki zo ba,naje gidan aysha ban sameta ba shiyasa nazo nan n xatta ma tana nan yanzu dai ki taimaka ki lallabamin aysha. Karki damu safeeyah ISA zamuzo da haka sukayi sallama.
Washegari da yamma hindatu taje gidan aysha tana mata zancen bikin safeeyah.
Bazanje ba hindatu,ba abunda zai kaini bikin safeeya ko a garin nan zaayi balle kuma a wata uwa duniya.
Saboda me? Hindatu ta tambayeta fuskarta dauke d damuwa.
Kinga nifa rainin wayo ne banaso,ita safeeyah ko kunya bataji ba batazo bikina n balle bikinki shine zata kwaso qafa tace zata kawo mana kati qaryar banza kawai.
Kinga Aysha idan bazaki je ba kawai kice bakki zuwa,ina dalilin wannan wulaqancin,tsaki aysha tayi tana kada qafa hindatu tace to nidae zanje,kema idan kin canza raayi saiki mun maganar tunda akwai ragowar 1 wk.
Ke kika sani dai, kuma wazai barki kije keda mijinki baya nan?
Tabe baki tayi tace idan ya dawo saina fada masa, amma yanzu dai sai naje kuma ki cire kanki.
Ba ruwana hindatu kiyi yanda kikaga dama tunda ke bakya hankali, naji din hindatu ta fada tareda ficewa,ranar cikin sa'a sa'ad ya kirata, anan take fada masa zataje KT biki ya hanata tareda qwaqwqwaran kashedi, amma taqi ji data shirya tafiyar ma cewa ummy tai sa'ad ya barta taje har a gama biki,b musu ummy t barta.
Hindatu kam biki ya mata dadi sosai harta manta d wata damuwa batasan meyake faruwa a kano ba.
Qarfe 10:40 sa'ad ya sauka a Nigeria, dayake surprise yakeson yiwa kowa taxi ya dauka ta kaishi har gida, ummy na qoqarin fita ya shigo, mamakin ganinsa ya lullubeta a dole t fasa fita, abinci tasa aka kawo masa kala2 har saida yace ya gaji danshi matarsa kawai yakeson gani. Ummy ko hindatu batanan ne? Naga banji
[02/05, 20:01] 80k: Miss collapse
👠SATAR FITA💃🏽
(153)
What?! Abba yace a matuqar gigice, binshi da kallo dukansu sukayi shikuma yayi shiru yana sauraran abunda police din yake cemasa, a sanyaye ya sauke wayar yana qoqarin maida qwallar data zubo masa baffa ya riqe masa kafada yace Alh.sadauki lafiya dai meya faru? Kasa magana Abba yayi gaba1 jikinsa ya mutu bakinsa ya masa nauyi matuqa har saida baffa ya sake tambayar sannan baffa y iya bude bakinsa daqyar yace sa'ad ne .... sai kuma yayi shiru,a zabure ummy da umma suka tashi, meya samu sa'ad din? Allah y masa rasuwa,ya hadu d hadarin mota a hanyarsa ta zuwa katsina, zubewar ummy ce ta hana Abba qarasawa sukayi kanta a gigice, mai aikin ummy ce takawo ruwa aka zubawa ummy, d sunan sa'ad ta farka a gigice, sa'ad! Son! Bazaka mutu ka barni ba,karka mun haka. Ganin tana qoqarin zarewa ne yasa umma ta rungumeta tana lallashinta gaba1 suka fashe da kuka, har saida ummy tayi mai isarta ta samu nutsuwa lokacin su baffa sun fita zasuje dauko gawar sa'ad, dama ya dawone sa'ad din bamu saniba? Cikin sheshsheqar kuka ummy ta labarta mata abubuwan dasuka faru, kuka sosae umma ta fashe dashi,yau hindatu tayi sanadin mutuwar mijinta,ta kashe mijinta Allah wadaran hali irin na hindatu ga irin abunda yawonta ya janyo mata,kafin wani lokaci gidan ya cika taff d mutane anata koke2 babu ya aysha datake ganin tafi kowa laifi kuma tanada kamasho a mutuwar yayanta, qarfe 5:00 aka shigo da gawar sa'ad,anan kuka ya dawo sabo dan saida ummy tayi suma 3, kiran duniya aka yiwa wayar hindatu amma a kashe.
