Ummi ta yi sororo a rude tana
kallon Anas yayin da shi kuma
Anas ya dubeta a tsorace baki na
rawa ya ce.
"Ummi...wannan kuma wacce
mahaukaciya ce?"
Ummi ta yi ajiyar zuciya a kidime
kana ta ce.
"A iya sani na dai tana da
hankali." Ta dan yi shiru, sannan
sai ta dauke hannunta daga kan
kofar motar.
"Daman kun dade da sanin juna
ne kai da ita?" Cikin sauri Anas ya
girgiza kai "Ko kusa ko alama ni
ban ma taba ganinta ba wallahi
sai yau." Ga mamakinsa sai ya ga
Ummi ta zunkuda kafada sannan
ta haskake shi da murmushi ta
ce.
"Me yiwuwa wani ne mai kama
da kai ya taba yaudarar ta na san
halin Hasiya wani sa'in rudaddiya
ce."
"Yauwa ko da na ji fa" Anas ya ce
gami da ajiyar zuciya, sannan ya
share gumi lokaci guda kuma ya
yi sauri ya sauya zancen da cewa.
"Ummi wai don Allah uwa daya
uba daya ki ke da Abdulmalik."
"Ummi ta fashe da wata
sassanyar dariyar jin dadin ganin
Anas yana kishi a kanta.
"Har yanzu dai ba ka yarda ba
kenan."
"A'a ba wai ban yarda ba
ne...amma ni abin ne yake bani
mamaki, ni sai na ga kamar
shima sonki yake."
Ummi ta girgiza kai ta ce.
"Anas, wallahi yayana ne, uwa
daya uba daya, ni dai abin da
nake tunani me yiyuwa wani abu
ne daban yake damunsa ko
kuma ganin zai tafi ya bar ni ni
kadai ka san tun muna kanana
bama rabuwa tare muke duk
inda zamu tafi yawan lokuta ma
barci ne ke rabamu to ka san ban
taba yin saurayi ba sai a kanka
ina jin abin da yake damunsa
kenan." Anas ya karkada yan
makullayen dake hannunsa ya ce,
"Na yarda da ke Ummi." Sannan
sai ya hango inda su Hasiya da
samarinta suke tsaye gabansa na
faduwa, haka nan wani zazzafan
gumi ya fara sartu akan doron
wuyansa tabbas sai yanzu ya
tuno ta. A daidai lokacin ne to ya
dubi agogo sai ya ga ashe har
goma na dare ta wuce. Sannan
ne to ya ji gaba daya duniyar nan
ta yi masa bakinkkirin. Mabaruka
ce ta fado a ransa kwata-kwata
ganin kyakkyawar fuskar Ummi
ya gama mantar da shi komai a
wannan lokacin baya iya ganin
komai sai Ummi.
"Ummi ni zan tafi...sai yaushe
kenan?" Ummi ta dubi fuskar
Anas sai ta ga duk ta jike da
gumi nan da nan ta fahimci halin
da ya ke ciki.
"Oh...na san fa ashe tana can tana
jiranka ko?" Anas ya sunkuyar da
kai "Ummi tun da na yi aure ban
taba samun farin ciki kamar na
yau ba...dan haka ina rokonki da
ki yi shiru da bakin ki kada ki
bata min farin cikina na wannan
rana ta farin ciki." Yana gama
fadin haka sai ya shiga motar ya
rufe kofa sannan ya sako kansa
ta tagar motar ya ce.
"Ummi tun da nake ban taba
kaunar wata mace a duniya da
gaske har zuciyata ba sai a
kanki." Ummi ta dan rankwafa
kadan ta ce "Na yarda da kai
Anas...sai yashe za ta sake bamu
ranar haduwa?"
"Wa ki ke nufi? ban fahimce ki
ba."
"Matarka mana Mabaruka na yi
mamakin ma yadda aka yi ta
barka kazo."
Anas yaji kamar ta watsa masa
wuta a fuska.
"Ba ta isa ta juya ni ba Ummi duk
lokacin da naga dama zan iya
zuwa gurin ki." ya dan yi shiru
sannan sai ya ce "Ki jira ni zan zo
jibi" A haka ya tuka motar ya fice
daga layin
Ummi ta bi motar da kallo ga
mamakinta sai ta ji gaba daya ma
ta shiga cikin rudani domin a da
kafin ya zo ta dauka idan ya zo
ba za ta iya rabuwa dashi ba sai
da kuka saboda tsabar kaunar da
take yi masa amma a yanzu ta
shiga wasi-wasin zuciya, bata
san mene ne dalili ba.
A can cikin motar Anas ya ji
hawayen bakin ciki ya fara sartu
akan kuncinsa Shin ya ya
abubuwa zasu zama haka ne ya
ya aka yi duk sa'a ta ta kwace
min, don me yar iskar nan Hasiya
za ta yi min haka.
A da kafin Anas ya zo ya dauka
zai bar gurin Ummi dauke da
farin cikin da bai taba jin irinsa a
duniya ba To amma a yanzu
wani karamin digo na kalanzir ya
riga ya fada a cikin kokon ruwan
shan kaunarsa ya kuma ji a
jikinsa cewa in ba wani abu daga
Allah ba dan digon kalanzir din
nan sai ya gurbata dukkan
illahirin dandano na ruwan shan
kaunarsa A karo na farko tun
bayan da ya girma sai Anas ya
fara kokarin yin addu'a to sai dai
kuma har sa'ar da ya fara
hangen fitulun lantarkin da ke
makale a jikin katangar gidan
Mabaruka gurguwa bai iya tuno
koda addu'a daya ba
***
Sidi mai jaka ya yi shiru kana ya
harari kwanon tubanin da ke
gaban sa ya mika busassun yan
yatsunsa guda uku ya cafko wani
katon tubani mai siffar kwado ya
dago shi sama yana nazarinsa
sai da ya dade a haka sannan ga
mamakina sai na ga ya mayar da
tubanin cikin kwanon ya dubeni
cikin nadama ya ce
"Nas cikina ya gama cika amma
har yanzu bakina na muradin ci
gaba da taunar tubanin nan."
"Haka ne" na ce da shi
"Ci gaba Baba Sidi na matsu in ji
karshen labarin nan...sai na ji duk
ma ka dada ruda labarin." Sidi
mai jaka ya saki wata
kekasasshiyar dariya"Ci gaba Baba Sidi, na matsu in ji
karshen labarin nan...sai na ji duk
ma ka dada ruda labarin." Sidi
mai jaka ya saki wata
kekasasshiyar dariya ya dubeni
ya ce.
"Ai Nas zararrukan labarin ma
sun zo karshe...bari na yi sauri na
saka maka na karshe sai mu
hadasu da sauran zararrukan
labarin mu daure."
"Haka ne." Na ce da shi.
Sidi mai jaka ya dubi kwanon
tubanin cikin takaici ya yi kamar
zai dauki daya sai dai ya sauya
shawara ya dubeni ya ce.
Nas, tun karfe takwas na daren
ranar da Anas ya tafi gurin Ummi,
Mabaruka ta caba kwalliya,
sannan ta sa hadiman gida suka
shirya musu kayan shaye-shaye
da tande-tande na musamman.
Shiru-shiru karfe tara ta wuce
babu Anas babu labarinsa,
wannan shi ya sa Mabaruka
gurguwa rarrafawa gaban dan
gajeren madubin da aka yi mata
na musamman ta dubi
mummunar fuskarta a jiki sai ta ji
kamar ta fashe da kuka, domin ta
lura duk kwalliyar da ta yi ta
damalmale. Cikin sauri ta rarrafa
zuwa bandakinta na musamman
ta kuma kwashe mintuna talatin
tana wanka gami da shafe-shafe
da goge-goge, fitowarta ke da
wuya daga bandakin sai
tangamemen agogon azurfa
wanda mahaifiyarta ta bata ya
dauki rurin karfe goma na dare.
"Na shiga uku." Mabaruka ta fada
a fili kai ka dauka tare suke da
wani a dakin "Me ya tsayar da
Anas ne har yanzu?" Mabaruka ta
tambayi kanta, Nan da nan sai ta
ji jikinta ya dauki rawa, zuciyarta
ta fara harbawa sannan sai ta
fara zargin kanta da wauta. Dan
me zan bar shi ya tafi shi kadai?
Ta kuma tambayar kanta to sai
dai wannan karon Mabaruka na
da amsar tambayar cikin zuciyar
ta.
Anan sai Sidi mai jaka ya dan yi
shiru yana kallona, sannan sai ya
ce. "Nas akwai wani sirri da
Mabaruka take son sanar da
Anas tun kusan kwanaki uku da
suka shude amma yar rashin
jituwar da suka samu a daren da
aka yi liyafar nan shi ya sa ta
boye masa.
"Wanne sirri ne wannan?" Na
tambayi Sidi mai jaka.
"Bi ni a hankali Nas, ni ma zakin
mazallako ne kawai da daga ciki
yana rokon uba kwabo shi ya
sani azarbabin fada ma, amma
da sannu zan kawo ka kan
zancen, kai dai bani aron
hankalin ka mu koma kan zaren
labarin da muke.
"Na baka." Na ce da shi. Sidi mai
jaka ya dan faki idanuna sannan
sai ya mika hannu ya zaro tubani
guda ya jefa a bakinsa kana ya ci
gaba da cewa.
"Abin da ya sa Mabaruka ta bar
Anas ya tafi shi kadai shi ne ta
san cewa Anas fa ba kaunarta
yake yi ba ko kankani, ita ce dai
ke kaunar sa, haka nan ta
tabbata muddin ta uzura da
manne masa, to za ta sa ya kuma
tsanarta a cikin zuciyarsa wanda
hakan na iya kawo sanadiyyar
rabuwarsu. Duk da irin kuri da
cika baki da mabaruka ke masa
cewa idan ba zai iya ba ya ajiye
mata duk dukiyarta ya bar mata
gidanta, babu abin da
Mabarukan take tsoro da fargaba
irin rabuwa da Anas, domin ta
san idan ta rabu da shi tana iya
haduwa da cutar da za ta kawo
ajalinta a kusa, wannan dalili shi
ya sa duk da tana zargin karya
Anas yake yi ba gurin abokansa
za shi kawai ba Mabaruka ta
kyale shi ya tafi shi kadai, tare da
fatan me yiwuwa idan ta bashi
yana yan walawa shi kadai yana
iya dan kaunar ta ko daidai da
kwayar zarra ne, haka nan tare
da karfin gwiwar cewa idan ya
dawo zata fada masa abin me
yiyuwa zai iya sa shi farin cikin
da dole ne ma ya tarairayata ko
da bai so ba. Wannan shi ya sa
Mabaruka ci gaba da kwalliya tun
magriba har zuwa karfe goman
dare bata gama ba.
"Bari in sa wannan shudiyar
rigar me yiwuwa ta burgeshi, na
ga ran nan da na sa irin ta kamar
yana satar kallona."
Mabarua ce ta ci gaba da zance
da kanta sa'ar da take kokarin sa
rigar. Bayan ta gama sai ta sake
rarrafawa zuwa gaban madubi
ta kuma duban kanta a karo na
goma sha uku. Abin da ta gani ya
dan faranta mata rai babu dai
yabo babu fallasa, domin ba
katon goshinta ba kawai, hatta
dan tababben hancinta mai
kamar kataura ya dan mike
sakamakon matsar da ya sha a
hannunta, haka nan fuskarta na
dan sheki, to sai dai kuma ta
fuskanci kamar hoda ta so ta yi
mata yawa a fuskar
Wannan ya sosa mata rai, dan
haka a fusace sai ta mika
hannunta zuwa kan gado ta
janyo wani abu da take
tsammanin me yiwu rigarta ce,
da zummar ta yi sauri ta goge
hodar dake fusakarta domin duk
sosunan kwalliyar sun hade da
kalolin hodoji iri-iri sun baci.
Janyo abin ke da wuya sai ta ga
ashe wandon Anas ne. Cikin farin
ciki sai ta kara wandon mijin
nata akan fuska, sannan ne fa
kudundunnaniyar takardar fara
ta fado daga cikin aljihun
wandon. Mabaruka ta ji gabanta
ya fadi ras, tun kafin ma ta dauki
takardar. Hannunta na rawa ta
dubi takardar cikin tsananin
zargi sannan sai ta jefar da
wandon gefe guda ta dauki
takardar ta fara karantawa....
.
".....Ni ce Ummi."
Mabaruka ba ta iya maimaita
karatun takardar a karo na biyu
ba, sai ta kifa kai a jikin gadon ta
fashe da kuka mai karfin gaske
wanda har rawar da gangar
jikinta ke yi ta sa gadon shima ya
dauki rawa Kofar dakin ta bude
a hankali sannan Anas ya shigo
fuska a turbune shigowarsa ke
da wuya sai ya tsaya turus kamar
wanda ya ji shi cikin fasassun
duwatsu a cikin duhun dare.
"Ku...kukan me ki ke yi Mabaruka
ba gani na dawo ba."
Mabaruka ta dago kai jiki na
rawa cikin kuka ta ce.
"Mene ne amfanin dawowar ka
tsohon mayaudari! Ai sai ka
koma can gidan su Ummin ka
kwana a can...!" Ta kara fashewa
da kuka.
"Ban fahimci abin da ki ke nufi
ba." Anas ya ce cikin shakka,
domin bai san munafukin da ya
fada mata daga gidan su Ummi
yake ba.
"Ya za a yi ka fahimce ni, tun da
ka tsaneni! Ba ka kaunata!! So
kake na mutu da bakin cikin
kaunarka ko Anas?"
Hakan da ta fada sai Anas ya ji
tausayinta ya kamashi. Ga
mamakinsa sai ya ga Mabaruka
ta rarrafa inda ya ke tsaye ta rike
kafafunsa cikin kuka ta ce.
"Anas....don Allah ka yi min rai ka
kaunace ni ko da daidai da na
kwana daya ne... Haba Anas don
ka ga ni mummuna ce...dan ka ga
ni gurguwa ce....shi ne kake son
kashe ni." Ta sake fashewa da
kuka.
Anas ya ji kwalla ta zo idanunsa,
cikin sauri ya durkusa a gabanta
ya dafe kanta.
"Daina kuka Mabaruka bari in yi
miki bayanin abin da ke
zuciyata."
"Ba sai ka yi ba Anas, na ri ga na
sani...ni dai ina rokon don Allah
ka kauna ce ni kada ka sa bakin
ciki ya kashe ni, ni da danka da
ke cikina!" Anas ya ji kamar an
zunguri zuciyar sa da allura.
"Wanne dana ki ke nufi a
cikinki?" Ya tambayeta a rude.
Mabaruka ta dada kankameshi
sannan ta fashe da kuka ta ce.
"Anas tun shekaran jiya na ke
son fada ma likita na ya sanar da
ni ina da ciki wata uku!"***
Na dubi Sidi mai jaka a rude nace
"Haba Baba Sidi ya ya tun dazu
ka ke labarin nan amma ba ka ce
tana da ciki ba sai yanzu?"
Sidi mai jaka ya dubeni da
busasshen murmushinsa ya ce.
"Nas ke nan, abin da ba ka sani
ba shi ne idan na fada maka tun
dazu cewa tana da ciki ai na
ragewa labarin dadi, haba Nas
kai sai ka ce ba marubuci ba. Bari
in sako maka zaren labari na
karshe sai in hadasu da wannan
na kulla ko ma kai ga karshen
labarin nan."
"Haka ne." Na ce dashi ba musu.
Yauwa Nas, ta yanzu ina son ka
sa a zuciyar ka cewa ga Ummi
nan ta fito daga dakinta a rude,
wannan kuwa fitowa da ta yi a
washe garin ranar da Anas ya zo
mata zance ne.
Ummi ta dubi dan karamin
agogon da ke sanye a santalelen
hannunta, karfe hudu da
mintuna biyar agogon ya nuna.
Cikin sauri sai ta nufi kofar dakin
Abdulmalik ta kuma
kwankwasawa, a karo na goma
sha takwas a ranar. Shiru ba a
amsa ba, Ummi ta dada rudewa.
Shin ina Yaya Abdulmalik ya tafi
ne tun da sassafe har yanzu bai
dawo ba.
Abin da ya dada tayar mata da
hankali shi ne a daren jiya sa'ar
da ta shigo gida bayan sun rabu
da Anas, ba ta tsaya a ko ina ba
sai dakin Abdulmalik, domin tana
da tambayoyi masu yawan gaske
da take bukatar amsarsu. Lokacin
da ta isa kofar dakin sai ta hango
wutar dakin a kunne take, to sai
dai kuma kamardakin a rufe. Me
yiyuwa har ya yi barci. Ummi ta
ce a ranta, to amma sa'ar da ta
matsa kusa da kofar dakin sosai,
sai ta ji motsi a cikin dakin kamar
ana taba takardu.
"Salamu alaikum." Umma ta yi
sallama lokaci guda kuma ta tura
kofar dakin. Ga mamakinta sai ta
ji kankam kofar dakin a rufe take.
