[6/9, 3:36 PM] ρяσυ∂ℓу мє∂ι¢αℓ яє¢σя∂: TSATSUBA
Littafi Na Tara (9)
Part A
.
Marubucin Littafin
Abdul azis Sani M/Gini
AA Misau Me Magana
.
Labari ya Zowa Shagala Cewar:.....
.
LOKACIN DA DAKARUN SARKI, shardas suka fice daga
cikin falon gasar domin cika umarnin da yayi musu
na zuwa bayan gari su dauko masa matar attajiri
amsar bayan sun kashe dakarun dake tsaron lafiyarta.
Kawai sai sarki shardas ya tsugunna a gaban attajiri
amsar wanda har a sannan bai daina kakarin mutuwa ba
ya tallafo keyarsa da hannu guda ya dubeshi yace
ta yaya kake tsammanin cewa zan barka ka rayu alhalin
kafi ni kudi kuma kana da kyakkyawar matar da
bani da kamarta kuma kana da karfin sihirin tsafi na
ban mamaki
ta yaya zan barka ka lashe wannan gagarumar gasa
ka barni da abin kunya ?
To ka sani cewa komai sammakonka wani a tafe ya kwana, tun daga lokacin da akayi shelar wannan gasa nasa
bokana ya shiga bincike akan sirrinka, don haka da
gayya na gayyaceka izuwa wannan gasa domin naga
bayanka
sai a jiya ne bokan nawa ya gano cewa gaba daya
tasirin sihirinka na tsafi yana jikin kwagirin da kake rikewa
a hannunka
in ba don na fisgeshi daga hannunka ba da ba zan
taba iya kashe ka ba kaga kenan yanzu mutuwa zaka yi
na gaje duk dukiyar nan da ka zo da ita kuma na gaji
wannan kyakkyawar mata taka, Bani da wani buri
a doron kasa wanda ya fi na ajiye tarihin da babu wani
sarki ko wani boka ko jarumin da ya ajiyeshi, gama
fadin hakan keda wuya sai attajiri amsar ya yunkura
cikin karfin hali ya cakumi kwalar rigar sarki shardas ya
budi baki da kyar cikin murmushin karfin hali yace tabbas
ka sami nasarar hallakani to amma ka sani matata
tana da kariyar dani kaina bani da ita don haka ina tabbatar
maka da cewar har abada bazaka mallaketa ba
sannan kuma matata tana dauke da juna biyu tsawon wata biyar duk abinda ta haifa
namiji ko mace sune zasu dauki fansar raina a hannunka
bakin azzalumi
Koda gama fadin hakan sai idanun Attajiri amsar suka
kafe gaba dayan jikinsa ya sandare ya zama gawa
koda ganin haka sai sarki shardas ya kurma uban ihu
wanda ya razana kowa dake cikin dakin gasar
kawai sai ya zare takobinsa ya dubi wazirinsa ya
damka masa kubar gidan darul daulat yace kowa
ya fita ka kullue mini gidana, yanzu zan tafi izuwa
can bayan gari na gani ko dakaruna sun cika aikinsu
yana gama fadin hakan ya juya ya cife daga cikin gidan da
gudu ya shiga jirgin ruwa aka ketare kogin dashi
yana isa bakin gabar kogin ya fito daga cikin jirgin ruwan
ya sake hawa doki ya zabureshi da gudu ya nufi hanyar
bayan gari
da karfin sihirin tsafi sarki shardas ya shafe tafiyar kwana
uku a cikin yini guda kacal
amma kuma yana isa inda su matar attajiri amsar
suka yada sansani bai iske komai ba sai gawarwakin
dakarunsa dana attajiri amsar gaba dayansu babu
wanda ya tsira da rayuwarsa, ga keken dokin da matar
attajiri amsar ke ciki amma babu ita babu alamarta
Al amin Ahmed Misau, nan fa sarki shardas ya dimauce
kuma ya haukace yayi ta neman mahaifiyata a cikin daji
yana ihu yana kwallah mata kira amma shiru kamar
maye yaci shirwa
bisa dole ya hakura ya juya ya koma birninsa cikin tsananin
bakin ciki da
takaici
lokacin da yarinya Rulaiya tazo dai dai nan a labarinda take
baiwa yarima hulkas sai tayi shiru ga barin zancenta a lokacin
da hawaye ya zubo mata, cikin kaduwa da zumudi yarima
hulkas ya dubeta yace to daga nan kuma menene ya faru
ga mahaifiyarki shin guduwa tayi sa adda dakarun sarki
shardas suka kawo musu hari, koda jin wannan tambaya sai yarinya rulaiya
tasa hannu ta share hawayanta sannan tace mahaifiyata
ba gudu tayi ba ta bani labarin cewa agaban idanunka
aka fafata KAZAMIN YAKI tsakanin dakarun sarki shardas
dana mijinta masu tsaron lafiyarta kuma gaba dayansu
sai suka yi RAGAS
Faruwar hakan keda wuya sai taji jiri ya fara dibarta daga
can kuma sai ta yanke jiki ta fadi kasa sumammiya
lokacin da mahaifiyata ta farfado daga suman da tayi ne
sai ta tsinci kanta a cikin wannan gida kwance a kas a gaban
wani Aljani ma abocin kwarjini da ko a labari bata taba jin
kamarsa ba
Ba tare da aljanin ya gabatar da kansa a gareta ba ya dubeta
a lokacin da gaba dayan jikinta yake karkarwa saboda
firgita da ganinsa yace ki kwantar da hankalinki ya ke matar
sarkin attajiran duniya kiyi sani cewa babu mai cutar
dake anan iya tsawon rayuwarki, domin na daukarwa
mijinki wannan alkawari
Anan ne kadai zaki iya tsira daga sharrin abokan gabar
mijinki irin sarki shardas
Al amin Ahmed Misau, koda jin wannan batu sai
zuciyar mahaifiyata ta buga da karfi ta dafe kirjinta
da hannayanta biyu sannan ta dubi aljanin tace
ina labarin masoyina amsar shin an gama wannan ga sa ne
ta siyan gidan darul daulat ? Maimakon aljanin
ya bata amsar wannan tambaya sai yayi nuni da hannunsa
izuwa ga jikin bango take hoton duk abinda ya faru a
dakin gasar ya bayyana tun daga ranar farko har izuwa
zagaye na karshen gasar
koda mahaifiyata taga sarki shardas ya kashe mijinta
sai ta kwalla uban ihu ta sake sulalewa kasa sumammiya
wannan shine asalin sanadin da ya sa mahaifiyata
ta kamu da cutar ciwon zuciya kuma ciwon ne ya zamo
sanadin ajalinta bayan haihuwata da shekara shida
Bayan mutuwarta ne wannan aljani ya cigaba da
kula da
Ni kuma ya zamana cewa kullum yana koya mini yaki
yana mai cewa nan gaba zan dauki fansa akan makiyina
sarki shardas da ya kashe min mahaifina amma ba
yanzu ba sai idan lokacin yayi, lokacin da ban sani ba ke nan
har kawo i yanzu gashi
gaba dayan rayuwata ta kasance a cikin kadaici in ban da
uwata da kuma wannan aljani da ya cigaba da kula dani
kaine mahaluki na uku da na gani a gaba dayan
fadin wannan duniyar, koda yarinya rulaiya tazo nan
a labarinta sai ta fashe da matsanancin kuka
Al amin Ahmed Misau, Al amarin da ya sa yarima hulkas
yaji ya kamu da tsananin tausayinta kenan gami da matukar kaunarta fiye
da ko yaushe, don haka bai san sa adda shima idanunsa
suka kama zubar da hawaye ba, tsawon yan dakiku dayansu
baice uffan ba daga can sai ya dubeta cikin nutsuwa yace
yake rulaiya ai labarina da naki duk kusan iri daya ne
kuma abokin gabarmu guda ne, nan take yarima hulkas
ya zaiyane mata tun daga farko har karshe da yadda
akayi ma ya tsinci kansa a wannan gida nata da kuma
shirin da suke yi na tafiya neman hular lamsara don daukar
fansa akan sarki shardas
koda rulaiya taji wannan labari sai ta kamu da tsananin
Al'ajabi sannan tayi shiru tana tunani da nazari
daga can sai ta dago kai ta dubi yarima hulkas tace
duk yadda akayi aljanin da ya ceci rayuwar mahaifiyata
ya kawota nan kuma ya koya mini yaki shine ya daukoka
ya kawoka nan lallai akwai wata manufa a cikin hadamu da
yayi tunda duk burinmu iri guda ne, kash !
Zanso ace nima zanga yadda karshen gasar fadan
yar uwarka jaruma siyama zai kasance da sadauki Darkus
kuma zanso ace tare dani za ayi wannan gagarumar tafiya
ta neman HULAR LAMSARA
Kafin Rulaiya ta gama rufe bakinta sai kawai sukaga aljani
Arwasul masadul ya bayyana tsuluum ! A gabansu yana
mai kyalkyala dariyar farin ciki
kawai sai ya dubesu duk su biyun cikin murmushi yace
tabbas na gama cika aikina yanzu zan doraku akan tafarki
na karshe wanda zaku dauki fansa kamar yadda na yiwa iyayenku
alkawari
daga nan zaku tafi izuwa can birnin sarki hulbasu tare
kuma gobene za ayi wannan gasar ta karshe
ke rulaiya ki boye fuskarki ga kowa kuma ki zamo mai
taimakon su hulkas bisa duk abinda yazo musu
zan baku wani tsuntsu wanda zai yi muku jagora izuwa
inda hular lamsara take
ku sani cewa yanzu haka makiyanku sarki shardas tare da bokansa basu da burin
da yafi su hadu dani domin na sanar dasu inda hular
lamsara take amma wannan damar tuni ta wucesu
ina mai gargadinku da ku kula sosai da wannan tsuntsu
da zan hadaku dashi domin ko yaya ku kayi sakaci ya
subuce muku to fa zai koma hannun su sarki shardas ne
ya kai su izuwa inda
hular Lamsara take
idan kuwa sarki shardas ya rigaku taba hular lamsara to
dayanku ba zai tsira da rayuwarsa ba bare ma ya dauki
fansa akansa
koda gama fadin wannan jawabi sai Aljani Arwasul masadul ya bude tafin
hannunsa ya lumshe idanunsa yana mai karanta wadansu
dalasiman tsafi
faruwar hakan keda wuya ai ga wani farin tsuntsu dan
karami wanda baifi girman kanari ba ya baiyana akan
tafin hannun nasa gwanin ban sha awa, kawai sai ya
mikawa yarima hulkas tsuntsun yace kaine ka
cancanci rike wannan tsuntsu saboda kai kadai ne
ka haye jarrabawata a duniya kai yakamata ka mallaki
hular lamsara amma zanyi maka gargadi guda daya
Gargadin kuwa shine duk abinda zaka so to ka soshi
SAISA SAISA idan kuwa ka zurma a cikin soyayyarsa tabbas
wannan abu shine Ajalinka,
Hm Al amin Ahmed Misau Sunana, da wannan furuci nake
yi muku bankwana na karshe har abada ba zamu sake
haduwa daku ba
ina mai yi muku fatan samun nasara akan babban
makiyinku amma fa ku sani cewa aikin dake gabanku ya wuce yadda duk kuke zatonsa dole ne ku fuskanci
BARAK WUYA da hadarurrukan da ba lallai ba ku kaiga
gaci
Aljani Arwasul Masadul na gama fadin hakan sai ya bace
bat !