Tun wajen 12 takejin jikinta wani iri ga mugun faduwar gaba datake ji, a sukuku suka qarasa bikin dan amaryar ma kano za'a kawota shiyasa ta yanke biyo motocin amarya da zasu taho, katsina babu nisa da kano wajen qarfe 4 suka tashi, 5:40 tayi masu a kano, batafi 5 mins a gidan amarya ba ta dauko adadaita sahu, gidanta ta fara wucewa a cewarta ta dauko gajiya saida tayi wanka ta canza kaya sannan ta fito, gidan ba wuta dan haka gidan ummy zata
[02/05, 20:01] 80k: Miss collapse
👠SATAR FITA💃🏽
(154)
ummy zataje kota samu tasha iska, tun jiya basuyi waya ba saboda charging ta ya qare kuma an sace mata charger, mamakin yanda tsirarun mutanen dake unguwar suke kallonsu takeyi daga baya dai tace can muku ta dauki keke nepep sai gidan ummy, tun a farkon unguwar mutane suke kallonta suna qus2, ganin an cika maqil yasa ta fara tunanin ko daurin aure akeyi amma ganin taron da yamma yasa ta canza tunani, da turmutsutsu ta samu damar kutsawa gidan har cikan falon,yanda mutane suke kuka yasa jikinta ya fara rawa tayi saurin qarasawa kusa da ummy tana tambayar meya faru ummy amma ba amsa,sai a lokacin ma ta lura da gawar dake shimfide,hannu tasa ta bude gawar jiki na rawa,a tsorace ta matsa baya saboda yanda gawar ta qone kwata2 ba'a gane mamacin, baya tayi a tsorace bakinta na rawa cikin qaraji tace ku fadamin mana gawar wanene wannan! waya mutune!
Tagwayen mari ne suka amsawa hindatu tambayoyinta, har saida kunnenta ya dode ta juyo a gigice sukayi kwalli da umma da fuskarta ta kumbura tayi jawur, kinaso kisan waye ya mutu hindatu! Zan fada miki! Mijinki shine ya mutu! Kin kashe mijinki sa'ad kin kashe dan uwanki! Dagowa hindatu tayi ta kakkafe umma da idanuwa,ita ba kuka ba ba kuma ihu ba tama kasa motsi gaba1.
Cikin kuka umma ta cigaba dacewa hindatu nayi danasanin sanda na haifeki, nayi Allah wadai da ranar dana fara shayar dake daga jikina, hindatu wani irin fadane bamuyi miki ba nida mahaifinki akan wannan mummunar dabi'ar taki ta SATAR FITA! wani kuka nayi masifa nayi cuta duk saboda ke,nayi tunanin cewa tunda kikai aure kin daina halinki Ashe tsugunne bata qareba ashe sai kinyi sanadin mijinki bawan allah!.
Hindatu kin cuceni kinyi watsi da tarbiyyata, wlh gara na kasheki na huta da balai,kin dandana mana madaciyar da zata dawwama a cikin zuciyarmu har abada,bakida wani sauran amfani a duniya,kanta umma tayi ta rufeta da duka amma hindatu ko motsi kaman wanda aka sassaqa, mutanen dake gurin ne suka rirriqe umma
[02/05, 20:01] 80k: Miss collapse
👠SATAR FITA💃🏽
(155)
rirriqe umma ganin irin illar da tayiwa hindatu gashi maza masu daukan gawa sun qaraso, ya ishaq ne yayi kan hindatu dake a yashe jikinta duk jini yana girgizata amma taqi motsi, da sauri ya dauketa yayi gaba da ita mutanen dake gurin babu Wanda ya damu yabi ta kanta,a motarsa ya sakata yayi gaggawar kaita asibiti,da sauri doctors din suka karbeta sukayi emergency da ita.
