Wani matsiyacin tsaki taja me karfi ganin sunan Zeey kan screen din wayar, tuni ranta yay wani mugun 'baci taji zuciyarta na wani irin tafarfasa tamkar zata tsaga kirjinta ta fito waje haka takeji, hannunta na karkarwa ta datse kiran tana kara jan wani tsaki!! idanunta har sun kada sunyi jawur ranta bai ta'ba 'baci ba irin yau! Wai me matar nan take nufi ne? Jin tana ta jan tsaki ya sanya ya bud'e fuskarshi yana kallonta,tana rike da wayar tashi a hannunta sai dubawa takeyi.
Shuru yay mata dan shima jikinshi ya bashi Zeey din ce dama dai-dai wannan lokacin take kiran wayarsa shi abin ma mamaki yake bashi sam bata da zuciya ko kadan yana jin ko aure zaiyi ba zai aureta ba dan shi yafi son ya auri mace wacce tasan ciwon kanta ba me bibiyar maza da kanta ba.
Zeey Sarkin 'yan naci aikuwa sai ta sake kira second guda bata 'kara ba ta d'aga wayar a fusace! murya a sama tace"Ke! mahaukaciya idan kina cin 'kasa to ki kiyayi ta shuri wallahi! saboda rashin kamun kai da iskanci da wulakanci zaki dinga kiran waya duk daran duniya kina damun mutane? wallahi to duk sanda kika sake kiran me wayar nan sai nazo har inda kike naci miki uwa! ni *Wasilatu 'Yar gaske!* na wuce da tunaninki bana d'aukar rainin hankali! idan auranki zaiyi yaje ya aureki ban hanaba amma kada ki kuskura na sake ganin kin kirashi a waya lokacin da yake cikin gidanshi, duk sanda kika kuskura kika sake kiran wayarsa a dai-dai wannan lokacin sai na dauki tsatstsauran mataki a kanki wallahi."! A fusace! take maganar tana wani irin huci jikinta na kyarma tamkar wacce tasha tsumin 'yan bori sai faman hura hanci take.......Mi'kewa yay zaune da sauri yana 'kokarin fizge wayarsa, ta mike da sauri ta bar gurin tana cigaba da sauraran maganar da Zeey ke mata."
"Ke har wata abace da zaki ce zaki dauki mataki akaina to mu zuba ni dake shege kafasa aure kuma nida governor kamar anyi an gama sai dai ki mutu dan babban mutum mai 'kima da mu'kami gami da mutunci bai cancanci! ya zama miji a gareki ba." A fusace! tace"Da Uwarki ya cancanta."! Zeey ta mike zaune da sauri tana mamaki! kafin ma ta dawo daga cikin mamakinta taji muryar Wasila na fad'in "Nace da Uwarki ya cancanta!? Shegiya dabba! wacce ta rasa mashinshini! tana bin mazan mutane a waje, zan nuna miki isa da mu'kamina a gurin shi wanda kike ganin ban isa na zama mata gareshi ba, zakiji da kyau wallahi zai za'ba a tsakaninmu ni ko ke! shashasha! mahaukaciya kawai."! Tana karashe maganarta ta kashe wayar tare da fashewa da wani irin kukan ba'kin ciki da takaici.
Ya jima kanshi a 'kasa ransa yayi masifar 'baci! ashe dama yarinyar nan ba tayi hankali ba wannan ai shashanci da rashin hankali da zata tsaya tana gundume gudunmen ashar da wata ransa ya sake 'baci sosai da abinda tayi dan duk a ganinsa laifin ba na kowa bane nata ne tunda be ce ta daga waya ba cewa yay ta kashe masa waya.......A d'an kausashe yace." Kiyi min shuru kada ki tasar min da yarinya daga bacci."! Cikin 'kuluwa da tsabar bakin ciki ta kalleshi, tace"Sai me! idan ta tashi ai laifin ba na kowa bane naka ne ni wallahi tallahi nagaji nagaji! ana cutata kuma ace ba zanyi magana ba kawai ka za'ba ni ko wannan 'yar iskar mahaukaciyar matar dake kiranka a waya."
Cikin tsananin bacin rai yace."Ranki zaiyi mutukar 'baci idan kika sake yi min irin wannan maganar kece zaki tsara min abinda nayi niyya idan nace Zeey na za'ba me Za kiyi.!?
Aikuwa sai ta fusata sosai idanunta ya rufe shaf ta manta waye a gabanta ta dinga zazzaga masa rashin kunya da fad'in "To same? dan ka za'bi Zeey ka ajiyeni dama ai hausawa suna cewa duk wanda yaci moriyar ganga zai yada koranta dama ai nasan tuntuni bani kake so abinda ke jikina kake so, dan haka ko sakina ma kayi ni bazan damu ba dan nasan Allah yayi min baiwar da in na rabu da kai in auri wanda yafi ka komai da komai na rayuwa sai me? dama dole akayi min me zanyi da tsoho! (me saisayayyan kai Inji *Nafeest* Lol🤭) ta cigaba da cewa " ai dama kai d'in kwata kwata ba'asan aurena bane dama da Zeey din kafi dacewa." Kallonta yake wani irin gumi na tsiyaya a jikinsa, tunda yake ba'a ta'ba ci masa fuska irin y
au ba, wannan yarinyar shi takewa rashin mutunci da d'ibar albarka? wai shin ma duk me ya jawo hakane? tambayar kansa da kansa yake da yaga bashi da amsa ga wani irin ciwo da kansa ke masa sai kawai ya mike zai fita daga d'akin! tayi gaggawar tarar gabanta tana kuka da fad'in "Sai ka sakeni tunda kace ka za'bi Zeey dani wallahi na gama zama da kai dama baka cancanta dani ba."! Cikin wani irin yanayi na tsananin damuwa da rud'ani! ya kifa mata mariku masu tsakanin shiga jiki, ta zube akasan dakin tana rirrike kafafunshi ihu! take sosai wanda ya tashi su Hajja daga bacci duk sukayo waje cikin tsananin tashin hankali da damuwa.
Kafarsa yake janyewa tana sake ri'kewa duk tabi ta cikwiye masa a jikinsa
Ga wani irin jiri da ciwon kai na nema su zautar dashi.
Hajja ta dinga buga kofar d'akin tana fad'in " Innalilhi wa'ina ilaihi raji'un jama'a meke faruwa ne? Amadu Wasila ku bude kofar mana komai yayi tsanani maganinsa Allah."
Jin muryar Hajja ya sanya Wasila tayi zumbur ta mike tsaye, saboda yanayin kwarin jikinsa har sai da ta tureshi ta bude kofa a guje ta fita daga dakin ta rungume Hajja tana wani irin kuka da shashsheka! "Hajja! nagaji da wannan zaman nagaji kullum sai ya dokeni ya sani kuka kullum cikin 'kuntata min yake baya kulani baya sakar min fuska nayi masa lefi na bashi hakuri yaki hakura, kullum sai muna kwance budurwa zata kirashi a waya suyi ta hira kuma a gabana bashi da lokacina ko magana nake masa baya saurarata, yanzu da bakinsa yace" Ya za'bi budurwarsa a kaina, dama nasan haka zata iya faruwa tunda dani da iyayena duk be dauke mu da mahimanci ba sabida muna talakawa, dama budurwarsa tace ni bancancani da na zama matarsa ba dan haka ni kawai ya sauwa'ke min na huta da wannan zaman."!
Hajja tace"Subahanallahi Wasila daina irin wad'an nan maganganun sam basu dace ba, kiyi hakuri kinji ko ansan ba'a kyauta miki ba amma komai a sannu ake binsa dama ni tuntuni na fuskanci matsala a tartare daku dama kuma naso in zauna daku din gobe idan Allah ya kaimu kiyi hakuri kinji ko duk da kince anyi miki laifi amma ina so kiyi hakuri dan duk wacce kika gani a gidan mijinta hakuri takeyi, maganar saki ki daina yi tunda har Allah yasa kun fara haihuwa ke dashi ai babu maganar rabuwa shi kuma aure lokaci gareshi idan Allah ya 'kaddara mijinki zai 'kara wani auran babu wanda ya isa ya hanashi abinda kikeyi bai dace ba kin san bashi da lafiya amma a maimakon ki kwantar masa da hankali sai kuma tashin hankali haba Wasila." Hajja ta kare maganarta cikin damuwa da kuma tausasa harshe.
Wani irin bala'in shaushin matar ya turnu'keta! hakan da tayi yana nuna mata cewar tana goyan bayansa kenan! A fusace! ta shige dakinta ta bugo kofar dakin da karfi!!!!! Hajja da rashida suka bita da kallo cikin mamaki, dama Amadu shi tuntuni ya shigewarsa dakinshi tsabar takaici bai tsaya ya saurari sharrin da take shirya masa gurin Hajja ba abinda bata sani ba kuwa Hajja ko kad'an bata son abinda zai 'bata masa rai!
Wannan abinda tayi yay masifar 'batawa Rashida rai! bata ta'ba yin turrr! da halin 'yar uwartata ba sai yau, kamar ta fashe da kuka tace" Dan Allah Hajja kiyi hakuri."! Hajja tayi murmushi a hankali tace"Ai babu komai Rashida Wasila na cikin 'bacin rai a yanzu komai zata iyayi kishi ne ke damunta."
Rashida ta girgiza kanta rai a 'bace! tace"To Hajja kishi hauka ne ni wallahi banji dad'in abinda takeyi ba."
Hajja tayi hanyar daki tana fad'in" Rashida kenan wani idan kishinsa ya tashi mancewa yake da komai da kowa kada ki damu nayi mata uziri."
Rashida ta girgiza kanta ta nufi dakin Wasilan.....Zaune ta tarar da ita had'a tagumi! hannu bibbiyu tana zubda hawaye duk ta wani firgice!.
Rashida tace"Yanzu anti Wasila wannan abin da kikayi shine dai-dai? nifa dole na fada miki gaskiya saboda in kika kashe wannan auran ba kanki kawai kika cutar ba har damu! Ashe har kin manta da al'kawarin da kika d'aukawar su Mai allo, shin wai me mutumin nan yake miki? meye bai miki ba na jin dadin rayuwa? ina ruwanki da auransa! ya auri mata dubu mana kin san dai ba zaki ta'ba hana abinda Allah ya halasta ba, to duk wannan tashin hankalin da damuwa
r da kikeyi na banza ne wallahi, wai har Hajja zaki zum'burawa baki ki buga mata kofa kawai saboda tana fad'a miki gaskiya meye laifinta dan tace ki bawa mijinki hakuri tana jin tsoro kada ki kwana cikin fushin Ubangiji duk macan da take furta kalmar saki ga mijinta Allah na fushi da ita! ni wallahi anti Wasila wani lokacin idan kina wani abun har mamaki kike bani."
Murya na rawa rashida ta karashe maganar.
Maganganun ne suka sanya ta dawo hayyacinta nutsuwa ta shigeta sai ta dinga tunanin abubuwan da suka faru ita dashi a baya, gabanta ya buga da mugun karfi! kada fa yayi zuciya ya kara sakina irin na baya! abinda ta ayyana kenan cikin ranta..... Ta goge hawayen fuskarta tana kallon babynta dake bacci, Rashin kunyar da tayi masa ta tuna, jikina yay sanyi duk taji tsoro ya shigeta tasan halinshi baya barin takwana idan anyi misho sai ya rama kuma ta lura ranshi ya baci sosai, tsoranta Allah tsoranta Annabi kada ya saketa da jego! gashi ta daukarwa su Mai allo alkawarin zama dashi har abada.
Ta kalli rashida jiki duk a sanyaye tace"Rashida Wallahi raina ne ya 'baci shiyasa kuma nasan ko ke akewa irin haka ba zakiji dad'i ba, amma nima nagane ban kyautaba."
Rashida tace"Nifa a ganina duk wannan abinda ke faruwa tsakaninku rashin bashi kulawa ne da tun farko da ya nemi agajinki kina agaza masa kina rarrashinsa da lallabashi da biya masa bukatunsa to da duk haka bata faru ba, wallahi laifin ba na kowa bane naki ne."!