"Yaya Abdulmalik bude min na
dawo" Ummi ta ce Shiru ba a
amsa ba
"Yaya Abdulmalik." Ta sake kiran
sunan a karo na biyu
"Ina jin ki Ummi..ki bari sai gobe
ma hadu"
Ummi ta ji gabanta ya fadi nan
da nan ta ji jikinta ya dauki rawa
kamar zazzabi zai rufe ta
Wannan shi ne karo na farko da
yayan nata ya fara fushi da ita
amon muryarsa ya fadi sakon da
ke zuciyarsa
"Yaya Abdulmalik..me na yi
maka? Ka bude min mana"
"Babu abin da ki ka yi min Ummi
ta fi dakinki kawai ma hadu
gome...yanzu wasu yan rubuce-
rubuce nake yi bana son a dame
ni"
ummi ta ji kamar ya watsa mata
wuta Cikin kunan rai ta jingina
bayanta a jikin kofar dakin
idanunta suka fara ambaliyar
kwalla na mintuna biyu sannan a
hankali sai ta nufi dakinta domin
ta tabbata ba zai bude mata
kofar ba Tana zuwa dakinta sai
ta fada akan gadonta ta fashe da
kuka tabbas jinin Abdulmalik bai
hadu da na Anas ba Ummi ta
fada a ranta***
Na dubi Sidi mai jaka a rude na
ce
A wan nan lokacin ne to kalaman
Hasiya suka fado mata
"Ki bi a hankali Yaya Ummi kardai... wan nan lokacin ne to kalaman
Hasiya suka fado mata
"Ki bi a hankali Yaya Ummi kada
ki sake dashi domin ba zan so
ace kin fada a tarkon sa ba"
Shin ko abin da ta fada gaskiyar
ne, shin ko Yaya Abdul Shima ya
san halin Anas ne shi yasa yake
fushi da ni. Ummi ta kuma
tambayar kanta, sannan sai ta
dada fashewa da kuka, a haka
barci ya dauketa. To amma kafin
barcin ya saceta sai da ta yiwa
kanta alkawarin cewa in dai har
alakarta da Anas ne ya batawa
Abdulmalik rai, to babu mamaki
za ta rabu da Anas duk kuwa da
irin kaunarsa da take yi, domin
da ta bakantawa yayanta
Abdulmalik gara ta rabu da abin
da take kauna.
Washe gari da sassafe, tana idar
da sallah sakamakon makara da
ta yi da bata tashi da asuba ba,
sai ta nufi dakin Abdulmalik cikin
sauri ta tura kofar dakin babu ko
sallama sai ta ji kofar a rufe. Cikin
sauri ta juya da baya a kidime ta
nufi dakin mahaifiyarsu.
"Mama ina Yaya Ya tafi?"
"Ya fita tun da duku-duku nima
ban san ina za shi ba, ya dai ce
dani ba zai dawo ba sai can
yamma. Tun daga wannan lokaci
Ummi ke ta faman safa da
marwa daga dakinta zuwa dakin
Abdulmalik har zuwa yanzu babu
shi babu alamarsa.
Hawayen bakin ciki ya yi sartu
akan kumatunta. Ummi ta yi sauri
ta goge sannan ta nufi dakinta ta
zauna a bakin gado ta kurawa
kofar dakin nata idanu cikin
takaici. Wannan shi ne lokaci
mafi tsayi a rayuwarta da ta taba
zama ita kadai ba tare da dan
uwanta Abdulmalik ba a kusa da
ita.
Tana nan zaune ta zubawa kofar
dakin nata idanu tana jiran ta ga
ta inda Abdulmalik zai bullo, sai
aka yi sallama. Da farko muryar
mahaifiyarta ta fara ji daga waje
tana cewa.
"Ki shiga tana ciki." Cikin sauri
Ummi ta goge hawayen da ke
kumatunta ta mike tsaye, a daidai
lokacin da ta ji an sake cewa.
"Salamu alaikum." Sannan sai ta ji
an nufo kofar dakin.
Ummi ta dubi Hasiya sa'ar da ta
shigo dakin.
"Sannu da zuwa Hasiya dama
wallahi ina son ganin ki."
"Ni ma son ganin naki ne ya
kawo ni Yaya Ummi." Hasiya ta ce
lokaci guda kuma ta zauna a
bakin gadon ta dubi Ummi.
"Ga ni me ki ke son yi min?"
"Ke ma ai kin sani." Ummi ta ce
tana dubanta "Wai dan Allah abin
da ki ke fada min jiya a gaban
wannan saurayin nawa gaskiya
ne?"
Hasiya ta fashe da dariya ta ce
"Oh! Yaya Ummi kenan, ta wallahi
kima daina kiransa da suna
saurayin ki...don kin ga nima din
nan babu irin abin da bai fada
min ba amma daga karshe ya
koma kan wata kawata
Samira..wallahi sai da na yi
rashin lafiya da kyar Allah ya yaye
min masifar kaunar sa daga
zuciyata na huta." "Wai ki na
nufin ki ce saurayin ki ne da?"
Ummi ta tambaya.
Kina shakka kenan to bari ki ga
zahiri." Hasiya ta bude cikin jakar
da ke kan cinyarta sannan ta
zaro wani hoto ta mikawa Ummi,
"Kalli wannan." Ummi ta zurawa
hoton idanu cikin kaduwa.
Tabbas Anas din ta ne, shi da
Hasiya a bakin otel din da suka yi
liyafar bikin zagayowar ranar
haihuwar Mabaruka gurguwa,
abin da ya fi kona mata rai a
hoton shi ne, hannun Anas na
hagu dare-dare yake akan
kafadar Hasiya. Hannun Ummi na
rawa ta mikawa Hasiya hoton.
"Ungo abin ki." Hasiya ta girgiza
kai ta ce "Ki rike shi a gurinki,
idan ya dawo ki nuna masa
hoton ki tambaye shi me ya sa
bai aure ni ba." Hasiya ta mike
tsaye ta ce "Bari in karasa gida
Yaya Ummi...daman daga
unguwa nake shi ne na ce bari in
biyo ta nan domin ba zan bari
wannan kyakkyawan macijin ya
sake saran yar uwata mace ba.
Sai an jima." Da haka ta fice daga
dakin ta bar Ummi cikin kaduwa
dauke da hoton a hannunta, ba
tare da ta iya yi mata ko da rakiya
ba.
Bayan ta kalli hoton na mintuna
biyar sai ta mike tsaye, sannan ta
daga karkashin matashin kanta
ta jefa hoton, kana sai ta mike
cikin sauri ta nufi dakin
Abdulmalik domin ta sake
dubawa ko ya dawo. Tana zuwa
kofar dakin sai ta sake turawa
babu sallama domin a tunanin ta
idan ta yi sallama Abdulmalik ya ji
muryarta me yiyuwa ba zai bude
ba, zuciyarta na harbawa das!
Das!! Das!!! Ta shiga dakin, tana
shiga sai ta yi turus, Abdulmalik
baya cikin dakin. Sannu a hankali
ta shiga dakinta jikinta na rawa
sannan ne to ta hangi tarin
takardu farare an cikesu da
rubutu akan wani dan teburin
gilashi dake kusa da gadon
Abdulmalik, sannan sai idanunta
ya kai ga wata takarda fara
kwaya daya jal akan gadon a
jikinta an rubuta kamar haka;-
Masoyiyata Ummi ki karanta
takardun dake kan teburin nan
domin amsoshinki duk suna
cikin takardun..."
Hannunta na rawa ta dauki
takardar ta juyata a hannunta
sannan sai ta dauki sauran
takardun dake kan teburin jiki
na rawa ta zauna akan gadonsa
ta fara karanta wani abu mai
kama da almara..labarin
wadansu mutane da yaki ya
korosu suke gudun hijira.
Sidi mai jaka ya dubeni da
murmushi ya ce "Ina fatan dai
kana biye dani Nas?"
"Kwarai kuwa Baba".
"Yawwa Nas, to bari mu koma
kan wancan tsohon zaren
labarinmu inda muka bar Anas a
durkushe a gaban matarsa
Mabaruka gurguwa. Sidi mai jaka
ya yi shiru sannan sai ya sake
zarar wani katon tubani ya jefa a
bakinsa ya dubeni ya ce.
"Ba zan iya hakura da cin tubani
ba Nas, sai dai tumbina ya fashe
Tsawon dakika talatin Nas, Anas
yana durkushe a gaban
Mabaruka cikin tsananin kaduwa
yaya ma za ta bari ta yi ciki? Anas
ya tambayi kansa, wani bakin ciki
ya lullube zuciyarsa. A haukan
Anas ya gama imani da cewa
babu makawa Mabaruka
mummunan jariri ko jaririya za ta
haifa masa a matsayin dansa.
Wannan tunani shi ya sa wani
zazzafan gumi barkowa akan
goshin Anas. Cikin karfin hali
Anas ya ciccibi Mabaruka ya
kwantar da ita akan gado
sannan ya kwanta a kusa da ita
ya yi shiru, domin kwakwalwarsa
lokacin ba za ta iya tunanin
komai ba sai na Ummi. A
zuciyarsa yana cewa, ina ma ace
cikin nan Ummi ce ta yi shi a
matsayin matarsa.
Tsawon lokaci suna nan haka a
kwance ba sa ko motsi cikin
bacin rai, can sai Mabaruka ta yi
ajiyar zuciya ta ce a tausashe.
"Anas..."
"Na'am."
Anas ya amasa bayan jinkirin
kusan minti guda.
"Ban ji ka ce komai ba ko ba ka
farin ciki da dan da zan haifa ma"
Anas ya ji kamar Mabaruka ta
soka masa kibiya a tsakiyar
zuciya. Shiru na yan dakiku, Anas
bai amsa ba.
"Anas...ba ka ce komai ba!"
Mabaruka ta ce cikin wata irin
shakakkiyar murya tana shirin
fashewa da kuka.
"Me ki ke so in ce dake?" Anas ya
ce da ita a fusace. Hakika tuni ya
gama yankewa zuciyarsa
shawara shi fa ya gaji da
wannan daurin talala da mulkin
mallaka.
Cikin kaduwa da jin abinda ya ce
Mabaruka ta turar da hannunsa
ta dan dago kai ta dubi fuskarsa
a cikin dan hasken fitilar dakin
dake ajiye akan wani teburi na
alfarma.
"Anas...ba ka kaunata ko?..." Anas
ya yi shiru na yan dakiku bai
amsa ba sannan sai ya tashi
zaune ya ce.
"Mabaruka ya kamata mu
fuskanci gaskiya, sanin kanki ne
tsakani da Allah cusa min ke aka
yi...ba wai bana kaunarki bane
amma..."
"Ya isa haka!" Mabaruka ta daka
masa tsawa cikin wata
karyayyiyar murya.
"Ba sai ka karasa ba Anas, na
yarda tabbas ba ka kaunata."
"Ka da ki zarge ni, ki zargi
mahaifiyarki Mabaruka da kuma
ke kanki."
Aka sake yin shiru na yan
mintuna.
"Ummi ce ko?" Mabaruka ta bata
shirun da wannan tambaya.
"Ba zan boye miki ba
Mabaruka...wall ahi duk duniya
babu wacce nake kauna kamar
ta.
Mabaruka ta ji kamar ya watsa
mata wuta a doron zuciya. Wani
abu mai kamar amai ya zo ya
toshe mata makogwaro.
"Anas...mu sawwake wa juna ina
ganin shi zai fi ko?"
"Kwarai kuwa...nima da niyyar da
na zo kenan." Cikin sauri kamar
da wasa sai Anas ya lalubi
aljihunsa ya zaro takardar da tun
a cikin mota ya rubuta a lokacin
da zai yi fakin da ita a gareji.
Hannunsa na rawa ya mika mata
ya ce baki na rawa.
"Na sake ki saki biyu." Mabaruka
ta karbi takardar ta karata a
kirjinta, kana ta lumshe idanu, ga
mamakin Anas, sai ya ga ta
dubeshi ta ce.
"Don Allah taimaka ka kaini falo."
Anas ya ciccibeta, cikin damuwa
domin tausayinta ya gama lullube
zuciyarsa, to amma babu abin da
zai iya akan hakan. Lokacin da ya
ajiyeta, sai ta dube shi ta kuma
cewa.
"Dan Allah koma daki ka jirani."
Ta dan yi shiru sannan sai ta
kuma cewa "Za ka bari gari ya
waye ko yanzu za ka fita?" Anas
ya dubeta a rude sannan ne to fa
dimbin asarar da zai dibga ya
darsu a zuciyarsa, tabbas ya san
ya rabu da masifa ya fada masifa.
Domin a gurinsa Mabaruka
masifa ce, haka kuma rabuwa da
ita ma na nufin sake shiga cikin
masifar talauci Koda yake dai ai
ina da yan kudi a banki da gida
da mota da kuma otal din da
mahaifiyarta ta bani Anas ya
fadawa kansa
"Duk abin da ki ka ce haka za a yi
in ba kya son ganina yanzu ma
sai in tafi" Mabaruka ta danne
kukan dake kokarin kufcewa
daga makogwaronta.
"Dan jirani a dakin to ina zuwa"
Anas ya koma cikin dakin ya
zauna gami da ajiyar zuciya Ga
mamakinsa sai ya ji tamkar an
dauke masa wani katon kaya mai
nauyin tsiya daga doron bayansa
Sannan ne to ya jiyo sautin
muryar Mabruka daga cikin falon
tana yiwa Mahaifiyarta waya
Tsawon mintuna talatin Anas na
nan zaune yana jran dawowar
Mabruka gurguwa lokacin ne ya
juyo sautin injin mota an shigo
farfajiyar gidan Cikin sauri Anas
ya mike a rude ya nufi taga ya
leka. Tun kafin ya gama bude
labulen tagar ya hangi dogon
direban gidansu Mabaruka ya
budewa Hajiya Aliya kofar
katuwar (Jeep) din nan baka ta
fito jikinsa na rawa Anas ya nufi
falon inda Mabaruka take Anas
ya sameta zaune akan kilishin
dake mamaye da tsakar dakin
kan talfon din rike a hannunta ta
kwantar da kanta akan kujerar
dake daf da ita gaban rigarta
sharkaf da hawaye
"Me ya kawo mahaifiyarki kuma
cikin wannan maganar? Don me
ba ki fada min ita za ki kirawo
ba?" Mabaruka ba ta dago kai ba
balle ma ta kalleshi sai ta ce a
sanyaye
"A GABANTA MUKA FARA
AGABANTA NAKE SON MU ƘARE."
A GABANTA MUKA FARA
AGABANTA NAKE SON MU KARE."
Kofar babban falon ta bude
Hajiya Aliya ta shigo a fusace bata
ko damu da ta zauna ba sai ta
dubi Anas ta ce
"Tun da ka sake ta me kuma ka
ke jira sai ka fice ka bar mata
gidanta."
Babu kunya, babu tsoro sai Anas
ya dubeta ya ce "Gidanta ko
gidana? Na dauka ke ki ka fada
da bakinki kin bani gidan nan?"
Hajiya Aliya ta dubeshi shekeke
ta ce
Duba bayan ka wannan shine
Yarima Gangariya na mallaka
masa wan nan
gida kuma daga zarar ta haihu
za'a daura musu aure
Hajiya Aliya ta dubeshi shekeke
ta ce "Kai dai jahili ne wallahi
Anas kai ka taba gani inda aka
baiwa mutum kyautar gida babu
shaidu kuma babu takardu? Ko
ka taba ganin inda aka baiwa
mutum kyautar otal babu shaidu
kuma babu takardu?"
Anas ya ji wani zazzafan gumi ya
karyo masa Hajiya Aliya ta
dubeshi ido da ido ta ce
"Ka yiwa kanka matsiyaci sai ka
koma cikin talaucin ka motar da
na baka na kwace kayata domin
daman duk takardunta yana
hannuna haka ma gidan da
kuma otal din da na baka duk na
kwace su. Daga yanzu ba kai
babu karbar ko kwabo daga
kamfanunnukanmu matsiyaci."
"Bai kamata ki yi min haka ba?"
Anas ya ce cikin kaduwa domin
a shashancinsa bai taba tunanin
haka ba.
"Ba ka da hankali Anas tashi ka
fice min daga gida. Rufeshi zamu
yi a cikin daren nan in koma da
yata gida ka yi ma sa'a wallahi
da yan kudin da suke bankinka
ma sai na yi hanyar da za su
salwanta...amma ka yi sa'ar ta."
Ta dan yi shiru tana duban
Mabruka. "Ita ce ta ce na kyale
ma kudin da ke cikin ma'adanin
ka. Sai ka fice Allah ya bamu
alheri." Anas ya dubi Mabruka a
rude sannan sai ya juya zuwa
cikin dakin. Ba a dade ba ya hado
kayan sawarsa a cikin jakunkuna
guda uku ya ratayo su da kyar
sannan ya dubi Mabruka ya ce.
"Na gode Mabruka." Sannan sai
ya fice daga dakin.
Wani abin mamaki shi ne tun da
Mabruka take da Anas, bai taba
fada mata kalmar da ta amince
da ita har zuciyarta ba sai
wannan godiyar da ya yi mata.