Tamkar bai taba wanzuwa ba a wajan, cikin rudewa yarima
hulkas ya dubi yarinya Rulaiya yace saboda me wannan
aljani zai tafi ya barmu ba tare da ya gaya mana yadda
zamu iya kai kanmu can birnin sarki hulbasu ba da kuma
yadda yakamata mu tafiyar da komai a cikin wannan
gagarumar tafiya dake
gabanmu
koda jin wannan batu sai rulaiya tayi murmushi sannan
tace lallai kai so kake ma ka sami komai kenan a bati ?
To ka sani cewa ba a zama wane a banza kuma sai ansha bakar
wuya sannan ake shan dadi
barina kimtsa sannan mu tafi ka jirani anan kada kayi
karambanin zuwa ko ina ko taba wani abu a cikin dakin nan
muddin bana kusa
Rulaiya na gama fadin haka sai ta juya ta nufi cikin wani daki
ta shige cikinsa ta rufe kofa
Shi kuwa yarima hulkas sai ya kara kamuwa da tsananin
mamaki yace a cikin ransa
' to wai shin menene a cikin wannan gidan mai hadari
wanda har rulaiya zata gargadeni da kada in Tabashi ?
Ai kuwa matsoraci baya zama gwani don haka bari na
yawata a cikin gidan nan na morewa idanuna kallo
Gama ayyana hakan keda wuya sai yarima hulkas ya kama yawo
a cikin gidan ya nufi
wani bangare daban yana kalle kalle yana mamakin irin
yadda ginin gidan da kuma kayan alatun da aka zuba acikinsa
nan take wani tunani ya fado masa a cikin zuciyarsa yace ni kuwa bayan mun sami nasarar kashe sarki shardas sai
na shiga cikin gidan darul daulat na gani tsakaninsa da
wannan gida nasu rulaiya wanne yafi girma da kawatuwa
a cikinsa
koda yarima hulkas yazo nan a zancen zucinsa sai
zuciyarsa ta buga da karfi tsoro ya kamashi ya tambayi
kansa yace '
saboda me zan bar wa rulaiya wannan gida da dumbin
dukiyar dake cikinta data kasance dukiya mai tsananin yawa
alhalin yane ranar farko dana fara ganinta a rayuwata
shin wannan yana nufin ke nan na kamu da tsananin sonta
fiye da yadda ma nake son iyayena da yar uwata
siyama
tunda gashi zan mallaka mata abinda su ban mallaka musu
ba
ai kuwa idan hakan ne maganar Aljani Arwasul masadul
ce zata tabbata gaskiya, wato zan hallaka a dalilin soyayya
kai ! Ba zai yuwu ba dole ne na takawa wannan soyayya
birki komai zai faru gareni sai dai ya faru !!
Yarima hulkas na cikin yin wannan tunani ne yaga wata kofar daki ta bakin
karfe wacce gaba dayanta a lullube take da yanah
a kura tamkar ma ba a taba bude ta ba, kawai sai yarima hulkas ya tunkari wannan kofa
da zuwansa daf da ita ya sa hannu ya murda marukinta
bisa mamaki sai yaga kofar ta bude ba tare da shakkar komai ba ya kunna kai cikin
dakin
koda yayi taku uku a cikin dakin sai yaji kofar dakin ta kulle
kanta
cikin sauri ya koma da baya ya kama kofar da nufin ya bude amma sai kofar taki buduwa
sai da yayi iya karfinsa har ya jike sharkaf da gumi amma
ya kasa bude kofar
koda ganin haka sai ya saduda ya juya ya sake nausawa
cikin dakin
ba komai a cikin dakin face tarin gumaka na dakarun yaki
fululu babu adadi
sai dai kowanne badakare yanayin shigarsa daban da dan
uwansa
kuma makamin yakinsa ma daban, gaba dayan wadannan dakarun yaki
suna da siffa ta kwarjini da ban tsoro duk kuwa da
cewa gumaka ne komai jarumtakar mutum da dakewar zuciyarsa sai ya
firgita da ganinsu saboda gani zaiyi tamkar masu raine
ba gumaka ba
nan fa uarima hulkas ya cigaba da ratsawa ta tsakiyar gumakan
dakarun domin ya isa karshensu, sai da ya yi yar doguwar
tafiya sannan ya iso karshen dakim, nan take yayi
arba da abinda yai matukar daure masa kai, Al amin
Ahmed Misau, ba komai ya gani ba face tarin dukiya
mai tsananin yawa tsubi tsubi zube a kasa ta lu u lu u
zinare da yakutu wacce inda za a yi aikin kwasheta da
magalar rakuma sai an shafe a kalla kwanaki dari ana
dibarta bata kare ba
koda yarima hulkas ya dubi jikin bangon dake gaban wannan
dukiya sai yaga anyi rubutu kamar Haka '- WANNAN DUKIYA
HARAMTACCIYACE GA KOWANNE MAHALUKI, BABU WANDA
YA ISA YA DAUKO KODA KWAYAR ZARRA A CIKINTA HAR YA FITA
DA ITA DAGA CIKIN WANNAN DAKI !!
sa adda yarima hulkas ya gama karanta wannan jawabi
sai ya bushe da dariya yace ka ji wani zancen banza kuma
ya ma za ayi ace wai ba zan iya daukar koda kwayar
zinare daya ba alhalin babu mai gadin wannan dukiya a cikin
wannan daki face wadannan gumakan banza ??
Gama fadin hakan ke da wuya sai yarima hulkas ya luma
hannunsa a cikin tarin lu'u lu'un ya duntso cikin
hannunsa ya zuba a cikin Aljihunsa, koda ya juyo da nufin ya koma da baya
can inda kofar dakin take sai kawai yaga gaba dayan
wadannan gumaka na dakarun yaki sun yi girgiza
sun zama rayayyu suna karkade kurar jikinsu gami da zare
makaman yakinsu
kuma gaba dayansu sai suka durfafo inda yake
cikin firgita yarima hulkas ya daka tsalle bay a dai dai
lokacin da daya daga cikin su ya kawo masa wawan sara
da wani katon barandami, koda yarima hulkas ya goce
barandamin ya sari wata dirkar gini mai kaurin gaske sai
dirkar ta rabe gida biyu ta fadi kasa saboda karfin saran
da kuma kaifin barandamin
Al amarin da ya kara razana yarima hulkas kenan
babu shiri ya zare takobinsa ya tari dakarun aka
ruguntsume da AZABABBEN YAKI......
to nima dai Al amin ganin wannan azababben yakin da
ake fafatawa yasani dakatawa a wannan waje
saboda haka sai kuma Allah ya kaimu gobe zan
cigaba daga inda na tsaya
Kafinnan Nidinne Dai
Al amin Ahmed Misau
Inkiya
Guyson Ko A square
Nake cewa Mu zama
lafiya..
[6/9, 3:36 PM] ρяσυ∂ℓу мє∂ι¢αℓ яє¢σя∂: TSATSUBA
Littafi Na Tara (9)
Part B.
.
Marubucin Littafin
Abdul azis Sani M/Gini
AA Misau Ke Magana
.
Labari ya Zowa Shagala Cewar:.....
.
.
Al amarin Da ya kara razana yarima hulkas kenan babu
shiri ya zare takobinsa ya tari dakarun aka ruguntsume da azababben yaki,
hakika masu iya magana sunyi gaskiya da sukace
tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa kan doka nan fa dakarun
yakin suka kuntata yarima hulkas suka rinka kai masa
SARA DA SUKA ta ko ina ya zamana cewa da kyar yake iya
kare kansa
idan ba don ma yana da zafin nama ba da tuni sunyi
gunduwa gunduwa da sassan jikinsa, nan take ya raina
kansa
nadama tazo masa bisa gangancin da yayi ya taba wannan
dukiya alhalin an gargadeshi, cikin kankanin lokaci
dakarun suka yiwa yarima hulkas rauni har guda biyar a
jikinsa ya zamana cewa jini na zubar masa kuma jiri
ya fara dibarsa amma saboda jarumtaka da juriya da
mugun naci yaki yarda yaje kasa, a haka ya cigaba da
maida martanin sara da sukan da suke kawo masa yana
kare miyagun hare harensu kokarinsa shine ya kutsa ta
tsakiyarsu ya isa can inda kofar dakin take ya sake jarraba
budeta amma sai abun ya gagara, Ana cikin wannan bakin
gumurzu ne daya daga cikin dakarun ya shammaci yarima hulkas ya gabza
masa wawan naushi a kasan habarsa saboda karfin
naushin sai da yarima hulkas yayi sama ya gwaru da rufin
dakin jini yayi feshi daaga cikin hancinsa da bakinsa ya
fado kasa tIm magashiyan, ai kuwa sai dakarun suka
yunkura da nufin su gididdibashi, kwatsam ! Sai suka ji an doki
kofar dakin ta balle daga
jikin garu ta fado kansu sama suna juyowa suka ga ashe
Rulaiya ce ta dako tsalle sama izuwa tsakiyarsu tayi
wata irin katantanwa ta tarwatsasu da saran takubban
hannayanta biyu
kafin su sake taso mata ta dira a gaban yarima hulkas wanda
ke kwance magashiyan kawai sai ta kama kafarsa da hannu
daya ta dagashi sama ta zazzage su, nan take duk lu'u lu un da yarima hulkas ya diba
ya zuba a cikin Aljihunsa ya zubo kasa
faruwar hakan keda wuya sai gaba dayan dakarun
yakin suka kame suka koma gumakansu tamkar
basu taba motsawa ba
A sannanne Rulaiya ta sunkuya ta dauki yarima hulkas
ta sabashi a kafadarta ta fice daga cikin dakin ta kaishi
can turakarta ta shiga dinke raunikan dake jikinsa
cikin gaggawa don ceto rayuwarsa, jaruma rulaiya na cikin yiwa yarima hulkas dinkine
a raunikansa kawai sai taga ya suma, bayan ta gama dinke
raunikan sai ta shafa masa magani sannan ta koma gefe
daya nesa kadan da kan gadon da ta shimfideshi ta
zauna akan wata kujera ta kura masa idanu
nan take taga ashe yarima hulkas kyakkyawane na gaske
Uhm Al amin Ahmed Misau, abin kwatance kuma
yana da kira sosai irin ta manyan sadaukai
kawai sai taji zuciyarta tana mai ayyana mata cewa wannan
shine irin namijin da yakamata ta aura nan gaba idan
ta girma ta cika cikakkiyar ya mace, wata zuciyar kuma
sai ta kwabeta ta ce da ita baki da hankaline? Ashe har
kin manta da kashedin da Aljani Arwasul masadul yayi
miki cewar
kada ki kuskura kiyi soyayya da wani da namiji a
lokacin yarintarki face kin isa aure? Koda gama aiyana
hakan sai rulaiya ta mike tsaye da sauri ta
fice daga cikin dakin, domin ta daina kallon fuskar yarima
hulkas kada zuciyarta ta kamu da sonsa, yarima hulkas bai
farka daga dogon suman da yayi ba sai kashe gari da sassafe
A firgice ya farka yana yin
arba da rulaiya zaune a gabansa tana kalaci sai ya dubeta
cikin tsananin farin ciki yace A wanne lokaci muke a
yanzu
Dare ne ko Safiya?