Murya na rawa tace"Rashida kema laifina kike gani ko."? Rashida tace" Wallahi laifinki ne kan me yasa ba zaki kwantarwa da mijinki hankali ba tunda dai kin san baida hakuri ta wannan 'bangaran."
Hawaye ta goge murya na rawa tace"Kina so na mi'ka masa jikinta ya lalatani."
Rashida tace"Nifa ba haka nace ba, kiyi masa dabaru ma ki biya masa bukata, kuma ni banga wani abu ba banda kin sanyawa ranki kinje asibiti an tabbatar miki da cewar gurin nan ya warke to kuma zaman me kikeyi ki bawa me hakki hakkinsa kawai kin tsaya wani abu wallahi kece mai babban laifi."
Wasila tayi shuru tana sauraran 'kanwartata, tace"Naji shikkenan jeki dan Allah ni nagaji da wannan maganar na hakura idan na mika masa jikina ya fatattakani ya watsar dani shikkenan tunda haka kuke bukata." Rashida ta juya ta fita daga dakin ranta a 'bace!
Wasila ta jima zaune tana sa'ke-sa'ke yanda za'ayi ta gyara kwa'bar da tayi dan jikinta yay bala'in mutuwa sosai tana jin tsoro kada gari ya waye ya shigo mata da takardar saki irin na farko........Jikinta a sanyaye ta dauki babynta ta nufi dakin nashi......A hankali ta tura kofar dakin ta shiga ta mai da kofa ta rufe, da haske kadan a dakin shima na karamar wayarshi ne ya kunna.
Yana kwance cikin bargo zazzabin gaske ne ya rufeshi a d'azu dai zazzabi 'karya ya 'kir'kirarwa kansa amma yanzu tsabar tension d'in Wasila ya zuba masa zazzabi me zafin gaske.
Jin zamanta kusa dashi ya sanya ya bude idanunsa da sukayi masa bala'in nauyi sunyi jawur yana haska fuskarta da hasken wayarshi
Marairaice fuska takeyi tana kalato hawaye.....Ya 'bara rai mutuka yace"Tashi ki fitar min a d'aki."
Hannunsa ta ri'ke murya na rawa jiki na rawa tace"Kayi hakuri."!!!!! Ya janye hannunsa yace."Kin shigo nan ma ki zageni ke ga mara kunya ko."? Girgiza kanta tayi tace"Ba haka bane wallahi nayi kuskure raina ne ya 'baci! dan Allah kayi hakuri bazan sake ba."
Yace." Zaki hanani aure ne."? Shuru tayi gabanta na fad'uwa.
Ya sake maimaita magabarshi, girgiza kanta tayi alamun a'a hawaye na sauka a kumatunta, yace."To cewa nayi ki d'aga waya ta ko kuma cewa nayi ki kashe."?
"Cewa kayi na kashe." Yace." To me yasa kika d'aga min waya."? ''Babu komai." tafada tana dan matse hannunta da nashi dake game! Yace."Zeey ba sa'arki bace ta girmeki nesa ba kusa ba kuma da zan aureta da tun kafin na aureki na aureta bana son rashin arziki da rashin mutunci wallahi duk sanda wani ko wata ya sake kirana a waya kika d'auka kika zageshi sai na sa'ba miki kuma idan kikayi wasa sai nayi aure domin nagaji da wannan rashin hankalin naki."
Hannunsa ta rungume a kirjinta tana shashshe'kar kuka tace"Dan Allah kayi hakuri na daina kada kayi min kishiya
Allah bazan iya had'aka da ko wace mace ba ina sonka ina kishinka duk sanda naga kuna waya da Zeey ji nake kamar na mutu saboda bakin ciki da takaici."
Yace."Kina yi min irin wannan d'abi'un zan zauna dake ke kad'ai ki sanja hali idan kina bukatar hakan." Tana sake matsowa jikinsa sosai tace"Na daina wallahi Yanzu kome kake bukata zanyi maka dama dan dai na haihu ne amma yanzu idan ka shirya nima a shirye nake.........Ya watsa mata wani irin kallo yace."Ban shirya ba tukkuna kije ki huta ba yanzu ba." Sai ta sake rungume hannunsa sosai a kirjinta tana marairace masa fuska.......
_Namiji tamkar yaro 'karami yake duk ta inda kika tafiyar dashi zai tafi kuma ba zaki sha wuya dashi ba Namiji ba'ayi masa kutse! ba'ayi masa dole ba'a nuna masa iko idan kikace zakiyiwa mijinki wad'annan da'bi'un zakiyi masifar shan wahala.........Wasila itace babbar mai laifi dangane da wannan rikicin da sukeyi Team din Wasila Afuwa Amadu nada masifar sau'kin kai kuma yana son Wasila ni banga laifinsa ba idan ma yana da laifi bai ka nata ba, yanzu gashi lokaci 'kankani ta shawo kansa duk da rashin mutuncin da take masa amma tasirin son da yake mata ya hanashi daukar mataki a kanta ko yayi niyya ma baya iyawa saboda yana sonta dan haka Wasila kiyi kokarin ganin kin rike mijinki da kyau idan ba haka ba na kawo mishi santaleliyar mace wacce tafi ki komai da komai da kike ta'kama dashi🤭🤭_
Littafin na kudi ne....!
Kika futar min da book keda Allah kika karanta baki biya ba kema keda Allah! Whasap numbar
*07084653262*alliya:
'Yr Bngr Sys
*82*
Yace."Me yasa a sanda na nema baki bani ba sai yanzu da naji kwata-kwata bana sha'awa, kawai kije ki kwanta duk sanda na keso zanyi miki magana." Taji kamar ya da'ba mata wu'ka a ma'koshi yau itace ke masa tayin yin sex da ita yana kaucewa lallai yayi fushi da ita sosai! Jikinta a sanyaye ta saki hannunsa ta juya masa baya tana goge hawaye, Shima juya bayansa yay saboda baya so ya tsananta gurin kallonta domin kada ta rinjayeshi dan ya lura da rigar baccin dake jikinta me futar da tsaraici ce yana so ya tabbatar da shin da gaske tuban da tayi na gaskiya ne ko na karya dan ya daina yi mata rawar jiki ballanta ta cigaba da raina masa hankali.
Ganin ya juya mata baya yana jan bargon jikinsa ya sake sanyawa jikinta yin sanyi ta juyo tana kallonshi, wata zuciyar na bata shawara kawai tayi tafiyarta yayin da wata zuciyar ke cewa ki zauna dai ki cigaba da rarrashinsa kada kiyi fushi dashi.
Sai ta dauke baby zahra dake kwance a gefensu ta kwantar da ita a gadonta tayi mata addua a hankali ta dawo gadon ta kwanta kusa dashi tana nani'karsa, cikin bargon ta shiga ta zura hannunta ta rungumeshi sosai a jikinta tana sauke ajiyar zuciya,
Shima ajiyar zuciyar ya sauke yana dan sake takure jikinsa tsigar jikinsa na mikewa a hankali ya tura le'banshi na kasa a bakinshi yana dan cizawa shi kadai yasan abinda ke damunsa
Hannunta ta zura cikin rigar baccinsa ta kwance madaurin ta soma shafa faffad'an 'kirjinsa tana sake goga jikinta a nasa,
A dan fusace! ya juyo yana tureta yace."ba cewa nayi ki fita min a daki ba."
Ta narkar da muryarta tana dan hura masa iskar bakinta a fuskarsa tace"Umm! Umm! ni anan zan kwana kuma ina bukatarka a kusa dani."
Kamar ya kwada mata mari haka yaji wato tana so tasa shi yayi abinda baiyi niyya ba.
Yace."Okey ni bari na baki dakin tunda bakyajin magana."Kokarin mikewa yake ta haye jikinsa tana danne kirjinsa wai ba zai tashi ba."
Ji yay duk wani kuzari nasa ya kare dama ya yini cikin kasala da damuwa ga zazzabi sai kawai ya koma ya kwanta yana kallon ikon Allah.
Faffad'an 'kirjinsa ta shiga shafawa tana d'an murza nipple dinsa tana dan ja a hankali a hankali! Ya saki wata iriyar hamma! wacce bai san sanda ta fito ba ya wani sake mi'kewa sosai kan bed din yana mi'ka! hakan da yayi sai ya sake tabbatar mata da cewar sa'konta na ratsa masa jiki
A hankali ta soma lasar kirjinsa tana dan jan gashin kirjin da bakinta tare da tsotsar kan nononsa!
A gigice ya dafe mazaunanta! ya rike sosai ya shiga matsawa yana sakin wani irin nishi, kafin kice kwabo jijiyaraa ta kumbura tayi fam! tana jinta a jikinta na harbinta.
A gaggauce ta dam'ko wuyanta ya rankafo da ita jikinsa sosai ya kama bakinta cikin gigita da wani irin salo suka shiga tsotsar bakin junansu........Yanda suke sucking din junansu shi zai nuna maka da cewar lallai dukaninsu a bukace suke da junansu, duk sun wani gigice sai makale jikin jununsu suke suna sakin wani irin nufarfashi.....Sun jima cikin wannan yanayi kafin tayi dubarar zare bakinta ta dan gyara kafafunshi ta kwance igiyar dogon wandon dake jikinsa, ta zare wandon lokaci guda jijiyarsa tayi tsalle ta fito, ta sauke wata irin ajiyar zuciya tana lumshe idanunta tare da tand'ar baki, ji tayi wani irin ruwa na zuba a jikinta ganin joystick dinshi kawai ya sanya duk wata sha'awarta ta tashi, hannu biyu tasa kan joystick din ta shiga murzara a hankali a hankali tana shafa samanta ruwan dake fita a jiki na taimaka mata gurin wasa da ita.
Allah Sarki Amadu wargajewa yay ya saki jikinsa sosai yana ta cije le'bansa, sosai yake jin dadin abinda take masa.
Sanda ta soma shan joystick din kasa nutsuwa yay sai da ya bude idonsa ya kamo ta kamar mahaukaci ya yage rigar jikinta jikinsa sai kyarma yake yi ya soma mutsika nonowanta yana wani irin gurnani!
Wasila tayi masa wasa sosai har sai da ta tabbatar da ya samu gamsuwa sannan ta saurara masa aikam tasha addua gami da sa mata albarka yanzu duk wani lefinta da yake gani ya gushe tunda ta dauke masa damuwar dake damunsa tsayin kwanaki masu tsayi.
Tare sukayi wanka suka fito sai dai me? wani irin zazzabi ne me zafin gaske ya rufeshi wanda s
ai da ta taimaka masa gurin saka kaya ta lallabashi yasha magani kana ta rungumeshi a jikinsa tana ji tamkar ta dawo da zazzabin jikinta
Sai da bacci ya daukeshi sannan ta samu ta rintsa, aikuwa asuba nayi baby zahra ta tashesu, duk suka tashi a firgice shine yay gaggawar sakkowa daga bed din ya nufi gadon yarinyar yana dubata.
ta saka hannunta a bakinta tana ta tsotsa da alamun abincinta take nema.
Yace."Kizo ki dauketa ki bata nono tasha da alamu yunwa takeji." Ta cire bargon dake jikinta a hankali ta sakko daga bed din tazo ta dauki babyn shi kuma ya shiga toilet domin daura alwala.
'Karfe shida da rabi suna zaune a gurin karatu ita dashi suna dan hira sama sama koda rashida ta fito ta gansu haka sai ta shiga mamaki sosai! babu shakka duk wanda zai shiga tsakanin ma'aurata to kuwa watarana shine zaiji kunya......Hajja ma bayan sun gama karatun data fito ta gansu suna hira Wasila sai dariya takeyi sai ta shiga mamaki sosai, taji dadin hakan cikin ranta kuma dama tasan fadan nasu ba zaiyi tsayi ba tunda dukaninsu tasirin so na d'awainiya dasu.