Koda Anas ya nufi farfajiyar
gidan sai dogon direban nan ya
tare shi, ya karbi biyu daga cikin
jakunkunan uku ya ce.
"Mabruka ce ta ce duk inda ka ke
son zuwa na kai ka."
Anas bai san menene mutunci
ko so ba sai yanzu. Abin mamaki
sai ya ji hawaye ya yi sartu akan
kuncinsa.
Koda direban motar ya fara tafiya
da su sai Anas ya yi ajiyar zuciya.
A kalla dai ko da na rasa arziki
ina da wacce na fi kauna da so a
duniya Ummi! Anas ya ce da
kansa.
"Yallabai ina zan kai ka?" Anas ya
dubi direban a rude sannan yace.
"Bari in tuna"****
Ummi ta ji hawaye ya yi sartu
akan kundukukinta sa'ar da ta
gama karanta takardun.
Hawayen da ke zuba a yanzu
hawayen bakin ciki ne da farin
ciki. Bakin cikin shi ne ya ya ma
za a ce wai wadannan mutane
da tun da ta fara budar ido su
take gani a ce wai ba mahaifanta
bane yayin da kuma farin cikin
shi ne yanzu ta fahimci tana da
damar mallakar abin da ta dade
tana kauna tun da ta zo duniya.
Haba gaskiya fa ta ji ba ta san
rabuwa da shi tana bege da
shaukin son zama da shi ashe ba
dan uwanta ba ne na jini.
Ba ta ji shigowarsa ba sai
inuwarsa ta gani a kanta. Ta juya
a razane, sai suka yi ido biyu da
Abdulmalik. Nan da nan sai ya yi
murmushi sannan ya mika mata
wani farin kyalle ya ce a
tausashe.
"Goge hawayen ki."
Ummi ta ji kunyarsa ta rufe ta, ta
kasa hada ido da shi, kanta a
sunkuye ta karbi kyallen gami da
ajiyar zuciya.
"Abdulmalik, me ya sa baka fada
min ba tuntuni...kuma dan Allah
wannan abin da ka rubuta min
gaskiya ne?"
Abdulmalik ya dubeta da
murmushi ya ce.
"Na taba fada miki karya?" Ummi
ta yi sauri ta girgiza kai.
"Kuma na ji kin kira sunana kai
tsaye na dauka ni yayanki ne ko
kin fasa yayan da ni?"
Ummi ta rufe idanu a kunya ce ta
ce "Ni na isa, ai har abada kai
Yayana ne kuma..." Ta yi shiru ba
ta karasa ba.
Abdulmalik ya zo kusa da ita ya
zauna da murmushi ya ce.
"Karasa mana kuma me?" Ummi
ta fara wata sassanyar dariya.
"Ni ba zan karasa ba."
"Allah sai kin karasa." Abdulmalik
ya ce cikin dariya.
Uimmi ta dago kanta ba tare da
ta kalli fuskarsa ba, ta dubi
hotonta dake manne a jikin
bangon dakin sannan ta ce.
"Rufe idanunka, ka miko
hannunka na rubuta maka abin
da na ki karasawa."
Cikin farin ciki sai Abdulmalik ya
rufe idanunsa, sannan ya mika
mata tafin hannunsa.
Cikin sauri Ummi ta yi rubutu
akan tafin hannunsa, sannan sai
ta dauki takardun da ya bar mata
ta karanta ta rike a hannunta
sannan sai ta ruga a guje ta fice
daga dakin.
.
Abdulmalik ya zo kusa da ita ya
zauna da murmushi ya ce
"Karasa mana kuma me?" Ummi
ta fara wata sassanyar dariya.
"Ni ba zan karasa ba."
"Allah sai kin karasa." Abdulmalik
ya ce cikin dariya
Uimmi ta dago kanta ba tare da
ta kalli fuskarsa ba ta dubi
hotonta dake manne a jikin
bangon dakin sannan ta ce
"Rufe idanunka, ka miko
hannunka na rubuta maka abin
da na ki karasawa."
Cikin farin ciki sai Abdulmalik ya
rufe idanunsa sannan ya mika
mata tafin hannunsa.
Cikin sauri Ummi ta yi rubutu
akan tafin hannunsa sannan sai
ta dauki takardun da ya bar mata
ta karanta, ta rike a hannunta
sannan sai ta ruga a guje ta fice
daga dakin ta nufi dakin
mahaifiyar Abdulmalik domin ta
fasa kwai.
Abdulmalik ya bude idanu a
daidai lokacin da Ummi ta fice
daga dakin kana ya dubi tafin
hannunsa sai ya ga Ummi ta
rubuta YAYANA MIJINA !
.
Sidi mai jaka ya ja doguwar
hamma ya kuma karawa sannan
ya dubi kwanon tubanin dake
gabansa ya ce
"Nas na fa gaji." Na dube shi cikin
kasuwa na ce "Ka da dai ka ce
min karshen labarin kenan?" Sidi
mai jaka ya girgiza kai ya ce
"Ba karshensa ba kenan amma
saura dan kadan saurara na
karasa maka sai mu watse" Na
ce to, Sidi mai jaka ya dube ni
kana ya ci gaba.
Washe garin ranar karfe takwas
daidai dan kabu-kabu ya sauke
Anas a kofar gidan su Ummi
idanunsa sai zubar da ruwa suke
kamar tsohon kuturu domin
rabonsa da ya hau kabu-kabu
tun kafin satin da zai hadu da
Mabruka
Anas ya aika yaro zuciyarsa cike
da farin ciki duk kuwa da sauyin
rayuwa da ya same shi na
gaggawa cikin sa'a ashirin da
hudu kacal A daren jiya bai yi
barci ba duk kuwa da cewa a
dakin otal ya kwana amma dakin
bai kai ko da rabin dakin
kwanansu da Mabruka ba
*
A can cikin gida Ummi ta dubi
Abdulmalik ta ce.
"Mutumin ka ne, don Allah zo mu
je ka labe daga bakin kofa ka ji
yadda za mu kare da shi." Cikin
murmushi Abdulmalik ya dube ta
ya ce.
"A'a, kada mu koma kamar yara
kanana mana, ke dai je ki ku
gama da shi ina nan."
Ummi ta dube shi da dariyar
zolaya ta ce.
"Kai dai tsoro ka ke kada su
Mama su ganmu tare, to mene ne
kuma bayan sun san komai."
"Sun san me?" Abdulmalik ya
tambaya a tsora ce.
"Takardun da ka rubuta suna
gurin mama..." Ta fashe da
dariya, da haka ta fice ta bar shi
anan baki bude.
Anas ya ji wani farin ciki marar
misaltuwa ya lullube shi, sa'ar da
ya hango kyakkyawar fuskar
Ummi ta leka kofar gidan cikin
sauri ya tareta da faffadan
murmushi.
"Hajiya Ummita." Ummi ta dube
shi shekeke ta ce.
"Ranka ya dade...yau a kasa ka zo
ina motar?"
Anan ne to Anas ya gama
karkade dan sauran abin da ya
rage na kaunarsa dake zuciyarta.
"Wannan marar mutuncin
gurguwarce ta kwace motar...kin
san fa mun rabu da ita jiya da
daddare saboda ke."
Ummi ta dube shi cikin takaici ta
ce "Kana nufin ka saki
Mabaruka?" Anas ya gyada kai
"Mene ne to amfanin zama da
nacacciya. Matar da za ta hanaka
walawa." Ummi ta kura masa
idanu, yanzu kam ta tabbata duk
abin da Hasiya ta fada akan
wannan saurayi mai kyawun dan
maciji gaskiya ne. Ummi ta
dubeshi ido da ido ta ce.
"Amma bai kamata ba ace ka saki
Mabruka, dubi fa son da na ga
tana yi maka Anas yanzu kai ko
tausayinta ba ka ji?"
Anas ya fashe da tattausar
dariyar da ya sha satar zuciyar
yan mata da ita ya ce.
"Don me zan tausaya mata bayan
tana son ta raba ni da ke." Ummi
ta sake dubansa ta ce "Anas, wai
me ya sa ka ke kaunata?"
"Saboda kina da masifar kyau
Ummi, ko ke ba kya ganin kanki
ne."
"Shi kenan abin da ya sa ka ke
kaunata?"
Anas ya gyada kai sannan ya
dube ta ya ce "Ke fa me ya sa ki
ke kaunata?"
Ummi ta dube shi na tsawon
lokaci kana sai ta dauke kai gefe
guda ta ce "A da dai saboda kana
burge ni ne kawai idan na
dubeka shi yasa nake sonka."
Anas ya dubeta cikin mamaki ya
ce "A yanzu fa?"
Ummi ta girgiza kai ta ce "Ka
daina burge ni Anas, kai bari in
fada maka ma infact na tsaneka
domin ka fiye son kanka."
Anas ya ji wani abu kamar
tafasasshen ruwa ya fara wanke
masa fuska.
"Ummi in wasa ne wannan ki ke
yi dan Allah ki bari Ummi domin
yana iya sa ni hauhawar jini."
Ummi ta girgiza kai ta ce "Ban
taba yin wasa da kai ba,
wadanda suka sha wasan da kai
dai sun yi, irin su wadannan." Ta
zaro hoton da Hasiya ta ba ta, ta
mika masa.
Anas ya karba hannu na rawa,
nan da nan sai ya ji kwalla na
kokarin kwace masa.
"Haba Ummi, yanzu wannan yar
iska ce za ta rabani da ke'"
Ummi ta kuma girgiza kai ta ce
"Ka da ka sake daukar alhakin
baiwar Allah wanda ka dauka a
da ma ya ishe ka wallahi babu
ruwanta a cikin wannan zance."
Anas ya yaga hoton dake
hannunsa gida biyu a fusace
yace.
"To idan ba ita ba ce me ya sa za
ki ce kin tsaneni Ummi? Me ya sa!
Na dauka ke ki ka rubuto min a
takarda kina kaunata ??"TSOHON ALKAWARI-19
KARSHE
.
Na dauka ke ki ka rubuto min a
takarda kina kaunata?"
"Wannan da ke nan Anas jiya na
sake shawara ka san duniya juyi-
juyi kullum da irin abin da take
zuwa"
Anas ya matso kusa da Ummi
cikin kaduwa ya ce cikin
karyayyiyar murya
"Na ji na yarda Ummi kin tsane
ni amma ina son don Allah ki
taimaka ki fada min mene ne
dalilin da ya sauya miki ra'ayi a
kaina?"
"Yanzu ka yi tambaya?" Ummi ta
ce tana ja da baya cikin shirin
shigewa gida
"Abin da ya bani tsoro da kai
Anas guda daya ne jal shi yasa na
tsaneka akan dole"
"Mene ne." Anas ya tambaya
kusan cikin kuka.
"Ka da ka bada yan maza Anas
yanzun nan zan fada maka" Ta
dan yi shiru tana gyara lullubin
koren gyalen mai shara-shara da
yake kanta sannan ta dube shi ta
ce
"Ga ni na yi Anas aurenka yana
da hadari" "Saboda me Ummi?
Saboda me ki tuna fa ni mai
kaunar ki ne"
"Na yarda Anas kana kaunata"
Ummi ta ce cikin murmushi
"Amma abin da na yi tunani shi
ne, duk mutumin da bai tausaya
wa zuciyar gurguwa abin Allah
sarki ba to kuwa ba zai taba
tausayawa mai kafafu kamata
ba"
Ta juya cikin sauri ta shige gida
ta bar Anas sororo a tsaye yana
lissafin irin asarar da ya yi
.
Sidi mai jaka ya mike tsaye ya yi
doguwar mika ya ce
"Nas labarin nan fa ya kare in
kuma ba so ka ke in shiga yi
maka karya ba ka san kuwa karya
LINZAMIN SHAIDAN CE"
.
"Haba Baba Sidi ai ba ka fada
min yadda Mabruka ta kare da
cikin ba"
Sidi mai jaka ya dubeni da
murmushi ya ce "Nas kenan
daman da gangan na kyaleka na
dauka za ka mance da sauran
bakin zaren labarin da muka bari
bamu dinke ba amma tunda ka
tuna bari in dinke ma shi a
gurguje
Sidi mai jaka ya gyara tsayuwa ya
ce
"Nas watanni shida sun shude
kamar wasa an daura auren
Abdulmalik da Ummi har ma tana
da ciki wata dayashi kuwa
Anas ya koma matsiyacinsa yan
kudin ma da suka rage a
asusunsa duk ya kashesu a
banza domin dan zaman da ya yi
da mabruka ya yi sabo da jin
dadi
Haka nan ma Mabruka ta
haifarwa Anas wata kyakkyawar
ya mace amma kwanakinta
bakwai a duniya ta rasu. Anas ya
yi ta rusa kuka shi kadai a daki
domin ya so a ce ta rayu don ko
banza dai in Mabruka ta mutu
yar ce za ta gaji duk dukiyar shi
ko yana iya zuwa ya karbe yarsa
da dukiyarta ka ga ya zama
miloniya kenan
.
Sidi mai jaka ya dubeni cikin
murmushi ya ce Nas wato
mutum dai sai dai ka bar shi da
halinsa amma hali zanen dutse
ne"
"To yanzu ina Anas din yake?" Na
tambaye shi
"Nas kenan kai dai ka cika son jin
kwakkwafin labari na dai
fahimci so ka ke ka sa dattijo ya
shiga karya"
Anan sai na fashe da dariya Sidi
mai jaka ya dubeni da murmushi
ya ce
"Na ji an ce wai Anas din ma ya
samu tabin hankali tun da yar
jaririya da aka haifa masa ta
mutu amma fa labarin wai ne
har yanzu bani da tabbacinsa"
Sidi mai jaka ya dubeni kana sai
ya juya ya ce
"To Nas Allah ya dada sada mu
da alheri sai wata rana"
.
Dattijon ya shige cikin gida
abinsa ya bar ni nan tsaye ina kokarin
hada zarurrukan labarin
.
KARSHE
Sunday, February 16, 2020
TSOHON ALKAWARI Page 51 to 60
A bangaren Abdulmalik, sannu a
hankali har Ummi ta kai shekaru
goma sha bakwai. Kullum wutar
begenta sai dada ruruwa cikin
zuciyarsa take yi, ita ko in ka
dauke soyayya irin ta yan
uwantaka bata dauke shi a bakin
komai ba. Amma duk da haka
nan dai kullum suna tare basa
rabuwa.
Wata rana da yamma Ummi ta
shiga dakin Abdulmalik ta ci
kwalliya, fes,fes, hakan shi ya sa
zuciyar Abdulmalik harbawa. A
ranar ne to Abdulmalik ya ji
kamar ya amayar mata da
boyayyen sirrin zuciyarsa, to
amma sai ya tuna kashedin da
mahaifinsa ya yiwa duk wani
mutum dake gidan inda yake
cewa.
"Kada wani daga cikinku ya sake
ko da da wasa ya fadawa Ummi
cewa mu ba iyayenta ba ne."
Wannan shi ya sa Abdulmalik
hadiye maitarsa.
Zuciyarsa na harbawa ya dago
kai ya dubeta cikin yabawa da
abin da ya gani ya ce.
"Kai, amma fa kin kara kyau
Ummi." Ummi ta dube shi cikin
dariya ta ce "Na gode yaya
Abdul." Ta dan yi shiru tana
kallon jeren hotunanta ko ina a
cikin dakin sannan ta dubi
Abdulmalik ta ce.
"Duk duniya babu yan uwan
dake kaunar juna kamar mu,
dubi fa Yaya Abdulmalik duk ka
bi ka wani shagwaba hotunana
kamar wata budurwarka.
Wannan ko budurwa ce ai ba
karamin kaunarta kake yi ba."
Abdulmalik ya sunkuyar da kai da
dan murmushi, wata zuciya na
cewa da shi, fada mata kawai
cewa ita fa ba yar uwarka ba ce
ta jini. To amma sai gargadin
mahaifinsa ya sake dawowa
zuciyarsa dan haka sai ya dago
kai ya dubi Ummi da Murmushi
ya ce.
"Ummi kenan. Ina za ki ne na ga
kin caba kwalliya haka?" Ummi ta
dube shi da murmushi sannan ta
ce.
"Ina zani, ko dai ina zamu, bikin
taya murnar ranar haihuwar
wata kawata zaka rakani."
Abdulmalik ya dubeta cikin
mamaki ya ce.
"Kin manta ne cewa ina da
jarrabawa ta karshe a
makaranta, kin san ina bukatar
karatu."
Ummi ta yi sauri ta rufe fuska
cikin dariya.
"Oh! Dan Allah Yaya Abdulmalik
ka yi hakuri, wallahi mantawa na
yi ashe kana da jarrabawa gobe."
Abdulmalik ya mike tsaye.
"Mu je na raka ki sai na dawo."
Ummi ta mike tsaye ta dube shi
ta ce.
"Wallahi nima dan muna bala'in
mutunci ne da MABRUKA da ba
zan je ba tun da kaima ba za ka
ba." Abdulmalik ya yi murmushi.