Shin mun makara wajen zuwa birnin sarki hulbasu domin
ganin gasar karshe ta yar uwata
Koda jin wannan tambaya
sai rulaiya tayi tsaki tace
ai idan ma muka makara kaine ka janyo ashe kunnenka na
kashi ne ban sani ba
me yasaka ka ki bin umarnina alhali na gargadeka
akan ka tsaya a inda na barka kuma na gaya maka
cewa kada ka taba komai a cikin gidan nan
in ba don nayi gaggawar kawo maka dauki ba da tuni
yanzu ka zama gawa
koda rulaiya tazo nan a jawabinta sai yarima hulkas ya Yunkura da kyar cikin
matukar karfin hali ya tashi zaune daga kwancen da
yake ya zuro kafafunsa daga kan gadon da nufin
ya takesu amma sai ya ji ya kasa saboda raunikan dake
kan cinyoyinsa
nan take takaici ya kamashi har kwallah ta ciko a idanunsa
ya dubi rulaiya cikin alamun karayar zuciya yace
ina rokonki da ki gafarta mini bisa rashin bin umarninki
kuma ina kara rokonki daki daukeni a haka cikin halin
da nake ciki ki kaini birnin sarki hulbasu akan lokaci
domin naga gasar nan ta karshe tsakanin yar uwata jaruma
siyama da sadauki Darkus
Koda jin wannan batu sai Rulaiya tayi tsaki tace
amma dai kai wawa ne wato kai bama ka damu da
lafiyarka ba kawai so kake na kaika kaje kayi kallon
gumurzun wasa
to ka sani cewa kai rago ne ba jarumi ba kuma baka iya
komai ba a yaki
Ba zaka iya tsinana abin arziki ba a cikin gagarumar
tafiyar dake gabanmu dole sai na baka horo mazaka
dauko dan jagoranmu ka rikeshi a hannunka yanzu nan
zamu tafi birnin sarki hulbasu kafin a fara wannan gasa
ga jagoran namu can a bayanka, koda gama fadin haka sai
rulaiya ta bude wata akwatu dake kusa da ita ta
debo kayan yaki ta shiga yin damara, shi kuwa yarima
hulkas sai ya waiga bayansa da sauri nan take yayi arba da
Wannan tsuntsun sihiri wanda aljani Arwasul masdul
ya bashi
kawai sai ya bude tafin hannunsa shi kuwa tsuntsun sai ya taso
a sama yana mai kada fuka fukansa ya dira akan hannunsa yana
mai kura masa idanu cikin murna, cikin kankanin lokaci rulaiya ta gama yin gagarumin
shigar yaki ta rataya tagwayen masu a gadon bayanta
bayan ta sanya wani bakin sulke da bakaken takalmi dogaye iya
kwaurinta sannan ta lullube
kanta da fuskarta da bakin mayafi ya zamana cewa
idanunta kadai ake gani a fili, koda gama wannan
kimtsawa sai ta suri yarima hulkas daga kan gadon da yake
kwance tamkar ta dauki buhun auduga ta goyashi a
bayanta suka fice daga cikin gidan gaba daya, shi kuwa
yarima hulkas sai ya damke tsuntsun sihirin a cikin
tafin hannunsa guda yana mai matukar farin ciki
bisa ganin cewa zasu tafi izuwa birnin sarki hulbasu
wajan iyayensa da yar uwarsa, da fitowarsu kofar gidan
sai yarima hulkas ya ga wani farin ingarman doki a tsaye
shi kadai yana harbin iska tamkar aikoshi akayi garesu
ba tare da jiran komai ba kuma ba tare da rulaiya ta dorawa
dokin sirdi ba sai ta kama dokin ta haye bayansa tana
goye da yarima hulkas din sannan tace dashi maza ka saki
wannan tsuntsu dake hannunka shine zai nuna mana hanyar
da zamu isa can inda kake so muje, koda jin haka
sai yarima hulkas yai sauri ya bude tafin hannunsa
nan take wannan farin tsuntsu ya tashi sama ya bi gabas
ai kuwa sai rulaiya ta zaburi dokin da gudu suka bi inda
tsuntsun ya nufa
nan fa yarima yaga dokin nasu yana yin wani irin
matsanancin gudu na ban al ajabi tamkar tashi sama
yayi domin karfin gudunsa yafi gaban kwatance
Al amin Ahmed Misau, abin da yarima hulkas ya
ayyana a ransa kawai shine wannan ba doki ba ne irin sauran dawakai kuma
tabbas yayi imani shi wannan sihirtaccen dokine
domin gani yake kamar dokin zai iya zagaye duniya
gaba dayanta a cikin rabin sa a
wannan shine abinda ya faru ga yarima hulkas bayan barci ya daukeshi a turakar
yarima barmas kuma ya farka ya tsinci kansa a wani wuri
daban mai ban Al'ajabi..
'' '' ''
AL AMARIN sarki shardas da bokansa labarusa kuwa
sai da suka kara shafe kwanaki tara cif a cikin daji suna
farautar Aljani Arwasul masadul amma duk tsawon wadannan
kwanaki basu sake haduwa da shi ba kuma ko duriyarsa basu
gani ba
Al amarin da yai matukar fusata sarki shardas kenan
ainun
bai san sa adda ya cakumi kwalar boka labarusa ba ya daka masa tsawa yace
kai labarusa ! Nifa na gaji da wannan farauta ta jaki
mai kaho ya zama dole a gareka ka gaggauta yin
bincike a cikin hallarar tsafinka ka gano mana wata
hanyar daban da zamu bi mu iya zuwa inda hular lamsara
take cikin gaggawa
Koda jin wannan batu sai boka labarusa ya fisge kwalar
rigarsa daga hannun sarki shardas ya dubeshi yace ka kwantar da hankalinka ya
shugabana idan ba don ance tsafi kogi bane da sai ince
dakai bamu da wata mafita ko hanya da za a samu wadda
zata kaimu ga mallakar hular lamsara cikin sauki da gaggawa
to amma ba a koda yaushe
kuma a kowanne irin yanayi a ko'ina komai na iya
sauyawa lokacin da ba a zata ba, ba zan ki ta taka ba
bari na duba mana na gani ko akwai wata mafitar
bayan wannan
gama fadin hakan keda wuya sai boka labarusa ya zauna a
kas dirshan cikin rairayi
sannan ya fiddo madubinsa na tsafi ya shiga karanta
wadansu dalasimai na tsafi irin wadanda sarki
shardas bai ma taba jin su ba, sai da boka labarusa ya dauki
lokaci mai tsawo yana shafa madubin tsafin nasa
idanunsa a rufe sannan ya tsaya cak, boka
labarusa yace ya dodon sarakai ka yi sani cewa a cikin
binciken nawa na gano mana wata hanya mafi sauki
wacce zata kaimu ga isa kogon da aka ajiye hular lamsara cikin
sauki da gaggawa
amma sai dai akwai wata matsala babba data bullo a cikin
wannan lamari
ka sani cewa yanzu a halin da ake ciki Aljanin da muke
farauta ruwa a jallo aljani Arwasul masadul sun hadu da
yarima hulkas harma ya bashi tsuntsun tsafi wanda zaiyi
masa jagora izuwa inda hular lamsara take
sannan kuma sai abu na biyu yarima hulkas ya hadu
da wata babbar sabuwar abokiyar gabar taka mai suna
Rulaiya
wadda take da burin daukar fansa akanka kuma a yanzu
haka ta goya yarima hulkas akan wani dokin sihirin
tsafi da Aljani arwasul masadul ya hadasu dashi
sun tafi izuwa birnin sarki hulbasu inda matarka shadila take
bisa jagorancin wannan tsuntsun sihiri da Arwasul masadul
ya bashi
Al amin Ahmed Misau, na gano cewa akwai wani
mugun shiri da ake yi maka a can birnin sarki hulbasu
don haka lallai ina tabbatar maka da cewa sarki hulbasu
yaci amanarka kuma yana son ya rabaka da matarka
shadila
a yaune za ayi gasar karshe ta jarumtaka a birnin nasa
kuma a yau dinne ya shirya kashe gaba dayan dakarunka
dake tsaron lafiyar gimbiya shadila, idan bamu je birnin ba akan lokaci zamu iske tuni
ya gama dasu
kuma yabi su yarima hulkas izuwa dauko hular lamsara
koda boka labarusa yazo dai dai nan a jawabinsa sai kan
sarki shardas ya daure ya cika da tsananin mamaki
da fargaba da kuma takaici, ya dubi boka labarusa
cikin damuwa yace akan wanne dalili sarki hulbasu
zaici amanata
alhalin yana tsananin sona?