Wasila wata iriyar kunya ce ta lullu'beta ganin Hajjan yasa ta tuno rashin kirkin data yi mata dazu.
Kai a kasa ta shiga gaishe daita, Hajja ta amsa fuskarta dauke da fara'a ta nuna kamar ma wani abu bai faru ba tace"Ina 'Kawata take."? Tace"Bacci take har yanzu bata tashi ba." Hajja tace"Ashe kuwa zan tafi bamu gaisa ba."
Amadu yace."Haba Hajja da wuri haka." Tace."Ka manta da maganar da mukayi d'azu daka shigo gaisheni."
Yace."Me zai hana anan ayi abun sadakar ko dole ne sai kin koma gida." Tace"Nafi so dai na koma gida nayi can kaga nan ko anyi babu makarantu da kuma 'yan 'kananun yaran da za'a bawa."
Yace."Shikkenan Hajja Allah ya saka da alkairi. " Ta amsa da "ameen ya rabbi."
Ta cigaba da cewa"Naji dadi sosai dana fito na ganku haka dan Allah ku dinga hakuri da junanku dama kwanaki naso na fahimci wani abu a tsakaninsu to sai banyi magana ba saboda nasan zaku iya shirya tsakaninku kamar dai yanzu dana dauka kamar abin zaiyi tsayi sai gashi har kun sasanta alhamdullhi dama haka akeso ku d'inke duk wata 'baraka da shaid'an zai samu gurbin zama a tsakaninku....Ke Wasila kece 'kasa dashi ke kanki kin tabbatar akwai tazara me tsayi a tsakaninku, a zamantakewar ku na lura dake kina da taurin kai wani lokacin dan Allah ki daina wannan d'abi'a domin ba hali ne mai kyau ba, duk abinda mijinki ya umarce ki dashi to kiyi kokari gurin ganin kinyi masa biyayya Ubangiji Allah ya cigaba da baku zaman lafiya gami da zuria mai albarka."
Suka amsa da "ameen" Hajja ta kalleshi a nutse tace"Dan Allah tun da dai yarinyar nan tayi ar'bain to ka kaita taga 'yan uwanta 'bangaran uwa da uba wallahi mutanan suna da kawaici kuma suna da kirki sosai, ka dinga kokarin sadata da 'yan uwanta."
Yace."Insha Allahu Hajja."
To Hajja na karyawa Garba ya shigo ya dauki jakar kayanta, Wasila da rashida kamar suyi kuka saboda alhini ita kanta Hajjan jikinta duk yayi sanyi daurewa kawai takeyi tana fad'in "Ai zan dinga zuwa akai-akai ina dubaku."
Amadu da kanshi ya kar'bi key d'in motar hannun Garba yaja domin kai Hajjan gida, su Wasila suka koma ciki da sa'bulallan jiki.
Rashida kwanciya tayi kan kujera jikinta duk a sanyaye ita kuma Wasila cikin dakinta ta shiga tana goge hawaye, wanka ta shiga tayi ta fito ta shirya jikinta sosai tayi kwalliya cikin wani irin boyal me ruwan zuma d'inki irin buba akayi masa da wani uban sirfani a wuyan rigar da yaji stons sai sheki takeyi tayi amfani da gold dinta na fitar sunan Zahra ado taci tamkar wata amarya ta baza turarruka masu kamshi a jikinta, ta shirya Zahra suka fito palo, Rashida ta dinga kwarzanta kyawun da tayi tana fad'in kamata yay kafin kowa ya fara ganin kwalliyar nan Abban Zahra ne zai fara gani.
Wasila ta wani d'ora ka'fa daya kan d'aya Rashida na daukarta a hoto da wayarta.
Sai da sukayi pictures sama da ashirin wasu ita kadai wasu ita da Rashidan da baby zahra wani kuma ita da babynta sunyi kyau har sun gaji.
Har wajen karfe hud'u da rabi na yamma bai dawo ba, tun bayan da ya tafi kai Hajja gida, kwalliyar da tayi duk ta tsufa! bayan ta idar da sal
lah ta yanke shawarar kiransa a waya.
Suna tare da Khalifa a guest house dinsa kiran wayarta ya shigo ba kasafai yake son amsa mata waya a ko'ina saboda tsaro dan ba Khalifan ne kawai a gurun ba su kusan hudu ne, sai kawai ya kashe wayar,
Ranta taji ya 'baci jikinta yay sanyi tace"Kodai bai hakura bane? Whsap ta shiga dama numbarshi ce kadai da ita, tana dubashi sai ganshi a online! abinda bata sani ba shine Amadu datar sa sai tayi kwana da kwanaki a bude saboda ba sosai yake shiga whasap din ba ko ya shiga baya dadewa yake sauka, sai kawai ta shiga tuttura masa pictures dinsu ita da baby zahra tana gama turawa ta kashe datar ta mike ta fita daga dakin.
Kicin ta nufa ta dauko had'inta na ni'ima cikin fridge ta zauna tana sha sai da tasha sosai ta mayar ta tsiyayi ruwan kaninfarin ta daya tsumu! har wani ja yayi tasha tana rinste ido saboda yaji da gafinsa da ya game mata baki, cup din ta ajiye ta fita daga kicin din.
Ya d'an dauki wayar yana duba lokaci kawai yaga sa'kkoni na shigo masa ta whasap kuma da numbar ta, da sauri ya shiga yana dubawa, Pictures din yake kallon yana sakin murmushi gabakid'aya hankalinsa nakan hotonan wanda sukayi masifar kyau da dauke masa hankali.......Khalifa yace."Wai me kake dubawa cikin waya ne sai murmushi kake."? Alhaji Nura yace."Da'alama dai bazawararsa ce tayi masa text mai daukar hankali."
Kashe wayar yay yana kallonsu da murmushi a fuskarsa yace."Ni zan koma gida dama kai Khalifa nace maka bana jin dadi dan jiya da zazzabi na yini na kwana, komai za'ayi ayi idan da yuwuwar A bawa Alhaji Munzali rance kud'in nan a bashi amma dai a tabbatar da cewar akwai shaidu sannan kuma kowa ya sanya hannu." Khalifa yace."Kafin ka tafi sai kasa hannu tunda kaina zaka bada kudin in yaso sai musa namu daga baya."
A gaggauce ya 'karbi takardar ya saka hannu ya mika masa yana gyara babbar rigarsa ya mikawa Alhaji Nura Hannu yana fad'in "Alhaji Saduwar alkairi." Alhaji Nura yace."Mutumina da alama dai madam ce tayi kira irin wannan sauri haka."
Khalifa na sane yace."Kasan yarinya 'karama ya aura shiyasa yake wannan rawar jikin." Alhaji Nura yasa dariya yana fad'in "Nima daf nake da na auri 'yar 'kankanuwar yarinya domun in more yanda ya kamata."
Gabad'aya dariya suka saka, suna mi'kewa tare da yin musabaha ga junansu, suka sauka da bene kowanne yana baza babbar riga Garba yay gaggawar bude masa mota ya shiga ya zauna yana dagawa Khalifa hannu wanda shima ya shiga motarshi tare da direbansa,
Kusan tare motocin suka fita daga gurin kafin ko wace mota ta dauki hanyarta.
Cikin 'kananun kaya ta shirya jikinta ta matse sosai ta saki dogon gashinta ya kwanta a bayanta le'bunanta sun sha jan janbaki tayi kyau sosai
Cike da wasa Rashida tace"Lallai yau anti Wasila amarci ake ci bari na koma daki kafin Abban Zahra ya shigo naji kunya." Wasila ta harareta tana kai mata duka, rashida ta kauce tana 'yar dariya tace"Ni wallahi wannan soyyayar taku mamaki take bani ayi fad'a a shirya humm! Murmushi tayi tace"Baby zahra a gurinki zata kwana yau tunda kin daure min gindi na mi'ka kaina gurin dadynta yau zamu kwana muna abu daya."
Rashida tasa hannunta ta rufe bakinta tana dariya cike da kunyar yayar tata tace"A'a anti Wasila ni ban daure miki gindi ba dan Allah ki sassautawa Abban baby kada ya zauce! baby zahra kuma na amince zan rike miki ita har gari ya waye amma dan Allah ki sasaautawa abbanta." Wasila tasa dariya tace"Shi zaki fad'awa kice ya sassauta min amma bani ba." Rashida ta dinga dariya tana fad'in "Anti Wasila shifa salihi ne ke kam ai babu sauki! Allah ma yasa Zahra ta samu k'ani."
Wasila ta kai mata duka tana 'bata rai tace"Ciki yanzu Allah ya kiyaye min rashida har yanzu ban manta wuyar dana shaba."
Tana rufe bakinta ya shigo palon, idanunsu suka sarke guri guda wani irin kallo suke jifan junansu dashi.
Rashida tayi masa barka da zuwa ya amsa yana me kauda idonsa daga kan Wasila, baby zahra ya kar'ba daga hannunta yana mata wasa.
Cikin wata irin murya tace"Sannu da zuwa." Ya amsa da "Yawwa."! yana kokarin shiga dakinshi da baby zahra a hannunsa......Mi'kewa tay tabi bayanshi tana wata irin t
afiya sasaan jikinta na wani irin rawa.
Agogon hannunsa yake kokarin cirewa ta 'karasa da sauri tana karba tana cire masa, ya tsira mata ido bako kiftawa, murmushi tayi tace" Dazu nayi ta kiran wayarka baka dauka ba." Anutse yace."Ina tare da jama'a ne duk sanda kika kira waya kikaga ban daga ba ina wani uziri ne.
Ta ajiye agogon kan drowar ta fara kokarin cire masa babbar rigar jikinsa, ta ajiye kan bed tana 'balle masa botiran rigar cikin, ya zauna da dogon wando da singlet a jikinsa,
Tace."Ko na had'a maka ruwan wanka."?
Yace."Bari naci abinci tukkuna."
Tace."Tom bari na kawo maka." Juyawa tayi da niyyar futa daga dakin ya bita da kallo har ta fice ya sauke wawar ajiyar zuciya yana me lumshe idanuwansa.
Da kanta ta bashi abincin yaci ya koshi tana masa hira sosai yake mamakinta, yana adduar Allah yasa zamansu ya dore a haka.
Tun da ya gama cin abincin jikinsa ya mutu murus! bacci bacci wani irin feeling mara dadi ne yake taso masa,
sai kawai yay kwance kan chanis carfet din dake gefan bed din, Ta shigo dakin taga yana kokarin yin bacci, zama tayi kusa dashi kamshin jikinta ya bugeshi, da sauri ya bude idonsa yana kallonta, hannunta ta dora a kirjinsa tace"Ko jikin ne ya dawo kada kayi bacci da yamma Annabi ya hana." Yaji kamar ya daure sai dai ya kasa! janyota yay ta fad'a saman 'kirjinsa ya rungumeta 'kam! yana sauke wata zazzafar ajiyar zuciya.
Littafin na kudi ne...!
Kika futar min da book keda Allah! kika karana baki biya ba kema keda Allah! Whasap numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
*BINTA UMAR ABBALE*
*BINTA UMAR ABBALE*alliya:
'Yr Bngr Sys
*83*
Kwanciya tayi saman kirjinsa tana jin yanda yake shashshafa sassan jikinta yana sakar mata wasu zafafan kesses wanda ya sanya a take ita jikinta ya mutu ta langwabe a jikinsa tana so ta biye masa, gashi magariba ta gabato, sun jima a haka har sai da yaji ya dan samu sassauci a tare dashi kana ya cireta daga jikinsa ya mike ya nufi toilet domun daura alwala,
Sai da yayi wanka sannan ya daura alwala ya fito har yanzu tana nan takure a kasan kafet, ya dan kalleta yana nazarinta
ganin ta d'ago kanta sun hada ido ya sanya ya fahimci halin da take ciki, Yace."Lokacin sallah yayi ko bakyajin kiran sallah ne."?
A sanyaye tace"Yanzu zan tashi nayi alwala." bai ce komai ba ya fita daga dakin.