"Ai ba komai. Yaushe zaki
dawo?" Ummi ta lumshe idanu ta
dan daga kai sama. Abdulmalik
ya kurawa wasu siraran zane
guda uku da suka yiwa
kyakkyawan wuyanta kawanya.
"Nan da karfe tara na dare zamu
dawo."***
.
Sidi Mai Jaka ya dubeni ya ce ina
fatan kana fuskantar inda labarin
ya dosa da kyau? Na gyada kai
cikin sauri.
"Ina fuskanta." Sidi Mai Jaka ya ci
gaba.
A daren ranar da Ummi ta dawo
daga walimar bikin zagayowar
haihuwar Mabaruka ne to
Abdulmalik ya fara ganin canjin
yanayin karara a fuskar Ummi
Karfe tara na dare da yan
mintuna ta dawo, Abdulmalik ya
ji shigowarta babban falo dan
haka sai ya ji wani farin ciki ya
lullubeshi domin tuntuni ya
matsu da ya ga ta dawo domin
baya iya yin sama da sa'a biyar
bai ganta ba Wani sa'in ko a
makaranta yake sai ya yi ta bugo
mata waya duk bayan sa'a guda
dan kawai ya ji muryarta Don
haka sa'ar da ya ji motsin
dawowar Ummi sai ya ajiye
takardun bokon da yake
karantawa ya lumshe idanu yana
jiran shigowarta domin ya san
alkawari ne sai ta shigo dakin.
Tsawon lokaci shiru babu motsin
UmmiDomin ya san
alkawari ne sai ta shigo dakin.
Tsawon lokaci shiru, babu
motsin Ummi sannu a hankali
har mintuna talatin suka shude
bata shigo dakin ba. Abdulmalik
ya mike tsaye cikin tsananin
damuwa da mamaki domin a iya
saninsa da Ummi ko kayan
jikinta ba zata sauya ba sai ta zo
gare shi su yiwa juna Sallama
Cikin sauri Abdulmalik ya fita
daga dakinsa ya ratsa ta falo ya
nufi dakin Ummi. Abdulmalik ya
dan kwankwasa kofar dakin a
tausashe sannan sai ya yi sallama
ya shiga.
Ummi na kwance akan gado,
sanye da kayan da ta fita da su
walimar, ko cire su bata yi ba, ta
kurawa saman dakin idanu bata
ko kiftawa kamar mai kallon allon
sinima. Abdulmalik ya tsaya cak a
tsakiyar dakin kamar an dasa shi,
ya kurawa Ummi idanu cikin
tsananin mamaki da kaduwa
domin ya fahimci ashe Ummi
bata san ma ya shigo dakin ba.
"Ummi..." Ya sake maimaitawa a
karo na biyu kamar mai biya
karatu. Ummi ta juyo firgigit ta
tashi zaune akan gadon. Ta dubi
Abdulmalik.
"Tunanin me ki ke yi haka?"
Ummi ta dubeshi da murmushi.
"Ka yi hakuri don Allah
Abdulmalik wallahi ban san ka
shigo ba." Abdulmalik ya matsa
kusa da ita ya zauna daga can
nesa da ita a bakin gadon ya
kura mata idanu.
"Na ji shigowarki, ina ta jira ko za
ki zo, ba ki zo ba shi ne na ce
bari ni nazo da kaina na gani ko
lafiya." Ummi ta sunkuyar da kai
sannan ta yi ajiyar zuciya kana ta
dago kai da murmushi ta dubi
Abdulmalik ta ce.
"Lafiya lau Yaya Abdulmalik
bala'in gajiya na yi." Tun kafin ta
gama fada Abdulmalik ya san
karya take yi, domin alamun
damuwar dake fusakarta tamkar
bakin rubutu ne akan farar
takarda. Abdulmalik ya ji
zuciyarsa ta sosu, bai ji dadin
abin da ta fada ba, domi a duk
iya tsayin zamani, tun ranar da
aka haifeta ya fara daukarta, har
zuwa yau bata taba fada masa
karya ba sai yanzu.
Abdulmalik ya dubi Ummi cikin
shakka, ya girgiza kai ya ce.
"Kada ki ce haka Ummi, ba gajiya
ba ce kawai ke damunki akwai
matsala ta daban." Ummi ta
dubeshi da wani fatalwan
murmushi akwai alamun kunya a
fuskarta ta ce.
"Gaskiya ne Abdulmalik wallahi
akwai abin dake damuna, ka
kuma yafe min dan Allah ka san
ban taba yi ma karya ba sai yau..."
Ta dan yi shiru tana murmushi
sannan sai ta dada da cewa.
"Yau din ma kunya ce wallahi ta
sa ni yin karya." Abdulmalik ya yi
ajiyar zuciya kana ya dubeta cikin
shauki ya ce.
"Na yafe miki Ummi...ai kin san
duk laifukanki a gurina yafaffune
har ma da wanda ba ki yi ba."
Ummi ta yi dariya ta sake
sunkuyar da kai Abdulmalik ya
sake nazarin fuskar Ummi cikin
damuwa ya ce.
"Fada min sirrin dake zuciyar ki
Ummi me ke damun ki ne?"
Ummi ta dauke kai gefe guda na
tsawon lokaci, haka nan a duk
iya tsayin wannan lokaci akwai
alamun murmushi-murmus hi
da
kuma damuwa-damuwa a
fuskarta. Shi dai Abdulmalik ya
kura mata idanu cikin mamaki
bai tari numfashinta ba. Tsawon
lokaci, sannan Ummi ta juya ta
dubeshui, ta ce bakinta na rawa.
"Yaya.....Abdul malik...wallahi
irin
abin da nake yawan karantawa
ne a cikin littattafan labarai na
Hausa ya faru a kaina."
Abdulmalik ya ji gabansa ya fadi
ras! Ya dubi Ummi.
"Me ki ke nufi." Ummi ta dauke
kai gefe guda a kunyace ba tare
da ta hada idanu da shi ba ta ce.
"Wallahi...wani na gani a gurin
liyafar nan naga ya burge ni."
Abdulmalik ya ji zuciyarsa ta
harba.
"Har yanzu ban fahimce ki ba
Ummi, waye wani, kuma ya
burge ki kamar ya ya." Ummi ta
sake dariya ta ce.
"Yaya Abdulmalik ji na yi wallahi
ina masifar kaunarsa a zuciyata,
a yanzu din nan haka ji nake yi
kamar mun dade da sanin juna."
Ta dan yi shiru ganin Abdulmalik
bai ce wani abu ba sai ta dada da
cewa
"Za ka yi mamaki idan na ce da
kai Mabaruka ce kawai ta turani
na yi kiransa." Abdulmalik ya
dago kai ya dubeta da
murmushin karfin hali, amma a
badini tuni har zazzabi ya rufe
shi
"Ummi kenan. To yanzu ya ya za
ki yi kenan? Kin ga mutum kin ce
kina sonshi amma ba ki san ko
wane ne shi ba ba ki san inda
yake ba baki san ko da sunan shi
ba." Ummi ta matso kusa da
Abdulmalik ta ce
"Ma'aikacin otal din da aka yi
liyafar ne, na ji Mabaruka ta kira
shi da suna ANAS!" Abdulmalik ya
sunkuyar da kai Ummi ta
dubeshi cikin damuwa. A
tunaninta halin da ta tsinci kanta
ciki ne ke damun Abdulmalik
domin ta san irin yadda yayan
nata Abdulmalik ke matukar
sonta don haka sai ta ce dashi a
tausashe
"Ka da ka dami kanka Yaya
Abdulmalik na san duk abin da
ya shafe ni kai ya shafa. Ni dai
abin da nake so shi ne ka tayani
don Allah mu same shi ka ga
kaunarsa" Ta dan yi shiru
sannan sai ta dubi Abdulmalik ta
ce
"Kana jin kuwa zai iya
kaunata?"***
Sidi mai jaka ya yi shiru kana ya
dubeni da murmushi sannan ya
dubi tubanin Tubanin dake
gabansa cikin damuwa domin
tuni ya hadiye sama da kashi uku
bisa hudun tubanin
A zuciya ta na ce kai wannan
tsoho da cin
tsiya yake domin na tabbata
yawan tubanin da ya hadiya tun
daga rana zuwa yanzu ya ishi
katti goma su ci su koshi amma
sai gashi shi kadai duk ya
hadidiye su kamar rumbu
"To Nas ka ga abin da nake fada
maka tun farko ko? Sai da na ce
da kai ni ne mai saka labari
kamar injin saka, na hade ma shi
guri guda, gashi kuwa sannu a
hankali na nuna maka alakar
zarurrukan labarin guda biyu."
"Haka ne Baba Sidi." Na ce dashi
Sidi mai jaka ya canko wani
katon tubani mai kama da
dankali ya gutsiri rabi, sauran ya
fado a cikin kwanon
Sidi mai jaka ya dubeni ya ce.
"Nas, wannan shi ne karshen
wannan dogon zaren labarin,
yanzu abin da ya rage shi ne na
gaggauta na daura ma bakin
zarurrukan labaran guda biyu
kafin nan da sallar magariba,
domin bana son labarin ya kai
mu har bayan sallar magariba."
Na yi sauri na gyada kai na ce.
"Ni ma ai na fi son haka." Sidi mai
jaka ya gyada kai ya ce.
"To Nas, bari yanzu ne zan koma
kan wancan tsohon zaren labarin
da muka bari lokacin da zamu
tafi sallar azuhur, inda mauka
baro Anas yana karatun wasikar
da Ummi ta bashi." Ya dubeni ido
da ido.
"Ka tuna da gurin?" Na gyada kai
na ce.
"Kwarai kuwa, ba inda ka ce har
ma yana jiyo kukan matarsa
Mabaruka ba daga cikin
bandakin?" Sidi Mai jaka ya fashe
da dariya yace.
"Nas kenan, da ace yadda kake
rike labari a kwakwalwarka haka
nan kake rike karatu da ba
karamin malami za a yi ba wata
rana, to sai dai kuma na fahimci
kamar kwakwalwarka ta fi iya
rike labari fiye da komai." Nima
sai na fashe da dariya, na ce.
"Baba Sidi kena." Sidi mai jaka ya
yi gyaran murya sannan ya ce.
"Nas, dauki zuciyarka cancakat ka
mayar da ita cikin bandakin nan,
inda muka baro Anas dazu yana
karatun wasikar da Ummi ta
bashi."
"Na mayar." Na ce dashi.
Yauwa Nas. Anas ya ci gaba da
juya takardar a hannunsa,
zuciyarsa dauke da abubuwa
guda uku masu kama da kishiyar
juna. Ka ga na farko dai akwai
farin ciki, domin Anas bai san
abin da zai iya kwatanta farin
cikinsa da kalmar Ummi ba, inda
tana kaunarsa da kanta. Na biyu
akwai tsana mai tsanani cikin
zuciyarsa, domin a yanzu duk
duniya babu abin da ya tsana
kamar matarsa Mabaruka. Domin
tuni Anas ya riga ya san wannan
mummunar gurguwa ita kadai ce
katangar karfen dake tsakaninsa
da babbar masoyiyarsa Ummi.
Abu na uku kuwa dake dafe a
zuciyar Anas shi ne tsananin
fargaba, don Anas ya tabbata sai
dai ya zabi tsakanin mummunan
aski da sa kai a wuta, domin
muddin ya ci gaba da mu'amula
da Ummi, rabuwarsa da
Mabaruka ta zo kenan, shi ko ya
san a yanzu koma me yiwuwa
har abada Mabaruka ita ce
babbar rumfar da ta rufe kansa
da inuwa ta yi masa katanga da
zafin ranar talauci.
Wadannan abubuwa guda uku
su suka hadu suka cunkushe
zuciyar Anas, don haka yana nan
bandakin yana maimaita karatun
wasikar Ummi har sai da ya
karanta ta sau kusan talatin. Bai
tashi komawa dakin kwanan su
ba sai da ya tabbata a lokacin
Mabaruka ta gama fushinta ta yi
barci.
Anas ya nufi dakin kwanansu
cikin sanda, a lokacin kusan biyu
da rabi ne na dare. Ko kusa ko
alama baya son ya sami
Mabaruka ido biyu bata yi barci
ba, domin Anas ya gama gajiya
da ita, kai hatta muryarta baya
son ji. Murya daya ce kawai ke
yawo cikin kwakwalwarsa
muryar Ummi.
Anas ya yi boyayyiyar ajiyar
zuciya sa'ar da ya tura dakin
kwanan nasu ya shiga. Domin ya
ga a cikin duhu yake. Tabbas ta yi
barci, Anas ya ce cikin zuciyarsa
Sannu a hankali ya sauya kayan
dake jikinsa sannan ya lallaba ya
haye bisa gadon ba tare da ya yi
wani kwakkwaran motsi ba ya
kwanta haka nan bai ma yarda
koda jikinsa ya taba jikinta ba
Anas ya yi lamo kamar ya mutu
gashi dai baya ko motsi amma
idanunsa a bude yake garau
Zuciyarsa dauke da hoton
kyakkyawar surar Ummi Yana
nan kwance zuciyarsa fari fat
lokaci guda kuma yana tunanin
hanyar da zai bi a gobe ya
gujewa Mabaruka domin ya sami
damar ganawa da Ummi Anas
na nan cikin wannan haki can
sai ya ji agogo ya buga karfe
daya sannan ne fa ya ji abin da
yasa gashin jikinsa mimmikewa
tsaye
"Anas." Muryar Mabaruka ta ratsa
duhun dake dakin ta daki dodon
kunnensa. Anas ya zabura cikin
kaduwa Bai taba tsammanin
Mabaruka ba barci take yi ba.
"Mab...Mabaruka ...dama ba barci
ki ke yi ba." Mabaruka ta yi ajiyar
zuciya ta ce a sanyaye cikin
karayar zuciya.
"Ya zan iya barci Anas bayan
kana fushi dani." Hakan kawai da
ta ce sai Anas ya ji dan tausayinta
ya kamashi.Ya zan iya barci Anas, bayan
kana fushi dani." Hakan kawai da
ta ce sai Anas ya ji dan tausayinta
ya kamashi. Don haka sai ya yi
karfin hali ya ce.
"Ki yi hakuri Mabaruka...wann
an
duk wani al'amari ne na rudin
shaidan." Ga mamakin Anas sai
ya ji Mabaruka ta yi wani irin
nannauyan ajiyar zuciya, sannan
sai ta juyo shi ta rungume shi ta
kankameshi ta ce.
"Ka yafe min Anas, ka kuma
manta da duk abubuwan da na
fada ma na bakaken maganganu,
wallahi masifar kaunarka da
kishinka ne suka sani..." Ta yi
shiru tana numfashi sama-sama
daga nan bata kara cewa komai
ba, a haka barci ya dauke ta
hannayenta kankame da jikin
Anas babban masoyinta a duniya.
Shi ko Anas, yadda ya ga rana
haka ya ga dare bai runtsa ba. Ga
dai Mabaruka rungume da shi
cikin shaukin bege, amma shi ji
yake yi kamar a rungume yake da
kaya.
Washe gari da safe suna karin
kumallo sai Anas ya fuskanci duk
da yake dai ba cikin fushi
Mabaruka ta tashi ba amma babu
alamar walwala sosai a fuskarta
haka nan da kyar ta kai abinci
sau biyu bakinta.
Ka bi ta a hankali dan samari
wannan gurguwa ita ce babbar
inuwar rayuwar ka
Wata zuciya ce ke baiwa Anas
Shawara
Wata zuciya ce ke baiwa Anas
shawara. Anas, ya mike tsam
daga inda ya ke ya koma kusa da
Mabaruka ya zauna, sannan ya
dauki yan siraran hannayenta ya
rikesu a tausashe ya sa alamun
damuwa na karya a fuskarsa,
sannan sai ya matsa da bakinsa
kusa da kunnen ta ya ce.
"Mabaruka...me ke damunki ne,
na ga duk kamar ba kya cikin
walwala, ko har yanzu fushin ki
ke yi dani? Ba na nemi afuwar ki
yafe min ba?" Mabaruka ta
langabe kai duk da yake dai bata
yi masa murmushi ba, to amma
fuskarta ta nuna alamun jin
dadin tarairayar da ya yi mata.
"Anas, wallahi zuciyata ce ke cikin
fargaba." Anas ya dubeta cikin
mamaki, sannan ya matse
hannayenta a cikin nasa ya ce.
"Fargabar me kuma, Mabaruka?
Kina da kudi da duk wani jin
dadin duniya da ki kebukata, tun
da dai Allah ya hore miki dukiya,
haka nan kuma kina da ni, ga ni
kusa da ke, to mene ne kuma na
fargaba?" Mabaruka ta dago
kanta ta dubi Anas cikin mamaki
ta ce a sanyaye.
"Ina da kai fa ka ce?" Anas ya
gyada kai ya ce. "Kwarai kuwa
kina da ni, ni ba mijinki ba ne?"
Mabaruka ta dan lumshe idanu
sannan sai ta bude su ta dubi
Anas.