Shin wacece wannan sabuwar abokiyar gaba tawa wacce
naji ka ambashi sunanta rulaiya wacce suke tare
da yarima hulkas? Koda jin wadannan tambayoyi
sai boka labarusa yace wannan sabuwar abokiyar gaba
taka ba wata bace face Yar attajiri Amsar wanda ka kashe shi
a cikin gidan darul daulat
bayan yaci gasar da kukai ta siyen gida a karshe ka gaje
dukiyarsa
babban burin wannan yarinya rulaiya a duniya shine
ta dauki fansar ran mahaifinta akanka kuma ta mallaki gidan darul daulat tunda
mallakin mahaifinta ne Attajiri Amsar, haka shima a yanzu
yarima hulkas bashi da wani buri wanda ya wuce ya hallaka ka
don daukar fansar abinda ka yiwa ubansa hailur da dukkan zuriarsu
ina mai sanar dakai cewa a halin yanzu tuni
hailur da matarka gimbiya shadila sun mayar da
auransu a cikin birnin sarki hulbasu Al amin Ahmed Misau
har sun tare a cikin wani kasaitaccen gida da
sarki hulbasu ya basu
koda boka labarusa yazo dai dai nan a zancensa sai
sarki shardas ya takarkare ya kwarara uban ihu
irin wanda ke tarwatsa mazaje a filin fama komai jarumtakarsu
da rashin tsoronsu
Kai inda ace akwai mace mai ciki a wajen da tuni ta
kama nakudar dole saboda firgita da za tayi na jin wannan
ihu na sarki shardas
kananun jarumai da dakarun yaki kuwa firgicewa
zasuyi su dimauta su kama sakin fitsari a wando
hehe Al amin Ahmed Misau, shi kansa boka labarusa
wannan ihu na sarki shardas ya razanashi yasa
zuciyarsa ta buga
tsuntsaye da dabbobin dake cikin dajin kuwa gaba dayansu
sai da suka kama guje guje da iface iface
suna sauya sheka da shigewa cikin ramuka
cikin matsanancin fishi sarki shardas ya dubi boka
labarusa yace maza ka hanzarta kaini birnin sarki hulbasu
kafin su yarima hulkas su isa can, cikin rawar jiki
boka labarusa yayi tsafi wani katon Aljani ya bayyana tsulum
a gabansa suka haye bayansa ya tashi dasu sama ya
luluka izuwa cikin gajimare yana mai tsala azababben gudu
tamkar tauraruwa mai wutsiya, Abinda sarki shardas bai sani ba shine shi
kansa boka labarusan bashi da tabbacin zasu iya isa
can birnin Na sarki hulbasu akan lokaci kafin komai ya gudana
+i ++ ++
ACAN birnin sarki hulbasu kuwa gari na wayewa aka tashi
da tsananin tashin hankali a gidan sarautar saboda an nemi yarima
hulkas sama da kasa an rasa
babu inda ba a duba ba acikin birnin ba har da cikin
dazuzzuka amma kamar maye yaci shirwa ga shi kuma
a can filin gasa jama a sun taru makil ana ta shewa
da ihu ana jiran isowar sarki hulbasu da su jaruma siyama
babu wanda yafi kowa tashin hankali sama da shadila
domin tunda akace yarima hulkas ya bata take ta faman
rusa kuka saboda gani take kamar ya fada hannun
sarki shardas ne
Da kyar hailu ya shawo kanta ya rarrasheta don kada ta
tarwatsa musu dukkan shirinsu na ranar inda ya tabbatar
mata da cewa yayi bincike a hallarar tsafinsa ya gano
cewa yarima hulkas na nan a raye kuma zai dawo kafin a gama
wannan gasa
nan dai ya lallabata suka shiga cikin ayarin sarki hulbasu
aka tafi filin gasa
koda jama a suka jiyo bushin Algaita da bugun
tambura alamar cewa sarki ya iso filin gasar sai filin
ya sake rudewa da shewa gami da tafi
nan fa aka bude kofar filin gasar sarki da mukarrabansa
suka shigo bisa
dawakai dakaru na take musu baya, amma abin da ya daurewa
kowa kai shine sarki hulbasu yayi gagarumar shigar yaki
tamkar yana cikin jaruman gasar
haka ma dakarunsa na musamman masu tsaron lafiyarsa
kuma a cikinsu
har da wadansu bakin dakaru wadanda suka rufe fuskokinsu
ba wasu bane wadannan
bakin dakarun da ke bayan sarki hulbasu ba face su jarumi hailur
Lokacin da dakarun sarki shardas masu tsaron lafiyar
gimbiya shadila sukaga sarki hulbasu ya fito da
wannan shiri sai suka sha jinin jikinsu suka fara
zargin cewa lallai akwai wani abu dake shirin yi musu
don haka sai suka fara yin kus kus a tsakaninsu
Al amin Ahmed Misau, Abinda basu sani ba shine
wanda duk ya rigaka kwana dole ne ya rigaka tashi
kuma maso abinka yafika dabara, jaruma siyama na daga cikin
tsakiyar dakarun sarki tayi gagarumar shigar yaki tare da
mahaifiyarta bisa doki guda,
koda yan kallo suka ga siyama sai suka rude da ihu aka
kama yi mata jinjina, ita dai kawai jaruma siyama tana
yin murmushin karfin haline amma hankalinta a wannan
rana a tashe yake saboda rashin ganin dan uwanta
yarima hulkas
Bayan sarki hulbasu da tawagarsa sun gama shigowa
filin gasar kuma sun zauna a inda aka tanadar musu sai
mai gabatarwa ya fara da kirawo sunan sadauki darkus
nan fa magoya bayan darkus suka rude da shewa gami
da tafi suka shiga yi masa kirari gami da jinjina
koda aka bude wata kofa sadauki darkus ya fito yana
tafiya kamar wani toron giwa a cikin gagarumar shigar
yaki sai filin gasar ya yi tsit tamkar mutuwa ta gifta
saboda kwarjininsu da karar sautin takun sawayensa
har sai da sadauki darkus ya iso tsakiyar filin gasar
ya tsaya mai gabatarwa ya kirawo sunan jaruma siyama sannan filin gasar ya sake
kaurewa da shewa gami da yafi, cikin nutsuwa jaruma
siyama ta fito daga cikin tawagar sarki hulbasu ta shiga
filin gasar, har sai da ta isa
Daf da sadauki darkus sannan ta ja ta tsaya a lokacin da
tazarar dake tsakaninta da sadauki darkus bata wuce taku uku ba, ba tare da bata
wani lokaci ba alkalan gasar suka bada umarnin a fara
gasa nan take, aka buga tambarin fara gumurzu
kamar hadin baki sai duk su biyun a lokaci guda
kowannansu ya juya da baya
yayi taku bakwai sannan suka tsaya suka juyo suna
masu zare takubbansu, kawai sai suka ruga da masifaffen
gudun tsiya tamkar zasu tashi sama suna masu
kwallah ihu mai firgitarwa suna jijjiga makamansu a
sararin samaniya
kafin su hadu sai kowannansu ya daka tsalle sama yakaiwa
dan uwansa mummunan sara..
Kai nima Al amin Ahmed Misau
ganin wannan saran ne yasa na tsaya a nan
nake cewa sai Allah ya kaimu gobe kafinnan
nidinne dai Al amin Ahmed Misau
inkiya Guyson Ko A square
daga Kaduna State..
[6/9, 3:36 PM] ρяσυ∂ℓу мє∂ι¢αℓ яє¢σя∂: TSATSUBA
Littafi Na Tara (9)
Part C.
.
Marubucin Littafin
Abdul azis Sani M/Gini
AA Misau Ke Magana
.
Labari ya Zowa Shagala Cewar:.....
.
Kafin su hadu sai kowannan su ya daka tsalle sama ya kaiwa
dan uwansa mummunan sara , duka su biyun a tare suka duro kasa lokacin suna
masu juyawa junansu baya, bisa mamaki sai aka ga
kowannansu ya tsaya cak a inda yake ba tare da
ya juyo ya cigaba da yaki ba, Al amarin da ya baiwa
kowa mamaki kenan A filin Gasar harni kaina Al amin da nake
typing aka sake yin tsit a karo na biyu
daga can kuma sai aka ga jaruma siyama da sadauki
darkus sun waigo sun fuskanci juna shi yana mai dafe saman
kirjinsa jini na zuba ita kuma tana mai dafa hakarkarinta
Na hagu jini na zuba
A sannan ne yan kallo suka gane cewa ashe kowannansu
ya samu nasarar yiwa dan uwansa mugun rauni
Cikin matukar juriya da jarumtaka sadauki darkus ya yagi
rigarsa ya daure kirjin nasa tamau don tsaida jini
itama jaruma siyama sai tayi sauri ta cire mayafin dake
zagaye a wuyanta ta daure hakarkarin nata
ba tare da jiran komai ba sai suka rugo izuwa kan juna suka
kacame da masifaffen yaki mai matukar ban tsoro da ban
al ajabi
a wannan lokaci mahaifiyar siyama na zaune daf
da hailur kuma tuni ta fara kuka bisa ganin yadda aka
yiwa yarta rauni tun a farkon fara wannan gasa
shikuwa hailur sai ya dubeta yace kwantar da hankalinki
yake matata ni na san ko wacece yata ina mai tabbatar miki
da cewa ba zata mutu ba kuma ita ce zata lashe
wannan gasa
sai da aka shafe sa auku cur ana wannan mummunan
BAKIN ARTABU tsakanin sadauki darkus da jaruma
siyama ya zamana cewa sun galabaitar da juna domin kowannan ya sami rauni kimanin guda biyu a jikinsa jiri ne ke
dibarsu tamkar zasu sake yin RAGAS saboda karfi
yazo daya
ana cikin haka ne sadauki darkus ya shammaci jaruma
siyama
ya dankara mata wani karkarfan naushi a ciki saboda karfin
naushin sai da jaruma siyama tayi sama da baya bayanta
yaje ya gwaru da katangar filin gasar ta fado kasa da rub
da ciki a matukar galabaice tana aman jini
koda sadauki darkus yaga ya sami wannan nasara sai ya
bushe da dariyar mugunta ya
daga takobinsa sama ya ruga izuwa inda
take ya daka tsalle sama da nufin ya duro kanta ya soke gadon
bayanta
tuni a wannan lokaci kowa ya gama sallamawa cewa
jaruma siyama ta mutu
ba zato ba tsammani sai aka ga jaruma siyama ta mirgina
can gefe guda takobin sadauki darkus ta lume a cikin
kasa
kafin sadauki darkus ya zaro takobin tuni siyama ta doki
kasa da tafin hannayanta biyu kawai sai gani
akayi tayi sama kuma tayi katantanwa sannan ta doki kirjin sadauki
darkus da kafafunta biyu, saboda karfin dukan sai da
shima sadauki darkus yayi sama yaje ya gwara bayansa
a jikin katangar filin gasar ya fado kasa a kan fuskarsa
fuskar tasa ta dauje jini ya rufe masa idanu
kafin a goge jinin dake kan idanun nasa tuni siyama ta daka
sufa a sama izuwa inda takobinsa take ta zarota daga cikin
kasa ta luma masa ita a ciki
take takobin ta faso gadon bayansa sadauki darkus yayi
mutuwar tsaye ya sandare
kawai sai jaruma siyama tasa kafarta ta sake dukan kirjinsa
sannan gawar tasa ta fadi kasa
rikica kamar giwa ta fadi
nan fa filin gasar ya rude da shewa gami da tafi ana yiwa jaruma siyama
kirari bisa wannan gasa bayan ta kashe sadauki
darkus
a wannan lokaci ne kuma kwatsam sai aka ga jaruma siyama ta yanke jiki
ta fadi kasa sumammiya
A guje likitan sarki hulbasu da masu taimaka masa
suka ruga zuwa filin gasar kan jaruma siyama don bata
taimakon gaggawa
a dai dai wannan lokaci ne hailur yazo daf da kunnen
sarki hulbasu yayi masa rada yace ya shugabana gada
daya fa dakarun sarki shardas da suka rako shadila duk sun
sulale sun gudu ga dukkan alamu sun
gano shirinmu da jin wannan batu sai sarki hulbasu yayi
murmushi yace ai nima tun dazu na lura da hakan amma ko kadan ban damu ba saboda
na san cewa duk shirin da zasu yi a yanzu ba zai kai namu ba
maza kaje ka karasa shirin komai ni da dakaru zamu fara yin gaba saika taho
da sauran iyalansu
gama fadin hakan keda wuya sai aka ga wani karamin tsuntsu ya shigo filin gasar
a sama
bai dira a ko ina ba sai akan jaruma siyama wacce ke
kwance magashiyan likita na yi mata magani
tsuntsun na dira akanta sai aka ga ta bude idanunta ta
rmike tsaye zumbur tamkar babu abinda ya sameta ta kurawa bakin kofar fita
daga filin gasar idanu
A dai dai wannan lokaci ne aka jiyo sukuwar doki ya nufo
cikin filin gasar
tashin kurane ya hana ganin dokin amma kurar na lafawa
sai aka ga ashe wani farin ingarman doki ne dauke da mutum biyu
na gaban dokin yarima hulkas ne na bayansa kuwa
wani jarumi ne a cikin shigar bakake tufafi
goye da tagwayen masu
koda jaruma siyama ta hango dan uwanta yarima hulkas
bisa doki ya tunkarota sai fuskarta ta fadada da murmushi
ta ruga gareshi da gudu
Nan take shima yarima hulkas ya duro daga kan dokin ya
karasa gareta a guje suka rungume juna cikin
tsananin farin ciki yana ma tayata murnar lashe wannan gasa
a dai dai wannan lokaci ne yarima hulkas yaji an dafa
kafadarsa ta baya
yana waigawa yaga ashe sarki hulbasu ne shima ya rungumeshi cikin farin ciki