Ta jima zaune tana so ta dawo dai-dai abin ya faskara muguwar sha'awa ce ke damunta. Da kyar taje ta dauro alwala ta fito, ta tada sallah, tana idarwa, ta fita parlo lokacin Rabe har ya shirya musu daining Rashida na daki ita kadai kunyar zama take a palon gudun kada masu gidan suyi abin kunya a gabanta.
Dakin ta shiga ta tarar da ita tana kallo da plate din abinci a gabanta tana ci.
Tace"Rashida yau babu kallo kenan."?
Rashida tace"Anti Wasila yau nan zan zauna nayi kallona ina kewar Hajja Wallahi da tuni muna tare.
Wasila tace."Bake kadai ba nima kewarta nake! wallahi matar nada kirki......juyawa tayi da niyyar futa daga dakin Rashida tace"Sai da safe Anti Wasila."
Tace"Allah ya tashemu lafiya."
Amadu be shigo gidan ba sai bayan sallahr isha'i, lokacin tayi wanka ta sauya kaya wannan karon ma kananu ne wanda suka matse mata jiki gashi tayi amfani da turarrika masu kamshin gaske duk inda ta gifta kamshi ne ke tashi, Da kyar ya daure ya iya zaman cin abincin, a daddafe suka nufi bedroom ita dashi, duk sun d'okanta da junansu. wata iriyar rayuwa sukayi a ranar wacce ba zasu ta'ba mantawa da ita ba, sun mori kansu da kansu kuma dukaninsu sun biya wa junansu bukata, sukayi wanka tare kamar yanda suka saba kana suka kwanta rungume da junansu.
Koda asuba tayi yaje masjid ya dawo sai da suka sake komawa ruwa basu saurarawa kansu ba sai da gari yay haske sosai san suka sarara sukayi wanka suka shirya tsaf! Wasila ta shirya babynta ya karbeta suka fito palo a tare sai wani kyallin goshi yakeyi....Rashida data gaji da zaman jiran fitowarsu gurin karatu sai kawai ta bar gurin ta koma kan kujera ta zauna tana duba wani littafin addini.
Sai da ya ganta da littafi a hannu sannan ya tuna da karatu, suka gaisa a nutse yace."Yau bamuyi karatu ba ko."? dan mirmushi tayi tace"Ai baka jin dad'i."
Yace."Lefin yayarki ne da bata tasheni a bacci ba." Wasila taji karshen maganarsa lokacin ta fito daga daki ta dan harareshi irin na soyyaya tace" Ni babu ruwana wane irin tashi ne ban maka ba mybe maganin daka sha ne ya sanya maka bacci." Da sauri yace."Nima nafi tunanin haka."
Dainnig ta nufa ya bita da kallo cikin sha'awa shi dai ba zai ta'ba gajiya da ita ba a rayuwarsa, Rashida ta kar'be baby zahra dake hannunshi Shi kuma ya wuce dainig domin karyawa
Ko a gurin break din ma sai da sukayi wassanin su iya son ransu sannan sukayi break din cike da farin ciki gami da annushuwa, da kwata kwata baiyi niyyar fita ba yaso ya zauna gida ya yini tare da iyalinsa to dole ne ya fita saboda akwai babban abinda zai sanya ya fita din, harda kuka da zai fita tana ta shagwaba da dire diren kafafu shi kuma sai biye mata yake yi, da kyar dai ta barshi ya fita daga gidan.
****
Tsaf malam Mai allo ya shirya cikin manya kaya yayi wa matarsa Bitan sallama dama duk abinda ke faruwa ya shaida mata saboda ya yarda da ita da nutsuwarta Bitan macace mai hankali da sanin ya kamata, fatan alkairi tayi masa gami da dawowa gida lafiya.
Mai allo bai sha wahala ba gurin zuwa gidan Kawu Madu dake Pataskum dan Wasila tayi masa kwance sosai kuma sai da ya tambayi Madu mai itace ya sake tabbatar da cewa shi d'in ba 'boyayye bane.
Allah ya taimaka Kawu Madu nan bai fita ba yaro ya shiga gidan ya shaida masa yayi ba'ko......Kawu Madu na fitowa yaga fuska irin ta Yahuza me rasuwa.
Yace."Hala dai kaine Yayan Yahuza mijin Uwani mahaifiyarsu Wasila ko."
Mai allo ya washe baki
nsa yana mi'ka masa sannu yace."E kwarai nine malam ashe ka shaida ni."
Kawu yace."Haba malam ai duk wanda yaga fuskarka yasan kai dan uwan Yahuza ne ai kuna kama sosai.
Mai allo yace." Masha Allah masha Allah! Kawu madu yace."Bisimillahi malam shigo ciki." Mai mai allo yace"Da mun zauna ma a zaure magana ce mai muhimanci nake tafe da ita.
Kawu yace."To babu damuwa bari na dauko abun zama." Yay saurin shiga cikin gidan yana washe bakinsa,
Mai allo ya shiga soron gidan ya tsaya yana jiran fitowarsa.
Sai da suka sake gaisawa suka nutsu tukkuna kafin Mai allo yay gyaran murya yana fuskantar Kawun yace."Magana ce nake tafe da ita Malam Adamu ina fatan kuma zaka dauki maganar tawa da mahimanci." Kawu Yace."Ina sauraranka Malam Mai allo yace."Nazo nan ne da niyyar auran Uwani ina fatan amincewarka.".
Kawu madu yace."Alhamdullhi! kai amma naji dad'i wannan magana da kake tafe da ita dama ko jiya sai da mukayi magana da ita dake nan d'in ma tana samun zawarawa sai nace to ta futar da miji tayi aure sai ta nuna min duk cikin zawarawan dake sonta babu wanda yay mata a cikinsu, amma jikina na bani kai ba zata watsa maka kasa a ido ba ko banza tasan "yayanta sun samu Uba nagartacce."
Mai allo yace."Nayi istahara dangane da al'marin kuma alhmdullhi Jikina na bani akwai alkairi shiyasa nayi gaggawar zuwa domin na sameta mu tattauna kuma ku sani insha Allah gobe zanje in samu Kawunta na can kano idan mun tsaida magana da ita."
Kawu Madu yace."Hakan yayi kyau malam babu shakka idan Al'amarin ya 'kullu ni zanfi kowa farin cikin hakan.
Mikewa yay ya nufi cikin gidan yana fadin'"Bari na kira maka ita ku tattauna.
Koda Kawu madu ya shaidawa Uwani zuwan Mai allo sai ta shiga mamaki sosai jikinta yay sanyi tun bataji abinda yake tafe dashi ba, hakika yanzu take nadama gami da dana sanin abinda ta dinga yi masa a baya.
Ta dauki mayafi kalar atamfar dake jikinta ta yafa a jikinta ta fita zauran.....Cikin nutsuwa take masa barka da zuwa tana sunkuyar da kanta kasa, sosai Mai allo yayi mamakin nutsuwarta, zauran yay shuru na minti biyar kafin mai allo yay gyaran murya a hankali yace."Ina fatan Kawu Madu ya fada miki abinda yake tafe dani.''
Uwani ta dago kanta tana kallonsa, haiba da kwarjininsa ya sanya ta sunkuyar da kanta kasa a hankali tace"Bai fada min ba."
Mai allo ya sakeyin gyaran murya a karo na biyu yace."Wata magana ce mai muhimanci nake tafe da ita ina fatan idan kikaji zaki aminci da ita.".
Tace."Malam ka fad'i ko wace irin magana ce ina sauraranka."
Mai allo yace."Nazo nan ne da bukatar auranki." Uwani gabanta ya yanke ya fadi sai ta kasa dago ido ta kalleshi.
Mai allo yace."Nasan zakiyi mamaki ko? to ki sani ba'a mamaki da ikon ubangiji tabbas wannan auran namu akwai albarka a cikinsa a yanzu babu abinda nake bukata daga gareki sai amincewarki."
Uwani ta jima kanta a kasa ta kasa cewa komai dan har Malam din ya cire tsammanin za tayi magana, sai kuma yaji tace"Babu komai malam na amince Ubangiji Allah ya tabbatar mana da alkairi a ciki, sannan don Allah ka gafarce ni kan abubuwan dana dunga yi maka a baya.
Mai allo yay murmushi farin ciki ya cika masa zuciya yace."Alhamdullhi Naji dadi sosai da kika aminci kai tsaye ba tare da mun kai ruwa rana ba, ni kuma nayi miki al'kawarin rike ki tsakani da Allah da manzon Allah dik wani abu da kikayi min a baya na yafe miki Allah ya yafe mana baki daya."
Uwani ta amsa da ameen Yace."Sati biyu kacal nake so a daura aure ko ya kika ce."?
Murmushi tayi cike da kunya gami da jin nauyinsa tace"To shikkenan Allah ya nuna mana."
To kafin malam ya tafi sai da suka tsayar da magana shi da Kawu Madu kan cewa kafin cikar kwanakin da suka d'iba zai kawo sadaki da duk abinda ya sawwa'ka." Kawu Madu yace."Kada ka takura kanta malam kawai ka kawo sadaki a daura aure."
Malam yace."A'a dole sai yayi mata suttura da sauran abubuwan amfani." Cike da girmama juna sukayi sallama Malam ya wuce ya tafi zuciyarsa wasai yana jin wani irin so da kaunar Uwanin na ratsa jikinsa.
***
Masha Allah Addua bata bar komai ba kuma hausawa nacewa duk abinda hakuri bai baka ba to babu shakka rashinsa ba zai baka ba
, alhmdullhi gidan Amadu yayi kyau komai na tafiya dai-dai dukaninsu sun kwantar da hankalinsu suna kula da junansu kamar zasu cinye kansu, mutukar na gida suna daki a kulle suna soyyaya baby Zahra kam har ta saba da Rashida in ba nono zata sha ba baka ganinta gurin Wasila, al'amarin Zeey kuwa tun ranar data kira waya ta haddasa musu rigima bata sake kira ba saboda sosai taji zafin zagin da Wasila tayi mata, tayi ta tsammanin ko Amadun zai kirata taji shuru bai kirata ba, nan ta gane ashe itace take haukanta dole tilas ta sanyawa zuciyarta dangana ta rubuta masa text wanda lokacin da ya karanta test din sai da ya tausaya mata so masifa ne, shi kam yana ganin ko ya aureta wuya zata sha ko bakin ciki ya kasheta dan ba zai iya kwantata da Wasila ba, kwata kwata yanzu babu wacce take gabansa sai Wasila da babynta.
Yana tsaye tsakiyar daki yana fesa turare ta shigo dakin tana zum'bura bakinta, taki kallonsa ta wuce taje ta kwanta kan bed tana hawaye, tun jiya suke ta tafka rigima tana so taje su gaisa da Mai allo kana su wuce pataskum amma yayi biris da maganarta idan ta dameshi yace zasuje sai an kwana biyu har yanzu kwana biyun ba tayi ba.
Ganin tana kuka sai yaji babu dadi yazo ya tsaya kanta yana tambayarta menene? cikin kuka da shagwaba tace"Lokacin da Hajja take nan naji tace maka ka dinga bari muna zuwa gaishe da mahaifanmu amma yanzu nayi nayi da kai ka'ki barinmu, ni wallahi gurinta zan kai 'kararka."
Ya zauna gefan bed din yana dariya dan maganarta dariya ta bashi yace."Ke! ni zaki kai 'kara."? Tana goge fuska da turo baki tace"To ai kana jin maganarta watakila ita idan tayi maka magana ka amince." Ya sasauta fuskarsa yace."Ba hanaku zuwa nayi ba, kinga Rashida jarrabawa zasu fara ranar Monday kuma tare zakuyi keda ita shine dalilin da ya sanya na dakata tukkuna kuyi jarrabawar sai muje tare nima ai ina so mu gaisa da Malam d'in."
Ajiyar zuciya ta sauke ta rike hannunsa tana shafawa tace"Shikkenan Allah muna gama jarrabawar nan ko kwana daya baza mu kara ba zamu tafi."