"Ka ga ni kuwa fargabar da nake
yi gani nake yi kamar kwace min
kai za a yi, rabuwarmu ta zo." A
wannan dan takin lokacin da
take kalamin sai Anas ya ji
tausayinta ya sake kama shi a
karo na biyu. Tabbas ya san
batunta gaskiya ne, domin tuni
ma in dai batun soyayya ne an
riga an raba su, abinda ya rage
tsakaninsa da ita a yanzu shi ne
auren kaddara.
"Ka da ki ce haka Mabaruka, bai
kamata ba irin wadannan
kalamai marasa dadi suna fitowa
daga bakin ki." Anas ya dauke kai
gefe guda fuskarsa cikin
damuwa. Da ace za ka ga
fusakarsa a lokacin, mutum sai ya
rantse da Allah cewa abin da
yake fada har zuciyarsa haka nan
yake.
Mabaruka ta yi wata kwakkwarar
ajiyar zuciya ta dubi Anas.
"Ba ni lemo na sha." Anas ya mike
cikin sauri ya tsiyayo mata
tacaccan lemo cikin kofin
alfarma sannan ya zauna kusa
da ita kana ya dan janyota jikinsa
ya kara mata kofin a bakinta
Cikin farin ciki mara misaltuwa
Mabaruka ta fara shan lemon
kadan-kadan har sai da ta
shanye gaba daya. Abin ya baiwa
Anas mamaki domin bai taba
ganin ta yi haka ba. Amma ga
Mabaruka hakan da ta yi akwai
dalili mai karfi dalilin kuwa shi ne
rabon da Anas ya yi mata irin
wannan tarairaya tun daren
amarcinsu na farko
"Lemon ya ishe ki ko na karo
miki?" Anas ya tambayi Mabaruka
a tausashe Mabaruka ta dubeshi
da murmushi a karo na farko ta
girgiza kai
"Ya ishe ni." Ta dan yi shiru
sannan sai ta ce
"Ina ma ace kullum haka muke
da na fi kowa farin ciki a duniya"
Anas ya sunkuyar da kai gami da
murmushin yake shi kansa
kunyar hada ido yake yi da ita
domin a zuciyarsa cewa yake yi
ina ma wannan tarairayar da
yake yiwa Mabaruka ace Ummi
ce
Abin da Mabaruka ba ta sani ba
shi ne duk wannan tarairaya da
Anas ke yi mata kokari yake yi ya
sami hanyar da zai bi ya sulle ya
ziyarci Ummi
"Daga yanzu zan manne ma
kamar cingam duk inda za ni
muna tare." Kalaman Mabaruka
suka fado zuciyarsa Anas ya ji
gumi ya fara tsiyaya ta bayansa
duk kuwa da cwa wayewar gari
kenan kuma koda ma babu
sanyin iskar safiya akwai na
na'urar sanyaya daki.
"Tunanin me ka ke yi Anas?"
Mabaruka ta tambayeshi babu
zato babu tsammani ashe duk
abin da yake yi tana lura da
fuskarsa
Adaida lokacin ne to
wata dankareriyar karya ta darsu
a zuciyar Anas ya riga ya san ita
ce damar sa ta karshe ta samun
damar zuwa gurin Ummi dan
haka sai ya dubi Mabaruka ya ce
a tausashe.
"Kin san ina da abokai a cikin
gari da yawa wadanda rabon da
mu gana dasu tun kafin na
aureki shi yasa ki ka ga na shiga
cikin damuwa saboda ina
fargabar kada su ga kamar dan
na sami canjin rayuwa ne shi
yasa na watsar da su." Mabaruka
ta dan yi shiru na lokaci tana
kallon kofin da ke gabanta.
Zuciyar Anas ta fara harbawa da
karfi, yana jiran ya ji abin da za ta
ce, ya san idan ta ki amincewa
bashi da damar ganin Ummi,
haka nan kuma idan tare zasu
fita nan ma bashi da damar zuwa
gurin Ummi kenan.
Tsawon lokaci, sannan Mabaruka
ta dubeshi a tausashe ta ce cikin
murmushi.
"Kuma ka ki ka sanar dani tun
dadewa ko tsorona ka ke ji?" Ta
dan fashe da dariya. Jin haka shi
ya sa Anas ya washe baki har
kunne, zuciyarsa kamar ta fasa
kirjinsa saboda doki. Anas ya
dada rungumo Mabaruka.
"Ya ya zan ji tsoron matata?"
Wannan abu da ya fada shi ya
kara narkar wa da Mabaruka
zuciya, cikin sauri ta dubi Anas.
"Yaushe za ka je ku gaggaisa da
abokan naka?" Anas ya yi sauri
har zai ce yau, sai wata zuciya ta
ce dashi bi a hankali Anas,
wannan nannadaddiyar matar ta
fi ka wayewa.
"Duk lokacin da ki ka ce
Mabaruka haka za a yi, in ma kina
ganin za ki iya jure shiga
gargada da kwari da tudu irin na
unguwanninmu na yan Allah
baku mu samu sai mu tafi tare ki
rakani, domin ba na son rabuwa
da ke." Mabaruka ta dage kai
cikin murmushi, sannan ta
girgiza kai ta ce.
"A'a ni ba zan iya shiga gargada
ba, kana ganin ma so nake yi mu
tafi london hutu, amma rashin
doguwar tafiya a jirgi ya hanani"
Ta dan yi shiru.
Zuciyar Anas sai harbawa take yi
yana jiran ya ji abin da za ta ce.
"Anas." Ta kira sunansa a
sanyaye.
"Na'am, Mabaruka." Anas ya amsa
cikin kwararren murmushinsa na
mayaudara. Mabaruka ta ce.
"Idan ka tafi kamar karfe hudu
na yamma sai yaushe za ka
dawo?" Anas ya dan yi jim
sannan sai ya dube ta, ya ce.
"In ba dan abokan nawa suna da
yawa ba da sai in ce dake karfe
takwas ma ina gida, to amma me
yiwuwa na kai har wajen tara."
Ya dubeta ido da ido.
"Babu damuwa?" Mabaruka ta
kama hannunsa cikin farin ciki ta
gyada kai ta ce.
"Na kara ma awa daya, amma
kada ka wuce karfe goma, domin
ko ruwa ba zan sha ba sai ka zo
ka ba ni." Ta dan yi shiru tana
duban Anas, suka yiwa juna
murmushi.
"Idan za ka fita sai ka dauki
motata shudiyar lexus din nan,
kada abokan ka su raina min
kai!"
***
Sidi mai jaka ya dubeni babu ko
saurarawa ya ce.
A can gidan su Ummi, Abdulmalik
ya tsinci kansa cikin damuwar da
bai taba shiga irinta ba, domin
kwanansa guda cur) babu dare
ba rana, yana ta faman rubutu
ne.
Na dubi Sidi mai jaka cikin
mamaki.
"Rubutun me kuma?" Sidi mai
jaka ya ce.
"Saurareni da kyau ka ji dalili."
Ka ga Nas, tun ranar da Ummi ta
halarci liyafar gidan Mabaruka,
inda ta baiwa Anas yar
rubutacciyar wasika, tana
komawa gida sai ta wuce kai
tsaye zuwa dakin dan uwanta
Abdulmalik.
"Yaya Abdulmalik." Ta kira
sunansa tun daga kofar dakin
cikin doki da farin ciki.
Abdulmalik ya dago kai cikin
damuwa ya dubi kyakkyawar
fusakarta domin ya san labarin
da ta zo dashi ba zai taba faranta
masa ba. Daman tun da yamma
kafin ta tafi sai da ta sameshi ta
ce.
"Yaya Abdulamalik...M abaruka
ta
gayyace ni liyafa a gidanta."
Abdulmalik ya boye kunar
zuciyarsa ya dubeta da
murmushin da bai kai zuci ba.
"Ki ce yau kin sami damar ganin
mutumin na ki." Ummi ta
sunkuyar da kai.
"Uhm, shi da ma yake da mata, ni
na san ma ai zai yi wuya in zai
kulani." Abdulmalik ya ji zuciyarsa
kamar za ta fashe.
"Namiji ai na mace hudu ne."
Ummi ta gyada kai ta ce.
"Yanzu yaya Abdulmalik idan
mun hadu da shi ya ya zan yi?"
Abdulmalik ya dube ta ya ce.
"Duk da yake dai nima ba sanin
irin al'amuran soyayyar nan na yi
sosai ba, to amma ina ganin
tunda dai ke mace ce, ba za ki
rasa dabarar da za ki bi ba wajen
nuna masa cewa kina kaunarsa.
Sai dai kuma ki bi a hankali kada
babbar kawarki ta kamaki kina
kokarin sace mata miji." Suka
fashe da dariya, A haka suka
rabu.
Wannan shi ya sa lokacin da ta
dawo sai ta shiga dakin cikin
farin ciki ta zayyanawa
Abdulmalik duk abin da ya
gudana tsakaninta da Anas
"Yaya Abdul kana jin zai zo gobe
din kuwa?" Abdulmalik ya ji
murmushinsa ya fara daukewa
"Me zai hana, tun da dai idan aka
yi la'akari da abin da ki ka ce
shima ashe ya dade yana kaunar
ki" Ummi ta yi tsalle a tsakar
dakin ta dire cikin farin ciki ta ce.
"Wallahi Yaya Abdul ba ka ga
yadda na ruda shi ba jikinsa har
rawa yake yi" Abdulmalik ya cije
baki sannan ya dage kai. Ummi ta
daina tsallen da take yi ta dube
shi cikin damuwa.
"Yaya Abdul...ba ka da lafiya ne na
ga kana cije baki?" Abdulmalik ya
dubeta.
"Kaina ne ke sara min da ciwo
tun da safe" Ummi ta dube shi cikin.TSOHON ALKAWARI-14
.
"Kaina ne ke sara min da ciwo
tun da safe" Ummi ta dube shi
cikin damuwa.
"Bari in dauko ma magani"
Abdulmalik ya yi sauri ya girgiza
kai. Sannan ya yi mika.
"Ina tsammanin gajiya ce ta yi
min yawa, na san idan na sami
isasshen barci zan warware
zuwa safe" Ummi ta kura masa
idanu cikin damuwa na tsawon
lokaci.
"Bari to na tafi na barka ka huta,
domin zuwa na yi mu yi
bankwana, na kuma fada ma
cewa gobe ne da daddare muka
yi dashi zai zo...in dai zai zo din"
Ta mike tsaye. Abdulmalik ya dubi
kyakkyawar fuskarta.
"Ina taya ki fatan alheri Allah ya
sa ya zo din" Ummi ta yi
murmushi ta ce.
"Ameen Yaya Abdul, Allah ya karbi
addu'arka, wallahi yau da kyar
zan yi barci"
"Ai ba ke kadai ba" Abdulmalik ya
ce cikin zuciyarsa.
"Sai da safe Yaya Abdulmalik."
Ummi ta ce da faffadan
murmushi. Sannan sai ta fice
daga dakin.
Tana fita sai Abdulmalik ya kifa
kai akan cinyarsa, ga mamakinsa
sai ya ji wani zazzafan hawaye ya
fara kwaranya akan fuskarsa.
Yana nan zaune har karfe biyun
dare ta gota barci bai samu ba,
domin Abdulmalik ya riga ya san
cewa idan ya yi lako-lako yana ji
yana gani kwado zai leko daga
tafki ya yi masa kafa ya koma.
Tabbas idan ya yi wasa yana ji
yana gani Ummi, abin da ya fi
kauna fiye da komai a duniya za
ta sulale ta tsakanin yan yatsun
ikonsa. A lokacin ne to dabarar ta
fado zuciyar Abdulmalik. A kullum
zuciyarsa kan fada masa cewa
hanya daya ce kawai zai bi ya
magance wannan bala'i dake
kokarin afka masa. Ita ce ya kira
Ummi ya yi mata bayanin cewa
ita fa ba yar uwarsa ba ce ta jini,
ya kuma yi mata bayanin irin
yadda ta shige zuciyarsa. To
amma kashedin mahaifinsa shi
ke taka masa birki. Wata zuciyar
ta kan ce dashi me zai hana ka
sanar da mahaifiyarka halin da
ake ciki. Kunya ba za ta bari ba.
Ita ce amsar da Abdulmalik ke
fadawa zuciyar tasa.
Yana cikin hakan ne to ya kasa
barci, kawai sai dabara ta fado
masa
Abdulmalik ya dauko littafin
rubutu, mai shafi dari da sittin, ya
dauki biro ya fara rubuta labarin
tun farkon haduwarsa da
marigayi Saifullahi mahaifin
Ummi.
Sidi mai jaka ya dubeni da
murmushi "Nas, wannan labari
da Abdulmalik ya rubuta shi ne
sanadiyyar duk wani labari da
nake baka a halin yanzu."
"Kamar ya ya kenan, ban fahimce
ka ba Baba Sidi?" Na ce dashi.
Sidi mai jaka ya ce.
"Za ka fahimce ni ne, amma sai
nan gaba, kai dai rabu dani na
karasa labarin nan, na ga
magriba ta karaso, bana son
labarin nan ya kaimu har bayan
isha." ya dauki tubani ya jefa a
baki sannan ya ci gaba.
Washe gari tun kafin magariba
Ummi ta shiga wanka, ba ita ta
fito ba sai karfe shida da rabi.
Bayan ta yi sallah sai ta shiga
kwalliya, sai da ta shafe sa'a
guda tana kwalliya. Bayan ta
gama shafe-shafe da feshe-
feshen turare, sai ta wuce kai
tsaye zuwa dakin Abdulmalik
domin tun da safe suka yi dashi
cewa shi ne zai rakata hirar,
domin Ummi ta ce dashi ba ta
son a san alakar a cikin gida har
sai Anas ya zo a kalla sau uku.
"Har kin shirya kenan?"
Abdulmalik ya dubeta cikin
karaya. Ummi ta yi murmushi ta
dubeshi ta ce.
"Dubanni da kyau Yaya
Abdul...dan Allah na yi kyau? Idan
ban yi ba fada min na yi sauri na
sake shiga kada ya zo ban gama
shiryawa ba." Abdulmalik ya
kurawa kyakkyawar halittar
idanu. Ba wai yana kallon Ummi
bane don ya ba ta amsar
tambayar da ta yi masa ba, yana
kallonta ne da idanun bege da
tsananin shaukin ina ma ace shi
ya mallake zuciyar ta baki daya.
Kai wannan Anas da sa'a yake a
duniya. Abin da ya fi damun
Abdulmalik da kuma bashi
mamaki shi ne, wai shin shi
wannan Anas din kamar ya ya
yake, wane irin kyawun siffa ce
dashi, ko kuma Ilimi, ko kuma
dadin baki, da har wannan
kyakkyawar ta mace da tsananin
kaunarsa.
"Ya ya ka ganni Abdulmalik, na yi
kyau?" Zazzakar muryar Ummi ta
sake ratsa kunnen Abdulmalik. Ya
yi ajiyar zuciya ya ce.
"Kin yi kyau wallahi sosai ma
kuwa." Ummi ta yi tsalle cikin
murna ta ce.
"Har na ji dadi wallahi, tashi to
mu tafi." Abdulmalik ya mike
tsaye da kyar kamar ya hadiyi
tabarya sannan ya ce.
"Idan momi ta tambaye kin inda
za mu ki ce da ita kanti zamu je
siyayya."
***
Karfe takwas saura kwata na
yamma Anas ya shigo titin a cikin
katuwar motar shudiya kirar
Lexus yana tafe yana bin wakar
kidan turawa abinsa cikin farin
ciki da wannan rana. Tun da ya
auri Mabaruka bai taba samun
yanci irin na wannan rana ba. Ga
shi dai daman tun ranar da ya
aureta ya yi tsalle ya fice daga
kurkukun talauci ga motocin
hawa sai wacce ya zaba ga
sutura
Kusan kullum sai ya sa sabon
kaya na yamma daban na
safe daban. Ga aljihunsa a cike
taf da mikakkun takardun kudi
na kashewa, amma duk a banza
bai jin dadinsu ba don kome ba
kuwa sai dan wannan nacacciyar
gurguwa kamar yadda ya kirata,
wacce ke manne da shi kullum
kamar cingam. Dan haka a yanzu
da ya shigo cikin titin sai ya dubi
kujerar motar dake hannun
damansa cikin farin ciki domin
yau Allah ya raba shi da cingam,
lokaci guda kuma sai ya dubi
takardar da ke hannunsa na
dama, yayin da hannunsa na
hagun kuma yake sarrafa
matukin motar. Tabbas titin ne.
Anas ya ce cikin zuciyarsa,
sannan sai ya dada kallon
takardar kwatancen da Ummi ta
bashi, kana ya sake dago kai
yana nazarin jerin gidajen dake
gurin yana kokarin hangen mai
lamba ashirin daga cikin su. A
daidai lokacin ne to hasken fitilar
motarsa ta hasko masa abin da
ya sa yar autar hantar cikinsa
kadawa. Sannan sai ya fara musu
da zuciyarsa, kai wannan ba ita
ba ce, ya ce da kansa, sa'ar da ya
hangi kyakkyawar hallitar tsaye a
jikin katangar wani sabon gida
da ba a gama ginin sa ba. Ita da
wani saurayi ne kyakkyawa dogo
fari mai dogon saje da dogon
hanci mai doro daga tsakiya sai
ka ce hancin Larabawa. Anas ya ji
wani bakin kishi ya turnuke
zuciyarsa sa'ar da ya tabbata
lallai Ummi ce ba wata ba.