sarki hulbasu yayi masa rada a kunne yace bamu
da isashshen lokacin
Lokacin yin wani bayani ga juna yanzu domin yin
hakan zai sa mu bata lokaci yanzu mun gama shirin komai
dama kai kadai muke jira
maza ka dauko yar uwarka akan wannan doki naku duk da
cewa ku uku ne ku sameni a bayan gari mahaifinka ma zai riskemu a can
nan take aka kawowa sarki hulbasu dokinsa ya hau
dakarunsa suka take masa baya a lokacin da ya
zaburi dokin nasa da gudu ya fice daga filin gasar
Al amarin da ya daurewa yan kallo kai ke nan suka cika
da tsananin mamakin dalilin da ya hana a tsaya a bayar
da kyauta ga jarumar da ta lashe wannan jarumtakar da
akayi wato jaruma siyama
nan dai filin gasar ya waste mutane suka tafi suna
hasashe da zargin cewa lallai babu lafiya yau
Al amin Ahmed Misau,
Al amarin dakarun sarki shardas kuwa ashe gaba dayan
suka sulale daga cikin filin gasar suka ruga izuwa cikin daji
inda suka sake haduwa suka tattauna akan yadda za su sace gimbiya shadila cikin ruwan
sanyi
domin su mayar da ita gida kada fishin sarki shardas
ya hau kansu
nan take shugabansu sadauki Murzanu ya dubesu yace
na yarda da jarumtakarku da nacinku gami da iya
yakinku
saboda haka yanzu zamu koma izuwa cikin wannan birni
na askandariyya daya bayan
daya kamar yadda muka hadu a nan yanzu
kuma sai dare ya raba sannan zamu shiga har cikin gidan
sarautar sarki hulbasu mu aiwatar da nufinmu
A halin yanzu sarki hulbasu ya gaya mini cewa yanzu
zai mana rakiya tare da gimbiya shadila da dakarunsa domin mu isa gida lafiya
na nuna masa cewa na amince da hakan amma na san karya
yake yi so yake ya shirya mana wani tuggun ya cutar damu
shi yasa nace mu rarrabu mu buya a cikin birnin nasa ba
tare da ya sani ba
tuni na aika da dakarun yan leken asiri domin su kai labarin abinda
yake faruwa ga can birninmu
saboda a sanar da sarki halin da muke ciki ta hanyar
karfin sihiri a duk inda yake
koda sadauki murzanu yazo nan a zancensa sai ya sallami
gaba dayan dakarun nasa suka rarrabu a cikin
shiga ta bad da kama suka bi hanyoyi daban daban
shi dai sadauki marzanu tare da wadansu dakarun
nasa mutum dari biyu sai suka bi wata barauniyar
hanya ta bayan wani katon tsauni sai da suka yi yar doguwar
tafiya ta kusan tsawon dakika dari bakwai da arba in sai suka
yi kicibis da sadauki Ruhaisu babban yaron hailur shima dakarunsa mutum
dari biyu da goma na take masa baya, cikin tsananin kaduwa
da mamaki sai sadauki marzanu suka tsaya cak suka
dora hannayansu akan kufen takubbansu domin basu
taba zaton cewa za a tarfasu ba haka, suma su sadauki
ruhaisu sai suka dora hannayansu akan kufen takubban
aka fara kallan - kallo
Al amin Ahmed Misau, Take sadauki marzanu ya
tuno da sadauki ruhaisu sa adda suka fafata kazamin yaki
a can shekarun baya sa adda sarki shardas ya kaiwa
kabilar su hailur hari suka karkashe su har sarki shardas yaje fa hailur kasan
wannan tsauni mai tsawon gaske kuma ya dauke
matarsa shadila ya tafi da ita
koda shima ruhaisu ya gene sadauki marzanu sai zuciyarsa ta kama tafarfasa
kamar zata kone saboda tsananin kiyayyar dake taso masa
cikin tsananin fishi ya dubi sadauki marzanu yace
yakai tsohon abokin gaba kayi sani cewa jama arku da sarkinku sun dasa
mana bakin cikin da har abada ba zamu taba mantawa
dashi ba
amma na dade ina jiran wannan rana da takobina zata dau fansar
jinin kabilata akanku
na rantse da darajar shugaba hailur tsakaninmu daku dole ne wasu su zama
gawa anan kafin
mu rabu
koda jin wannan batu sai sadauki marzanu ya bushe da dariyar mugunta yace
kai samari hakika tsautsayi ne ya sa kuka yi wannan
babban ganganci na tunanin taremu da yaki
da kuma kokarin kwacewa sarki matarsa, ina mai tabbatar
maka da cewa a wannan karon sai mun karar da ku gaba dayanku
ta yadda har abada ba za a kara ganin irin
zuri arku ba a doron kasa, koda sadauki marzanu
yazo nan a zancensa sai sadauki ruhaisu ya tari
numfashinsa yana mai daka masa tsawa yace kai
wawa mara hankali da tunani shin ka manta ne cewa sarkin
naku ne ya fara kwatar matar mu ?? Yanzu ne zamu dawo
da abarmu garemu kuma mu dauki fansar jinin yan uwanmu da kuka salwantar ka
sani cewa ku azzalumai ne masu cin zarafin talakawa
sata kwace da danne hakki tsawon shekaru
to ku sani cewa shi ramin karya kurarre ne kuma gaskiya
dokin karfe ce wanda baya taba mutuwa
koda gama fadin hakan sai sadauki ruhaisu ya zare takobinsa ya yiwa
dakarunsa nuni da a afkawa abokan gaba, ai kuwa ba su tsawa jiran komai ba sai
suka zare takubbansu cikin hanzari suma su sadauki marzanu suka zare nasu
takubban aka ruguntsume da azababben yaki
nan fa wuri ya hargitse kura ta tashi karar karafa da
kururuwar mazaje ta fara cika kunnuwa
-- -- --
RAGOWAR dakarun murzanu kuwa su dubu daya da dari
takwas sun sake rarrabuwa izuwa mutum dari hurhudu
wannan shine babban kuskuren da suka tafka domin
inda a cure suke gaba daya sai an kai ruwa rana kuma an kai
gwauro an kai mari kafin a ci galaba a kansu
++ ++ ++
MUTUM dari hudu da suka nufi gabashin birnin askandariyya
sai suka yi kicibis da tawagar sarki hulbasu
nan ma sai aka kacame da
Yaki amma da yake su sarki hulbasu sun ninkasu sau
goma a yawa nan suka karkashesu a cikin kankanin lokaci basu bar daya ya tsira
da rayuwarsa ba
++ ++ ++
DAKARUN da suka nufi yammacin birnin kuwa sai sukayi
kicibis da yarima hulkas jaruma siyama da jaruma rulaiya
bisa doki guda su uku, koda ganinsu sai yarima hulkas
da siyama suka zare takubbansu da nufin su afka musu amma
sai jaruma rulaiya ta dakatar dasu tana mai daga musu hannu
har izuwa wannan lokaci
rulaiya bata yarda koda jaruma siyama taga fuskarta ba
domin a rufe take cikin bakin kyalle, take jaruma
rulaiya ta duro kasa daga kan dokinta ta dubi
dakarun nasu sadauki murzanu taga basu fi su dari
hudu ba
kawai sai tayi tsaki sannan ta juya ta dubi yarima hulkas
tace ai abin kunya ne ace mu ukun nan ne zamu yaki wadannan
kananan kwari kawai ku barni dasu rabin sa'a tayi
min yawa na gama dasu
koda gama jin wannan batu sai dakarun sadauki marzanu suka
fusata ainun suka zare takubbansu suka afkawa jaruma rulaiya gaba dayansu
Wohoho Hakika mai karfi sai Allah ya isa kuma duk wanda
ya iya ya huta
ana fara wannan yaki sai jaruma siyama ta cika da tsananin mamaki bisa ganin irin
jarumtakar jaruma rulaiya da kuma tsananin zafin namanta, domin duk yawan dakarun su
dari hudu sai ya zama na
banza
saboda duk inda ta kutsa a cikinsu sai dai kaga maza na zubewa kasa
domin gididdibasu ta rinka yi sassan jikinsu
ya rinka zubewa yana faduwa kasa suna ihu kuma jini
na feshi da fantsama
Al amin Ahmed Misau
Nan fa aka rasa mutum daya daga cikin dakarun wanda
ya sami nasarar koda lakutar jikin jaruma rulaiya nan take
jaruma siyama ta raina dukkan jarumtakarta ta fara
tunanin cewa duk yadda akayi wannan hatsabibiyar bakuwar jaruma wacce yarima hulkas yazo da ita ba
mutum bace Aljana ce
Koda gama ayyana hakan a cikin zuciyarta sai ta kasa
hakuri ta dubi yarima hulkas tace yakai dan uwana wai shin
wacece wannan bakuwar jarumar da ka zo da ita
kuma a ina ka sameta har yanzu ta fa ka bani labarin
inda ka tafi ba muka nemeka muka rasa
koda jin wannan tambaya sai jarimi hulkas yayi murmushi yace me yasa baki da hakuri
ne yake yar uwata yanzu ina nake da lokacin baki
labari a cikin wannan yanayi da muke ciki ki bari sai mun
gama da wadannan abokan gaba namu tukunna
mun isa can inda hular lamsara take in yaso bayan mun
daukota mun kashe sarki shardas sai mu zauna na
baku labari keda iyayenmu a cikin nutsuwa da kwanciyar
hankali
koda jin haka sai jaruma siyama ta bata rai tace yama za ayi
nayi ta hakurin jin wannan labari har sai mun kai ga
wannan lokaci
me ye tabbacinka ma cewa zamu tsira da rayukanmu
har mu sami nasarar dauko hular lamsara
har yarima hulkas yabudi baki zai ce da ita wani abu
sai ya ga jaruma rulaiya ta daka tsalle sama ta kama yin
wata irin katantanwa a sama
tana fille kawunan dakarun
sarki shardas
nan da nan ta karar da sauransu gaba daya
ya zamana cewa babu dayansu da ya rage a raye
saboda tsananin mamakin wannan gagarumar jarumtaka
da jaruma rulaiya tayi
yarima hulkas da siyama basu sansa adda suka wangame
bakunansu ba suna kallonta
koda jaruma rulaiya ta dago kanta ta dubesu sa adda take goge
jinin takobinta a jikin gawar abokan gabar da ta kashe taga ririn kallon da suke yi mata na al ajabi sai
tayi murmushi ta dubi yarima hulkas tace
kuzo mu yi sauri mu karasa gaba tunda bamu san halin
da sauran yan uwanmu suke ciki ba
ba tare da wani bata lokaci ba sai suka kara hawa kan
wannan dokin sihiri na
jaruma rulaiya su ukun suka zabureshi
da gudu izuwa gaba saboda girman wannan doki
da cikarsa duk su ukun sai da suka zamo yan kanana akansa
Al amin Ahmed Misau
++
ACAN Inda yaki ya ruguntsume kuwa tsakanin su sadauki
ruhaisu da su murzanu abin ya kazanta babu kyan gani saboda karfin yazo daya domin ragargazar kowanne bangare ake yi
har ta kai cewa ana ta yin ragas
sai da aka shafe sa a daya da rabi ana wannan mugun yaki
har ya zamana cewa an karar da gaba dayan dakarun kowanne bangare
saura mutum biyu kacal suna fafatawa, wato saura
Sadauki Ruhaisu da Murzanu gashi dai kowannansu ya yiwa
dan uwansa raunika har guda uku uku jini na zuba a jikinsu
juwa na dibarsu amma saboda tsananin nacinsu
da mugun buri na son ganin bayan juna kowannansu
yaki yarda yaje kasa
Lokacin da bala'i yakai bala'i ya zamana cewa sun
gaji likis sai suka zube kasa bisa guiwoyinsu suna haki da numfarfashi
kamar ransu zai fita
bayan dan wani lokaci sai kowannan su ya mike
tsaye da kyar
sannan suka ja da baya taku bakwai bakwai
tamkar sun hakura da yakar juna kwatsam kuma sai suka rugo
da gudu
izuwa kan juna suna masu kwalla ihu cikin mugun nufi
duk wanda yaga lokacin da wadannan manyan
jarumai suka tunkari junansu kasan cewa mugun gamo
za ayi ko dai a mutu ko kuma ayiwa juna mugun
lahani
da zai iya zama sanadin Ajali, ai kuwa yana ragewa
saura taku uku kacal su hadu sai kowannansu ya daka
tsalle sama suka kaiwa junan su suka da takubbansu
cikin sa'a kuwa kowannansu ya lumawa abokin
fadansa takobi a ciki ta faso ta gadon bayansa
lokaci guda suka kurma uban ihu sakamakon
Tsananin zafi da zogin da suka ji suka rikito kasa a matukar
galabaice suka kurawa juna idanu sa adda suka fara kakarin
mutuwa bisa mamaki sai sadauki murzanu yaji sadauki
Ruhaisu ya bushe da dariyar farin ciki don haka sai ya dubeshi
cikin matukar karfin hali ya budi baki da kyar yace
yakai makiyi abokin gaba tayaya aka yi kai da zaka mutu
amma kake yin dariyar murna, koda jin wannan batu sai sadauki ruhaisu ya yi kakin jini ya tofar
sannan shima ya budi baki
da kyar yace
ina farin ciki ne zan mutu bayan na cika burina na
yiwa takobina wanka da jininku yanzu ne yan uwana da kuka
kashe zasuyi barci mai dadi a cikin kabarurrukansu
hm Al amin nake typin Dan Misau, kuma idan naje na
riskesu zasu yi alfahari dani kai fa da wani farin ciki zaka
mutu ? Shin zakayi alfahari ne da cewa ka mutu dan
bautar sarki shardas wanda ya maishe daku karnukan
farautarsa ko kuwa ?