Doctor duk abunda kake ganin ya dace kayi daganan jana'iza zanje,lafiyarta tanada matuqar muhimmanci daga haka ya fice.
A ranar kowa ya shaida ankai sa'ad makwancinsa na har abada,Allah ya kyautata namu zuwan, yasha addua sosae daga gurin mutane,tun a maqabarta Adam ya fara suma dan a lokacin sabuwa mutuwa ta zamo masa shima dole aka dangana dashi asibiti, a gida kam baa magana dan duk wanda yasan sa'ad ya sanshi da alkhairi hindatu kam tasha bakin mutane, washegari qarfe 10 aysha da ishaq har khadija sukaje duba Adam, ba qaramin rama yayi ba gashi fuskarsa ta kumbure,har a lokacin kuka yakeyi daqyar suka lallabashi yayi shiru daganan suka wuce duba hindatu amma khadija ta rantse baxata ba sai a mota suka barta ta jirasu, a dakin da aka kaita suka sameta tana sharar bacci ga drip yana diga a hankali sai bandages a jikinta saboda duka datasha,wani bangaren n zukatansu tausayin hindatu yake wani bangaren kuma haushinta,shigowar doctor ce ta katse musu tunani suka gaisa ya zare mata drip din sannan yace su sameshi a office.
Zazzaune suke a office din kowa da abunda yake saqawa a ransa har doctor ya gama rubuce2nsa sannan ya kallesu bayan ya cire glass din idonsa yace a cikinku waye mijinta? Kallon2 sukayi was junansu Adam yana matsar qwallo ishaq yayi qarfin halin cewa doctor mijinta Allah ya masa rasuwa jiya.
I'm sorry doctor yace cikin jimami ya cigaba d cewa amma nayi mamaki ita da mijinta ya rasu ya za'ayi mata wannan mugun dukan, saidai kuma I don't want to interfere in your family matter amma a halin da take ciki bai kamata kuna daga
[06/05, 19:33] 80k: Miss collapse
👠SATAR FITA💃🏽
(156)
I'm sorry doctor yace cikin jimami ya cigaba d cewa amma nayi mamaki ita da mijinta ya rasu ya za'ayi mata wannan mugun dukan, saidai kuma I don't want to interfere in your family matter amma a halin da take ciki bai kamata kuna daga mata hankaliba balle duka.
Wani hali kenan doctor? Aysha ta tambaya tana matsar kwallah.
Binciken danayi mata ya tabbatar da cewa ta samu minor heart attack sanadiyyar wani abu mai firgitarwa dataji ko tagani gashi kuma jininta ya hau. Subhanallah sukace gaba1 doctor yace duk wannan ba shine damuwar ba,abunda ke cikinta shine matsalar,indai har haka ya cigaba da faruwa ya zama dole a zubar da abunda ke cikinta.
Cikin mamaki suka kalli doctor din Adam ne yayi qarfin halin cewa doctor bamu ganeba.
She's pregnant, doctor yace yana kallonsu gaba1
Pregnant! Suka maimata gaba1 cikin mamaki, qwarai kuwa, doctor ya fada yana dubansu gaba1. Doctor y take,y jikin nata?
Da sauqi madam,saidai gaskiya yanzu tana buqatar hutu da kuma nutsuwa,zuwa nan da jibi za'a sallameta. OK sukace dukkansu tareda miqewa.
dakin da aka kwantar da hindatu suka shiga gaba dayansu, kowanne zuciyarsa a karya take, itama din ta rame sosae dan yanzu ma jini ake qara mata saboda jinin data zubar.
Hawayen da Adam yake maqalewa ne suka fito da qarfinsu,sosai yake kuka Aysha na tayashi, ya zama dole a tausayawa Adam, yafi kowa jin mutuwar,kusancinsu da amincinsu babu wanda zai iya fada.
Ishaq ne yayi qarfin halin dafa kafadarsa dan shima kukan ne yake cinsa,dan bubbuga masa kafadar yakeyi cikin salon bada haquri.