Abin da ya fi bata masa rai shi ne
saurayin da ke tsaye da ita shima
kyakkyawa ne, duk da yake dai
Anas bai ga alamun saurayin ya
zo da mota ba, to amma a
yanayinsa babu alamar talauci ko
kankani a jikinsa.
Sannu a hankali ya ja birki ya
tsaya a daf da su kana sai ya rage
hasken fitilar motar kadan ya
dada nazarin fuskar Ummi. Abin
ya bashi mamaki, domin ya lura
da cewa sun juyo inda yake, sun
zubawa motar idanu.
Sidi mai jaka ya yi shiru, kana ya
sheka wata uwar hamma ya
dubeni a yatsine ya ce.
"wato Nas, tubani na da dadi,
amma tsiyata da shi saurin sa
mutum barci, ga shi da sa cikin
mutum ya yi nauyi wata sa'ar sai
in ji kamar na hadiyi duwatsu."
"Dan ma ka saba cin sa." Na ce
dashi a kagauce domin na matsu
na ji yadda za a yi.
Sidi mai jaka ya dafa cikinsa da
busassun yan yatsunsa gami da
dan runtse, idanu sannan sai ya
dubeni ya ce.
"Sannu a hankali Nas, Anas ya
tuko motar zuwa inda suke ya
tsaya, lokaci guda kuma ya sauke
gilasan motar.
Cikin sauri Ummi ta nufo gindin
tagar motar, Abdulmalik na biye
da ita a baya, a lokaci guda kuma
ya ji wani matsanancin bakin ciki
ya lullube shi
Na shiga uku ya ce a cikin zuciyar
sa, Ashe Anas din shima
kyakkyawa ne."
"Anas..." Mabaruka ta kira
sunansa a kunya ce. "Ummi..."
Shima ya kira sunanta, sai dai har
yanzu zuciyarsa na bugawa
domin bai fahimci matsayin
saurayin dake biye da ita a baya
ba.
Ummi ta lura tun da ta zo gurin
idanun Anas akan Abdulmalik
suke don haka sai ta yi sauri ta
dube shi ta ce.
"Anas...ga Yayana Abdulmalik ba
ku gaisa ba." Sannan sai ta juya
ta dubi Abdulmalik da faffadan
murmushi ta ce.
"Yaya Abdul...ga Anas dina da
nake baka labari yau dai Allah ya
hada ku."
Cikin sauri gami da ajiyar zuciyar
jin dadi abin da ta ce, Anas ya
bude kofar motar ya fito, sannan
ya mikawa Abdulmalik hann.
"Yaya barka da yamma." Samarin
biyu suka cafke hannun juna,
kana suka dubi juna ido da ido,
Abdulmalik ya riga ya san
matsayin Anas a gurin Ummi, to
sai dai shi Anas bai san matsayin
Abdulmalik ba a gurin Ummi, duk
da yake dai ta ce dashi wai
Yayanta ne, akwai wani abu a
yanayin fuskar Abdulmalik da ya
jefa shakka cikin zuciyar Anas,
tabbas abin ya jefa shi cikin
kaduwa, domin irin yanayin da
yake gani a fuskar Abdulmalik, ya
sha ganinsa a fuskokin gomomin
samarin da ya sha kwace musu
yan mata a baya, to amma da
yake a yanzu bashi da wata
kwakkwarar hujja abar dogaro,
sai ya dubi Abdulmalik ya kuma
cewa.
"Ya ya ayyuka...ko kuma ya ya
karatu zan ce..."
"To, karatun dai...ai har yanzu
yayan naka dalibi ne." Abdulmalik
ya ce a karo na farko.
Aka sake yin shiru na yan
mintuna, Ummi na kallon Anas,
shi kuma na kallon Abdulmalik,
Ummi ce ta fara bata shirun.
"Yaya...Abdulma lik yau dai Allah
ya hadaku da Anas din da nake
baka labari."
Ba na fatan na kara haduwa da
shi. Abdulmalik ya ce cikin
zuciyarsa, sannan sai ya ce a fili.
"Malam...Anas, ta sha bani
labarin ka...ga shi sai yau Allah ya
hadamu." Ya dan yi shiru yana
duban Ummi kana sai ya ce.
"Daman zuwa na yi mu gaisa da
wanda kanwata ke so...ni zan
koma, gara na barku ku dan
zanta." Yana gama fadin haka sai
ya fara juyawa da baya.
Ummi ta dubeshi cikin mamaki-
mamaki kaduwa-kaduwa, domin
ta fahimci lallai yana cikin
damuwa. Na shiga uku. Ummi ta
ce a ranta.Ummi ta dubeshi cikin mamaki-
mamaki kaduwa-kaduwa, domin
ta fahimci lallai yana cikin
damuwa. Na shiga uku. Ummi ta
ce a ranta. Yaya Abdulmalik
jininsa bai hadu da na Anas ba.
Ta kuma fadi cikin zuciyarta,
sannan sai ta ce a fili.
"Yaya Abdulmalik...ta fiya za ka yi
tun yanzu?"
"Eh mana, ai gara na ba ku waje
ku yi hirar ku...na sa kannena a
gaba?" Ya fadi gami da jeho wani
takurarren murmushi. To sai dai
kuma ba Anas ba wanda tuni
daman ya gama fahimtar
Abdulmalik, hatta Ummi ta gane
cewa murmushin yake ne tabbas
ta san yayanta yana cikin
damuwa.
"Sai an jimanku..." Abdulmalik ya
kuma fada sannan cikin sauri ya
juya ya nufi gidan su.
Suka zuba masa idanu har sai da
ya shige cikin gidan ba a samu
wanda ya ce kala ba. Ummi ta yi
ajiyar zuciya sannan ta sunkuyar
da fuskarta akan kirjinta cikin yar
damuwa.
"Ya ku ke da shi?" Anas ya
tambayi Ummi yana dubanta
cikin zargi, wani bakin kishi na
kokarin tsaga masa zuciya.
"Yayana ne." Ummi ta bashi amsa
kai tsaye lokaci guda kuma ta
kalleshi ido da ido.
Anas ya dubi fuskarta na tsawon
lokaci yana nazari a cikin duhun
daren, abin ya bashi mamaki
domin a yadda ya ga tana
kallonsa da karya take yi ba za ta
taba iya hada idanu da shi ba. To
amma me ya sa kyakkyawan
saurayin mai hancin larabawa
yake irin wannan dabi'a haka
kamar wanda yake tsakiyar
kogin begen Ummi? Tambayar
kenan da Anas ya kasa amsawa
kansa.
"Kina nufin yayanki na uwa daya
uba daya ko kuwa dai kawai
yaya ne na yan uwa."
A wannan karon Ummi ce ta
dube shi da wani tattausan
murmushi ta ce.
"Oh...Anas kenan, lallai na fahimci
kai ma kana da kishi kamata." Ta
dan yi shiru lokaci guda kuma ta
dafa kofar motar dake bude da
hannunta na hagun ta dubi Anas
ta ce.
"Ka da ka bari kishi ya hana
mana jin dadin hirarmu ta farko
da kai."
Cikin sauri Anas ya sassauta
fuskarsa duk kuwa da cewa har
yanzu zuciyarsa tafasa take yi.
"Ki gafarce ni Ummi, masifar
sonki ce ta yi min yawa a cikin
zuciya, irin yadda nake kaunar ki
ko kuda ya sauka a kanki sai na
yi kishi da shi...to ballantana
kuma wannan kyakkyawa da ki
ka ce wai yayanki ne."
Ummi ta fashe da wata zazzakar
dariya, wacce sautinta ya sa
wasu yan gajerun samar dake
can gefe guda suna jiran fitowar
tasu budurwar suka juyo cikin
sauri suka kalli bangaren da su
Ummi da Anas suke.
"Kai Rabe...ka ji wata cika tana
dariya kamar ana busa sarewa."
"Ummi kenan." Daya saurayin ya
ce da abokin sa "Duk unguwar
nan babu cikar da ta kai
haduwar ta, ba ka ganin
gashinta daga nan har sheki
yakeyi kamar madubi, to don ma
da daddare ne da rana ce in ka
kalli gashin kanta sai ya dauke
maka idanu." "Allah mutumi
na...to ko barin wannan kucakar
zamu yi mu koma can mu gwada
sa'ar mu." Daya saurayin ne yake
fadawa Rabe haka.
"Rufawa kanka asiri." Rabe ya ce
da saurayin.
"Ummi me shegen girman kai
kamar ibilishiya tun da nake ban
taba ganinta da wani saurayi ba
sai yau...kuma in ban da
rigimarka ma ina kai ina Ummi?
Zoben dake danyatsanta guda
daya fa sai ya yi ma dinkin sallah
karama da sallah babba har sau
uku, kuma ya bar ka da ya canjin
kashewa...samar i yan hutu ma
masu kafafu hudu da iya kwalisa
ba ta sauraresu ba sai kai mai
katon kai da fadi kamar faranti."
"Ka ga bana son iskancin
banza...kai din kyau ne da kai ko
dan ba ka kallon madubi."
Saurayin ya ce da Rabe a kufule.
A daidai lokacin da Rabe ya fara
kokarin mayar da martani ne to,
kofar wani gida ta bude sannan
wata yar gajeriyar budurwa fara
ta fito cikin sauri ta nufi inda su
Rabe suke, ko da ta zo giftawa ta
kusan inda su Ummi suke, sai ta
tsaya turus ta Kalli Anas sama da
kasa sannan ta dauke kai ta dubi
Ummi ta ce.
"Yaya Ummi ina wuni."
"Lafiya kalau Hasiya...ya ya ki ke?"
"Lafiya nake." Shiru Hasiya ta dan
yi sannan sai ta sake duban
Fuskar Anas ta ce.
"Lalatacce mayaudari nan kuma
ka dawo?" Anas ya ji gabansa ya
fadi sannan zuciyarsa ta harzuka
ya dubi budurwar a kidime yana
kokarin tuna inda ya san ta.
"Ai ba za ka iya tunani ba
mayaudari tun da muna da yawa
a gaban ka." Tana gama fadin
haka sai ta juyo ta dubi Ummi ta
ce.
"Ki bi a hankali Yaya Ummi kada
ki sake dashi domin ba zan so
ace kin fada tarkon sa ba." Tana
gama fadin haka sai ta juya gami
da cewa.
"Bari in je in fatattaki wadancan
yan iskan...duk sahunsu guda da
wannan da yake gabanki, kar ki
yarda da shi mai kyan dan maciji
ne."*****
Share this
TSOHON ALKAWARI Page 41 to 50
Mabaruka ta yi ajiyar zuciya
sannan ta daga dan yatsa ta
nuna shi ta ce.
"Idan kuma kana ganin da
takura, to ina shawartarka da ka
rubuta min takardar sakina
yanzun nan, sai ka hada naka ya
naka ka bar min gidana, amma
ka tuna daga lokacin ka daina
karbar albashin naira dubu dari
biyu ka daina karbar kudin da
mahaifiyata ta ke baka duk wata
ka kuma daina hawa motocina
kai hatta kayan da ka saya da
kudin mahaifiyata sai ka ajiye
min kayana kuma sai ka yi
sallama da fita wata kasa a
duniya domin na san a rashin
zuciya da lalaci irin naka da
wahala in zaka yi arziki a duniya
mutumin da ko sallah baya iya
yi!"
Anas ya yi tsaye sororo cikin
tsananin kaduwar da bai taba
irinsa a duniya ba. Wani abu mai
kamar gare-gare ya fara yawo a
cikin kwakwalwarsa, nan da nan
ya ji cikinsa ya murda kamar zai
yi amai
Cikin sauri ya dubi Mabaruka baki
na rawa ya ce
"Ki yi hakuri Mabaruka abin duk
bai kai da zafin haka ba." Anas ya
dada dafe ciki sannan ya dubi
Mabaruka.
Mabaruka ta sake fashewa da
kuka. Anas ya ji ba zai iya
daurewa kukanta ba dan haka
sai ya ruga bandaki a guje yana
zuwa sai ya fara keta amai. Bayan
tsawon lokaci ya gama zubar da
abincin da ya ci a wurin liyafar.
Daga bandakin yana iya jiyo
shisshikar kukan Mabaruka
hakan shi ya tuna masa da
guntuwar takardar da Ummi ta
bashi cikin sauri ya laluba
aljihunsa ya dauko takardar
sannan sai ya warwareta ya fara
karantawa......
.
Anas Tun da nake a duniya ban taba
sanin mene ne so ba domin ni
ko zance ma bana fita wurin
samari
To amma tun ranar da na dora
idanuna a kanka sai na ji duk
duniya bani da abin so kamar ka.
Na yi matukar farin ciki sa'ar da
na dubi cikin kwayar idanunka,
sai na tabbata kai ma kana
kaunata. Haka nan na yi bakin
ciki da ya kasance wannan
gurguwa ta yi min shigar sauri ta
aureka.
Wannan shi ya sa na yi amfani da
damar wannan liyafa domin na
isar da sakon zuciyata zuwa
gareka Na gode, zan tsaya anan,
idan har abin da nake zargi
gaskiya ne, na san zaka so mu
hadu.
Ga adireshina nan a kasa, zan
jiraka gobe gida tun daga karfe
bakwai na dare har zuwa goma
na dare...sai na ganka mai...
Ummai.
Anas ya kankame takardar a
kirjinsa cikin farin ciki sannan
kuma cikin tsananin rudewa.
"Daga yanzu duk inda za ka
muna tare zan manne maka
kamar cingam!"
Ya tuna da kalaman Mabaruka.
"Ina jiranka gobe a gida..."
ya kuma tuna da kalaman Ummi
na karshe.
Anas ya lumshe idanunsa,
sannan ya kara takardar wasikar
akan hancinsa, ya shaki kamshin
turaren jikin Ummi dake jikin
wasikar, cikin jin dadi.
Daga can falo ya jiyo gurnanin
kukan Mabaruka. Anas ya yi sauri
ya toshe kunnensa domin baya
son kukan ya bata masa farin
cikin da yake, kai da zai yiwu ya
gwammace ya kwana cikin
bandakin rungume da wasikar
Ummi!
Sidi mai jaka ya yi shiru lokaci
guda. Na dubeshi cikin kaduwa
na ce bakina na rawa.
"To mana Baba Sidi...ci gaba
mana ya ka tsaya bayan labarin
ya gama daukar dadi."
Sidi mai Jaka ya dubi kwanon
tubanin dake gabansa cikin
takaici, sannan ya dubeni da
kyau ya ce.
"Kada ka bari dadin labari ya
dauke ka, saurara da kyau ka ji
kiran sallah ake yi. Tashi ka je ka
yi sallah idan an idar da sallar sai
mu sako wani sabon zaren
labarin." Yana gama fadin haka
sai ya mike tsaye ya dauki
tsohuwar butarsa ta karfe mai
kwarin tsiya ina tsammanin
butar tafi shekaru arba'in.
Na mike tsaye cikin sauri na ce.
"Baba Sidi dan Allah...da na gama
sallah fa zan dawo." Baba Sidi ya
dubeni da murmushi ya ce.
"Idan za ka dawo ka tabbata ka
dawo min da karin tubani, domin
idan babu shi, to babu labari Nas,
na riga na fada ma ni da tubani
tamkar tsohuwar mota ce da
man fetur.
Ya juya cikin sauri da butarsa a
hannu ya nufi waje zai yi alwala.
***
Ban sami damar dawowa wajen
Sidi mai jaka ba sai bayan sallar
La'asar sakamakon tsayawa da
na yi a sake dafa min sabon
tubani.
"Kai dan nema, bana son
shakiyancin banza, me kuma
zaka sake yi da tubani. Na dauka
dazu-dazun nan na yi ma cikin
kwano guda?" Kakata ce ke fadin
haka. Na dubeta da dariya.
"Kin ga in za ki dafa min ki dafa,
in kuma ba haka ba yanzun nan
in baki takardar saki akan
tubani." Ta fashe da dariya.
"Amma kuwa da ka yi abin kunya
wallahi ka saki matarka saboda
tubani?"
Daga karshe bayan mun sha
cacar baki kusan mintuna
bakwai, na shawo kanta da kyar,
ta sake cika min kwano da
tubani, a wannan karon har sun
fi wadancan girma domin ba a
son ranta ta yi su ba.
Na riski Baba Sidi mai jaka zaune
akan tsohuwar kujerar
katakonsa yana jan carbi, tun
kafin na gama yi masa sallama ya
dago kai ya dubi kwanon dake
hannuna cikin fara'a, kamar
karamin yaron da ya yi ido biyu
da alewa mai tsinke.