Me kabar wa iyalinka wanda zasu cigaba da rike kansu
bayan ka mutu ?
Na sani cewa kan yiwa sarki shardas bauta saboda kana
tsoronsa amma ba don kuna samun wani abu a hannunsa ba
yanzu me ce ribarka a cikin bautar sarki shardas ga shi kayi
mutuwar banza idan ma shardas yazo nan yaga
gawarka yawu zai tofa maka tunda baka cika aikinsa ba
wannan batu sai nan take sadauki murzanu yaji
yayi nadamar rayuwarsa a karon farko domin ya gane
kuskurensa nan take hawayen takaici da bakin ciki ya zobo masa kawai sai
ya sake dannan takobin Ruhaisu a cikinsa ya zama cikakken
Gawa.....
Wow Nima Al amin A nan zan dakata sai Allah ya kaimu Gobe zakuji ni da part na karshe
a cikin littafin tsatsuba
Kafinnan nidinne dai
Al amin Ahmed Misau
Inkiya
Guyson Ko A square
[6/9, 3:36 PM] ρяσυ∂ℓу мє∂ι¢αℓ яє¢σя∂: TSATSUBA
Littafi Na Tara (9)
Part D.
.
TAKUN KARSHE..
Marubucin Littafin
Abdul azis Sani M/Gini
AA Misau Ke Magana
.
Labari ya Zowa Shagala Cewar:.....
.
Koda jin wannan batu sai nan take sadauki murzanu yaji
yayi nadamar rayuwarsa a karon farko domin ya gane
kuskurensa nan take hawayen takaici da bakin ciki ya zobo masa kawai sai
ya sake dannan takobin Ruhaisu a cikinsa ya zama cikakken
Gawa.
Shi kuwa sadauki ruhaisu yana cikin wannan hali ne
na kakarin mutuwa ya hango hailur bisa doki da a
sukwane tare da sauran tsirarun yan kabilarsu
Tun daga nesa da hailur ya hango sadauki ruhaisu
zaune a kasa dirshan ga takobi a cikinsa sai ya rusa
uban ihu cikin kwalla masa kira kuma ya fashe da
kuka yana mai karawa dokinsa kaimin gudu
Yana isowa daf dashi sai yayi turjiya ya sauko
daga kan dokin ya durkushe a gabansa sannan ya kamashi
ya rungume a kirjinsa yana mai sake fashewa da
sabon kuka cikin Karfin hali sadauki ruhaisu ya daga hannunsa
ya kama kumatun
hailur suka dubi juna kowannansu na zubar da hawaye
amma sai sadauki ruhaisu yayi murmushi a gareshi
yace yakai dan uwana bai kamata kayi mini kuka ba
tunda na mutu akan tafarkin cika burin kabilar mu
alfaharina guda daya ina so ka dauke gawata ka kaita zuwa
can asalin birninmu wanda sarki shardas ya baje ka binneta
wannan itace kadai wasiyyar da zan bari bayan
raina
koda gama fadin haka sai idanun sadauki ruhaisu
suka kafe suka daina motsi kuma gaba dayan jikinsa ya
sandare
koda ganin haka sai hailur ya sake kwarara uban ihu a
karo na biyu ya rungume gawar sadauki ruhaisu
kuma ya sake fashewa da matsanancin kuka
nan take ragowar dakarun nasa dasu shadila suka kamu
da tsananin tausayi kuma suka kama kuka
basu bar wannan waje ba sai da hailur ya sa aka je aka
dauko akwatun gawa na katako aka sa sadauki ruhaisu
a ciki aka kulle sannan suka kara gaba inda suka iske tawagar
sarki hulbasu da su yarima hulkas suna yin wata irin
tafiya ta ban Al'ajabi domin da karfin sihirin tsafi suke yinta
cikin tsananin gudu na ban al ajabi kuma wannan farar
tsuntsuwa ta sihiri ce take yi musu jagora don zuwa inda hular lamsara take..
Al amin Ahmed Misau
ACAN BIRNIN askandariyya kuwa sai bayan tafiyar su yarima
hulkas da tazarar sa a bakwai sannan aka ga wata irin gagarumar iska tana saukowa kasa daga sama
wadda ta dugunzuma hankalin komai da kowa dake
birnin saboda karfinta
nan fa bishiya suka rinka karyewa suna zubewa kasa rufin gidaje ya rinka kwayewa kasa
ya kama girgiza
ba komai ne ya haddasa wannan masifa ba face iskar
fuka fukan aljanin dake dauke da sarki shardas da bokansa
labarusa
sai da aljanin ya duro kasa bisa tsakiyar gidan sarautar
sarki hulbasu sannan inda ya duro din ya wawake yayi rami
mai zurfi sannan iska ta dauke
nan fa jama a suka kama guje guje da iface iface aka dimauce sosai kai kace
sama da kasa ce zata hade saboda tsananin razanar da
jama ar suka yi sakamakon ganin abubuwan uku wato
ganin wannan shirgegen Aljani da kuma sarki shardas
da bokansa Labarusa
har sarki shardas ya zare takobinsa zai nausa cikin
gidan sarautar sarki hulbasu sai boka labarusa ya
tsaidashi ya dauko madubinsa na tsafi ya nunawa sarki
shardas abin da ya faru a birnin kafin su iso
koda sarki shardas yaga yadda aka kashe gaba dayan
dakarunsa su sadauki murzanu a bayan gari da dukkan
shirin da su yarima hulkas sukayi aka gudu da matarsa
shadila sai ya kamu da tsananin bakin ciki nan take gaba
dayan jikinsa ya kama makyarkyata kamar wanda aka tsoma a cikin ruwan
kankara
Al amin Ahmed Misau, zuciyarsa kuwa ta kama tafarfasa
kamar zata kone bai san sa adda ya dakawa bokan nasa
labarusa tsawa ba yace tsayuwar me muke yi a nan
alhalin kana gani makyanmu sun tafi dauko hular
lamsara maza muje mu kure musu gudu mu karkashesu
cikin alamun tsananin tashin hankali da karayar zuciya
boka labarusa yace ai zuwa da wuri yafi zuwa da wurwuri
idan muka ce zamu cigaba da wannan tafiya a wannan
aljani ba zamu taba iya riskar abokan gabarmu ba
kafin su isa inda hular lamsara take, wannan dokin
sihiri da yarima hulkas yake bisa yafi wannan aljani
namu karfin gudu sau arba in dole ne mu samo wani
doki wanda zai iya cin musu, cikin zakuwa sarki
shardas ya ce
to taya zamu iya samo namu dokin da zai cimma
nasu?
Koda jin wannan tambaya sai bokan ya zauna a kasa
dirshan ya karanta wadansu dalasiman tsafi na musamman guda uku ya
tofa akan tafin hannunsa na hagu sannan ya doki kasa da
tafin hannunsa sau uku
faruwar hakan keda wuya sai kasa ta fara girgiza a gabansa
nan take ta dare sai ga wani murgujejen jan doki
ya faso daga cikinta girman wannan doki ya ninka
nasu yarima shardas sau uku
koda ganin wannan doki sai boka labarusa ya mike
tsaye zumbur cikin matukar farinciki ya shafi dokin
sannan ya dubi sarki shardas cikin murmushi yace ya shugabana
ina tabbatar maka da cewa
a cikin sa a iku kacal
wannan doki zai iya cimma su yarima hulkas muna
riskarsu sai mu kashesu mu kwace wannan tsuntsu na
sihiri tayi mana jagora izuwa inda hular lamsara take
koda jin wannan jawabi daga bakin boka labarusa
sai sarki shardas ya daka tsalle ya haye bisa kan jan
Dokin
shi kuwa boka labarusa sai ya bace bat ya sake bayya
akan dokin kuma a gaban sarki shardas ya juyo ya dubeshi
cikin murmushi
yace to sarkin sauri saika sarrafa dokin na gani idan
zaka iya
sarki shardas ya mai dawa boka labarusa murmushi yace
ai kowa a bangarensa sarki ne inda dai batun karfi ne ko jarumtaka nine
zan jagoranceka wannan aikinka ne ba nawa ba
da jin haka sai boka labarusa ya bushe da dariya
Nima Al amin Ahmed Misau na tayasu sannan ya shafi
wuyan dokin kawai sai dokin ya zabura da karfi ya
falfala da azababben gudu na gaban kwatance da al ajabi
saboda karfin gudun dokin har tashi sama yake yana
tsallake gidaje koguna da tsaunika kuma a cikin dakika
biyar kacal ya ke shafe tafiyar sa a goma,
Hakika tsafi gaskiyar maishine in ba tsafin ba babu yadda
za a yi a sami doki mai irin wannan karfin gudun '
''
AL'AMARIN su yarima hulkas kuwa bayan sun shafe tafiyar
wata guda a cikin sa'a bakwai da karfin sihirin tsafi sai
dare ya fara riskesu a cikin wani daji don haka sai
sarki hulbasu ya bayar da shawarar a tsaya a yada zango ba tare da wata gardama ba
hailur dasu yarima hulkas suka amince, nan da nan aka
kafa tantuna sannan kuyangin sarki hulbasu suka
shirya abinci
hailur ya zauna tare da yayansa yarima hulkas da jaruma
siyama da kuma matansa shadila da zalina, shima sarki
hulbasu sai ya zauna tare da matarsa luzuraina da kuma dansa yarima barmas
suna cin abinci
ita kuwa jaruma rulaiya wacce har yanzu babu wanda ya
taba ganin fsukarta ko ya san labarinta face yarima
hulkas sai ta koma can gefe daya ta nisanta da kowa ta
zauna tana cin abincinta
ita kadai a kusa da farin dokinta na sihiri a lokacin da
dokin ke yin kiwo abinsa yana cin ciyawar kasa
koda sarki hulbasu ya hango jaruma rulaiya a can gefe
daya ita kadai sai ya dubi yarima hulkas yace me yasa
waccan abokiyar tafiyar taka har yanzu taki yarda tabude
fuskarta
mu gani kuma me yasa take gudun jama a shin ba zaka bamu labarinta yanzu ba ?