Ya d'age mata gira yana dan kashe idonsa yace."Wai idan kin tafi ni ya zakiyi dani kin san dai kin saba min da abubuwa da yawa." dariya tayi mishi tace"Kayi zamanka ka huta dama ai wataran cewa kake na dameka."
Yace."Ba wannan ba, kwana nawa zakiyi." Da hannunwanta tayi masa alama wai kwana ashirin zatayi."
Yace."Bana jin zan bari ki kwana Madam muje mu dawo a rana daya......Rungumeshi tayi tana cikwikwiya masa shaddar jikinsa tana kuka tace."A'a wallahi ni kwana daya be isheni ba."
Cikin mutuwar jiki da kasala ya cireta daga jikinsa yana duba jikinsa yace."Duba saboda sangarta nayi adona kin 'bata min jiki, ni dai na gama magana ba zaki kwana ba."
Da gudu ta d'ane jikinsa tana kuka "Wallahi sai ka amince nayi sati daya." Abinda take fada kenan tana cusa fuskarta a kirjinsa.
Jikinsa ne ya mace suka zube ita dashi kan bed din tayi kwance a saman kirjinsa tana masa dukan wasa sai kuka takeyi, rungumeta yay jikinsa na rawa ya shiga sumbatarta ta ko'ina...
****
Cikin ikon Allah Wasila ta shige cikin 'yan mata 'yan ajinsu Rashida ta saje dasu ba zaka ta'ba cewa matar aure ce ba, kuma babu abinda ya gagareta gurin karatun dan dama kafin zuwan ranar jarrabawar yana dan koya mata wasu abubuwan dake kuma tana da saurin fahinta babu wani abu da shige mata duhu ko ya daga mata hankali sukayi jarrabawar fita daga secondary skull cikin narasarori masu yawa.
*****
Ana ya gobe zasu tafi Garko Kawu Habibu ya kira wayar Amadu yake shaida masa halin da ake ciki, cewar malam mai allo zai daura aure ranar juma'a mai zuwa, kuma ba da kowa sai da mahaifiyar matarshi Uwani, Amadu yayi mamaki sosai da maganar Kawu Habibu daga karshe yayi addua gami da fatan alkairi ya kuma tabbatar wa da Kawu Habibun cewa insha Allahu suna tafe kafin zuwan ranar..........Kasa hakuri yay ya kirata a waya yace."Akwai albishir din da zan shigo miki dashi, amma meye tukwicina." Tana dariya tace"Ai kaima kasa ni." Yace."Nasan me? kawai ki fad'amin tukwicina." Tace."To zan barka kayi sau goma." Dariya ya 'kyal'kyale da ita yana sake rike wayar a hannunshi, yace."Kamar gaske ko?
yarinyar daka amfara zaki hau ihu kina cewa na daina ke zafi kikeji."
Ma'kale wayar tayi sosai ta wani lumshe ido tace"E mana ai kaine kakeyi da 'karfi shiyasa." Yace."To me yasa idan na bari ke kikeyi da 'karfin."? Kunya ce ta rufeta ta hau inda inda! Yace." Ai nagane wannan kukan da kikeyi na sharri ne dan dana bari ke kuma kikeyi da kanki kukan d'adi ne ko."?
Sai ta soma shagwaba da sangarta tana fad'in "Ya bari ita bata so." Yana daiya yace."Na bari shikkenn idan na dawo gida bazan fada miki albishir din ba sai nayi sau goma kamar yanda kika fada kin amince." ? "Umm."! tace" Tana lumshe idonta wannan 'yar wayar da suke tasa gabakid'aya hankalinta ya tashi sha'awa duk ta taso mata......
Littafin na kudi ne.....!
Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah! Whasap numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*'Yr Bngr Sys
*84*
Aikuwa da ya dawo gidan ta dameshi kan lallai sai ya fad'a mata albishir d'in shi kuwa yay ta ja mata rai, sai da suka gama komai na rayuwarsu sannan yake shaida mata abinda ke faruwa, farin ciki ya lulli'beta tamkar anyi mata albishir da gidan aljanna gaskiya taji dad'i sosai da wannan abu dama itama sam bata son zaman mahaifiyarta ta a haka tunda dai ba wuce auran tayi ba, koda Rashida ma taji labarin abinda ke faruwa tayi ta murna da farin ciki da 'kyar sukayi bacci a ranar saboda farin cikin da suke ciki.
Gari na waye wa ta tashi da walwala da farin ciki sai shiri takeyi shi kam yana kwance yana kallonta kwata kwata baya son tayi nesa dashi dan dai bashi da yanda zaiyi ne kawai, ya shirya cikin manya kaya kamar dai yanda ya saba, duk ranshi babu dadi kawai dai yana kokarin daurewa ne amma duk da haka sai da fahimta to itama nata bangaran tasan tilas tayi kewarsa amma haka zata hakura dan gaskiya tana so taje ta gaisa da iyayenta sosai.....Kafin su tafi sai da ya fara kaisu gidan Hajja suka gaisa sosai Hajja tayi mamakin girman baby zahra yarinyar tayi wayo sosai sai kace wata 'yar wata biyar.
Hajja ta ke'be da Wasila tace"Dama inata so inzo gidan naku Allah be nufa ba to tinda Allah ya kawoki sai ki tafi da ajiyar da nayi miki."
Wani garin magani ne a cikin wani madaidaicin bokiti tace"Kullum ki dinga sha da madara ko nono daga can sakwatto nasa aka hada miki, ita kuma wannan zuma ce kada kiyi wasa da ita kullum kina shan murfi biyu safe da dare, idan kikaji dad'insu nasan da kanki idan sun kare zaki bukaci ayi miki wani." Wasila ta sunkuyar da kanta kunyar Hajja takeji sosai godiya tayi mata cike da kunya tana kara jin kaunar matar a cikin ranta.
Hajja har mota ta rakosu tana fad'in "Su gaishe da mahaifiyar tasu insha Allah ranar daurin aure tare da ita za'azo."........Garba ne ke driving Rashida na kusa dashi da baby a hannunta....Ita dashi kuma suna bayan mota sai kalamai take mishi wai ya kwantar da hankalinsa insha Allahu sati guda kamar yau ce."
Ya kalleta sosai yace."Ni nace miki sati guda zakiyi."? Ta kalleshi tana marairace fuska a langwabe tace"Hakafa kace dani shekaran jiya."
Yace."Takura min kikayi shiyasa na fada miki haka, yau laraba ko."? Ta daga kanta tana kokarin mai da hawaye, yace."Zan iya daurewa kuyi kwana biyu shima dan dai babu yanda zanyi ne! Ranar juma'a idan na shigo daurin aure sai mu tafi."
Murya na rawa tace"To baza muje pataskum din ba." Yace."Wane pataskum kuma Itama Momyn ai nan za'a kawo ta sai ku had'u kawai ku gaisa."
Tace."Ai sai dare za'a kawota kuma lokacin nasan mun tafi." Yace."Ni zanyi magana da Malam d'in kancewa ana daura aure a tura mota a daukota ke Ni da kaina ma zan tura Garba ya daukota da sauran 'yan uwa sai ku gaisa da juna.'
Shuru tayi masa domun ta fahimci duk dubarar da zatayi masa ba zai amince ba.
Haka suka isa Garko kowa na jin damuwa cikin ranshi mussaman shi Uban gayyar da yake fargarbar dare yay yasan kuma shi da bacci sai dai yaga anayi.
Amadu kafin ya tafi babu inda bai je sun gaisa ba cikin dangin Wasila yau kowa yaga mijin da take aure suka zama abun kallo a garin ba'yan uwansu kadai ba harda jama'ar gari fitowa suke suna kallonsu mussaman da wani matashin saurayi dake shiga kano sarin kaya ya gane fuskarshi sosai ya dinga watsawa mutane ai shine *Amadu Musa Ba.Iya.ka d'an takarar governor Kano* Aikuwa Jama'ar garin Garko tamkar an musu albishiri da gidan aljanna! suka fito kwantsinsu da kwarkwartasu suna ihu da fad'in "Allah ya baka mulki jahar kano fari mai farar anyi maliya mai ruwan 'kare kukanka." Ganin yanda Jama'a suka nuna masa 'kauna sukayi dafifi a jikin motarsa ya sanya ya koma cikin motar tashi ya bude wata ma'ajiya da yake aje kudi ya daukosu dami guda, ya wakilta mutane biyar yace."kowa a bashi abinda ya samu." Aikwa Jama'a sukayi layi suna ihu da 'kara yi masa kirari.....Wannan damar da ya samu ce ya sanya ya Umarci Garba da yayi maza maza yaja motar su bar gurin dan idan ba haka ba jama'a baza su bari ya tafi ba.
Su Wasila na cikin gidan Malam mata dam'kam tamkar suyi mata sujjada ita abun ma mamaki yake bata sai wani bata girma ake kowa so yake yayi tozali da ita, wato tun mijin nata bai zama governor ba har sun soma kiranta da matar governor dariya kawai take musu itama ta fito da kudi daga jakarta ta shiga raba musu......Deluwa sarkin kanzagi tace"Hajiya Wasila ina fatan idan kun samu mulki a Hannuku baza ki manta da Kauyen Garko ba domin dai nan ne tushenki asalinki Karamar hukumar garko na bukatar hanyoyi masu kyau, na bukatar wuta da ruwa da kuma makarantu gami da asibitoci sannan muna bukatar tallafi domin mu inganta harkokin noma da sauransu."
Wasila dukanin abinda Deluwa ta fad'a sai da ta rubuta a wayarta tace"Insha Allahu duk su kwantar da hankalinsu idan mijinta ya samu mulki a hannunsu Wannan karamar hukuma zata zama city za'a gyara sosai yanda kowa zaiyi sha'awarta.
Sai bayan magariba suka samu sassaucin mutane a gidan, Bitan ta shigo dakin bayanta goye da zahra tace"Oh! ai shikkenan kuma gidan nan zai zama sansani na jama'a duba dai mutane sun kasa bari ki huta abincin ma sun hana kici cikin nutsuwa."
Wasila tayi dariya tace"Bitan ai haka siyasa take dama zakiga mutum kwata kwata baida nutsuwa daga zarar na bar garin inace shikkenan kuma." Bitan tace"Aikuwa dai kuna kokari wallahi ga baiwar Allah nan itama an shiga hakkinta." Tafada tana kokarin kwance zahra daga bayanta.
Tace"Ki bata nono tasha Rashida zata shigo muku da abinci."Yarinyar na ganin mamanta ta soma cilla kafafu tana b'angala dariya.
Bitan tace"Ji ja'aira wai ta san uwarta."
Wasila na dariya tace"Bitan wannan yarinyar wayo ne da ita ai."
Bitan tay dariya tana kokarin fita daga dakin tace"Ai yaran yanzu dama da wayonsu ake haifarsu.
Tana fita Inna Hajara ta shigo gidan tare da dan autanta da yake dauke da kwanukan abinci."
Bitan tace"Yanzu Hajara sai da kika yi girki bayan komarwar ki gida."
Hajara tace"Murhu biyu nayi shiyasa nayi sauri."
Bitan tace"A gaskiya dai mana." Kicin ta nufa ita kuma Inna Hajara ta shige masaukin su Wasila.
Wasila tace"Inna Hajara sannu bakya gajiya da zurga zurga koda yake babu nisa sosai ai.....Hajara ta zauna tana fad'in"Ke ni zurga zurgar da nakeyi kullum ai koda kudi aka hadaki ba zaki iya ba." Wasila tayi dariya tace"Ai kam wallahi bazan iya ba, tace"Inna hajara shine tun bayan tafiyarki baki sake zuwa ba ko."
Inna hajara tace"Ke rabani da zuwa wannan gidan da ba'a bukatata a ciki."
Wasila kamar tayi dariya sai dai ta daure tace"Haba Inna waye baya bukatarki." Tace"Rufe min baki kina so ki kare mijinki ko? bayan kin san shine ya koreni daga gidansa to me zai kaini ni ba kwad'ayayya bace."