"Tsohon alkawari a karo na biyu,
lallai Nas ka kyauta min." Ya ce
sa'annan ya mika hannu ya karbe
kwanon daga hannuna tun ma
kafin na ajiye shi da kaina. Sidi
mai jaka bai jira komai ba, sai
kawai ya bude kwanon tubanin
ya fara juya tubanin da yan
yatsunsa bayan wani dan lokaci
ya tabbata da cewa sun juyu
yadda ya ke so don haka sai ya
can ku wani kato ya jefa cikin
bakinsa sannan ya dubeni.
"Nas, ina fatan dazu kana biye
dani a labarin da na fara baka."
Cikin sauri na gyada kaina.
"Kwarai kuwa ka tsaya inda Anas
ya shiga bandaki ya fara karanta
wasikar Ummi harma take cewa
dashi tana son ganinsa a daren
washe garin ranar
Sidi mai jaka ya gyada kai da
murmushi.
"Wani lokaci ina son mutum mai
saurin rike al'amura a cikin
kwakwalwa nan da nan ba tare
da mantuwa ba." Na dubeshi da
murmushi a karo na farko na ce.
"Ai kuwa in ka dauke labarai
babu abin da kwakwalwata ke
iya rikewa domin koda sunan
mutane in ba dadewa muka yi da
kai ba sai ka yi ta zuwa ina
kiranka da kai!" Sidi mai jaka ya
fashe da dariya sannan ya canko
wani katon tubani ya sha ya ji
jajur dashi ga girma kamar
dankali ya miko min.
"Ungo wannan Nas jefa a bakin
ka." Na yi saurin girgiza kai cikin
kaduwa.
"Allah kuwa karbi baka jiba
yadda tubanin nan ya yi dadi.."Ungo wannan Nas jefa a bakin
ka." Na yi saurin girgiza kai cikin
kaduwa.
"Allah kuwa karbi baka jiba
yadda tubanin nan ya yi dadi har
ya fi na dazu." Na dada girgiza
kai. Sidi mai jaka ya zunkuda
kafada, "Ka cuci kanka Nas, ni
duk abincin duniya ban ga abin
da zai zo a na biyun tubani ba a
gare ni. Ya sake tsikaro guda ya
jefa a bakin salatinsa sannan ya
juya ya dubeni idanunsa na
zubar hawaye kamar kuturu.
"Nas, zaren labarin dana fara
baka labari dazu ya kare iyakarsa
kenan." Na dubi Sidi mai jaka
cikin kaduwa.
"Haba Baba Sidi, kai fa ka ce dani
Ummi ta ce tana son ganinsa
washe garin ranar, kuma yanzu
ka ce dani wai zaren labarin ya
kare."
Sidi Mai Jaka ya yi murmushi
"Haba Nas kai fa yanzu mun
zama jiki sai dai ka fadawa wani
ni, sanin kanka ne idan na ce da
kai zaren labari ya kare to ya kare
din tabbas, dole ne sai na sako
sabo sannan na jona ma shi da
bakin wannan tsohon labarin da
na saka. Ya dan yi shiru, sannan
ya sunkuyar da kai.
Nas ina son ka dauki zuciyarka
cancak ka maishe da ita can wani
lokaci, kuma wani zamani mai
dan tsayi na a kalla shekaru
ashirin da biyar da suka gabata.
Na dubi Sidi mai Jaka cikin
mamaki bani da abin cewa dan
haka sai na gyada kai na ce dashi
"Na mayar."
Sidi Mai jaka ya ce "Yauwa Nas
haka nake so da kai."
*
*
Shekaru ashirin da biyar da suka
wuce wani dogon mutum fari
siriri buzu-buzu balarabe-balarabe, ya sauka a garin nan dauke
da yar tabarmarsa ta kaba akai
yana neman inda zai sauka. Ba
don komai ba kuwa sai don
lokacin da ya sauka a garin nan
cikin dare ne tare suke da
matarsa ita ma kusan irin kirar
su daya to sai dai kuma
kyakkyawa ce ta gani a fadawa
sarki. Wannan mutum dogo fari
siriri babu komai a cikinsa sai
hanji domin rabonsa da abinci
kwana biyu kenan haka ma
matarsa. Haka nan kuma yadda
cikinsa yake hakanan aljihunsa
yake, karaf babu ko karfanfana.
Mutanen guda biyu mace da
mijinta suka shigo birni, mijin na
gaba dauke da tabarmar kaba,
ita ko matar na biye dashi a baya
dauke da wasu tsummokarai da
ita kanta bata san amfaninsu ba.
Me yiwuwa dai tana dauke da
tsummokaran ne don cika
umarnin mijinta, babu mamaki
kuma sabo da yi ne wai gawa da
gatsine. To koma dai mene ne
wannan mutane dauke suke da
muguwar yunwa ga kishi ga
gajiya, ga babu tabbacin gurin
kwana, sannu a hankali suna
yawo cikin birni tsakanin manya-
manyan gine-gine na alfarma can
sai matar ta jefar da kayan
tsummokaran dake kanta ta
durkusa, ta rike ciki.
"Wallahi...mai gida ni na gaji." Ta
ce cikin wata irin bakuwar
Hausa.
Mutumin ya ajiye tabarmar keson
dake kansa sannan ya dubi
dankareren gidan dake gabansu
wanda ke ci reras da fitulu kamar
rana. Ya dubi matarsa cikin
tsananin tausayi.
"Ban ga laifinki ba HINDATU, ai kin
yi ma kokari." Ya dan yi shiru
idanunsa akan katon gidan dake
gabansu.
"Gashi wannan gidan ma kamar
babu kowa a cikinsa, da sai in
karasa na barato mana dan abin
da zamu sa a bakinmu."
Matarsa Hindatu ba ta ce komai
ba, maimakon hakan ma sai ta
kwanta a kasa ta dora kanta
akan kullin tsummokaran ta
kurawa sararin subhanahu
idanu. Hankalin mijinta ya dada
tashi, ya san cewa dadin ta
yunwa ce kawai, duk wannan
mai sauki ne, domin sun riga sun
saba da jin yunwa, tun sa'ar da
yaki ya barke tsakanin buzaye
yan tawaye da gwamnatin
kasarsu basu kara samun damar
wani jin dadin rayuwa ba. Koda
yake can ma ba wani cikin
kwakkwaran jin dadi suke yi ba,
to amma akalla dai kafin
barkewar yaki suna da
kwanciyar hankali wannan da
sauran matsalalo halayyar yaki
marasa adadi su suka sa
wadannan mutane sabo da duk
wata irin wahala, a cikinsu har
da ma jimirin yunwa. Dan haka
abin da ya sa hankalin mijin
matar nan Hindatu ya tashi shi
ne, ya san tana da juna biyu,
akalla zai kai wata uku. Tun sa'ar
da ya ki ya barke suka fita gudun
hijira mutumin ya fitar da ran
cewa matarsa zata sami damar
haife cikin, kullum kwanan
duniya cikin zullumi yake, yana
sauraron zubewar cikin, amma
cikin ikon rabbana har zuwa
wannan lokaci matar bata ko
taba ciwon kai ba ballantana a yi
zancen zubewar cikin sai yanzu
da ta fadi a gabansa ta ce dashi
ta gaji ga kuma muguwar
yunwa.
Dogon mutumin ya mike tsaye
sannan ya sake duban matarsa
cikin damuwa kana ya dubi
sararin samaniya sai ya ga tuni
ya hade da gajimare an kuma
fara rugugin aradu haka nan
Walkiya sai haskawa take yi wal-
wal kamar tana daukar hotonsu.
"Sannu Hindatu dan jirani kadan
na karasa kofar gidan can me
yiwuwa idan nayi sa'a ko
masamu wani ya taimakomu da
abin da za mu sa a bakinmu."
Hindatu ta runtse idanu sannan
ta budesu cikin karfin hali ta dubi
mai gidanta ta ce.
"Kada ka damu je ka gani, Allah
baka sa'a." Cikin sauri na ban
mamaki idan aka yi la'akari da
rama da kuma bakar wahalar
dake jikinsa mutumin ya nufi
kofar gidan kai tsaye kirjinsa na
harbawa.
Har sa'ar da ya kai ga
tangamemiyar kofar me kamar
kofar gari bai ga motsin ko da
halitta daya ba a duk tsawon
kwararo sai wasu karnuka guda
uku dake can karshen kwararon
suna ta faman haushin babu
gaira babu dalilin kamar sun yi
ido biyu da aljan.
Mutumin ya matsa kusa da kofar
ya tsaya cikin shakka, domin bai
san abin da ya kamata ya yi ba
Shin buga kofar zai yi ko kuwa
sallama zai yi. To idan ma ya yi
sallama wa zai ji shi? Ya tambayi
kansa. Yana nan tsaye cikinsa na
kugi kamar tukunyar talge, sai ya
ji kamar dagacan sashen hagu
na katuwar kofar ana tabata.
Mutumin ya yi sauri ya dan ja da
baya lokaci guda kuma ya dubi
bangaren hagu na jikin kofar. A
lokacin ne to ya fahimci ashe a
jikin katuwar kofar akwai wata
yar karamar kofa daga hannun
hagu wacce akalla mutum guda
zai iya wucewa ta ciki, wannan
yar karamar kofa ita ce ake
motsawa ba a ko dade ba sai ta
bude. Wani dan matashin yaro
fari kyakkyawa ma'abocin
kyawun sutura da cikar hallita ya
fito daga cikin gidan sannan ya
kurawa dogon mutumin idanu
baya ko kiftawa. Dogon mutumin
ya dubi yaron, sai ya rasa ma me
zai ce masa. Domin da ido
mutum na iya tsammanin dan
saurayin yaron ya kai shekara
goma sha uku ko sha hudu, to
amma a gaskiyar al'amari yaron
shekarunsa goma cif-cif da
kwana biyu, domin shekaran
jiya-jiya din nan aka yi bikin cikar
shekarunsa goma da haihuwa.
"Sannu Malam." Yaron ya ce da
mutumin cikin ladabi.
"Yauwa dana, sannunka dai." Ya
dan yi shiru sannan sai ya dubi
yaron ya ce.
"Da Allah dan samari idan da hali
taimakon abinci nake nema duk
kankantarsa, wallahi mu baki ne
bamu san kowa ba, ga matata
can kwance akan titi, yunwa ce
ta hanata tafiya" Yaron ya dubi
mutumin na dan tsawon lokaci, a
zuciyarsa yana tunanin ja da
baya a guje ya rufe gida domin
me yiwuwa mutumin nan dake
tsaye a gabansa mahaukacine,
dubi fa kayan dake jikinsa, koda
yake dai irin kayan da yake gani
ne jikin buzayen dake gadin
gidansu, to amma shi wannan
nasa sun ji jiki da yawa.
"Ka ce abinci kake so?" Yaron ya
tambaya.
Mutumin ya gyada masa kai
sannan ya dada da cewa.
"Ko da kadan ne wanda zan
bawa matata da Allah a taimaka
min, so nake na bata ta dan ci
mu yi gaba" Yaron ya daga kai ya
dubi hadarin da ya mamaye
sararin samaniya, sannan sai ya
dubi mutumin cikin tausayi ya ce.
"Ina zuwa" Cikin sauri ya shiga
cikin gida. Ba a dade ba sai ga
yaron tare da masu gadin
gidansu mutum uku biyu buzaye
daya tsohon soja, hakanan kuma
da wani mutum dogo kakkaura
wankan tarwada sanye da
babbar riga amma kansa babu
hula, ko shakka babu shi ne ya yi
kama da mamalakin dankareren
gida.
Dogon mutumin dake tsaye, ya
dubi mutumin a tsorace, domin
ya tabbata kashinsa ya bushe a
tsammaninsa kamashi zasu yi a
matsayin barawo ko mahaukaci.
Tun kafin su karaso gurin
mutumin sai ya ji maigidan nan
na cewa sauran masu gadin.
"Wai wani mutum ne da matarsa
anan kofar gidan suke neman
taimakon abinci a gurin
Abdulmalik shi ne na fito da
kaina gara mu je mu gani ko
wane irin mutum ne, duniyar nan
yanzu ba abin yarda ba ce."
Dogon mutumin ya zube gaban
mai gidan ya gaida shi. Maigidan
ya dubi dogon mutumin ya ce.
"Malam kaine me neman
taimakon abinci?"
Mutumin ya gyada kai ya ce.
"Ni ne ranka ya dade, wallahi
zuwan mu kenan garin nan ni da
matata, ga ta can a bayan yunwa
ce ta kayar da ita ta kasa tafiya
kuma tana da ciki wata uku,
wannan shi ya takurani nake
neman wannan abinci kafin Allah
ya bani masauki, domin mu ba
mutanen wannan kasa ba ne
yaki ne ya koromu gudun hijira."
Kalamin dogon mutumin ya karya
zuciyar maigidan, nan da nan sai
ya ji tausayinsa ya kamashi,
musamman ma daya ji tare suke
da matarsa kuma tana da ciki
wata uku. Wannan shi ya fi tayar
masa da hankali. Domin yau
shekarunsa ashirin da yin aure,
tun daya auro matarsa Hajiya
Sa'adatu basu sami damar
haihuwa ba sai bayan shekaru
goma suka haifi Abdulmalik, tun
daga kansa kuwa basu kara
samun koda batan wata ba har
zuwa wannan lokaci.
"Yanzu ina matar taka take?"
Dogon mutumin ya nuna can
bayansa ya ce.
"Ga ta can yallabai" Mai gidan ya
dubi masu gadinsa guda uku ya
ce.
"Ku je dashi ku taho da matar, ku
sameni a tsakar gida." Sannan sai
ya kama hannun Abdulmalik suka
shige farfajiyar gidan
ma'abociyar shuke-shuken da
kamshin furanni.
Ba'a dade ba, masu gadin suka
shigo farfajiyar gida tare da.Ba'a dade ba, masu gadin suka
shigo farfajiyar gida tare da
dogon mutumin da kuma
matarsa Hindatu. Suna isowa sai
mutumin da matar tasa suka
zube gaban alhaji suka sake
gaidashi. Mai gidan ya dubi
tsohon sojan nan mai gadinsa ya
ce.
"A kaisu dakin nan na kusa da
injin bada wuta su kwana a ciki
yanzu zan sa a kawo musu
abinci ina son kuma a lura dasu
kaji ko?" Tsohon sojan ya rusuna
ya ce
"An gama alhaji" Sannan sai ya
dubi dogon mutumin da matarsa
ya ce.
"Ku biyoni mu tafi." Ramammun
mutanen guda biyu kyawawa
suka bishi a baya, gami da
godiya.
Mai gidan ya bisu da kallo cikin
tausayi yana tunanin abin da ya
kamata ya yi domin taimakonsu.
"Wallahi baba mutanen abin
tausayi ne dubi matarsa da kyar
take tafiya" Mutumin ya dubi
dansa Abdulmalik ya gyada kai,
bai ce komai ba.
Sidi mai Jaka ya yi shiru sannan
ya dubeni ya ce.
"Nas, ina fatan kana biye dani
akan wannan dogon zaren
labari" Na gyada kai cikin
kaguwa na ce.
"Ina biye da kai baba Sidi, sai dai
kuma ni wannan labarin duk
jinsa na ke yi kamar sabo daman
har yanzu ban ji alakarsa da
wannan ba"
Sidi Mai Jaka ya dubeni da
murmushi sannan ya dubi
kwanon tubanin dake gabansa
ya cafka daya ya jefa abakinsa ya
dube ni.
"Nas kenan, amma dai yanzu ai
ka isa ka baiwa wani labari,
sanin kanka ne in har na sako
sabon zaren labari to ko shakka
babu in Allah ya yarda sai na
hade shi da wancan na baya, shi
yasa ba ka gane alakarsu ba, to
amma ka jira sannu a hankali
lokacin da zaren labarin zai rikida
ya koma kan wancan su hade da
juna ba zama ka sani ba"
"Haka ne, ina to sauraronka" Sidi
Mai Jaka ya dada jefa tubani daya
a baki ya ce "Dadina da kai kenan
Nas, iya sauraron labari, ba ka
gajiya da saurare" Na fashe da
yar dariya. To ai labarin naka ne
wani sa'in dole ma a saurareka
domin sai kayi kamar kayi gabas
da mutum sai an jima can sai a
sameka a yamma" Baba Sidi ya
fashe da dariya sannan ya dube
ni ya ci gaba da cewa.
"Nas, tun daga wannan rana da
mai gidan ya sauki dogon
mutumin nan da matarsa basu
kara barin gidan ba, har sai da ta
Allah ta kasance a kansu." Na
dago kaina na dubi Sidi mai jaka
cikin sauri na ce dashi.
"Kada kace na tari numfashinka
baba Sidi, ina da tambaya."
Sidi mai jaka ya dubeni cikin
mamaki.
"Me kake son tambaya." Na
dubeshi na ce.