A hankali ya dago ya kalli ishaq cikin dashashshiyar murya yace ya ishaq bansan meya kamata nayi ba yanzu,farin ciki ko baqin ciki, wanda tayi sanadiyyar mutuwar sa'ad itace xata masa babbar kyauta a duniya saidai kuma gashi shi baya duniyar balle yagani.
Tsam Aysha ta rungumeshi tana cewa kyautace daga Allah ya Adam ka daina fadan haka, haka suka rarrashi juna.
Qarfe 9 hindatu ta tashi daga wahalal
[06/05, 19:33] 80k: Miss collapse
👠SATAR FITA💃🏽
(157)
Qarfe 9 hindatu ta tashi daga wahalallen baccin datake yi,a hankali takebin dakin da kallo lokaci 1 hankalinta ya dawo jikinta da sauri ta miqe zaune tana tana qoqarin tashi daga kan gadon Aysha da wata nurse suka shigo, da sauri suka qarasa suka rirriqeta aysha tana cewa hindatu ki nutsu mana bakida lafiya kina asibiti.
Aysha sakeni mana, sa'ad! Gurin saad zanje he must be missing me dan Allah ki sakeni.
Hindatu bakida hankali ne! Sa'ad ya rasu! Mijinki ya sa'ad ya rasu ya mutu yabar duniya bazai dawoba ki nutsu pls!
Tauuu! Hindatu ta dalleta da mari tareda riqeta tana jijjigata da qarfi tana cewa qarya kikeyi aysha! U r lying! Mijina bai mutuba he can't leave me alone kice qarya kikeyi, duk yanda nurse din tayi qoqarin rabasu ta kasa dole ta fita da gudu ta kirawo doctors din,daqyar aka banbare aysha tareda manna mata allura, kafin a zare bacci ya kwasheta mai nauyi.
Wasa2 har anyi kwana 3 da mutuwar sa'ad kuma ranar za'a sallamo hindatu, ko kusa umma bata taba tambayar ina hindatu take ko ya take ba,da ishaq yaje yimata bayani akan hindatun ma fada ta rufeshi dashi ba tareda ta saurareshi ba,shi baisan inda zaikai hindatu ba gashi khadija tayi tsalle ta dire tace hindatu bazata zauna mata a gida ba shikuma kunyar ummy yakeji gashi Adam yanzu sosai yakejin haushin hindatu dan ko ganinta bayason yi dole yaje ya roqi doctor din ya qara mata kwana 1 saboda yanason yayi settling wasu abubuwa. Daga qarshe dai Abba da ummy ya samu da maganar.
A falo ya samu abban da carbi a hannunsa yanaja ummy na zaune da abinci a gabanta amma ta kasaci,idanuwanta sunyi jajir harda dan wuya, a gefen Abba ya zauna yana dan danna yatsunsa Abba ya qwaqwulo murmushi yace ishaq da alama da magana a bakinka koh?
Gyada kai yayi yace ehh Abba dama zancen hindatu ne ya kawoni.
Miqewa ummy tai zata bar gurin Abba yayi saurin kiranta ta dawo ta zauna zuciyarta a raunane. Ina jinka ishaq Abba ya fada yana gyara zama.
[06/05, 19:33] 80k: Miss collapse
👠SATAR FITA💃🏽
(158)
Abba nasan abunda hindatu tayi ba qaramin abu bane,tayi abunda ni kaina bazance ku yafe mata ba amma Abba ita kanta hindatu yanzu halinda take ciki dole ku tausaya mata.
Lafiya dai koh ishaq? Abba ya tambaya.
Abba hindatu tana asibiti tun ranar da sa'ad ya rasu, doctor ya tabbatar da cewa tana daukeda juna biyu amma kuma matsalolin da suka faru ya haifar mata da matsaloli har doctor din yana hasashen cewa she's mentally unstable saboda tashin hankalin data shiga.
Mentally unstable! Pregnant! Meyasa baka taba fadamun ba! Dan sa'ad! My grandchild! Ishaq tashi k kaini gunta.