Wasila tasa dariya tace"Haba Inna yaushe zai koreki a gidansa Wallahi bakiji yanda yaji rashin dadi ba da ya dawo yaga bakya nan yayi ta fada wai nice nayi miki laifi shiyasa kika tafi."
Tace"Oho! dai ni duk abinda nakeyi dominsa nakeyi da har zai dinga jin haushina dan nace ki gyara kanki ai shine zai mora shiyasa ai koda ki kayi ar'bain banyi gigin zuwa ba dan nasan dole zaki zo da kafafunki, in yaso sai nayi miki abinda nayi niyya ba don halinsa ba kome za'ayi ai shi za'ayi wa amma saboda tsabar rashin hakuri irin nasa yake ganin aibun mutune."
Wasila tace"Dan Allah Inna kiyi hakuri magana ta wuce Yace a baki hakuri." Ta'be baki tayi tace."Uhmm! ni dama ai ba bakuwar zafi bace, Wannan kwanon da kike gani roman 'yan shilla ne mai had'e da maganin gyaran matantaka da kuma ni'ima ki cinye tas ki shanye roman duk wani abu da kika rasa gurin haihuwa idan kinsha wannan roman zai maye gurbinsa.
Wasila tace"To shikkenan Innata nagode sosai babu shakka duk wanda ya rasa iyaye a duniya dole yayi kuka." murya na rawa ta 'kare maganar.
Inna hajara tace"To meye abin kuka kuma mu dai kullum fatanmu ki zauna dakin mijinki lafiya kiyi masa biyyaya domin ki samu rabauta duniya da lahira, itama Rashida addua muke kan Allah ya kawo mata miji nagari kamar naki."
Wasila tace"Ameen Inna insha Allah Rashida zatayi aure komai nada lokaci dama.
Tace"Inna gaskiya bazan boye miki ba naji dadi sosai da faruwar wannan abu Kawuna Malam zai auri Uwani wallahi ji nake tamkar babu wanda ya kaini farin ciki da faruwar al'amarin.
Inna Hajara tace" Shi al'amarin Ubangiji dama haka yake ai Allah ya kaddara akwai aure tsakanin Mahaifiyarki da Malam babu abunda zamuce sai dai muyi fatan alkairi shi kuma Yahuzu Allah ya jikansa ya gafarta masa."
Tana goge hawaye ta karashe maganar, itama Wasila taji zuciyarta na kokarin karyewa tuno mahaifinta da tayi sai dai kawai ta daure ta cigaba da yi masa adduar samun rahamar Allah a cikin zuciyarta.
Inna Hajara bata bar gidan Malam ba sai da ta tabbatar da Wasila ta shanye roman 'yan shillan nan sannan tayiwa Bitan Sallama ta tafi gidanta.
Koda malam ma ya dawo suka ke'be suna sake gaisawa da tambayar bayan rabuwa Wasila tace"Malam ji nake kamar nafi kowa murna da farin cikin da kasantuwar wannan abu kai da Uwani Allah Ubangiji ya sanya alkairi a ciki."
Mai allo ya dinga amsa cike da walwala da farin ciki, Yace."Hakan shine suttura da kuma mutumcin mahaifiyar taku."
****
Sai bayan goma da rabi ya shiga gida a gajiye sosai dan bayan sun bar garin Garko can 'karamar hukumar *Gaya* suka Wuce shi da Khalifa da jama'arsu, sai yamma lis suka dawo saboda yasan masu gidan basa nan yasa ya yada zango guest house dinshi Khalifa ya zauna yana d'eba masa kewa Sai da Hafsa taga dare yayi mijinta bai dawo ba ta kirashi a waya, sannan ne suka rabu kowanne ya tafi gidanshi
Yana sane ya'ki kiranta a waya sabida yana so yaga shin zata manta dashi ko a'a bini bini zai duba wayarshi babu text dinta babu kiran wayarta gashi sha biyu na dare har ta wuce........Allah sarki Wasila tana can network ya sakata a gaba tun bayan tafiyar Inna Hajara take ta kiran numbarshi tana 'kin shiga ko kuma data fara ringing sai ta katse har kuka tayi saboda bakin ciki kowa na kwance a daki cikin dare ta fito tsakar gida wai ko dakin ne babu network nan ma tayi tayi kiran baya tafiya, sai ta koma daki ta kwanta lamo tamkar mara lafiya bini bini ta duba wayarta ko zataga test dinshi shuru duk ta rasa abinda ke mata dadi da kyar bacci ya dauketa.
To shima nashi 'bangaran hakane, da kyar bacci ya daukeshi wanda tun yana saka ran ganin test dinta ya cire ya rungume filo kamar wani maraya yana fizgo bacci da karfi, gabadaya gani yay dare yayi mishi tsayi, dan haka uku da rabi nayi ya tashi yaje ya dauro alwala ya hau dadduma yay nafila, kafin ta dauki cazbaha ya wuce masallaci.
Da safe da kyar ta karya duk takaici ya isheta, ga mutane sai shigowa sukeyi wai sunzo gaisheta sai kawai ta koma daki ta kwanta tace da Rashida duk wanda yazo tace musu bacci takeyi.
Haka kuwa Rashida ta dinga sallamarsu, da cewar bacci take wasu masu naci zama sukeyi wai sai ta tashi sun gaisa da ita Wasu kuwa sai suce bari su tafi sa dawo da yamma.
Wasila na ciki tana ta famar kiran wayar tashi wannan karon tana shiga sai dai kuma bai daga ba, nan ma zuciyarta ta sake hasala ta goge hawaye tana mikewa zaune......Sake kiran wayar tayi a karo mara adadi dai-dai lokacin da ya fito daga toilet da alama wanka yay dan ga jikinsa nan duk ruwa, da sauri ya karasa inda wayar take ya dauka, ajiyar zuciya ya sauke ya zauna gefan bed kana ya daga wayar.
Kuka ta fashe dashi harda shashsheka, yaji duk jikinsa yay sanyi gabakidaya a rayuwarsa ya tsani yaji tana kuka....
A tausashe yace."Menene."? Tace"Me yasa ka ki daukar waya zuciyata kamar zata fashe."
Ya sauke ajiyar zuciya yana furzar da wani huci daga bakinsa, yace."Sai kuma kiyi kuka babu sallama da gaisuwa da tambayar yaya na kwana."?
Tace."Duk hankalina ne a tashe wallahi zuciyata sai sa'ke sa'ke take min."
Yace."Ina Mommyna." A hankali tace"Tana can gurin Bitan."
Yace."Kun tafi kun barni da damuwa ko."? Tace."Wallahi nima da kyar nayi bacci ban san haka nake sonka ba sai da na kasa samunka a waya ji nake kamar nayi tsuntsuwa nazo inda kake."
Yaji wani irin dadi na ziyartasa, yace."Nima haka naji na kuma gane kece mahad'in rayuwata." Dariya tayi tace"Nagode mijina, yanzu kayi break fast ko."
Yace."Nakasa komai tunda na tashi kinga ni da kyar ma nayi wanka." Tace."Wayyo babyna da ina nan Wallahi ni zanyi maka wanka in rungumeka in shafa maka mai in saka maka kaya."
Yayi wani killer smile kafin yace."Tunda ni baby ne idan kinyi min wanka kin shafa min mai kuma kin sa min kaya sai ki bani nono nasha ko."
Ta saki dariya da shashsheka tace"Allah da ina kusa zan baka kasha."
Yaji tsigar jikinsa ta tashi Yace."Mu bar wannan maganar kada kisa nazo inda kike yanzu."
Ta 'kyal'kyale masa da dariya tace"Ai dama kaina ka fara maganar." Yace."Tom na daina maganar." ya cigaba da cewa yau zan tafi katsina amma kuma komai dare zan dawo insha Allah." Tace"Wayyo Habibi Katsina me zakaje kayi."? Yace."Zanje Gurin abokina mana mutumin da yazo dubaki lokutan da baki da lafiya."
Jiki a sanyaye tace"To Allah ya tsare min kai ya dawo da kai lafiya." Ya amsa da "ameen." Yace."Kinga yanzu na dan samu sassauci zan iya cin abinci sabida kin bani kulawa duk da bakya gabana naji dadi sosai Allah yay miki albarka."
A nutse tace"Ameen." Bari na bari ka nutsu kayi break sai na sake kiranka ko."
Yace."Okey my Princess! Murmushi tayi ta kashe wayar tana fad'in "Nazama gimbiya kenan.....Cike da nishadi ta fito tsakar gidan gidan malam ta cigaba da hada hada da jama'a masu shigowa.
Gangami!! da turnu'kun!! haya'ki!!! nake hangowa kan titin zuwa gidan gomnati wato government house, mutane sunfi dari biyu sun kashe titi sai 'kone -'kone sukeyi suna tada 'kura gami da 'kona tayoyi suna watsa fetur suna 'kyasta ashana, sai ihu sukeyi suna buga ganguna, guri ya hargitse da hayaniya gami da haya'kin! wuta, dan wasu ma har sun soma galabaita duk da sune suka saka kansu abunda sukeyi din basu sare ba so sukeyi su shiga cikin government house din domin su cimma manufarsu kan mai girma governor Lawan Rabo, mafi akasarin jama'ar da suka tada wannan tarzomar iri-iren wad'anda aka rusawa gidaje ne da masana'antu gurun aikin titin jirgin 'kasa wanda ko rabin aikin ba'ayi ba an dakata gashi su kuma anyi musu al'kawari za'a biya su diya shuru kakeji malam yaci shirwa kullum 'karya daban ta gobe daban sam basa gajiya da shiga gidan redio suyi karya, sukuwa suka ga rainin hankalin yay yawa kawai suka yanke wannan hukuncin duk da sun san wannan abun da sukeyi din xai iya barazana ga rayuwar wasu daga cikin amma dai duk da haka sukaji suka gani domin suna so su kwaci hakkinsu da'aka danne musu,
Mai girma governor Lawan Rabo hankalinsa yay masifar tashi sosai ya lura Jama'ar Jahar kano suna so su ga karshen sa dan duk abinda ke faruwa a kan titin yana gani ta cikin CCTV Dan haka sai kawai ya umarci Securities kan suje suyi aman wuta da alburusai a gurun wanda kwanansa ya 'kare shi ya jawo kansa.
Ba tare da 'bata lokaci ba kuwa, Police din gidan gomnatin suka shiga motocinsu suka durfafi kan titin suna sakin harbi ko ta ina!
Littafin na kudi ne.....!
Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah! Whasap numbar
07084653262
*BINTA UMAR ABBALE*alliya:
*'YAR BANGAR SIYASA!!*
*END🔚*
*ALHAMDULILLAHI*
*85*
Gurin ne ya sake hargitsewa da hayaniya dalilin zuwan Securities din, kafin kice kwabo jama'ar da sukayi dafifi a kan titin sun soma gudu saboda gabakidaya harbin bindigar da Police din keyi yayi masifar razanasu, sai kowa ya soma kokarin ceton ransa, amma dai duk da haka sai da harbin ya samu wasu daga cikinsu suna kwance a gurin suna ihu jini tamkar yay magana kan titin yayi kaca kaca sai hayaki ne yake tashi a gurin gashi gari ya soma duhu magariba ta gabato.....Governor na ganin abinda ke faruwa ya kira d'aya daga cikin mutanan da ya tura yace."Maza a kwashi wa'inda suka jikkata akai su asibiti, Allah sarki mutum kusan bakwai sun mutu 'yan uwansu sai kuka suke suna d'ora hannu aka hade da tsinewa Lawan Rabo albarka suna tur da wannan mulki nashi....Amadu na katsina tare da Abokinshi Alh Muktari labari ya samesu dan sai da suka ga abinda ke faruwa a labarai, hankali a tashe sukayi sallama da abokinshi ya dauko hanyar dawowa gida.....Koda ya iso bai nufi gida ba kai tsaye gidan redio na *Salama* ya umarci Garba ya saukeshi, abinda bai ta'ba faruwa ba kenan wai ya shiga gidan redio dan ya yad'a manufarshi,
Tashar redion Salama taji dad'i sosai da zuwanshi, kafin kice me sun fara sanarwa yanzu yanzu d'an takarar governor kano mai girma *Amadu Musa* zaiyi magana dangane da abubuwan dake faruwa a wannan jahar.