"Ni tun da ka fara bada sabon
zaren labarin, kake ta ambaton
wani dogon mutum, da kuma
mai gidan daya sauke su, gashi
dai ka siffanta su, kace sunan
matarsa Hindatu, sunan dan mai
gidan daya sauke su Abdulmalik,
to shi dogom mutumin da mai
gidan ya ya sunansu?" Baba Sidi
ya dan yi shiru na dan lokaci
sannan sai ya dubeni da
murmushi ya ce.
"Wani lokacin mutane kan bani
mamaki, wai idan kana basu
labari dole ne sai ka fadi sunan
mutunen," Sidi mai jaka ya danyi
shiru sannan sai ya ce.
"Sunan dogon mutumin
Saifullahi, mai gidan kuma Alhaji
Kabiru. Nas ina fatan ka gamsu."
Na gyada kai na ce "Eh, ci gaba"
Sidi mai jaka ya dora daga inda
ya tsaya.
Washegarin ranar da Alhaji Kabir
ya sauki bakin, tayi mutukar
faran tawa bakin rai, domin yasa
masu gadin gidansa sun
bincikesu daga karshe suka gane
cewa lallai da gaske yan gudun
hijira ne kuma ya ki ne ya koro
su. Dan haka sai Alhaji Kabiru ya
ce a ci gaba da basu abinci, daga
nan har zuwa ranar da matar
Saifullahi zata haihu. To amma
duk da haka sai da alhaji Kabir ya
gana da masu gadinsa a sirrance
ya ce suna fa kula da bakin nan,
domin mutum na yau ba abin
yarda bane domin sai ka dauko
mutum daga rana ka sashi a
inuwa, shi ko ya tura ka cikin
wuta
Sidi mai jaka ya dubeni cikin
mamaki
A haka Saifullahi da matarsa
Hindatu suka zauna cikin farin
ciki, a karshen watan da suka
sauka a gidan ne to wasu
sangartattun yan fashi suka
ziyarci gidan alhaji Kabir
A ranar da yan fashin suka zo tun
karfe hudu na yamma ake tafka
ruwan sama haka nan yan
fashin basu tashi zuwa ba sai
ana daf da fara sallar asuba
lokacin suka karaso ko shakka
babu sun rigaya sun gama sanin
abin da za su yi dan haka cikin
ruwan sanyi barayin su goma
sha tara kamar tururuwa suka
cafke masu gadin buzaye cikin
ruwan sanyi yayin da tsohon
sojan nan ya yi kokarin kawo
musu turjiya hakan shi yasa cikin
ruwan sanyi suka danne shi suka
yi masa yankan rago kai tsaye
kuma suka wuce inda Alhaji
Kabir yake shi da iyalinsa.
"A can bangaren hadiman gidan
Saifullahi ya ji idanunsa sun bude
ya farka daga nannauyan barci
sannan sai ya ji jikinsa ya fara
rawa babu gaira babu dalili cikin
sauri ya taba matarsa Hindatu.
.
Matar ta mike zaune cikin firigice,
ta dube shi a tsorace da yake har
yanzu razanar ya ki bata gama
saketa ba.
"Me...nene?" Saifullahi ya dubi
matarsa ya ce.
"Ji na yi haka kawai idanuna sun
bude, duk yadda aka yi wani
mugun abu ne ke shirin faruwa a
gidan nan." Ya dan yi shiru yana
saurare kamar zakara.
"Dauko min damarar layuna da
guraye na."
Cikin sauri na mamaki ga macen
dake da ciki wata uku da kuma
magagin barci jikinta, ta mike ta
nufi inda tsummokaransu suke
ta mika masa jakar gurayen. Cikin
yan mintuna Saifullahi ya daura
gurayen, sannan ya mike tsaye.
"Bari in je in gani." Hindatu ta
dubeshi da murmushin karfafa
gwiwa ta ce.
"To, Allah kiyaye bacin rana Allah
bada sa'a."
Saifullahi ya juya cikin sauri ya
fice daga dan dakin.
Hindatu ta bishi da kallo, ko kusa
ko alama bata fargabar komai,
domin ta yi imani da cewa in dai
ba karfin kaddarar karar kwana
ba, babu abin da zai sami
maigidanta, ta riga ta san sirrin
dake tattare da gurayen, ta ga
yadda suka ratsa ta tsakanin
sojojin yan adawa akan iyakar
kasarsu, suka tsallako ba a gansu
ba, ba a kuma samesu koda da
alburushin bindiga guda daya ba
duk kuwa da irin barin wutar da
ake yi.
Saifullahi ya matsa wata katuwar
laya mai kamar makami da ke
kwibinsa na hannun dama.
Sannan ya nufi cikin gidan, ya
tabbata a lokacin in ba Allah ba,
ko ifiritu bai isa ya ganshi ba.
Saifullahi ya hangi barayin daya
bayan daya har su goma sha tara
sun mammakale a loko-loko
guda biyar daga cikinsu tsaye a
kofar babban dakin shakatawar
gidam. Saifullahi ya zaro wani
bakin guru daga kugunsa wani
dogo mai kamar maciji ya zagaya
barayin dashi har sau biyu, nan
da nan barayin suka sankare a
gurin basa ko motsi kamar
itatuwa. Saifullahi ya barsu a
gurin, sannan ya ringa bin
barayin daya bayan daya yana
zagaya su da gurun ba tare da
sun ganshi ba har sai da ya
kamar dasu baki daya, sannan
sai ya nufi kofar falon, ya zagaye
barayin ya kwankwasa kofar
dakin shakatawar a hankali.
Shiru-shiru bai ji motsin komai
ba, Saifullahi ya dada kwankwasa
kofar da karfi, har sau goma.
Tswon lokaci, sai ya ji kamar
motsi an nufo kofar a hankali
kamar a tsorace.
"Alhaji ni ne...Sanifullah i."
Saifullahi ya ce cikin tattausar
muruya.
"Saifullahi...l afiya ina masu
gadin?" Saifullahi ya tausasa
murya ya ce.
"Yan fashi ne suka kama su, sun
kuma kashe tsohon soja." Alhaji
Kabir ya rike numfashi a tsorace.
"Yanzu ina barayin?" Ya tambaya
a tsorace.
"Gasu anan waje duk na kama
maka su."
"Kai kadai Saifullah?"
"Kwarai kuwa ai ikon Allah ya fi
da haka."
Tsawon lokaci, bai fito ba, can sai
ya leko a hankali a tsorace
sannan sai ya ja da baya saboda
mutanen da ya gani guda biyar
duk a sankare kamar itatuwa.
"Kada ka ji tsoro Alhaji, kana iya
fitowa, babu abin da zasu iya har
sai idan na ga dama da ikon
Allah, sannan zasu yi motsi."
Alhaji Kabir ya dubi Saifullahi
cikin kaduwa.
"Jirani to ina zuwa, bari na
bugawa yan sanda waya."
Mintuna goma bayan haka gidan
ya cika da jami'an tsoro. An kame
barayin gaba dayansu, tun daga
wannan rana sai Saifullahi ya
sami cikakken yanci, Alhaji Kabir
ya gama yarda dashi, ya kuma
bashi shugabancin masu gadin
gidansa.
Sannu a hankali watanni suka
shude, har cikin Hindatu matar
Saifullahi ya isa haihuwa, ran nan
da safe sai ta fara nakuda, Alhaji
Kabir da kansa ya bada mota a
kaita asibiti. Kusan sa'o'i biyu
suna jiran labarin haihuwa, a
cikin masu jiran akwai Alhaji
Kabir, matarsa Hajiya Sa'adatu,
Abdulmalik da kuma Saifullahi.
A cikin wannan sa'ar ne
abubuwa biyu suka faru, farin
ciki da bakin ciki, domin Hindatu
ta haifi wata kyakkyawar
budurwa, mai kyawu na ban
mamaki, ita kuwa Hindatu Allah
ya yi mata cikawa.
Tun daga wannan rana Saifullahi
bai sake samun lafiya ba. A ranar
da za a radawa jaririyar suna,
jikin mahaifinta Saifullahi ya
matsa, tun da sassafe ya sa masu
gadi suka roki Alhaji da ya zo
yana son ganawa da shi domin
ba zai iya zuwa da kansa ba.
Alhaji kabir ya zo dakin mai
gadin cikin gaggawa, Saifullahi
ya dago kansa da kyar ya dubeshi ya ce bakinsa na rawa "Alhaji, jikina ya tsananta min,
haka nan kuma bana jin zan
warke daga wannan rashin lafiya
tawa."
Alhaji Kabir ya matsa kusa da
mutumin cikin tausayawa ya ce.
"Ka da ka ce haka Saifullahi, ai ita
cuta ba mutuwa ba ce" Saifullahi
ya girgiza kai ya ce.
"Ba zan rayu ba Alhaji, domin na
ji a jikina, Shi yasa na kiraka
domin na baka abu daya da na
mallaka a duniya wanda da shi
ne kadai zan iya saka maka abin
da ka yi min a duniya" Ya dan yi
shiru yana mayar da numfashi.
"Alhaji a duniya bani da wanda
ya fi ka, na dauke ka a matsayin
dan uwa, amini, ka mutunta ni,
ka taimakeni a lokacin da nake
matukar bukatar taimako"
Saifullahi ya tura hannunsa cikin
wasu tsummokara dake gefensa
ya dauko wata tsohuwar jaka ta
bakin yadi ya mikawa Alhaji
Kabir.
"Wannan shi ne kyautar da zan yi
maka ta musamman, guru ne, da
layu guda uku. Sirri ne na tsarin
kai da mahassada, da su ne Allah
ya taimakeni na kama barayin
nan" Ya dan yi shiru sannan ya ci
gaba.
"Ga Yata nan jaririya, na baka ita,
ka taimake ni dan Allah ka rike
min ita, idan an jima in za a sa
mata suna, ka sa mata suna Nana
firdausi, domin sunan mahaifiya
ta ne" Ya fara tari, sannan sai ya
yi karfin hali ya dago ya dubi
Alhaji Kabir idanunsa na zubar da
kwalla.
"Alhaji wannan ita ce alfarmar da
nake nema, za ka yi min..?" Cikin
sauri Alhaji Kabir ya amsa masa.
"Na amince Saifullahi, in Allah ya
yarda zan rike ta kamar yar da na
haifa a cikina kuma ina fatan ma
Allah ya baka lafiya"
Washe gari da aka yi sunan
Firdausi mahaifinta Saifullahi ya
bar duniya, a lokacin kwananta
takwas kawai a duniya.
Bayan an binne Saifullahi, sai
Hajiya Sa'adaru ta fito dauke da
kyakkyawar jaririyar ta sami
maigidanta zaune a falo shi da
dansa Abdulmalik, ta zauna kusa
da maigidanta, sannan ta kurawa
jaririyar idanu ta ce.
"Oh, Allah mai yadda ya so, Allah
gwanin iya halitta, ka dubi
wannan kyakkyawar halitta, kai
wallahi Alhaji ina bala'in son
jaririyar nan, ba don komai ba.
Sai don irin maraicinta, da kuma
kasancewar sunan mahaifiyata
ne nima aka sa mata"
Alhaji Kabir ya dubi matarsa ya
ce.
"Ki riketa da kyau cikin aminci da
kulawa kamar yadda za ki rike
danki Abdulmalik." Hajiya
Sa'adatu ta rungume jaririyar ta
dubi maigidanta, sannan sai ta
dubi kyakkyawar fuskar jaririyar
ta ce.
"Daga yau kin zama yata, Allah ya
raya ki UMMI na"
Tun daga wannan rana ne sunan
Ummi ya bi wannan jaririya.
Sidi mai jaka ya juyo da
murmushi ya dubeni.
Ni kuma na dubeshi cikin bazata.
"Baba Sidi, kana nufin ka ce min
wannan jaririyar ita ce Ummi din
da Anas ya kamu da ciwon
Kauna?" Sidi Mai Jaka ya fashe da
dariya ya ce.
"Nas kenan, ai daman sai da na
fada ma sai na baka mamaki,
sannu a hankali zan dawo da kai
na jone ma bakin zaren labarin,
gashi kuwa tun ma kafin na jone
shi din har ka fara ganin alakarsu
da wancen tsohon zaren labarin
da muka saka" Na dubi Sidi mai
jaka cikin kaduwa.
"Wai Baba Sidi kana nufin ka ce
ita wannan kyakkyawar Ummi
din iyayenta ba ma wata tsiya ba
ce a garin nan" Sidi mai jaka ya
gyada kai ya ce.
"Kwarai kuwa Nas, dan ma ka
tari numfashina, domin har
yanzu zaren labarin bai kare ba,
bari in gama saka ma shi, idan na
gama zaka fahimci rudanin dake
cikin wannan labari" Na gyara
zama na dubi Sidi mai jaka cikin
doki na ce "Ci gaba, ina saurare"
Sidi mai jaka ya jefa tubani daya
a baki ya ci gaba.****
Sannu a hankali Nas Ummi ta
fara girma kullum ta Allah
kyawunta karuwa yake yi. Ba
mutumin dake ganinta a waje ba
lokaci-lokaci hatta Alhaji Kabir da
matarsa Sa'adatu dake ganinta
kullum suna mamakin kyawu irin
na Ummi
Wani abin ban mamaki shi ne
tun ranar da aka haifi Ummi
kullum a hannun Abdulmalik take
wuni yana yi mata wasa. Gashi
dai shi ba mace ba amma kullum
yana makale da jaririyar dan
haka har sa'ar da Ummi ta kai
shekaru goma a duniya, duk inda
zasu tare suke da Abdulmalik a
lokacin nan shi yana da shekaru
ashirin a duniya Amma duk da
haka kusan tsayin sa daya da
Ummi
Wani sa'in sai Abdulmalik ya
dauki Ummi a mota su yi ta yawo
kantuna-kantuna inda ake sayar
da kayan lashe-lashe da
makulashe idan sun je sai
Abdulmalik ya juyo ya kalli Ummi
cikin fara'a a tausashe ya ce
"Ummi, dauki duk abin da ki ke
so" Cikin farin ciki da kauna irin
ta dan uwa sai ta dubeshi ta ce
"Abdulmalik kana shagwaba ni!"
A duk lokacin da ta ce haka sai
Abdulmalik ya ji zuciyarsa ta dada
narkewa da begenta domin tun
ranar da aka haifi Ummi
Abdulmalik ya fara sonta tun ma
bai san mene ne kauna ba. Don
haka sannu a hankali shekaru na
shudewa har wannan son ya
juye zuwa kauna. To sai dai
kuma abin da Abdulmalik ya kasa
fahimta shi ne a duk tsawon
zamanin nan Ummi a matsayin
dan uwanta na jini ta daukeshi
domin bata taba sanin cewa ba
uwarsu daya ba ubansu daya ba.
Abdulmalik ya riga ya fi kowa
sanin cewa Ummi ba yar uwarsa
ba ce ta jini Domin shi ne ma ya
yi sanadiyyar haihuwarta a
gidan, to amma daidai da rana
daya bai taba nuna mata alamu
ba
A bangaren iyayen Abdulmalik
kuwa sun dade suna kallon irin
alakar mai karfi dake kulluwa
tsakanin yaran guda biyu, koda
yake ga zuciyar Alhaji Kabir bai
taba daukar alakar yaran a bakin
komai ba face kawai sabo da
kuma yan uwantaka.
.
To amma ranar wata laraba da
yamma sai matarsa Sa'adatu ta
dubeshi ta ce.
"Alhaji, wai kuwa kana lura da
al'amarin yaran nan?" Maigidanta
Kabir ya dubeta cikin mamaki.
"Kamar ya ya ina lura dasu?
Wannan ai dole ne domin kuwa
yayana ne." Sa'adatu ta dubeshi
cikin yar damuwa ta ce.
"Ba abin da nake nufi kenan ba."
"To me ki ke nufi?" Sa'adatu ta
gyara zama ta ce.
"Wato ni gani na ke yi kamar
Abdulmalik kaunarta ya ke yi."
Alhaji Kabir ya dubeta baki bude
cikin mamaki ya ce.
"Yau ga ikon Allah, to daman
mutum ba dole ne ya kaunaci
dan uwansa ba." Sa'adatu ta
girgiza kai.
"Abin ya wuce da haka ina
tsammanin begenta ya ke yi."
Alhaji Kabir ya kura wa matarsa
idanu na tsawon lokaci, sannan
sai ya yi kasa-kasa da murya ya
ce.
"Kada fa ki manta cewa, har
yanzun nan Ummi ba ta san
cewa ba mune iyayenta ba."
Sa'adatu ta yi murmushi.
"Idan ita ba ta sani ba, ai shi
Abdulmalik ya san ba yar uwarsa
ba ce ta jini. Kuma abin da ya sa
ka ji na fada ma haka shi ne,
yanzu da ka leka cikin dakinsa za
ka ga duk ya zagaye shi da
hotunan Ummi, kowannensu ya
rubuta (My love)
Alhaji Kabir ya
dada duban matarsa na tsawon
lokaci, akwai alamun tunani a
fuskarsa, can sai ya yi ajiyar
zuciya ya ce.
"To, sai mu bar wa Allah komai,
ya yi ikonsa, Allah zaba musu
abin da ya fi alkairi."