Yanda ummy ta rude duk saida suka tausaya mata, a hankali Abba ya riqeta yana dan bubbuga bayanta cikin sigar rarrashi.
Ishaq ne yadanyi gyaran murya sannan ya cigaba da cewa ummy hindatu tanada ciki, amma matsalar itace har yanzu taqi yadda cewa mijinta ya rasu, ummy inaso ki taimaka kibar hindatu ta zauna a gidan nan zuwa lokacin da zata haihu.
Cikin sheshsheqa ummy tace ishaq hindatu yata ce kuma tana daukeda cikin jikana,idan bata zauna a gidan nan ba ina zata zauna,nan gidanta ne ishaq zata zauna har lokacin da taso tafiya.
Nagode ummyna,n gode ishaq ya fada, tun a ranar suka je duba hindatu,bacci takeyi kuma dan haka tun a ranar suka gama shirin komai da safe xasu tafi da ita.
Qarfe 8 suka zo asibitin suka karbi sallama magunguna hindatu, ummy ce ta fara shiga dakin da aka kwantar da hindatun, zaune ta sameta akan gadon tanashan tea, waro ido tayi cikin mamaki tace ummynah, murmushi ummy tai mata tana qoqorin share qwallar data zubo mata ta qarasa, kwabe fuska tayi tace ummy sai yanzu kikazo dubani,gaskiya nayi fushi.
Ba haka bane hindatu kinsan nayi tafiya ne shiyasa amma yanzu gashi n dawo sai mu tafi gida koh.
Murmushi tayi tareda gyada kai ta tashi da dan saurinta ta shiga toilet, wanka tayi ta canza kaya zuwa wata doguwar riga mara nauyi da ummy ta kawo mata, tare suka jero dan Abba na tareda ishaq a wajen asibitin, mota
[06/05, 19:33] 80k: Miss collapse
👠SATAR FITA💃🏽
(159)
mota suka shiga, ishaq na driving Abba na gefensa sai hindatu da ummy a baya, surutai sosai hindatu take musu, a yanda suka fahimta ma yi take kamar ta manta da duk abubuwan da suka faru a baya, suma din basuyi qoqarin tuna mata ba sabida doctor y gargadesu.
*** **** ****
Taraba- jalingo
Hibba kin cika zumudi wlh, dadynki yace ki bari ya fito ku tafi tare, ke kumah
Yeeeeh dady.... cewar wadda aka kira hibba,da gudu ta tafi ta rumgeme mutumin tareda cewa dady muyi sauri plx,tunda doctor yace yanason ganinmu jiya wlh ko baccin arziqi n kasa.
Murmushi matar tayi tace ai dai kya bari kuci abinci koh? No mom,idan mun dawo munci byeee tace tareda jan hannun dad din, da kanta taja motar dad n gefenta suna hira har suka qaraso, cikin asibitin suka kutsa har zuwa office din babban doctor din,cikin fara'a doctor din ya miqawa mutumin hannu fuskarsa a sake yana fadin sannu da zuwa sir,nayi tunanin ma hibba zata turo.
Aa doctor, wannan patient din yanada matuqar muhimmanci a gurina tunda hibba tana qaunarsa haka,kasani kuma duk duniya babu wanda nakeso sama da yayana 2,hibbatu da jibon dan haka duk abunda sukeso dole na soshi.
Gyada kai doctor yayi cikin gamsuwa da alhini yace,saidai kuma alh labarin dazan fada maka bawai mai dadi bane.
Uhm go on, general wada yace yana riqe da hannun hibbatu.
Alh. Kayi haquri duk yanda mukaso ceto patient dinka mun kasa ba yanda muka iya dole saidai y shiga coma.
Dafe qirji hibbatu tayi cikin kaduwa coma doctor! Allahumma ajirni fi musibati.