Jama'a duk suka maida hankalinsu gurin sauraran jawabinsa.....Ya fara da bisimillah had'e da addua kamar yanda annabi ya koya mana kana yace."
*Hak'ika banji dad'in wannan abunda ya faru ba a yau! hankalina ya tashi matuka! ganin yanda jama'a suka jikkata wasu har suka rasa ransu, Duk abinda wannan gomnati tayi muku bai kamata ku dauki irin wannan mataki ba, don yin hakan ba zai amfanar daku komai ba sai 'bacin rai gami da nadama da dana sani, na tabbata yau wasu daga cikinku suna nan cikin bakin ciki da damuwa rashin Iyaye da 'yan uwa mata na gida suna kuka saboda wannan tashin hankalin Wata mijinta ya mutu wata mijinta ya 'kone ko ya karya, duk saboda wannan hatsaniyar data afku, wannan abun da jama'ar wannan jaha sukayi bai dace ba shi wanda kukeyi dominsa din baza ku ganshi ba ballanta ku cimma burinku akansa, duk abinda hakuri bai baku ba rashin sa ba zai baku ba, kuyi hakuri ku barshi da Allah bisa ga zalintarku da yayi sannan kuma cigaba da yi mana addua kan Allah ya cika mana burinmu a cikin wannan tafiya, mutukar Ubangiji Allah ya dam'ka min mulki wannan jahar zan share muku hawaye zakuyi mamaki sannan dukanin wanda yay asarar gidanshi ko masana'antar sa wannan gomnatin insha Allahu Ni Amadu! na kar'bi wannan mulki nayi muku alkawarin biyanku hakkinku, wannan titin kuma da suka d'auko gadan! gadan! sunayi ni dama nasan ba iyawa zasuyi ba ku zuba musu ido, mu idan muzo namu salon daban yake da nasu, babu wani abu nasu da suka bari wanda zamu d'ora aikinmu akai komai sabo zamu 'kir'kira! babu algus babu almundahana a ciki, zamuyi mulki bisa amana da tsoron Allah Insha Allah! Daga karshe nake muku fatan alkairi al'ummar wannan jaha mai albarka ku cigaba da addua kan Allah ya kawo mana sauyi mafi alkairi sannan kuma na umarce ku da kada ku kara tada wata tarzoma, saboda yin hakan bashi ne mafita ba, mafita shine ku bamu had'in kai aranar za'be! kowa ya fito ya za'bi Jam'iyyar mu mai albarka tun daga sama har 'kasa, ku za'bi Jam'iyyar CPC Sa'a! Wasalamu alaikum."*
Amadu na gama Jawabinsa gari ya dauka anata hayaniya kowa na fadar albarkacin bakinsa, haka can ma gidan gomnatin Governor Lawan Rabo da mataimakinsa da kuma mabiya bayansu hankalinsu yay bala'in tashi, governor Lawan Rabo ya dinga da ya sanin hukuncin da ya yanke na tura securities da yayi suka dinga harbi, yasan har duniya ta nad'e jama'a ba zasu ta'ba mantawa da zamaninsa, ba, aikuwa yana jikin wannan jimamin kiran mai girma shugaban 'kasa ya sameshi, lallai yau yake so ya nufi Abuja domin yana so ya zauna dashi.
Lawan Rabo ya shiga rudani mutuka yayin da mataimakinsa yayi nasa guri dama shi d'an ba ruwa na ne tunda duk shawarar da zai bashi baya dauka yanzu data kwa'be masa sai y
aje yaji da matsalarsa.
As da sauran jama'arsa ne suka rakashi can fadar shugaban 'kasar.
Duk da suna cikin karkara sai da labari ya samesu, dan Wasila har jawabin mijinta sai data saurara, hankalinta a tashe ta dinga kiran wayarshi domin taji lafiyarsa, wayar bata shiga da alama dai gidan Malam bai da network me kyau.
Sai misalin goma shaura na dare ya shiga gidanshi, yay wanka ya fito palo wanda yay dai-dai da shigowar Khalifa suka zauna suna sake tattauna maganar.........A dai-dai lokacin ta sake gwada kiransa a waya a kaci sa'a wayar ta shiga, zazzafar ajiyar zuciya ta sauke tace"Habibi sannu da hanya ina fatan ka dawo lafiya."
Yace."Na dawo lafiya lou har yanzu ban samu sukunin kiran wayarki ba."
Tace."Nima tun dazu nake ta neman wayarka network yana hanawa, na saurari Jawabinka dazu kano babu lafiya ashe." Yace."Eh gashinan jama'a nata fama wai sai sun halaka governorn ku Lawan Rabo."
Tace"Dan Allah daina cewa governor mu wallahi na tsaneshi mugu ne." Yace."A haba dai yanzu kin fita daga jam'iyyarsu kenan."? Kamar zatayi kuka tace"Ka bari bana so dan Allah."
Ya dan shafa saisayayyar sumarshi yace."To na bari ina Mommyna." Tace"Tana goye a bayan Bitan." Yace."Wai ita wannan Bitan din bata gajiya da hidima ne."?
Murmushi tayi tace."Mutuniyar kirki kenan." Yace."Ina kaunar matar sosai saboda tana kaunarki gashi yanzu tana gwadawa kan Mommyna." Mirmushi kawai tayi, yace."Kin san wani abu."? Girgiza kanta tayi tana lumshe ido yace."Gabad'ayansu Malam Kawu Habibu Inna Hajara Momynmu da ita Bitan! Dukaninsu zasuje Umara insha Allah sati biyu masu yawa." Wani irin farin ciki ne ya lullubeta kamar tayi masa ihu a wayar sai dai ta daure ta dinga zabga masa godiya da addua muryarta sai rawa takeyi......Yace."Babu komai ai dangina nayiwa meye abin godiya." Tace"Eh duk da haka nagode." Yace."Idan sun dawo zamuje namu umarar." Tace"Tom shikkenan yanzu kuwa zanje na fadawa Kawu wannan albishir din." Murmushi yay yace."Sai Allah ya kaimu gobe ko."? Tace"Tom Allah ya kawo ku lafiya."
Kashe wayar yay yana murmushi, suka hada ido da Khalifa dake zaune ya zuba masa ido, hummm! Wai Amadu ne ke hirar soyayya wanda da idan ance zaiyi sai yace shi bashi da lokacin yin haka.
Murmushi yay yace."Dama kana nan a zaune."? Khalifa ya murmushin takaici yana jan 'karamin tsaki yace."Ai baza ka gane ina gurin ko bana gurin ba tunda idanunka sun rufe."
Ya dan shafa kanshi As'usel da murmushi a fuskarsa yace."Khalifa ina son yarinyar nan wallahi." Khalifa ya mike yana fad'in "Ai ba sai ka fada ba duk ga alamu nan sun nuna." Mikewa yay ya bashi hannu suka tafa suna dariya a tare suka fita daga palon.
Wasila ta sanar da Malam alherin da Amadu yay musu, malam ya shiga tsananin farin ciki mara misaltuwa ya aika aka kira masa Kawu Habibu shima ya dawo gida saboda daurin auran ya tarasu ya shaida musu abinda ke faruwa, Inna Hajara ta dinga rangwada 'buda a gidan tana fad'in "Haihuwa mai rana Yau ni Hajara nice zanje wannan guri sai ta fashe da kuka tana fyatar hanci tace" Allah ya ji'kanka dan uwana insha Allahu kana aljannar furdausi, Bitan tace ta dinga rarrashinta da ta daina kuka domin yin hakan zai sanya su Wasilan hankalinsu ya tashi, da kyar Inna Hajara tayi shiru ta kama Wasila ta rungume a jikinta tana mata addua gami da hud'uba kan zamantakewar aure.
****
Alhamdullhi an d'aura auran Uwani da malam a gidan Kawunta dake Tudun maliki, bayan daurin aurane sai suka kuma nufi can pataskum din domin gaisuwa sannan kuma da dauko amarya, malam sai washe baki yake yana baza babbar riga Shi kuwa Amadu kunya ce take kamashi wai daurin auran Uwar matarshi ake sai dai kawai ya girgiza kansa yana murmushi.
Uwani tayi ado dai-dai gwargwado kuruciyarta ta sake fitowa tamkar bata haifi Wasila ba wani cewa zaiyi yayarsu ce anyi mata kitso da jan lalle tana sanye da sabuwar atamfa 'yar ingila jama'a sun cika gidan Kawu Madu sai hidima ake Kuluwa sai washe baki takeyi tana karbar baki, Kuluwa yanzu ta dan rage kazanta dan Kawu Madu ya soma dawowa hayyacinsa asirin da tayi masa ya karye dan da ya farga da irin kazantar da takeyi yace."Wallahi ta kuka da
kanta idan ya tashi aure zai aure mace mai tsabta 'yar gayu tunda shi ba kazami bane."
Aikuwa Kuluwa ta tsorata sai ta dage da wanka da wani had'e da kitso akai akai kuma garin Allah yana wayewa zata sa brush ta wanke bakinta tun yana futar da jini har ya daina, amma duk da wannan abun da takeyi Kawu Madu bai saduda ba yana nan da bazawarsa 'yar 'kwalisa har sun tsayar da ranar daurin auransu, Kuluwan bata sani ba sai dai jama'a da yawa sun sani shuru kawai akayi mata ana jiran ranar da amarya zata zo aga me zai faru.
Amadu kasa shiga gidan yay sai ya zauna cikin motar.....Kunyar hada ido yake da mahaifiyar matar tashi, to itama Uwanin tunda taji jama'a nata surutu da amabatar sunan mijin 'yar tata sai ta kasa fitowa tsakar gida ta zauna cikin daki abinta
Kawu Madu da kansa ya fita har bakin motar da yake ciki suka gaisa cikin mutuncin da karamci sannan fa mutane suka farga dashi sai suka dinga zuwa daya bayan daya suna gaisawa, ganin hakan kamar bai dace ba yasa ya fito daga motar yana gaisawa da jama'a cikin sakin fuska da dattako.
Karfe shida sun iso gidan......Lokacin Rashida da Wasila sun saka turare mai kamshi a dakin mahaifiyar tasu wanda ya sha jere mai kyau kuma na zamani, katon gado ne da katifa mai kyau sai katuwar sif mai murfi shida akwatinanta akai sai mudubi da drowars guda biyu koran kafet ne malale a dakin labule koraye da net dinsu, dakin yayi kyau sosai.
Su Kuluwa da Ina Tabawa da Ita mai waina suka rako Uwani dakinta Bitan ta karbesu hannu bibbiyu aka gaisa cikin mutunci da mutuntawa............Wasila bata samu sun ke'be da mahaifiyarta ba ya dinga kiranta a waya ta fito su tafi saboda dare ya soma yi....Uwani tace"Ki shige ku tafi daga baya sai ki dawo ina laifi ma da ya barki kikayi kwanaki biyu, Babu yanda ta iya haka tasa yara suka dauki jakar kayanta Rashida kam fujirewa tayi wai tunda babu makaranta ba zata bisu ba sai jarrabawarsu ta fito, Uwani kam bata ce mata komai ba itama zata fiso ta zauna a gabanta.....Wasila ta fito tana sallama da jama'ar dake gidan duk zuciyarta babu dad'i Inna hajara tasa yara suka fitar mata da kayayyakinta wajan motar......Ita Kuluwa fad'i take "Kice ina gaisheshi." Wasila ko kallonta batayi ba ta fice daga gidan, sukayi karo da malam zai shigo sai ta zube a kas tana kuka, Yace."meyasa kike kuka Wasila. Tace"Wallahi Kawu bana so na tafiya yau." Yace."Kiyi hakuri kibi umarin mijinki Allah yay miki albarka." Ta amsa da amin tana mikewa, Yace."Ina Rashidar."? Tace"Wai anan zata zauna sai sanda jarrabawarmu ta fito." Malam yace."Zancan banza zancen hofi! jirani anan na fito da ita."Ya shiga gidan yana baza babbar rigarsa, Rashida na dakin Uwani malam ya shiga gidan yana fadin"Ina Rashida. tace."Gani Kawu." Yace."Maza ki fito ku tafi ni bana son shashanci." Tace."Kawu Uwani ce tace."Na zauna." Sai ya daga labulen dakin yana fad'in "Uwani anya hukuncin nan yayi dai-dai kuwa."?