Sa adda yarima hulkas yaji wadannan tambayoyi sai yayi dan guntun murmushi
sannan yace ba don waccen bakuwar ba da tuni na
dade da shekewa barzahu ta ceci raina a baya don haka
tana bina bashi
labarinta yana da yawa gami da ban tausayi da al ajabi kuyi hakuri sai mun sami
lokaci isashshe
caraf sai hailur ya tari numfashin yarima hulkas yace
ai kuwa ni indai haka ne bai kamata ka barta ta rinka
kadaita haka ba
tashi kaje wurinta ka debe mata kewa saboda na ga alamar
cewa kamar tana cikin damuwa da tunani tunda tama
kasa cin abincin sosai
koda jin haka sai yarima hulkas ya mike tsaye cikin murna
ya tafi wajen jaruma rulaiya,
da ganin haka sai yarima barmas ya dubi jaruma siyama yace
kawata idan bazaki damu ba nima ina son nayi wata
magana mai muhimmanci tare dake
koda jin haka sai jaruma siyama ta murtuke fuskarta ta daka
masa harara amma tana hada idanu da hilairu sai ta mike
tsaye ta kama hannun yarima barmas taja shi
izuwa gefe daya suka kama hira cikin raha da nishadi
lokacin da yarima hulkas ya isa inda jaruma rulaiya ke zaune
sai ya isketa cikin tunani mai zurfi don haka sai da ya
kira sunanta sannan tasan da zuwansa, yarima hulkas ya dubeta cikin alamun
damuwa ya ce yake jarumar mata kuma sarauniyar kyawawa
me ya faru naga kinyi tagumi kina tunani mai zurfi haka
koda jin haka sai rulaiya tayi doguwar ajiyar
zuciya sannan ta dubeshi cikin alamun fargaba ta
ce
yakai hulkas kayi sani cewa tun da muka yada zango a nan
wajen naji zuciyata na bugawa da karfi ina ji a jikina
cewar akwai wani mugun abu dake shirin samunmu
lallai zamanmu anan yana da matukar hadari kasani
cewa dama ina da niyyar baka irin horon yakina a cikin wannan
tafiya tamu saboda na san cewa zai amfaneka
don haka yanzu saika mike tsaye mu fara, tana gama
fadin haka sai ta mike tsaye ta zare takobinta guda biyu
shima yarima hulkas sai ya mike tsaye ya zare tasa takobin
nan take suka ruguntsume da azababben yaki mai
tsanani
koda su sarki hulbasu suka ga jaruma rulaiya na kaiwa
yarima hulkas mugayen hare hare tana neman hallakardashi har ma ta dan yankeshi
kadan a damtsen hannunsa na hagu sai gaba dayansu
suka yunkura zasu afkawa jaruma rulaiya amma sai jaruma
siyama tayi tafi tasha
gabansu tace kada ku shiga wannan yakin domin baso take ta hallaka shi ba yaki take
koya masa
kuyi tunani mana inda kasheshi take son yi ai ba za ta
ceci rayuwarsa ba a baya ba kuma idan a yanzun take son kasheshi gaba dayanmu
babu wanda ya isa ya hanata don karfin damtsenta
da iya yakinta da kuma karfin sihirinta domin karfin
tasirin sihirin tsafinta ya ninka namu sau goma
gama fadin haka keda wuya sai suka fara ganin abin
al ajabi domin nan take suka ga yarima hulkas ya fara iya
duk irin yanayin yakinta sai gashi yana iya kare hare haren
ta kuma yana mai da martani sai da suka shafe rabin sa'a
suna bakin gumurzu har ma yarima hulkas ya sami nasarar dukan kirjin jaruma
rulaiya
ta fadi kasa cikin hanzari ya ruga gareta ya bata hannunsa
ta kama ya tasheta tsaye sannan ya
dubeta cikin damuwa yace
Ki gafarceni yake jarumai jarumai koda jin haka Al amin
Ahmed Misau, sai jaruma rulaiya tayi murmushi tace
aini farinciki na yi da naga yanzu ka sami nasarar kani
kas
tabbas ka sami horon yaki irin nawa, gama fadin
hakan keda wuya sai jaruma rulaiya ta dafe kanta
ta kwalla ihu kuma ta sulale kasa sumammiya
al amarin da ya razana kowa ke nan a wajen aka rugo
izwa kanta sa adda yarima hulkas ya rungumeta a kirjinsa
cikin dimauta
cikin hanzari aka yayyafa mata ruwa nan da nan kuwa
ta farfado cikin tsananin mamaki da kaduwa yarima
hulkas ya dubeta yace menene ya sameki kikayi ihu
kika fadi kasa sumammiya alhalin kina tsaye cikin
koshin lafiya
Jaruma rulaiya tace '' A duk sa adda wannan Aljani wanda
ya raineni yayi mini wahayi haka nake kasancewa
barci ne yake daukata mai nauyi shiyasa kaga kamar na suma
aljani Arwasul masadul ya sanar dani cewa abokan gabarmu
sarki shardas zasu iso nan ya riskemu a cikin sa a biyu
kacal
mai zuwa don haka ya gargadeni da mu hanzarta a
cigaba da tafiya kuma yayi mini albishir cewa zamu
iya isa kogon da hular lamsara take a cikin sa a biyun
koda jin wannan batu sai kowa ya mike tsaye zumbur
aka shiga shirin gaggawa aka kwashe komai aka
hau dawakai aka kama tsala azababben gudu a cikin
daren wannan farin tsuntsu na sihiri nayi musu jagora
a sama a cikin iska
dokin jaruma rulaiya ne akan gaba yana dauke da mutum uku
wato ita kanta jaruma
rulaiya yarima hulkas da jaruma siyama
a cikin sa a biyu cif suka iso bakin wani katon kogon
dutse wanda gaba daya bayansa sama da kasansa
a shafe yake babu alamar kofar shiga, Al amin Ahmed
Misau, kowa dake wajan sai da yayi iya kokarinsa
wajan gano inda kofar shiga take amma yarima hulkas na
dafa wani wuri a jikin dutsen sai kofa ta bude suka yi arba
da cikin kogon wanda yake da tsananin haske yadda ko allura ce ta fadi za a
iya ganinta
babu komai a cikin kogon dutsen face kayan yaki iri iri
masu tsohon tarihi na manyan sarakuna da manyan
jaruman da suka shude
nan take suka hango hular lamsara a can sama bisa kan wani dutse mai tudu
kowai sai jaruma rulaiya ta dubi yarima hulkas ta ce maza
kaje ka dauko waccen hula ta lamsara anyi tane domin kai kadai kuma kai kadai ne zaka
iya daukota a nan cikinmu
Saikuma Jarumi Al amin Ahmed Misau, Amma bari na
barshi yauko saboda naci girma hmm, koda gama
fadin hakan sai yarima hulkas ya ruga da gudu ya je ya
dauko hular lamsara yana daukowa kuwa
sai kofar gogon dutsen ta fara rufe kanta, A guje yarima ya
fito yana fitowa sai ya daga hular sama da nufin ya sanyata
a kansa amma sai yaji an doki kirjinsa
saboda karfin dukan bai san sa adda ya saki hular
lamsara tayi sama ta fada kan wani tsauni mai tsawon
gaske ta kama gangarawa a lokacin da shi kuma yai
sama izuwa kan tsaunin ya fado kasa magashiyan yana
aman jini yana daga kansa sama sai yaga sarki shardas
tsaye a kansa yana yi masa murmushin mugunta boka labarusa na tsaye bisa wani jan doki a gefe guda
kawai sai sarki shardas ya yunkura da nufin ya ruga inda hular
lamsara take ya dauketa ya sanyata amma sai yaji an daure kafafuwansa
da hannayansa da wata tufkekiyar sarkar karfe ta sihiri
ba wani ne ya daure hannun sarki shardas ba face bokansa
boka labarusa cikin tsananin mamaki da kaduwa sarki shardas ya dubi boka
labarusa yace saboda me zaka ci amanata ka hanani
daukar hular lamsara?