Kiyi haquri hibbatu,bamuda yanda zamu iya,amma kiyi haquri zamuyi duk iya qoqarinmu wajen ganin ya tashi zuwa wani dan lokaci, da sauri hibbatu ta miqe ta fice da sauri ta fashe da kuka mai tsuma zuciya, tun lokacin da suka tsinci bawan Allah nan ita da dad dinta takejin qaunarsa a zuciyarta amma yanzu gashi ance ya shiga coma, kuma takeyi sosae har saida dad dinta ya fito,da lallami suka koma gida ba tareda sun sami gani
[10/05, 16:04] Hassan India: Miss collapse
👠SATAR FITA💃🏽
(160)
zuciyarta amma yanzu gashi ance ya shiga coma, kuma takeyi sosae har saida dad dinta ya fito,da lallami suka koma gida ba tareda sun sami ganinsa ba.
5 months later-
Ummy har yanzu sa'ad bai dawoba, naso ace yana nan yaga babynsa, kinsan meya cemun kwanaki?
Gyada kai ummy tayi a sanyaye hindatu tace cewa yayi idan muka haifi baby girl sunanki za'a saka idan kuma namiji ne sai asa sunansa,nikuma ummy a lokacin sai nace bazan haihu dashi ba saboda bana sonshi.
Amma ummy wlh yanzu inason ya sa'ad,inason mijina,inaso ya dawo yaga yayanmu kuma ya dauk....rungumeta ummy tayi cikin tausayawa da lallashi tana bata haquri.
2 months later, agogo ya nuna qarfe 5:50 na asbah, a zaune hindatu tayi sallah saboda tun jiya takejin azaba gashi har yanzu bai daina ba,kasa miqewa ma tayi yanzu sai kukan datake yi qasa2, tun tana daurewa harta fara ihu,da gudu ummy ta shigo dakin, hindatu naquda kikeyi! Ganin ba amsa yasa ummy ta kira masu akinta suka taimaka wajen saka hindatu a mota, ita da Abba ne suka kai hindatun asibiti,da sauri doctors din suka amsheta, kusan 3 hours ana abu daya, hindatu haihuwa taqi zuwa,kowa ya hallara a asibitin banda umma da baffa,doctor din ne ya fito a gaugauce,da sauri sukai kansa suna tambayar ya hindatun take? Ajiyar zuciya doctor yayi yace tana nan har yanzu bata sauka ba,amma tanata kiran sunan umma d baffa,idan suna nan ya kamata suje.
Doctor lafiya dai koh? Ummy ta tambaya jikinta a sanyaye,karki damu hajiya, kudai tabbata kun kirasu,daga hk ya koma ciki.
Alh ya kamata muje,nasan hindatu ta aikata kuskure babba amma a yanzu tana matuqar muqatar mu, alh kasan yanzu hindatu tana tsakanin duniya da lahira ne ya kamata muje mu ganta alh. Umma ta fada cikin marairaicewa. Ba yanda baffa ya iya,haka yaja umma suka tafi,sama2 suka gaisa da mutanen kafin su shiga, sautin ihun hindatu da salatin ta ne kawai yake tashi a dakin, da sauri umma ta qarasa ta tallabeta tana kiran sunanta, daqyar hindatu
[10/05, 16:04] Hassan India: Miss collapse
👠SATAR FITA💃🏽
(161)
daqyar hindatu ta iya cewa ummanah, qara damqe hannun umma tayi cikin axaba take cewa umma kema haka kikasha wuya da kika haifeni,ashe haka aka haihuwa! Umma ki yafemin wlh duk wanda baibi iyayensa ba ya tabe!ummah mutuwa zanyi baxan iya haifar babyn nan ba ki yafemun,baffah na na roqeka ku yafemun! Daqyar umma ta iya controlling kanta ta riqo hindatu dakyau tace xaki iya hindatu,duk macen da kika ganta da yaya haka take haifarsu kiyita salati zaki haihu,kiyi addua kinji.... wata gigitacciyar qara hindatu ta saki,cikin sauri doctor ya sallami su umma ya koma aikinsa,tsammaninsu haihuwa ce tazo,kusan 1 hour doctor ya fito,kansa sukayi d tambayoyi,daqyar ya samu suka nutsu sannan yace har yanzu bata haihu ba,haihuwar tazo gadan2 sai aka samu wata matsala, cikin firgici sukace matsala? Wata matsala doctor?