Ta dago kai ta kalleshi tace" Malam ai ba cewa nayi ta zauna gabadaya ba idan jarrabawarsu ta fito zata tafi."
Yace."To! to ai babu komai Allah ya kaimu." Labulan dakin ya saki Ya nufi dakin Bitan! lokacin ita kuma tana kicin tana ta kokarin raba abinci dan su Kuluwa suna nan basu tafi ba sai gobe tukkuna.
Dama tuntuni Garba ya shigar mata da kayanta cikin motar daga ita sai baby zahra da jakarta ta nufi motar, wanda yana hangota ya bude motar yana kallonta har ta 'karaso ta shiga tana kumbura fuska, baice mata komai ba ya mayar da murfin motar ya rufe, Garba ya shiga da sauri yaja motar suka dauki hanya.
Baby zahra ya kar'ba daga hannunta yana mata wasa sai kyalkyala dariya takeyi,
Yace."Momyna nayi missing dinki da yawa amma na lura ke da momynki baku damu dani ba, kunyi ki'ba kunyi lafiya kwana biyu."
Kallonsa tayi tana dan sassauta murya tace"Allah Habibi ka yanke min jin dadina ina tare da 'yan uwana kawai sai kace lallai sai mun tafi."
Yace."Akwai wani jin dadi wanda ya wuce ace kina tare dani."?
Shuru tayi masa tana gyara fuskarta, Yace."Ina Rashida."? A hankali tace"Wai ba zata dawoba sai jarrabawa ta fito." Yace."To karatun isilamiyyarmu fa." Ajiyar zuciya ta sauke tace."Ni na ma
nta ma wallahi sabida bana cikin nutsuwa kuma dai Uwani ce tace dole sai ta zauna."
Yace."To tunda Momy ce ta yanke wannan hukuncin bani da magana amma dai naso ta dawo yanzu domin mu had'a izifi talatin d'inmu da ita."
Tace."Itace ta jawowa kanta, idan ta dawo na koya mata inda aka wuceta." Yace."To malama." Shuru motar tayi na minti biyar ya dan kalleta yana kashe ido yace."Wane tanadi kikayi min." ? A hankali yay maganar saboda Garba. Fari tayi da ido tace" Kabari muje zaka gani."
Ya sauke ajiyar zuciya a hankali yana Allah Allah su sauka gida yayi masifar d'okanta da kasantuwa a tare da ita.
A daran ranar sunyi soyayya sosai wacce ta sanya su zubar da hawaye dukaninsu suka tabbatar wa da kansu cewar idan babu d'ayansu a cikin rayuwarsu to babu shakka rayuwarsu tana cikin kalubale mai girma.
Bayan dawowarta da kwana uku Hafsa ta haihu d'a namiji ta haifa A ranar data haihu sukaje ganin jinjiri Hafsa ta 'karewa Wasila tanadi sosai tace"Wallahi kinji kunya ace wai wannan zuwan da kikayi shine na farko gidana ai ina sane dake shiyasa nima bana zuwa inda kike koda yake laifin ba na kowa bane na governor ne gashinan ai yana jina.
Amadu da yaga Hafsa ta fusata tana sakin maganganu sai ya fara kokarin kare kanshi da cewar shifa ba laifinsa bane nata tunda yana cewa suzo sai tace tana da uziri.
Wasila ta dinga mamakinsa babba dashi da karya, Hafsa tace" Ai nasan kafad'a ne domun ka wanke kanka dama ina ciki da kai kaine ke hanata zuwa inda nake nagode.
Sai ya shiga bata hakuri Wasilan na tayashi da kyar Hafsa ta sako ta basu jaririn suka dauka......Afnan ta samu abokinyar wasa, baby zahra ta makale jikin Wasila wai lallai sai ta bita su dinga wasa da babynta.
Amadu yace."Kome zakiyu ba zamu tafi dake ba ki hanamu kwanciyar hankali....Khalifa na dariya yace"Afnan fa tayi wayo yanzu ta daina kuka.'' Yace."Kome zaka fada kan Afnan ba zan yarda ba ai ni yarinyar ta shani na warke...........Amadu da Khalifa suka fita sabida bakin dake zuwa, Cikinsu harda Zeey da sauran 'yan gidansu, Zeey tamkar ba gidan 'yar uwarta tazo ba ta kasa sakin jikinta duk dan ganin Wasila a gidan wani irin kunyar yarinyar takeji sosai sai yanzu ta gane cewar abinda tayi itama bata kyauta ba.
Ana ya gobe suna wata 'kawar Hafsa tazo musu da lafiyayyan garin magani mai suna 'kare kukanka maganin na wahalar samu itama yayarta ce take can Ghana acan suke hadashi, maganin na kyau sosai sai dai tsada amma amfani daya zakayi dashi ka gane amfaninsa a jikinka, Wasila bata ji nauyin kud'insa ba ta dauki roba biyu dubu dari uku kenan duk roba daya dubu dari da hamsin....Tace zata bawa Hafsa kudin insha Allah.
Ita yanzu mutukar magani ta tabbatar da kyansa da ingancinsa ko nawa ne zata iya sawa ta siya domin ta gyara kanta da mijinta.
Saboda yawan 'Korafin da Matan Kawunsa Almu keyi masa na rashin zuwan Wasila gidansu ya sanya ya dauketa ya kaita gidan ta wuni tare dasu, sosai Wasila ta yaba da mutuncinsu gami da karamcinsu sun karbeta hannu biyu sun dauki Zahra sun rike wannan ya dauka wannan ya ajiye kamar zasu cinyeta wannan kadai ya sanya taji tana masifar kaunar su, basu tafi ba har sai da Kawu Almun ya dawo daga kasuwa suka gaisa ya dinga sa musu albarka gami da adduar samun zuria mai albarka, a gurguje sukaje gidan Hajja itama suka gaisheta, sai bayan goma na dare sannan
suka koma gida.
********
*BAYAN SHEKARU HUDU*
Abubuwa da yawa sun faru a cikin wad'annan shekarun da suka gabata masu dadi da marasa dad'i to masu dad'in dai sunfi yawa Inda Wasila da Rashida suka sauke al'kur'ani mai girma da sauran litattafan addini kana kuma suka samu gurbin karatu a jami'ar bayaro university Wasila na karantar harkokin kasuwanci wato business administration ita kuma Rashida tana so ta zama malam asibiti ne Wasila mijinta ne ya za'ba mata abinda yake so sai tabi ra'ayinsa domin a zauna lafiya, cikin shekara biyu da ta gabanta *Amadu Musa* Ya kar'bi mulki jahar kano daga hannun Lawan Rabo ya cigaba da tafiyar da mulki kan tsari babu cuta babu cutarwa yanzu al'ummar jahar kano hankalinsu ya kwanta basu da da wata fargaba tunda komai na rayuwa yay sauki! !!!!
a jahar duk wani al'kawari da Amadu ya dauka ya sauke musu tare da taimakon mataimakin shi Sunusi Alhasan *Khalifa* Su Wasila ana gidan gomnati ana cin duniya sosai tayi wani uban kyau! da k'iba da kwarjini ta zama babbar mace, shekarun Zahra biyar, Wasila ta soma sha'awar haihuwa sai dai ta riga ta sanya inplan duk saboda karatunta wanda takeyin basaja, gurin shiga makarantar duk da ko bata rufe fuskarta da niqab ba babu wanda zaice ita matar governor ne sai dai kawai idan an duba yanayin fatar jikinta da hutu da kuma irin manya manyan motocin da ake kawota makarantar dan wataran ma harda securities suke tafiya, idan taga jama'a naso su fahimci wani abun sai kawai ta hana securities din binsu, tasa Rashida tajasu a mota.
Senator Nura mai wakiltar kano ta tsakiya shine ya kwallafa ransa kan Rashida wanda tun tana janyewa har dai ta amince masa saboda ta lura da mutumin yana da kirki da mutunci kuma yana sonta tsakani da Allah, yanzu haka saura watanni Biyu daurin auransu.
*****
Camas! Kuka wiwi takeyi gami da nadamar abinda ta shuka yanzu neman Wasila take ruwa a jallo ta nemi yafiyarta bata san yanzu ganin Wasila ma wani gagarimin aikine babba, kusan kullum sai taje government house din securities suka koreta dan babu wanda yake mata kallon mai hankali tana yawo da yaggagun kaya shaye shayen da ta dinga yi ya mai da ita shudu shudu! Ga mahaifinta ya dade da rasuwa, sai mahaifiyarta suke zaune a gida duniya gabakid'aya ta juya mata baya duk wanda suka buga harkar siyasa sun watse As da su Alhaji Ma'aruf suma takansu suke dan Amadu ya kama governor Lawan Rabo ya gar'kame! suma sai da yasa hukumar Efcc ta tuhumesu, duk wani satar kudi da sukayi da kadarorin da suka siya sai da suka fadi inda suke Amadu duk ya kwace komai yace kudi na talakawa ne......Dukaninsu da gidan da suke ciki suka dogara shima kawai ya bar musu ne albarkacin aure da Haihuwa.
****
*BAYAN SHEKARU BIYU*
Wasila ta kammala karatunta cikin nasarori da samun cigaba, a rayuwa yanzu Wasila tana da ilimin da zata iya gogayya da duk wani jinsin mutum ba'kar fata ko farar fata, tana jin turanci sosai dan watarana ma idan ba tayi ra'ayin yin hausawa ba da turanci take magana, a cikin shekaru biyun da suka gabata, akayi bikin auran Rashida ta tare a gidanta, Uwani kuma ta haifi tagwaye duk maza tare da malam mai allo, hakanan Hafsa ma ta sake haihuwa inda ya kasance tazararsu da kishiyarta Aysha babu yawa, dan tun bayan samun gomnatinsu Khalifa ya kara aure yanzu haka Khalifa nada yara hud'u inda Amadu keda 'Daya........Ganin ana barinsa a baya sai ya tashi hankalinsa, yace."Tunda an gama karatun aje a cire inplan d'in.
To itama dama a dame take haihuwar take muradi, Rashida ce ta cire mata aikuwa aranar da aka cire yini tayi tana zubar da jini ga jikinta yay tayi mata ciwo, sai da ta kwanta jinyya na kwana biyu sannan ta dawo hayyancinta, Jini na daukewa Yallabai ya bud'e Wuta, kullum in bai fita ba yana aikin abu guda, Itama gwanar da yake kullum cikin gyara take bata damuwa, Cikin ikon Allah kuwa ciki ya bayyana a jikinta, sosai sukayi farin ciki ita dashi, ba tare da 'bata lokaci ba ya shirya musu tafiya zuwa 'kasa mai tsarki domin suje sununa farin cikinsu gurin Allah Subahanahu wata'alah!!!
*ALHAMDULILLAHI*
```Jama'a nan na kawo 'karshen wannan littafi mai suna 'YAR BANGAR SIYASA! Ina ro'kon Ubangiji Allah ya yafe min zunubai na, Abinda na rubuta dai-dai Ubangiji Allah ka bani lada, abinda na rubuta na rashin dai-dai Allah ka yafe min👏🏻 Ku d'auki abinda yake da amfani ku watsar da mara amfani Nagode Jama'ata Allah ya 'kara kauna❤️ Sai mun sake saduwa daku a cikin sabon littafina mai suna```
*A KWAI WATA A 'KASA!!*