Koda jin wannan batu sai boka labarusa ya bushe da
dariyar mugunta sannan ya murtuke fuskarsa yace
dashi
tabbas sai yaune na tabbatar da cewa kai wawa ne mara basira
kana zaton tsawon
shekarun danake yi maka bauta inayi ne saboda kaunarka
idan har ka dauki haka to kayi babban kuskure
masu iya magana sunce so sone amma san kai yafi kowanne Ai
Al amin Ahmed Misau Nake , Aski yazo gaban goshi
domin A halin yanzu littafi ya kusan karewa, ina yi maka
bauta ne saboda zuwan wannan rana da zan mallaki
hular lamsara saboda nasan cewa idan na mallaketa tamkar
na mallaki duniyar nan ne gaba dayanta, dukkanin
sarakunan duniya sai sun dawo karkashin ikona, duk
wata dukiya ta duniya sai ta zama tawa ni kadai a bincike
na nagano cewa kaine kadai sarkin da zanjingina
dashi na tsorata dukkanin bokaye da sarakunan duniya
tunanin mallakar hular lamsara tunda an san kana
nemanta kuma kowa yana tsoronka, koda boka labarusa yazo nan a zancensa
sai sarki shardas ya kuma wani gagarumin uban ihu cikin
bakin ciki ya dubi boka labarusa yace in dai don hular
lamsara ka daureni da wannan sarkar sihiri to ina umartar
ka da ka gaggauta kwanceni domin na yaki makiyana gasu
tsaye a gabana kada su kashe ni a banza na rantse
da darajar iyayena nabar maka hular lamsara bana bukatar
ta
ni dai ka barni na tsare mutuncina da rayuwata, koda jin
wannan batu sai boka labarusa ya bushe da dariyar mugunta
lokaci guda ya murtuke fuskarsa yace haba shardas ta
yaya kake zaton cewa bera zai taba yarda yayi
zumunci da mage ? Kada ka manta cewa sama da
shekaru talatin bayanake tare da kai tun kana matashi babu
wanda ya san
halinka
Sama dani yaudara cin amana da rashin imani duk takenka ne
shin a rayuwarka ta duniya mata nawa ka mayar gwagware ? Shin a rayuwarka ta duniya
yayaye nawa ka mayar marayu ? Al amin Ahmed Misau
Nayi imanin cewa baka san adadinsu ba
ai dama ance rana da yawa ta barawo rana daya tak ta
mai kaya
koda gama fadin haka sai boka labarusa ya dubi sarki
hulbasu yace ga wanda ya sa ka yanka danka da hannunka
kuma yasa bakin ciki ya kashe ubanka sai ka dauki fansa akansa boka labarusa ya sake
duban jaruma rulaiya wacce har a sannan fuskarta a rufe
take cikin bakin kyalle yace da ita ke kuma ga wanda ya
kashe ubanki ya mallake dukiyarsa gaba daya ya janyo kika girma a inda babu
mutane sai ki dauki fansa kema ni bani da wata alaka daku
burina kwai na mallaki duniya koda gama fadin hakan
sai boka labarusa ya tashi sama kamar tsuntsu ya dira
a can sama bisa wannan tsauni ya nufi inda hular lamsara
take koda ganin haka sai jaruma rulaiya ta dubi yarima
hulkas tace idan muka bar wancan bokan ya mallaki hular
lamsara zalunci zai shimfida a doron kasa, muma sai mun
zama bayinsa
ni zanje na yakeshi na kawai dashi kai da jaruma siyama
da sarki hulbasu ku yiwa sarki shardas irin kisan gillar da kuke son yi ku daukar mana
fansar zaluntarmu da yayi koda gama fadin hakan sai jaruma rulaiya ta cire bakin
kyallen dake fuskarta su jaruma siyama sukayi arba da
tsananin Kyawunta
sai suka cika da tsananin mamaki kawai sai suka ga jaruma
rulaiya ta daka tsalle sama tamkar daga cikin baka aka
harbota ta dira akan wannan tsauni ta nufi inda boka
labarusa yake yarima hulkas, jaruma siyama sarki hulbasu suka tunkari inda sarki shardas yake daure a cikin sarkar
sihiri koda yaga sun durfafo shi sai ya kama kyalkyala dariya
al amarin da yayi matukar basu mamaki kenan sarki hulbasu
ya dubeshi yace saboda me kake dariya alhalin ka san
cewa KISAN GILLAH zamuyi maka domin mu huce takaicin
bakin cikin da ka kunsa mana, al amin Ahmed Misau
Sarki shardas yayi murmushi yace ina yin wannan dariya ne
saboda dalilai guda biyu rak !
Dalilin farko shine, ba zaku iya kasheni ba inda bana daure
cikin wannan sarkar tsafi, kunga kenan ku ba jarumai bane
nikuwa na zalunceku ne saboda nafi karfinku, babu
yadda zakuyi dani don haka zan mutu ina mai farin ciki
da alfaharin na mutu a jarumi abin tsoro, dalili na biyu
kuma da yasa nake yi muku dariya shine ko kun
kasheni yanzu kamar kun kashe maciji ne baku sare
kansa ba
saboda wannan bokan nawa boka labarusa idan ya mallaki
hular lamsara sai yafini barna da zalunci a doron kasa kun
ga kenan a karshe kuma kuma rayuwarku zata
kasance a cikin bautarsa da takaicin zaluncinsa wata kila duk ya karkasheku
sarki shardas na gama wannan jawabi sai ya cigaba
da kyalkyala dariyarsa
Yana cikin dariyar ne sarki hulbasu ya zare takobinsa ya kafta masa
mummunan sara a kaurin kafarsa ta hagu nan take kafar
ta guntule jini yai feshi da tsartuwa sarki shardas ya kwarara uban ihu sakamakontsananin zafi da zugin da ya
ratsa sassan jikinsa koda ganin haka sai shima yarima
hulkas ya zare tasa takobin ya sare kaurin kafar
sarki shardas ta dama wato suka mayar dashi gurgu :)
the Al amin Misau A dai dai wannan lokaci ne suka jiyo karafkiyar karafa
a can saman wannan tsauni suka gane cewa azababben yaki ne aka kaure dashi tsakanin
boka labarusa da jaruma rulaiya, cikin alamun fishi
hailur ya dubi yarima hulkas yace yakai dana ka tafi
izuwa ga jaruma rulaiya wacce ta ceci rayuwarka kuma kayi
mata halarci ka ceci rayuwarta ka bar mu da wannan
tsohon azzalumin abokin gabarmu mu dauki fansa a kansa
koda jin wannan batu sai yarima hulkas ya ruga da gudu izuwa jikin tsaunin
nan ya kamashi ya fara hawa shi dai wannan tsauni
saboda tsananin tsawonsa duk abin dake kansa daga
kasa ana hangoshi dan mitsitsi tamkar kuda ne
Abinda su yarima hulkas basu sani ba shine ashe can karshen
wannan tsauni wutace take dafa dutse yana narkewa saura
kadan dutsen yayi bindiga ya fara aman ruwan wutar
lokacin da yarima hulkas ya shafe dakiku masu yawa yana hawa
kan wannan tsauni yaga ko rabin tsawon tsaunin bai
kai ba sai hankalinsa ya dugunzuma ya fara
tunanin cewa anya kuwa ma zai iya kaiwa can saman tsaunin
har ya taimaka wa jaruma rulaiya ba tare da ya gaji ba ya
subuto kasa ya hallaka
Al amin Ahmed misau
++ ++ ++
ACAN kasan tsaunin kuwa sai su sarki hulbasu suka taru
su uku akan sarki shardas suka rinka yankar naman sassan jikinsa da kadan kadan yana ihu
da kururuwa saboda tsananin zafi da zogi da azabar da yake ji
hatta kunnuwan sarki su hulbasau daban -daban suka
yankesu sannan suka kwakule idanuwansa daya bayan
daya
A haka dai suka yi tayi masa azaba kala iri iri har rai yayi
halinsa cikin mummunan kisan gilla wato sarki shardas
ya zama Gawa !
A dai dai lokacin da su hailur suka kashe sarki shardas ne
shi kuma yarima hulkas ya isa can saman wannan dogon
tsauni da kyar da sidin goshi bayan duk jikinsa ya
kukkuje
sau tara yana zamewa a saman kamar zai fado
Kasa amma cikin sa a sai ya sake chafe tsaunin
hakika yarima hulkas yasha
bakar wuya wajen hawa kan wannan dogon tsauni
domin kaiwa jaruma rulaiya dauki, yana isa saman tsaunin sai yayi arba da jaruma rulaiya
da boka labarusa kwance a kasa jina jina sun yiwa junansu mugayen raunika
suna jan ciki sun nufi inda hular lamsara take wacce
ke sakale a jikin wata karamar bishiya a can karshen gabar tsaunin
A wannan lokaci ne kuma tsaunin ya fara girgiza alamar
cewa wutar da ke ci a karkashinsa na yin bindiga
a sannan ne kuma hailur da sarki hulbasu da siyama suka
hau kan tsaunin da karfin sihirin tsafi kawai sai suka hango
boka labarusa da jaruma rulaiya sun durfafi taba
hular lamsara da hannayansu shi kuwa yarima hulkas ya ruga
garesu da gudu
Al amin Misau ai kuwa sai saman tsaunin ya dare gida
biyu jaruma rulaiya da boka labarusa suka gangara
zasu fada can kasa inda dafaffen dutsen ke ambaliya
ga wuta a cikinsa muraran
cikin tsananin sa a jaruma rulaiya ta ruko wani dutse bata
fada can kasan tsaunin cikin wutar ba amma sai taji caraf
shima boka labarusa ya cafko kafarta nan fa nauyin boka
labarusa ya fara rinjayar jaruma rulaiya koda ganin haka
sai yarima hulkas ya samu da kyar ya daka tsalle sama ya dira
a karshen tsaunin shima ya cafo hannun jaruma rulaiya ya zamana
cewa nauyinta
dana boka labarusa ya dawo hannunsa, hailur da jaruma siyama da sarki hulbasu
kuwa
sai suka rasa yadda zasu yi su kai wa su yarima hulkas dauki
saboda tsaunin cigaba yake da daddarewa ko taku
daya suka kara hallaka zasuyi , hular lamsara dake sakale
a jikin karamar bishiya itama rawa take yi wanda ke nuna
alamar a koda yaushe itama zata iya fadawa cikin
ruwan wutar nan ta kasan tsaunin ta narke
koda hailur yaga halin da ake ciki sai ya kwallawa yarima
hulkas kira yace yakai dana ka saki hannun jaruma rulaiya
domin ka ceci rayuwarka, kuma kaje ka dauko hular lamsara
kafin ka rasata har abada
Koda jin wannan batu sai yarima hulkas ya juyo da fuskarsa
ya dubi hailur a lokacin da hawaye ya zubo masa yace
yakai abbana ka gafarceni ba zan iya zabar hular lamsara
ba na bar masoyiyata rulaiya ta hallaka saboda
tana bina bashin ceton rayuwata da tayi, nikam na zabi
soyayya akan duniya ku dauki danganar rashina
itama wancan hular ta lamsara gwara a barta ta fada
cikin wutar can ta narke hakan ne kadai zai haifar da zaman
lafiya a duniya
gama fadin haka keda wuya sai nauyin boka labarusa da
na jaruma rulaiya ya rinjayi yarima hulkas su duka
ukun suka rikito daga saman tsaunin suka
fada cikin wutar dutsen dake kasan tsaunin suka hallaka
gaba dayansu !!
Koda ganin abinda ya faru sai hailur da sarki hulbasu
da kuma siyama suka kurma uban ihu suka fashe da
matsanancin kuka na bakin ciki, yayinda nima kaina Al amin
na tayasu
ALHAMDULILLAH
a nan ne wannan labarin hikayar yazo karshe Inda marubucin
yace domin jin cigaban labarin mu hadu a littafin DARUL DAULAT, domin jin cigaban LABARIN SARAUNIYA LARBISA,
karfa ku manta cikin labarinta muke sannan muka
tsunduma cikin kuma labarin sadauki Hulkas
wanda sai yanzu aka kammala, idan Allah ya sa littafin
darul Daulat ya fito zan siyo na zo na karas muku domin
kuji yadda wasan zai kasance, kafinnan kuma zanso
kowa da kowa ya baje kwakwalwarsa ayi muhawara akan wannan hikaya
shin Da gaske ne kai/ ke zaku iya shekawa ta sanadin masoyi ?
Nidai... Baridai naji daga gareku
Amma kafinnan nidinne Al amin Ahmed Misau
Inkiya
Guyson Ko A square
nake cewa Sai Allah ya kaimu gobe zaku jini da wani Sabon Littafi wanda nasan cewa zai kayatar daku Matuka
Up Up Up Up Up
comments da likes dinku yana matukar kara mana kwarin guiwa saboda haka aci gaba da suburbudowa ehem