Hajiya matsalar da aka samu shine dan ya juya kuma yayi sama sosae, Ya zama dole ya juyoshi.
INNANILLAHI WA INNA ILAYHI RAJI'UN, umma tace dan bata mantawa irin matsalar data samu kenan lokacin d zata haifi hindatu,matsalar data taba mata mahaifa shiyasa bata sake haihuwa ba.
Shiru doctor din yayi sannan ya cigaba d cewa,a gaskiya akwai radadi mai tsanani d zata fuskanta, addua ce kawai zata fiddo ta,idan kuma har bata samu haihuwa ba ya zama dole ae mata operation, survival percentage 50/50. Bugun zuciyoyinsu ne ya qaru ummy ta fara qoqarin zubewa aka tarota, umma ce ta bawa doctor din go ahead, iya azaba hindatu tasha dan kusan 3 hours aka kwasa ana qoqarin juyo da babyn amma abu yaci tura, masu raunin zuciya n kuka masu dakiya idansu yayi jajir,kowa k ganshi kaga tashin hankali, Doctor din ne ya sake fitowa sukai kansa, shima cikin raunin murya yace babyn ya fara fitowa,washe baki suka farayi doctor ya girgiza kai cikin jimami yace amma ta qafafunsa! Ya ilahi,zo kuga tashin hankali,hajiya kuyi haquri we tried our level best amma abunda ya faru kenan, yanzu ya zama dole ku zaba ko DAN ko UWAR, a razane suka
[10/05, 16:04] Hassan India: Miss collapse
👠SATAR FITA💃🏽
(162)
a razane suka dago suka kalleshi, 2 mins decision hajiya. Save my daughter! Ummy tace a wahale, da sauri doctor ya juya, tausayin ummy gaba1 sukeji yanda ta qwallafa ranta akan cikin nan,kullum hirarta 1 amma yanzu gash..... sautin kukan babyn da sukaji ne yasa suka miqe a gaugauce, me hakan yake nufi?
A halin yanzu kam masu kuka sune suka rinjayi gurin dan kowa yayi tunanin hindatu ta mutu, kallon doctor din kawai sukeyi daya fito, baffa ne yayi qarfin halin cewa gawar tana ciki kenan?
Wata gawa kenan? Doctor ya fada a mamaki yace bance kowa ya rasu ba,in fact congratulations zance she gave birth to twins yanzu ma suna ciki ana gyarasu.
What! Da sauri sukai hanyar dakin doctor yace suyi haquri a gama gyarasu.
*** *** ***
Jalingo--
Gaba 1 family din gen. wada sun bayyana a asibitin kamar yanda doctor ya buqata,gskia gen. Nayi matuqar mamaki fardadowar patient dinka daga coma, mutane d dama sukanyi shekaru a coma qarshe ma su mutu amma gashi yaron ya fardado yanzu ya kamata kuje Ku ganshi, da saurinsu sukai dakin hibba ce a gaba, suna shiga ya bude idonsa, cikin sauri hibbatu ta qarasa tana cewa sannu,ya kake s jikinka? Shiru y musu bai tanka ba har suka fara tunanin ko baya mgn, hibbatu ce tayi tunanin zuwa ta kirawo doctor,har takai bakin qofa sukaji yace hindatuuu.....
Tsamm ta tsaya sannan ta juyo tana kallonsa, da sauri ta qaraso,gefen gadon ta dawo tana kallon parents dinta cikin mamaki sannan ta kalleshi da kyau tace ya akai kasan sunanah? Lumshe ido yayi baice komai ba ganin haka yasa hibbatu fita da gudu ta kirawo doctor, tambayarsa suka shiga yi amma ya musu shiru har doctor din yana tunanin ko kurma ne can sukaji yace ina ne nan?
Hospital! Hibba ta fada bakinta na rawa, ka dade anan, 7 months kuma b wanda y nemeka! Ya sunanka! K fadamun number wayan yan gidanku. Da ido ya bita kaman yanason tuno wani Abu, katseshi tayi tace malam sunanka nk tambaya.